JARUMAN DUNIYA Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 A wani zamani can baya mai tsawo daya shude,lokacin da jahilci yayi katutu a zukatan bil'adama, karfi da jarumtaka suka zamo jari,rashin tausayi da adalci yayi kaura da zukatan mutane. A lokacin an yi wata nahiya a yankin ƙasashen larabawa mai suna mufrad. Nahiyar mufard tayi kaurin suna a fagen yake-yake,zalunci da sihiri, Duk sarkin daya fi dan uwansa karfin runduna ko na sihiri sai ya yake sa ya mamaye kasar sa ta dawo izuwa karkashin mulkin sa. Akwai manyan kasashe guda biyu da su kayi fice anahiyar. Ƙasa ta farko ana kiran ta da suna madinatul-husuf,sarki Baddadul-arus shi ne ke rike da kambun mulkin ta. Sarki Baddadul-arus yakasance garjejepn kato mai kirar samudawan farko yana da matukar jarumtaka dadin dadawa kuma yakasance mashahurin matsafi. Yana da wata kyakkyawar ya guda ɗaya mai su na uzaima, uzaima ta taso cikin gata da kwanciyar hankali kuma ta kasance basadaukiya mace maikamar maza. Duk lokacin da sarki Baddadhl-arus zai kai farmaki wata kasa shi da yarsa uzaima kadai suke yakar garin su yiwa sarkin JUYIN MULKI. A rayuwar sarki Baddadul-arus babu abinda yake so sama da wannan ya tashi, bisa wannan dalili ne yasanya duk inda zashi baya rabuwa da ita face kwanciyar barci. Ƙasa ta biyu kuwa ana kiranta da suna Darul-kushur,sarki Himras ne ke mulkin ta,sarki Himras ya kasance gwarzon mayaƙi mai tarwatsa maza afilin daga, ya shahara ainun a sanin ɗalasiman tsafi da tarin dukiya. Yana da ɗa guda ɗaya mai suna muzaifar, Yarima muzaifar ya kasance kyakkyawan gaske kuma gwarzon duniya, Domin shi kaɗai ya na iya baje gari guda ya ci su da yaƙi batare da wani ya taimaka mashi ba. Saboda matuƙar jarumtakar shi yasa wasu suke ganin cewa yafi mahaifinshi sarki Himras ƙarfin damtse Gaba ɗaya jama'ar birnin Darul-kushur suna matukar tsoran yarima muzaifar kasancewar shi azzalumi maras tausayi. A ƙasar Darul-kushur akwai ƙananan sarakuna guda bakwai dukkanin su suna karkashin mulkin sarki Himras, Duk shekara sarakun kan biya Himras harajin da yakai dinare miliyan takwas da dubu ɗari biyar gaba ɗaya sarakunan sarki himras ne yayi musu juyin mulki ta karfin tsiya. *** Gaba ɗaya wadannan sarakuna biyu, sarki Himras da sarki Baddadhl-arus sun kasance abokan gabar juna, A kan hakan sun gwabza yaƙi sau arba'in da biyu amma ɗayan su baya samun nasara sai dai ayi ragas! Burin dayansu shi ne ya yiwa abokin gabarsa juyin mulki ya zamana shine sarkin sarakunan nahiyar baki daya. Saboda tsananin gabar dake tsakanin sarakunan biyu, babu wanda ɗan kasar shi ya isa ya shiga ƙasar ɗayan face hukuncin kisa ya tabbata akanshi. Gimbiya uzaima da yarima muzaifar suna matuƙar gaba da juna wacce ta huce ta haifansu. Lokacin da sarakunan biyu su ka fahimci cewa bazasu iya kawar da juna da karfin runduna ba sai dukkanin su su ka nutsa cikin halarar tsafin su domin su gano hanyar da ɗayansu zai iya mallakar nahiya. A rana guda sarakunan su ka gano mafitar, sai dai mafitar nada matukar wahalar gaske. Abin da sarakunan su ka gano shine ɗayan su bazai samu nasarar kawar da abokin gabar sa ba face ya mallaki wadansu abubuwa masu wahalar gaske waɗanda nemo su dai dai yake da buɗe taskar ANNOBA DARI. Da farko dai sarakunan zasu mallaki wata salƙar tsafi dake ajiye a wani tsohon ƙabari abirnin rum, shi dai ƙabarin an gina shi ne a cikin wani ɗaki yau shekaru ɗari tara babu wanda ya taɓa shiga inda ƙabarin yake. Asalin ƙabarin na wani hatsabibin boka ne da ya yi mulki a birnin na Rum. Idan mutum ya mallaki wannan sarƙa da ita zai yi amfani wajen tashin wani boka a birnin kisra. wannan boka shi ne kadai yasan dokoki da ƙa'idojin tafiyar da sarakunan zasu yi, wannan boka ana kiran shi da suna sharubu, a yanzu haka ya shekara ɗari bakwai da mutuwa. Abu na biyu da sarakunan zasu mallaka shi ne, SIHIRTACCEN KUNDI dake ajiye a cikin wata tsohuwar rijiya a can fadar boka zammar da zamanin shu ya shuɗe a can baya. Abu na ƙarshe da sarakunan zasu mallaka ita ce wata sihirtacciyar takobi da akewa laƙabi da TAKOBI SIHIRI, Takobin tana ajiya ne a fadar sarkin bokayen duniya na uku. Baza a samu damar shiga fadar ba face an karanta waɗansu ɗalasiman tsafi dake cikin wancan SIHIRTACCEN KUNDI. Takobin tana ɗauke da wadan su sirrika guda hudu. sirri na farko shine idan mutum yana tare da ita babu wani tsafi dazai yi tasiri akan shi. Sirri na biyu shine dukkan abin da ka sara da takobin walau mutum ko aljan nan take zai zagwanye ya narke. Sirri na uku idan mutun ya mallake ta zai zamo abin tsoro a cikin yan uwanshi mutane kuma zai iya sarrafa ta yadda ya ga dama. Bokayen duniya sunyi ittifaƙin cewa a kaf sarakunan aljanu na duniya ba a taɓa yin hatsabibi kamar boka Ayyamul-layal ba, domin shi kaɗai ne ya taɓa yaƙar rabin sarakunan duniya su ka dawo ƙarƙashin mulkinshi. Bai kai ga yaƙar sauran ba rai ya yi halin shi sakamakon gwanbza yaƙi da yayi da wani jarumi ma'abocin addinin musulunci. Kafin mutum ya isa fadar boka Ayyamul- layal sai ya ketare waɗansu miyagun dazuzzuka guda tara. Har yau har gobe bokaye sun gaza gano adadin musibun dake tattare da dazuzzukan. lokacin da sarakunan biyu su kaga gagarumin aikin dake gaban su na ɗaukoTAKOBIN SIHIRI sai hankalansu ya dugunzuma ainun domin suna ganin ajali zai iya riskar su kafin su cika burin su amma da suka tuna irin gabar da ke tsakanin su sai kowanne ya yi aniyar shiga duniya mallako takobin. *** Wata rana daga cikin ranakun da yarima muzaifar kan zagayawa cikin gari domin yin nisaɗi da walwala. Yana tafe akan ingarman doki shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro, waɗansu irin samudawan dakaru masu jajayen tufafi na take mashi baya. kallo ɗaya za ka yi musu kasance cewa sun cika ZARATAN MAYAKA masu dakakkiyar zuciya, gaba ɗaya dakarun su na ɗauke da miyagun makamai masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi. Lokacin da yarima muzaifar da waɗannan dakaru su ka cigaba da tafiya a cikin babbar birnin Darul-kushur, sai ya zamana cewa duk inda jama'a suka hangosu sai kaga sun tarwatse tamkar sun ga mutuwarsu, Masu kasuwanci ba a barsu a baya ba domin tattare hajar su su ke yi suna cika wandunansu da iska saboda tashin hankali. Idan kuwa har su yarima da dakarun sa suka riska mutum bai gudu ba, Nan take dakarun zasu gabzawa mutum duka da kulaken dake hannunsu take zai faɗi ƙasa matacce ko shurawa bazai yi ba. Sai da yarima da dakarun suka shafe sa'a uku suna tafiya babu sassauci, Ana cikin wannan tafiya ne yarima muzaifar ya fahimci cewa dokinshi yana bukatar ya sha ruwa, koda gama ayyana hakan sai yarima ya hangi wata hijiya nesa kaɗan da inda suke ga jama'a nan A wajen wasu na shayar da dabbobin su wasu suna ɗauraye tufafinsu. Nan take yarima yasakarwa dokinshi linzami ya durfafi rijiyar. Ai kuwa koda mutanen dake wajen suka hango su yarima sai suka cika wandon su da iska su ka bar wajen tamkar sun hango mutuwarsu, kafin kiftawar ido babu kowa a wajen sai wata budurwa da wani tsoho tukuf ne basu gudu ba. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa yarima kai kenan kuma ya bashi mamaki, Domin tun da yake fitowa rangadi hakan bai taɓa faruwa ba. Shin wannan budurwa mai take taƙama da shi da har zata gan shi bata razana ba. Abin da yafi Ɗaure yarima muzaifar kai shi ne tufafin dake jikin budurwar sun kasance tsofaffi tukuf!, saboda tsufan su har waɗanda ke jikin tsohon sun fi nata Tsafta kuma budurwar bata tare da wani makami ajikinta da za tayi taƙama da shi. Dakarun dake bayan yarima kuwa sai zuciyar su ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone jikkunansu su ka kama tsuma, kawai umarni suke jira su afkawa budurwar. Da isowar su yarima bakin rijiyar sai kawai yaga budurwar taci gaba da ɗebe ruwa Guga tana zubawa a salkarta batare da ta waigo ta dube shi ba, sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata kone, har dakarun dake bayanshi sun yunƙura zasu afkawa budurwar sai kawai yarima ya rike linzamin dokinshi ya sauko ƙasa, ya taka da kafafunshi har izuwa inda budurwar take ya dube ta yana mai dakamata tsawa yace. "wace ce ke da bazaki girmamani kamar yadda jama'a ke girma ma ni ba? Ba tare da budurwar ta ba shi amsar tambayar ba, kawai taci gaba da ɗebe ruwan tana zuba acikin salkarta. Al,amarin daya ƙara fusata yarima muzaifar kenan bisa ganin cewa ya mace wacce ba kowa ba, tana wulaƙantashi a matsayinshi na hamshaƙin BASARAKE kuma GWARZON DUNIYA. cikin fushi yarima ya kai mata wawan naushi a gefan kuncinta na hagu da nufin bazar da ita a kasa. Cikin gwanin ta kyakkyawar budurwar ta sunkuya hannun yarima ya naushi iska. Nan take su kacame da azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa cikin matukar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, A wasu lokutan sai kaga budurwar ta daka tsalle ta raba kafafunta biyu akan rijiyar tana cigaba da kaiwa yarima muzaifar naushi da bugu cikin zafin nama naban al'ajabi. Duk wannan artabu da ake fafatawa tsakanin yarima muzaifar da kyakkyawar budurwar daga can nesa mutane sun buɗe tagoginsu suna kallon abinda ke faruwa. Koda su ka ga irin masifaffan yakin da a ke yi sai suka cika da marukar mamaki. Abin da ya basu mamakin shi ne wai ace yau yarima ne ke fafata yaƙi da ya mace. Nan take su ka raya a zuckatansu cewa an ya kuwa wannan jaruma ba gimbiya uzaima ba ce yar sarki Baddadul arus tayo badda kama domin ta yaki yarima muzaifar?. Amsar tambayoyin da su ka kasa bawa kansu kenan kawai su ka zuba idanu domin su ga abinda zai faru. Koda yarima yaga an shafe sa'a ɗaya ba tare da ya samu nasara akan budurwar ba, sai kawai ya canza salon fadanshi, inda ya dunga daka tsalle yana kaiwa budurwar naushi da bugu hannu da ƙafa. Wohoho! tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da su ka ce "idan kaga ki gudu to fa sa gudu ne bai zoba." kuma haƙiƙa idan gwani ya haɗu da gwani dola ne ƙananan jarumai su zamo yan kallo. To hakanne ya faru da dakarun birnin domin ana cikin wannan yaƙi ne su ka rugo izuwa wajen ɗauke da miyagun makamai. ko da suka ga irin baƙin artabun da ake yi sai suka koma gefe guda suka zuba idanu. Ana cikin wannan yaƙi ne wani tunani ya fadowa yarima muzaifar, Tunanin kuwa shine "wai wannan wata irin hatsabibiyar jaruma ce yau ya haɗu da ita wacce take nema ta kunya tashi a gaban jama'a, lallai fa wannan shi ne masu iya magana ke cewa "Gaba da gabanta aljani ya taka wuta". ko da gama tunanin hakan sai yarima ya yiwa dakarunshi inkiya ta wutsiyar ido dake nuni da basu umarni. Kamar dakarun jira suke sai kawai su ka ɗaga makamansu sama suna ihu da kururuwa mai firgitarwa su ka yunkura izuwa kan wannan tsoho makaho mahaifin budurwar domin su hallakashi. ko da ya rage bai fi saura taku shida su afka masa ba, kwatsam! bazato babu tsammani sai makahon ya dako wawan tsalle daga inda yake sannan ya sanya kirjinshi ya daki kirjin ɗaya daga cikin dakarun da dukkan karfinshi saboda karfin dukan sai da badakaren yayi sama tamkar an janyeshi da kugiya sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim! tamkar an jefar da bijimin sa. Ko da ganin hakan sai sauran dakarun su ka firgice bisa ganin yadda tsohon makaho yayi wannan bajinta haka lallai akwai alamar tambaya ?. kawai sai suka afkawa ma shi da azababban yaki suka shiga kai ma shi sara da suka da makamansu gami da bugu da kulakensu. Shi kuwa ya wanzu yana kare hare-haren su da sandar da yake dogarawa tare da mayar da martani cikin Matuƙar JURIYA DA BAJINTA taban al'ajabi. Da ace mutum yana wajen lokacin da ake fafata wannan yaƙi sai ya rantse yace tsohon yakasance mai idanu ba makawo ba. kallo ɗaya mutum zai yi ma shi ya fahimci cewa a lokacin da yake samartaka ya cika GWARZON DUNIYA, mai karfi na Allah ya isa koda cewar ya tsufa akwai alamun sadaukantaka a tare dashi. kaico! nanfa makahon ya zamewa dakarun alaƙaƙai kuma kadangaren bakin tulu suka rasa yadda zasu yi dashi ya wanzu yana mako su daga kan dawakansu su na yin MUGUWAR HALLAKA. Koda yarima muzaifar ya kyallara idanu, yaga halin da dakarunshk ke ciki sai zuciyarshi ta harzuƙa fiye da ko yaushe. kawai sai ya shammaci budurwar ya gabza ma ta wawan naushi afuska a lokacin data raba kafafunta biyu akan bakin rijiyar. Ai kuwa sai kafarta ta zame ta fada cikin rijiyar amma sai ta tokare da wani dutse sannan ta maidawa yarima martanin naushin a lokacin da ya daka tsalle ya dira abakin rijiyar. Nan take ƙafafun yarima su ka zame ya afka cikin rijiyar, Amma saboda gwaninta irin ta JARUMAN DUNIYA sai ya ƙi yarda ya kai ƙarshen rijiyar ya rarraba kafafunshi a tsakanin rijiyar su ka cigaba da kaiwa juna naushi da bugu a hakan cikin juriya da nacin tsiya. Tabbas yau yarima muzaifar yayi gamo da mace mai kamar maza kuma BASADAUKIYA UWAR SADAUKAI. Sai da rabin sa'a ta shuɗe su na kaiwa juna naushi da bugu, Duk sa'adda ɗayan su ya naushi ɗan uwanshi sai kaga ya gwara kan shi da jikin rijiyar kuma yayi kasa lu! zai afka rijiyar amma sai kaga ya turje ya mayar da martani. Babu abin da zai bawa mutum mamaki ga jaruman biyu face yadda su ka shafe lokaci mai tsawo su na artabu ta hanyar yiwa juna lugudan naushi amma ko kaɗan babu alamun gajiya a tare dasu. Ana cikin wannan yaƙi ne Budurwar ta shammaci yarima muzaifar ta gabza masa naushi a fuska kanshi ya gwaru da jikin rijiyar, ya tsage jini yayi tsartuwa saboda tsananin zafin da yarima ya ji bai san sa'adda ya tsandara ihu ba kafafunshi suka zame ya afka ciki. koda samun wannan gagarumar nasara sai kyakkyawar budurwar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mai kallon yarima dake kwance tsamo-tsamo acikin ruwan, tana mai yi ma shi murmushi mai taushi. Sannan ta shiga kama bangon rijiyar tana yo sama kamar yadda kadangare yake tafiya a jikin garu. koda fitowar kyakkyawar budurwar daga cikin rijiyar. Dakarun dake yaƙi da mahaifinta su kayi arba da ita sai dukkaninsu su ka dakatar da yaƙin su ka ja da baya a tsora ce. kyakkyawar budurwar ta tsugunna ƙasa ta ɗauki salkar ruwanta ta rayata a gadon bayanta sannan ta je ta kama hannun mahaifinta suka juya su ka tafi gaba ɗaya dakarun dake wajen su ka bisu da kallo cike da matukar mamaki da al,ajabi. Ana cikin wannan hali ne yarima muzaifar ya fito daga cikin rijiyar jikinshi ya jiƙe sharkaf da ruwa ga kanshi ya tsage jini yana zuba. koda dakarun su kayi arba da halin da yarima yake ciki sai hankulansu yayi mummunan tashi kuma a ka ra sa wanda zai tare sa. Shi kuwa yarima sai ya kura kyakkyawar budurwar idanu batare da yayi yunƙurin komai ba, kawai sai a ka ga budurwar ta tsaya cak sannan ta waigo tare da yiwa junan su lallausan murmushi a lokaci guda su duka biyun su kaji sun kamu da matuƙar soyayyar junan su. kyakkyawar budurwar ta ɗauke dubanta daga na yarima su ka ci gaba da tafiya sai dai su yarima su ka daina hango su. jiki a sanyaye yarima ya je ya kama linzamin dokinshi yayi gaba, Sauran dakarun su ka mara ma shi baya suna masu zaburar dawakansu. Tun da aka fara wannan tafiya har aka iso gidan sarauta yarima bai ce kalaba. ***** Fada ce ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da kayan alatun jin dadin rayuwar duniya, Duk isar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan fada dola ne ya zamo cikekken ɗan kauye kuma ya rai na kanshi. Zaune a bisa karagar mulkin, sarki Baddadul-arus ne. Sarki Baddadul-arus yakasance garjejen kato mai kama da giwa yana da ɗan mitsitsin kai da katon ciki tamkar an kifa ƙwarya a habarshi yana da ɗan mitsitsin gemu fari rol! da tsawon shi bai huce kamu ɗaya ba. A gefen hannunshi na dama gimbiya uzaima ce, zaune a bisa wata kayatacciyar kujera ta alfarma ta na sanye da tsaleliyar alkyabba mai fatsi-fatsi, shigar tayi matukar fito da kyawun surar jikin ta. Haƙiƙa duk inda kyawu yake gimbiya uzaima ta cika kyakkyawa domin ko gasar kyau Za ayi zata iya zamowa ta daya. A wannan lokaci gaba ɗaya mutanen fadar babu abinda su ke kallo face satar kallon gimbiya uzaima, kai bama maza hatta 'yan uwanta mata idan su kayi arba da ita sai kaga sun wan game bakunan su suna dalalar da yawu, saboda yadda kyawun ta ya burgesu. Gaba ɗaya fadar tayi tsit! tamkar mutuwa ta gifta, Daga can sai gimbiya ta katse shirun daya wanzu ta dubi mahaifinta sannan ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa tace "ya Abbana wai yaushe ne zamu tafiya nemo abubuwa guda uku domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ?, Tabbas na ƙagu naga anyi wannan tafiya domin na sake yin ido biyu da abokin gaba ta yarima muzaifar domin ayi ta takare. Koda jin wannan tambaya daga bakin uzaima sai sarki Baddadul-arus ya bushe da dariyar mugunta har da kyakyatawa sannan daga bisani ya dubi uzaima yace "ya yata mafi soyuwa agareni kiyi sani cewa bakomai ne ya hanamu tafiya nemo abubuwa uku ba domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ba sai domin akwai wani sauran birni guda daya da nake so na cinye shi da yaƙi, dazarar na kammala zamu fara shirye -shiryen tafiya, ina fatan kin gamsu da wannan bayani. Uzaima ta gyaɗa kai alamar gamsuwa sannan ta buɗi baki a karo na biyu tace, "ya Abbana a sanina babu wata ƙasa da tarage a yankinmu da bamu cinye ta da yaki ba. kafin uzaima ta ƙarashe maganar ta sarki Baddadul-Arus ya tari numfashin ta yace. "wannan birni dazan kai farmaki baya iyaka da ƙasata na gano boyayyen birnin ne a lokacin da nake gudanar da bincike bisa halarar tsafi na. Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Baddadul-arus ya haɗe hannayenshu biyu ya karanto wadansu dalasiman tsafi jim kadan sai ga hoton wani kasaitaccen birni ya bayyana akan tafukan nashi. Gine-ginen birnin sun kasancce cikin tsari, hatta tufafin su abin sha'awa ne. Nan take uzaima taji birnin ya burge ta sannu A hankali hoton yana canza launi har ya bayyana hoton wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kayan ado na sarauta. Tun da gimbiya uzaima tazo duniya ba ta taɓa gani ko jin labarin da namijin da yakai saurayin kyawu ba. Nan fa uzaima ta ƙurawa saurayin idanu tana nazarin shi, koda sarki Baddadul-Arus ya lura da halin 'yar tashi shiga sai ya karanto ɗalasiman tsafi ya tofa akan hannunshi, Faruwar hakan keda wuya sai hoton ya bace bat!, Tamkar bai taɓa wanzuwa ba. A sannanne uzaima ta dawo hayyacinta tana mai sauke ajiyar zuciya, sarki Baddadul-arus yayi gyaran murya ya dubi uzaima yace"wannan birni dazan kai farmaki ana kiransa da suna JARUL-IMAN. Yaushe ne zamu kai MAMAYAR BAZATO birnin?. Uzaima ta tambaya a kagauce. Baddadul-arus ya bushe da dariya sannan yace "Haba 'yata mai ki ke ci na baka na zuba ai saura kwanaki kaɗan mu kai wannan farmaki, ke dai kawai ki yi tanadi kafin ranar. Ko da jin wannan batu sai uzaima ta cika da matukar farin ciki maral-musaltuwa. koda gama fadin hakan sai sarki Baddadul-arus ya rike hannunta suka miƙe tsaye daga kan kujerunsu su ka nufi wata yar siririyar hanya dazata sadasu da gidan sarauta. **** Al’amarin wannan kyakkywar budurwa da mahaifinta kuwa, lokacin da suka kammala fafatawar yaƙi da yarima muzaifar sai suka ci gaba da tafiya babu sassauci, duk sa’ada su zo giftawa ta wani waje sai ka ga mutane sun tarwatse sun basu hanya sannan su bisu da kallo, Al'amarin daya sa su duka biyun su ka cika da mamaki ke nan. Haka kuma suka ci gaba da tafiya har ya zamana sun shafe tsawan sa'a uku suna wannan tafiya har suka fice daga cikin kasar suka shiga cikin dajin dake arewa da kasar. Tafiyar sa'a huɗu da daƙiƙa talatin kadai su ka yi suka isa wani madaidaicin gida a dajin. shi dai wannan gida angina shi ne da zallar duwatsun wuta manya manya yana da tagogi guda shida da kofa guda ɗaya jal!. Kofar an yi tane da zallar mulmulallen bakin karfe tsawanta ya kai kamu goma inda za'a sanya karti majiya karfi tsakanin ashirin ba zasu iya bangaje kofar ba. Kai tsaye kyakyawar budurwa ta je bakin gidan sannan ta sanya hannunta ɗaya ta tura kofar ta bude. Nan take ita da Dattijon suka kunna kai ciki budurwar na gaba dattijon na biye da ita. Daga ciki gidan ya kasance yana ɗauke da manyan dakuna uku,Daga ɓangaren yamma akwai banɗaki guda biyu da kuma wani dan fili da aka yi rumfa domin shaƙatawa. Kai tsaye suka shiga izuwa ɗakin dake yamma, sannan budurwar ta ta fice daga cikin dakin. jim kaɗan sai gata ta dawo ɗauke da akusuhi da salkar ruwa ta ajiye gaban mahaifinanata ta sanya hannunta ta bude akushin ta shiga ɗibar abincin dake ciki tana bawa mahaifinnata a baki. Sai da ta tabbatar ya ƙoshi sannan ta ɗauki salkar ruwa ta kafa mashi a baki ya sha ya ƙoshi. A sannane ita ma Kyakyawar budurwa ta sanya abincin a gaba domin ta fara ci amma sai hakan ya gagara, Ba komai ne ya hanata cin abinci ba sai saboda tunanin Yarima Muzaifar. Shiru ne ya wanzu a a tsakaninsu na tsawo lokaci can sai mahaifinnata ya yi gyaran murya sannan ya buɗe baki ya ce. "Ya 'yata shin ina dalilin rashin cin wannan abincin naki?". Ko da jin wannan tambaya sai Sharilat ta dubi mahaifinnata ta ce. "Ya Abbana ka yi sani cewa ba komai bane ya sanya ni cikin wannan hali ba face tunanin yadda rayuwarmu ta kasance cikin kunci da talauci. Koda jin hakan sai tsoho Kuhairu ya yi murmushi ya dube ta ya ce. "Haba 'yata shin me ya sanya zaki ɓoye mini gaskiyar al'amari, ki sani cewa ina da yaƙinin ba wannan abu ne yake damun ki ba dubu da yanayin yadda fuskarki ta nuna. Koda jin haka sai Sharilat ta sunkuyar da kanta ta ce. " ka gafarceni ya abbana Tabbas na ɓoye maka Gaskiyar abinda yake damuna. Tsohon Kuhairu ya yi murmushi sannan ya dafa kafaɗun Sharilat ya dubeta ya co. "Kar ki damu ya 'yata ki sani cewa ke kaɗaice ki ka rage mini daga cikin zuri'ata ya zama dole ki gaya mini abin da ke damunki. Domin baki da wanda ya fini, ni nasan abinda yake damunki shi ne, kin kamu da soyayyar Yarima Muzaifar Jarumin da ki ka fafata yaki da shi ko ba haka bane.? Cikin alamun jin kunya sharilat ta sunkuyar da kanta kas! Kamar mai tunanin wani abu. Ba ta yi mamakin don mahaifinnata ya san abinda ke damunta ba, Domin ba baƙn al'amarin ne a wajen ta ba. Cikin alamun takaicin tsoho kuhairu ya dubi sharilat ya ce, " ya 'ya ta ki yi sani cewa da kin san abin da zai faru da kin gaggauta cire soyayyar Yarima daga zuciyarki, Domin gudun matsalar da zata faru. Cikin kaɗuwa Shirilat ta dubi mahaifinta ta ce da shi "Ya abbana shin wace irin Matsalar zan fuskanta na kamuwa da soyayyar Yarima?". Tsoho Kushairu ya ce " A yanzu bai kamata ba ki san matsalar ba, Domin sanin ta a yanzu ba shi da amfani,Tabbas anan gaba zaki gasgata batuna." Koda jin hakan sai ta yi shiru tana mai zurfafa cikin kogin tunani. Abu na farko da ya faɗo mata a rai shi ne ta yaya zata iya cire son Yarima a zuciyarta?. Shin yanzu idan taki cire son na shi matsalar da mahaifina ya faɗa zata faru kuwa?. Abu biyu shi ne ya aka yi mahaifinta ya gano sunan Yarima, Bayan cewa tunda suke basu taɓa gani ko jin labarin shi ba. "Babban abinda hankalinta shi ne da ta yi nazari sosai a ɗazu, Irin kallon da yarima yake yi mata iri ɗaya ne sak! da na mahaifinta, duk dacewar mahaifin nata ya tsufa amma yana ɗaukar kamanni da Yarima, A yanayin fuska da kirar jiki. Har Sharilat ta buɗi baki zata ce wani abu sai suka jiyo ihu da kururuwa a can waje. Al'amarin da ya sanya gaba ɗayan su suka miƙe tsaye zumbur!. Tsoho Kushairu na rike da sandarsa ita kuma Sharilat tana rike da wani mashi suka ruga waje da gudu. Aikuwa koda fitowarsu sai suka yi arba da waɗansu girɗa-girdan dakaru shirye-shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai tsananin kwarjini da ban tsoro. Gaba ɗayan su suna zaune akan dawakai, a hannayensu suna ɗauke da makamai daban-daban irinsu gatari, da al'amudi. Tabbas wadannan Dakaru sun zama abin tsoro, Domin komai dakewar zuciyar mutum baza iya kare musu kallo ba, face JARUMIN KWARAI, mai dakakkiyar zuciya. A ƙalla adadin su ya kai guda ɗari tara. Lokacin da dakarun suka yi arba da Sharilat da tsoho Kushairu sai aka fara kallon kallo, Sharilat tsoho da Kushairu suna masu gyara tsayuwarsu. Sai da aka shafe tsawon lokaci ana kallon kallo. Sai daga bisani ne wani garjejen kato mai jajayen idanu daga cikinsu, wanda yafi sauran munin siffa ya fito daga cikin mayaƙan yana mai zaburo dokinshi ya nufo inda Sharilat take tsaye. Koda ya rage saura taku biyar a tsakanin su ba sai shugaban dakarun ya ja linzamin dokinshi ya tsaya ya karewa Sharilat da tsoho Kuhairu kallo tunda daga ƙasa har sama, kawai sai ya bushe da dariya mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska kamar an aiko masa SAKON MUTUWA ya dubi Sharilat a cikin kallo na kaskanci da wulakanci, sannan ya fara magana da muryarshi mai kama da gurnanin damisa ya ce. "Ya Sharilat ki yi sani cewa yau nazo gareki cikin gagarumin shirin daban taɓa yin kamar shi ba. Ki sani cewa yau ba zaki kuɓuta daga tsananin ukubata ba …! Kafin shugaban ya ƙarashe zancenshi Sharilat ta tari numfashin shi ta na mai daka masa tsawa ta ce, "Kaiconka ya kai Huzlan tabbas ka tafka babban kuskure da har kake ganin cewa zaka samu nasara akaina. Lallai yau zan yi maka kisa mafi muni ka yi MUGUWAR HALLAKA domin hakan ya zama darasi ga masu muguwar ɗabi'a irin taka. Haƙiƙa zalunci da azzalumai basa ɗorewa aban ƙasa face an samu abu biyu ya kawar dasu, walau dai mutuwa ko kuwa wata haitta ta kawar dashi aban ƙasa. Koda jin wannan batu sai Shugaba Huzlan ya kuma bushewa da dariya a karo na biyu a wannan karon sai ya kusa suɓutowa daga kan dokinshi saboda da dariyar, Sannan ya tsagaita ya dubi Sharilat ya ce. "Haba yarinya ki sani cewa ai karo dani a yau dai dai-dai yake da buɗe taskar ANNOBA DARI. Domin a yau na zo da gagarumin shirin da ban taba yin kamar shi ba, ki sani cewa wannan gafalallen tsohon na ki ba zai hanani cimma buri na ba. Yau shekaru shida ke nan muna gwabza yaƙi dake, Babu wanda ke samun nasara amma a yau za'a yi ta ta ƙare. Koda gama fadin hakan sai Huzlan ya zaro wata zabgegiyar adda dake rataye a gadon bayanshi. Sannan ya wangame bakinshi ya kwarara ihu ya dako tsalle daga kan dokinshi, kai ka ce ba ya jin nauyin jikinshi ya afkawa Sharilat da dukkan karfinshi. Su duka biyun suka kaceme da azababben yaki, su ka wanzu suna kawai junansu mugggun hare hare cikin zafin nama. Koda ganin hakan sai tsoho Kuhairu ya kwarara uban ihu ya falfala da azababben gudu kan dakarun Huzlan hannun shi na hagu rike da wannan sanda, koda ya rage baifi saura taku huɗu tsakaninsu ba, sai sandar ta rikiɗa izuwa dogon mashi iri ɗaya sak da na hannun Sharilat. In da ace mutum zai ga yadda tsohon Kuhairu ya tari waɗannan Ɗaruruwan mayaƙa dole ne ya jinjina ma shi ya san cewa ya cika tsoho mai ran karfe kuma. Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin dudufniya suna turmutsustsu,ƙarar HADUWAR TAKUBBA ta cika dodon kunne, ƙiri-ƙiri gashi dai dakarun sun fi Kuhairu karfin damtse amma sai ya zamana ya zame musu kaifin takobi ya wanzu ya aika rayukan su barzahu, Ta hanyar tsire su da mashi, A wasu lokutan sai kaga ya mako badakare ya bazar da shi a kas. Nan fa waje ya cika ihu mazaje suka dunga yin muguwar hallaka, jini ya dunga kwaranya, fantsama da tsartuwa. Kafin cikar daƙiƙa arba'in Kuhairu ya samu nasarar kashe dakaru sama da saba'in. Al'amarin daya yi mutuƙar dugunzuma hankalin dakarun ke nan kuma suka harzuƙa ainun suka ƙara afka ma shi da yaƙi yafi muni. A ɓangaren Sharilat da Sadauki Huzlan kuwa sun wanzu suna kawai junansu sara da suka cikin zafin nama JURIYA BAJINTA ta ban al'ajabi. A na wannan yaƙi ne cikin shammace Huzlan ya kawai Sharilat wani wasan sara da zabgegiyar addarshi domin tsinke mata wuya. Cikin zafin nama ta sunkuya addar ta sari iska, cikin Fushi ya kuma kai mata saran a kafaɗa. Shirilat ta wurkila ta zamewa Saran addarshi ta nutse cikin ƙasa. Kafin ya zare ta cikin ƙarƙashin ƙasa tuni Sharilat ta shammace shi ta soka masa mashi a kirji. Nan take jini ya fantsama a kirjin ya kwalla ƙara cikin karfin hali da juriya ya shammaci Sharilat ya dunƙule hannayenshi biyu ya gabza mata naushi a maƙogaronta Nan take su duka biyun suka zube ƙasa magashiyan. **** Kamar yadda Sarki Baddadul-Arus Arus ya faɗawa 'yarshi Uzaima haka al'amarin ya kasance. sai da mako guda ya shuɗe da yin maganarsu Baddadul-Arus. Sannan suka fara shirye-shirye shiryen tafiya birnin Jarul iman. Shi dai birni na Jarul- iman ya kasance mai tattare da albarkatun ƙasa. Sarkin dake mulkin jarul Iman ɗin ana yi masa lakabi da Huraisul-Zaman. Sarki Huraisu yakasance kyakkyawa nagaban kwatance mai shekaru ashirin da huɗu, yana da karfi na Allah ya isa. A rayuwar Sarki Huraisu baya tsafi kuma baya tasiri a kan shi, Babu wani al'amari da zai sanya gaba gaba face ya cimma nasara akan shi. Allah (S.W T) ya azurtashi da wata baiwa guda daya. Baiwar kuwa ita ce hikima, komai hikımar mutum da fasahar shi idan ya zo gaban Huraisu sai ya zamo daƙiƙi tamkar bai taɓa sanin komai ba. Baiwa ta biyu kuwa ita ce, Babu wa musiba ko annoba da zata afku face ya gano hanyar da za'a magance ta komai daɗewarta. Bakoyen duniya na wannan zamani sun labarta cewa, Asalin Sarki Huraisu ya kasance jinin jarumi Usmairu wanda shi ne ya taɓa shiga taskar boka Shuyudan wato Taskar ANNOBA DARI, kuma ya fito a raye. Sarki Huraisu bai yarda ya bautawa wani ubangiji ba face kawai yana dogaro ne da baiwar da yake da ita, saboda haka ne kowane mutum a birninshu yake bautawa abinda yake so. 