RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* KADUNA Da yammacin ranar Alhamis ne, Allah ya yalwata garin na Kaduna da ruwan sama. Hakan ya jawo boyewar jama’a da dama domin fakewa ruwan. Ruwane ake tsugawa mai Karfi kamar zai fasa saman kwanukan jama’a. Cikin hukuncin na Rabbi, wanda ya saukar da ruwan ba tare da wayonmu ko dabararmu ba, ya tsaida abin shi cak! Cikin lokaci Kalilan. Hakan ya sa jama’ar da ke Boye suka fara firfitowa kowa na KoKarin kama gabansa, domin gab ake da kiran Isha’i. A irin wannan yanayin da za ka ci nasarar leKa dakunan jama’a za ka tsinci kowannen su a Kundudune cikin rigar sanyi, ko kuma bargo. Marasa Karfi kuwa, irin almajirai da sauran su, suna Kudundune a lungu ko kuma cikin zannuwa. Alhaji Lukman ne zaune a mazaunin direba, yana tafiya a natse bisa shimfidaddiyar kwalta, fuskarsa babu alamun gajiya ko kuma Kosawa da irin cinkoson motocin da ya ci karo da su kafin, ya sami daman hawa saman gada. Hakan ya dasa masa tunani kala-kala a cikin Zuciyarsa. A wannan karon zuciyarsa ta gama karaya, har ya soma jin ya gaji da yadda hanyar ba ta motsawa. Babu abinda yake hange a yanzu kamar gidansa da ke cikin rukunin gidajen na Unguwar Rimi. Yana son watsa ruwa, haka ba . ya son isha’i ta riske su a hanyar. Duban agogon cikin motarsa ya yi wanda , yake nuna masa Karfe bakwai da rabi. A _ zuciyarsa ya ce, ya makaro. Cunkoson ababen hawan suna ci gaba da yawaita ne daga saman gadan, hakan ya sa ya dan waiwayo ya dubr * dansa Sultan da ke kallon gefen titi hankalinsa kwance.. Ta madubi ya dubi matarsa Hajiya * Salma, ita ma dai idanunta suna kafe a cikin jarida. Ya sake mayar da hankalinsa a kan kwaltar yana duban yadda kowa ke sauri domin isa ga muhallinsa. Ganin yawan cunkoson ya fi yawa ne daga saman gadar, yasa ya sauya ra’ayinsa, wajen sauka Kasa ya bi ta Kasan gada. Wanda yake hango tarin sauki fiye da tsayuwarsa a inda bai san lokacin isarsa gida ba. Hajiya Salma da ke hakimce a baya, ta dago daga karatun Jaridar da take yi, idanunta manne da farin gilashi, tana duban yadda Maigidanta ya sauya hanya, hakan ke tabbatar masu dole sai sun je Mando kafin su yi kwana. Babban dansu mai shekaru goma sha biyar a� duniya yana ci gaba da watsa idanunsa a bisa titin kamar mai son tuna wani abu. A cikin zuciyarsa kuwa ji yake kamar a dauwama a cikin irin wannan yanayin, kasancewarsa mutum mai tsananin son damina. Yanayin da ke sa shi farin ciki fiye da kowanne irin yanayi. Tun bayan fitowarsu daga Jaji, gidan. mahaifiyar Abbansa, suka shiga mota, babu wanda ya furta ko da kalma daya. Kowa da irin . sake-saKen da yake yi, kasancewar ita zuctya ba a raba ta da yawan tunane-tunane, duk da shirme yafi yawa a cikin dukkan tunanin. Haka tsarin su yake, ba su damu da dole sai sun yi surutu ba, idan kuwa za su yi sai ya kasance mai ma’ana ne, kasancewarsu ‘yan boko masu ji da kansu. Ko cikin gidan su ka shiga za ka sami gidan su shiru kamar babu kowa a cikinsa. Sau tari idan sun shiga za ka sami gidan shiru kamar babu kowa, shi ya sa da zarar masu surutu sun kawo ziyara gidan, suke tattara surutunsu, su ajiye tsakar gida. Suna fitowa suke nada gammo su dauki abinsu. Domin ko ka yi babu mai ba ka cikakkiyar amsa. Sau tari masu surutun cikin dangi suna fitowa daga gidan suke fara tsinewa bakin hali da son korar bako da Karfi da yaji irin na gidan Alhaji Lukman. Sultan ya dan dubi mahaifinsa, kamar zai basar, sai kuma ya ce, “Abba idan ka sami wuri ka tsaya kusa da tashar motocin can, zan sha kayan marmari sannan ina jin fitsari, zan je in yi,� Yana maganar yana yamutsa fuska kamar wanda akai wa dole sai ya yi. Hajiya Salma ta dago tana duban danta, “Sultan ka bari mu Karasa gida mana. Ba ka san ana daukar ciwuka wajen tsuguno a irin nan wajen ba ne?� ta yi maganar tana sake zura idanunta a kansa cikin kulawa. Idanunsa ya sake watsawa a bisa titin, yana nazarin har yaushe cunkoso zai ragu su isa gidan? Girgiza kansa kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba, ya dawo da kallonsa ga mahaifinsa da ya sami wuri ya tsaida motar. Gorar ruwa ya dauka ya fice daga motar. Idanu yake rarrabawa yana neman inda ya kamata ya yi fitsarin. Wurin ya jagalgale da yawa, don haka ya dinga jin Kyama ya kasa ajiye Kafafunsa yadda ya kamata. Lalacewar wurin ya darsa masa danasanin fitowarsa, amma kuma yadda yake jin fitsarin ba zai iya haKura ya koma ba. Bayan wata Katuwar mota ya samu ya zaga, sannan ya yi abinda ya kawo shi, ya mike hannunsa riKe da ragowar gorar ruwan yana son fita ya wanke Kafafunsa. Numfarfashin da yake ji sama-sama kamar akwai wani abu a kusa da shi, ya sa ya dan dakata da tafiyar da yake yi, tare da kasa kunnensa sosai Yadda yake jin numfarfashin yana Karuwa, ya sa Kafafunsa suka kama rawa-. Tsananin tsoro ya shige shi. Don haka ya yi tsalle gefe guda yana zare idanu. Ji ya yi kamar an sawa Kafafunsa dabaibayi. Ji ya yi kamar Kafafun sun gaza daukarsa. A hankali yake jiyo sautinta, “A taimake ni! Ruwa! Ruwa! Zan mutu.� Cikin Karfin hali da son ganin mene ne ya daga kafarsa daya ya sake daga dayar ya nufi wurin da sautin ke ratsa kunnuwansa. Gumi ke. � tsattsafo masa kamar ba shi ba ne ke jin sanyi. Duk yadda ya so ya yi Karfin halin tunkarar shiga wurin da yake jin sautin abin ya faskara. Da baya da baya ya koma yana sake waige kamar mai neman wani abu. Wani ya hango daga shi sai singlet da buta a hannu, rudanin da ya shiga ya hana shi mamakin yadda ake kwada sanyi, amma kuma babu riga a jikinsa. Da sauri ya bi bayansa, “Malam! Ina jin Kara a kusa da babbar motar can, don Allah zo ka duba ka gani. : . Mutumin ya zabga masa harara, “Kai! Me kake yi a nan? Idan ba ka wuce ba, za ka ci mutan gidanku.� Ya sa kai da nufin tafiya Sultan ya sha gabansa, “Don Allah ka zo ka gani.� Tsayawa ya yi yana Kare wa Sultan kallo cikin duhun, kafin ya ce, “Mutum ce a wurin sai kuma me kake son ji?� Mutumin da ya yi shayeshayensa ya baiwa Sultan amsa cikin Kufula a kan bata masa lokaci da yake neman yi. Sultan ya zazzaro idanu alamun firgici. “Mutum? To me yake yi a wannan wurin? Ku ce ya tashi wani abu zai same shi.� Sultan ya jero wadannan kalaman cikin kidimewa. Da alamun Sultan ya fara kai mutumin bango idan aka yi la’akari da kallon banzan da yake aika masa. | Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce, “Kai yaron nan akwai shegen naci, kamar irin kafiran farkon nan. Eh mutum! Mutum din ma mai numfashi. Ba namiji bane mace ce, Saudatu ce, take yaudarar jama’a da Hijabi sai ga cikin shege. Ko da yake arniya ce, ta shigo mana musulunci da masifa. A nan Kasan motar take kwana. Kila ma nakuda take yi, don yau kwananta biyu kenan ban ganta ba. Da a can take kwana aka koro ta.� Ya nuna wani wuri da hannu, wanda babu komai a gun Sal tayoyin babbar mota. Tunda yake magana Sultan ya kafe shi da idanu ta hasken motocin da ke wucewa, suna hasko su. Sai dai kafin ya ankare ya sake samo tambayar da zai yi masa har mutumin ya wuce abinsa, yana auna wa Sultan zagi. Numfarfashin da ya sake jin ya Ziyarci kunnuwansa, ya kanainaye zuciyarsa da wani irin tausayl. Damuwa ce manne a zuciyarsa. Wannan karon da rashin tsoro ya doshi Karkashin motar, wanda ga dukkan alamu motar ta jima da tashi aiki. Kai tsaye ya rankwafa-ya ~ shige. Ruwan saman da aka yi ya sami makwanci a KarKashin motar, “Sannu Anti. Anti me kike son in kawo maki? Don Allah Anti kiyi min magana kin ji?� Wasu hawaye suka sake tsinke masa, wasu suna korar wasu. Cikin hukuncin Allah aka hasko hasken fitila, wanda ya ba Sultan daman kallon fuskarta. Hawaye ne kwance a bisa fuskar. Idanunta a rufe. Bude idanun ta yi , ta zubawa Sultan, tana kallon yadda hawaye suka bata masa gaban riga. idanun ta mayar ta rufe. Ganin yadda take kuka yasa ya sake Kankameta yana kuka sosal. Tunda yake bai taba ganin babba yana kuka ba, sai a kan Saudat. “Anti ki yi hakuri ki daina kuka. Ki yi addu’a ne Anti don Allah.� Cikin sautin muryar marasa lafiya ya ji muryarta tana magana, “Na gode, na gode. Ku taimakeni ku raba ni da nan za a kasheni ne.Ina son ko ban rayu ba, abinda ke cikin cikina ya rayu, domin dasawa wanda ya kawo ni nan, bakin ciki da tabon da ba zai taba gogewa a tarihin zuri’arsu ba. In gaya maka wani abu, da kuma littafi ka tafi da shi ka miKawa wani babba, wanda zai iya taimaka min wajen yada labarin nan? Ka yi alKawarin ko bayan raina za ka taimake ni ka tona asirin wanda ya sa jefa rayuwata a cikin masifa? Kayi alKawarin za ka Kwatowa dan da zan Haifa ‘yancin sa?� Kwakwalwar Sultan ta yi karama da sauraren wannan kalaman na Saudat. Kukansa ya Karu ya gyada kansa ba tare da dogon nazari ba, alamun ya amince. Yana son yin magana a lokacin da ta mika hannu take nuna masa wani Boyayyen buhu a sakale, wani mutum ya fizgo shi da Karfin tsiya, kan Saudat din ya koma gefe. A gaban Abbansa suka tsaya a lokacin da yake jin muryarsa yana cewa, “Kada ka ji masa ciwo mana malam!�� Sultan ya fizge da Karfin tsiya daga irin rikon da mutumin ya yi masa ya zube a gaban mahaifinsa a bisa guiwowinsa ba tare da ya damu da cabalbalin wurin ba. “Abba ka taimake ni kada ta mutu. Abba ku bar ni in je inji abinda za ta gaya min. Abba za ta mutu idan muka tafi.� Abban ya kai kallo ga Hajiya Salma, wanda dukkansu mamakin Sultan din ne ya rufe su. Kafin su yi magana mutumin da ya finciko shi daga gun Saudat ya fara magana, “Alhaji ka kama yaron nan naka ku bar wurin nan. Yarinyar nan cikin shege ta yi, saboda rashin kamun kai ko da kuwa daki daya kuke kwana. Zai kasance akwai jahilci a cikin jama’a da suke tunanin H.1.V zai shafi makusancinka. Na gode.� Kallo ya bi shi da shi har ya isa ga matarsa ya ja suka wuce. Lokaci bayan lokaci yana jin dirar kukan yaronsa har tsakiyar kansa. Amma kuma babu wanda ya iya Kara cewa komai. A haka suka Karasa gidan, ‘yan Kannensa su biyu, Hafsat da Haidar suka taso da gudu daga hannun Mairo mai aikinsu, kai tsaye gurin Sultan suka nufa. Ya shafi kansu kawai ya wuce ciki. Duk: suka bi jikinsa da kallo, sannan suka dubi Abbansu suka ce, “Abba me ya sami Yaya Sultan jikinsa ya lalace? Ya fadi a kwata ne?� A nan ma babu wanda ya ce masu komai. Shi kuwa yana shiga ya fada bandaki ya yi wanka da alwala ya fito ya shimfida darduma ya gabatar da Sallarsa, a nan kan daddumar ya yi barci, tare da sa hannunsa a matsayin matashin kai. “Umma! Umma!! Abba!!! Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Me ta yi maku? A’a don Allah ku bar min Antina kada ku kashe ta.� A guje suka shigo dakin suna girgiza shi. Cikin tashin hankali da gigicewa ya tashi da Karfinsa ya ture su ya yi hanyar waje da gudun gaske. Cikin sa’a mahaifin ya kamo shi ya rungume shi a Kirjinsa yana shafar bayansa, “Ka natsu Sultan ni ne mahaifinka. Ka natsu ka ji? Mene ne?� Cikin hawaye masu yawa da ke sauka daga kwarmin idanunsa, “Abb� Abba..� Ajiyar zuciya ya saki da Karfi, kamar wenda zai hadiyi zuciya. “Abba idan bamu je mun taimaki Anti Saudat ba, nima zan tafi can da nisa inda ba zaku ganni ba.� Cikin jin zafin kalaman yaron kamar ya watsa mata ruwan zafi, ta Karaso har gaban Alhaji Lukman ta finciko yaron ta dauke shi da mari har sau biyu, kafin ta kai hannu ta buge masa baki tana huci. “Dan ubanka zo ka kwashe kayanka ka bar min gida shashashan yaro. Har kayi girman da Za ka fara� sa min ciwon kai Sultan? Duk cikin mutane ka rasa wacce za ka ce a taimaketa sai karuwa? Mazinaciya? Tubabbiya? Wacce iyayenta suka guje ta? Bare mu haduwar Kaddarar fitsari? Uwa uba mai dauke da cutar da kaf zuri’arku sai tabi ta kashe daya bayan daya. Na ji a jikina matsala ce ke shirin tunkarar mu shi ya sa na hanaka zuwa fitsarin nan, kayi min kunnen shegu.� Ran Alhaji Lukman ya kai matuKa a baci, ya dinga dubanta kamar bai taba ganinta ba. “Akan matsalar nan zaki dukar min yaro? Ke kin fi Karfin Allah ya jarabceki ne? Ko kuwa har kin gama tsara abubuwan da za su faru da ke a gidan duniya ne? Har kin gama tsara komawarki gare shi? Kina da yara mata kike tsinewa na wasu? Daman kina tunanin zaki dauwama a duniyar ne? zamu mutu, ta hanyar da Allah ya tsara mana a cikin littafinsa. Sultan yana dafe da Kuncinsa ya Karaso kusa da Abbansa ya ce, “Abba, Anti.� Sunkuyawa ya yi ya rungume yaron, “Ka yi hakuri Sultan, zuwa gobe sai mu Je mu dauko ta. Ka ga yanzu Karfe goman dare.� Sultan ya girgiza kai, “A’a Abba idan ba mu je yau ba, za ta mutu ni kuma bana son ta mutu.� Murmushi ya yi “Yadda kace haka za a yi Sultan. Amma ina son ka sa a ranka, kowani , rai sai ya dandani dacin mutuwar nan. Ba mu Zo domin mu zauna a duniyar ba. Ta so mu je.� Hajiya Salma, da taji gabanta ya fadi, ta fice daga dakin ranta a matuKar bace. Tun kafin ya fara tuki ya kira ‘yan sanda ya yi masu bayani tare da kwatanta masu wurin yana son su riga shi zuwa. Yana kashe wayar ya kira Asibiti, ya ce yana buKatar motarsu tare da kwatanta masu wurin. Sultan dai sai kallon fitilun gefen titunan yake yi ransa a jagule. ba kamar dazu ba, da yake jin nishadi. Gani yake kamar mahaifinsa baya sauri. Duban yaron ya yi bayan ya murza sitiyarin ya sha kwana, “Sultan, ka yi min murmushi mana. Ka ganka kuwa? Gabadaya fushi baya yi maka kyau, sai ka koma sak! Hajiya Gwaggo.� Kallon mahaifinsa ya yi idanunsa cike da hawaye, “Abba sai andauko anti.� Lallai tunda yau ya kasa samun fara’ar yaronsa, ya san abin da gaske ne. Shi kansa yana jin kwatankwacin abinda yaronsa ke ji. Tunda suka yi fakin Sultan ke bin motar ‘yan sandan zuwa motar asibitin da kallo. Gaba daya ya kasa sauka sai da mahaifinsa ya yi masa magana. Shi kansa Alhajin yadda ya kula da kamar hankalin ‘yan sandan a tashe ya isa ya gamsar da shi akwai matsala. A tare suka iso suna mai sake kafe su da idanu. Daya daga cikin su ya Karaso hannunsa rike da wayar sadarwa, “Alhaji muna isowa muka hadu da tashin hankali. Baiwar Allahn da ka kwatanta mana ita ga ta can kwance cikin jini, wasu marasa imani sun sassare ta har Allah ya yi mata cikawa. Mun iso dai-dai sun gama ta’asar. Mun yi iya bakin Kokarinmu mu kama su, amma hakan ya gagara-. Tarasu.� Sultan da jikinsa yake kyarma, ya durKushe Kasa yana wani irin kuka, “Ant Saudat!! Me za ki gaya min?� Iya abinda bakinsa da ke karkarwa ya iya furtawa kenan. Sauran maganar ta maKale a makoshinsa. Kuka ya tokare masa ya hana su fitowa, Alhaji Lukman ya lumshe idanunsa, “Ya Salam!� Hawaye suka cika masa idanu, yasa hannu ya sharce. Jikinsa ya yi matuKar sanyi, “Allah ya jikanki.� . Sultan ya mike cikin kuka ya isa kan gawar da ke shimfide da Katon cikinta a gaba. Duban ‘yan sandan ya yi yana ganin su dishidishi. Har sun kammala daukar hotunanta da kuma rubuce-rubuce. Idanu ya zuba mata har zuwa yatsunta da ke ‘dauke da wani zobe mai kyau. Kurawa hannun ido ya yi. Ya sa nasa hannun ya rike ta, yana jin kamar numfashin zai dauke. A hankali ya :zare zoben da ke hannunta ya mayar cikin aljihunisa. ‘Yan sandan sun so su raba shi da gawar, Abban ya dakatar da su, “Ku bar shi ya rage radadin da ke damunsa, tun dazu yake mana magiyar mu je mu dauko ta ashe mutuwa za ta yi .� Kwalla ta ziruro masa daga idanunsa, ya girgiza kai kawai. A dai-dai lokacin kiran Hajiya Salma ta shigo wayarsa. Ya ji duk ya tsaneta. Ya tabbata duk namijin da ya ce zai biye wa shawarar wata macen sai ta kaishi ta baro. Dauka ya yi ya sa a kunne yana magana cikin rawar murya, “Baiwar Allan da take miko hannu take bukatar taimako kika hana, saboda dalilin kin tsani zina, kin tsani mai dauke da cuta, kin tsani wacce ta tuba ta koma addininki. Wadanda suka fi ki tsanar wadannan abubuwan sun kashe ta sun kawar da ita daga duniyar gaba daya.� Sauke Shin me zai faru? Kudai kuci gaba da bibiyar mu 6/3/22, 17:34 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 2 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* JIYA MUN TSAYA Yan sandan sun so su raba shi da gawar, Abban ya dakatar da su, “Ku bar shi ya rage radadin da ke damunsa, tun dazu yake mana magiyar mu je mu dauko ta ashe mutuwa za ta yi .� Kwalla ta ziruro masa daga idanunsa, ya girgiza kai kawai. A dai-dai lokacin kiran Hajiya Salma ta shigo wayarsa. Ya ji duk ya tsaneta. Ya tabbata duk namijin da ya ce zai biye wa shawarar wata macen sai ta kaishi ta baro. Dauka ya yi ya sa a kunne yana magana cikin rawar murya, “Baiwar Allan da take miko hannu take bukatar taimako kika hana, saboda dalilin kin tsani zina, kin tsani mai dauke da cuta, kin tsani wacce ta tuba ta koma addininki. Wadanda suka fi ki tsanar wadannan abubuwan sun kashe ta sun kawar da ita daga duniyar gaba daya.� Sauke ZAMU TASHI wayar ya yi, tare da kasha ta, yana jin danasanin biye wa matarsa. Kallon likitan ya yi yana_ sauraren maganarsa. “Yallabai ina tunanin idan aka yi gaggawa zamu iya ceto abinda ke cikinta, ta hanyar yi mata aikin gaggawa.� Gabadaya aka yi amanna da bayanan likitan. Sultan yana rike da ita yana sharar hawaye, rigarsa duk jini gani yake kamar za ta tashi. Abbansa ya zame hannayensa bisa gawar saudat. Yana kallo aka sata a mota. “Ruwa! Ruwa!!� Sautin muryarta, ya dake shi. Kufe idanunsa ya yi domin ya baiwa hawayensa daman sauka. “Ku taimakeni ku raba ni da nan, za a kashe ni. Ku taimake ni ina son abinda ke cikina.� Kalamanta suna yi masa kuuwa da Karfi. Shiru ya yi yana duban su Abbansa. Ganin ba ya kallonsa ya shige Karkashin motar nan ya jawo buhun yana bincike a ciki, Ya ci karo da littafi Kato, dauke da hotuna wanda bai tsaya duba komai ba, ya mayar cikin nigarsa. Muryar Abba ya ji yana Kwala masa kira, ya yi sauri ya fito. Ya kama hanyar shiga motar hawaye suka sake tsinke masa. Yana goge wasu, wasu kuma suna sake kwaranya. Sun kama hanya, muryar Saudat ta ci gaba da yi masa kuuwa, “Zan gaya maka wani abu.� Sultan yasa hannu ya toshe kunnuwansa da Karfi. “Abba…� Ya ja sunan mahaifinsa da Karfi tare da fashewa da kuka. Abba ya cika da al’ajabin irin kukan da Sultan yake yi, domin har kiransa ake yi mai taurin zuciya. An sha a yi mutuwa kowa na kuka, amma idanunsa ko gezau baya yi. Abba da ya gama karya hanya yasa hannunsa daya ya jawo shi jikinsa. “Abba tana ta kirana da hannu, amma kuka rabani da ita, tana son ta min maganar da kowa ya kasa sauraronta, amma baku ji tausayinta ba, kuka hanani sauraronta. Ban san me take son gaya min ba. Me yasa Abba?�Shi kansa hawayen danasanin ne kwance a idanunsa. Bai san me yasa mutuwar Saudat ya tsaya masa a rai ba. Bai taba kawowa zai taba shiga irin wannan damuwar ba. “Kayi hakuri Sultan, Allah ya riga ya aiko bamu isa mu kaucewa Kaddarar mutuwarta ba. Kayi shiru ka daina kukan haka. Kukanka yana karyar min da zuciya. Ta fi buKatar addu’arka fiye da wannan kukan� Shi dai Sultan saurarensa yake ba don yana fahimtarsa ba. Kwanciyarsa ya yi a jikin mahaifinsa yana faman sauke ajiyar zuciya. Wannan karon duk sonsa da kallon titi, bai kalla ba, domin zuciyarsa a Kuntace take, ta yadda komai ba ya yi masa dadi. Kai tsaye aka iso da gawar (GIWA HOSPITOL) Asibitin da ake matuKar ji da shi a garin na Kaduna. Cikin gaggawa aka karbe ta tare da shirye-shiryen shiga da ita aiki. Su Abba suna nan tsaye aka wuce da ita, don hakane suka yi ta kaiwa da komowa. Tun suna sa ran fitowarsu har suka gaji suka koma gefe guda. Hajiya Salma kuwa duk da jikinta ya yi dan sanyi da mutuwar Saudat sai da ta tsinci bakinta da cewa, “An rage mugun iri. Da haka ake bin mazinatan nan, ana kashewa da masifu sun yi mana sauki.� Ita damuwarta danta da mijinta su dawo gida, Agogon yana buga sha biyu dai-dai na wannan dare, aka fito da yara biyu a nannade cikin zani. Daga ‘yan sandan har zuwa Sultan an rasa wanda ya riga wani isowa gun yaran.. Mikawa Abba yaran ta yi_, tana murmushi, “An ciro mace da namiji a cikin mahaifiyarsu. Sai dai yanzu za mu mayar da su, saboda yunwa ta fara lalata masu jiki. Ya yi wani irin yanayana alamun dai yunwa ce, don haka yanzu za a ci gaba da basu taimakon gaggawa. Sultan dai bai karbe su ba, amma kuma yana tsaye yana kallonsu daga hannun mahaifinsa. Doctor din ya Karaso ya ce yana son ganin Abba a office dinsa. Suna isowa ya dubi Abba ya ce, “Alhaji za a mayar da yaran domin kulawa da lafiyarsu , za kuma a bar mana ‘yan sanda a nan saboda kada mutanen da suka kasheta su sake dawowa kan yaran. Ita kuma idan Allah ya kaimu gobe sai mu bayar da gawarta. Allah ya jikanta ya raya marayun da ta bari.�Sultan da ke zaune ya hada kai da guiwa ya sharce hawayensa yana jin Kaunar da yake yi wa Saudat tana dawowa kan ‘ya’yanta, Yana ji a ransa Zai iya cikawa Saudat alKawarinta, ko da kuwa wannan shi ne aiki na Karshe da zai yi a duniya. Sai dai tarin damuwar rashin matar da a lokaci daya ta shiga ransa, ya kasa yunkurin barinsa ko taba yaran ya yi. “Me ya sa kuka yi gaggawar kashe ta? Me ta yi maku? Anti Saudat! Me za ki gaya min? Me yasa Umma ta hana ni saurarenki? Wasu hawaye suka shiga kwararowa daga idanunsa. Sosai yake shessheKa. Mahaifinsa ya kamo shi suka nufi mota. Sai da ‘yan sandan nan suka raka Alhaji Lukman har gida kafin suka koma. A falo suka ci karo da Hajiya Salma. A cikin Kwayar idanunsu ta karanci saKonni kalakala da kai tsaye yake mata nuni da haushinta suke ji. Kawar da kanta ta yi kamar bata san suna yi ba. Sultan kuwa zama ya yi a Kasa idanunsa sun ki daina zubar da hawaye. Barci ke fizgarsa, dole ya wuce dakinsa ya yi wanka ya cire kayan da jini suka bata masa. Zoben nan da littafi da hotuna kuwa, ko kallonsu bai yi ba, ya cusa a cikin wani akwatinsa ya mayar ya rufe. Jallabryarsa ce a jikinsa har barci ya kwashe shi a nan, ba tare da ya tuna da addu’a ba. Alhaji Lukman ya mike da nufin duba dansa, cikin rashin sa’a idanunsa ya hadu da na � Hajtya Salma. Dukkansu suka dauke kansu. Dakin Sultan ya shiga ya gyara masa kwanctyarsa tare da addu’a ya tofa masa. Ya fito ya jawo masa Kofa. A falon ya sameta, zai wuce ta sha gabansa. “Me hakan ke nufi?� Harara ya sakar mata, “Abinda zuciyarki ta gaya maki.� Shiru ta danyi tana nazarin inda kalamansa suka nufa. “Kana nufin akan wata za ka juya min baya?� “Eh idan har ta kasance abar halitta ce, kamarki zan yi abinda ya fi haka.� Zamewa ya yi zai wuce sai kuma ya juyo, “Ki shirya zaman yaran da aka ciro daga cikin mazinaciya, ki shirya renon yaran da aka ciro daga jikin mai dauke da ciwon nan da ke karya garkuwar jiki. Haka ki shirya zama inuwa daya da yaran da uwarsu ta aro addininki kike yi mata gori.� Kafin ta dawo daga doguwar sumar da ta yi, har ya shige dakinsa. Bata bishi ba, ta tsaya a falo tana faman kaiwa da komowa, “Wallahi! Babu wanda ya isa ya kawo min dan shege gida in rene shi. Ashe Alhaji ya dibo tashin hankalin da bana jin sauke shi zai yi masa sauki. Lallai a tsawon shekaru goma sha takwas da muka yi a tare, bai taba sanin wace ce, Salma ba, amma daga yau zan fito masa da asalin kalata.� Dakin ta shiga. A kishingide ta same shi, yana karanta labarai a cikin wayarsa. “Ina son magana da kai.� Hajiya Salma ta yi maganar cikin shan mur da nuna masa da gaske take, kuma tana nan akan bakanta. . “Kunne ke ji.� Ya bata amsa ba tare da ya dago ya dubi inda take ba. Ta gyara tsayuwarta ta sake cika ta yi tam! Ta ce, “Kada ka dauko masifa da hannayenka ka kawo cikin gidanka, kayi tunanin zaman lafiya.� Har yanzu bai dago ba kuma bashi da alamun dagowar. Ya ce, “Namiji ke da iko da gidansa, -shi ya sa aka halatta mana, mu je gidajenku neman aurenku, mu bada sadaki. Daga nan mu dauki nauyin ci da shan ku. Idan kuwa .har za ki iya shimfida doka a gidan mutumin da ke da ikon daga Kafafunsa ki shiga Aljannah, ina ganin da tuni an halatta maku ikon aurenmu, da kuma ikon mika sadaki.� “Duk maganar da ka gadama ka gaya min a kan matar da baka sani ba. Amma sai ka fara gaya min wacce waina kake tunanin za a toya a cikin gidan da ke dauke da shegu marasa addini?� Sai yanzu ya dago kai yana dubanta fuskarsa dauke da murmushin da ke nuni da murmushin takaici yake yi. Ya ce “Wainar Kasa za a toya. Dagowa ta yi a fusace ta ce� Sanin kanka ne wainar Kasa ba za ta taba ciwuwa ba.� Tashi ya yi da wayarsa a hannu zai bar dakin, dai-dai saitinta ya tsaya yana yi mata duban kin bani mamaki, sannan ya _ ce, “Kin san ba zai ciwu ba kuma kike� son ci? Kamar yadda kike tunanin wainar Kasa ba za ta ciwu ba, haka kema tsarin da kike son shimfidawa a gidan da ba mallakinki ba, ba abu bane mai yuwuwa ba. Don haka ki gyara wannan kuskuren da kike KoKarin tafkawa idan bahaka ba, zan auro wacce za ta iya tsayawa ta yi min rainon marayun nan, ta inganta min rayuwarsu, Kila a dalilin taimakon nan da zan yi inshiga Aljannah. Kada ki sake biyo ni idan ba haka ba, zanyi mummunar saba maki.� Ya sa kai ya fice abinsa. Hajiya Salma da wani irin kishi ya cika mata zuciya, ta durkushe Kasa tana kuka. Haushin Sultan yafi yawa a zuciyarta, da bai kawo masu masifar nan ba, da babu abinda zai Sanyata sa’insa da mijin da take matuKar so kamar ta kashe kanta. Mutumin da ya ce baya sha’awar aure yau shi yake fadin zai Karo mata kishiya? Ita kuwa da ya Karo wata mace a gidan nan da sunan aure gara mala’ikan daukar rai yazo ya dauki ranta tun kafin zuwar ranar. Ta rasa menene mafita? Allah-Allah take yi gari ya waye, ta kira Yayanta Alhaji Mu’azu, domin shi kadai ya isa ya gayawa mijinta ya Ji. A wannan dare Alhaji Lukman ya kasa barci, sai juyi yake yana tunanin ta hanyar da ya kamata ya biyowa matarsa. Ya tsani abinda zai ° kawo masu rashin jituwa a_ tsakanin su. Washegari da sassafe ya wuce Asibitin, ya bada * kudi aka yi wa yaran siyayya, daga can yasa aka daukota akayi mata Sallah a Masallaci aka kaita gidanta na gaskiya. Alhaji Lukman ya kira Kanwarsa ya nemi taimakonta, Anti lyami, ita ta tsaya akan yaran har aka basu sallama suka kwaso zuwa gida. A lokacin Sultan ya dawo daga Makaranta dama kuma tun da ya tashi gaisuwa ce kawai ta hada shi da mahaifiyarsa, haka yanzu din ma, gaishe ta ya yi ya nufi hanyar ficewa. Hannunsa ta jawo tana dubansa, “Yanzu Sultan akan bare kake fushi da ni? Insha wahala akanka amma yau da ni kake fushi? Kana son ka gama da duniyar nan lafiya kuwa? Abbanka ya yi min kaima kayi min?� Jikin Sultan ya danyi sanyi, don haka ya bata hakuri kansa a Kasa, sannan ya wuce. Duk da haka dai yaki sakewa. Jin Sallamarsu yasa Sultan dawowa da baya ya kafe mahaifinsa da ~ idanu, haka ya kasa murnar ganin jariran kamar yadda kowa ya za ta. Anti Iyami ta zauna tana gaban mahaifinsa yana gaida shi. Abban ya mika masa da namijin ya ce, “Sultan ga amanar da ka dauka. Wadannan ‘ya’yan ka dauka cewa ‘ya’yanka ne. Namijin Nawfal, macen kuma Nasreen. Ina fatan ka san ma’anar Nasreen?� Sultan ya daga masa kai ba tare da ya iya furta komai ba, haka kuma bai da alamun karbar yaron, kamar yadda mahaifinsa ya buKata. Anti Iyami ta mike tana murmushi, ta ajiye masa Nasreen a jikinsa, wacce take ta faman tsotson hannu. Karbarta ya yi ya tsura mata idanunsa, yana son dole sai ya Kare mata kallo. Yarinyar bata da auki, amma kuma sambaleliyar mace ce. Yatsun Kafafunta ya kafe da ido gabansa yana fadi da Karfin gaske. Amma kuma ya rasa dalilin irin wannan faduwar gaban. A hankali ya yi magana wanda kaf falon babu wanda baiji ba, “Allah ya rayaku. Allah yasa ku yi wa addinin musulunci hidima.� Sau tari Abba yana mamakin irin iya tsara magana da Sultan yake yi, wanda ko babba sai hakan. Hafsat da Haidar suka Karaso suna leKen yaran. Sai kuma suka dago suna duban Sultan, “Yaya Sultan Umma ce ta haife su?� Hajiya Salma da dama jira take yi ta mike tsalam jikinta har kyarma yake yi. “In ji uban wa? Allah ka raba zuri’ata da haihuwar kwararo haihuwar titi, haihuwar KarKashin babbar mota! Wadannan yaran da kuke gani, shegune ake neman liKa mana tsiya.� Abba ya mike jikinsa yana kyarma ya ajiye Nawfal ya daga hannu da nufin zabga mata mari, sai kuma ya dakata sakamakon muryar Sultan da ya ji ya ce, “A’a Abba!� Hajiya Salma ta ware manyan idanunta tace, “What! Alhaji ni za ka mara a kan ‘ya’yan arna? Ni za ka mara akan ‘ya’yan ‘shegu? TirKashi! Tun yanzu kenan suna cikin tsumma, ina kuma ga sun girma? Don Allah zo ka mare ni kada ka fasa. Kai kuma Sultan! Daga yau ka dauka cewa ni ba mahaifiyarka ba ce, ka je gun ubanka dake daure maka gindi ni na cire ka daga jerin ‘ya’yana.� . Ta sa hannu ta finciko Haidar da Hafsat, ta ce, “Daga yau su Hafsa sune jinina ba kai ba Sultan. Na yafewa duniya kai. Yaran nan kuma sai sun koma inda suka fito indai ni ce Ummu Salma!� Yaron ya zuba mata idanu kawai ba tare da ya iya furta komai ba. Haka bata ga ko alamun razana daga idanunsa ba. Abba ya dube ta jikinsa a sanyaye, domin baya son Salma tana yiwa ‘ya’yanta baki. “Salma� Ki dauka cewa. Nasreen RUBUTACCIYA ce daga Allah. Haka Nawfal RUBUTACCE ne daga Allah. Tunda Allah ya rubuta za su fito daga cikin matacciya kuma a raye, bana jin ke Karamar alhaki zaki iya yi masu abinda ba Allah ne ya rubuta ba. Sultan tashi mu je ciki.� Iyami ta mike tana yiwa Salma kallon mamaki, amma ko a jikinta. Tare suka shige, Iyami ta yi masu wanka, ta sauya masu kaya, sannan ta dauko madarar su mai dauke da sinadare ta basu suka sha sosai. Sultan dai kafe yaran ya yi da ido, ya rasa mai ke masa dadi. Ji yake kamar bashi bane wani Sultan din aka aro. A zuciyarsa ya maimaita, RUBUTACCIYYA. Hakika mahaifinsa ya yi gaskiya. Anti Iyami ta koma gida ta bar Sultan da yaran. Dole ya naimi taimakon Mairo mai aikinsu, don haka ne take taya shi kula da yaran. Hajiya Salma ce da Alhaji Mu’azzam_ babban wansu. wanda shi yake matsayin kamar mahaifinta, tunda shi ya raineta tun suna Kanana. � Malami ne sosai, haka bai taba sa doka ankarya masa dokarsa ba. Kusan halayyarsa guda da hajiya Salma, gashi dai yana da sani a addini sosail, amma kowa yasan mutum ne mai akida. Kowa tsoronsa yake ji. Alhaji Mu’azzam ya dubi Alhaji Lukman ya ce, “Wai da gaske ka kawo ‘ya’yan shegu cikin gidanka?� Alhaji Lukman ya hada rai sosai, “Na kawo marayu gidana, ba ‘ya’yan shegu ba ne. Ina kuma roKonka da kayi amfani da sanin da Allah ya yi maka, kayi adalci. Ya zama dole ko kare na kawo gidana Hajiya ta girmama min. Bai kamata ina fada tana fada ba.� Alhaji Mu’azzam ya mike yana dubansa, “Gaskiya na raina wayonka Alhaji Lukman, da girmanka da darajarka a idon duniya za ka je ka kawowa kanka masifa? Matarka tana KoKarin dawo da kai hanya, amma ka zama makaho? To ka sani, babu ruwana da mazinaci ma, ni idan na � ganshi zann iya kashe shi, ba na yiwa mazinaci uzuri. Bare kuma a kai ga cikin shege. An ce fa tsintar uwar ka yi. Ka canza tunani zan sake dawowa.� Ya mike ya fice abinsa. Alhaji Lukman ya bi shi da ido, yasan za a rina, Sai dai yana jin ko mahaifiyarsa ba za ta hana shi taimako ba, bare yayan matarsa. Karin Jin dadinsa ma, da Hajiyarsa ta nuna masa goyon bayanta akan renon yaran. Haka kowa ya bar gidan zuciyoyi babu dadi. Shi kuwa Sultan Makaranta kadai ke raba shi da yaran. Kullum yakan tasa su a gaba ya yi ta kallonsu kamar mai son gano wani abu. Mahaifiyarsa bata shiga sabgarsa, haka ta hana Kannensa shiga huruminsa, idan ya gaishe ta bata amsawa, shi kuma bai fasa ba. Hajiya Salma ta sauke wayar da ta gama yi da Kawarta Hajiya Ladidi ta kuma yi na’am da shawarar da Kawarta ta bata. Don haka ne ta sami Alhaji da ke zaune yana duba Jarida fuskar nan babu fara’a ta nemi wuri ta zauna, “Alhaji ka ~ yi hakuri ka yafe min, na tuba. Fushinka yana daga min hankali. Na amince ‘yan biyu su zauna � a gidana, amma da sharadi.� Alhaji Lukman ya dube ta da fara’a sosai a fuskarsa domin shi kansa ya yi kewar matarsa. “Ina jinki fadi sharadin.� Muskutawa ta yi tana murmushin mugunta, “Sharadina ba zan tsaya kulawa da yaran ba, ka ga kasuwancina ma ba zai barni ba, sai dai a Karo masu kula da yaran, ni zan dinga biyan ma’aikatan domin bada gudumawata. Shi kuma Sultan ina son in nuna masa kuskurensa na gujewa maganar mahaifiyarsa. Don Allah ka bar ni a hakan mu shirya kanmu.� Alhaji Lukman ya dubi matarsa, yana jinjina ita mace har tsufanta da yarinta a ciki. Don haka babu dogon tunani ya ce ya amince, ya kuma ji dadi da har Hajiya za ta iya bada gudumawarta wajen kawo masu aiki. Miji da mata sai Allah, a nan suka shirya kansu. Babban damuwar Sultan a yanzu bai wuce yadda mahaifiyarsa ta nunawa Kannensa Sultan a matsayin maKiyinta ba. Yanzu Kannansa bayan gaisuwa basa shiga huruminsa. Yau Asabar bayan ya tafi wurin motsa jika ya wuce Islamiyya daga nan, da _ yake Islamiyyarsu ba daya ba ne da Kannansa, don haka ya dawo gida ya zauna daga farfajiyar gidan ya kurawa Kasa idanu yana kallo. Ya rasa tunanin me yake yi, kunnuwansa suka jiyo masa kukan jariran. Tashi ya yi ya nufi dakin renonsu, a nan ya sami Haidar da Hafsat da bulalai suna tsulawa jariran nan. Babu kowa akansu, hakan ya tashi hankalin Sultan ya jawo su, ya yi masu wani irin mugun duka, wanda ya dasa masu 6/3/22, 17:53 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 3 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Yau Asabar bayan ya tafi wurin motsa jika ya wuce Islamiyya daga nan, da _ yake Islamiyyarsu ba daya ba ne da Kannansa, don haka ya dawo gida ya zauna daga farfajiyar gidan ya kurawa Kasa idanu yana kallo. Ya rasa tunanin me yake yi, kunnuwansa suka jiyo masa kukan jariran. Tashi ya yi ya nufi dakin renonsu, a nan ya sami Haidar da Hafsat da bulalai suna tsulawa jariran nan. Babu kowa akansu, hakan ya tashi hankalin Sultan ya jawo su, ya yi masu wani irin mugun duka, wanda ya dasa masu ZAMU TASHI soron shi fiye da tunanin su, kasancewar bai taba kai hannu jikinsu ba. . Hajiya Salma ta fito a gujen gaske tana ganin abinda ya faru, ta sa Salati da Karfi tare da dafe Kirji. Tana Karasowa ta dauke shi da mari. Ya rike fuskarsa zuciya tana wani irin cinsa. Ji yake kamar dukan da ya yi masu bai gamsar da shi ba, yana jin zai iya aikata komai akan yaran da ya Kwallafa ransa a kansu. Sultan ya juya kawai zai tafi, Umma ta sake fizgo shi, “Zo nan shugaban marasa imani, ba ka isa ka tafi ba, sai ka kashe su. Zo ka kashe su, ka fita duniya ka gaya masu ka nakasa Kannenka saboda ‘ya’yan shegu.� Sultan dai bai ce komai ba, har ta gama masifarta ta fice da yaranta. Shi kuma ya fice yana Kwalawa masu kula da yaran kira. Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sau tari suna mamakin yaro Karami ya tsaya yana basu manyan dokoki. Su dai sai hakuri suke bashi. Ya karisa ya dauki naufal yan girgizashi ya bashi madara Yasa bakinsa a kunnensa yana masa addu’a har barci ya kwashe shi. Nasreen dai ta ki __ yin shiru sai kuka take tsalawa. Ya karbeta yana kallonta. Yadda ta bude idanunta tana kallon Sultan ya sa ya yi murmushi, “Ke sarkin kuka. Ke ragguwa ce ko? Oya yi min shiru ko in zane dan bakin nan.� Cikin ikon Allah ta yi shirun, haka idanunta Kyar akansa. Hajiya Salma ce zaune da Hajiya Ladidi suna tattaunawa, “Wato ni abinda ke damuna, macen nan da aka Haifa. Tana iya girma ta zame mani matsala, Kila daga Karshe ta biyo halin uwarta na bin maza. Gara namijin bana jin akwai wata matsala da zai bani. Don haka ne nake neman shawararki yadda za a yi inbatar da Nasreen daga duniyar gaba daya.� Hajiya Ladidi ta numfasa, “Maganarki gaskiya ce. Ai ina ganin ki ba su Rainbow aikin nan a kwana daya za su kashe kayan banza su watsar.� Hajiya Salma ta yi na’am da wannan shawarar, don haka ta hadata da Rainbow ta gaya masu yadda take so. Cikin dare, Sultan ya idar da Sallar dare, haka kawai yake jin ba zai iya barci ba, idan har bai je yaga ‘yan biyu ba. A hankali ya fito yana takawa har ya iso dakinsu. A lokacin Rainbow ya shigo jin motsin Sultan yasa ya makale a gefe yana kallon ikon Allah. Nasreen ce idonta biyu, shi kuwa Nawfal sai shaikan barcinsa yake yi. Sumbatar yaron ya yl ya sake tofe shi da addu’a. Nasreen kuma ya dauketa yana dubanta. “Abba ya ce ke RUBUTACCIYA ce, zai yi wahala mai nemanki da sharri ya same ki.� . : Dauketa ya yi ya nufi dakinsa da ita yana jijjigata. Akan Kirjinsa ya kwantar da ita yana bubbuga bayanta har barci ‘ya sureta. A Kalla Rainbow ya kwatanta zuwa gidan yafi a Kirga, amma samun ko taba jikinta ya gagara, domin kullum yazo sai ya sami Sultan a tare da su. Wannan abu shi ya Karawa Umma jin tsanar Sultan a zuciyarta, kuma ta yi alKawarin indai ita ce sai taga bayan Nasreen. Shi kansa Abba yanzu hidimomin fice-ficensa sun sanya shi a gaba, don hakane baya samun wani cikakken zama Babu abinda zai baka mamaki sai yadda yaran suka yi bulbul suka yi wayo. Kullum kyawun yaran gai sake fitowa yake yi. Suna samun kulawa sosai daga Sultan, haka yaran sun yi wata shaKkuwa da Sultan har suna iya gane shi da zarar yazo wurin su. Rashin jituwa tana sake kusanto shi da mahaifiyarsa. � “Yau gaba daya suna zazzaune a falo suna cin abinci. Abba ya dubi Sultan ya ce, “Yanzu sai makarantar likitoci ko?� Sultan ya girgiza kai, “A’a Abba na sauya ra’ayi Dan sanda nake son inzama.� Umma ta dafe Kirji da Karfi, “Yau na shiga uku! Dan sanda a gidana? Wai me yake damun Kwakwalwarka ne? To ba ka isa ka zama dan sanda a wannan gidan ba. Yadda na tsani dan sanda Wallahi ba ka isa ba.� Abba ya kurbi ruwan shayinsa yace, “Oh me kuma dan sanda ya yi maki? Ke kin huta komai baki so.� Ya Karashe da yi mata gatse, Ta hada rai ta ce, “Ni dai na gama magana.� Sultan da kansa ke Kasa ya dago ya ce, ““Abba dan sandan nake son inzama insha Allahu. Umma ki sa min albarka kawai.� Umma ta sake zabura kamar za ta kai masa duka, “‘Albarkar wa? Ba zan sa ba shegen yaro kafaffe. Kaje indai dan sanda ne nawa ido.� Abu kamar wasa har sai da maganar ta iso gun Hajiya Gwaggo, wanda ta yi mata fada sosai, ta kuma tursasata sai da tasa masa albarka Mutane da yawa suna kallon Sultan a matsayin wani miskili wanda bai damu da magana ba, amma kuma idan ka same shi a cikin su Nasreen ya cika masu daki da kayan wasa, sai kayi ta mamaki kana cewa anya Sultan ne kuwa? A guje ta fito da ‘yar bebinta, kai tsaye jikin Sultan ta fada tana KyalKyaltan dariya. Sultan bai tabata ba, ya tsaya yana kallon wanda ya sa Nasreen irin wannan dariyar. Nawfal shima ya fito aguje yana bude haKoransa. Gaba daya gaban Sultan suka tsaya suna haki. Kamar ba zai yi masu magana ba, kasancewar bai jima da dawowa aiki ba, kuma ya gaji da yawa, amma dole ya amsa masu yana murmushi, “Me ya same ku kuke dariya haka?� Nasreen ta dube shi da idanunta kamar madara, ta ce, “Dee ni zan fara gaya maka, Bros Nawfal ne ya biyo ni zai dakeni. Shi ne Anti Hafsa ta biyo mu da bulala za tayi mana dukan gaske.� Fitowar hafsat a fusace yasa duk suka bita da kallo. Tana ganin Sultan jikinta ya yi sanyi ta koma da baya har tana tuntube. Nasreen ta shige jikin Sultan tana Boye kanta. Sultan ya dagota ya zuba mata ido kanta ya sha gyara da Kananun ribom masu kyau. Kurawa Kafafunta idanu ya yi gabansa yana ci gaba da fadiwa da Karfi. « BAYAN WASU SHEKARU Doguwar yarinya ce, mai yalwataccen gashin kai wanda ya taho tun daga goshinta har zuwa bayanta. Tana da saje irin na mata wanda yake nuni da alamun yarinyar tana da gashi. Ba fara ba ce kai tsaye kana kallonta za ka kira ta mai kalar choculate. Duk da hasken ya rinjayi duhun. Ko alama ba ta da jiki, siririya ce wanda sirrancin ya yi matuKar yi mata kyau kasancewar ba ta da rama. Kugunta a dan bude suke, haka daga samanta Allah ya wadata dukiyar na Fulani. Har yanzu akwai yarinta a tare da_ ita, kasancewar shekarunta ba za su wuce sha shida ba a duniya. Tana da sassanyar kyau, haka da za a shiga gasar kyawawa da ita, babu abinda zai hana ta cinyewa, Muryarta ta cika sanyi da yawa, haka komai take yi a sanyaye take yinsa, kamar wacce ba ta dauke da kayan ciki. Fuskarta kullum dauke yake da murmushi ko da kuwa kuka take yi, sai ka hango murmushin nan. Sanye take da kayan Makaranta mai kalar blue hijabinta kuma fari tas! Shigowar Sultan yasa ta Karaso kusa da shi tana mika masa hannayenta, “Dee ka taimaka ka cire min abin hannun nan kada a Kwace min a Makaranta.� Kafe ta ya yi da idanu yana tuna wasu abubuwa, sal kuma ya kama tsintsiyar hannun yana kokarin cire mata. Cikin sa’a ya dago kansa ita kanta shi ta kafe da idanu tana kallon sa. Manyan idanunta suka hade da nasa masu yawan lumshewa. Gaba daya suka sakarwa .. kansu murmushi, ‘sannan ya cire mata. “Lazy baby, ki yi sauri ni zan ajiye ku in wuce office.� Marairaicewa ta yi , “Ayyah Dee, Kila ma kai kayi min baki shi ya sa har yanzu nake Lazy.� Murmushi ya yi ya dauki jakar makarantarta suka fito. Umma ta dube shi ta riqe baki, “Oh wani sabon gulmar ce kuma yau Za ka rike mata jaka? Kullum da sabon salon iskancin da yarinyar nan take dauke da shi.� Wucewa tayi . Sultan suka kalli juna da Nasreen sai duk suka basar. Sultan zai tafi kwas wanda za a Kara masa girma, sai dai wannan ne karo na kusan hudu yana soke tafiya kwas dinsa sabod su Nasreen. Amma a yanzu tunda sun girma za su iya yin komai da kansu, yana da buKatar tafiya. Yafi tausayawa Nasreen da ta dora shaKuwar duniyar nan akan Sultan. Haka ya dinga shirye-shirye jikinsa babu Kwari. Nasreen ta shigo dakin ta dube shi ta ce, “Dee in kawo maka Assignment dina ka taya ni dubawa ko nayi dai-dai?� = Dubanta yake yi kamar yau ya fara ganin ta, “Nasreen kin ga na gaji da yawa, ki bari sai ~ an jima ko?� Gyada kanta ta yi tana duban yadda yake shirya kaya, “Dee ina za ka je da kayan nan? Na san ba za ka tafi ka bar ni da Umma ba ko? Umma ba ta sonmu ni da Nawfal, ban san me muka yi mata ba. Dee me muka yi mata?� Shafar gefen sajenta ya yi yana KirKiro murmushi, “Babu abinda kuka yi mata, tana son baku tarbiyya mai kyau ne, Tana sonku kun ji? Ko kin taba ganin inda uwa ta tsani ‘ya� yanta?� Nasreen ta yi narai-narai da idanun dake firgita “yan maza ta ce, “Ai ta ce ba ita ta haife mu ba, wai mu a Karkashin gada aka same Sultan da ya ji gabansa ya fadi, ya mike jikinsa har yana kyarma. Kai tsaye falon mahaifinsa ya nufa, wanda yake zaune da Umma. Ya dube su ransa a matuKar bace ya ce, “Umma don girman Allah ki daina cewa yaran nan bake kika haife su ba, har kina gaya masu daga inda suka fito. Yaran nan ba su san komai ba, bai kamata ana yi masu hakan ba.� Abba ya dube shi cike da mamaki, haka ya dawo da kallonsa gun Hajiya Salma tare da ware ~ idanu, “Salma! Kina nufin duk irin gargadin da nayi maki baki ji ba kenan? Me ya sa za ki dubi yara Kanana kina gaya masu irin wannan maganar?� Hajiya Salma ta dinga auna wa Sultan harara, ta kuma hada rai ta Ki yin magana. Haka Sultan yasa kai ya fice ransa a bace. Alhaji Lukman ya mike yana dubanta ya fice ya bi bayan Sultan. Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba. Sultan dai ya bar garin zuwa Enugu, ba tare da wata matsala ba. Haka ya jaddada amanar Nasreen a gurin Mairo ya fi a Kirga. Da zai tafi yaran suka yi masa layi kowannensu ya yi tagumi. Gabadaya ji yake ya karaya. Ya sa hannu ya yafito su duk suka Karaso gabansa yana dubansu. “Nawfal, Nasreen ba za ku yi min dariya ba?� « , Dukkansu suka fidda murmushi wanda kallo daya za ka yi masu ka fahimci iyakarsa fuska. Shafa kansu ya yi ba tare da ya iya furta komai ba, direba ya ja motar suka fice. Rintse idanunsa ya yi da Karfi yana jin gabansa yana tsananta fadiwa. Ji yake kamar ba zai dawo ya same su da rai ba. Hajiya Salma ta gama leka ko’ina ta tabbatar da babu Abba a gidan, hakan ya sa ta jawo Nasreen da Karfin tsiya ta fesa mata wani abu a cikin idanunta. Yarinyar ta sanya Kara mai Karfi, ta fadi tana shure-shure. Nawfal ya Karaso da gudu ya tallafo ta yana Kwala mata kira. Nasreen tana kuka Nawfal yana kuka, gaba daya an rasa wanda zai lallashi wani Nawfal ya dago ya zuba wa Hajiya idanu, yana jin haushinta da tsanarta a cikin ransa. Ko da yake yaron yana da tabbacin Umma bata kaunarsu. Yana kallon yadda su Haidar suke kwasar dariya. Hafsa ta ce, “Shegiya ba kina taKama da idanunki ba ne? To an nakasa su sai mu ga wani abin yangar.� Haka suka wuce suka barsu cikin kuka. Ita kuwa Nasreen saboda azaba a take ta suma. Umma ta sake dawowa, ta damki wuyar rigar Nawfal ta ce, “Wallahi kuka sake kuka fadawa waml Wai ni ce nay mata wani abun, sai na kashe ka Nawfal ya gyada kansa yana ci gaba da hayyacinsa saboda kuka. Cikin ikon Allah sai ga Abba ya dawo, kai tsaye ya nufi yaran don ya duba su. Haka yana son ya cika alKawarin da ya daukarwa Sultan zai hada shi da su. Ganinta a kwance bata motsi ya daga hankalinsa. Bai tsaya bin ba’asi ba, ya dauketa sai asibiti. Yana nan tsaye ya kasa zaune saboda tunanin mai ya sami Nasreen haka? Ya fi Karfafa zarginsa akan Hajiya Salma, idan kuwa ita ce, babu shakka zai ya sakinta ta koma gidan su. Kiran wayar Sultan na biyar kenan, yana kasa dauka. Dole yasa wayar a kunne yana cewa, “Sultan ban iso gidan bane. Ka kwantar da hankalinka ina isowa zan hadaka da yaranka.� Sultan ya cika da mamakin mutumin da ya ce masa yana kusa da gida, yanzu kuma zai ce bat iso ba. “Abba fa ka ce min kana kusa da gida, yanzu kuma ka ce baka iso ba. Abba ko dai da matsala ce?� Jikin Abba ya yi sanyi, yau ya yi wa dansa karya har ya kama shi, “Ka yi haKuri Sultan babu matsalar komai, har na kusa gida aka sake ~kirana, wani abokin mu bai da lafiya shi ne yanzu na iso asibitin.� Dole Sultan ya ajiye wayar yana ci gaba da saKe-sake. Lambar mahaifiyarsa ya kira, tana kallo ta Ki dauka gabanta yana fadi kada Nasreen ta farka ta ambaci sunanta. Da kiran Sultan ya yi yawa ta dauka cikin daga murya ta ce, “Wai menene haka kamar kana bi na bashi?��“Umma don Allah ki taimaka ki hada ni . da su Nasreen, Abba ya ce bai iso gida ba.� “Umma taja dogon tsaki, “To ba zan hada ka da su din ba. Ka ga Sultan? Ka kiyaye ni! Idan ba haka ba, ni na san yadda zan yi da kai. Kada ka sake kirana.� Kawai sai ta kashe kiran. Wayarsa yabi da kallo yana jin kashe wayar har tsakiyar kansa. Ya kasa jure rashin jin muryar yaran, don haka ne ya ci gaba da jin damuwa da bacinrai. _ Likitocin suka fito suka bukaci Abba da ya biyo su Office. A nan suka yi masa bayanin wani Chemical aka zuba mata a idanun, a sakamakon hakan da wahala ta sake gani da idanunta, sai kuma-_wani ikon Allah. Abba ya yi suman zaune. A yanzu me zai iya gayawa dansa? Dakin da Nasreen take zaune ya shigo yana dubanta, “Nasreen.� Lalube take yi tana fadin “Na’am Abba. Me ya sa bana ganinka? Abba ina Nawfal? Shi ma ba zan iya ganinsa ba? Abba ka bude min idanuna ina son inganka. Abba idanuna har yanzu Zafi suke yi min.� Hawaye mai dumi ya biyo idanun Abba. Zuciyarsa ta karye, ba shi da wani Karfin guiwa. Zama ya yi kusa da ita ya kamo ta, ya mayar da ita jikinsa, ‘“Nasreen dina. Wannan Kaddararkice, haka komai za a yi maki insha Allahu sai kin kai labari, domin ke RUBUTACCIYA ce, wanda Allah ya rubuta sai kin sha ruwa a duniyar nan. Ciwo kika ji za ki warke har ma ki fara gani da idanunki kin ji? Yanzu gaya min waye ya watsa maki abu a cikin idanu?� Nasreen da ta gigice ta hau girgiza kai “Ni ma bansan waye ba Abba: Ka kai ni wajen Dee in nuna masa idanuna, bana ganin kowa sai duhu.� Wannan karon kalaman bakin Abba sun Kare, dole ya koma kamar kurma. Satinta guda a asibitin, kullum Abba ke kulawa da ita, haka ya Ki yin magana ne yana jiran a sallamota. Nawfal da Mairo mai aiki suke zaman kulawa da ita. Ranar da aka sallame su, suka tattaro suka dawo gida. A bakin Gate suka sami Nawfal kusa da mai gadi ya zauna ya yl shiru, kasancewar a ranar Abba ya hana shi zuwa ya ce ya bari kawai yau za su dawo da Nasreen din. Yana ganinsu ya taso ya Karaso da saurinsa kamar zai kifa. Ganin Nasreen tana lalube yasa Nawfal kafe ta da idanu. Abba ya jawo Nawfal yayi masa dabarar duniyar nan amma ya Ki fadin wanda ya yi wa Nasreen wannan aikin. A tunanin Nawfal da gaske Abba yake yl, yau Nasreen za ta fara gani da idanunta, kafe ta ya yi da idanu, zuciyarsa tana gaya masa Nasreen ta tabbata makauniya.Sai kawai ya hau kuka mai tsanani yana tausayawa ‘yar uwarsa. Abba ya dubi wayarsa yana kallon kiran Sultan, ya dubi yaran ya ce, “Ga Daddynku zai yi magana da ku, idan kun dauka ku tabbatar masa kuna lafiya kun ji? Idan ya san abinda ya faru zai fasa aikinsa ya dawo nan, ku bari har ya gama sai ya dawo sai ya gani. Nasreen ke kuma insha Allahu zamu nemo maki magani ‘har ki warke.�Dukka yaran suka amsa masa. Da kansa ya kira Sultan ya mika wa Nawfal. Muryar Nawfal da yaji yasa ya saki ajiyar zuciya, suka gaisa da yaron yana masa ‘yan tambayoyi. Daga bisani ya ce, a baiwa Nasreen. Cikin Shagwababbiyar muryarta ta ce, “Dee…� Sai � kuma_ tayi shiru. Siririyar muryarta ta ci nasarar tsinka masa zuciya, “Nasreen kin ‘yi kuka, Nawfal ma ya yi kuka, gaya min waye ya 6/5/22, 10:27 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 4 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Abbansa. � A falon ya tara kowa yana faman kaiwa da komowa ransa a matuKar bace.,“Ya zama dole ku gaya min wanda ya aikata wa Nasreen wannan abin,:ko kuma in hada ku dukka in kulle.� Hajiya Salma da ba ta dauki lamarin zai yi irin wannan zafin ba, ta ware idanu, “Yanzu a kan wannan yarinyar za ka kulle su?� Alhaji Lukman ya Karaso har gabanta kamar zai dake ta, “Me ya sa kike cire kanki a cikin mutanen da zan dauki mataki a kansu? Ke ce mace ta farko da zan fara kiran “yan sanda su tafi da ke, su tuhumeki. Domin na fi zarginki, ZAMU TASHI sannan abinda yasa na hada da ‘yan aikin nan, saboda ban san aikin me suke yi da har za a yi wannan rashin hankalin wai a ce dukkanku babu wanda ya ji. Don haka idan kuka tsince ku a Police Station duk za ku yi bayani.� Yanzu Abban Sultan a kan yaran nan za ka zarge ni? Kana tunanin zan iya aikata wannan rashin mutuncin? Rashin imanina bai kai nan ba, duk abinda zan iya yi, ba zan iya kashe rayuwar idanun Nasrcen ba.� Kawai tasa kuka mai tsuma zuciya. A take nadama ya shige shi, haka kuma ya gaskata ba ita ba ce, to amma idan ba ita ba ce wace ce? Ta ya ya duk suna cikin gidan a ce an rasa gane wanda zai yi wa Nasreen hakan? A fusace ya fice daga gidan gabadaya. Kai tsaye gidan mahaifityarsa ya nufa ya zayyane mata komai. Hajiya Gwaggo ta dinga Salati tana Karawa. Cikin kuka take ambaton bala’i ga duk wanda ya aikata mata wannan mummunar aiki, Alhaji Lukman ya yi shiru yana sauraren addu’ar mahaifiyarsa haka kuma yana amsawa da Ameen. Yana sane da yadda mahaifiyarsa take Kaunar ‘yan biyun tamKar jininta. Karfe ukun dare agogon bangon ya buga, a wannan lokaci Alhaji Lukman ne tsaye cikin dogon nazari. An dade ba a yi abinda ya tashi hankalinsa ba, kamar mutuwar idanun Nasreen. Yana kallon yadda dan uwanta ke riKe mata sanda idan za su je Makaranta. Hankalinsa yana Kara tashi ne idan ya tuna duk ranar da Sultan ya dawo, me Zai gaya masa akan amanar Nasreen? Sultan ya dauki burin duniyar nan ya dora a kan yaran, yana hango masu tarin ilimi a nan gaba. Musamman Nasreen da take: gaf da sauke Alqur’ani. Yarinyar ta taso da wani irin ilimi na ban mamaki, wanda ya sake sanya Kyashi a zuciyar Hajiya Salma. Haka abinda ke damun ta, Hafsat ta zama cikakkiyar budurwa amma babu ko mutum daya da ya taba zuwa da sunan yana sonta. Amma Nasreen sai dai idan ba a ganta ba, sai an ce “Tubarkallah masha Allah.� Wannan abu yana damun_ Hajiya Salma, shi ya sa ta yanke shawarar mayar da ita makauniya tun kafin wataran Haidar dinta ko Sultan din da kansa wani ya ce yana sonta. Idan ta tuna hakan takan yi rantsuwa da sai ta batar da ita a duniyar gabadaya. Abba ya sami Kaninsa kasancewar shi ne babba a gidansu don haka suka zauna da Baba Sani ya yi masa bayanin tunaninsa da kuma hukuncin da ya yanke. Baba Sani, Anti Iyami, da kuma Hajiya Gwaggo duk suka yi na’am da wannan shawarar nasa. Suna zazzaune a falo, wayarsa ta yi Kara, ya daga yana murmushi. Haidar ya dubi Hafsat suka tabe baki, domin har sun gane idan har mahaifinsu yana fara’a to dan gaban goshinsa ne ya kira shi. Bayan sun gaisa ne, Sultan ya tambayi dukkan mutanen gida, daga bisani ya ce a baiwa Nasreen wayar. Abba ya Kwala mata kira, ta fito tana harba sanda, “Na’am Abbana gani nan zuwa.� Za ta fadi Abba ya Kwala kira, ‘“Nasreen kada ki fadi. Tsaya kawai in Karaso.� | Mamaki ya kama Sultan. Ya kasa gane me Abbansa yake nufi da kada ta fadi? Bai ce komai ba har lokacin da ya ji sassanyar muryarta tana kwarara masa Sallama. “Nasreen kina cikin “kuna cikin Koshin lafiya ko? Na ji Abba yana cewa kada ki fadi me ya sa za ki fadi?� Shiru ta yi_ ta rasa me za ta ce masa, sai kawai ta gaida shi, ta fara ba shi labarin Islamiyyarsu. Ya ce, “Yi min karatunku na jiya in ji.� Nasreen ta gyara murya ta fara karatun da kaf dakin suka kafe ta da ido. Yadda take baiwa kowanne harafi hakkinsa ya isa ya sanya ka fi Kaunarta. Sultan da ke kwance ya sake mayar da kansa ya lumshe idanunsa, dama kansa wani irin ciwo yake yi masa ga gajiya ga shi yana son yin barci. Jin Kira’anta yasa ya sake samun natsuwa, yana lumshe idanunsa har barci ya yi awon gaba da shi. � Nasreen tana saukewa ta shiga kiransa, “Dee.. Akwai gyara? Dee!� Ta cire wayar daga kunnensa, “Abbana duba ka gani ko ya kashe © wayar ne?� Abba ya karba yana sake duban Nasreen, ta burge shi Kwarai. Idan ya tuna rashin idanunta kuwa, sai ya ji kamar babu wanda ya kaishi zama cikin Kunci. Abba ya Kwalawa Nawfal � kira, ya shigo da Sallamarsa, ya dube shi, ‘“‘Nawfal kama hannun Nasreen ku koma ciki.� Nasreen ta ta yi murmushi wanda gefen kumatunta suka lotsa ta ce, “A’a Abbana ni ma ina son in zauna a wurinku, ko ba zan iya kallo ba, zan ji sautin muryar talabijin din.� Abba yana sake al’ajabin Karfin tawakkali irin na Nasreen, kwata-kwata bata da damuwa da irin wannan jarabawa da Allah ya yi mata. Nawfal ya riKe mata sanda suka Karaso falon ta zauna a Kasa tana aikin murmushi. Tana jin nishadi ne a duk lokacin da ta tsinci muryar Sultan yana mata magana. Hafsat tana son yin tsaki tana tsoron Abbanta, don haka ta yi shiru kawai tana kallon Nasreen cike da haushi da tsana. Abba ya sake kiran Sultan ya rarumi wayar ya manna a kunne yana sake lumshe idanu. Abba ya ce, “SP tashi mu yi magana.� Babu musu Sultan ya tashi zaune tare da tattaro natsuwarsa ya zuba su a kan Abban. “Ina saurarenka Abba.� Sai da Alhaji Lukman ya saci kallon Hajiya Salma sannan ya ce, “Jiya na je gidan Hajiya Gwaggo, ka san mitarta kullum ba za ka yi aure ba? Sultan na zuba maka idanu inga iya gudun ruwanka sai dai baka da alamun raya sunnar manzon mu. Ga Kaninka nan shima har ya tasa. Hafsat kuwa ko yau miji ya fito za_ ta yi aurenta. Don haka kana babba kai ya kamata ka fara yin abu mai kyau wanda zai sa su yi koyi da kai. Na yi maka magana ko kana da yarinya amma sai kace min babu. Mahaifiyarka ta nuna min wata yarinyar Kawarta da suka so su hada aurenku, nayi irin nawa binciken ba za ku shirya da yarinyar ba. Na san abinda za ka iya zama da shi ka sami natsuwa, amma ba ‘yar Hajiya Ladidi ba. Don haka mun taru da ni da ‘yan’uwana mun yanke shawarar za ka auri yarinyar Alhaji Mamman da ke karatu a Rasha. Yarinyar tana da natsuwa da kamun kai. Na tabbata ba za ka yi da-na-sanin zabina ba. Za mu daura auren baka nan, amma kana dawowa za ka sami goron bikin zan adana maka koda kuwa ya bushe ne sai ka ci. Ina fatan amsar magana ta za ta kasance eh ne ba a’a ba?� Sultan da gabansa yake tsananta faduwa ya rasa me zai cewa mahaifinsa? Kawai ya tsinci bakinsa da furta, “Duk abinda ka yanke a kaina Abba dai-dai ne. Wannan ne amfanin haihuwar, idan har za ka iya sanya yaronka ya yi, za kuma ka iya hana shi ya hanu. Abba na kasa amincewa wata mace ne, a dalilin duk yawancin mata halayyarsu iri daya ce. Ka dubi duk irin zaman da kake da Umma, yau a kan taimako Umma ta watsar da lamarinmu, ta tsame ni daga cikin ‘yan’uwana, ta sa suna yi min kallon wani mugun mutum. Duk irin ilimin Umma da kuma girman tarbiyyar gidansu, amma Umma ta kasa karbar Kaddara. Abba abokin aikina Mahbub macen da take tsananin Kaunarsa taso ta kashe shi, abokina Ashrmnaaan matarsa ce take kawo masa maza a cikin gidansa, abokina Haisam, matarsa ce take aikata madigo a cikin dakin aurenta, dakin sunnah! Ba ta taba jin tsoron akwai ranar da Allah zai hukuntata ba. Abba ireiren wadannan matsalolin suna nan da yawan gaske, ta yadda idan ba rufe ido mutum zai yi ba, ba zai taba iya yin auren ba. Ina tsoron aure sosai Abba. Amma tunda ka amince nima na amince.� , Abba da ke aikin murmushi ya ce “Kowacce da irin halayyarta, zai yiwu Fatima Dan borno ce ta sa. jarumanta a hakan, ba lallai a www.bankinhausanovels.com.ng a same su da irin halin ba, idan ma ansamu za ka gaa yanzu haka sun shiryu, tun daga lokacin da ta furta Alhamdulillahi ta kammala. Daman haushin abun daya ne, mutum yana aikata kuskure ya kasa tuba ya koma ga Allah, irin wadannan mutanen su ake gudu a rayuwa. Amma duk wanda zai tuba irin tuban da Allah ke so, ai abin a gode wa Allah ne. Sunan yarinyar Fa’iza bayan daura auren zan sa ta kiraka ku gaisa.� Hajiya Salma ta mike a fusace ta tsaya masa a tsakiyar kai, “Wai Sultan dinne ka zauna da danginka suka bashi mata? In haifi yaro wasu su nuna min sun fi ni iko da shi? Me yasa a lokacin da zan haife shi baka kira danginka sun amshi nakudar da nayi ba? Ban yarda da wannan auren ba, dole zabina zai aura. Daman nasan kai kake sawa yaron nan yake raina ni.� Sultan yana sauraren hayaniyar mahaifiyarsa hakan yasa ya yi saurin kashewa ya rike kansa, “Ya rasa asalin dalilin da yasa bai yi na’am da wannan auren ba. Zuciyarsa tana gaya masa akwai wani abu da yake so amma kuma ya rasa menene? Nasreen ta duKar da kanta tana jin damuwa sosai. Ta fi danganta damuwarta da irin tijarar Umma. Shi kuwa Abba har ta gama maganarta bai ce mata komai ba. Dukkansu suka mike fuuu suka fice. Falon ya rage daga Abba sai su Nasreen. Ya dubi Nasreen ya _ ce, ‘“‘Nasreen ke ma zan iya aurar da ke a kowani irin lokaci.� Nasreen ta yi dariya har jerin haKoranta suka bayyana, “Abbana, duka-duka shekaruna sha shida a duniya. Ai ban isa aure ba, anti Hafsat ce ta isa aure da Yaya Haidar. Abbana na Kasa a yi auren Dee, sai mu koma gidansa da zama ko?� Abba ya ce, “Kwarai kuwa.� Nawfal ya ce, “Abba ni kuwa na isa aure ko?� Gaba daya suka yi dariya. Haka Abba ya zauna a cikin su suna ta hirar su. Idan ya tuna Sultan zai dawo ya sami Nasreen babu idanu, sal yaji damuwarsa ta ninku. , Yau juma’a a yau ne Abba ya shigo hannunsa dauke da goro yana aikin murmushi. Hajiya Salma tana zaune idanunta sun yi jazir saboda kuka. Ajiye mata goron ya yi ya shige ciki wajen Nasreen. Goron ya dan gutsura ya ce, Nasreen bude bakinki insa maki wani abu mai zaKin gaske a baki.� Babu musu ta bude bakin tana fara’a “Abbana har na Kosa ka sanya min.� Ta bude bakin ya sanya mata ballin goro. Ta rufe bakin tare da taunawa, “Abbana akwai zakin sosai. � Ajiyar zuciya ya Kwace masa, � “Wannan goron na daurin auren Daddynki ne. Kiyi masa addu’a.� Murmushi ya _ wadaci zuciyarta zuwa fuskarta, “Allah ya basu zaman lafiya Abbana. Ka bani waya infara yi masa albishir.� Babu musu ya zaro wayarsa ya mika mata, bayan ya danna kiran Sultan. Muryarta yaji cikin sanyi tana magana, “Ina tayaka mura Dee, Allah ya kade fitina. Yanzu na ci goron daurin aurenka.� Sultan ya danyi jimm.. Alamun abin bai yi masa dadi ba, daga baya kuma ya ce, “Har andaura? Zan kawo maki tukuicin fara gaya min da kika yi. Allah ya yi maku albarka.� Sama-sama suke magana, wanda ta fahimci yana cikin damuwa, dole ta hakura da hirar suka yi Sallama. “Abbana sai naji kamar Daddyna baiyi farin ciki da wannan auren ba. Abba me yasa baka barshi ya nemi matarsa ba? Ka bani matarsa a waya ingaya mata matsayina na “yarsa don ta fara gyara mana dakina da na Nawfal tunda can zamu koma da zama. Abba ya ce, “Idan bai yi farin ciki a yanzu © ba, na tabbata akwai ranar da dole zai yi farin cikin. Akwai ranar da zai gode min. Matarsa kuma ki bari ta kusa gama karatunta ta dawo, da zarar ta kammala sai ayi bikin tarewarta.� Nasreen ta langwabar da kanta ta ce, “Haka Allah ke ikonsa. Na ci burin ganin irin matar da Dee zai aura. Ashe ba zan iya ganinta ba, sai dai in ji muryarta. Allah ya kawo mana ita lafiya.� Abba ya rage murya ya ce, “Insha Allahu ba zaki dauwama a hakan ba. Ki kwantar da hankalinki kinji? Ina jiran dawowar Sultan ne a shirya a fita da ke Kasar�waje Bata ce komai ba, sai duKar da kai da ta yi, hakan yasa Abba saurin ficewa yana girgiza kansa. Yana ficewa Nasreen ta sunkuyar da kanta ta kama kuka sosai. Furucin da Umma da su Hafsat suke jifansu da shi yana sanya ta cikin damuwa da tashin hankali. Tasha kwatanta tambayar Abba sai kuma ta fasa. Nawfal ya shigo ya dafa guiwowinta, “Nasreen menene? Me ya saki kuka a ranar daurin auren Daddy? mene ne ke damunki bai kamata kiyi kuka a irin wannan ranar ba.� Nasreen ta lalubi hannun Nawfal ta rike tsam. “Nawfal! Umma ce take ce min mu ‘ya’yan shegu ne, haihuwar Karkashin gada. Me hakan ke nufi Nawfal? Ko dai ba mu da alaka da gidan Abba ne? Idan bamu da alaKa me yasa muke diban kama musamman da Umma? Abin yana damuna.� Nawfal ya yi dariya, “Shi ne kike kuka? Mu ba shegu ba ne, Abba ya gaya min bata son mu ne kawai, ba wai don mun yi mata wani abu ba. Kuma mahaifinmu da mahaifiyarmu sun rasu ne a dalilin hatsari. Daddy shi ya yi ta kulawa da mu ya rene mu. Kuma ai ba mu kadai take yi wa hakan ba, hatta Daddy Sultan ba ta bar shi ba, kuma kin ga ita ta haife shi. Ki daina damuwa kin ji ‘yar uwata?�� Ta gyada kanta kawai tana jin zuciyarta babu dadi. Karfe daya na dare, ya dawo gidan, a matuKar gajiye. Tsaye yake daga bakin tagar yana kallon yadda hadari ya hadu walKiya kawai ake yi. Idanunsa sun riga sun soye baya jin ko alamun barci. Yana tsintar kansa a cikin nishadi da kuma tunanin abubuwa masu mahimmanci a cikin rayuwarsa, sai dai yau akasin hakanne kwance a zuciyarsa. Yana son mahaifinsa fiye da kowa, bai taba yi masa musu ba, haka baya son yadda ya nuna masa Kauna a lokaci guda ya watsa masa Kasa a idanu, yasan yin hakan zai jawo mutanen cikin gidan su suyi masa dariya. Ya kasa amincewa kansa wai shi ango ne, akwai igiyoyin wata a kansa. Bai taba kawowa kansa yin aure yanzu haka ba. Akwai matsayin da yake kwadayin hawa wanda idan yana da aure a yanzu, zai dinga kaucewa zuwa kwasa-kwasan nan na Karin girma, Nasreen! Zuciyarsa ta ambata da Karfin gaske. Ya rasa dalilin da kwana biyu yake yawan ganin yarinyar a cikin farkinsa tana neman taimakonsa. Gaba daya ya ji garin ya fice masa a rai. Gida kawai yake hange. Sannu a hankali ya fice daga cikin dakin ya tsaya a bakin Kofa yana kallon yadda ruwan saman ke zuba a hankali, Nawfal da Nasreen kadai yake hange. A irin lokacin nan ne Nasreen da ke kwance a Katon gadonta ta lume cikin bargo sal juye-juye take yi tana jin ciwon kan, yana sake ratsa kanta. Duhun da take gani kadai a idanunta yana damunta, bare kuma wani Katon abu da yake tokare a Kirjinta wanda yaki wuce wa haka ta rasa menene. Da gaske take kewar Dee dinta, ta Kosa ta ganshi ya dawo. Bata Kaunar ci gaba da zama a tare da Umma ta Kosa matarsa ta tare, su koma gidansa. Tashi ta yi ta yaye bargon da ta rufa, ta dinga lalube har ta isa ga bandaki. Alwala ta yi ta dawo ta fara gabatar da nafifili. Ta jima tana yiwa Sultan addu’a kafin ta bude Qur’ani tana karanta Suratul Maryam cikin natsuwa da zakin muryarta. Da safe ta gama shirin zuwa Makaranta jikinta yafi na kullum yin sanyi, ta jiyo hayantya, hakan yasa ta yafito Nawfal ta ce su je falon. Nawfal ya kafe Umma da idanu da ta rike Abba tana kuka tana fadin sai ya saketa ta bar masa gidansa, ba za ta iya ba. Ya sa danta ya rainata, yanzu kuma saboda a nuna mata iyakanta aka yi masa aure. Ta nemi a gaya mata wacece matar idan da hali a nuna mata hotonta amma yaki kallonta, don haka ita za ta bar masa gidansa. Haidar ne ya shigo yana duban mahaifiyarsu shi da Hafsat suka Banbare hannunta da Kyar Abba ya samu yana KoKarin ficewa daga gidan yana fadi a ransa zai yi maganinta. Kawai suka ci karo da Alhaji Mu’azzam! Kallon kallo suka aikawa juna sannan Abba ya dawo da baya suka gaisa babu yabo babu fallasa. Alhaji Mu’azzam. ya gyara zaman babbar rigarsa ya ce, “Anya Alhaji Lukman babu abinda ke damunka? Me yasa kake son mayar da kanka Karamin yaro ne? wanda bashi da ra’ayin kansa? Ta ya ya za ka yi wa Sultan aure wanda mu nan da muke dangin mahaifiyarsa bamu sani ba? Ko kana nufin bamu da hakki akansa ne? Akan ‘ya’yan zina kake son Sauya tsarin gidanka? To idan aure babu albarkar uwa auren nan bai dauru ba.� Abba ya yi saurin bashi amsa, “A fatawarka ba! Amma ni ne uban yaro kuma na aurar da shi ga diyar da ta dace. Zina kuma babu mai tabbacin wane yana aikata zina, sai idan yana da shaidu, kawo shaidun kuma akwai wahala. Ina yiwa kowa kyakkyawan zato. Kowa a duniyar nan yana da tarin matsala akansa, idan baka zina, kana shan giya, idan baka shan giya kana caca, idan baka aikata dukkan laifukan nan kana aikata mummunar laifi wanda yafi muni, wato shirka, hada Allah da wani. Ban ga dalilin da za ka dinga bin diddigin wani dole sai ka gano laifinsa ba. Kowa ya ji da tarin matsalarsa. Hajiya Salma kuma ta bi bayanka zan zo da abinda take buKkata, matar Sultan kuma bata isa ta santa ba, har sai ta tare, bare ta zagaya ta kashe masa auren. Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.� Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.� 6/5/22, 10:27 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 5 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.� Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.� ZAMU TASHI Daman ko bai ce ba, Hajiya Salma ba za ta iya tafiya ko nan da can ba. Don haka suka yi Sallama ya fice. Nasreen ta sa sandarta a Kasa tana KoKarin ficewa tun kafin fushinta ya sauka akansu. Nawfal ya rike mata sandar suka fice. Yau Sultan ya dawo garin, yana shaKar iskar garin Kaduna ya ji wata natsuwa tana shigarsa. Yana farin ciki yau zai ga twins dinsa. Mota tana yin parking a lokacin mahaifinsa ya fito zai fice. Farin ciki ya kama mahaifinsa, duk da sai da gabansa ya fadi. Rungume juna suka yi cike da farin ciki, haka yana nan a tsaye yana amsa gaisuwar ma’aikatan gidan. Daga nesa ya hangota fuskar nan dauke da farin ciki, tana rike da sandarta tana laluben hanya. Nawfal ya Karaso wurinta ya rike mata sandar yana cewa, “Idan na gadama insakar maki sandar inrigaki zuwa inyi masa oyoyo. Nasreen ta yi dariya, ta ce, “Ai nasan ba za ka yi min haka ba.� Sultan yana magana da mahaifinsa ya kasa Karasa abinda yake fada ya kafeta da ido babu ko kiftawa. Ya rasa wannan wani irin wasan kwaikwayo ne haka? Abbansa yabi inda yake kallo.da kallo, ba tare da ya furta komai ba. Nasreen tana Karasowa ta saki sandar ta ce, “Didina ka kama hannuna intabbatar da kai ne.� Sultan ya kasa yin motsi sai kallonta kawai yake yi. A zatonsa wasa take yi, amma yanzu ya tabbatar da babu wasa a lamarin nan. Nawfal ya kama hannun Sultan yana cewa, “Didi sannu da zuwa. Na riga wata yarinya rike hannun Didi.� � Nasreen ta saki dariya ta ce, “Babu damuwa zan rama watarana.� A lokacin ta sami daman rike hannunsa kawai ta rungume shi. Hawaye suna sauka daga idanunta zuwa bayansa. Yana jin digar hawayen hakan yasa ya dan rintse idanu ya ware su da Karfin gaske. A lokacin ne Hafsat da Haidar suka fito. “Sannu da zuwa Yaya.� Su kansu bai amsa masu “ba, hakan yasa suka tsaya suna duban yadda ya yi kamar wanda ya mutu a tsaye. Da gaske ya rasa me zai ce, wacce tambaya ya kamata ya fara yi, kuma idan zai yi din wa zai wa? “Abba Nasreen ta daina gani ne?� Wannan ‘tambayar ce ta Kwace masa da karfin gaske ta : fizzo kanta ta samu ta fito. Abba ya girgiza kai, “Nasreen bata ganin komai. Kaddara ce ta Ssameta, muna fatan mu samu mu cinye. Ku zo mu shiga ciki.� Hannunsa daya yasa ya dan shafi bayanta kafin ya dagota daga kwancen da take, yasa hannu ya dauke mata hawayen idanunta, sannan ya riKe hannunta suka shiga ciki Har yanzu jikinsa a sanyaye yake haka ya kasa gazgata abinda ya gani. Dakinsa ya shiga ya kintsa sannan ya fito falon ya iso har gaban mahaifiyarsa ya duka ya gaidata. Ita kanta Hajiya Salma ta sani, kaf cikin ‘ya’yanta babu mai biyayyar Sultan, sai dai wani ra’ayi nata da yasa take jin haushin abinda yake aikatawa. A hargitse ya yi maganar da yasa kowa yake kallonsa, “Abba ashe ba zan iya barin amana a rike min ba? Waye zai aikatawa Nasreen irin wannan mugun abun? Nasreen ta makance amma ba a taba gaya min ba? Ko waye ya aikata mata wannan abun ba zan taba daga masa Kafafu ba.� Ya ajiye maganar ba yadda ya kamata ba. Nasreen ta Karaso tana lalube har ta iso gabansa, “Dee, wanda ya aikata min hakan ya fi kowa sanin dalilin da yasa ya yi min. Kuma ni na yafe ma wanda ya yi hakan, Kada bakin ciki yasa ka furta wasu kalaman da suka cika yin nauyi. Kayi haKuri kamar yadda Abba ya ce min inkarbi Kaddarata haka kaima ya kamata kayi. Ni bana jin damuwa, ina gode wa Allah a yadda ya � bar ni. Idan kuma kace za ka dauki mataki bansan wurin wa za ka je daukar matakin ba, domin nima bansan wanda ya aikata min hakan ba.� Sultan ya dubeta yana jin zuciyarsa tana yi masa wani zafi. Yana kallon manyan idanun nan masu tsari yau sunée a rufe bata gani da su. “Nasreen zan yi bincike zan kuma dauki mataki kamar yadda na fada. Bincike biyu ke gabana kuma Insha Allahu duk sai na aikata su. Duk wanda ya aikata maki hakan babu ko shakka zai iya yin kisan kai.� Hajiya Salma ta yi maza ta tari numfashinta, domin Sultan gaf yake da zageta, “A’a ya isheni haka. Idan ka tashi yin binciken sai ka hado da ubanka domin shima a gidan ya kwana, ko kuma duk ka kama mu ka rufe har sai ka gama binciken. Idan za ka wuce kaje ka ci abincinka ka wuce, idan kuma tsayawa za ka yi ka samu a gaba kana yi mana tambayoyin rainin hankali Bismillah.� Sultan ya duKar da kansa-ba tare da ya iya furta komai ba. Abbansa ya dafa shi, “Sultan, ka yi haKuri, kullum da Nasreen nake kwana da ita nake tashi a zuciyata. Na rasa gano wanda ya yi wannan aikin. Ka je kayi bincikenka, nima idan na kama wanda ya aikata min wannan aikin insha Allahu zan tsaya sai naga anhukunta shi, ko wanene kuwa. Haka kaima ka dauki mataki, tunda a lokacin da za ka fara aiki, sai da kayi alkawarin tsayawa akan gaskiyarka, ko da kuwa ni mahaifinka ni ka kama da irin wannan laifin, don Allah ka dauki mataki kada ka ragawa mutum. Idan kayi hakan zan san dana ya tabbata a cikin dan sandan mai amana da gaskiya. Allah ya yi maka albarka. Zan � bayyana maka matarka da zarar ta kammala Makarantarta, wanda bana jin za ta dauki lokaci, domin tana shekararta ta Karshe ne. Tashi kaje ka ci abincin.� Sultan ya dan sami natsuwa da kalaman mahaifinsa, kafin ya tashi Nasreen ta fara tashi, tana lalube saura Kiris ta fadi ya Kwala mata kira, “Nasreen! Tsaya.�� Babu musu ta tsaya ya Karaso ya kama mata sandar suka fice. Hankalin Hajiya Salma idan ya yi dubu to ya tashi, Sai taga kamar da Nasreen ta makancen sai abin yafi sake yin muni, Hankalinta ya Kara tashi ne da Hajiya Ladidi ta tabbatar mata, tunda anyiwa danta aure, to Alhajin ne da kansa zai auri Nasreen din, domin kuwa shi namiji bashi da kunya. Zai reni abu ya kuma aureta. Hauka ne kawai Hajiya Salma ba ta yi ba, domin ita ta kasance mace mai zafin kishi, akan Alhaji Lukman za. ta iya kashe rai. Sultan ya tashi hankalinta Kwarai akan maganar binciken da ya ce, zai yi domin kuwa kallonsa take yi a matsayin mayen ‘yan sanda. A _ dalilin Kwarewarsa yasa ake ta Kara masa girma. Dole ta yi yunkurin daukar mataki akan abubuwan nan tun kafin tana ji tana gani danta ya garkameta a Police Station ‘yan jaridu su sami daman watsata a duniya. Haidar ta aika ya kirawo mata Sultan yana shigowa ta dube shi sosai. “Kana jina? Idan na sake jin ka sami ‘yan aiki kana yi masu bincike ko Kannanka ban yafe maka ba. Nasreen wani Kato ya shigo ya rufe mata baki ba mu ji ba, ya yi mata wannan abin. Kai baka yarda da Kaddara ne? Kai ka sani ko mugayen da suka kashe mahaifiyarta ne suka gane akwai yaran a gidan nan? Ni shi ya sa tun farko ban so rikon su ya zamana a nan ba. Bana son kaje garin tone-tonenka ka jawo mana masifa har cikin gida.� Sultan ya zubawa mahaifiyarsa idanu kamar mai son gano wani abu. Hankalinta ya Kara tashi ta ce, “Laaahh! Ni kake kallo haka kamar ka sami barauniya? To tashi ka wuce na gama magana. Bai ce komai ba, bai kuma tashin ba. Can ya nisa ya ce, “Umma wai har cikin dakinta aka shiga aka aikata hakan duk baku sani ba? A lokacin kina…� A zafafe ta ce, “Ina dakin ubanka ne a lokacin. Ingama ce maka ka bar maganar nan amma kuma saboda tsaurin idanu za ka koma yi min tambayoyi? Sultan wai yaushe ka sauya ne? . Zuwan yaran nan rayuwarka sun sauya mun dana. Yauwa Sultan wai wacece matarka? Na yi bincike sosai antabbatar min ba ‘yar gidan Alhaji Mamman ba ce. Anya ya kamata ka amshi auren nan kuwa? Bana son yazo baka yi sa’ar mata ba, dan nuna min ita ko a hoto ne.� A lokaci guda bayan ta gama masifar ta yi Kasa da muryarta kamar mai rada. Sultan da ya gaji da tsugunnon da yake, ya jawo wata ‘yar kujera ya zauna yana fuskantar mahaifiyarsa, bayan ya dauki dabino | daya ya Sa a bakinsa. “Umma ban santa ba, ban taba ganinta ba, ban san sunanta ba, haka ban san ko ‘yar gidan waye ba. Kasan da ta tafi karatun ma ban san shi ba. Kawai abinda nake buKata addu’a Umma. Idan kika yi min hakan kin gama yi min komai. Kuma insha Ailehu zanyi maku biyayya wajen karbar zabinku.� Umma ta Harare shi, “Wajen karbar zabin mahaifinka ko kuma zabina? Ni zabin da na ‘baka ka karba ne? Ina son ka bude kunnunwanka da kyau ka ji ni. Ka je ka sami mahaifinka kace sai ya hadaka da matarka ko gaisawa ce ku dinga _ yi. Ya zama dole musan wacece da me za ta shigo gidan. Idan ba ta yi ba, sai ka botsare masa ka saketa kawai ta kama gabanta.� Muryar Abba suka ji yana magana, “Allah kadai zai iya shiryaki Salma. A duk ranar da shawararki ta yi tasiri a zuciyar danki ina tabbatar maki sai kin yi mugun danasani. Ba zan bayar da hoton ba, bazan kuma hada su ba, har sai lokacin da na gadamar yin hakan. Kai Sultan zo ka wuce.� Babu musu ya mike ya fice abinsa yana al’ajabin mahaifiyarsa. Ita kuwa hajiya Salma dubansa ta yi ta ce, “Ka dai san babu kyau labe ko? Babu daman inzanta da dana sai ka hau masifa?� Dubanta ya yi ya ce, “Labe? Waye dan naki? Yaron da kika ware shi a_cikin ‘yan’uwansa kika jawo masu rashin shaKuwa da juna? Ai da wannan kadai idan na bar ki Salma sai Allah ya hukuntaki.� Bai tsaya saurarenta ba ya sa kai ya fice abinsa. Sultan yana nan ‘tsaye, bayan ya tabbatarwa mai tsaronsa ya wuce kawai ga shi nan zuwa. Yana nan a tsaye yana kallon tsakar gidan. Hafsat ta fito da wani dutse ta ajiye a hanya ta koma ciki. Ba ta kula da shi ba, haka shima bai kula da abinda hakan ke nufi ba, domin kuwa tunaninsa ya yi nisa. Nasreen ta fito tana lalube sai kawai ta ci tuntube da Katon dutsen nan ta fadi a wurin.Sultan ya zaro idanu a lokaci guda kuma Hafsat ta fito daga maboyarta tana kwasar dariya. Zata wuce kenan ta ji anfinciko ta. A razane ta dago tana hada idanu da yayanta ta tsure, “Yaya me nayi?� Dau! Ya dauke ta da mari, daman kuma hannunsa babu kyau, a take fuskar ta kumbure ~ ta yi jazir, abinka da farar mace. Ya sake daga hannu ya yi ta kwada mata. Sannan ya watsar da ita. A gujen gaske ta yi cikin gida, domin wannan shi ne karo na biyu da ya taba dukanta a duniya, kuma duk akan mutum daya. Karasowa ya yi inda Nasreen din ke zaune ta yi shiru kawal. Yasa hannu ya kamota suka koma inuwa suka zauna. Yana jin dadin Kare mata kallo, baya gajiya da hakan. Ciwon da ta dan ji yake dubawa, bayan ya kama hannunta. A hankah yake shafar ciwon wanda yake sanya mata wata kasala, tana sake lullumshe idanunta, labbanta kamar za ta yi © magana, amman hakan ya gagara. Yanayin da ta shiga yasa mamaki ya kama shi, tambayar kansa yake ko dai ba Nasreen ba ce? Irin yanayin nan masoya kadai ke iya kasancewa a cikinta. Dayan hannunta tasa ta rike hannunsa tana girgiza kai, “Dee.. Na daina jin zafin yanzu.� Murmushi kawai yaji, kafin kuma muryar Umma ta wargaza masu yanayin da suke ciki. “Sultan! Yanzu akan yarinyar nan za ka yi wa Hafsat irin dukan nan? Ba ka da hankali ne ko mene ne haka?� Sultan ya yi magana kamar baya son yl, “Umma idan kannena suka yi laifi babu daman in hukunta su kenan?. Haba Umma meyasa zaki wareni daban a cikin ‘yan uwana? Laifi ta yi na hukuntata. � Ta yi Kwafa kamar za ta kai masa duka, “Ita ta kusa da kai ba ta laifi ne ko me? Kada ka sake dukar min yara na gaya maka.� Bai bata amsa ba haka bata daina masifar ba, har sai da ta gaji ta juya abinta. Shi kuma ya kamo hannun Nasreen suka shiga mota. Wani wuri ya kaita © mai dauke da sanyi irin na korama. Tana zama ta shaki irin Kamshin da wurin yake yi, ta ce, “Deedina ina jin wani irin yanayi mai dadi a jikina. Dee da ba ka nan na yi ta kewar ka, amma kuma ina yi maka addu’a.� Sai da ya zauna bayan ya gama kallonta sannan ya ce, “Nima nayi kewarku ke da Nawfal kamar insa a kawo min ku, sai nayi tunanin karatun ku. Nasreen zaki iya tuna wanda ya watsa maki abu a idanu?� Hawaye suka gangaro fuskarta kamar daman tana jira ne, “Deena bansan waye ba. Ka bar maganar nan abinda Allah ya aiko kenan.� Jawota ya yi ta kwantar luf a Kirjinsa tana sakin Wani irin ajiyar zuciya. Hakan ya haifar da abubuwa masu girma da wahalar fassarawa a tsakanin su. Sultan kenan! Kowa kallonsa yake miskili mara son hayaniya, haka alamu sun nuna idan ya kama mai laifi baya sarara masu. Idan ka ganshi tare da Nasreen za ka iya rantsuwa ba Sultan dan sanda bane. A kunnenta yayi magana, “Kada ki damu, akwai zaman da zamu yi da abokaina akan wata matsala, don haka zanyiwa Dr. Aslaf magana, akan idanunki zai bamu shawarar Kasar da ya kamata mu tafi da ke sai a duba idanunki. Idan ba haka ba, waye zai aurar min Nasreen dina a haka?� Wani irin tafiya ta yi mai kama da tafiyar barci. Ga iska yana Kara kada su. Tana murmushi tana magana kamar wacce ta sha wani abin maye, “Deena, zan zauna tare da kai ba zan auri kowa ba.� Dagata ya yi saboda da gaske ya gane tana cikin wani yanayi. “Tashi muje Office dina.� Girgiza kai ta yi, “Ina son indauwama a nan wurin. Kamshin filawowin suna sanya min nishadi da sanyi a zuciyata, wanda rabon da in ji � hakan na jima. Dee wani abu ke tsaya min a Kirji yana min zafi sosai, ko nasha ruwa baya wuce wa.� Wannan Karon tausayinta ya kama shi, Nasreen ta yi Karama da yawa da shiga irin wannan yanayin, “Ki dinga addu’a Nasreen kin ji? Mu je Office dina akwai abinda zan dauka.� Da isar su Office din, “yan sanda suka taso ° suna sara masa, shi dai yana rike da hannun Nasreen. Gaba daya mutane idanunsu akan Nasreen yake, wani ma cewa ya yi koda take makauniya zai iya aurenta inhar Oga zai ba su ita. A kujera ya ajiyeta, a lokacin ne kuma aka gaya masa wani case ya ce, a shigo da matar a gurguje. . � Tana shigowa tana bayani bai dago daga abinda yake yi ba bare ya dubeta, “Yallabai mijina ne ya zaneni,� Yana rubutunsa ya ce, “Me kika yi masa har ya duke ki?� Ta share hawayenta ta ci-gaba da magana, “Ya musuluntar da ni ne, ya raba ni da kowa, ya ce min addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, nasha wahala da iyayena har na rabu da su, na zabe shi da addininsa. Amma tunda na aure shi kullum sai ya yi min gori akan addininsa, kullum idan na yi kuskure sai ya ce min matsalar tubabbe kenan. Yallabai ina son a raba aurena da shi, zan koma addinina, ko dan inhuta da gorinsa da na ‘yan uwansa.� Tun bayan da ta ambaci ta koma addininta ya ajiye rubutun yana dubanta. Damuwa ce shimfide a fuskarsa. Har yaushe musulman mu za suyi hankali? A hakan wasu suke son jawo wadanda basa addininsu su dawo addinin su? Bai yi magana ba, har sai da ya gama nazari sannan ya ce ta fada inda za a ga miinta. Ta kwatanta ‘ya bada umamnin a je a kawo masa shi yanzu. Ya dubi matar ya ce, “Amma kafin in ce komai, daina daukar musulunci haka yake. Musulunci abu ne mai sauki da kuma dadi. Idan kina cikin musulunci zaki sami hanyoyin warwarewar matsalarki, wanda ina ganin baki bi hanyar bane shi ya sa kike dan samun matsala. Haka kuma mu a cikin addininmu akwai jarabawa, da Allah yake yiwa bayinsa. A Karkashin jarabawar nan zaki sami hanyar shiga Aljannah. Misali a cikin Alqur’ani akwai waraka a ciki. Ko malamin da ya musuluntar da ke bai gaya maki hakan ba?� Sunkuyar da kanta Kasa ta yi ta ce, ‘“Malamin ya yi min bayani. Amma bai gaya min musulmi zai lya yiwa wanda ya aro addininsa gori ba, haka bai gaya min akwai duka a cikin sharuddan aurenku ba. Ina zuwa Islamiyya har yau ban ji inda malaman ta ce ana gorin addini ba.� Sultan ya rintse ido yana kallon rubutun suna komawa kamar yashi. Saudat! Ita ta fado masa arai. Mahaifiyar Nasreen da Nawfal. Tasha gori akan addininmu amma kuma tana rike da mu. Hatta mahaifiyarsa har yau tana yi wa su Nasreen gori akan addinin da Saudat ta aro. Sultan ya girgiza kansa, “Hakane, haramun ne ma musulmi ya ci zarafin dan uwansa musulmi. A cikin addininku akwai na banza akwai na kirki, haka muma a cikin addinin mu, akwai irin hakan, Amma mu ba mu gorin addini, haka kuma ke kin fi shi rashin zunubi, saboda kin tuba kin musulunta. Addinin musulunci akwai dadi idan kika natsu a cikinsa. Dokokin mu basu da tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.� A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?� Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.� Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.� 6/5/22, 10:27 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 6 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.� A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?� Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.� Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.� ZAMU TASHI Bala ya shiga yayyanka idanu, “Yallabai a yi min afuwa, sharrin shaidan ne ba zan sake dukan ta ba.� Sultan da zuciyarsa ke zafi, ya dubi Copral Ya ce, “Na tsani mutum ya aikata laifi da gangar yace sharrin shaidanne. Har yaushe musulmin Kwarai zai dinga barin shaidan yana shigowa cikin rayuwarsa, yana wanzar masa da sharri a cikin gidansa? Don Allah dauke min shi ka hukunta min shi har sai ya bani tabbacin shi ne shaidanin.� Bala ya gigice yana bayar da hakuri hakan yasa Sultan sake watsa idanunsa akansa, “Gaya min sharrinka ne yasa kake dukan matarka, kake yi mata gori akan ta aro addininka ko kuwa har yanzu na shaidan ne?� : Bala ya ce, “Yallabai sharrina ne kuma nayi kuskure.� Sultan ya ajiye biro yana dubansu, “Malam Bala musulunci bai yarda miji ya dinga dukar matarsa ba, domin ba ankawo maka ita bane domin ka dinga dukanta ba. Musulunci bai yarda da gori akan komai ba, bare har akai ga gori akan babban abu, wato addini. Musulunci bai yarda mumini ya dinga tauye hakkin iyalansa ba. Kai hakkin wani ma a waje haramun ne bare akai ga hakkin matarka. Yanzu kasa matarka ta hada mu gaba daya tana yi mana kudin goro, tana kallon malaminka da ya musuluntar da ita a matsayin mugu, tana kallon iyayenka da ‘yan uwanka a matsayin mugaye. Daga Karshe sai ta ji ta tsani musulunci tana neman ta koma wancan addinin da ka sameta a cikinsa. Bayan kai da kaje za ka aureta baka ji lokacin da malaminka ya ce hakkinka ne ka yi mata duka, da gori ba. Malam Bala ka ji tsoron Allah. Ka sani sai Allah ya saka mata, kamun Allah kuma ba.irin kamun mu bane mu hukuma. Kurkun Allah ba irin namu kurkun bane. Ka kiyaye abubuwan nan, za ka fi Karfin gidanka, cin matarka, shanta, rashin lafiyarta kaucewa gaya mata munanan kalamai. Domin kalamai wannan idan kana gaya mata su marasa dadi zaka wayi gari kalamanka su kasheta. Idan kuma kaima jahili ne ba ka san ilimin addinin musulunci ba, ka dauko ‘yar jama’a ka aurota kana yi mata koyarwa irin na jahilai don Allah kaje ka nemi ilimin addinin nan, kada kayi mana asarar mutum daya daga cikin musulunci. Ka � ka kare hakkin matarka, da mutuncinta. Ina son Copral ka tafi da su, a kawo min malamin da ya daura aurecn da kuma wanda ya musuluntar da ita. “Ni Office dina idan anzo irin wannan case din sai na bi diddigi naji dalilin da yasa ake hakan. Idan mutum ya yi alKawarin gyarawa bai gyara ba, ina da hukunci kala-kala da zai sa mutum ya gyara ba don yana so ba. Bana daukar shirme. Haka bana barin a ci mutuncin mata! Domin ita mace ta wuce komai, sai da ita za ka sami natsuwa, ita ce ta dauki cikinka tana amai, tana kasa barci cikin dare saboda laulayi, a hakan za ta girka maka abinci, ta kai maka ruwan wanka. Tana renon cikinka tana renonka. Idan ta tashi haihuwa, ta kai sati tana naKuda. Wata ko nan take mutuwa, ko shekara ba za a yi ba, za ka Karo wata. Idan ta tsallake ta Haifa, ta shayar ta lura da lafiyarsa. Idan bai da lafiya ta zauna cikin dare tana nemo dabara, kai kuma kana can kana barci. Ta wanke masa kaya ta wanke naka. Mace dai ita ta kawoka duniya ita ta reneka. Shi ne don rashin hankali ka rasa abin wulakantawa sai ‘ya mace? Ka tambaya wane ne Abdullahi Lukman! Bana daukar irin wannan shirman.� Jikin Bala da Karima ya yi matuar sanyi, hakika D.P.O dinnan na daban ne, yasan hakkin dan adam. Ya dubi Nasreen yaga hawaye shimfide a fuskarta. Hankalinsa ya tashi don haka ya taso ya dawo kusa da ita, yasa yatsa yana dauke hawayen. “Nasreen menene? Waye ya bata maki?� Fuskarta dauke da murmushi ta ce, “Babu wanda ya bata min. Ina godewa Allah ne da nayi sa’an dan uwan mahaifiya mai sanin ya kamata. Allah kadai yasan wahalar da mahaifiyata tasha kafin ta kawo ni gidan duniya. Allah ka sakawa mahaifiyata. Allah kasa mahaifina bai wulaKanta min ita ba. Daga Karshe Allah ya saka maka da renonmu da kayi tun muna cikin tsumma.� Sultan ya mike ya dago ta, Zuciyarsa take gaya masa ya rungumeta, Don haka ya mayar da ita Kirjinsa ya rufe da hannayensa, Sannu a hankali natsuwa ta ratsa su, Nasreen ta sake lafewa a Kirjinsa tana sakin ajiyar zuciya. Da kansa ya ga dacewar ya janyeta, ya kamo hannunta suka fice. Mansur da ya gama kallon hotunan Nasreen ya zuKo tabarsa yana fesarwa a fuskar su Hajiya Ladidi. Hajiya Salma ta Kufula don ta tsané rashin tarbiyya, za ta yi magana, Hajiya Ladidi ta matse mata hannu, dole tayi shiru suna ci gaba da kallonsa, “Hajiya wannan yarinyar ta hadu. Soyayyar Karya kuke son in nuna mata, amma a zahirin gaskiya ni sonta nake yi da yaske. Kuma Wallahi! Wallahi!! Sai na aure ta da Karfin tsiya. Wannan ai kalata ce. Hajitya ku bar kudinku wannan da kudina zan aureta.� Hajiya Salma da Hajiya Ladidi suka yi ‘murmushin jin dadi. Abu kamar wasa soyayyar Nasreen ya mamaye ko ina na zuciyar Mansur, wanda har ya kasa hakuri ya shirya cikin shigar kamala ya je gidan da sunan hira. . A falo Hajiya Salma ta tare shi, ta kuma turo Naareen. Gaba daya ya shagala wajen kallonta, kwafsi daya ne, matsalar idanu, amma shi sannan babu shi a zuciyarsa, babban burinsa ya mallaketa ko ta halin KaKa.��Wanene kai? Me kake nema a wurina?� Sai da ya shafi sajensa kafin ‘ya ce, “Sunana Mansur. Sonki nake yi, kuma Wallahi sai na aureki.� “Ni kuma bana sonka, ka tafi tun kafin Abbana ya zo ya sameka anan.�Www.bankinhausanovels.com.ng Mansur ya mike yana tunkarota. A lokacin Abba da Sultan suka sawo kai. Da Karfi Abba ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihirraji un.� Wani irin jiri ya nemi ya kwashe shi ya riKe jikin bango, yana sake watsa idanunsa akan Mansur. Tuni Nasreen ta mike a gigice tana cewa, “Abba Wallahi ban san shi ba, ban taba jin ko muryarsa ba, Umma ce ta ce dole sai na zo, amma ban san shi ba. Ka yarda da ni Abba ba zan yi maka, Karya ba. Ta sake rushewa da kuka.� _ Shi kuwa Sultan ya rasa dalilin da yake jin zai iya shake Mansur ya mutu har lahira. Don hakane ya wuce Abba ya shake shi, wanda duk Karfi irin na Mansur ya kasa Kwatar kansa daga irin rikon da Sultan ya yi masa. Idanunsa suka firfito waje. Umma da su Hafsat suka rugo a guje sakamakon jin Kakarin Mansur, Umma ce ta Kwace shi, sakamakon marin da ta dauke Sultan da shi, tana wani irin huci, “Sake shi mara mutunci kawai, Ina ruwanka idan saurayi ya zo wurinta? Ko za ka hanata aure ne? lyye Nace aure za ka hana tayi Nine nan nayi masa izini tunda ya ce yana sonta da aure, ai ba jiKata zamu yi mu sha ba, dole za ta yi aure.� Abba dai yana tsaye Kafafunsa duk sun yi sanyi. Sai yanzu ya sami ikon yin magana, “Kai zo ka fice min daga gida tun kafin ka yi nadamar haukan da kake shirin yi. Idan na sake ganinka a gidana zan yi maka mafi munin wulakanci. Nasreen share hawayenki baki da laifi. Laifin wancan ne, kuma zan dau mataki.� Ya fada yana nuna Umma da yatsa. Mansur har ya kai bakin Kofa ya waiwayo ya kafe Nasreen da idanu, “Ina nan dawowa in aureki matata. Zan aureki ko da kuwa wannan ne abu na Karshe da zan yi in mutu.� Sultan ya nufo shi, ya riKe wuyan rigarsa, “Za ka mutu kuwa! Idan wannan bai zama abu na Karshe da za ka yi ka mutu ba, zai zama ganganci na Karshe da za ka yi ka bakunci lahirar. Idan ka san da gaske kai mara kunya ne, anjima ba sai gobe ba, ka sake taka Kafafunka a Kofar gidan nan. Fice!� Ya tunkuda Kyayarsa zuwa waje. Ya koma kawai ya zauna a kujera ya yi tagumi yana kallon mahaifiyarsa. Abba ya nuna ta da yatsa ya ce, “Ke ce ajalina Salma. Idan na fadi na mutu ke ce sila.� Hajiya Salma ta ce, “Oh ni kada ka sa min sharrin kisa. Yarinya dai dole za ta yi aure. Kai kuma lafiya kake kallona kamar tsohon maye? Ko dukana nima za ka yi ne?� Mikewa ya yi kamar zai fita sai ya ji muryar Haidar yana cewa, “Gaskiya Abba ka tsani Umma da yawa, idan ba haka ba, menene a ciki don Nasreen ta yi soyayya? Duk kuka tashi hankalinku kamar kun kama ta da kwarto? Kuma…� Sultan ya juyo ya watsa masa idanu tare da mika dan yatsansa alamun gargadi. Hakan yasa Haidar hadiye kalamansa, domin bai san cewa bai fita daga falon ba, da babu abinda zai sa shi tofawa. Sultan ya kama hannun Abbansa suka fice kawai. Shi dai Abba a ranar ko barcin kirki bai yi ba, wani tunani ne a cikin zuciyarsa da yake tunanin irin kuskuren da zai iya tafkawa, inhar ya zubawa Umma idanu ta Sauya masa tsarinsa a kan yaran. Haka acan dakin Sultan ya kasa barci, sai tunani fal cikinsa. Dole ya koma dakin Nasreen tana kwance cikin bargo, yasa hannu ya yaye bargon. Abinda ya ganine yasa shi saurin rufeta yana ambaton dukkan addu’ar kariya daga fadawa _ tarkon shaidan. Motsinta ya ji ta tashi ashe ba tayi barci ba, tana KoKarin yaye bargon ta rungume shi, ya dakatar da ita ta ta hanyar rike bargon. Sai a lokacin ta tuna da irin kayan da ke jikinta, don haka ta shiga laluben hijabinta. Shi ya dauko ya taimaka mata tasa. “Nasreen! Me yasa kika fito wajen dan iskan nan? Don Allah Nasreen ki taimakeni inrike amanar da mahaifiyarki ta bani akanku. Na yi mata alKawarin zan iya, ki taimake ni in mutu ba tare da antambayeni yadda na rike amanarku ba. Na kasa barci Nasreen, ina da abubuwan ci gaba da nasa a gabana, amma saboda ku na kasa aikata komai, ina son in aurar da ke, Nawfal ya kama aikinsa, sai insamu nima inKarasa ayyukana. Za ki taimaka min nima burikan nan nawa su cika?� A gigice take magana, “Wallahi Dee ban san shi ba, ka yarda da ni. Ina dakina Anti Hafsat tazo ta yi min jagora muka je falon. Ya ce yana sona, nace bana sonsa. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yaso a daren ya shiga dakin Hafsat, sai kuma ya canza tunani. “Allah ya yi maki albarka koma ki kwanta kiyi barci.� Babu musu ta koma ta kwanta, amma kuma bata sakar masa hannun ba, Zuba mata idanu ya yi yana jin wasu abubuwa suna sake canza mazauni a cikin jikinsa. Yana jin_kansa kamar ba shi ba, Dayan hannunsa yasa ya mayar da gashin kanta baya da suke Kokarin | rufe mata fuska. A hankali ya matso sosai ya bata fake a goshi. Wannan lamari yasa Nasreen nutsewa wata duniya. Wanda har bata san lokacin da ya zare hannunsa ya fice daga dakin ba. Dakin Nawfal ya leKa ya same shi zaune akan dadduma yana Sallah. Ibadan yaran yana burge shi, ya sake. gode. wa Allah da, dukkan abubuwan da ya dora su akai babu wanda suka kuskure masa; A hankali yayi maganar da ya ratsa kunnuwan Nawfal. Nawfal kada ka mance ni a cikin addu’arka. Haka, kada ka mance da mahaifiyarka.� Ya sa kai ya wuce, Dakin Hafsat haka yake yana da yawan leKa Kannansa domin tabbatar da lafiya lau suke kwance. Yana lekawa ya sameta zaune tana waya. Tana ganinsa ta katse wayar tana zare idanu, “Da wa kike waya? Ba zaki bani amsa ba!� Jikinta na rawa tace “Abokin karatuna ne,� Sultan ya zaro ido, “Abokin karatunki a wannan daren? Haba Hafsat! A wannan lokacin da ya kamata ace kina ganawa da Mahaliccinki? Ance ki fito da miji ayi maki aure, kin ce baki‘da samari. Amma yanzu gashi kina waya da garjejen Kato ko? Ki kiyaye, ki kama mutuncin kanki, watarana ke uwa ce.� Juyawa ya yi abinsa ya fice. so Sultan yana Office ya sami kira daga abokansa, sun hadu za su fara meeting. Da sauri ya Karasa dukkan abubuwan da ke gabansa sannan ya kama hanya. Gaba dayan su sun sami isowa shine na Karshe. Tajuddeen Abdulsalam jarumin littafin (Kowa ya kwana laftya), Haisam � Hayat, Jarumin littafin (Zuciya), Aslaf Mai nasara Jarumin littafin (Sir) Mahbub Muhd Daura, Jarumin littafin (Mafarin lamarin), Ashmaan Ashraf Jarumin littafin (Akaran kaina) Sai kuma Soja, Khamis § Idris Jarumin littafin (Akaran kaina), ga kuma Al-ameen Rabi’u, jinin Sarauta jikan sarki, Jarumin (Akwai_ lokaci). Dukkansu suna zaune kowa da abinda yake yi. Sultan ya basu hannu yana murmushi, “Ga -ni kuma, jarumin Rubutacciyya! Na gaida Karfin Zumuci irin na ‘yar mutan Borno, hakika tayi Www.bankinhausanovels.com.ng namijin KoKari da bata barmu mun watse ba, da ba haka ba, Ashmaan shi ne mutum na farko da zai fara datse mana zumuncin nan.� Dukkansu suka yi murmushi_ sannan Mahbub ya bashi amsa, “Idan Ashmaan bai kashe zumunci ba, ai kai sarkin watsar da zumunci, za ka watsar da komai. Kai dai kawai Allah ya sakawa ‘yar mutan Borno, ita ta riKe mu ta dage lya lyawarta da ba haka ba, da tuni kanmu ya rabu.� Dukkansu suna ji da kansu, kowa ya ci ya ture. Haka ga -dukkan alamu suna_ cikin kwanctyar hankali suna samun kulawa daga matan su. “Tuzuru bude mana taro da addu’a Kila sanadiyyar hakan ka samu ka shiga daga ciki.� Aslaf yake tsokanar Sultan. Murmushin ya _ yi sannan ya yi addu’a mai tsawo. Suka shafa. Wannan taron gaba dayansa akan Sultan akayi shi, saboda shi ya gayyato su. Don haka ya fara magana, “Da farko dai andaura min aure. Sai dai bana son doguwar magana, ko Korafi, Abba ne ya daura auren, ban santa ba, ban taba ganinta ba, yanzu haka wai yana jiran ne ta gama karatu ayi bikin tarewa. Ban wani damu ba, domin bani da budurwa, hakan ke nuni da ina da bakin jini Irin na wannan yaran�� Ya nuna Mahbub da hannu, duk suka yi murmushi. a hakan sai da suka yi korafin meyasa tun a lokacin bai gaya masu ba? Share su ya yi kawai ya ci gaba, “Ina da babban Case a hannuna na kisan kai, Case din akwai buKatar natsuwa da kuma sanya hankali a cikinsa: Mahaifiyar Nasrecn nake son sanin waye ya kasheta tsawon shekaru goma sha shida? Me yasa aka kasheta? Ta bani wani littafi da wasu hotuna, suna cikin wannan files din. Ban taba budewa ba, daman burina inkammala da kulawa da su, sannan insan,abin yi. Duk wanda ya kashe ta babu shakka ya yi kisan nan ne saboda gudun kada ta tona masa asiri, nayi alkawarin idan mahaifina ne mai kisan nan, saina daukar mata fansa, Sai kuma Nasreen da aka watsa wa guba aka makantar min da ita.� Tajuddeen ya fara magana, ““Wannan case din case ne mai girma, musamman na kisan nan. Haka duk wanda ya yi kisan bai san Nasreen da Nawfal suna nan a raye ba, da sai sun nemi kashe su. Wadannan abubuwan da ke hannunka za su tabbatar mana da komai. Don haka zamu yi lya yin mu muga abinda Allah zai yi. File din kuma za ka iya bani, ko kuma ka ba Mahbub, ko Ashmaan. Sai mu fara bincike. Abinda binciken mu ya bamu sai mu sake dawowa ayi meeting ko ya kuka gani? Dukkansu suka yi na’am da wannan shawarar. Al-ameen ya dube su, “Maganar idanun Nasreen, zan dauki nauyin fita da ita waje, ina da wani aboki da ya Kware da aiki akan irin wannan. Kafin nan zan fara bata kulawa a Asibitina. Dukkansu suka ce basu amince ba, sai kowa ya bada gudumawarsa a kan samun lafiyar Nasreen. Sultan ya rasa bakin magana sai duban su kawai yake yi. Da ace haka abokai suke da hadin kai tabbas da duniyar ma gaba daya ta zama abar sha’awa. Haka aka tashi taron Sultan kuma ya damka komai a hannun Barrister Tajuddeen, ba tare da ya bude ko shafi daya ba. Mahbub ‘yan sandansa suka bude masa mota, haka ma Sultan sauran kuma duk suka ja abinsu suka bace bat! Sultan yana isowa gida, ya watsa ruwa kafin ya iso falo inda mahaifinsa ke zaune. Bayan ya gaishe shi ne, yake gaya masa yadda suka yi da abokansa, daga Karshe ya rufe maganar da fadin za a yi wa Nasreen aiki a idanu, abokan suka dauki nauyi. Wannan magana da Hajiya Salma da ke shirin shigowa falon ta ji, shi ya tashi hankalinta taja da baya ta koma. Ko tambayar mijinta ba tayi_ ba ta dauki gyale. A gidan Hajiya Ladidi taja burki. Tana shiga ta sami Mansur a dakin, da alamu sun gama sheKe ayarsu da Hajiya Ladidi ne ya fito yana gyara .kwalar riga. Yana ganin . Hajiya Salma ya daure fuska, “Yauwa Hajiya ki gaya mata sai na dauki mataki akan dan nan nata sannan zan koma indauke Nasreen. Narantse da Allah sai na dauketa. Amma kafin nan sai na gama gyarawa danki zama.� Hankalin Hajiya Salma ya tashi ta ce, nan fa daya. Kada ka kuskura ka taba min lafiyar da. Za ka iya yin komai amma banda taba Sultan. Kuma Wallahi idan ka ce za ka taba shi sai kayi danasani, domin kana ganinsa nan ba Karamin tsayayye bane.� Mansur ya yi Kwafa, “Na fi ki sanin hakan ni da ya shake ni na nemi sheKawa lahira. Amma duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.� Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.� Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.� . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu � sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.� 6/5/22, 10:27 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 7 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.� Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.� Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.� . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu � sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.� ZAMU TASHI Hajiya Ladidi ta saki dariya sosai sannan ta ce, “Ashe ‘yan iskan nawa suna da rana? Shi yasa nace maki a hada aurensu da ‘yata amma wannan kafaffen mijin naki ya hana. Wannan aiki ne mai sauki, Rainbow dinnan dai shi za mu sake sawa ya yi aikin nan.� A nan suka gama kintsawa akan idan Nasreen za ta je Makaranta a nan za a saceta ita da Nawfal. Tana isowa gida ta sami Sultan yana gyara mata gashinta, da take ta mitan yana damunta ya taimaketa ya aske mata. Bai ce mata komai ba, ya tattare mata gashin ya Kulle a cikin Katon ribom. Hajiya Salma kamar za ta yi magana, sai kuma ta hadiye da ta tuna da komai ya kusan zuwa Karshe. Mikewa ta yi tana fadin, “Dee kama ni ka kai ni daki ina son shirin zuwa Makaranta, bansan inda Nawfal ya tafi ba. Babu musu ya kamata ta shiga dakin, ya fitar mata da kayan Makarantarta kafin ya fice daga dakin ya tafi neman Nawfal. A tsakar gida ya same shi yana Kwallo, ya Karasa ya tallabi Keyarsa tare da riko kunnensa daya. “Kai baka jin magana ko? Karfe nawa yanzu?� Nawfal ya rike hannun Sultan yana rintse ido, “Wayyo Deedi ka yi hakuri don Allah na tuba ba zan sake ba.� Hannunsa riKe da kunnan Nawfal ya tasa shi gaba har cikin daki. Da suka tashi tafiya Makarantar shi ya dauke su da kansa ya kai su har Makaranta. Daren ya tsala wuri ya yi shiru, baka jin motsin komai, sai na tsuntsaye. Nasreen ta fito tana lalube a yanzu ta haddace inda komai na gidan yake, don haka ta nufi dakin Sultan. Yau bai kwana a office ba, yana gida don haka ta iso har kan gadonsa. Yana kwance yana kallonta, haka ya zuba mata ido ne kawai ya ga iya gudun ruwanta. Lalubansa take yi har ta tabbatar ga inda yake, sannan ta kwanta shiru a Kirjinsa, “Deena me yasa bana iya barci sai da tunaninka? Me ke shirin faruwa da rayuwata ni Nasreen? Ina jin damuwa a kwana biyun nan, ina jin kamar zan rasa ka. Deee ka tashi ka gaya min mene ne ke shirin faruwa da ni? Dee.,.� Ta ja sunansa tare da dora hannayensa a bisa fuskarta da ke kwararar hawaye. Shi dai bai ce komai ba, sai kallonta da yake yi. Ya zama dole ya ajiye wasan kwaikwayon nan shi da Nasreen ya tabbatar mata da yana sonta. Irin abinda Nasreen take ji, shi ya fi ta jin fiye da hakan. Hawayenta ya kafe da ido yana dubanta. Da gaske tana bashi tausayi musamman rashin idanun da yafi so fiye da komai. Idan ta ware idanunta tana dubansa, sai ya ji kamar ta kwashe dukkan kuzarin jikinsa ne. Ta ya ya zai iya fitowa ya ce Nasreen yake so? Me yasa? Idan ya yi hakan zai sa rayuwar Nasreen a cikin matsala! Haka kuma ba zai taba samun natsuwar da yake nema ba, saboda mahaifiyarsa duk za ta hana hakan, Sannan ba Zai iya ce mata yana sonta ba, har sai ya gano su waye iyayenta? Me ya jefa mahaifiyarta a cikin irin wannan halin bakar rayuwar? Yatsunta ya kafe da ido gabansa yana tsananta fadiwa. Babu inda ya tsunta ya bambanta da na Haidar Kaninsa. Kafafunta kuwa iri daya da nasu. Wannan abu yana sake daure masa kai Sai yanzu yake takaicin Kin bude hotunan nan ya fi tunanin a nan ne zai gano komai. Sai dai yasan ko wasu irin hotuna ne ba zai wuce hotunan . mahaifiyarta ba, shi kuma idan har zai dubi hotunan nan sai mutuwar Saudat ta dawo mata sabuwa fil! ‘““Nasreen.. Ya kira sunanta, wanda yasa ta yi firgigit! Ba ta yi magana ba, don haka ya dora, “‘Nasreen kina jin son Deedinki a cikin zuciyarki? Nasreen babu aure a tsakanina da ke. Ki dauke ni a yadda kike daukana a da kin ji? Nasreen Abbana shi ne mahaifinki anboye ne saboda wasu dalilai idan lokaci ya yi zaki san komai kinji? Nima da farko da bansan hakan ba, irin abinda kike ji shi nake ji, daga baya na sawa raina hakuri. Sannan idan auren za a yi, ban yi maki girma ba Nasreen? Yaro Karami zan baiwa aurenki, wanda bai wuce sa’an Haidar ba. Kin ga ni na wuce talatin ko? Maza _ ki share hawayenki.� Kukanta ya Karu da yawa, bata jin za ta iya cire abinda ke cikin zuciyarta, ba ta jin za ta iya rage son Sultan wanda bata ko tantama da soyayyarsa aka haifeta. Tana son tasan wacce irin alaKa ce ke tsakaninta da Deedinta. Duk da ta kadu da kalamansa, amma hakan baisa ko digo daya daga cikin soyayyarsa ta ragu ba. Tana sonsa da gaske. Ta shirya wa tunkarar kowacce matsala a kansa. Sake damKe hannunsa� ta yi tana jin duk wata kunya ta kau a idanunta, tana jin za ta iya gaya masa komai. “Dedena, ina son ka, zan iya mutuwa Ko babu aure a tsakaninmu zan zauna da kai. Ba zan taba iya yarda da wani namiji ba, yin hakan zai gurgunta rayuwata. Ka rike ni a gidanka zan zauna da matarka. Don Allah ka roKe ta kada ta raba ni da kai. Ban san kowa ba sai kai da Abba. Kai ka koya min wannan rayuwar, Sai dai na yi nisan da ba za ka iya cire min abinda ke cikin zuciyata ba.� | Kalaman da Nasreen take ambatowa sun yi matuKar bashi mamaki, ta yaya Nasrecn ta iya irin wannan kalaman? Ya aka yi Nasreen tasan soyayya haka? Yaushe ta cire kawaicinta ta iya furta masa wadannan kalaman? Tausayinta ya kwaranyo masa, baya jin zai iya hada Nasreen da kishiya bare har ta cutar masa da ita, Yana yi mata irin son da duk wanda ya kama da cutar da ita zai dauki matakin da sai duniya ta girgiza da irin matakinsa. Ya danganta rashin kawaicinta a yau da rashin idanunta, ya tabbata da za ta hada idanu da shi, ba za ta taba samun Karfin halin da za ta fada masa wadannan kalaman ba. Share mata hawayen ya yi ya rungumeta tsam a Kirjinsa. A lokaci guda yake jin kamar shaidan ke son cin galaba akansa, idan ya yi la’akari da yadda komai ya sauya daga cikinsa. Bisa labbansa yake magana, “Ina jin irin abinda kike ji Nasreen.� Shiru ya biyo bayan hakan, sakamakon saKon da ya bata mai matuKar tasiri. A lokaci guda ya zame kansa, yana jin meyasa zai zama mutum na farko da zai gurbata amanar da Saudat ta bashi? Sai da ya natsu sannan ya ce, “Nasreen ki tashi ki koma dakinki.�Shiru ta yi sakamakon yadda Kafafunta suke rawa. Haka ta tsinci kanta cikin wani baKon al’amari. Yawun baki wani irin abu ne mai kama da guba, idan suka hadu wuri guda suna sanya zazzafar soyayya da kuma shaKuwar dake da wahalar rabuwa. Hakan ce ta kasance da Nasreen @ wannan daren. Hannunta ya kama suna mikewa tsaye ta yi baya za ta fadi, ya yi saurin dawo da ita ta fadi a jikinsa, “Nasreen! No kada ki yi min haka. Ki Karfafa jikinki don Allah. Ki tuba ga Allah wannan abun haramun ne kin ji? Kada ki sa shi a ranki kin ji?� Ba tayi magana ba, amma ta dan Karfafa jikinta. Da kansa ya rakata dakinta ya kwantar da ita, tare da addu’a sannan ya jawo mata bargo ya rufeta. “Sleep!� Ya furta tare da hure mata fuska. Luf idanun suka sake rufewa. Ta shaki Kamshin bakinsa tana sake rurrufe idanun da daman a rufen suke. Ya tashi ya kashe mata wuta ya fice abinsa. Wannan lamari akan idon Umma ya faru, hankalinta idan. ya yi dubu to ya tashi. Abinda ya sake ba ta mamaki Abbansa ashe yana tsaye shi ma yana kallon su. Duban fuskar Abban ta yi da mamaki yadda yake ta murmushi. Ta sake leKa fuskar Abban ta tabbatar da murmushin yake yi. Kafin ta yi magana Sultan ya Karaso falon ya bude frij zai dauki ruawa. Domin ji yayi makoshinsa ya bushe saboda halin da ya tsinci kansa a ciki. Ji ya yi kawai an shaKo shi, kafin yayi wani abu, ya ji saukar mari ko ta ina @ fuskarsa, Sai huci take yi, “Kai kai! Baka isa ka kasheni ba, Zina kake aikatawa da Nasreen? ‘Ya’yan mazinatan ne suka shigo rayuwarka su Bata maka tarbiyya? Wallahi idan ka kasance mazinaci ba zan taba yafe maka ba a cikin gidan nan, sai na tsine maka kabi duniya! Kaf zuri’ata babu mazinaci, kai kuwa baka isa ka jawo min wannan abin kunyar ba. Dama sonta kake yi dan ubanka! Za ka yi min magana ko sai na kasheka a gidan nan?� Ta daga hannu da nufin sake marinsa, Ta ji anriKe hannunta. Abba ya tunkudeta gefe saura kadan ta kifa. Yana dubanta yana huci, “Insha Allahu ban haifi mazinaci ba, bana fata idan Allah ya jarabceni da da mazinaci ba zan tambaye shi dalili ba, haka ni nasan ban zagi ‘ya’yan wasu ba, sai dai idan alhakin zagin da kika yiwa ‘ya’yan wasu ne ya sauka akanki. Haka ba dai dana Sultan ba, sai dai idan ‘ya’yanki da kika lalata da irin halayyarki. Wannan yaron da kike gani, shi ne dan da nake fatan ya gado ni kuma na gode Allah. Kada ki sake danganta min da da zina, yin hakan zai jawo maki mummunan bacin rai Wallahi!� Umma ta dube shi da mamaki, “A gabanka fa ya fito manne da ‘yar iskar can!� Abba ya yi saurin tare numfashinta, “Sai _me? Idan kin ganshi rungume da ita nace sai mene? Kuma ina son ki gane, kin taba fuskar yaron nan na Karshe! Sultan ya wuce mari a yanzu sai dai nasiha. Kai Sultan zo ka wuce dakinka. Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya. Maza ka wuce.� Sultan ya juya kawai yana jin dacin furucin mahaifiyarsa akansa. Ya maimaita Kalmar zina tafi a Kirga. Hakan yasa ya kasa barci. Tunanin ya yi nesa da Nasreen da iyayensa suka darsu a zuciyarsa. Ita kuwa Nasreen ta lashi labbanta da suka yi laushi ya fi a Kirga. Tunanin Sultan ya ci gaba da gallabanta. A haka har barci barawo ya sace ta Washegari suka shirya zuwa Makaranta, a lokacin Sultan ya jima da barin gida. Akan hanyarsu ta dawowa ne aka tare direban su aka cunkusa su a wata mota. Nasreen dai tana rungume da Nawfal bakinta bai fasa addu’a ba. Wani irin Kunci ya ziyarceta, Yanzu mutanan nan ina za su kaita? Ita dai damuwarta kada a rabata da dan uwanta. Da zarar ta tuna da Sultan Sai taji wasu hawaye suna kwaranya. Nawfal dai ko Kwakkwarar motsi ya kasa yi. Tafiya ake yi tun suna sa ran sauka har suka sadakar da kwanakin su a duniya ya Kare. Sai wajen Magriba aka bude Kofar mota aka cillo su waje sannan suka Kara gaba. Nawfal ya dubi Nasreen cike da tausayawa ya ce, “Nasreen kin ga wata duniyar suka ajiye mu. Yanzu ina zamu dosa?� Nasreen ta ce, “Duba ka gani akwai jama’a a garin?� Ya dudduba ya ce, “Daji ne wurin babu wasu jama’a. Amma zo mu Kara gaba ko zamu sami abinda zamu ci.� Haka suka yi gaba babu wanda suka samu sai wata mai siyar da abinci da take shirin rufe wurinta. Nawfal ya fara magana, “Sannu. Don Allah wani gari ne nan?� Matar ta dube shi ta ce, “Ku kuma daga ina haka? Wannan garin Katsina ne Kankia. Me ya kawo ku nan?� Nawfal ya dan yi shiru, “Wallahi wasu ne suka sato mu suka kawo nan. Don Allah ina Zamu sami makwanci? Sai ki daukeni aikin wanke-wanke kina ba mu abinci, ° Matar mai suna Amina ta nuna masu Kofar shagonta wanda akwai rumfa, “Sai dai ku dinga kwana a nan domin ba zan iya baku makwanci ba, kun san duniyar babu amana. Ita wannan makauniya ce?� Ya dan durkusa, “Mun gode _ sosai. Makauniya ce� Ta dan tausaya masu, sannan ta cire zanenta daya ta basu ta ce, su lulluba. Har ta tafi ba ta daina waiwayarsu ba. Ita kuwa Nasreen umartar Nawfal ta yi da ya samo masu ruwa suyi alwala. Bayan sun yi alwala ne suka raba dukkan sallolin da ke kansu sannan suka dan rabe. Nasreen tana jin yunwa, amma kuma ta kasa gayawa Nawfal yunwa take ji, saboda kada ya shiga damuwa. Shi kansa yunwar yake ji amma ya kasa furtawa. Can ya tuna da awaran da ya siyo daga Makaranta don haka ya ciro jakarsa ya fitar, a lokacin ne kuma Nasreen ta jiyo Kamshi da fara’arta ta ce, ““Nawfal menene wannan kuma?� Sai da ya kai bakinta ta gutsura sannan ya bata amsa, ““Dazu ashe na siya wara na manta ne. Zai ishemu mu ci.� A nan suka cinye warar, Nawfal ya dibo masu ruwa suka sha. Cikin dare dukkansu suka kasa barci saboda azaban cizon sauro. Shi dai Nawfal sai korarwa Nasreen Sauron yake yi. Ga kwanciyar Kasa, ga cinnaku, ga sanyi da ke ratsa su. Nasreen ta dinga kuka ba tare da ta bari Nawfal ya sani ba. Can ta yi magana a hankali, “Nawfal waye zaiyi .mana haka? Me yasa za a raba mu da danginmu?� Nawfal ya girgiza kai, ‘“‘Nasreen idan kina tunanin su Abba danginmu ne ki daina tunanin hakan. Da wahala idan ba tsinto mu aka yiba. Rannan naji Umma suna magana da wata Kawarta take cewa Deedi ne ya rakito mu, ya kawo masu masifa cikin gida. Amma tabbas! Mu ba “yan gidan bane. Ya zama dole mu mance duk wani jin dadi, mu fuskanci abinda ke gabanmu. Mu koyi zaman wahala mu koyi nema da kanmu, mu koyi maraici, tunda dama mu din marayu ne. Idan muka ce zamu yi ta zama a gidan nan watarana Umma za ta sa ashana ta Kona mu. Kin ga ta nakasa maki idanu, yanzu haka ita ta sa,a kawo mu nan, Don Allah Nasreen mu mance gidan nan mu jure dukkan gwagwarmayar nan watarana sai labari.� Nasreen ta gigice da kalaman Nawfal, don haka ta bashi labarin yadda suka yi da Sultan a daren jiya, ta ci gaba da cewa, “Yanzu Nawfal mu dauka ba mu hada komai da su Abba ba, idan muka barsu munyi masu adalci? Wane hali yanzu su Deedi suke? Sun raine mu tsawon shekaru goma sha bakwai, yau don mun yi fushi sai mu guje su? Da wannan zamu saka masu kenan Nawfal? Ya kamata muyi tunani.� Nawfal ya ce, “Nasreen bamu yi laifi ba idan muka yi hakan. Zamu bi su da addu’a wanda duk nisan inda muke zai je ya same su. Maganar kuma babu aure a tsakaninki da Deedi ya dai fada maki hakanne domin baya son ki damu da lamarinsa, yana hango tashin masifun da zaki iya shiga ne idan har Umma tasan akwai soyayya a tsakaninku. Don Allah mu mance baya mu fuskanci gaba.� Nasreen ta fitar da kukanta fili, wanda har yasa zuciyar Nawfal ya karaya, “Nawfal ka yi min addu’a domin na fada cikin hatsarin son Deedi. Ba zan iya raba kaina da irin wannan soyayyar ba, domin bansan lokacin da ta shige ni ba.� A lokacin wani Katon sauro ya cije ta ta kai wa kanta duka, Nawfal ya share hawayensa ya ce, “Zan taya ki da addu’a insha Allahu komai zai zama labari.�Www.bankinhausanovels.com.ng A can garin Kaduna kuwa, Sultan yana Office ‘ya ga kiran mahaifiyarsa, abin ya ba shi mamaki domin ba zai tuna ranar da ta kira shi ba. Ya dauka da Sallama tun kafin ya gaisheta ta fara magana, “Sultan su Nasreen ba su dawo daga Makaranta ba, ko kuna tare ne?� Mikewa ya yi tsaye kafin ya ce, “Umma ban gane ba? Ina shi direban yake?� Umma ta tabe baki, “Babu direba, babu su Nasreen. Allah ya sa ba wani gantalin aka wuce ba.� Sultan ya katse wayar kawai ya hada ‘yan sanda suka fita a cikin motarsu. Kai tsaye hanyar Makarantar suka nufa, a nan suka sami direba a yashe, ga mota a gefe, haka mutane sun fara taruwa. Shi ya fara sakkowa daga motar ya tallabo Direban, Sumewa ya yi don haka yasa a kawo masa ruwa ya watsa masa, gabansa yana tsananta faduwa. Yana farfadowa ya ce, “Ina su Nasreen? Ina suke!� Ya daka masa tsawa. A gigice yake magana, “Yau na shiga uku! Wasu suka zo a farar mota suka tafi da su.� Sultan ya shake dircban nan jikinsa yana rawa, “Idan wani abu ya sami su Nasreen ina tabbatar maka sai na kashe ka! Ka gaya min da su waye ka hada baki aka sace min su? Gaya min waye ya turo ku?� Sultan fa ya haukace, ya fita hayyacinsa. Da Kyar ‘yan sandan nan suka Kwaci direba, sannan suka sa shi a baya tare da wani dan Sanda aka samu aka lallaba Sultan ya shiga motar gidansu dan sanda ya shiga ya wuce da shi gida. A lokacin Abba ya dawo, don haka ya Karaso gaban Abba jiki asanyaye. “Abba..� Ya ja sunan mahaifinsa, ya kuma kasa furta komai. Sai dan sandan nan ne ya korawa Abba “bsyani Da Karfi Abba yake Salati. Sultan kuwa ya kasa magana, sai idanunsa da sukayi jazir kamar gauta. Jikinsa har rawa yake yi. Ita kanta Umma yadda taga yaron nata ya sauya a lokaci guda yasa jikinta mugun sanyi.,,Gaba daya suka shiga falo, Abba ya baiwa dan sandan umarnin a bi ko ina a sanya cigiyarta. Kafin ka ce me? Gari ya dauka an sace “yan biyu mace da namiji, Sultan ya zauna a kujera jikinsa asanyaye babu Kwari, Haduwarsu kawai yake tunawa a jiya, ya kasa magana ya kasa duban Abbansa. Shi kuwa Abba tashin hankalinsa ya ninku da ya tuna bai sauke Katon nauyin da ke kansa ba. “Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.� Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace � ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.� Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar � gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu 6/5/22, 10:28 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 8 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.� Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace � ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.� Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar � gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu ZAMU TASHI ba? Allah ya kara nesanta su da mu, yasa ko a lahira haduwar ta yi wuya.� Hafsat ta mike ta ce, “Tabdijan! Nasreen matar Yaya Sultan? Allah ka tsaremu da hada zuri’a da shegu. Allah ya ga abinda ya gani.� Haidar ya mike yana fadin, “Af yanzu sai a nemo wata matar amma dai ba Nasreen ba.� Sultan bashi da Karfin furta komai, sai idanu da yake bin su da shi. Haka Abba ya kasa magana, ya tabbata yau zai yi barcin wahala na rashin ‘yan biyun da ya Kwallafa ransa akansu. Yaran suna da matuKar shiga rai. Sultan kuwa tunda ya duKar da kai bai sake motsawa ba. Shiru-shiru babu wanda ya sake yin magana hakan yasa mahaifinsa ya tsargu. Yana dago shi yaga baya motsi hakas yasa Abban sake gigicewa ya Kwala masa kirs yana girgiza shi. Umma da su Hafsat suka fito 8 guje. Ganin baya motsi yasa Umma ta dora hannu akai tana ihu. Haka ma Hafsat. Shi kanshi Haidar sai da ya yi Kwalla domin suna son? Yayansu fiye da komai, kawai hudubar uwarsu suke dauka. ) Cikin Kankanin lokaci aka isa da shi asibiti. Umma ta rike keken da ake gungura shi, tana bin nursis din Abba ya fincikota daga jikin keken yana huci, “Ina ruwanki da shi? Dama kina sonsa kika ganshi a cikin wani hali kika sake tura shi ciki? Ashe kina sonsa kike watsa masa kalaman batanci? Idan Sultan ya mutu ke kika kashe min da kuma ba zan barki ba, dan sai nayi shari’a da ke. Salma ina matukar zarginki akan bacewar yaran nan. Yau da ina da hujja a hannuna da babu abinda zai hana ban kai ki Kara ba. Amma a juri zuwa rafi.. Abba ya koma gefe kawai yana sharar Kwalla. Ya sani, ya sani duk inda Nasreen suke suna cikin mawuyacin hali. Ya fi tausayawa rayuwarsu fiye da ta dansa. Umma kuka take yi sosai, ba don danasani ba, sai don halin da danta yake ciki, Sultan yana farfadowa ya zubawa mutanen cikin dakin idanu. Tabbas ya tabbata ba mafarki yake yi ba kamar yadda yake fata ba. “Abba angano inda su Nawfal suke? Abba a ina za su kwana? Wa zai dubi maraicin su ya basu abinci? Wa zai taimaka min ya yi aikin lada ya kula min da su? Abba a ina zan samo su? Shi kenan rayuwarsu Nasreen ya tafi kenan? Me ya sa ba ka gaya min Nasrecn matata ce ba? Da ka gaya min da na gaya mata Kalmar da take ta dako ta ji daga bakina. Da ban yi mata Karyar babu aure a tsakanin mu ba. Da na bata kulawa a matsayinta na matata ko da sau daya ne tak! Abba ba zan taba sararawa wanda ya yi min wannan yankan Kaunar ba.� Abba ya zura masa idanu yana kallon yadda Sultan ya fita hayyacinsa a wuni guda. Shi ya san Sultan zai shiga halin da ya fi wannan ma, akan su Nasrecn. Sunkuyawa ya yi yana shafa kansa, “Sultan kai ba yaro bane, bare in ce har yanzu baka gama tantance menene Kaddara ba. Kana da hankalin tantance baki da_fari. Rayuwarmu bata tafiya a dai-dai dole sai jarabawa ta dinga ratsa mu. ‘Insha Allahu Nasreeri za ta dawo ku ci gaba da rayuwa a matsayin miji da mata. Kada ka mance Nasreen RUBUTACCIYA ce, tun tana cikin mahaifiyarta take haduwa da Kaddara, har yanzu tana rayuwa. Dole duk inda Nasreen take ta dawo domin bata da wani wurin da ya wuce nan gidan. Ka kwantar da hankalinka mu dage da addu’a.� Lumshe idanunsa ya yi yana tunanin a wani hali suke a yanzu? Wasa-wasa sai da Sultan ya yi kwanaki biyar yana jinyar kansa. Ko da ya dawo gidan ma sai ya koma yi masu yajin magana. A take ya kira su Mahbub ya gaya masu komai, hakan yasa dukkansu suka baro aikin su suka iso wurinsa. Barr Tajuddcen ya fara magana kamar kullum, “Sultan akwai sarkakKiya a_ cikin wannan lamarin. Ta ya ya hakan zai faru? Ta ya ya za a sace Nasreen da dan uwanta? Dole mai wannan aikin yana kusa da kai ne. Nasreen -matarka ce? Daman da ita Abba ya daura maka aure? TirKashi! Abin akwai sarKaKiya.� Haisam ya karBe da cewa, “Ko dai mahaifinsu ya gano akwai ‘ya’yansa a gidanku ne? Zai yuwu sai kawai ya aiko a sace su.� Aslaf ya girgiza kai, “Ni ma tunanin da nake yi kenan, idan ba haka ba waye zai sace su?�� Mahbub ya girgiza kai, ““A’a mahaifinsu bai san da zaman su ba, bana jin shi ne zai yi wannan aikin. A dai sake bincike.�Ashmaaan ya dago yana duban kowa, har anfidda rai zai yi magana, sannan ya tanka, “Ku natsu sosai ku dubi maganar Mahbub, Idan har mahaifin nasreen yasan suna raye, ba zai bari su kawo wannan shekarun ba, zai aika a yi farautar ransu kamar yadda ya yi na uwarsu. Amsar wanda ya aikata hakan yana wurin Sultan domin kuwa shi ne yasan mutanen da take takun saKa da su.� Khamis ya dan murmusa ya ce, “Dadina da kai kaifin basira dan mutan Sudan. Maganar gaskiya ba mahaifinsu ba ne ya yi aikin nan, wanda ya aikata laifin nan makusancin Sultan ne, na kurkusa. Sultan kayi sakaci gaskiya. Yaran da suke dauke da abubuwa masu rikitarwa, za kabar su kara zube? Kana da irin matsayin nan a hukumance amma kake barin ~wani lagwanin direba ya jasu zuwa Makaranta? Ai yaran nan tsaro suke bukata. Ka mance na yi irin wannan sakacin aka tafin min da mata? Ka mance Ashmaan ya yi irin wannan gangancin aka kusa kashe masa mata? Daga Karshe me ya biyo baya? Dabararsa ta Kwace shi, da ya dauke matarsa ya turata London. Shi Mahbub da ya fimu dabara, ai hada matarsa ya yi da ‘yan sanda ya kuma sanya doka mai tsanani akanta. Yanzu dai menene abin yi?� Al-ameen ya ce, “Aikin gama ai ya gama. If not da gidajen daya daga cikin mu ya kawota aka boyeta har a gama bincike, mu zaKulo masu laifukan. Yanzu maganar bincike a kan wadanda suka yi kisa dole a dakata tunda shaidun sun Bace. Kawai mu mayar da hankali wajen nemanta.� Sultan ya girgiza kai, “Mahaifiyata ce kadai ta tsani Nasreen da dan uwanta tsana mai tsanani. To kaina ya kulle ko ita ce za ta sanya ayi hakan domin nisanta su da mu? Sai kuma wani dan iska da ya taba zuwa wai yana sonta Wai sai ya aure ta. A lokacin bansan andaura mana aure ba, zafin da mahaifina ya dauka ya bani mamaki. Su dai nake zargi.� Barrister Tajuddeen ya danyi rubutu ya -. dago yana duban Sultan, “Sorry to say Sultan, Umma ita ce asalin suspect! Amma kuma tafi Karfin mu gaskiya. Sai dai mu bi komai a hankali har Allah ya warware mana ‘wannan tashin hankali. Sannan zamu sa malamai suyi ta sauka suna addu’a. Allah ya bayyana maka matarka da dan’uwanta,� Gabadaya aka amsa da Amin. Sultan ya dan shafi sajensa ya ce, “Zan bar garin nan. Ba zan iya zama a cikin gidanmu ba, sai in ga kamar zan ga Nasreen. Yarinyar da bata ganin gabanta ya za tayi rayuwa a wurin da babu tattali? Ba zan yi aure ba, zan tsaya in jirata har ta dawo gareni.ba� Babu wanda ya nemi ya dakatar da shi, domin dukkansu sun dandani dacin soyayya. Haka suka tashi suka yi musabaha sannan duk suka rabu. Sultan yana isowa gida ya same su suna zaune ya gaida su, sannan ya dube su fuskar nan babu fara’a. “Abba nan da wasu lokuta insha Allahu zan koma Abuja da aiki. Sai a taya ni addu’a.�� Abba ya dube shi da tausayawa ya ce, “Sultan ya zama dole kayi aure. Ba zan zuba ido ka kai wannan shekarun babu mata ba. Ka yi hakuri kada kayi fushi, ka raya sunnar manzo. Kullum matsayi sake zuwar maka yake yi, amma ka kasa haKuri da Kaddararka.� Shiru ya yi yana sauraren Abbansa. “Abba zan jira ta har ta dawo.� Shiru dakin ya yi har yaushe za a tsaya jiran dawowar Nasreen? Wa ya san rana? Kyale shi kawai ya yi domin ya samu natsuwa. Umma zata yi magana ya daga mata hannu. Sultan har ya fice zai shiga dakinsa ya dawo da baya yana kallon Kofar dakin Nasreen da babu kowa a ciki. Girgiza kansa kawai ya yi ya wuce., Duk wasu kayayyakinsa da yasan zai iiya nema ya tattara su wuri daya. Hoton da suka dauka su uku ya kafe. da idanu. Shi Nasreen sai kuma Nawfal. Ya jima yana kallon hotunan kafin ya zuba su a cikin kayansa. Cikin gaggawa aka daga shi zuwa Abuja, a lokacin ne kuma ya sauya sabuwar rayuwa. Da asubahi suka tashi suka gabatar da Sallah, a lokacinne kuma mai abinci ta 1so tana Kokarin hada murhu. Nasreen da Nawfal suka gaishe ta, Ya jawo hannun Nasreen ya zaunar da ita a gefe guda, ya taya mai abincin hura wuta. Duk ruwan da ake dibo mata shi ya-diba mata, hakan yasa ta fahimci yaron yana da zafin nama, duk da jikinsa yana nuna hutu. Gari yana yin haske mutane suka shiga zuwa siyan abinci, a lokacinne kuma ta zuba masu nasu abincin ya {Karasa inda Nasreen take zaune ta yi tagumi ya janye tagumin yana dubanta, ‘‘Nasreen ki daina damuwa bana so. Ga abincin ki ci, ni zan je inwanke mata kayan miya.� Tausayin Nawfal ya kama ta, yau kwatakwata bai huta ba. Tana cin abincin tana kuka. Ta rasa ta yadda za a yi ta taimakawa dan uwanta yau yasha wahala sosal. Basu suka samu suka zauna a inuwa ba, har sai da aka kira Magrib. Haka idanuwan mazan nan ya koma kanta. Da zarar suka fahimci makaunlya ce sai su tausaya masu. Haka basu yarda angane a wurin � suke kwana ba. Sai da dare ya yi sannan ya zagaya ta baya ya ajiye mata ruwan wanka, saboda Amina ta basu aron bokiti da soso. Ya ce, “Nasreen ta shi kije ki yi wanka.� Babu musu ta tashi ta zagaya. Yana nan tsaye yana gadinta har ta gama kintsawa, ta mayar da kayan makarantarta…RiKe hannun Nawfal ta yi, tana kuka, “Nawfal kana shan wahala da yawa. Nawfal ba zamu iya wannan rayuwar ba.� Shima riketa. ya yi “Zamu_ iya Nasreen, ki Karfafa zuciyarki zamu _ iyaWatarana sai labari.� Da haka ya samu yake Karfafa mata guiwa, Haka suka kwana cikin cizon sauro da cinnakai, gaba daya jikinta sun yi rudu-rudu saboda azabar cizo. Washegari ta ce, “Nawfal ba zamu nemi wani wurin kwanciyar ba? Na gaji da, nan. Sai da ya yi murmushi sannan ya ce, “Allah ya bamu.sana’a mai dan Karfi ko Daki ne mu kama sai mu ga abinda Allah zai yi. Nasreen ta yi na’am da bayanan Dan uwan nata, wanda ya fita nisan tunanin, A kwanaki biyar kadai Nasreen ta fita hayyacinta, shi kuwa Nawfal har ya fara sabawa da wahala da kuma kwanar siminti, Sultan. kullum yana ¢ikin ransa, yasha komawa gefe ya yi kukansa yadda ransa ke so, ya dawo ya share hawayensa. Ana hakanne akayiwa Amina Sata a shago, aka likawa Nawfal wai shi ya saci kudin,: Wannan abu ya yi wa Nasreen ciwo. Amma sai Nawfal ya nuna mata babu kemai jarabawa ce, Haka ta kore su a ~ gaban jama’a ta kunyata su, ta dora masu laifin sata. Suka fice titi Nasreen tana bara ana ba su kudi a nan ne suke samun na cin abinci, Nawfal ya dube ta zaune a gefen titi ya ce, “Nasreen dole mu san abin yi, bara alamun mutuwar zuciya ce da ke addabanmu ‘ya’yan hausa, bana son mu kasance daga cikin su. Gara mu bemi na kanmu Zan dinga zuwa wajen mai garuwan nan yana bani ina siyar masa sai ya bani wani abu. Ni yanzu makwancin mu yafi damuna. . Na gaji da bin kangon nan da muke yi.� Nasreen ta sharce hawayenta ta ce, “Nawfal ina son ganin Deedi, bansan halin da yake ciki ba, Nawfal mu koma gida don Allah.� Girgiza kansa ya yi, “Gara mu mutu a nan da mu koma gida. Nasreen Umma tana neman rayuwarki ne, idan ta kashe min ke wa zan gani inji sanyi a raina? Wacce irin rayuwe zanyi ni kadai babu ‘yar uwar haihuwata? Nasreen har yanzu na kasa yafewa Umma da ta makantar min da idanunki. Na kasa ganin farinta. Don haka kiyi haKuri da talaucin mu, mu nemi-na kanmu. Zanje wani gida mai zaure mai kyau inroka mu dinga kwana a ciki kin ji?� Kanta kawai ta daga ba tare da ta iya furta komai ba. Zazzabi ne mai zafi ya rufeta sai karkarwa take yi. Hankalin Nawfal ya kai matuKa a tashi dole ya fice ya nemo karare ya kunna mata, sannan ya nufi Chemist da ragowar � kudin hannunsa ya siya mata magani. Wasawasa sai da Nasreen ta koma sai andagata ankwantar. Kullum magana daya take yi masa ya kaita wajen Deedinta kada ta mutu. Shi kuma ya yi alKawarin babu inda za su sake komawa a gidan nan.� Kasancewarsa mutum mai zuciya. Haka kuma yana da lambar Sultan akansa da ta Abba, amma yaki barin ma tasan da hakan, domin yasan za ta matsa sai an je an kira su, shi kuwa roKon Allah yake yi Allah ya Kara nesanta Su. Sultan cikin ikon Allah ya dinga samun daukaka da kuma Karin girma akai akai wanda hankalinsa yafi kwanciya da yake nesa da mahaifiyarsa, sai dai Nasreen da take nan daram kamar yau ya fara sonta. Ya Kara kyau da haske, sai “yar rama da ya yi: Baya son magana idan ba ta kama dole ba. Haka baya ziyartar gida aikin kawai yasa a gaba. Katon gidansa babu abinda babu na more rayuwa, haka gidansa cike yake da ‘yan sanda masu kare lafiyarsa. Ya zama aiki yake yi babu ji babu gani, wanda a yanzu ya hau kujerar G Wannan girma ba shi kadai ya shafa ba, hatta iyayensa da ke garin Kaduna sai da abin ya zame masu abin alfahari, a dan shekarunsa ya taka matsayin da ba kowa yake da wannan arzikin ba. Farin jininsa a jini yake, ya zama dan gaban goshi a cikin ‘yan sanda. Ganinsa wahala yake yiwa jama’a haka bai cika zama a gida ba, saboda ayyuka. Da zuwansa ya kawo sauye-sauye na ban mamaki. Ya zuwa yanzu ya gama fahimtar ya rasa Nasreen har abada. Sai dai kuma ya fara samun surutai a gidajen jaridu akan rashin matarsa. Tun abin baya damunsa har ya koma yana daga masa hankali. Babban burinsa. Nasreen ta dawo ta shiga dakinta. Yau a wurin aiki ya kwana, saboda wasu mahimman tattaunawa da suke yi da IG. Yana dawowa gida daya daga cikin ‘yan sandansa ya sanar masa da zuwan iyayensa. Haka kawai ya ji baya farin ciki da zuwansu. Yana shigowa ya ga mahaifinsa yana zaune yana karanta Jarida. Farin cikin ganin mahaifinsa yasa shi murmushi. Frij ya nufa ya fincike hancin Coke ya dora a cikinsa, tare da _ furta, “Alhamdulillahi. Abbana na ji dadin zuwanka.� A Kasa ya zauna sai ka ce ba shi ba ne idan zai fita yake shan, mur, ana biye da shi kamar wani sarki, Umma ta fito ita da wata yarinya, kallo daya ya yi mata yaji wani irin tsanarta a ransa. Kai da ganinta ka ga mara tarbiyya. Sama-sama suka gaisa, kafin Abbansa ya dube shi ya ce, “Sultan baka da alamar aure. Baka san hakan tonon asirinka bane? Duniya tana kallon kowane shige da ficenka. Girma ne ya same ka tun kana da Kananun shekarunka. Don haka mahaifiyarka ta samo maka mata har andaura auren da kanmu muka kawo maka. Nasan kai mai biyayya ne, baka taba ce min a’a ba. Me kika ce Hajiya?� . Sultan. ya .kafe mahaifinsa da idanu, sai yanzu ya kula da wata rama da ya yi abin akwai al’ajabi. Haka ya cika da mamakin yadda mahaifinsa zai amincewa mahaifiyarsa wajen nema masa mata. A sanin da ya yi wa mahaifinsa mutum ne mai Zafi, ba ya son wargi, haka ummansa tana shakkarsa duk kuwa_ irin masifarta. Yau ga shi Abba yana mata magana cike da ladabi. Yau ga Abba yana bin dukkan shawararta. Haka ya nuna alamun tsoronta da yake ji Karara. Sake zuba masu ido ya yi yana son ganin Karshen wasan, Umma ta dubi yarinyar da fuskar nan ta sha kwalliya ta ce, ‘“Kaima Alhaji sai ka bari ingabatar da ita. Wannan dai sunanta Zakiyya, ita ce ‘yar Hajiya Ladidi da na taba yi maka maganarta. Ba ta da matsala za ka ji dadin zama da ita. Bana son Kananan maganganu don haka nake son ka riketa da amana, ka fito da ita duniya ta santa. Ko ya kace Alhaji?� Abba yana magana kamar jikinsa har rawa yake yi, idan har ba idanunsa ne suke yi masa gizo ba. “Haka ne Hajiya. Ai shi Babana bai taba yi min musu ba. Allah ya yi maka albarka.� Bai iya amsawa ba, sai idanu da yake bin kowannensu da shi. Suna nan zaune mai aikinsa ya kawo masu abinci, kowa ya zuba yana ci, amma Sultan ya kasa kai koda cokali daya bakinsa. Zama ya yi kawai yana zare safar Kafarsa, ya mike yana fadin zai dan watsa ruwa. Umma ta Kyafta mata idanu Abba sai faman yashe bakinsa yake yi. Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?� Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.� Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.� Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen, 6/5/22, 10:28 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚* CHAPTER 9 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?� Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.� Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.� Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen, ZAMU TASHI Sultan har yanzu babu labarinsu. Wannan ciwon na tabbata da shi zan koma ga Mahaliccina.� Hawayen da Abba yake Kokarin dannewa sai da suka zubo, ya sa hannu da sauri ya goge kamar mai tsoron wani ya gani. Sultan ya kasa cewa uffan har Abban ya gaji ya juya wurin motarsu da ‘yan, sanda za su jagoranci tafiyar tasu, saboda yanayin hanyar. Hannu kawai ya iya daga masu har suka fice. Cikin sauri-sauri ya shirya cikin kakinsa ya fito hannunsa dauke da wayoyl. � Zakiyya ta yi narainarai da idanu tana dubansa, “Ka zauna a gida ma.. Hannu ya daga mata ya wuce abinsa. Abinda bai sani ba, yana fita Zakiyya ta gayyato ma’aikatan jaridu tasa aka dauke ta hotuna, tayi bayani dalla-dalla a matsayinta na matarsa. Ta kuma cewa a daina cewa mijinta bai da mata ita ge matarsa, Kwanan Sultan biyu bai leKa gidansa ba, ita kuwa ko a jikinta. Haka tana sane da ya sallami mai girkin gidansa kasancewarsa namijl, amma ko sau daya ba ta taba Sa tsintsiya ta share ko da falo ba. Haka ruwan fridge ya dinga zuba yana shiga KarKashin kafet din, nan da nan dakin ya dauki wari. Kitchen kuwa wasu abubuwan da ba a sanya a fridge ba, har sun lalace suna wari. Ko a jikinta, ita dai idan ta samu ta ci abinda take son Ci, Za ta nemi wuri a falo ta sa film din batsa tana kallo. Gabadaya Sultan ya mance da Allah ya yi ruwan wata Zakiyya a cikin gidansa. Tunanin halin da mahaifinsa yake ciki ya fi komai daga masa hankali. Kai tsaye ya gane mahaifiyarsa ta yi amfani da bokayen tsubbu domin cimma burinta. Mahaifiyarsa ta yi nisan da ba ta jin kira, � tayi nisan da take mance girman Aljannah, da kuma abubuwan da ya kamata ta bi domin shigarta Aljannah. Gabansa ne ya fadi da Karfi da ya tuna da Kannansa da ke cikin gidan, yana —tsoron lalacewar tasu tarbiyyar. Ya zama dole ya je idan har abin da matsala ya kwashe su daga gabanta. Yana tsoron bakin da Umma take yi wa ‘ya’yan wasu ya faru akan ‘ya’yanta. Duk yaron da ta gani dan iska ne, nata ne masu kirki. Kowa ta gani mazinaci ne, nata ne masu kare kansu daga sharrin zina, kowa ta gani aron addininta suka yi, nata ne wadanda suke da asali a cikin addini. Ta ya ya Allah ba zai aiko da jarabawa cikin gidansu ba? Ta ya ya Zakiyya ba za ta zamo matarsa ba? A bayyane ya yi magana, “Ya Allah! Ban kasance mazinaci ba, kada ka jarabceni da rayuwa da mazinaciya. Allah ban taba jayayya da yinka ba, kada ka jarabceni da_laifin mahaifiyata. Allah mahaifina bai ° kasance azzalumi ba, kada ka jarabce shi da macen da za ta zalunce shi. Allah ka warware mana wannan matsalar da ke tunkaro mu, ka kare min Kannena a duk inda suke. Allah ka bayyana min Nasreen da dan uwanta cikin Koshin lafiya.