'ya'yan Sarakuna daga biranan duniya, suna aiko da wasikar soyayyar su zuwa ga sarki Huraisu akan ya amince ya aure su amma sai ya ƙi amincewa da yawa daga cikin su sun mutu, sanadin kamuwa da soyayyar shi. Bakomai ya sanya Huraisu baya amincewa da soyayyar su ba, Burinshi shi ne ba zai auri kowa ce ya mace ba face ya samu macen da ta ɗara shi a yawan baiwa kuma wadda tai mu'amala da shi har sa'a ɗaya amma bata kamu da son shi ba duk irin kyawun surar shi. Gaba ɗaya jama'ar birin Jarul Iman suna mutuƙar kaunar Haraisu kamar ɗan cikinsu, saboda yadda yake tafiyar da mulkinshi babu kama karya. Wannan shi ne taƙaitaccen labarin Sarki Huraisu na birnin Jarul Iman. Tun da duku-dukun safiya mayaƙa suka yi sahu-sahu a kofar gidan sarautar Sarki Baddadul-Arus, wasu suna zaune a bisa dawakai, rakuma wasu a ƙafa, makaman yaƙinsu kuwa gasu nan birjik bila adadin. Jim kaɗan sai ga sarki Baddadul Arus da 'yarshi Uzaima, sun fito daga gidan sarauta cikin gagarumar shigar yaki mai mutukar kwarjini, shigar baƙaƙen tufafi su ka yi hatta takalman ƙafarsu bakake ne. jikinsu kuwa suna sanye da makaman yaƙi sama da kala arba'in, kuma suna zauna ne akan bakaken dawakai ingarmu. Ko da fitowar Sarki Baddadul Arus da Uzaima sai miliyoyin Mayaƙan su ka risina da kawunansu domin girmamawa a gareshi. Kai tsaye Badaddul-Arus da Uzaima suka durfafi kofar suna fira cikin nishaɗi da annashiwa. A sannane miliyoyin mayaƙan su ka ɗago da kawunansu suka zaburi dawakansu da gudu suka mara musu baya. Da isarsu bakin kofa waɗansu Girɗa- Girdan dakaru masu kirar samudawa suka yi hanzarin wangame kofa suna masu sunkuyar da kansu kas, Domin girmamawa a garesu. Sai da Badaddul Arus da Uzaima suka yi nisa da su sannan suka dago kawunansu suna masu karewa sauran mayaƙan kallon,Da fitarsu sai suka shiga cikin daji aka ci gaba da gudu babu sassauci ana cikin wannan tafiya Uzaima ta dubi Mahaifinta ta ce "Ya Abbana ina da wata tambaya?" Ko da jin hakan hakan sai Badddaul-Arus ya ce, "Fari tambayarki ya 'ya ta." Uzaima ta yi ajiyar zuciya gami "da gyaran murya ta ce," Ya Abbana wai shin me ya sanya wannan karon mu ka taho da mayaƙa, alhalin idan Za'a kai YAKIN BAZATO ni da kai kaɗai muke zuwa.? " Ko da jin wannan batu sai Baddadul Arus ya bushe da dariya mai ka ma da kukan Jaki ya ce. "Da sannu za ki ga amfanin wadannan mayaƙa ina mai tabbatar miki da cewa wannan yaƙi da za mu yi bamu taɓa yin kamar shi ba lallai za ki sha kallo. Ko da gama fadin hakan sai Uzaima ta yi murmushi wanda ya tona asirin kyawun ta, Daga bisani da gaba da tafiya batare da dayansu ya ce uffan ba. wanan shi ne abinda ya faru ga Sarki Baddadul-Arus da 'yar shi Uzaima a lokacin da zasu kai farmaki birnin Jarul-Iman. ***** Lokacin da Sarki Himras ya rabu da Yarima Muzaifar akan gobe zai shiga cikin halarar tsafin shi domin ya gano sunan ɓakuwar jaruma da na mahaifinta. Ko da Sarki Himras ya kaɗaita a cikin turakarshi sai barcı ya gagareshi kuma zuciyarshu ta kama tafarfasa tamkar zata faso kirjinshi ta fito waje. Ba komai ne ya hana Sarki Himras ya kasa rintsawa ba fa ce Jarumar da ta fafata yaƙi da Yarima 'ya ce ga ɗan uwanshi sarki Kuhairu. Abu na farko daya faɗo mashi a rai shi ne yaya aka yi aka samu wani mahaluki daya iya horon yaƙi irin nashi ya san cewa shi da ɗan uwanshi Kuhairu ne kaɗai suke da irin shi, ya aka yi Kuhairi ya rayu shi da matar bayan cewa ya yi kisan da ba za su ƙara ba dai-dai da daƙiƙa ɗaya a duniya ba. Ya yinda Sarki Himras ya zo nan a tunanin shi sai ya cika da baƙın ciki maral- musultuwa har ta kai kwallar takaici ta zubo ma shi. Babban abinda ya hana Sarki Himras gudanar da binciken akan wannan al'amarı shi ne. Matsawar ya tabbata cewar jaruma sharilat 'ya ce ga Ɗan uwanshi Kuhairu a aka yi rashinsa'a to nan take Zai yi Dukkan sirrikan tsafinshi zasu lalace, bisa ƙa'idar tsafin baya tasiri akan junansu. Sa'adda Sarki Himras ya zo nan a tunanin shi sai ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu wanda ya haddasa girgizar gidan sarautar baki daya. Al'amarin daya firgita gaba ɗaya dakarun gidan ke na, suka ɗebo makamansu suka rugu izuwa ɓangaren Sarki domin rabon su da Sarki Himras ya yi wannan kururuwa yau shekara biyu tun ranar mutuwar matarshi. Su kansu kuyangun da bayin gidan da yawansu sai da suka farka daga barcinsu saboda jin wannan ihu, Domin su san duk sa'adda suka ji wannan ihu. Wannan shi ne abinda ya faru ga Sarki Himras bayan ya rabu da Yarıma Muzaifar ya kaɗaita a cikin turakarshi. ***** Cikin tsananin JURIYA DA BAJINTA a lokaci guda su duka biyun suka miƙe tsaye zumbur suka ci gaba da kaiwai junansu hare-hare da zummar halaka juna a duk lokacin da makamansu suka haɗu da juna sai ka ga sun haddasa tartsatsin wuta gami da ƙara marar daɗin sauraro. Al'amarin daya ƙara fusata jaruman biyu ke nan suka zage damtse suna kawai junan hare hare-hare na ban al'ajabi. A ɓangaren tsoho Kuhairu kuwa ya zamo kamar shaidɗani a tsakiyar dakarun ya wanzu yana kare harin da suke kawo mashi na sara da suka. ya wanzu yana tsire su da mako su ƙasa suna zubewa kasa matattu. A wasu lokutan ma sai ka ga dakaru sama da shirin sun yanyayame shi suna neman su kaishi ƙas, Amma sai ka ga ya tarwatsa su ko ka ga ya yi katantanwa a Ƙasan su ya doki kafafuwan su da dawakansu sun zube kasa. Kaicol Tabbas idan TSANANIN DA UKUBA a yaƙi suka tsananta, Hanyoyin tsira su toshe, sai ga ZARATAN MAYAKA suna neman su cika wandonsu da iska domin su TSIRA DA RAYUKANSU. Hakanne ya faru ga yaran Huzlan, Domin koda suka ga irin kisan gillar da Kuhairu ke yi masu sai da yawa daga cikin su suka yunkura zasu gudu, Amma kafin su kai ga hakan tsoho Kuhairu ya afka musu ya hana su sakat!. Ana cikin wannan yaƙi ne Huzlan ya shammaci Sharilat ya sareta a cinya ya yi mata wani lafcecen rauni jini ya yi tsartuwa duk irin tsananin jarumtakar Sharilat sai da ta kwalla ƙara bisa tsananin zafi da zugi da ta ji. Cikin gwaninta da juriya Sharilat ta shammaci sadauki Huzlan ta soka ma shi mashi a cinya, nan take inda ta suken shi ya haddasa wani katon rauni, tamkar an saka ɗan buda a wuta sannan aka cakamashi a cinyar, Huzlan ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu saboda yadda yaji raɗaɗi . Kafın cıkar rabin sa'a sun yiwa junansu raunuka fiye da sha biyar. Al'amarin da ya sanya su duka biyun suka galabaita ainun, saboda yadda jini ke zuba ajikinsu, Amma a hakan suka ci gaba da yaƙin. Gaskiyar masu masu iya magana da suke ce kyan faɗa a kwana ana yi kuma tabbas idan ka ji ana ga ƙi gudu, To sa gudu ne bai zo ba". Sai da aka shafe tsawon sa'a daya ana wannan gurmurzu babu sassauci, a dai- dai wannan lokaci ne fa duhun dare ya fara kawo kai, koda fahimtar hakan sai Sadauki Hazlan ya shammaci Sharilat ya kirɓa ma ta naushi a fuska. Saboda ƙarfi naushin sai da sharilat ta yi sama tamkar an janye ta da ƙugiya sannan ta bugu da wata bishiya kanta ya tsage jini ya yi tsartuwa baje a ƙasa magashiyan numfashinta na fita sama sama Koda samun wannan nasara sai Huzlan ya bushe da dariyar farin ciki kawai sai yaje inda Sharilat take ya raba kafafunshi akanta. sannan ya ɗora kaifin Addarshi akan wuyan sharilat yana mai yi ma ta murmushi mugunta. Kwatsam! ba zato babu tsammani sai aka ga jaruma Sharilat ta gabzawa Sadauki Huzlan wawan naushi a maƙogaronshi, saboda ƙarfin naushin sai da Huzlan ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabaice Numfashinshi na fita sama-sama. Kafin ya yi wani yunƙuri Sharilat ta miƙe tsaye zumbur! suri mashinta ta caka ma shi a kirjinshi, take ya fasa kijinshi ya billo ta gadon bayansa, jini ya dunga kwaranya ya na tsartuwa sama. Kaino! Tabbas gaskyar masu iya Magana da suka ce idan TSANANIN DA UKUBA a yaƙi suka tsananta wuya ta yi wuya sai ka ga ZARATAN MAYAKA suna neman cika wandonsu da iska domin su TSIRA DA RAYUKAnsu Hakanne ya fatu ga sauran mutanen Huzlan domin koda suka yi arba da gawar Huzlan kwance sai suka yunƙura da nufin tserewa, Amma sai tsoho Kuhairu ya dunga ƙure musu gudu yana makosu daga kan dawakansu suna yin MUGUWAR HALLAKA. Kafin cikae daƙiƙa ashirin Kuhairu ya hallaka mayaƙan ɗayansu bai tsira da rayuwarsa ba, cikin mutukar farin ciki mara misaltuwa Sharilat ta ruga da gudu ta je ta rungume mahaifinta, Tsawon lokaci a rungume da juna, sannan daga baya Sharilat ta janye jikinta daga na abbanta su ka sake juyawa su ka shigo cikin wannan gida, suka bar gawar Huzlan da jama'arshi kwance cikin jini. Bakomai ne ya haddasa gaba tsakanin Huzlan da su Sharilat ba face rigima a kan wannan daji da suke ciki, asalin dajin na wani tsohon mafarauci ne da ya taimaki tsoho Kuhairu da matarshi Hasmila. Bayan mutuwar mafarauci Kamzil ne sadauki Huzlan ya ƙudiri aniyar kwace dajin saboda irin arbarkatun dake tattare da dajin. Babban burin Huzlan a duniya shi ne da zarar ya mallaki dajin zai gina wani katafaren birni wanda yake ababu kamarsa,Kasancewar Huzlan mashahurin attajiri, Saboda sana'ar fashi da makami da yake yi. A ƙalla Huzlan da su tsoho Kuhairu sun yaƙi junansu sau ashirin da huɗu amma babu wanda yake samun nasara sai dai ayi ragas. wannan shi ne dalilin kulluwar gaba a tsakanin su. **** Lokacin da Sarki Badaddul-Arus da 'yarshi Uzaima su ka ci gaba da jagorantar miliyoyin DAKARUN YAKInsu sai su kaci gaba da ratsa dazuzzuka da bira ne sai suka shafe tsawon sa'a tara suna tafiya babu sassauci. Sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai ga shi Sarki Badaddul-Arus da jama'arshi sun shafe tsawon kwanaki biyar suna tafiya, a iya tsawon tafiyar babu abin da ke tsaida su face idan gimbiya ko Sarki sun yi buƙaci da dakatar da tafiyar. A kwana na shida ne a lokacin da rana ta zo tsakiya Sarki Badaddul Arus da jama'arshi suka iso birnin Jarul Iman, koda isowarsu sai Badaddul-Arus ya umarci magatakarda ya rubuta wasika sannan ya shi manzo ya tura shi izuwa birnin. Lokacin da jakadan ya isa fadar birni sai ya tarar da fadar ta cika ta batse da jama'a a wannan lokaci Sarki Huraisu na zaune a kan karagar mulkin wcce aka sana'anta ta da zallar zinare a ka yi mata feshi da ruwan rukut, Ya na sanye da doguwar shuɗiyar alkyabba da a ka yi mata cin baki da zaren lu'u-lu'u takalmin dake kafarshi an yi mashi ado da gashin ɗawisu sanye a kanshi akwai KAMBUN MULKI da a yi shi da zallar zinare ya na ta walwali da daukar ido. Tabbas wannan shiga da Sarki Huraisu ya yi ta mutukar fito da kyakkyawar surarshi babu wata 'ya mace da zata yi wannan arba da shi face ta kamu da matuƙar kaunarshi a zuciyarta. A gefe guda kuwa yan majalissa ne a zazzaune bisa shimfiɗu na alfarma, dakaru kuwa sun yiwa fadar kawanya su na ta kai komo dan tabbatar da cikakken tsoro. A wannan lokaci gaba daya mutanen dake fadar su kuma satar kallon Sarki Huraisu suke yi kuma a na fira cikin nishaɗi da walwala. jakadan ya shigo fadar da zuwan shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da wasika. Sarki Huraisu ya umarci magatakardar da ya karbi wasikar dake hanun badakaren ya warwareta sannan ya fara karanta abin da ke cikin fili kowa ya na sauraro. Takarda daga dodon Sarakuna Sarki Baddadul Arus. Zuwa ga ɗan tatsitsin sarki a cikin sarakuna Sarki Huraisu. Ya kai wannan kaskantaccen Sarki ka yi sani cewa bai rubuto wannan wasika ba sai domin baka umarni. Ina so ka mallaka komai naka zuwa gare ni, idan kuwa ka yi girman kai ma'ana ka saɓawa umarnina, to ba makawa da zan shafe ka da jama'arka daga doron ƙasa kamar yadda na saba yi ga ƙananan Sarakuna masu taurin kai irin ka. Ka sani cewa bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne, tabbas idan kunne ya ji jiki ya tsira. Lokacin da magatakarda ya zo nan a karatun wasikar sai Sarki Huraisu ya mike tsaye daga kan karagarshi ya tako da kafafunshi har inda ɗan aiken Sarki Baddadul Arus yake ya shammace shi ya dunkule hannayenshi biyu ya gabza masa naushi a a wuya, nan take wuyanshi ya karye ji kake rukus. Take ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba, kawai sai Sarki Huraisu ya yi umarni a dauke gawar ɗan aiken aka goge jinin da ya zuba da wani farin kylle. Sarki Huraisu ya kalli gaba ɗaya mutanen fadar a cikin matuƙar fushin da bai taɓa yin kamarshi ba ya buɗi baki cikin maɗaukakiyar muryar ya ce: "Ya ku mutanen fada mai albarka ku sani cewa, wannan yaƙi babu gudu babu ja da baya, kuma ban ɗaukewa kowa ba babba da yaro. " Koda gama faɗin haka sai Sarki ya juya ya nufi wata 'yar siririyar hanya da za ta sada shi da gidan sarauta, wasu ZARATAN DAKARU ma'abota bakaken tufafi suka mara mashi baya har suka kule da zuwa gidan sarautar. Koda ficewar Sarki sai fadar ta hargitse, mutane zasu dinga zuwa gudaddajin su suna shigar yaƙi domin tunkarar abinda zai kawo karshensu. **** Lokacin da Sarki Baddadul-Arus suka ga an shafe tsawon sa'a ba a ga ɗan aikensu ya dawo ba, sai kawai Baddadul- Arus ya ba da Umarnin da a afkawa birnin a karya kofa ya shiga. Kawai sai aka jiyo an busa ƙahon yaƙi daga cikin birnin Jarul-Iman sai ga kofar ta ta buɗe mayaƙa suna tururuwar fitowa. Lokacin da mayaƙan suka gama fitowa sai aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu har ya zamana an shafe wasu 'yan daƙiƙu. Kawai sai Sarki Baddadul-Arus da Uzaima suka saki linzamin dawakansu suka durfafi in da tawagar Sarki Huraisu take. Koda ganin haka sai shi ma Huraisu da sarkin yaƙinshi mai suna Bilar su ka sakarwa dawakansu linzami don tarar juna, yayin da a ka zo daf da juna sai suka tsaya cak!. Aka sa ke yin kallon-kallo a karo na biyu sannan Sarki Baddul Arus ya ce "Ya kai wannan Sarki Ma'abocin taurin kai a garemu ka sani cewa ko ba a gwada ba ka san cewa linzami yafi karfin bakin kaza haƙiƙa runduna ta Ninka taka a yawa da karfi. Ni sarki Badaddul-Arus mai burin zamowa shugaban nahiyar Mufrad baki ɗaya na zo ni da 'ya Uzaima lallai ba zan koma ƙasata ba face na baje birnin ka daga doron ƙasa domin hakan ya zama darasi ga ' yan tsakin sarakuna irinka. Koda jin wannan batun sai Sarki Huraisu bushe da dariya kamar bazai daina ba. Al'amarin da ya yi mutuƙar ba wa Badaddul-Arus da Uzaima mamaki kenan kuma ya ya fusata su ainun. Bisa ganin cewa duk kasaitarsu amma yau wani mahaluƙi ya wanzu a gabansu ya na neman ƙasƙantar da Darajarsu. Sarki Huraisu ya haɗe rai sannan ya ƙurawa Uzaima idanu ko ƙiftawa ba ya yi, sannan ya juya ya dubi Badaddul Arus ya ce. "Ya kai Badaddul-Arus kayi sani cewa na daɗe ina jiran wannan rana mai cike da farin ciki domin a wannan rana. ne na taba fita yaƙi a rayuwata, A iya tsawon rayuwata tun da nake ban taɓa sanya wani al'amari a gabana ba face na cimma nasara akanshi, Ina mai tabbatar maka da cewa yawan mayaƙan ba zai bani tsoro ba, Domin Ni kaɗai zan iya ja da su na kawar da su cikin 'yan daƙiƙu. " Sa'adda Sarki Huraisu ya zo nan a Zancenshi sai Sarki Baddadul-Arus da 'yarshi Uzaima su ka tuntsire da dariya, Domin suna ganin cewa Huraisu ya yi wauta, kafin dayansu ya kara cewa wani abu Badaddul Arus da' yarshi Uzaima sun zaro makamansu suka sakarwa dawakansu linzami su ka yunƙura kan Sarki Huraisu. Ko da ganin hakan sai shi ma Sarki Huraisu ya zaburo dokinshi ya durfafi su Badadul Arus ya na mai ya dakatar da Sarkin yakin shi da hannu yana nuna ya dakata. Koda Sarki Badaddul-Arus da Uzaima su ka yi arba da Sarki Huraisu ya durfafo inda suke batare da riƙe wani makami ba, sai suka cika da mamaki amma sai su ka raya a zuciyarsu, cewa lallai Sarki Huraisu ya zama wawa marar tunani to amma masu iya magana na cewa "idan ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa to ji ya yi ya taka dutse. Lallai akwai wani abu da Huiraisu ke takama da shi. Koda gwarazan jaruman uku suka haɗu sai a ka kacame da masifaffan yaƙi, su ka wanzu suna kaiwa junansu hare-hare cikin mutuƙar zafin nama da JURIYA DA BAJINTA. Sarki Huraisu ya wanzu ya na kare hare-haren Badaddul-Arus da Uzaima kawai batare da ya yi yunƙurin zare makami ba. wannan shi ne abinda ya faru ga Sarki Badaddul-Arus da gimbiya Uzama a birnin Jarul-Iman domin su kawar da Sarki Huraisu. *** Gari na wayewa tunda dukun-dukun safiya Yarima Muzaifar ya kammala shiri tsaf, sannan ya ɗebi dakaru suka shiga cikin gari bisa dawakai amma wannan karon su Yarima ya ƙi sanya kayan yaƙi ajikinshi kuma ya rufe fuskarshi da rawani ta yadda babu wanda zai iya shaida shi. Lokacin da su ka ci gaba da tafiya a cikin birnin sai ya zamana sa'a biyar ta shuɗe batare da Yarima ya ji duriyar bakuwar jaruma ba. Al'amarin da ya Ɗugunzuma hankalin Yarima Muzaifar kenan ya shiga damuwa ainun. Lokacin da dakarun suka ga Yarima bai samu baƙuwar jaruma sai suka shiga kasuwa suka shiga bincike jama'a. Koda buhun hatsi mutum yazo dashi sai an bincika, rumfuna da saƙo da lungu. Tabbas gaskiyar masu iya magana da suka, "idan Raƙumin ka ya ɓata ko akurki ka gani sai ka leƙa. Nan fa gaba ɗaya su Yarima su ka hargitse kasuwar mutane suka shiga guje - guje gami da iface- ifacen tamkar sun ga mutuwar su, masu karfi suka dinga ta ke masu rauni suna suna Faɗuwa ƙasa ana tattake su, sai da yarima da dakarun su ka shafe tsawon Sa'a biyar suna tafiya a cikin babban birnin Darul-Kushur ba su ji labari ko Ɗuriyar bakuwar jaruma ba. Al'amarin da ya sanya zuciyar Yarima ta karaya kenan ya shiga damuwa kamar zai fashe da kuka ga yunwa da kishi sun addabe shi, tare soyayyar Almajirar dake Addabarshi a zuciya. Abin da Yarima bai sani ba shi ne, ita ma baƙuwar jarumar tunda duku-dukun safiya ta shigo cikin gari domin ta sadu dashi. Sa'adda baƙuwar jarumar ta ga har yamma tayi bata ga inda su yarima suke ba sai ta yanke shawarar ta ɗan huta a ƙasan wata bishiya sannan ta fice daga birnin. A na cikin wannan hali ne sai ga Yarima da dakarunshi sun zo giftawa ta wajen, ko da Yarima ya yi arba da jarumar sai ya ja linzamin dokinshi ya tsaya sannan ya taka da kafafunshi har inda take, tare da yiwa junansu murmushi ba. Da isowarshi ya tsugunna a gabanta ya dubeta fuskarshi cike da Annuri ya ce. "Marhaban da sake saduwa da tauraruwar Abar haskawa, sarauniyar matayen duniya. Ya ke jaruma ma'abociyar kyawu ki yi sani cewa tun ranar da mu ka fafata yaƙi a junanmu na ji na kamu da mutuƙar kaunarki, ina fatan za ki ba ni kujerar zama a fadar sonki.? " Baƙuwar jarumar dubi Muzaifar cikin murmushi mai taushi ta ce "Ya kai Muzaifar ka yi sani cewa tun ranar da muka haɗu ni ma na ji na kamu da kaunarka, bisa wannan dalili ya sanya na fito neman ka domin zuciyata taƙi hakura ta danne soyayyarka face na yi arba da kai. Lokacin da baƙuwar jaruma ta zo nan a zancenta sai su duka biyu suka kurawa junansu idanu suna yiwa juna tattausan murmushin mai mai tattare da tsantsar soyayya. Cikin nutsuwa yarima ya yi ajiyar zuciya ya dubi jarumar ya ce, "Ya abar kaunata idan ba zaki damu ba ina buƙatar nayi miki waɗansu tambayoyi." Ko da jin haka sai Jaruman ta ce , "Fadi tambayarka ya masoyi ina mai sauraren ka. Yarima ya yi ajiyar zuciya sannan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya ce, "Menene sunanki da na mahaifinki.? Kuma menene labarin rayuwarki." Koda jin waɗannan tambayoyin sai jarumar ta runkui da kanta ƙas batare da ta ce uffan ba, duk Wannan abu dake waka a tsakanin yarima da jarumar, Dakarun Yarima na tsaye a gefe guda Suna kallon abinda ke faruwa. Koda su ka ga abin da ke wakana sai suka cika da matuƙar mamaki domin a iya sanin su tunda suke ba su tuba ganin Yarima ya kula wata 'ya mace ba, duk irin tsananin kyawunta. Amma sai zukatan su suka shiga cikin wasi-wasi domin gaza gane wannan jaruma, a da sun yi tsammanin gimbiya Uzaima ce 'yar Sarki Badaddul-Arus ce ta yi ɓadda kama, amma a yanzu abin ba baka yake ba. Jarumar ta ɗago da kanta ta yi murmushi ga Yarima mai ɗimauta zuciyar duk wani da namiji mai hankali sannan ta buɗe baki ta ce. "Da farko dai ni sunana Sharilat Bintu Kuhairu game da tambayarka ta biyu kuwa labari ne mai tsawo wanda da zamu kwana ba zan iya kawo karashe shi ba. Saboda haka ka yi mini uzuri wannan tambaya na yi maka alkawari idan mun sa ke saduwa zan sanar da kai labarin rayuwarta. Da jin wannan jawabi sai Yarima ya ce, "Babu damuwa ya masoyiyata idan mun sake Haɗuwa sai ki bani tarihin rayuwarki ni ma in ba ki tawa. Koda gama faɗin hakan sai Sharilat ta miƙe tsaye ta juya ta nufi kofar fita gari, ta na mai waigen yarima su na yi juna murmushi mai tattare da santsar so da kauna. Sai da Sharilat ta yi nisa cikin tafiyar har ta ɓace Yarima ya daina hangota, sannan yarima yaje ya kama dokinshi ya hau sannan ya sakarmashi linzami ya yi gaba dakarun shi su ka mara ma shi baya, zuciyar Muzaifar cike da farin ciki ciki mara misaltuwa. ko da su yarima suka iso gidan sarauta sai ya huce kai tsaye izuwa cikin turakarshi ya shiga kewaye ya tsala wanka, ya ci abinci sannan ya fice ya nufi tukarar mahaifinshi. Tun kafin yarima ya isa su ka haɗu da sarki Himras shi ma ya na shirin zuwa wajenshi koda budurwar ta su sai suka garzaya wani ƙasaitaccen lambu dake nesa kadan da turakar Sarki. Bayan sun zauna a bisa waɗansu ƙayatattun kujeru na azurfa, sai shiru ya wanzu a tsakanin su na ɗan wani lokaci. Daga can sai yarima ya yi gyaran murya ya dubi mahaifinshi ya ce,"Ya Abbana ka yi sani Cewa a yau ne na sadu da wannan jaruma kuma ta sanar da ni sunanta dana mahaifinta. Abin da ta gaya min shi ne sunanta Sharilat sunan mahaifinta Kuhairu, na yi iyakar ƙokarin sanin labarin rayuwarta sai dai hakan bai samu ba. Sa'adda Sarki Himras ya ji wannan batun daga bakin Yarima sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata zata ƙone kuma ya cika da matuƙar baƙin ciki da takaici mara misaltuwa. Amma saboda kada yarima ya gane halin da ya ne ciki sai ya bar abin a ranshi, ya sa ki tattausan murnmushi ga Yarima mai kama da yaƙe ya ce, "Babu damuwa ba dole ba ne sai na ji tarihin rayuwar jarumar tabbas na gamsu da bayaninka. a yau da safe na gudanar da bincike a bisa halarar tsafina nagano dukkan abin da ke faruwa tsafin ya Bayyana mini cewa, lallai Sharilat da mahaifinta za su ba mu gagarumar gudunmowa a tafiyarmu ta ɗauko TAKOBIN SIHIRI. "Ya na da kyau a cikin daren nan na gana da Sharilat da mahaifinta domin na nemi goyan bayansu domin tafiya neman abubuwa uku wato sarkar tsafi dake ajiye a tsahon ƙabari a Birnin Rum. SIHIRATACCEN KUNDI dake ajiye a fadar Boka Zammar domin Ɗauki TAKOƁIN SIHIRI. Ya yin da Yarima ya ji Wannan bayani sai ya dubi mahaifinshi ya ce. "Ya Abbana shin ban ji ka min bayani ba akan yadda Sharilat da mahaifinta suke da horon yaki irin na mu ba. Koda jin wannan tambaya sai Himras ya bushe da dariya sannan ya dubi Yanma ya ce " In banda abinka ai ranar da zan ziyarci su Sharilat zan gane gaskıyar wannan al'amari, kai dai kawai ka je ka kwanta domin huce gajiyar dake tattare da kai, tunda a yanzu duhun dare ya kawo kai ni zan ɗan shaƙata a nan. Koda jin hakan sai yarima Muzairaf ya miƙa tsaye tsam! Ya taka da kafafunshi ya nufi kofar fita daga lambun ya ną mai waigen mahaifinshi. Koda ficewar shi Ysai Sarki ya mike tsaye zumbur! Ya dunga kai komo a cikin lambun cikin matuƙar tashin hankali tamkar zai fashe da kuka. Bakomai ne ya sanya Himras ya shiga damuwa a lokacin da yarima Muzaifar ya sanar da shi sunan wannan Jarumar da mahfinta ba, Fa ce a yanzu ya gano cewa Kuhairu ɗan uwanshi ne wanda ya sanya a ka kashe ya ɗare kan karagar mulkin shi. Abin tambaya a nan shi ne ya aka yi Kuhairu da matar Hashmilat suka rayu har suka samu Haihuwa bayan cewa ya tabbatar an yi musu kisan da baza su iya ci gaba da rayuwa ba. Abu na farko da ya faɗo Himras a rai shi ne tabbas idan a ka yi sakaci har Yarima ya gano ɓoyayyen sirrin dake tsakaninsa da tsoho Kuhairu lallai za a samu babbar matsala, ya zamana dole ka gana da Kuhairu a wannan dare. Sa'adda Sarki Himras ya zo nan a tunaninshi sai ya runtse idanunshi ya karanta Ɗalasiman tsafi faruwar hakan ke da wuya sai ya ɓace ɓat daga lambun tamkar bai taɓa wanzuwa ba. ***** Dalilin ƙulluwar gaba tsakanin Sarki Himras da tsoho Kuhairu kuwa shi ne. Sarki saruful-uzwar ya kasance ƙasaitaccen Sarki ya shara asanin dalisiman tsafi ya na da tarin dukiya dangin lu'ulu'u u dadin daɗawa kuma ya kasance sadauki mai tarwatsa maza a filin daga. Ya na da matar aure mai suna Muzaira ta haifa masa 'ya'ya guda biyu Yarima Kuhairu shi ne babba sannan a ka haifo Yarima Himras a rayuwar Sarki Saruful-uzwar babu abinda yake so sama da waɗannan ' ya'ya na shi kasancewar ya na ganin cewa su kaɗai ne suka rage ma shi a cikin zuri'arshi. Mutanen ƙasar Darul-kushur suna mutukar kaunar Sarki Sariful saboda gudanar da mulkinshi bisa adalci babu cutarwa. Hatta Sarakunan dake maƙwaftaka da kasarshi suna jin dadin mu'amala da shi, domin ko wani sarki ya yi niyyar zaluntar wani, sai Sarki Sarifu yana kai ma shi ɗauki. Wannan dalili ya zaman lafiya da kwanciyar hankali hankali suka mamaye. Masana tarihin duniya ke kiran Nahiyar da suna Mufrad, ma'ana ƙasashen sun zama bisa turba ɗaya. Yarima Himras da Kuhairu sun ta so cikin jarumtaka ta ban mamaki domin tun suna yara koda 'yan tsirarun abokan gaba suka kawo farmaki suke tarar su su gwabza yaƙi samu nasara a kansu. Kasancewar Sarki Sarifu shekarunsa sun ja tsufa ya fara riskarshi ba zai iya bawa su Yarima horon yaƙi ba, Sai Ya tura su wani babban birni da ake horar da mayaƙa sai da suka shekara a shirin sannan suka dawo gida. A wannan lokaei sai ya zamana sun cika ZARATAN MAYAKA da babu kamarsu. Domin akwai wata rana da wani hatsabibin Sarki da ya zo kasar domin ya raba Sarki Saruful-uzwar da karagarshi, Yarima Kuhairu da Himras kaɗai suka yaƙi Sarkin da rundunar shi basu bar mutum ɗaya ya tsira da rayuwarsa ba. Lokacin da Sarki Sarifu ya ga cewa shekarun shi sun ja tabbas ajali zai iya zuwa masa akowanne lokaci sai ya karkata ga Yarima Kuhairu a matsayin mai jiran gado. Lokacin da Yarima Himras ya ga cewa mahaifinsu ya zaɓi ɗan uwanshi Yarima Kuhairu a matsayin mai jiran gado sai baƙin ciki da ƙyasi suka mamaye zuciyarshi, Amma sai ya bar abin a ranshi bai bayyana ba. Amma kullum sai ya yi kukan baƙin ciki kuma ya ƙudiri aniyar in dai ya na numfashi a doron ƙasa, ba zai bar ɗan uwanshi Kuhairu ya gaji mahaifinsu ba. Bayan shekara ɗaya da dawowar su yarima Himras sai Sarki Sarifu ya kamu da matsananciyar rashin lafiya ya zamana sai an kwantar an tayar, Sai hankalin Yarima da mahaifiyarsu ya Ɗugunzuma bisa ganin halin da mahaifinsu yake ciki, nan fa suka bazama nemo masa magani amma kullum cuta ƙara gaba ake yi. Wata rana Yarima Kuhairu da Himras suna zaune a gaban mahaifinsu a cikin turakarshi suna kallon shi suna masu zubar da hawayen. A na cikin wannan hali ne sai suka ji mahaifinsu ya yi gyaran murya ya ce, "Ya ku 'ya'yana ku matso kusa gare ni. Koda jin hakan sai duk su biyun suka cika da matuƙar mamaki domin a iya saninsu rabon da Sarki ya buɗi baki ya yi magana yau tsawon wata uku ke nan ko wani abu yake son faɗa sai dai ya yi nuni da hannu ko da baki. Himras da Kuhairu suka matsa kusa da mahaifinsu wanda ke kwance bisa kan gadon sarautar ta yadda suna iya jin numfashin juna domin su ji abinda zai sanar da su. Sarki Sarifu ya yi gyaran murya a karo na biyu sannan ya buɗi baki da ƙyar ya na duban Kuhairu, Himras ya ce. "Ya ku 'ya'ya na abin alfaharina ku yi sani cewa na ji ajikina wannan cuta tawa da ta same ni bata ta shi ba ce, kai Kuhairu kai ne babba dole kai zaka gaji KAMBUN MULKI na domin bisa al'adar wannan ƙasa babban ɗa shi ne ke gadar mahaifinshi. Sa'adda sarki Sarifu ya zo nan a Zancenshi sai tari ya turnukeshi da ƙyar ya samu tarin ya tsaya ya ci gaba da ce wa. "Ya ku 'ya'yana ina mai neman alfarma a wajenku da ku ci gaba da tafiyar da wannan ƙasa bisa adalci da tausayawa ku kasance masu kyautatawa mu'amala tsakanin ku, ka da kwaɗayin mulki da na dukiya ya sanya gaba a tsakaninku, kai kuma Himras ina so ka zama mai biyayya ga ɗan uwanka domin rayuwarku ta kasance mai kyau. A yanzu zan baku dukkanin sirrikan tsafina domin su zame muku kariya. Gama faɗin hakan ke da wuya sai Sarki ya sanya hannunshi na dama a na Yarima Kuhairu na hagun a na Himras suka ƙanƙame juna. Faruwar hakan ke da wuya sai wani irin farin haske ya dunga fita daga sarkin Sarifu yans shiga hannayensu yarima. ko da hasken ya kammala shiga jikinsu yarima sai Sarki Sarifu yana kama kakarin mutuwa. jini ya dunga fita daga bakinshi, Nan take gagarumin karfi mai karfi ya shige su tamkar za su iya iya tunkarar Mayaƙan duniya. Faruwar hakan ke da wuya sai jikin Sarki ya sandare, komai na ya daina motsi kuma idanunshi suka ƙafe alamar rai ya yi halin shi. Koda ganin hakan sai su Yarima Kuhairu suka fashe da kukan baƙin ciki su na masu rungume gawar mahaifinsu. A dai dai wannan lokaci ne mahaifiyarsu ta rugo izuwa cikin turakar a dimauce bisa jin kuka da ta yi, Ya yin da ta isa inda su Yarima suke ta ga halin da suke ciki, sai ita ma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Su ukun suka ci gaba da rusa kuka kamar ba za su daina ba. Al'amarin da ya haddasa hargitsewar gidan sarautar ke nan mutane su ka dunga guje guje-guje da ifice-ifice cikin tashin hankali, a wannan rana gaba ɗaya mutanen kasar Darul-Kushur sun kasance cikin tsananin baƙin ciki da jimamin mutuwar Sarki Sariful-Uzwar Su kansu manyan da kana nan sarakuna dake makwabtaka da shi sun shiga cikin tararrabi, Domin suna ganin sun yi babbar hasara. Kuma gaba ɗayansu sun halarci bikin binne Sarki Sarifun. Bisa al'adun kasar Darul-Kushur, Ranar da Sarki ya mutu kashe gari ake bikin naɗin sabon sarki." Hakanne ya sanya tun a daren da Sarki Sarifu ya mutu bayan binne shi a ka yi shela izuwa ƙasashe da birane na naɗin sarautar Yarima Kuhairu. Kashe gari da sassafe a ka ta shi da shiryen nadin sarauta Yarima Kuhairu, nan fa birnin ya cika ya batse da baki manya da ƙanana a Attajirai da sarakuna. Bayan an gama shiri tsaf fada ta cika maƙil da jama'a sai ga Yarima Himras da Kuhairu sun shigo fadar, suna sanye da suturu iri daya sak hatta takalmi da hulunan dake kansu iri ɗaya ne, kuma su na riƙe da wata sanda da ka yi mariƙinta ta siffar damisa. A wannan lokaci fusakunsu cike da annuri suna fira a cikin Nishaɗi. koda shigowarsu sai fadar ta rude da hayaniya kowa na faɗin albarkacin bakin shi, ba a samu damar yin shiru ba har sai da su Yarima suka zauna a kan kujerun da a ka tanadar musu. Shiru ne ya mamaye fadar tamkar an yi ruwa an ɗauke daga can sai yarima Kuhairu miƙe tsaye ya fuskanci jama'a ya yi gyaran murya ya ce. "Da farko dai ina yiwa dukkannin mutanen da suka halarci wannan fada mai albarka, na yi mutukar jin daɗi bisa gani yadda manyan sarakuna, attajirai, talakawa da sauran mutanen gari su ka halarci wannan naɗin sarauta tawa. Sannan daga bisa ni ina mai taya ' yan uwa jimamin mutuwar mahaifin mu Sarki Sarifu, ina fatan mutanen wannan fada suna mutuƙar kwaɗayin kasancewa sabon sarkinsu a yau. Ya yin da Yarima Kuhairu ya zo dai dai nan a Zancenshi sai fadar ta sake ruɗewa da suratai karo na biyu mutane Suna masu nuna goyan bayansu a kan Kuhairu ya zamo Sarkinsu. Koda Yarima Himras ya ga yadda jama'ar fadar ke nuna tsananin kaunar ɗan uwanshi ya zamo Sarkin su, sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone yaji tamkar ya zare takobi ya afkawa Kuhairu da yaƙi. Kuhairu ya ɗaga hannunshi sama mutane suka yi shiru sannan ya koma bisa kujerarshi ya zauna. Faruwar hakan ke da wuya sai ma'ajin sarauta ya gabato da alƙyabba da kambun sarauta na Sarki, Domin bisa al'ada dazarar Sarki ya mutu za a cire kayan sarautar shi a damƙa a hannun ma'ajin sarauta, sai ranar da za a yi naɗin sarauta sannan ma'aji ya kawo su fada. Ba tare da ɓata lokaci ba Yarima Kuhair ya sake miƙewa tsaye waziri ya ƙarɓi kayan dake wajen Ma’aji sannan ya sanya Yarima alkyabbar ganin da KAMBUN Mulkin, Nan take Yarima ta taka da kafafunsa har inda karagar Sarki take ya hau ya Hakimce. Faruwar hakan ke da wuya sai 'yan majalisar kasar su sha biyu suka durƙusa ƙasa su na masu sunkuyar da kawunansu a gaban yarima Kuhairu. Nan take jama'ar fadar suka kaure da shewa gami da yiwa Yarima Kuhairu jinjina, Nan take zuciyar Yarima Himras ke zaune a gefe guda ta ci gaba da tafarfasa tamkar Zata ƙone, kuma ya cika da mutukar baƙin ciki mara mara Misaltuwa, amma saboda gudun kada mutane su lura da halin da yake ciki sai ya saki fuskarshi ya dunga shewa da tafi ga Kuhairu. Bayan kammala naɗin sarauta sai kuma a ka shiga hidimar ciye- ciyen abinci da abin sha amma da a ka fara wannan walima sai Yarima Kuhairu ya miƙe tsaye daga kan karagar mulkinshi, ya taka da kafafunshi har inda Yarima Himras ke zaune ya rike kafaɗunshi ya tashe shi ya riƙe hannun shi har inda kujerar mulkin take suka zauna tare sannan a kawo musu abinci da abin sha suka ci tare suna Firarsu cikin nishaɗi. A wannan rana dai haka aka yi gagarumar walimar naɗin sarautar Yarima. Mutane ba su bar fada ba sai da Sarki Kuhairu da Yarima Himras suka yi suka shiga gidan sarauta sannan mutane suka bar fadar. Sarakunan da suka halarci bikin Suka fara shirin tafiya izuwa biranen su. *** Ƙayataccen lambu ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan marmari da furanni, Wata irin Daddaɗar iska na kaɗawa tsirrai da bishiyu na yin rangaji abin gwanin ban sha'awa. Idan mai mai kallo ya kai duban shi ga ɓangaren yamma a lambun zai yi ido biyu da waɗansu ƙayatattun kujeru, a tsakiyar su an ajiye wani madaidaicin teburi na azurfa mai ɗauke da kofunan zinare, Zaune akan kujerun waɗansu zaratan samari ne guda Biyu, Suna sanye da tufafi na ma'abota sarauta. Duk irin duhun dare, da na bishiyun lambun, Kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci cewa sun kasance ZARATAN MAYAƘA masu dakakkiyar zuciya. Ba waɗansu ba ne samarin ba face sarki Kuhairu da Yarima Himras, Kuhairu ya ɗauki dogon kofin dake kan teburin ya tsiyaya ruwan inibin a cikin ƙananan kofuna guda biyu ya ɗauki ɗaya ya miƙawa ɗan uwanshi Himras, ya ɗauki ɗayan, A lokaci guda suka kai kofunan Izuwa bakunan suka shanye ruwan inibin. Bayan Shirun da ya wanzu a tsakanin su sai sarki Kuhairu yayi gyaran murya sannan yace"Yakai Himras kayi sani cewa Haƙiƙa har abada kai ɗan uwana ne na jini, Yanzu Gashi an naɗani a matsayin halifan Mahaifinmu, Shin wace shawara za ka bani domin ganin nayi jagorancin wannan ƙasa tamu mai albarka?. Koda jin wannan jawabi daga bakin Kuhairu sai Himras ya yi shiru yana mai sunkuyar da kanshi ƙasa tamkar mai tunani wani abu, Daga bisani kuma sai ya ɗago da kanshi sama ya dubi Ɗan uwanshi yace. "Ya ɗan uwana ina mai matuƙar farin ciki bisa zamowarka matsayin halifan Mahaifinmu, Shawara ta Farko da zan ba ka ita ce, Wajibi ne a hukunta dukkan mai laifi tsakanin talakawa da Attajirai, shawara ta biyu bawa mayaƙa horon yaƙi, tare da sabunta makaman yaƙi, Domin tunkarar HARIN BAZATO. Karɓar Haraji a hannun 'yan kasuwa domin gudanar da aiyukan cigaban al'umma, Abu na ƙarshe shine aure, Aure shine cikar darajar kowane BASARAKE. Koda jin waɗannan shawarwari sai sarki Kuhairu ya cika da matuƙar farin ciki maral misaltuwa, ya dubi Himras cikin Tattausan murmushi yace"Haba ɗan uwana ko ka manta ne cewa a rayuwata ban taɓa yin budurwa ba, Hasalima bana shiga sabgar mata, taya zan iya gano macen da ta dace na aura. Himras ya bushe da 'yar ƙaramar dariya sannan yace"Kwantar da hankalin ka yakai ɗan uwana na amince maka ka auri masoyiyata na tabbata cewa zata soka fiye dani kuma idan ku kayi aure za'a samu zuri'a mai inganci. Cike da matuƙar mamaki maral misaltuwa Kuhairu ya dubi yarima yace " kana so ka ce mini ka Amince na auri masoyiyarka sharzila 'ya ga waziri Zuraisu, wacce ku ke soyyayya tun kuna yara ƙanana?. Himras ya gyaɗa kai yace " ƙwarai kuwa haka nake nufi, ya ɗan uwana kayi sani cewa babu wani abu da na mallaka a wannan duniya face na baka shi, Ni da kai duk abu ɗaya ne, Domin uwa ɗaya uba ɗaya yafi ƙarfin wasa. Sa'add yarima yazo Nan zancenshi sai sarki Kuhairu ya cika da matuƙar farin ciki maral misaltuwa, bai san sa'adda ya tashi daga kan kujerarshi ba yaje ya rungume yarima, su duka biyun suka fashe da kukan farin ciki, Tsawon daƙiƙa goma suna rungume da juna sai daga bisani ne Kuhairu ya janye jikinshi daga na Yarima ya riƙe hannun shi suka nufi hanyar da zata fitar dasu daga lambun, sai da su ka zo wata mararraba sannan kowanne yayi nashi ɓangaren. Lokacin da yarima Himras ya kaɗaita a cikin turakarshi sai kawai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta. Sai da yayi dariyar ta isheshi sannan daga bisani ya tsuke bakinshi ya karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi, ya rikiɗa Izuwa wani kyakkyawan tsuntsu ya ratsa rufin turakar tamkar yadda danshi ke ratsa ƙasa ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba. A cikin wani ƙayateccen lambu ya bayyana yana mai fitar da sautin wani kuka mai Daɗin saurare, jim ƙaɗan da aiwatar da hakan sai ga wani Dattijo ya riƙo hannun wata kyakkyawar budurwa sun shigo lambun da zuwa suka samu waɗansu ƙayatattun kujeru suka Hakimce, kyakkyawan tsuntsun ya rikiɗa izuwa surar yarima Himras yaje ya zauna abinda kujerar dake fuskantar mutane biyu. Kyakkyawan murmushi yarima ya sakarwa budurwar ita ta mayar mashi da martani. Ita dai kyakkyawar budurwar ta kasance mai matsakaicin tsawo da kauri, tana da dara-daran idanu farare ƙal, tamkar tacecciyar Madarar shanu ƙwayar cikin su sun yakance baƙaƙe siɗik, masu ɗaukar hankalin duk ɗa namiji mai hankali, Batun diri da ƙira kuwa tamkar ita ce ta tsara kanta yadda take buƙata, Ba wata ba ce wannan kyakkyawar halitta ba face gimbiya sharzila'ya ga waziri Zuraisu. Bayan shiru da wanzu a tsakanin su na ɗan wani lokaci sai waziri ya buɗi baki ya dubi yarima yace "ya sarkin ƙasar Darul-kushur na gobe shin wane labari kake tafe da shi?, Daga yadda fuskarka ta bayyana akwai bayani mai kyau, kasan masu iya magana na cewa labarin zuciya a tambayi fuska". Yarima yayi gyaran murya yace " Ya waziri kayi sani cewa Haƙiƙa haƙanmu ya kusa cimma ruwa, Nan da lokaci ƙafan idan na samu goyan baya daga gareku, Ya sirikina kayi sani cewa a daren jiya na gana da ɗan uwana, kuma na amince mashi ya auri masoyiyata sharzila. Cikin alamun fushi waziri ya dubi yarima yace"Wannan wace irin maganar banza ce ka ke yi? Da jin hakan sai Yarima ya bushe da dariya. Al'amarin da yayi matuƙar bawa waziri da gimbiya mamaki kenan suka ƙura ma shi idanu, domin su ga iya gudun ruwan shi. Lokaci guda yarima ya haɗe rai sannan yace"ya sirikina kayi sani cewa tun lokacin da mahaifinmu ya rasu mun mallaki dukkan sirrikan tsafinshi, Bisa binciken da na gudanar a halarar tsafina na gano cewa babu wata hanya da zan bi domin kawar da ɗan uwana face ta hanyar makirci. Bisa wannan dalili ya sanya na nuna goyon bayana akan ya auri masoyiyata sharzila, domin da ita ce kaɗai zata iya samun nasarar sato mini gurin tsafin sarauta wanda babu wani mahaluki da zai mallake shi face duk wata halitta dake wannan birni tayi biyayya a gare shi, Ya waziri kayi sani cewa da yawa daga cikin sarakunan duniya ƙarfin rundunar mayaƙa, shirin tsafi ba ya kawar dasu face ta hanyar shirya musu makirci da matayen auren su, Abinda nake muradi kawai shine masoyiyata sharzila ta so ɗan uwana Kuhairu so mai tsanani domin samun nasara akan Abinda mu ka sanya a gaba. Kaga kenan da zarar sharzila ta auri Kuhairu Nan da wata guda zan zamo sabon Sarkin birnin Darul-Kushur tare da ɗaurin aurena da gimbiya sharzila. Sa'adda yarima yazo nan zancenshi sai waziri da gimbiya suka cika da matuƙar mamaki gami da farin ciki maral misaltuwa, Batare da wani jinkiri ba su ka rabu akan cewa gobe yarima zai sake bayyana ya sanar da su abinda yake wakana. Bayan kammala hakan sai Yarima ya sake rikiɗa Izuwa wannan kyakkyawan tsuntsu ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa. *** Kamar