� Zare rigarsa ya yi ya kama hanyar gidansa jikinsa a sanyaye. Har a lokacin babu dan sandan da ya gaya masa cewa Zakiyya ta gayyato ‘yan jarida. Yana sa Kafafunsa a cikin gidansa hankalinsa ya ninku a tashi. Ransa ya yi mugun baci, ya dubeta rai a Bace ya ce, “Ke ba ki da hankali ne? So kike ki mayar min da gida dafidalin wari? Ko bola kika samu ne? Ki tashi ki gyara gidan nan tun kafin bacin raina ya sauka akanki.� Jikinta yana rawa_ saboda_tsoron yanayin da taga Sultan, ta wuce kitchen domin dauko tsintsiya. A lokacinne ya bayyana a kitchen din. Ya ma kasa magana saboda azabar warin da ya ziyarci hancinsa. Dole ya sa hannu ya toshe hancinsa. Haka ya koma hankalinsa a tashe. Sultan ya tsani Kazanta fiye da tunanin mutum, dakinsa ya koma ya kwanta yana kallon sama, cikin tunanin da shi kansa bai san ko na menene ba. Nazari yake yi ta yadda za a yi ya iya rayuwa da Zakiyya a matsayin mata. Yana nan kwance bai motsa ba, ta gyara dakunan sama-sama ta je ta sheKa wanka ta antaya maganin da uwarta ta ba ta, sannan ta Kara shiga ruwan zafi, kamar yadda Hajiya Ladidi ta karanta mata, domin aikin da aka yi mata don ta koma budurwa har yanzu tana dan jinsa. Ita kanta yadda aka dinke ta abin yana bata tsoro, haka tana shakkar zai iya ganewa cewar ita ba budurwa ba ce, idan hakan ya faru tana da tabbacin Sultan korar kare zai yi mata. Shi kuwa wanka ya shiga ya fito daure da tawul yana tsane ruwan jikinsa. Ta shigo dakin babu ko sallama, kallo daya ya yi mata ya dauke kansa gabansa yana fadiwa. Babu laifi yarinyar tana da kalar tata kyan, sai rashin kamun kai da ke dawainiya da ita. Jikinsa ta Karaso tasa hannu ta rungume shi. Kamshin maganin da ta yi amfani da shi, ya yi ta dawainiya da shi, don haka ya fara mayar mata da martani, da taimakon tsaftace jikinta da ta yi. Ba shi ya farka ba, sai da asubahi. Ware idanunsa ya yi yana duba irin barnar da ya yi wa ‘yar mutane. Mamakin samunta a budurwa yafi komai tsaya masa a rai, domin yadda yaga bai taya taba, ita ta fara kawo kanta yasan da matsala. Haka wannan budurcin da ya samu ya sanya ya Kara ganinta da girma da mutunci a idanunsa. Gabadaya zanen gadonsu ya lalace da uban jini. Tana nan kwance kamar kayan wanki tana shakar barcinta. Mamaki ya sa ya kafe ta da ido, yaushe za a yi wa mace hakan ta kwantar da hankalinta? A hankali ya zame kansa ya shiga bandaki ya tsaftace jikinsa, kafin ya sa hannu ya tasheta, tana bude idanu ta fara magana cikin magagi, “Bilal ka rabu da ni barci nake ji.� Sultan ya zaro idanu yana sake dubanta, “Bilal kuma? Waye Bilal?� Ware idanunta ta yi gabanta ya fadi da Karfi, sai yanzu ta tuna abinda ya faru, don haka ta fara raki, “Wash! Don Allah ka taimaka min ba zan itya tashi ba.� Sultan dai kallon ta kawai yake yi, haka kuma zai iya makara yin Sallar asuba, don haka yace “Ki yi haKuri Zakiyya zan makara.� Ya sa kai ya fice abinsa. Yana fita ta mike ta shige bandaki ta gasa jikinta, sannan ta cire zancn gadon ta shimfida masa wani ta sake hayewa gadon tana shaKar barcinta. Babu Sallah bare Salati. Yana dawowa ya dube ta yana tantaman anya ta yi Sallah? Sai kuma ya kau da wannan tunanin a cikin ransa, ya yi tagumi. Wannan ranar ya tanadarwa Nasrcen dinsa, sai ga shi a lokaci guda Allah ya yi ikonsa, wanda babu wanda ya isa ya yi jayayya da yinsa. Shirin zuwa office ya fara, yana tunanin dole sai an samo ma’aikata sun yi masa gyaran gidansa domin har yanzu wari yakeyi sosai. Tashinta ya yi yace ta koma dakinta zai rufe Kofarsa. Ba ta yi mamakin rashin mutuncinsa ba, domin tuni ta fara haddace su. Tana dingishi ta fice. Faruwar wannan lamari tsakanin Zakiyya da Sultan ya sanya mata wani irin sonsa, a cikin zuciyarta kamar ta mutu. Tana jin bata taba mu’amala da wani namijin da ya gigita tunaninta irin Sultan ba. Duk inda ake neman namiji mai mantar da mace damuwarta, Sultan ya hada abubuwan nan. Tana jin ko dukanta zai dinga yi kullum ba za ta rabu da shi ba. Haka ta raina iyawar Bilal duk yadda take yabonsa kuwa. Shi kuwa ya kasa farin ciki da irin sabon lamarin da ya shiga, abin ya kasa burge shi, haka shi bai san yadda budurwa take ba bare ya fahimci abinda Zakiyya ta yi. Yan sandan ya basu umarnin su samo masu aiki a tsaftace masa cikin gidansa, a fitar da dukkan abubuwan da suka lalace.. Jaridar da ya samu a cikin motar ya dauka yana dubawa. Gabansa ya fadi da ya ga hotonsa hade da na Zakiyya. Cikin sauri ya ware ya fara karantawa. Ya gigita iya gigita, don haka ya ce wa direba ya juya gidan. Yana fitowa daga mota ya dubi-~daya daga cikin ‘yan sandansa yana tambayarsa yaushe akayi wannan hirar? Cike da tsoron yadda ya ga yanayin Ubangidansa ya gaya masa komai. Sultan ya daga hannu ya wanke shi da mari, ya sake daga hagunsa ya dauke shi da mari yana huci. “Ashe baka san aikinka ba aka kawo min kai? Ashe idan kashe ni za a yi zaku iya ba barawon hanya? A cikin gidana zaku bar ‘yan jarida su shigo har falona? Wannan wani irin shirme ne� sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.� Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?� Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?� Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.� Sultan mutum ne mai son 6/5/22, 10:28 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1 KARSHE🦚* CHAPTER 10 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.� Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?� Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?� Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.� Sultan mutum ne mai son mutumin da ZAMU TASHI zai aikata kuskure ya kuma amsa ya aikata har ya bada hakuri. Don haka ya sassauto, “Ki kiyaye kanki, ki kiyaye mutuncinki, matar aure ce ke, bai kamata ace kin fito a haka a gidan jarida ba, kamar ba matar aure ba. Idan kin siya min mutunci kanki kika siyawa. Daga Karshe kada wani ya sake shigo min gida ba tare da izinina ba, yin hakan zai jawo maki tarin matsalar da baki taba tunani ba.� Ya juya abinsa cike da takaici. Ashmaan ya kira shi a waya, sun jima suna tattaunawa, sannan suka yi Sallama. Yana isa office yaga babu wani aikin kirki, ya shirya motar ‘yan sanda suka kama hanyar Kaduna. Nasreen tana zaune ta hada kai da wani abun, gaba daya ta yi baki, ta rame ta sauya daga Nasrcen din Sultan ta koma Nasrcen Kankia. Nawfal ya koma kamar mai sana’ar bola, haka duk inda ake meman dan uwa Nawfal ya wuce hakan. Hakika da babu Nawfal da rayuwar Nasrecn ya zama abar Kyama. A zaman su maza sun sha kawo mata farmaki, Nawfal ke tsayawa kai da fata wajen ganin ya kareta. A Kalla da zuwansu garin nan, sun yi sana’a yafi kala ashirin. Haka sun kwana a wurare mabambanta, A yanzu haka ma Kosai ya siyo mata ya ajiye a gabanta tana ci, sai da ta gama sannan ta fara shan kokon, idanun Nawfal suka hasko masa hoton Sultan. Ya yi saurin dauka yana dubawa. Hotonsa ne tare da matarsa. Nawfal ya kafe su da idanu, ya gama karantawa yana al’ajabin irin wannan matsayin da Sultan ya samu, wanda a yanzu wane su su iya tunkarar gidansa? Bakinsa ya subuce ya ce, “Nasreen Deedinmu ya tare da matarsa yanzu ya zama A.I.G Kin ga yadda ya Kara kyau kuwa? Sai dai matar ko lullubi babu a jikinta.� Nasreen ta gigice iya gigicewa ta hau lalube, “Nawfal a ina ka gani? Ya zan yi in gani ni ma?� Bai dube ta ba ya ci gaba da duban jaridar Kosan, “A jarida na gani, wanda a ka Kunsa maki Kosai. Nasreen ke da ba idanu gareki ba ya za a yi ki iya gani?� Nasreen ta goce da kuka. Hakan yasa Nawfal ajiye jaridar ya kafeta da idanu ya rasa me zai ce mata kawai sai ya zuba mata idanunsa wanda shima hawayen ke zuba daga kwarmin idanunsa. A hankali ya fara magana, “Kin gani ko? Deedi ya fi Karfinmu a yanzu. Dole zamu ci gaba da zama a nan, domin gujewa abinda zai sa hankalinsa tashi. Na san soyayyar da zamu nuna masa kenan mu yi nesa da su. Ki kwantar da hankalinki akwai ranar da wahalar nan za ta zama labari.’� Muryar wani suka ji yana cewa, “Alhamdulillahi gasu can a lungun can.� Nawfal duba Nasreen yace, “Mun shiga uku, waka gani waye?� , ne Mansur ya Karaso yana kwasar dariya, “Nasreen ni ne nan mijinki Mansur. Zuwa nayi insauya maku rayuwa inkuma ajiyeki ki zama matata.� Nawfal zai yi magana, wasu suka kama shi suka tura cikin mota, haka ita ma Nasreen din aka dauketa sai mota. Lalube ta shiga yi tana neman Nawfal, hakan yasa ya kama hannayenta, ta shafa fuskarsa zuwa kansa ta tabbatar da shi ne, don haka ta saki ajiyar zuciya. Ta riga ta sadakar mutuwa za ta yi, ta fi son idan za a kasheta Nawfal ya kasance yana kusa da ita. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske, kafin suka sauka a wani Kauye. A kuma Kofar wani gidan Kasa. Haka suka sauka suka shiga ciki Mansur ya umarci mutanansa da a shigar da su. Nawfal ya ce, “Dakata! Za mu iya shigar da kanmu ba sai wasu sun sake taba mu ba. Ya kamo hannun Nasreen suka shige ciki. Mansur ya nuna masu daki ya ce su shiga zuwa anjima zai zo. Haka suka shiga suka dunKule wuri guda daki komai sai ledan Kasa. Aka kawo musu abinci maradadi, haka suka tuttura suka sha ruwa Mansur bai bata lokaci ba ya dawo hannunsa dauke da kwanon sha cike da fura yana isowa gabansu ya dubesu duba a tsanake sannan ya fara magana, “Na sha matuKar wahala wajen nemanki Nasreen. Hajiya Salma ta bani aiki akanki, domin in aureki in wahalar da ke, a lokaci guda kuma sai na ji ina son ki da gaske. Da naje gidanku sai Sultan ya watsa min Kasa a idanu, ya wulaKanta ni, ya shake ni yana neman ya kai ni inda ban shirya zuwansa ba. Ina cikin shirya wa Sultan kawai naji labarin Hajiya Salma tasa a sace ku saboda wasu dalilanta marasa tushe. A ranar da na sami labarin nan na yiwa Hajiya Salma gargadi akan duk abinda ya sameki ita ta siya da kudinta dan sai na fanshe bacin raina akanta. Hakan yasa ta tsorata ta gaya min inda aka kaiku. Daga Karshe take sanar min ashe kece matar da aka daura maki aure da Sultan. Bacewarki ya sa mahaifinsu gaya masu gaskiya, Sultan mijinki ne.� Nasreen da Nawfal suka ji dirar maganarsa kamar wani labari wanda ba zai taba faruwa ba. Ta gigice, ta shiga rudu, tana son ta Karyata shi domin Nawfal yaga jarida dauke da matarsa. Don haka ta girgiza kai tana kuka, “A’a ni ba matarsa ba ce, matarsa a yanzu haka tana gidansa.� Mansur ya kafe ta da ido, duk da ta lalace, amma har yanzu yana sonta, kuma da gaske yake ya shirya fuskantar kowacce irin matsala akanta. Zai jure koma menene yaga ya mallake ta. Girgiza kansa ya yi yana murmushi, “Ke ce matar Sultan ta farko, daga baya ne da aka yi ta jiran dawowarki aka ga shiru sai Hajiya Salma ta shiga ta fita ta mallake Abbanku, daga nan aka hada aurensa da Zakiyya ‘yar wajen Hajiya Ladidi, ba tare bada saninsa ba, sai ganin mata ya yi. Ya so ya ci musu ya Ki karbanta a matsayin mata, sai mahaifinsa ya yi masa nasiha, kasancewarsa mutum ne mai jin maganar mahaifinsa shi ne ya karbi Zakiyya a matsayin mata. Allah kadai ya sani ko suna zaman lafiya ko basa zaman lafiya. Amma tabbas ke matar aure ce, matar Sultan, Zakiyya ita ce matarsa ta biyu. Ni kuma ina son ki a yanzu haka, na shiryawa mutuwa akanki. Ki yi tunanin mafita, ina sonki babu idanun zan iya zama da ke. Zuwa anjima zan dawo in ji shawarar da kika yanke, ko aurena, ko kuma ki zama dadirona.� Mansur ya miqe ya fice, ya barsu cikin tashin hankali mara yankewa. Nasreen ta labubo hannun Nawfal ta ce, “Nawafal saita ni gabas don Allah.� Nawfal ya saita ta ta kai goshinta Kasa ta yi sujjada, “Allah na gode maka. Allah kai ne Allah, Allah ka bamu ikon bauta maka a bisa hanya madaidaiciya. Allah kai ka shirya wannna lamarin ka kawo min Karshensa. Allah na gode maka da ka amsa addu’ata a lokacin da ban za ta ba. Allah ka nuna min ranar da mijina zai dawo gareni.� Farin ciki ya kama Nawfal ta yadda bakinsa ya kasa rufuwa. Haka ya shiryawa komawa ya damKawa Sultan matarsa. Ya kafe Nasreen da idanu yana kallon yadda take cikin farin ciki da annashuwa, wanda rabon da ya ga hakan tun suna gidan su Sultan. Daga baya kuma ya ga ta fara kuka tana magana cikin kuka, “Me muka yi wa Umma haka? Me yasa za ta sa rayuwar Abbanmu a cikin matsala? Duk Kokarin da Abba yake yi don yaga ya faranta mata sai da ta kai shi mahallaka? Me ya sa Deedi zai auri Zakiyya? Umma da kanta take siyo masifa tana kawowa cikin gidanta da sunan gyara? Rayuwar Abba a yanzu shi yafi bani tausayi. Yanzu tuntuni ni matar aure ce? Dama goron da Abba ya kawe min cikin farin ciki na daurin aurena ne? Me yasa Abba bai gaya min ba? Ina tafe da igiyar aure akaina ban sani ba? Allah ka sake hada idanuna da suke rufe da mijina ko da sau daya ne. Nawfal yanzu za ka daina nesanta ni da mijina? Yanzu ka amince son da nake yiwa Deedi a cikin jinina yake? Ka amince Allah ya riga ya hada jinin mu da su Umma? Abu daya ya rage mana shi ne mu gano su waye danginmu? A ina suke? Waye zai gano mana su? Deedi kadai yake da amsar wannan tambayar.� Nawfal yasa hannu ya goge mata hawayen fuskarta, “Nasreen ba wannan ne a gaban mu ba, abinda ke gabanmu yafi Karfin wannan. Ta ya ya zamu iya rabuwa da mutumin da ya kira kansa da Mansur? Yanzu yafi Umma zama matsala a cikin rayuwar mu.� Cak! Ta daina kukan, ta yi shiru kamar mai tunani, “Nawfal tunani ya Kare min, ban san ya zanyi ba. Mu ci gaba da addu’a kawai.� Dakin ya yi shiru Kowa da irin tunaninsa. A haka Mansur ya dawo ya same su, ya yi maganar duniya babu wanda ya iya ce masa ko zo ka c1 kanka. Sultan ya iso Kaduna cikin awannin da basu gaza biyu ba, ya wanzu a Kofar gidansu. Kallo daya ya yi wa gidan Nasreen ta fado masa a rai. Har ya juya ya ji muryar mahaifinsa yana masa sannu da zuwa. Ya dubi mahaifinsa sosai, a irin wannan lokacin kamata ya yi ace yana Office. Tare suka shiga ciki suna rike da hannun juna. “Abba barka da gida.� Bai amsa ba, sai da ya dire shi a falon, sannan suka zauna. “Sultan idonka kenan?� Kafe hoton Nasreen ya yi da idanunsa har yanzu ba a cire hoton ba. “Abba ka yi haKuri na kasa . mance Nasreen. Abba komai ya sauya a rayuwar gidanmu abin yana ba ni tsoro. Ina Umma?� Abban ya dan yi shiru kafin ya ce, “Bana dan jin dadi ne shi ne na turata Office din taje ta sallami mutanen da suka yi Order tasa hannu.� Sultan ya girgiza kai yana al’ajabin yadda Umma za ta shiga harkar da ba nata ba. Haka kuma duk tsauri irin na Abba yau shi ne yake ba Umma izinin tafiya Office dinsa? Hafsat ta shigo ya kafeta da idanu, ta yi wani irin haske ta rame. “Barka da zuwa Yaya.� Murmushi ya yi ya mika mata hannu ta Karaso kusa da shi tana sunkuyar da kal, “Hafsat babu abinda ke damunki ko?� Girgiza kai ta yi tana sake duKar da kai. Sallamar Umma da Hajiya Ladidi yasa duk suka bi su da kallo. Hajiya Ladidi tana shigowa ta kwaye lullubnta tana satar kallon Abba. Ta jima tana kwadayin Alhaji Lukman a matsayin miji, amma bai taba kallonta ba. Sultan ya dan rankwafa ya gaida su, suka amsa cike da farin cikin ganinsa. Hajiya Ladidi ta ce, “Oh ashe kai ne a tafe? Shi ya sa muka ga garin hadari ya hadu. Ya su Zakiyyan? Ai mun ga � hira a jarida hira ta yi kyau sosai.� Sultan ya kauda kai kamar bai ji ba, ya dubi mahaifiyarsa ya ce, “Umma daga ina haka?� Tana shirin yin magana Haidar ya shigo yana sunkuyar da kai. Mamakinsa ya karu. Me yasa yaran basa son hada idanu da shi ne? Bayan sun � gaida shi ya dubi Haidar ya ce, “Haidar ka kammala karatunka me kuma kake jira?� Ya dan sosa kai, “Har yanzu aikin bai fito bane. Jinjina kansa ya yi, “Ka ba ni takardunka soja zan turaka. Zan ba Khamis shi zai yi maka komai.� Haidar baya son aikin soja, hankalinsa ya fi kwanciya a irin aikin Yayansa, amma kuma ba shi da yadda zai yi dole ya yi shiru kuwai. “Umma ki ba ni Hafsat intafi da ita Abuja.� Hafsat ta zaro idanu, yadda ta tsani takura idan ta koma gidansa ai ta shiga uku. “Ni dai Yaya nafi son nan.� Bai ce komai ba ya mayar da hankalinsa kan mahaifiyarsa da gaba daya ta sauya kamar ba ita ba. Umman ta daure fuska sosai, “Lafiya kake kallo na haka? Ni ka sanni Sarai na tsani irin kallon nan mai kama da na raini.� Murmushi yayi sannan ya dubi agogo, “Ya kamata in zo inkoma kada inyi yamma.� Abba ya girgiza kansa, “Babu inda za ka je, muna da bukatarka yau a gidan nan. Ka bari sai gobe sai ka koma.� Sultan bai zo da niyyar kwana ba, don haka ya fara zare agogonsa zuwa cire takalminsa. “Abinda kace ayi shi za a yi Abba. Idan ma kace in ajiye masu kakinsu indawo gida hakan zan aikata.� Abba ya ji dadin kalaman Sultan ba kamar su Haidar ba, da kullum suke yi masa rashin kunya. Zuwan Sultan ne yasa suke yi masa komai cikin girmamawa. Ya Kosa Hajiya Ladidi ta tafi, amma sai ta zauna a tsakiyarsu ta hana su motsawa. Hakan yasa ya dubi Abban ya ce, “‘Abbana zan je gidan Hajiya Gwaggo.� Abban ya mike yana satar kallon Hajiya Salma, “Muje nima na rabu da zuwa wurinta.� Sultan ya dan dakata yana kallon Abbansa. Bai iya yin magana ba, suka fito aka bude masu mota suka shiga. Sun fara tafiya ya dan waiwayo ya dubi Abba, “Yanzu Abba kana nufin Hajiya Gwaggon baka zuwa duba ta?� Abba ya hadiye yawu da Kyar ya ce, “Wato Sultan Hajiya Salma ta wuce duk yadda kake tunani. Ta kama komai ta yi kane-kane a kai. Yaran nan kada ka so kaga rashin kunyar da suke yi min. Ni na gaji watarana zaku iya nemana ku rasa.� Sultan ya yi shiru bai yi magana ba, gudun kada ‘yan sandansa su ji sirrin cikin gidan su. Hajiya Gwaggo tana jin murya ta tsaya kawai tana kallon su, kafin tai wuf ta shige cikin daki tana share hawayenta. Abba ya durKusa a gabanta yana roKo. amma ko kallon sa ba ta yi_ ba. Sultan ya harde yana dubansu, har sai da ya tabbatar da ba za ta yi maganar da gaske ba, sannan ya shigo ya zauna kusa da ita. “Hajiya fushi kike da Abbana? Hajiya kin taba zama kinyi tunanin dalilin da zai sa danki ya gujeki bayan yafi kowa zumunci duk_ cikin ‘ya’yanki? Ashe danki ba zai iya shiga hatsari ki jawo shi jiki ki ji matsalarsa ba? Hajiya kin taba zama da danki kin ji matsalarsa? Mahaifina yana cikin wani halin da yake da buKatar addu’arki.� Sultan ya Karashe maganar idanunsa jazir, yana jin da zai iya zubar da hawaye babu shakka mahaifinsa zai fara yiwa kuka.� Hajiya ta dan sassauto ta dubi Sultan ta ce, “Sultan har gidansu naje a gabansa Hafsat da Haidar da uwarsu suka wulaKanta ni, amma ya kasa magana. Ban yi fushi ba, na sake dawowa haka suka sake cin mutuncina. Kai ba zan. taba mance wannan abun ba.� Sultan ya dan yi shiru kafin ya girgiza kansa, “Hajiya ki yi hakuri. Abba ya sauya daga Abban da muka sani shekaru talatin baya. Umma tana neman tasa Abba a wani hali. Hajiya kiyi wa Abba addu’a ta haka ne zai sami sassaucin abinda ke damunsa. Abinda yasa na tsani zuwa gida Hajiya kin sani, saboda su Nasreen. Da zarar na shigo sai zuciyata ta dinga gaya min zan gansu a kwance a daki. Hafsat kuma da Haidar ki zuba ido ki ga irin matakin da zan dauka akansu. Kin wuce mu tsaya muna kallon wasu su wulakanta mana ke, bare kuma mu da kanmu.� Haka ya yi ta ba ta baki har ta sauko ta kuma sawa Abba albarka, wanda yake jin kamar ansauke masa wani tarin kaya ne a kansa. Hajiya Gwaggo ta kawo masu_ tuwon shinkafa, suka ci kwano daya da mahaifinsa, sannan ‘suka bar gidan. A hanya suka wuce gidan Alhaji Mu’azzam, wanda ya fada harkar siyasa babu ji babu gani, kullum yana gidajen radio yana kumfar baki. Shi kansa ya ji dadin ganin Sultan har ya nemi taimakonsa akan abubuwan da yasa a yaba, Sultan ya nuna masa babu damuwa. Abin mamaki har suka dawo Hayjiya Ladidi tana nan a gidan, hakan yasa ya wuce dakinsa yana kallon yadda aka tsaftace dakin. Shiru ya yi yana tuna ranar da ya kasance tare da Nasreen, wannan daren ya kasa Bace masa, haka sai da aka gaya masa matarsa ce ya tuna da irin murmushin da Abban ke jifarsu da shi a ranar da ya kamata ya yi masu fada. Rintse idanunsa ya yi, Ashmaan yana can yana bincike a kan mutuwar mahaifiyar su Nasrcen, ya Ki bari wai sai sun bayyana tukunna, kamar yadda suke tunani. Yana nan kwance ba barci yake yi ba, jira yake Hajiya Ladidi ta bar gidan ya ci mutuncin° Kannansa, domin abinda suka yi wa Hajiya Gwaggo ya tsaya masa a rai. Daga dakin yake jiyo surutai hakan yasa ya fito yana duban yadda Hafsat da Haidar suka hayayyakowa mahaifinsu, suna cewa yaje ya kwashe komai ya gayawa Sultan. Sultan ya kirawo ‘yan sandansa ya ce yana son su sauyawa Haidar kamanninsa. Ita kuma Hafsat ya zare belt ya dinga auna mata. Umma fa ta gigice, sai ta yi wurin da ake dukan Haidar da gudun gaske tana kuka, sai kuma ta koma tana zagin Sultan tana cewa idan bai daina dukan Hafsat ba za ta tsine masa. Ko kallon ta bai yi ba, hukunci kawai yake yi. Sai da Abbansa ya yi magana sannan ya dakata da dukan Hafsat ya kuma dakatar da dukan Haidar, wanda tuni ya zube a nan yana numfarfashi. Sultan ya dinga masifar da ya basu tsoro, ya botsare masu ya sauya kamar ba Sultan din da suka sani ba. Yana ji a ransa ba zai iya barin mahaifinsa a cikin gidan nan ba, kada watarana su kashe masa mahaifi su barshi da maraici. A take ya kira Khamis ya zayyane masa komai, Khamis ya ce, kawai ya turo shi Abujan shi zai yi maganinsa, kuma dole ya tafi aikin sojan nan. Don haka Hafsat kadai zai barwa Umma a gidan. Umma ta Karaso tana masifa ya dube ta duba sosai ya ce, “Umma zan dauke mahaifina daga gidan na rasa me ke masa dadi? Tunani ne fal a cikinsa. Ji ya yi ankwanta a bayansa, bai hanata ba, haka bai hantareta ba, kamar yadda zuciyarsa ke gaya masa, Haka ta shammace shi suka sake komawa wata duniyar. Shi dai ko dan bai saba bane? Idan ba haka ba, ya kasa jin wani abu mai kama da dadin kasancewarsa da ita. Amma kuma tana da Kima a idanunsa musamman da ta kama kanta. Barci take shaKa harda minshari, wannan abu ya sake daure “masa kai. Minsharinta ya dame shi Kwarai domin ya tsani namiji ma mai minshari bare kuma mace, Bubbuga ta yayi ta farka tana sake luma idanunta a cikin nasa; Zakiyya wata irin jarababbiyar yarinya ce, wanda a farko ta yi masa kawaici amma a yanzu ba za ta iya ba, ya zama dole su sake komawa duniyar da suka fito. A idanunta ya fahimci abinda take nufi, ya ce, “TirKashi! Ni mace ma ba ta gabana bare har in iya yin abinda kike nufi.� � Mikewa ya yi ya shige bandaki ya sa key Zakiyya ta mike ta shige dakinta tana cizon yatsa Ya riga ya dandana mata zuma mai wahala mancewa. Shigewa dakinta ta yi ta kira mahaifiyarta, “Momi mutumin nan fa ya iya komai Naji dadi da kika hada ni da shi. Wallahi yanda nake jin sa babu abinda zai raba ni da shi, gashi baya ~ son hayaniya.� A nan ta yi ta ba mahaifiyarta labarin yanayin Sultan, wanda karaf sai a kunnensa. MU HADU A LITTAFI NA BIYU 6/5/22, 10:38 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 1 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Minsharinta ya dame shi Kwarai domin ya tsani namiji ma mai minshari bare kuma mace, Bubbuga ta yayi ta farka tana sake luma idanunta a cikin nasa; Zakiyya wata irin jarababbiyar yarinya ce, wanda a farko ta yi masa kawaici amma a yanzu ba za ta iya ba, ya zama dole su sake komawa duniyar da suka fito. A idanunta ya fahimci abinda take nufi, ya ce, “TirKashi! Ni mace ma ba ta gabana bare har in iya yin abinda kike nufi.� � Mikewa ya yi ya shige bandaki ya sa key Zakiyya ta mike ta shige dakinta tana cizon yatsa Ya riga ya dandana mata zuma mai wahala mancewa. Shigewa dakinta ta yi ta kira mahaifiyarta, “Momi mutumin nan fa ya iya komai Naji dadi da kika hada ni da shi. Wallahi yanda nake jin sa babu abinda zai raba ni da shi, gashi baya ~ son hayaniya.� A nan ta yi ta ba mahaifiyarta labarin yanayin Sultan, wanda karaf sai a kunnensa. ZAMU TASHI RUBUTACCIYA 2 Sultan ya gama sauraren dukkan maganganun da take yi a waya, ya zuro kansa cikin dakin cike da takaicin jin matarsa tana bude masa sirrinsa. Yana sanye da jallabiyarsa fara sol sai Kamshi ke fita daga jikinsa. Shigowa ya yi ya zauna yana duban ta. “Ke kuma haka Allah ya halicce ki fadin sirrin mijinki ko? A haka dai kamar mai wayo ashe sakarya ce. To daga yau na bar sake zama kusa da ke, tunda baki da sirri.� Zakiyya ta gigice ta ce, “Wallahi ba wata bare nake gayawa ba, Momi ce ta kira nake bata labari kayi hakuri ba zan sake ba.� Sultan ya zaro idanu sosai. Kamar zai yi magana sai kuma kawai ya fice abinsa. Mamaki ya ci gaba da dawainiya da shi, ta yadda yarinya za ta iya kallon idanun mahaifiyarta ta gaya mata sirrin da ke tsakaninta da mijinta, abin ya yi masa tsauri sosai. Duk yadda Mansur yaso ya ga ya sami kan Nasreen abin ya faskara, hakan yasa ya daina basu abincin, ya koma ba su wahala yana gana masu azaba kala-kala. Da Nawfal ya gaji ne ya ce, ‘Nasreen ki amsa masa ko za mu samu a rangwanta mana. Ba ki jin tausayina ne Nasreen? Ina shan wahala.� Nasreen ta goge hawayenta, tana laluban Nawfal da kwana biyu ya Ki yarda ta taba shi, sakamakon jikinsa da ya yi zafikamar wuta, “Nawfal don Allah ka zo kusa da ni, ka daina guduna kaji Nawfal?� Nawfal ya Karaso ta rungume shi, a lokacin ta ji jikinsa zafi rau! Ta goce da kuka sosai, “Nawfal baka da lafiya ne? Me ya sameka? Nawfal so kake ka kashe min kanka? So kake ka sani maraici?� Dukansa take yi da dukkan hannayenta tana kuka. Shi ma kukan y.ake yi azaban ya ishe shi haka. “Nawfal� bari Mansur ya zo sai ya nemo maka magani.� Girgiza kansa ya yi, “Mansur ba ya nan, ya tafi ya barmu a Karkashin kulawan Kattan nan.� Ajiyar zuciya take yi da Karfi. “Nawfal lallaba ka je waje ka samo ruwan_ sanyi ingoga maka a jikinka ko zai rage zafin.� Babu musu ya aiwatar da abinda ta ce, ta sa gefen hijabinta a ruwa tana jiKawa tana goga masa a jiki. Sun dauki tsawon lokaci a hakan har jikinsa ya fara sanyi sannan ta sa kansa a Kafafunta tana tofa masa addu’a. Wani ya shigo yana dubansu ya ce, “Yanzu sai ki fara takaba barayi sun kashe Sultan.� � Wani abu ta ji ya ratsa mata tsakiyar kanta, tunda ta fasa wata Kara ta kifa kanta a jikin Nawfal bata sake sanin inda kanta yake ba. Nawfal ya tashi yana rintse idanunsa, da Kyar ya iya duban mutumin ya ce, “Ka ji tsoron Allah. Yaushe Deedi ya rasu? Na san kun yi� hakan ne domin ku cimma wata manufarku ,akanmu.� Mutumin ya girgiza kai jikinsa,a sanyaye, “Da gaske Sultan ya rasu. Ni kaina naji rasuwarsa, kasancewar kisan wulakanci akayi masa. Haka kuma anrasa gane su waye ke da alhakin wannan _,aikin. Ka. taimaka ‘wa ‘yar uwarka ta farfado.� ~*~ ~ . Nawfal yasa kuka mai sauti yana jin zuciyarsa tana yi masa ciwo. Cikin kuka ya � dubi mutumin ya ce, “Don girman Allah ka sadamu da� gidansu Deedi muyi masa addu’a. Mutuwar Deedi tamkar tonan asirin mu ne.. Mun shiga uku don Allah ku taimake:mu ku kaimu gida mu zauna cikin ‘yan uwanmu domin yi wa Deedi addu’a.� Mutumin da ya fara jin tausayin su har cikin zuciyarsa ya girgiza kai, “Yin hakan zai iya jawo nima inrasa rayuwata agurin Oga Mansur, Zan baku shawara ku bi shi a hankali za ku rabu lafiya. Ka duba lafiyar ‘yar uwarka bari in kawo maku abinci ku ci.� Nawfal ya fara watsa wa Nasreen ruwa, ta ja dogon numfashi, taso Kwarai yau da idanunta suna gani ta kalli mutumin da ya kawo mata wannan mummunar sakon. A yau ta sake kukan rashin idanunta. Tun Nawfal yana iya rarrashinta har ya koma ya zuba mata ido kawai. Ta kasa ci ta kasa sha, sunan Deedi kawai take fitarwa daga bakinta. Ta tabbata lokacin mutuwarta ce ta yl. Fuskarta suka kumbura suka yi suntum saboda tsabar kuka. Washegari Mansur ya shigo gidan yana duban Nasreen, “Yanzu za ki iya aurena? Ki fara zaman takaba, ki samu ki gama so nake muyi auren gaske. Shi ya sa ban taba yunkurin cutar da ke ba. Ki zauna kiyi zaman takaba idan kika gama zan kawo malamai gidan nan a daura mana aure da ke. Allah ya jiKan Sultan yasa ya huta.� Nasreen ta sake sa kuka mai ban tausayi tana girgiza kai, “Deedi bai mutu ba, ban yarda ba, idan da gaske Deedi ya mutu ka dauke mu ka kaimu gida.� Harararta ya yi ya ce, “Dama ance makahon mutum shegen kafiya gare shi. Da ni aka yi jana’izar mutuwar Sultan. Don haka ba yardarki nake nema ba. Zan fara Kirga daga yau.�� Nawfal yana jin su bai ce komai ba, shi kadai yasan abinda yake saKawa a cikin zuciyarsa. Haka bai taba jin zai iya daukar mataki wajen ficewa daga wannan wurin ba, � sai yau dinnan da aka sanar da shi mutuwar Sultan. Kai tsaye ya fara dora laifin akansa, ~* tunda babu yadda Nasreen ba ta roKe shi ba, a kan su koma gida, amma ya Ki amincewa. Mansur yana fita ya dubi� Nasreen ya ce, “Nasreen. Gobe ki cewa Mansur kin amince da shi a matsayin miji.�� Nasreen ta rarumi sandarta za ta kwada masa, ya sa hannu ya amshe sandar. Cikin zafi take magana, “Wallahi ba zan taba yin wani auren ba, tunda Deedi ya rasu me kuma zan nema a duniyar nan? Na rasa shi na rasa farin cikina. Nawfal kana ta juya min rayuwata kamar kai ka kawo ni duniya? Na gaji da irin abubuwan da kake yi ka fita ka bani wuri tun kafin fushina ya Kare akanka. Kana da yadda za ka yi mu koma gida, amma ka bar mu cikin wahala, har abin ya kwabe mana. Yanzu kana ganin waye zai iya fitar da mu a cikin gidan nan? Nawfal mutuwa zan yi, zan mutu Nawfal komai ya tsaya min, zuciyata tana yi min ciwo na kasa amincewa na rasa tsayayyen mutum kamar Sultan. Don Allah ya zan yi? * Ya zan yi? “Nawfal Dee shi ya dauki dukkan dawainiyar mu, shi ne gatan mu a gidan duniya. Ya juri abubuwa masu yawa saboda kawai ya faranta mana rai. Yau ga mu muna da yadda zamu yi mu isa gare shi, amma muka gwammace mu nesanta kanmu daga gare shi, muka gwammace mu katange kanmu a wurin da bai kamata ba. Idan Umma ta yi mana laifi ba za ta ci albarkacin danta mu yafe mata ba? Na tabbata Dee ba zai taba yafe mana ba. Nawfal ka fice min daga dakin nan tun kafin indaga sandar nan in kwada maka.� Yadda ya ga tana cikin fushi ya sa ya fice kamar yadda ta ba shi umarni. Hada kansa ya yi da guiwa yana shessheKan kuka. Tana jin irin kukan da yake yi wanda bata taba jinsa yana irinsa ba. A take danasani ya shigeta, yau da babu Nawfal a rayuwarta da tafi haka wulakanta. Ya zama dole ta yi masa uzuri. ; “Nawfal!� Ta Kwala masa kira, babu shiri ya taso ya Karaso wurinta suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi. “Nawfal ka yi hakuri bacin rai ne yasa na gaya maka magana.. Amma kasan bamu yi wa Dee adalci ba, ba mu kyauta masa ba. Ga shi Dee ya yi kwanan Kabari babu mu a cikin masu yi masa addu’a. Nawfal gaya min kana da mafita? Ko wurin Abba ne mu samu muje na tabbata kafin mutuwarsa ya bar mana abinda za mu dinga tunawa da shi.� Nawfal ya goge hawayensa, haka ya sa hannu ya goge mata nata hawayen da suke ta zuba. “Nasreen ya zama dole ki nunawa Mansur kin hakura kin amince da shi, ta hakane zai saki jiki damu har mu samu hanyar da za mu gudu. Ina da lambar Dee, ina da ta Abba, ban yarda Dee ya rasu ba gaskiya. Ki natsu ki bi Mansur har in . sami mafita.� Gyada kanta kawai take yi hawaye na . kwarara, bakinta ya mutu, ta ji dadin kalaman Nawfal a kan Sultan yana nan a raye bai mutu ba. Idan kuwa ya tabbata yana da rai, sai ta yi azumi uku domin nuna godiya ga Allah da ya bar mata Sultan a raye na wani lokaci. “Yanzu Nawfal ya za mu yi? Ni na tsani Mansur dinnan duk wani mummunar labari daga bakinsa muke fara ji. Don Allah kada ka dauki lokaci wajen nema mana mafita, kuma Nawfal tuntuni kana da lambobin su Abba ka kasa kiran su?� Nawfal ya dan yi shiru kafin ya ce, “Kuskure ne anriga anyi Nasreen sai mu tari gaba.� Bata ce komai ba, ta kwantar da kanta a jikin bango kawai tana jin sanyin simintin yana shigarta. Sultan ya yi bala’in daukewa Zakiyya wuta, ta yadda ya rage zaman gidansa, kullum yana cikin aiki. Yau Lahadi, sanye yake da wando iya guiwarsa sai t shirt mai ° dauke da sunansa a baya. Shigar ta yi matuKar dacewa da shi, fatan jikinsa ta sake laushi sai walKiya take yi, kallo daya za ka yi masa ka fahimci yana cikin natsuwa, sai dai a zuciyarsa ba haka abin yake ba. Yana zaune a cikin garden dinsa ya_ harde Kafafunsa a kan wani yana karatun jarida. Wayarsa ce ta dan yi Kara hakan yasa ya fahimci kira ne, don haka ya dauka ya manna wayar a kunne. Ashmaan ya ce, “Ka jira mu sati mai zuwa zamu zo gidanka. Na samo wasu bayanai akan Saudat bayanan suna da mahimmanci, don haka ne nake son mu hadu mu dukka domin ganin yadda zamu bullowa abin.� Sultan ya rasa bakin magana, ya rasa yadda zai fara godewa abokansa, da suka hana kansu barci saboda shi? Kafin ya yi magana har Ashmaan ya datse wayar. Murmushi ya yi ya ce, “Girman kai a wurinka Ashmaan abin ba a cewa koma. Ibtihal ce kadai ta isa ta yi min * maganinka.� Zakiyya da ta dade tsaye akansa tana � Kare masa kallo, ta lumshe idanunta tana jin waye ya kaita sa’an miji? Dogo ne tsayayye mai faffadar Kirji. Yana da haske irin hasken nan mai kyau da daukar hankalli. Hancinsa ya dace da bakinsa. A hankali ta Karaso tana washe hakora. “Ina son magana da kai.� Ta fada masa tana tsaye a kansa tana yi masa wani shu’umin kallo wanda yasa ya tamke fuska. “Ina jinki. Kuma ke baki iya gaisuwa bane? Menene na tsaya min akai haka?� Zagayowa ta yi sannan ta gaida shi, bai amsa ba, haka bai daina kallon ta ba. Shi tunda yake anya ma ya taba ganinta babu kwalliya? Har yanzu ba zai ce ya taba ganin asalin fuskarta ba. “Dama ina son ingaya maka ne, ni ba zan iya jure rashin kusanto ni da kake yi ba, sai ka dinga ja baya da ni sai kace ba matarka ba. Ina da buKatar mijina.� Sultan dai yana ganin abin al’ajabia_ � duniyarsa, “To na ji ki shiga ciki zan zo.� Babu musu ta mike tana tafiya tana » yanga, abinda bata sani ba, ko daga kansa bai yi ba, bare har ya dubi 1rin takun da take yi. Tunani ya yi tunda yarinyar nan ga kalarta gara ya yi iya yinsa ya sauke hakkokinta tun kafin watarana ta kawo masa Kato cikin gida. Rintse idanunsa ya yi kasancewarsa namiji mai tsananin kishi musamman a kan abinda ya shafi iyalansa. “Ta kawo min wani gidana? Ashe da na kashe ta kowa ma ya huta.� Yana jin dadin yanayin wurin don haka ya kasa tashi yana nan zaune har sai da ta sake dawowa. Babu shiri ya mike sam ba ya jin sha’awar komai, haka ya same ta. Maganin da ta shafa a jikinta shi ya rinjaye shi har ya aikata abinda take so. Wani abu da Sultan ya gama fahimta da Zakiyya shi ne ba ta Sallah kwata-kwata hakan ya tashi hankalinsa har ta kai yau ya yi mata magana, “Wai ke me yake hanaki Sallah ne? Kina nufin in zauna da kafira a � cikin gidana? A’a ba za a yi hakan da ni ba, idan baki iya bane zan tattaraki da direba ya * kai ki gidanku ki koyo yadda ake ibada, kafin mu iya zaman aure. Domin bana jin ko wankan tsarki kin iya yi.� . Idanun Zakiyya ya raina fata sai � girgiza kai take yi alamun babu inda za ta je. Tsaki ya ja ya fice daga dakin kawai. Washegari ya gama shiryawa zai wuce aiki, yana fitowa Zakiyya ta fito da gudu kamar mahaukaciya ta kama _ Kafar wandonsa. Kunya ya kama shi, ya kafeta da ido kawai. Yau babu kwalliyar a fuskarta, hakan yasa ya fahimci dalilin da yasa take kwana da kwalliya. Kallon ‘yan sandan shi kawai ya yi gaba daya suka watse. Dubanta ya yi cike da takaici ya ce, “Me yake damunki ne Zakiyya? Baki ganin ina gaban yarana ne? Me kike tunanin abinda kika yi zai jawo min? Kada ki sake yi min haka.� Kin sakinsa ta yi tana magana cikin kuka, “Wallahi zan dinga yin Sallah kada ka ce inkoma gidanmu.� Sai yanzu ya fahimci dalilin haukan da take yi, “To koma ciki.� Sakinsa ta yi ta kama hanyar cikin gida, ya bi bayanta da ido. Ya tsani ya ga mace tana sanye da riga daban zani daban, amma Zakiyya kamar hakan ya zame mata jiki, za ta yi kwalliya yadda ya kamata ta dauko riga daban zane daban ta sanya, ita kuma ba ‘yar kauye ba. Tunda tazo gidan bai taba cin wani abu da ya shafi girkinta ba, ita kanta baa bin arziki take dafawa ba, wataran kuma ta ba masu gadi kudi su yo mata order. Shi ya sa yake ta tunanin yadda zai yi da su Ashmaan da suke shirin zuwa gidansa, kuma ya tabbata za su zo ne daga nan su ci abincin amarya. Ya zama dole yasan yadda zai yi kafin ranar tazo idonsa ya raina fata. Yana kan hanya ya kira mahaifinsa a waya suka fara tattaunawa akan matsalar su Nasreen. Abba ya nisa ya ce, “Sultan mutanen da suka bace menene amfanin bin diddigi akan Saudat?� Sultan ya shaki iska ya fesar, “Abba “na yi wa Anti Saudat alKawarin zan Kwato mata ‘yancinta. Ko su Nasreen suna nan, ko basa nan, sai na nemo wanda ya kashe Anti Saudat na hada shi da hukuma ta hukunta shi dai-dai da irin laifinsa.� Abba ya gyada kai ya ce, “Idan kuma mutumin ya mutu fa?� Sultan ya ce, “Irin wadannan azzaluman Allah yana jinkirta mutuwarsu domin suga ishara tun a gidan duniya. Abba ka bari duk yadda al’amuran suka kasance zan sanar da kai insha Allahu.� Suka yi Sallama ya ajiye wayarsa. Duban yaransa ya yi ya ce, “Ranar Lahadi insha Allahu za ku nemo min ma’aikata masu aikin abinci za su kawo mana lunch, ina da baki.� Da girmamawa suka amsa masa. . Sultan ya Kurawa gefen titi idanu, har yanzu yana nan da halayyarsa na son kallon gefen titi. Haka abubuwan da suka faru shekarun baya suna nan manne a ransa sun Ki gogewa. Yana jin yanzu ne zai dauki fansa akan koma waye ya ingiza rayuwar Saudata ° cikin Kunci. Nasreen tana zaune a gaban Mansur ° ya ajiye mata nama zuciyarsa cike da farin cikin yadda Nasreen ta kwantar da hankalinta. Doguwar riga ya kawo mata ya ce ta sauya wanda za ta yi zaman takaba da ita. Yana fita ta rungume doguwar rigar ta shaki kukanta yadda ranta ke so. Sannan ta sauya kayan kamar yadda ya buKata. Bata san ya shigo ba, sai muryarsa ta ji, “Kin yi kyau sosai. Bari ki gama takabanki za ki ga yadda zan mayar da ke Nasreen. Idan har za ki dinga bani hadin kai ni kuma zan mayar 6/5/22, 10:47 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 2🦚* *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Ranar Lahadi insha Allahu za ku nemo min ma’aikata masu aikin abinci za su kawo mana lunch, ina da baki.� Da girmamawa suka amsa masa. . Sultan ya Kurawa gefen titi idanu, har yanzu yana nan da halayyarsa na son kallon gefen titi. Haka abubuwan da suka faru shekarun baya suna nan manne a ransa sun Ki gogewa. Yana jin yanzu ne zai dauki fansa akan koma waye ya ingiza rayuwar Saudata ° cikin Kunci. Nasreen tana zaune a gaban Mansur ° ya ajiye mata nama zuciyarsa cike da farin cikin yadda Nasreen ta kwantar da hankalinta. Doguwar riga ya kawo mata ya ce ta sauya wanda za ta yi zaman takaba da ita. Yana fita ta rungume doguwar rigar ta shaki kukanta yadda ranta ke so. Sannan ta sauya kayan kamar yadda ya buKata. Bata san ya shigo ba, sai muryarsa ta ji, “Kin yi kyau sosai. Bari ki gama takabanki za ki ga yadda zan mayar da ke Nasreen. Idan har za ki dinga bani hadin kai ni kuma zan mayar ZAMU TASHI da ke bin alfahari a idon duniya. Ki kwantar da hankalinki zan nuna maki ba Sultan ne kadai mai Kaunarki ba.� Kuka ya taho mata da gudun gaske ta shanye kukanta tana sakin ajiyar zuciya. Tana jin dadi ne idan ta tuna bata da idanun da za ta dube shi bare har bakin cikinsa ya kasheta. Shi dai Nawfal yana nan daga waje, yaki amincewa ya yi nisa da inda suke, gani yake yi kamar Mansur zai iya cutar da ita. Mansur ya fahimci abinda Nawfal yake nufi don haka ya yi masa wani inn kallo kafin ya bushe da dariya ya Kara da cewa, “Ji dan tatsitsin yaron nan! Wanda baka wuce in fyato ka daga hancina ba, wato ka tsaya kai a dole ga mai gadin ‘yar uwarsa. Idan wani abun zan yi mata tuni zan sa a banKare min kai a wancan bishiyar.� Ya nuna wata bishiya dake tsakar gidan. Nawfal ya dube shi ido cikin tdo babu wata alama ta tsoro, ““Ni ma ban ce maka ina gadinta ba. Haka baka isa ka yi mata abinda Allah bai tsara zai faru da ita ba.� Mansur ya sake bushewa da dariya, hakan yasa Nawfal wuce shi ya afka dakin da Nasreen take. Ya rada mata a kunne ta yi wata magana da za ta nuna alamun tana son Mansur. Nasreen ta cije lebbanta tana jin daci a wuyanta sannan ta daure ta fara magana muryarta tana rawa, “Nawfal me ya sa za ka gayawa Mansur magana? Ka mance shi yake shirin taimakona ya aure ni duk da bana gani? Ka mance shi ya rabo mu da zaman KasKancin da muke yi a Kankia ya kawo mu nan? Ba mu da matsalar abinci, haka shi yake bamu dukkan abinda muka buKata. Ka daina gaya masa magana ka ji Nawfal?� : Mansur da ya labe yana sauraransu farin ciki ya kasa barinsa har sai da ya bayyana a gabansu. “Nasreen za ki ji dadina fiye da tunaninki. Zan mayar da ke tauraruwa a cikin gidan nan. Kai kuma kayi min biyayya.� Nawfal ya hade rai yana dubansa, “Babu biyayyar da zan yi domin ban gama yarda da kai akan ‘yar’uwata ba. Idan da gaske kana son ta me zai sa ni ma ka dinga takura min kana hanani yin abinda nake so? Idan ita mace ce ai ni namiji ne, a bar ni infita in nemo gumina saboda ban saba da zama ba.� Mansur ya dan yi shiru, “Za ka iya sana’ar fashi da makami?� , Nawfal ya zaro idanu, “Allah shi kyauta ya tsareni. Ce maka na yi zan je in nemi halalina ba hakkin wasu ba.� Mansur ya yi murmushi ya fice yana jinjina Karfin taurin kai irin na Nawfal. Yana fita ya dubi Nasreen ya ce, “Kin gani ko? Sai kin dinga daurewa idan kina son mu fita daga gidan nan lafiya lau. Bana son koke-koken nan da kike yawan yi bana jin dadi. Ki daurewa zuciyarki za ki iya Nasreen.� Gyada kanta kawai take yi, amma ita kadai tasan menene a can Kasan zuciyarta. Ashmaaan ne zaune a cikin mota a unguwar Magajiya da ke Kaduna. Idan bai yi Karya ba nan ne gidan su Kawar Saudat da aka nuna masa, wanda aka tabbatar masa a nan gidan take aure da ‘ya’yanta. Ya rasa ta yadda zai yi ya sami shiga cikin gidan ba tare da wata matsala ba, kasancewarsa musulmi. Dole ya aika yaro a yi masa kiran mai gidan. Aka tabbatar masa da baya nan .. yaje gona, sai dai matarsa. Idan lissafinsa ya yi dai-dai zuwansa na shida kenan yana . neman gidan bai taba cin sa’a ba, sai yau da aka tabbatar masa da nan ne gidan Nora. Haka hoton Saudat da ya nuna angane ta har aka furta sunanta da Justina. Yana nan zaune har Allah ya fito masa da matar da yana ganinta ya gane ta, ita ce ta cikin hoton nan. Fitowa ya yi daga motarsa ya Karaso kusa da ita, “Sannu madam.� Ta dube shi da tsoro a idanunta ta ce, “Yauwa sannu.� Bakinsa ya rufe ne sakamakon yadda take tafiya tana waiwayarsa, alamun ba za ta tsaya ba. Da sauri ya taka ya biyo a, “Madam ina neman gidansu Justina ne.� Ya fada hakan ne domin ya sa mata razana a jikinta, kuma ya ci sa’a domin kuwa jikinta yana kyarma ta dawo da baya, tana dubansa. “Ka ce kana neman waye? Justina?� Ashmaan ya daga mata kai alamun haka ne. Matsowa ta yi daf da Ashmaan sannan ta ce, “Justina ta dade da mutuwa, ba mu ga ; gawanta ba, ba mu san inda take ba. Amma ta mutu. Ni ban santa sosai ba, a unguwa kawai mun tashi.� Ashmaan ya zaro idanu, “Ta mutu? Ina neman ta ne in bata kudadenta miliyan biyu da ta taba ba Babana aro, shi ne ya ba ni hotonta ya kwatanta min unguwar nan ya ce duk ranar da na dawo Kasar nan in neme ta in ba ta saboda ta taimake shi.� Nora ta zaro idanu kasancewarta mayyar abin duniya, “Miliyan biyu? Waye ne zai ba Justina miliyan biyu? Ina ganin Alhajin nan ne zai bata, ita kuma saboda tsoro za ta bada aro. Ka yi haKuri mu koma inuwa, nice babbar Kawarta bata da Kawa kamana a nan unguwar.� Ashmaan ya saki ajiyar zuciya ganin abinda yake nema zai same shi ba tare da yasha wahalar da yake tunani ba. “Tunda ke babbar Kawarta ce na san kin san family dinta sosai, zan iya ba ki kyautar dubu dari biyar ki hada ni da iyayenta domin in ba su _ � kadarorinta.� Nora ta rufe ido ta sake budewa. � Tunda take bata taba ganin ko da dubu hamsin ba, amma yau gashi ance za a bata dubu dari biyar domin kawai ta fada inda gidan su Justina yake. Tuni ta sauke daron da -ke kanta tana dubansa, “Babu komai Alhaji.� ; Ashmaan ya dan saita abin daukar maganarsa, ya ce, “Amma me ya kashe ta ne?� A nan kuma sai Nora ta yi sit! Domin ba ta mance irin gargadin da aka biyo ta har gida aka yi mata ba, kasancewarta wacce tasan komai akan rayuwar Justina. Girgiza kai ta yi, “Ban sani ba woo.. Ka ba ni kudin in kai ka gidan da kake so ka sani, ba mu da nisa.� Ashmaan ya rikKe kansa, ya san zai sha wahala a gun Nora matuKkKa. “An ce an kashe ta ne?� Nora ta yi wani irin zabura, sannan ta dauki daronta ta aza a kai ta yi gaba abinta, tana tafe tana sake waiwayo Ashmaan, sai kuma ta yi kamar za ta dawo idan ta tuna makKudan kudaden sai kuma ta tuna da rayuwarta tana gaba da komai, don haka ta hakKura ta ci gaba da tafiyarta. Mutuwar Justina ta dawo mata sabuwa, tana son Justina fiye da tunanin mai tunani. Ashmaan ya rikKe kansa, dole ya tattara ya koma Hotel din da yake ya kwanta shiru. Kewar Ibtihal dinsa yana sake damunsa, dole ya jawo waya ya kirata. Sai dai ‘yan tagwayensa ne suka dauki wayar, hakan ma ya yi masa dadi, domin sun taimaka masa wajen rage masa dukkkan damuwar sa yake dauke da ita. Sai wajen yamma, a lokacin wurin ya yi sanyi, don haka ya fito cikin shigar Kananan kaya. Abin mamaki Sultan ya gani, shima cikin shigar kayan gida, yana daga zaune yana latsa waya. Har zai yi masa magana, ya Kyafta masa idanu, don haka ya basar kawai. Wannan karon mai gidan ne ya fito da kansa, Sultan ya ba shi hannu suka gaisa. “Ba ka gane ni ba ko? Ni abokin Samuel ne. Ina neman gona ne shi ne ya ce min in zo wurinka za ka taimaka min.� Daniel ya cika da farin ciki, ya san zai dan sami wani abu, don haka ya washe bakinsa suka sake gaisawa. Ashmaan yana daga nesa yana mamakin irin salon Sultan. Zama suka yi yana bashi labarin yadda wuraren suke da kuma irin amfanin da zai samu. Sultan ya aikawa Ashmaan text a kan ya zo ya aiwatar da aikinsa,. Ashmaan ya Karaso ya ba su hannu duk suka gaisa. Sultan yana yi masa wani irin kallo kamar bai taba ganinsa ba. Nora ce ta fito da nufin zubar da shara, tana ganin Ashmaan ta zaro ido tana nunawa Danicl ta ce, “Daniel ga mutumin nan shi ne.� Daniel ya ce, “Sannu. Ka yi haKuri ba mu San mene ne ya samu Justina ba.� Sultan ya dube su ya ce, “Wace ce kuma Justina? Ko matar nan da ta mutu shekaru kusan ashirin baya?� Gabadaya suka kafe Sultan da ido. Ashmaan ya dubi Sultan, ya riKe shi, “Don Allah kana da labarinta ne?� Sultan ya fizge kansa, “Sake ni mana malam. Na sani lokacin ina yaro Karami.� Ya fada tare da kawar da kansa. Ashmaan ya ce, “Zan ba ka miliyan daya idan har za ka gaya min labarinta. Kawai abinda nake son naji kenan, sannan ka dauke ni ka kai ni gidan iyayenta.�* Jin miliyan daya ya sake kidima Nora da mijinta. Sultan ya ware idanunsa ya ce, “Miliyan daya? TirKashi! Ni yanzu ma sai in gaya maka. Justina an kashe ta ne, saboda tana da cutar Kanjamau, shi ne wasu suka sassare ta suka kashe ta. A kan idona abin ya faru. Da farko ma ana tunanin tana da ciki ne, ashe duk sharrin mutane ne, bata dauke da komai. Nora da Daniel suka zaro idanu jin Sultan yana ta sakin Karya kuma hankalinsa a kwance. Yana gamawa ya ce, “Sai muje innuna maka gidansu ka bani kudina.� Ashmaan ya ce, “Amma na gode abokina. Nayi maka alKawarin inhar _ maganganun da ka gaya min gaskiya ce, zan daukeka har Kasar nan ka bari. Kai musulmi ne?� Sultan ya kalle shi ya ce, “A’a ni _ inyamuri ne.� Ashmaan ya yi murmushi, “Kayi haKuri ba fada bane.� Daniel ya ce, “Wannan labari akan Justina ba gaskiya bane. Mune munsan gaskiya.� Nora ta ware � idanunta ta ce, “Daniel! Ka zo mu yi shawara ya dawo gobe.� Sultan ya ware idanu, “Au labarin da zaku bayar ne sai kun yi shawara? Ga kudi har miliyan daya? Wanda za ku iya yin shekaru goma kafin ku same su. Ni babu ruwana ka Kyale su kawai ka zo mu je ingaya maka komai.� Daniel da ya kidime ya ce, “Pls ka dawo gobe zamu san abin yi, har ka ji yadda akayi Justina ta mutu.� Ashmaan ya yi masu sallama ya wuce. Yana tafiya Nora ta dubi Daniel gaba daya ta mance Sultan yana wurin, kuma ko ta tuna ba za ta kawo komai a ranta ba, kasancewar tare da mijinta ta gan _ shi. “Daniel kasan mutumin nan a lokacin irin wahalar da ya dinga bamu saboda kawai yana tunanin zamu je mu tona masa asiri? Ni ina jin tsoro kada ya kashe mu.� Daniel ya girgiza kai, “Yanzu mutumin ya mance � da mu, yasan kowa ya manta da maganar mutuwar Justina, don haka babu idon kowa akanmu ki yarda da ni.� Sultan ya rufe idanunsa ya nausa duniyar tunani, “Waye wannan mutumin? Me yasa yake bin duk wanda yasan yana da alaKa da _ sanin mutuwar Justina? Insha Allahu komai ya kusan zuwa Karshe.� Nora ta koma ciki Daniel kuma ya dubi Sultan yana harararsa, “Kai ina tunanin wani Alhaji ne mai kudi, da kazo maganar gona, sai gashi kana jin ance miliyan dayaka gigice. To noman nawa za ka yi?� Sultan ya dube shi yana sake nazarinsa, “Dubu hamsin gareni na kawo a bani gona muyi noma.� Daniel ya zaro ido, “Duk a dubu hamsin din?� Sultan ya ware idanunsa yana gyada kansa domin kan yana matuKar sara masa, ji yake kamar ya shake su. Daniel su gaya masa komai._ Daniel yaja dogon tsaki, “Ka tafi kawai. Ban san inda za ka sami wadannan � � abubuwan ba.� Sultan ya wuce abinsa yana taka Kasa kamar mai tausaya mata. Kansa a Kasa yake tafiya tunani ne kala-kala a cikin kwanyar kansa. “Sai ka zo mu tafi.� Muryar Ashmaan ya ji, don haka ya waiwaya, ya Karasa tare da bude motar ya shiga. Duk kwanar da suka zo sai Sultan ya ce su dakata, abin mamaki duk inda suka tsaya ‘yan sandansa ne cikin shigar fararen kaya. Ashmaan duk yadda yake tunanin lamarin Sultan ya wuce hakan. Sun nausa titi babu wanda ya iya cewa_ uffan! Ashmaan ya yi magana ba tare da ya dube shi ba, “Zamu wuce wurin da aka kashe Saudat!� Sultan idanunsa suna kafe a bisa titin kamar mai son sanin yawan motocin da ke wuce wa. “� Yan sandana suna wurin. Na sa daya aikin faci a wurin, na kai daya koyon kanikanci na babbar mota, daya _ _kuma yana can ya zama mahaukaci bashi da wurin zama da ya wuce wurin da akayl kisan nan. Suna nan dai sun mamaye wurin.� Ashmaan ya gyada kai, “Da haushi kake bani da nake zaton baka dauki abin da mahimmanci ba, amma yanzu na gama ganewa kalar naka daban ne. Ya akayi ka gano su Nora? Bayan komai yana hannun mu?� Sultan ya dan waiwayo ya dube shi, ‘Na gano ta ne, a dalilin C.1.D na, su suka yi min wannan KoKarin.� , Babu wanda ya sake cewa uffan, har suka iso Hotel din da Ashmaan ya kama Hotel. Ashmaan ya zauna a falo yana mayar da ajiyar zuciya, Sultan kuma ya wuce ciki ya watsa ruwa. Abincin da aka jere masu babu wanda ya dubi abincin. Sultan ya mike ya dauki Power Horse ya kai bakinsa, yana jin yadda sanyin ruwan ke sauka a cikin maKoshinsa. Yana nan tsaye a _ windo yana duban waje, sannan ya saki labulan ya dawo yana magana, “Ashmaan matar nan tana da shegen kafiya, da wahala ko goben ka koma ta saki jiki ta bamu_ .abinda muke so. Ya zama dole mu nemo mafita, domin ita ce take dauke da dukkan .bayanan da muke nema. Ina son sanin waye mahaifin Nasreen! Ko ma waye mahaifin Nasreen akwai wani boyayyen lamari a tsakani mai girman gaske. Ashmaan ko ban sake ganin Nasreen ba, zan_ sauke alKawarina da na dauka! Ni zan zama gatan Anti Saudat, ko da kuwa yin hakan zai iya sawa inrasa aikina, inrasa iyalaina, inrasa mutuncina, in rasa dukiyoyina. Zan aikata hakan da Karfin guiwana. Ashmaan mu nemo abin yi tun kafin wannan damar ta kubuce mana.� Sultan ya yi nisa, sannan ya ce, “Zan tura ma’aikata su kwaso min ita da mijinta, ba tare da sanin kowa ba. Yin hakan zai taimaka mana wajen sanin abinda ya kamata mu sani. Lokaci baya jiranmu, yau idan mutumin da ya aikata wannan laifin ya mutu ba tare da ya san da akwai Kwansa a duniyar nan ba, ba zan yafe wa kaina ba, zan kalli kaina a matsayin mutum mai sakaci da rashin mayar da hankali a kan abu mai mahimmanci.� Ashmaan ya gyada kansa, “Hakan zai iya yuwuwa. Amma Sultan baka ganin idan aka kama su ta Karfi za su iya botsare mana su hana mu jin abinda muke son ji? Kasan ita Nora tana da kafiya, duk baKar talaucin da suke ciki hakan bai sa ta saki jiki da mu ba.� Sultan ya sake kai Power Horse bakinsa ya zukKa, sannan ya dawo da dubansa ga Ashmaan, “Dan sanda yana sa Shugaban ‘yan daba ya yi bayanin da kudi basu isa su sa shi ba. Muna da abin da za mu jona masu suyi bayani ko basu yi ninya ba.� Ashmaan ya yi murmushi, “Kada ka wahalar da su, na tabbata za su yi bayanin.� Zakuda kafadunsa ya yi, “Kada ma su yi. Idan miliyan daya bata sanya su bayani ba, ina tabbatar maka batir da wayan wuta za su kawo bayanai dalla-dalla.� Sultan yana nan zaune, yana jin yadda Ashmaan yake soyyaya da matarsa kamar yau aka daura masa auren. Sai da ya sauke wayar Sultan ya dan dube shi ya ce, “Kasan wani abu ne? Wallahi ina mancewa ina tare ~ da wata mata a cikin gidana. Abinda ke daga min hankali yarinyar nan duk abinda muka yi sai ta gayawa mahaifiyarta? Kai ranar da naji da kunnena ban iya barci ba.� Ashmaan ya shafi kansa ya ce, “Mahaifiyarta fa ka ce? Wannan kam yafi Karfina. Wayewar ta yi yawa.� Sultan ya ce, “Yauwa kasan Allah? Idan ka sake ce min ni musulmi ne sai nasa anboye min kai, inga yadda Ibtihal za ta yi . Baka san dazu 6/9/22, 09:25 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 3 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* A JIYA MUN TSAYA Dan sanda yana sa Shugaban ‘yan daba ya yi bayanin da kudi basu isa su sa shi ba. Muna da abin da za mu jona masu suyi bayani ko basu yi ninya ba.� Ashmaan ya yi murmushi, “Kada ka wahalar da su, na tabbata za su yi bayanin.� Zakuda kafadunsa ya yi, “Kada ma su yi. Idan miliyan daya bata sanya su bayani ba, ina tabbatar maka batir da wayan wuta za su kawo bayanai dalla-dalla.� Sultan yana nan zaune, yana jin yadda Ashmaan yake soyyaya da matarsa kamar yau aka daura masa auren. Sai da ya sauke wayar Sultan ya dan dube shi ya ce, “Kasan wani abu ne? Wallahi ina mancewa ina tare ~ da wata mata a cikin gidana. Abinda ke daga min hankali yarinyar nan duk abinda muka yi sai ta gayawa mahaifiyarta? Kai ranar da naji da kunnena ban iya barci ba.� Ashmaan ya shafi kansa ya ce, “Mahaifiyarta fa ka ce? Wannan kam yafi Karfina. Wayewar ta yi yawa.� Sultan ya ce, “Yauwa kasan Allah? Idan ka sake ce min ni musulmi ne sai nasa anboye min kai, inga yadda Ibtihal za ta yi . Baka san dazu ZAMU TASHI naji haushi ba? Ashe haka mutum yake ji yana da addininsa a cire masa da Karfi da yaji?� Ashmaan ya yi murmushi har sai da hakoransa suka bayyana, “Kawai a lokacinne sai ka juye min sak!� Kafin ya Karasa Sultan ya jefe shi da gwangwanin Power Horse kuma ya ci sa’a ya same shi. Ko waiwayarsa bai yi ba ya tunkari Kofar fita yana cewa, “Zanje ingaida ‘yan gidanmu. Ashmaan ya mike, “Jirani mana malam. Kai kadai za ka kwashi ladan? Nima zan je.� Sultan da kansa yake janmotar, Ashmaan yana gefensa. A tsakiyar titi yaja burki da Karfi, sakamakon ganin wani a gefen titin yana wankawa mace da namiji mari, haka kowa ya tsaya yana kallo babu wanda ya iya cewa komai. Da Karfi ya ce, “Nasreeen!!� Ashmaan ya ware idanu, “Kashe mu za ka yi ne? Wacce Nasreen kuma?� Bai bashi amsa ba, sai balle belt din da ya yi ya fito yana Karasowa ya dinga wanke mutumin da mari yana Karawa. Ashe wai soja ne, yaran sun kusa sanya shi ya yi hatsari shi ne ya dage yana hukunta su. Yaso suyi dambe da Sultan amma ina� Karfin ma ba daya ba. Ashmaan yana tsaye yana kallon wanda ya fi shi zafi da zuciya. Daga baya ya Karasa ya finciko yaron daga hannun Sultan yana dubansa, “Kai baka da hankali da A.I.G za ka yi fada?�� Tsoro da firgici suka shige shi, a take ya sara masa yana mazurai. Sultan ko dubansa bai yi ba, ya Karaso gurin yaran yana duban su. Ko alamar kama basu yi da Nasreen ba, idanunsa kawai ke gizo yana nuna masa wasu mutanen daban a matsayin Nasreen. Sultan ya basu kudi yasa su a dai-daita sahu, sannan ya fincike Id card din gaban rigar mutumin ya gama dubawa, sannan ya. jefar masa. Har bakin mota mutumin ya bi su yana bashi hakKuri, Sultan ya dube shi sosai ya ce, “Kunsa ana zagin kaki, kunsa ana yiwa Soja kallon mara hankali, mara sanin ciwon kansa. Kun sa tsofaffi, yara, malamai, da ‘yan iskan gari, da zarar suka ji fadi sunan hukuma sai su kama tsine mana, wanda bamu san bakin wasu ba, kai tsaye tsinuwar ke isowa garemu ba tare da wani shamaki ba. Kuna sa kaki kuna wulaKkanta duk wanda tsautsayi yasa ya biyo ta layinku, wai a ganinku wani matsayi gareku. Kun mance idan za a kaiku lahira kwaye kakin za a yi a ajiye a gefe. Mutum baya taba tafiya da muKaminsa lahira iyakarsa a duniyar nan da ya samu, sai dai ya je can ya dibi dukkan zunuban da ya kwaso wa kansa. Ni zan yi maganin irinku sannu a hankali. Bana zalunci ban yarda a yi ba!� Sultan ya jawo Kofar motarsa suka wuce. Sannan ya shafi kansa ya ce, “Kasan wani abu ne? Bana tuki saboda idan har nayi sai idanuna sun hasko min Nasreen. Hakan yake sawa nake take burki a ko ina ba tare da nayi la’akari da motar da ke bayana ba.� Ashmaan ya ware idanu, “Da gaske kake wannan maganar? Dan tsaya a nan akwai abinda zan yi.� Sultan bai kawo komai ba, ya ja ya tsaya. Ashmaan ya fito daga motar ya zagaya ta wajen zaman direban ya ce, “Fito! Ka fito mana.� Sultan ya fito yana dubansa. Ashmaan ya shige mazaunin direba ya yi wa mota key, sannan ya ce, “Zagaya ka zauna mu tafi. Ina da mata da ‘ya’ya uku, idan na mutu Ibtihal za ta iya haukacewa, kai kuwa baka ma san zaKin macen ba. Ka . bari in lallaba rayuwata mu tsufa tare. Ta ya ya zan zauna kana jana a mota kana taka � burki a tsakiyar titi saboda soyayya? Ko zamanin nawa soyayyar a hankali na dinga bi da kaina, har na samu na mallaketa.� Sultan ya yi murmushi abinsa, ya wuce suka ci gaba da tafiya. Sun iso cikin gidansu sun kuma sami Abba, don haka ya yi ta basu shawarar yadda ya kamata su yi. Ashmaan ya ji dadin kasancewarsa a cikin gidan su Sultan domin yaga kara da karramawa. Gabadaya suna zaune a Katon falon kowannen su gabansa dauke yake da laptop Kanana masu tsada da kyau. A tsakiyar falon Nora ce da Daniel jikinsu babu inda baya rawa. Sun gama sakankancewa Alhaji ne ya turo mutanen nan domin ya ji ko sun mance labarin, sai aka yi rashin sa’a kwadayin abin duniya yasa suka furta wasu kalaman da yake nema ya jawo masu masifa. Sultan ya ba yaransa umarnin su fice daga falon, sannan ya dawo da kallonsa a kan Nora, “Sunana Abdullahi Lukman, wanda aka fi sani da Sultan wato S. Lukman. Ni jami’in ‘yan sanda ne, a tare da ni kuma akwai abokaina. Ina nufin a nan akwai Soja, akwai Dan jarida, ga kuma Barrister da likitoci. Ina nufin bamu neman wasu ma’aikata a waje, shi ya sa muka hada kawunan mu domin duk irin taimakon da muke nema a cikin mu akwai masani akan abin. Ku saki jikinku, bamu cutarwa, amma idan ka yi mana gardama ina da kayayyakin aikin da za su sanya a yi maganar gaskiya. Ina son sanin tarihin Justina, da kuma dalilin da yasa aka biyota cikin dare aka sassareta da ciki. An tabbatar min kina da masaniya akan komai. Shi wancan barazana ya yi maki zai kashe ki ko? Ni kuma bana barazana, sai dai insa bakin bindiga indauke numfashinki.� Yana maganar yana shafa mata bindiga a hanci. Nora ta kidime iya kidimewa. Daniel kuwa tuni ya yi alKawarin bayar da wadannan amsoshin domin gujewa tarin masifar da mutanen nan masu kwarjini suke dauke da shi. Kafin ya yi magana Nora ta fara magana, “Mu ba mu san komai ba, a kan mutuwar Justina, ku yi haKuri kada ku kashe mu.� Sultan ya dubi Ashmaan, sun tabbatar da kafiyar matar nan ya wuce tunanin su, haka za ‘ta yi wahalar shigowa cikin musulunci, saboda irin kafewarta. Sam Sultan baya son taba lafiyarsu, yana son yadda aka dauko su salin alin a mayar da su Don haka dabara tana neman ta Kwace masu. Khamis ya mike ya kama dan yatsan Nora ya yi mata wani irin izaya da yasa ta bude bakinta tana magana cikin wahala da tashin hankali. “Zan gaya maku komai zan gaya maku.� Ya sake ta yana murmushi, sannan ya jawo Stool ya zauna kusa da_ ita. “Dukkanmu nan muna da abubuwan yi, ki yi maza ki gaya mana abubuwan da muke son ji. Idan kika yi mana Karya, akwai littafin da ta yi rubutu zamu gane gaskiyar ki ne idan kina magana muna duba littafin. Khamis ya ware littafin wanda rubutun ba ta yi su a bude ba, bayanai ne dai irin wanda zai iya sa ka isa ga inda kake da_ buKata. Daniel ya dubi Nora ya ce, “Nora ki gaya masu, yaranmu suna buKatarmu a raye.� Nora ta dago kanta tana son Kare masu kallo, amma kwarjininsu ya wuce dukkan yadda take tunani. “Sunana Nora, sunan Kawata Justina, mun taso a unguwar Magajiya. Justina yarinya ce mai kyau da ilimi, yanayinta yafi kama da Fulani, shi ya sa mutane daban-daban suke cewa suna sonta, tun tana ‘yar Karamarta. Abin mamaki harda hausawa. Hakan yasa iyayen Justina suka dage akanta, kasancewar suna sonta kamar su kashe kansu. Komai suka samu ita suke siyowa. Justina ‘yar gata ce da ta taso cikin so da Kaunar iyayenta. Sun ci buri akan iliminta, haka kullum sai sun kaita wajen addininmu an yi mata addu’a saboda suna ganin idon mutane yana kan yarinyarsu. Asalin su ‘yan Zangon kataf ne, . amma an ce asalin Mamanta ‘yar Adamawa ce. Watarana muna hanyar dawowa daga Makaranta, wani saurayi ya tare mu ya ce yana son magana da Justina, ta Ki tsayawa. Haka saurayin nan kullum idan muna hanyar dawowa sai ya biyo mu, tun ba ma tsayawa har ta koma tana saurarensa. Na yi mata magana na ce, “Justin ba addininki daya da mutumin nan ba, me zai sa ki tsaya kina kula shi? Kin san halin iyayenki idan suka ji duk yadda suke sonki sai sun bata . maki rai.� Ba ta ba ni amsa ba, amma na ga tana ta murmushi. Sai daga baya nasan sunan saurayin Sani, haka Justina bata da hira sai na Sani, daga baya ma ta gaya min tana son Sani. Na damu sosai haka ina tsoron kada iyayenta su sani, shi ya sa nake basu wajen hira daga nesa da gidajenmu. Sani ya nunawa Justina yana son ya aureta, amma yana son ta musulunta ita kuma ta gaya masa gaskiya addinin shi baya burge ta ba za ta musulunta ba. Idan Justina za ta kama hannun Sani sai ya gaya mata addininsa ya hana hakan, haka ya ta6lba yin tafiya ya dade bai dawo ba, ranar da ya dawo ta ruga za ta rungume shi saboda farin ciki, amma sai ya dakatar da ita, ya gaya mata shi addininsa bai amince masa da aikata hakan ba. Da haka ya fara jawo hankalinta, har ta fara zama tana jin abubuwa akan addininsa. Ya ci gaba da ce mata, “Addininmu addini ne mai sauKi, a wajen jarabawa ce kadai mutane suke fadiwa imaninsu yake rauni.� Bayanan nan nasa yasa ta koma gida tana ta tunani, da naje gidan su take bani labari, nayi mata fada, na jawo hankalinta akan kada ta yarda iyayenta su ji. ““A hankali shigarta ta fara komawa ta addinin musulunci, tun iyayen basu kula har hankalin su ya dawo kanta. Babu Bata lokaci suka dauketa suka kaita wajen addu’a ° a ganinsu wani abu ne ya shiga kanta. A maimakon abun ya ragu sai ya cigaba da � Karuwa. Hakan yasa suka tsananta bincike suka sa aka kama Sani har tsawon kwana biyu yana kulle. Justina ta yi kuka ta Ki ci ta Ki sha, shi kuma yaki amincewa a sanar da kowa. Wannan lamari yasa Justina kwanciya ciwo har sai da aka sake shi. “Bayan ya fito ne ya yi ta neman hanyar da zai sake ganin Justina, amma abin ya faskara, domin ko Makaranta anhanata zuwa. Ni na nake kai mata wasika idan ya rubuto sai ta bayar da amsa inkai masa. Justina ta rame ta lalace amma kuma iyayenta basu tausayawa mata ba. Babanta ma cewa ya yi gara ta mutu da ya ganta tana cikin musulunci. Rana ta Karshe ne, ta gudu, taje ta sami Sani. A ranar ma ni na raka ta. Ya kama hannayenta a karo na farko ya ce, “Justina daga yau sunanki Saudat kin ji? Zan dauke ki in kai ki wurin wani babban Malami domin ya musuluntar da ke, ki daure komai zai zo mana da sauKki kin ji?� Babu musu ta amince masa, suka je wurin malamin ya gaya mata dokokin shiga musulunci ta ce, ta yarda. Sannu a hankali ya mayar da ita gidansu, ba tare da ansan ta fita ba, ta koma tana yin addininta a Boye haka duk lokacin da za su hadu da Sani ni nake hada yadda haduwarsu za ta kasance. Sani ya taimaka sosai wajen koyawa Justina _abubuwan addininsa. . “Da yake yarinya ce mai Kwakwalwa nan da nan take kwashe dukkan bayanansa. Har aka zo gabar aure. Ya tabbatar mata da zai aureta, zai dauketa ya kaita wajen babban yayansa. Haka suka shirya suka tafi wajen Yayansa. Sai dai ya Boye masa sauya addinin da ta yi zuwa nasa, kasancewar yasan halin Yayan akwai tsauri da Kin addinin da ba nasa ba. Don haka yasa Alkhairi ya nuna masa zai tura a nema masa aurenta. Sai dai suna fita daga gidan yayan yasa aka bi bayan su, har aka gano komai akan Justina. “Da aka gayawa Yayan hankalinsa ya ~ tashi jin cewar ba addininsu daya ba, amma kuma da yake yana da irin nasa burin sai ya � share ya bar zancen. Justina taje ta nemi gafarar iyayenta tace masu ba za ta Kara ba. Hakan yasa suka amince da ita, suka Kyaleta ta ci gaba da zuwa Makaranta. A hanyar dawowarmu ne aka sace mu da ni da ita aka sanya mu a cikin mota sai wani gida. A nan wurin mutumin nan ya yi wa Justina fyade. Tana kuka aka dauke mu aka dawo da mu inda aka dauko mu. Justina ta yi kuka, ta yi kuka kamar ranta zai fita. Ni nake ta ba ta haKuri, na kuma gaya mata ta kira Sani ta gaya masa komai, sai ta ce min, “Nora kin san waye ya yi min haka? Yayan Sani shi ya aikata min haka. Ba zan iya gayawa Sani ba, ko na gaya mashi ba zai yarda ba. Ya gaya min Yayansa malami ne. Me yasa zai yi min haka? Yanzu Nora ya zanyi?� Na ce mata ta yi_ shiru ta bar maganar. Abu kamar wasa sai da yayan “Sani yasa aka sace mu sau uku yana biyan buKatarsa da Justina.