yadda yarima Himras ya faɗa haka al'amarin yakasance, A cikin Abin da bai gaza mako huɗu ba, soyyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin sarki Kuhairu da gimbiya sharzila, Har yazamana cewa an sanya ranar da za'a ɗaura musu aure. A iya tsawon waɗannan kwanaki a kowane dare sai Yarima ya bayyana a lambun shaƙawar waziri da 'yarshi sharzila, sun tattauna akan abubuwan da zasu aikata. Lokacin da labarin soyyayyar sarki Kuhairu da gimbiya sharzila ya watsu a gari, sai jama'a suka cika da matuƙar mamaki, su na masu tambayar kansu cewa, Shi ya akayi sharzila ta koma soyyayya da Kuhairu alhalin tun suna yara ƙanana suke matuƙar juna ita da yarima Himras, Shin ko kwaɗayin mulki ne yasanya ta aikata hakan, Amma da su ka ga Yarima Himras bai nuna damuwa ba sai ma farin ciki, sai suka cire dukkan shakku daga zukatansu. A cikin kwanaki biyar kacal sarki Kuhairu ya aika jakadu Izuwa ƙasashen dake nahiyar, akan yana gayyatar su ɗaurin auren shi. A ranar ɗaurin aure kuwa, ƙasar Darul-kushur ta cika ta batse da jama'a babu masaka tsinke, saboda matuƙar yawa wasu ma a bayan gari suka tsaya, basu samu damar shigowa wajen ɗaurin auren ba. A wannan rana anyi shagalin bikin da ba'a taɓa yin kamar shi ba tsawon wanzuwar ƙasar Darul-kushur, saboda mutum koda ruwa ya ƙasa sai ya samu arziƙi. Sarki Kuhairu da Yarima Himras kuwa sai su dunga rabon dukiya da suturu ga talakawansu, bayan an kammala shagalin biki, kowa ya koma gidan shi Lafiya cikin farin ciki saboda arziƙin da ya wadata. Sarki Kuhairu da Amaryarshi sharzila suka tare cikin farin ciki, Tun daga wannan rana sarki Kuhairu ya cigaba da gudanar da mulkinshi cikin kwanciyar hankali da annashiwa, Sannu-Sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba, sai gashi sarki Kuhairu ya cika shekaru gida batere da Amaryarshi ta samu Haihuwa ba, Al'amarin da yayi matuƙar jefa shi cikin damuwa kenan, kuma ya yanke shawarar ƙara aure. Abin da Kuhairu bai sa ni ba shine, A duk lokacin da zai Kusanci sharzila, sai Yarima Kuhairu ya bayyana cikin siffar duhu ya samar da wata mace ta sihiri mai matuƙar kama da sharzila sannan ya ɗauke sharzila suje su sheƙe ayarsu, shi kuwa yana saduwa ne da wannan mace ta sihiri. Abin da yasanya Kuhairu bai gano hakan ba shine saboda bisa ƙa'idar tsafin su, ɗayansu ba shi da ikon gudanar da bincike a kan ɗan uwanshi. Lokacin da Sarki Kuhairu ya buƙaci ƙara aure, sai wani daga cikin fadawanshi ya amince ma shi ya auri 'yar shi Hashmila. Bayan mako guda da ɗaura auren, sarki Kuhairu na zaune da uwar gidanshi sharzila, sharzila ta ɗora hannunta akan ƙafafun mai gidan ta ta ƙura ma shi idanu sannan ta dubeshi cikin alamun damuwa tace"Ya uban 'yayana shin yaushe ne burinmu zai cika na samun magaji, zan fi kowa farin ciki idan aka ce yau jinana ne ke mulkin kasar Darul-Kushur?. Koda jin wannan batu sai idanun sarki Kuhairu ya cika da matuƙar damuwa ainun ya buɗi baki yace"ya mafi soyuwa agareni kiyi sani cewa haƙiƙa na fiki damuwa akan wannan hali da muke ciki, Babban abinda ke Ɗugunzuma hankalina shine halarar tsafina ta gaza bayyana mini mafita. Koda jin wannan batu daga bakin Kuhairu sai sharzila ta dubeshi cike da damuwa ƙarara tace" ya sanyin idaniyata zan kasance mai roƙon abin bauta gunki sabrat akan ya cika burinmu. Yanzu abinda ya kamata shine ka shiga kewaye kayi wanka ka huce gajiyar dake tare da kai, sannan kayi kalaci. Koda jin hakan sai sarki Kuhairu ya miƙe tsaye ya cire alƙyabbarshi ya nufi kewayen wanka yana mai waigen sharzila suna yi wa suna murmushi mai tattare da alamar tsantsar so da ƙauna. Koda shigewar sarki Kuhairu izuwa kewayen,sai sharzila ta miƙe tsaye zumbur ta sanya hannun a cikin alƙyabbar sarki ta ɗauko wani gurin tsafi, A dai-dai wannan lokaci ne Yarima Himras ya bayyana a turakar ya riƙe hannunta su ka ɓace bat!. tamkar basu taɓa wanzuwa ba. A cikin lambun shaƙawar waziri suka bayyana, batare da ɓata lokaci ba sharzila ta ɗauko wannan gurin tsafi na sarki Kuhairu ta miƙawa Himras ya ƙarɓa ya saka a damtsen hannunshi na hagu, Faruwar hakan ke da wuya sai alƙyabba,kambu gami da kwagiri suka bayyana a jikinshi. Nan take sharzila da yarima suka bushe da dariyar mugunta tamkar ba zasu daina ba, sai daga bisani ne Yarima Himras ya buɗe baki ya ƙwallawa waɗansu dakaru kira,Dakarun suka bayyana gareshi suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa. Yarima ya dubi wani garjejen ƙato wanda da ala shi ne shugaban su yace da shi "ya kai Rauzub kayi sani cewa bakomai ne yasanya na kira ka nan ba sai domin ina so ka ɗebi dakaru har Izuwa turakar ɗan uwana Kuhairu, ka tabbatar da cewa ka hallaka shi tare da Amaryarshi Hashmila. Rauzub ya risina yace"An gama ya shugabana, Kafin ya sake furta wani abu yarima Himras ya miƙa hannunshi na hagu Izuwa sama yana mai karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi sai waɗansu masuna guda biyu suka bayyana akansu. Kawai sai ya miƙawa Rauzub ya dube shi karo na biyu yace "Idan ya tabbata ka yi amfani da waɗansu masuna wajen hallaka ɗan uwana Kuhairu da Amaryarshi, Nayi maka alƙawarin zan ɗaga darajar ka daga shugaban dakarun gidan waziri Izuwa shugaban dakarun wannan ƙasa baki ɗaya. Koda jin wannan batu sai Rauzub ya miƙe tsaye ya huce gaba, dakarunshi na biye da shi su ka fice daga lambun, Nan take Yarima Himras da sharzila suka bushe da dariyar mugunta, A dai-dai wannan lokaci ne waziri Zuraisu ya shigo lambun yana mai taya su dariyar. **** Lokacin da sarki Kuhairu ya fito daga kewayen wanka sai ya nufi gadonshi domin ya ɗauki alƙyabbarshi, Nan take yaga babu ita koda ya shafa damtsenshi Nan take yaji babu gurin tsafinshi, Nan take ya tabbatar dacewa garin nashi na cikin alƙyabbar. Abin tambaya a nan shi ne wane ne ya ɗauke alƙyabbata alhalin babu kowa da yake da ikon shigowa wannan turaka face Ni da uwar gidana sharzila, Shin koda sharzila ta aka haɗa baki aka ci amanata. Amsar tambayar da ya ka sa bawa kanshi kenan hawayen baƙin ciki suka zubo daga idanuwanshi Izuwa kan kuncinshi,. A dai-dai lokacinne ya jiyo ihu da kururuwar dakaru, ko da jin hakan ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gefen gadonshi ya falfala da azababban gudu yana mai ficewa daga turakarshi hawaye na cigaba da zuba daga idanuwanshi. Yana cikin wannan hali ne ya hango dakarun sumame sun rugo Izuwa inda yake ɗauke da miyagun makamai suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Ko da ganin hakan sai ya zare wani kwari da baka a gadon bayanshi ya shiga harbin dakarun cikin gwaninta, kafin cikae daƙiƙa ashirin ya hallaka dakaru fiye da arba'in. Ko da dakarun su ka ga irin mugun kisan da kuhairu ke yi ma su, sai suka firgita ainun, Domin sun san cewa suna kusantarsu ne, amma da suka tuna wanda ya umarce su da hakan sai suka harzuƙa ainun. Kafin cikar daƙiƙa Hamsin Kuhairu ya hallaka fiye da mutum ɗari, koda ganin hakan sai kuhairu ya mayar da bakanshi Izuwa gadon bayanshi ya zare Takobinshi ya daka wawan tsalle tamkar an janye shi da ƙugiya ya sauka a tsakiyar dakarun ya afka musu aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni,Ban tsoro da ban al'ajabi, ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu gami da hargowar dakarun ta cika dodon kunne. Duk in da kuhairu ya sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga, jini ya dunga kwaranya,tsartuwa yana malala a ƙasa. Tabbas sarki Kuhairu ya cika GWARZON MAYAKI mai ƙarfi na Allah ya isa, ina da ace mutum ya na tsaye a wannan waje lokacin da Kuhairu ke raba kai da gangar jiki da kafin takobinshi dole ya jinjina ma shi ya tabbatar da cewa ya cika sarkin sadaukai. Ga shi dai ƙiri-ƙiri dakarun suna kai ma shi miyagun hare-hare, kuma suna ƙara tuttuɗowa daga gidan sarauta, Amma basu samu nasarar koda lakutar jikin shi ba. Dukkan abin da ke wakana tsakanin kuhairu da dakarun sumame, yarima Himras, waziri Zuraisu da gimbiya sharzila sun gani a cikin madubin tsafin yarima a lokacin da suke zaune a lambun shaƙawar waziri. Yayin da suka ga yadda Kuhairu ke samun nasara sai hankulansu suka ɗugunzuma ainun, Domin a cikin abin da bai gaza daƙiƙa Hamsin ba yana kashe dakaru fiye da guda ɗari, Tabbas nan da lokaci kaɗan zai hallaka su ba ki ɗaya. Kawai sai yarima ya buɗe bakinshi ya karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi, yana gama yana kammalawa sai waɗansu tsuntsaye na sihiri suka bayyana a sararin samaniya, Su dai tsuntsayen sun sha Bamban da waɗanda idanu su ka saba gani. Su na girma tamkar mikiya, bakunan ya furzar da wani irin dafi, koda bayyanar su sai kawai su ka kaɗa fuka-fukansu suka durfafi gidan sarauta cikin matsanancin gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya. Nan take Yarima, waziri haɗi da sharzila suka taƙarƙare su ka bushe da dariyar mugunta tamkar ba zasu daina ba. **** Shirye yake cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini, kuka kuma ya rufe fuskarshi da rawani idanunshi kaɗai ake gani, a gadon bayanshi yana rataye da waɗansu dogayen ma su guda biyu. Ba wani ba ne wannan mayaƙi ba face sadauki Rauzub wanda yarima Himras ya umarci ya hallaka sarki Kuhairu da Amaryarshi Hashmila. Tafe a cikin wata hanya ta musamman yana ƙara kunna kai Izuwa ciki kai da gani kasan cewa hanya ta musamman da ba kowa ne ya san da ita ba, domin badakare koda guda ɗaya. Lokacin da ya shafe tsawon rabin Sa'a yana tafiya a dai-dai wannan lokaci ne ya fara hango katangun turakar sarki Kuhairu, Don haka sai ya ƙara azama. Koda yazamana cewa saura taku goma tsakanin shi da turkar, kwatsam! bazata Babu tsammani sai ya hango wani badakare ya bayyana tsulum a gabanshi, Badakaren yana shirye cikin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke ya rufe fuskarshi da baƙin yanki a kafaɗarshi yana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi. Nan fa Rauzub ya cika da matuƙar mamaki maral misaltuwa, abin da ya ba shi mamakin shine wane badakare yasan cewa ya biyo ta wannan hanyar har yayi GABA DA GABA da shi. Koda Rauzub yazo nan a tunaninshi sai ya fusata ainun ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a damtsenshi ya falfala da azababban gudu Izuwa kan Badakaren yana ihu da kururuwa mai firgitarwa. Koda ganin hakan sai Badakaren yayi koyi da shi ya zare Takobinshi ya ruga gareshi, Yayin da su ka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni,ban tsoro da ban al'ajabi. Duk sa'adda takubbansu su ka haɗu da juna sai dai kaji sun ba da sauti ƙal ƙal ƙal!, tartsatsin wuta ya tashi, Babu abin da zai burge mutum ya kuma ba shi sha'awa ga jaruman biyu face yadda suke kaiwa junansu hare-hare cikin mutuƙar zafin nama, Sai da suka lalata makaman dake hannun su, su ka yi jifa da su suka ciri wasu sabbin a jikin su suna cigaba da kaiwa junansu hare-hare. **** A cikin gidan sarauta kuwa sarki Kuhairu ya cigaba da ragargazar dakarun babu sassauci, lokacin da Sa'a ɗaya ta cika a dai-dai lokacinne ya hallaka mayaƙan ba ki ɗayan su. Kwatsam! Sai ya hango waɗansu tsuntsaye sun bayyana a sararin samaniya, idan ɗayansu ya sauka a turba sai kaji tamkar an jefar da ɗan maraƙi, bayan sun kammala sauka ne aka fara kallon kallo tsakanin su da Kuhairu. A iya tsawon rayuwar Kuhairu koda a tarihi bai taɓa gani ko jin labarin tsuntsaye ma su kwarjini irin su ba, Abin tambaya anan shine ya aka yi tsuntsayen su ka ketare tsoron dake gidan sarautar, bayan cewa fiye da shekaru goma hakan bai taɓa faruwa ba. Sa'adda kuhairu yazo Nan a tunaninshi sai ya sake zurfafa cikin Kogin tunani, Nan take ya fahimci cewa tabbas ɗan uwanshi Yarima Himras ne ya aiko waɗannan tsuntsaye, Domin shi ne ƙaɗai sihirin tsafin shi zai yi tasiri akan nawa. Ko da yazo nan a tunaninshi sai hawayen su ka kwaranya daga idanunshi yana mai cewa yanzu a ce ɗan uwana Himras ne ke farautar rayuwata saboda kwaɗayin mulki, haƙiƙa mulki musiba ne. Kawai sai kuhairu yayi jifa da Takobinshi da ta rine da JININ SADAUKAI, Ya ciri sabuwa a jikinshi ya afkawa tsuntsayen aka ruguntsume da azababban yaƙi. Ana fara wannan gumurzu ne duka ɓangarorin biyu su ka fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba'a abinci mai nauyi ba. Sai da aka shafe tsawon Sa'a guda ana wannan ɗauki badaɗi babu alamun nasara, Abinda sarki Kuhairu bai sani ba shine, Takobin dake riƙe a hannun shi yana sana'anta ta ne da shirin tsafin da Mahaifin su ya ba shi, haka ma tsuntsayen da ya ke gumurzun da su yarima Himras ya samar da su ne da sihirin. Bisa hakan ya sanya ya kasa samun nasara akan tsuntsayen. Lokacin da sarki Kuhairu ya fahimci cewa tabbas wankin hula zai kai shi dare, sai kawai yayi wurgi ta takobinshi ya shiga yaƙar tsuntsayen da ƙarfin damtsenshi, Nan fa labari ya sha Bambam yana zamana cewa duk sa'adda kuhairu ya naushi wata gaɓa a jikin su sai kaji tayi ƙara ruƙus! Ƙas ta karye, Nan fa tsuntsayen suka dunga yin kururuwa suna faɗuwa ƙasa magashiyan, waɗansu kuma matattu. Amma su ma tsuntsayen sun yi ma shi miyagun raunuka da faratansu, kafin cikar daƙiƙa hamsin ya hallaka tsuntsayen, A wannan lokaci jiri na ɗibarshi tamkar ya sha barasa ya bugu, Amma saboda juriya irin ta JARUMAN DUNIYA a haka ya cigaba da tafiya yana mai Kusantar ɓangaren turakar Amaryarshi Hashmila. Aɓangaren Sadauki Rauzub da wannan Badakaren kuwa, tuni labari ya sha bamban, Domin yanzu yaƙi ya canza salo Badakaren ba ya iya mayar da martani, Sai dai ƙoƙarin kare kanshi. Ana cikin wannan gumurzu ne Rauzub ya kaiwa wani badakaren hari, cikin matuƙar zafin nama Badakaren ya sunkuya ya kaucewa harin, amma duk da hakan sai da takobin Rauzub ta zaftare wani yanki da ya rufe fuskarshi. Nan take fuskar Badakaren ta bayyana a fili ƙarara, Yayin da Rauzub yayi arba da fuskar mahayin sai ya cika da matuƙar mamaki. Abin da ya ba shi mamaki shine ba wani bane Badakaren ba face Hashmila, Rauzub ya bushe da dariyar mugunta tamkar bazai daina ba, daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa. Ya dubi Hashmila a wulaƙance yace" Amma fa kin burgeni ainun da har kika fafata yaƙi da ni, sai dai kuma kinyi babban kuskure da ki ka kawo kanki Izuwa gareni, yanzu batare da ɓata lokaci ba zan hallaka ke mai gidan ki, domin kuwa nan da lokaci kaɗan zan zamo Sarkin mayaƙan wannan ƙasa. Kafin Rauzub ya gama rufe bakinshi, Hashmila ta tari Numfashinshi yana mai daka ma shi tsawa tace"kaiconka yakai azzalumi kuma maci amana, haƙiƙa ka tafka babban kuskure da ka ke tsammanin cewa za ka iya hallaka mu, ka yi sani cewa yarima Himras ba zai cika ma ka burinka ba, shin ko ka manta ne cewa kuhairu ɗan uwanshi na jini ya ci amanar shi, to ina ga kai karan kaɗa miya, kuma ban taɓa tsammanin kai butulu ba ne sai yau, ka da fa ka manta cewa da kai bawa ne, kuhairu ya 'yan taka ka zamo ɗa. Kuma yayi ma ka aure, ka sani cewa ramin ƙarya ƙurarre ne. Caraf! Rauzub ya tari Numfashin ta ya na mai cewa "ke ƙaramar alhaki kiyi sani, A halin yanzu tamkar yarima Himras ya zamo Sarkin wannan birni Darul-kushur, Domin ya hallaki alƙyabba,gurin tsafi haɗe da kambun sarauta na Sarki, tabbas tamkar burina ya cika ne. Caraf! Hashmila tace"Ga maza nan bisa kan ka, tana gama faɗin hakan ta yi wurgi da takobinta, ta afka ma shi da dukkanin ƙarfin damtsenta. Koda ganin hakan sai Rauzub ya bushe da dariyar mugunta ya dunƙule hannayenshi biyu ya ruga Izuwa kanta, su ka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro, suna kaiwa junansu naushi da bugu hannu da ƙafa. Ana fara wannan artabu ne Hashmila ta fara gane kurenta domin ƙarfin naushi Rauzub ya nunka nata sau huɗu, Duk sa'adda Rauzub ya gabzamata naushi sai kaga Hashmila tayi sama tamakar an janye ta da ƙungiya, Sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim, Amma sai ya miƙa tsaye zumbur. Cikin abinda bai gaza daƙiƙa ashirin ba Rauzub ya haɗa ma ta jini da Majina,tana layi jiri na ɗibarta. Wohoho! Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce ƙyan faɗa akwana ana yi, kuma idan gwani da gwani suka haɗu, juriya da naci suka game waje guda dole ne tsagwaron ƙarfin damtse yayi aiki. Ana cikin wannan artabu ne Rauzub ya shammaci Hashmila ya ƙirɓa ma ta naushi a ciki, saboda ƙarfin naushin sai da ta maku da wata katanga, sannan ta faɗi ƙasa magashiyan cikin mawuyacin hali dake tsakanin rayuwa da mutuwa. Koda samun wannan gagarumar nasara sai Rauzub ya ya zare wani mashi a gadon bayanshi ya durfafi inda take kwance yana mai yi mata murmushin mugunta, yana isa zuwa inda take ya ɗaga mashin domin ya caka mata a ƙirji. Kwatsam bazato tsammani sai Rauzub yaji waɗansu kibbau sun sokeshi a gadon bayanshi, duk da irin raɗaɗin da yake ji amma sai ya waiga domin yaya wanda ya harbeshin, Aikuwa sai yayi arba da shi ba wani bane face sarki Kuhairu ya falfalo Izuwa inda yake yana kurma ihu. Ko da ganin hakan sai Rauzub ya shafi wani gurin tsafi a damtsenshi take ya ɓace ɓat! Kuhairu ya durƙusa ƙasa bisa gwiwoyinshi yana mai tallafo wuyan Hashmila yana mai zubar da hawaye cikin matuƙar tashin hankali. Yana cikin wannan hali ne Rauzub ya bayyana a gare shi ya jefa ma shi wannan mashi, mashin ya tafi cikin matsanancin gudu yana keta iska, kafin kuhairu yayi yunƙuri mashin ya sokeshi a idanunshi na hagu, kuhairu ya kurma ihu, Cikin zafin nama ya sa Rauzub ya sake cire mashin ya caka mashi a idanunsa na dama sannan ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzu ba. Nan take Kuhairu ya sake kurma ihu a lokacin da idanuwanshi ke zubar da jini yana gani dishi-dishi, kawai sai ya miƙe tsaye ya ɗauki Hashmila ya goya ta a gadon bayanshi, ya falfala da azababban gudu Izuwa hanyar da za ta sadashi da gidan sarauta, yana cikin gudun ne ya hango dakaru fiye da dubu bisa dawakai na harbo ma shi kibbau, Amma sai yazamana Kuhairu yana Yana zillewa kibbau ɗin cikin baƙin zafin nama, Da ya ke a wannan lokaci dare yafara Kunno Kai, sai kuhairu ya dunga amfani da hannunshi yana kashe fitilun dake jikin katangun. Lokacin da kuhairu ya shafe tsawon Sa'a yana wannan gudu a dai-dai wannan lokaci ne ƙarfin gudun Kuhairu ya fara raguwa, kuma da ƙyar ya ke iya zillewa haren dakarun. Har yazamana Dakarun sun harbeshi sau bakwai a gadon bayanshi jini na zuba. Kawai sai kuhairu ya hango wata ƙorama a gabanshi, Don haka sai ya karanto waɗansu ɗalasiman tsafi yana mai nuna ƙaramar da hannun shi na hagu, take ƙormar ta ɓace ɓat!. Lokacin da kuhairu ya haure Nan take ƙoramar ta sake bayyana tayi ma shi katanga tsakanin sa da dakarun. Nan fa dakaru fiye da hamshin tare da dawakansu su ka afka ciki su na masu ihu da kururuwa mai firgitarwa. A dai-dai wannan lokaci ne Yarima Himras,waziri tare da sauran hadimanshi su ka bayyana a bisa dawakai,yarima Himras ya dubi Rauzub ya ce ka tabbatar ka cakawa ɗan uwana wannan masu da na baka? Rauzub yace "kwarai kuwa na aiwatar da komai yadda ya kamata ya shugabana. Yarima ya bushe dariyar mugunta a karo na biyu, Sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa yace" Na tabbatar da cewa ɗan uwana Kuhairu ya jima da hallaka yanzu zan shimfiɗa mulkina yadda nake buƙata. Ko da gama faɗin hakan sai Yarima yayi wuf! Ya zare wata takobi a damtsenshi ya shammaci Rauzub ya caka ma shi ita a ciki, Rauzub ya kwalla ƙara yana mai dafe raunin a lokacin da jini ke zuba tamkar an ɓalle kan fanfo, kuma ya durƙushe ƙasa bisa gwiwoyinshi. "Kana tunanin cewa zan bar ka a raye ne bayan cewa kai kaɗai ne kasan sirrin dake tsakanina da ɗan uwana, tabbas mutuwar ka ita ce dai-dai, yana zuwa nan azancenshi sai kawai ya sanya takobin ya sare wuyan Rauzub, kan na shi yayi fitar burgu, gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica! Kafin ɗaya daga cikin dakarun Rauzub yayi wani yunƙuri yarima ya afka masu da yaƙi, cikin abin da bai gaza daƙiƙa ashirin ba ya hallaka su baki ɗaya ya zubar da gawarwakin su a ƙasa. Nan take Yarima Himras da waziri Zuraisu suka ci gaba da bushe da dariyar mugunta tamkar bazai daina ba. Haka dai kuhairu ya cigaba da gudu bisa kan ingarman dokin har ya su ka samu Nasarar ficewa daga cikin gidan sarauta suka nausa Izuwa cikin daji. Su na cikin gudun ne bisa kuskure sai dokin yayi karo da wani dutse nan take ta hantsila Izuwa ƙasan wani makeken rami, Kuhairu yana mai kurma ihu, kafin su kai Izuwa karshen ramin dukkanin su sun sun sume.yayin da suka faɗa Izuwa cikin ruwan sai igiyar ruwan ta shiga gudu a da su har ta kawo su Izuwa gaɓar wani kogi. **** Al'amarin yarima Himras da waziri Zuraisu kuwa, bayan sun kammala kyalkyala dariyar, sannan yarima ya karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi suka duka biyun suka ɓace daga wajen tamkar ba su taɓa wanzuwa ba, basu bayyana a ko ina ba sai a kofar shiga faɗa,koda tsayuwar su sai yarima Himras ya ƙwallawa wani badakare kira, Badakaren ya bayyana gareshi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa kanshi a sunkuye, Yarima ya dube shi yace "yakai abu-salimat kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka sanya ayi shela Izuwa ƙasashe birane da ƙauye na naɗin sarautata tare da shagalin ɗaura auren na da gimbiya Sharzila, sannan a hana shige da fice a cikin wannan birni, face kawai iya baƙin da zasu halarci naɗin sarauta. Koda jin wannan umarni sai Abu-salimat ya risina yace"An gama ya shugabana, yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye ya juya ya nufi inda dokin shi ya ke ya kama ya hau ya sakar ma shi linzami, waɗansu zaratan dakaru ma'abota jajayen tufafi su ka mara ma shi baya suna masu zaburar dawakansu. Kamar yadda yarima Himras ya faɗa haka al'amarin yakasance, wato tun a daren jiya baƙi suka yi cincirindo a ƙasar Darul-kushur, kafin wayewar gari ya cika ya batse, gaba ɗaya jama'ar birnin babu wanda yayi farin ciki da zamowar Yarima sabon Sarkinsu, kuma zukatansu cike suke da tambaya akan a wane hali sarki Kuhairu da Amaryarshi Hashmila ke ciki sun mutu ne ko su na raye, amsar tambayoyin da su ka kasa bawa kansu kenan, saboda tsaron yarima sai kowa ya tsuke bakin shi. Su kansu sarakunan da suka halarci shagalin bikin naɗin sarautar sun halarta ne kawai saboda girmamawa ga marigayi sarki saruful-uzwar, Da yawa daga cikin su sun so su tambayi sarki Himras cewa shin ina sarki Kuhairu ya shiga, amma sai su ka bar abin a zukatan su. Tun daga wannan rana yarima Himras ya zamo sabon sarkin ƙasar Darul-kushur, ya fara shimfiɗa mulkin zalunci, Nan fa sata, kwace, fashi da makami gami danne haƙƙin masu rauni ya yawaita a birnin, Kafin Kuhairu ya cika shekaru biyu da hawa karagarshi ya mamaye dukkanin birane da ƙasashen dake maƙwabtaka dashi ya cinye su da yaƙi ta ƙarfin tsiya, sun dawo zuwa ƙarƙashin daularshi. Sai wata ƙasa guda ɗaya da wani sarki mai suna Baddadul-Arus ke mulki ita ce ta gagreshi ya mamaye ta. Daga wannan rana zaman lafiya yayi ƙaura daga nahiyar baki ɗaya, Kowa ne sarki ba shi da burin da ya huce ya mamaye biranen dake makwabtaka dashi ya cinye su da yaƙi. **** Kuhairu da Hashmila basu farfaɗo daga dogon suman da suka yi ba sai da safiya tayi, ai kuwa koda suka buɗe idanuwansu su ka gansu kwance a bisa waɗansu kadaje na itace masu kwari, a cikin wani ɗaki da akayi da zallar itacen bishiya masu kwari aka rufe saman da fatun dabbobi. Zaune a gefen gadon da kuhairu ke kwance wani Dattijo ne ma'abocin cikar kamala, shekarun shi ba zasu Haura hamsin da ɗoriya ba, bisa gefen gadon da hashmila ke kwance, wata tsaleliyar kyakkyawar budurwace sanye da fararen tufafi. Koda ganin su kuhairu sun farfaɗo, sai kyakkyawar budurwar ta miƙa tsaye ta fice daga cikin turakar, jim kaɗan bayan shuɗewar daƙiƙa ashirin sai gata ta dawo ɗauke da wani ƙaton akushi da salkar ruwa ta ajiye a gaban su kuhairu. Dattijon ya dubi kyakkyawar budurwar yace " Ai bai kamata su fara cin abinci mai nauyi ba, zai fi su sha abin da zai warware musu cikin su sannan su ci abincin, ko da jin wannan batu sai budurwa ta risina ta juya ta fice a karo na biyu Batare da tace uffan ba. Zuwa can sai kaga ta dawo ɗauke da tacecciyar Madarar shanu a cikin akushi guda biyu, duk wannan abu dake wakana tsakanin Dattijon da kyakkyawar budurwar, sarki Kuhairu da Amaryarshi Hashmila na kallo, Yayin da su ka yadda suke ɗawainiya dasu sai su ka cika da matuƙar mamaki, su na masu tambayar kansu kansu akan cewa taya ya waɗannan Mutane suka taimaka masu bayan cewa basu taɓa ganin juna ba. Amsar tambayar da su ka kasa bawa kansu kenan, kawai suka zuba idanu suna kallo. Ko da kyakkyawar budurwar ta kawo Madarar shanun sai Dattijon da budurwar su riƙe kafaɗun kuhairu da hashmila su ka tashe su zaune su ka kafa mu su akushin baki ya shiga kwankwaɗar Madarar har sai da su ka sha suka ƙoshi, Sannan su ka shiga ɗibar abincin a baki suna basu suna ci, har sai da su ka kimtsa cikin su. Da yake Kuhairu da hashmila sun gaji ainun, kuma raunukan dake jikin su sunyi tsami, Nan take su ka ɓingire su ka shiga sharar barci, koda ganin hakan sai Dattijon da kyakkyawar budurwar suka sanya mayafi su ka lulluɓe su, su ka miƙa tsaye su ka fiye ɗakin su ka janyo kofar ɗakin su ka rufe rufe!. Sai da Dattijon da 'yar shi uzaima su ka shafe tsawon kwanaki talatin suna kula da su kuhairu, har yazamana raunukan sun warke sumul!, Wata rana da hantsi sarki Kuhairu, Hashmila tare da Dattijon da 'yar na zaune a cikin turakar sai ƙuhairu ya dubi Dattijon yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye yace, "Yakai wannan Dattijo ma'abocin tausayi da jin ƙari, idan bazaka damuba ina buƙatar nayi maka waɗansu tambayoyi, Tambaya ta farko shin wane ne kai? Kuma mene ne dalilin da ya sanya ka ceci rayuwarmu?. Ko da jin waɗannan tambayoyi sai Dattijon yayi shiru yana mai sunkuyar da kanshi ƙasa,daga bisani ya ɗago ya dubi kuhairu yayi gyaran murya a karo na farko yace" Da farko dai sunana kamzal ibn Abbas, wannan budurwa kuwa 'yata ce humaira. Yakai kuhairu ka yi sani cewa bakomai ne yasanya na ceci rayuwarku ba sai domin Amincin da ke tsakanina da mahaifinku sarki saruful-uzwar, A duk sa'adda da yaje farauta yakan zauna anan wajena yayi 'yan kwanaki kafin ya huce, haƙiƙa mahaifin ku mutumin kirki ne, na samu dukkan labarin abinda ya faru tsakanin da ɗan uwanka kuhairu, ina neman alfarma a wajen ki da ku zauna tare da mu da yardar Ubangiji za mu baku dukkan wani jin daɗin rayuwar duniya. Sa'adda kuhairu yaji wannan jawabi daga bakin Dattijo kamzal sai ya cika da matuƙar mamaki ya dube shi yace" ya amintacce ga mahaifaina haƙiƙa zan riƙe tamkar abbbana kuma zamu zauna a tare da ku har Izuwa ƙarshen rayuwarmu. Daga wannan furuci ne kowa yayi shiru, kawai sai kamzal ya miƙe tsaye ya shimfiɗa wani buzu da aka yi shi da fatar damisa ya tayar da Sallah yana mai fuskar gabas humaira ya tsaye a bayan shi tana mai yin koyi da shi. Nan fa kuhairu da Hashmila su ka cika da matuƙar mamaki bisa ganin yadda kamzal da 'yarshi ke gudanar da ibadat su cikin Nutsuwa da annashiwa, saɓanin tasu ta bautar gumaka mai cike da kaɗe-kaɗe da raye-raye. Tun daga wannan rana ne kuhairu suka kasance cikin farin ciki da su kamzal, idan kamzal zai je farauta tare suke tafiya, idan sun dawo sai Hashmila da humaira suka shiga gyara naman dabbar su gasa kowa yayi kalaci. A cikin waɗannan kwanaki ne ciki ya bayyana a jikin hashmila, murna a wajen Kuhairu kuwa ba'a cewa komai, domin kwana yayi bai yi barci ba, duk bayan daƙiƙa goma sai ya duba yaga a wane hali Hashmila ke ciki. Gaskiyar masu iya magana da suka ce Sannu-Sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba, sai gashi cikin Hashmila ya cika wata tara, a wata rana ne da maraice naƙuda ta kamata ta haifi kyakkyawar jaririyarta, sai da kuhairu ya zubar da hawayen farin ciki. Yayin da mako guda ya kewayo aka raɗa yarinya suna sharilat, sharilat ta taso cikin ƙwazo da hikima, domin tun da tana Shekara tara a duniya ta ƙware ainun a horon yaƙin da kuhairu ke koya ma ta, don haka ko dakarun sumame suka kawo hari ita kaɗai ke fatattakarsu, wannan fa shine masu iya magana ke cewa "Barewa baza tayi gudu ba ɗanta yayi rarrafe". A lokacin da sharilat ta cika shekaru ashirin ne Dattijo kamzal da mahaifiyarta Hashmila suka rasa rayukansu sakamakon waɗansu miyagun 'yan fashi da su ka kawo musu farmaki, Su Kuhairu sun yi kukan baƙin ciki tamkar ransu zai fita, bayan mako guda ne humaira tayi bankwana da su domin cika burin mahaifinta na yaɗa addinin Musulunci suna kukan rabu da juna. Tun daga wannan rana Tsoho kuhairu da 'yarshi sharilat ke zaune a cikin wannan daji cikin ƙuncin rayuwa. Wannan shi ne dalilin da ya haddasa gaba tsakanin tsoho kuhairu da sarki Himras mahaifin yarima muzaifar. **** Al'amarin Yarima Muzaifar kuwa Tun Sa'adda ya rabu Da Mahaifinshi Sarki Himras A lambun shaƙawa Bayan Ya Sanar Da sarki Abin da ya Wakana Tsakanin shi Da Jaruma Sharilat. Sai Kawai Ya Huce Kai Tsaye Izuwa Turakarshi Ya Fara Sharar Barci, Bai Farka ba Har Sai Da Rana Ta hudo, Sa'adda Ya Buɗe Idanuwanshi Ya lura Cewa Ya Makara Wajen Fita Fada, Sai kawai Ya ƙwallawa Wata Kuyanga Kira Mai Suna Shahira. Shahira Ta Bayyana A Gareshi Ta Zube Ƙasa Ta Kwashi Gaisuwa Cikin Ladabi Kanta A Sunkuye. Yarima Ya Dube ta Yace" Ya ke Shahira Shin ina Dalilin Rashin Tashi Na Daga Barci?. Shahira Ka Gafarceni Ya Shugabana Ai Tuni An kai Ruwan Wanka Izuwa Kewaye Kuyangi Suna Can Su na jiranka, Kuma Mai Martaba Ya ce A faɗa Maka Idan Ka Kammala Yana Jiran Ka A Turakarshi Domin za kuyi Kalaci. Da Jin Amsar Wannan Tambaya Sai Yarima Ya Miƙe Tsaye Daga Kan Gadonshi, Shahira Ta Shige Gaba Domin Yi Ma Shi Jagora, Shi kuwa Na Biye Da ita Su ka Fice Daga Cikin Turakar. A Can Turakar Sarki Himras Kuwa Yana Zaune Bisa Wata Ƙasaitacciyar Kujera Ta Alfarma A jiye A Gaban Shi Akwai wani Dogon Teburi Mai Ɗauke Da Nau'ikan kayan Ciye-Ciye Da Tanɗe-Tanɗe, wani Irin Ni'imtaccen Ƙamshi Ya Gauraye Turakar Haɗi Da wata Ɗaddaɗar Iska Na Kaɗawa. Haƙiƙa wannan Turaka Ta Cika Aljannar Duniya Komai Ƙasaitar Basarake Ko Attajiri idan Ya Tsinci Kanshi a Wannan Waje Dole Ya Tabbatar Da Cewa Gaba Da Gabanta, Ko iya Kilishin Da aka shimfiɗe Turkar Abin Kallo ne Ballantana Batun Kayan Kyale-Kyale Waɗansu Ma idanu Basu Taɓa Gani ko Jin Labarin su ba. Yana Cikin Wannan Hali ne Yarima Muzaifar Ya Turo Kofar Shigowa Turakar, Cikin Matuƙar Farin ciki Sarki Himras Ya Miƙa Tsaye Ya Tare Shi Suka Rungume Juna Fuskokinsu Cike Da Annuri, Sai Daga Bisani ne Sarki Ya ja Hannun Yarima Har zuwa Kan Kujerar Su ka Zauna A Tare. " Ina Fatan Sharilat Da Mahaifinta Sun Amince Za su yi Tafiya Da mu Izuwa Ɗauko TAKOBIN SIHIRI. Yarima Muzaifar Ya Tambaya A ƙagauce". " Me kake Ci Na Baka Na Zuba Daɗi Na Da Kai Gajen Haƙuri Ai Saboda Da wannan Magana Na Sanya Kazo, Yanzu Sai ka Bari Idan Mun yi kalaci Sai Mu Tattauna". Sarki Himras Ya Ba shi Amsa". Daga wannan Jawabi ne Suka Shiga Kimtsa Cikinsu Sai Da Suka ci Su ka Ƙoshi Sannan Sarki Yayi Gyaran Murya Ya Dubi Yarima yace " Ya Abin Alfaharina Kayi Sani Cewa A'a daren Jiya Na Samu Ganawa Da Sharilat Da Mahaifinta Kuma Sun Amince Zasu yi Tafiya Da mu Domin Ɗauko TAKOBIN SIHIRI, Sai Wani Hanzari Ba Gudu ba Matsawar Ka bari Wata Alaƙa Ta Shiga Tsakanin ka Da Sharilat To fa Baza mu Samu cika Burin Mu Na Mallakar TAKOBIN SIHIRI ba Yaushe Sauran Mako Guda Mu Gudanar Da Wannan Tafiya. Ko da jin Wannan Bayani Sai Yarima Muzaifar ya Cika Da Matuƙar Farin ciki Maral-Musaltuwa, Amma Sai Ya Tambayi Kanshi A Cikin Ran shi Yana Mai Cewa, Shin Mene ne Ya haɗa Alaƙata Da Sharilat Da Mallakar TAKOBIN SIHIRI, Taya ya Zan iya Goge Alaƙar Dake Tsakanin mu Bayan Cewa Mun Daɗe Da Tsunduma Haɗe Da Ninƙya Cikin Kogin Soyayya. Ko da Yarima Ya zo Nan A Tunanin shi Sai Yaji Zuciyarshi Ta Buga Da ƙarfi Kuma Jikinshi Yayi Sanyi. Daga Wannan Batu ne Sarki Ya Miƙe Tsaye Tsam Ya kama Hannun Yarima Suka Kofar Fita Daga Turakar Domin isa Fada, Duk inda Su ka Gifta a Cikin Gidan Sarautar Sai Kaga Kuyangi,Barorin, Dakaru,Hadimai Haɗe Da Bayi Na Zubewa Ƙasa Suna Kwasar Gaisuwa Kawunansu A Sunkuye Tamkar Zasu yi Sunada. Lokacin Da Suka iso Wata Ƙofa A Gidan Sarautar, Sai Waɗansu ZARATAN MAYAƘA Ma'abota Jajayen Tufafi Su ka Mara Ma su Baya. Kamar Yadda Sarki Himras Ya Faɗawa yarima Muzaifar Haka Al'amarin Yakasance, Wato Ranar Da Mako Guda Ya Cika Sai Yarima Da Sarki Suka Shiga Shirye-Shiye, Bayan Sarki Himras Ya Bada Riƙon Sarautar shi A hannun Waziri Huzmal, Sai ya kira Wani Hadimin Aljaninshi Mai Suna Narguz Ya Ɗauke Su Ya kai Su Izuwa Jejin Da Su Sharilat Ke zaune. Har Sarki Himras Ya Yunƙura Zai Sauko Daga Kan Narguz, Sai Kawai Ya Hango Sharilat Da Kuhairu Sun fito Daga Cikin Gidan su Gaɓa Ɗayansu Suna Sanye Cikin Tufafi Da akayi su Da Fatar Barewa, Kuhairu Na riƙe Da Sandarshi. Ko da ganin Hakan Sai Kuhairu Da Yarima Su ka Yunƙura Su ka Sauko Daga kan Aljani Narguz Suka Taka Da Ƙafafunsu Suka Durfafi in da su Sharilat Ke Tsaye Tun kafin Su Haɗu Yarima Da Sharilat ke jifan Juna Da ƙayataccen Murmushi Mai Tattare Da So na Kauna. Lokacin Da Yazamana Saura Taku Biyu A tsakanin su Sai Su ka ja Suka tsaya, Sarki Himras Yayi gyaran Murya Yace" Ya Abokan Tafiyar mu ina Fatan Kun kammala Dukkan Shirye shirye-shirye?. " Mun kammala komai Yanzu Tafiya ce Kaɗai Ta Rage". Kuhairu Ya Ba shi Amsa. Ko da jin Wannan Batu Sai Sarki Himras Da Yarima Himras Su ka Shige Gaba, kuhairu Da Sharilat Na Biye da Su aka durfafi in da Aljani Narguz yake Tsaye, Narguz Ya shimfiɗe gadon bayanshi Sarki Himras, Mazaifar, Kuhairu Da Sharilat Suka haye suka zauna Sannan Ya buɗe manyan fuka-fukanshi Ya Yunkura Ya tashi zuwa Sararin Samaniya Yana Mai Tsala Azababban gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya. Cikin Fushi Sarki Himras Ya Daka mashi Tsawa Ya Dube shi Ya ce "Aikin Banza Kai Da kake wannan Gudu Shin Kasan inda Za ka Kaimu?. Ko da Jin wannan Batu Sai Aljani Narguz Ya Tsaya Cak A Cikin Iska Ya Buɗi Baki Cikin Ladabi Yace " Ka Gafarceni Ya Shugabana. " Yakai Narguz ibn Shamlazul-jafsul Kayi Sani Cewa Ina So Yanzu Ka kaimu Izuwa Birnin Rum Domin Mu Ɗauko Sarƙar Tsafi a cikin Tsahon ƙabarin boka Auladu ibn Zumar. Ko da Jin Wannan Batu Daga Bakin Sarki Sai Aljani Narguz Yace "An Gama Ya Shugabana Bin Umarninka Shine Ibada Yana Gama Faɗin Ya Kaɗa fuka-fukanshi Ya Shiga keta Gajimare Cikin Matuƙar Gudu. Tun da Aka Fara Wannan Tafiya Babu Wanda Yace Ƙala, Amma Fuskokin Yarima da Sharilat Cike Da Annuri Har ma Suna Satar Kallon Junansu. Wannan shi ne Shi ne Abinda ya Wakana Tsakanin Su sarki Himras Da su Tsoho Kuhairu A lokacin Tafiya Ɗauki TAKOBIN SIHIRI. ***** Al'amarin Sarki Baddadul-Arus da 'yarshi Uzaima Kuwa, Tun Sa'adda Daga Ranar Da Suka Fafata Artabu da Sarki Huraisu Na Birnin