� * Al-ameen da ya yake jin sunan Justina din yana Bata masa rai ya dubeta ya ce, “Anti pls kira ta da Saudat dinta.� Kowa ya gyada kansa don sun fi gamsuwa da Saudat din fiye da Justina. Nora ta gyada kanta ta ci gaba da magana tana hawaye, “Ana haka kawai sai ga ciki. Ta shiga tashin hankali da bayyanar cikin nan, haka ta gaya min ba za ta iya zubarwa ba, domin angaya mata hukuncin wanda ya zubar da ciki tamkar ya kashe rai ne. Babu yadda ban nuna mata irin matsalar da za ta iya shiga ba, amma taki amince wa maganata. A lokacin da iyayenta suka ankare sai suka yi mata dukan tsiya suka koreta, ni na boyeta a gidanmu nasa aka nemo Sani ta fito tana kuka ta gaya mashi komai, sai ya gaggaya mata magana, ya zazzageta ya kuma ce-bai yarda fyade akayi mata ba, taje ta nemi wanda ya yi mata ciki � amma kada ta sake tunawa da wani mai suna irin nasa. RoKon duniyar nan mun yi � wa Sani amma yaKi taimaka mata. Ita kuma ta Ki gaya masa wanda ya yi mata hakan, sai � take ganin wannan wani al’amari ne mai girman da bai kamata yaji ba. Da farko a gidan mu ta fara zama, iyayena suka koreta shi ne tabi titi. Saudat tasha wahala a duniya, ta koma bara, tana samun abinda take ci, duk da hakan tana nan a cikin musulunci kullum da dogon hijabinta. Har sana’ar wankin mota ta yi domin ta dinga samun abinda za ta ci. Daga baya ne da mutane suka ankare da cikin jikinta shi ne musulmanku suka tsaneta, suka sa ta tsani duniyar gaba daya. Hakan yasa ta je har gidan Yayan Sani, ta bada sako a ba shi. Wannan lamari ya daga_ hankalin Yayan Sani har ya aiko mata da barazana. Haka ta ci gaba da renon cikinta cikin wahala da Kuncin rayuwa, shi kuma ya ci gaba da farautar rayuwarta, har Allah ya bashi ikon cimma burinsa na ganin ya kasheta. Wannan shi ne abinda na sani a kan Saudat! Idan an gaya maku wani labarin . sabanin wannan to Karya ake yi, wanda na gaya maku a yanzu shi ne gaskiyar.� � Sultan ya sauke ajiyar zuciya ba yadda ya kamata ba. “Kinsan waye Yayan Sanin? Kin taba ganinsa? Me ya sa ya kafa maki doka yake bibiyar rayuwarki?�� Ajiyar zuciya ya Kwace mata ta ce, “Ban taba ganinsa ba, ban san shi ba. Duk abubuwan da yake yi yana turowa ne. Kamar lokacin da aka kashe Justi� Ku yi haKuri aka kashe Saudat. Sai aka ce ba a ga gawanta ba, haka ba asan me ya biyo bayan kasheta da aka yi ba. Shi ne yake zargin ta gayawa wani ne kamar yadda ta yi ta aiko masa da barazana akan cikinta, da kuma cewar za ta tona masa asiri. Anduba kayanta babu wasu hujjoji, don haka aka biyoni gida akayi bincike a gidana aka ga babu komai,__, daga nan aka yi min gargadi da za a iya kasheni idan har na kuskura na fada wani abu. Iyayen Saudat sunyi kuka, sun so ko gawanta su samu, sun yi danasani. Yanzu haka Babanta yana kwance yana fama da ciwon zuciya, saboda rashin ‘yarsa. Amma ni har yanzu ban taba ganinsa ba, ko � gunansa ban sani ba, ku yarda da ni ba zan yi maku Karya ba.� Sultan ya bugi bango da Karfi yana jin babu ma amfanin wannan tatsuniyar. “Shi . Sanin ya za a yi mu gan shi?� Girgiza kanta ta yi, “Ban san yadda za a yi mu ganshi ba, amma akwai abokinsa wanda shi yake hadamu da shi a duk san da muke son ganinsa, zan je innemo shi sai ya gaya mana inda za mu je mu ganshi.� Sultan ya gyada kai yana dubanta, “Za mu mayar da ku gidanku, zamu sa ‘yan sanda su kula da shige da ficenku. Ina buKatar sanin inda zan je inga Sani a kwana biyu kacal. Kada’ki wuce hakan. Maganar miliyan dayanku da muka yi maku alkawan ‘yan sandanmu za su tafi maku da kudin sai kuyi amfani da su. Ya zama dole mu gano wanene azzalumin da ya aikatawa Saudat fyade ya kuma aika aka kasheta.� Sai da aka fice da su kafin suka zubawa juna ido da alama sun rasa mafita. Ashmaan ya fara magana yana duban su, “Zan watsa hotunan Saudat a duniya, zan rubuta muna neman wanda ya kasheta, akwai kyauta mai tsoka. Bayan nan da wasu kwanaki zan watsa hotunan Nasreen da Nawfal in kuma ambatar babban kyauta ga duk wanda Allah yasa ya gansu.� Mahbub ya dube shi a tsanake, “Mene ne fa’idar yin hakan?� Aslaf ya zare glas din idanuns *a yana sake duban Ashmaan, 6/9/22, 09:31 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 4 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Sultan ya gyada kai yana dubanta, “Za mu mayar da ku gidanku, zamu sa ‘yan sanda su kula da shige da ficenku. Ina buKatar sanin inda zan je inga Sani a kwana biyu kacal. Kada’ki wuce hakan. Maganar miliyan dayanku da muka yi maku alkawan ‘yan sandanmu za su tafi maku da kudin sai kuyi amfani da su. Ya zama dole mu gano wanene azzalumin da ya aikatawa Saudat fyade ya kuma aika aka kasheta.� Sai da aka fice da su kafin suka zubawa juna ido da alama sun rasa mafita. Ashmaan ya fara magana yana duban su, “Zan watsa hotunan Saudat a duniya, zan rubuta muna neman wanda ya kasheta, akwai kyauta mai tsoka. Bayan nan da wasu kwanaki zan watsa hotunan Nasreen da Nawfal in kuma ambatar babban kyauta ga duk wanda Allah yasa ya gansu.� Mahbub ya dube shi a tsanake, “Mene ne fa’idar yin hakan?� Aslaf ya zare glas din idanunsa yana sake duban Ashmaan, “Idan kayi hakan ZAMU TASHI Ashmaan za a sami matsala. Wanda muke nema zai gane magana bata mutu ba, daga nan zamu fara wasan buya.� Al-ameen ya girgiza kai ya ce, “Tabbas zai iya ankarewa da muna nemansa, ko ya gudu, ko kuma ya sanya mu fara farautar juna.� Haisam ya ce, “Zai fi kyau mu fara gano wanene Sani? A ina za mu gan shi?� Barrister Tajuddeeen idanunsa yana kan Laptop da alama shi ba zai yi Korafin ba. Sultan ya zare glas ya ce, “Abinda Ashmaan yake fada akwai alamun hakan za a yi. Yanzu lalube muke yi a duhu, a yanzu ne za a fara wasan. Kawai ya gudu a cikin daji mu kuma muyi farautarsa. Idan muna binsa a boye zamu ci gaba da samun matsaloli, gara yasan muna nemansa, ta hanyar guduwarsa ne za mu iya gane shi.� Ashmaan ya ce, “Very good mutumina. Hasashena kenan. Idan muka sa hoton Saudat zamu yi amfani da kalamai wajen jawo hankulan jama’a akan abinda ke faruwa, daga nan hankalinsa zai tashi, zai fara farautar Anti Nora. Ita ce macen da yake da tabbacin inhar hukuma ta gana da ita, kashinsa ya bushe. A lokacin da za a kaiwa Nora farmaki, mu kuma mun dauke su daga wannan wurin, haka yaranmu za su yi ta kula da motsin kowa. Tarko zamu kafa masa insha Allahu zamu kamo shi. Amma idan aka ce a nemo inda Sani yake, amsar ita ce babu wanda yasan a wacce duniyar Sanin yake ciki a yanzu. Kun ga ashe wahala za mu ci gaba da sha, har mu ji mun gundura da abin. Ku bar min wannan aikin @ hannuna ni na san yadda zan yi. Sai mu dage da addu’a domin ba a fara ba, yanzu dai za a fara wasan.� Wannan bayanai na Ashmaan da Sultan ya gamsar da kowa haka kowa a wurin ya jinjina wa kaifin tunanin su. Haka suka tashi taron kowa ya kama gabansa. Dukkan abubuwan da Ashmaan ya tsara, ya tsara su ne tare da taimakon Sultan, cikin ikon Allah aka_buga bayani akan mutuwar Saudat, yadda aka kasheta, da kuma yadda ake neman Nora, da kuma wanda ya yi kisan, ganin Nora kadai ne zai Sa a gano waye ya yi kisan nan. Hankula sun tashi, yanayi ya sauya, wurare sun canza Haka sun dauke Nora da mijinta, Abin mamaki da al’ajabi sai gashi anshiga an sace Nora da mijinta, a lokacinne ‘yan sanda suka ci nasarar kamo wanda yaje da ninyar yin kisan. Sai dai yin hakan ya Kara tada hankalin wanda ya aikata wannan . mummunar aikin. Haka Karin jin dadinsa bai bari wadanda ya tura sun san fuskarsa * ba, bare har a ambaci sunansa a Police Station. Wahalar duniyar nan sun sha a � wurin Sultan amma babu takamaiman bayani. Wannan abu ya Kara jefa Sultan a cikin dogon tunani. A kwanaki biyun nan babu ranar da ba zai yi mafarkin Nasreen �. dinsa a cikin wahala da masifa ba. A cikin garin na Kaduna Sultan ne tsaye yana , Karewa gidan su kallo da har sun mance da � wata Nasreen da ta yi rayuwa a cikin su. Yana shiga ya sami babu kowa, don haka ya kwanta, wani irin barci na babu gaira babu dalili ya kwashe shi. A Katon falon da shigowarsa kenan ya samu. Ya sami Abban zaune a falo ya Kurawa tv idanu, ita kawa Umma sai aikin masifa take yi, tana yi tana Karawa. Cike da mamaki ya shigo falon, sai ya dubi Umma sai kuma ya dubi Hafsat da take kuka kamar ranta zai fita. “Yauwa gara da Allah ya kawo min kai, ba zan iya ganin wannanr tashin hankalin ba.� Abba ya dube ta cike da _ takaici, wanda hakan ke nuni da idan ma asirin ake banka masa, to Allah ya kubutar da shi, “Kada ki kuskura ki sa min da a cikin shirmanki da ‘ya’yanki. Ba su ba ne ‘ya’yan so? Alhamdulillahi. Tun yaran nan suna Kanana nake gargadinki da ki daina zagin ~ ‘ya’yan wasu, amma kika sawa kunnenki auduga kika toshe. Ke baki son mazinaci ko? Kin tsani zina ko? ‘Ya’yan zina ba su isa su zauna a cikin gidanki ba, har sai da kika kora su suka bi duniya. Yau ga ‘yarki da dan zina a cikinta, kuma Wallahi! Babu mai zubar da cikin nan sai an haife shi. Haka babu matakin da zan dauka ‘yarki ce ki yi duk yadda kika gadama da ita. Daman ‘ya’yan so ai Karshen su kenan.� Sultan da yaji wani irin jiri mai Karfi ya shige shi, ya fada cikin kujera cikin wani irin jiri wanda bai san lokacin da ya zauna din ba. Yana ta kallon Hafsat na kallon tsoro da firgici. Hafsat ta Bata wayonta, amma bai ga laifin kowa ba, sai laifin mahaifiyarsa. Mace ce mai tsananin son kanta, sai Allah ya nuna mata ishara tun a gidan duniya. Yana son ya yi magana Abban ya daga masa hannu. “Babu ruwanka ban kuma yarda kayi magana ba, ka zuba masu idanu su Karata can. Ai kaf zuri’arsu babu mazinaci, don haka babu wani yaro da ya isa ya aikata zina a gidan Hajiya Salma.� Sultan ya mike ya dinga kifa mata mari yana Kwallo da ita, domin ji yake gara ya kashe ta da ya ga irin wannan abin kunyar. Firgigit ya farka daga irin barcin da yake yi, jikinsa duk ya jike da gumi. Idanunsa ya watsa a kan Hafsat wacce ita ta zo tashinsa. A dimauce ya ce “Ke zo nan. Uban me kike jira baki fitar da mijin aure ba? So kike sai kin gama zama Mama a gida kafin ki yi aure?� Hafsat ta turo baki tana mamakin nawa take da har za ta yi aure yanzu? Shi dai Sultan ya kasa dawowa hayyacinsa da irin mummunar mafarkin da ya yi akan Hafsat. Haka sai kallon cikinta yake yi kamar mai son dole sai ya tantance cikin gareta ko kuwa sharrin mafarki ne? Tirkashi! Duk ranar da Hafsat ta yi cikin shege babu ko tantama kashe ta Umma za ta yi ta huta. Ya fi kowa sanin yadda Ummansa ta tsani zina, ko da yake tsanar Zina a jinin zuri’ar Umma yake, kaf dinsu ba su Kaunar mazinaci ya matso inda suke, shi ya sa kullum a cikin tsaftace kansu suke. Nasreenn ta farka cikin dare tana ja da baya, haka hawaye masu yawan gaske suke zuba daga idanunta. Tabbas ta ji hannayen wani a jikinta, amma kuma ba ta san ko wane ne ba, sannan tana da tabbacin Mansur baya gidan, hasalima yayi mata sallama da zai yi tafiya. Idan wani ne ya shigo ina masu tsaronta? Lalubawa ta yi tana neman Nawfal bata ji shi ba, ga hucin mutum a dakin, Cikin kuka ta fara kwala kira, “Nawfall� Ji ta yi an toshe mata baki, ta yadda baza ta iya Kwacewa ba. Tashin hankali ya sake bayyana a bisa dakalin fuskarta. Da Karfi ta daddage ta ingice shi ta yi hanyar waje da gudu, sai dai bata sani ba, ta doshi bango ta buga kanta da karti. Tsananin azabar da ta tsirga mata yasa ta ja da baya, duk da haka bata daina Kofarin ficewar ba. Hannunsa yasa ya dawo da ita baya, yana Kokann banKadeta, Tana son yin ihu babu dama haka kuma karfinta ya soma Karewa. Mutumin da ke kwance akanta yaji anbuga masa wata sanda, mai girma da kauri. Da Karfi ya rike kansa sannan ya dago yana mazurai. Nawfal ya zaro dukkan idanunsa, “Mansur! Kai ne? Kai da ka yi tafiya yaushe ka dawo har kake KoKarin kashe Nasreen? Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Nasreen Mansur ne yazo yake son nakasa maki rayuwa. Ai na gaya maki mutumin nan baya sonki amma kika nuna min Karya nake yi. Ga shi ai shi yake baki wahalar nan.� Nasreen ta shafi goshinta da yake mata radadi, “Nawfal ai Mansur baya garin nan ya akayi ya dawo? Mansur baka sona ka fitar da ni daga wannan gidan Wallahi na gaji.� Mansur ya dan shafi kansa. “Kin gane ko? Kawai ina can ne aka yi min waya wai kuna son ku gudu ku bar gidan nan, ni kuma � da na ankare sai na shammaci kowa na dawo. Abin mamaki sai na sami kuna nan, Shaidan ne ya rinjayeni a kan ki Nasreen ke 6/9/22, 09:41 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 5 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Hannunsa yasa ya dawo da ita baya, yana Kokann banKadeta, Tana son yin ihu babu dama haka kuma karfinta ya soma Karewa. Mutumin da ke kwance akanta yaji anbuga masa wata sanda, mai girma da kauri. Da Karfi ya rike kansa sannan ya dago yana mazurai. Nawfal ya zaro dukkan idanunsa, “Mansur! Kai ne? Kai da ka yi tafiya yaushe ka dawo har kake KoKarin kashe Nasreen? Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Nasreen Mansur ne yazo yake son nakasa maki rayuwa. Ai na gaya maki mutumin nan baya sonki amma kika nuna min Karya nake yi. Ga shi ai shi yake baki wahalar nan.� Nasreen ta shafi goshinta da yake mata radadi, “Nawfal ai Mansur baya garin nan ya akayi ya dawo? Mansur baka sona ka fitar da ni daga wannan gidan Wallahi na gaji.� Mansur ya dan shafi kansa. “Kin gane ko? Kawai ina can ne aka yi min waya wai kuna son ku gudu ku bar gidan nan, ni kuma � da na ankare sai na shammaci kowa na dawo. Abin mamaki sai na sami kuna nan, Shaidan ne ya rinjayeni a kan ki Nasreen ke ZAMU TASHI ma kin san na yi matukar Kokari a kanki kamata ya yi ki jinjina min. Zo mu ga goshin.� Yana foKarin kai hannu_jikinta, Nawfal ya mika hannu kamar wanda zai Kwace ta, Nasreen ta buge hannunsa tana ci gaba da danna wurin da hannu, “Mansur na � yarda da kai a duniyar nan, ban san meyasa za ka bari har shaidan ya ci galaba akanka ba. Ni nace maka ka kwantar da hankalinka. Amma ji yadda kake yi min kamar baka taba sanina ba? A zatona ma wasu ne suke son cin amanarka?� � A nan fa Mansur ya gigice yana ta bata haKuri sannan ya fice ya barta daga ita sai dan uwanta. Yana ficewa Nawfal ya Karaso da sauri ya zauna kusa da ita, “Sannu Nasreen ba ki ji ciwo ba? Sannu kin ji?� Nasreen ta dan ture hannunsa ta ce, “Nawfal me yasa za ka dinga yin nisa kana barina? Yanzu da wannan mutumin mai warin bunsuru ya sami nasara akaina fa? Gaskiya ni Nawfal na gaji da zaman nan, ka taimakeni ka fitar dani idan ba haka ba zan iya rasa raina. Wannan gida da zamansa gara zaman mu a can Kankia tunda zamu fita gari muna jin hayaniyar jama’a. Mansur din nan bashi da imani Karya yake yi baya sona, mai sona mutum daya ne shi ne Deedinmu. Nawfal kayi wani abu mana kada na mutu abarka da gawa.� Nawfal ya girgiza kansa yana jin saukar kowacce kalma ta Nasreen kamar ana buga masa guduma. “A’a Nasreen insha Allahu ba za ki mutu ba, da Kafafunki zamu koma gida. Kin ga ina hada mana yadda zamu fita daga gidan nan, shi ya sa hankalinsa bai kwanta ba, yake tarwatsa dukkan shirin mu. Amma ki kwantar da hankalinki mu ci gaba da addu’a insha Allahu muke da nasara.� Nasreen da ta riga ta sare tace, “Wani abu kake yi akan fitar mu?� Kansa ya riKe dole tana son sai ta Kureshi, “Zan gaya maki kin ji? Ni dai ki kwantar da hankalinki.� ********((( Zakiyya da ta kwankwadi magungunan mata harda na hauka tashin hankali ya sauka a jikinta, sai wahala take tana nishi tana mayar da numfashi. A lokacin ne cikin sa’a Sultan ya shigo gidan da ninyar daukar wata takarda. Sai dai rashin sa’ar da ta tafka Sultan baya cikin hayyacinsa, hankalinsa yana kan binciken Nasreen da wani ya tabbatar masa yaga _ Nasreen tana yawon bara ita da dan uwanta. Sultan ya dube shi rai a babace, “Ka ga Nasreen ka kasa zuwa ka sanar min? Har kake cewa ka basu sadaka? Ta ya ya za ka yi min haka?�� Mutumin da yake matsayin kamar yaron aikinsa ya girgiza kai, “Ka yi hakuri yallabai a lokacin bansan sun bata bane, shi ya sa kawai nake ta yi masu kallon sani. Sai yanzu da nake ji. Amma tabbas Nasreen ce na gani da idanuna tana riKe da sandar bara, a Cikin garin Kankia.� Sultan fa ya gigice damuwarsa kawai ya isa garin Kankia da kansa ba aike ba. Zakiyya ta rungume shi tsam a jikinta tana sakin wani irin mahaukacin ajiyar zuciya. A duniya Sultan ya tsani yaga ana wulaKanta mace, shi ya sa yake daurewa kansa akan Zakiyya yana kiyaye abubuwa da dama. _ “Zakiyya kiyi haKuri inje indawo ina da aiki mai matuKar mahimmanci.� ; Kauda ta ya yi daga jikinsa y. shige � abinsa yana amsa waya, yana gaya masu Nasreen tana Kankia yanzu haka can za su nufa. Karaf a kunnen Zakiyya, a take ta nemi duk wata sha’awa ta rasa. A tunaninta Sultan ya gama zama da wata mace fece ba ita ba, ta ya ya ma za ace anga Nasreen? Ta daure iya dauriya ta ji, har ya kai bakin kofa ya juya yana kallonta da tausayawa. Allah ya gani baya sonta dai-dai da minti «: ya, amma martaban _ samunta a budurwa da kuma yadda ta kwantar da kanta ta zauna, ya sanya masa har ya ji a zuciya: yana_ tausayinta. Dawowa ya yi ya shafi kumatunta yayi mata sumba a goshi. Bai taba yiwa wata mace hakan ba, sai Nasreen dinsa, haka bai taba tusanin wata mace za ta iya samun kulawan.ba, idan ba ita ba. A natse ya yi amagana, “Idan kika zama mai haKuri za ki ji dadin zama da ni.� Kawai ya juya ya fice, yana jin takaicin yadda ko arziKin addu’a bai samu ba. Yana ficewa ta dauki waya jikinta hqr kyarma yake yi. A lokacin Hajiya Ladidi tana gidan . Hajiya -salma don haka ta amsa babu ko gaisuwa tsakaninsu ta hau bata labari, “Mama mun shiga uku. Angano Nasreen a Kankia, yanzu haka Sultan ya kama hanya ya tafi da ‘yan sanda. Mama idan Nasreen ta dawo na shiga uku domin sai ta koro ni waje. Yanzu mama ya zamu yi kenan? Ko za ki kaini wajen bokan nan ne tunda naga aikin malamin yakan yi masa aiki.� maman ta yi shiru na wani lokaci sannan ta ce, “Ki wantar da hankalinki Nasree: bata Kanki., tana can Mansur ya kusa aureta. Amma yanzu ina gidansu ne tunda “ya fara jin Kanshinta zai iya lalubota j? ba tare da mun ankare ba. Bari inyi magana da mahaifiyarsa zan sake kiran ki.� Ta sauke wayar jiki a sanyaye tana duban Hajiya Salma, “Hajiya yaronki Sultan yana da taurin kai, haka baya jin maganarki sam! Yanzu haka ya tara ‘yan sanda roka guda, wai sun je neman Nasreen a Kankia.� Hajiya Salma ta ware manyan idanunta gabanta yana tsananta fadiwa. � “tirkashi! Lallai ma yaron nan! So yake ya tona min asiri? To Wallahi bai isa ba, ba dai a wannan gidan ba. Kai akan yarinyar nan ina iya tsine masa in yi masa Allah ya isa nonona da ya sha. Bari in kira shi ingaya masa idan ya sake ya Karasa garin nan ban yafe ba.� Raruman_ wayarta ta yi tana daddannawa, ta sa a kunne. Zuciyar Hajiya Ladidi fari Kal! A zuciyarta ta ce, Mahaukaciyar banza! Yaushe zan iya wulakanta dana akan wata can! Yaro yana maki biyayya duk wata kina da kudi masu tsoka daga wurinsa, amma da yake banza ce ke sam baki fahimta. Ki tsine masa din mana ni ‘yata bata da asara, sai ya sako min ita ta auri wani miji goma ai ba uban goma bane. Firgigit ta yi a lokacin da Hajiya Salma take ce mata, “Kin ga ya ki dauka ko? Sultan saboda ya taka matsayin nan ne shi ya sa idan za a kwana ana kiransa baya dagawa? Zan ci gaba da kiransa har caji ya Kare da ni yake zance.� Sultan kuwa suna hanya, wayarsa tana Silent, bai ga kiran mahaifiyarsa ba, sai can ya lura da hasken wayar, yana kallo har ta tsinke bai dauka ba, haka kawai hankalinsa bai kwanta da ya dauki wayar ba. Isowarsu Kankia suka bazama nemansu. Da kwatance har suka iso wurin mai abinci. Tana ganin mota ‘yan sanda sun fito hannayensu dauke da bindigogi hankalin Mai abinci ya tashi.ta nemi ta tsure a nan tsaye. Aka budewa Sultan Kofa ya fito yana Karewa wurin kallo. Da ganinsa ka ga fulanin Yola, fuskar nan tasa babu fara’a bare alamun murmushi. Abin mamaki har gaban-mai abincin ya tsaya yana dubanta, � “An-ce Nasreen da Nawfal suna wurinki, ki nuna min inda suke.� Hantar cikinta ya kada ta girgiza kai tana zaro idanu, “Wallahi sun dade da barin wurina, tun lokacin da dayan almayirina ya ce, Nawfal ya satar min kudi na kore su, amma ada a bakin shagon nan suke kwana shi da ‘yar uwarsa.�� Sultan da yaji wani irin jiri yana neman kifar da shi, ya tsaya tare da tokarewa yana sake zuba mata idanunsa da suka sauya kala saboda bacin rai. “Nawfal ne barawo? Saboda Kaddara ta kawo shi wurinki kike tunanin barawo ne? Ni ban raini barawo ba, haka ban ba Nawfal tarbiyyar sata ba. Yarinyar da_ bata gani makauniya, da Kananun shekarunsu kika kore su? Bakin shagonki kawai kika bar masu su dinga kwana, cikin Kazanta, cikin sauro, cikin sanyi? Hasbunallahu wani imal wakil.� Sultan ya dinga nanata addu’ar nan yana sake jin idanunsa suna lumshewa. . “Babu damuwa mun gode. Amma daga yau ki cire a ranki Nawfal ba zai iya satan koda abincin ci ba, bare akai ga kudi.� Juyawa ya yi kamar zai hau mota sai ya juyo yana kallon yadda mutane suka taru suna dubansa, “Don Allah duk wanda ya ganta ko yake da labarinta, a kawo min ita zan bada kyautar miliyan goma, da wasu abubuwan more rayuwar dan adam. Ko da kuwa basa cikin hayyacin su ne, ko kuma � gawarsu.� Yana Karasawa ya fada mota. Dan sanda daya ya Karasa ya rubuta address din da za a iya samun su, idan har Allah yasa angansu. Yana wucewa a bakar motarsu, ‘yan wurin suka hau cecekuce, suna fadin ai ko da ganin yaran kasan ba talakawa bane, kaddarar rayuwa ce kawai ta kawo su irin wurin nan. Kowa da abinda yake fada, haka jin makudan kudaden nan yasa kowannensu cizon yatsa, wasu ma cewa suka yi za su bazama nemansu a duk inda suke a fadin duniyar nan. Sultan dai ya tafi ya barsu da cizon yatsa. Wannan yana cewa da ya sani shi ya dauke su ya ajiye a gidansa. Kai tsaye Sultan gidan Al-ameen ya wuce da tuni yasan da zuwarsa, aka shirya masa abinci kala-kala. Bayan sun kintsa ne, Jidda ta shigo dakin tana dariya. Sultan idan yana tuna abubuwan Jidda sai kawai ya hau murmushi, “Jiddan Uncle kina lafiya?� ; Ita ma murmushin ta yi ta Boye a bayan Al-ameen, “Ina yini Yaya Sultan?� Sai da ya sha sassanyan zobonsa tukun sannan ya amsa, “Lafiya lau. Idan zan tafi za ki hada min irin zobon nan naki mai * dadi insa a firij.� Ta amsa masa sannan ta zauna tana dubansa, “Yaya Sultan ka ga Uncle ko? Sai ya yi ta fushi da ni.� Sultan ya zaro idanu, Sai yanzu ya kula da yadda Al-ameen ke shan mur. “Rabu da shi Kanwata yau zanyi maganin Uncle.� Mikewa ta yi tana kwashe kayan da suka ci abinci. Tana fita Sultan ya dube shi, ‘““Meke faruwa ne Prince? Jidda fa ba macen da za ka dinga yin fushi da ita bane. Mace ce wacce samun irinta a wannan duniyar tamu da take cike da makwadaitan mata sai antona.� Al-ameen ya sha zobon yana lumshe idanu, “Sultan nasan halin Jidda, fushi kawai zan yi da ita ta shiga taitayinta ba wai “kalaman baki ba. Ni kaina Karfin hali nake yi, idan ba haka ba, sai yarinya ta rainaka.� Sultan ya ce, “Idan ka karanci mace ka gama cin ribarta. Amma kuma tunda ka iya haKuri da ita a zamanin can baya tun kafin ma ka aureta, ai a yanzu din ma za ka iya fiye da hakan. Ina yaran ne ban ji motsin su ba?� “Akansu muke fada. Daga an sa yaran nan a babban Makaranta ta addini da boko, a can suke gabadaya saboda akwai masu kula da yara a wurin. Sultan ina son yarana su taso cikin ilimi. Yara biyu kawai? Haihuwa ai yanzu ta fara. Amma sai yarinyar nan ta sa min rigima wai indawo mata da ‘ya’yanta sai kace ita kadai take son su ta shaKu da su. Yaran da a Kirjina suke barci sannan nake iya raba su da jikina. Babu lallamin da ban yi mata ba, amma taki, banda kukan cikin dare babu abinda Jidda take yi. Baka ga yadda ta rame ba? Ni har na manta laggonta fitinarta tasa na tuna “da ta tsani inKyaleta. Yanzu ka ga ai ta shiga taitayinta.� Sultan ya yi murmushi kawai yana fadin, “Sai a daina fushin hakannan kada a tarwatsa zuciyar Kanwata. Gobe zanje in gaida mai martaba, daga nan zan koma gida.� Sai yanzu Sultan ya tuna da kiran mahaifiyarsa don haka ya zaro wayar ya kira layinta. Tana dauka ta hau shi da masifa, “Kai ashe baka da hankali? Yanzu yaran nan ka tafi ka sake nemansu ko? Wai Sultan me ke damunka ne? Tun bayan barin yaran nan cikin gidan mu komai ya dawo mana, ka dinga samun daukaka, shi ne yanzu za ka dawo mana da masu fararen Kafafu? To baka isa ba! Ina baka umarni da kada insake jin wai kaji labarin su ka sake neman su. Yaran da aka ce duniya ma tsine masu take yi saboda halin karuwanci da Nasreen din ta koma? Shi kuma Nawfal din ai Sace-sace na ji an ce yana yi. Mazinata za ka dawo min da su cikin zuri’a? Wato kai ka rantse sai ka gurbata min zumri’a ko? Wannan ne kuma kayi kadan Wallahi.� Hajiya Ladidi ta dinga yi mata famfo. Dama kuma lokacin da zai auri Zakiyya, sai da Hajiya Ladidi ta hada da asiri, ta kuma yi mata rantsuwa Zakiyya tana Kyamatar maza. Amma kuma ai tafi kowa sanin Hajiya Salma ‘yar gari ce a wannan harkar. � Da Kyar ta amince shi ma saboda tana tsoron kada Hajiya Ladidi ta tona mata asiri ta gayawa duniya abinda suke aikatawa. Amma har gobe bata daina Kyamatar Hajiya Ladidi ba. Gabadayan su munafuntar juna suke yi, abinda bata sani ba, Hajiya Salma ta hada baki da Mansur ta bashi maKudan kudade aka zubawa Zakiyya maganin hana daukar ciki mai tsananin Karfi. Ta ce ba ta amince ta hada jini da su ba, za ta natsu ta samo masa yarinya a dangi, yarinya Karama mai natsuwa ko da kuwa a cikin gidan Alhaji Mu’azzam ne, daga nan sai su haihu. Hajiya Ladidi tana yiwa Hajiya Salma kallon biri, ita kuma tana yi mata kallon ayaba. Sultan da ya ji zuciyarsa tana suya daga irin kalaman Umma akan matarsa da dan uwanta sai ya sauke wayar kawai. Alameen bai tambaye shi ba, domin ya fahimci family issue ne. Yana tausayin abokinsa matuka, domin yanzu shi ne yake fuskantar tasa Kalubalen. Sultan ya mike kawai ya fice zuwa bayan gidan, a nan ya dinga kallon dokunan suna bashi sha’awa. Shi kadai yasan irin tunanin da yake yi. A ranar bai iya barci ba, haka Al-ameen bai matsa masa ba. Washegari da sassafe suka juya ba tare da sun sami cikar burin su ba. Yana zaune a falonsa yana shan ruwan . lipton da ya hadawa kansa yana jin kamar yana shan ruwan magani. Soyayyar Nasreen ta ci gaba da gallabar zuciyarsa tana hana shi zaman lafiya. Zakiyya ta shigo tana sanye da Kananan kaya. Tana zuwa ta zauna a gefensa, tana yi masa wani shu’umin kallo. Hannu ta kai bisa kafadunsa tana murmushi mai kama da kuka. Dayan hannunsa yasa ya zame nata a jikinsa ya dan dubeta, “Zakiyya sai mutum yana da natsuwa sannan yake samun Karfin guiwar aiwatar da wasu abubuwan. Bani da natsuwa ina cikin damuwa ki yi haKuri na tabbata ba zan dauwama a hakan ba, ki bari � da kaina zan nemeki Zakiyya kin ji?� Yadda ya yi maganar ta dan ji tausayinsa, amma kuma da ta tuna akan wata yake yin hakan sai ta ji duk bacin rai ya dawo mata, don haka ta kira Umma babu kunya ta zayyane mata komai. Daman Hajiya Ladidi da Hajiya Salma sun shirya zuwa don haka ta ce ta kwantar da hankalinta tana nan zuwa. Kwanaki biyu a tsakani Umma suka iso cikin shigar alfarma. Kallo daya za ka yi masu kasan naira ta yi kuka a wurin su. A Kalla idan ka tsaya duba nairorin da ke jikinsu za ka iya Kiyasta dubu dari biyar zuwa sama. Zakiyya ta fito da gudu daga ita sai rigar barci, a lokacin Sultan yana amsa waya, ya dubi su Umma ya Karaso gabansu. Ganin Zakiyya yasa ya bi shigarta da kallo cikin tsananin bacin rai. Yana kallon yadda ‘yan sandansa suke kawar da kai. Irin kallon da yake mata yasa Umma da Hajiya Ladidi suka dubeta, ita kanta Umman ta ji babu dadi, domin ita ta tsani rashin tarbiyya irin wannan. Babu wanda ya yi magana har suka shiga ciki a tsakiyar falo Umma ta fara magana, “Ke Zakiyya wani irin rashin hankali ne wannan? Me zan gani? Haka kike fitowa a gaban wadancan mutanen masu kama da dogare? Ni bana son rashin tarbiyya sam!� Hajiya Ladidi da ranta ya baci ta danne tana dan murmushi, “Amma dai ke baki da hankali. Me zai sa ki fito kai ko dankwali babu?� Sai a lokacin Umma ta kai duba akanta, idanunta suka dinga nuna mata ta yi 6/10/22, 00:45 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 6 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Hajiya Ladidi da Hajiya Salma sun shirya zuwa don haka ta ce ta kwantar da hankalinta tana nan zuwa. Kwanaki biyu a tsakani Umma suka iso cikin shigar alfarma. Kallo daya za ka yi masu kasan naira ta yi kuka a wurin su. A Kalla idan ka tsaya duba nairorin da ke jikinsu za ka iya Kiyasta dubu dari biyar zuwa sama. Zakiyya ta fito da gudu daga ita sai rigar barci, a lokacin Sultan yana amsa waya, ya dubi su Umma ya Karaso gabansu. Ganin Zakiyya yasa ya bi shigarta da kallo cikin tsananin bacin rai. Yana kallon yadda ‘yan sandansa suke kawar da kai. Irin kallon da yake mata yasa Umma da Hajiya Ladidi suka dubeta, ita kanta Umman ta ji babu dadi, domin ita ta tsani rashin tarbiyya irin wannan. Babu wanda ya yi magana har suka shiga ciki a tsakiyar falo Umma ta fara magana, “Ke Zakiyya wani irin rashin hankali ne wannan? Me zan gani? Haka kike fitowa a gaban wadancan mutanen masu kama da dogare? Ni bana son rashin tarbiyya sam!� Hajiya Ladidi da ranta ya baci ta danne tana dan murmushi, “Amma dai ke baki da hankali. Me zai sa ki fito kai ko dankwali babu?� Sai a lokacin Umma ta kai duba akanta, idanunta suka dinga nuna mata ta yi ZAMU TASHI Kari, don haka tasa hannu ta yamutsa gashin kanta, sai ga dinkin atachimen a tsakiyar gashin kanta. Da Karfi Umma take Salati tare da zazzaro idanu, “Yanzu Karin gashi kike yia gidan nan? Gashin doki? Zakiyya da wannan abun kike zuwa gaban Allah kina gaida shi?� Hannunta ta fizgo tana duba Kumbunanta. Umma fa ta gigice sosai, “Kumban nan da su kike Sallah? Hajiya Ladidi ina tsoro gaskiya! Kin san halina kin san abinda na tsana da wanda nake Kauna. Ya kamata Zakiyya ta gane bambancin Musulmi mai Sallah, da kuma wanda yake zaune zaman kafirci, wato mara addini. “Zakiyya ta yi tsuru-tsuru ta kira Umma domin ta Kwatar mata ‘yancinta, amma sai ta buge da wulaKanta ta a gaban Sultan. Dole dabara ta zo mata, ta ce, “Lahh ji yadda Umma ta rude. Jiya ne da naga bana Sallah shi ne na ce bari indanyi ado. Ai nima bana sawa Wallahi, kawai nace ne bari inkwatata tunda bana Sallah.� ta dan saki ajiyar zuciya, “Yanzu na ji magana. Amma duk da haka kada ki sake sawa kin ji Zakiyyata? Kada ki yarda su rinjaye mu gara mu su dinga ganin abubuwan mu suna yin koyi da mu. Kai kuma ka tsaya kana kallon mu ko magana babu. Ai da naga kana amsa waya ka bani mamaki. A zatona ciwon kunne kake yi shi ya sa baka amsa waya, ashe wanda ka raina � ne baka amsa masa.� Murmushi ya yi sannan ya gaida su ya � dora da cewa, “Ina amsawa. Abubuwa ne idan suka yi mana waya bamu sanin ma inda muka ajiye wayar.� Umma ta yi Kwafa ta ce, “Rufe min baki. Ina jin ka kusan kullum sai kayi waya da mahaifinka. Wato shi ne naka ni kuma ko oho ko? Allah ya yi Haidar magana duk da yana wajen training dinnan duk san da ya samu dama sai ya kirani yana jaddada min irin kewata da ya yi. Yanzu gidan babu dadi daga ni sai Auta, daman ita daga Makaranta sai daki ne baiwar Allah samarin ma taki kula su duk wanda ya zo sai ta ce sai ta gama Makaranta.� Sultan ya nufi fridge ya kwaso masu abubuwan sha, tunda ya kula Zakiyya bata iya taran baki ba. Sai da ya dawo gaban umman yana ajiye lemuka, sannan ya ce, “Umma kenan. Ita ba za ta yi aure ba, sai Karatu kawai? Ai kamata ya yi a yanzu a ce Hafsat tana dakin mijinta. A Kalla tana cikin shekaru ashirin da hudu kenan a duniya.� � Umma ta zaro idanu, “Duka-duka Hafsat din nawa take? In aurar da ita bakin cikin ~ ya kasheta ko? Ai gasu nan muna gani auren yanzu duk babu dadi, kai kanka cutar da ‘yar wasu kake bare har indauki ‘yar tatsitsiya kamar Hafsat inbada ita a kashe min ‘yata. Bari dai idan ta isa yi sai in aurar da ita amma ba yanzu ba. Ada ne nake wannan tunanin amma a yanzu na tsorata.� Sultan ya kama hanya zai fita, Umma ta kirawo shi ya dawo yana dubanta, “Yanzu fita za ka yi Sultan? Ai ka bari mu dan yi hira tukun ko?� Makullin mota yasa a kunne yana sosawa, sannan ya ce, “Zan aika ayo maku Order din abinci ne, Zakiyya bata jin dadi shi ya sa ba za ta iya girki ba, tana fama da yawan jiri da ciwon kai.� _ Zakiyya da’Hajiya Ladidi ji suka yi kamar su sa Sultan a Aljannah domin suna zuwa Zakiyya ta fara yanka idanu tana tsoron kada Umma tasan bata iya girki ba. � Haka sun dauki wani matsayi mai girma sun dorawa kansu akan Sultan yana sonta ne shi � ya sa ya ‘kareta.� Shi kuwa_ mitar mabaifiyarsa né baya so yasan idan ta sani _yau babu mai barci a cikin gidan. Ita kuwa _umma gabanta ne ke fadiwa kada yazo Zakiyya ciki gareta, domin tazo da magani ‘don ta, sake sanya mata a cikin tsumin mata ta bata tasha a matsayin za ta gyara ta. Tunawa da. abinda Zakiyyar ta fada na cewar tana al’ada yasata dan saki ajiyar zuciya. Yana fita� ta ‘yafito Zakiyya tana. wani shu’umin murmusHi ta ce, “’Yata ko + dai ciki gareki ne? Ko,da yake da kina da ciki ai da ban ji kin ce kina al’ada ba, duk da wasu suna yi ko da cikin.� Zakiyya ta yi dariya ta ce, “Babu komai Umma.� A nan hira ya barke masu kamar Kawayen juna, har Umma ta ci nasarar bankawa Zakiyya magungunan hana daukar ciki. Ita kuwa Hajiya Ladidi dadi ya Kara kamata ana son ‘yarta. Hajiya Salma ta dan dube ta ta ce, “Kin ga ki kwantar da . hankalinki Sultan ba zai sake ganin Nasreen ba, ta tafi kenan. Mansur ya tabbatar min � yana bata dukkan tsaron da ya dace da ita. Babu inda ta isa ta fito ko nan da Kofar gida. Abinda nake so da ke a yanzu ki dage da tsafta. Gidan nan sam ba a tsaftace shi. Ke kanki baki gyara kanki shi namiji ai dan gyara ne. Da zarar yasa hancinsa a wani wuri ya ji da wari shi kenan kin zube masa.� Zakiyya ta dinga amsawa da to. Shi kuwa Sultan mamaki ne ya kashe shi ganin gashin Zakiyya ba gashinta bane. Shi kwata-kwata bai taba kula ba, gani yake yi yarinyar Allah ya bata gashi, har yana yaba wa gashinta. Wannan shi ne acuci mazan kenan. A bangaren su Nasreen kuwa sun gama tsara komai yau suke son su gudu. Sai da suka tabbatar da masu tsaron nasu suna daga bakin Kofar tsakar gida, Mansur kuma baya nan. Nawfal ya kamo hannun Nasreen suka kama hanyar shiga bandaki. Suna � shigewa Nawfal ya fara taimaka mata ta dira ta baya, hakan yasa ta taka Kusa ta � � toshe bakinta saboda irin azaban da take ji har tsakar kanta. Nawfal ya bi bayanta ya dubi Kafafun da suka fara zubar da jini. Ga Magriba tayi, don haka ya fizge mata ta sake toshe baki tana hawaye. Shi kuwa sai fadin sannu yake babu KakKautawa. Tausayinta yake ji da gaske. A haka suka taka har suka isa wani lungu ya fita ya samo ruwa suka yi alwala. Bayan sun idar da SaHar ne suka yi addu’a suka shafa. Nawfal da Nasreen ba sa wasa da sallah idan lokacinsa ya yi. Haka idan ta fara al’ada shi yake zuwa ya samo mata tsumma, sai dai bata yarda daga wannan ya sake taimaka mata ba, tun tana jin kunyarsa har ta saki, domin babu mai taimaka mata sama da shi, shi kadai ne dolenta. Wani Kyalle ya samu ya daure mata Kafarta sosai ta yadda jinin ya matse baya iya fita. Tafiya suke babu ko waiwaye, domin garin Kauye ne babu abin hawa wadatacce, haka za su iya kiran garin da Dajin Allah, mutane . Kalilan ne. Nawfal ya tari mashin, yana son ya kai su cikin gari, sai dai bashi da ko naira da zai basu. Tunani kawai ya yi idan mutumin ya kaisu inda ya kamata suna sauka su ce basu da kudi. “Ina sake jan hankalin ku, ku guji abinda ba naku bane, ku guji cutar da musulmi koda da kalaman bakin ku ne. Daga Karshe kada ku ci hakkin wani, domin bashi ne watarana za ku biya a inda baku da shi.� Nasreen da take riKe da hannunsa daya ta dan girgiza shi, “Nawfal! Tunanin me kake yi? Bamu da sauran lokaci fa. Mu yi sauri mu gudu kada su biyo mu.� Mai mashin din ya ce, “Ka tare ni kuma ka tsaya dogon tunani. Idan ba za ka je ba ka gaya min intafi.� Nawfal ya girgiza kai hawaye kwance a Kwayar idanunsa, “Ka yi haKkuri ka tafi. Na tuna bamu da kudin mashin.� Mai mashin din ya dube shi, “To ku hau muje insauke ku a bakin titi domin nima can na nufa.� Cike da farin ciki, ya saita Nasrcen ta hau, sannan ya hau bayanta. Sun yi tafiya mai tsawon gaske, hakan yasa Nawfal ya dinga godewa mai mashin din yana jinjina Irin nisan wurin da titi. A bakin titi ya sauke su, Suna ta yi masa godiya har ya bace wa ganin su. Wajen wani mai gyaran robobi ya nufa ya roKe shi yana son ya ara masa wuKa zai gasawa ‘yar uwarsa Kafafu ne. Babu musu ya bashi, Nasreen ta zauna daga wani wuri da ta hango ankunna fitila. A nan ya dinga gasa mata Kafa yana mamakin yanzu har isha� ta yi amma mai likin roba yaki tashi ya haKura hakannan. Sai da ya gama gasa mata Kafar sannan ya maida masa wuKar yana godiya. Nasreen ta yi magana cikin galabaita, ““Nawfal ka matso inkwanta a kafadarka ina jin numfashina yana kasa min.� Nawfal ya goge hawayensa ya dan kwantar da ita a jikin bishiyar ya nufi wani_ wuri ya roKi ruwa sannan ya dawo ya bata. Tasha sosai sannan ya ce, duk su yi alwala su yi Sallah isha�1. Bayan sun idar ne suka mike suka ci gaba da tafiya cikin duhun nan. Nasreen tana makale da Nawfal kamar tana tsoron wani abu ya same shi. Wata mota ce ta tsaya a kusa da su, ba tare da sun tsaya tantance irin motar ba, aka fizgo su ciki. Jin Nasreen tana ihu yasa suka fesa masu wani irin fauda, tun daga nan basu sake sanin inda kawunansu yake ba. Tunda Sultan ya fita siyo abinci bai sake waiwayo gidan ba, domin sako ya baiwa Dan sanda yaje ya yi order ya kawo cikin gidan. Tun Umma tana sa ran ganinsa har ta cika ta yi tam! Bayan Isha’i ya shigo gidan ya tunkaro Umman da suke zaune a falon suna kallon film. Umma ta ce, “Ni? Abdullahi ni za ka wulaKanta? Da ni kake zance.� Sultan ya dubeta yana murmushi, “Umma yau kuma Abdullahi kai tsaye? � Babu ruwana idan Baba Mu’azzam ya jiyo ki.� Harara ta sakar masa ta kawar da kanta. � “Ki yi hakuri Umma a office aka kiramu muka yi ganawa da Shugaban Kasa, kan tabarbarewar hanyar nan _ shawarar yadda ya kamata mu biyo wa lamarin.� ya Dubi Hajiya Ladidi ya ce, “Mama baki da buKatar komai ko?� Hajiya Ladidi aka saki fara’a mai nuni da ta ji dadin kulawar da Sultan ya bata, “Ba ni da tunanin komai Sultan an gode.� Hajiya Ladidi ta jawo ‘yarta saboda su baiwa Umma da Sultan wuri, domin sun ji ta ce, jiransa take yi sai ta yi masa ta tas akan Zakiyya. Suna tashi suka ci gaba da hirarsu tsakanin da da mahaifi sai Allah. A cikin hirar ne take ja masa kunne akan rike amanar Zakiyya. Ta kuma tambaye shi ya ya halayyar Zakiyyar take?� Ya dubeta ido cikin ido ya ce, “Umma ni yaushe na zauna da ita ‘bare insan halayyarta? Saboda ita ne ma nake Kwace kaina da Karfin tsiya nake dawowa, amma bani da lokaci.� Umma ta zaro idanu, “Wani irin aiki ne haka Sultan da ba zai baka dama akan � iyalanka ba? Shi ya sa na gaya maka na tsani aikin dan sandan nan.� Shafa kansa ya ci gaba da yi yana lumshe idanu, “Umma da yake nayi aiki sosai ina da buKatar inhuta. Barci zan je inyi.� Umma ta sawa idanunta toka ta ce, ita babu inda zai je ta dade bata ga danta ba, ya zama dole yau su yi hirar abubuwan da ke faruwa. Bai musa mata ba, shima yana bukatar mahaifiyarsa da ya rasa kulawarta tun yana dan shekaru goma sha biyar a duniya. Ya rasa gane dadin uwa sai a ‘yan tsakanin nan. “Yaya maganar Nasreen? Yarinyar nan bata san da akwai aurenta a kanka ba, zai fi kyau ka saketa saki uku, ka ga ko ta yi wani auren babu laifi, amma yanzu kana barinta da kaya ne a kanta. Ga hukuncin aikata zina, ga hukuncin laifi mafi � girma, wato igiyar aure. Idan da gaske kana son Nasreen zai fi kyau ka tsinka igiyoyin � auren da ke tsakaninka da ita.� _ Sultan yana ji a duniya mahaifiyarsa ce kadai za ta iya fadin hakan a kan Nasreen bai dauki mummunar mataki a kanta ba. “Umma waye ya gaya maki Nasreen tana aikata zina? Umma shaidar zina akwai wahala. Shi ya sa ake son ka kyautatawa mutum zato. Kamar misali Zakiyyar nan kowa ya ga girmanta da yadda idanunta suke a bude sai ace ‘yar iska ce, bayan ba haka bane.� Umma ta ji dadin wannan yabon da Sultan ya yi wa Zakiyya, haka ta rage fargaba, tasan halin Sultan idan dai akan gaskiya ce sai ya fada sai dai a mutu. Amma dai duk da hakan hankalinta bai kwanta ta hada zuri’a da Zakiyya ba. Mikewa ya yi ya ce, “bobe fitan asuba zan yi. Mu kwana lafiya.� Ya shige dakinsa ta bishi da idanu kawai. Yana shiga ya sami Zakiyya har ta yi Sallama da iyayenta tazo wajensa. Babu musu ya biye mata har ta sami natsuwa. Ya rasa dalilin yadda shi kwata-kwata baya samun irin gamsuwar da ya kamata da ita. Yana jinta tana shirgar barci, amma kuma shi barcin ya � gagare shi. Tashi ya yi ya shige bandaki ya yi wanka ya natsa, sannan ya dauko Alqur’ani yana karantawa. Yana _ kallon agogo har biyu ta gota, ya tashi ya sake alwala sannan ya tada Sallah. A gaban Allah yake cikin rauni da KasKantar da kai, yana yiwa Allah kirari, daga bisani ya kwararo buKatansu wanda dukka a kan Nasreen ne da Nawfal. Yana ji a jikinsa suna nan a raye, amma kuma ba a cikin natsuwa ba. Ya jima yana kwararo addu’o’i cikin salon _ Qira’ar Sudais. Bayan ya yi addu’ar Istahara ne akansa da Nasreen ya yi kwanciyarsa a nan yana Salatin Manzo har barci ya dauke shi. A wata sassanyar lambu me, ma’abota ‘ya’yan bishiya masu kyau da_ sanya sha’awa. Yanayin wurin yana kadawa a hankali alamun ruwa yana iya kecewa a ko wanl irin yanayi. Yanayin ya sanya masa mugun kasala da dogon tunanin da kullum a cikinsa yake. Nasreen ta Karaso cikin shigarta na vest da wando wanda suka yi matuKar dacewa da jikinta. Kanta babu dankwali don hakane gashin yake a tubke a tsakiyar kai. Tun dazu take nemansa amma ta rasa inda ya Buya. Ganinsa a kwance yasa ta Karasa a hankali, ta kwanta kusa da shi, ba tare da ya ankare akwai mutum a kusa da shi ba. “Amincin Allah su tabbata a gareka, ya kyakkawan mijina, mai rikita ‘yan mata.� Ware idanunsa ya yi ya juyo yana dubanta tana kwance, kuma sama take kallo. “Kina ganin na cancanta ki nema min aminci? Na barku a lokacin da kuke da buKatata, na Ki yin abinda ya kamata domin nemanku.� Ita ma waiwayowa ta yi suna shaKar numfashin juna, domin bata san sun zo daf da juna haka ba. “Ka yi iya yinka Deedina, sai ka zuba ido ka barwa Allah sauran. Mu ne muka yi maka laifi, a lokacin da muke da_hanyar da zamu iya nemanka bamu yi hakan ba. Abinda nake so da kai, addu’ar nan da_ � kake yi mana kada ka daga Kafa da rana daya ka ci gaba da yinsa watarana sai labari.� Hancinta ya dan ja, ya ce “Wai wa ya koya maki magana ne? Nasan ki magana ma wahala take yi maki.� Juyar da fuskar ta yi tana kallon wani abu can ta ce, “Malamina ne ya koyar da ni tun ina jaririya.� Hannunsa yasa ya juyo da ita yana murmushi, “Yanzu kin fi malaminki iya komai, kin fi shi iya tsara zance.� Ta kasa jurewa irin sakon da yake aika mata cikin salonsa na dauke hankalin duk wata mace da ke kusa da shi. Da rabin hakan ya dauke hankalin Zakiyya da take jin za ta iya daukar wuKa domin yaki da ko wace ce a kansa. A hankali ta yi magana cikin sanyinta, “Idan kana gefena, kana katange -ni daga dukkan damuwa, damuwa tana samun muhallin zama ne a zuciyata da zarar * kayi min nisa. A lokacin ne nake jin kaina yana KoKarin raba kansa da jikina. Da ace zan 1ya yin ihu inyi shela inkirawo mutane su amsa kirana, da na ambaci mijina a gaban dubban jama’a a matsayin gwarzon da babu irinsa. Da zan sami dama, da na shiga daji, na kirawo za ki da kura, da dukkan wani nau’in ababe masu rayuwa a cikin dokar daji, in tambaye su akwai za ki kamar mijina? In tambaye su da kai da su waye jarumi kuma waye gwarzo?� Sosai ta hada fuskarsu wuri guda, numfashinta yana sauka a bisa hancinsa, “Na tabbata amsar 6/10/22, 00:48 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 7 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Hancinta ya dan ja, ya ce “Wai wa ya koya maki magana ne? Nasan ki magana ma wahala take yi maki.� Juyar da fuskar ta yi tana kallon wani abu can ta ce, “Malamina ne ya koyar da ni tun ina jaririya.� Hannunsa yasa ya juyo da ita yana murmushi, “Yanzu kin fi malaminki iya komai, kin fi shi iya tsara zance.� Ta kasa jurewa irin sakon da yake aika mata cikin salonsa na dauke hankalin duk wata mace da ke kusa da shi. Da rabin hakan ya dauke hankalin Zakiyya da take jin za ta iya daukar wuKa domin yaki da ko wace ce a kansa. A hankali ta yi magana cikin sanyinta, “Idan kana gefena, kana katange -ni daga dukkan damuwa, damuwa tana samun muhallin zama ne a zuciyata da zarar * kayi min nisa. A lokacin ne nake jin kaina yana KoKarin raba kansa da jikina. Da ace zan 1ya yin ihu inyi shela inkirawo mutane su amsa kirana, da na ambaci mijina a gaban dubban jama’a a matsayin gwarzon da babu irinsa. Da zan sami dama, da na shiga daji, na kirawo za ki da kura, da dukkan wani nau’in ababe masu rayuwa a cikin dokar daji, in tambaye su akwai za ki kamar mijina? In tambaye su da kai da su waye jarumi kuma waye gwarzo?� Sosai ta hada fuskarsu wuri guda, numfashinta yana sauka a bisa hancinsa, “Na tabbata amsar ZAMU TASHI daya za su taru su bani. Babu wani sai mijina. Kai ne na farko a cikin zuciyar Nasreen haka kaine na Karshe. Wannan maganar da nake gaya maka, ba daga bakina suke fitowa ba, a’a daga cikin zuciyar Nasreen din Deedinta suke fita. Don Allah mijina gaya min waye yake da sa’a kamar Nasreen dinka?� Sultan ya shaki Kamshinta mai sake rikirkita shi, ya lumshe idanu ya sake bude su tsaf a cikin nata. Idanun suka lume a cikin na juna suka shiga cikin jijiyo zuwa cikin kwanyar kansu; daga nan suka nausa duniyar jijiyoyin jiki suna bada wani irin ma’anoni da su kansu sanyin jikin su bai iya barin su sun gano wani abu da yake shirin wanzarwa ba. Cikin nuna alamun kalamanta sun dade da tafiya da shi ya ce, “Nasreen ina son idanunki, ina son bakinki, ina son komai naki Nasreen. Na rayu da sonki ne tun kina cikin mahaifiyarki.� Ruwan sama . ya ci gaba da sauka ba tare da iska ko kuma da Karfi ba. Sauka yake yi a hankali yana zuba bisa fuskokin su. A lokacin ne kuma suke amsar sakonnin da_ suke_ baiwa kowannen su. Sun yi nisa, hankalin su ya rabu da jikin su, Nasreen ta ji saukar wani abu mai zafi a cikinta hakan yasa ta saki gigitacciyar Kara. Sultan ya ware idanu a gigice, sai dai kafin ya ankare har Zakiyya da ke rike da wuKa ta fara ja da baya tana . neman hanyar guduwa. Nasreen yake gani cikin jini Zakiyya ta soke ta da wuKa. Bai � san lokacin da ya Karaso gaban Zakiyya da jikinta yake kyarma ba. Wukan ya amshe cikin fita hayyacinsa ya luma mata a ciki ya hankadata ta fadi tana shure-shure. Wurin Nasreen ya dawo yana jijjigata, ‘“‘Nasreen! Nasreen!! Ki tashi! Na _ yi alKawarin idan na rasa ki sai na Karar da dukkan zuri’ar Zakiyya! Sai ya kasance duk wanda aka ce masa ya san Zakiyya zai ji tsoron danganta kansa da ita.� Zakiyya da ta gama jin kalaman Sultan tana tsaye akansa ta yi matuKar kaduwa. Ta jijjiga shi ya bude idanunsa cikin firgici da tsoro. Kansa ya rikKe da Karfi yana jin kan yana sara masa. Har yanzu Mafarkin yana nan manne & kansa, haka kuma ya gaza fassara komai. Zakiyya ta sunkuya a gabansa tana kuka, “Me nayi maka za ka Karar da zuri’a ta?� Www.bankinhausanovels.com.ng Haushi da takaici yasa ya ja tsaki ya mike yana dubanta, “Ke kin yarda mafarki gaskiya ce? Idan kika aikata abinda na gani_. a Mafarkin me zai hana ban dauke kanki daga jikinki ba? Kisa kika yi, wanda ya yi � kisa shima a kashe shi.� Ya shige bandaki ba tare da ya sake waiwayota ba. Gudun kada ta gayawa Umma yasa ya shirya gaba daya ya wuce ‘masallaci, daga can ya yi gaba abinsa zuwa office. Yana kallon kiran Umma tsoro ya hana shi dauka gara dai idan ya dawo ko me za ta yi masa babu laifi tunda yana gabanta ne. Kiran Abbansa da ya gani yasa ya dauka. Abba ya ce, “Sultan ya maganar neman wanda ya kashe Saudat? Sultan ya saki ajiyar numfashi ya ce, “Abba ka taya mu da addu’a. Khamis ya je Ashmaan ya yi hira da shi, ya yi bayanin yana da alaKa da ita, kuma ya ci burin sai ya kama duk wanda yake da hannu a kashe ta. To bayan fitar hirar ne, Khamis ya sami kiran waya daga gun wani babban mutum mai suna Alhaji Kabiru, ya yi masa ikirarin idan bai fita a cikin maganar nan ba, zai jawowa kansa � matsala. Haka da lamba iri daya aka‘sake _ kiran Ashmaan shi ma dai ana yi masa gargadi a kan ya kiyayi buga irin wannan abubuwan. Mutanen dai ko su waye suna da wayo haka hatsari ne zaman su a cikin al’ummarmu. “Mun sa an bibiyi lambar da akayi kiran da ita, babu register a haka aka siya layin. Illolin da masu siyar da sim dauke da register suke yi mana kenan. Haka da muka duba location din ma’ana inda aka tsaya domin amsa kiran, sai muka ga a garin Kaduna ne, a dai-dai bakin ruwa. Da alama wanda zai yi wayar sai da yaje wurin da babu gidaje sai ruwan sannan ya tsaya ya yi waya. Haka mun so muje gidan iyayen Saudat din, mun jinkirta faruwar hakanne har sai su Nasreen sun bayyana, ta yadda za su ji dadin ganin jikokin su, tunda angaya mana sun yi kukan rashinta na tabbata za su rungume su a matsayin jikoki, haka gano mahaifinsu zai rage masu radadin da suke ji a game da rashin dangi wanda kullum sai Umma ta yi masu gori. Dazu take ba ni .umarnin insaketa tunda ba asan inda take ba Kila tana can tana iskanci da aurena a kanta.� Abba ya_ girgiza kansa_ yanayin � fuskarsa ta sauya kamar Sultan� yana ganinsa, “Sultan ku bi case din nan a hankali, bana son ka sa wani abokinka a cikin matsala. Ita kuma mahaifiyarku ba zan daina yi mata addu’ar shiriya ba. Na kawo idanu na zuba mata duniya ce kayi mai kyau “ma ya kaya Kare bare kuma baka yi ba?° Kul! In ji ka yanke igiyar aurenka da matarka, ina yawaita yin Istahara_ ina ganinta da tarin ‘ya’ya a gabanta, na tabbata wadannan ‘ya’yan naka ne _ Sultan, wadannan ‘ya’yan jikokina ne. Ka kwantar da hankalinka Allah yana tare da kai, kai dai kada ka saki addu’a kamar yadda na saki har mahaifiyarku ta ci galaba akaina. Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniyar nan lafiya.� Sultan ya nemi damuwarsa da ciwon kan da yake fama da ita tun mafarkin da ya yl ya rasa. Jinsa yake kamar babu wata sauran damuwar da ke cikin Kwakwalwarsa. “Na gode mahaifina.� Suka yi sallama cikin so da Kaunar juna. Yana son mahaifinsa, kuma ya tabbata babu mutumin da yake sonsa sama da mahaifinsa. Lumshe idanunsa ya yi, ga dai yunwa yana ji, amma tarin damuwa sun hana shi neman abincin da zai ci. Yau bai jima a Office din ba, ya dawo gida, kada damuwa ta kashe shi, gara ya zo ya zauna da mahaifiyarsa zai fi samun _natsuwa. Haka ya kwashe dukkan tarikitan shi ya fice da su. Gudu suke shararawa a bisa kwaltan ba tare da sun ja burki a ko ina ba, sai cikin katafaren gidan da suke ajiye dukkan � mutanen da suka sato. Nasreen ta laluba ta rike Nawfal bakinta dauke da addu’a. “Nawfal ina ne nan kuma? Yau mun shiga uku. Haka zamu yi ta gararamba har lokacin mutuwarmu tayi?� . Wani takurarren tsoho ya dube ta sosai, ya tabbatar makauniya ce, ya ce, “Yarinya kwantar da hankalinki ai lokacin mutuwar taki tayi. Ke dai kawai ki yi fatan cikawa da imani. Tsawon shekaru ashirin ana tsafi a nan gidan kin ga kuwa zuwanki ba zai sa a fasa ba.� Nawfal ya dubi takurarran tsohon nan da bai wuce a hure shi ya fadi Kasa matacce ba, ya sake waiwayawa, yara ne sun fi ashirin a Katon dakin. Nasreen ta furta cikin sanyi da karaya, “Hasbunallahu wani imal wakil! Allah mun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai kai Allah. Allah kai kake aiko mana da_ jarabawa, Allah ka bamu ikon cinye dukkan jarabawar da ta tunkaro mu. Bamu da dabara, bamu da wayo haka ba mu isa mu tambaye ka dalili ba. Ya Allah ka .hada ni da Deedina ko sau daya ne kafin ka dauki raina. Allahumma ajimi fi m sibati wa akhlifni min khaira minha. Allahumma…� Wata Kara suka ji mai Karfi da ya hargitsa su, haka ya kusa kaseewa Nasreen dodon kunne, wanda yasa ta yi saurin tura dukkan hannayenta a kunne ta. Da kuma ta tuna da Nawfal, tuni ta saki kunnen ta rarumo shi gam! Bata yada ko kashe su za a yi, a fara kashe mata Nawfal ba, ta fison � ya fara ganin gawarta zai fita dauriya akan ita ta daina jin motsinsa. A hankali Karan ya sauka sai kuma wata mata da ta bayyana tana magana cikin wata murya wanda tunda Nasreen take bata taba jin labarin irin muryar nan ba, “Idan kika sake yi mana addu’a a nan babu shakka za ki bakunci lahira tun lokacin tafiyarki ba ta yi ba. Za mu toshe maki maKogoro, kin ga baki gani kuma ba ki ji bare ki mayar. Mun fi buKatarki a kan kowa da ke dakin nan. Kinsan iya lokacin da muka kai muna binki? Tun ranar da aka dauki cikin ki. Sai dai ranar da muka zo mu dauke ki, a ranar wani yaro yasa aka daukeki suka ci gaba da baki kariya da Addu’a. Idan mun zo cikin . dare za mu dauke ki sai mu sami mayen yaron nan yana kanku yana yi maku addu’a. Akan rashin kawo ki nan yasa har yanzu ba a bani kambuna na sarautar Sarauniya ba. Yanzu ina murna burina ya cika shi ne za ki fara yi mana addu’a?l Ki kiyayi kanki!� Bat! Suka nemeta sama ko Kasa suka rasa. Nasreen ta sake fasa kuka, tana jin labarai masu kama da almara a cikin dan takurarren rayuwarta. Ko ina nemanta ake yi kamar wacce ta yi masu sata. Wani irin Kaunar Sultan ya sake mamaye zuciyarta, tabbas Sultan namiji ne, ya taimakawa rayuwarsu. Mahaifiyarsu haihuwarsu kawai tayi, amma Sultan shi ne uwa shi ne uba. Ya yi masu abinda ko iyayensu suna raye iya abinda za su yi kenan. Farin cikin jin Sultan baya barci saboda su yasa ta lumshe matattun idanunta, hawaye suna ci gaba da sauka. Za ta yi magana Nawfal yasa mata hannu a baki ya rufe bakin, “Ke kada ki sake magana. Jirani ina zuwa.� Nasreen ta � Kankame shi, “Wallahi ba za ka tafi ko ina ka barni ba.� Dole ya koma ya zauna kanta � _-yana bisa kafadarsa. Nawfal ya kafe yaran da idanu dukkansu suna takure kuma da kayan Makaranta a jikinsu, hakan ke nuni da daga Makaranta aka kwaso su domin cika burikan duniya kacal! Nasreen ta fara magana cikin hawaye, “Idan sun kashe ni, duk yadda za ka yi ka yi domin ganin ka sada gawata ga Deedina. Idan ka yi min wannan ka gama min komai dan uwa.� Girgiza kai ya yi yana jin Kwarin guiwa ba tare da ya sare ba, “Ba su isa suyi maki komai ba.� Tsohon nan ya sake kallon Nawfal da alama a Kufule yake da shi, “In ji uban wa ya ce maka ba za a yi mata komai ba? A matsayinta na wace? Iyye! Na ce a matsayinta na wace?� Nawfal ya zabga masa harara ya ce, “A matsayinta na RUBUTACCIYA! Kuma baiwar Allah. Ki kwantar da hankalinki -Nasreen, tunda makircin masu yinta basu kashe mu tun muna ‘yan jinjiraye ba, bana jin Karamin tsafi irin wannan zai iya taba lafiyarmu. Babu wanda ya isa ya sauya abinda Allah ya rubuta. Ina da tabbacin ko zamu mutu Allah ba zai bari mu mutu ta hanyar tsafi ba.� Tsohon ya dube shi ya tabe baki. Kawai sai ya shiga habaici, “I war haka gobe ai har mun manta ansha jinin � wasu, anyi farfesun kayan cikin su.� Babu wanda ya tanka masa ita dai Nasreen duk addu’ar da ta zo bakin ta yi take yi. Haka shi ma Nawfal idan ya yi addu’ar sai ya tofa mata. Cikin rada ta ce, “‘Nawfal bamu yi sallah ba.� Girgiza kansa ya yi, “Ba za su barmu muyi Sallah a nan ba. Mu yi addu’a kawai Allah ya kubutar da mu.� Shiru dakin ya yi sai kukan yara da ke tashi lokaci zuwa lokaci. Cikin dare kowa ya yi barci amma banda Nasreen da dan uwanta. Dukkansu saKe-saKe suke yi kowa da irin abinda yake ayyanawa. Ce mata ya yi zai je bandaki sannan ya samu ta sake shi. Yana fita ya dinga kallon hanyar yana mamakin irin girman gidan. Kai tsaye dakin tsafin ya leKa, a lokacin ne kuma kunnuwansa suka ji yo masa maganganun matsafan, haka kuma ya zura_ idanunsa, idanuwansa suka gane masa abinda ya gigita shi. Wata ce a shimfide kamar gawa. Shugaban tasu tana zaune a kan kujerarta, wata kuma wacce babu ko tantama ita ce, ta bayyana dazu ta yi wa Nasreen gargadi. Shugaban ta fara magana, “Muna taya ki murnar zama_ sarauniya gobe. Tsawon shekaru ashirin kin kasa karban kambun nan sai gobe za ki karba? Ni nafi ganin rashin Kwazonki ne ya jawo maki wannan abun. Idan ba haka ba, na shiga gidan malamai ma, na dauko yarinya na kuma sha jininta, bare gidan masu alaka da marasa addini? Gobe da kanki za ki ba dodo jininta, mu kuma za mu sha kayan cikinta, za mu fasa kanta mu shanye Kwakwalwarta, idan muka yi hakan za mu sami Karin lafiya.� , Gabadaya suka maimaita yi wa Sarauniyar gobe murnar samun wannan_ kambu. Ta ci gaba da magana kamar ba za ta yi ba, “Kai kuma sai yanzu ka kawo mana wannan yarinyar? To ba zan ce baka yi KoKari ba, ka yi namijin Kokari. Kun burge Kungiya a lokaci guda kun kawowa dodo kawunan da ba zai taba manta ku ba, haka zaku yi ta samun daukaka a duniya. Sai kuma ke Sarsarina, kina da taurin kai, mun baki nan zuwa gobe ki kawo mana mahaifiyarki da ranta, kuma ta budi idanu ta ganki a matsayin wacce ta kawo ta wajen tsafi, ki amshi tsinuwa daga gareta, sannan mu aikata lahira. Kuna gani nan, ban sami daukaka ba, sai da na kawo mahaifina da mahaifiyata da suka dauki son duniya suka dora min, haka nima bani da wadanda nake so kamar su. Amma na rufe idanuna na dauke su na kawo su gaban dodo, suka dube ni cikin dimuwa suka tsine min, suka yi min fatan tsiya, suka ce ba zan gama da duniya . lafiya ba. Kun ji mutanen da suke Karyar suna sona, amma sun kasa sadaukar min da � Kaunar da suke yi min ta hanyar bani rayuwar su.� Gabadaya dakin aka fashe da dariya. Abin mamaki labarin da ya kamata ayi ta mata kuka, wai dariya suke yi mata har da kifawa suna tashi. Sai da ta daga wata sanda sannan duk suka yi shiru. Ita dai wacce aka kira da Sarsarina babu fara’a a fuskarta. “Ya shugabata, ban taba yi maki musu ba, anbuKaci mahaifina na dauke shi na bayar da shi, anbuKaci mijina duk na bada su. Mahaifiyata ta sha wahala akaina, bana _ fatan inzama sanadiyyar barinta duniya. Ya shugaba a bar ni da wannan daukakar ta isheni, bana son Kungiya ta sake bani wata daukaka ko matsayi.� Nan da nan annurin fuskar wacce aka kira da shugaba ya bace bat! “Ke! Kada ki kawo mana zancen banza kin ji? Ya zama dole ki kawo mahaifiyarki da kanki ba sako zan ba wani ya kawo min ita ba, albarkar da ) na samu agun iyayena kafin su bar duniya, sai kowannenku ya sami wannan albarkar. Za ki kawo ta ko kuma sai na dauki mataki akanki? Zan iya daureki shekaru dari ina gana maki azaba, bayan kuma na daukota da Karfin tsiya.� Sake KasKantar da kanta tayi, “Ina neman tuba ya shugabata. Na amince zan kawo mahaifiyata da ranta. Farin cikinki a kullum shi ne nawa.� A nan suka yi wasu maganganu wanda su kadai suka san abinda suke cewa. Sannan aka ba wani wuka ya karba yana mai sake rusunawa alamun girmamawa. Wannan yarinyar da ke kwance kawai ya caka mata wukan, wanda yasa Nawfal gigicewa ya ture wani abunda bai san ko mene ne ba, jikinsa babu inda baya rawa. A gigice suka walwayo basu ga kowa ba, a take aka tura wasu guda biyu su je su bincika waye yake yi masu leken asiri? Jikin Nawfal yana rawa, yana KoKarin komawa dakin da aka kai su sai dai ko sama ko Kasa ya rasa gane wani dakin ne? Hakan yasa ya sami wuri ya labe jikinsa yana kyarma. Ita kuma Nasreen da ta ji shiru, sai kawai ta fito tana lalube tana neman Nawfal. Duk a tunaninta sun tafi da Nawfal dinne shi ya sa ta gigice, tana tafe tana cin karo da abubuwa. Don haka mutanen nan suna fitowa suka yi arba da ita tana lalube. Cak! Suka dauketa suka kai dakin tsafin. Nawfal yana jin shiru ya koma yana duba dakin, da Kyar ya gano dakin yana shiga babu Nasreen babu dalilinta. Ya duba ko ina bai ganta ba, hankalinsa ya sake tashi, ya fito yana dube-dube. Kai tsaye dakin tsafin 6/10/22, 00:48 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 8 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Nan da nan annurin fuskar wacce aka kira da shugaba ya bace bat! “Ke! Kada ki kawo mana zancen banza kin ji? Ya zama dole ki kawo mahaifiyarki da kanki ba sako zan ba wani ya kawo min ita ba, albarkar da ) na samu agun iyayena kafin su bar duniya, sai kowannenku ya sami wannan albarkar. Za ki kawo ta ko kuma sai na dauki mataki akanki? Zan iya daureki shekaru dari ina gana maki azaba, bayan kuma na daukota da Karfin tsiya.� Sake KasKantar da kanta tayi, “Ina neman tuba ya shugabata. Na amince zan kawo mahaifiyata da ranta. Farin cikinki a kullum shi ne nawa.� A nan suka yi wasu maganganu wanda su kadai suka san abinda suke cewa. Sannan aka ba wani wuka ya karba yana mai sake rusunawa alamun girmamawa. Wannan yarinyar da ke kwance kawai ya caka mata wukan, wanda yasa Nawfal gigicewa ya ture wani abunda bai san ko mene ne ba, jikinsa babu inda baya rawa. A gigice suka walwayo basu ga kowa ba, a take aka tura wasu guda biyu su je su bincika waye yake yi masu leken asiri? Jikin Nawfal yana rawa, yana KoKarin komawa dakin da aka kai su sai dai ko sama ko Kasa ya rasa gane wani dakin ne? Hakan yasa ya sami wuri ya labe jikinsa yana kyarma. Ita kuma Nasreen da ta ji shiru, sai kawai ta fito tana lalube tana neman Nawfal. Duk a tunaninta sun tafi da Nawfal dinne shi ya sa ta gigice, tana tafe tana cin karo da abubuwa. Don haka mutanen nan suna fitowa suka yi arba da ita tana lalube. Cak! Suka dauketa suka kai dakin tsafin. Nawfal yana jin shiru ya koma yana duba dakin, da Kyar ya gano dakin yana shiga babu Nasreen babu dalilinta. Ya duba ko ina bai ganta ba, hankalinsa ya sake tashi, ya fito yana dube-dube. Kai tsaye dakin tsafin ZAMU TASHI ya koma ya sake labewa. Ganin Nasreen a hannunsu yasa jikinsa ci gaba da bari. Har yanzu yarinyar da suka kashe tana nan kwance an sa wani KoKo antara jinin. Nawfal ya rasa abin yi yana nan a labe ya ji suna cewa, “Makauniyar banza! Me zai sa ki fito kina yi mana bari bayan ke ba ganin komai kike yi ba? Sai gobe da daddare zamu yankaki saurin me kike yi da za ki kawo kanki?� : Nawfal ya saki ajiyar zuciya. A lokaci daya tsoronsa ya dawo da yaji shugaban~ � tana cewa, “Ina jin Kamshin mutum a kusa da mu. Ba yarinyar nan ce muka ji motsinta ba, saboda sai da aka caka wukKan nan sannan muka ji barin abu alamun antsorata. Ku je ku sake duba min sosai, haka ku duba dan uwanta dinnan naga yana da tsaurin ~ idanu, idan shi ne ku kawo min shi inyanke kansa musha farfesu. Nawfal ya lallaba cikin sa’a ya koma dakin ya kwanta kamar mai barci. Duban duniyar nan sunyi basu ganshi ba, da suka koma dakin suka haske shi, suka tabbatar da barcin yake yi, kafin suka fice. Hankalin Nawfal yana gun Nasreen, idan bata dawo ba, ya zama dole ya-tashi ya bi bayanta sai dai komai zai faru ya faru. Yana jin aka shigo da ita, sannan wanda ya shigo da ita din ya fice abinsa. Nawfal ya tashi zaune ya jawota jikinsa yana jin yadda take kyarma, “Nawfal ina ka tafi ka barni? Nawfal me yasa za ka . dinga yin nesa da ni?� Hakuri kawai yake ba ta. Yunwa da ~ Kishin ruwa sun hadu suna neman su yi masu illa, domin tunda aka kawo su sun KI cin komai haka sun ki shan komai. Gaba daya sun soma galabaita. Sai ga wani namiji da abinci da ruwa ya kawo yana hararar su, “Ga irin abincin da kuke son ci nan ankawo maku. Kin ci sa’a ba ma yanka mutum idan « yana jin yunwa, da haka zamu sha farfesun ki. Maza ku cinye.� Nasreen ta ce, “Oh Nawfal kana jin yadda ake fadin yanka mutum kamar za a yanka rago?� Nawfal ya dinga diban abincin yana sa mata abaki, haka take amsa tana ci tana shan ruwa har cikin ya cushe, sannan shima ya ci sosai. Tsohon nan ya dube su ya tabe baki. Nawfal yana son sanin dalilin kawo wannan tsohon a cikin yara. Haka ya ishe su da kallon rainin hankali. Washegari kamar yadda suka yi alkawari haka suka shirya Nasreen za a kaita a kasheta. Tsohon nan sai ya dubi_.� Nawfal ya tuntsure da dariya. Nawfal dai addu’a yake yi iya Karfinsa bai daina ba, + haka ma Nasreen gabanta yana fadiwa tana addu’a. Tunda suka kama hanyar dakin da ita, ta nemi duk wani tsoro ta_ rasa. Damuwarta daya Nawfal da za a raba su. Ta fara tirjewa suka jawota da Karfi. Nawfal ya ~ dubi ruwan da suka sha suka bari, ya dauko ya kafa kai yana addu’a. A lokacin ita kuma aka shiga da ita, aka kwantar da ita. Shiru. ta yi tana ambaton sunayen Allah. Bayan sun gama surKullensu ne aka daga wuKar da ninyar soka mata. Ba tare da sun ankare ba, suka ji saukar ruwa kamar yayyafi, wanda Nawfal ya watso. A take kowannensu ya fara atishawa tun suna yi har suka bar dakin, ba tare da Nawfal yasan ina suka buya ba. Shi dai ya Karasa ya daga Nasreen yana janta tana cewa, “Nawfal har yanzu Kafata da ciwon nan bana iya taka ta sosai. Shi dai janta kawai yake yi. Bai san inda yake tsoma Kafafunsa ba. Tsayawa ya yi yana haki a lokacin da yaga Kofofi sun rabu biyu. Nasreen da ba gani take yi~ba ta ce, “Nawfal me yasa muka tsaya?� Ya ce, “Nasreen Kofofi biyu na gani na rasa wacce zamu shiga?� “Ka duba hannun dama mu bi hanyar. Kafin ka shiga mu _ karanta Ayatul Kursiyyu.� Babu musu ya aikata abinda ta gaya masa. Yana tsoma Kafafunsa ga mamakinsa sai gasu a waje a bakin titi. Waiwayowa ya yi yana son ganin Kofar. Sai dai ko sama ko Kasa babu wannan Kofar. Nawfal ya saki KakKarfar ajiyar zuciya ya ce, “Allah mun gode maka. Nasreen kin ganmu nan a titi.� Nasreen ma ta yi godiya ga Allah sannan ta ce, “Ka tari a dai-daita sahu daga nan ka tambaye shi nan ina ne? Sai ya kaimu tasha muyi shatar mota zuwa Kaduna ko?� Babu musu ya aikata abinda ta gaya masa. Abin mamaki antabbatar masu suna cikin garin Abuja ne. Don haka suka tari taxi suka ce ya kai su tasha. Sun kama ~ hanya dukkansu da kalar tunanin su, ita dai Nasreen sai addu’a take yi Allah ya kaisu ~ gida lafiya ba tare da wata matsala ta sake samun su ba. Sultan yana zaune a cikin mota yana duba jarida, kansa yana matuKar sara masa, ya rasa meke masa dadi. Dole ya ayjiye jaridar ya koma dabi’arsa na kallon gefen titi. Nasreen tana yawan zuwar masa a cikin mafarki abin har ya kai ya fara samun sabani a tsakaninsa da Zakiyya. Duk da su Umma sun koma, hakan baya hana Zakiyya kiran Umma ta kai Kararsa. Shi kansa yawan shirunsa yana damunsa, hatta I.G sai da ya kula da hakan. Da yake tafe yake da motar ‘yan sanda, hakan yasa ake basu daman wucewa, ba kowa ne ke iya shiga gabansu ba, sai dai cikin tsautsayi taxi din da ke dauke da su Nasreen ya shiga gabansu wanda kafin ya ankare har motar ‘yan sandan nan ta yi ciki da su. Hakan ya kawo * mummunar hatsari. Sultan yana cikin mota bai san wainar da ake toyawa ba, domin ba ~ motar da yake ciki ba ne abin ya faru, sai da yaga antsaya cak! Wani daga cikin dayan motar ya Karaso cikin gaggawa, yake sanar da abinda ya faru, ya ce a wuce da Sultan za su ji da komai. Shi dai ko tari bai yi ba, haka ya rasa dalilin da gabansa ke fadiwa. Can ya yi firgigit ya ce, “Kuna tuki cikin ganganci da nuna isa a titi, wanda shi titi babu ruwansa da muKaminka ko girmanka, haka shi bai da sabo. Yanzu wannan matsalar ta faru kuna fadin mu wuce ku zaku ji da komai akan me? Su wadanda aka buge din ba mutane ba ne? Ko kuwa basu da gata ne? Dakata infita.� Da yake sun san halinsa don haka suka tsaya ya fito gaba daya suka rufa masa baya. Abin takaici . babu wanda ya yi yunKurin daukar mutanen da aka buge, da suke kwance cikin jini, sai ma daya daga dan sandansa da ke neman dukan direban. Sultan ya girgiza kai, yana dubansu, “Yanzu don Allah menene amfanin wannan abun? Me yasa haka? Zaku � ji da mutanen da aka buge ne ko kuwa zaku tsaya surutu ne har su Karasa? Sultan ya � ratsa cikin jama’ar haka hanyar gaba daya bata motsawa saboda sun rufe hanyar. Yana zuwa kusa da su ya ware idanunsa. Ko shekaru dari suka yi basa tare ba zai taba mance su ba. Cikin sauri ya Karaso gabanta, � “Nasreen!� A hankali ta kai hannu tana lalube, ba ta da idanun da za ta iya kallonsa, amma kuma zuciyarta ta gano ko waye, “Dee…� Luuu ta yi baya. Kafin ta zube, gabadaya har ya samu ya tarota. Ya sa hannu ya tallabeta sosai. Ya rasa farin ciki zai yi ko kuwa bakin cikin ganin yadda Nasreen ta koma? Ya zama dole ya yi farin ciki da Allah ya bashi ikon sake ganinta. Cikin daga murya yake fadin, “A kawo mota cikin gaggawa.� Jikinsu yana Bari aka kawo mota yasa aka dauki Nawfal � shi kuma yana rungume da ita, ya hana � kowa ya taba ta, suka shiga mota sai asibiti. Kura mata idanu ya yi yasa hannunsa yana � shafar fuskarta, yana mamakin ina suka shiga haka da gaba daya kamanninta suka sauya? Ji yake kamar ta bude idanunta suyi ta kallon juna. Gaba daya dabara ta Kwace masa. Babu bata lokaci suka shiga da ita asibitin Dr. Aslaf. Cikin sa’a daga shi har Aminu suna nan a office. Don haka su suka karbi su Nawfal. Yumnah tana tsaye akan Nasreen shi kuma yana can tsaye akan Nawfal. Shi kuwa Sultan gaba daya a rikice yake ya rasa me ke masa dadi sai kaiwa yake yana komowa. A lokacin ne Dr Aslaf ya fito daga inda suke kula da Nawfal. A gigice ya Karaso gabansa ya ce, “Dokto ya jikinsa? Ya farfado kuwa?�� Dokto Aslaf ya dube shi kamar bai taba ganinsa ba, ya tabe baki, “Ka biyo ni office.� Sai yanzu ya tuna da Dokto Aslaf ne fa ba wani ba, don haka ya harare shi tare da jan tsaki. A lokacin ne kuma Yumnah ta fito don haka ya rabu da Aslaf ya Karaso gurinta, ““Kanwata ya ake ciki ne?� Fuskarta cike da fara’a za ta yi magana, Aslaf yasa hannu ya jawo hannunta ya ce, “Ba’a sani ba. Kin ji zo mu je kiyi min wani abu.� Sultan ya dube shi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Dole sai da ya biyo su office Yumnah tana dariya ta ce, “Wallahi Yaya Sultan babu ruwana laifinsa ne. Nasreen tana cikin Koshin lafiya, dan buguwa kawai tayi, yanzu haka barcinta . take yi.� Sultan ya saki ajiyar zuciya ya ce, “Kada ka damu zan rama.� Mikewa ya yi ya shige bandakinsa ya dauro alwala ya zo ya shimfida dadduma. Nafila ya yi ya gode wa Allah ya kuma yi addu’ar Allah yasa Karshen wahalar kenan.� Yumnah ta bude masu abinci, amma fir Sultan ya Ki cin abincin, shi damuwarsa kawai ya ga Nasreen da Nawfal. “Yumnah ki taimaka kiyi min jagora inga Nasreen. Babu musu Yumna ta mike Ta jawo hannun mijinta suka fice a tare. A bakin gadon ya zauna yana Kare mata kallo. Yumna ta dube shi cike da damuwa a fuskarta ta ce, “Don Allah Yaya Sultan ka barni da Nasreen da dan uwanta su dawo gidana na wasu lokuta ingyara maka matarka. Dubi Nasreen sai ka ce ba ita ce yarinyar nan da ke jikin hotunan nan ba? Anya ba a cikin rami suke rayuwa ba? Dazu sai da nayi mata kuka, gudun kada my Dokto ya ganni ya yi min fada yasa na share hawayena. Ina ganin ka ara min ita indawo da ita asalin Nasreen dinta, sannan ka gayawa duniya ka ganta, idan kayi saurin cewa ka ganta a irin wannan yanayin, masu neman ta za su ci gaba da farautarta ne.� Sultan ya yaba da abinda Yumnah ta yi masa, amma jin cewar masu farautarta za su sake bibiyarta yasa ya dube ta, “Idan a lokacin baya sun ci nasarar cutar min da ita, a wannan karon babu wanda ya isa Wallahi! A baya sun yi ganganci, a yanzu kuwa duk ‘wanda ya ce, zai sake aikata wannan � gangancin ina tabbatar maki sai ya kasance yaji a ransa me ya sa_uwarsa ta haife shi bata zubar da cikin ba? Na amince zan Boye dawowar Nasreen saboda matsalar cikin gidana. Bayyana dawowarta a yanzu tamkar wata hanya ce ta ruguza farin cikina agurin Umma.� Sultan ya saki ajiyar zuciya da ke nuni da yana cikin tashin hankali. Haka mafarkin da ya yi akan Zakiyya yaki goge masa. Dokto Aslaf yana zaton Sultan zai koma gida ne, sai dai ya sha mamakin yadda ya nannade hannun rigarsa ya jawo kujera ya kafeta da idonsa, haka hannunta mai Karin ruwan yana cikin nasa. Aslaf ya zaro idanu, “Haba haba! Muna da mutanen da za su kula da lafiyarta. Don Allah ka tashi ka je gida ka huta.� Sultan ya girgiza kai, “Ba zan iya tafiya ko ina inbar Nasreen ba. Ka taimaka min don Allah ka sa a dawo da Nawfal nan, saboda insami sauKin zirga-zirga. Ni zan kwana da su.� Aslaf zai yi magana, Yumnah ta sa � hannunta a kunnensa ta murde ta ce, “Juya � mu tafi mu aiwatar da abinda Yayana ya ce. , Ba gara kowa ba da kai? Soyayya ce kowa yana yinsa, a fili ko a sirrince, don haka ina . bayansa ya zauna ya kula da ita. Yayana ‘yanzu za a dawo da Nawfal nan.� Sultan ya kafe su da ido yana kallon yadda ta tasa shi a gaba har suka fice. Ya ; dawo da kallonsa kan Nasreen ya zuba mata * kyawawan idanunsa, wadanda suke Boye a cikin glas fari. “Sorry Nasreen. Za ki ji , sauki. Na yarda da maganar Abba da ya ce ke Rubutacciya ce. Na shirya_ tunkarar kowacce irin matsala akanki. So gaskiya ne, duk wanda ya Karyata faruwar hakan, bai zo kansa bane. Nasreen ki tashi ko ba za ki iya ganina ba, idan naji muryarki zan sami gamsuwa.� Shiru Nasreen bata tashi ba. Dole ya � _yi alwala ya tafi Masallaci kafin ya dawo har an dawo da Nawfal dakin. : Kai tsaye gaban Nawfal ya nufa, ya kamo hannayensa, “Nawfal..� Ya kira . sunansa a Sanyaye, sai dai ko motsi bai yi ba. Kallon tausayi yake yi masu, babu abinda yake tunawa sai amanar da Saudat ta damka masa. Sai -yake ganin_ tsabar sakacinsa ne ya jawo masa wannan abun. A bayyane ya yi magana bayan ajiyar zuciyar da ta Kwace masa mai _ karfi, “Alhamdulillah! Allah na gode maka.� Yana nan zaune kiran waya ta shigo wayarsa, duk da tana silent hakan bai hana shi ganin hasken wuta ba. Ya Kurawa lambar idanu yana son sanin waye mai layin nan? Baya daukar layin da bai sani ba, don ‘haka ya katse. Can saKo ya shigo ya zubawa sakon idanu, haka ya karanta yafi sau a Kirga. “Ina da buKatarka, kaje ka zauna.� Har yanzu ya kasa gane waye zai aika masa da irin wannan saKon? Haka kuma menene dalilin aikowar? Babu bata lokaci ya biyo lambar. Muryar Zakiyya ya ji tana magana kamar � wacce tasha wani abu. A hankali ya sauke wayar yana mamakin inda ta sami lambarsa, * domin shi tunda yake da ita bai taba kiranta ba, bai ma san lambarta ba. Daga kansa ya yi sama yana tunanin ta yadda za a yi irin wannan zaman. Matar da babu Nasreen ma baya dubanta bare kuma Nasreen tana nan? Ya zai Kare da Ummansa? Gabansa ya fadi da Karfi domin ya san akwai tashin hankali mai girma a gabansa. Ada mahaifinsa ke tsayawa yana Kwatar masa ‘yancinsa agun Umma, to a yanzu Umman tabi dukkan hanyar da za ta bi, ta kanainaiye Abban sai abinda ta gaya masa sannan yake iya aikata shi. Tunani yake yi ya kira Abban a waya ya gaya masa dawowan su Nasreen, sai dai ya bi shawarar zuciyarsa da take gaya masa gara ya bari ta murmure ya dauke su ya kai su gabansa da kyan gani. Yana nan a zaune har Aslaf ya dawo ya matsa masa sai da yasa wani abu a cikinsa, sannan suka yi Sallama ya wuce gida. Misalin Karfe ukun dare take Kokarin , bude idanunta da suke a rufe. Lalube take yi tana magana cikin muryar marasa lafiya, s “Nawfal..� Sultan yana nan zaune yana kallonta. Farin ciki ya tsirga masa. Yumnah ta gaya masa babu wata matsala mai girma, amma abin mamaki sai yanzu Nasreen ta farka. Hannunta da taji a hannun mutum yasa ta yl shiru. Ta dora tunaninta akan abinda ya faru kamar cikin Mafarki. Ko mutuwa ta yi ta dawo, inhar Sultan zai zauna a wun kawai ya tashi sai ta gane, bare kuma ace wai yana kusa da inda take. Ta gigice da yawa, sai kama hannunsa da tayi, “De� Don Allah Dee kayi min magana. Kana kusa da ni kai ne, hannunka ne. Dama dama zan sake jinka a kusa da ni? Deee..� Cike da nishadi, ya sa dayan hannunsa ya lakaci hancinta, “Deee� Ga Dee a kusa da Nasreen dinsa. Bana son kuka, baki da lafiya ki koma ki kwanta kin ji?� . Babu abu daya da ta iya aikatawa a cikin abinda ya ambata mata. Sai sake jawo 6/10/22, 00:48 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 9 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Sultan yana nan zaune yana kallonta. Farin ciki ya tsirga masa. Yumnah ta gaya masa babu wata matsala mai girma, amma abin mamaki sai yanzu Nasreen ta farka. Hannunta da taji a hannun mutum yasa ta yl shiru. Ta dora tunaninta akan abinda ya faru kamar cikin Mafarki. Ko mutuwa ta yi ta dawo, inhar Sultan zai zauna a wun kawai ya tashi sai ta gane, bare kuma ace wai yana kusa da inda take. Ta gigice da yawa, sai kama hannunsa da tayi, “De� Don Allah Dee kayi min magana. Kana kusa da ni kai ne, hannunka ne. Dama dama zan sake jinka a kusa da ni? Deee..� Cike da nishadi, ya sa dayan hannunsa ya lakaci hancinta, “Deee� Ga Dee a kusa da Nasreen dinsa. Bana son kuka, baki da lafiya ki koma ki kwanta kin ji?� . Babu abu daya da ta iya aikatawa a cikin abinda ya ambata mata. Sai sake jawo shi ta yi ta kwantar da kanta a bisa kafadunsa. “Dee kada ka sake barin a rabamu da kai. Mun sha wahala. Nawfal ya yi Kokari, Dee ina Nawfal? A dawo min da dan uwana kusa da ni.� Zuba mata ido ya sake yi yana kallon yadda Kasusuwa suka fito mata kwance a wuyanta. Ko bata gaya masa ba, ya san sun sha wahala. Hannu ya sa a cikin gashinta da duk suka dunkule saboda wahala, “Allah ya yi maku albarka. Allah ya sakawa Nawfal ya baki ikon kyautata masa. Nawfal yana nan kwance kusa da gadonki bai da lafiya, ZAMU TASHI ki kwantar da hankalinki dukkanku ina kulawa da ku, insha Allahu ba zan sake barin ko da kuda ne ya cutar min da ku ba. Koma ki kwanta ki daina kukan nan kin ji? Idanunki idan kina kukan nan za su sake rufewa ne idan aka zo yi maki aiki asha wahala.� Nasreen ta koma ta kwanta tana ajiyar zuciya, a natse kuma ta fara magana, “Idan wannan ne Karshen ganina a iduniya, inhar � ina tare da kai ba zan damu ba. Ina cikin wahala da tashin hankali ma, ban damu ba, ~ bare yanzu da Allah ya kawo min Karshen wahalata. Dee har matsafa sun sa min kayan da za su yanka ni, idan kayan jikina jajayene har yanzu to sune kayan da aka sa za a yanka ni.� Sultan ya shiga rudu da tashin hankali, don haka ya dubi kayan jikinta a gigice. Sai dai ba su ba ne a jikinta Yumnah tasa an sauya mata kayan jikinta da doguwar riga wanda ta aika aka kawo mata. Ya dan rintse idanunsa yana mayar da ajiyar zuciya. “Allah ka Kara bamu kariya da ikonka da isarka.� Nasreen ta dinga surutai har barci ya sake yin awon gaba da ita. A lokacin ne kuma Nawfal ya motsa tare da ware idanunsa. Daman tun suna Kanana Nasreen ke fara tashi, idan ta koma Nawfal zai bude nasa idanun. Sultan bai san ya farka ba, kawai yaji a jikinsa ne ana_ kallonsa. Juyowan da ya yi suka yi ido hudu. Nawfal ya cika da al’ajabin wannan lamari. KoKarin » dole sai ya tashi yake yi yaje ya rungume shi, sai akasin hakan domin Kafafunsa sun . rike kuma suna yi masa zogi. Da ka kalle shi za ka tabbatar da cike yake da wani irin matsanancin farin ciki. Sultan ya Karaso har gaban gadon yana murmushi. Suka rungume juna Sultan ya dinga shafa kansa yana jin Kaunar yaron yana sake ratsa shi. “Allah ya yi maka albarka Nawfal.� Abinda bakinsa yake ta maimaitawa kenan babu tangarda. Nawfal ya fara zubar da hawaye, domin ya rasa a cikin masu sa’a su din wasu iri ne? Bai taba tunanin zai sake yin ido hudu da Sultan ba. “Deedi we really miss you. Please Deedi forgive us for our mistakes!� Sultan ya shafi kansa yana bubbuga bayansa, “Be a Man. Stop saying that! Ka gode wa Allah Nawfal babu abinda kuka yi min.Ka daina bari hawaye suna zuba a, idanunka, kada ka zama ragon maza. Mata aka sani da kuka ba namiji ba. OK?� Nawfal ya shanye wani irin kuka da ya taho masa aguje. “Ok Decdi. Ina Abbana?�� Bubbuga bayansa ya ci gaba da yi kamar mai lallashin yaro Karami, “Abba is fine! Go back to your bed please.� Babu musu ya koma ya kwantar da kansa ba tare da ya saki hannun Sultan ba. Haka idanunsa tunda suka kalli Nasreen ya kauda idanunsa yana ci gaba da kallon Sultan, ya tabbata Nasreen tana cikin kyakkyawar kulawa tunda har Sultan yana kusa da ita. Rufe idanunsa ya yl yana son yin magana, amma yadda Sultan ya kafe shi da idanu yasa ya kasa Kwakkwarar motsi har sai da barcin ya sake kwasarsa. Sultan ya yi ajiyar zuciya ya mike ya shige bandaki ya dauro alwala domin sake mika godiyarsa ga Allah. Haka Sultan ya yi ta zarya a kan su � Nasreen ya kuma Ki gayawa kowa abinda ke faruwa. Har yau dinnan da aka sallame * su yana wurin aiki don haka ya ce Yumna ta wuce da su kawai zai biyo baya. Abinda Yumnah ba ta sani ba, tuni Sultan yasa “yan sanda su bi bayansu har su raka su gida, haka ya sa wasu gadin gidan Aslaf. Mamaki ya kama Aslaf da masu gadin gidansa suka koma ‘yan sanda. Nawfal aka sauke shi a bangaren baki, ita kuma Nasreen suka wuce da ita ciki. Yumnah ta zage ta fara gyara Nasreen babu ji babu gani, haka tana yi tana koya mata wasu abubuwa ta hanyar yi mata bayanin su. Hatta rayuwar aure da yadda ya kamata ta riKe mijinta sai da Yumnah ta karanta mata. Haka ba ta yi. bayanin banza ba, domin duk abubuwan da take gaya mata suna nan a cikin KwaKwalwar kan Nasreen. Sai yamma likis Sultan ya taso daga Office a gajiye kai tsaye gidan Aslaf ya wuce. Yana fitowa daga Motar ya hango Nawfal ya zauna ya yi tagumi shiru, da alamun ma bai san ya shigo ba. Cikin takunsa na isa, ya * Karaso har gabansa ya durKusa yana sake nazarin yaron. “Nawfal me ya yi maka zafi � haka?� Dago kansa ya yi cike da hawaye, “Deedi ina son ganin Abbana ina son inyi masa wata tambaya.� Gaban Sultan ya fadi da Karfi, ya daure ya sake zuba masa ido, “Me za ka gayawa Abba bayan ga ni? Nawfal ka taimakeni ka kwantar da hankalinka a cikin gidan nan, zuwa wani dan lokaci zan kwashe ku muje gaban Abba. Idan na kaiwa Abba ku a irin wannan yanayin ciwon hawan jininsa yana iya tashi saboda bakin ciki. Ka saki jikinka nan gidanku ne, duk abinda za ka yi a gidana a nan gidan ma za ka yi mafiyinsa.� Nawfal ya gyada kai, kafin ya kamo hannunsa suka tashi suna jerawa. Duk wanda ya gansu zai rantse da Allah yaya da Kaninsa ne, haka kamannin su da juna ya sake fitowa fes! Sai dai wasu abubuwa da Sultan din zai nunawa Nawfal, musamman ta fuskar shekaru. A bakin babban falon suka yi Sallama, Nasreen ce kadai zaune da sandarta a gefenta. Fuskar nan dauke da matsanancin farin ciki. Tokarewa ya yi a bakin Kofa yana kallon yadda ta yi kyau, , duk da haskenta bai fito ba. Yadda ya kashe ta da idanu yasa Nawfal zame kansa ya fice ya koma gun ‘yan sandan. Bata dauki sandar ba, ta miKe tana bin Kamshin turarensa. Har ta kusa taba shi ya lallaba ya sauya wuri. Ta sake bin inda ya tsaya ya sake kaucewa. Yana tsaye sai murmushi yake aika mata, zai so idanunta suna bude ne. Tuni ya ji damuwa ta lullube shi, baya son ya yi mugun baki a kan wanda ya aikata mata hakan, domin jikinsa yana ba shi Ummansa ce ba wata ba. Cikin muryarta mai sanyi take magana, “Ka gani ko? Wallahi Deedi sauya wurin tsayuwar kake yi don ka ga bani da ido bana gani.� A natse ya Karaso gabanta ya jawo hannunta ya hade ta da jikinsa ya rungume. Dukkansu suka saki ajiyar zuciya KakKarfa. Nasreen da bata taba tunanin wannan ranar za ta zo ba, ta sake shige masa sosai tana jin saukar hawaye a idanunta. Bai iya hanata kukan ba, domin shima da yana da iko da ya Sanya su sun zubo ko zai huta da radadin da yake ji a zuciyarsa. Sannu a_hankali tsayuwar tana neman gagararsa don haka ya jawota zuwa kujera suka zauna. “Ina Yumnah take?� Ya tambaye ta yana dubanta. Ta ba shi amsa da tana ciki, don haka ya dan yi shiru kamar mai nazari. “Share hawayenki ki daina kuka inbaki wani laban mai dadi.� Babu musu ta share hawayen ta kwantar da kanta a kafadarsa. “Ki daina kuka kin ji? A duk lokacin da kika tuna wani abu kiyi fara’a ki godewa Allah. Dukkan abubuwan nan da_ suka faru. jarabawa ce, ke malama ce kin sani dole sai� mun shiga aji mun dauki darasi, daga nan kuma jarabawa ta biyo baya. Kuka ba ita bace mafita, haka idan kina tayar da hankalinki ba za ki murmure ki yi Kiba ba, bare har indauke ki zuwa wajen Abba. Kinga muna da tafiya zuwa Lagos, amma saboda ke na kasa tafiya, idan kina kukan nan sai intafi abuna, amma idan kika kwantar da hankalinki sai mu zauna muyi ta shan hira, kina yi min labari� da wannan muryar taki mai dadin sauraro.� Murmushi ta sakar masa. Mamakin yadda take maKale masa ya_ ci gaba da kama shi, yarinyar da a idanunta idan ka kalla za ka tabbatar da tsoron Sultan ne kwance a cikin su. Shi bai san cewar tasan ita matarsa ba ce, haka ya rasa ta hanyar da zal gaya mata. Danna wayarsa ya yi ya kira daya daga cikin ‘yan sandarisa ya ce a kira masa Nawfal. A lokacinne kuma Aslaf da Yumnah suka shigo falon. Ya daure fuska sosai ya ce, “Mene ne haka? Ai sai ku tsaya kuyi Sallama inbaku izinin shiga, ba wai ku fado mana daki haka kawai ba.� Nasreen tana KoKarin janye jikintadaga na Sultan, amma sai ya: hana hakan. Aslaf suka dubi juna da Yumna sannan ya � ce, “Duk irin sallamar da muka yi bai gamsar da kai ba?� | , Dukkansu suka nemi wuri suka zauna, suna kula da yadda Nasreen taki sakin jikinta hakan yasa ya Kyaleta ta raba kanta da jikinsa. Sultan ya dubi Aslaf ya ce, “Dokto wai kuwa kunsan ranar da aka buge su Nasreen a mota daga gidan matsafa suke?� Daga Aslaf har Yumnah suka zaro idanu. Sultan ya ci gaba da magana yana duban Nawfal, “Nawfal fada mana yadda akayi kuka baro gida daga _hanyar dawowarku Makaranta.� Nawfal ya dan yi shiru, gaba daya yanayinsa ya sauya. Sannu a hankali ya basu labarin komai. Nasreen ta yi magana cikin sanyi, “Nawfal baka gaya masu Mansur ya ce mana Deedinmu ya rasu ba. Wai kuma an daura mana aure..� Sai da ta fada kunya da danasani suka kamata, ta sunkuyar da kanta_ Kasa. Gabadaya suka yi mata murmushi. Haka , labarin su ya taba zuciyar duk wani.halitta da ke cikin dakin. Aslaf ya dube shi ya ce, “Yanzu za ka iya gane gidan da aka kaiku na matsafa? Za ka gane gidan da Mansur din yake?� Nawfal ya dago yana duban Aslaf ya ce, “Uncle ko kun je ba za ku ga kowa ba. Gidan tsafin kuma bamu san ta inda aka shiga damu ba, ba zamu iya gane komai akan gidan ba. Amma ai shi Deedi yasan Mansur din ya taba zuwa gida.� Sultan ya dube shi, “Nawfal ka gaya ‘min gaskiya, waye kaji sun ce ya turo su su sace Nasreen? Yanzu kuna da ‘yan Kananun Shekarunku kuka dibi irin� wannan gwagwarmayar? Nawfal ka yi namijin KoKari, haka ake son dan uwa. Gaya min waye kuka ji sun ambaci sunan su?� A yadda Nawfal yaga fushi a idanun Sultan yasan akwai matsala idan ya gaya masa gaskiyar lamari, don haka ya girgiza kai suka hada baki da Nasreen kamar wadanda suka gayawa juna abinda za su ce, “Ba su gaya mana wanda ya turo su ba.� � Sultan ya rintse idanunsa, zai so ace yasan waye mai wannan halin. Haka suka ci * gaba da tattaunawa har Ashmaan ya shigo ya same su. Sosai yake kallon Nasreen sannan ya yi ajiyar zuciya ya ce, “Har na tuna da _ Ibtihal dina da aka ba ni ita a matsayin kurma.� Sultan ya ce, “Kwarai kuwa, basu san wannan dan jaridar na gaske bane.� Sannu a hankali aka sake ba shi labarin su Nasreen ya jinjinawa Nawfal haka yaran sun burge shi da yadda suka riki addini a lokacin da suke cikin tsanani. Daga nan suka ce Yumna ta kama Nasreen su koma ciki, su kuma suka zauna suna ci gaba da tattauna hanyar da ya kamata su bi wajen ganin komai ya zo masu a cikin sauki ba tare da wata matsala ba, musamman wajen yin takatsantsar da su Nasreen, domin suna son su buga cewa ‘ya’yan da Saudat ta Haifa suna nan da rai, kuma sun girma a yanzu. Haka suka zauna su Kullawa wannan su kwance wancan, har aka kira Sallah suka mike suka nufi Masallaci. Da Karfe goman dare yana nan zaune a falonsa Zakiyya tana latsa remot, ita a dole fushi take yi da shi, kasancewar kwana biyun nan duk ya sauya mata, haka yaki tsayawa ma ya ji matsalarta bare har ya bata hadin kai akan rayuwarsu ta aure. Lokaci zuwa lokaci tana satan kallonsa amma shi ko waiwaye. Shi ji yake kamar bai da lafiya a jikinsa, musamman ta bangaren kiyaye hakkin aure. Ji yake idan har wannan abin shi ne auren, to baya daya daga cikin irin mazan da suke da lafiyar aikata hakan. Haka zamansu da Zakiyya zai yi wahala, domin ita bata san komai a aure ba, sai 6/10/22, 00:48 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚* CHAPTER 10 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* *KARSHEN Book two* MUN TSAYA ciki, su kuma suka zauna suna ci gaba da tattauna hanyar da ya kamata su bi wajen ganin komai ya zo masu a cikin sauki ba tare da wata matsala ba, musamman wajen yin takatsantsar da su Nasreen, domin suna son su buga cewa ‘ya’yan da Saudat ta Haifa suna nan da rai, kuma sun girma a yanzu. Haka suka zauna su Kullawa wannan su kwance wancan, har aka kira Sallah suka mike suka nufi Masallaci. Da Karfe goman dare yana nan zaune a falonsa Zakiyya tana latsa remot, ita a dole fushi take yi da shi, kasancewar kwana biyun nan duk ya sauya mata, haka yaki tsayawa ma ya ji matsalarta bare har ya bata hadin kai akan rayuwarsu ta aure. Lokaci zuwa lokaci tana satan kallonsa amma shi ko waiwaye. Shi ji yake kamar bai da lafiya a jikinsa, musamman ta bangaren kiyaye hakkin aure. Ji yake idan har wannan abin shi ne auren, to baya daya daga cikin irin mazan da suke da lafiyar aikata hakan. Haka zamansu da Zakiyya zai yi wahala, domin ita bata san komai a aure ba, sai ZAMU TASHI wannan abin, ko gyara gado bata sani ba, yadda ya fita ya bar gadonsa a haka zai dawo ya same shi, yadda ya fita ya bar kitchen haka zai dawo ya same shi, wataran ma shi da kansa yake zaKewa ya gyara abubuwan, musamman idan yaga ya yi datti. Zanen gado kuwa tunda aka kawo ta cikin gidan nan bata taba sauya zanen gado ba, har ya fara canza kamanni. Gara ma na dakinsa idan ya gaji da ganin kala daya yana sauyawa da kansa. _ Komai a gidan kaca-kaca kamar ba Sultan _ din da ba. Da ta gaji ta tabbatar ba zai kawo kansa ba, ta mike ta shiga ciki ta manna wannan turaren. Tana fitowa ya riga ya kintsa yana sauri Zai je ya duba Nasreen. A lokacin kuma ya sami nasarar shakar Kamshin, amma saboda yana sauri ya kasa tsayawa yana tafiya tana binsa, “Ka tsaya mana don Allah. Bai tsayan ba, ya ce, “Kada ki damu yanzu zan dawo.� Yana jin wani abu yana fizgarsa amma baya jin da akwai dalilin da zai tsaida shi daga zuwa duba Nasreen. A wahalar ce ya iso gidan bai ga Nawfal ba, bai kuma duba shi kamar yadda ya saba ba, kawai ya zura kansa falon tare da Sallama. Babu kowa a falon ya kwantar da kansa yana lullumshe idanunsa kamar wanda yake jin barci. Nasreen kuwa tunda aka ce ga Sultan take jin wani irin sany1 yana ratsata. Fitowa ta yi cikin shigarta ta atamfa ta yi mata kyau. Ta riga ta saba da inda yake zama. Ya so Kwarai da yana da � karfi a jikinsa, da ya fara tarota kafin . , isowarta. Yana nan zaune yana kallon yadda take tafiya, rashin idanun nan suna damunsa_. sosai. Tana zama yasa hannu ya jawota gaba daya jikinsa tare da sauke ajiyar zuciya, wanda ke nuni da alamun yana cikin wani hali. Shinshinar Kamshinta yake yi, cike da gamsuwa da irin kulawan Yumnah haka tana shan albarka a cikin zuciyarsa. Yana son ya � yi mata magana amma kuma a irin halin da yake ciki yasa ya kasa magana, jikinsa babu inda baya rawa. Tun Nasreen tana daukar � wasa yake yi har abin ya fara zarce tunaninta. Ta gigice da yawa, don haka ta fara kuka, “Deedi menene wannan? Dee kayi hakuri ba zan iya ba, ina jin wani iri.� Ba ya jinta baya fahimtarta, Zakiyya ta manna masa jaraba ta barshi da abin kunya a cikin gidan jama’a. Nasreen ta samu ta fizge kanta ta ruga cikin gida, tana tafe tana hadewa da garu. Yana kallonta bai yi yunKurin hanata guduwar ba, shima zai so hakan gudun kada ya yi abinda bai kamata ba a cikin gidan jama’a. Rufe idanunsa. gyam! Ya yi yana da buKatar komawa gida ya sami Zakiyya. Idan ba haka ba, a yadda yake ji , komai zai iya faruwa da shi. Ita kuwa Nasrecn dakinta ta shige jikinta yana kyarma. A haka Yumnah ta shigo ta same ta kasancewar tana kitchen ta hango shigowarta a gigice. Dafa ta ta yi hakan yasa ta sake razana, “Don Allah ka yi haKuri ka bar ni.� Saboda gigicewa ta kasa bambance hannun Yumnah da na mijinta. “Ki natsu Nasreen menene haka? Me ya faru?� Nasreen ta riga ta dauki Yumnah a matsayin ‘yar uwarta ta jini don haka ta fara magana, “Wai Dee ne� Wai…� Sai kuma ta yi shiru. Yumna ta ce, “Ki yi magana mana wai mene?� Sai da ta shaki iska ta saki ajiyar zuciya mai Karfi, “Yana min wasu abubuwa kamar_ . ya fita hayyacinsa.� Murmushi Yumnah ta yi ta ce, “Amma dai Nasreen na raina wayonki. Menene ba mijinki bane? Ashe duk irin son da Yaya Sultan yake gwada wa akanki a wurinki ba haka ba ne? Na tabbata idan da ke ce kike cikin mawuyacin hali irin wannan da babu abinda zai hana shi ya taimaka maki ko da kuwa a tsakiyar kasuwa ce. Baki kyauta ba, da baki tarerayi mijinki a lokacin da yake da buqatar hakan ba. Yanzu idan ya tafi titi ya nema fa? Me za ki cewa Allah? Maza tashi kije ki taimaka masa, na tabbata duk irin fita hayyacinsa da ya yi ba zai ce zai dauke budurcinki a lokaci irin wannan ba, zai so ya sami wuri mai cike da natsuwa domin ya kafa tarihi mai wahalar gogewa. Maza ki je ki sami mijinki.Nasreen da natsuwa ya shige ta ta girgiza kai, “Ina son Dee, amma ina tsoro ba zan iya ba.� Da Kyar Yumnah ta samu ta lallabata har ta sake fitowa, sai dai tana ta lalube tana cewa, “Dee kayi hakuri ba zan sake gudunka ba.� Shiru hakan yasa ta yi , waje tana lalube. Nawfal ya hangota ya Karaso da sauri, ganin za ta ci Karo da tukunyar filawa yasa ya riKeta, “Menene kuma? Ina za ki je?� Idanunta cike da hawaye ta ce, “Dee nake nema. Nawfal Dee ya tafi ko?� Dariya ma abin ya bashi cikin dariya ya ce, “Tun _ yaushe? Ai bai ma jima ba ya tafi, kuma ko? gaisawa bamu yi ba, ina sauri inKaraso har ya shige mota abinsa. Fuskarsa kamar dauke * take da damuwa me kika yi masa? Kai nasan ba ke bace domin ko giyar wake kika sha ba za ki taba iya bata masa rai ba.� Hankalin Nasreen ya Kara tashi ta dinga girgiza kanta. Ganin tana hawaye yasa Nawfal ya zare idanu, “Mene ne haka Nasreen? Me kuma ya faru?� Juyawa ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba, ganin tana cikin wani yanayi yasa ya yi mata jagora. Abinda bata sani ba, Sultan yana nan zaune yana kallonta haka shi ya Kyaftawa Nawfal idanu har ya fahimci abinda yake nufi. Tana shigowa falon taja ta tsaya. “Mu je mana in raka ki.� Girgiza kai take yi, “Nawfal Dee yana cikin dakin nan yana nan a dakin nan bai yi nisa da ni ba. Don Allah Dee idan kana nan ka yi min afuwa ka yi magana, rashin aikata , hakan zai iya sawa in kwana cikin bakin ciki da dogon tunani.� : Da hannu ya yi wa Nawfal alamun ya fita kawai. Nawfal ya fice yana dariya. Jin falon shiru ya sa ta ce, “Nawfal! Ina kuma ka. shiga ne? Allah sarki don kun ga bani da idanu sai ku dinga yi min abinda kuka gadama. Babu damuwa na gode.� Ta juya za ta tafi, har ta kai bakin Kofa tana son ta ji ko daya daga cikin su zai yi magana amma shiru. Hakan yasa ta sauya hanya da gangar ta nufi bango gadan-gadon. Sultan ya rintse idanunsa ya ce, “Nasreen tsaya!� Babu musu ta ja ta tsaya fuskarta cike da farin ciki. Ba ya son sake tunkarota, domin zai iya nanata abinda ya aikata da farko. A nutse ya Karaso yana duban labbanta. “Ki je ki huta zuwa anjima zan dawo muyi magana.� Gyada kanta ta yi ba tare data kawo komai a cikin ranta ba. Ya manna mata sumba a goshi ya dawo bisa labbanta. Murmushi ta yi bayan ta lashe dukkan tausasan labbanta, haka ta kasa ci gaba da__, tafiya. Komai na Sultan daban yake da sauran maza. Bai cika yin abu cikin garaje ba, shi ya sa komai nasa yake cikin tsari. Yana nan tsaye har ta shige sannan ya saki ajiyar zuciya ya fice abinsa. Yana isowa gida bai yi wata-wata ba ya biyewa Zakiyya har ya faranta mata fiye da tunaninta, kasancewar da Nasreen ya dawo a zuciyarsa, don haka ya shigo mata da tarkacen Nasreen. Farin ciki kamar ya kashe ta, bayan ya kintsa ne yana zaune a falo ya kirawo Zakiyya ta zo ta zauna ya dube ta sosai ya ce, “Zakiyya kina son zaman mu ya dore?� Ta gyada kanta, “To don Aliah ki dinga tsafta. Hatta jikinki yadda kike tsafta ce shi bai yi ba. Banga dalilin da za ki yi wanka amma kuma sai ki fito kina wari ba, dole akwai dalilin faruwar hakan. Haka ba zai yuwu gidana ya zama Kazantacciyar gida ba. Saboda kina ciki ne shi ya sa na sallami mai aikina, ankawo maki mai aiki amina banga amfanin da take yi ba. Ke kallo ita barci. To na kai Karshe idan kina son mu shirya gara tun wuri ki gyara halayyarki. Bana son Kazanta, babu zama da Kazami a cikin tsarina�� Zakiyya da ta gama muzanta ta yi yake, “Zan gyara insha Allahu.� Zakiyya ta koma daki tana shinshinar kanta amma bata ji warin ba, tana mamakin ta yadda babu kawaici kawai za ace mata tana wari, kai tsaye ba tare da tunanin abinda za ta _ ji a cikin ranta ba. Wannan kalma ta Kona Mata rai, domin tasan tana wanka tana iya bakin KokKarinta wajen bulbula turare. Ya zama dole ta ci gaba da sanya turaruka masu Karfi, domin ta burge shi. Abinda Zakiyya ta manta ko ince bata sani ba, wannan wankan tsarkin da ba ta yi shi yake kawo mata dukkan matsalolin nan, tana da Karancin ilimin addini sosai. Ko da yake dama ita bata taba yin wata Islamiyya ba, Kyale ta dai da boko. Ita dai tasan ana cewa mutum yaje ya yi wanka, kuma tabbas tana yin wankan, ko da kuwa ta jinkirta hakan. Haka wani abinda ya sake jawo mata babbar matsala a farjinta idan ta gama iskancinta sai ta shirya ta fice ba� tare da ta wanke lungu da saKo ba, hakan ya jawo danKarewar datti, wanda yake haifar ~° mata da mugun� warin gaba. Ita kanta tana jin warin bare kuma Sultan. Kullum burinsa ya daure kada ya gaya mata har ankai matsayin da dole ya fito yagaya mata domin a zatonsa za ta iya gyarawa ne. Sultan ya kasa samun natsuwa dukkan motsin da ya yi sai ya tsargu sai ya dinga jin warin jikinta a jikinsa. Ya yi wanka a Kalla sau hudu, amma bai daina ji ba. Ya rasa wani irin shirme ke jawo shi Zuwa gareta. Wasa-wasa sai da Sultan ya yi kwana uku bai je ya duba su Nasreeen ba, aiki yayi masa yawa, duk da yana da daman ya Zo ya dubata din ya yi hakanne saboda yana son ya nesanceta kada ya aikata abinda zai bata mata. Ita kuma a can ta dami da kuka, akan Sultan ya yi fushi da _ ita ne.Yumnah ta yi masa kiran duniya amma yaki daukar waya, da yake sun san halinsa, mutum ne mai wahalar daukar waya. Hatta iyayensa kuka suke da shi, wanda tuni ya riga ya zama jinin jikinsa, duk yadda yaso ya ga ya gyara wannan hali abin ya _ faskara. (Hallayarsa sak! Halayyar Yaya Adamu.) Aslaf yana zaune a falonsa yana karanta jarida Yumnah ta Karaso, “Doktona ka kira Yaya Sultan ‘yan biyun gidan nan sun daina yiwa kowa walwala saboda rashinsa. Na kira shi ka dai san halinsa ya Ki daga wayar.� Aslaf ya janye jaridar daga idanunsa ya dubeta sosai, “Kin yi kyau likitan zuciyata.� Murmushi ta yi tana jin dadin yabawan mijinta akan komai nata. Ya zaro wayarsa ya kira wani dan sanda da ya tabbatar ko wani irin lokaci suna tare. “Kai baiwa Sultan wayar.� . ; A take ya Karasa kusa da Sultan ya sara masa kafin ya miko masa wayar. Bai karba ba ya dube shi, “Waye ke kirana?� “Yalla6ai Doctor ne sir!� Sultan ya gane waye, don haka ya ci gaba da danna Laptop dinsa sai da ya gama : komai tsaf sannan ya waiwayo ya karba, Baka da layina ne za ka kira layin yarona?� “Eh ba ni da layinka. Idan mainadaita , bata da rijista don haka babu amfanin kiran layin wanda marabarsa da layin da aka binne__a Kasa, shigowar kira. Malam ba abinda ya kawo ni kenan ba, na kiraka ne ingaya maka, ka zo ka kwashe ‘ya’yanka domin idan suka mutu bana jin kai ka isa ka tambayeni dalilin mutuwarsu.� Sultan ya shaki iska ya waiwaya hakan ya sa kowa ya fice ya bashi wuri, “Aslaf ba za ka gane bane. Aiki ne ya yi min yawa, amma su zama cikin shiri zan zo inkwashe su a wannan hutun Karshen makon zan kai su gun Abba. Sai ka shirya ka raka ni idan ba ka wani abu.� Aslaf da ya ji damuwa, domin har ya saba da nawfal sosai, haka yaransa ma sun saba da ‘yan biyun bare Yumnah da take jin kamar a bar mata Nasrcen ta zama Kawarta. Aslaf ya girgiza kai, “A’a Sultan kamar ya yi wuri ka dauke su, ka dai dinga basu lokacinka idan ka yi hakan zai rage mesu kewarka. Kuma idan ka kai su wajen Abba acan za ka bar su?� Gabansa ya fadi da Karfi da ya tuna da wacece Umma. Shafar kansa ya yi yana jin tarin damuwa a zuciyarsa. “Aslaf akwai matsala sosai. Idan naje zamu yi kwana biyu, sannan indawo da su. A take zan raba masu girki ita da Zakiyya, kowacce _ inbata bangarenta, shi kuma Nawfal Makaranta zan tura shi, shi dai dan sanda zai yi, daga nan sai muyi zaman meetin yadda za a yi a sami Doctor din da zai yi aikin idanun sai ya bamu Date. [dan idanun Nasreen sun gyaru, ka gaa lokacin sai mu shiga aiki sosai da sosai, dama rashin yaran yasa muka dakatar da komai. Don haka zan zo kamar yadda na gaya maka zan tafi da su. Na gode Aslaf Allah ya Kara mana zumunci.� Aslaf ya katse shi da cewa, “A’a menene kuma na godiya? Mun riga mun zama daya, zai fi kyau ka ajiye godiyarka. Ka rike wayar zan aika wa Nasreen Kila mu sami dariyarta yau.� Girgiza kansa ya yi kamar yana ganinsa, “A’a ka cewa Yumnah ta rike wayarta zan kira sai ta ba ta.� Aslaf ‘ya dubi Yumna ya ce, “Fushi take yi da kai, ta kiraka har ta ji babu dadi, amma baka daga ba.� Murmushi ya subuce masa, “Ka ce mata ta yi hakuri da ni. Kuma babu kyau Kanwa tana fushi da yayanta.� Haka suka kashe suna raha, ya kira mai wayar ya bashi, sannan ya ci gaba da abinda yake yi. Da yamma likis ya dawo gida kawai ya shige dakinsa ya rage kayan jikinsa sannan ya shiga wanka. Sai da ya gama natsawa tsaf! Sannan ya haye gadonsa shi kadai yasan abinda ke cikin zuciyarsa. Tunanin Nasreen yana neman ya illata shi. Daga wayarsa ya yi ya kira Yumnah bata daga ba, ya sake kira a karo na biyu, har ta kusa tsinkewa sannan ya ji alamun anraba Karar bugun da wayar, wannan ke nuna masa ana kan layi. “assalamu alaikum.� Ya ji sassanyar muryarta ta wuce ta kunnensa ta isa har makogoronsa. Sake lumewa ya yi cikin gadonsa, yana jin sanyi yana tsirga masa. �*Yar babyna, mai kuka don ba ta ga Deedinta ba. Oya yi min kukan yanzu in ji ko “kin iya ko inzane dan bakin nan da bulala na . mai zafi.� Fara’a ce kwance a fuskarta hakan yasa Yummnah ta fice tana girgiza kai. “Deedina ina yini? Ya su Anti Zakiyya?� Kiran sunan Zakiyya da ta yi ne ya sa ya ankare da yana da wata matar. � Murmushi ya yi ya ce, “Lafiya lau. Zakiyya tana fushi da ke, tunda ba ki kula mata da mijinta.� Rau-rau ta yi da idanunta sannan ta ce, “Dee fushi kake yi da ni ko? Kayi hakuri ba zan sake ba. Dee bana son fushinka yana hanani barci.� Bangon dakinsa ya kafe da ido kamar mai karanta wani sako mai mahimmanci, sannan ya bata amsa, “Kin taba ganin inda Yaya yake fushi da Kanwarsa? Ba na fushi da ke aiki ne ya sha kaina. Nasreen duk yadda naso ki dinga jin yadda bugun zuciyata ke sauyawa a duk lokacin da muke tare bakya ji. Na tabbata da kina ji, da ba za ki dinga kallo na a matsayi wanda zai cutar da ke ba.� “Wayyo Dee ban taba kallonka a * hakan ba. Nima ina sonka haka Deee. Shi ya sa kayi mana yaji ko? Ko bana ganinka idan * kazo ai zuciyata tana ganinka kuma tana sauraren ka. Nawfal ba ya dariya da kowa saboda rashin jinka da ganinka.� “Ki ba shi hakuri zan zo mu _ wuce Kaduna wajen Abba, nasan yanzu kun murmure ko?� Bata bashi amsar ba, sai murna da take yi za ta je ta ga Abbanta. “Deee.. wai da gaske an daura mana aure?� Wannan tambayar kullum sai Nasreen ta maimaita ta, haka tana kwana cikin tambayar kanta da gaske ne wai ita matar aure ce? Murmushi ya yi ya ce, “Irin tunanin da kike kwana kina yi, irinta nima nake kwana ina yl. Zan gazgata ke matata ce kadai idan har na kaiwa Abba ke ya bani izinin intaho da ke Abuja, inmallaka maki dakinki a matsayin dakin matata. Ki shiga turakana da sunan kin zo wajen mijinki. Idan hakan ya faru a wannan ranar zan kwana ina godewa Allah.� Juyi ta yi bisa gadonta ta lalubo filo ta manna a Kirjinta, “Ni kuma a lokacin ina can _� duniyar wahala, na yi alKawarin zan yi azumi uku idan har Deedina yana raye. Ka ga har nayi azumina na kammala. A ranar da za ka kwana kana Sallah, tare zamu kwana Dee, nima bana gajiya da godewa Allah, saboda shi ma baya gajiya da biya mana dukkan bukatun mu.� Sultan ya sake jifan bangon dakinsa da murmushi, ba tare da ya lalubo abinda zai gaya mata ba. Tsintar muryarta ya yi tana cewa, “Na so in riga Nawfal fara ganin fuskarka, naso inga irin kyan da na ji ana kururutawa ka Kara, sai dai hakan bai yuwu ba sakamakon makanta da ta toshe min idanun yin hakan. Sai dai kafin Allah ya karbi idanun da ya bani aro, ni shaida ce Dee mai kyau ne, Dee yana da kwarjini a idanun kowa.� Kalaman yarinyar suna yi masa kama da mai son cusa masa rauni a Zuciya. ““Nasreen kada ki damu za ki gan ni da zarar muka ci karo da Dokto din da zai yi maki aiki.� Cikin rauni ta ce, “Don Allah zan roKe ka wani abu. Amma sai a ranar da Za a yi min aikin.� “Allah ya kaimu ranar.� Ya mayar mata da amsa yana jin barci yana son kwasarsa. Zakiyya ta shigo dakin tana Kare masa kallo, “Da waye kake waya?� Firgigit ya bude idanunsa, “Kin ajiye ni ne kike min tambaya irin wannan? Ban sani ba.� Zakiyya ta shaKa iya shaKa ta fara antayo masa maganar da duk tazo bakinta, “Wallahi na dade ina zargin ka koma bin matan banza, ga ni a gida sai ka je waje kana neman na wasu, saboda haram tana da dadin aikatawa,� Sosai ya ware idanunsa, “Ashe kina iya bambance Haram da halas? Idan kika sake danganta ni da aikata zina sai kin yi danasani. Idan na fita waje na nema ina ruwanki? Ki gyara kanki mana ki ga yadda namiji ke zama a like da matarsa. A Kazantar naki ne zan zauna da ke? Ke fice min a daki tun kafin fushina ya sauka a kanki.� Zakiyya ta fasa kuka ta fice. Nasreen kuma tana gama saurara ta sauke wayar jikinta a sanyaye. Ta fara hango tarin Kalubale a cikin zamanta da Zakiyya. Kalmar warin da Sultan ya yi amfani da ita, ta tsaya mata a rai. Wannan ke yi mata nun 6/10/22, 09:15 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 1 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Sultan ya sake jifan bangon dakinsa da murmushi, ba tare da ya lalubo abinda zai gaya mata ba. Tsintar muryarta ya yi tana cewa, “Na so in riga Nawfal fara ganin fuskarka, naso inga irin kyan da na ji ana kururutawa ka Kara, sai dai hakan bai yuwu ba sakamakon makanta da ta toshe min idanun yin hakan. Sai dai kafin Allah ya karbi idanun da ya bani aro, ni shaida ce Dee mai kyau ne, Dee yana da kwarjini a idanun kowa.� Kalaman yarinyar suna yi masa kama da mai son cusa masa rauni a Zuciya. ““Nasreen kada ki damu za ki gan ni da zarar muka ci karo da Dokto din da zai yi maki aiki.� Cikin rauni ta ce, “Don Allah zan roKe ka wani abu. Amma sai a ranar da Za a yi min aikin.� “Allah ya kaimu ranar.� Ya mayar mata da amsa yana jin barci yana son kwasarsa. Zakiyya ta shigo dakin tana Kare masa kallo, “Da waye kake waya?� Firgigit ya bude idanunsa, “Kin ajiye ni ne kike min tambaya irin wannan? Ban sani ba.� Zakiyya ta shaKa iya shaKa ta fara antayo masa maganar da duk tazo bakinta, “Wallahi na dade ina zargin ka koma bin matan banza, ga ni a gida sai ka je waje kana neman na wasu, saboda haram tana da dadin aikatawa,� Sosai ya ware idanunsa, “Ashe kina iya bambance Haram da halas? Idan kika sake danganta ni da aikata zina sai kin yi danasani. Idan na fita waje na nema ina ruwanki? Ki gyara kanki mana ki ga yadda namiji ke zama a like da matarsa. A Kazantar naki ne zan zauna da ke? Ke fice min a daki tun kafin fushina ya sauka a kanki.� Zakiyya ta fasa kuka ta fice. Nasreen kuma tana gama saurara ta sauke wayar jikinta a sanyaye. Ta fara hango tarin Kalubale a cikin zamanta da Zakiyya. Kalmar warin da Sultan ya yi amfani da ita, ta tsaya mata a rai. Wannan ke yi mata nuni sai ta sake tashi tsaye wajen ganin ta zage dantse domin Kwato mijinta, don ganin ta faranta masa. ZAMU TASHI A zahiri kowa ya san ita ce uwargida ba amarya ba, amma yanzu dole ta amsa suna har kala biyu, gata amarya gata uwargida. Yumnah tana shigowa ta kwashe abinda ta ji a tsakanin Sultan da matarsa ta gaya mata. Yumnah ta yi shiru daga bisani ta ce, � “Mijinki ma dan Kyale-Kyale ne, ko da yake wani. namijin ne a duniya baya son gayu? . Waye zai ce baya son tsafta? Ko Kazami yana _, son tsafta. Zan sake gaya maki wasu * abubuwa, abinci kuma ko da baki gani ai kinga ina yi maki bayanin yadda na hada abubuwa ko? Na tabbata idan kuka dawo daga Asibitin Dr Al-ameen za a ajiye ki a ci-:gaba da ba ki kulawa, kuma nasan gidansa za ki zauna kafin ki gama ganin likita. Ga Jidda can gwana ce na tabbata za ta tsaya maki ki iya komai. Kunya halak ce amma ba koda � yaushe za ki dinga jin kunyar ba, kada ki tauye hakkin mijinki.� Haka suka ci gaba da tattaunawar su, Nasreen tana fatan taga fuskar Yumnah domin ita kanta tana da labarin Six lovers, bata mance su ba, haka labarin rashin jinta ita da Yumnah suna kama da juna, duk da Jidda ta dameta ta shanye. Shi kuwa Sultan tana fita ya dubi wayarsa ya kashe, bai ji dadi ba, da Nasreen ta ji matsalarsa da matarsa, kasancewarsa namiji ne da ya tsani wani yana jin matsalar gidansa. Kamar zai sake kiranta yaso Kwarai ta yi masa karatun nan nata mai dadi Kila ya taimaka masa wajen samun barci mai cike da natsuwa. Duk da hakan ya sami natsuwa a ‘yar hirar da suka yi. Yanzu abu daya ya rage masa ya fara shirin baiwa Abbansa mamaki, � yana da tabbacin mahaifiyarsa za ta ba shi mamaki fiye da wanda ya baiwa Abban. Cikin ‘yan kwanaki ya gama tsara komai. Kafin ya tafi ya ba wani dan sanda umarnin ya kai Zakiyya Kaduna gidan mahaifiyarta ta gaidata. Hakan ya faranta ran Zakiyya domin tana kewar gidansu. Tana tafiya, yasa ma’aikata su kwashe komai dake gidan a shimfida sabo. Hatta fentin gidan yasa a sauya. Sai da ya tabbatar ya bar masu kula da � komai sannan ya kama hanya a nufi gidan Aslaf cike da saKe-sake. A farfajiyar gidan ya ganta tana zaune tana cillawa yaran Yumna ball suna kwasar dariya, Nawfal kuma yana wurin filawowi yana tsinkowa yaran. Ganinsa yasa Nawfal Karasawa yana aikin dariya, “Dee na yi fushi.� Sultan ya matse kunnensa ya ce, “Gaya min kalan fushin da kayi.� Ya riKe hannunsa yana fadin ya tuba bai yi fushi ba. �= * *Yan sandan.suna ta murmushi saboda yadda suka burge su. Nasreen tana cilla Ball din Sultan ya cafe yaran suka zo da gudu � guna fadin “Deedi Oyoyo.� . Farin ciki ya kama Nasreen, kawai ta sa dukka tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana dariya. . . Yana Karasowa ya sa hannu ya bude � fuskar yana cewa, “’Yar baby babu kyau fa abinda kike yi babu kyau rowar fuska.� Sosai take aikin dariya irin wanda bai taba gani a fuskarta ba. Ya kama hannunta suka shige falon. Yana shiga a tsaye suka gaisa da � Yumnah ya ce ta fito mata da kayanta sauri yake yi za su wuce. � Jikin Yumnah asanyaye ta fito mata da kayanta, daman tuni sun shirya. Nasreen ta rungume yaran tana gaya masu za ta dawo, gabadaya kuka suke yi. Sultan ya kirawo su. yana son lallashin su, suka Ki zuwa suka fice suna kuka. Yumnah idanunta sun kawo ruwa * ya ware idanu, “Kiyi kukan ki ga abinda zanyi maki.� Aslaf ya shigo yana hararar Sultan, ‘““Me za ka yi mata idan ta yi kukan? Kai haka ake lallashi? Ko kuwa matarka kadai ka iya lallashi ba ka iya na Kannenka ba? Kin ji yi kukanki amma kadan mu ga abinda zai yi maki.� Yumnah ta kwantar� da kanta tana dariya a jikin mijinta. Nasreen dai sai wasa take da hannayenta, kanta a Kasa domin ba Karamin kunyar Aslaf take ji ba. Sultan ya yi banza da shi, yana jin haushin yadda yaki raka shi. Haka aka kwashe kayayyakin su aka zuba a mota. Nasreen tana kusa da shi, Nawfal ma yana gefensa, gaba daya sun sanya shi a tsakiya. Nawfal yake bashi labarin yadda Aslaf ke daukarsu shi da yara ya kai su wuraren shaKatawa. Sultan ya ce, “Iyye ‘yan gata ita kuma Nasreen fa?� Nasreen abin nema ya samu, sai kawai ta kwanta a kafadarsa ta ce, “Ni basa fita da ni, wai cewa suke yi ni matar aure cé. Watarana in yi kuka.� Sultan ya yi murmushi, “Lallai Uncle Aslaf bai kyauta ba sam! Ki kwantar da hankalinki idan muka je Kaduna zamu je wuraren shaKatawa kala-kala nasan za ki ji dadi a zuciyarki ko?� gyada kanta ta yi. Nawfal ya fara yin barci ya kwantar da kansa a jikin Sultan, ita ma ta kwanta a daya barin. Ajiyar zuciya ya Kwace masa. Haka yana ci gaba da godewa Allah da ya sake dawo masa da farin cikinsa a karo na biyu. Yanzu tunanin masifar da ke gabansa kadai ke fadar masa da gaba. Cikin hukuncin Allah suka dinga keta dazuzzuka da garuruwa, har suka iso garin na Gwamna. Suna isowa cikin gidan -su, Hafsat tana fitowa, ganin Yayanta yasa ta koma da sauri ta sanar da Abba da Umma. Dama kuma Zakiyya da mahaifiyarta sun zo gidan don haka suka cika da mamaki domin babu wanda yasan zai zo. Gaba daya aka fito kamar sun zo ganin gwamna. Sultan ya fara fitowa, kai tsaye gaban mahaifinsa ya nufa, ya dan rankwafa yana gaida shi, Abban ya kamo shi suka rungume juna yana bubbuga bayansa. . � Sultan ya yi magana cikin sanyi da mutuwar jiki, “Abba na dawo maka da farin cikinka, bansan irin tarbar da za su samu ba,a karo na biyu.� Abba bai fahimci abinda yake nufi ba, don haka ya dago shi daga rungume juna da suka yi, ya kafe shi da ido, hakan yasa ya dubi ‘yan sandansa ya yi masu alamu da su bude motar. Nasreen da Nawfal suka fito, fuskokin su cike da farin ciki. Nawfal yake riKe da sandar Nasreen. Ba Umma ba, hatta shi kansa Abban sai da ya fazana da ganin ‘yan tagwayen sun Kara girma, Abba ya kasa magana sai sakin Sultan da ya yi ya nufe su gadan-gadan. Nawfal ya saki sandar Nasreen ya rungume Abba sai hawaye. Nasreen ma ta samu ta lallaba har ta taba jikin Abba ta ce, cikin kuka, “Abbana ne? Allah na gode maka.� Abba ya hada su ya rungume a Kirjinsa, sai hawaye, “Allah kaine abin godiya. Yau ga ‘yan biyuna sun sake dawowa. Allah kada ka sake jarabtana da rasa su don isarka Allah.� Abba ya yi ta surutai yana maganganu. Umma ta dubi Hajiya Ladidi, haka ta dawo da dubanta ga Zakiyya da ciwon hauka yake shirin kamata. Umma ta yi iya dauriya bata furta komai ba, bare ita Hajiya Ladidi da bata da ikon cewa komai. Zakiyya ta zabura za ta yi magana Hajiya Ladidi ta datse mata Kafa, haka Umma ta Kyafta mata idanu. Shi dama Sultan idanunsa yana kan su Abba da ‘yan biyu don haka ya harde yana kallonsu yana murmushi. Daga bisani ya ce wa su Abba su zo su shiga ciki. A babban falon gaba daya suka zauna idanun Sultan Kyam akan Nasreen har baya son ya kauda idanunsa. Dukka dakin . suna kula da hakan amma sai suka share. Sultan ya sake gaida iyayensa duk suka amsa babu yabo babu fallasa. Ya dubi Nasreen ya ce, “Ku tashi ku gaida Umma.� Nasreen ta fara ta shi tana lalube. Kamar za ta fadi Sultan ya yi saurin kamata, ya iso da ita gaban Umma yana murmushi, “Umma ga diyarki ta dawo.� Umma ta saki yake ta ce, “Oh ka barta mana kake ta shisshige mata. Ka barta ai zamu gaisa.� Sultan ya barta ba tare da ya kawo komai a ransa ba. Abba ya sake duban yaran cike da farin ciki ya ce, “Yanzu ni wani irin tukuici zan baka? Na rasa shin mafarkin da na saba yi ne nake yin sa ko kuwa da gaske ne idona biyu?� Umma ta ce, “Ba mafarki ba ne da gaske ne, Hajiya gwaggo ce ta dawo.� Dukka dakin babu wanda ya ji mai ta ce, sai Nasreen da ke sunkuye a kusa da ita, hakan yasa ta dan sha jinin jikinta. Abba ya dubi Zakiyya da fara’a ya ce, “Zakiyya kin ga ‘yar uwar zamanki Allah ya yi dawowarta ko?� Nan ma shiru babu wanda ya yi magana, shi kuwa Abba bakinsa ya gaza rufuwa. “Sultan tun yaushe ka gansu ne?� Sultan ya dan saci kallon Umma ya ce, “Ai sun kwana biyu a hannuna, na ajiye su ne kawai ina son basu kulawa kafin in kawo maka su.� Umma ta zabura saboda mamaki da kuma gigicewa, da halin Sultan, da ace lokacin da ta haife shi akwai wata a dakin haihuwar da sai ta rantse ba jininta bane, ansauya mata ne. Kowa ya juyo ana kallonta, , Sai kuma ta wayance kamar tana muskutawa. Zakiyya ce ta daddage ta fashe da kuka, hakan ya jawo hankalin kowa kanta. Abba ya ce, “Assha! Me kuma ya kawo_ kuka Zakiyya? Me aka yi maki?� � Zakiyya ta fara magana cikin kuka, “Abba ina gidan nan tare da Yaya Sultan amma bai taba gaya min an ga Nasreen ba, ai da. na taya shi da kula da ita. A zatona Nasreen ai ‘yar’uwata ce, me zai sa ya Boye min idan ba ya dauke ni muguwa ba?� Abba ya ji dadin kalaman Zakiyya don haka ya girgiza kai, “Ba ka kyauta ba Sultan, ko ba za ka gaya mana ba don kana son ka bamu mamaki ita ai matarka ce, sai ka gaya mata komai, ana boyewa kowa abu amma banda mata.� Sultan ya dube ta bai yi mamaki ba, idan har da gaske goyon Hajiya Ladidin da ya sani ne, babu abinda ba za taiba. “Zan kiyaye Abba.� Ya baiwa mahaifinsa amsa saboda ba ya son damuwa. Umma dai sai ta zama:kamar wacce ta zauce, sai ta dubi Nawfal sai kuma ta dubi Nasreen, a lokaci guda kuma ta watsa idanunta akan Abba da Sultan. Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Abbana kullum sai na ganka a mafarkina.� Abba ya sake cika da farin ciki. A nan Nawfal yake basu labarin dukkan wahalar da suka sha, daga ciki har da sunan Mansur da ya kusa aure Nasreen a cewarsa Sultan ya rasu. Sai dai ya boye sunan Umma. Hakan yasa ta saki ajiyar zuciya mai Karfi. Hakan kuma bai sa ta ji ko alamun tana son yaran ba, haka bata ji tausayin su ba, kamar yadda Abba yake jin tausayin nasu yana ratsa shi. Nasreen ta Kara da cewa, “Abba na gode Allah da na sake jin muryoyinku a duniyata.� Umma da taji kamar ta shaKeta ta mike, domin gani take yi kamar da gangar suke yin hakan domin su sanya mata ciwon kai. Tana mikewa Zakiyya ta bi bayanta, sannan Hajiya Ladidi. Falon ya rage daga Abba sai Sultan da ‘yan biyun. Babu wanda ya yi mamakin yadda Umma taki jajanta masu. Sultan dai ya Kosa ya sami dama daga shi sai Nasreen dinsa. Ji yake kamar za a sake raba shi da ita. Abba ya dubi Nawfal ya ce muje a fitarwa ‘yan sanda da abincin su. Abba ya yi hakan ne domin yana karantar yanayin dan nasa. Suna ficewa Sultan ya _ dawo kusa da ita, ya ja dogon hancinta ya ce, “Nasan da matsafan nan sun yi yunKurin kasheki, da hancin nan za su fara, sai kuma lips dinnan masu kyau da daukar idanu.� Hannunsa ta rike tana murmushi sannan ta ce, “Deedina wai da gaske ne tun ina Karama suke nemana? Abin ‘ya ba ni tsoro, wai sun sha zuwa za su sace ni Sai su ganka tsaye akanmu kana yi mana addu’a.� Sultan da ya shigar da ita cikin jikinsa sosai ya kai bakinsa cikin kunnenta yana magana, “Zai yuwu da gaske ne zai yuwu kuma Karya ‘ce kawai irin nasu. Kila akwai wanda ya sanni ne ko yasan ku a cikin gidan -nan. Mutanen nan idan ba ka yi hankali da su ba, sai su dulmiyar da musulmai. Ko sun yi ninyar shan jininki kin fi Karfin su Nasreen, ,_, Kina dauke da abinda ba su da shi. Ke jikinki a tsaftace yake, su kuma babu Allah a ransu. Kullum cikin Kazantar tsafi suke.� Nasreen ta sa hannu tana KoKarin ture � shi, sai dai yadda jikinta yake a mace ba ta iya daga hannunta yadda ya kamata. “Dee, � babu kyau fa.� Murmushi ya yi, “Mene ne babu kyau a ciki? Fada min sunan abin sai in daina.� Ta kasa magana sai mayar da ajiyar zuciya take yi a Kagauce. Ya rasa wani irin Kamshi ne haka yake ratsa shi a jikin Nasreen, Kamshin, akwai sanyi da kwantar da hankalin duk wanda ya shaka. Ga shi abin burgewa wanda yake nesa bai isa ya ji � Kamshin ba, sai ka matso kusa da ita sosai, “Babyna Kamshin nan wai a ina aka samo shi ne? Yana gigita ni da yawa, a gaya min nawa ne kudin turaren sai inbada a siya da yawa kada ya Kare.� Ita kanta bata san lokacin da take bashi amsa ba, domin kuwa ta fita hayyacinta, “Dee ba turare bane, humra cé irin ta Maidugurin nan. Ko ya Kare ya riga ya kama jikina ba zai daina Kamshin ba…� Ba ta kai ga ajiye numfashi ba, ya sake biyo mata da hanyar da maganar ma ta gagareta, sai ajiyar zuciyar A can dakin kuwa Hajiya Ladidi ta dubi Umma ta ce, “Kin gani ko? Karamar alhaki tana neman ta tsole mana idanu Daman Mansur ya fada mana ya ce tunda suka kubuta daga hannun mu za su dawo, hakan ya sa ya ajiye yaransa a bisa layi, ta yadda suna ganinsu kafin su shigo a sake dauke su, ta ya ya har yaran nan suka sami ganin Sultan, duk yadda ganinsa ke da matuKar wahala? Ya aka yi ma suka san yana Abuja?� Hajiya Salma ta Harare ta, “Ta ina kike jin magana ne Hajiya Ladidi? Ba ki jin a cikin labarin da yaron yake badawa ya ce motar su Sultan ce ta buge suba? Ni ba wannan ba 6/10/22, 09:22 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 2 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Ta kasa magana sai mayar da ajiyar zuciya take yi a Kagauce. Ya rasa wani irin Kamshi ne haka yake ratsa shi a jikin Nasreen, Kamshin, akwai sanyi da kwantar da hankalin duk wanda ya shaka. Ga shi abin burgewa wanda yake nesa bai isa ya ji � Kamshin ba, sai ka matso kusa da ita sosai, “Babyna Kamshin nan wai a ina aka samo shi ne? Yana gigita ni da yawa, a gaya min nawa ne kudin turaren sai inbada a siya da yawa kada ya Kare.� Ita kanta bata san lokacin da take bashi amsa ba, domin kuwa ta fita hayyacinta, “Dee ba turare bane, humra cé irin ta Maidugurin nan. Ko ya Kare ya riga ya kama jikina ba zai daina Kamshin ba…� Ba ta kai ga ajiye numfashi ba, ya sake biyo mata da hanyar da maganar ma ta gagareta, sai ajiyar zuciyar A can dakin kuwa Hajiya Ladidi ta dubi Umma ta ce, “Kin gani ko? Karamar alhaki tana neman ta tsole mana idanu Daman Mansur ya fada mana ya ce tunda suka kubuta daga hannun mu za su dawo, hakan ya sa ya ajiye yaransa a bisa layi, ta yadda suna ganinsu kafin su shigo a sake dauke su, ta ya ya har yaran nan suka sami ganin Sultan, duk yadda ganinsa ke da matuKar wahala? Ya aka yi ma suka san yana Abuja?� Hajiya Salma ta Harare ta, “Ta ina kike jin magana ne Hajiya Ladidi? Ba ki jin a cikin labarin da yaron yake badawa ya ce motar su Sultan ce ta buge suba? Ni ba wannan ba ZAMU TASHI ne a gabana ba, ta ya ya za ayi dana ya zauna da ‘yar zina! ‘Yar da bata da asali? Kai .Wallahi da sake ba zai yuwu ba. Ni Ummu Salam ba.zan lamunta ba, basu san da wa suke zance bane. Dole zan koma Abujan da zama, duk hanyar da zan bi inhana wani abu ya faru a tsakanin su babu shakka zan bi inKkwato dana, kafin insan hanyar da zan.° batar da ‘ya’yan shegun gaba daya kowa ma _ ya huta. Wallahi zan iya kashe yaran nan-: musamman ma Nasreen din da hannayena. ° Kai ina ba zai sabu ba! Kaf zuri’ata babu . shegu, babu mazinata babu arne babu yaddaza a yi ace wai dana ne da kansa zai kawo. min wannan masifar. Yau har gara ‘a Kwankwasa min Kofa ace mahaifiyar Sultan ce ta zo tana fadin Sultan ba dana bane, ba_ jinina bane. musayarsa aka yi min. Yaron da.. ko irin dokin mahaifiyar nan da wasu yaran suke yi baya yi? Kwata-kwata Sultan bai ~. .~ damu da ni ba.� Sai kuma tasa kuka. Jikin :: Hajiya Ladidi ya yi sanyi, ta tabbatar da� ‘gaske Hajiya Salma take yi ta tsani yaran tsana mai tsanani, hakan ya dan ragewa Zakiyya irin tarin matsalar da ke cikin zuciyarta, domin ji take yi kamar ta kashe kanta ta huta. Umma ta ce, “Zo mu je falon, ba zan taba barin su su sami sukuni ba indai ni ce.� Nawfal yana shigowa ya hango su Umma da Hajiya Ladidi da Zakiyya sun nufo falon, haka yana da tabbacin Sultan yana tare _ da Nasreen, don haka dabara ta fado masa, ya yi sauri ya riga su Karasowa bakin Kofar ya dinga magana da Karfinsa, “Nasreen Abba ya ce mu je mu ci abinci.� � Sai da ya maimaita sau biyu sannan dukkan su suka ji, Sultan ya dinga jujjuya dalilin da zai sa ya tsaya yana magana da ihu, daga bisani ya mike ya barta a nan ya taho bakin Kofar don yaga abinda ke faruwa. Umma ta watsawa Nawfal harara ta ce, “Mene ne haka zan gani? Meye na yi mana ihu a gida bayan kasan gidan nan ba a ihu? Ko bayan makantar da ke gareta har ta koma kurma ce?� � A take Sultan ya gane abinda Nawfal ke nufi ya saki murmushi yana jinjina wayon _yaron. Umma ta dube shi tana mamakin dama su biyu ne a falon? A Kufule ta ce, “Ina Abban naka?� Daga baya Abba ya ce, “Ga ni wa ke nemana?� Umma ta sake cika da al’ajabi. Da gaske take yi ta shirya zama ta yi _ gadin Nasreen da Sultan. Falon ta kutsa abin mamaki Nasreen barcinta take yi. Umma ta waiwayo tana duban Sultan, “Ita Nasreen din har tayi barcine?� ~~ � Sultan ya saki ajiyar zuciya, yana sane da idanunta biyu amma sai ya yi fuska ya ce, “Ni ma yanzu na shigo falon na sameta tana barcin.� Umma ta gyada kanta ta koma ta zauna tana zazzare idanu. Hajiya Ladidi ta bar Zakiyya a nan ta ce ta zauna taga abinda ke faruwa, sannan ta yi masu sallama da za ta tafi Sultan ya dibi dubu ashirin ya bata. Ta dinga godiya sannan ta wuce tana tunanin mafita. Taso ta turo Mansur, sai dai irin tsaron da suke tafe da su, sun yi matuKar razanata. Dare ya tsala wuri ya yi shiru babu abinda kake ji sai kukan abubuwan daji da ba za a rasa ba. Sultan idanunsa biyu ya kasa barci, haka Umma idanunta biyu, Zakiyya ma idonta biyu. Nasreen kuwa ta yi nisa cikin barcinta, a cikin dakinta da take tunanin ba za ta sake zama a cikinsa ba. Sultan yana tsaye ta windo yana kallon wutan dakin Umma a kunne. Ya riga ‘ya fahimci abinda take nufi. Yana nan tsaye a bakin windo yana kalle-kalle ya ga Umma ta wuce dakin Abba hannunta dauke da ruwan zafi, hakan yasa tana wuce wa ya fada dakin Nasreen. Sai da ya murza dan makulli sannan ya haye gadon, ya jawo ta jikinsa. Cikin magagin barci ta sake shige masa, ya saki ajiyar zuciya. “I love you� Wife.� Ya furta a fili yana Karewa kyakkyawar fuskarta kallo. Wannan karon ta farka sai dai yadda gabanta yake faduwa ya sa ta kasa nuna masa ta tashi. Wani sako ya aiko mata mai matukar mahimmanci da tasiri ga jikinta, hakan ya sa ta riKe hannunsa ta ce, “Wash! Deedi zan mutu kaina ciwo.� Ya rada mata a kunne, “Sorry za ki ji sauki kin ji?� ‘Yadda take mutsu-mutsu .ya sa ya rungume ta kawai ya ce su yi barci. Nasreen tasa masa rigima ita ba za ta iya ba, shi kuma ya yi rantsuwa ba zai kwanta a ko ina ba sai a dakin nan. Haka ta hakura ita kanta tafi son ta ji ta a kusa da shi. Daga shi har ita suka yi wani irin barci mai dadi da sanya natsuwa. Ya jima bai yi barci mai dadin na yau ba. Hancinsa yana shakar daddadan Kamshinta mai ratsa Zuciya. , A kunnensa aka kira sallar asubahi, don � haka ya sake jawota sosai cikin jikinta ya ce, “Wife ta shi an kira Sallah.� Ta rasa yadda za ta gaya masa ba ta yin Sallah, sai kawai ta tura kanta cikin jikinsa, “Dee sai anjima zanyi.� Yadda ta yi maganar yasa shi murmushi, ya kuma kai hannunsa ya laluba ya ji alamun ta sanya pad ya ce “Iyye “yar yarinyar nan ta girma fa. Nasreen har yanzu ina mamakin girmanki. Ashe matata nake reno. Mu maza mun more, mu ci zamanin mu mu ci na ‘ya’yanmu daga Karshe kuma mu ci na jikokin mu.� Nasreen ta yi matuKar jin kunya hakan yasa ta KanKame jikinta a cikin nasa tana ‘yar dariya. Da Kyar ya Kyale ta ya shiga bandaki ya yi alwala a gurguje bai yi garajen fitowa ba, har sai da ya leKa ta windo sannan ya fito. A lokacin kuma Umma ta fito daga dakin Abba, sai kallon-kallo tsakaninta da Sultan. Gabanta ya fadi tana tunanin ashe gadin banza ta yi jiya kenan tunda gashi ya shiga dakin Nasreen ba tare da ta sani ba. “Kai dai ka ji kunya. Uban me ka je yi a dakin yarinyar nan? Da wani lokacin ma ka shiga? Yau na ga masifa anya yarinyar nan ba mayya ba ce?� Sultan ya yi murmushi cikin salonsa ya ce, “Umma da mayya ce ai babu wanda zai sha a cikin gidan nan. Ba ki gan ni da alwala ba? Yanzun nan na leKa ta in ga yadda ta tashi tunda kin san ba idanu gareta ba.� Umma ta sake Kufula duk da ta sami natsuwa da ya ce yanzu ya leKa ta, ta ce “Ban sani ba! Na ce maka ban san makauniya ba ce, amma yanzu ai da ka gaya min ka ga na fahimta. Iskancin banza kai Yau ta fara shiga bandaki ita kadai? Ko kuwa kai kake yi mata jagora a lokacin da suka tafi yawon gantalin su? Ga Zakiyya can da ta baro gidansu ta zo nan ta kwana ka je ka duba ta? Bana son rashin adalci, idan ka fara bambanta matanka ni ina tabbatar maka zan dauki mataki.� Sultan bai ce komai ba yana KoKarin wucewa Masallaci Abba ya fito suka hada hanya. Nawfal ma ya fito daga dakinsa duk suka dugunzuma. Sai bayan sun fito ne Sultan ya gaida mahdifinsa, sannan Nawfal ya gaida su. Suna hanyar dawowa Abba ya dubi Sultan cike da damuwa ya ce, “Sultan ka bi a hankali da mahaifiyarka, ka kiyaye mata tun kafin ta hanaka zaman lafiya a tsakaninka da iyalanka. Bana jin dadin abinda � Salma take yi, amma babu komai akwai lokacin da ko kudi aka bata ba za ta aikata ba: Kai dai ka zama tsayayyen namiji a cikin gidanka, duk yadda kafi son dayaka daure ka � dinga boye soyayyarta a zuciyarka idan ba haka ba, za ka siyo masifa ne da kudinka ka kawo cikin gidanka. Ita mace haka Allah ya Halicce ta komai ta fi son ta ji ance ita ce gaba. Saken da namiji yake yi a cikin gidansa � shi ke kawo matsalar� zaman lafiya. Sai ka jajirce ajiye mace fiye da daya a cikin gida sai Jarumi, jarumin kuma yana wahalar samu, shi ya sa Za ka ga namiji har namiji amma ba shi da wani Karfi a cikin gidansa, ina nufin muna da Karancin jarumai. Ina fatan za ka ba ni mamaki wajen ganin ka hana matanka jin zafin juna irin wanda addini baya so?� � Sunkuyar da kansa ya yi ba ya iya boyewa Abbansa komai don haka ya ce, “Abba akwai wahala gaskiya. Bana son Zakiyya na yi iya bakin KoKarina in ga nasa soyayyarta a zuciyata tun kafin in gano Nasreen abin ya faskara. A yanzu kuma bayan bayyanar Nasreen sai na ji na.sake tsanarta. Abba da ina da yadda zan yi da ba zan zauna da Zakiyya ba, domin tarbiyyar _ yarinyar ba ta yi min ba. Abba ko sallah Zakiyya ba ta yi, bare har a kai ga wataran ta dora abinci a tukunya. Har yanzu siyan abinci nake yi a kasuwa sannan in ci.� Abba ya dubi Sultan, haka ya jinjina masa a cikin zuciyarsa, bai taba tunanin Sultan zai iya haKuri da mace har irin hakan ba. Abba ya ce, ““Yadda ka yi haKuri da ita a farko haka za ka sake yin haKuri da ita a yanzu. Ka dinga nuna mata mahimmancin addini kana sanya idanu a kan yadda take addininta, domin mace babu addini tamkar gidan da akayi shekaru da zama ne ba a shiga ba. Ban taba sanin ba ta da addini ba, saboda daman zabin mahaifiyarka ce, amma idan ka tsaya ta gyara kaima kana da lada Sultan. Sannan ina gargadinka da boye soyayyar Nasreen, idan baka Boye soyayyar Nasreeen ba, idan ba ka nuna kamar Nasreen ba ta gabanka ba, za ka sha wahala a gun mahaifiyarka da gun matarka. Ya zama dole ka Boye dokin da kake yi a kanta. Ka san jiya hango mahaifiyarka na yi ta windo tana ta leKenka? “Ganin hakan ne ya sa na _ yanke shawarar aikenta ta kawo min kofin shayi. Sultan ka siyawa Nasreen zaman lafiya ka boye soyayyarta, duk da abu ne mai matuKar wahala, amma za ka iya. Dan lokaci ne kawai watarana a gabanta za ka nuna kana son Nasreen hakan zai faranta mata rai, watarana za ka iya bata wa Nasreen mahaifiyarka ta nuna maka bacin ranta. Sultan ya girgiza kai, “Abba gani nayi kamar wannan ranar ba za ta zo ba. Tu Nasreen tana cikin mahaifiyarta, Umma ta furta tsanarta ga uwarsu, har suka zo duniya bata sauya ba. Abba sai mun tsufa sannan zata sota?� Abba ya yi dariya a lokacin da suk karya kwanar shiga gidansu, “Ni na gaya maka za ta sauya ina raye ko ina ciki Kabarina za ka tuna da ni watarana. Idan ka dukkan shawarwarina za ka ga abin ya zaizo maka da sauKki.� Nawfal duk yana jin abubuwan da suke tattaunawa, har kowa ya koma dakinsa domin samun barci. Kamar a mafarki ya ji mutum kusa da shi, yana ware idanu yaga Zakiyya tana zaune ta hade rai kamar za ta yi “kuke Ji ya yi kamar ya kwasa mata mari sai kuma ya dake yana dubanta, “Lafiya kike tashina_ina barci?� Ta dan dube shi, “dama..damaaa…� Ya daka mata tsawa ya ce ta fice masa, yana dubanta cike da takaici, “Ke yanzu a gaban Umman kika wuce kowa saboda ke ce sarkin narasa kunya, kika zo dakina? In yi maki nene? Don Allah tashi ki fita barci nake ji.� Jiki a sanyaye ta mike har ta kai bakin ‘kofa ya ji a zuciyarsa bai kyauta ba, da ya yi mata hakan, ya tabbata da Nasreen ce ta shigo cikin bargo zai maidata. Ya zama dole ya jinga Kokari wajen ganin ya bi shawarar nahaifinsa. “Zakiyya.� Ya kira sunanta cikin sanyi. Ta waiwayo cike da mamaki. Har hawaye sun sami daman zubowa. Gabansa ya fadi, domin ya san kai tsaye gun Umma za ta wuce. Hannu ya mika mata, hakan ya sa ta dawo da sauri ta kama hannunsa ya zagayo da ita kusa da shi. Hijabin da tasa ya yaye sannan ya hadata da jikinsa. Warin attachment din kanta da Karni suka dake shi, ya dan kawar da hancinsa sannan ya fara magana cikin lallabawa, “Zakiyya ba na son ina bata maki rai amma ke kike sawa. Ki yi hakuri kin ji? Ba na son a yi maki kallon mara kunya ce, ki koma cikin jama’a.