Jarul-Iman, Sai Su ka kasance Cikin Shirye-shiryen Tafiya Izuwa Birnin Rum. Wata Rana Sarki Baddadul-Arus Na Zaune A Turakarshi Da Aka Ƙawata ta Da Nau'ikan kayan Ƙawa Da Alatun Jin Daɗin Rayuwar Duniya, A wannan Ya na Shan Taceccen Ruwan Inibi A cikin wani ƙayateccen Kofin Zinare. Yana Cikin wannan Hali ne Kawai Sai Ya Ajiye Kofin Ya Zira Hannunshi A Aljihunshi na Hagu Ya Ɗauko Madubin Tsafin shi Ya karanto waɗansu Ɗalasiman Tsafi Yana Gama Rufe Bakinshi Sai Ga Hoton Aljani Narguz Ɗauke Da Su Sarki Himras yana Tsala Azababban gudu A Sararin Samaniya. Ko da ganin Wannan Al'amari Sai Ya Taƙarƙare Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Tamkar Ba zai Daina ba, Sai da Yayi Dariyar Ta Ishe Shi Sannan Daga Bisani Yace Amma Sarki Himras Ya Cika Waqa Marasa Fahimta, Shi Yanzu Har Ya na Tunanin Cewa Zai Riga Ni Mallakar Sarƙar Tsafi. Bayan Cewa Nine Nake Da Hadimi Mafi Ƙarfin Gudu A Cikin Jinsin Aljanu JARUMAN DUNIYA. Yana Gama Faɗin Hakan Sai Ya Miƙe Tsaye Tsam Ya Shiga Yin Shirin Yaƙi, Baƙaƙen Sulke Ya Saka Tun Daga Ƙasa Har Sama, A jikinshi Yana Sanye Da Makaman Yaƙi Fiye Da Guda Arba'in, A Gadon Bayanshi Yana Rataye Da Waɗansu ZARATAN Takubba. Haƙiƙa Shigar Da yayi Ta yi Matuƙar Yi Ma Shi Kyawu Da Kwarji. Kawai Sai Ya Durfafi Hanyar Da Zata Sadashi Da Turakar Gimbiya Uzaima, Yana Cikin Tafiyar Sai kawai Yayi Turus!, Ba wani Abu Ya Gani ba Face Gimbiya Uzaima Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Iri Ɗaya Sak Da Tashi. Yayin da Da Su ka iso Daf Da Juna Sai Uzaima Ta Rungume Mahaifinta, Sai Daga Bisani ne Sarki Ya Janye Jikinshi Daga Na Uzaima Ya Dube ta Yace" Ya Annurin zuciyata Shin Ya A kayi Kika San Cewa Na Kammala Shirin Tafiya? Koda jin Wannan Tambaya Sai Uzaima Ta Saki Tattausan Murmushi Ga Abbbanta Sannan tace" Ya abbana Shin Ka Manta Cewa Ni ma Nasan Wani Abu Game Da Shirin Tsafi, Ka Sani Cewa Na gudanar Da Bincike ne Bisa Halarar Tsafina Na gano Dukkan Abinda Ke Wakana Da Kai, Da Abinda Ya faru Da Abokan Gabarmu Su Sarki Himras. Ko da jin Amsar Wannan Tambaya Sai Daga Bakin Uzaima Sai Sarki Baddadul-Arus Ya Ƙwallawa Hadimin Aljaninshi Mai Suna Zamzaru Kira, Gama Rufe Bakinshi Ke da wuya Sai Wata Walƙiya Gami Da Tsawa Suka Bayyana A Sararin Samaniya, Al'amarin Da ya Firgita Jama'ar Dake Gidan Sarautar Kenan Su Ka Shiga Guje-guje Gami Da ifice-ifice Har Dakarun Gidan Sarautar Saboda Da Firgici Sai Suka Dunga Cika Wandonsu Da Iska, Kai Wasu Har da Sakin Fitsari A Wando, Saboda Tsawa Da Walƙiyar Sun Saɓa Da Irin Waɗanda Idanu Su ka Taɓa Gani. Tsawon Daƙiƙa Hamsin Ana Cikin Wannan Hali, Sai Daga Can Sai A Hango Wata irin Shirgegiyar Halitta Ta Ketowa Daga Cikin Gajimare Ta Sauka A turba Tana Mai Shimfiɗe Fuka-fukanta, Ba Wata Ba ce Wannan Halitta ba Face Aljani Zamzaru. A lokacinne Walƙiya Gami Da Tsawar Suka Ɗauke, Komai Ya Samu Saisaituwa, Cikin Matuƙar Biyayya Aljani Zamzaru Ya Buɗe Wawakeken Bakinshi Mai Kama Da Ƙofar Gari Yayi Gyaran Murya Yace "Umh Ya Shugabana Gani Gareka Shin Wata Buƙata Ka ke Da ita A gare ni?. Ko da Jin wannan Tambaya Sai Sarki Baddadul-Arus Ya yi Gyaran Murya Sannan Ya kawo Gwaron Numfashi Ya Ajiye Yace " Ya kai Zamzaru Bakomai Ya Sanya Na Kirawo ka Nan ba Sai Domin Ina So Ka Ɗauke ni Da 'yata Uzaima Ka Kaimu Zuwa Birnin Jarul-Iman Domin Mu Ɗauki Sarki Huraisu, Sannan Mu Huce Izuwa Birnin Rum Domin Ɗauko Sarƙar Tsafi Dake Cikin Ƙabarin Boka Aulad Domin Mu Tashi Boka Sharubu Daga KUSHEWAR Shi, Ina So ne Ka kaimu Waɗannan Wajajen A Cikin Abinda Bai Gaza Sa'a Uku ba, Domin Mu rigayi Abokan Gabarmu Su Sarki Himras isa Izuwa Can ɗin. Ko da Jin Wannan Bayani Daga Bakin Baddadul-Arus Sai Aljani Zamzaru Ya Saki Wata Atishawa, Sannan Ya Samu Nutsuwa Ya Buɗi Baki Cikin Ladabi Yace "Ya Shugabana Na ji Dukkan Bayanin ka Sai Da Wani Hanzari Ba Gudu ba, Kasan Cewa Wannan Shine Aiki Na Ƙarshe A Gareka Ma'ana Wanda Da Zarar Na Kammala Zan Samu 'yanci. Ko da Jin Wannan Batu Sai Dariya Ta Suɓucewa Baddadul-Arus Har da Ƙyaƙyatawa Sai Bisani Ya Shi Fuskarshi Cike Da Annuri Yace " Haba SARKIN SADAUKAI MUTUWAR SARAKAI Mai Ka ke Ci Na Baka Na Zuba Ai Alƙawarin mu Yana Nan Daram, Kamu Wani Abu Da Baka Sani ba Shine Matuƙar Mu Kayi Nasara A Wannan Tafiya Bayan Na 'Yan Taka Zan yi Maka Wata Gagarumar Kyauta Wacce Ni Kaɗai Nasan ta. Da Jin Wannan Batu Sai Aljani Zamzaru Ya Shimfiɗe Gadon Bayanshi Sarki Baddadul-Arus Ya Hau Ya Zauna 'Yar Shi Uzaima Tayi Koyi Dashi, Sarki Baddadul-Arus Ya Ƙwallawa Hadimin Shi kira Mai Suna Hulaifa Take Ya Tawo Izuwa Gareshi Tare Da Waɗansu Dakaru Ɗauke Da Abin Guzuri Suka Ɗora Bisa Kan Aljani Zamzaru Jikin Na Ƙyarma Tamkar A ce Ƙyat Su Falfala Da Gudu Saboda Matuƙar Tsoro, Sannan Zamzaru Ya Buɗe Manyan FukaFukanshi Ya Ta Shi Izuwa Sararin Samaniya Yana Mai Keta Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya. Tafiyar Rabin Sa'a A kayi Aka Iso birnin Jarul-Iman Domin Haka Sai Zamzaru Ya Sauka A Turba, Ko da Tsayuwar Sai Baddadul-Arus Ya Buɗe Bakin shi Ya Karanto waɗansu Ɗalasiman Tsafi Yana Gama Rufe Bakinshi Sai Wani Kyakkyawan Tsuntsaye Ma'abocin Kyawun Launi Ya Bayyana A Gareshi, Kawai Sai Tsuntsun Ya Kaɗa fuka-fukanshi Ya Durfafi Hanyar Birnin Jarul-Iman. A Birnin Jarul-Iman kuwa Sarki Huraisu Na Zaune A bisa karagar mulkinshi, Sanye Da Ƙayatattun Tufafi Na Hamshaƙan Sarakai, Fadawanshi Na Kewaye Da Shi, A Gefe Guda Kuwa Sauran Jama'ar Gari ne Zaune Ana Tafiyar Da Sha'anin Mulki Cikin Annashiwa Da Jin Daɗi. Ana Cikin Wannan Hali ne Ƙwatsam Sai Aka Hango Wata Ƙyakƙyawar Tsuntsuwa Ta Shigo Fadar, Har Dakarun Dake Tsaro Sun Zare Makamansu Domin Su Afka Ma ta Sai Sarki Huraisu Ya Ɗaga Musu Hannu Yana Mai Nuni Da su Dakata. Sannu A Hankali Tsuntsuwar Ta iso in da karagar Mulki Take Sai Kawai Aka ga Ta Sauka ƙasa ta Sunkuyar Da Kanta Alamun Tana Miƙa Gaisuwa, Sannan Ta Buɗe Baki Tace" Yakai Wannan Sarki Mai Daraja Kayi Sani Cewa Bakomai Ba ne Ke Tafe Da ni Izuwa Gareka ba Sai Domin Na Gabatar Ma ka Da Aiken Shugabana Sarki Baddadul-arus, Sakon Da Ya Aiko ni Da shi Shi ne, A halin Yanzu Shi Da Tawagar Suna Bakik ƙofar Gari Suna jiran ka Domin Gudanar Da Tafiyar ku Izuwa Birnin Rum, Domin Ɗauko TAKOBIN SIHIRI. Ko da jin Wannan Batu Sai Fuskar Sarki Huraisu Ta Faɗa ɗa Da Murmushi, Al'amarinDa Yayi Matuƙar Ba wa Jama'a Mamaki Kenan Domin Basu Taɓa Ganin Dabba Mai Hankalin Wannan Tsuntsuwa ba Tabbas Akwai Aiki Na Sihiri A Tattare Da Wannan Tsuntsuwa. Koda Tsuntsuwar Ta Kammala Wannan Jawabi Sai Kawai Ta Kaɗa Fuka-fukanta Ta Yashi Sama Ta Fice Daga Fadar jama'a Su ka Bi ta Da Kallo. Kawai Sai Sarki Huraisu Ya Miƙe Tsaye Tsam Daga Kan Karagar Shi Ya Fuskanci Jama'a Sannan Yayi Gyaran Murya Yace "Ya ku Jama'a ta Kuyi Sani Cewa A Yau ne Nake Farin Cikin Sanar Da ku Cewa Zan Shiga Izuwa Duniya Domin Samun Abokiyar Rayuwar Da Nake Da Muradin Aure, Na sani Cewa Kun So ni Tamkar Ɗan Da Ku ka Haifa, Kuma Za ku So Ashe Banyi Ne sa Da ku ba. Duk Da Cewa Nasan Waɗansu Za Su Ƙalubalance Akan Cewa Duk 'yan Matan Da ke Cikin Birnin Nan Na rasa Wacce Zan Kaunata, Sai Dai Idan Mu kayi Lakari Da Wani Batu Na Masu Iya Magana Da Suke Cewa Garin Masoyi Baya Nisa, Kuma Shi So Ba'ayin Ma shi Dole, Don Haka Za'a Yi Mini Uzuri. Da wannan Nake Yi Maku Fatan Alkairi Sai Mun Sake Damuwa, I na Mai Bar Muku Waziri Rufyan A Matsayin Halifana Da Zai Cigaba Da Tafiyar Da Sha'anin Mulki. Ko da Gama faɗin Hakan sai Sarki Huraisu ya taka da Ƙafafunshi Ya Sauko Daga Matattakalar Fadar Ya durfafi Wata Ƙofa, Take Waɗansu ZARATAN MAYAƘA masu Jajayen Tufafi Hannayensu Ɗauke Da Miyagun Makamai Su ka Mara Ma shi Baya, Nan fa Fadar Ta Ruɗe Da Ce-ce ku ce Kowa Na Faɗin Albarkacin bakinshi, In da Waɗansu Ke Nuna Alhininsu Kan Tafiyar Sarki, Wasu Har Suna Zubar Da Hawaye. Sai Da Sarki Da Dakarun Shi Su ka Ƙule A cikin Wannan Ƙofa Sannan Fadar Watse Kowa Ya Kama Gaban shi. ***** A can in da Sarkin Baddadul-Arus Da Gimbiya Uzaima Suka Yada Zango Bisa Kan Aljani Zamzaru Suna Jiran Dawowar Wannan Tsuntsuwar Tsafi, Sai Suka Shafe Tsawon Daƙiƙa Talatin A Cikin Wannan Hali, Sannan Tsuntsuwar Ta iso Kuma Ta Bayyana Mashi Dukkan Abinda Ya Wakana Tsakaninta Da Sarki Huraisu, Koda Kammala Bayar Da Saƙon Sai Baddadul-arus Ya Sake Nuna ta Da Hannun shi Ta Ɓat Tamkar Bata Taɓa Wanzu ba. Daga Can Sai Aka Hango Sarki Huraisu Tare Da Wani Hadimin Shi Sun Durfafo Wajen A bisa Dawakai, Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Mai Matuƙar Kwarjini Da Ban Tsoro. Tun Daga Ne sa Uzaima Ta Ƙura Mashi Idanu Ko Ƙiftawa Bata yi, Matuƙar Kyawun Surar Shi Suna Sake Fuzgar Zuciyarta. Lokacin Da Ya Zamana Tazarar Dake Tsakanin Su Bata Huce Taku Ashirin ba Sai Dawakansu Da Suke A Kai Su ka Yi Turjiya Gami Da Haniniya Suna Ɗaga Ƙafafuwansu Sama Suna Neman Jefo Da su, Bakomai Ne Ya Haddasa Hakan ba Sai Bisa Arba Da Aljani Zamzaru Da Dawakan Su kayi. Ba Shiri Sarki Huraisu Da Hadimin Suka Kama Linzamin Dawakan Su ka Sauko Ƙasa Haɗe Da Takawa Da Ƙafafuwansu Su ka Durfafi In da Su Baddadul-Arus Su ke Tsaye. Baddadul-Arus Ya Dube Su Fuskarshi Cike Da Annuri Yace "Lale Marhaban Da Sarki Huraisu Na Birnin Jarul-Iman Kuma GWARZON DUNIYA. Ko da jin Wannan Batu Sai Dariya Ta Suɓucewa Huraisu Har Fararen Haƙoranshi Suka Bayyana Masu Haske, Ya Ƙurwa Uzaima Idanu Na Ɗan Wani Lokaci Daga Bisani Ya Buɗe Bakinshi Yayi Gyaran Murya Yace "Umh Barkan ku Da Zuwa Ya Abokan Tafiyata, Wannan Da Ku ka Ganni Tare Da shi Hadimi ne Shaibat Da Nake Matuƙar Ƙauna Kuma Ina So ne Ayi Wannan Tafiya Tare Da shi, Shaibat Ya Risina Ga Sarki Ya Miƙa Gaisuwa Sarki Ya karɓa Sannan Yace " Ai Sai Ku Zo Mu Tafi. Ko da jin Wannan Batu Sai Huraisu Da Shaibat Suka Haye Bisa Kan Aljani Zamzaru Suka Zauna Ne Sa Kaɗan Da In Da Baddadul-Arus da Uzaima Su ke, Sannan Zamzaru Ya Yunƙura Ya Tashi Zuwa Sararin Samaniya Yana Mai Keta Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya. ***** Fadar ta Ƙawatu ainun Da kayan Ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da ma abin da Idanu Basu Taɓa Gani ba, Duk ƙasaitar BASARAKE ko Attajiri Idan Ya Tsinci Kanshi A Cikin Wannan Fada Dole Ya Zamo Cikekken Ɗan Ƙauye Kuma Ya Tabbatar Dacewa Gaba Da Gabanta. Duk inda Mutum Ya Kalla A Fadar Kawunan Bil'adama ne Babu Masaka Tsinke Tamkar DANDAZON kiyashi, 'yan Majalissar Sarki Na Zaune A Bisa Waɗansu Ƙayatattun Kujeru Na Alfarma, Dakarun Duk yiwa Fadar Ƙawanya Ɗauke Da Miyagun Makamai Suna Kai Komo Domin Tabbatar Da Cikekken Tsaro. Nesa Kaɗan Da in da 'Yan Majalissa ke Zaune Bisa In da aka yi Matattakala Hudu bisa Wani Gayayyen Tudu A Nanne Aka Ajiye Wata Ƙasaitacciyar Karagar Mulki Da Akayi ta Da Zallar Dutsen Zubar Daju Aka Yi Mata Feshi Da koren sinare Ta na Sheƙi Da Ɗaukar Idanun Duk Mai Kallo. Bisa Karagar Wani Shirgegen Mutum ne Ma'abocin Kasumba Da Gemu Baƙaƙe Siɗik, Sanye Cikin Tufafin Alfarma Irin Na Hamshaƙan Sarakai, Sanye A kanshi Akwai Kambi Na Sarauta Da Aka Sana'anta shi Da Zallar Zinare Da Lu'ulu'u, A Gadon Bayanshi Yana Rataye Da Wata Sharɓeɓiyar Takobi, Kuma Ya Ɗora Ƙafarshi Ɗaya Kan Ɗaya, Takalmin Dake Ƙafar Tashi An yi Ma shi Ado Da Gashin Ɗawisu Yana Canza Launi Lokaci zuwa lokaci, Fuskarshi cike Da Annuri Ana tafiyar Da Sha'anin Mulki. Ana Cikin Wannan Hali ne Kwatsam Sai Aka Hango Boka Hushaib Ya Bayyana A Fadar Fuskarshi A Murtuke Babu Annuri Tamkar An Aiko Mashi Da Wasiƙar MUTUWA, Ya Zube Ƙasa Ya Kwashi Gaisuwa Cikin Ladabi, Sarki Ya Dube shi Yace "Ya Abin Dogaro Shin Ina Dalilin Zuwan ka A wannan Lokaci ?. Ko da jin Wannan Tambaya Sai Boka Hushaib Ya Sake Murtuke Fuska Saboda Fushi Har Hatsine Take yi, Sannan Ya Gyara Zaman shi Yayi Gyaran Murya Cikin Kakkausar Murya Mara Daɗin Saurare Yace " Ya Shugabana Kayi Sani Cewa Ba Wani Abu ne Ya Kawo ni A wannan Fada ba Sai Domin Na Sanar Da kai Wata Guguwar Musiba Dake Tunkaro Wannan Birni Namu, Ta Bayyanar Waɗansu ZARATAN SARAKAI biyu Sarki Baddadul-arus Da Sarki Himras Na Kasar Darul-kushur Domin Su Ɗauke Sarƙar Tsafi Dake Ajiye A Cikin KUSHEWAR Margayi Boka Aulad. Sanin ka Ne Cewa Fiye Da Shekaru Dubu Uku Baya Ba'a Samu Mahaluƙin Da Ya Taɓa Shiga inda KUSHEWAR Take Ba Har Ya Ɗauke Sarƙar. Binciken Dana Gudanar Bisa Halarar Tsafina Ya Tabbatar Dacewa Matsawar Mu ka Rasa Wannan Sarƙar Burinmu Zai Faɗa Cikin Musibar Fari, Yunwa, Cututtuka Guda Casa'in Da Tara Waɗanda Basu Da Magani. Ko da Jin Wannan Batu Daga Bakin Boka Hushaib Sai Hankulan Jama'ar Dake Fadar Ya Ɗugunzuma Ainun, Sarki Kuwa Sai Fuskarshi Ta Canza Daga Annuri zuwa Tashin Hankali Ya Dubi Boka Hushaib Cikin Kaɗuwa Yace " Ya Abin Dogaro na Shin Mene ne Mafita Game Da Wannan Musiba Dake Tunkaro mu ? Kuma Tsawon Kwanaki Nawa ne Su ka Rage Sarakunan Su Iso Nan?. Da jin Waɗannan Tambayoyi Sai Boka Hushaib Ya Buɗi Baki A karo Na Uku Yace "Ya Shugabana Sarakunan Za Su Iso Wannan Birni Namu ne Nan Da Kwanaki Huɗu, Mafita Kawai Ita ce Mu yi Shirin Yaƙi Domin Jiran Zuwan su. Da jin Amsar Wannan Tambayoyi Sai Sarki Usulul-Haibar Ya Miƙe Tsaye Tsam Daga Kan Karagarshi Cikin Matuƙar Fushi Ya Fuskanci Jama'a Cikin Kakkausar Murya Yace "Ya ku Jama'ar wannan Fada Tawa Mai Albarka Kun ji Dai Dukkannin Bayanin Da Boka Hushaib Yayi Sanda Da Haka Kowannen ku Ya Fara Shirin Yaƙi Kuma Ban Ɗaukewa Kowa ba, Domin Kare 'Ya'yanmu Da Dukiyoyinmu Har Ma Birninmu. Ko da Gama Wannan Jawabi Sai Sarki Usulul-Haibar Ya Tako Matattalar Fadar Ya Sauko Ƙasa, Ya Nufi Wata Ƙofa Ta Musamman A Fadar Dakarunshi Na Take Mashi Baya. Nan Take Fadar Ta Watse Kowa Ya Kama gabanshi cikin tashin Hankali. **** Sarki Usulul-Haibar Ibn Zumar Yakasance Ƙasaitaccen Sarki Kuma GWARZON MAYAKI Mai Tarwatsa DANDAZON JARUMAI a filin fama. Mutum ne Shi ma'abocin tarin dukiya dangin Lu'ulu'u Da Zinare, Yana Matuƙar Ƙaunar Jama'arshi Da Son Ganin Ya kyautata masu, A Jerin Sarakunan Da Su ka Yi Mulki A Birnin Rum Shine Sarki Na Ɗari Uku, Kuma Ba'a Taɓa Yin Sarkin Da Arzikin Birnin Rum Ya Bunƙasa A Zamanin Shi ba Kamar Shi. A Gaba Ɗaya Nahiyar Babu Birnin Da Yakai Na Rum Saboda Yadda Suka Tara ZARATAN MAYAƘA Masu Juriya A Filin Fama. Sarki Usulul-Haibar Yana Da Wata kyakkyawar Yara Guda Ɗaya Jal Mai Suna Hulaifa, Gimbiya Hulaifa Yakasance Tsaleliyar Budurwa Mai Kyan Diri Da Sura Tamkar Ita Ce Ta Ƙera Kanta Yadda Take Buƙata, Ta Gaji Mahaifinta A Ƙarfin Damtse Gami Da Son Talakawa, Kuma Ita Ce Kaɗai Ta Rage Ga Usulul-Haibar A Cikin Zuri'arshi. Bisa Wannan Dalili Ne Ya Sanya Sarki Usulul-Haibar Ke Matuƙar Ƙaunarta Fiye Da Komai A Rayuwar Shi, Baya Son Abinda Zai Ɓata Mata Rai Ko Sa Ta A Damuwa, Domin Akwai Wata Rana Da Wani Hatsabibin Boka Ya Zo Birnin Domin Ya Aure Gimbiya, Sarki Usulul-Haibar Ne Kaɗai Ya Yaƙi Bokan Da Tawagar Shi Bai Bar Ɗayansu A Raye Ba, Tun Daga Wannan Rana Sarakunan Dake Nahiyar Suke Shakkar Sarki Usulul-Haibar Da Girmama Shi, Domin Dai Masu Iya Magana Na Cewa Idan Gemun Ɗan Uwanka Ya Kama Da Wuta Sai Ka Shafawa Naka Ruwa Domin Tsira Da Daraja Da Mutumcin ka . Wannan Shi Ne Abin Da Ya Wakana A Birnin Rum Dake Yamma Maso Gudancin Duniya. ***** Lokacin da Aljani Narguz Ya Cigaba Da Keta Sararin Samaniya Yana Ratsa Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya Ɗauke Da Sarki Himras, Yarima Muzaifar, Tsoho kuhairu Da Jaruma Sharilat. Sai Sarki Himras Ya Dubi Yarima Muzaifar Fuskarshi Cike Da Annuri Ya yi Ajiyar Zuciya Yace "Ya Ɗana Abin Alfahari Naga Kana Cikin Alamun Damuwa, Duk Da Cewar Bansan Mene ne Ya Haddasa Maka Damuwar ba, Bari Na Baka Wani Labari Da Zai Ɗebe Maka Kewa. Ko da Jin Wannan Batu Sai Yarima Ya ce Ina Sauraren Ka Ya Abbana. Sarki Himras Ya yi Gyaran Murya Ya Gyara Zama Sannan Ya Fara Dacewa". **** Kimanin Shekaru dubu ɗaya da ɗoriya bayan zamanin Sarki Nu'umanu na birnin Zainul-Ansar, An yi wata Gawurtacciyar Basadaukiya Mai Suna Nashmira Bintu Abu-Hizam. Nashmira Takasance Ƙyaƙƙyawa Ta Gaban Kwatance Mai Ƙyan Diri Da Sura Kuma Mace Mai Kamar Maza, Bokayen Duniya Da Masu Hasashe Sun Tabbatar Da cewa, A kaf Nahiyar Larabawa Baƙaƙen Fata Babu Jaruma Mai ƙarfin Damtsenta, Domin An Ce Tana Iya Yaƙar Gari Guda Ta Cinye Su Da Yaƙi, Tana Iya Gudun Sa'a Goma A ƙafa Batare Da ta Gaji ba, Kuma Tana Iya Shafe Tsawon Sa'a Uku Tana Yaƙi Batare Da Ta ci ko Ta Sha ba Ballantana Ta Gaji Har Ayi Mata Ƙwarzane. A Rayuwar Jaruma Nashmira Babu Abin Da Ta Tsana Fiye Da 'ya'ya Maza, Bakomai Ne Ya Janyo Hakan ba, Sai Domin Tun Da Ta Taso A Rayuwarta A Hannun Mahaifiyarta Ta Girma Ita Ce Ke Kula Da Komai Na Rayuwarta, Duk Sa'adda Nashmira Ta Tambayi Mahaifiyar ta Shin Ina Abbana Yake? Kuma Wane ne Shi Ya Tafi Ya Bar mu A Cikin Wannan Hali Na Ƙuncin Rayuwa? Sai Mahaifiyarta Ta Ta Kasa Bata Amsar Wannan Tambaya Ta Shiga Zubar Da Hawaye, Nan Take Nashmira Zata Rungume Ta Ta Fashe Da Kukan Baƙin Ciki, Har Mahaifiyarta Ta Rasu Bata Sanar Da ita Wane ne Mahaifinta ba. Abin Da Nashmira Ta Fahimta Shi ne Tabbas Akwai Wani Rashin Adalci Da Mahaifinta Ya yiwa Ummanta. Bisa Wannan Dalili Ne Yasanya Nashmira Ta Sha Alwashin Cewa Matuƙar Tana Numfashi A Doran Ƙasa Sai Ta Mayar Da Dukkanin MAZAJEN DUNIYA Bayin Mata. Lokacin Da Nashmira Ta Ga Ta Cika Kyakkyawar Budurwa kuma Basadaukiya Sai Ta Ziyarci Wani Boka A Birnin Kisra Mai Suna Shahamar Ibn Ubaidah. Lokacin Da Nashmira Ta Kaɗaita Da Boka Shahamar Sai Ta Buɗi Baki Da Nufin Ta Bayyana Mashi Abin Da Je Tafe Da Ita. Kafin Ta kaiGa Hakan Boka Shahamar Ya Dakatar Da Ita Ta Hanyar Ɗaga Mata Hannu Yana Mai Nuna Tayi Shiru, Sannan Ya Sanya Hannunshi Na Hagu Ya Shafi Dogon Gemunshi Fari Sol, Kana Ya Bude ta Da Jajayen Idanuwanshi Masu kama Da Garwashi, Ya Buɗi Baki Cikin Kakkausar Murya Mai Kama Da Haniniyar Doki Yace "Yake JARUMAR JARUMAI Shin Mene ne Dalilin Da Ya Sanya Zaki Wahalar Da Kanki Wajen Sanar Dani Buƙatar Dake Tafe Dake, Ki Sani Cewa Fiye Da Shekaru Arba'in Nasan Da Zuwan ki Nan, Abin Da Ke Tafe Dake Ɗin Shi ne Ki Na So Ki Maishar Da Dukkan Mazajen Duniya Bayin Mata Ko Ba haka Bane?. Cike Da Matuƙar Mamaki Nashmira Ta Ce "Tabbas Zancen ka Dutse Ya Madubin Bokaye". Shahamar Yayi Gyaran Murya Karo Na Biyu Yace "Yake Nashmira kiyi Sani Cewa wannan Buƙata Taki Dai-dai Take Siyen Ajalinki Da Kuɗinki, Haƙiƙa Kin Ɗebo Ruwan Dafa Kanki, I na Mai Baki Shawara Da ki Janye Wannan Ƙudiri Baki, Domin Ta Yaya Maza Zasu Zamo Bayin Mata, Shekarun Da Su ka Gabata An Samu Mata Masu Irin Wannan Mummunar Aƙida Taki Amma Basa Kai Ga Cika Burin Su Ajali Ke Riskar Su. Tun wanzuwar Duniyar Nan fa Maza Ne Ke Mulkin Duniya, Kuma Haka Ne Zai Cigaba Da Tabbata Ƙarni Bayan Ƙarni. Ko da Jin Wannan Batu Sai Nashmira Ta Fusata Ainun Ta Dakawa Shahamar Tsawa Cikin Matuƙar Fushi Tace" Zancen Banza Ke Nan Ya kai Shahamar Kayi Sani Cewa Ban Kowa Maka Ziyara Domin Ka Bani Shawara ba, Abin da Nake Buƙata Kawai Shi ne Ka Bayyana Mini Hanyar Da Zan Cimma Burina, Idan Kuwa Kayi Wani Ganganci To Kai ne Namiji Na Farko Da Zan Fara Hallakawa. Da Jin Wannan Batu Sai Dariya Ta Suɓucewa Boka Shahamar Mai Kama Da Haniniyar Doki Wacce Ta Ƙarawa Fuskarshi Muni Ya Dubi Nashmira Yace "Haƙiƙa Yaro Man kaza Ne Bai San Wuta ba Sai Ta Narka shi, kuma Duk Tsuntsun Da Yaja Ruwa Shi Ruwa Ke Doka. Kuma Masu Iya Magana Dai Na Cewa Ba'a Ƙwacewa Yaro Garma. "Yake Nashmira kiyi Sani Matukar Kina So ki Maishar Da Dukkan Mazajen Duniya Bayin Mata, Wajibi Ne Ki Nemo Waɗansu Abubuwa Da Mallakar Su Dai-dai Ya ke Da Buɗe Taskar ANNOBA ƊARI. Da Farko Wajibi Be ki Nemo Waɗansu ZARATAN JARUMAI Mata Waɗanda Shekarunku Da Kamanninku Suka Zo Ɗaya Sak Tamakar An Tsaga Kara. Ta Farko Ita Ce Jaruma Siyasar Bintu Sha'aban, Sai Shuraiba 'Yar Ƙaura Hubbaru Na Birnin Sin. Abu Na Biyu Shi Ne Wani Mashi Da Garkuwa Dake Ajiye A Cikin KOGON TSAFI kafin Mutum Ya Isa Inda Kogon Yake Sai Ya Ƙetare Waɗansu Miyagun Dazuzzuka Guda Sha Biyu A Yanzu Da Nan Gaba Babu Wani Mahaluƙi Da Ya Isa Ya Gano Adadin Musibun Dake Tattare Da Dazuzzukan. Abu Na Uku Shi Wani Sihirtaccen ƙwai Dake Ajiye A Cikin Tekun Bahar Maliya Wanda Shugaban Tsuntsayen Ta Tsare Shi Ta Ciro Shi Daga Cikin ta Kafin Ya ƘyanƘyashe Kanshi,Fiye Da Shekaru Dubu Shugabar Kifayen Na Matuƙar Buƙatar Haihuwa. Na Huɗu Shi Ne Waɗansu Kayan Yaƙi Riga Da Wando Dake Ajiye A Fadar Uwar Mayu. Abu Na Ƙarshe Shi Ne ƊAMARAR SIHIRI Ta Sarkin Matsafan Aljanun Duniya Matsafi Kashmil. Waɗancan Jarumai Biyu Mata Zasu Taimaka Miki Ne Wajen Cimma Burinki Kuma Su Taimaka Miki Waɗancan Abubuwan, Sihirtaccen Mashi Da Garkuwa Kuwa Sune Makaman Da Babu Kamar Su A Duniya Kuma Suna Dauke Da Muhimman Sirrika Kamar Haka. Sirri Na Farko Shi Ne Matukar Kana Tare Dasu Babu Wani Abu Da Zaka Sa A Gaba Face Ka Cimma Nasara, Dole Kowa ce Halitta Tayi Biyayya A Gareka, Komai Tsananin Rundunar Abokan Gaba Idan Ya Tunkare Su Zai Iya Hallaka Su Domin A Cikin Abin da Bai Huce Daƙiƙa Goma Yana Kashe Mutum Dubu, Sirri Na Ƙarshe Shi Ne Daga Inda Mutum Yake Yana Iya Tura Makaman Su Hallaka Mashi wanda Yale So Batare Da Shan Wata wahala ba. Kwai Na Sihirin Kuwa Za'a Yi Amfani Da Shi Ne A lokacin Da Za'a Shiga Kogon Tsafi, Ɗamarar Sihiri Kuwa Da Makaman Yaƙi Da Zarar Kin Sanya A Jikin ki Za ki Mallaki Rabin Sirrikan Tsafin Duniya Dake Jikin Ɗamarar Da Kayan Yaƙin, A Sanne Zaki Zamo Babu Wata Halitta Da Ta Kai ki Karfin Damtse Walau Mutum ko Aljan. Waɗannan Sune Abubuwan Da Zaki Mallako Domin Cika Burinki Bautar Da Mazajen Duniya. Sa'adda Jaruma Nashmira Taji Dukkan wadannan Jawabi Daga Bakin Boka Shahamar Sai Hankalinta Ya Ɗugunzuma Ainun Taji Tamkar Ta Janye Ƙudirinta Na Mayar Da Dukkanin MAZAJEN DUNIYA Bayin Mata, Amma Koda Ta Tuna Halin Da Mahaifiyarta Ta Rasu Akai Sai Kawai Ta Zurfafa Cikin Kogin Tunani Daga Can Sai Ta Dubi Boka Shahamar Ciki Tattausar Murya Tace "Ya Dodon Bokaye Ka Sanar Dani Sunayen Jaruman Da zasu Kasance Abokan Tafiyata Amma Baka Sanar Dani In da Zan Same Su ba. Ko da Jin Wannan Tambaya Sai Shahamar Ya Buɗi Baki Cikin Kakkausar Murya Yace" Ai Jaruma Siyamat Na Zaune A wani Ɗan Karamin Gari Da Ake Kira Da Latul-Habrus Dake Arewacin Birnin Hindu. Jaruma Shuraiba Kuwa Na Birnin Sin Kamar Yadda Na Sanar Dake, Da Wannan Nake Ya Maki Fatan Samun Nasara. Ko da Gama Faɗin Hakan Sai Ya Shafi Wani Gurun Tsafi A Damtsenshi Take Ya Ɓace Ɓat Tamkar Bai Taɓa Wanzuwa Ba. Kawai Sai Nashmira Ta Miƙe Tsaye Tsam Daga Kan Kujerar Da Take Zaune, Ta Fice Daga Ɗakin Bakwai Tsafin Tana Fita Ta Kama Dokinta Ta Haye Ta Sakar Mashi Linzami Ta Fara Falfala Azababban Gudu. Sai Da Ta Shafe Tsawon Zango Ɗaya Tana Tafiya, Tana Cikin Wannan Hali ne Kwatsam Sai Taga Wani Mahayi Yayi Fitar Burgu Daga Cikin Duhuwar Bishiyoyin Dake Dajin. Shi Zai Mahayin Yakasance Zabgegen Saurayi Kyakkyawa Na Gaban Kwatance Dogon Gashin kanshi Ya Zuba Akan kafaɗunshi, Yana Sanye Da Kayan Fata Riga Da Wando Da Akayi Su Da Fatar Damisa, A Gadon Bayanshi Yana Rataye Da Wani Rantsatstsen KWARI DA BAKA, Kuma Yana Zaune Bisa ingarman Doki Fari Sol, Kallo Ɗaya Zaka Yiwa Jarumin Ka Fahimci Cewa Ya Cika GWARZON MAYAKI Saboda Yadda Ya Tara Ƙwanji. Babu Wata 'ya Mace Mai Hankali Da Zata Yi Arba Da Wannan Kyakkyawan Saurayi Face ta Kamu da matuƙar ƙaunar shi. Sa'adda Jaruma Nashmira Tayi arba da mahayin sai ta ji linzamin dokin ta ta tsaya cak!, Aka fara Kallon-Kallo tsakaninsu na wani Lokaci. Daga bisani Nashmira Ta Katse Shirun Da Ya Wanzu Ta Hanyar Dakawa Mahayin Tsawa Cikin Matuƙar Fushi Tace Da Shi "Shin Wane Ne Kai Da Zaka Tsare Mini Hanya, Hanzarta Amsa Mini Wannan Tambaya Kafin Na Yanke Maka Hukunci Bisa Laifin Da ka Aikata Mini. Ko da Jin Wannan Batu Daga Bakin Nashmira Sai Mahayin Ya Bushe Da Dariyar Mugunta, Lokaci Guda Ya Turɓune Fuska Tamkar An Aiko Mashi Da Wasiƙar MUTUWA Ya Dube ta Cikin Gadara Ya Buɗi Baki Yace "Ai ke Ce Yafi Cancanta Ki Bani Amsar Wannan Tambayoyi Da Kika Yi Mini. Da Jin wannan Batu Sai Nashmira Ta Fusata Ainun Ta Sake Dakawa Mahayin Tsawa A Karo Na Biyu Tace Yakai Wannan Jarumi Ma'abocin GAJEREN KWANA, Haƙiƙa Ka Taɓo Tsiliyar Dodo, Kuma Ka Jefa Kanka Cikin Taskar ANNOBA ƊARI Mai Wuyar Fita, Sai Ka Shirya Ga Maza Nan Bisa Kanka. Tana Gama Faɗin Hakan Sai Ta Zaburi Dokinta Tayi Ɗauki Kanshi Gami Da Dunkule Hannayenta Tare Da Kai Mashi Naushi Domin Hanɓaroshi Daga Kan Dokin Shi. Cikin Ɓakin Zafin Nama Mahayin Ya Sunkuyar Da Kanshi Ƙasa Hannun Nashmira Ya Naushi Iska. Nan Take Suka Ruguntsume Da Azababban Yaƙi Mai Matuƙar Kwarjini, Muni, Daban Al'ajabi, Suka Wanzu Suna Kaiwa Juna Sara Da Suka Cikin Matuƙar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Ta Gaban Kwatance. Wohoho! Haƙiƙa Artabun Gwanaye Daban Yake Dana Ƙananan Ƙari, Idan Basadaukiya Ta Haɗu Da GWARZON MAYAKI Dole Gumurzu Ya Zamo Tashin Hankali, Kuka kuma Ranar Bikin Gwanaye Sai Wance Da Wance Ne kaɗai Ke Fitowa Su Taka Rawa. Babu Abinda Zai Burge Mutum Kuma Ya Bashi Sha'awa Fiye Da Yadda Jaruman Ke Yaƙar Juna Ta Hanyar Bugu Da Naushi Tamkar Jikkunansu Basu Kasance Na Jini Da Tsoka ba. Sai Da Suka Shafe Tsawon Rabin Sa'a Suna Wannan Ɗauki Badaɗi, Hatta Dawakansu Kaiwa Juna Hari Da Ƙafa Suke Yi Suna Turmutsutsu Kofatunsu Na Kartar Ƙasa Suna Tayar Da Ƙura. Sa'adda Jaruma Biyu Suka Ga Sun Shafe Tsawon lokaci Batare Da Ɗayansu Ya Samu Nasarar Koda Lakutar Jikin Abokin Gwaminshi ba Sai Suka Fusata Ainun Suka Faɗa Izuwa Kogin Tunani. Abu Na Farko Daya Faɗowa Nashmira A Rai Shi ne Ta Yaya Za'a Ce Wani Jarumi Ya Gagareta Duk Da Kasancewarta Jaruma Mafi Karfin Damtse Akaf Nahiyar Anya Kuwa Wannan Saurayi Bil'adama Ne. Aɓangaren Mahayin Kuwa Abun da Ya Faɗo Mashi A Rai Shi Ne Taya Za'a Ce Ya Kasa Samun Nasara Akan 'Ya Mace, Shin Ko Bokanshi Ya Yaudare Shi Ne Daya Faɗa Mashi Cewa Shine Jarumi Mafi Karfin Damtse A Nahiyarsu. Ko da Jaruman Biyu Su kazo Nan A Tunanin Su Sai Suka Ja Da Baya Suka Canza Tsayuwa, A Lokaci Guda Tamkar Haɗin Baki Suka Zaburi Dawakansu Suka Sake Afkawa Juna Suna Masu Canza Salon Faɗansu. Wohoho! Haƙiƙa Masu Iya Magana Sun Yi Gaskiya Da Suka Ce Idan Kiɗa Ya Canza Dole Ne Rawa Ta Canza, Faruwar Hakan Keda Wuya Sai Jaruman Suka Fara Galabaitar Da Juna, Suna Haɗawa Juna Jini Da Majina Suna Layi Jiri Na Ɗibar Su Tamkar Sun Sha Barasa Sun Bugu. Ana Cikin Wannan Artabu ne Mahayin Ya Shammaci Nashmira Ya Kirɓa Mata Naushi A Fuska, Saboda Ƙarfin Naushin Sai Da Tayi Sama Tamkar An Janye Ta Da Ƙungiya, Sannan Ta Faɗo Ƙasa Tim! A Matuƙar Galabaice. ***** Sa'adda Sarki Himras Yazo Dai-dai Nan A Labarin Da Yake Bawa Yarima Muzaifar Sai Ya Juya Ya Dubi Yarima Dake Gefanshi Aikuwa Sai Yaga Fuskarshi Cike Da Alamun Damuwa. Yarima Ya Buɗi Baki Cikin Damuwa Yace "Ya Abbana Shin Ina Dalilin Tsayar Da Wannan Labari, Haƙiƙa ina So Naji Shin Wane ne Wannan Mahayi, Nashmira Na kuɓuta Daga Hannun Sa Har Ta Tafi FARAUTAR 'Yan Mata Biyu, Tana Burinta Na Mayar Da Dukkanin MAZAJEN DUNIYA Bayin Mata?. Ko da Jin Wannan Tambayoyi Daga Bakin Yarima Muzaifar Sai Sarki Himras Ya Dube Shi Cikin Murmushi Mai Taushi Yace " Ya Farin Cikina Duba Can Ka Gani Ai Mun iso Izuwa Birnin Rum, Ina Mai Tabbatar Maka Dacewa Bayan Mun Samu Nasarar Ɗauko Sarƙar Tsafi Zan Cigaba Da Baka Wannan Hikaya, Idan Hakan Bai Samu Ba Kuwa Sai Dai Ka Nemi Littafin MAZAJEN DUNIYA Wanda Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi Ya Wallafa Domin Cigaban Hikayar Nashmira. Da Jin Amsar Wannan Tambayoyi Sai Yarima Muzaifar Ya Sunkuyar Da Kanshi Ƙasa Aikuwa Sai Yayi Arba Da Dogayen Gine-Ginen Birnin Rum. Sarki Himras Ya Dubi Aljani Narguz Yace "Yakai Narguz Sai Ka Sauke Mu A Turba Domin Mun Iso Birnin Rum. Kafin Hirmas Ya Gama Rufe Bakinshi Narguz Ya Saki Fuka-fukanshi Yayi Ƙasa Luuu! Ya Sauka A Turba, Aikuwa Koda Sakarsu Sai Suka Yi Turus !, Bawani Abu Suka Ga Ya Basu Mamaki ba Face Wata Ƙasaitacciyar Runduna Cikin Shirin Kota Kwana, Zaune A bisa Dawakai, Wasu A Giwaye Wasu A Raƙuma Wasu A Ƙafa, Makaman Yaƙinsu Kuwa Gasu Nan Birjik Marasa Adadi, A Gefe Guda Sarki Baddadul-Arus Ne Tare Gimbiya Uzaima,Sarki Huraisu Tare Da Hadimi Shaibat Zaune A Bisa Kan Aljani Zamzaru Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Ta GWARAZAN JIYA. Sa'adda Su Sarki Baddadul-arus Suka yi Arba Dasu Sarki Himras Sai Suka juya Daga Fuskantar wannan Runduna Aka Shiga Yin Kallon-Kallo Tsakaninsu Cikin Ƙiyayya Gami Da Mugun Tanadi. Sai Da Aka Shafe Tsawon Daƙiƙa Talatin A Cikin wannan Hali, Sannan Kowane Ɓangare Suka Tawo Domin Tarar Juna Batare Da Sun Sauka Daga Kan Abin Hawan Su ba, Lokacin Da Yage Saura kamar Taku Goma A Tsakani Sai Kowannen su Yaja Ya Tsaya, Aka Sake Yin Sabon Kallon-Kallo Na Ɗan lokaci. Sarki Baddadul-Arus Ya Ƙatse Shirun Daya Wanzu Ta Hanyar Budar Baki Cikin Kakkausar Murya Fuskarshi A Murtuke Yace "Yaku Abokan Gaba Na Har Abada Ku Sani Cewa A yaune Za'a Tantance Tsakanin Aya Da Tsakuwa, Naso Ace Na Isa Inda Sarƙar Tsafi Na Mallaketa Sannan Na Kawar Daku Baki Ɗaya. Caraf Sarki Himras Ya Tafi Numfashin shi yace " Kai Tsohon Maƙiyi Na Har Abada Kayi Sani Cewa Yaushe Ranar ka Ta Ƙarshe Kai Da 'Yarka Uzaima Domin Nazo Da Gagarumin Shirin Da Bantaɓa Yin Kamarshi ba. Baddadul-arus Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Sannan Yace "Ai Yaƙi Tsakanin Mu Ɓata Lokacine, Domin Dai Dole Ne Sai Dayanmu Ya Kawar Da Rundunar Dake Gabanmu Sanna Zai Samu Nasarar Kutsawa Cikin Birnin Rum, Yanzu Dai Shawara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya, Duk Wanda Ya kawar Da Rundunar Shine Ke Da Nasara. Ko da Gama Faɗin Hakan Sai Sarki Baddadul-arus Ya Zare Wata Rantsattsiyar Takobi A Damtsenshi Mai Matukar Faɗi Tsawo Gami Da kaifin Tsiya, ko da Ganin Hakan Sai Gimbiya Uzaima, Sarki Huraisu Da Hadimi Shaibat Suka yi Koyi Dashi Suna Masu Zare Nasu Makaman, Take Aljanu Zamzaru Ya Yunƙura Izuwa kan Abokan Gaba Yana ihu Da Kururuwa Mai Firgitarwa. Ko da Ganin Hakan Sai Sarki Himras, Yarima Muzaifar, Jaruma Sharilat, Tsoho kuhairu Suka Zare Makamansu, Cikin Matuƙar Zafin Nama Aljani Narguz Ya Yunƙura Izuwa kan Rundunar Abokan Gaba. A Lokaci Guda Tawagar Biyu Suka Afkawa Rundunar Birnin Rum Aka Rincaɓe Da Azababban Yaƙi Mai Matuƙar Muni, Bantsoro, gami Da Tashin Hankali. Komai Dakewar Zuciyar Mutum Da Rashin Tsoron shi Idan Yaga Yadda Filin Yaƙin Ya Rincaɓe Dole Ne Ya Firgice, Haƙiƙa Tashin Hankali Ba'a Sa Mashi Rana, Kuma idan Kaji Ana Ga Ƙi Gudu To Sa Gudu ne Bai Zo ba. Nan Fa Ihun Mazaje Ya Gami Da Ƙarar karafniyar Ƙarafa Ta Cika Dodon Kunne, Kofatun Dawakai Na Kartar Ƙasa Suna Tayar Da ƙura, Jini kuwa Ya Dunga Kwaranya, Tsayuwa, Yana Malala A ƙasa. Sassan Jikkunan Bil'adama Suka Dunga Washagi A Sararin Samaniya Suna Zubowa A Ƙasa Tamkar Ana Ruwan su ne Daga Saman. Duk In da Sarki Himras Da Baddadul-arus Suka Sanya A Gaba Sai Dai Kaga Dakaru Na Zubewa Ƙasa Matattu Suna Samar Da Fili Fetal, Tamakar Suna Sassabe A Gonar Auduga. Nan fa Manyan Sarakunan Biyu Suka Zamo Tamakar GOBARAR ANNOBA A Filin Yaƙin, Yazamana Suna Ƙoƙarin Kutsa kai Izuwa Cikin Birnin. Wani Abu Da Yake Ɗaure Masu Kai Shine, Gashi Dai Hallaka Dakarun Suke Tamakar kiyasai, Amma Tuttuɗowa Suke Daga Cikin Birnin Tamkar Bazasu Ƙare ba. A Ɓangaren Birnin Rum Kuwa Sa'adda Sarki Usulul-Haibar, Gimbiya Hulaifa Da Boka Hushaib Suka ga Irin Mummunar Ɓarnar Da Sarakunan Biyu Ke Yi Masu, Sai Zukatansu Suka Fusata Ainun Suka Kama Tafarfasa Tamkar Zata Ƙone. Cikin Matuƙar Fushi Boka Hushaib Ya Rintse Idanuwanshi Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi Gami Da Ɗaga Sandarshi Sama, Faruwar Hakan Keda Wuya Sai Akayi Wata Tsawa Da Walƙiya Sai Ga Waɗansu Irin Tsuntsayen Tsafi Sun Ratso Daga Sararin Samaniya Suna Sauka A Turba. Cikin Baƙin Zafin Nama Boka Hushaib Yakama Tsuntsun guda Ɗaya Ya Haye, Gimbiya Hulaifa Da Sarki Usulul-Haibar Suka yi Koyi Dashi, Kowannen Su Ya Zare Wasu Makaman A Jikinsu Yazamana Suna Riƙe Da Makamai Biyu. A Lokaci Guda Tsuntsayen Suka Yunƙura Izuwa kan Su Sarki Baddadul-arus, Suna Kai Masu Miyagun Hare-hare Ta Ko ina Cikin Baƙin Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Suna Ƙoƙarin Hanasu isa Izuwa Birnin. Nan fa Filin Yaƙin Ya Sake Rincaɓewa Da Masifaffan Artabu Mai Tayar Da Hankali. Wohoho! Haƙiƙa Duk Mahaluƙin Daya Taɓa Ziyartar Filin Fama Yaga Yadda Mazaje Ke Yin MUTUWAR JARUMTA Rayukan Mutane Na Salwanta Suna Rabuwa Da Gangar Jiki, Haƙiƙa Shine Yaga ma Ganin Tashin Hankalin Da Babu Kamar Shi. Sai Da Aka Shafe Tsawon Sa'a Uku Cur Ana Wannan Artabu Har Yazamana cewaiSu Sarki Himras Sun Samu Nasarar Kutsawa Cikin Gari Duk bar Su Sarki Baddadul-Arus A Baya Sun Basu Tazara Mai Yawa, Ana Cikin Wannan Artabu ne Sarki Usulul-Haibar Dake Shawagi Akan Tsuntsun Tsafi A Sama Ya Kaiwa Sarki Himras Wawan Hari Da Takobinshi Cikin Nasara Ya Yanke shi A Kafaɗa, Inda Ya Sareshin Ya Haddasa Wani Lafcecen Rauni, Kuma Ya Suɓuto Daga Kan Aljani Narguz. Ko da Himras Ya Shafa Kafaɗarshi Da Hannunshi Yaji Jini Sai Kawai Ya Taƙarƙare Ya Kurma Wawan Ihu Ya Miƙe Tsaye Zumbur Yayi Jifa Da Takobinshi Ya Cire Wani Makami A Jikinshi Mai Kama Da Lauje Ya Kurma Wawan ihu Ya Falfala Da Azababban Gudu Izuwa kan Usulul-Haibar Yayin da Ya Rage Saura kamar Taku Goma Sai Ya Dako Wawan Tsalle Sama Tamkar An Janye Shi Da Ƙungiya Ya Kaftawa Tsuntsun Da Usulul-Haibar Dake Kai Sara Take Tsuntsun Ya Ɓace Ɓat Tamkar Bai Taɓa Wanzuwa Ba, Usulul-Haibar Ya Faɗo Ƙasa Tim. Cikin Matuƙar Zafin Nama Da Fushi Ya Miƙe Tsaye Zumbur Ya Riga Izuwa Kan Himras A Lokacin Da Himras Ɗin Ya Rugo Gareshi Makaminshi Na Kartar Ƙasa Yana Fitar Da Wata Koriyar Wuta. Yayin da Ya Rage Saura kamar Taku Biyu Tsakanin su Sai Kowannen su ya Dako Tsalle Sama Ya Kaiwa Ɗan Uwanshi Sara A Fuska, Cikin Matuƙar Zafin Nama Suka Sanya Makamansu Suka Kare Harin, Sannan Suka Diro Ƙasa Bisa Gwiwoyinsu Suka Cigaba Da Kaiwa Juna Sara Da Suka Cikin Matuƙar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Ta Gaban Kwatance. Ana Fara Wannan Artabu ne Sarki Usulul-Haibar Ya Fara Gane Kurenshi Domin Ya Gane Cewa Shayi Ruwa ne Ba Abinci Mai Nauyi ba, Yazamana Daƙyar Yake Iya Mayar Da Martani, Sarki Himras ɗin Kuwa Ya Samu Nasarar Yi Mashi Sara Fiye Da Goma, Duk Sa'adda Makamansu Suka Haɗu Da Juna Sai kaji Wani karai Mara Daɗin Saurare Tamkar An Sanyawa Dutse Nakiya Yayi Bindiga. A Ɓangaren Tsoho kuhairu kuwa Wani Abin Mamaki ne Ya Faru Domin Duk da Kasancewar Idanuwanshi Basa Gani A Zahiri Amma Sai Yazamana Yana Iya Kare Hare-haren Dakaru Gami Da Mayar Da Martani, Duk Sa'adda Yaki Hari Da Mashin shi Sai Kaga Dakaru Na Zubewa Ƙasa Matattu, Kuma Yana Wurƙilawa Da Zamewa Hare-hare Batare Ya Suɓuto Daga Kan Aljani Narguz ba. Haƙiƙa Babu Wani Bil'adama Ko Aljan Dazai Ga Yadda Tsoho kuhairu ke Yin Wannan Bajintar Face Ya Tabbatar Da Cewa Ya Cika SARKIN SADAUKAI. Al'amarin Jaruma Sharilat kuwa Ta Wanzu Tana Hallaka Dakarun Sukesu