� Zuciyar Zakiyya fari sol! Ji take yi kamar duk duniya babu ‘ya macen da ta yi dacen da ta yi. Yana kallon ta ta fice tana ‘yar dariyarta. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yana son ganin Nasreen yana son ya yi barci wuri guda da ita, ta haka ne zai iya samun natsuwar da yake da buKata. Sai dai maganar mahaifinsa ita ke danne shi, dole ya mayar da kansa kawai ya kwanta. ********* A daddafe suka kai kwanaki biyu, yau ne kuma suke sa ran tafiya. Shiru-shiru Sultan yana jiran mahaifinsa ya hada su amma bai yi hakan ba, don haka ya ci gaba da zuba idanu. Yana daki yana shiri aka aiko Nawfal wai ya zo. Babu bata lokaci ya iso falon, abin mamaki dukkan halittun dake cikin gidan suna nan zaune a falon nan. Nasreen tana zaune kusa da Abba kanta a Kasa. Umma kuwa ta cika ta yi fam! Sai girgiza Kafafu take yi. 6/10/22, 09:35 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 3 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Jiki a sanyaye ta mike har ta kai bakin ‘kofa ya ji a zuciyarsa bai kyauta ba, da ya yi mata hakan, ya tabbata da Nasreen ce ta shigo cikin bargo zai maidata. Ya zama dole ya jinga Kokari wajen ganin ya bi shawarar nahaifinsa. “Zakiyya.� Ya kira sunanta cikin sanyi. Ta waiwayo cike da mamaki. Har hawaye sun sami daman zubowa. Gabansa ya fadi, domin ya san kai tsaye gun Umma za ta wuce. Hannu ya mika mata, hakan ya sa ta dawo da sauri ta kama hannunsa ya zagayo da ita kusa da shi. Hijabin da tasa ya yaye sannan ya hadata da jikinsa. Warin attachment din kanta da Karni suka dake shi, ya dan kawar da hancinsa sannan ya fara magana cikin lallabawa, “Zakiyya ba na son ina bata maki rai amma ke kike sawa. Ki yi hakuri kin ji? Ba na son a yi maki kallon mara kunya ce, ki koma cikin jama’a.� Zuciyar Zakiyya fari sol! Ji take yi kamar duk duniya babu ‘ya macen da ta yi dacen da ta yi. Yana kallon ta ta fice tana ‘yar dariyarta. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yana son ganin Nasreen yana son ya yi barci wuri guda da ita, ta haka ne zai iya samun natsuwar da yake da buKata. Sai dai maganar mahaifinsa ita ke danne shi, dole ya mayar da kansa kawai ya kwanta. ********* A daddafe suka kai kwanaki biyu, yau ne kuma suke sa ran tafiya. Shiru-shiru Sultan yana jiran mahaifinsa ya hada su amma bai yi hakan ba, don haka ya ci gaba da zuba idanu. Yana daki yana shiri aka aiko Nawfal wai ya zo. Babu bata lokaci ya iso falon, abin mamaki dukkan halittun dake cikin gidan suna nan zaune a falon nan. Nasreen tana zaune kusa da Abba kanta a Kasa. Umma kuwa ta cika ta yi fam! Sai girgiza Kafafu take yi. ZAMU TASHI Abba ya _dubi Nasreen� ya _ ce, “Althamdulillahi, dukkan godiya ta tabbata ga Allah da ya sake ba mu aron wannan ranar. Nasreen na sanki mace ce mai hakuri da rashin son hayaniya, tun a lokacin da naga shakuwarki da Sultan na tabbatar da babu namijin da zai riKe ki irin rikon wanda ya san darajar kansa ya san abinda yake yi sai Sultan. Ya fi kowa sanin darajarku ke da dan uwanki, yana sonku fiye da ~ tunanin mutum, saboda shi ya reneku tun kuna cikin tsumma. A yau zan damKa masa ke a matsayin matarsa ta har abada. Sai ki yi hakurin ; zaman aure, ki kwantar da hankalinki, ki yi wa mijinki biyayya. Allah ya yi maki albarka, Allah ya ba ki sa’an yi wa aure bauta.�� Nasreen da ta ji wani abu ya tsirga mata, a yau dai ta tabbatar da da gaske ne ita matar aure ce, auren ma na Sultan dinta. Kuka take yi sosai tana jin ko iyayenta ne iya abinda za su yi mata kenan, tausayin kanta ya kamata, tsoron wani irin zama za ta yi da kishiyarta suka sake wanzuwa a zuciyarta. Bata fatan ta baiwa Abba kunya a cikin rayuwar aurenta. Abba ya dan goge Kwallar da suke _ Kokarin zubo masa ya dubi Sultan, “Allah ya yi maka albarka Sultan, tabbas da ba dan kai ba, da ban samu tarin ladan nan ba. Ga matanka nan Zakiyya da Nasreen, ka riKe su amana, ka zama adalin namiji, kada ka yarda gidanka ya lalace ta hanyar baiwa wata Karfin da za ta mulki gidanka. Ka zama jarumi a cikin matanka. Daga Nasreen har Zakiyyar dukka naka ne, sai ka dinga kallon su a matsayin jininka.� Ya dawo da dubansa ga Zakiyya ya ce, “Zakiyya ga Nasreen nan ‘yar uwarki ce ba kishiyarki ba, kada zuciyarki ta sa maki da kishiya kike zaune a’a da ‘yar uwarki ce ta jini. Ga amanarta nan na baki. Kin girme ta nasan za ki fita hankali da sanin abinda ya . kamata. Ku hada kawunanku kuyi ta zane Sultan a cikin gidan.� . Zakiyya ta yi murmushin da ba ta yi ninya ba. Haka Abba ya ja masu kunne cikin sigar lallashi. Ya dubi Umma ko za ta yi magana, sai ta kauda kanta ta ce, “Wacce magana kuwa zan yi? Allah ya tsare sai na zo.� Babu wanda ya gane abinda take nufi. Nawfal a nan gidan zai zauna tukuna kafin ya wuce Makaranta. Nasreen ta sa kuka ba za ta tafi ta bar Nawfal ba. Haka ta KanKame Nawfal tana kuka mai tsuma zuciya. Jikin Sultan ya yi sanyi ya dubi Abba ya ce, “Abba a bar mana Nawfa! don Allah.� Abba ya girgiza kai, “Idan Nasreen tana kuka saboda babu Nawfal ranar da ya tafi Makaranta kuma fa? Kai ka san irin kukan da za ta yi ? Ku tafi kawai.� Nasreen ta sake sa kuka, Nawfal ya yi mata magana Kasa-Kasa, “Ki daina kuka Nasreeen zan zo insha Allahu. Ba rabuwa muka yi ba.� Shi ma hawayen ke zuba sosai a idanunsa, . domin yau ce rana ta farko da za su rabu. Tausayin ‘yan biyun ya kama Abba. Nasreen ta laluba ta kama Kafar Abba kawai tana kuka, gaba daya ta kasa magana. Abba ya shafi kanta, “Allah ya_ tsare hanya. Allah ya yi maki albarka.� Abba ya dagata ya kai ta har cikin mota. Kuka take yi tana kiran Nawfal, amma ina babu Nawfal sai � dai Sultan. Kukan da take yi yana daga masa hankali, ga shi Zakiyya ta kafe ta tsare bare ya bata kulawa. Duk da hakan sai da ya zaKala hannunsa cikin gyalenta ya ce, “Kiyi haKuri ki daina kuka kinji? Gobe insha Allahu Nawfal zai iso. Shiru kawai ta yi tana ajiyar zuciya ba don ta yarda � da abinda yake fadi ba. Zakiyya tana kula da » Nasreen yadda take kwance a kafadar Sultan, hakan ya sa ita ma ta kwanta tana gyangyadin Karya. Duk yana kula da ita bai ce komai ba. Suna isowa cikin gidan su gaba daya gidan ya sauya komiai sabo. Ita dai Nasreen bata san komai ba, domin ba idanu gareta ba, sai lalube take yi. Sultan ya kamo ta suka shiga ciki. A nan falon dukkansu suka zauna. Duk da gidan ya burge Zakiyya, amma sam ba ta yi farin ciki da wannan gyara ba, domin lokacin da za a kawota babu wani gyaran da akayi, a take kishin babu gaira babu dalili ya kamata, haka ta kasa tashi ta basu wuri. Gani take da zarar ta je ko nan da kitchen ne za a yi wani abun. Shi kuwa idanunsa Kyar a kan tv, wanda a zahiri ba tvn yake kallo ba, Nasreen yake kallo ba tare da Zakiyya ta ankare ba. Ya dube ta cike da Kosawa ya ce, “Tashi ki je ki hada min ruwan wanka.� Zakiyya ta dube shi sosai, ta fahimci yana son raina mata hankali ne, domin bai taba sanyata tara masa ruwan wanka ba. Zamanta ta gyara tana hamma, “To zan tara maka zuwa anjima yanzu na gaji da yawa ne.� Nasreen ta mike, “Deedi ina ne hanyar dakina?� Shima ya mike yace “Zakiyya, dama kin san sashenki. Ita kuma bari in kaita nata falon da kuma dakinta, wannan babban zai zama nan ne mahadinmu tunda falona ne.� Zakiyya ta saki baki tana kallonsa. Kafin ya kama Nasreen har Zakiyya ta kamo ta tana fadin, “Mu je sashen naki daga nan in gani.� Babu musu ta bi bayanta Sultan ya yi shiru yana nazarin matakin da ya kamata ya dauka don ba zai yarda da wannan iskancin ba. Haka ya taka Kafafunsa bai bi su ba ya shige bandaki ya watsa ruwa. Ya fito yana tsane jikinsa, Zakiyya ta shigo tana dubansa. “Na kai ta dakinta bangarenta gaskiya ya fi yi min kyau sosai.� Ko dubanta bai yi ba ya ce, “Bayan mun je wurin Abba da ya ganta ya tambaye ni kayan dakinta na ce masa na siya maku iri daya ya ce ai alhakin siya mata kaya yana wuyansa ne, shi ya bada izinin aka kwashe irin nakin na zuba su a dakin baki, shi kuma ya sa aka shimfida mata wanda ya bada kudi aka siyo. Don haka idan basu yi maki ba, sai ki gayawa Hajiyarki ta siya maki wasu.� Baki a sake take kallonsa, yadda ya soka mata magana ya kuma daure fuska. “Kana nufin gori kake yi min kenan? Na gode Allah ina da uba, kowa yasan ubana ba haihuwar titi ba ce.� Sultan ya juyo cikin tashin hankali, ya daga hannu ya wanke fuskarta da mari, yana dubanta, “Na san za ki iya yin karambanin nan, amma ba zan dauka ba. Wallahi duk ranar da kika kuskure kika yiwa Nasreen irin wannan gorin har ta ji, sai kin sha mamakin irin matakin da zan dauka a kanki. Ban auro Nasreen domin inkawota ki ce za ki taka ta, da haukan da ke kanki ba. Ubana shi ne uban Nasreen, zan bugi Kirji infadawa duniya hakan. Babu wanda zai sheganta min ~ mata in zuba idanu ina kallonsa, babu. Yadda kike taKamar namiji ya yi cikinki aka kawo ki gidan duniya, haka Nasreen ma za ta bugi Kirji ta ce namiji ne sanadiyyar kawo ta duniya ba mace ita kadai ba. Fice min a daki.� Jikinta na kyarma, hannunta a fuskarta ta fice. Tsoro da firgici suka shige ta, ba ta taba ganinsa a cikin bacin rai irin na yau ba. Ta fahimci yana iya yin Kasa-Kasa da ita. Tana shiga daki ta rufe Kofa ta shaki kukanta. Can ta wanke fuska ta fito domin tana tunanin Kila yana can wurin Nasreen. A falonsa ta same shi, bai je gun Nasreen din ba, sakamakon Kuncin da kalaman Zakiyya suka sanya shi. Yana nan kwance ya ji Sallama _ don haka ya daga kai ya ga ko waye. Mamaki shimfide a fuskarsa yake duban mahaifiyarsa. “Umma? Me ya faru kuma? Lafiya? Ina Abba?� Gaba daya ya rude yana tunanin ko wata matsalar ce ta sami Abbansa shi ne har ta taso ta ZO. Umman ta harare shi sannan ta shigo tana ~ bayar da umarnin inda za a ajiye mata Katon akwatinta. “Lafiyar ta kawo haka. Zuwa na yi ni ma in huta in yi kwana biyu, mahaifinka ya karbe office dinsa, don haka zan zauna a nan in sami hutu sosai. Hafsat ta dan durKusa tana gaida Sultan Shi kuwa mamaki da bakin ciki sun taru sun hana shi sakat. Duban Hafsat ya yi ya ce, “Yanzu fa muka taho muka bar ku a Kaduna. Ke Hafsat makarantar kuma fa?� Hafsat ta ce, “Ai sun yi hutu.� Kan Sultan ya sake daurewa bai fahimci dalilin da zai sa mahaifiyarsa ta yi wannan abin ba, bayan ta san mahaifinsa bai da wata mata idan ba ita ba. “Amma Umma shi Abban da wa kuka bar shi a gidan?� Umma ta ja tsaki ta nemi wuri ta zauna tana fadin, “Wash!� Tta gaji. Sultan ya sake maimaita mata tambayar ransa a bace. Umma ta zazzaro idanu, “To zo ka dake ni ubana! Ko kuma kawai ka ce min in bar gidanka sai in san na haifi dan da ya gagare ni. Kana kallon yadda kake yi min magana kamar ubana? Ban sani ba! Ka je ka gaya masa ya Kara aure mana tunda na ga kaine ubanmu daga ni har shi! Ban bar shi da kowa ba, sai ka nemo masa mace ka sa masa a cikin gidan. Shashashan yaro kawai mara kishin kansa. Ke dauki kayan nan ki kai min dakin Nasreen a nan zan sauka.� Zakiyya da farin ciki ya gama kashce ta, ta kwashi kayan ita da Hafsat suka nufi dakin Nasreen. Tana zaune bisa dadduma tana lazimi, sai kawai ta ji shigowar mutane babu sallama, mamaki yasa take tambayar ko su waye. Zakiyya da Hafsat ba su yi magana ba har sai da suka dire kayan sannan suka dawo gabanta, “‘Umma ce da Hafsat suka zo, za su yi kwana biyu, shi ne muka ajiye kayan a dakinki don a nan za su sauka.� Nasreen ta Kara cika da mamaki, don haka tace ‘“Wacce Umma kuma? Haba ba dai Umma ba, yaushe muka tafi muka barta a gida? Ko ba Umman Kaduna kike nufi ba?� Zakiyya da Hafsat suka yi ta mata dakuwa da hannu suna yi mata gwalo, sannan ta bata amsa, “Mence ne na yi min irin wannan tambayar? Ko dai in koma in ce mata kin ce a kwashe kayanta ne? In ba haka kike nufi ba meye na dogon magana?�� Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Babu wanda ya isa ya hana Umma zama a duk inda ta gadama. Kuma ni farin ciki nayi da har ta � tsallake dakin kowa ta zabi dakina. Ina yi mata barka da zuwa. Ga ni nan fitowa.� Duk suka bita da kallo, sannan suka fito suna cewa Umma Nasrcen sai tambayoyi take yi masu. Ran Umma ya sake baci ta zabura za ta shiga dakin Sultan ya mike ya sha gabanta. “Don girman Allah Umma kiyi hakuri.� Umma ta dawo ta zauna tana dubansa duba na takaici. Sultan ya mike ransa a Bace ya fice ya kira mahaifinsa, “Abba meke faruwa ne na ga Umma? Ko wani abu ya hada ku ne?� Abba da yake zaune a tsakar gida ya yi tagumi, idanunsa jazir saboda bacin rai, ya ce *Wallahi ban sani ba. Bayan kun tafi kawai naga tana shiri ban ce mata komai ba, har sai da suka gama kintsa kayansu sannan ta gaya min wai gidanka za taje Duk yadda nayi domin ta ajiye tafiyar amma taki. Na_ gaji da lamarin mahaifiyarka sakinta zanyi.� Sultan ya ji babu dadi, haka ya ji tausayin mahaifinsa, amma fadin sakin nan yasa gaba daya Karfin guiwarsa ya suki. Baya Kaunar dalilin da za ace mahaifiyarsa bata tare da auren mahaifinsa. Don haka ya ce, “A’a Abba ka yi hakuri kada ka yi min haka. Abba mu ‘ya’yanka ba za mu taba son a ce wai babu mahaifiyarmu a gidan mahaifinmu_ ba. Shawara daya zan ba ka Abba, ka duba a cikin mata masu hankali da natsuwa ka aura.� Abba ya dan yi shiru cikin dogon tunani. Daga bisani ya ce, “Sultan ni wa na sani da zan aura? Ka barni kawai inzauna ni dayan babu komai watarana sai labari.� Girgiza kai Sultan ya yi cike da tausayin mahaifinsa, “Abba ka auri Mairo mai aikinmu, naga tana da hankali da natsuwa. Yin hakan Kila ya sanya Umma ta dawo hayyacinta. A zuciyar Abba ba ya son wata “ya mace . da ta wuce matarsa, Haka ba shi da ra’ayin Kara aure, amma halin masifa irin na Salma ya saya amince da abinda yaron ya gaya masa, don haka suka sa ranar da Sultan zaije a yi magana. Yana datse Wayar ya rintse idanu yana jin tausayin mahaifinsa da gaske. Nasreen da ta jima tsaye tayi magana cikin muryar kuka, “Deedi da bakinka kake cewa ayi wa Umma kishiya? Me yasa ba za a lallaba ta ta koma ba? Ina jin tsoron abinda zai je ya dawo.� Sultan ya mayar da idanunsa kan. makauniyarsa ya ce, “Nasreen na gaji da halin Umma. Idan aka yi mata kishiyar Kila za ta _ sauya. Amma kishiya kam dole sai Abba ya yi mata. Nusreen taci gaba da cewa, “Kishiya ba ita bace mafita kayi tunani da kyau.� Sultan ya karaso gabanta yana_ son Nasreen fiye da tunanin mutum, “Nasreen ki bar wannan maganar na rufe ta. Ya aka yi kika zo nan?� Ajiyar zuciya ya Kwace masa. Mai aiki ta saita ni har inda kaKake. Su Umma suna ciki suna cin abincin da dan sanda ya kawo. Yanzu kana ganin haka zamu zauna ana siya mana abinci? Ni ba idanu gareni ba bare in shiga kitchen.� Sultan ya ce, “Wallahi ni kaina abinda ke damuna kenan. Yanzu ya zaa yi?� _ Sai da ta jingina da bango kafin ta ce, “Ina ganin a shawara, ka sanya a nemo mana mai aiki wacce ta Kwarai a iya ayyukan abinci sai mu mayar da ita mai girkinmu. Amma ya ka gani?� Sai da ya lakaci hancinta sannan ya ce, *‘Abinda kika ce shi za a yi. Wannan ma shawara ce mai kyau. Yanzu kin gane dalilin da yasa Umma ta sauka a dakinki?� Girgiza kai ta yi cike da rashin fahimta, : “Wallahi ban gane komai ba.� : Nan da nan fuskarsa ta nuna bacin rai, “Umma ta zo garin nan ne saboda ba ta son mu _ kadaice ni da ke. Na rasa irin wannan abinda Umma take yi.� Nasreen ta yi murmushi, “In dai haka ne ai ni ta taimaka. Allah ya Karawa Umma lafiya.� Mamaki yasa ya murde hannunta ya ce, “Maimaita abinda kika ce. Ni kuma tunda kika 6/10/22, 09:45 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 4 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Nusreen taci gaba da cewa, “Kishiya ba ita bace mafita kayi tunani da kyau.� Sultan ya karaso gabanta yana_ son Nasreen fiye da tunanin mutum, “Nasreen ki bar wannan maganar na rufe ta. Ya aka yi kika zo nan?� Ajiyar zuciya ya Kwace masa. Mai aiki ta saita ni har inda kaKake. Su Umma suna ciki suna cin abincin da dan sanda ya kawo. Yanzu kana ganin haka zamu zauna ana siya mana abinci? Ni ba idanu gareni ba bare in shiga kitchen.� Sultan ya ce, “Wallahi ni kaina abinda ke damuna kenan. Yanzu ya zaa yi?� _ Sai da ta jingina da bango kafin ta ce, “Ina ganin a shawara, ka sanya a nemo mana mai aiki wacce ta Kwarai a iya ayyukan abinci sai mu mayar da ita mai girkinmu. Amma ya ka gani?� Sai da ya lakaci hancinta sannan ya ce, *‘Abinda kika ce shi za a yi. Wannan ma shawara ce mai kyau. Yanzu kin gane dalilin da yasa Umma ta sauka a dakinki?� Girgiza kai ta yi cike da rashin fahimta, : “Wallahi ban gane komai ba.� : Nan da nan fuskarsa ta nuna bacin rai, “Umma ta zo garin nan ne saboda ba ta son mu _ kadaice ni da ke. Na rasa irin wannan abinda Umma take yi.� Nasreen ta yi murmushi, “In dai haka ne ai ni ta taimaka. Allah ya Karawa Umma lafiya.� Mamaki yasa ya murde hannunta ya ce, “Maimaita abinda kika ce. Ni kuma tunda kika ZAMU TASHI fada hakan a gabanta zan dinga daukarki in wuce dakina da ke.� Tana Kyalkyatar dariya ta ce, “Wallahi na yarda.� Shi ma murmushin kawai ya yi suka ci gaba da ‘yar hirarsu. Da suka gaji ne ya kama hannunta ya saita ta a kan hanya sannan ya tsaya yana kallon ta har ta shige, shi kuma ya fice Zuwa gidan Ashmaan. Ba shi ya dawo ba sai dare, abin mamaki har yanzu suna nan zaunea a falon wai suna kallo. Sai da ya dan saci kallon Nasreen baiwar Allah barci take yi a zaune. Ya dubi Umma ya ce, “Umma ku tashi ku ~ je ku kwanta dare ya yi.�� Umma ta tashi tana hamma ta bubbugi Nasreen ta tashi tana magagi, ta kamo hannunta ta juyo tana duban Sultan. “To sai da safe, ina ganin kamar Zakiyya ta yi barci ka tasheta.� Dama tuni Hafsat ta shige abinta. Takaici da bakin ciki suka hana shi sakat ya bi su da kallo kawai har suka shige. Gyara zamansa ya yi a falon, daman shi bai ce zai yi wa Nasreen komai ba, yana jiran har sai ta sami lafiyar idanu, ta yadda yana kallon kyawawan idanunta, tana kallonsa. Amma yana da buKatar kwana kusa da matarsa. Zakiyya ta tashi kamar tana magagi wanda a zahiri idanunta biyu, “Muje mu kwanta.� Ya dubeta cike da bakin ciki, “Kwananki ne? Ina zaton sai Nasreen ta yi kwanaki bakwai dinta kafin ma a raba girki? Ki je dakin ki taho min da ita.� Zakiyya ta dube shi shekeKe da alamun har ta mance irin marin da ya yi mata dazu ta ce, “Wallahi ba zan je ba. Ni lokacin nawa ai ba wata ta kirawo ni ba, ni na kai kaina da kaina. Kuma ina zaton ko za ka yi kwanakinka ai sai ka jira Umma ta tafi ko? Ko kuwa a gabanta za ta dinga tsallake Umman tana zuwa wurin miji?� Shikam Sultan kansa ciwo yake yi, amma duk da hakan sai da ya ba Zakiyya amsarta, “Kin ga bambancin Zakiyya da Nasreen ko? Kin kawo kanki wurin miji ba tare da ya neme ki ba, babu aji ko kadan, dole miji ya dinga yi maki kallon wacce bata kai ba, ita kuma saboda kunya ba za ta iya kawo kanta wajen miji ba. Ina gaya maki ki dinga sanin irin maganar da za ki gaya min, idan ba haka ba jikinki ne zai dinga gaya maki, daga Karshe ki bar min gida, domin ba ayi yarinyar da zan auro ta zo har cikin gidana tana gaya min abinda ranta ke so ba, ya zama dole ki koyi ladabin magana.� Ya shige dakinsa yasa dan makulli. Zakiyya ta je ta taso Umma tana gaya mata tana kuka. Nasrcmeen dai tana kwance a gado tana jin su tayi shiru, da farko tana zaton Sultan hasashe yake yi akan abinda Umma take nufi, a yanzu kuma ta fahimci da gaske Umma take yi ta shirya rabata da Sultan. Hawaye kawai ke sauka a idanunta, domin a zahirin gaskiya tana buKatar ko babu abinda zai hadata da Sultan ta kwana a gefensa suna hirarsu da baya gundurarta. Umma ta fito tana kwankwasa Kofar Sultan, kamar ba zai bude ba, jin muryar Umma yasa ya bude fuskarsa babu ko alamun fara’a. Umma ta dubi Zakiyya ta ce, “Maza shiga gun mijinki. Me yasa ka rufe Kofa ka bar matarka?� Kamar ya ce mata wancan ba matarsa ba ce? Sai kuma ya share kawai. Ya bar Kofar a bude ya shige. Zakiyya ta kutsa kai. Da taga ba zai bata hadin kai ba, sai ta koma ta sanya wannan turaren ta dawo. Babu shiri ya amince ya aikata abinda take so ba tare da natsuwar zuciyarsa ba, Warin nan nata yana nan har yanzu babu canji. Ganin ta kwanta tana shirgar barci yasa ya bubbugeta yace sai ta tashi ta je ta yi wanka, sannan zai kwanta gado daya da ita. Bayan ya fito wankan tana kallonsa ya zauna gaban madubi ya matso wannan turarcn ya matso wancan. Sai da ya tabbatar da Kamshinsa ya saje ko ina na jikinsa sannan ya saki ajiyar zuciya. Ya koma ya haye gado, tunanin Nasrcen kawai yake yi. Kwanaki biyar a tsakani Sultan ya shirya yaje aka daura auren Abba, wanda shi ya bayar da sadaki akayi komai. Hajiya Gwaggo ta ji dadin wannan auren don haka ta hada su ta yi � masu fada. Mairo mace ce mai alkunya da kawaici, . haka ansha wahala matuka kafin Mairo ta amince da auren da take ganin tsabar cin amana ne ta auri mijin uwar dakinta. Ita kuwa Umma ta kafe ta tsare, ta hana Sultan Karasowa kusa da matarsa. Shi kuwa iya haKurinsa ya kai Karshe don haka yau ya yi rantsuwa sai ya san yadda zai yi ya shaki Kamshin matarsa. Yana shigowa falon ya same su gaba daya suna kallo ya duba ko ina babu Nasreen, don haka ya mike ya kama hanyar dakinsa. Zakiyya ta shigo ta sami har ya fara barci don haka ta koma suka ci gaba da hirar su. A hankali ya fito babu wanda ya ankare da shi ya shige sashen Nasreen, Tana _tsaye hannunta dauke da turaren wuta da mai aikinta ta kawo mata tana turara dakin. A hankali ya shigo kawai ya tsaya yana kallonta. Ga mamakinsa sai yaga tana murmushi, har ya sha jinin jikinsa ko dai idanunta sun bude ne? “Barka da shigowa Deena. Nayi matukar kewarka ta yadda baki ba zai iya fadin iya adadin kewar ba.� Sultan ya ce, “Oh ya akayi kika san na shigo?� Sai da tasa bakinta ta hura masa hayakin � turaren sannan ta bashi amsa, “Ashe dai ba gaskiya ba ne da ake cewa idan har jini ya hadu wuri guda rabuwarsu abu ne mai matuKar wahala? Ina da tabbacin idan jini ya hadu bin ilahirin jiki yake yi yana kaiwa da komowa alamun ya riga ya hade da dukkan sauran jinin da ke jikinka. Ka ga kuwa mai iya raba wannan jinin sai ya zo da shiri ba na wasa ba. Ko a gida ko a Office ko a kasuwa, ko a cikin hawan idi, ko a filin sukuwa ko kuma a cikin taron jama’a da yawansu ya kai iya adadin buhun gero, inhar jan Gwarzona zai gifta, jinina zai motsa alamun farin cikina yana kusa da ni. Bare kuma a gidana, a gidan nawa ma a cikin tsakiyar falona, a falon nawa ma a kusa da ni. Sannu da zuwa mijina, ba irina mai sonka za ka boyewa kanka ba. Me ka samo mana ne?� Yarinyar kullum sake rikide masa take yi, a hankali ya Karaso ya karbe turaren wutan, ya dauketa cak! Sai cikin dakinta yasa key ya rufe. Tana girgiza masa kai, sai dai bai kai cikinta ba, domin cike take da kewarsa sosai. Suna nan kwance sun lula wata duniyar, suka ji Kwankwasa Kofa. Nasreen ta gigice tana son yin magana, ya sake hade bakin su wuri guda, hakan ya hanata furta komai, sai gabanta da ke faman bugawa da Karfi. A hankali ya yi mata magana “Ki natsu ki kwantar da hankalinki da muijinki kike tare ba kwarto ba. Bansan dalilin da yasa Umma ta zo ta sa mana Katon lullubi ba a tsakanin mu, bayan tuni Allah ya yaye mana wannan Katon hijabin, ya bani dama inyi abinda na gadama da ke domin ke matata ce. Yau a dakin nan zamu kwana ni da ke, na bar sake raba makwanci da ke Nasreen, Ni kadai nasan wahalar da na sha da baki kusa da ni a kwanakin nan biyu. Ki daina tsoro kin ji?� Gumi ne ke tsattsafo mata a kowani irin bugun Kofa da Hafsat take yi. Bata damu ba, ba ta kawo komai a ranta ba, ta juya abinta. Ta dubi Umma tace, “Rufe Kofar ta yi. Kina ganin makiran yarinyar nan? Tun ranar da kika rabata da Yaya kullum kwanan kuka take yi.� Umma ta tabe baki, “Karshen rufe Kofa ta zo ta koremu ne daga gidan. Ita da Sultan sai dai ta hango wata da shi amma Wallahi ba dai ita ba. Sai naga ta inda dangantakan musulunci da rashin addini suka hada hanya.� Zakiyya ta dubi wayar Umma da ke Kara � ta ce, “Umma, Abba ke kiranki.� Umma ta harari wayar cike da bakin ciki. Dallah ja can ki bani � wuri ba zan dauka ba. Ya addabeni da azaban kira kamar tsohon makahon da ya rasa gane hanyar gida.� Zakiyya da Hatsat suka yi dariya suka tafa. Nasreen da ta lume a cikin wata duniya, ta kasa ko da motsa hannunta ne. Shi kansa ya fahimci yadda ya wahalar da ita, tausayinta ya kama shi, da ace bai dau alKawarin ba zai amshi hakkinsa ba, har sai idanunta sun bude yau da ya nunawa su Umma shima namiji ne cikukke mai lafiya. Haka ya tashi kafin ya tafi ya manna mata sumba, sannan yace“I love you Wife.� Ta kasa magana sai motsa labbanta da ta yi ta mayar masa da martani. Ya gane abinda take nufi don haka ya jawo bargo ya rufeta, ya fice tare da jawo mata Kofar. Jin kansa yake yi kamar sabon ango, dukkan Kuncin da yake tare da shi, ya kau, sai murmushi yake saki abinsa. Umma da Zakiyya da Hafsat suka bi shi da kallo cike da mamaki. Hankalin Umma idan ya yi dubu to ya tashi, “Kai da kake barci yaushe ka fito ka shiga dakin Nasreen? Me kaje yi a dakinta?� Tambayar taso ta bashi dariya, sai ya kirne kawai yana murmushi, “Umma don na shiga dakin Nasreen kawai sao a ce min me naje yi? Naje inkai mata waya Nawfal ya addabi Abba sai an bashi Nasreen. Sai na sami dakin a rufe. Da Kyar ta bude Kofar tana magagi wai barci take yi, ni kuma na fito na Kyaleta zuwa anjima sai insake kiransa suyi magana. Ta gabanku na wuce na shiga, abin mamaki babu wanda ya kula da ni. Hira ta yi dadi kenan. Ke Hafsat dauko min fura a frij da Cup.� Yana maganar tare da gyara zama, haka yaki yarda su hada idanu da mahaifiyarsa domin , ya sani tana kallon Kwayar idanunsa ta gama gano shi. Domin idanun a lumshe suke sunyi jazir, ga wani irin kasala da yake fama da ita. Yana nan zaune yana shan furar, Nasrcen ta shigo tana bin bango. Yana son zuwa ya Karaso da ita, idanun Umma yana kafe akansa. Ta laluba ta zauna tana gaida Umma cikin yanayinta na sanyi. Babu wanda ya amsa mata, don haka_ tayi shiru tana wasa da ‘yan yatsunta. Babu wanda ya yi maganar Kamshin Sultan da ke fita* daga jikin Nasreen, amma kuma zuciyarsu a cike suke. Sultan ya mike, ya Karaso gabanta ya kama hannunta ya manna akan kofin furar sannan ya ce, “Gashi ki shanye ragowata.� Nasreen ta yi murmushi ta kafa kofin a baki, shi kuma ya sha mur kawai ya wuce ciki. Umma_ ta yi shiru tana nazarin irin wannan farin cikin da Sultan yake ciki na menene? Zakiyya ta dubi Umma tana son yin kuka, Umma ta harareta, hakan yasa ta dake kawai. Cikin dare kowa yana barci, Sultan yana kwance tsakiyar gadonsa ya kasa tsaida KwakKwarar tunani. Ya Kosa su sami appointment kamar yadda Al-ameen ya gaya masa, su bar Kasar nan. Sauko da Kafafunsa ya yi yana jin zai bi shawarar da zuciyarsa take gaya masa. A hankali ya fice zuwa dakin da Nasreen take kwance kusa da Hafsat. Sai da ya wuce Ummansa a falo tana kwance a nan, da alamun yau a wurin take jin kwana. Nasreen ma idanunta biyu, tana jin motsi ta ji Kamshinsa ta rufe idanunta tana Salati a zuciyarta, ta tabbatar yau zai tona mata asiri. Dauke numfashinta ta yi a lokacin da ya dauketa cak! Tsoro sosai ya _ Shigeta, za ta yi magana yasa bakinsa ya hanata maganar. Sai da ya tabbatar da ta yi _ laushi sosal, sannan ya fice da ita. Yana kusa da � mahaifiyarsa ya ji motsinta, hakan yasa ya dakata har sai da ya tabbatar da ba tashin za ta yi ‘ba, sannan ya wuce abinsa. A tsakiyar gadonsa ya shimfideta ya dora kansa a bisa kafadarta, “Nasreen..� Ya kira sunanta cikin wata murya wacce bata san yana Boye da irinta ba. Ta kasa amsawa sai ma sake tattaro natsuwarta da ta yi akansa. Hannunta ya kama ya tura a cikin gashin gansa kafin ya fara magana, “Nasreen, ina shan wahala a sakamakon rashin ki kusa. A baya nasha wuya, a zatona Karshen wahalar ta zo? Ashe yanzu aka fara? Ki gaya min ta inda zan iya ci gaba da zuba idanu, ganinki ma yana neman ya gagareni. Sai inje wurin aiki ban saki a idanuna ba, idan na dawo zan ga kowa zaune a falo amma banda ke Nasreen. Don Allah ki dinga daurewa kina yakice dukkan wata kunya kina fitowa nima in ganki kin ? Gobe ki shirya zan gayawa Umma zan kai ki asibiti a duba idanunki za ki ga likita kin ji? Yi min alKawarin za ki biyo ni.� Tana jin sonsa kamar ta faso Kirjinta ta ciro Son ta nuna � masa don ya fi gazgata ta. Ta rasa ta yadda zata iya yi masa bayanin irin abinda take ji a cikin zuciyarta a sanadiyyarsa. , A hankali ta yi magana, wanda da ba don yadda ya tattaro natsuwarsa akanta ba, da babu abinda zai ji, “Na amince Deena, duk abinda ka yi dai-dai ne, ina jin tsoron Umma ne shi ya sa, kuma ta ce min in daina zama a falo. Ban san me na yi wa Umma ba bata sona Dee, ban san me zan yi wa Umma in burge ta ba, ban san mene ne musababbabin wannan tsanar ba, don Allah ka sanar min dalilin ka gaya min idan laifi na yi mata zan ba ta hakuri.� Ta fara fitar da hawaye, ya sa hannunsa ya dauke hawayen yana sake duban ta, “Ba ki yi wa Umma komai ba, ban san mene ne dalilin da ya sa Umma take gwada maki irin wannan tsanar ba, kamar ba jininta ba.� Nasreen ta girgiza kanta, “Ka daina zolaya ta da irin wadannan maganganun Deee, tuni na yi hankalin bambance fari da baki, na sani, da ni da Nawfal ba jininku ba ne, ba mu da wata alaka da ku, na sani akwai wani boyayyen labari mai matukar muni a tsakanin mu da gidan ku, ban sani ba, ko tsinto mu aka yi. Sai dai idan na tuna kalaman Abba da yake cewa tun muna ciki kake dawainiya da mu, haka kai ma kana yawan gaya min tun muna ciki kake son mu, sai indimauce, inrude ina neman wanda zai buda min wannan sarkakKiyar da ke faruwa. Don Allah ku sanar da ni abubuwan nan domin infahimta. Su waye lyayena? ‘““Wacce Kaddara ce haka a jikinmu da har Umma take tsananin Kyamatar mu? Da gaske mu din haihuwar Karkashin mota ce? Ko kuwa wata Hausar ce daban? Ka gaya min wacece ni? Kai kadai za ka iya bude min komai kai tsaye. Ban taba tunanin tambayarka ba ne, saboda ina tsoron jin irin amsar da za ka ba ni, ko kuma irin yadda za ka daukenwac 6/10/22, 09:54 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 5 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA A hankali ta yi magana, wanda da ba don yadda ya tattaro natsuwarsa akanta ba, da babu abinda zai ji, “Na amince Deena, duk abinda ka yi dai-dai ne, ina jin tsoron Umma ne shi ya sa, kuma ta ce min in daina zama a falo. Ban san me na yi wa Umma ba bata sona Dee, ban san me zan yi wa Umma in burge ta ba, ban san mene ne musababbabin wannan tsanar ba, don Allah ka sanar min dalilin ka gaya min idan laifi na yi mata zan ba ta hakuri.� Ta fara fitar da hawaye, ya sa hannunsa ya dauke hawayen yana sake duban ta, “Ba ki yi wa Umma komai ba, ban san mene ne dalilin da ya sa Umma take gwada maki irin wannan tsanar ba, kamar ba jininta ba.� Nasreen ta girgiza kanta, “Ka daina zolaya ta da irin wadannan maganganun Deee, tuni na yi hankalin bambance fari da baki, na sani, da ni da Nawfal ba jininku ba ne, ba mu da wata alaka da ku, na sani akwai wani boyayyen labari mai matukar muni a tsakanin mu da gidan ku, ban sani ba, ko tsinto mu aka yi. Sai dai idan na tuna kalaman Abba da yake cewa tun muna ciki kake dawainiya da mu, haka kai ma kana yawan gaya min tun muna ciki kake son mu, sai indimauce, inrude ina neman wanda zai buda min wannan sarkakKiyar da ke faruwa. Don Allah ku sanar da ni abubuwan nan domin infahimta. Su waye lyayena? ‘““Wacce Kaddara ce haka a jikinmu da har Umma take tsananin Kyamatar mu? Da gaske mu din haihuwar Karkashin mota ce? Ko kuwa wata Hausar ce daban? Ka gaya min wacece ni? Kai kadai za ka iya bude min komai kai tsaye. Ban taba tunanin tambayarka ba ne, saboda ina tsoron jin irin amsar da za ka ba ni, ko kuma irin yadda za ka daukeni a matsayin butulu wacce ta ZAMU TASHI kasa godewa Allah da irin baiwar da ya bani, wajen suturtani a cikin gidanku, ya yi min baiwar ilimin addini da na boko.� Sultan idan hankalinsa ya yi dubu to ya tashi, ya jima yana tsoron zuwar wannan ranar domin ba shi da cikakken amsar da zai iya ba ta, haka har yanzu ba ta yi girman da za ta iya daukar tashin hankali irin wannan ba, ya so ne sai komai ya natsa sannan ya dauke ta zuwa gun dangin mahaifiyarta. Haka yana tsoron ya gaya� mata ta tada hankalinta wajen neman ubanta, wanda a yanzu bai san wanene wannan uban ba.: Sai da ya tattaro dukkan natsuwarsa sannan ya ja dogon hancinta, wanda kullum ya hadu da ita sai ya taba, “Nasreen na san idan na rantse maki za ki yarda da ni ko? Wallahi ba a KarKashin mota aka haife ku ba, ina kika taba jin an haihu a KarKashin mota? Kuma kina da uwa kina da uba kina da dangi kamar kowa. Ina jiran mutane su gama abubuwan su ni kuma a lokacin ne zan ba kowa kunya, zan dauko mahaifinki ki gan shi har ku zauna kusha hirarku. Don Allah kada ki sake yi min irin maganar nan kin ji?� Babu musu ta daga kanta, “Na ji, don Allah ka yafe min don Allah. Insha Allahu, ba zan sake yin maganar ba. Sai da yasa hannunsa ya warware gashinta. da ta tubke sannan ya ce, “Ba ki yi min komai ba, haka yin maganar da kika yi, ba zaisa ince maki butulu ba, har abada kin gama min komai da kika zauna a matsayin matata. Ki Kara haquri watarana sai labari.� Ba ta yi magana ba, domin sakon da yake tura mata suna cin nasarar isowa inda ake bukatar su iso. Sun yi nisa a wata. duniya suka ji bugun Kofa hakan yasa ta. Kankame shi. Ya zame kansa ya mike zai je ya bude, ta kame shi ta mayar da shi Kirjinta da yake sake gigita shi, ta yi magana a hankali, “Za ka bude kofa a yanayin da nake ciki?� Sai yanzu ya dawo da dubansa jikinta, ta dan haskem fitilar ya fahimci abinda take sufi, don haka ya mayar mata da kayanta a natse kamar ba shi bane ake buga masa kofa da Karfin tsiya. Ya maidata ya kwantar ya jawo mata bargo, sannan ya kashe wutar dakin gaba daya ya dawo duhu. Yana budewa Zakiyya tana kokarin cusa kanta a cikin dakin. Ya kalleta tare da yamutsa fuska yana * kallon su Umma da Hafsat da duk suka yi cirkocirko, “Umma lafiya kuwa? Me ke faruwa ne?� Umma ta tabe baki, “Yau sai Nasreen ta bar gidan nan. Ashe yawon dare yarinyar nan take fita?� Sultan ya bata fuska, “Haba Umma ki dinga kyautata zato a gun dan’adam. Me ya faru kuma?� Umma ta ce, “Idan Nasreen ba tana tare da kai bane, to babu ita a cikin gidan nan.� Sultan ya zaro idanu kamar gaske, ya kuma nuna tashin hankalinsa a fili, hakan ya sa dukkansu da suke zargin Nasreen tana tare da shi * suka kauda tunanin, “Nasreen ta fita a gidan nan? Kuma anduba ko ina? Kai babu yadda za a° yi ta iya fita bayan ga “yan sanda. Mu je gurin su din.� A Kaggauce suka fice, Umma tana jin dadi a ranta ta riga tasan Karshen zaman Nasreen ne yazo a gidan, domin ita zarginta ya koma ko tana tare da daya daga cikin ‘yan sandan ne?� Suna ficewa Nasreen ta laluba ta nufi Kitchen, ta laluba ta tara ruwan zafi a famfo ta tsaya shiru gabanta yana fadiwa da Karfi. Tunani ne fal a cikin cikinta, haka kalaman Umma da ta ji suna ta yi mata yawo a tsakiyar kai, tana mamakin yadda Umma za ta dinga cewa tana bin maza, tana dangantata da Zina, wannan abun yana matuKar yi mata ciwo. . Sultan ya tsaya a gaban daya daga cikin ‘yan sandan wanda idanunsa biyu ya ce, “Kun ga Nasrcen ta fitonan?� Ya girgiza kai ya ce, “Oga sir, ina nan zaune ban tashi ko‘ina ba, babu wacce ta fito nan. Kawai Sultan ya juya yana cewa, “Anya Nasrcen ta bar gidan nan a tsohon daren nan? Babu mutumin da zai iya fita a gidan nan ba tare da izinina ba, bare kuma ficewar dare, ai da na sallame su domin sun zama marasa amfani. Mu koma ciki a sake duba bandaki ko wani wurin.� Hafsat ta yi carab ta ce, “Har bandakin na duba babu ita.� Banga komai ba, suka dawo falo yana . magana da Karfi, “Yanzu ina Nasrccn taje? Lallai idan ya tabbata ta fitan, zan kuwa bata mata rai. Ko da kuwa nan da Gate ta je. Yarinyar da bata iya dogon tafiya ita kadai shi ne za ta fice?� Nasrcen ta saki ajiyar zuciya, sannan ta dan kwarawa Kafarta ruwan zafin da ta dibo, duk da babu zafin kirki sai ta fasa Kara, hakan yasa Sultan yayi hanyar kitchen da sauri har ya riga su shiga. Yana zuwa ya riketa sosai a jikinsa, kasancewar akwai Kamshin turarensa a jikin Nasreen Umma tana iya ganewa suna tare shi ya sa ya yanke hakan. Gabadaya aka shigo ana leken Kafafun da take ta wash! Wash!! Sultanya dubi� Hafsat ya ce, “Ke kawo min gishiri. Haba Nasreen na fara gajiya da : lamarinki, kina’sane da ba gani kike yi ba, amma � sai ki dinga zuwa inda za ki ji ciwo don ki bar ni . da wahala ko? Me ya sa:ba za ki tashi Hafsat ta kawo maki ruwan zafin ba?� Hafsat ta murguda baki tace “Kuma � Yaya idonta biyu*lokacin, ashe ta sadada ta fita.� Sultan ya dago yana dubanta cikin takaici, “Cewa na yi ki:samo.min gishiri.�* Nasren ta fara fitar da hawayen bakin cikin yadda Umma bata taba kamata da wani ba, amma take dangantata da zina. Bayan ta sani shaidar zina a musulunci abu ne mai matuKar wahala. . . Umma da Zakiyya suka dub juna cike da farin ciki yau Sultan ya taba ‘yar Gold. Da kansa ya shafamata gishirin kadan don yana sane da ba konewa ta yi ba. Yana dago ta ya ce. “I love you wife.� A hankali ya yi maganar babu wanda ya ji sa ita da aka fada dominta. Sakon ya ratsa ta har ta saki murmushi cikin hawayen ta motsa labbanta. A wurin duk suka aika wa juna sako wanda a zahiri babu wanda ya gani haka babu wanda ya fahimta, duk wayewar da Umma take kirawowa kanta. � A falo ya ajiye ta ya dubi Hafsat ya ce, � “Ke, hado mata tea.� Babu musu ta wuce ta hado tea, ya mika mata tana sha. Bayan ta sha fiye da � rabi ne ta ajiye a nan. Umma ta tabe baki, “In banda iyayi wai * tashin shan tea a daddare, da a can gidan matsafan waye yake kawo maki tea cikin dare? Ke ni bari in gaya maki ba na son tashin dare, ki daina bana so. Wannan iskancin ba zan taba daukarsa ba.� Sultan ya kafe mahaifiyarsa da idanu yana jin dacin abubuwan da take fada akanta, sai dai ba shi da daman hanawa, da yan. dama da bai bari har abin ya yi nisa haka ba. Ya dube ta yadda ta yi shiru ya ce, “Gobe zan kai ki asibiti a sake duba idanun nan, kafin tafiyarki London ya tabbata. Sai ki shirya da wuri in kai ki in dawo in mayar da ke gida.� Umma ta dubi Zakiyya sai kuma ta ce, “A‘a bai kamata ka je kai ta asibits ita kadai ba, kamar babu mutine a gidan. Ke Zakiyya da Hafsat ku shirya goben ku raka su.� Dukkansu suka amsa, shi kuwa kallon mahaifiyarsa kawai yake ransa a Bace. yanzu ba shi da halin fita da matarsa har sai an hada shi da ‘yan rakiya? Shi kenan tsakaninsa da matarsa an sa Hijabi kenan? Rintse idanunsa ya yi yace. “Hafsat, kama hannunta ku koma ciki� ~ Umma ta ce, “A kama hannun wa? ~ Yarinyar da ta iya zuwa kitchen, ta iya shigowa nan, ita ce yau saboda gulma za a kama ~~ hannunta? Ban yarda ba, ban amince ba_ Ta tashi ta lalubi bango ta koma inda ta fito. Ke hafsat wuce ki bar ta.� Nasreen ta yi saurin miKewa tana dan rintse idanu, “Deedi ka bari zan iya tafiya da kaina ba sai an kai ni ba. Mu tashi lafiya�™ ta yi gaba abinta. Da idanu ya rakata yana jin tausafiitta, ana cin zarafinta a wurin da aka fi Karfinsa;Saboda bakin ciki a nan falon ya kwanta, musamman da yaga Zakiyya ta ki tafiya don haka yake zargin idan ta bi‘shi za ta gane Nasreen ta shiga dakin don haka yaki amince mata ya kwanta a nan falon. Sai da asuba ya koma ciki, a nan ya ga ribom dinta haka gadon gaba daya a yamutse yake. Murmushi ya Kwace masa, ya shinshini ribom din ya tura shi cikin kayansa sannan ya yi alwala ya wuce . Da safe ya gama shirinsa tsaf! Ya fito zuwa dakin Zakiyya, abin mamaki ba ta nan, don haka ya wuce dakin Nasreen. A nan ya sameta ita da Hafsat sun caba kwalliya kamar wadanda za su je gun biki. Gaishe shi suke yi, ya kasa amsawa saboda mamaki, “Ina za ku je haka kuka yi wannan kwalliyar?� Gaba daya jikin su ya dan yi sanyi, don haka suka hau kame-kame. “Asibiti da Umma ta ce za mu raka ku.� Mamakin fuskarsa ta Karu. Ya waiwaya yana duban Nasreen, tana zaune daga ita sai doguwar riga, hannunta rike da dan Karamin carbi tana ja. Ya sake waiwayawa yana duban . Umma da ke zaune tana karyawa hankalinta kwance. Ya ce, “Amma dai kuna da Karfin hali, ita wacce za a kai ta asibitin ba ta shirya ba, sai ku ne iyayen iyayi ko? To babu inda zaku je.Tunda baku da lissafi.� Umma ta karkace bayan ta danna dankalin turawa a baki ta kurbi ruwan tea sannan ta ce, “Babu abinda zai hana su, zuwa Asibitin nan. Karyar banza kake yi Wallahi. Ai ba sai ka zo gabana kana kushe su ba, na sani sarai ban isa da kai ba, amma ina tabbatar maka duk abinda ka shuka a gidan duniya sai ka girbe shi.� Sultan ya shafi kansa, “Umma ki yi wa Allah kada ki yi min baki akan yaran nan. Ni abin ne ya bani mamaki, ta yadda daga zuwa Asibiti sai ayi kwalliya, sai ka ce wanda na gaya masu za mu je gidan biki. Ke me ya hanaki . shiryawa?�� Kafin ta yi magana Umma ta yi carab, “Gulma mana! Wai ita mai addini ta tsaya tana jan carbi kamar sabuwar tuba. Ko da yake menene ma..� Sultan ya yi saurin taran numfashinta, “Umma ki barta a haka za ta tafi kin san ita bata kwalliya.� � Umma ta tabe baki, “To ina makauniya ina kwalliya? Ai ko ta yi sai dai ta bata fuskarta, tunda ba kallon madubi za ta yi ba.� Sultan yana kallon yadda fuskar Nasreen ta sauya, bai ce komai ba, ya dubeta, “Nasreen tashi ki dauko Hijabinki.� Babu musu ta tashi ta nufi dakinta. Tana shiga ya bi bayanta. Umma ta saki baki tana kallonsa. Abinda ya yi zato shi ya tarar, tana share hawayenta wasu suna sake zuba. Jawo ta ya yi jikinsa hakan yasa ta fashe da kuka. “Bana son kuka Nasreen, idan kina kukan nan sai in ga kamar baki dauki Umma a matsayin uwa a gareki ba. Ya kamata a ce kin saba da dukkan irin wannan halayyar na Umma.� Nasreen ta ce a zuciyarta, shi cin mutunci ba a sabo da shi, domin kullum danye yake sake komawa, a maimakon a barshi ya bushe har ganyen ya kakkabe. A zahiri kuma sai ta shiga goge hawayenta yana taya ta. Ya dauko hijabin ya sanya mata, sannan ya dube ta ya ce, “Baki ga yadda hijabin ya yi maki kyau ba.� Ya sumbaci goshinta sannan ya kamo hannunta suka fito. Suna kawowa falon ya saki hannun ya Karasa gun Umma ya ce, “Za mu tafi sai mun dawo.� Ta amsa da a dawo lafiya. A hanya babu wanda ya cewa wani zo ka ci kanka, kowannen su da irin tunaninsa. Shi Sultan tuni ya gama kissima dukkan abubuwan da zai yi. Suna isa Asibitin ya ajiye su a Receiption Ya jawo hannun Nasreen ya ce su zauna anan, su za su je su ga Dokto. Ya zagaya ta baya, ya shiga mota Nasreen ma ta shiga, duk basu sani ba, dan sanda ya ja mota suka fice. Kai tsaye babban Hotel ya wuce da ita, ya kama daki ya shige abinsa. Nasreen dai binsa take yi bata san inda suka shiga ba, har sai da ta ji sanyin A.C. bayan ta zauna a bisa shimfidadden gadon, “Dee ina ne nan kuma? Wurin wa muka je? Dee ina tsoro kada su Hafsat su ankare bamu nan. Don Allah mu koma.� Sultan ya rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita tare da cire mata Hijabin, gashinta da yake ta walKiya suka zubo kafadunta. Ya _ tura hannunsa yana yi mata susa, “Nasreen ina shan wahalar rashinki a kusa da ni, Umma kuma ta kafe ta tsare. Bansan ya suke son in yi da rayuwata bane. Yanzu kin ga Hotel muka zo zan samu in yi barcin da na rasa zuwa anjima sai mu je mu dauke su. Karki damu idan suka sha wahala gobe ba za su sake cewa za su biyo mu ba. Ita Zakiyyan duk irin dadewar da muka yi tare, ai ya kamata ta daga min Kafa tunda babu laifi na sauke dukkan hak KoKinta.� Nan take fuskar Nasreen ta sauya, da gaske take jin kishinsa akan Zakiyya, ta fi son abinda bata sani ba, akan alaKarsu ta boye sirrin su, idan ya bari tana jin irin wannan kalaman za ta iya shiga wani hali na kishin da halitta ce a jikin mace, sai dai kowa da irin yanayin danne kishinsa. Sultan ya Kura mata ido yana murmushi, bai taba sanin tana da kishi ba sai yau, dama kuma abinda yake son ya gani kenan. “Kishi kike yi ne?� Ya tambaye ta cikin zolaya. Sake Bata fuska ta yi ta ce. “Dee ni tsoro nake ji me zai kawo mu Hotel? Bai kamata ba, ga gidanmu na sunna sai mun je wani Hotel? Dee gaski…� Ba ta samu daman Karashe abinda take son Karasawa ba, ta hadu da zazzafar soyayyar Sultan da take kashe ta a kowani irin lokaci. Dole ta sakar masa jikinta, ba don ta so ba, sai dan salon soyayyarsa daban yake. Sun jima a wata duniyar da bata san wacce ce ba, daga bisani ya Kyale ta dan kansa, domin bai mance 6/10/22, 10:06 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 6 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Sultan ya rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita tare da cire mata Hijabin, gashinta da yake ta walKiya suka zubo kafadunta. Ya _ tura hannunsa yana yi mata susa, “Nasreen ina shan wahalar rashinki a kusa da ni, Umma kuma ta kafe ta tsare. Bansan ya suke son in yi da rayuwata bane. Yanzu kin ga Hotel muka zo zan samu in yi barcin da na rasa zuwa anjima sai mu je mu dauke su. Karki damu idan suka sha wahala gobe ba za su sake cewa za su biyo mu ba. Ita Zakiyyan duk irin dadewar da muka yi tare, ai ya kamata ta daga min Kafa tunda babu laifi na sauke dukkan hak KoKinta.� Nan take fuskar Nasreen ta sauya, da gaske take jin kishinsa akan Zakiyya, ta fi son abinda bata sani ba, akan alaKarsu ta boye sirrin su, idan ya bari tana jin irin wannan kalaman za ta iya shiga wani hali na kishin da halitta ce a jikin mace, sai dai kowa da irin yanayin danne kishinsa. Sultan ya Kura mata ido yana murmushi, bai taba sanin tana da kishi ba sai yau, dama kuma abinda yake son ya gani kenan. “Kishi kike yi ne?� Ya tambaye ta cikin zolaya. Sake Bata fuska ta yi ta ce. “Dee ni tsoro nake ji me zai kawo mu Hotel? Bai kamata ba, ga gidanmu na sunna sai mun je wani Hotel? Dee gaski…� Ba ta samu daman Karashe abinda take son Karasawa ba, ta hadu da zazzafar soyayyar Sultan da take kashe ta a kowani irin lokaci. Dole ta sakar masa jikinta, ba don ta so ba, sai dan salon soyayyarsa daban yake. Sun jima a wata duniyar da bata san wacce ce ba, daga bisani ya Kyale ta dan kansa, domin bai mance ZAMU TASHI alKawarin da ya yi ba. Nasreen tana gigita shi ta yadda yake jin kansa kamar sabon Sarki. Yana sonta ya shirya fuskantar kowani irin Kalubale ne akanta. Tana kwance a gefensa barci ya kwasheta, shima a nan ya sami natsuwa har barcin ya kwashe shi, cikin kyakkyawan mafarki mai cike da natsuwa. Zai iya rantsewa bai taba samun irin wannan barci ba kamar yau. A Kalla sun kwashi awa biyar suna barcin sannan Nasreen ta fara farkawa, ta lalubo shi tana bugunsa a hankali. “Dee ka tashi mu tafi bansan Karfe nawa ne . yanzu ba.� Sultan ya sake jawota jiki ya rufe su da bargo ya ce, “Yanzu Karfe goma sha daya na safe, sai Karfe daya zamu koma.� Bata da yadda za ta yi dole ta koma ta kwantar da kai. Irin abubuwan da yake yi mata ne, yasa ta riKe hannunsa tana girgiza masa kai kamar za ta yi kuka. Yana son salon shagwabar yarinyar. Karfe daya ya fada bandaki ya watsa ruwa, ya taimaka mata itama ta yi wankan, duk da bata iya yi a gabansa ba har sai da ya fice saboda kunya. Alwala suka yi, sannan ya ja su Sallah suka gabatar da Sallar azahar, sannan ya rike hannunta suna jerowa. Duk wanda ya zo wuce Wa Sai ya sake waiwayowa ya dube su, sun yi matuKar kyau, haka sun dace da juna. Suka fito suka koma Asibitin, ta inda suka bi ta nan suka sake biyo wa suka dawo inda suka bar su Hafsat. Gaba daya kwalliyar nan da suka sha, ta watse, fuska sai maiko take yi saboda wahala. Sun gaji da zama, har sun siya maltina sun sha, amma duk da hakan sai mita suke yi. Suna ganin sun iso, kowacce ta ja bakinta ta yi shiru. Yadda Zakiyya ta kafe su da ido yasa Sultan daure fuska sosai, ya kuma kamo hannun Nasreen ya ce, “Mu je cikin mota.� � Babu musu ta biyo shi, sauran ma suka mara masu baya. A mota kowacce tambaya ce cike da cikinta, amma babu fuskar aiwatar da hakan. � , Bayan sun iso gida ne, Umma ta ce, “Ya na ganku duk kun sha wahala?� Hafsa ta hada rai ba tare da ta ce komai ba, sai Zakiyya ce ta ce, “Umma tunda suka shiga cikin asibitin babu wanda ya sake sanya su a idanunsa. Muna zaune duk mun sha wahala mun lalace.� Umman ta dubi Sultan, wanda tuni ya kama hanyar barin falon. Umma bata iya cewa komai ba, har ya bacewa ganinta. Juyo wa ta yi gun Nasreen tana harararta, wai aikin banza a harara a duhu, domin kuwa Nasreen bata san ma tana yi ba. Ta antayo mata tambayar da ya gigita ta, “Ke Nasreen ki gaya min gaskiya tun kafin in yi Kasa-Kasa dake wani lungun kuka shige a asibitin? Ina ya kai ki?� Nasreen ta dan diririce, hakan yasa Umman ta sake hasko wani abin, ta gyara zama, “Ina takardun da Doctor ya baki? Me ya ce akan idanun?� Nasreen ta rude ta kasa magana, sai muryar Sultan suka ji yana magana, “Doctor ya ce mu dawo gobe za su sake gwada idanun, daga nan kuma sai su bamu result Umma ta Harare shi, a lokaci guda Nasreen ta saki KaKarfar ajiyar zuciya. Bata kallon Umma, amma jikinta yana bata tana shan uwar harara. Umma ta zame mata kishiya, ta hanata sakat! Ta Ki amincewa ta barta da mijinta, ta amince ta kashe nata auren ta zo ta zauna tana zaman kashe auren danta. Da za ta iya da ta baiwa Umma shawarar auren Sultan Kila ta sami natsuwar irin wannan dakon da take yi Ita kuma Zakiyya da ta zama bita zai-zai da za ta iya da ta bata shawarar ta koma ta nemi dukkan abubuwan da za ta gyara kanta, domin dawo da martabarta agun miji, a maimakon zaman sa ido da take yi masu, da kuma kasa Kyale su su zauna su biyu. Sai dai duk wayonta, duk irin gadin da take yi wa mijinta, duk irin matakan tsaron da take sakawa, hakan bai hana mijinta nuna mata cewar shi namiji ne mai cikakken wayo da dabara ba. Ya nuna mata har yanzu mata basu yi wayon da za su iya gwada wayon su da na mijin su ba. Ya nuna mata ita Karamar ‘yar sa ido ce, sai dai idan bai yi ninyar aikata abu ba, amma da gudu zai aikata ba tare da wata ta taka masa burki ba. Suna ta gadinta, shi kuma yana daukarta a duk lokacin da ya so ya maidota lokacin da yake so. Da za su gane da sun daina wahalar da kansu wajen sanya masu idanu a cikin rayuwar amarcinta. Umma ta dube shi rai a Bace, “Wai shin kai na tambaya ne? Kana bani mamaki idan kana da gaskiya menene naka na tsoma min baki? Ka barta mana ta yi magana da bakinta, ai makauniya ce kawai ba kurma ba. Kar ko ka dauki mataki akanta tana son raina ni ina magana ta yi banza da ni? Jiya-jiya na gaya maka matar nan taka yawon banza take fita, amma ka yi min kunnen uwar shcgu, kai a dole baka son laifinta ko? Wallahi ba baki nake yi maka ba, jiki magayi, lokacin da za ta nuna maka asalin kalarta, nawa idanu.� Nasrcen ta dafe Kirjinta tana cewa a zuciyarta, “Insha Allahu, babu ranar da Dee zai yi danasanin aurena, babu ranar da zai kamani da ha’intarsa. Allah ka raba ni da hada aurena da zina, idan nayi hakan me zan gayawa Mahallicina? Da wasu idanun zan dubi mijina in ce ya yafe min?� Tuni hawaye suka tsinke mata, idan da abinda ta tsana bai wuce a hada ta da sharrin zina ba, da a ce Zakiyya ta yi wannan maganar, da har tashin dare sai ta yi ta roki Allah ya saka mata wannan Kazafin, ta tabbata Allah ba zai jinkirta amsar addu’arta ba. Sai dai wacce ta yi wannan addu’ar ta fi Karfinta, hasalima a matsayin uwa take kallonta. Sultan ya shafi kansa yana satan kallon Nasreen tana kuka, duk sai ya ji babu dadi, ya tsani a taba masa Nasreen, baya son ganin hawayenta tun tana Karama bare kuma yanzu da ta girma. “Ki yi hakuri.� Ya fada yana duban Umma, wanda a zahiri da Nasrcen yake yi, yaci gaba da cewa, “Bana son in zama ni ne sanadin zubar da hawayenki, ki dinga yi min addu’a ne watarana sai labari.� Nasreen da maganganunsa suka shigeta, ta ji wani irin sanyi yana shigarta, tabbas saKon da ya aika mata sun iso har cikin kunnuwanta zuwa zuciyarta, da ke narkewa da wani abu mai sanyi, sabanin dazu da yake tafarfasa saboda bacin rai. Umma kuwa sai ta sakankance da ita yake yi, don haka ta ji sanyi a ranta. Sultan ya juya kawai yana cewa, “Allah na gode maka. Nayi amfani da kalamai masu Karanci, na wanzar da farin ciki a zuciyoyi biyu masu matuKar_. mahimmanci a zuciyata. Allah ya saka maki Umma, ke kika kawo ni duniya kika rene ni, har na girma na ga mahaifiyar Nasreen na zama silar taimakonta. Da baki haifeni ba, Umma da ban zama abinda na zama ba. Allah ya saka maki mahaifiyata, Allah ya haskaka maki duk wani abu da kike ganinsa a cikin duhu. Har abada ke nake fara yi wa addu’a kafin kowa ya biyo baya.� Kai tsaye Office ya nufa, yana jin nishadi idan ya tuna kasancewarsa da Nasreen dinsa. Yana tashi daga office kai tsaye ya nufi gidan � Yumnah ya sameta da mijinta a falo suna shan hirar su. Ya shigo suka zauna yana cin abinci suna dan taba hira. Yumnah ta mike za ta basu wuri domin taga sun dauko maganar case din su. Sultan ya dube ta ya ce, “Kanwata zo mana, wurinki na zo.� Yumnah ta dawo da baya ta zauna tana dubansa. Ya tashi zaune ya ce, “Don Allah wannan Kamshin da na ji a wurin Nasreen, da yadda fatarta ta yi kyau gashinta ya sake wani tsawo da sheki, a ina kika samo wadannan abubuwan ne? Da gaske nake yi, da kaina zan je innemo mata kayayyakin nan. Ni kadai nasan irin farin cikin da nake tsintar kaina da zarar na shaki Kamshin nan.� Yumnah ta yi dariya, haka ma Dr Astlaf, kuma gaba daya suka zuba mata idanu domin da gaske suke yi, suna jin dadin Kamshin nan. Yumnah ta dauki wayarta ta ce, sanya lambar nan tukun, 08068906212. Babu musu ya kwafe lambar yana sake dubanta domin neman Karin bayani. Ai kuwa ta dan gyara zama, “Sunansa Jafar, yana kasuwan sabon gari a birnin Zaria, haka duk inda kake a fadin duniyar nan yana aiko da kaya. Shago ne da ya amsa sunansa, kaf Zaria suna alfahari da shi. Kana zuwa Sabon Gari wajen kasuwar mata, ma kawai ka ce shagon Jafar kake nema, za a kai ka har can. Duk kalolin sabulai humura dilka da komai da komai da ya Kunshi Kamshi yana saidawa, haka yana siyar da kaya Original baya kawo kaya marasa kyau. Idan kana neman ko misk ne, indai mai kyau ne, to ka garzaya shagonsa.� Ta dan muskuta ta gyara zamanta sosai, don ta ji dadin yi masa bayani. Ta ce “Kuma babu abinda zai baka mamaki sai idan na gaya maka da dubu dayanka ma idan kaje shagon Jafar za ka sami abubuwa masu inganci.Yadda kasan domin talakawa aka bude shi, Idan a wani shago ana siyar da abu dari uku a wurinsa za ka samu a dari biyu da hamsin. Ban taba ganin wanda ya siya abu a gunsa ya dawo yana danasani ba. Kayan gyaran gashi kuwa, abin ba’a magana, ka dai ga yadda kan Nasreen ya yi kyau da cika da tsawo, wannan duk aikin shagon nan ne dai da nake gaya maka na Jafar. Za ka gane abinda nake gaya maka ne, idan ka je shagon ka gan shi cike da matan Shuwa, sai abin ya baka tsoro. Hausawan mu ma ba a bar su a baya ba, duk sun gane sirrin. Doktona ka matsa min kana son sanin sirrin Kamshina, yau dai ga Yayana ya sanya na fada ban shirya ba, kuma abinda ya sa na gaya masa, don dai Nasreen din mu bata gani ne, haka bata san gari ba.� . Ta Karasa tana zura idanunta a cikin na mijinta, a lokaci guda ta kashe masa idanu tana jifansa da shu’umin murmushi. Shi kuwa Sultan ji yake idan ma miliyan ne zai kashe a shagon Jafar. Zai je da kansa ba aike ba, ya sake siyawa Nasreen, duk da ta gaya masa Kamshin ya zauna sosai a jikinta, hakan ba zai hana sake siya mata ba. Babu namijin da a ~ duniya zai ce baya son Kamshi sai dai idan bai samu ba. , Aslaf ya dubi matarsa cikin kulawa ya ce, “Na gode maki da wannan bayanin, nima yanzu zan tura wa amaryar da zan Karo lambar Jafar din,ta je ta nemi Kamshin nan, domin kuwa abinda ya hanani Kara aure kenan, tunanin yadda zan iya hada shimfida da wata, bayan bata kasance mai irin Kamshinki ba, ko bata iya girki ba. Babu matsala zan ci da hakuri, amma rashin Kamshin nan matsala ce, saboda tana cire soyayya a Zuciyar miji.� Yumnah ta kafe shi da idanu har ya dire maganar sannan ta yi murmushi, “Oho sai-ta Zo. Akwai inda har abada bata isa ta kamo ni ba, in dai ni ce babu duka babu zagi, babu habaici, da Kafafunta za ta fice ta bar min gidana, domin sunanta wacce ta zo kallon baKin ciki.� Sultan ya shafi kansa yana murmushi, “Mata! Kun shiga uku da kishi. Kun ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, anya da gaske ne? Idan gaskiya ce, ai murna za ki yi da zuwanta, sannan ki gaya mata dukkan sirrikan rije miji.� Yumnah ta dalalo idanu ta dafe Kirji, “Wa? Ni? Allah ya tsareni Yaya Sultan. Ai lokacin da zan gaya mata sirrina na shiga uku na lalace, a lokacin ni kuma za ta yi ta Kokarin ganin ta watso ni waje, da ni da ‘ya’yana. Mutanen yanzu ne sam babu Allah a zuciyarsu, za ka ga kai ka rike mutum da zuciyarsa guda, shi kuma yana can yana haKa maka Katon rami. Wallahi idan na ga mutum a rana ba zan sake ingiza shi ba, amma kuma zan ratsa in wuce shi. Kai dai Allah shi kyauta, Allah kuma ya tsare Nasreen da wannan Zakiyyar don naga babu Allah a ranta.� Kamar ta fama wa Sultan inda yake masa KaiKayi ya yi murmushi wanda iyakarsa fuska ya shafi sajensa yana sake duban yadda Aslaf ya ~ kafe Yumnah da idanu kamar mai son fahimtar wani abu. “Ni zan koma gida, tunda na sami abinda nake so. Haka kuma Umma tana gida takan so in zo mu zauna muna ‘yar hira.� Aslaf ya mike yana cewa, “Yumnah babu abinda zai sa in Karo maki kishiya, saboda matan yanzu ba a Kwankwasa su bare ka gane ta gari. Kada in zo in auro wacce za ta raba ni da ke, ta raba ni da ‘ya’yana. Kin ga kuwa mutuwa zan yi, tunda ku ne rayuwata.� . Sultan ya jinjina kai ya ce, “Kai dai kawai ayi addu’a. Da Umma za ta bar ni sai na dauke Nasreen daga gidana, in sauya mata wani gidan. Idan basu ganin juna komai zai zo da sauKi.� Aslaf ya dubi Sultan ya ce, “Ahaf! Ni tausayinka nake ji duk ranar da Umma tasan cewar ka zuga anyi mata kishiya. A wannan ranar sai ka gwammace baka fito duniyar ba.� Sultan ya yi murmushi, “Kasan Kara auren kamawa take yi, yanzu hankalin mahaifina da na danginsa duk sun kwanta. Abbana ya yi Kiba ya ci gaba da harkokinsa kamar kowa. Duk da har kullum yana yawan yi min maganar Umma, Abba yana son Umma Aslaf, amma Umma ta kasa gane hakan. Ni insha Allahu ma ranar da za ta san da wannan labarin tuni bana Kasar, ina can _ ina neman lafiyar idanun matata.� Cikin raha suka rako shi suna ‘yar hira atsakani. Aslaf ya tabbatar masa da zai zo ya gaida Umma. Da isarsa gida ya sami Nasreen ce kadai a falo tana goge-goge. Saura Kiris wata kwalba ta fado mata, ya Karasa cikin sauri ya rike kwalbar tare da sauya mata wuri. Ransa ya kai matuKa abaci don haka ya ce, “Ke! Waye ya sa ki wannan aikin? Iyye Nace wa ya sanya ki aikin nan?� Nasreen ta yi shiru saboda wani irin tsoronsa da take ji, ga shi dama dazu ta gama kukan rashin Nawfal dinta a kusa da ita, da yana nan duk irin ayyukan nan zai iya amsa yayi Ga masu aiki nan birjik a gida, amma Umma ta tsani ta ganta a zaune yanzu za ta hau Kirkirar aiki tana sanyata. Ita ba gani take yi ba..Ta Kone a hannunta, don haka bata son ya guni ta dunKule jikinta, duk da . irin azaban da hannun yake yi mata. Da Karfi ya � daka mata tsawan da yasa ta daya hannunta har ya ci nasarar ganin Konewar da ta yi. Shiru ya yi yana duban hannun, hakan yasa hawayen � fuskarta Samiun daman ci gaba da sauka. Yana da 6/10/22, 10:23 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 7 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Da isarsa gida ya sami Nasreen ce kadai a falo tana goge-goge. Saura Kiris wata kwalba ta fado mata, ya Karasa cikin sauri ya rike kwalbar tare da sauya mata wuri. Ransa ya kai matuKa abaci don haka ya ce, “Ke! Waye ya sa ki wannan aikin? Iyye Nace wa ya sanya ki aikin nan?� Nasreen ta yi shiru saboda wani irin tsoronsa da take ji, ga shi dama dazu ta gama kukan rashin Nawfal dinta a kusa da ita, da yana nan duk irin ayyukan nan zai iya amsa yayi Ga masu aiki nan birjik a gida, amma Umma ta tsani ta ganta a zaune yanzu za ta hau Kirkirar aiki tana sanyata. Ita ba gani take yi ba..Ta Kone a hannunta, don haka bata son ya guni ta dunKule jikinta, duk da . irin azaban da hannun yake yi mata. Da Karfi ya � daka mata tsawan da yasa ta daya hannunta har ya ci nasarar ganin Konewar da ta yi. Shiru ya yi yana duban hannun, hakan yasa hawayen � fuskarta Samiun daman ci gaba da sauka. Yana da ZAMU TASHI tabbacin Watarana sai sun kashe masa ita sannan hankalin su zai kWanta. Sakin hannun yayi yana sake dubanta cikin tausayawa ko wanene yayi masa hakan bai kyauta masa ba. Umma ce ta fito tana fadin, “ihun da kake yi na menene? Babu yadda ba ayi da yarinyar nan ba, ta bari ga masu aiki nan amma ta ki amincewa: Shi ne ta Kone� amma bata haKura ba. Duk nan babu wanda zai tsaya wai sai ya lallaba Nasreen, domin ta fi kowa sanin abinda ya kamata da wanda bai kamata ba.� Ran Sultan ya sake baci, kawai ya rufe ta da fada, “Na gaji da lamarinki Nasreen, na kusan daukarki in mayar da ke gurin Abba. Me zai sa ke ba gani kike yi ba ki ce wai dole sai kin yi ayyukan nan, ina kika taba ganin hakan? Kinsan Allah nan gaba kika sake yin rashin hankalin nan. dukan tsiya zan yi maki.� Farin ciki ya kama Umma yana kallonta da gefen idanu yadda take murmushin mugunta. Nasrecn kuwa kuka sosai take yi. Ga zafin Kuna � ga zafin sharrin da Umma ta yi muta, ga kuma zatin kalaman Sultan akanta. Kuka tayi sosai har da shessheka. Umma ta ce, “Oh ji gulma. Ke shi kenan babu wanda ya isa ya yi maki dada sai ki kama kuka? Duk kai ka lalata yarinyar nan Wallahi.� Sultan dai bai ce komai ba, sai kamo hannun Nasreen da ya yi yana cewa, ‘Mu je insa maki magani a ciwon. Idan kin gadama ki yi kukan jini ma bai dameni ba, jikinki ne ke kike jin zafin ba ni ba.� Sultan ya kama hannun Nasreen suka shiga cikin dakinsa, a lokacin su Hafsat suka fito suna KyalKyatar dariya, har da tafawa. Sultan yana shiga dakinsa ya mayar da Kofa ya rufe, ya maidota jikin Kofar ya rungumeta tsam yana mayar da ajiyar zuciya. Sai a wannan lokacin ta tsagaita da kukan, itama ajiyar zuciyar ce ta Kwace mata da Karfi. Cikin natsuwarsa yake magana, “Sorry Wife. Ciwon nan da kika ji ya gigitani matuKa. Bana son dai-dai da sauro ya cizar min fatan nan naki. Ban yarda ke kika kai kanki wajen wuta ba. So gaya min me ya faru?� Nasreen ta sake sanya . marainiyar kuka, ita ta san ta tabbata marainiya. Bubbuga bayanta yake yi, daga bisani ya rabata da jikinsa ya dubeta yadda take kukan, yasa hannu ya dauke hawayen fuskarta sannan ya Sake mayar da ita kafadarsa, “Bana son kukan nan Nasreen, idan kina irin wannan kukan zuciyata tana Kuna ina jin kamar ina cutar da ke, idan hakanne kina sane da sai Allah ya kama ni? Ki yi hakuri ki natsu.� Ta daina kukan amma hawayen nan kamar ruwan famfo. Hannunta ya kama ya dawo da ita kan gado ya zaunar yana sake dubanta. “‘Nasreen naso a ce kina iya ganina da kin ga irin tashin hankalin da nake ciki, duk da haka za ki iya fahimtar yanayin da nake a ciki idan kika taba zuciyata da ke Jullue a cikin Kirjina.� Hannunta ya tura a daidai saitin zuciyarsa, tana iya jin yadda yake bugawa da Karfi. Jikinta ya yi sanyi ta yada kanta a fadarsa, ya ci gaba da cewa, “Idan nayi maki fada a gaban Umma, ba wai nayi da gaske bane, a’a nayi ne domin su yi zaton bana sonki, yin hakanne kadai zai rage maki wahalar da Umma take shirin baki a cikin gidan nan. Ina jin daci idan na zo na sami fuskarki ba yadda na barki ba, ina jin ciwo idan naga kina aikin da bai kamata a ce kina yin sa ba. Gara in yi maki fada a gaban jama’a in shigo daki in lallashe ki. Soyayyar da nake yi maki ta yi yawan da bana iya boyeta a gaban kowa, shiyasa na nemawa kaina Control.� Nasreen har yanzu bata yi magana ba, amma kuma tausayin Kanta da na mijinta yana sake kama ta. Bata san a nan gaba me kuma zai faru ba. A hankali ta yi magana, “Ka yarda da ni Dee? Ka amince ba zan taba ha’intarka ba? Ka yarda da tarbiyya irin naka Sultan ya sake dauke hawayen fuskarta yana dubanta, “Idan har za ki iya aika ta idan kika ji zafi za ki kiyaye sake Kona min fatan jikin ki.� Nasrecn tana murmushi tana daga kanta alamun ta amince. A gadon ya mayar da ita ta kwanta, ya hada kansu wuri guda ya dan bata fake, ta shafi kumatunta tana murmushi, “Idan irin wannan horon shi ne horo, lallai kullum zan dinga aikata laifuka masu tarin yawa don in sami horo mai sanyi daga gun Dee.� Shi ma murmushin yake yi, yana son ganinta cikin nishadi.Mikewa ya yi da nufin dauko abu, kawai ya ji anbanko Kofar dakin , babu Sallama. Ya mance shaf bai sa key a Kofar ba. Zuba wa Hafsat idanu yayi yana jin ransa yana Kuna. Ta yaya za a koyawa budurwa shiga dakin matar aure babu Sallama? Idan ta taso a hakan watarana za ta yi hakan a in da bai kamata ba. Ita kuwa Nasreen tsoron Karar Kofar da ta ji yasa ta maKale jikinta. Sultan ya kafe ta da -idanunsa da suka rine saboda bacin rai, “Ina jin ki wani uzurin gareki kika shigo min daki babu Sallama?� Kame-kame ta kama yi, ta rasa me Za ta ce, sai kawai ta juya da nufin fice wa daga dakin. Sultan ya fincikota ta dawo, ya hada kanta da bango wanda yasa ta saki razanannan Kara. Tuni ya rufe Kofarsa ya murza dan makulli. Ya je ya dauko Belt dinsa ya dinga shimfida mata a jiki. Ihun Hafsat kawai ake ji, a ya yin da Umma da Zakiyya suke ta buga Kofar, Umma tana masifa tana cewa idan bai bude Kofar ba, sai ta tsine masa, amma ina Sultan baya ma jin abinda take cewa. Nasfeen kuwa kuka take yi da iya Karfinta tana roKonsa, sai dai itama baya _ sauraren muryarta. Dole ta tashi tana lalube, Hafsat tana . ganin hakan ta fahimci so take ta taimaketa, don haka ta koma bayan Nasreen tana kuka tana roKonsa, idanunsa sun rufe baya gane komai, domin yana ji a ransa da ta zo ta same su a wani yanayi bai san irin kunyar da zai ji ba. Haka yana da tabbacin sai ta gayawa mahaifiyarsa. Nasreen tana KoKarin kareta, Sultan yasa hannu ya fizgo Nasreen ya watsar da ita gefe, hakan yasa ta fadi akan hannunta har hannun ya yi wani irin Kara. Nasreen ta fasa ihu, ta zube a wurin. Hakan ya jawo hankalin Sultan akan abinda zuciyarsa ta jawo masa ya aikata. Cikin tashin hankali ya Karasa wurinta, yana jijjigata. Abinda bai sani ba, tuni hannun ya gurde, idan ba karaya ba, gocewan Kashi. Hafsat kuwa sauri ta yi ta bude Kofar ta fada jikin Umma da suka gaji da bugun Kofar, � suka tsaya jigun-jigun. Kuka take yi sosai saboda duk ta gigice. Ga jini ta gefen bakinta, haka jikinta duk ya farfashe saboda duka. Umma ta zura kanta cikin dakin nasa, sai dai a yadda suka ga Nasreen yasa kowa ya tsaya kallon ikon Allah. Sultan gaba daya ya fita hayyacinsa girgiza ta kawai yake yi, yana shafar kanta, amma babu ko alamun motsi. Cak ya dauketa da nufin kaita asibiti, Umma ta Harare shi ta ce, “Gidan uban wa za ka kaita? Maza ajiyeta babu ida za ka je da ita. Al shi mai zuciya Karshensa danasani ne. Mayar da ita. Ke Zakiyya samo ruwa a watsa mata. Yadda Hafsat ta sha wahala ita ma sai ta dandani wahalar nan. In banda ka raina ni, saboda ina zaune a gidanka shi ne za ka tasa Kanwarka da irin wannan duka kamar ka sami jaka? � Kawai Umma ta sa kuka. Hankalin Sultan ya sake tashi ganin mahaifiyarsa tana zubar masa da hawaye. Dole ya mayar da ita ya shimfide ya karbi ruwan da Zakiyya ta kawo yana shafa mata a hankali. Dago kansa ya yi yana son rokon mahaifiyarsa ta yi hakuri ta bari a kaita asibiti, sai dai dukka sun watse babu kowa akansa. Mayar da idanunsa ya sake yi kan Nasreen, ya rasa me ke masa dadi. Ganin tana motsi ya sa ya saki ajiyar zuciya da Karfi, “Nasreen ki yi hakuri ki tashi, ban san lokacin da na aikata maki hakan ba. Bai kamata ina daki da matata, Kanwata ta fado dakin babu Sallama ba, idan ‘na barta haka za ta ci gaba, har ta zo watarana ta aikata hakan a in da za ta yi danasani. Ki yi haKwri Nasreen.� KoKarin tashi take yi ta ji hannunta ya riKe wani azaba ya ziyarci Kwakwalwarta, ta fasa Kara. Da sauri ya mayar da ita ya kwantar yana shafar gashin kanta, “Nasreen kin fadi akan hannunki akwai matsala a ‘hannun, ki bari zan kira mai dori yanzu ya zo ya duba ki. Ina tunanin karyewa kika yi, yadda hannun ya saki.� Nasreen ta mayar da kanta ta kwanta, sannan ta yi magana a hankali, “Allah ya rubuto sai hakan ya faru. Ka daina tayar da hankalinka Dee, babu wanda ya isa ya kauce wa faruwan hakan.� Tana magana tana cije wa saboda tsananin azaba. Bai iya furta komai ba, ya mike ya bar ta a nan yana tafe yana sake waiwayo ta. A falo ya sami Umma tana ba Hafsat taimako. Bai dube su ba, ya yi waje abinsa, hakan ya sake Kona wa Umma rai. Yana fito wa ya tashi dan sanda daya ya tura shi ya zo da mai dori a duba Nasreen. Yana dawowa ya sake wuce su Umma ya nufi gun Nasreen, domin har yanzu ji yake kamar ya fizgo Hafsat ya ci gaba da jibganta.Tana nan yadda ya barta, sai rintse idanu take yi saboda zafi. Mayar da kanta ya yi jikinsa, sannan ya manna mata sumba a goshi. “Ina son ki Wife.� Cikin rufewar idanu tace “Ina son komai naka Dee. Zan jure komai idan hakan zai faranta maka.� Ji ya yi kamar baa taba gaya masa kalamai masu sanyin wannan kalaman ba, ga su dai ba su da yawa amma sun > gamsar da shi. Zakiyya ta shigo take gaya masa � zuwan mai gyaran, ya ce bari ya fito da ita. A hankali suka ta ko zuwa falon, Umma ta zabga masu harara ya kauda kansa zuwa gefe, yana jin damuwa a can Kasan ransa. Da za a fara kama hannun Nasreen Sultan ya saketa yana son fice wa, a lokacin da ita kuma ta riKe hannunsa sosai. Duban mai gyaran ya yi ya ce masa, “Zan dan fita ba zan iya tsaya wa a gyara hannun a gabana ba. � Umma ta ce, “Wallahi a gabanka za a gyara hannun, ashe kana da imani akan matarka? Akan Kanwarka kuma ko a jikinka ko? To sai ka tsaya an gyara hannun, sai ka hadiyi zuciya ka mutu, ‘yar Gold dinka ta sami matsala.� Sultan dai bai ce komai ba, ya koma ya sake riKe ta sosai ya yl magana a hankali wanda ita kadai ta ji mai yake cewa, sai kuwa nai gyaran da ya dago yana duban su cike da sha’awa, “Wife kada ki damu babu inda zan je ina tare da ke.� Nasreen ta dinga daga kai alamar ta ji. Ana riKe hannun ta yi iya bakin KoKarinta domin ta daure abin ya ci tura, dole ta dinga kuka tana fizge kanta. Sultan din kadai ya isa ya rike ta, idan ba haka ba, riKe ta sai wanda yaci ya Koshi. Umma suna nan zaune ko kallo bata ishe su ba, Sultan kuwa ji yake kamar naman jikirisa ake yanka. Sai da ta kai ya dago yana duban mai gyaran, yace “Don Allah ka yi mata a hankali.� Mai gyaran ya: yi murmushi yana kallon tsantsar Kauna, shi bai taba yarda akwai irin wannan son a tsakanin mata da miji ba, sai yanzu da idanunsa suka gane masa, “Ka yi haKuri yallabai, idan aka ce za a tsaya lallabawa ba zai yi kyau ba, gocewar Kashi ne.� Sultan ya kauda kai ya ce, “Duk da hakan ka yi a hankali.� Mutumin ya amsa yana murmushi ya ci aba da abinda yake yi. Ana gamawa Nasreen ta saki ajiyar zuciya, ta laluba ta kamo dayan annun Sultan, ta yi magana a hankali cikin yanayinta, ‘“‘Dee ka kira min Nawfal, don Allah ka awo min Nawfal.� Tausayinta ya sake cika masa zuciya, kamar ya taya ta kukan, ya ce. “To ki daina kukan insha Allahu zan tafi da kaina in je in kawo maki shi.� tana son ta daina kukan amma wahala ta hana, don haka ta sake cewa, ‘“‘Dee ka samo min maganin barci idan nasha zan daina jin radadin.� Ya so Kwarai ya zolayeta akan idan ta tashi haihuwa ya za ta yi? Sai kuma ya ga idanun Umma gaba daya akansa don haka ya basar yana duban Umma, ta kauda kanta wanda ke nuna alamun tana fushi da shi, yana son ya gama da Nasreen ne, kafin nan ta sauko sannan ya je ya lallaba ta. Da Kyar Nasreen ta iya tashi ya kaita cikin dakinta, shi kuma mai gyara dan sandan ya Sallame shi. Tana kwanciya ya ce, “Wife ranar haihuwa ya za mu yi kenan? Likitoci ba za su barni in zauna kusa da ke ba, bare ki rike hannuna.� Nasreen ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba. Ya sunkuya dai-dai fuskanta yana gaya mata kalamai a hankali kuma ya dinga hura mata iska a fuska, tana jin kasala tana shigarta, hade da barci wanda ba ta san lokacin da barcin ya yi awon gaba da ita ba. A fili yace, “Allah ya baki lafiya Wife.� Ya sumbaci goshinta ya fice. A falo ya sami Umma da hafsat fuskar nan tata ta kumbura gwanin ban tausayi. Har zai wuce Umma ta ce, “Zo nan ina son magana da kai.� Babu musu ya dawo ya zauna yana duban Umman, sannan ta fara magana, “Ka ji tsoron Allah Sultan ka gaya min me Hafsat ta yi maka haka da zafi da har kayi mata irin wannan dukan? Gaya min me ta yi maka? Idan babu laifin da ta yi tsabar mugunta ce kawai, ka gaya min sai in dauki mataki.� Sultan bai ji dadinl da Umma za ta yi masa magana irin hakan a gaban su Hafsat ba, wannan kamar ta ce gobe su sake aikata irin laifin ne. A natse yake magana kamar babu abinda ke damunsa, “Umma ina daki yarinyar nan ta fado min babu Sallama, ta yaya za ayi da girmanta ta dinga shigo wa mutane babu Sallama? Ashe karatun addininta, da yadda kika ba mu tarbiyya 6/11/22, 17:32 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 8 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Nasreen ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba. Ya sunkuya dai-dai fuskanta yana gaya mata kalamai a hankali kuma ya dinga hura mata iska a fuska, tana jin kasala tana shigarta, hade da barci wanda ba ta san lokacin da barcin ya yi awon gaba da ita ba. A fili yace, “Allah ya baki lafiya Wife.� Ya sumbaci goshinta ya fice. A falo ya sami Umma da hafsat fuskar nan tata ta kumbura gwanin ban tausayi. Har zai wuce Umma ta ce, “Zo nan ina son magana da kai.� Babu musu ya dawo ya zauna yana duban Umman, sannan ta fara magana, “Ka ji tsoron Allah Sultan ka gaya min me Hafsat ta yi maka haka da zafi da har kayi mata irin wannan dukan? Gaya min me ta yi maka? Idan babu laifin da ta yi tsabar mugunta ce kawai, ka gaya min sai in dauki mataki.� Sultan bai ji dadinl da Umma za ta yi masa magana irin hakan a gaban su Hafsat ba, wannan kamar ta ce gobe su sake aikata irin laifin ne. A natse yake magana kamar babu abinda ke damunsa, “Umma ina daki yarinyar nan ta fado min babu Sallama, ta yaya za ayi da girmanta ta dinga shigo wa mutane babu Sallama? Ashe karatun addininta, da yadda kika ba mu tarbiyya ZAMU TASHI akan ko falo ne bamu isa mu shigo maki babu Sallama ba, baiyi mata amfani ba. Shiyasa na koya mata darasi ta hanyar nan.’� Umma ta zaro idanu, “Shi ne dalilin irin wannan duka? Ai ni ina zaton sata ta yi maka, ka kama ta da duka irin na barayi. Sultan fito ka gaya min kawai kafi son Nasreen akan Hafsat. Ko kuma ka gaya min baka da gaskiya shiyasa kake tsoron a shigo maka daki babu Sallama.� Sultan dai ya yi shiru ba tare da ya sake furta komai ba. Kafe Kanwarsa da idanu ya yi yana jin tausayinta yana ratsa shi. Bai kula da irin barnar da ya yi mata ba, sai yanzu. Ta tsorata sosai da shi, domin ko a yanzu din ta kasa sakin jikinta, a falon haka ta Ki yarda su hada idanu. Ita kanta Madam rawar kai Zakiyya ta shiga hankalinta. A hankali ya kirawo sunanta, wannan shi ne karo na farko da kallon Rahama ya hada ta da Yayanta. A hankali ta dago hawaye suna sake bin idanunta. Da kai ya kirata, ta matso jikinta yana rawa. Hannunta ya duba zuwa fuskarta. Jikinsa ya sake yin sanyi ya ce, “Hafsat kin gani ko? Kullum ina kiyaye taba lafiyar jikinki amma kin kasa fahimta, har sai da kika Kure ni. Tashi mu je in kai ki asibiti.� Muryarta na rawa ta ce, “Don Allah Yaya kayi hakuri.� Girgiza kansa ya yi cikin rauni da soyayya irin ta jini ya ce, “Ya wuce Hafsat, bana son kukan.� Ta shiga goge hawayenta. Umma kuwa jikinta ne ya yi sanyi a karo na farko, duk a tunaninta Sultan ya tsani Kannansa ne, amma yanzu ta ga asalin Kauna a Kwayar idanunsa. Haka ta sauko sosai daga irin fushin da ta yi da shi. Idanunsa ya mayar kan Umma yana dubanta, “Umma ki yi hakuri ki yafe min bata maki da nake yawan yi. Na fi buKatar addu’arki fiye da irin wannan fushin. Fushin ki masifa ce a gareni.� Umma ta girgiza kai, “Na yafe maka Sultan, Allah ya yi maku albarka, ya Kara hada min kawunan ku.� Gabadaya suka amsa da Ameen, sannan Hafsat ta fito suka shirya zuwa asibiti. A can Garin Kaduna, Mairo ce tsaf da ita ta Kara kyau da haske. Dama rashin gyara ne duk ya canza ta. A yanzu kuwa ta zama ‘yar gayu da ita sai Kamshi ko ta ina a cikin gidan. Shi kansa Abban ya sami natsuwa sosai. Yau Hajiya Ladidi ta biyo ta Unguwar, don haka zuciyarta take gaya mata tunda babu Hajiya Salma za ta iya zuwa da sunan duba Alhaji Lukman. Sai da ta sake gyarawa tsaf sannan ta doshi hanyar gidan. Naufal baya nan yana Makaranta, gidan babu kowa daga ita sai Abba. Don haka tayi ta kwada Sallama. Abba ya dubi Mairo dake matsa masa Kafafu yace, “Maryama kamar buga Kofar nan ake yi, maza je ki ki ga waye.� Mairo ta mike ta nufi Kofar, Abba ya bi ta da kallo, tana matuKar _ KoKari wajen kyautata masa, sai dai soyayyar Salmarsa halitacciya ce a zuciyarsa. Yana yi wa Salma soyayyar da ita kanta bata san da ita ba. Sai dai zuciya tana son mai kyautata mata, rashin kyautatawar Salma shi ya rage kashi daya daga cikin manyan kason da ke ransa. Mairo tana bude Kofa aka hau kallon kallo. Hajiya Ladidi ta yi bala’in rudewa sai kallon Mairo take yi cike da mamaki da tsoro. Mairon da ta sani da, a yanzu ba ita ba ce ta sauya fiye da tunanin mutum. Baki sake Hajiya Ladidi take dubanta. Duk da ta gaisheta da girmamawa, amma kuma ba kamar yadda take yi mata a baya ba, ta saba sai ta durkusa har Kasa take gaida ta, ba kamar yanzu ba, da ta dan rankwafa. Hajiya Ladidi bata amsa ba, ta sa kai ta shiga tana sake dubanta. Abba yana ganin Hajiya Ladidi ya ji gabansa ya fadi, domin har yanzu tunani yake yi duk ranar da Salma ta san wannan lamarin, bai san ta yadda za a kwashe ba. Mairo kuwa shige wa ciki ta yi gabanta yana fadiwa da Karfi. Hajiya Ladidi ta sake bin hanyar da Mairo ta bi da kallo tana jinjina kai, dole da akwai wani abun da ke faruwa wanda ake boye wa. Sama-sama suka gaisa ta dube shi tace, “Amma na ga Maro ta sauya sosai ko ta daina aiki a nan ne?� Abba ya sha mur sosai yace, “Da ta daina aiki a nan me za ki ganta tana yi kuma?� Hajiya Ladidi ta saki yaKe ta ce, “Haka ne kuma. Dama na zo ne in gaya maka abinda ya’dade a cikin zuciyata. Tunda Hajiya Salma ba dawowar yanzu bace ba, shi ne na ce me zai hana mu yi aure sai zumuncin mu ya Karu?� Abba ya dube ta kawai yana girgiza kai, mata kenan su babu ruwan su da abinda zai je ya dawo. Babu ruwansu da matsalar ‘yar uwarsu idan har su din za su sami abinda suke so, basu damu da matsalar wata ba. Kullum cewa ake ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ce, wannan ba haka yake ba, zai fi amincewa da ace ciwon ‘ya mace na da namiji ne, domin da namiji a yanzu shi ne mace za ta gaya masa matsalarta ya nemo mata mafita ba tare da ya bari wani yaji ba, sabanin ‘ya mace da kana gama gaya mata matsalarka za ta nuna a gabanka ta tausaya, idan aka sami makira har ta fara kuka, kuna rabuwa za ta yi dariya, ta sanya katin dubu ta fara kira tana gayawa duniya dukkan abubuwan da ke faruwa. Zai fi kyau mace ta kama Allah ta rabu da duk wata Kawa, idan ma za ta yi Kawar ta yi wacce za a hadu a gaisa ayi dariya a rabu, haka ta boye mata matsalarta ta bayyana mata samunta. Dubanta ya yi sosai ya gyara zama ya ce, “Amma Hajiya Ladidi kin bani mamaki sosai, ban yi tunanin duk irin amintarku a ce za ki iya zagayowa ki ce za ki auri mijin aminiyarki ba. Kada ki manta akan farin cikin ‘yarki ta bar gidana taje ta Kwato mata ‘yancin da take tunanin Sultan zai tauye mata. Abin mamaki sai ga shi kin zaga yo ke baki da burin da ya wuce ki aure mata miji, ki Kuntata mata.� Hajiya Ladidi ta dubi Abba cikin kissa irin nasu na ‘yan duniya ta ce, “Alhaji ba haka bane, naga tuni Hajiya Salma ta fita batunka, tunda tana samun maza masu debe mata kewa, tana harkokinta, gidan malamai ma da ita muka je ta ce a mallake mata,kai. Abubuwanta sun Kazanta. Bari ka ga gaskiyata.Ta bude wayarta ta bude masa sakonnin message din da tabbas da lambar Hajiya Salma ce, wanda babu komai sai maganganun da suke . nuna cewar tana alaKa da wasu mazan. Sai dai kuma ba lallai abinda take nufi kenan ba, idan aka yi la’akari da mutum yana iya yin wata magana a sauya masa, haka kuma ko hoton Hajiya Salma aka kawo masa tana tsirara tare da wani, ba zai taba yarda ba, zai fi amincewa kansa kwamfuta ce ta hada wannan sharrin ba dai Salmarsa ba. Salma ta tsani mazinaci, fiye da irin tsanar da za lta yi wa wanda ta ga ya kashe rai, me zai sa a lokaci guda a dangantata da zina? Murmushi ya yi sannan ya ce, “Na gode da wannan sheda da kika bani akan Salma, na kuma ji dadi sosai.� Yana duban yadda Hajiya Salma take aikin murmushi da alama murna take yi ta ci galaba za ta tsinka igiyoyin aure, farin ciki take yi za a girgiza al’arshin Allah, farin ciki take yi za a aiwatar da abinda shaidan yake murna a kai, Allah yake fushi akan aikata shi. Yace, “Hajiya Ladidi shaidun da kika kawo min sun yi min kadan akan Hajiya Salma, zai fi kyau ki bari sai idan tana cikin hotel sai ki kirawo ni inganta da idanuna, kai Wallahi a cikin hotel din ma, sai Salma ta rike ni ta ce min Lukman ni ce Salma matarka, uwar Sultan da Haidar da Hafsat. Kila idan na ga hakan in amince cewa Salma fasiKa ce. Ki fadi wani abu akanta ba zina ba, ina cikin daya daga cikin mazajen nan masu dogon tunani da nazari kafin daukar mataki, ina daya daga cikin mazajen da suka amincewa iyalansu. Idan har Salma za ta iya aikata fasiKanci babu shakka nima zan kasance daga cikin su, ban kasance fasiki bana Kasance mai kyakkyawar zuciya, bana zaton zan zauna zaman aure da fasiKa. Ki bar ganin dana Sultan ya kasance da ‘yarki, ki yi tunanin halayyar dana iri daya ne da halayyar “yarki. Ko daya babu ta inda Sultan ya zama mai irin wannan halayyar. Allah ya Kadarta auren su ne, saboda ya nuna wa Salma ishara, domin ta tsani masu aikata munanan laifika a maimakon jawo su jiki da nuna masu abubuwan da suke aikatawa Allah ya haramta hakan. Ke kanki kin sani, a gabanki Salma tana nuna Kyama da irin wani abun da kike aikatawa, ita haka take bata iya boye tsanar da ta yi wa abu Kin yi matuKar KoKari wajen zuwa gaban miji, uban ‘ya’yanta ki aibatata da munanan kalamai. Bana jin zan taba mance ki. Kina iya tafiya.� Jikin Hajiya Ladidi ya yi matukar sanyi, bata ji dadin irin wannan gwasalewar ba, ita kanta ta sani Hajiya Salma mace ce mai tsananin gudun zina, haka ta tsani mai aikata shi, amma kuma duk wanda ya ganta tana Kawance da Hajiya Ladidi dole ya kawo wani abu a cikin ransa. Ta saki ajiyar numfashi ta sake dubansa, “Ban san wacce yarda ce take a tsakaninka da matar da ta gujeka, ko wayarka bata daga wa, saboda yadda ta riga ta cireka a cikin tsarin mazajen da take so ba ada can baya. Kuma ni iya gaskiyata nake gaya maka matarka dai tana mu’amala da wasu mazan.� Ransa ya soma Baci da irin Batancin da Hajiya Ladidi take yi wa Salma, don haka ya gyada kansa cike da bacin rai, ““Na ji na gode. Ina sonta a hakan, idan ita ce magajiyar karuwai, ni a wurina mai tsafta ce, bana daya daga cikin sakarkarun mazan da kike tunani. Don Allah tashi ki bar min gidana. Kuma da kike maganar ta mallakeni, idan da abinda yafi mallaka, ina son tamin ta cancanci mallakeni din tun tuni Hajiya Ladidi ta mike tana yamutsa fuska, Sai da ta tabbatar da ta yi nesa da gidan, Kafin ta zari wayarta ta kira Hajiya Salma. Bata iya jin gaisuwar da Hajiya Salma take yi mata ba, tace, “Ni tsaya min. Yanzu na dawo gidanki, nazo wucewa nace bari in leKa mu gaisa. Abin mamaki sai na kama mijinki da mai aikin Ki a filin falo, suna aikata abinda ba zan iya furtawa ba,, Yanzu haka na tafi na barshi da Kunya da kame-kame, Duk, da Hajlya, Salma, tayi matuKar,razana da gigicewa, har bata san lokacin data furta, “Kan uba! ,Wacce Mairon?� Wai da wa Kika kama ta? Mijina Alhaj_Lukman din?* Daga baya kuma taja bakinfa ta tsuke kamar Wacce aka yiwa, ishara data rufe bakinta, ta _kuma dawo cikin hayyacinta. hakan yasa a lokaci guda ta tattaro dukkan ‘yar sauran natsuwar da ta rage mata, ta hada su wuri guda, sannan ta saki ajiyar zuciya, har ta koma tana jin ‘haushin kanta. “Amma dai Hajiya Ladidi yadda kika ci nasarar jefa shaidan a zyciyata, Allah ya rama min. Me kike fada ne? Abban Sultan� Har abada ‘babu wanda zai danganta Abban Sultan da abinda kike fada in gasgata shi koda Kuwa Wacce ta tsuguna ta haife nine ta kirawoni tana gaya ‘min mdganar nan bazan amince ba Bare Kuma ké da kika Kware wurin‘makirci. Ta yaya ma zuciyata zata Aminta dake? ‘Yaushe� ya fara aikata masha’a bayan Shekarun da yayi a turai, inda ya hadu da mata masu jida kansu ya kaucewa sharriin su Saida ya dawo kasata� Najeriya, da girmansa, zai aikata hakan? Kuma agun mai aikina? ‘Ki dai tuna ‘abinda’Kika gan shi ‘yana aikatawa ba� abinda Zuciyarki ta Sanar dake ba� Hajiya Ladidi -tayi ‘rantsuw tana -yi_ tanta sakewa, *don haka ‘Hajiya Salma ta fara� jin zuciyarta� tana ‘rawa yar yardar data bashi ta nemi fizge abinta da Karfin tsiya jin tayi shiru yasa Hajiya Ladidi ci-gaba da’yi mata famfo,-har sai da jikinta ‘ya kama rawa‘ta datse waydr tana ‘jin ’wani irin� Kunci a ranta� ji take! har abada ba *zata iya zama da miazinaci ba haka ko ranta za,a ‘zare ba za ta iya rabuwa da� soyayyar� Alhaji Lukman’ba� da tayi mata rassa! Ta hade da jinin jikinta.“Ta -‘rasa me take ji a ranta ‘a tsakanin tsanarsa� da� tausayinsa� da “Kuma: kishinsa da � sonsa? Ta tafi ta bar shi ne saboda tana tsoron Nasreen ta ci galaba akan danta, haka kuma tana da tabbacin Sultan ba zai iya kwatanta adalci a tsakanin Zakiyya da Nasreen ba. Kankat! Ta zo nan ne domin ta sake raba Nasreen da zuri’arta. Can daki ta shige yadda babu mai iya jinta, sannan ta kira Alhaji Lukman a waya. A lokacin yana zaune tare da Mairo fuskarsa da alamun damuwa, Mairo ta yi magana cikin sanyi, “Abba me yasa za ka damu da maganar Hajiya Ladidi? Kafi kowa sanin duk a cikin zancenta babu gaskiya. Na zauna da Umma nasan halinta, nasan abinda za ta iya aikatawa nasan wanda ba za ta iya ba. Maganar mallaka kuma da take yi Karya take, ita ce ta yaudari Hajiya ta ce, akwai wani malami a cikin Alqur’ani yake ciro addu’a ya yi idan ya yi addu’ar sai ta sha mamakin irin yadda za ka koma tamkar yaron Umma. A kunnena na ji Umma tana cewa ita idan har ta tabbatar da babu kaucewa za ta iya yi, saboda kana yawan yi mata gardama akan kome ta gaya maka. Ka ji ta inda ta yi wa Umma dabara kenan, kasancewar ta san Umma ta tsani shirka. Haka maganar bin maza duk Karya ce, ina ji wasu lokutan Umman ke yi mata fada akan rayuwarta, har ma tana nuna Kyama ga Hajiya Ladidi. Don haka ka daina damuwa.� Abba ya saki ajiyar zuciya, “Lallai sun yi hakan kuma sun sami nasara akaina, ba wai don bana ibada ba, sai don Allah ya aiko min da jarabawa kuma na karbeta. Maryama ba maganar Hajiya Ladidi ya sanya ni damuwa ba, don bana jin akwai abinda za ta fada akan Salma har ya dameni, nasan wacece matata tun Kuruciya, na santa da zafafa kiyayyarta akan abinda ta furta ta ce ta tsana bata so. Kawai-ina jin damuwar yadda Salma ta yi zamanta a gidan danta ta nuna bata damu da ni ba, duk irin son da take gwada min.� Ya Karashe cikin damuwa, sai -kuma ga kiran wayarta, don haka jikinsa na rawa ya dauka, domin ji yake kamar ana Kara masa sonta. Yana yin Sallama ta kasa jurewa, sakamakon wani kishi da ya tokareta, ta fasa kuka. Iya gigicewa Alhaji Lukman ya gigice, tambayarta kawai yake waye ya mutu? Cikin kuka take cewa, “Abban Sultan yau ni za ka yi wa haka? Duk yadda na baka kulawa na hana kaina kwanciyar hankali don in kyautata maka, yau kuma dan bana nan shi ne za ka kasa jure wa har sai ka aikata Barna? 6/11/22, 17:43 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 9 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Haka maganar bin maza duk Karya ce, ina ji wasu lokutan Umman ke yi mata fada akan rayuwarta, har ma tana nuna Kyama ga Hajiya Ladidi. Don haka ka daina damuwa.� Abba ya saki ajiyar zuciya, “Lallai sun yi hakan kuma sun sami nasara akaina, ba wai don bana ibada ba, sai don Allah ya aiko min da jarabawa kuma na karbeta. Maryama ba maganar Hajiya Ladidi ya sanya ni damuwa ba, don bana jin akwai abinda za ta fada akan Salma har ya dameni, nasan wacece matata tun Kuruciya, na santa da zafafa kiyayyarta akan abinda ta furta ta ce ta tsana bata so. Kawai-ina jin damuwar yadda Salma ta yi zamanta a gidan danta ta nuna bata damu da ni ba, duk irin son da take gwada min.� Ya Karashe cikin damuwa, sai -kuma ga kiran wayarta, don haka jikinsa na rawa ya dauka, domin ji yake kamar ana Kara masa sonta. Yana yin Sallama ta kasa jurewa, sakamakon wani kishi da ya tokareta, ta fasa kuka. Iya gigicewa Alhaji Lukman ya gigice, tambayarta kawai yake waye ya mutu? Cikin kuka take cewa, “Abban Sultan yau ni za ka yi wa haka? Duk yadda na baka kulawa na hana kaina kwanciyar hankali don in kyautata maka, yau kuma dan bana nan shi ne za ka kasa jure wa har sai ka aikata Barna? ZAMU TASHI To ya yi kyau sosai, ina tabbatar maka ba zan koma gidanka ba, sai ka bani takardata.� : Alhaji Lukman ya _ yi kasake’~ yana Saurarenta, “Me nayi maki kuma Salma? Me yasa za ki jefe ni da irin wannan kalaman?� . Ajiyar zuciya ta yi tana Kokarin share hawayenta, “Hajiya Ladidi bata kama ka da mairo ba? Bata kama ka ba? Me yasa za ka wulakanta ni a idon mai aikina? Ban ga laifin Mairo ba, laifin wanda ya bata fuska ne, amma na gama zama da mazinaci. Tsawa ya daka mata jikinsa yana rawa, “Ya isa Salma! Haba!. Me ke damunki ne? Za ki iya jifana da ko wacce kalma amma banda Kalma mafi muni da Kazanta. Har kullum ku mata Karamin tunani ke gareku, namiji zai iya kare martabarki a ko ina, ko da kuwa kin sauya, amma ku babban burinku a gaya maku zunubin mazajen ku, ku fita duniya kuna ihu kuna fadin ba a kyauta maku ba, kuna fadin a sake ku. Na ji ciwo da Salmar da nake yi wa irin wannan son ne take gaya min maganganu masu dacin nan, nayi tur da wannan halin da kika ara kika dora wa kanki. Idan aka bani AlKur’ani zan iya dafa wa matata ita ce za ta bayar da shaidan Kwarai akaina, sai dai abin takaicin yau da raina nake jin Kazaman kalamai daga bakin wacce na mallakawa zuciyata. Gara ki ce min ba zaki dawo ba, sau dubu da ki ce min mazinaci. Ki dinga bincike kafin yanke hukunci, idan ba haka ba za ki yi ta samun matsala da jama’a da dama daga Karshe ki rabu da mutanen kirki ki kama na banza.� . Abba ya kashe wayar yana jin zuciyarsa babu dadi. Ita dai Mairo tagumi ta yi ta zuba masa idanu, tana kallon son uwargidansa a idanunsa, ita dama tasan ya dai aureta ne kawai, ba dan tana burge shi ba. Sai yanzu ta sake gazgata abinda bahaushe yake cewa, tsohuwar zuma da ita ake magani, haka duk kyan amarya da yadda take ganin mijinta yana sonta, har abada uwargidansa daban take a cikin zuciyarsa, domin kuwa ita ce Mafarinsa. Don hakane take taya duk macen da ta zama Uwargida murnar samun sarauta mai girma a zuciyar mijinta. Zuciyar Mairo ta nemi ta fara zafi, saboda wannan halittacen kishin da ke maKale a zuciyar kowacce mace, sai ta yi saurin karanta A uzubillahi. Ta kori shaidan, domin idan har ta yi kishi da matar da ta zauna a KarKashinta bata yi adalci ba. � Ba za ta iya yi masa magana a irin yanayin nan da yake ciki na halin bakin ciki ba, dole ya na buKatar zama shi daya don haka ta mike za ta fice, ya kirawo sunanta_ cikin natsuwa, “Maryama zo ki zauna.� Babu musu ta dawo ta zauna, ya dubeta cikin kulawa, “Na ga fuskarki ta sauya ina fatan ba ni bane na bata maki?� Girgiza kai ta yi, tana murmushi hakan yasa ya gyada kai, suka kuma yin shiru, domin ya rasa me zai ce mata. Ita kuwa Umma ji ta yi danasani yana shigarta, ta san halin Hajiya Ladidi ta hada fada, amma kuma ta kasa gano irin ribar da za ta ci idan har ta hada ta fada da mijinta. Zuciyarta ta kasu gida biyu, sai dai yarda da mijinta ya fi yawa a cikin zuciyarta, tana jin ta amince da shi, ba za ta taba yarda a ce wai Alhaji Lukman zai iya zama kujera daya da Mairo ba, “Lallai da sai na kasheta idan ya so nima a kasha ni.� Ta fada a sarari tana huci. Sultan da Hafsat suka dubi juna, kafin suka dawo da kallon su gun Umma. Sultan ya ce. “Wa za ki kashe Umma?� Tana ganin su ta mike sai kuma ta fara kuka, ta dubi Sultan ta ce, “Ka ji Hajiya Ladidi wai Abbanku yana neman Mairo mai aikin mu.� Gaban Sultan ya fadi, lallai yasan akwai yaki a nan gaba. Ya kasa magana sai dubanta kawai yake yi. Hafsat ta dora hannu a kai kamar wacce aka yi wa mutuwa, “Umma mun shiga uku! Kai Karya ne Abba ba zai taba duban wacce ta fi Mairo ba, bare kuma Mairo. Gidanmu cike yake da ma’aikata maza da mata, babu yadda za ayi Abba ya wulakanta kansa a cikin su. Mun bani Yaya Sultan ka kira Abba baya boye maka komai za ka ji gaskiya a bakinsa.� . Umma ta kamo hannun Sultan suka zauna, ta ce, “Gaskiyar Hafsat ce, na kira shi yana ta min wasu maganganu wai anyi masa sharri, amma yanzu kira shi ka Kara murya sai mu ji abinda zai ce ta hakanne kadai ragowar zuciyar da bata amince da shi ba, za ta Karasa yarda da shi. Sultan na gigice da yawa, nasan halin Abbanka ba zai aikata hakan ba.� Sultan da gabansa ke fadi ya dubi Umma ya ce, “A’a Umma ba sai na kira shi ba, ni na yarda da mahaifina babu abinda zai aikata da ake zarginsa. Kawai sharri ne.� Umma ta share hawayenta, “Eh na sani Sultan kai dai ka kira shi.� Nasreen ce ta shigo tana lalube, ran Umma ya sake baci ta daka mata tsawa, “Ke! Fice ki bamu wuri muna tattauna abinda ya shafe mu ne, ban ga dalilin shigowan bare ba.� Nasreen ta gigice sosai ta yadda har ta taba hannun da aka yi gyara, ta sake komawa da baya ta kusa faduwa, Sultan ya mije da sauri zai iso wurinta, Umma ta sake riKe hannunsa tana harararsa dole ya koma ya zauna yana dubanta. Zakiyya da har ta sawo kai ta ji irin tijarar da aka yi wa Nasreen sai ta koma gefe, ta labe tana sauraran su. Nasreen kuwa ta yi matukKar daurewa bata yi kuka ba, har sai da ta samu isa dakinta sannan ta fasa kuka mai Karfi. Gabadaya Sultan ya daina fahimtar mahaifiyarsa hankalinsa ya koma kan Nasreen, ya san cewar tana can tana kuka, don haka ne yake jin damuwa a ransa. Babu shiri ya fitar da wayarsa ya danna lambar wayar Abba gabansa yana ci gaba da fadiwa, ya tabbata idan Abba ya dauka asirinsa da na Abbansa ya gama tonuwa, yana da tabbacin tsine masa kawai za ta yi. Cikin ikon Allah aka sanar da lambar Abba 2 kahe take, hakan yasa Umma ta sake gigicewa. Sultan ya tattaro natsuwarsa sannan ya yi magana, “Ki kwantar da hankalinki Umma gobe insha Allahu zan je Kadunan za ki ji komai.� Umma ta yi hamdala ta kuma ba shi Karfin guiwar ya tafi ba tare da ya sanar masa da zuwansa ba. Da Kyar ta sallame shi yana fitowa kai tsaye dakin Nasreen ya shige ya same ta tana kuka, ya jawota jikinsa yana share mata hawaye, sannan ya rungume ta yana bubbuga bayanta, “Na taba gaya maki na tsani in ga kina kukan nan? Haba Nasreen yaushe za ki saba da halin Umma? Tana cikin bacin rai ne, maganar nan ne na Mairo aka gaya mata sai dai cewa aka yi Abba yana nemanta, kin dai san Umma da kishi shi ne yanzu duk ta tashi hankulan mu. Don Allah ki daina kukan nan.� Nasreen ta yi luf a jikinsa, tana jin ba za ta iya magana ba, domin da gaske kalaman Umma sun yi mata ciwo, tana son sanin su waye danginta? Duk lalacin su za ta iya zama da su. Sultan ya ji duk zuciyarsa ta jagule. Ya rasa me zai ce mata, kawai sai ya kafe ta da idanunsa. A lokacin ya sami kiran gaggawa, za su fita wani aiki. Cikin gaggawa ya mike zai fita, sai kuma ya dawo, ba zai iya barinta a cikin wannan halin ba. “Babyna ta shi ki raka ni wajen aiki. Zan siya maki babyn roba ki dinga wasa da ita.� Murmushi cikin kuka ya subuce mata. Hakan yake son gani don haka ya ji sanyi a zuciyarsa, haka yana da tabbacin zai sami natsuwa wajen fitar. Hannunta ya dauka yasa a kansa, “Yi wa mijinki addu’a zai fita gun aiki. Addu’arki za ta taimaka in je lafiya in dawo lafiya. Ki kauda damuwa a fuskarki idan kika yi haka mijinki zai kwantar da hankalinsa a cikin jama’arsa.� Nasreen ta shanye kukanta ta yi magana cikin sanyi, “Ya Allah ga mijina, yana da . kamanta gaskiya, ya hana kansa cin haram, ya tsarkake zuciyarsa ta hanyar neman halak! Ya goya marayu, ya inganta karatunsu, ya hana su kukan maraici, ya Allah ka taimake ni ka kare min shi, ka bashi sa’a a dukkan lamuransa, ka makantar da idanunsa a lokacin da aka kusance shi da haram, ka Kara masa hasken idanu a lokacin da Halak take tunkaro shi. .Allah ya tsareka Dee, ya baka nasara akan dukkan abinda ka sanya a gaba.� Sultan ya tsinci kansa da jin dadin addu’ar Nadsreen, duk da ta Karashé muryarta tana rawa, hakan bai hana shi sumbatarta ba, ya dubeta “Kin yi min alqawarin in tafi in kwanta da hankalina ba za ki yi kuka ba? Idan kin san za ki yi kuka in fasa fita in zauna ina renon hawayenki don ganin na hana su zubo wa.� Murmushi ne shimfide a fuskarta, za ta so ta iya kallonsa a lokacin da yake wannan maganar, don haka ta daga kanta, “Nayi maka alKawari.� Cikin sauri ya shafi Kanta ya fice. Bai ga ‘Umma ba, bare Hafsat, hakan ke nuna masa lallai yau Umma tana cikin damuwa. Zakiyya tana ganinsa ta biyo bayansa, bai ce mata komai ba, ya fitar da uniform dinsa ya sanya, ya dauké takalmansa da safa ya zura, ya dauki ‘hula ya sanya. Zakiyya ta bude baki tana kallonsa, zata iya rantsewa bata taba ganin mutumin da Unifoam yake yi masa kyau ba, kamar Sultan gaba daya kayan sun Kara haskaka shi. Shi Kansa. ya gamsu kayan sun karbe shi. Duban ta yayi lokacin da yake gyara zaman hularsa yace, zanje Office.�Zakiyyatace,“To.�Ya dube ta kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya kama hanyar fita. Ba zai iya wucewa. bai sake zuwa ya duba Nasreen ba, yana komawa dakin ya same ta zaune ta yi Shiru.Tun kafin ya yi magana ta fara murmusho “Ka yi kyau tamkar dawisu Mayar da kanta tayi ta kwanta a gadon tare da rigingine, “Dee kullum idan na yi Sallah ina sake gode wa Alla da ya bani kai a matsayin mijin aure, tabbas ita din ta daban ce a cikin ‘mata. Ban taba ganin mutumin da yake kyau-da kaki ba, sai akanka.� � Sultan ya zaro ido sosai yana dubanta. Yadda ta kwanta tana kallon sama, yasa ya Karaso ya hada kansa da nata suna shakar Samshin juna, “Anya baki ganin komai Nasreen? Abubuwan da kikeyi suna yi min kama da macen da take gani, ba makauniyar dana sani ba. Nasreen ta yi murmushinta dake Kara kawata fuskarta ta ce, “Babu makauniya a duniyar nan, musamman akan wanda takeso. Makantar zuciya ita ce Makanta, ba ta idanu ba, zuciyata tana ganinka, tana jinka tana iya siffantaka, tana iya idan kana wuri Zuciyata za ta makance ne Kawai a duk ranar da ta daina son ka, hakan kuma ba zai faru ba, ko da kuwa an dauke numfashina daga jikina.� Sultan ya nemi ya mance abinda ke gabansa, sai da ya fara KoKarin cikuikuye unifoam din da ya sha guga, sannan ta ankarar da shi. Jiki a mace ya mike ta yi masa sai ya dawo ya fice. Ajiyar zuciya ya Kwace mata, tana son jin Naufal a kusa da ita, Kila hakan zai kwantar mata da hankali, da gaske ta yi kewarsa tana son jin dan uwanta a kusa da ita. Zakiyya da bakin ciki ya isheta ta rasa me za ta yi? Sai kawai ta fice ta dawo ta ajiye ruwan zafi a dai-dai hanyar da Nasreen za ta wuce ta koma dakinta. Nasreen cikin ikon Allah da ta tashi fitowar sai ta zagaye ta wuce ruwan zafin. Sai kuma ga Umma ta fito tana tafe kamar bata gani ta buge ruwan zafin, ya zubar mata a Kafafu. Ta fasa Kara wanda ya jawo hankalin dukkan mutanen da ke cikin gidan. Zakiyya ta rude iya rude wa musamman da ta ga Kafar Umma ana taba wa tana sabulewa. Hafsat ta gigice ta rike Umma tana kuka. “Wa ya ajiye ruwan zafi a kan hanya?� Zakiyya ta fara kame-kame. Hafsat ta mike a fusace ta shaKo ta, “Gaya min waye ya ajiye wa Umma ruwan zafi? Ba ki isa ki ce Nasreen ba, domin kina sane da makauniya ce.� Zakiyya da ta ji shaka ta ce, “Dama� Dama� Na ajiye ne saboda Nasreen.� Ji kake tas! Hafsat ta dauke ta da mari tana huci, “Ashe ke mahaukaciya ce? Ba ki san Kofar dakinta bane za ki ajiye a nan? Kawai ki ce kin shirya kasheta. Daman Hajiya ta je gidanmu tana neman ta hargitsa mana iyaye shi ne ke kuma_ _ bari ki kasheta ko? Yau sai kema na Kona ki. Hafsat ta fizgota tana KoKarin jefa Kafafunta cikin ragowar ruwan zafin. Umma ta girgiza kai, “Hafsat rabu da ita ba da gangar ta yi ba.� Nasreen tana sauraren su ta yi shiru tana nazarin wani irin Kiyayyace haka da har za a ajiye mata ruwan zafi akan hanyarta, don kawai an ga bata gani?� Sultan ne zaune a Katon dakin taron gabansa kudadene masu yawa, a cikin wata ‘yar akwati. Ya kafe kudin da kallo yana sauraren jawabin manya-manyan mutanen da suke son a kashe wani Case wanda shi yake jagoranta, haka yaga da damar da zai iya kashe Case din, Ogansa da kansa da suka shaKa masa kudi, ya amince za su wargaza Case din musamman yadda yake shirin taba mutuncin su. Yanzu Sultan ne ya rage, duk da suna tunanin Ogansa ya isa ya gaya masa ya ji, amma da Ogan ya yi masu bayanin wanene Sultan sai suka tsorata ainun, don haka suka yi shiri sosai, sannan suka tunkare shi. Kalaman Nasreen sun taimaka masa Kwarai wajen sake cusa masa tsanar damin kudaden da suke gabansa, “Allah ya makantar da kai daga haramun.� A bayyane ya ce, “Ameen Nasreen.� Ya dube su sosai yana nazarin su, “Gaskiya ba zan karbi kudinku ba, wai don kawai ina son in faranta maku in Kuntatawa wasu. Allah ya riga ya amsa addu’ar matata ya nesanta ni ga Haram, ya makantar da ni ta yadda bana iya ganin kudaden da ke zube a gabana. Ku yi haKuri gaskiyata ta kawo ni kujerar nan, bana jin abinda ban aikata, tun ina Karamin dan sanda ba, zan iya aikata shi a yanzu da nake jin kaina na kai. Ku yi hakuri mu bi wannan case din a hankali har mai gaskiya ya yi nasara, amma ba ta wannan hanyar ba. Ina da abubuwan yi a gabana, ban yi tunanin wannan dalilin ne zai sanya 6/11/22, 17:51 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 10 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Sultan ne zaune a Katon dakin taron gabansa kudadene masu yawa, a cikin wata ‘yar akwati. Ya kafe kudin da kallo yana sauraren jawabin manya-manyan mutanen da suke son a kashe wani Case wanda shi yake jagoranta, haka yaga da damar da zai iya kashe Case din, Ogansa da kansa da suka shaKa masa kudi, ya amince za su wargaza Case din musamman yadda yake shirin taba mutuncin su. Yanzu Sultan ne ya rage, duk da suna tunanin Ogansa ya isa ya gaya masa ya ji, amma da Ogan ya yi masu bayanin wanene Sultan sai suka tsorata ainun, don haka suka yi shiri sosai, sannan suka tunkare shi. Kalaman Nasreen sun taimaka masa Kwarai wajen sake cusa masa tsanar damin kudaden da suke gabansa, “Allah ya makantar da kai daga haramun.� A bayyane ya ce, “Ameen Nasreen.� Ya dube su sosai yana nazarin su, “Gaskiya ba zan karbi kudinku ba, wai don kawai ina son in faranta maku in Kuntatawa wasu. Allah ya riga ya amsa addu’ar matata ya nesanta ni ga Haram, ya makantar da ni ta yadda bana iya ganin kudaden da ke zube a gabana. Ku yi haKuri gaskiyata ta kawo ni kujerar nan, bana jin abinda ban aikata, tun ina Karamin dan sanda ba, zan iya aikata shi a yanzu da nake jin kaina na kai. Ku yi hakuri mu bi wannan case din a hankali har mai gaskiya ya yi nasara, amma ba ta wannan hanyar ba. Ina da abubuwan yi a gabana, ban yi tunanin wannan dalilin ne zai sanya a ZAMU TASHI raboni da iyalaina ba, da babu abinda zai sa in fito.� Sultan ya ture kudin gefe guda ya mike ya sara wa Ogansa sannan ya juya Zai fita. Muryar Ogansa ya ji a tsakiyar kansa yana cewa, “Sultan kana da taurin kai, kana da kafiya. Ban san yadda kake yi da iyalanka ba, Ka kwantar da hankalinka, ka ceci rayuwarka da ta iyalanka ka amsa wannan maganar. Ina sama da kai, na baka umarni ka ki bi, mutanen nan shuwagabanni na ne, sun bani umarni ni kuma na baka, amma saboda taurin kai kaqi kallona a � matsayin Oganka. Shin haka dokar aikin mu ya ce? Ka da ka yi wa Oganka biyayya?� Sultan ya dinga kallonsa wani iri, haka kawai yake jin kamar ya make shi kowa ya huta, “Sorry Sir! Dokar aikin mu ya ce in yi maka biyayya, a lokaci guda kuma ya hore mu da kada mu ci hanci, har ya tanadi laifi mai tsauri ga wanda ya yi hakan. Ni ba Barawo bane, bare kudin haram ya burgeni. lyalaina kuma idan ina numfashi babu wata barazana da za ta firgita su, akwai kariya daga Allah, haka ni ne bangon su. Bana tunanin akwai barazanar da za ta sanya idanuna bude wa akan Haram. Kai ma kuma kaji tsoron Allah, domin,,,,,,, talakawa ne ba wakilcin shaidan aka turoka ba Ogansa ya daga hannu cikin bacin rai zai mari Sultan, fuskarsa dauke da murmushi ya riKe hannun Ogan yana yi masa wani shu’umin kallo, sannan ya watsar da hannun ya daure fuska a lokaci guda yace “Aiki nayi na sami wannan matsayin ba siyan kwalin nayi ba, haka ba ta sama na biyo ba, training na shiga nayi kafin insanya unifoam. Ba Karamin jarumi ne zai iya sa hannu a jikina ya zauna lafiya ba. Ka da ka ‘sake gigin taba tsaftataccen jikina, yin hakan zai jawo maka kuskuren da babu shakka sai ka cire wannan kakin da kake taKama da shi. Ba a fada da ni a ci riba. Ina fatan za ka rufa wa iyalanka asiri da rayuwar da kake yi a lullube cikin Kazantar haram ka fita a cikin sabgata.� Ogan bai yi mamakin dukkan irin taurin kan da Sultan yake da shi ba, domin kuwa kowa ya san shi, kaifi daya ne. Mutanen suka yi shiru suna dubansa cike da tsoron lamarinsa.Sultan ya fice abinsa, hakan ya sa daya daga cikin mutanen ya ce, “Haba Me zai sa ka yi masa haka? Mutumin da ya kamata ka lallaba shi? An gaya maka irin wadannan mutanen barazana tana damun su ne? Baka gansa a tsaye ba? Ai mammakeka zai yi ya karya ya watsar. Ya zama dole a bi shi a hankali maganar fushi ba namu bane. Yanzu dai a daga masa Kafa zuwa kwanaki biyu mu ga abinda Allah zai yi. Sultan yana dawowa gida ya zauna a nan falon yana cire safa, yana gama wa ya fara cire maballin rigarsa ya rintse idanunsa yana Kara gode wa Allah da irin ni’imar da ya yi masa wajen guje wa haram. Hafsat ta fito idanunta jajir. Allah ya dora wa yaran Hajiya Salma wani irin sonta, da kuma shakuwa da ita. Musamman_, ma ‘yar auta Hafsat. Sultan ya kafe ta da idanu yana neman Karin bayani. Ta yi masa sannu da zuwa bai amsa ba, ta ci gaba da cewa, “Anti Zakiyya ce ta sa ruwan zafi a hanya wai saboda Nasreen ta tsoma Kafafunta, shi ne Umma ta sa Kafafun ba tare da ta sani ba, yanzu haka Umma tana can Kafarta ta saBule.� Ta Karasa da wasu hawaye. Sultan ya sake kallonta cike da mamakin dalilin da zai sa Zakiyya ta ajiye ruwan zafi saboda Nasreen. Mike wa ya yi cikin fusata, ya tabbata yau abinda zai hana shi kakkarya Zakiyya sai ya ganshi. Nasrecn ya ci karo da ita a bakin Kofa tana rike da hannunta da ke dauke da gocewar Kashi. Yanayin tsayuwarta kamar wacce take iya kallon komai. Sassauta bacin ransa ya yi yana gudun kada ya sake ji mata ciwo. Hucin alamun wucewarsa ta ji, hakan ke tabbatar mata da sai ya aikata abinda ya yi ninya akan Zakiyya. Kara ta sanya ta riKe hannunta , tana fadin “Wayyo hannuna.� Ba Sultan ba, hatta Hafsat sai da ta Karaso wurinta tana riKeta. Sultan ya kama ta, ya kai cikin daki yana mata sannu. Hankalinsa yana kan Zakiyya ji yake kamar za ta gudu kafin ya Karaso. Rike hannunsa Nasreen ta yi hakan ya sa ya dan dube ta, “Nasreen sakar min hannu ina zuwa,� Hannunta ta kai Kirjinsa tana Karasa cire masa maballin riga idanunta cike da hawaye ta ce, “Idan ka yi fushi kada kayi magana, domin kuwa ba kai bane shaidan ne. Fushin da ka yi shi yasa ka watsar da ni, har na sami wannan matsalar, kayi wa Anti Hafsat duka wanda daga baya ya zame maka danasani. Me kake zaton zai ci gaba da faruwa idan har baka iya kaucewa irin fushinka ba? Me kake tunanin zai ci gaba da faruwa idan har kullum sai kayi fushi ka aikata barna daga baya ka dawo kana danasani? Hannunka ba shi da kyau, ko yaya ka taba mutum sai ka ji masa ciwo mai wahalar warkewa, da za ka daure ka nema natsuwa a daidai lokacin da kayi fushi da baka zabi wannan hanyar a matsayin hanyar daukar mataki ba. Anti Zakiyya matarka ce, idan ka daki Kanwarka kana nufin har matanka ma dukan su za ka dinga yi? Gidanka cike yake da ma’aikatan da suke aiki a KarKashinka, idan suka ji ihun matarka, shi kenan sunanka ya lalace, yadda kake da zafi a Office har a gidanka ma zafin gareka, dukan matanka kake yi. Daga nan duniya za su fara yi maka addu’ar yadda kake dukan ‘ya’yan wasu haka za a daki naka, saboda ba su san dalili ba, haka kuma babu uzuri ga mai iya dukan mace. Na yarda Anti Zakiyya ta yi kuskure, amma banda mu da muka sani waye zai je waje yana gayawa duniya dalilin dukan da kayi mata har a saurare shi?� Hannunta ta tura a cikin rigarsa tana murmushi, “Idan ana son a Kuntata min a zagar min miji. Idan aka zageka ji nake kamar in cire zuciyata daga jikina in huta da radadin da nakeji. Ka sauya hanyar hukunci, amma banda duka, idan kana dukan wata ina kallo, ina jin dadi watarana kaina za ka juya, saboda ina da tabbacin dole watarana insaba maka. Duk dan adam tara yake bai cika goma ba. Kayi mata haKuri don girman Allah, kayi mata nasiha ne a maimakon duka.� Sultan ya dade yana duban Nasreen, yarinyar a haka kamar ba za ta iya furta magana mai tsawo ba, amma dubi yadda take tsara kalamai daya bayan daya ba tare da ta ci tangarda a hanya ba. Ji ya yi kamar ankwashe masa. bacin ransa, idanunsa sun bude haka ya janye maganar dukan da ya yi niyyar ya yi mata, sai dai fa za ta sha fadan da sai ta gwammace ya daketa din. Hannunta ya kama saboda abinda take yi masa yana jinsa har tsakiyar kansa, “Nasreen na gode da tunatarwa. Amma kuma dole zan dauki mataki akan Zakiyya. Bata jin tausayinki ne? Kina dauke da lalura sai ta Kara maki wani? Idan na Kyale Zakiyya gobe rushin wuta za ta samo ta sanya maki akan hanya. Wallahi makantar nan naki yana damuna, ko jiya na kira Al-amecn akan matsalar nan.� Fuskarta tana nan manne da murmushi tace “Duk duniya babu wanda ya isa yayi wa bawa abinda Allah bai rubuto ba, ka Kaddara Allah ya rubuta sai hakan ya faru. Ni dai ka zauna kusa da mi har sai ka sami natsuwar zuciyarka sannan sai ka fita, bana son aikin danasani.� Yadda ta marerece tana maganar abin sai ya burgeshi. Ya manna mata sumba a gosh yace“Ko a yanzu zuciyata fes take. Ganinki kadai yana faranta min rai, bare har inzauna kusa da ke inshaki daddan Kamshin nan mai rikita ni. Shi dai Jafar din nan ya huta, yana kuma taimakon ‘yan uwansa maza sosail, musamman yanda yanzu mata kuka lalace da Kazanta, wata kuma ga tsaftar har tsafta amma babu Kamshi, kin ga babu mace kenan.� Nasreen ta dan shiga duhu, don haka ta ce, “Ban gane ba? Waye kuma Jafar?� Sultan ya shafi gashin kanta ya ce, “Na Je gidan Yumnah nabi diddigin Kamshin nan da laushin fatan da kike dauke da shi, duk ta yi min bayani. Yanzu haka idan naje Kaduna gobe insha Allahu zan biya ta Zaria din, don na kira shi a waya ya tabbatar min zan same shi, amma matsalar akwai mutane sosai ne a shagon. Kin ga idan naje Zaria, akwai wata ‘yar uwar abokina Hauwa’u Dan Borno ita zan aika ta siyo min komai. don naji an ce Fatima Dan Bornon ma nan take siyayyan su Humrarta.� Nasreen ta ji dadi sosai, haka za ta so ta je wurin idan idanunta sun bude, Kila ta samu ganin Fatima Dan Bomo a wurnin tana da tarin tambayoyin da ta tanada za ta yi mata, haka ta amince da ingancin kayan Jafar, da ke sabon garin Zana. Tunda har su Fatima Dan Bomo suke zuwa siyayya a wurin, uwa uba ita kanta ta yi amfani da kayayyakinsa ga shi duk ta sauya, kamar yadda ta ji mijinta yana fada. Bata son ta nuna zumudinta ya tambayeta ina ta santa? Domin bai san ta yi karatun littafan Hausa ba. Firgigit ta yi, a lokacin da ta ji anjawo babbar yatsan Kafarta, ta ce ‘Wash! Za ka karya ni ne?� Mikewa tsaye ya yi yana son fice wa, “Ina na isa inkaryaki? Idan na karyaki wurin wa zan je in sami natsuwar barci?� Cike da zolaya ta ce “Wurin Anti Zakiyya.� Har ya buda baki zai ce wannan Kazamar? Sai kuma ya tuna idan yaci gaba da nuna rashin mahimmancinta Za ta iya raina shi, don haka ya wuce kawai yana cewa, iyya lallai ‘yar yarinyar nan ta yi baki kwana biyu, amma na kusa rufe bakin nan.� Kai tsaye wurin Umma ya � shiga, bai yi zaton Kunan har haka ne ba, don haka ya ware idanunsa yana jin zuciyarsa tana jagulewa, da Karfin nasihar Nasreen ya daidaita natsuwarsa. Duk da haka sai da ya dubi Umma yace, “Umma sai na hukunta Zakiyya.Umma ta dube shi cike da takaicin yadda ya je wurin Nasrcen ya kuma dade a wurinta, a maimakon ya fara zuwa ya dubata. Ta ce, “Babu abinda za ka yi mata dan rainin hankali. Ni za ka . raina? A ce maka matsala ta same ni shi ne ka wuce ka fara duba Kanwar uwarka ko?� ; Sultan ya yamutsa fuska, ransa ya sosu Kwarai, sai dai wacce ta isa ce take magana a gabansa, don haka ya KasKantar da kai, ba shi da abinda zai iya kare kansa. “A yi hakuri Umma. Ina ganin Hafsat ta shirya ki mu je a kaiki babban asibiti.� Umma ta tabe baki tana yi masa wani kallo hadi da girgiza kai, “A’a bawan Allah ni kuma a wa? Ka duba tsaf ka gani, an duba min Kafafuna har ansa magani, don haka kaje ka dauki makaunoya ka kaita babban asibiti a bata lafiyar idanu, ba ni Salamatu ba. Ka tashi ka ba ni wuri. Ina nan zan sa ido idan ka san ka cika mara kunya in sake ganin Kafafunka a hanyar dakin Nasreen wai ka je dubata. Na gama kula ka raina ni sosai, saboda ina zama a gidanka ina kuma yi maka dariya.Sakaran namiji, yarinyar da ka rena da hannunka yau ita ce kake jin tsoron ka batawa, kake yi mata biyayya, ka zama sai yadda ta ce da kai. Ka zama mijin tace.� Sultan ya shafi kansa yana jin bakinsa yana masa daci. Ya ce, “Umma kiyi hakuri. Gobe naso zuwa wajen Abba, amma tunda ba ki jin dadi zan bari ki warware tukun.� Umman ta saki baki tana duban danta, wato ba zai tanka wa maganarta ba, sai dai ma ya sauya wata magana. Ajiyar zuciya ta yi, tana son Sultan ya je ya binciko mata gaskiyar lamani, don haka ta ce, “Ina ruwanka da jin sauKina? Ko ka zauna baka tafi ba, ai goben fice wa za ka yi a gidan sai an ganka. Goben ka kama hanya ka tafi ina son jin gaskiyar abinda ke faruwa, kaina yana cikin duhu Sultan. Idan mahaifinka ya yi hakkun ai na kusa dawowa. Ni da nake son ka raba matanka, Nasreen mu koma Kaduna da ita, Zakiyya ta zauna a nan, saboda idan daya tana Kaduna zamu dinga ganinka sosai.� Sultan da yaji kansa ya yi mugun sarawa, ya kafe muahaifiyarsa da idanu babu ko Kyaftawa. Umma ta dube shi da mamaki, “Lafiya kake yi min irin kallon nan? Ko ba za ka bari Nasreen ta koma Kadunan bane?� Sultan ya mike ba tare da ya iya furta koma ba, yana jin lallai a wannan karon Umma sai dai ta yi haKuri idan ma za ta tafi da daya sai dai ta dauke Zakiyya. Ya so Kwarai ya koma dakin Nasreen sai dai gargadin Umma yana nan maKale a kansa, don haka ya koma falonsa ya kwanta shiru a dogon kujera. Yana son zuwa Kaduna da Nasreen, amma yasan hakan ba mai yuwuwa bane. Zakiyya ce ta shigo falon cikin zuciya ya mike kamar zai mareta, suna hada idanu gabansa ya fadi da Karfi. Kokarin addu’a yake yi, amma hakan ya gagara, kamar an riKe bakinsa da cingam. Zakiyya ta ci gaba da yi masa gizo tana sauya masa daga macen da ya tsana, zuwa macen da yake jin sonta yana ratsa shi. Haushinta da yake ji gabadaya ya kau. Bai san lokacin da ya mika mata hannunsa ba. Kamar jira take ta kama hannun tana jifansa da wani shu’umin murmushi. � Ya kasa sarrafa kansa, ya rasa me ke shirin faruwa da rayuwarsa. Ko ma mene ne » mahaifiyarsa ta taimaka Kwarai wajen wannan aikin. Haka ta kama hannunsa suka shiga daki. A ranar sai da dukkan Karfinsa ya Kare wajen Zakiyya, ya sha wahala fiye da tunaninsa. Haka ya kasa ko da motsawa. Ita dai Nasreen ko da ta ji shiru bata damu ba, saboda ta riga ta san da wahala Umma ta sake barinsa. Duk da zuciyarta tana gaya mata sai ya san yadda zai yi ya shigo. Shiru-shiru babu Sultan babu dalilinsa. Tun tana iya jurewa har hawaye suka fara aikin su. Har bayan Sallar isha’i babu wanda ya sa Sultan a idanunsa. Umma ta gaji ta aika Hafsat ta dubo shi. Hafsat tana shiga sashensa ta tsaya tana Kwankwasa Kofa. A lokacin Nasreen ta fito falo, haka itama Umma tana zaune da Kafarta, tana addu’ar Allah yasa lafiya Sultan bai fito ba, gaba daya ta shiga damuwa. Hafsat ta jima a tsaye, sannan Zakiyya ta bude Kofar ta tokare tana dubanta sama da Kasa. “Lafiya kike Kwankwasawa mutane Kofa?� Mamaki yasa Hafsat Kare mata kallo, sannan ta ja tsaki ta ce, “Malama ba wurinki na zo ba, gun Yaya na zo.� 6/11/22, 18:01 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 11 *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Haka ta kama hannunsa suka shiga daki. A ranar sai da dukkan Karfinsa ya Kare wajen Zakiyya, ya sha wahala fiye da tunaninsa. Haka ya kasa ko da motsawa. Ita dai Nasreen ko da ta ji shiru bata damu ba, saboda ta riga ta san da wahala Umma ta sake barinsa. Duk da zuciyarta tana gaya mata sai ya san yadda zai yi ya shigo. Shiru-shiru babu Sultan babu dalilinsa. Tun tana iya jurewa har hawaye suka fara aikin su. Har bayan Sallar isha’i babu wanda ya sa Sultan a idanunsa. Umma ta gaji ta aika Hafsat ta dubo shi. Hafsat tana shiga sashensa ta tsaya tana Kwankwasa Kofa. A lokacin Nasreen ta fito falo, haka itama Umma tana zaune da Kafarta, tana addu’ar Allah yasa lafiya Sultan bai fito ba, gaba daya ta shiga damuwa. Hafsat ta jima a tsaye, sannan Zakiyya ta bude Kofar ta tokare tana dubanta sama da Kasa. “Lafiya kike Kwankwasawa mutane Kofa?� Mamaki yasa Hafsat Kare mata kallo, sannan ta ja tsaki ta ce, “Malama ba wurinki na zo ba, gun Yaya na zo.� ZAMU TASHI Zakiyya ta saki malalacin murmushi sannan ta ce, “Sai ki koma domin bai tashi barci ba, kuma ke baki isa ki sa in tashe shi ba.� Daga ciki Hafsat ta ji muryar Sultan yana cewa, “Zakiyya wace ce?� Cikin isa ta ce, “Hafsat ce, na kuma gaya mata kana barci, sai idan ka tashi.� Ba ta sake jin muryarsa ba, hakan yasa Hafsat ta juya tana cike da mamaki, haka Zakiyya ta dinga jifarta da murmushi daga bisani ta rufe Kofar. Yadda Umma ta ga Hafsat abin ya bata tsoro matuka don haka ta ce, “Me ya faru? Yau na shiga uku, Sultan bai da lafiya ko? Zo maza ki daga ni mu je in ganshi, na san haka kawai ba zai ki fitowa gaida Ubangijinsa ba.� Nasreen kusan ta kusa sumewa_ saboda firgici, bata da burin da ya wuce Hafsat ta yi magana, tana gudun maganar Umma ce, da ba haka ba, da ta riga kowa isowa ga Sultan. Hawaye suka cika mata idanu tana fatan jin jikinsa da sauki. Hafsat da ta yi yaraf a zaune kamar wacce aka cirewa laka, ta dubi Umma idanunta cike da hawaye ta mayar mata da duk yadda suka yi. Nasreen ta saki baki, a lokaci guda jikinta ya Karasa mutuwa murus! Ji take kamar Karya Hafsat take yi ba Dee dinta yake dauke da wannan lamarin ba. Dakin ya dauki shiru na wasu ‘yan dakiKu, Umma ta kasa furta komai, zargin aminiyarta ya darsu a zuciyarta, tana da tabbacin Hajiya Ladidi ta kai sunan danta gidan Malami, kuma burin su ya cika. Haka kowa ya ci gaba da zama jigun-jigun, Umma ta mike domin tana son zuwa ta tabbatar da abinda Hafsat ta gaya mata. Ta jima tana Kwankwasa Kofar amma babu alamun za a bude, sai da ta juya za ta tafi, ta ji alamun bude Kofa. A hanzarce ta juyo tana Karewa Zakiyya kallo, daga ita sai daurin Kirji. Umma ta saki baki galala tana kallonta, daga ciki ta ji Sultan yana Kwala mata kira. Umma ta harareta ta ce, “Ke! Kirawo min Sultan.� Zakiyya ta tabe baki tana dubanta sama da Kasa, “A’a Umma ba zai yuwu yana barci in _tashe shi ba, shi ya bani wannan umarnin.� � Umma ta juya kawai ba tare da ta furta komai ba. Tana fito wa ta dubi Hafsat ta ce, “Shikenan Hajiya Ladidi ta kai sunan dana ankafe shi, sai wani ikon Allah. Yadda ta mayar da mahaifin Zakiyya kafin ya rasu, haka za ta mayar da dana.� Nasrcen ta mike tana laluben hanya, zuwa dakinta. Har ta kusa fita suka ji muryarta tana cewa, “Akwai sanin Allah.� Ta Karasa shigewa a lokacin da wani irin kuka ya taho mata da Karfi. Ta jima tana zubar da hawayenta masu yawa, daga bisani ta tuna kukan babu abinda zai yi mata, don haka ta dinga Salatin Annabi tana jin natsuwa tana zuwar mata. Agogon bangon ya buga Karfe goma na dare, a dai-dai lokacin da gabanta ya fadi da Karfi. Haka Karar bugun Agogon ya ci nasarar isowa har cikin zuciyarta. Ta kasa barci, ta kasa haKurin rashin Sultan. A daddafe ta mike ta dawo falo. A lokacin su Umma sun gaji da jiran fitowarsu sun shige ciki. Nasreen ta zauna shiru ta rasa abinda yake mata dadi. Ji take kamar ta bi shi dakinsa ta kwantar da kanta a kafadarsa ya lallasheta, kamar yadda ya saba. Muryarsa ta ji, wanda yasa ta yi firgigit, sai dai babu idanun da za ta gan shi. Don haka ta duKar da kai hawaye suna zuba, sai yau ta sake tsanar makanta, domin tana son ganin halin da Sultan yake ciki. Muryar Zakiyya ta ji tana cewa, “Sweetheart ka gama kallon labaran mu koma ciki barci nake ji. Ko kuma bari inkwanta a kafafunka idan ka tashi kawai ka dauke ni ka mayar da ni dakin mu.� Tun bayan dora idanunsa akan Nasreen ya tsinci kansa da kunyarta, haka ya kasa amsawa Zakiyya dukkan maganganunta. Da tausayawa yake dubanta, tsoron mitan Zakiyya yasa ya kasa yi mata magana. Dukkansu suna nan zaune, tana son ta tashi, amma _ Kafafunta suna_cikin dabaibayi. Shiru-shiru babu wanda ya _ sake magana, Sai surutan Zakiyya da take yi babu kai. Nasreen bata san tana da kishi ba, sai yau dinnan da Kirjinta ke barazanar rabuwa da gangar jikinta. Ta sha Karyata mata,.tana ganin kawai kishin hauka gare su, haka bata yarda cewa kowacce mace tana da kishi mai zafi haka ba, sai yanzu da ya faru akanta. Ji take da za a mika mata bindiga ace wa za ta harbe babu ko shakka, Zakiyya ita ce mace ta farko da za ta fara rabata da duniyar gaba daya. Sultan ya gama karantar komai a fuskarta, don haka ya sake jin babu dadi. Ko babu soyayya a tsakaninsa da Nasreen akwai Kauna da shakuwa irin wanda ba zai taba gogewa daga zuciyarsa ba. Sai dai da ya yunKura sai yaji kamar ansa Katon dutse andanne shi. Kallon kawai yake yi, amma baya fahimtar komai. Da haka har barci ya yi awon gaba da Zakiyya. Ita kuwa Nasrcen tana nan zaune kamar andasata. Ta kasa danne hawayen da ke malala har cikin baki daga makafin idanunta. Da Karfin addu’a ta mike tana laluben hanya. Za ta kauce hanya ya yi maza ya cire kan Zakiyya da ke jikinsa ya Karaso ya riKe ta. Ji take kamar ta fizge kanta, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, ta tabbata Sultan ya fi Karfin dukkan wulakancin daga gareta. Ko da kuwa kullum zai dinga dukanta yana watso kayayyakinta waje ne za ta durKusa ta bashi hakuri. Shi kadai ne sauran gatanta a duniya. Tana jin hucin jikinsa a cikin nata, wanda*ya haddasa mata kasala, ta Karasa zubewa a jikinsa, ta yi shiru, kamar babu wata halitta a wurin. Shima Karasa rungumeta ya yi jikinsa yana kyarma Dukkansu zuciyoyinau buyawa suke yi da Karfi, yana jin tamkar yayi shekara ne babu ita. Tana jin alamun yana lalubon wani wuri daga sassan jikinta, ta rike hannunsa tana girgiza kai, a hankali kuma ta raba jikinta da nasa, hawaye suna ci gabu da gudu a fuskurta, “Dukkan abinda zai faru da kai, ko na asiri, ko . na gangar ka sanya Ubangyji a farko, iyayenka su biyo baya. Kana da lafiya, ka kasa zuwa gaida Ubangijinka? Kana da lafiya ka kasa zuwa duba Umman mu da ke cikin halin jinya? Mace tana samun nasarar cutar da mijinta ne, a duk lokacin da take aikata kuskure yake biye mata. Idan Nasreen matarka ce, kana ganin kana da hurumin share lamarinta, Ubangijin mu da rayuwarmu take hannunsa ba abokin wasan mu bane, muna halin rashin lafiya ma bai dauke mana gaida shi ba, sai da aka kawo hanyoyi ma bambanta wajen aiwatar da ibada, idan muna halin rashin lafiya. Idan ni matarka nayi maka uzuri babu wanda zai yi maka hakan. Ba a hanaka soyayya da matarka ba, amma kada ka shiga lokacin bautar Allah, kada ka shiga lokacin iyayenmu. . “Dee wannan tarbiyyar akanta ka dora mu, idan ka sauya mu ma zamu iya sauyawa saboda da kai muke koyi har gobe. Ka daina yin azkar ya kamata ka koma ka ci gaba da yi, domin idan ka bar Allah da kwana daya tak! Zai barka da shekara. Allah ba abokin wasan mu bane, ina sake nanata maka. Ibadanmu shi zai sadamu da Rahamar Ubangiji wanda kowa ke nemanta ido rufe. Sai da safe.� Za ta wuce ya sa hannu ya dawo da ita, jikinsa a matukar sanyaye. A kunne yake mata magana, kasancewar itama dukkan maganar da take yi masa cikin sanyi take yi, kuma a natse. Don haka ya yi mata magana shi ma cikin irin tasa natsuwar, “Baby ban san abinda ke damuna ba, na rasa gane asalin matsalata. Ki daina cire kanki a cikin masu daraja agurina, kina da darajar da ke kanki baki san kina da ita ba. Bansan me yake damuna bane, ban san me ya hana ni amsa kiran mahaifiyata ba, ban san me yasa na kasa zuwa in dubaki ba, ban san dalilin da yasa na kasa zuwa gaida Ubangijina ba. Don Allah ki taya ni addu’a in iya cinye jarabawata. Don Allah Nasreen.� Muryarta tana rawa, ta cire hannunsa daga kafadarta ta ce, “Allah ya yaye maka.� Yana . kallonta har ta shige, ya kasa binta kamar yadda zuciyarsa ke gaya masa. Dole ya koma ya dauki Zakiyya suka yi cikin daki. Nasreen dai barci ya Kaurace mata, tun tana sa ran ganinsa har ta cire rai, Zuciyarta kuwa babu abinda bata gaya mata akan mijinta yana can yana manne da Zakiyya, yana bata irin kulawar da yake ba ta. Da gaggawa ta ce, “Astagfirullah.� Ta furta tana mai jin damuwarta tana sauka a hankali. Ta fahimci babu abinda ke wanzar da bakin kishi, da kuma jawowa kai masifar bin bokaye da malamai, wajen ganin ancutar da kishiya, da mata za su gane su cire dukkan tunanin wani abu a tsakanin su da mazajen su babu shakka da an zauna lafiya, da kishiya ta zama ‘yar uwa ta jini, sai dai yanzu zuciyoyin mata sun cika da bakin kishi da mugun tunani, wanda baka isa ka KwanKwasa zuciyar mace ba, bare ka gane ta Allah, wata za ta nuna duk duniya babu wacce take so sama da ke, amma da za ki leka zuciyarta, sai kin fahimei akwai Katon ramin da take hakawa take KoKarin tura ki ciki, kina zurmawa za ta mayar da Kasa ta rufeki. Don haka dole mata su fi yawa a cikin wuta, idan har aka ci gaba da tafiya irin haka. A hankali take addu’a akan Allah ya hanata zuciyar cutar da wata akan dai da namiji. A hankali ta ji zuciyarta tana sanyi sai dai tunanin mijinta da halin da yake shirin kasancewa a ciki sun taru sun hanata sakat Dole ta lalubi bandaki ta doro alwala, ta hau kan dadduma tana nemawa mijinta sauKin kan jarabawar da ke tunkaro shi.Tana son kasancewa mace ta gari agun mijinta, Zakiyya tana ganin wayo ne yasa ta aikata hakan, ta kasa tuna makomarta a nan gaba. Washegari da sassafe Sultan ya shirya da ‘yan sandansa suka wuce Kaduna, kamar yadda ya yi alkawari. Da isowarsa ya sami Abbansa da Naufal da Mairo suna karyawa, a cikin natsuwa kamar babu abinda ke damun su. Sai dai Abba da ke riKe da kofi yana jujjuya shayin ba tare da ya iya ci gaba da sha ba. Sallamar Sultan yasa duk suka dubi Kofar, sun sha mamakin yadda ba su ji hayaniyar shigowarsa ba, kamar yadda sukan ji dirar motoci idan ya shigo. Kai tsaye bisa shimfidar Abban ya Karaso inda suke zaman karyawa. Naufal ya dube shi cike da farin cik1, yana shirin miKewa. Sultan ya girgiza masa kai, suka kama hannun juna. Mairo ta dan durkusa tana gaida Sultan, ya sakar mata murmushi ya ce, “Anti Mairo kina son in sami albarka kuwa? Ban taba jin in da uwa take gaida danta ba. Ki bari in natsa zan biyo ki har in da kike in gaidaki.� Mairo da ke tsananin ganin girman Sultan ta dan sunkuyar da kai, tana jin dadin irin girmamawarsa a gareta, duk da tarin matsayinsa. Abba ya dubce shi, suka sakarwa juna murmushi a lokacin da ya kai dankalin turawa bakinsa yana lumshe idanu, ““Abbana ko karyawa ban yi ba, na fito babban burina in yi tozali da Abbana.�� Abba dai bai yi magana ba, sai murmushi da yake yi, wanda kallo daya za ka yi masa ka gane yana cikin damuwa. Sultan ya saki jiki ya _ ci abincinsa, haka yana yi wa Abbansa hirar Office dinsa, hakan yasa shi ma Abban ya saki jiki yana bashi labarin yadda kasuwancinsa ya kasance. Abin mamaki sai ga shi Abba ya ci abinci sosal. Gaba daya suka yi Hamdala. Duk suka mike domin komawa cikin falon saman kujeru. Sai a lokacin Nautal ya rungume Sultan fuskarsa tana ‘nuna tsantsar farin cikin ganinsa. Sultan ya ce, “Wai! Nasreen tana can tunaninka yasa duk ta rame, bata da zance sai naka, amma kalli yadda kake Kiba abinka baka da wata matsala. Abba me kake bashi ne?� Abba ya ce, ““Maryama za ka tambaya, da ni da Naufal duk kiwonta ne. Mamanka din dai za ka je ka tambaye ta abinda take bamu.� Sultan ya ce, “Nima na zo kenan sai na yi irin Kibar Naufal zan koma.� Gaba daya suka yi dariya banda Sultan da yake jin kamar wani abu yana damunsa. Ya so Kwarai ya tafi da Naufal Abba yace masa ba zai yuwu ba, shi kadai yake debe masa kewa, ga kuma Karatunsa. Naufal ya mike ya fice gun ‘yan sanda, tunda ya kula akwai maganar da suke son tattaunawa. Sultan da ke zaune a Kasa kusa da Kafafun mahaifinsa ya dube shi da kulawa yace “Abba, Umma ta gaya min dukkan abubuwan da suke faruwa. Abba na shiga tashin hankali, ko kuma in ce maka ina cikin damuwa. Amma ina son ka kwantar da hankalinka, na fahimtar da Umma da hafsat kuma ta fahimta sosai, dama kuma bata amince ba. Don haka ka kwantar da hankalinka ina ji a jikina komai ya kusan zuwa Karshe insha Allahu lamarin zai zo kamar ba ayi ba. Idan kana sa damuwa a ranka bana samun natsuwa Abba.� Abba ya saki ajiyar zuciya mai nuni da ya sami natsuwa sosal. “Na gode Sultan. Allah ya yi maka albarka. Bana cikin natsuwata, kalaman mahaifiyarka ya daga min_hankali sosai. Amma yanzu na sami natsuwa, ni dama damuwata kada ta zargeni da abinda tun yarinta ban taba waiwaya ba. Ka je kaci gaba da hakuri watarana sal labari. Sultan ya amsa masa yana ci gaba da cewa, “Abba Zaria zan je akwai shagon da zanje a Zaria din, wai shagon Jafar, zan yi wa Nasreen siyayya.� Abba ya saki fara’a, “Sai ka hada da Zakiyya.� Gabansa ya fadi ras! Jin an ambaci sunan Zakiyya, sosa kansa ya yi ya ce, “Eh amma ba zan karbar masu iri daya ba, ko kuma ita Zakiyya tunda tasan wurare sai inbata kudinta ta siyo nata, itama Nasreen din irin wanda take so zan siyo mata.� Abba ya jijjiga kai alamun ya fahimta. Sultan ya mike ya shiga gun Mairo yana kallon Kofar mahaifiyarsa a rufe, ya girgiza kai. A daki ya sami Mairo ya gaidata sannan ya ciro kudi masu yawa ya mika mata Da Kyar ta karba, ya fito ya tasa Naufal suka tafi Zaria tare. A cikin mota Naufal yake bashi labarin yadda Abba yake kasancewa a cikin damuwa. Sultan ya dafa kafadarsa, ““Kada ka damu insha Allahu komai zai zo Karshe.� Kai tsaye wurin Hauwa’u Dan Borno suka tsaya daga can suka wuce Kasuwan sabon garin. Sai dai bai shiga ba, ya tura Hauwa’u ita ta siya masa komai, ya yi mamakin da ta dawo masa da canji. Kudi ya Kara mata yace itama ta siya 6/11/22, 18:17 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚* CHAPTER 12 KARSHE Book three *BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO* MUN TSAYA Abba Zaria zan je akwai shagon da zanje a Zaria din, wai shagon Jafar, zan yi wa Nasreen siyayya.� Abba ya saki fara’a, “Sai ka hada da Zakiyya.� Gabansa ya fadi ras! Jin an ambaci sunan Zakiyya, sosa kansa ya yi ya ce, “Eh amma ba zan karbar masu iri daya ba, ko kuma ita Zakiyya tunda tasan wurare sai inbata kudinta ta siyo nata, itama Nasreen din irin wanda take so zan siyo mata.� Abba ya jijjiga kai alamun ya fahimta. Sultan ya mike ya shiga gun Mairo yana kallon Kofar mahaifiyarsa a rufe, ya girgiza kai. A daki ya sami Mairo ya gaidata sannan ya ciro kudi masu yawa ya mika mata Da Kyar ta karba, ya fito ya tasa Naufal suka tafi Zaria tare. A cikin mota Naufal yake bashi labarin yadda Abba yake kasancewa a cikin damuwa. Sultan ya dafa kafadarsa, ““Kada ka damu insha Allahu komai zai zo Karshe.� Kai tsaye wurin Hauwa’u Dan Borno suka tsaya daga can suka wuce Kasuwan sabon garin. Sai dai bai shiga ba, ya tura Hauwa’u ita ta siya masa komai, ya yi mamakin da ta dawo masa da canji. Kudi ya Kara mata yace itama ta siya ZAMU TASHI turarukan da Mumran. Cikin KanKanin lokaci Kamshi ya cika motar, yana da tabbacin Malam Jafar yana siyar da manyan turarukan maza, ya sha alwashin zai dawo ya sake siya. Naufal ya ce, “Dee, wasu abubuwa ne masu Kamshi haka? Kamar na taba jin Nasreen da irin Ramshin, duk da wannan yafi nata dadi.