Da Mashinta Suna Faɗuwa ƙasa Matattu. Da Wannan Dama ne Aljanu Narguz Yayi Amfani ya mangare Dakarun Dake Gabanshi Ya kusa Cikin Birnin, Duk Inda Ya Sanya Gaba Baka Ganin Komai Face Gwarwakin Dakaru Kwance Fulu-Fulu Cikin Jini Babu kyawun Gani. Haƙiƙa Waɗannan Dabarun Suna Ganin Tashin Hankalin Da Basu Taɓa Ganin Kamarshi ba, kai Hatta Duwatsu, Bishiyu,Dabbobi Haɗe Ƙananan Ƙwari Suna Cikin Wannan Tashin Hankali. A Ɓangaren Sarki Baddadul-arus, Gimbiya Uzaima,Sarki Huraisu Tare Da Hadimi Shaibat, Sun Wanzu Suna Kare Hare-haren Su Boka Hushaib Dake Shawagi A Saman Su Bisa Tsuntsayen Tsafi, Gami Da Mayar Da Martani Cikin Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA. Sa'adda Su Sarki Baddadul-Arus Ya An Shafe Tsawon lokaci Basu Samu Nasarar Lakutar Jikin Abokan Gwanin su ba, Sai Suka Fusata Ainun Zukatansu Suka Kama Tafarfasa Tamkar Zasu Ƙone, Kawai Sai Baddadul-arus Ya Buɗe Bakinshi Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi A lokacin Guda Ya Kaiwa Boka Hushaib Da Gimbiya Sara Da Nufin Tsinke masu Wuya. Cikin Baƙin Zafin Nama Suka Wurlila Domin Kaucewa Harin, Amma Duk da Sai Da Takobin Ta Zaftare Wani Yanki Na Gashin Kansu, kuma Ta Sauka Akan Fuka-fukan Tsuntsayen Tsafin Da Suke Zaune Akai. Nan take Suka Rikito Ƙasa Suna Masu Tsandara Ihu, Makaman Yaƙinsu Suka Faɗi Can Gefe Guda. A dai-dai Wannan Lokaci ne Sarki Baddadul-arus Ya Lura cewa Su Sarki Himras Sun Basu Tazara Mai Yawa. Koda Ganin Hakan Sai Ya Fusata Ainun Idanuwanshi Suka Kaɗa Suka yi Jawur, Jikinshi Ya kama Tsuma Yana Kyarma Har Wani Farin Hayaƙi Na Fita Daga Jikinshi. Kawai Sai Ya Kurma Wawan ihu Ya Daka Tsalle Yana Tafiya A Sama Tamkar yana Tsaye A Turba, Yana Mai Sanya Takobinshi Yana Sare Kawunan Dakarun Sarki Usulul-Haibar Suna Zubewa Ƙasa Matattu. Koda Ganin Haka Sai Gimbiya Uzaima Da Sarki Huraisu Suka Dako Wawan Tsalle Daga Kan Aljani Zamzaru Tamkar An Harbosu Daga Cikin Baka, A Dai-dai Lokacin Da Boka Hushaib Da Gimbiya Hulaifa Dake Kwance Suka Miƙe Tsaye Zumbur, Suka Zare Sabbin Makamai A Jikinsu Suka Tari Su Gimbiya Uzaima Aka Kacame Da Azababban Yaƙi Mai Cike Da Al'ajabi. Nan fa Ihu Da kururuwar Mazaje Haɗe Da Haniniyar Dawakai Suka Cika Dodon Kunne, Jini Ya Dunga Kwaranya,Tsartuwa Yana Kwaranya A ƙasa, Sassan Jikkunan Bil'adama Na Zubewa Ƙasa. Lokacin Da Aka Shafe Tsawon Sa'a Ɗaya Ana Fafata ƙazamin Artabu Tsakanin Sarki Himras Da Sarki Usulul-Haibar Kawai Sai Himras Ya Shammaci Usulul-Haibar Ya Tafka Mashi Wani Wawan Sara Al Kafaɗarshi Ta Hagu, In da Ya Sare Shin Ya Haddasa Wani Lafcecen Rauni, Usulul-Haibar Ya Kurma ihu Sannan Ya Zube Ƙasa Yana Nishin Wahala NunfashinShi Na Fita Sama-Sama. Ko da Samun Wannan Gagarumar Nasara Sai Himras Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Ya Shafi Wani Gurun Tsafi A Damtsenshi Ya Ɓace Ɓat Daga Filin Yaƙin Tamakar Bai Taɓa Wanzuwa ba. Bai Bayyana A ko ina ba Sai A Cikin Wani Ƙasaitaccen Ɗaki Ma'abocin Tsawo, Faɗi, Gaba Ɗaya Gininshi An yi Shine Da Waɗansu Duwatsu masu Daraja, Duk In Mutum Ya Kalla A Ciki Babu Abinda Zai Gani Face Kayan Ƙawa Gami Da Alatun Jin Daɗin Rayuwar Duniya Duk Yanar Gizo-Gizo Ta Lulluɓe Su Alamun Dake Nuna Cewa Wata Halitta Ta Daɗe Bata Ziyarci Wajen ba. Idan Mai Kallon Yakai Duban Shi A Ɗakin Zai Yi Arba Da Wani Gayayyen Tudu Mai Tsawo Da Faɗi Da Akayi Shi Da Zallar Karfe Zinare Da Lu'ulu'u Aka yi Mashi Feshi Da koren Ruwan Yaƙut, Wani Irin Koren Haske Na Zagaye Wajen, Daga Saman Shi Akwai wani Ɗan Madaidaicin Kasko Na Azurfa Mai Ɗauke Da Ruwa Garai-Garai Ruwan Yana Zubowa Kan waɗansu Kyawawan Furanni Dake Gazaye Da Wajen Gwanin Ban Sha'awa. Bakomai Ba ne Wannan Zagayayyen Tudu ba Face Ƙabarin Boka Aulad Ibn Zumbar Daya Fara Tun Mulki A Birnin Rum Bayan YAKIN DUNIYA na Ɗaya. Ko da Bayyanar Sarki Himras A Ɗakin Sai Kawai Ya Matsa Daf Da Kabarin Cike Da Matuƙar Farin Ciki Maral-Musaltuwa. Yana Isa Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi Yana Mai Nuna Ƙabarin Da 'yatsanshi Na Hagu Take Ƙabarin Ya Tsage Gida Biyu Wata Ƙofa Ta Bayyana Da A Kayi ta Da Karfen Jauhari Wani irin Farin Hayaƙi Ya Tuttuɗo Daga Cikinta, Batare Da Wata Bargaba ba Sarki Himras Ya Zira Hannunshi A Cikin Ƙofar Sai Gashi Ya Ɗauko Wata Sarƙar Tsafi Da Aka Sana'anta Da Zinare Da Zubar Daju Tana Sheƙi, Walwali Da Ɗaukar Idanun Duk Mai Kallo. Koda Samun Wannan Nasara Sai Sarki Himras Yayi Kamar Taku Uku Ya Sanya Hannunshi A karo Na Biyu Da Nufin Ya Shafi Gurin Tsafin shi Ya Ɓace Ɓat, Ƙwatsam! Bazato Babu Tsammani Sai Yaji An Gabza Mashi Naushi A Ƙeyarshi, Saboda Ƙarfin Naushin Sai Da Yayi Karantawa Sau Biyu Sannan Ya Faɗi Kasa Tim inda Aka Naushe shin Na yi Mashi Raɗaɗi. Cikin Matuƙar Fushi Ya Miƙe Tsaye Zumbur Yana Mai waigawa Bayanshi Domin Yaga Wanda Ya Naushe Shin, Yana Waigawar Yayi Arba Dashi Ba Wani ba ne Face Sarki Baddadul-arus Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Zaune A Ƙasa Ya Tanƙwashe Ƙafafuwanshi Hannunshi Riƙe Da Wani Gabgegen Gatari Na Ƙarfen Jauhari, A Wuyanshi Yana Rataye Da Wata Sarƙa Mai Matuƙar Kama Da Wacce Sarki Himras Ya Ɗauko A Cikin Ƙabarin Boka Aulad, Fuskarshi Cike Da Annuri. Sa'adda Sarki Himras Yayi Arba Da Baddadul-Arus Sai Ya Cika Da Matuƙar Mamaki Yace A Cikin Ranshi Ya Akayi Baddadul-arus Ya San Dacewa Ina Cikin Wannan Ɗaki, A Ina Ya Samo Waccan Sarƙa Dake Wuyanshi Da Tawa Da waccan Ɗin Wacce Ce Ta Gaskiya?. Amsar Tambayoyin Da Sarki Himras Ya Kasa Bawa Kanshi Kenan, Nan Take Zuciyarshi Ta Kama Tafarfasa Tamkar Zata Ƙone, Kawai Sai Ya Zare Wata Gabgegiyar Takobi A Damtsenshi A Cikin Kubenta Ya Falfala Da Azababban Gudu Izuwa kan Baddadul-arus Yana Mai kurma Wawan ihu. Yayin da Sarki Baddadul-Arus Ya Hango Sarki Himras Ya Rugo Izuwa Gareshi Yana Kurma ihu Hannun shi Riƙe da Takobi Tsirara, Sai Kawai Ya Taƙarƙare Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Sai Da Yayi Dariyar Ta Ishe Shi Sannan Ya Murtuke fuska Tamkar An Aiko Mashi Da WASIƘAR MUTUWA Yayi Wuf! Ya Miƙe Tsaye Ya Ruga Gareshi Domin Tarar Juna, Lokacin da aka haɗu Sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro haɗe da tashin hankali. Lokacin Da Aka Ruguntsume Da Azababban Yaƙi Tsakanin Sarki Baddadul-Arus da Himras A Ɗakin KUSHEWAR Margayi Boka Aulad, Sai Suka Wanzu Suna Kaiwa Juna Sara Da Suka Cikin Matukar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Ta Gaban Kwatance. Duk Sa'adda Makamansu Suka Haɗu Da Juna Sai Dai kaga Tartsatsin Wuta Ya Tashi Gami Da Ƙara Mara Daɗin Saurare, Sai da aka shafe tsawon Rabin Sa'a ana wannan Fafatawa, Har Yazamana Cewa Duk Makamansu Sun Lalace Sun Durƙushe A ƙasa Amma Har A Wannan lokaci Basu Samu Nasarar Lakutar Jikin Abokan Gwaminsu ba. Al'amarin Daya Harzuƙa Zukatansu Kenan Suka Kama Tafarfasa Tamkar Zasu Ƙone, Suka Faɗa Izuwa Kogin Tunani Domin Samun Mafita. Abu Na Farko Daya Faɗowa Sarki Himras A rai Shine Me Yasanya ya kasa samun Nasara Akan Baddadul-Arus Bayan Cewa Yana Riƙe Da Sarƙar Tsafi A Hannunshi, Shin ko Sarƙar Jabu ce, wacce ke Sanye A wuyan A Wuyan Baddadul-arus Ita ce Ta Gaskiya. A ɓangaren Sarki Baddadul-arus Kuwa Abinda Ya Faɗo Mashi A rai Shine Tunda Yanzu Sarki Himras Ya kasa Tantance wacce ce Sarƙar Tsafin Ta Gaskiya Me Zai Hana ka Shamma Ce shi ka kwace Sarƙar. Sa'adda Sarakunan Biyu Suka Zo Nan A Tunaninsu Sai Suka yi Wurgi Da Makamantansu kuma Duka ja Da Baya Sukayi Cirko-Cirko Ana kallon juna, Tamkar waɗansu zakaru. Kawai Sai Kowannen su Ya Dunƙule Hannayenshi Ya Ruga Izuwa kan juna Suna ihu Da Kururuwa Mai Firgitarwa, Suna haɗuwa Suka kacame da Sabon Azababban Yaƙi Suna Kaiwa Juna Naushi Da bugu hannu da kafa. Wohoho! Haƙiƙa Maza Sune Maganin Maza Ana Canza Wannan Salon Faɗane Sai Labari Yasha Bamban, Domin Cikin Abinda Bai Gaza Daƙiƙa Talatin ba Jaruman Sun fara haɗawa juna Jini Da Majina Suna Layi Jiri Na Ɗibarsu. A wasu lokutan Idan Ɗayansu ya gabzawa Abokin Gwaninshi Naushi Sai kaga ya kife A Ƙasa Amma Sai ya Miƙe Tsaye Zumbur Yana Nishin Wahala, Shi ma ya mayar da martanin. Lokacin Da Manyan GWARAZAN JIYAn Suka Ga Cewa Ana Yin Kare Jini Biri Jini Ma'ana Karfi Yazo Ɗaya Sai Suka Shiga yin Amfani Da ƙarfin Sihirin Tsafi Suna Turawa Juna Miyagun Abubuwa Domin Hallaka juna Idan Sarki Baddadul-arus Ya Tura Himras kibiyoyin Shiri kafin Su Isa inda Hirmas ke Tsaye Ya Nuna su Da Ɗanyatsanshi Na Hagu Take Zasu Barke Su Zama Ruwa Su Narke A Ƙasa, Sai Himras Ɗin Ya Turawa Baddadul-arus Bakar Wuta shi kuma Baddadul-arus Sai Ya Tura mashi Ƙanƙara Idan Suka Haɗu Da juna Sai Kaji sunyi Bindiga Tamkar Saukar Aradu. Haka dai Zaratan Jaruman biyu Yazamana Cewa sun turawa Juna Miyagun Abubuwan Sihiri Fiye Da Kala Saba'in Amma Basu Nasarar Lakutar Jikin juna ba. Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA Abin Tsoro ne Babu Abinda Zai Ɗimauta Zuciyar Mutum Face yadda GWARAZAN MAYAKAN Ke Yakin Cikin Matuƙar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Tamakar Waɗansu Fusattun Zakoki Da suka Shafe mako guda basu yi kalaci ba Suka yi Arba Da Barewa Guda Ɗaya. Ana Cikin Wannan Guguntsumin Artabu ne Sarki Baddadul-arus Ya Shammaci Sarki Himras Ya Gabza Mashi Naushi a Haƙarƙarinshi Na Dama, Saboda ƙarfin Naushin Sai Da Yayi Katantanwa A sama Sau uku Sannan ya faɗo Ƙasa Tim Yana Mai Tsandara Ihu Sarƙar Tsafin dake Hannunshi Ta faɗi Can Gefe Guda. Kafin Sarki Himras Yayi Wani Yunƙuri Baddadul-arus Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi Ya Face Ɓat Tamkar Bai Wanzuwa ba Yana Mai Ƙyalƙyala Mashi Dariyar Mugunta. Cikin Matuƙar Fushi Mara Misaltuwa Sarki Himras Ya Miƙe Tsaye Zumbur Yana Mai kai dubanshi Izuwa inda Sarkar Tsafinshi Ta faɗi Aikuwa Sai Yaga wayam Babu ita, kawai Sai Ya Taƙarƙare Ya Kurma Wawan ihu, kawai Sai Ya Shafi Gurun tsafin Ya Shafe shi Da hannun shi Na hagu Take Ya ɓace ɓat Tamkar Baitaɓa wanzuwa ba. Bai Bayyana A ko ina ba Sai A Filin Yaƙi Sai Ya Cika Da Matuƙar Takaici Da Baƙin Ciki, Bakomai Ya Gani ba face Babu sarki Baddadul-Arus Da Dukkanin Tawagarshi. Cikin Matuƙar Fushi Ya Zira Hannunshi A Aljihunshi ya Ɗauko Madubin Tsafin Ya Shafe shi Da hannunshi Na Hagu Take Aljanu Zamzaru ya Bayyana Ɗauke Dasu Sarki Baddadul-arus A Gadon Bayanshi Yana Tsala Gudu A Sararin Samaniya. Ko da Ganin Hakan Sai Sarki Himras Ya Falfala da Azababban Gudu yana nufi inda Aljani Narguz Yake Yana banke dakarun Dake Gabanshi Yana Samarwa Da Kanshi Hanya Ta ƙarfin Tsiya, Yana Isa Ya Daga Tsalle Ya Haye Gadon Bayan Nargzu Yana Mai Cewa Da shi " Ya Hanzari Ka Ɗauko Yarima Da Abokan Tafiyarmu Ka bi Sahun su Aljani Zamzaru. Da jin Wannan Umarni Sai Narguz Yayi Wuf! Cikin Baƙin Zafin Nama ya Sanya Hannunshi Ɗaya Ya Ɗauko Yarima Muzaifar, Jaruma Sharilat da Tsoho kuhairu Ya Ɗora su bisa Gadon Bayanshi Ya Buɗe Fuka-fukanshi Ya Luluƙa Cikin Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya. ****** Sa'adda Sarki Usulul-Haibar, Gimbiya Hulaifa da Boka Hushaib Suka ga Irin Gagarumar Ɓarnar Da Da su Sarki Himras suka yi masu Sai Suka Cika Da Matuƙar Baƙin Ciki Maral-Musaltuwa. Cikin Hanzari Boka Hushaib Ya Ɗauko Madubin Tsafin shi Ya Shafe shi Da hannunshi Na Hagu Ya Shiga Gudanar Da Bincike, Amma Sai Madubin Yayi Bindiga Ya Tarwatse. Koda Ganin Wannan Al'amari Sai Sarki Usulul-Haibar Ya yanke Jiki Ya Faɗi Ƙasa Sumamme Cikin Figici Boka Hushaib Ya ƙwallawa Masu Magani kira Suka Ɗauki Usulul-Haibar bisa Wani Ƙayataccen Gado Suka Ruga dashi zuwa Cikin gidan Sarauta Domin Ceto Rayuwar shi. A Sannanne Jiri ya fara Ɗibar Gimbiya Hulaifa Da Boka Hushaib sakamakon jinin Dake Zuba A Jikin su, Cikin Hanzari Aka Ɗauke Su A Cikin Wani Ƙasaitaccen Keken Doki Aka nufi Gidan Sarauta masu magani Suka Shiga Basu Taimakon Gaggawa. A Dai-dai Wannan Lokaci Ne Dakaru Suka shiga Kwashe Gawarwakin waɗanda suka Rasa Rayukansu, Waɗanda Suka Samu Miyagun Raunuka Kuwa Aka Shiga Basu Taimakon Gaggawa. Nan fa Gaba Ɗaya Birnin Rum Ya Kaure Da koke-koken Jama'a Yara,mata da tsofaffi wasu na kuka ne bisa Rasa Masoyansu Da iyayensu. A iya Tsawon Wanzuwar Birnin Rum Basu taɓa Ganin Tashin Hankali kamar Na Wannan Rana ba, Domin babu wani Mutum Da bai Rasa Ɗan Uwanshi Na Jini ba. Babu Abinda Zai Jefa Tausayi A Zuciyar Mutum kuma Ya Sanya shi Zubar Da Hawaye Face idan Yaga Yadda Ƙananan yara ke Rungume Gwarwakin Mahaifansu Suna Rusa kuka abin Ban Tausayi Tamkar Ransu Zai Fita. Wannan Shi ne Abinda Yafaru A birnin Rum Bayan Sarki Baddadul-arus Ya Sami Nasarar Ɗaukar Tsafi Dake Ajiye A Cikin Tsohon ƙabarin Boka Aulad. ***** Lokacin da Aljani Narguz Yabi Sawun su Sarki Baddadul-arus A Gadon Bayanshi Yana Ɗauke Da Sarki Himras, Yarima Muzaifar,Tsoho Kuhairu Da Jaruma Sharilat, Sai Ya wanzu yana keta Gajimare . Sai da Akan Shafe Rabin Sa'a ba'a ji koda Ɗuriyar su Sarki Baddadul-arus ba, Al'amarin Daya Ɗugunzuma Hankalin kowa Kenna musamman Sarki Himras Ya Zira Hannunshi A Aljihunshi Ya Ɗauko Madubin Tsafin shi ya Shiga Gudanar Da Bincike Domin Gano inda su Sarki Baddadul-arus suke, Daƙyar da Siɗin Goshi Ya Gano dalilin Daya Sanya ya kasa Ganosun Dalilin Hakan kuwa Shine, Matsawar Suna Riƙe Da Wannan Sarkar Tsafi Babu wani sihiri Da zai yi tasiri a kansu. Sa'adda Sarki Himras yaga Wannan Al'amari Sai Ya Cika Da Matuƙar Baƙin Ciki Har Kwallar Takaici Ta Zubo Daga Idanuwanshi. Al'amarin Daya Sanya Yarima Muzaifar Dake Zaune A gafen shi Ya Shiga Damuwa Kenan Ya Dubeshi Yace " Ya Abbana Shin ina Dalilin Wannan Ƙwalla taka?. Ko da jin Wannan Tambaya Sai sarki Himras Ya share Hawayen dake Fuskarshi Ya Dubeshi Yace " Ya Abin Alfaharina kayi Sani binciken da na Gudanar A Halarar Tsafina Na gano cewa Matsawar Su Sarki Baddadul-arus suna Tare Da wannan Sarƙar Tsafi Bazamu iya Samun Nasara Akan su ba. Don haka akwai bukatar mu yada zango Domin Mu Tattauna, Sanin kankane Cewa Babu Wanda Ya Isa Ya mallaki TAKOBIN SIHIRI Face Ya Tashi Boka Sharubu Daga KUSHEWAR shi Domin Shine Kaɗai Yasan Ƙa'idojin Tafiyar. Ko da jin Wannan Bayani Sai Yarima Muzaifar Ya Shiga Cikin Matukar Damuwa, Batare Da wani Ɓata lokaci ba Sarki Himras Ya Dubi Aljani Narguz Dashi "Yakai Narguz Ina So Mu Yada Zango Anan. Da Jin Wannan Batu Sai Nargzu Yace "Ya Shugabana Shin Mun Haƙura ne Da bin sawun abokan gaba ne. Ko da jin hakan Sai Himras Ya Fusata Ainun Ya Dakawa Narguz Tsawa wacce Ta Sanya Hantar Cikinshi Ta Kaɗa Tsaro Ya Kamashi, Ya Dube shi Cikin Fushi Yace " Zancen Banza kenan, Yakai Narguz kayi Sani Cewa Duk Abinda Na Faɗa Umarni nake Baka bawai Neman Shawara Nake ba. Sa'adda Narguz yaji wannan batu sai Jikin shi yakama Tsuma Yana Kyarma, Bakinshi Na Kyarma Yace "An Gama ya Shugabana Tuba nake yi, Yana Gama Faɗin Hakan Ya saki Manyan Fuka-fukanshi Yayi Ƙasa Luuu! Ya Sauka A Turba. Inda Ya aka Sauka Yakasance Waje Mai Tattare Da Bishiyu, Duwatsu,koramu Wata irin Ni'imtacciyar Iska Na kaɗawa Rassan Bishiyu Nayin Rangaji, Waɗansu Tsuntse Masu Ƙyawun launi Na Shawagi A Sararin Samaniya Suna Fitar Da wani Sautin Kuka Mai Ɗankaran Daɗi. Tabbas Wannan Waje Ya Cika Mai Matuƙar Abin Sha'awa, Babu Wani Bil'adama Da Zai Arba Da shi Face Ya kwaɗitu Ya Rayu A Wajen. Batare da ɓata lokaci ba kowa ya Shiga Tsaftace Jikin shi Da Ruwan Korama, Sannan Aka Kafa Ta tuna, Yarima Tare Da sarki Sharilat Da Tsoho kuhairu, Shi kuwa Aljanu Narguz Sai Ya Zare Wata Rantsattsiyar Takobi A Damtsenshi Ya Shiga Yin Rangadi Domin Tabbatar Da Tsaro A Tsakanin Tantunan Kasancewar Duhun Dare Yafara kawo Kai. Lokacin Da Yarima Muzaifar Da Sarki Suka Samu Nutsuwa Sai Suka Ɗauko Abin Guzurinsu Suka Shiga Kimtsa Cikin su. Bayan An Kammala ne Sai yarima ya Dubi Sarki Yace Ya Abbana Shin Baka ƙara sa bani labarin jaruma Nashmira ba wacce take burin Bautar Da Mazajen Duniya? Ko da Jin Wannan Tambaya Sai Sarki Yayi Shiru Sannan Ya ce "Ya Ɗana Duk da cewar A halin yanzu ina Cikin Damuwa bisa Suɓucewar Sarkar Tsafi Amma zan baka cigaban Hikayar Nashmira a kaƙaice, Sai ka saka kunne kaji yadda Takasance. ****** Ko da samun wannan nasara sai baƙon Mahayin ya sauko daga kan dokin shi ya zare wata Sharɓeɓiyar takobi a Damtsenshi yana mai bushewa da dariyar mugunta, ya taka Ƙafafuwanshi har zuwa in da Nashmira ke Kwance babu alamun numfashi a tare da ita. Ko da ya rage rage bai wuce taku ɗaya tsakanin su ba sai sai kawai ya ɗaga takobin domin ya datse mata wuya. Kwatsam bazato babu tsammani sai ya ga Nashmira taja Gwauron numfashin Idanuwanta sun buɗe, cikin zafin nama ta wurƙila gefe guda takobin ta nutse a cikin ƙarƙashin ƙasa. Cikin zafin nama ya sa ke zare takobin ya kaiwa mata sara a karo na biyu, ta kaucewa harin a karo na biyu, sannan ta sanya ƙafafuwanta biyu ta bugi Ƙafafun shi take ya faɗi ƙasa rikica! takobin shi ta faɗi can gefe guda. Cikin Gwaninta Nashmira ta yi wuf ta mike tsaye ta ɗauki takobin Mahayin ta sanya tsininta akan wuyan shi, har tsinin ya yanke shi jini ya zuba kaɗan, ta ƙura ma shi idanu. Sannan daga bisani ta ɗauke takobin ta jefer da ita Sannan ta taka da ƙafafuwanta ta nufi inda dokin ta yake takama ta haye ta sakar mashi linzami, amma sai ta taga mahayin yasha gabanta Fuskarshi cike da annuri ya dube ta ya ce "ya JARUMAR JARUMAI kiyi sani cewa iya tsawon rayuwata bantaɓa yin Artabu da wata jaruma da tayi nasara akai na ba sai ke, lokacin da mahaifina ke raye ya taɓa faɗa mani cewa har abada bazan taɓa cika burina na zamowa SARKIN SADAUKAI ba face na haɗu da Jarumar da na fafata yaƙi da ita ta yi rinjaye a kai na. Saboda haka ina roƙon ki ki sanar da ni labarin rayuwar ki domin na gasgata wasiyyar abbana. Ko da jin Wannan batu daga bakin mahayin sai Nashmira ta bushe da dariya daga bisani ta ƙura mashi idanu tana yi mashi wani kallo mai ɗauke da alamar tambaya, sannan tayi gyaran murya tace "yakai wannan jarumi kayi Sani cewa ni ma kai ne jarumi na farko a rayuwata da ya taɓa samun nasara a kai na, amma ina mai baka shawara da ka janye niyyar ka na jin labarin rayuwata, domin babu abinda zai jefa ka face wasu musibun. Koda Jin wannan batu sai mahayin ya cika da matuƙar mamaki ya ce "ya Ma'abociyar kyawu shin mene ne ke tattare da labarinna ki?. Da jin wannan tambaya sai murmushi ya suɓucewa Nashmira ta ce "yakai wannan jarumi ka yi sani cewa a rayuwata babu abinda na tsana fiye da 'ya'ya maza, burina shine na mallaki waɗansu abubuwa da zasu kai ni ga waccan matsayi na mayar da dukkan MAZAJEN DUNIYA bayin Mata, ina so Yazamo cewa 'ya'ya mata ne ke riƙe da Sarautar ƙasashen duniya. Da jin amsar wannan tambaya sai Mahayin ya cika da matuƙar mamaki maral-misaltuwa, ya yi shiru ya na mai Sunkuyar da kanshi ƙasa yana zurfafa cikin Kogin tunani. Daga can sai ya ɗago da kanshi ya dube ta cikin tattausar murmushi ya ce “ Ya ke sarauniyar kyawawa a sani na tun wanzuwar Duniyar maza ke riƙe da Sarautar duniya. Shin ta ya za a ce maza su zama bayin Mata, Amma masu iya magana na cewa ba a ƙwacewa yaro garma Kuma tabbas duk Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan daka. Da farko dai suna na Hufairu Ibn shaddad mahaifina mashahurin Matsafin ne kuma maƙeri da ya yi shura a nahiyar mu. Kasancewar ni da mahaifina muna rayuwa ne a daji babu abin da ke rabu mu ko da kwanciyar barci haka ne ya sanya mu ka shaƙu ainun da juna. Tun ina da shekara sha biyar a duniya na ke shiga daji na farauto muguwar dabba, Akwai wata rana da ‘yan fashi tsautsayi ya kawo dajin mu, Ni kaɗai na afka ma su da yaƙi na hallaka su baki ɗaya. Cikin Matuƙar farin ciki mahaifina ya rugo Izuwa inda nake ya rungume ni a ƙirjinshi. Yana mai cewa haƙiƙa ɗana ka gajeni a sadaukantaka ɗari-bisa-dari sai dai ina so ka zamo mai cika babban burina. Cikin matuƙar mamaki na dubi Abbana na ce “Ya Abbana shin yanzu akwai wani burinka da ya huce na gaje ka a jarumtaka? Mahaifina ya yi Murmushi mai taushi ya dafa kafaɗuna bayan ya janye jikin shi daga nawa sai ya dube ni a karo na biyu ya ce “Ya farin Cikin Zuciyata kayi Sani cewa babban burin da na ke so ka cika mini a duniya shine ka mallaki wata Sihirtacciyar Ɗamara. Shekaru ɗari da suka gabata na taɓa ƙera wata ɗamara a lokacin ina bauta a ƙarƙashin wani mashahurin sarki mai suna Hafzul-Masnur. Hafzul-Masnur yakasance mashahurin Matsafin attajiri kuma Gwarzon mayaƙi a filin fama. Bisa wannan dalili ne ya sanya ya yi fice Kuma ya zamo gagarabadau a nahiyar. Wata rana Hafzul-Masnur yana gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi sai ya gano cewa na sa’anta wata ɗamara wacce ni kai na bansan amfanin ta ba, Ya gano cewa ɗamarar tana ɗauke da waɗansu muhimman sirrikan tsafi guda miliyan biyu, Domin na ƙera ɗamarar ne da karfen zoben tsafin sarkin bokaye Aljanu. Babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki Ɗamarar face yazamo ANNOBA ƊARI ga Duniya kuma SARKIN SADAUKAI. Bisa wannan dalili ne yasanya sarki Hafzul-Masnur ya buƙaci na ba shi ɗamarar ni kuma na ƙi ba shi goyon baya. Saboda hakan ya yi ta gana mani azaba iri daban daban. Da na fahimci cewa idan ban bashi ɗamarar ba zan iya rasa rayuwata sai kawai na yanke shawarar na na shi. Bayan na mallaka ma shi ne wani hatsabibin boka ya sace ɗamarar domin ya mallaki sirrina tsafin da ke jikin ta. Amma Sai ajali ya riske shi bai cika wancan burina shi ba. Ya ɗana kayi sani cewa ba zaka iya cika mani wannan burina wa ba face na ka haɗa kai da wata hatsabibiyar jaruma da binciken halarar tsafi ya tabbatar da cewa ba zai yiwu na iya ganin siffofin Jarumar ba. Kawai dai alama ta farko da za ka gane Jarumar shi ne idan ka fafata yaƙi da ita za ta yi nasara a kan ka, Alama ta ƙarshe ita ce tana da wani ƙazamin ƙudiri na ta na mayar da dukkan MAZAJEN DUNIYA bayin mata. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin rayuwata ya JARUMAR ASALI. Sa’adda Jaruma Nashmira ta ji wannan jawabi daga bakin jarumi Hufairu ɗan maƙeri kahzib sai ta cika da matuƙar mamaki kuma ta yi shiru ta na mai zurfafa cikin Kogin tunani. **** Lokacin da sarki Himras yazo dai-dai nan a labarin da ya ke bawa yarima muzaifar sai ya dube shi ya ce “Ana zan tsaya da baka wannan Hikaya ta jaruma Nashmira da Hufairu Ibn kahzib, Domin mu tattauna akan muhimmin abin da ke gaban mu, Sai ka biyo ni Izuwa masaukin su Sharilat amma idan kana son cigaban wannan hikaya sai ka nemi littafin FARAUTAR MAZAJE wanda fashin masanin hikayoyin nan ya wallafa wato SUFI. Ko da gama faɗin hakan sai sarki ya miƙe tsaye ya fice daga tantin, cikin hanzari yarima ya yi koyi da shi fuskar shi cike da alamun damuwa bisa katse hikiyar jaruma Nashmira da sarki ya yi ma shi. Da isowar su zuwa bakin tantin sai sarki ya yi gyaran murya sau biyu sannan ya kunna kai zuwa ciki yarima na biye da shi, Suna shiga ciki suka zauna a bisa kujeru dake fuskantar su sharilat. Da ya ke a wannan lokaci tantin a haskake ya ke da fitilar ice, Suna ganin fuskokin junan su ƙuru-ƙuru sai yazamana Yarima Muzaifar da Jaruma Sharilat na satar kallon junansu cike da tsantsar so da ƙauna. Sarki Himras Ya shirun da wanzu ta hanyar buɗe baki ya ja gwaron numfashi ya yi gyaran murya ya ce “Ya abokan tafiyarmu kuna da sani akan abin da yafaru tsakanin mu da su Sarki Baddadul-arus na kuɓucewar Sarkar Tsafi daga hannun mu shin yanzu me abin yi ?. Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Himras sai kowa ya yi shiru aka rasa wanda zai ce kala. Sai daga can tsoho kuhairu ya yi gyaran murya ya ce “Yakai wanan sarki mai daraja kayi sani cewa ai koda su sai sarki Baddadul-Arus sun samu nasarar tashin boka Sharubu daga kushewar shi babu tabbacin zai amince da buƙatar su ta yi masu jagora Izuwa fadar Sarkin bokaye domin ɗauko SIHIRTACCEN KUNDI da takobin sihiri, Domin masu iya magana na cewa ƙaɗe mage ba yankawa ba ne. A iya nazarin da na yi game da wannan tafiya tamu, Tunda dukkanin mu Sadaukai ne majiya ƙarfi za mu iya jure duk wata musiba da bala’i, Zai yi kyau mu tafi kai tsaye zuwa fadar Sarkin bokaye domin ɗauko takobin sihiri, Tun da dama saboda ita ne zamu nemi buƙatar boka Sharubu. Lokacin da tsoho kuhairu yazo nan a jawabin shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki, Domin suna ganin cewa kuhairu ya kawo shawara mai kyau. Shiru ne ya mamaye wajen a karo na biyu sai daga bisani sarki Himras Ya dubi kuhairu cikin alamun matuƙar damuwa ya ce “ Ya kuhairu haƙiƙa ka kawo shawara mai kyau sai dai ina so ka kiyi tunanin cewa ta ya zamu mallaki SIHIRTACCEN KUNDI bayan cewa boka Sharubu shine yasan dokokin tafiyarmu? Ko da jin wannan tambaya sai kuhairu ya yi guntun murmushi mai kama da yaƙe sannan ya dube shi ya ce “A wasu lokutan ilimin tsafi yana bayyana mana abinda ba zai tabbata ba, Abin da za ka yi nazari akai shi ne shin kafin a mallaki SIHIRTACCEN KUNDI ne boka Sharubu zai yi amfani ko kuwa bayan an mallaka, Idan kana so ka tabbatar da hakan sai ka sa ke gudanar da bincike bisa halarar tsafin ka kafin wayewar gari. Sa’adda sarki Himras ya ji wannan ƙarin bayani daga bakin tsoho kuhairu sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, Batare da wani ɓata lokaci ba su ka yi bankwana da su Sharilat su ka koma Izuwa tantinsu. Wannan shi ne abin da ya wakana a bangaren su Sarki Himras. ****** Al’amarin su Sarki Baddadul-arus kuwa, Tun sa’adda aljani Zamzaru ya ɗauke su daga filin yaƙi, Bayan sarki Baddadul-Arus ɗin ya samu nasarar kwace Sarƙar tsafi daga hannun Sarki Himras a cikin ɗakin kushewar boka Aulad. Sai Zamzaru ya cigaba da tsala azababban gudu babu sassauc, Ana cikin wannan tafiya ne Gimbiya Uzaima ta sunkuyar da kanta ƙasa ta yi shiru tana mai zurfafa cikin Kogin tunani. Abu na farko da ya faɗo mata a rai shi ne tabbas zuciyar ta ta kamu da matuƙar kaunar sarki Huraisu wacce baza ta iya jin kira ba, Shin yanzu ta wace hanya zan bayyana ma shi sirrin dake zuciya ta, Wani ɓangaren kuwa na cewa da ita idan ki ka yi haka kin zubar da darajar ki da ƙimar ki, Wai shin ma kin manta ne cewa sarki Huraisu ya yi wannan tafiya da ku ne domin ya samu irin macen da ya ke da burin ya aura, Kenan yanzu ke kina yin son maso wani ne ƙoshin wahala. Sa’adda gimbiya Uzaima tazo nan a tunanin ta sai hankalin ta ya ɗugumzuma ainun. Yanzu duk tsananin kyawuna da ‘ya’yan sarki ke mutuwa saboda da soyyayya ta amma ace yau ni ce wani namiji zai yi tarayya da ni fiye da Sa’a ashirin amma bai kamu da SO na ba. Aɓangaren sarki Huraisu kuwa babu abinda ke yi ma shi yawo a zuciya face ya lura da irin kallon da gimbiya Uzaima ke ma shi a lokacin da suke fafata yaƙi tabbatar ya nuna ta kamu da matuƙar ƙaunar shi. Amma kuma ai Uzaima ba ta cika sharuɗɗan da nake so wacce zan rayu da ita ta kasance ba, Wato ta ɗara ni a baiwa, Kuma ta yi tsawon sa’a goma tare da ni batare da kamu da so na ba duk da irin. Matuƙar kyawuna, Haka dai sarki Huraisu ya cigaba da wannan tunani. Ana cikin wannan hali ne sarki Baddadul-Arus ya ji Jikin shi ya na yi ma shi tsami sakamakon raunukan da ya samu a filin yaƙi. Kuma ga shi duhun dare ya fara kawo kai don haka sai ya umarci aljani Zamzaru da ya sauka a turba. Bayan sauka ne sa aka kafa tantuna kowa ya shiga yin kalaci, Shi kuwa Baddadul-Arus sai ya cire sulken yaƙin dake jikin shi ya sanya kanshi magani kawai sai ya kwanta bisa gadon shi ya fara sharar barci. Wannan shi ne abin da ya wakana da tawagar sarkin Baddadul-arus. ****** Lokacin da likitocin birinin Rum su ka duƙufa akan sarki Usulul-Haibar domin ceto rayuwar shi. Sai suka shafe tsawon sa'a ɗaya amma ba su ga ya yi wani motsi ba, Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin su kenan. Ana cikin wannan hali ne boka Hushaib da Gimbiya suka bayyana a gare su cikin tashin hankali. Ya yin da suka iso daf da gadon da sarki ke kwance sai shugaban likitocin wani dattijo mai kakkaura mai cikar Kamala ya dubi boka Hushaib cikin ladabi ya ce "Ya shugabana dukkan ƙoƙarin mu ya gaza na ceto rayuwar sarki abu ya ci tura. Ko da jin wannan batu daga bakin likita zayyan sai hankalin boka Hushaib da Gimbiya ya sake dugunzuma ainun. Cikin matukar damuwa Gimbiya ta matsa daga da inda sarki ke kwance ta zauna a gefen gadon tana mai ƙura ma shi idanu. A dai-dai wannan lokaci ne boka Hushaib ya ɗagawa likita zayyan hannu, Kamar zayyan yasan abin da ya ke nufi sai kawai ya ja tawagar shi su ka fice daga turakar yazmana cewa saura mutum uku kacal, wato Gimbiya Hulaifa, Hushaib da sarki Usulul-Haibar. Ko da ficewar su likita Xayan sai boka Hushaib ya shiga yin wasu 'yan tsibbe-tsibben shi ya na mai zagaya izgar tsafin shi akan sarki usulu-haibar. Sai da daƙiƙa ɗari biyu ta shuɗe a cikin wannan hali ne har Hushaib ya jiƙe sharkaf da gumi tamkar an tsoma shi a ƙaramar, Amma bai ga sarki usulu-haibar ya yi motsi ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin shi tare da gimbiya Hulaifa, Har gimbiya Hulaifa ta fara zubar hawaye domin ta na ganin cewa shi kenan sarki ya mutu. Ana cikin wannan hali ne sai kawai aka ji sarki usulu-haibar ya saki ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya ja gwauron numfashi sannan ya buɗe idanunsa shi a hankali. Cikin matuƙar farin ciki gimbiya Hulaifa ta rungume mahaifinta su duka biyun suka fashe da kukan farin ciki. Tsawon daƙiƙa ashirin a cikin wannan hali ne sai daga bisani ne gimbiya ta janye jikinta daga na shi, Usulu-haibar ya yunƙura domin ya miƙa zaune amma sai ya ji sashin jikinshi na hagu ya yi ma shi nauyi bazai iya tashi ba. Ko da ganin hakan sai boka Hushaib ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya na mai nuni da yatsanshi na hagu ga ɓarin jikin sarki na hagu. Kawai sai aka ga fuskarshi ta canza daga annuri izuwa ɓacin rai, Idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur tamkar garwashin wuta ya dubi gimbiya cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "Ya shugabata ina mai baƙin sanar da ke cewa mahaifinki ya kamu da cutar shanyewar ɓarin jiki, Kuma shine mutum na farko da ya taɓa kamuwa da ɗaya daga cikin cututtukan da za su addabi al'ummar mu sakamakon suɓucewar sarƙar tsari mai daraja daga wajen mu. Ko da jin wannan jawabi daga bakin boka Hushaib sai gimbiya Hulaifa da sarki Usulu-haibar suka sake rungume juna a karo na biyu suna masu fashewa da kukan baƙin ciki. Al'amarin da je fa tausayi a zuciyar boka Hushaib kenan har ya ji kwalla ta cika ma shi idanu. Daga bisani ne gimbiya ta janye jikinta daga na sarki ta dubi Hushaib fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Ya abin dogaro shin yanzu ta wace hanya mahaifina zai warke daga wannan lalura da ta same shi?. Sa'adda boka Hushaib ya ji wannan tambaya daga bakin gimbiya Hulaifa sai ya yi shiru yana mai sunkuyar da kanshi ƙasa ya shiga dogon nazari. Daga can sai ya dago da kanshi sama ya dubi gimbiya Hulaifa ya yi gyaran murya sannan ya buɗe baki ya ce "Ya tauraruwar birnin Rum ki sai cewa mai martaba da dukkan wanda ya kamu da wata cuta a wannan birni namu da ya kamu da da wata cuta ba zai taɓa warkewa ba face yasha ruwan sassaken wata itaciya wacce a halin irin gud ɗaya ce jal ta rage a duniya bishiyar ta na cikin wani kogon dutse da ke cikin dajin sarirul-maut da ke yammacin duniya. Kafin mutum ya isa dajin inda bishiyar Shajarul-kair ta ke dole ne sai ya ƙetare waɗansu miyagun dazuka. Daji na farko yakasance na waɗansu hatsabiban kuraye sara da suka ba sa tasiri a kan su, tsakanin ƙarfin damtsen su da yawan ya huce tunani. Daji na biyu na wani hatsabibin maridi ne saboda shirin shi yana ina canza siffa duk yadda ya ke so, ƙarfin damtsen mutum bazai ƙwance shi ba face matuƙar sa'a da rabi. Na ukun kuwa yakasance na waɗansu miyagun mayaƙan aljanu masu shan jinin bil'adama, A halin yanzu sun shekara goma ba su sha jinin ba don haka suna cikin matuƙar buƙata. Daji na uku na waɗansu baƙaƙen macizai ne marasa adadi, ba sa da wani abin kalaci da ya huce shan kwanyar bil'adama. Daji na biyar na wani zakin sihiri ne wanda ɓarin jikin shi na wuta ne ɗayan ɓarin kuwa na ƙanƙara ne, a halin yanzu babu wata dabba mai ƙarfin damtsen shi. Daji na ƙarshe na wata aljana ne da ake yiwa laƙabi da zaitul-ukub, bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu babu matsafiya tamkar ta, wasu ma na na ganin cewa ita ce uwar bokayen duniya. Bayan mutum ya samu nasarar ƙetare waɗannan miyagun dazuka bazai iya sassaƙar bishiyar Shajarul-kair ba face ya mallaki wata takobin sihiri. Takobin sihiri takasance mallakin sarkin bokayen duniya boka Ayyamul-layal, takobin ce kaɗai za ta iya tasiri akan Shajarul-kair. Sa'adda boka Hushaib yazo nan a jawabin shi sai hankalin gimbiya Hulaifa ya dugunzuma ainun ta dubi Hushaib a karo na biyu ta ce "Ya masanin ilimin tsafi shin a ina ne zamu samo takobin?. Hushaib ya ce"A halin yanzu takobin na ajiye ne a fadar Sarkin bokayen kuma sarakunan da suka zo wannan birni namu suka raba mu da sarƙar daraja sun yi haka ne domin mallakar takobin domin ɗayan su ya samu nasarar hallaka abokin gabar shi don ya zamo sarkin sarakunan nahiyar su. Ko da jin wannan ƙarin bayani sai gimbiya Hulaifa ta ɗora hannayenta akan kafaɗun mahaifinta ta ce "Ya Abbana ina mai yi maka alƙawarin cewa za shiga duniya ba zan dawo ba face na samo maganin da zai warkar da kai daga wannan lalura. Sa'adda Hulaifa tazo nan a zancenta sai duk su biyun suka sa ke fashewa da matsanancin kuka mai tsuma zuciya gami da ban tausayi. ***** Kamar yadda tsoho kuhairu ya faɗa haka al'amarin yakasance, wato tunda duku-dukun safiya bayan kowa ya ɗauko abin kalaci ya ci ya ƙoshi an kammala shiri tsaf, Sai Aljani Narguz ya ɗauke su su duka huɗun ya tashi izuwa sararin samaniya ya shiga tsala azababban gudu domin isa fadar boka zammar. Sai da aka shafe tsawon kwanaki ashirin ana tafiya babu sassauci, Yazamana cewa babu abinda ke sanyawa a yada zango face idan wani zai yi bawali ko lokacin barci ya yi, kuma ba a haɗu da wani abu mai cutarwa ba. A ranar kwana na talatin ne aljani Nargzu ya sauke su a cikin wani ƙasaitaccen daji, shi dai dajin yakasance yana ɗauke da waɗansu irin bishiyu baƙaƙe,duwatsu, kwazazzabai da sarƙaƙiya haɗi da ƙoramu, hakan ne yasanya duhu ya mamaye dajin. Nan fa kowa ya sha jinin jikin shi domin ko ba a ce komai ba dole ne a samu halittu masu cutarwa a cikin dajin. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ashirin ana tafiya a turba, Wohoho! haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu" inda ace su sarki Himras sun san abinda zai faru da ba su yi gangacin shiga dajin ba. Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu miyagun mayaƙa na fitowa daga kowa ce kusurwa a dajin. Su dai dakarun sun kasance masu ƙirar samudawan farko sun tara ƙwanji tamkar duwatsu aka cusa masu, suna ɗauke da miyagun makamai ma su barazana ga rayuwar bil'adama, adadin su haura dubu hamsin da ɗoriya. Tabbas wadannan dakaru sun cika abin tsoro domin komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da su dole ya ɗimauce ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa. Dakarun sun kasance arnar daji sun wanzu a dajin fiye da shekaru dubu, a duk sa'adda da suka tare ayarin fatake zasu kai su ga shugaban su ya aure mayen ciki mazajen kuwa a kai su kurku ba ci ba sha azaba ce zata hallaka su. Sa'adda sarki Himras,yarima Muzaifar, tsoho kuhairu,jaruma sharilat da aljani Narguz su ka yi arna da dakarun sai suka ɗimauce ainun, domin a iya tsawon rayuwar su basu taɓa gani ko jin halitta mai kwarjini tamkar su ba. Shi kanshi aljani Narguz duk da kasancewar shi gwarzon mayaƙi sai da ya firgita ainun. Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su da arnar dajin na wani lokaci sai daga bisani ayarin arnan dajin suka ɗaga makaman su suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga. Ko da ganin hakan sai su sarki Himras suka zare kaman su suna masu gyara tsayuwa, shi ma aljani Narguz sai ya zare wani zabgegen gatari a damtsenshi cinyar shi domin yin gumurzu. Da ya ke arnar dajin sun yi masu ƙawanya ne sun rugo ta ko ina sai jaruma sharilat ta fuskanci na ɓangaren yamma,Muzaifar ya tari na gabas,Himras na arewa, Kuhairu na kudu, Aljani Narguz kuwa sai ya fuskanci wadanda ke tasowa daga ƙarƙashin ƙasa. A lokacin da aka haɗu sai aka yamutse da masifaffan yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro. Wohoho! tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce " idan ka ji ana ga ƙi guda to da gudu ne bai zo ba", kuma haƙiƙa tashin ba'a sa ma shi rana. Idan gwarzontaka ta haɗu da ƙarfin damtse juriya da naci suka game waje guda dole ne artabu ya zamo abin tsoro da tashin hankali. Ana fara wannan yaƙi ne dukkan ɓangarorin biyu suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kowannen su ya wanzu yana kaiwa abokin gwamin shi sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta. Duk sa'adda makaman su suka haɗu da juna sai dai kaji an kwantsama wata tsawa tamkar hadari zai gangamo a kece da ruwan sama. Sai da aka shafe tsawon rabin sa'a ana wannan artabu babu sassauci, al'amarin da ya yi matukar bawa kowane ɓangare mamaki kenan bisa ganin babu wanda ke da rinjaye. Su dai arnar dajin suna mamaki ne bisa ganin cewa iya tsawon wanzuwar su fiye da shekaru dubu ɗari basu taɓa yin artabu da halittar da ta gagare su ba sai a wanann rana . Su sarkin Himras kuwa suna mamaki ne bisa ganin cewa dukkanin su suna artabun da dukkan ƙarfin damtsen su da zafin nama amma sun gaza koda yiwa dakarun ƙwarza ne. Lokacin da ɓangarorin biyu suka zo nan a tunanin su sai zukatansu suka harzuƙa ainun suka sake tsanantawa juna da yaƙi suna kai hare-hare cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta. Idan sarki Himra,yarima Muzaifar, tsoho kuhairu da jaruma sharilat suka kaiwa arnar dajin sara da makamansu sai kaga ƙura ta tashi ko gezau basu yi ba tamkar dutse suka sara. Sai da sa'a ɗaya ta sake shuɗewa ana wannan artabu, Ana cikin wannan hali ne wani daga cikin arnar dajin ya shammaci sarki Himras, da kuhairu ya gabza masu naushi a fuska. A lokaci guda su duka ukun suka rikito daga kan alajni Narguz suna masu kurma ihu, kafin wani daga cikin ya yi wani yunƙuri arnar dajin sun turmushe su sun ɗaure hannaye da ƙafafuwan su da wasu sarƙoƙi, sannan wasu daga cikin arnar dajin suka gabato da wani katon keji da akayi da zallar mulmulallan bakin ƙarfe, suka ɗauki su sarki Himras suka saka su a ciki suka mayar da kejin suka rufe. Sannan wani narkeken ƙato ya ɗauko wata hodar sihiri a aljihun shi ya busawa jaruma sharilat da aljani Narguz take suka ɓingire ƙasa suka fara minshari. Cikin matuƙar farin ciki narkeken ƙaton ya ɗauki sharilat ya saɓata a kafaɗarshi tamkar ya ɗauki sillan kara, zaratan samari uku suka ɗaure Narguz da waɗansu sarƙoƙi suka shiga jan shi a ƙasa tamkar wani shirgegen dutse, dakarun uku suka ɗauki kejin da su sarki Himras ke ciki suka aka ɗunguma izuwa cikin daji cikin matuƙar farin ciki. Sa'adda sarki Himras ya ga halin da suke ciki sai ya shiga yin amfani da ƙarfin shirin shi domin ya ceto rayuwar su amma shiru babu labari. Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankulan su kenan suka shiga damuwa ainun. Tafiyar daƙiƙa ɗari biyu kacal aka yi aka fara hango dogayen gine-ginen birnin da aka yi su da zallar duwatsun wuta masu kwarin gaske gami da itace manya-manya. Lokacin da jama'ar birnin suka hango jaruman su sun dawo daga farauta ɗauke da ganima sai suka cika da matuƙar farin ciki suka fito suka tare su suna masu yi masu kiɗa da kirari. Sa'adda da su Himras suka tsinci kansu a birnin sai suka cika matuƙar mamakin yadda birnin yakasance, gaba ɗaya gine-ginen birnin an yi su bisa tsari mai ƙayatarwa tamkar alkannar duniya, Gaba ɗaya jama'ar birnin maza da mata yara da manya basa sanye da tufafi sai dai bante na fatun dabbobi da suka rufe tsiraicin su alamun ƙarfin damtse ya bayyana ga maza da matan su, kuma matuƙar yawan su ya huce hankali. Haka dai arnar dajin suka ci-gaba da tafiya suka ratsa saƙo da lungu na birnin har suka iso ƙofar suka ja suka tsaya can. Ko da tsayuwar ta su sai wani basamuden kato ya zira hannun shi a damtsenshi ya ciro wani zungureran ƙaho ya kafa a baki ya busa da dukkan ƙarfin shi. Faruwar hakan keda wuya sai ga jama'ar birnin na tuttuɗowa daga kowace kusurwa a birnin suna taruwa a wajen kafin wani lokaci fadar ta cika maƙil babu masaka tsinke. Jim kaɗan sai aka hango sarki da tawagar fadawanshi sun shigo fadar. Shi dai sarkin arnar dajin yakasance basamuden kato mai ƙirar sadaukai, sanye ya ke da tufafi riga da wando na fatar damuwa da suka sha ado da ƙyale-ƙyale na sarauta, a kanshi yana sanye da kambun sarauta,hannun shi riƙe da wani kwagiri na sarauta, a ƙafarshi yana sanye da takalmi da aka yi mashi ado da gashin ɗawisu, A gefen hannun shi na dama wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce tagaban kwatance sanye da doguwar aljanna shuɗiya mai ratsin fatsi-fatsi, gashin kanta baƙi ne siɗik mai ƙyalli ya zuba har izuwa kan gadon bayanta. Haƙiƙa wannan budurwa ta cika kyakkyawa tagaban kwatance da babu wani ɗa namiji da zai ganta face ya kwaɗaitu da soyayyar ta, Waɗansu irin samudawan dakaru na take masu baya shirye cikin gagarumar shigar yaƙi tamkar za su ci babu sai muzurai su ke yi. Lokacin da sarki da ayarin shi suka iso wani gayayyen tudu a fadar sai gaba ɗaya jama'ar da ke fadar suka sunkuyar da kawunansu domin girmama a gare su, kuma fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara. Tsawon daƙiƙa ashirin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sarki ya yi buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan hali ya ce "ya ku jama'ar wannan fada tawa mai albarka kuyi sani cewa wannan farauta da jaruman mu suka yi a yau cike take da ɗumbin tarihi, sanin kanku ne cewa fiye da shekaru ɗari biyu ba'a taɓa farauto aljani ba sai a yau. Sa'adda sarki yazo nan azancen shi sai jama'a suka ruɗe da shewa da tafi. Sarki ya ɗaga hannun shi sama fadar tayi shiru sannan ya cigaba da cewa "Sanin ku ne cewa mai girma abin bauta kungi zabbuba yana fushi da mu saboda rashin yanka ma shi bil'adama a shayar da jinin shi, Dalilin hakan mun faɗa yunwa da ƙishi da cututtuka, Ina mai farin cikin sanar da ku cewa kayan mu ya tsinke a gindin gaba, domin a gobe da safe zamu yankawa abin bauta waɗannan fursunoni da aka farauto mana". Ya ƙare Maganar ta shi yana mai yana mai nuna su sarki Himras dake cikin keji da kwagirin dake hannun shi. Sannan bincike ya tabbatar mini da cewa wannan kyakkyawar budurwa da ke cikin fursunonin ita ce mace ta ƙarshe da zan aura na samu gagarumin ƙarfin sihirin tsafi da jarumta fiye da kowa a wannan nahiya ta mu. A lokacinne zan ɗaukaka wannan birni namu da ƙabilarmu fiye da kowacce a wannan nahiya. Ko da jin wannan ƙarin daga bakin sarki sai jama'a suka sa ke ruɗewa da shewa da murna. Sarki ya juya ya shige gaba yana riƙe da hannun 'yarshi, take tawagar shi suka mara masa baya tare da wannan badakare da ke ɗauke da sharilat a hannun shi, koda suka zo giftwa ta gaban kejin da su sarki Himras ke ciki sai yarima Muzaifar ya lura da kallon da 'yar sarkin arnan dajin ke yi ma shi har suka shige izuwa cikin gidan sarauta. Sa'adda yarima Muzaifar ya ga an shige da jaruma sharilat izuwa cikin gidan sarauta sai Idanuwanshi suka ciko da ƙwalla ya shiga rusa kuka, Tsoho kuhairu kuwa duk da cewar ya makance amma da ya ji kukan yarima sai da ƙwalla ta cika ma shi idanu. Ko da shigewar sarki izuwa gidan sarauta sai waɗannan samudawan dakaru suka ɗauki kejin da su sarki Himras ke ciki suka durfafi wata hanya a birnin. Waɗansu dakarun na daban kuwa suka ɗaure Narguz a jikin waɗansu diraku, suka zare makaman su suka shiga yin rangadi a ƙofar gidan sarautar domin tabbatar da cikekken tsaro. Sai da dare ya raba su sarki Himras suna zaune a cikin kejin har dakarun dake gadin su suka ta fi wasu sabbi suka zo, batare da an ba su ko da ƙwayar hatsi ba, nan fa ya zamana cewa tsananin yunwa ya addabe su da ƙishi suka fara galabaita ainun a lokaci guda su duka ukun suka fashe da kukan baƙin ciki. Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai su sarki Himras suka ga waɗansu kibbau na sauka a kan dakarun dake tsaron, kafin shuɗewar daƙiƙa ashirin gaba ɗayansu sun sheƙa barzahu, Shine wane ne ya hallaka waɗannan dakaru ?, Shin yana so n ya ceto rayuwar mu ko kuwa Sharilat ta tsira daga sharrin sarkin arnan dajin?. Amsar tambayoyin da su Tsoho kuhairu suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu domin su ga wane ne. Kwatsam sai suka hango wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa shirye cikin gagarumar shigar yaƙi rataye da kwari da baka a gadon bayanta a gwiɓin cinyarta kusa tana ɗauke da wata sharbebiyar takobi a cikin kuben ta. Budurwa ta kasance mai matsakaicin kaurin jiki baza a kira ta da doguwa ko gajera ba, gashin kanta baƙi ne dogo siɗik mai ƙyalli ya zuba har zuwa kan Kwankwasonta, cikinta kuwa a shafe ya ke tamkar bata taɓa cin komai ba, tana da kyawun diri, batun hanci,baki,wuya tamkar ita ce ta tsara kanta yadda ta ke buƙata. Sa'adda Sarki Himras,tsoho kuhairu da yarima Muzaifar suka yi arba da kyakkyawar budurwar sai suka cika da matuƙar mamaki ba wani abu ne ya ba su mamakin ba face sai bisa ganin cewa budurwar ita ce 'ya ga Sarkin arnan dajin. Tun daga nesa yarima Muzaifar ya lura da irin ƙayataccen kallon da budurwar ke yi ma shi nan take ya ji ya ɗimauce saboda kyawun surar ta. Lokacin da budurwar ta iso daf da su yazamana tazarar da ke tsakanin su bata huce taku biyu ba sai ta ja ta tsaya cak!, a kayi kallon-kallo, Sannan daga bisani budurwar ta buɗi baki cikin zazzafar murya tamkar sarewa ta ce "ya ku waɗannan fursunoni kuyi sani cewa ba na zo nan ba ne domin wani abu sai domin na ceto rayuwar ku daga sharrin jama'ar birnin mu nasan cewa za ku yi tsammanin cewa ni ma na kasance azzalauma kamar yadda mahaifina ya ke, a rayuwa ta babu abin da na tsana fiye da zalunci gami da ɓakin zaluncin Abbana, babba buri na shine na rabu da jama'ar birnin mu har da mahaifina na tafi can wata nahiya ko da zan rayu a matsayin baiwa. Na ji a jikina cewa ku ne mutanen da zasu taimaka mini cimma wannan buri nawa na ƙauracewa abbana, Yanzu idan kun amince za ku cika mini alƙawarin bisa gaskiya ku faɗa mini ni kuma nan take zan buɗe ku dags cikin wannan keji. Ko da jin wannan jawabi daga bakin budurwar sai kowa ya shiga juya al'amarin a ran shi. Sai daga bisani ne sarki Himras ya dubi budurwar ya ce " ya ke wannan gimbiya kiyi sani cewa ni da abokan tafiyata mun amince da wannan sharaɗi na ki amma bisa sharaɗin cewa za ki taimaka ki ceto abokiyar tafiyar mu wacce mahaifin ki ya ke shirin aura a gobe. Ko da jin wannan batu sai budurwar ta yi tattauna murmushi ta ce " in dai don wannanne ba ku da matsala matsawar kun bani goyon baya akan aniyata. Gama faɗin hakan ke da wuya sai ta nuna kejin da su sarki himras ke ciki da hannunta na hagu tana mai karanta dalasiman tsafi nan take ƙarafan suka fara narkewa suna ɗigewa a ƙasa tamkar ruwa zuwa can sai sarki Himras, kuhairu, da yarima Muzaifar suka faɗo daga cikin kejin tim ! a matuƙar galabaice. Sannan suka mike tsaye da kyar suna masu ƙarƙaɗe ƙurar da ke jikin tufafin su, a sannanne suka lura cewa har yanzu aljani Narguz na ɗaure a jikin wannan dirka da sarƙoƙi yana sharar barci, Har sarki Himras ya yunƙura da nufin ya yi wata tsatsuba ya tashi aljani Narguz daga barci sai budurwar ta daga mashi hannu ta na mai nuni da cewa ya dakata ta ce "ya ke wannan jarumi kayi sani cewa bisa dokar wannan birni na mu babu wani tsafi da ya ke tasiri face na mutanen mu, matsawar kayi yunkurin wani sihiri ta ke asirin mu zai tonu, kuma ina so kuyi sani cewa haidar sihirin da aka shaƙawa abokan tafiyar na ku zata ɗauki tsawon sa'o'i kafin ta sake su. Ko da kammala wannan jawabi sai budurwar ta tsugunna ƙasa ta zare kibbau ɗin da ke jikin dakarun da ta hallaka gami da mayar da su cikin kwanson da ke gadon bayanta, Sannan ya shige gaba tana mai yafito su sarki Himras da hannunta da ke nuni da su biyo bayan ta, batare da gardamar komai ba kuhairu, Himras,da Muzaifar suka mara mata baya su ka durfafi wata hanya ta musamman a birnin suka bar aljani Narguz kwance yana ta minshari tamkar an yanka raguna arba'in suna kakarin mutuwa. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa hamsin ana ratsa saƙo da lungu na unguwannin birnin yazamana duk inda budurwar ta ɗauke sawunta nan su sarki himras ke ajiye ƙafafuwan su, Har aka fara shiga daji ana bishiyu da duwatsu nan fa su sarki Himras suka cika da matuƙar mamaki, "Wannan fa shi ne masu iya magana ke cewa da ɗan gari akan ci gari yanzu gashi wannan budurwa ya fitar da mu daga birnin su batare da mun fita ta kofa ba". Sarki Himras ya yi wannan furici a cikin ran shi batare da ya bayyana ba, Sai da aka samu wani waje mai tattare da ni'ima da ƙoramu sannan aka yada zango bayan an tsaya ne sai budurwar ta cire wata jaka a gadon bayanta ta ɗauko abin guzuri ta miƙawa su sarki Himras, da ya ke suna cikin matuƙar buƙatar abincin nan take suka shiga kimtsa cikin su bayan sun kammala sun sha ruwan ƙorama sun ƙoshi. A bun ka da waɗanda suka kwaso gajiya nan take suka ɓingire ƙasa suka fara sharar barci a sannanne budurwar ta ƙurawa yarima Muzaifar idanu tana duba irin kyawun halittar shi nan take tsananin ƙaunar shi ya mamaye zuciyar shi. ***** A can birnin Rum kuwa kamar yadda gimbiya Hulaifa ta ɗaukarwa mahaifinta sarki Usulu-haibar alkawari haka al'amarin yakasance. A daren ranar da sarki ya kamu da cutar shanyewar ɓarin jiki ne gimbiya Hulaifa ta fara shirye-shiryen tafiya nemo maganin lalurar shi. A iya tsawon lokaci ne fiye da rabin jama'ar birnin su ka kamu da cutuka daban-daban gami da Annobar fari da yunwa, Nan fa jama'a suka shiga cikin ƙunci da matsin rayuwa, A daren kwana na uku ne gimbiya Hulaifa ta sanya aka yi shela a birni da ƙauye cewa ana buƙatar ganin kowa a fada a gobe. Aikuwa kashe gari tunda duku-dukun safiya suka yi cincirindo a fadar maza,mata,yara da manya tamkar DANDAZON kiyashi babu masaka tsinke, da yawa daga cikin su ko kalacen safe ba su yi ba. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa latalin ana cikin wannan hali ne sannan aka fara jiyo bugun tambura da bushin algaita alamar gimbiya na daf da bayyana, Daga can sai aka hango gimbiya tafe shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, a ɓarin hannunta na hagu boka Hushaib ne cikin shigar yaƙi irin ta su ta hamshaƙan matsafa, a hannun dama kuwa wani kyakkyawan saurayi ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya cika Gwarzon mayaƙi saboda yadda ya tara gwanji damatsanshi suka tumbatsa, Wa bani ba ne face sarkin yaƙin barnin Rum da ake kira da suna Nuhairu ibnu uzaib. Sa'adda jama'a suka ga gimbiya Hulaifa da tawagar ta sun iso fadar sai suka sunkuyar da kawunansu domin girmama a gare su, Kai tsaye gimbiya ta huce izuwa kan karagar mulki ta hakimce, boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu suka je suka zauna akan waɗansu ƙayatattun kujeru da ke daf da na 'yan majalissa, Ɗaya-bayan-Ɗaya 'yan majalissar suka dunga zuwa zubewa a gaban gimbiya suna kwasar gaisuwa, bayan an kammala ne fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara. Sannan gimbiya ya miƙe tsaye ta fuskanci jama'a ta yi gyaran murya ta ce "Yaku jama'ar wannan fada mai albarka da farko ina maku Barka da zuwa da amsa wannan kira nawa, Dalilin da ya sanya na tara ku ana shi ne domin in sanar da ku cewa a yanzu ne zan tafi nemo maganin da zai warkar da sarki da jama'ar birnin mu daga cututtukan da suka same su sakamakon suɓucewar sarƙar tsafi a gare mu, Da wannan na ke maku fatan alheri sai mun sa ke saduwa da alheri. Lokacin da gimbiya tazo nan a jawabinta sai fadar ya ruɗe da shewa kowa na faɗin albarkacin bakin shi ina da su ke nuna goyonsu akan tafiyar. Daga wannan gimbiya ta miƙe ta shiga izuwa cikin gidan sarauta suka yi bankwana da sarki suna masu zubar da hawayen rabuwa da juna, Sannan ta dawo fada ta tarar da abokan tafiyar ta su boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu sun kimtsa ita suke jira suna zaune akan waɗansu jajayen dawakai ɗauke da abin guzuri. Kawai sai ta je inda dokin ta ya ke ta kama ta haye ta sakar mashi linzami ta shige ga ba, boka Hushaib da Nuhairu suka mara mata baya sauran jama'a kuwa su ka bi su a baya ɗuhhh!. Duk inda aka huce a cikin birnin sai ka ga jama'a na ɗaga ma su hannu suna masu fatan samun nasara akan abin da za su tafi nema. Sai aka iso mararrabar hanya sannan mutane suka koma izuwa cikin gari lokacin da su gimbiya suka nausa izuwa cikin daji suna fara tsala gudu. **** Āl'amarin su sarki Baddadul-arus kuwa, tun da duku-dukun safiya bayan hudowar rana kowa ya farka daga barci shi aka yi kalaci bayan an kimtsa sai aka sake hayewa bisa kan alajni zamzaru domin isa birnin kisra domin tashin boka sharubu daga kushewar shi, Sai aka shafe tsawon Sa'a shida ana tsala gudu a sararin samaniya ana keta gajimare, yayin da sa'a bakwai ta cika a dai dai wannan lokaci ne aka iso birnin kisra aljani zamzaru ya sauka a turba, Shi dai birnin kisra yakasance ƙasaitacce da aka ƙawata shi da dogayen gine-ginen zamani, babu wata halitta a doron duniya walau mutum da aljan da zata tsinci kanta a cikin wannan birni face ta zamo cikakkiyar 'yar ƙauye. Ya yin da aka tsaya sai sarki Baddadul-arus ya ɗauko madubin tsafin shi ya shafe shi da hannun shi na hagu ya shiga gudanar da bincike, sai daga bisani ya juya ya dubi abokan tafiyar shi ya ce "Yanzu sai kowannen ku yakasance cikin shiri domin shirin ko ta kwana domin binciken da na yi yanzu ya tabbatar da cewa akwai manyan musibu a tare da kushewar boka sharubu. Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-arus sai hadimi shaibat ya dube shi cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "ya shugabana shin yanzu ta ya zamu iya yaƙar dakarun da ke tsaron kofar birnin bayan cewa sun ɗora na birnin Rum yawa da kwarjini ?. Da jin wannan tambaya sai Baddadul-arus ya bushe da 'yar ƙaramar dariya sannan ya murtuke fuska ya ce " Yakai Shaibat ka yi sani cewa matsawar muna tare da wannan sarƙar tsafi babu wani abu da zamu saka a gaba face mun samu nasara. Ko da gama faɗin hakan sai ya nuna gimbiya uzaima, sarki Huraisu, hadimi shaibat da aljani zamzaru da hannunshi na hagu ta ke suka ɓace ɓat tamkar ba su taɓa wanzu ba, Su ka bayyana a cikin wani ƙasaitaccen kogon dutse, shi dai kogon dutsen yakasance mai matuƙar tsawo,girma, da ban tsoro. Komai dakewar zuciyar jarumi idan ya tsinci kan shi a cikin wannan kogon dutse dole ne tsoro ya kama zuciyarshi, saboda yadda kogon yakasance mai tattare da sarƙaƙiya kuma ya yi tsit tamkar babu wata halitta mai numfashi a ciki, Sai dai abin da ya bawa su sarki Baddadul-arus mamaki kuma ya ɗaure masu kai shi ne yadda wani farin haske ya gauraye kogon tamkar an ajiye fitila. Kawai sai sarki Baddadul-arus ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen shi ya kunna kai izuwa cikin kogon batare da wata fargaba ba, Ko da ganin hakan sai sarki Huraisu, gimbiya Uzaima, hadimi da shaibat suka yi mara mashi baya suna masu zare makaman su aljani zamzaru ne a ƙarshe. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu ana tafiya batare da an iso ƙarshen kogon ba kuma ba a haɗu a wata halitta mai cutarwa ba. Ana cikin wannan hali ne aka ji wani mahaukacin gurnani ya cika kogon baki ɗaya ya fara girgiza kamar zai rushe wata irin wata walƙiya ta dunga bayyana a saman kogon tamkar hadari ya gangamo za a ɓarke da ruwan sama. Ba shiri su sarki Baddadul-arus su ka sanya hannayensu suka toshe kunnuwan su gami da sunkuyar da kawunansu ƙasa, domin tsoron ka da walƙiyar ta makantar da su. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙu a cikin wannan hali sannan komai ya ɗauke kogon dutsen ya daina raurawa. Daga can kuma sai aka ɓarke da wata irin mahaukaciyar dariya mai ban tsoro, Cikin hanzari su sarki Baddadul-arus suka ɗauko da kawunansu domin su ga wanda ya ke ƙyalƙyala dariyar, Ya yin da suka yi arna da shi sai hankalin su ya dugunzuma ainun har hadimi shaibat ya ja da baya, Ba wani abu suka gani ba face wani narkeken aljani mai matuƙar kwarjini. Aljanin yakasance narkeken ƙato mai ƙirar sadaukai yana da tsawo har ya tokare da saman kogon, fuskarshi mummuna ce mai ɗauke da manyan idanuwa ƙwala-ƙwala tamkar garwashin wuta, bakin shi tafkeke ne tamkar bakin rijiya yana da zabgegen gemu mai kamu goma, A gwaiɓin hammatar shi hagu da dama yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda biyu. Haƙiƙa wannan aljani ya cika abin tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, duk da dakewar zuciya irin ta aljani zamzaru sai da ya firgita ainun tamkar a ce ƙyat ya zura da gudu, domin gaba da gabanta aljani ya taka wuta. A lokaci guda aljanin ya tsuke bakin shi daga dariyar sannan ya ƙurawa su sarki Baddadul-arus idanu cikin wata Irin kakkausar murya mai tattare daban tsoro ya ce "Lale marhaban da zuwan bil'adama ma'abota gajeran kwana izuwa Kogon Garul-Shimshan matattarar dukkan musibun duniya, Ya ku waɗannan bil'adama kuyi sani cewa haƙiƙa ilimin tsafi ya yaudare ku da ya bayyana ma ku cewa za ku iya tashin mai gidana sharubu daga kushewar shi har ya yi maku rakiya izuwa ɗauko shirtaccen kundi domin mallakar takobin sihiri. Kafin aljanin ya gama rufe bakinshi sarki Baddadul-arus ya tari numfashin shi ya ce " ƙaryarka ta sha ƙarya ya kai wanan rafkanannan jarumi a jerin JARUMAN DUNIYA. Ba ka san ko mu ɗin su waye ba kuma baka san wane ne bil'adama shin ka manta cewa mai gidan na ka da kake ƙoƙarin karewa shi ma bil'adama ne kamar mu. Ko da jin wannan batu daga bakin Baddadul-arus sai aljanin ya fusata ainaun jikin shi ya kama tsuma har wani irin tiririn ɓakin hayaƙi na fita daga ƙofofin hancinshi. "Wai yau har ni bil'adama zai kalla ya ce mani rafkanannan jarumi na rantse da gemun mahaifina ɗayan ku ba zai tsira da rayuwar shi ba. Yana gama faɗin hakan sai kawai ya kurma ihu mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga ya shiga kaiwa su sarki Baddadul-arus naushi da bugu hannu da ƙafa. Sarki Baddadul-arus, Uzaima, hadimi shaibat, sarki Huraisu da aljani zamzaru suka shiga kare hare-haren shi aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. ***** Kashe gari tunda duku-dukun safiya kafin hudowar rana jama'ar birnin arnar daji suka dunga tururuwa a kofar fadar birnin, manya,yara mata da maza, zukatansu cike da matuƙar farin ciki domin a yau ne za su shayar da abin bautar su jinin su sarki Himras tare da murnar ɗaura auren sarki da sharilat. Lokacin da suka kammala taruwa sai suka ga wani abu da ya dugunzuma hankulan su kuma ya ɗimauta su, Abin da su ka gani shine kejin da aka saka su sarki Himras wayam babu kowa a ciki, Shin wane ne ya kuɓutar da waɗannan fursunoni? Sannan ma taya ya aka hallaka waɗannan dakarun masu tsaron ƙofa?. Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu suna jiran fitowar sarki daga cikin sarauta, A dai-dai wannan lokaci ne aljani Narguz ya farka daga dogon barcin da ya ke yi sakamakon hodar sihirin da arnar dajin suka shaƙa ma shi. Shin wane ne ya kawo ni nan, su wane ne waɗannan mutane ina kuma su sarki Himras su ke?, Amsar tambayoyin da Narguz ya kasa bawa kan shi kenan kawai ya zuba idanu yana ganin abin mamaki. Sai da daƙiƙa hamsin ta shuɗe ana jiran fitowar sarki daga cikin gidan sarauta amma shiru ka ke ji malam ya ci shirya, Al'amarin da ya haddasa ce-ce ku-ce tsakanin jama'a kenan kowa na faɗin albarkacin bakin shi. **** Al'amarin su sarki Himras kuwa lokacin da safiya ta yi kowa ya yi kalaci ya kimtsa cikin shi, Sai wannan kyakkyawar budurwa 'yar sarkin arnan daji da ake kira da suna Mashlira ta dubi sarki,yarima da tasoho kuhairu ta ce "Ya ku waɗannan fursunoni masu daraja ku yi sani cewa a halin yanzu ba mu ga ta zama ba domin nasan mahaifina yana cikin ƙunci da baƙin ciki bisa tseratar da ku da na yi, don haka dole mu kasance cikin shiri domin a kowa ne lokaci za'a iya kawo mana farmaki, a yanzu ne mu ke da ikon kai farmaki zuwa birnin mu. Ko da jin wannan jawabi daga bakin Mashlira sai su sarki Himras suka shiga yin shirin yaƙi, ita kuwa sai ta shiga izuwa cikin duhuwar bishiyu domin ta yi bawali, Tabbas rashin sani ya fi dare duhu inda Mashlira ta san abin da zai faru da bata shiga wannan dubuwa ba, domin tana ƙoƙarin cire tufafin ta ne kwatsam bazato babu tsammani sai ta ji an bangaze ta ta baya saboda ƙarfin bangazar sai da ta yi ƙundumbala sau biyu ta kife a ƙasa kanta ya daku da wani ɗan ƙaramin dutse jini ya yi tsartuwa. Cikin baƙin zafin nama ta miƙe tsaye zumbur ta gyara tsayuwar ta tana mai zare takobin ta daga cikin kube, Ai kuwa sai ta yi arba da wata murgujejiyar zakanya tana gurnani, A iya tsawon rayuwar Mashlira bata taɓa ganin halitta mai kwarjinin ta ba, Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su na wani lokaci daga can sai zakanyar ta dako watan tsalle tana mai buɗe farantanta ta yi ɗauki kan Mashlira domin ta yi mata farat ɗaya. Cikin matuƙar zafin nama Mashlira ta daka tsalle guda zakanyar ta bangazi wata bishiya da ƙirjinta take bishiyar ta jijjigo da saiwoyinta ta faɗi ƙasa rikica!, Nan take suka kacame da azababban yaƙi, zakanyar ta wanzu tana kaiwa Mashlira yakushi da farata da cizo da bakinta, Mashlira ta wanzu tana zillewa hare-haren cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta gami da mayar da martani. Ana fara wannan gumurzu ne fa gimbiya Mashlira ta fara gane kuren ta yazamana cewa duk sa'adda ta kaiwa zakanyar hari da takobin ta sai ta ji tamkar dutse ta sara, a wasu lokutan bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanta. Sa'adda aka shafe daƙiƙa hamsin ana wannan artabu babu sassauci sai yazamana Mashlira bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanta, Ana cikin wannan hali ne zakanyar ta dako wawan tsalle ta bangazi ƙirjin ta, Saboda ƙarfin bangazar sai da ta yi katantanwa sau uku a sama sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabaice numfashin ta na fita sama-sama. Ko da samun wannan nasara sai zakanyar ta ja da baya tana wani gurnani da ke nuna samun nasara, Kawai sai ta dako tsalle a karo na babu adadi domin ta turmushe Mashlira ta yaga sassan jikinta, Nan fa Mashlira ta shiga ƙoƙarin kare kanta da ƙarfin shirin tsafi amma shiru babu labari al'amarin da ya sanya ta miƙa wuya cewa babu wata hanya da zata tsira daga sharrinta. Ko da ya rage saura kuma biyu zakanyar ta cimma ma ta bazato babu tsammani sai wani kyakkyawan saurayi ma'abocin kwarjini da haiba sanye da fararen tufafi a kwiɓin cinyarshi yana ɗauke da salkar ruwa, a gadon bayanshi yana rataye da wata sharbebiyar takobi ya yi fitar burgu da ga Cikin duhuwa, kafin zakanyar takai ga sauka akan Mashlira ya saurayin ya gabzawa mata wawan naushi a wuya, take wuyan ya karye ji ka ke ruƙus ƙas!, Ta fado ƙasa matacciya ko shurawa ba ta yi ba. Sa'adda Mashlira ta ga gagarumar bajintar da saurayin ya yi sai ta cika da matuƙar mamaki domin a bata taɓa ganin jarumi mai bajintar shi ba, Kawai sai ta miƙe tsaye ta ƙura saurayin idanu ya dube shi ta ce "Ya kai wannan ma'abocin kwarjini da jarumtaka shin wane ne mai kuma mene ne ya kawo ka wannan nahiya ta mu?, Mene ne ya sanya ka ceto rayuwa ta ? Ko da jin waɗannan tambayoyi sai saurayin ya yi tattausan murmushi a gare ta sannan ya buɗe baki cikin Murya mai daɗi ya ce "Da farko dai a tsarin addinin mu an horar da mu da mu taimaki dukkan halittar Allah, Bayan haka ni dai suna na Humairu ibn kamis ni ma'abocin addinin Musulunci ne na fito ne daga nahiyar gabashin duniya domin na yaɗa addini na a sassan duniya. Ko da jin amsar waɗannan tambayoyin daga bakin saurayi Humairu sai mamaki ya kama Mashlira ta dube shi ta ce "Shin dama akwai wani Addini da huce tsafi a doron ƙasa ?. Da jin wannan tambaya sai dariya ya suɓucewa Humairu har fararen haƙoranshi suka bayyana masu ɗauke da wushirya ya ce "Tabbas akwai wani Addini bayan sihiri wato addinin Allah Ubangiji maɗaukakin sarki mahaliccin kowa da komai wanda bai haifa ba ba a haife shi ba. Cikin matuƙar mamaki Mashlira ta ce "Haƙiƙa ikon Ubangijin ka cike ya ke da daban al'ajabi ya kai wanan jarumi ma'abaocin kyawu da jarumtaka ka yi sani cewa nafara gamsuwa a zuciyata cewa Ubangijin ka shine ya can-canta a bauta mashi tun da ga shi ya tseratar da ni daga sharrin wannan zakanya. Amma abu ɗaya ne zai sanya na bada gaskiya da Ubangijin na ka shine ka tseratar da rayuwar wata budurwa daga sharrin mahaifina da ke shirin aure ta, domin ya samu gagarumin sihirin tsafin da zai zamo gagarabadau a cikin sarakunan nahiyar mu. Ko da jin wannan batu sai jarumi Humairu ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya na mai zurfafa cikin Kogin tunani, Daga bisani ya dubi Mashlira ya ce "Wannan buƙata ta ki mai sauƙi ce tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai, matuƙar baza ki saɓawa alkawari ba. Sa'adda jarumi Humairu ibn kamis yazo nan azancen shi sai suka ji alamun motsi a gefen su ko da suka waiga sai suka yi arba da su sarki Himras shirye cikin gagarumar shigar yaƙi ashe tun ɗazu suna laɓe cikin duhuwa sun ga abin da ya faru tsakanin Humairu da zakanyar. Har Mashlira ta huɗi baki da nufin ta ce wani abu sai sarki Himras ya tari numfashin ta fuskar shi a murtuke babu annuri ya ce "Ya ke Mashlira kiyi sani cewa ni da 'yan uwana za mu iya yaƙar mahaifin ki da jama'ar shi har mu ceto rayuwar sauran abokan tafiyar mu batare da mun nemi taimakon wannan jarumi ba don haka sai ki zo mu tafi ko. Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Himras sai gimbiya Mashlira ta dube shi a nutse ta ce "Tun da kunga dukkan abin da ya faru tsakani na da baƙon jarumi to ai babu bukatar na sake wani bayani domin tattaunawar da mu ka yi da Humairu ni kaɗai ta shafa ba ɗaya daga cikin ku ba don haka Humairu na ƙarƙashin kulawa. "Tabbas masu iya magana sun ce wai ba'a ƙin ta Mutum". Yarima Muzaifar ya faɗi yana gyara tsayuwar shi. "Amma ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, kuma masu iya magana na cewa tsautsayin akuya gaishe da kura". Inji sarki Himras". Ko da gama faɗin hakan sai sarki Himras ya juya ya shige gaba da nufin ya fara tafiya, amma sai jarumi Humairu ya yi zumbur ya shige gaba Mashlira ta bi bayan shi da sauri, Himras, kuhairu na mara mata baya yarima Muzaifar ne a ƙarshe a ka cigaba da tafiya. Lokacin da aka fara wannan tafiya sai su sarki Himras suka cika da matuƙar mamaki, abin da ya basu mamakin shine yadda Humairu ke ratsa saƙo da lungu na dajin yana bin hanyar da Mashlira ta biyo da su a lokacin da ceto rayuwar daga hannun jama'ar ta, tamkar wanda ya ke bin hanyar a koda yaushe, Wani abu da ya fi basu mamaki shine yadda tafiyar ke yin sauri. "Haƙiƙa wannan shi ne zai ceto 'ya ta Sharilat domin na ga yakasance ɗaya cikin Mutanen su tsoho kamzal wato ma'abota addinin Musulunci shin ko Humairu yana da alaƙa ne da Humaira 'yar tsoho kamzal". Tsoho kuhairu ne ya yi wannan furici a cikin ran shi batare da ya bayyana ba. Haka dai aka cigaba da wannan tafiya ana ratsawa duwatsu, ƙoramu da kwazazzabai, ana cikin wannan tafiya ne yarima Muzaifar ya lura cewa Mashlira na satar kallon Humairu har ta na yi mashi murmushi mai taushi. Al'amarin da ya sanya ya ji azababban kishi ya turnuƙe shi, amma sai ya shiga tuhumar kan shi yana mai cewa shin mene ne ya sanya zan yi kishi akan Mashlira bayan cewa ina da tawa abar ƙaunar wato sharilat, Amsar tambayoyin da ya kasa bawa kanshi kenan ya ce a cikin ran shi wannan shine masu iya magana ke ce "So tsuntsu ne ". ***** A can birnin arnar daji kuwa, sai da jama'a suka shafe sa'a ɗaya cur a tsaye a kofar fada suna jiran fitowar sarki, sannan suka ga an buɗe gidan sarauta sai ga sarki ya fito tare da tawagar shi shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, zaratan dakaru ɗauke da miyagun makamai na mara mashi baya. Tun daga nesa jama'a suka fahimci cewa sarki yana cikin matuƙar fushi da alama akwai wani mummunar al'amari da ya faru, Sai da sarki da tawagar shi suka yi kamar taku goma sannan suka ja suka tsaya, sarki ya yi gyaran murya cikin matuƙar fushi maral-musaltuwa ya yi buɗi baki ya fuskanci jama'a ya ce " ya ku jama'a ta ku yi sani cewa bakomai ne ya haddasa jinkirin fitowa ta daga cikin gidan sarauta ba sai domin wani abun baƙin ciki da ya same mu, 'ya ta mashira ta da na fi so fiye da komai a rayuwa ta ta ci amanata ta tseratar da rayuwar fursunonin da aka farauto mana domin shayar da jinin su ga abin bauta. Haƙiƙa dole ne ya yanke wa Mashlira hukunci laifin da ta aikata Mani, binciken da na gudanar bisa halarar tsafi ya tabbatar mini dacewa 'ya ta mashira da fursunonin da suna zaune a dajin wannan birni namu, Saboda haka na fito ne yanzu domin mu farauto su domin bayar da jinin su ga abin bauta, daga nan kuma za'a shiga shagalin ɗaurin auren mu. Sa' adda sarki shabbar ya zo nan a jawabin shi sai jama'a suka cika da matuƙar baƙin ciki maral-musaltuwa kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinshi. Har sarki shabbar ya buɗe baki a karo na biyu da nufin ya sake furta wani abu sai kawai aka jiyo ihu da kururuwar dakaru masu tsaron ƙofa, Kafin ayi wani yunƙuri sai aka ga waɗansu irin azababbun kibiyoyi na sauka a wajen jama'a suna hallaka, Cikin matuƙar fushi sarki shabbar da ya ruga izuwa tsakiyar gari dakaru suka mara mashi baya. Nan fa wajen ya kaure da guje-guje gami da ifice-ifice ana banke jama'a masu rauni suna faɗuwa ƙasa magashiyan. **** Sa'adda gimbiya Hulaifa, boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu suka fice daga birnin Rum suka nausa izuwa cikin daji suka wanzu suna gudu bisa dawakan su suna ratsa kwazazzabai, sarƙaƙiya da duhuwar bishiyu. Sai da suka shafe tsawon Sa'a biyar da daƙiƙa hamsin suna wannan tafiya ana cikin halin Gimbiya Hulaifa ta fahimci cewa dawakan su sun fara gajiya, don haka sai ta ɗaga hannunta sama aka tsaya cak domin a yada zango, Bayan an tsaya ne aka shiga kafa tantuna inda aka tsaya yakasance mai tattare da ni'ima. Bayan an kammala ne kowa ya shiga na shi tantin ya shiga yin kalaci, Jim kaɗan bayan kammala hakan sai boka Hushaib ya zira hannunshi a aljihun shi ya ɗauko madubin tsafin shi ya shafe shi da hannunshi na hagu ya shiga gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi sarkin yaƙi na zaune a gefen shi. Tsawon daƙiƙa hamsin yana gudanar da binciken sai daga bisani ne ya mayar da madubin ya juya ya dubi sarkin yaƙi ya ce "Sai ka taso muje zuwa tantin gimbiya domin akwai wata muhimmiyar magana da zamu yi yanzu". Boka Hushaib na gama faɗin hakan sai ya miƙe tsaye ya fice daga tantin su sarkin yaƙi ya mara mashi baya cikin hanzari, Lokacin da suka isa bakin tantin sai boka Hushaib ya yi gyaran murya gimbiya ta yi masu izinin shigowa, kai tsaye suka kunna kai ciki suka samu waje suka zauna bisa shimfiɗa, a wannan lokaci gimbiya Hulaifa na zaune a bisa gado ta tanƙwashe kafafuwanta, bayan shiru ya wanzu a tsakanin su na wani lokaci sai boka Hushaib ya yi gyaran murya ya ce " ya shugaba ta ki yi sani cewa binciken da na gudanar bisa halarar tsafin ya tabbatar mani da cewa baza mu taɓa mallakar takobin sihiri ba domin samun sassaken bishiyar Shajarul-kair ba sai mun nemi taimakon wani jarumi ma'abaocin addinin musulunci wanda zai mallako mana duka abubuwan biyu a cikin kwanaki ɗari kacal kafin jama'ar birnin mu su hallaka daga Annobar fari da cutuka, Sai dai binciken bai bayyana mani inda jarumi ya ke ba kin ga kenan akwai buƙatar mu kwana a wannan waje domin mu gano inda zamu sadu da jarumin ". Lokacin da boka Hushaib ya zo nan azancen shi sai gimbiya da sarkin yaƙi suka cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Wannan shi ne abin da ya wakana da su gimbiya Hulaifa akan hanyar su ta nemo maganin da zai warkar da al'ummar birnin su. **** Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin su sarki Baddadul-arus da hadimin boka sharubu wato wannan narkeken Aljani a cikin kogon Garul-Shimshan. Sai sarki Baddadul-arus, Uzaima, sarki Huraisu, Hadimi shaibat da aljani zamzaru suka wanzu suna kare miyagun hare-haren da aljanin ke kawo masu na naushi da bugu, duk sa'adda da ya kai masu naushin suka zille duk abin da hannun shi ya nausa sai kaga ya tarwatsa ya yi bindiga koda dutse ne idan kuwa a ƙasa ne sai kaga ƙasar wajen ta zaftare ta haddasa katon rami mai kamu goma, Nan fa yazamana cewa halitta guda ɗaya jal ta zamo GOBARAR DAJI tsakanin ZARATAN MAYAƘA biyar, yawan su ya zamo a banza, kuma suka tashi hankalin kogon dutsen baki ɗaya tamkar zai tsage ya rugeje. Sai aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan artabu batare da su sarki Baddadul-arus sun samu nasarar fitarwa aljanin jini b, haka shi ma bai samu nasara akan su ba, a zahiri ga duk wanda ya ke kallon yadda artabun ke wakana dole ne ya tabbatar da cewa aljanin ya fi su Baddadul-arus ƙarfin damtse da juriya domin kafin su kai mashi hari sau uku ya kai ma su goma. Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka saba gwagwarmaya a GUMURZUN SHEKARA DUBU da ZARATAN MAYAƘA ke FARAUTAR MAZAJE domin Cinye GASAR JARUMTA domin zamowa GOGA SHA FAMA, Tabbas idan juriya da naci suka haɗu waje guda jarumta ta haɗu da Gwarzontaka dole ne artabu ya zamo tashin hankali da ban tsoro, Babu abin da zai tayar da hankalin mutum fiye da yadda jaruman shida ke bawa hammata iska domin hallaka juna. A wasu lokutan su sarki Baddadul-arus har daka tsalle sama suke yi su kaiwa aljanin hari Sannan su diro ƙasa bisa diga-digansu cikin gwaninta. Ana cikin wannan gumurzu ne sarki Baddadul-arus ya daka tsalle tamkar an harba shi daga cikin baka, yana saman ya zare ya kaiwa aljanin sara bisa sa'a sai ya same shi a fuska ya yi mashi wani lafcecen rauni jini ya yi tsartuwa. Ya yin da aljanin ya ji raɗaɗi a fuskarshi kuma ya ga jini na zuba sai kawai ya shammaci Baddadul-arus ya gabza mashi naushi a fuska a lokacin da yake kokarin dira ƙasa, take ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya bugu da saman kogon, sannan ya faɗo ƙasa fuskar shi ta daddauje jini na zuba cikin mawuyacin halin da ke tsakanin RAYUWA DA HALAKA. Kafin su gimbiya Uzaima su yi wani yunƙuri aljanin ya daki wani bangare a kogon ya zaftare ya faɗo kansu ya danne su, Ko da samun wannan gagarumar nasara sai aljanin ya matsa daf da inda suke ƙwance ya daga ƙafarshi domin ya murƙushe su su hallaka. **** Sa'adda sarki shabbar shugaban arnar daji tare da tawagar dakarun shi suka riga zuwa bakin Kofar gari ɗauke da miyagun makamai a hannayensu sai suka hango gimbiya Mashlira da su sarki Himras a tsakiyar dakaru suna hallaka su. Cikin matuƙar fushi sarki shabbar shabbar ya falala da azababban gudu izuwa gare su yana mai kwarara wawan ihu lokacin da ya rage bai huce saura taku goma tsakanin su ba sai ya daka tsalle sama tamkar an harba shi daga cikin baka ya sauka a daf da inda gimbiya Mashlira ta ke tsaye ya dube ta cikin matuƙar fushi a lokacin da Idanuwanshi suka kaɗa su ka yi jawur ya ce "Ya 'yata ban taɓa tsammanin cewa zaki haɗa kai da maƙiya na domin cutar da ni ba har ki ci amana ta, Shin kin manta ne cewa ke kaɗai ce kika rage mani a cikin zuri'a. Ko da jin wannan batu daga bakin sarki sai Mashlira ta dube shi babu alamun nadama a fuskarta ta ce "Ya abbana kayi sani cewa bakomai ne ya sanya na juya maka baya ba sai saboda irin baƙin zaluncin da ka ke aiwatar wa a wannan birni namu na ɗauki tsawon lokaci ina roƙon abin bauta ya kawo ƙarshen wannan ɗabi'a taka". Kafin Mashlira ta gama rufe bakinta sarki Shabbar ya kai mata wawan mari a fuska, cikin baƙin zafin nama ta sunkuya hannun domin kaucewa amma sai da hannun sarki ya shafi gefen kuncinta nan take ta yi adungure ta kife a ƙasa, Amma sai ta miƙe tsaye zumbur ta kaiwa sarki sara da takobin ta, cikin baƙin zafin nama sarki ya sanya takobin shi ya kare harin tartsatsin wuta ya tashi da ƙara mara daɗin saurare. Nan take suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta. A dai-dai wannan lokaci ne dakarun sarki shabbar suka afkawa su sarki Himras aka yamutse da masifaffan yaƙi, mai matuƙar muni ihun mazaje, ƙarar karafniyar ƙarafa gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne, jini ya dunga kwaranya yana tsartuwa yana kwaranya a ƙasa, Sassan jikkunan bil'adama suka dunga shawagi a sararin samaniya suna zubowa kasa tamkar ana ruwan su ne daga saman, ƙura kuwa ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin dudufniya kofatunsu na kartar ƙasa. Duk inda sarki Himras, Yarima Muzaifar da tsoho kuhairu suka sanya a gaba sai dai kaga dakarun arnar dajin na zubewa ƙasa matattu. A ɓangaren Humairu ma'abocin addinin Musulunci kuwa lokacin da ya ƙwala kabbara sai ya tari abokan gaba ya wanzu yana ragargazar su da tsagwaron ƙarfin damtsenshi batare da ya zare makami ba duk inda ya sanya gaba sai dai kaga fili fetal dakarun sun zube ƙasa matattu wasu cikin mawuyacin halin da ke tsakanin RAYUWA DA AJALI. Inda ace mutum zai ga yadda Humairu ke yin yaƙin dole ya jinjina mashi ya tabbatar dacewa ya cika SARKIN SADAUKAI, Domin duk tsananin yawan dakarun arnar dajin da zafin naman su ya tashi a banza domin sun kasa samun nasarar koda lakutar jikin shi, A wannan lokacin arnar dajin ƙara tuttuɗowa suke daga kowa ce kusurwa a birnin akan raƙumi, giwaye da dawakai ta gabas, yamma, kudu, arewa, ɗauke da makamai kuma mazan su da matayen su. Tun daga nesa arnar dajin suka lura da cewa Humairu ya fi yi masu ɓarna, don haka sai kaso huɗu bisa bisa shidan su suka taru akan shi domin yi masa rufdugu. Shi kuwa sai ya wanzu a tsakanin su tamkar wani shaiɗani duk wanda ya gabzawa naushi a fuskar shi sai kaji ya kurma ihu ya faɗi ƙasa, a wasu lokutan har dawakan su ya ke haɗawa. A ɓangaren sarki shabbar da 'yar shi Mashlira kuwa sun wanzu suna bawa hammata iska, ana fara wannan artabu ne Mashlira ta fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin ƙarfin damtse da gwanintar yaƙin mahaifin ta ya nunka na ta sau goma, idan ya kai mata hari ta sanya takobi za ta kare sai kaga har durƙushewa ƙasa take yi. Kafin shuɗewar wasu daƙiƙu sarki ya rikita ta da hare-haren shi yazamana bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kai. A wasu lokutan idan shabbar ya kai mata sara ta kare har faɗuwa ƙasa ta ke yi amma saboda juriya da naci irin na MAZAJEN DUNIYA sai ta miƙe tsaye a cigaba da fafatawa. Ana cikin wannan hali ne shabbar ya shammace ta ya make takobin da ke hannunta sannan ya gabza mata wawan naushi a fuska ta yi sama tamkar an janye ta ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa magashiyan jini na zuba daga bakinta da hanci. Koda samun wannan gagarumar nasara sai sarki shabbar ya bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da saƙon mutuwa ya taka ƙafafuwan shi har izuwa inda 'yar shi Mashlira ke kwance magashiyan ya dube ta cikin matuƙar takaici da baƙin ciki ya ce "Ya ke 'ya ta haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kika fafata yaƙi da ni shin kin manta ne cewa ni ne na fi kowa ne jarumi ƙarfin damtse a cikin birnin mu, ke kan ki dukkan sirrikan tsafin da kike taƙama da su daga gareni kika same su, Yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan yanke maki hukunci dai-dai da laifin da kika aikata. Ko da gama faɗin hakan sai sarki shabbar ya karanta dalasiman tsafi ya nuna Mashlira da ɗan yatsanshi na hagu take waɗansu irin igiyoyin tsafi suka ɗaure hannaye da ƙafafuwanta, sannan wata bulalar sihiri ta bayyana ta shiga zane ta a dukkan sassan jikinta, Duk inda bulalar ta sauka a jikinta sai ta kurma saboda matuƙar raɗaɗin da ta ke ji. Sa'adda jarumi Humairu da ke tsaye a cikin abokan gaba ana gwabza yaƙi ya hango abinda ke wakana tsakanin Mashlira da mahaifinta sai kawai ya shiga neman taimakon Ubangijin musulunci a cikin ran shi, kawai sai ya falfala da azababban gudu yana mai make dakarun da ke gaban shi yana samarwa kan shi hanya domin ya isa inda sarki shabbar ya ke. Lokacin da sarki shabbar ya hango shi sai ya rugo gareshi yana mai ƙwala kabbara da ƙarfi kawai sai shi ma ya rugo gare shi domin tarar juna, Lokacin da ya rage saura taku goma tsakanin su sai ya daka wawan tsalle ya sauka a daf da inda Humairu ya ke ya kai mashi sara da dukkan ƙarfin shi. Cikin baƙin zafin nama Humairu ya sunkuya takobin shabbar ta sari iska, sannan suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban sha'awa, Suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance. Wohoho haƙiƙa duk wanda Allah ya ba shi jarumtaka ya huta domin komai hassadar Mutum idan ya ga yadda Humairu ke kare hare-haren shabbar dole ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya cika SARKIN SADAUKAI. Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan artabu babu sassauci amma shabbar bai samu nasarar lakutar jikin Humairu. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa shabbar kai kenan kuma ya fusata shi, Abin da ya bashi mamaki shine ya a ka yi a matsayin shi na Gwarzon mayaƙi da ya saɓa gwagwarmaya da ZARATAN MAYAƘA amma wannan jarumi ya gagare shi, Shin dama a wannan nahiya akwai wani jarumi da ya kai shi ƙarfin damtse, Abin da ya fusata shi shin ne ya za a ce gwarzon mayaƙi Kamar shi wani jarumi ya wanzu a gaban shi ya gagare shi hallaka. Lokacin da sarkin arnan dajin yazo nan a tunanin shi sai ya zurfafa cikin Kogin tunani domin samun mafita, koda samun mafitar sai ya shiga yin amfani da karfin sihirin tsafin shi a inda ya dunga turawa Humairu miyagun abubuwa, idan ya tura mashi cuta sai Humairu ya karanta addu'a ya tofa take wutar zata nace ɓat ta zama hayaƙi, idan kuwa ya tura mashi kibbau kafin su isa inda ya ke sai su narke su ɗige a ƙasa. Haƙiƙa duk wanda Allah ya yarda da shi sai ya zamo garkuwa a gare shi, domin wasu lokutan ma wutar har kama tufafin Humairu take amma bata tasiri. Sai da sarki Shabbar ya gama amfani da dukkanin sirrikan tsafin shi domin ganin ya cutar da Humaira amma babu nasara, al'amarin da sanya ya fusata ainun kenan ya ja da baya yana haki tamkar mayunwacin zakin da ke shirin tunkarar DANDAZON MAYAƘA ya yi wurgi da takobin shi gefe gudu kawai sai ya sanya hannayenshi biyu ya tsarga rigar shi gida biyu ya yi wurgi da ita, Take ƙirjin shi ta bayyana a fili ɗauke da gauraye da layu na sihiri yana da manyan damatsa masu curin tsoka tamkar duwatsu aka cusa mashi a ciki. Duk da dakewar zuciya irin ta Humairu koda ya yi arba da sarki Shabbar a cikin wannan hali sai da zuciyarshi ta buga da ƙarfi ya tabbatar da cewa yau ya gamu da gamon shi. Shabbar ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dubi Humairu ya ce "Yanzu tun na kasa samun nasara akan ka da makami sai mu gwada 'yar ƙashi ina mai farin cikin sanar da kai cewa yanzun nan zaka zamo gawa. Koda gama faɗin hakan sai shabbar ya cire layu da gaurayen da ke jikin shi ya yi jifa da su suka ƙone suka zama hayaƙi, sannan ya falfala da azababban izuwa kan Humairu yana mai kurma wawan ihu gami da dunƙule hannayen shi biyu, Koda ganin hakan sai Humairu ya yi koyi da shi ya ruga izuwa gare shi yana mai ƙwala kabbara da ƙarfi tare da dunƙule hannayen shi, Ana haɗuwa aka ruguntsume da sabon azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini. A ɓangaren su sarki Himras kuwa sun wanzu a tsakiyar arnar dajin suna shayar da su azabar KAIFIN TAKOBIN su duk inda suka sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar suna sassabe a gonar auduga. Duk da irin ɓarnar da suke yiwa arnar dajin amma suma sun yi masu manyan raunuka fiye da shida kowanne na zubar da jini, wani abu da ya ɗaure masu kai shi ne Gashi dai kashe arnar dajin suke amma ƙara kwararowa suke daga kowa ne saƙo na birnin mazan su da matan su. A sannanne su sarki Himras suka fahimci cewa tabbas sun gamu da gamon su, ana cikin wannan artabu ne wani garjejen ƙari ya kaiwa tsoho kuhairu wawan sara a kafaɗar shi. Cikin wani irin baƙin zafin nama kuhairu ya sanya mashin shi ya kare harin wani tartsatsin wuta ya tashi, kafin katon ya mayar da martani kuhairu ya soka mashi mashin a ƙirji ya billo ta gadon bayanshi, jini ya yi feshi gami da tsartuwa ko shurawa bai yi ba ya sheka barzahu. Cikin zafin nama irin na gawutattun JARUMAN DUNIYA kuhairu ya cizge mashin na shi ya make fuskokin waɗansu dakaru biyar, take suka baje a ƙasa suna kurma ihu hanci da bakunansu na zubar da jini. A can cikin gidan sarauta kuwa, al'amarin jaruma Sharilat bayan dakarun arnar dajin sun shigar da ita zuwa gidan sarauta, Sannan hodar sihirin da aka shaƙama ta bata sake ta ba sai da rana ta hudo ta yi haske, koda buɗe idanunta sai ta tsinci kanta a cikin wata irin ƙasaitacciyar turaka da aka ƙawata ta nau'ikan kayan alatu na jin daɗin rayuwar duniya. Yayin da ta buɗe idanunta taga an canza mata tufafin dake jikinta an canza ma ta Waɗansu ƙayatattu na sarauta, kuma taga kada ina ciki turakar ɗauke ya ke da barori da kuyangi na ta hidima suna ta kai komo, sai kawai ta yunƙura domin ta buɗe bakinta tayi magana kuma ta tashi zaune amma sai ta ji hakan ya gagara. Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan ta shiga damuwa ainun, abin da Sharilat tun a daren jiya sarki Shabbar ya shayar da ita wani tsumin tsafi ta yadda bazata iya aiwatar da wani abu ba face da umarnin shi. Sa'adda ta tsinci kanta a cikin wannan hali sai Kawai ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya. A can filin yaƙi kuwa sarki Shabbar da jarumi Humairu sun wanzu suna kaiwa juna bugu da naushi hannu da ƙafa cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta, Idan ɗayan su ya kaiwa abokin gwamin shi naushi sai kaga shi ma ya mayar da martani cikin matuƙar zafin nama, Wohoho haƙiƙa artabun Manyan Mazaje daban ya ke da na ƙananan kwari inda ace mutum zai ga yadda jaruman ke naushi da bugun juna sai ya rantse cewa jikkunnan su ba su kasance na jini da tsoka ba. Ana cikin wannan artabu ne sarki Shabbar ya shammaci Humairu ya ciri wata wuta siririya mai ɗauke da guba ya caka ma shi a gefen cikinshi ta shige ciki, Humairu ya ƙwala kabbara da ƙarfi sakamakon raɗaɗi da zugin da ya ji. Kafin ta sake yin wani yunƙuri Shabbar ya taƙarƙare ya haure shi da ƙafa a ciki, Saboda ƙarfin dukan sai da Humairu ya yi katantanwa sau biyu a tsaye sannan ya faɗi ƙasa magashiyan yana mai dafe cikin shi yana turmutsutsu. Ko da samun wannan gagarumar nasara sai sarki shabbar ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da saƙon mutuwa, ya taka da ƙafafuwanshi har zuwa inda Humairu ke kwance ya raba ƙafafu a kan shi ya dube shi cikin murmushin mugunta ya ce "Shi yaƙi da ka ke gani ɗan zamba ne ai dama na faɗa maka bazaka samu nasara akai na ba yanzu zan maishe ka gawa. Gama faɗin hakan ke da wuya sai sarki Shabbar ya ɗaga hannunshi ɗaya izuwa sama wani zabgegen gatari na sihiri ya bayyana a gare shi, kawai sai ya ɗaga gatarin domin ya datse wuyan Humairu, Al'amarin da ya jefa tausayi a zuciyar gimbiya Mashlir kenan ta shiga zubar da hawayen baƙin ciki. ***** Lokacin da ya rage saura taku biyu aljanin ya isa inda su Sarki Baddadul-arus suke na da nufin ya talitse su, kwatsam bazato babu tsammani sai Baddadul-arus ya miƙe tsaye zumbur ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsenshi ya sokawa aljanin a cinyarshi ta hagu jini ya yi tsartuwa ya kurma wawan ihu. Kafin ya yi wani yunƙuri Baddadul-arus ya dako tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka yana saman ya zare ƙananun wuƙaƙe masu kaifin gaske ya soka a idanuwan shi, take jini ya dinga kwaranya tamkar an ɓalle kan fanfo, take aljanin ya faɗi ƙasa rikica! tamkar an jefar da toron giwa ko shurawa bai yi ba. Cikin gwaninta sarki Baddadul-arus ya sauka bisa turba, sannan ya matsa izuwa inda gimbiya Uzaima ta ke kwance magashiyan ya shiga ƙoƙarin ture dutsen da ya danne su, da ƙyar da siɗin goshi ya ture dutsen sannan ya sa ke faɗuwa ƙasa a galabaice. Cikin hanzari aka ɗauko jakar guzuri Kowa ya sanyawa raunukan shi magani, kuma aka yi kalace bayan kowa ya samu nutsuwa ne sai sarki Baddadul-arus ya dubi kowa ɗaya-bayan-ɗaya sannan ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku abokai na tafiya ta ku yi sani cewa duk da a halin yanzu a matuƙar galabaice mu ke sakamakon artabun da mu ka yi da wannan aljani, amma yazama wajibi mu cigaba da tafiya domin isa inda kushewar boka Hushaib ta ke". Ko da jin wannan batu daga bakin sarki sai hadimi Shaibat ya dube shi cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "Ya shugabana shin kana ganin cewa idan aka cigaba da tafiyar ɗaya daga cikin mu bazai rasa rayuwar shi kuwa ?. Sa'adda Baddadul-arus ya ji wannan tambaya daga bakin Shaibat sai ya dube shi ya ce "Ya kai Shaibat shin ka manta cewa a halin yanzu abokan gabar mu suna biye da mu a kowa ne hali su na iya cinma na baka tunanin cewa za a iya yin abun nan da masu iya magana ke cewa "kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi" na fi ka sanin wane ne sarki Himras da makircin shi". Da zafi-zafi a kan doki ƙarfe ina ji masu iya magana". Sarki Huraisu ya yi wannan furici yana duban Shaibat. Kafin wani ya sake furta wani abu Baddadul-arus ya miƙe tsaye zumbur ya zare wata sharbebiyar adda a gadon bayanshi ya sake kunna kai izuwa cikin kogon, ko da ganin hakan sai sarki Huraisu, Uzaima, hadimi shaibat su ka yi koyi da shi suna masu mara ma shi baya da sauri aljani zamzaru a ƙarshe aka cigaba da tafiya. Sai da aka shuɗe sa'a ɗaya ana tafiya a cikin kogon Garul-Shimshan, sannan aka iso kushewar boka sharubu, Ita dai kushewar an gina ta ne da zallar farin gilashi mai ƙyalli an ƙwata ta da da zinare, jauhari da lu'ulu'u, wani irin farin haske na musamman ya gauraye wajen baki ɗaya ta yadda ko da allura ce ta faɗi da mutum ya duba zai ganta, Saman ƙabarin an sanya wani narkeken murfi da aka yi shi da zunzurutun ƙarfen jauhari mai nauyin tsiya, inda za a sanya ƙarti majiya ƙarfin mutum hamsin baza su iya buɗe murfin ba, kuma murfin yana ɗauke da wani kwaɗo na musamman. Ya yin da aka yi arba da kushewar sai kowa ya sha jinin jikin shi, Sarki Baddadul-arus ya matsa kusa da inda kushewar ta ke ya sanya addar shi ya sari kwaɗon dake jikin murfin da dukkan ƙarfin shi, amma bisa mamaki sai ya ga ko motsi bai yi ba, Abu Kamar wasa sai da sarki ya shafe daƙiƙa hamsin yana saran mukullin amma shiru babu labari har ya tara zufa yana haki. Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin kowa kenan ya shiga damuwa ainun, Sarki Huraisu ya matsa kusa da Baddadul-arus ya dube shi ya ce "Tun da yanzu ka gaza samun sa'a sai ka ba ni na gwada tawa sa'ar. Ko da jin wannan batu sai Baddadul-arus ya ja da baya yana haki da huci, Huraisu ya ƙurawa murfin idanu yana nazari tsawon lokaci. Daga bisa ya juya ya dubi Baddadul-arus ya ce "Bisa nazari da na yi baza mu iya buɗe wannan kwaɗo ba face mun ɗauko wani mukulli a cikin wannan kogo". Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Huraisu sai Baddadul-arus ya ce "Zancen ka dutse tabbas dole mu nadama neman wannan mukulli tun da babu damar na gudanar da bincike bisa halarar tsafi na domin na gano inda mabudin ya ke. Sa'adda sarki Baddadul-arus ya zo nan azancen shi sai ya kunna kai izuwa cikin kogon Garul-Shimshan aka cigaba da tafiya. Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga ƙasa ta na motsawa wani irin tiririn ɓakin hayaƙi yana sirnamowa daga cikin ta, sannu a hankali hayaƙin yana canza launi har ya rikiɗa izuwa wata irin shirgegiyar maciji mai kawuna casa'in da tara, kowa ne kai ɗaya ya kai girman namijin zaki kowa ne baki na furzar da dafi, A bisa saman kawunan akwai wani kai guda ɗaya da ya kasance na bil'adama mai ɗauke da jajayen idanu, hanci, gami da baki masu matuƙar muni gami da ban tsoro. Sa'adda sarki Baddadul-arus, Uzaima, Shaibat, sarki Huraisu da aljani zamzaru suka yi arba da macijiyar sai cikin su ya duru ruwa, har Shaibat na sakin fitsari a wando saboda da firgici. Ko da macijiyar ta ga halin da su sarki Baddadul-arus suka shiga sai kawai ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko ma ta da WASIKAR MUTUWA, ta buɗe baki cikin kakkausar murya mai ban tsoro ta ce " Ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa yau fiye da shekaru dubu biyu babu wata halitta walau mutum ko aljan da taɓa shigowa wannan kogo na Garul-Shimshan sai ku, Na rantse da mai gidana boka sharubu ɗayan ku bazai fita a raye ba, domin kun shigo da kan ku cikin taskar ANNOBA DARI mai wahalar fitarwa, Ina mai tabbatar maku da cewa daga kan ku babu wata halitta da zata sake kwaɗayin zuwa nan. Kafin ɗaya daga cikin su ya furta wani abu macijiyar ta kanannaɗe su da jelar kuma waɗannan bakuna nata guda casa'in da tara suka shiga kafta masu sara a sassan jikkunan su. ***** Kamar yadda boka Hushaib ya faɗawa gimbiya Hulaifa da Sarkin yaƙi Nuhairu haka al'amarin yakasance, wato a daren ranar ya sake gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi inda ya gano cewa ba za su taɓa samun nasarar riskar jarumi Humairu face sun yi tafiyar sa'o'i goma. Bayan boka Hushaib ya sanar da gimbiya hakan sai kowa ya yi kalace ya kimtsa cikin shi, sannan aka cigaba da tafiya babu sassauci aka wanzu ana ratsa duwatsu tsaunuka da ƙoramu. Wannan shi ne abin da ya wakana da su boka Hushaib akan hanyar su ta nemo sassaƙen bishiyar Shajarul-kair domin magance cutukan da suka addabi al'ummar su. ***** Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga Humairu ya na daga kwancen ya sanya ƙafafuwanshi ya daki sarki a cikin shi da dukkan ƙarfin shi, Saboda ƙarfin dukan sai da Shabbar ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabaice jini na zuba a baki da hancinshi addar da ke hannunshi ta faɗi can gefe. Cikin matuƙar zafin nama Humairu ya miƙe tsaye zumbur ya raba ƙafafuwanshi akan wuyan sarki Shabbar ya dube shi ya ce a lokacin da ya ke kakarin mutuwa ya "Ya kai wannan sarki yanzu gashi kana kan gaɓar mutuwa shin bazaka bada gaskiya da Ubangijin da ya haliccin duniya da abin da ya ke cikin ta ?. Ko da jin wannan batu daga bakin Humairu sai sarki Shabbar ya bushe da dariyar ƙarfin hali ya furzar da gudan jini daga bakin shi, sannan ya dubi Humairu Muryar shi na sarƙewa ya ce "Ya kai wannan hatsabibin jarumi ka yi sani cewa lokacin ina yaro ƙarami mahaifiya ta ta taɓa faɗa min cewa akwai wani addini na gaskiya ba namu na bautar gumaka ba, Sai dai baza mu bi addinin ba saboda ba shi ne mu ka Gada a wajen zuri'ar mu ba, Ni ma tun da iyaye na basu bi addinin ba ni ma bazan bi shi ba. Ko da sarki Shabbar ya zo nan a zancen shi sai ya sanya hannayenshi ya murɗewa kan shi wuya ya sheƙa barzahu ko shurawa bai yi ba. Nan take Jarumi Humairu ya cika da matuƙar baƙin ciki bisa ganin yadda sarki Shabbar bai ƙarɓi addinin musulunci ba. A dai-dai wannan lokaci ne sauran dakarun marigayi Shabbar suka zubar da makaman su suka yi mubaya'a bisa ganin an kashe shugaban su, Kawai sai Humairu ya taka da ƙafafuwanshi har izuwa inda gimbiya Mashlira ke kwance ya karanta ayatullah kursiyyu ya tofa ma ta take igiyoyin da suka ɗaure ta suka ɓace ɓat kuma ta miƙe tsaye cikin ƙoshin Lafiya tamkar babu wani abu da ya shafe ta. Ta dubi Humairu cikin annurin fuska ta ce "Ya kai SARKIN SADAUKAI ka yi sani cewa tabbas a yanzu zan cika maka alƙawarin da na yi na ƙarbar addinin musulunci, Sai dai kafin hakan ina roƙon wata alfarma a wajen ka?, alfarmar kuwa ita ce ina so ka amince mani na bika duk inda zaka a cikin wannan duniya. Ko da jin wannan batu sai Humairu ya sunkuya kanshi ƙasa yana nazari, daga bisani ya ɗago da kai ya ce "Na amince da wannan alfarma ta ki amma kuma yanzu muka tafi tare wane ne zai cigaba da riƙe sarautar birnin ku?. Da jin wannan tambaya sai Mashlira ta yi murmushi ta ce "Ba buƙatar na ɗauki nauyin al'umma akai na zan ɗora dukkanin wanda ya dace a bisa KARAGAR MULKI. Ko da gama faɗin hakan sai ta ƙwallawa wani badakare kira daga cikin dakarun su, badakaren ya bayyana gabanta ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, Mashlir ta ce "Ya kai Luhzul ka yi sani cewa ina so ka sanya a busa ƙahon shela ina so kowa ya taru anan. Ko da jin wannan umarni sai barde Luhzul ya risina ya ce "An gama ya shugabata, Yana gama faɗin hakan ya koma gefe guda ya hau bisa wani dogon gini ya ɗauko wani zungureran ƙaho a aljihun shi ya kafa a baki ya busa da ƙarfi, ƙarar sautin busar ya mamaye wajen ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin, Faruwar hakan ke da wuya sai ga jama'a na tuttuɗowa daga kowa ce kusurwa, saƙo da lungu, maza, mata, yara da manya suna taruwa a waje guda, A dai-dai wannan lokaci ne yarima Muzaifar ya hangi jaruma Sharilat a cikin dandazon jama'a ta rugo zuwa gare shi fuskarta cike da annuri. Abin da yarima bai sani ba shi ne bakomai ne ya hana Sharilat ta fito daga cikin gidan sarautar sarki Shabbar ba ba, Sai domin sihirin da ya yi mata bai karye ba sai da ya mutu sannan sihirin ya karye. Ya yin da Sharilat ta iso daf da su sarki Himras sai ta rungume mahaifin ta tsoho kuhairu su duka biyun sun fashe da kukan baƙin cikin rabuwa da juna, sun ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani Sharilat ta janye jikinta daga na mahaifin ta ta jefi yarima Muzaifar da wani irin ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar SO da ƙauna. Sannan ta mayar da duban ta ga Humairu ko da ta haɗa idanu da shi sai ta ji tsikar jikinta ta tashi kuma wani abu ya ɗarsu a zuciyarta wanda ya kasa tantance ko mene ne?. Ashe duk wannan abu da ke faruwa tsakanin Humairu da Sharilat, sa'adda ya ga irin kallon da Sharilat ke yiwa Humairun sai ya ji kishi ya turnuƙe shi ya ce a cikin ran shi shin me Sharilat ke nufi da wannan kallon da take yiwa Humairu?. A inda wani ɓangare a zuciyarshi kuma ke cewa da shi baka tunanin cewa matuƙar mamakin ganin Humairu ne ya sa ta ke yi ma shi wannan kallo? ba wai don ta kamu da soyayyar shi ba, amma kuma masu iya magana na cewa labarin zuciya a tambayi fuska, tabbas kallon da Sharilat ke yi ma shi akwai alamun soyayya. Amsar tambayoyin da yarima ya kasa bawa kan shi kenan, nan take ya ji zuciyarshi ta yi ma shi ƙunci. Lokacin da kawo ya kammala hallara a filin sai gimbiya Mashlira ta ɗaga hannunta kowa ya tsuke bakin shi tamkar mutuwa ta gifta, ta kawo gworon numfashi ta ajiye sannan ta yi gyaran murya cikin tattausan lafazi "Ya ku jama'ar wannan birni namu mai albarka ku yi sani cewa fiye da shekaru ashirin mahaifina sarki Shabbar na shimfiɗa mulkin KAMA KARYA amma ba a samu wani mahaluki da lashi takobin kawo KARSHEN ZALUNCI na abbana sai wannan baƙon jarumin da ya ke tseratar da rayuwar mu daga sharrin sarki, Na sani cewa da yawa daga cikin ku suna bin abbana ne saboda tsoron makircin shi ne saboda babu yadda za su yi. Da wannan nake yi maku fatan alheri da cewa kowa ya samu 'yanci zan ƙarɓi addinin wannan Jarumi domin haƙiƙa shi ne addinin gaskiya. Sa'adda gimbiya Mashlira ta zo dai-dai nan azancen ta sai ta juya ya dubi Humairu ta ce "Ya kai SARKIN SADAUKAI yanzu a shirye nake ka shigar da ni addinin ka mai daraja. Ko da jin wannan batu daga Mashlira sai Humairu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ya karantawa Mashlira kalmar shahada ta maimaita, nan take ya yi kabbara da salati domin nuna godiyar shi ga Allah, Kana ya buɗi baki ya dube ta fuskarshi cike da annuri ya ce "Ya ke Mashlira ki yi sani cewa daga yau kin zama 'yar uwata a musulunci duk wani hukunci na addini ya hau kan ki. Koda jin wannan batu sai Mashlira ta juya ta fuskanci jama'ar ta ta karanta masu kalmar shahada dukkanin su suka maimaita, nan fa farin ciki ya sake mamaye zuciyar Humairu ya yi godiya ga Allah bisa shiryar da ma'abota bautar gumaka izuwa TAFARKIN GASKIYA. Har Mashlira ta juya da nufin ta shige izuwa cikin gidan sarauta sai kawai aka jiyo ƙarar takun sawaye da haniniyar dawakai daga can bakin ƙofar gari, cikin hanzari kowa ya waiga domin aka kowa su wane ne?. Ya yin da aka yi arba da su sai aka shiga yin kallon-kallo tsakanin su da jama'ar birnin, Ba wasu ba ne face boka Hushaib, gimbiya Hulaifa da Sarkin yaƙi Nuhairu, duk daga nesa su boka Hushaib suka ƙurawa su sarki Himras idanu fuskokinsu a murtuke babu annuri. Abu na farko da ya faɗowa su boka Hushaib a rai shi ne, tabbas su sarki Himras da su ke nema ruwa a jallo domin ɗaukar fansa akan raba su da sarƙar tsafin su mai daraja?. Shin yanzu za su tattauna da Humaira ne domin tunkarar matsalar da ke gaban su?. Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kan su kenan, lokacin da yazamana tazarar da ke tsakanin su da jama'a ba sai suka ja linzamin dawakan su suka tsaya cak. Ciki maɗaukakiyar murya boka Hushaib ya buɗi baki ya ce "Ya ku jama'ar wannan birni ku yi sani cewa bakomai ne ya kawo mu gare ku sai domin mu sadu da Jarumi Humairu ma'abocin addinin Musulunci. Ko da jin wannan batu daga bakin Hushaib sai Humairu ya taka da ƙafafuwanshi ya durfafi inda suke jama'a suna masu darewa suka buɗe ma shi hanya, ya yin da ya isa gare su sai ya dube su ɗaya-bayan-ɗaya ya yi gyaran murya ya ce cikin annurin fuska "Ya ku waɗannan baƙi masu daraja kuyi sani cewa tun kafin zuwan ku Ubangiji na ya bayyana mani buƙatar ku da zuwan ku nan a cikin mafarki na, Abin da ke tafe da ku ɗin shi ne kuna so na yi maku rakiya izuwa ɗauko TAKOBIN SIHIRI daga nan a nemo Shajarul-kair wacce za'a yi amfani da ita ne wajen saro sauwar bishiyar, domin warkar da al'ummar birnin ku da cututtukan da suka addabe su sakamakon suɓucewar sarƙar tsafin ku. Ko da jin wannan jawabi daga bakin Humairu sai su boka Hushaib suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi. Boka Hushaib ya yi gyaran murya a karo na biyu sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye ya ce "Ya kai jarumi ma'abaocin al'ajabi ka yi sani cewa haƙiƙa mun yi matuƙar mamakin yadda aka yi ka san da buƙatar da ke tafe da mu izuwa gare ka, muna fatan za ka biya buƙatar cikin abinda bai gaza kwanaki ƙalilan ba ?, Sannan ka faɗi ladan da za mu biya ka da ya danganci zinare, jauhari da yaƙut. Ko da jin wannan batu daga bakin boka Hushaib sai jarumi Humairu ya yi murmushi mai taushi da ya daɗawa fuskarshi kwarjini ya dubi Hushaib ya ce "Ya kai wannan dattijo ka yi sani cewa na amince zan biya maku buƙatar ku amma abin da kawai na ke buƙata ku bayar da gaskiya da Ubangiji na. Ko da jin wannan batu daga bakin Humairu sai boka Hushaib ya ce "Ka ɗan bani lokaci zan tattaunawa da abokan tafiya ta, Humairu ya gyaɗa kai alamar gamsuwa. Boka Hushaib matsa kusa da su Hulaifa inda ya dube su ya ce "Yanzu dai kun ji abin da Humaira ya ce shin yanzu kuna ganin za mu amince da buƙatar shi ta imani da Ubangijin shi bayan cewa namu abin bautar na tare da mu ba ku tunin cewa zai yi fushi da mu?. Ko da jin wannan batu sai gimbiya Hulaifa ta buɗe baki a karo na farko ta yi gyaran murya ta ce "Ya abin dogaro ina ganin fa babu wata hanya da za mu bi face mu amince da buƙatar Humairu domin bijirewa hakan tamkar rushe birnin mu ne baki ɗaya". Cikin ladabi sarkin yaƙi Nuhairu ya dubi gimbiya ya ce "Ina ganin abin bautar mu ya fi kowa sanin halin da mu ke a ciki me ya sanya bai kawo mana ɗauki ba shin mene ne amfanin Ubangijin da bazai share hawayen bayin shi ba, Amincewa da buƙatar Humairu shi ne mafita kawai, sannan ina so na ja hankalin mu kada wani a cikin mu ya yi yunƙurin ɗaukar fansa akan su sarki Himras domin hakan zai rushe cikar burin mu baki ɗaya. Sa'adda boka Hushaib ya ji wannan batu daga bakin sarkin yaƙi Nuhairu sai ya gyaɗa kai alamar gamsuwa, sai kawai ya durfafi inda Humairu ke tsaye ya dube shi ya ce "Ni da abokan tafiya ta sun amince da buƙatar ka kuma ba zamu taɓa yaudarar ka ba. Sa'adda Humairu ya ji wannan batu sai ya a cika da matuƙar farin ciki ya yi wa gimbiya Hulaifa wani kallo mai ɗauke da alamar tambaya da ya sanya su dukan biyun zukatan su suka buga da ƙarfi. "Ya ku zauna da ni a wannan birni zuwa wani lokaci kaɗan kuna cikin kulawa ta, sannan mu shirya tafiya. Humaira ya yi wannan furici yana satar kallon Hulaifa. Ko da gama faɗin hakan sai jarumi Humairu ya juya ya shiga gab, boka Hushaib, gimbiya Hulaifa da sarkin yaƙi Nuhairu na biye da shi suna masu sakarwa dawakan su linzami, nan take aka ɗunguma izuwa cikin gidan sarauta shi ma aljani Narguz ya yi koyi da su. ***** Lokacin da wannan macijiya mai kawuna casa'in da tara ta shiga kaftawa su sarki Baddadul-arus sara a dukkan sassan jikkunan s. sai nan take dukkan su suka taƙarƙare suka kurma wawan ihu sakamakon raɗaɗi da azabar da suka ji. Amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta hamshaƙan sarakai kuma JARUMAN DUNIYA a cikin wannan hali ne suka zare makaman su suka shiga kaiwa macijiyar sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da nacin tsiya. A duk sa'adda makamansu suka sari jakinta sai su ji tamkar dutse suka sara ko gezau ba ta yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare. Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin su sarki Baddadul-arus kenan suka shiga damuwa ainun bisa ganin babu alamun nasara, sai da aka shafe tsawon rabin sa'a da daƙiƙa hamsin ana wannan artabu babu sassauci, yazamana cewa babu alamun nasara ga ɓangaren su Baddadul-arus amma ita macijiyar ta yi masu sara fiye da goma. Wohoho haƙiƙa tashin hankali ba'a sa masa rana, wutar bala'i kafin ta zo ake tunanin ya za a yi da ita, idan kuwa ta zo sai dai a nemi mafita kawai, lokacin da sarki Baddadul-arus ya ga cewa shi da abokan tafiyar shi sun jigata ainun sai nan take ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita. Ko da samun mafitar sai kawai ya dunƙule hannayensa ya damƙi kawunan macijiyar guda shida a lokacin da suka kawo ma shi hari ya kanannaɗe su tamkar zai tufka igiya, ya cizge kawunan da dukkan ƙarfin shi nan take jini ya yi tsartuwa ya zuba a ƙasa, macijiyar ta kurma wawan ihu kuma ta saki su sarki Huraisu da ta kanannaɗe su da jelarta suka faɗo ƙasa tim a matuƙar galabaice. Kafin macijiyar ta sake wani yunƙuri sarki Baddadul-arus ya daka tsalle sama tamkar an harbo shi daga cikin baka ya sanya hannayenshi biyu ya gabza mata wawan naushi a idanuwanta biyu dake jikin wannan ƙaton kai na bil'adama. Take idanun suka fashe jini ya shiga kwaranya tamkar an buɗe kan fanfo, take ta faɗi ƙasa ko shurawa ba ta yi ba, sannan ta rikiɗa izuwa wani farin haske ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba, a sannanne duhun dake kogon ya ragu ainun, kuma su Baddadul-arus suka hango wani ƙasaitaccen makulli na zinare ajiye a ƙasa ne da kaɗan da inda suke. Cikin matuƙar farin cikin sarki Baddadul-arus ya miƙe tsaye zumbur ya taka zuwa inda makullin ya ke, sarki Huraisu, gimbiya Uzaima, shaibat da aljani zamzaru suka miƙe tsaye tsaye. Baddadul-arus ya dube su ya a nutse ya ce "Ya abokan tafiya ta ku yi sani cewa wannan makulli da kuka gani a hannu na shine mabudin kushewar boka sharubu, duk da mawuyacin halin da mu ke ciki amma yazama wajibi gare mu mu isa ida kushewar take domin kammala aikinmu. Ko da jin wannan batu daga bakin Baddadul-arus sai kowa ya gyaɗa kai alamar gamsuwa, kawai sai ya shiga gaba ya fara tafiya yana tunkarar kushewar su gimbiya Uzaima na biye da shi. Ya yin da aka iso sai kowa ya ja ya tsaya, sarki Baddadul-arus ya sanya wannan makullin a wata siririyar rami na kwafi dake jikin murfin da ya rufe kushewar ya murɗa har sau uku, take kwaɗon ya buɗe kanshi, Baddadul-arus ya sanya hannunshi ya dage murfin, haƙiƙa komai hassadar mutum idan ya ga yadda Baddadul-arus a lokacin da ya ke ɗage murfin da aka yi da zallar jauhari dole ne ya jinjina masa ya tabbatar da cewa ya cika GWARZON DUNIYA. Murfin na kammala buɗe wa sai wani farin haske da hayaƙi na musamman ya tuttuɗowa daga kushewar ya gauraye kogon baki ɗaya ta yadda ko allura ce ta faɗi da zarar mutum ya duba zai ganta. Cikin matuƙar farin ciki Baddadul-arus ya ɗauko sarƙar tsafi a cikin aljihun rigarshi ya sanya ta a bisa wuyan gawar boka sharubu wacce ke rufe a cikin wani mayafi na sihiri da ba a iya ganin fuskar shi. Faruwar hakan ke da wuya sai gaba ɗaya kogon na Garul-Shimshan ya shiga girgiza aka kwantsama wata tsawa mai ban tsoro tamkar hadari zai gangamo a ɓarke da ruwan sama, al'amarin da ya sanya sarki Baddadul-arus, Uzaima, Shaibat, sarki Huraisu da aljani zamzaru suka ɗimauce suka durƙusa ƙasa bisa gwiwoyin su suna masu sunkuyar da kawunansu, Tsawon lokacin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne kogon dutsen ya samu dai-dai to kuma a ka ɓarke da wata dariya mai kama da kukan jaki. Tamkar ɗaukewar ruwan sama dariyar ta ɗauke sannan wata kakkausar murya ta ce "Lale marhaban da zuwan sarki Baddadul-arus na birnin madinatul-husuf mai burin zamowa sarkin sarakuna na nahiyar mufrad tare da sarki Huraisu ma'abocin baiwa da hikima izuwa kogin Garul-Shimshan, sai ku yi hanzari ku ɗago da kawunanku domin ku yi arba da sarkin bokaye Sharubu ibn shalyasu. Ko da jin wannan batu daga bakin boka Sharubu sai su Baddadul-arus suka ɗago da kawunansu ya yin da suka yi arba da boka Sharubu sai suka firgice jikkunansu suka kama tsuma suna ƙyarma ba su san sa'adda suka faɗi ƙasa ba suka yi sujjada a gare shi. Shi dai boka sharubu yakasance garjejen kato mai ƙirar samudawan farko, fuskarshi mummuna ce mai cike da kwarjini, Idanuwanshi jajaye ne tamkar garwashin wuta, hancinshi faffaɗa ne tamkar mazirari, bakinshi kuwa tafkeke tamkar ƙofar gari, gashin kanshi fari ne sol, ƙasumba da gemunshi baƙaƙe siɗik, kuma yana sanye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke tun daga ƙasa har sama. Haƙiƙa duk inda ake neman gwarzon mayaƙi boka sharubu ya cika, domin babu wata halitta mai numfashi da za ta yi arba da shi face ta ɗimauce. Boka Sharubu ya bushe da dariya a karo na biyu Sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da saƙon mutuwa ya dubi su sarki Baddadul-arus a lokacin da suka ɗago daga sujjadar ya ce da su "Ya ku waɗannan sarakuna ku yi sani cewa a rayuwa babu wata halitta da ta taɓa taimako na kamar ku, haƙiƙa ina mai tabbatar maku da cewa zan cika maku burikan ku na ɗauko littafin SIIHIRTACCEN KUNDI domin mallakar takobin sihirin sarkin bokayen duniya. Na rantse da rayuwa da mutuwata idan har aka yi ganganci na dawo duniya domin sake Sabuwar rayuwa sai na zamo wa duk wata halitta gobarar daji. Ko da gama faɗin hakan sai boka Sharubu ya sanya hannunshi na hagu ya shafi damtsenshi na hagu wani dogon mashi na sihiri ya bayyana ya nuna su Baddadul-arus da tsinin mashin, take su ka ji wani irin gagarumin ƙarfi ya shige su, duk wata lalura da ke jikin su ta fice, Sannan ya sake nuna su karo na biyu take dukkanin su suka ɓace ɓat tamkar ba su taɓa wanzu ba. Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Baddadul-arus a cikin kogon Garul-Shimshan mafakar dukkan wata musiba a duniya. ***** Al'amarin su jarumi Humairu kuwa, Sai da Humairu ya shafe kwanaki bakwai ya na koyar da gimbiya Mashlira da jama'ar ta yadda ake gudanar da bautar Ubangiji, Tun daga alwala, sallah da karatun Alkur'ani mai tsarki. Lokacin da gimbiya Mashlira da jama'ar ta suka tsinci kan su cikin sabuwar rayuwa mai cike da tsafta da farin ciki, Sai suka cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, Yazamana cewa duk wani abu da za su gudanar sai da umarnin shi. Boka Hushaib, Yarima Muzaifar, Sharilat sai da suka cika da matuƙar mamakin yadda a lokaci guda Humairu ya canza halayen arnar dajin, har da sanya tufafinsu da zamantakewar su. A safiyar kwana na goma ne bayan jarumi Humairu ya yi wa gimbiya Mashlira da jama'ar ta limancin sallar asuba sai ya sanar da su sarki Himras da su gimbiya Hulaifa cewa yau ne za su yi bankwana da jama'ar birnin arnar dajin domin cigaba da tafiyar su. Bayan kammala shiri ne sai jarumi Humairu ya naɗa wani dattijo mai suna Abu-damzur da ya ɗara kowa fahimtar addinin Islama a matsayin sabon sarkin birnin arnar dajin har zuwa lokacin da za su dawo daga tafiyar su. Ko da zartar da hakan sai aljani Narguz ya ya ɗauke su duka ya tashi zuwa sararin samaniya ya na mai tsala matuƙar gudu, A halin yanzu dai tafiya ta koma ta mutum tara saɓanin huɗu, wato sarki Himras, yarima Muzaifar, tsoho kuhairu, jaruma Sharilat, gimbiya Hulaifa, boka Hushaib, sarkin yaƙi Nuhairu gimbiya Mashlira da jarumi Humairu. A na fara wannan tafiya ne jarumi Humairu ya dubi sarki Himras dake zaune daf da yarima Muzaifar ya ce da shi "Ya kai Himras shin yanzu ina za mu nufa kai tsaye?, Ko da jin wannan tambaya sai Himras ya murtuke fuska tamkar aiko ma shi da WASIKAR MUTUWA ya ce "Ya kai Humairu shin na manta alkawarin da ke tsakanin mu da kai na cewa kana ƙarƙashin kulawar Mashlira ka ga kenan yanzu ita ce ya dace ta yi mani wannan tambaya, Al'amarin su sarki Himras kuwa sai da suka shafe tsawon Sa'a huɗu suna tafiya a sararin samaniya bisa kan aljani Narguz sannan suka iso fadar Sarkin bokayen duniya, Bayan kowa ya sauko daga kan aljani Narguz sai jaruma Sharilat ta dubi mahaifinta ta ce "Ya abbana a halin yanzu ne ya kamata mu karɓi addinin Humairu domin buɗewar idanuwanka kafin mu shiga fadar Sarkin bokaye". Da jin wannan batu sai kuhairu ya ce "Zancen ki dutse ya ke 'yata haƙiƙa kin kawo magana mai kyau, Yanzu sai ki je ki sanar ma shi da hakan. Ko da jin wannan batu sai Sharilat ta juya ta nufi inda Humairu ya ke tsaye ta dube shi ta ce "Ya Sarkin Sadaukai kuma jarumin jarumai ka yi sani cewa a halin yanzu ni da mahaifina mun amince mu karɓi addininka, yanzu ma haka shi ne ya ce na zo na same ka. Ko da jin wannan batu daga bakin Sharilat sai fuskar Humairu ta faɗaɗa da murmushi ya juya ya shige gaba Sharilat na biye da shi suka durfafi inda kuhairu ya ke tsaye. Suna isa inda kuhairu ya ke sai jarumi Humairu ya ɗaga hannunshi sama yana mai cewa "Ya Ubangijin halitta don tsarkin mulkinka ka buɗe idanun wannan bawa naka kuhairu ka ba shi lafiya. Haƙiƙa Ubangiji shi ne mai yiwa bayinshi komai ba wani abun halitta ba, Humairu na kammala yin wannan addu'a sai idanun tsoho kuhairu suka buɗe tarwai tamkar bai taɓa yin makanta ba, Saboda matuƙar farin ciki Sharilat bata san sa'adda faɗa bisa ƙirjin mahaifinta ba suka rungume juna cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Duk wannan abu da ke faruwa tsakanin Humairu da su kuhairu su sarki Himras suna tsaye a gefe guda suna kallo cike da matuƙar mamaki, Amma a ɓangaren Himras kuwa zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone,Abu na farko da ya faɗo ma shi a rai da ya fusata shi shi ne haƙiƙa buɗewar idanuwan kuhairu abu ne mai haɗari a gare shi, domin ya kowa sanin wane ne kuhairu, Abin tambaya a nan shi ne yaushe kuhairu da Sharilat suka yanke wannan shawarar Ba tare da sun ne mi izinin shi ba?. Amsar tambayoyin da Himras ya kasa bawa kanshi kenan zuciyarshi na cigaba da yi ma shi ƙuna, Wani tunani da ya faɗo ma sa a yanzu ma shi ne tabbas buɗewar idanuwan kuhairu zai iya janyo zuciyar yarima Muzaifar zuwa addinin Musulunci. Sai da Sharilat da mahaifinta suka ɗauki tsawon lokaci a rungume da juna, sannan daga bisani kuhairu ya janye jikinshi daga na ta ya dubi Humairu da Idanuwanshi fuskarshi cike da annuri ya ce "Ya kai jarumin jarumai ka yi sani cewa a shirye mu ke mu karɓi addininka domin cika ma ka alƙawari". Ko da jin wannan batu sai Humairu ya karanta kalmar shahada, kuhairu da Sharilat suka maimaita take ya yi kabbara domin nuna godiyar shi ga Allah SWT. Ko da sarki Himras ya ga cewa kuhairu da 'yarshi sun karɓi Musulunci sai ya fusata ainun ya nufe su ya na isa gare su ya dube su ya ce "Ya kai kuhairu haƙiƙa kun tafka babban kuskure da kuka karɓi addini Humairu yanzu ta ya ya zamu iya shiga fadar Sarkin bokaye har mu ɗauko TAKOBIN SIHIRI. Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Himras sai kuhairu ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da wasikar mutuwa ya dube shi ya ce "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa wannan abu da ka tuhume mu baya daga cikin sharaɗin tafiyar mu tare da ku, saboda haka wannan abu bai shafe ka ba". Ko da jin wannan batu sai zuciyar Himras ta kama tafarfasa tamkar za ta tsaga ƙirjinshi ta fito waje, ya ji tamkar ya zare takobinshi ya afkawa kuhairu da yaƙi, Amma sai ya fasa bisa wani tunani da ya faɗo ma shi, tunanin shi ne, ko da su kuhairu sun karɓi addinin Musulunci sun yi aikin banza domin ka na gab da mallakar takobin sihiri da zarar hakan ta faru za su zamo bayin ka sai yadda ka yi da su. Da wannan tunani ne ya matsa kusa da ɗan shi Muzaifar aka fara kallon-kallon yadda ƙofar shiga fadar Sarkin bokaye ta kasance. Sarki Himras ya buɗe Sihirtaccen kundi ya shiga karantawa tsawon daƙiƙa ɗari biyu amma babu alamun ƙofar za ta buɗe har sai Himras ya tsagaita da karatun aka yi shiru babu wanda ya ce uffan, Daga can sai Humairu ya yi gyaran murya ya ce "Ya abokanan tafiyata shin yanzu haka za mu tsaya muna jiran gawon shanu, idan kun amince mani sai na buɗe kofar bisa taimakon Ubangijina, Da jin wannan batu daga bakin Humairu sai kowa ya yi shiru, ya yin da Humairu ya fahimci cewa babu wani mai jayayya da maganarshi sai ya matsa daf da ƙofar ya karanta sunayen Allah tsarkaka, Nan fa wani abun al'ajabi ya wakana ai kuwa sai aka ga Humairu ya na tura makekiyar ƙofar fadar da aka yi ta da zallar ƙarfen jauhari mai nauyin gaske wacce inda za a sanya ƙarti majiya ƙarfi mutum hamsin ba za su iya ture ta ba, Jim kaɗan bayan buɗewar ƙofar sai a ka ga wani irin farin haske baban mamaki ya ratso daga cikin fadar. Ba tare da fargabar komai ba sarki Himras ya kunna kai izuwa ciki hannunshi na hagu ɗauke da Sihirtaccen kundi na daman kuwa rike da wata sharbebiyar takobi,take Yarima Muzaifar,boka Hushaib, gimbiya Hulaifa, gimbiya Mashlira, Sarkin yaƙi Nuhairu,aljani Narguz suka mara mashi baya, jaruma Sharilat tsoho kuhairu da jarumi Humairu ne a ƙarshe, Aka fara tafiya babu sassauci nan fa aka dunga ganin abubuwan al'ajabi nau'i daban-daban. Tabbas na zaune bai ga gari ba, haƙiƙa fadar sarkin bokaye ita ce ƙarshen aljanna duniya, Gimbiya Mashlira ce ta yi wannan furuci a ranta batare da ta furta wani ya ji ba, Nan fa kowa ya sha jinin jikinshi bisa ganin yadda shiru ya wanzu a fadar tamkar babu wani abu mai numfashi a cikin ta, Duk sa'adda ɗaya daga cikin tawagar ya ajiye ƙafarshi ɗaya sai ka ji ƙarar takun sawun ya mamaye fadar. Da ga cikin waɗansu ɓangarori a fadar na ɗauke da waɗansu gumaka da aka sassaƙa su da surorin dodanni da miyagun aljanu, Duk da kasancewar su a sandare suke sai su sarki Himras suka ji hankulansu sun dugunzuma ainun, Tsawon lokaci ana cikin wannan tafiya kwatsam sai ganin fadar ya fara tsagewa wani irin ƙara da rugugi tamkar aradu ya fara bayyana, Ba shiri kowa ya ja ya tsaya aka shiga lalle kalle da dube-dube domin ganin mene ne zai faru, Jim kaɗan kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu miyagun samudawan dakaru na ratsowa daga cikin garun fadar tamkar yadda ruwa ke tsattdafo wa daga cikin ƙarƙashin ƙasa, Su dai dakarun sun kasance daga ƙugunsu zuwa yatsun ƙafafuwansu suna da jiki ne irin na gwaggwan biri, a tsakiyar kawunansu suna ɗauke da wani ƙaho irin na ɓauna, a gwiɓin hammatarsu hagu da dama suna ɗauke da fuka-fukai irin na tsuntsun batoyi, idanuwansu jajaye ne tamkar garwashi a hannayensu suna ɗauke da waɗansu sharɓa-sharɓan takubba na haske. Haƙiƙa Waɗannan dabaru sun cika abin tsoro, babu wata halitta mai numfashi da zata arba da su face ta yi nadamar wanzuwar ta a doron duniya, Nan fa jikkunan su sarki Himras ya kama tsuma saboda matuƙar tsoro, Tsoho kuhairu, Sharilat da jarumi Humairu ne kaɗai ba su razana ainun ba su ma ɗin sirrin kalmar shahada ne ya sanya ba su firge ba, Domin duk wanda ya ji tsoron Allah sai Allah ya dauke ma shi tsoron halittarshi. Ko da sarki Himras ya fahimci cewa dakarun ba su da niyyar afka ma su, sai kawai ya kurma ihu ya ɗaga takobinshi sama ya afkawa dakarun ko da ganin hakan sai su yarima Muzaifar suka yi koyi da shi, kuhairu, jaruma Sharilat, Humairu suna ƙwala kabbara da ƙarfi, Sa'adda dakarun suka ga cewa su sarki Himras sun tunkaro su cikin mugun tanadi sai suka tare su aka yi KARON BATTA aka yamutse da masifaffan yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro. Haƙiƙa KARON MAZA sai 'yan maza, kuma idan jarumta ta haɗu da juriya dole ne KARFIN DAMTSE su yi aiki, Da a ce mutum na tsaye a wannan waje zai yi arba da irin yawan dakarun sai ya ce su sarki Himras sun taru a radu da ka amma dai masu iya magana na cewa duk wanda ya ƙona rumbunshi ya san inda toka take daraja. Nan fa ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance, Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan artabu batare nasara ga kowa ne ɓangare ba. Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankulan su sarki Himras kenan, suka fahimci cewa tabbas idan za a kwana biyu ana wannan artabu waɗannan dakarun ba Za su gaji ba, Wani abu da ya fi dugunzuma hankulan su shi ne duk sa'adda takubbansu suka sauka a bisa dakarun sai su ji tamkar dutse suka sara ko gezau basa yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare. A ɓangaren dakarun kuwa sa'adda suka ga an shafe tsawon Sa'a batare da sun samu nasara akan su Himras sai suka cika da matuƙar mamaki kuma suka fusata ainun, A tsawon wanzuwar su a fadar ba su taɓa yin artabu da halitta mai zafin nama tamkar su sarki Himras ba har yazamana an shuɗe wannan lokaci ba tare da samun nasara ba, Abin da ya fusata su shi ne taya ya za a ce MAZAN JIYA irin su da suka saba yin bakin artabu a Dajin mutuwa a ce bil'adama ya gagare su hallaka wa, Ko da suka zo nan a tunanin su sai suka canza salon faɗansu yazamana sun zage damtse wajen kaiwa su sarki Himras miyagun hare-haren fiye da ɗazu. Faruwar hakan ke da wuya sai labari ya sha bamban domin a halin yanzu dakarun sun fara samun nasarar yiwa su Humairu manyan raunika fiye da shida kowanne na ZUBAR DA JINI, Sa'adda jarumi Humairu ya fahimci halin da suke ciki sai kawai ya shiga neman taimakon Ubangijin talikai ta hanyar yin kamun ƙafa da tsarkakan sunayen Allah (SWT). Kafin wani lokaci jiri ya fara ɗibar su sarki Himras sun shiga cikin mawuyacin hali, kafin wani lokaci kowa ya zube a ƙasa magashiyan, Sai Humairu, Sharilat, kuhairu da Mashlira ne kaɗai ba suke tsaye, Ko da ganin hakan sai Humairu ya ƙwala kabbara da ƙarfi, ya afkawa dakarun, Al'amarin da ya sanya kuhairu, Sharilat da Mashlira suka ji wani sabon ƙarfi na musamman ya shige su suka rufa ma shi baya aka yamutse da sabon masifaffan yaƙi, Tabbas duk wanda ya yi imani da Ubangijin halitta sai ya zamo ma shi jin shi da ganin shi, Ana fara wannan sabon artabu ne sai wani abun mamaki ya fara gudana domin a wannan lokacin duk inda ɗaya daga cikin su Humairu ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga. Nan fa ihun mazaje ƙarar karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne jini ya dinga kwaranya tamkar an buɗe ƙorama, sassan jikkuna suka dinga shawagi a sama suna zubowa ƙasa, duk inda mutum ya kai duban shi babu abin da zai gani face gawarwakin dakarun duku-dukun kwance cikin jini babu kyawun gani. Su Humairu suka wanzu suna aika rayukan dakarun barzahu ta hanyar sara da sukar su da takubbansu cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta Dakarun musulunci ko a ce irin ta Bajakade, Al'amarin da ya yi matuƙar bawa su sarki Himras dake kwance magashiyan mamaki kenan bisa ganin wannan gagarumar bajinta da su kuhairu ke yi, Kuma ya sanya Sharilat, Mashlira da kuhairu suka ji sun ƙara imani da Ubangiji a zukatansu. Sai da aka shafe tsawon rabin sa'a ana wannan ƙazamin artabu bisa taimakon Ubangiji su Humairu suka hallaka baki ɗaya dakarun ba su bar ɗayan su a raye ba, Bayan komai ya dai-dai su sarki Himras sun sanya raunukan su magani sai aka sake ɗunguma aka tusa kai izuwa cikin fadar ana tafiya cikin hanzari. *** Al'amarin su sarki Baddadul-arus kuwa tun sa'adda suka ɓace daga cikin wannan ƙasaitaccen gida bayan sun ga abin da ya faru da abokan gabar su su sarki Himras a cikin halarar tsafin boka Sharubu ba su bayyana a ko ina ba sai a ƙofar fadar sarkin bokayen duniya. Ko da bayyanar ta su sai boka Sharubu ya kama kalle-kalle da dube-dube yana nazarin takun sawayen su sarki Himras, Kawai sai aka ga ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu daga bisani Kuma ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da saƙon mutuwa, fuskarshi har gatsine ta ke yi saboda matuƙar fushi ya dubi Baddadul-arus, Gimbiya Uzaima, Sarki Huraisu, Hadimi Shaibat da aljani zamzaru ya ce "Ya ku abokanan tafiyata ku yi sani cewa wannan takun sawayen da kuke gani ba na wani ba ne face na abokan gabar mu, Kuma bisa nazari da na yi na gano cewa suna kusa da mallakar TAKOBIN SIHIRI, Kun ga kenan a halin yanzu shiga fadar Sarkin bokaye bai taso ba zai fi kyau mu yada zango a nan mu jira fitowar su domin a yi GUMURZUN SHEKARA DUBU da ba shi da mara ba da ɓallewar taskar ANNOBA DARI, Ana mai tabbatar maku da cewa zan shiga maku burinku na mallakar TAKOBIN SIHIRI, Ni kuma zan shanye jinin jarumi Humairu domin cika burina na zamowa duniya GOBARAR ANNOBA kuma Gagarabadau makashin maza. Ko da jin wannan batu sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. *** A cikin fadar Sarkin bokaye boka oAyyamul-layal kuwa al'amarin su jarumi kuwa sun cigaba suna haɗu da miyagun aljanu da musibu mara adadi, Duk lokacin da aka faɗa wata musiba Humairu, Sharilat, kuhairu da Mashlira ne ke fitar da su sarki Himras, yazamana duk ƙarfin damtse da girman jiki irin na aljani zamzaru ya tashi a banza, Bisa nasarar Ubangiji Humairu ya samu nasarar ɗauko Takobin Sihiri a cikin wata tsafaffiyar kwalba ya damka a hannun sarki Himras, amma kowannen su takobinshi da tufafinshi ya rine da jini. Lokacin da aka aka ɗunguma aka fito daga fadar sai kawai aka yi turus ba wani abu suka gani ba face su sarki Baddadul-arus a tsaye, Nan fa aka fara kallon-kallon tsakanin su cikin matuƙar ƙiyayya da baƙar gaba, Sarki Himras ya katse shirun da wanzu ta hanyar bushewa da dariyar mugunta ya dubi sarki Baddadul-arus ya ce "Ya kai babban abokin gaba na har abada yanzu ga shi ina ɗauke da takobin sihiri wacce kowannen mu ya yi imanin cewa da ita ne kawai za mu iya hallaka junan mu, Shawarar da zan baka ita ce ka rubuta wasiyyar ka zuwa al'ummar ƙasar ka kafin na zare ruhinka daga gangar jikinka ka yi mutuwar wulakanci". Ko da jin wannan batu daga bakin Himras sai Sarki Baddadul-arus ya bushe da dariyar ƙarfin hali daga bisani ya murtuke fuska ya daka mashi tsawa ya ce "Kai tsohon maci amana ka yi sani cewa koda cewar kana ɗauke da takobin sihiri ba zai sa ka yi nasara a kaina ba domin ai masu iya magana na cewa kaɗe mage ba yankawa ba ne, kuma mugu shi ne makwantar mugu, Ka sani cewa kamar yadda ka ci amanar ɗan uwanka kuhairu ka nemi ka raba shi da rayuwar shi to yanzu kai ne za ka rabu da ta ka rayuwar domin har kullum ƙaikayi shi ne ke koma kan masheƙiya, kuma idan za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere yadda idan ka faɗa za ka iya fitowa". Ko da jin wannan batu sai zuciyar yarima Muzaifar ta buga da ƙarfi ya ce a ranshi dama Kuhairu uwa ɗaya uba ɗaya suke da mahaifina kenan Sharilat 'yar uwata ta jini ashe ba a banza kuhairu ya ke kama da ni ba kuma salon yaƙin mu yazo ɗaya ni da Sharilat a lokacin da muka fafata yaƙi da ita a kasuwar birnin Darul-kushur? Amsar tambayoyin da yarima ya kasa bawa kanshi kenan ya ji gaba ɗaya Kunyar Sharilat da kuhairu ta kama shi, Ya ƙura wa gimbiya Uzaima idanu yana yi mata kallo mai tattare da tsantsar gaba da mugun tanadi. Kafin sarki Baddadul-arus ya sake furta wani abu sarki Himras ya ɗaga takobin sihiri izuwa sama ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa gare shi, Ko da ganin hakan sai Baddadul-arus ya zare takobinshi ya ruga gare shi domin tarar juna, Ko da ganin sai yarima Muzaifar da gimbiya Uzaima suka zare makaman su suka ruga izuwa kan junan su suna ihu da kururuwa mai firgita ZARATAN MAYAKA a FILIN DAGA, Aljani Narguz da Aljani Zamzaru suka ruga kan juna domin KARON BATTA batare da sun zare makami ba Boka Sharubu kuwa sai ya zare mashinsa ya ruga kan jarumi Humairu Lokacin da ɓangarorin huɗu suka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni da tashin hankali, Ko da ganin an fara fafatawar sai jarumi Sharilat, Mashlira, Gimbiya Hulaifa, boka Hushaib da sarkin yaƙi suka koma gefe guda gami da zuba idanu suna kallon fafatawar da ake yi. Ƙarar karafniyar ƙarafa gami da ihun mazaje ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, duk sa'adda makaman jaruman takwas suka haɗu da juna sai ka ga sun haddasa wata tsawa da walƙiya da ka iya kurumtar da kunnuwa, Kaico! Haƙiƙa gumurzu Mazaje daban ya ke da na ƙananun jarumai, kuma Idan BABBAR GIWA ta fito Filin fama babu wanda ya ke iya tunkarar ta ayi KARON BATTA face JARUMAN DUNIYA da suka saba yin ɗauki ba daɗi a birnin MAZAN JIYA. A ɓangaren sarki Baddadul-arus da sarki Himras kuwa sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta duk sa'adda Himras ya kaiwa Baddadul-arus hari da takobin sihiri idan ya zillewa harin duk abin da takobin ta sauka a kai sai ka ga ya narke ya zama ruwa, idan a kan bishiya ta sauka kuwa sai kaga ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus. A ɓangaren yarima Muzaifar da gimbiya Uzaima kuwa sun wanzu suna ɗauki ba daɗi suna kaiwa juna hare-hare cikin gwaninta da salon yaƙi irin na JARUMAN DUNIYA, Kafin shuɗewar daƙiƙa ashirin sun yi junan su raunuka guda biyu kowanne na ZUBAR DA JINI, Rauni na farko a damtsen cinyarsu ta hagu suka yi wa juna, Na biyun kuma a kafaɗa. Sa'adda Jaruman suka ga yadda jini ke zuba a jikkunansu sai suka fusata ainun suka ZAGE DAMTSE tare da kaiwa juna sabbin hare-hare. A ɓangaren MAZAN JIYA kuwa Jarumi Humairu da boka Sharubu sun wanzu suna shayar da junansu azabar KAIFIN TAKOBIN su babu sassauci, Komai hassadar mutum idan ya ga yadda suke yaƙin dole ne ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika ZARATAN JARUMAI masu ƙarfin damtse. Sai da aka shafe tsawon Sa'a biyu ana wannan ƙazamin artabu babu sassauci Kuma babu alamun nasara ga kowa ne ɓangare, Sai da ta kai jaruman shida na yanke jiki suna faɗuwa ƙasa magashiyan amma saboda juriya da bajinta irin ta MAZAN JIYA da suka saba gumurzu a BIRNIN SADAUKAI sai su miƙe tsaye zumbur su ci gaba da mayar da martani. Wohoho! haƙiƙa a wannan rana an fafata ƙazamin artabu da ba a taɓa yin kamar shi ba, Inda yarima Muzaifar da gimbiya Uzaima suka yi RAGAS ma'ana sun galabaita ainun numfashi su yana fita sama-sama. Sarki Baddadul-arus da Himras kuwa MUTUWAR KASKO suka yi inda suka karya takobin sihiri gida biyu kowanne su ya sokawa abokin gabar shi a kan ƙahon zuciya suka yi mutuwar wulakanci, Kaico! ka ji aikin kafirai duk abin da aka aikata an tafi an bar shi a duniyar, Yanzu duk cin amanar da sarki Himras ya yi wa ɗan uwanshi tsoho kuhairu saboda ƙwaɗayin mulki yanzu ga shi ya tafi ya bar duniyar a banza, Allah ka raba mu da mutuwar asara, A ɓangaren Aljani Zamzaru da Narguz kuwa su ma mutuwar kasko su ka yi ta hanyar murɗewa junan su kawuna a lokaci guda. Jarumi Humairu kuwa daƙyar da siɗin goshi ya samu nasarar hallaka boka Sharubu ta hanyar sare mashi wuya da takobinshi amma shi ma kan shi yasha ɓakar wahala, Bayan ya hallaka shi wani baƙin aljani ya bayyana mai munin halitta ashe shi ne wanda ke sarrafa ke sarrafa gangar jikin boka Sharubu, Domin Allah ya yi alƙawarin cewa babu wata halitta walau MUTUM DA ALJAN da zata wanzu a doron ƙasa face ta zamo gawa, don haka boka Sharubu ya mutu ba shi ne ya dawo duniya ba kawai lamari ne na ma'abota shirka da sihiri. A wannan karon sai da Humairu ya sha baƙar azaba tamkar zai rasa rayuwar shi sannan ya hallaka aljanin ta hanyar tofa mashi Ayatul-kursiyyu ya ƙone ƙurmus!, Haƙiƙa a wannan rana su tsoho kuhairu sun ga iko da buwayar Ubangijin halitta kuma zukatansu sun ƙara samun nutsuwa da Ubangiji. Ko da samun wannan gagarumar nasara sai Humairu ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme, Cikin kaɗuwa Sarkin yaƙi Nuhairu ya ruga zuwa inda yake ya shiga ba shi taimakon gaggawa, Gimbiya Hulaifa ta nufi inda gimbiya Uzaima ta ke domin bata taimako, Boka Hushaib kuwa ya ruga zuwa ga yarima Muzaifar ya shiga ba shi kulawa gimbiya Mashlira bintu Shabbar na taimaka ma shi. Sai da aka kwana uku a wannan waje kowa ya yi jinyar raunukan jikin shi ya warke sumul, A ranar kwana na huɗu ne da hantsi kowa na zaune sai Humairu ya dubi su boka ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku abokanan tafiyata yanzu ga shi mun rasa takobin sihiri wacce da ita ne za a yi amfani a saro sauwar bishiyar Shajarul-kair domin warkar da al'ummar birninku daga Annobar cutukan da ke addabar su shin yanzu mene ne abin yi?. Ko da jin wannan tambaya daga bakin Humairu hankalin gimbiya Hulaifa,boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu ya dugunzuma ainun aka rasa wanda zai ce ƙala a cikin su, Sai daga bisani ne gimbiya Hulaifa ta dubi Humairu fuskantarta cike alamun damuwa ta ce "Ya kai Jarumin jarumai ka yi sani cewa a halin yanzu ba abin da zamu iya cewa dukkanin rayuwar al'ummar ƙasarmu ta dogara ne akan ka sai abin da ka ce, Amma bisa nazari da na yi a tafiyar mu na ga iko da buwayar Ubangijin ka ina ji a raina cewar zai iya warkar al'ummata batare da an yi amfani da saiwar Shajarul-kair ba. Ko da jin wannan batu daga bakin Hulaifa sai Humairu ya ce "Haƙiƙa zancen ki dutse babu wani abu da ya gagari Ubangijina, Abin da nake so da ku shi ne ku yi mani alƙawarin za ku bayar da gaskiya da Ubangijina idan har ya warkar da jama'ar ki. Ko da boka Hushaib, gimbiya Hulaifa da sarkin yaƙi Nuhairu suka ji wannan batu daga bakin Humairu sai suka ce mun amince da hakan ya JARUMIN JARUMAI kuma SARKIN SADAUKAI. A can inda tsoho da 'yarshi Sharilat ke zaune kuwa suna fira cikin nishaɗi, sai suka hango yarima Muzaifar ya tawo gare su yana zuwa ya zauna a daf da kuhairu ya dube shi cikin ladabi yana satar kallon Sharilat ya ce "Ya abbana ka yi sani cewa a halin yanzu na gano cewa mahaifina ne ya ci amanar ka saboda ƙwaɗayin mulki da son abin duniya, a halin yanzu bani da wasu 'yan uwa na jini da suka rage mani face ku, ina roƙon ku da ku yafewa mahaifina kada laifin shi ya shafe ni ku riƙe ni da wani abu, kuma kada Sharilat ta yi watsi da soyayyata". Sa'adda yarima Muzaifar ya zo nan azancen shi sai kawai ya fashe da kuka hawaye na zuba daga idanuwanshi, Al'amarin da ya sanya Sharilat da kuhairu suka ji sun kamu da matuƙar tausayin shi har ƙwalla ta cika masu idanu, Kawai sai kuhairu ya miƙe tsaye ya tashi kafaɗunshi ya dube shi fuskarshi cike da annuri ya ce "Ya kai Muzaifar ka sani cewa ba ka yi mana komai ina mai tabbatar maka da cewa ba za mu rike ka da komai ba, zan riƙe ka tamkar 'yata Sharilat, Kuma zan aura maka ita domin bani da wani buri a duniya da ya huce naga zuri'armu a tare da juna cikin matuƙar farin ciki, Sai dai inda gizo ke saƙar shi ne a halin yanzu mu musulmi ne saɓanin kai. Ko da jin wannan batu murmushin yaƙe ya suɓucewa Muzaifar ya ce "Ya abbana ai tuni na bayar da gaskiya da Ubangijin halitta kawai dai tsoron fushin mahaifina ne ya sa ban bayyana ba". Ko da jin wannan batu sai kuhairu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ya rungume yarima a ƙirjinshi, Sai daga bisani ne ya janye jikinshi ya tafi ya ba su waje suka shiga firar soyayya tsakanin sa da Sharilat. Kamar yadda Humairu ya faɗa haka al'amarin yakasance wato sun gabatar da sallar azahar sai ya kira wani hadimin aljanin shi mai kyawun sura mai suna Hadimul-khair ya ɗauke su baki ɗaya ya nufi birnin Rum yayin da aka isa ne jarumi Humairu ya karanta ayatul-kursiyyu a ruwan ƙoramar garin duk wanda suka kamu da cututtuka suka sha ruwan har da sarki Usulu-haibar suka warke sumul!. Nan take suka cika alkawari suka karɓi kalmar shahada sannan aka ɗaura auren gimbiya Hulaifa da sarkin yaƙi Nuhairu, Sannan aka sake ɗunguma aka nufi birnin Madinatul-husuf aka ɗaura auren gimbiya Uzaima da sarki Huraisu ma'abocin baiwa ashe tun sa'adda da ya fafata yaƙi tare da ita da mahaifinta ya kamu da soyayyar ta amma bai bayyana ba, bayan sun ƙarbi addinin Musulunci sai sarki Huraisu ya zamo sabon sarkin ƙasar Madinatul-husuf aka ƙarya dukkan gumaka, Shi kuwa hadimi Shaibat sai ya koma izuwa birnin Jarul-iman a matsayin halifan sarki Huraisu domin tabbatar da addinin Musulunci. Sannan aka sake ɗunguma aka nufi Kasar Darul-kushur aka ɗaura auren Jaruma Sharilat da yarima Muzaifar, Jarumi Humairu da Gimbiya Mashlira yar shugaban arnar daji marigayi Shabbar, Labari kuma ya watsu a nahiyar cewa kuhairu ya na raye kuma dawo tare da 'yar shi Sharilat kuma sarki Himras ya mutu, Nan fa sarakunan suka dinga zuwa suna yin mubaya'a a gare shi tare da nuna farin cikinsu, A wannan rana an yi gagarumin shagalin bikin da ba a taɓa yin kamar shi a gaba ɗaya nahiyar. Bayan an kammala ne sai rigima ta ɓarke akan wane ne zai gaji karagar mulki, inda wasu ke ganin cewa yarima Muzaifar ne ya cancanta yazama sarki domin shine zai gaji mahaifin shi, wasu kuwa suka ce ai Humairu ne ya kamata domin kuwa shine ya zamo silar samuwar duk wani farin ciki tsakanin su, Wasu kuwa suka ce kuhairu ne ya fi kowa dacewa domin ai dama can baya sarautar ta shi ce bata marigayi sarki Himras ba, Yarima Muzaifar da jarumi Humairu kuwa sai suka dage akan cewa ba za su karɓi sarautar ba sun kyale wa kuhairu. Haka kuwa aka yi aka naɗa tsoho kuhairu a matsayin sabon sarkin birnin Darul-kushur, Farin ciki a wajen al'ummar birnin kuwa ba a cewa komai tamakar su zuba ruwa a ƙasa su sha, wasu har da zubar da hawaye domin sun tuna irin ƙuncin da suka shiga a lokacin mulkin sarki Himras bayan jin labarin cewa an hallaka kuhairu, Yarima Muzaifar kuwa aka naɗa shi Magajin gari, jarumi Humairu kuwa ya zamo sarkin yaƙin birnin domin tabbatar da addinin Musulunci. Tun daga wannan rana a kawo KARSHEN ZALUNCI zaman Lafiya da farin ciki ya ci gaba da wanzu a ƙasar Darul-kushur da nahiyar baki ɗaya musulunci ya ci gaba da bunkasa, aka rushe dukkan gumaka da shaiɗanu, arzikin birnin ya dunga bunƙasa wanda ba'a taɓa samun kamar shi tun kafuwar birnin saboda HASKEN MUSULMI. Alhamdulillah Ƙarshe Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe. MANSUR USMAN SUFI 08137237071