� Sultan ya yi ,murmushi ya ce, “Dukka nata ne, ita ta aiko ni.� Naufal ya yi dariya yana jin dadi. Kai tsaye suka dawo Kaduna, a Kasan gada suka tsaya. Nan da nan fuskar Sultan ta sauya, shi dai . Naufal sai kallonsa yake yi kamar ya sami tv. Suna tsayawa, Sultan ya sauka, hakan yasa Naufal bin bayansa ba tare da yasan yana binsa ba. A gaban dan sanda ya tsaya wanda yake tsaye da kayan aikin kanikanci. “Rankashidade muna ci gaba da bincike, sai dai ko waye makashin matar da ta haifi ‘yan biyu a KarKashin mota…� Sultan ya daka masa tsawa, “Wacece ta haifi ‘yan biyu a KarKashin mota?� , Mutumin ya Kame masa ya ce, “Sorry sir! Ina nufin matar da ta yi rayuwa da ciki a wurin. Mutumin yana da wayo, bai yarda anyi magana da shi a wayar sadarwa ba, sai ya tura wani mai suna Alhaji Kabir wanda yake KoKarin nuna cewa shi ne yake da case din, wanda a zahiri ba shi bane. Amma wannan takardun suna dauke da bayanan abubuwan da na samo a dalilin bincike na. Zamu ci gaba da yin bincike har inda Karfin mu ya Kare insha Allahu.� Sultan ya amshi takardun ya bugi kafadarsa, “Aikinku yana kyau sosai. Ina fatan zaku ci gaba a yadda na sanku. Idan muka gano waye Alhaji Kabir babu shakka zamu gano sauran.� Sultan yana juyowa, suka yi ido hudu da Naufal da ke , duban kowa duba irin na mamaki. Sultan yaso ya yi masa fada sai kuma ya kasa. Suna shiga mota ya dinga dauke kansa baya son amsa tambayar da ya gani a cikin idanun Naufal yana sonyu masa. “Deedi wai� Kafin ya Karasa Sultan ya dubi gefen titi ya ce, “Naufal lokacin ina Karami babu abinda yake faranta min rai sama da kallon gefen titi, hakan yana sa ni nishadi.�Naufal ya dan yi dariya ya ce, “Ashe kai na biyo da kallon gefen titi Deedina.� Sultan ya yi murmushi, “Eh ni ka biyo mana. Driver tsaya mu siya kayan marmari.� Suka dan dakata, a lokacin ne idanun Naufal ya hasko masa Mansur, cikin gigicewa ya ce, “Dee ga mutuimin da ya sace mu Can ya ce zai auri Nasreen.� Sultan ya juyo cikin gaggawa, a lokaci guda ya ba ‘yan sanda daman zuwa su cafko shi, sai dai ihun da Naufal ya yi ya ci nasarar isowa cikin kunnuwan Mansur, haka kuma ya ji dukkan abinda yake gayawa Sultan, don haka ya Kara da gudu. Duk Kokarin da suka yi domin ganin sun kama shi, inaaa hakan bai yuwu ba. Hakan ya bata ran Sultan ya so ya kama shi, domin jin wanda ya sa su wannan aiki na * wahalar masa da Nasreen. Haka suka je suka ajiye Naufal wanda ya kasa yi masa tambayar da yake son yi, a dalilin fushi da ya gani a idanunsa. A matuKar gajiye Sultan ya dawo gida. sai dai yana shiga falan bai ci karo da kowa ba, hakan yasa ya nufi’sashen Nasreen tana nan a _kwance shiru. A hankali ya Karaso kusa da ita ya ajiye mata kayayyakin da ya siyo a shagon Jafar, bai yi mayana ba sai jin muryarta ya yi cikin rauni ta ce, “Sannu da zuwa.� Bai amsa ba, sai da ya bata Fake a goshi sannan ya ce, “Yauwa Nasreen. Ga saKon kayan Kamshin ki nan duk ya cika mana mota. Bari in je in gaida Umma.� [Ta kai ta amsa, sannan ta dan tashi da girmamuawa ta ce, “Na gode Allah ya Kara maka budi yasa ka fi hakan. Ina na Anti Zakiyya da su Umma?� Murmushi ya kufce masa. Duk yadda yake cikin bacin rai, in har zai zauna a gaban Nasrren sai ya nemi damuwar ya rasa. “Ban siya masu ba, amma zan ba kowa kudi iya adadin abinda na siya maki din. sai su je su siya ko?� Ya bata amsa tare da sake cusa mata tambaya. Nasreen ta yi murmushi wanda iyakarsa fuska ta ce, “Hakan yana da kyau, amma idan da hali ka basu fiye da nawa, Kila abinda za su siya yafi nawa tsada. Kayi Sallah ko?� Ya miqe yana tafiya yana bata amsa, “Na yi Sallah Nasrcen, zan basu dubu talatin talatin kamar yadda kika roKa. Sai na fito zan sake dawowa.� Yana fita kai tsaye dakin Umma ya nufa ya � sameta tana gyangyadi, tausayinta ya kama shi ya Karaso yana duban ta, “Sannu da hutawa Umma.� Ya gaidata yana KoKarin sunkuyar da kai. Kamar za ta share shi sai kuma ta amsa babu yabo babu fallasa. Haka hafsat ta gaida shi itama babu wata fara’a a tare da ita. Shiru suka zauna babu wanda ya sake yin magana. Zuciyar Umma tana tafarfasa tana jin ashe haka Hajiya Gwayyo taji, a lokacin da ta hana Abba saurarenta? Ashe haka uwa take ji a zuciyarta? Sunkuyar da kai ta yi babu alamun nadama ko danasani a zuciyarta, sai tsabar jin zafin Zakiyya da uwarta da ke sake nuKurKusanta. Ta kira Hajiya Ladidi yafi a Kirga amma ta ki dauka. Ganin shirun ya yi yawa yasa ya mike yana mata Allah ya Kara sauki amma ko uffan bata ce ba. Sultan ya ce, “Oh umarninku na bi na zauna da Zakiyya, wacce nake so kunsa min Katanga a tsakanin mu, ban san ya kike son in yi maki ba Umma. Ga shi yanzu wacce nake bin umarninku saboda ita ta sami abinda take so a wurina.� Ya wuce abinsa, ba tare da ya bari Umma ta ji maganganun da yake yi ba. Tunda ya shige babu wanda ya sake ganin Kyeyarsa, haka Sallar Isha’in ma bai yi ba, sai wajen asubahi da ya tashi ya hada gaba daya. Yana tashi ya wuce Office abinsa. Lamarin da suke ganinsa kamar da wasa abin ya fara yin nisan da kowa yake ji a jikinsa. Wannan lamari bai sa Umma ta sauko daga irin tsanar da take ji akan Nasreen ba. Don haka ne Nasreen ta fi kowa shan wahala, mutumin da shi kadai yake tausaya mata a yanzu bata ganinsa ma. ‘yar Kibar da ta yi duk sun tafi. Babu wanda take sha’awar ya dawo kusa da ita kamar Naufal, ta sani idan da yana nan ba zai taba barin hawayenta su zuba ba. Zaman gidan duk ya fita akanta. Zakiyya yanzu ita ke yin dukkan abinda ta gadama a lokacin da ta so. Umma duk masifarta ta kasa cewa komai ta zuba mata idanu. Addu’a take yi Kunan da ke Kafafunta su warke, za ta tattara ta koma Kaduna sai ta nunawa Hajiya Ladidi kuskurenta. Haka tana nan akan bakanta sai ta tafi da Nasreen, don ba za ta bar gurbatattu biyu a wuri guda ba. Ita kuwa Nasreen kwana biyu idanunta Kaikayi suke yi mata saboda yawan kuka. Yau da kanta ta fito, bayan tana da tabbacin baya cikin falon. Ta dinga lalube har ta iso waje, tana ci gaba da tafiya. Gate din gidan ta nufa da ninyar fita, “yan sandan suka tare ta da tambayar, “Hajiya ina za ki je?� Ta girgiza kai, “Ina son ganin gari ne.� Suka hana ta fita, suna roKonta ta koma, ita kuma ta dage ba za ta koma ba, daga Karshe tasa kuka. Sultan ya fito hannunsa dauke da Kwallo ya hango su, don haka ya Karaso. Da idanu ya kalle su duk suka bar wurin. Jikinta ya bata yana wurin don haka ta sunkuyar da kanta. Ya Karaso ya tsareta da idanunsa, “Nasreen. Ina za ki je?� Ta kasa magana sai ruwan hawaye da suke sake kwaranya. Sultan ya juya yana dubawa ko Zakiyya tana nan, domin ya tsani dukkan abinda zai bata mata rai, haka Nasreen tana nan a zuciyarsa, kawai Zakiyya ce ta yi masu tsakani. Hannunta ya kamo suka zagaya baya, ya rungumeta tsam a Kirjinsa. Rabon da ya ji sanyi irin na yau tun ranar da ya rabu da jikinta. Shinshinarta yake yi da gaske kamar zai cinyeta danya. Ita kanta jikinta rawa yake yi Da kanta ta yi Kasa tana kuka mai ban tausayi. Shima sunkuyawa ya yi kusa da ita yana , mata duban tausayi, “Nasreen kina fushi da Dee ko? Dee ya yi maki laifi ko? Gaya min irin horon da za ki yi min na shirya karba, amma don Allah kada ki horani da barin gidana.� Nasreen ta girgiza kai, “Baka yi min komai ba Deee. Kawai bana jin dadin yadda gidan ya koma ne, ina son ka mayar da ni gidan Yumnah Aminu, ko kuma ka kaini Kaduna in zauna da Abbana. Idanuna suna yi min zafi kamar za su fado.� Sultan ya kafeta da ido yana jinjina irn wannan rama da ta yi. “Kin gaji da ni za ki ce � Nasreen, kin gaji da halina ba wai kin gaji da gidan ba. Gaya min abinda kike so amma banda abubuwan da kika zayyano. Idan na kai ki gidan Abba zai yi fushi da ni, inhar ya ga irin ramar da kika yi. Abbana bai taba fushi da ni ba, sai a ranar da aka sace ku, kina ganin a yanzu idan na kai ki kina da damuwa ba zai tsine min ba? Nasan ba za ki so hakan ba. Haka ba zan iya kaiki gidan Yumnah ba. Idanunki kuma da suke zafi Nasreen kukan da kike yi ta yi yawa. Ya kamata ki ragewa kanki yawan kukan nan. Bari * inkira Al-ameen yanzu sai in ji yadda za ayi. Jibi zan sa dan sandana ya dauke ki ya kaiki a yi ~ maki komai da komai na fita waje.� Nasreen dai ba ta ce komai ba, sai ajiyar zuciya take yi. Zama ya yi akan wani dan baranda ya jawota jikinsa ta kwantar da kai a bisa kafadar da take kewa. Hakan yasa sanyi ya dinga ratsata. Tana jin su suna waya da Alameen wanda yake tabbatar masa su zauna cikin shiri domin likitan ya dawo yana London, don haka a can za.ayi aikin idanun. Sun jima a wurin ba tare da sun dawo cikin gidan ba, har barci ya soma kwasar Nasreen, kasancewar ta dade bata barci sai tashin dare, tana yi wa mijinta addu’a. Iska yake hura mata daga sassanyar bakinsa, tana shaKar iskar wacce take shiga har cikin maKoshinta tana cin nasarar kauda duk wani Kishin ruwa da ke danKare a makoshinta. Haka iska yana sake kadawa, yanayin dole yasa masoya a cikin nishadi kamar yadda ya ci nasarar sa Sultan da Nasreen. Tare suka shigo gidan yana rike da hannunta, sai aka ci sa’a Zakiyya tana falon. Idanu a waje take dubansu, “Yaya Sultan me zan gani haka? Ai na yi zaton ka ce min babu ruwanka da ita domin wari take yi maka, haka kai ka tsani ta matso kusa da kai. Ko dai halinku na maza za ka nuna min masu zama da mata fiye da daya?� � Sultan ya zaro idanu yana jin wani sabon sharri. Lallai idan bai nuna mata halin su na maza masu mata fiye da daya ba, ita za ta nuna masa halin makircin mata, masu son dole sai sun baKantawa ta kusa da su. Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Da gaske ne ya ji wari a jikina, amma ya gaya min kuma na gyara, insha Allahu daga yanzu ba zan sake barin hancinsa ya shinshini wani abu ba Kamshi ba, domin na fahimci warin da na bari ya shaKka ya cutar da shi, har hakan yasa yake guduna.� Zakiyya ta ware idanu tana jin dacin maganar Nasreen, gani take yi Sultan ya zagaya ya gaya mata tana wari shiyasa ma take gasa mata magana. Ta dubi Sultan ta ce, “Au ashe gulmata kake yi kai da matarka? Har kake gaya mata ina wari.� Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Au ashe warin kike yi? Me yasa kike zagin wani bayan ga abin zagi a jikinki?� Zakiyya ta yi kukan kura ta fizgo Nasreen ta haye jikinta ta hau duka. Babu abinda zai baka * mamaki Nasreen ko tari bata yi ba. Ran Sultan ya yi matuKar baci, har bai san lokacin da yasa hannu ya fizgo Zakiyya ba, ya wawwanke mata fuska da mari yana huci. Tsananin azaban marin yasa ta shiga taitayinta ta koma gefe tana zare idanu. Sai da ta dawo hayyacinta ta dage ta kurma ihu, tana fadin yau sai ta karya Nasreen sai dai idan ba zai fita a gidan ba. Umma da Hafsat suna kallon duk abubuwan da ke faruwa, amma babu wanda ya tanka. Sultan ya jawo Nasreen yana dubawa ko ta ji mata ciwo. . Zuciyar Nasreen cike da kuka, amma ta ci alwashin Zakiyya bata isa taga hawayenta ba. Sultan ya ce, “Idan kin cika mara kunya ki zo ki sake tabata ni kuma nayi maki alKawarin kakkarya Kafafunki. Karamar mara kunya, mahaukaciya za ki mutu da hauka da sunan kishi. Idan kinsan kina da kishi bai kamata ki auri mijin wata ba, sai ki nemo mijinki ki kafa masa doka, ba wai mijin da tuni ya yi aurensa aka kawo masa ke a matsayin Kari ba. Aurenki ko auren Kaddara! Nasreen duk abinda za ta ce kada ki tanka mata, mahaukaciya ce take neman abokin da zai taya ta hauka.� Umma ta dubi Hafsat duk suka ci gaba da zuba masa idanu. Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Albarkacinka Dee, Zakiyya za ta yi min abinda ta gadama. Kuma bambancin mai ilimi da jahili aiki da abinda ya sani. Dambe? Haushi? Ba su daga cikin dabi’un da na koyo, ka koya min hakuri da tausasa zuciya a yayin fushi, ba wai haushi da zage-zage ba, irin rayuwar dabbobi da karnuka.� Wayyo Nasreen tana caccaka mata magana, tana jin kowani harafi da Nasreen take yi tamkar tana soka mata mashi. Kalaman Nasreen basu da yawa, amma suna da kaifin da za su iya raba mutum da rayuwarsa gaba daya. Wato ita ce mahaukaciya? Wani kukan kura ta yi ta sake yo kanta, Sultan yasa mata Kafa ta fadi Kasa. Umma ta dube shi, “Sultan amma kana cikin hayyacinka kuwa? Kana son mayar da gidanka dandalin ‘yan kokawa? Idan fada za su dinga yi maka a gida gara duk ka sallame su su tafi. Kana sakin su jibi zan daura maka aure da tsala-tsalan ‘yan mata wadanda suka fi ku, ku kuwa sai ku yi shekaru goma kuna yawo babu mashinshini, da anzo neman aurenku ace ai fada suke yi da kishiyoyi, suna ya lalace. Shi namiji yake, ko me zai yi ado ne akan ku. Kananan ‘yan iska. Kada ka sake kula kowa ni zanji da su, zo ka wuce.� Zakiyya da ta ji maganar takarda sai kuma idanunta suka bude. Duk da haka sai da ta mike tana duban Umma sama da Kasa ta dubi Nasreen ta fara bata amsa, “Uwarki arniyar nan ita ce kare ba ni ba. Ke kuma da kike cewa ya sake mu, ai ni ko ya sake ni babu inda zanje domin naci gida Wallahi, saboda abinda ke cikina dole shi ne magajinsa. � Sultan ya ja ya tsaya cak! Daga barazanar dukan da yake shirin kai mata. Maganar ciki ya razana dukkan mutanen da ke cikin dakin daga ciki har da Umma. * Mu hadu a littafi na 4, kuma na Karshe. 6/29/22, 12:24 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA duk ka sallame su su tafi. Kana sakin su jibi zan daura maka aure da tsala-tsalan ‘yan mata wadanda suka fi ku, ku kuwa sai ku yi shekaru goma kuna yawo babu mashinshini, da anzo neman aurenku ace ai fada suke yi da kishiyoyi, suna ya lalace. Shi namiji yake, ko me zai yi ado ne akan ku. Kananan ‘yan iska. Kada ka sake kula kowa ni zanji da su, zo ka wuce.� Zakiyya da ta ji maganar takarda sai kuma idanunta suka bude. Duk da haka sai da ta mike tana duban Umma sama da Kasa ta dubi Nasreen ta fara bata amsa, “Uwarki arniyar nan ita ce kare ba ni ba. Ke kuma da kike cewa ya sake mu, ai ni ko ya sake ni babu inda zanje domin naci gida Wallahi, saboda abinda ke cikina dole shi ne magajinsa. � Sultan ya ja ya tsaya cak! Daga barazanar dukan da yake shirin kai mata. Maganar ciki ya razana dukkan mutanen da ke cikin dakin daga ciki har da Umma. ZAMU TASHI Sultan yana jin maganar ciki ya cika da farin ciki, Allah ya dora masa son haihuwa a rayuwarsa, har addu’a ya sha tashi cikin dare ya yi akan Allah ya amshi addu’arsa. Danasanin dukan da ya yi mata kawai yake yi. Tsoron kada cikin ya zube ya shige shi. Ita kuwa Zakiyya tana ganin tarkonta ya kama abinda take so ta saki ajiyar zuciya. Umma kuwa kamar za ta yi hauka jin Zakiyya tana dauke da ciki. Nasreen kuma har cikin zuciyarta ta ji dadin cikin nan, a ganinta za ta riKe dan Dee dinta kamar yadda take fata. Umma ta liliyo wani ashar ta watsa tana duban Zakiyya, “Allah ya tsareni da hada zuri’a da ku. Wailahi idan ina numfashi baki isa ki haihu a gidan nan ba. Yaushe za ki haifo mana masifa kamar yadda uwarki ta haifawa mahaifinki masifa.� Nasreen dai tana farin ciki amma kuma ta kasa daina maimaita arniya. Idan ta fahimta mahaifiyar da ta kawota duniya ba ta Sallah kenan? Ya zama dole Sultan ya amsa mata wannan tambayar. Zakiyya kuwa juyawa ta yi ta shige daki abinta. Sultan ya koma gun mahaifiyarsa yana ce mata bai kamata tana irin kalaman nan ba, kawai ta yi masu addu’a. Umma fa duk ta rude tana mamakin yadda akayi har Zakiyya ta yi ciki. Shi kuwa Sultan barin gidan ya yi cike da farin ciki ya rasa me zai yi wa Zakiyya ne domin ya faranta mata? Gaba daya ya mance da wata Nasreen, har sai da yamma-da ya dawo daga Office ya tarar da ita zaune a Kofar gida. Don haka ya daure fuska kamar tana ganinsa, zai wuce ya ji sassanyar muryata tana magana, “Sannu da zuwa Dee. Da. gaske mahaifiyata � arniya ce? Su waye mu? Bamu da dangi ne?� Ta Karashe muryarta tana rawa. Wani irin tausayinta ya karyo masa, dole ya dawo da baya yana dubanta. . A gabanta ya durkusa yana Kare mata kallo. Fuskar nan ta rame babu abinda kake hange sai dogon hancinta, da dan bakinta mai kyau. “Nasreen kuna da dangi, ni Abdullahi Lukman ni ne danginki, ki gayawa kowa da babbar murya, ni ne danginku,haka babu wanda ya isa ya cire ni daga cikin danginki. Na san idan na gaya maki magana za ki yarda da ni, Wallahi mahaifiyarki ta rasu tana cikakkiyar musulma, ita ba arniya bace Zakiyya ta gaya maki hakanne dan ta Bata maki rai, ba dan tana da tabbaci akan hakan ba. Bana son ki baiwa wani.fuskar da zai iya baga maki rai, haka bana son kalaman Batacin ya zauna a zuciyarki. Ina fatan kin fahimce ni?� Cikin shessheKa ta daga kanta. Yau bai da lokacin lallashin ta, don haka ya mike ya shige ciki babu ko waiwaye. Zakiyya an hau dokin zuciya, da Kyar ya lallashe ta suka koma gidan jiya, ko ta kan Umma bai bi ba, wacce take can cikin tashin hankalin cikin da Zakiyya take dauke da shi. Ita kuwa Nasreen jin mahaifiyarta musulma ce ya rage mata irin radadin da take ji. ************** A cikin wani katafaren falo mai tsananin girma, haka yana dauke da kayan alatu. Karya ne ka tsinci kanka a cikin falon nan ba ka rude ka gigice ba, domin kai tsaye zaka Karyata kanka idan aka tabbatar maka a cikin Kasarmu Najeriya kake. Wasu manyan mutane ne, wadanda kallo daya zaka yi masu ka tabbatar da sun ci sun Koshi, haka naira ta zauna masu. Kai tsaye idan akace akwai rashin imani a tattare da su. za ka Karyata hakan. Gaban su kayan marmari ne cike, wanda a Kalla sai su kwashe fiye da Sati suna sha basu Kare ba. Haka daga fasan kafet din da ke malale a tsakiyar falon, wasu banKararrun, kaji ne, da naman rago sai tashin Kamshi suke, sun ji tattasai da albasa. A gabansu wasu yara ne ‘yan kanana da aka kawo masu, kowanne yana duba wacce tayi masa. A Kalla yaran ba za su wuce shekaru goma goma a duniya ba. Kallon wata Katuwa Alhaji Kabir ya yi yana zare idanu, daga bisani_.ya dubi murdeden mutumin da ke tsaye kamar andasa bishiya yace, “Kai Boy ya akayi ka kawo mana yarinyar da ta . wuce shekarun da muke nema? Wannan yarinyar ai ta san namiji idan ka kula da yadda take zazzare idanu.� Gaba daya manyan mutanen suka yi dariya suna sake duban yaran da kayan Makaranta a jikinsu hakan ke nuna cewa daga Makarantar aka kwaso su. Akwai wani Alhaji a cikin su wanda magana bata dame shi ba, da alamun dai shi ne babba a cikin su, domin kalan girmamawan da ake yi masa daban ne. Tunda ake abubuwan nan sai yanzu ya dago yana duban yarinyar da aka ce ta cika girma. Da hannu ya yi masa alamun ya fita da yarinyar, babu musu daya daga cikin su ya fita da ita. Daya bayan daya yake duban su, sannan ya mike yatsa ya nuna wata wacce duk ta fi su Kankanta ya kuma nuna dakin da za u shiga da ita. Wannan ce dabi’ar manyan mutanen masu lalluBe cikin kayan mutunci wato Babbar riga. Dabi’arsu ce a kawo masu yara Kanana su aikata fyade da su, su mayar su watsar a tith, Wannan mummunar aikin ya jawo tarin matsaloli a garin Kaduna, wasu suna mutuwa, wasu kuma suna kamuwa da cutar yoyon fitsan, a ya yin da wasu suke Kare rayuwarsu a gadon asibiti. Haka anrasa su waye suke aikata irin wannan muguwar Barnar a cikin al’ummarmu? Da yawa ana ganin samarin kan layi ne, hakan yasa aka sa masu idanu, tun basu damu da lamarin ba, har su kansu idanunsu ya bude da aikata irin wannan barnar. Babu tausayi bare imani, babu tunanin makoma, bare a tuna cewar watarana za ayi wa ‘ya’yan su. Ko da yake suna ganin suna da wayo ne sun killace nasu suna bata na wasu, abinda suka manta shi Allah babu ruwansa ba a yi masa wayo ko dabara. Su Alhaji Kabiru suna nan zaune suna jin ihun yarinyar nan har ta sume, a lokacin ya kammala da biyan buKatarsa ya sa a ka fita da ita aka kawo wata. Sai da ya tara da yara biyar a lokaci guda, kamar wani injin sannan ya fito ya sa a watsa sauran a cikin daki zuwa anjima. Su Alhaji Kabiru su ma suka shiga da nasu. Sai bayan sun natsa ne, sannan ya dubi Alhaji Kabir yana magana cike da nishadi, “Alhaji Kabir ya maganar case dinnan da yaran nan marasa kunya suke bi? Sun isa su tona min asiri? Tun kafin a haife su nake shaKar numfashi a duniyar nan, kuma nake aiwatar da aikina babu kuskure, me yasa rana tsaka suke tunanin za su iya tona min asiri?� Alhaji Kabir ya saki dariya ya ce, “Mai ja da kai ba a haifi uwarsa ba, bare shi kansa. Ai idan zan yi waya can in da ka turani anan nake yi in cillar da layin. Yanzu halin da ake ciki dai sun . ki hakura, idan ka je wajen garejin nan, za ka sami ‘yan sandansu sun badda kama. Yanzu haka an tabbatar min Nora da iyalanta suna wurin su, sun sama mata wuri mai kyau. Sai dai kuma Nora bata san komai akan mu ba, hakan yasa dukkan bayananta suka zama masu rauni. Ka kwantar da hankalinka ka ci gaba da dukkan abubuwanka idan muna raye babu wanda ya isa ya taba ka. Ka dauka kamar an gama wulaKanta nufin su. Yanzu dai mu yi maganar yara biyar din da Malam ya ce ka tara da su, zuwa anjima sai inkai masa saKon kenan?� Bai amsa ba, sai gyada kansa da ya yi. Yana nan zaune aka dinga fita da yaran da ya lalata masu rayuwa, yana jin wani nishadi a ransa, gani yake duk duniya babu wanda ya kai shi zama cikin natsuwa. Can kamar an tsikare shi ya ce, “Saudatu ta mutu da cikinta, sakamakon sassare ta da yarana suka yi, me zai sa mu amincewa wata barazana akan akwai yara? Wannan ba abinda hankali zai iya dauka ba ne. Shi kuma Khamis S. Idris da yake nuna jarumta da shi kansa Ashmaaan din da muka nemi hadin kansa ya Ki amincewa zamu iya kawo Karshen rayuwarsu kowa ya huta. ‘Yan jarida nawa suka yi mana girman kai muka gama da su? Nawa suka botsare mana muka afka da su cikin rami? Bare wadannan Kananun Kwarin. Idan muka ga da gaske suna son fitar da dayan fuskarmu ina ganin sai a gama masu aiki, ba wai don yana soja ne zai ba mu tsoro ba, sojojin da yawa suna suka tara. Mu sojojin mu da muka basu training kisa suka iya ba duka ba. Wai waye dan sandan da aka ce shima ya tsaya akan lamarin?� Alhaji Kabir ya ce, “Allah ya taimake ka. Ina ganin kamar IG ne ya tsaya a kan lamarin.� Sai yanzu Alhajin ya yi wani shu’umin murmushi wanda ake yi masa lakabi da Alhaji na titi, ya ce, “Mu Allah na tuba ko J ne da Z bai dame ni ba, ban jin ma zai dameni. Kada ku neme shi ku bar su da kansu za su Zo su ce sun � janye maganar. Ban ga dalilin shisshigi a cikin abinda bai shafeka ba, na fahimci neman suna ne. da kuma neman ace IG yana da gaskiya ga shi ya binciko abinda kowa ya kasa bincikowa. Ni kuma ba zan taba barin sunan IG ya bunKasa nawa kuma ya zama a Kasa ba, har gobe ban yarda da rashi ba, nafi yarda da samu.� A nan suka ci gaba da tattaunawa suna yi suna shan kayan itatuwan da ke gaban su. Sultan ya kasa tsaye ya kasa zaune wajen shirye-shiryen tafiyan Nasreen, za ayi tafiyan ne da Jidda matar Al-ameen, da kuma Naufal. Kan Sultan ya dau zafi, haka ya hada Nasrcen da dan sanda suka je akayi mata duk wani abinda ake buKata na tafiya. E passport dinta yana hannunta. Don haka lokaci kawai suke jira jirginsu ya tashi. Ta Lagos za su wuce, don haka za su bi jirgi zuwa Lagos daga can za su wuce. Al-ameen shi zai jagoranci tafiyar tunda Sultan babu dama, kuma daman Al-ameen shi ke da masaniya da asibitin. Asibitin mai suna THE LONDON CLINIC (EYE HOSPITAL AND OPHTHALMOLOGY) Duk wanda yasan fitaccen asibitin London Clinic yasan Eye Centre � ne mai kyau da Kwarewa wajen sanin makaman aiki Karin abin burgewa dan uwanmu ne musulmi zai yi wannan aiki. Sai da ya gama komai sannan ya sanarwa Umma, aikuwa ta ce ita a kasheta a rufe bata yarda Nasreen ta bar Kasar nan ba. Hankalin Sultan ya tashi, yasan abokansa sun yi masa kara, ba zai yuwu sun gama kashe kudinsu sannan ya zo ya ce masu tafiyar babu ita ba. Gabadaya ya fita hayyacinsa, ga rigiman Zakiyya da kullum kwanan mita take yi akan zai fita da Nasreen waje Yau ya gaji ya dubi Zakiyya da yake rasa sonta yake ko kuma Kinta? Ya ce “Haba Zakiyya ya kuke son in yi? Nasreen amana ce agurina a kan me zan bar rayuwar idanunta ya salwanta? Haka zalika babu wasu kudina abokaina ne suka yi min wannan karan Sai in ce bana so? Ko Nasreen ba matata ba ce dole zan nema mata lafiyarta, wannan hakkina ne. Da za ki kwantar da hankalinki idan ~ za ki haihu sai infita da ke ki haihu a duk Kasan__ . da kike so.� Zakiyya ta yi shiru, saboda tana sane da bata da komai a cikinta, ita kanta ta Kosa ta sami cikin nan dan ta kula shi ne farin cikin Sultan. Haka ta Kara samun matsayi ne a ranar da ta furta maganar ciki. � Bayan ya samu ya shawo kan Zakiyya, sai ya koma gun mahaifiyarsa yana rokon ta, amma fir taki yin magana, dole ya danganta maganar ga mahaifinsa, ransa ya yi matukar baci don haka ya kira Hafsat a waya ya ce ta kai mata wayar. Tana dauka ya lullube ta da fada ta in da yake shiga bata nan yake fita ba, ya kuma Ja mata layi akan abinda take shirin aikatawa. Dole ta janye Kudurinta, amma kuma ta gaya masa ana dawowa da ita ya tabbatar ya dawo da ita Kaduna, domin itama komawa za ta yi, ta gaji sosai da rashin mutuncin Zakiyya, uwarta kawai take son gani a wannan gabar. An shirya Sultan shi zai yi masu rakiya har zuwa Lagos. Ana gobe za su tafi, su Yumnah da ibtihal da dukkan sauran jaruman mata suka sami isowa. Umma ta karbe su hannu bibbiyu sai daga baya aka bar matan suna tattaunawa. Sai dai ita Nasreen bata iya cewa komai ba, ta yi nisa a cikin tunani. Yumnah ta tabota ta ce, “Wai me ke damun ki ne haka? Tun da muka zo na fahimci kina cikin damuwa. Ga shi duk kin rame kin lalace. Ko dai tunanin tafiya ki bar Yaya Sultan kike yi? Idan ba SIRRI ba ne ki sanar da mu Kila mu taimaka.� Ibtihal ta dube ta ta ce, “Gara ke, ba jimawa za ku yi ba, ni kuma da na bar Najeriya tun ina da cikin ‘yan biyu fa? Wallahi Yumnah yadda kika san zan mutu da rashin mijina. Babu waya babu wata hanya da zan ganshi. Ai nasha wahala duk da AKARAN KAINA, na hakura da hakan, don ina da tabbacin yana can yana Kwato min ‘yancina. Tasleem ta kafe wayarta da ido tana murmushi, hakan yasa Yumnah ta fizge wayar tana harararta. Kallon su ta yi, sannan ta saki murmushi. “Ni kuma da miskilancin mijina na sha wahala. A lokacin da kaina nake cewa KOWA YA KWANA LAFIYA, shi ya so. Amma yanzu ai na sauke komai. Ki cire damuwa a ranki Nasreen, akwai ranar da za ki yi dariya, indai da gaske ke din Jarumar ‘yar mutan Borno _ ce, za ta kawo maki mafita cikin ruwan sanyi, har ma ta tsatso maki girma da mutunci a idon duniya.� � Shahida ta musKuta ta ce, “Ni har gobe ZUCIYA ta kasa mance Yaya Shahid, sai dai Karfin karamcin Yaya Haisam ya danne komai. Kamar duk cikin ku babu wacce ta kaini shan wahala, tunda har hauka na yi na bi titi. Wallahi sai na ga kamar ni ce ‘yar mutan Borno ba ta so a duk cikin jarumanta.� Khairi ta dube su ta ce, “A’a Shahida, nima nayi rayuwar daji, rayuwar rashin dace da Kawar arziki. Ganin komai nake yi kamar A MAFARKINA. Amma yanzu ai ya zama labari.� Jidda ta yi tagumi daga bisani ta janye tana cewa, “Allah ka sakawa mijina da alkhairi. Uncle Al-ameen ya bani kulawa a lokacin da ya kamata ya daure ni ya jefar a masai. Na ba shi ciwon kai amma yana tare da ni. Daga Karshe ya kawo ni cikin zuri’arsu na sa masu damuwa, a lokacin da na shaKu da su aka kashe min su. Tabbas na amince AKWAI LOKACI, da komai zai zama labari. Mu dai ci gaba da bin ‘yar mutan Borno na tabbata za ta ci gaba da hada mana zumunci mai Karfi ta yadda mutanen duniya za su yi koyi da mu, wajen hada kai da tallafawa dukkan macen da take da buKatar taimako. Zumuncin mu ya fita daban ba irin nasu bane. Nasreen ki gaya mana damuwarki ko muna da shawarwari, idan kuma abin ya fi Karfin mu sai mu dangana da uwar dakin mu Fatima Dan Borno.� Gabadaya suka yi na’am da zancen. Muslima ta ce, “Ni ma nasha wahala, har dan fashi na aura. Allah ya saka wa Mahbub da alkhairi ya Kara masa kwarjini a idon duniya. Idan kana yin abu baka tuna MAFARIN LAMARIN, dole abin zai kwabe maka, da muka dogara ga Allah ba ga shi yanzu ya zama labari 6/29/22, 12:30 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Tabbas na amince AKWAI LOKACI, da komai zai zama labari. Mu dai ci gaba da bin ‘yar mutan Borno na tabbata za ta ci gaba da hada mana zumunci mai Karfi ta yadda mutanen duniya za su yi koyi da mu, wajen hada kai da tallafawa dukkan macen da take da buKatar taimako. Zumuncin mu ya fita daban ba irin nasu bane. Nasreen ki gaya mana damuwarki ko muna da shawarwari, idan kuma abin ya fi Karfin mu sai mu dangana da uwar dakin mu Fatima Dan Borno.� Gabadaya suka yi na’am da zancen. Muslima ta ce, “Ni ma nasha wahala, har dan fashi na aura. Allah ya saka wa Mahbub da alkhairi ya Kara masa kwarjini a idon duniya. Idan kana yin abu baka tuna MAFARIN LAMARIN, dole abin zai kwabe maka, da muka dogara ga Allah ba ga shi yanzu ya zama labari ZAMU TASHI ba? Mata suna kuka da halin maza amma mu mun fita daban. Mazajen mu sun kasance ‘yan Aljannah masu koyi da fadin Allah da Manzonsa.� Nasreen ta dago, tana jin damuwa tunda bata iya kallon su, ta ce, “Ina jin damuwa dukka jaruman ‘yar mutan Borno suna iya ji suna iya ganin junan su, amma ni akwai sabanin hakan a tare da ni. Ko da yake na yarda na amince ni RUBUTACCIYA ce, in ji Abbana da Deedina, haka ma dan uwana Naufal yana yawan gaya ° min hakan. Ku yi min hakuri idan na sami lafiyar idanu yadda zan ganku sosai, sai mu ~ tattauna. Gabadaya sun yi na’am da _wannan maganar. A ranar a gidan Sultan suka kwana su dukka, washegari abin burgewa, dukkan su suka shiga kitchen kowacce tana baje basirarta wurin girka abinda ta fi Kwarewa. Cikin KanKanin lokaci gidan ya cika da Kamshi. Jidda tana hada lafiyayyan zobonta suka ji muryar Zakiyya a bayan su, “Sannunku da aiki, naso in fito in tayaku wani abun, sai dai ina wurin mijina ina bashi tasa kulawan.� Jidda ta fara dagowa kasancewar har yanzu ba wai ta daina halin nata gaba daya bane ta ce, “Oh wai a hakanne kike kula da miji? Dube ki fa, ko wanka baki yi ba. Matsalata da wasu matan kenan, sun Kware wajen biyayya akan shimfida, amma sun kasa gane me miji ke so. Ni ki je ki tambayi wacece ni, idan Kazanta kike takama da ita Jidda ta take ki, amma da na fahimci babu amfaninsa ai na watsar. Ko da yake ni girman Kauye ce ba girman mutanen Kaduna ba.� Mamaki yasa Zakiyya zuba mata idanu, domin dai bata taba ganinta ba, za ta yi mamakin dalilin da zai sa ta dinga danKara mata magana. Kai tsaye zuciyarta ta gaya mata Nasreen ce ta gaya masu komai. Yumnah ta dago tana murmushi, ta so a ce Six lover’s suna kusa da tuni ta yi masu yaren da su kadai suke fahimta, kuma za ta samu amsar da take da buKata. Duk da hakan sai da ta furta. “Oh su Roro ba a iya samun wuri ba, sai a buge da watsa na doki a tsakiyar ka?� Gaba daya sun fahimce ta, tana nufin Attachment din da ke kanta. Musulima ta yi saurin karbe zancen, “Akwai abin tausayi, musamman yadda Uwale ke manna kashin kaza mai kwanci a dai-dai Kasan na shanu.� Sun fahimceta, kashin kaza mai kwanci wari ne da shi, tana nufin Kasan mamanta ba a wanke wa, musamman yadda suka zube kamar wacce ta shayar, ta tabbata akwai wari a ciki, Dukkansu suka yi murmushi. Za su ci gaba da magana, Nasreen ta shigo tana cewa, “Don Allah duk wacce ta gama ta zuba min, Dee yana ta tambayar ba a gama bane? Nima kuma ina da buKata.� Zakiyya ta shaKo wuyan rigarta, tana huci, “Ke kika gaya wa ‘yan gidan nan sirrin cikin gidan nan ko? Yau sai na kakkarya ki idan ya so daga can sai a duba lafiyar Kafar.� Jidda ta juyo a fusace tana dauraye hannunta, Yumnah ta riqe rigarta. Hakan yasa ta! waiwayo tana duban Yumnah. Dole ta sakar mata hannu. Tasleem da sauran gaba daya suka isa har gabanta suna dubanta. “Idan kika taba ta, babu shakka sai naki Kafafun sun karye.� Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Sakar min kwalar riga, bansan me yasa idan baki yi haushi ba, bakya jin dadi. Na fada maki Zakiyya ke karya ce, wacce kullum take haushi a titi ana korarta da dutse. Kin Kware a dambe da wulakanta dan adam, kin ce miji na bar maki abinki, shi ne yanzu duk bai yi maki ba sai kin tozartani a gaban jama’a? Kin ji kunya Wallahi, kin yi girman banza! Kina nan kina dariya duniya tana can tana zaginki. Yabawar duniya tana taimakawa har zuwa makwancinki. Kin fitar da halinki kin jawowa kanki. Duk yadda miji ke sonki idan kin kasance daga fitinannu kin zama koma baya a wurinsa, wannan ba sai na gaya maki ba, nasan kin san hakan.� Sau tari idan Zakiyya tana rigima da Nasreen, kaifin kalamanta kawai take tsoro, domin duk ranar da ta gaya mata magana kwana take babu barci. Jidda ta samu ta Karaso ta fizgo Zakiyya daga irin riKon da ta yi wa Nasreen ta waska mata mari mai tsananin zafi. Ta hankada ta baya. “Ki je ki gayawa duk wanda ya daure maki gindi ni Jidda Junaid na mareki.� Zakiyya ta fita da ihu tana fadin ankasheta. Su kuma suka ci gaba da aikin su. Kowa zuciyarsa babu dadi. Ita kuwa Zakiyya kai tsaye falon ta shiga ta sami Sultan da su. Al-ameen suna tattaunawa. Zakiyya ta shigo tana kuka ta zayyana masa komai. Sultan bai ji dadi ba, amma saboda kawaici ya ce, “Ke kika jawo. Kuma babu yadda za ayi Jidda ta mareki haka kawai dole da abinda kika yi Al-ameen da ransa ya yi matuKar baci ya dubi Zakiyya, “Kiyi hakuri Zakiyya zan dauki mataki akanta.� Zakiyya ta juya tana kuka, Al-ameen ya mike yana huci. Sultan yace’menene haka? Don Allah zauna kada ka bata mata rai, ta ce ta fasa raka mu. Ka san dai halin Jidda.� Al-ameen ya koma ya zauna bai ce komai ba. Suna nan har su Jidda suka fito da abincin da ( suka girka suna shirya falon. Jidda da kanta ta ~ kaiwa Umma komai sai albarka take sa masu. Tana shigo wa, Zakiyya ta leKo tana son ganin irin hukuncin da zai yanke a kan Jidda. Za ta fice yasa hannu ya fizgota ta fada jikinsa, ta zaro idanu sosai, “Me na yi maka don Allah?� Ta fada tana me zura idanunta a cikin nasa, sai da ta tabbatar da ta ci nasara sannan ta zame kanta tana dubansa. Da Kyar ya ce, “Wai me Zakiyya ta yi maki kika mare ta? Ba ki jin magana ko?� Kanta ta dora a kafadarsa tana magana cikin natsuwa. “Ba haka bane shigowa ta yi na ganta duk datti, sai na gaya mata idan Kazanta ce bata kaini ba, nayi mata maganganu, shi ne da shigowar Nasreen ta shake ta, wai sai ta yi mata dukan da idan muka fita waje sai dai ayi aiki biyu. Ni kuma da naga taki sakinta na dora mata tafi.� Ta Karasa maganar da dago kanta ta dan shafi fuskarsa ta ce, “Ka ji abinda ya faru.� Dukka dakin suka yi ajiyar zuciya. Sultan kuwa jikinsa ne ya yi sanyi ya ce, “Matar da ke dauke da juna biyu menene nata na cewa za ta yi dambe?� Yumnah ta juyo tana dubansa, “Waye ke da cikin? Ba dai Zakiyya ba?� Ya gyada kai yana dubanta, “Zakiyya dai.� Ba ta sake magana ba, suka shirya masu komai._—_Jirgin yamma za su bi don. haka kowa ya gama shiryawa, sai a lokacin idanun Nasreen ya fara kawo Kwalla. Naufal ya Karaso kusa da ita yana magana Kasa-Kasa, “Nasreen kada kiyi kuka idanunki za ki taimakawa. Ta gyada kanta. Motocin masu dauke da sunan dukkan littafan da suka fito a ciki, sune a jere a hanya za su nufi Airport. Da Kyar Umma ta yi masu addu’a ita kuwa Zakiyya dakinta ta shige abinta. Hafsat ce ma ta raka su har wurin mota. Haka su Al-ameen suka wuce da Sultan wanda bai gayawa kowa zai yi rakiya zuwa Lagos ba. Da isowarsu ke da wuya suka nufi masauki domin sai gobe za su wuce London din. Nasreen bata shiga huldan Sultan ba, sai ma ware kanta da ta yi ita da Naufal ta bar Jidda da ke maKale da mijinta. Sultan ya fahimci akwai + wani abu a zuciyar Nasreen tunda ya ga tana gudunsa. Gajiya ya yi ya Karaso wurin su hannunsa rike da power Horse da shansa ya zame masa jiki. “Hutawa kuke yi, kuka ware Dee dinku?� Nasreen ta dan yi yaKe, Naufal ya dube shi yana dariya, “Dee mun barka ne kaima ka huta.� Idanun Sultan suna manne akan Nasreen. Dubanta ya sake yi ya ce. “Nasreen babu abinda ke damun ki?� Bata yi magana ba, sai daga kanta da ta yi. A tsakiyar su ya zauna suna dan taba hira da Naufal. Kiran Abba ya shigo wayarsa ya dauka yana fadin gata Abba. Ya sawa Nasreen wayar a kunne. Tana dauka ta gaida Abba cikin natsuwa. Abba ya ce, “‘Nasreen na sanki da Addu’a ki sake dagewa, mu ma nan muna nan muna yi insha Allahu za ayi aikin cikin nasara. Allah ya kaiku lafiya.� Muryarta tana rawa hawaye suna zuba take godiya. Sultan ya karbi wayar ya fice yana magana. Naufal ya dubi Nasreen cikin takaici ya ce, “Na ga Deedinmu yana maki magana kina sharewa ne? Me yake damunki?� Nasreen ta ce, “Naufal ina ta son insami dama in gaya maka. Dee yana KarKashin ikon Zakiyya ne a yanzu, ba ya kula ni baya zuwa in da nake. Umma ta yi min, Zakiyya ta yi min, shima kuma baya tausayina., Ka fada min me zan yi? Na gaji da wannan abin.� Naufal ya dube ta ya ce, ““Haba Nasreen, ke da ya kamata kiyi masa addu’a? Ki daina fushin nan tunda tafiya za ki yi mai nisa, ko me Deedi zai yi ya fi Karfin wulakanci daga garemu, mu zama masu tuna alkhairi ba sharri ba. Ki dauka ya isa ya aikata komai na cin mutunci akanki, ba tare da kin ji kin gundura ba. Idan yana ganinki a cikin damuwa shi ma zai damu, don dai baki gani ne da kin ga yadda yanzu fuskarsa ta sauya a lokacin da yake kallonki.� Bata ce komai ba, ta yi shiru kamar marainiya. Zuwa can suka je suka ci abinci kowa ya gabatar da Sallah, sannan suka yanke shawarar zuwa wani park mai kyau domin baiwa idanunsu abinci. Al-ameen yana kula da yanayin da Sultan da Nasreen suke ciki, don haka ya jawo Naufal da Jidda suka nausa wani wurin. Nasreen ta ji ankamo hannunta, ta gane hannun Sultan ne don haka ta saki ajiyar zuciya ya kamota suka zauna a wani wuri. Kwantar da kanta ta yi a kafadarta ta yi shiru. Bai dubeta ba ya fara magana, “‘Babyna fushi kike yi da ni? Ki yi hakuri babu wanda ya taba yin hakuri a Karshe ya tabe. Mai haKuri shike da nasara.� Nasreen ta sake narkewa a jikinsa, tana jin nasihar Naufal tana ratsa ta. “Babu abinda kayi min mijina, idan da akwai shi ma na yafe maka duniya da lahira. Ba ka ba ni kudi ba, amma ka gina min rayuwata wanda a yanzu kudi bai isa ya siya ba. Ka bani kulawa. Da gaske nake yi na yafe maka dukkan abinda kay min da ma wanda za ka yi min anan gaba. Sumba ya yi mata a tsakiyar kanta sannan ya shafa kan. “Na gode Nasreen. Ki dAina kuma cewa nayi maki abubuwa, idan kina fadan hakan sai in yi tunanin kamar ba dolena bane yi maki wadannan abubuwan. Ki dauka ya zama dole in yi maki kin ji?� Shiru suka dan yi sannan ya ce, “Gobe za ku tafi ku bar ni. Zan yi kewarki sosai.� Murmushi ne manne a fuskarta, “Babu wata damuwa tunda muna kwana mu tashi baka ganni ba, baka j1 muryata ba, don haka wannan tafiyar ba za ta daga maka hankali ba, insha Allahu zamu je lafiya mu dawo lafiya.� Ya gane abinda take nufi, da yake bai da abin kare kansa sai ya yi shiru. Can ya ce, ; “Nasreen akwai abinda kike� son ki yi min * magana akai, idan kika bude baki sai ki fasa. Gaya min mene ne?� “Babu komai, Dama so nake inrokeka ranar da za a bude idanuna idan aikin ya yi kyau ina son ka zama mutum na farko da zan dora idanuna akansa. Kai kadai nake so ka zama mutum na farko, Naufal zai zama na biyunka insha Allahu. Ka yi min wannan alKawarin.� Shiru ya yi yana tuna ayyuka ne a gabansa ba na wasa ba, amma yana jin ba zai iya ce mata a’a ba a irin halin da take ciki, don haka ya ce, “Babu damuwa, zanyi iya bakin kokarina inyi hakan ya faru. Na gode da kika zabeni a cikin mutane na farko da zan hada idanu da ke. Wannan karramawar ba zan taba mance ta ba. Ina sonki Nasrcen, soyayyarki tana ilata ni a duk lokacin da ban ganki ba. Nasreen baki gani ne da sai kin tabbatar da raman da na yi. Zakiyya ta zame mani masifa, idan ban yi abinda tace ba, ji nake kamar an zuba min karara.�� Nasreen ta ce, “Kullum sai na yi maka maganar ibada, amma sai kayi fatali da maganata, ka nesanta kanka da Allah shiyasa wannan abubuwan suke ta faruwa da kai. Kadage da addu’a ka yaki duk mai nufinka da ; sharri.� Ya ce, “Babu komai zan sake dagewa, idan zan je Masallacin sai in ji kamar ansa igtyoyi andaure ni.� Suka sake yin shiru, can yace “Barci nake ji ko za ki raka ni?� Bata karga mayana ba, wayarsa ta dauki kara. Ganin lambar Umma yasa ya dauka, “Gidan uban wa kaje? Ashe da kai za a tafi lagos din shi ne bani da mutuncin da zaka gaya min?� Sultan ya shafi kansa kamar tana ganinsa ya ce, “Umma ki yi hakuri don Allah, gobe insha Allahu zan dawo.� Umma ta ce, “Ya yi maka kyau Sallamammai. Saura ka takura mata tunda kana sane aiki za ayi mata.� Umma ta fada haka cike da damuwa da addu’ar kada Sultan ya aikata wani kuskure da zai hada jininta da shegu. Sultan ya dubi Nasreen yana sauke wayar, yasan ta ji dukkan abubuwan da Umma take gaya masa, sai ya share kawai Da daddare kowannen su suna dakin su, Nasreen tana kwance a Kafafun Sultan yana aika sako ta Email dinsa. Bayan ya gama ne ya daga ta ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito, itamia ta shiga tayi wanka da ruwan da ya tara mata ta nufi ‘yar Jakarta ta shafa man Kamshin da ya karbo mata daga shagon Jafar, ta shafe jikinta. Kamshin yasa ya dago yana dubanta da Katon Hijabi a jikinta. Murmushi ya Kwace masa, gaba daya ya fara mance sakon me yake aikawa 6/29/22, 12:36 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Nasreen ta ce, “Kullum sai na yi maka maganar ibada, amma sai kayi fatali da maganata, ka nesanta kanka da Allah shiyasa wannan abubuwan suke ta faruwa da kai. Kadage da addu’a ka yaki duk mai nufinka da ; sharri.� Ya ce, “Babu komai zan sake dagewa, idan zan je Masallacin sai in ji kamar ansa igtyoyi andaure ni.� Suka sake yin shiru, can yace “Barci nake ji ko za ki raka ni?� Bata karga mayana ba, wayarsa ta dauki kara. Ganin lambar Umma yasa ya dauka, “Gidan uban wa kaje? Ashe da kai za a tafi lagos din shi ne bani da mutuncin da zaka gaya min?� Sultan ya shafi kansa kamar tana ganinsa ya ce, “Umma ki yi hakuri don Allah, gobe insha Allahu zan dawo.� Umma ta ce, “Ya yi maka kyau Sallamammai. Saura ka takura mata tunda kana sane aiki za ayi mata.� Umma ta fada haka cike da damuwa da addu’ar kada Sultan ya aikata wani kuskure da zai hada jininta da shegu. Sultan ya dubi Nasreen yana sauke wayar, yasan ta ji dukkan abubuwan da Umma take gaya masa, sai ya share kawai Da daddare kowannen su suna dakin su, Nasreen tana kwance a Kafafun Sultan yana aika sako ta Email dinsa. Bayan ya gama ne ya daga ta ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito, itamia ta shiga tayi wanka da ruwan da ya tara mata ta nufi ‘yar Jakarta ta shafa man Kamshin da ya karbo mata daga shagon Jafar, ta shafe jikinta. Kamshin yasa ya dago yana dubanta da Katon Hijabi a jikinta. Murmushi ya Kwace masa, gaba daya ya fara mance sakon me yake aikawa ZAMU TASHI cikin wayarsa? Da kansa ya tako ya jawo ta � gabadaya jikinsa tayi luf’a Kirjinsa. “Babyna ina son Kamshin nan, idan naji rikitani yake yi.� Yana magana ne yuna aika mata sakonni. Ita kanta Wasu maganganu take yi wanda bata san kansu ba. Kai tsaye suka yi wa kansu makwanci a faffadan gadon suna jin wata natsuwa tana shigarsu. Da gaske sun yi kewar juna, Sultan ji yake kamar ya yi shekara rabonsa da ita. A hankali ya yi mata magana a kunne, “Baby kinyi kewata?� Ba ta yi magana ba, sai daga kanta da tayi yace, “Ok nuna min irin kewata da kika yi sai in yarda Kunya ta sa ta cusa kanta a Kirjinsa tana ‘yar dariya, a lokaci guda tana zakuda kafada alamun ba za ta iya ba. Washegari bayan sun karya ne suka hau shiri babu ji babu gani. Ita dai Nusreen gani take yi kamar ma ba za ta sake dawowa ba, kamar ta tafi kenan. Da suka isa filin jirgi ne idanunta suka kawo hawaye, yasa hannu ya dauke su, ya kamo kafadanta, “Me yasaki kuka? Ko baki gaji jiya bane insake mayar da ke gado in yi maki abinda yafi hakan? Kwanciya ta yi a jikinsa tana murmushi mai hade da hawaye, tana girgiza kai, sannan ta sa dan yatsanta ta ce, “A’a kai ne bana son intafi in barka. Ka kula min da amanar kanka, ka ci gaba da yi wa Umma biyayya. Daga Karshe ka kiyayi shiga hakkin Allah. Allah ya dafa maka a dukkan lamuranka na alkhairi, ya nesantaka da dukkan wani sharni. Addu‘ar iyaye tana tare da kai, bana tunanin ze ka tabe“Ina son ka Dee, na san kasan hakan kuma zaka ci gaba da riKe hakan a zuciyarka, ko bayan raina. Sai watarana.� Ta Karashe muryarta tana rawa. . Hannunta ya kama dukka biyun yana duban su masu kyau da haske. Ya manna masu kiss � wanda har sassanyar yatsunsa suka sauka abisa hannun. Ta ji sanyi har cikin zuciyarta, hakan ya haifar mata da sakin ajiyar zuciya a bayyane. “I love you too, Baby Girl.� Bata iya sake yin magana ba, ta juya abinta, tana jin wasu hawaye sabbi suna sauka daga idanunta. Naufal ya Karaso ya rungume Sultan, ya ce “Ka cika dukkan sharuddan kasancewarka Uba. Allah ya biyaka da gidan Aljannah, ya sakawa dukkan mutanen da suka yi sanadin tafiyar ‘yar uwata. Ba zan manta wannan abun ba. Mum gode Father.� Ya sake rungume shi hawayensa suna ci gaba da sauka a jikin Sultan. Gaba daya jikin Sultan ya muta ya rasa meke masa dadi? Ya yi Karfin halin dago shi yana duba shi, tare da share masa hawayensa, “to maza azo a wuce saura kaje kana yi masu Kauyanci don nasa a daukar min dukkan abinda ke faruwa acan. Kai ga mai “yar uwa ko? Maza wuce kada a tafi a barka kukanka ya fara, dan wannan kukan ta gulma ce.� Naufal ya yi dariya shima. Alameen ya Karaso a jokacin da Jidda take rike da Nasreen. Suka mikawa juna hanno suka gaitsa tare da rungume yuna. Sultan� ya fara magana cikin damuwa, “Prince ba ni da abinda zan ce sai Allah ya biyaka. Kayi min dukkan abinda wani dan uwanka ma ba zai iya yi maka ba. Kun nuna min Kauna tunda kuka nunawa Nasreen. Kasan komai ba sai na sake tunatar da kai ba, ka kula min da Nasreen. Na gode da wannan sadaukarwar.� Al-ameen ya yi murmushi, “Ba wannan ne a gabanmu ba, samun lafiyar idanunta sune babban matsalolin mu. Idan kana gode mana sai muga kamar bamu cika sharuddan zama ‘yan uwa ba. Ka dinga cin abinci sosai Abdullah, domin ka rame da yawa, ya kamata Nasreen ta bude idanunta ta ganka kafi da cika da kwanciyar ‘Rankali. Ka bar damuwa da Zakiyya idan ba haka ba, za ta iya kasheka ba tare da ta yi asara ba.� Sakin juna suka yi yana tabbatar masa zai yi abinda ya ce masa. Ba ya son yin Sallama_ da Jidda don haka ya ce wa Al-amecn, “Ka fayawa ‘yar Kauyen matarka, saura ta je can ta ga turawa ta manne masu tana cewa, ‘yan uwan mamanta ne, ko kuma ta ga mutum ta yi zaton gunki ne tana shafa fuskarta.� Al-ameen ya yi murmushi yana ccwa, “Wallahi ka ci bashi za kuma ka biya shi.� Haka suka tafi jirginsu ya daga, Sultan kuma ya bi jirgin da ya yi booking ya koma Abuja cike da damuwar rashin Nasreen. A can gida bayan Umma ta gama waya da .Sultan Zakiyya ta fito tana waKe-waKe saboda ta ji lokacin da Umma take waya da Sultan, kuma ta kira shi yaKi dagawa, don haka ta fito da rashin mutuncinta. Kafar Umma ta take da Karfi Umma tasa Kara, hakan yasa Hafsat fitowa da. tana duban Umman. Jin irin sayin da take yi wa Zakiyya ne ta fahimi abinda ke faruwa, don haka ta dora mata tafi a fuska tana huci. “Ke uwata ba sa’arki ba ce. Butulu kawai mun yi maki rana kin yi mana dare. Ki bar ganin ana Kyaleki wawuya wai idan an tambaye ta wai tana da ciki, bacin mun san komai babu komai a cikin. Ai shi ciki ba a Karyarsa domin nan da watanni uku dole ya bayyana kansa.� Zakiyya ta yi kukan kura za ta shako Hafsat Hafsat ta nuna ta da yatsa, “Idan kika yi tsautsayin kwatanta hakan zan baki mamaki, don Wallahi sai kin koma gida kin yi jinyar kanki. Kada kuma ki ce ban gaya maki ba.� Dole Zakiyya ta dakata da abinda ta yi ninya, ta koma daki tana kuka ta gayawa uwarta, hakuri ta bata ta ce ta barsu tana nan tana sabon shiri akan su. Sultan yana isowa gida ya sami Umma ta gama shiryawa tsaf tana zaman jiran Sultan. Yana ganin abinda ke faruwa ya dubi Umma cike da mamaki ya ce, “Umma ina za ki je?� Umma ta fara hawaye ta ce, “Sultan ni zan tafi. Zakiyya ta ci mutuncina a gidan nan, haka kaima baka dauke ni a matsayin uwa ba. Zan koma gun mijina na tabbata shi kadai yake sona ko da kuwa nayi wani mugun abu ne.� Zakiyya ta fito tana taunar cingam, ta dubi Sultan ta mika masa takarda fara Kar da biro, “Ka sake ni ba zan iya ba. Kuma cikin nan zubar da shi zan yi. Ba zai yuwu wasu can su dake ni baka ce komai ba, haka Salamatu ta ce za ta kai hannu jikina. Dubi fuskata Hafsat ta mare ni.� Sultan ya dubi fuskokin kowa ya tabbatar da ba Karamin abu akayi ba. Ya riga yasan Zakiyya ‘yar dambe ce ta Karshe don haka kome za a ce ta yi ba zai musa ba. Yana son fara ba Umma hakuri domin zuwanta Kaduna wani tashin hankalin ne da zai hana shi samun natsuwa. Haka yasan Ummansa tana iya tsine masa akan dai kishiyar da za ta tarar. Don haka ya durKusa yana roKonta kada ta koma yanzu, ta bari ya sami natsuwa agun aiki a lokacin sai ta koma. Da Kyar ya shawo kan Umma, ita kuwa Zakiyya dubanta ya yi ya ce, “Wace ce kuma mai sunan da kika ambata?� Ta dube shi sosai ta ce, “Wai Salamatu? Ga ta nan a gabanka.� Sultan ya mike cike da fusata zai yi kanta, Umma ta girgiza kai, “Kada ka taba ta ka barta da halinta, zan je Kadunan har gidan uwarta. Kuma ni ba ni ta kira kai tsaye ba, uwarta Ladidi ta kira. Shashasha wacce bata san ciwon kanta ba.� Zakiyya ta juya ta tafi tana taunan cingam da Karfi yana bada wani sauti. Shi dai Sultan yana gama lallaba Umma ya zayaya ya kira Abba ya kwashe komai ya gaya masa, Abba ya saki ajiyar zuciya yace“Sultan ka Kyale ta ta dawo nima ina son dawowar nata, � gara tasan komai ta yi abinda za ta yi kowa ya daina fargaba. Idan muka jure babu shakka zai zo ya wuce. Dole duk boye-boyenka watarana za ta sani. Zakiyya kuma kayi ta hakuri da ita ita kanta wataran sai ta yi danasani.� Sultan ya amsa yana cewa, “Abba ko za ta zo ba zan bar ta ta dawo yanzu ba, ina cikin damuwa abubuwa duk sun Kwace min. Ga Office dina ina fuskantar barazana akan wani Case na fyade da aka yi wa wata ‘yar yarinya, so suke su bani kudi saboda kada sunansu ya baci, ni kuma naki karbar kudin, shi ne da su da Ogana suke aiko min da barazana. Kankat daga can sama gargadi ake yi min. Ni kuma na yi alkawarin ko wannan ne dalilin cire kakina sai na dau mataki a kansu.� Abba ya jinjina kai, “Hakane Babana Allah ya taimaka ya dafa maka. Ina Kara gargadinka da ko ni mahaifinka ka kama da aikata dokan da ta sabawa aikinka, ka kama ni ka hukunta ni daidai da laiifina. Allah ya yi maka albarka.� Sultan ya ji dadin furucin mahaifinsa haka yana samun natsuwa ne a duk lokacin da ya sanya masa albarka. Haka suka sauke wayar sannan ya nufi cikin gida wurin Zakiyya. Bai wani sha wahalar lallashinta ba, domin ya gaya mata ya daina lallashin mace, hakan yasa ta yi tunanin ko asirin ya yi sanyi ne? Dama kuma asiri sai dai ka dora, amma aikinsa kwana arba’in ne kawai, ya tashi aiki. Tunda Zakiyya ta riKe shi a daki ta hana shi fita, hankalinsa yana kan su Nasreen, haka yana kallon kiran waya da lambar waje, mai dauke da +44 ya tabbatar da Code din London ne don haka ya ki dauka ta gagare shi. Tafiyar awa shida da minti kusan arba’in da uku ya kawo su Kasar London. Kai tsaye aka nufi da su shahararren Hotel din Marriot Hotel wanda babu nisa a tsakaninsa da eye Centre din da za ayi mata aiki. Tana jin Naufal da Jidda suna santin wurin amma ita babu idanun da za ta gane haduwar wurin, sai dai ta shaki iskan Kasar. Kai tsaye suka nufi gun Abokinsa Dr. Sadiq da ya iso da kansa yana murmushi. Bayan sun gaisa ne ya dubi Nasreen ya ce, “Ita ce patient din namu? Al-ameen ya amsa masa, sannan suka shiga ciki. Jidda tana tare da Nasreen, Bayan sun gama cin abinci Jidda ta ce, “Wai don Allah ina kika samu wannan Kamshin ne? Tun a Najefiya nake son tambayarki. Idan kin zo da shi dan sammin in je dakin Abban ~ Muhsin nasan zai ji dadinsa. Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wallahi ~ Yumnah ta bani a lokacin da na je gidanta, shi ne Dee ya ji Kamshin ya matsa sai da.aka basa lambar Jafar din ya yi tattaki ya tafi har Zaria, yasa Kanwar Anti Fatima Dan Borno ta je ta siyo masa, da yake ance ita kanta Anti Dan Bornon acan take siyayyan duk wasu Kamshi da take amfani da su. Idan kika je ma za ki iya haduwa da ita taje nata siyayyan.� Jidda ta zaro idanu ta ce, “Ko dai agunsa ne Anti Bintu take siyan kayan Kamshin jiki da na gyaran fata? Ita ma daga Zaria ake sako mata a mota.� Nasreen da hankalinta gaba daya yake gun Sultan ta ce, “Shi ne ma, shima a Sabon garin Zaria yake, wai kafin akai Police Station. Kuma ya riga ya yi sunan da kowa ya san shi. Yanzu haka Yumnah ta ce min idan na dawo za ta ba ni wani sirri da ta siya a wurinsa, wai ba kowa yasan sirrin ba. Karin abin burgewa talaka ma zai iya zuwa da kudinsa kadan ya mallaki abinda yake so. Bari in dibar maki ki je za ki ba ni labari.�� Jidda ta ce, ‘“‘Lallai ma Yumnah wato so sone son kai ya fi. Yanzu duk yadda nake da ita bata kawo min wannan na gwada ba?� Nasreen ta miko mata, kai tsaye ta fada wanka ta fito ta goga man ta shafa dan humran ta fito tana tashin Kamshi. Babu kunya Jidda ta shige dakin mijinta, ta bar Nasreen da dogon tunani. A lokacin ne kuma Naufal ya shigo hannunsa dauke da waya ya miKawa Nasreen ya ce, “Ki yi magana Dee ne yake kan layi.� Shi ma ya fice abinsa harabar Hotel din yana kallon yadda tsarin su yake abin akwai sha’awa da sanya nishadi. Yana sanya masoya a cikin wani hali na samun natsuwa. Nasreen ta lume akan gadonta tana jin sany1 yana ratsata, ta fara magana cikin sanyi da ruda dukkan wanda ya _ saurari wannan murya, “Amincin Allah ya tabbata a gareka uban marayu. Da fatan zuciyar da na bari a cikin shauki cike da soyayyata tana cikin kwanciyar hankali da natsuwa?�� Sassanyar murmushi ya saki sannan ya bata amsa cike da kewarta da ke nuKurKusansa, “Wannan zuciya da kika tafi kika bari, kin barta ne cikin sonki da kewarki hakan ya taimaka wajen Kuntatawa wannan zuciyar. Me yasa ma bature bai fitar mana da yadda zaka zama tsuntsu ka je dukkan garin da ka gadama a lokacin da ka. so ba? Ai da yanzu na iso bisa gadonki na tayaki barci irin na Lagos.� Murmushi ya subuce mata, ta sake jawo filon ta KanKame. “Anan wurin haka tawa zuciyar take ciki. Sai dai jin muryarka ya kore dukkan wani Kishirwa da ke cikin maKoshina, hakan ke nuna min ruwan da yake nema ne aka kawo akan lokaci kuma aka shayar da makoshin har ya gamsu.� Ya gamsu da bayanan matarsa akansa, ya gamsu soyayya tana matuKar riKe aure, musamman ma idan ladabi yana ciki. Domin ladabin aure shi ne magin cikin aure, soyayya kuma ya goya masa baya ya zama gishirin da ke cikin aure. Haka suka ci gaba da hira cike da annashuwa, haka kamar ba kudi ake cirewa ba. Ya ce mata ta riKe wayar zai dinga kiranta. Ta yi godiya ta ajiye wayar tana jin natsuwa tana shigarta. Jidda ce ta shigo tana murmushi, sai dai Nasreen ba ganinta take yi ba, don haka ta yi shiru. Jidda ta ce, “Wallahi muna dawowa Najeriya zan ziyarci shagon Jafar dinnan da kaina ba sako ba. Kai amma dai Yumnah ta ci amanar zaman tare, shegiya sai shige-shige ka rasa wa yake gaya mata irin wadannan sirrikan.� Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wa zai gaya mata idan banda ‘yar mutan Borno? Ita ta gaya mata komai. Shiyasa na gama kula kamar ta fi son Yumnah akan mu.� Jidda ta girgiza kai, “Ke kike ganin hakan, amma ni nasan ta fi sona akan kowa.� Nasreen ta gyada kai “Zai iya yiwuwa. Yanzu na gama waya da Dee, ya ce yana gaida ku.� 6/29/22, 12:42 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA soyayya tana matuKar riKe aure, musamman ma idan ladabi yana ciki. Domin ladabin aure shi ne magin cikin aure, soyayya kuma ya goya masa baya ya zama gishirin da ke cikin aure. Haka suka ci gaba da hira cike da annashuwa, haka kamar ba kudi ake cirewa ba. Ya ce mata ta riKe wayar zai dinga kiranta. Ta yi godiya ta ajiye wayar tana jin natsuwa tana shigarta. Jidda ce ta shigo tana murmushi, sai dai Nasreen ba ganinta take yi ba, don haka ta yi shiru. Jidda ta ce, “Wallahi muna dawowa Najeriya zan ziyarci shagon Jafar dinnan da kaina ba sako ba. Kai amma dai Yumnah ta ci amanar zaman tare, shegiya sai shige-shige ka rasa wa yake gaya mata irin wadannan sirrikan.� Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wa zai gaya mata idan banda ‘yar mutan Borno? Ita ta gaya mata komai. Shiyasa na gama kula kamar ta fi son Yumnah akan mu.� Jidda ta girgiza kai, “Ke kike ganin hakan, amma ni nasan ta fi sona akan kowa.� Nasreen ta gyada kai “Zai iya yiwuwa. Yanzu na gama waya da Dee, ya ce yana gaida ku.� ZAMU TASHI Ta nufi bandaki tana cewa, “Shi ya sa na ga fuskarki fes babu damuwa, sai fara’a kike yi, ashe soyayya kika sha.� Nasreen ta dan muskuta ta ce, “Ke kuma ruwa kika je kika ba shi kenan.� Jidda ta KyalKyace da dariya ta shige abinta. Cikin dare Sultan ya kasa barci, yana kallon yadda Zakiyya take shakan barcinta minshari yana biyo baya. Gaba daya idan tana barci sai muninta ya sake fitowa. A cikin natsuwarsa ya mike ya fito falonsa yana kaiwa da komowa, gaba daya ya rasa meke masa dadi? Yana son sake jin kalaman Nasreen, wanda yake masa kama da wacce take busan sarewa. Wayarsa ya zaro ya danna layin da ya gaya mata ta rike wayar, yana addu’ar Allah yasa ta amsa ko a cikin magagin barci ne. Tunda yasan awa daya ne a tsakanin su da London. Ita kanta bata yi barcin ba, ta kasa samun natsuwa. Jidda kuwa tuni ta gudu wurin mijinta, daga cewa tana zuwa. Nasreen ta Kosa idanunta su bude tana son ganin Sultan, tana da burin ganin yadda Naufal dinta ya koma. Farin ciki ya Kara kamata, ta y! juyi ta sake Kankame filonta. Karar wayar ya ankarar da ita, ba tare da dogon tunani ba, ta lalubi madannin wayar ta danna ta kara a kunne. Kafin ta yi magana ta ji saukan ajiyar zuciyarsa. Ita ma bayansa ta bi da ajiyar zuciyar tana jin tarin natsuwa yana sake ziyartarta. “Na yi kewar muryarka. Na Kosa inganka na kasa mance zaman mu a Lagos na kwana daya tak! Sai nake jin kamar shekara muka yi.� Lumshe idanunsa ya yi yana sake cusa kansa a windo yana Karewa tsakar gidansa kallo da ya wadatu da Kwayaye masu haske. “Na fi ki tunawa da kwanan mu a Lagos, domin kina ta guduna, hakan ya rage mana jin dadin mu. Kina zaton zan yi maki wani abu ne? Babu abinda zan maki, ina sane da Kasar da za ki je, idan nayi maki hakan waye zai taimaka ya lallaba min ke kina narkewa ina lallabaki? Nasan abinda nake yi Nasreen, ina tattalin lafiyarki fiye da nawa. Bani labarin yadda kuka sami London.� Ta dan shagwabe ta ce, “Ba na gani Dee, bana iya tantance fari da baki a cikin Kwayar idanun nan nawa. Amma naji Naufal da Jidda suna ta kururuta Kasar. Ka bani labarin Kasata Najeriya su Umma suna lafiya ko?� Idanunsa Kyar akan windo yana mamakin ganin kamar ‘yan sandan nan dukkan su barci suke yi. Kuma barci irin wanda ba Karamin nisa suka yi ba. Sai dai bai kawo komai a zuciyarsa ba ya ci gaba da cewa, “Kasarmu akwai dadi sai dai kwanciyar hankali da sakin jiki kayi barci sai turai. Gidan ya yi mana fadi saboda babu majidadin cikin gidan.� Murmushi ya Kwace mata, “Irin sarautar da ka bani kenan? Zan fi kyau da sarauniyar zuciyar mijinta.� “Uhm! Babu sarautar da ban baki ba, ni da na baki sarautar Naufal gaba daya?� Nasreen ta tuntsure da dariya, hakan ba Karamin faranta masa ya yi ba, ya jima bai ji dariyarta haka ba. Sultan ya shaki numfashi ya fesar a cikin wayar, wannan numfashi shi ya yi sanadiyyar mutuwar duk wani abu da ke jikinta, ya saukar mata da wani irin kasala. Itama ta sakar masa nata, a lokacin da bata zaci fitowarsa ba. Hakan yasa dukkansu suka yi shiru na wasu lokuta, wanda da ba dan saukar ajiyar zuciyarta ba, da zai iya cewa babu ita akan layin. A wannan lokacin ne kuma ya ware idanunsa masu tsananin haske ya watso a waje yana sake nazarin gidan. Motsi ya ji a in da bai kamata ba, hakan ya gane an shirya masa wani abu a cikin gidansa, cikin gaggawa ya koma ya dauko bindigarsa ya fice a hankali. Shi kansa bai san bai kashe wayar ba, kawai mayar da wayar ya yi a cikin aljihu ya labe sosai, ta in da babu wanda ya isa ya ganshi. Ta nan ne yake hango mutane masu bakaken kaya, mamaki ya kama shi, ya kafe su da ido. Yau lalacewa ta yi lalacewar da barayi za su tako su shigo har gidan AIG? Ta ya ya suka ci nasarar sanya masu gadinsa barci? Baya buKatar kira a zo daga office shi kadai zai iya da su. Tuni zuciyarsa ta gaya masa daga inda suka fito, don haka ya sake samun Karfin guiwa. Kafafun daya daga cikin su ya saita a lokacin da suke KoKarin neman hanyar da za su shiga cikin gidan, ya danna masa harbi. Hakan ya gigita su, har suka yi zaton tabbas akwai wadanda maganin barcin bai yi masu amfani ba, sai dai idan suka tuna Karfin farin hodan da suka watsa suna da tabbacin ba tashin yanzu ba, sai dai idan akwai wasu a cikin gidansa. Amma kuma yawan ‘yan sandan da ke gidan an gaya masu ko su nawa ne, kuma gasu reras a kwance. Tunawa da Sultan din jan wuya ne ya sa duk suka sake gigicewa, suna KoKarin dauke wanda aka harba, suka sake jin harbi. Gashi ko ma waye mai harbin ya Kware a saiti, indai ya harba sai ya sami mutum. Su Umma suka ji Karar bindiga don haka suka fito falon a gigice. Zakiyya ma jikinta yana rawa ta fito. Sultan ya dan waiwaya yaga Umma da Hafsat suna doso shi suna kuka, ya dan walwaya yana girgiza masu kai, “Umma ku koma ciki ku rufe Kofa insha Allahu babu abinda zai same ni.� Hafsat ta fasa kuka ta yi bayan Sultan ta KanKame shi, Umma ma ta kama dayan hannunsa tana KoKarin jansa suna kuka, “Yaya ka taimake mu ka zo mu je mu Boye kada su kashe mana kai. Yaya ka zo mu je, ba zamu iya tafiya mu barka ba.� Umma ta sake rike shi sosai tana fadin ‘‘Wallahi sai dai a kashe mu tare, ba zamu barka ka tafi ba, sai dai a kashemu.� . Sultan yasan halin mata da gigicewa shiyasa bai so da suka tashi ba. Zakiyya kuwa tuni ta yi cikin daki da gudu ta rufe Kofa tana fadin wani miji ba za ta kashe kanta ba, su dai da suka ga za su iya su tsaya. Sultan ya juya da su Umma suka shiga daki ya yi masu dabara ya rufe su ya fice tsakar gidan gaba daya. Nasreen ta fasa Kara tana Salati, fadi take yi “Shi kenan sun kashe min shi, ankashe Deeedi wayyo! Ashe turo ni kayi nan Kasar saboda akasheka? Naufal! Na shiga uku bani da idanu ina zan ga Naufal?� Kuka take sha babu KakKautawa, ita Karan harbin da ta ji shi yake gaya mata ankashe Sultan. A can bangaran kuwa tuni sun ci nasarar guduwa sai suka bar wanda aka harba. Sultan ya fito yana duban mutumin idanunsa a rufe. Sai a lokacin ya tuna da wayarsa, haka kudin ciki bai Kare ba, ya daga ya mayar kunne yana fadin Hello! Sai dai baya jin komai sai sautin kukanta da irin kalaman da take yi tana fadin. “Ka san zaka mutu ne shiyasa ka turo ni nan? Wayyo rayuwata ta zama abar tausayi, waye zai sake zama gatana a gidan duniya?� Kashe wayar ya yi tare da kiran Office din su, cikin gaggawa motar ‘yan sanda suka bayyana a gidansa. Yana nan tsaye aka tafi da shi, wasu suka tsaya a gidan, haka ya hana a taba ‘yan sandan ya ce a bar su har su tashi da kansu. Shi kuma ya koma ciki ya zauna a falon yana mayar da ajiyar zuciya. Sai da ya dan natsu sannan ya je ya bude Kofar su Umma da suka dami ko ina da ihu. Yana budewa gaba daya suka fada jikinsa, ya ce, “Umma lafiyata Kalau don Allah ku daina kukan nan.� Umma ta ce, “Idan suka kashe min kai ba zan taba yafe jinin dana ba, Sultan duk tsaron da ke gidanka me yasa ‘yan fashi suka iya shiga cikin gidanka? Ina ‘yan sandan?� Furzar da huci ya yi mai zafi sannan ya dawo falo ya zauna haka suka biyo bayansa kamar wanda zai sake bace masu. Wayarsa ya zaro ya kira Nasreen, tana jin kukan waya ta dauka hannunta na rawa, “Hello.� Yadda ya ji muryarta tana rawa yasa shi yin murmushi, ““Waye ya gaya maki an kashe ni? Kukan nan da kike yi kamar za a zare ranki na menene? Wa ya gaya maki har kin tabbata marainiya? Kina nan da gatanki insha Allahu, share hawayenki ki kwanta zamu yi magana gobe.� Ta kasa magana sai hawayen farin ciki da ke sauka a kumatunta. Ya katse wayar yana duban su Umma har yanzu hankalinsu baya cikin jikin su. “Umma turo su akayi akan wani Case da ake son dole sai na ci hanci. Ni kuwa ko rayuwata za su dauke ba zan bi su ba. Umma Case din fyade ne ‘ya’yanmu da Kannanmu ake Gatawa rayuwa. An yi wa babbar budurwa fyade ta mutu bare Kananan yara wadanda basu wuce shekaru hudu ba? Umma a Kaduna a kowacce rana sai mun sami case din fyade idan yau mun sami na yara ‘yan shekaru hudu gobe zamu samu na ‘yan shekaru biyar, jibi za mu samu na ‘yan shekaru shida. Umma a haka za a yi ta bata rayuwarsu? Sannan ba za mu Kwato masu ‘yancin su ba, sai a nuna wa hukuma kudi ko kuma a dauki rayuwarsu? Bana jin ko mahaifina na kama da wannan abin zan iya barinsa, duk girman son da nake masa kuwa.� Umma da tunda ya fara maganar idanunta suke bude saboda tsoro, ta gyada kai, “Na tsani mazinaci, mazinacin ma mai bata rayukan yara Kanana. Ina tare da kai Sultan ka Kwatowa � ‘ya’yanmu hakkin su. Ka tona asirin su duniya ta gansu. Mutanen nan-su suke bata mana Kasa. Na amince maka ka tafi ka Kwatowa bayin Allah hakkin su.� ; Sultan ya sake samun Kwarin guiwa yanzu ya kula da babu Zakiyya, haka Hafsat tana Kudundune tana aikin kuka. Ya yi murmushi ya ce, “Hafsat zo nan kusa da ni. Ashe haka kike son Yayanki? Lallai yau na ji dadi tunda naga kulawar Hafsat akaina.� Ba su san lokacin da suka yi murmushi ba, Anan falon suka yi barci shi kuma ya tashi yana Kwankwasa Kofar dakinsa da Zakiyya tasa key, Da Kyar ta bude sai da ya tabbatar mata da shine. Ko a yanzu ya gane su waye dolensa? Su waye suka shirya sadaukar da rayukansu akan tasa rayuwar. Bai yi barci ba, bai kuma yi mata magana ba. Kawai yana zama ta zauna ta hau taba shi. Tana cewa, “Wai kai ko irin wasa na ma auratan nan baka iya yi bane? Kullum fuskarka babu wani annuri.� Sultan ya fizge jikinsa yana aikata mata wani irin kallo. “Ke wacce irin macece mara tunani? Ba ki iya bambance lokacin da mijinki ya ke cikin farin ciki da akasinsa? Ban iya wasan ba, idan za ki iya zama da ni a haka ki zauna idan ba za ki iya ba ga hanya Please! Kin ga ta inda Nasreen ta fi ki kenan, ita tana da natsuwar da take bambance lokacin wasa da_ lokacin lallashi. Duk da tana yarinya Karama amma ta fi ki hankali da sanin ciwon kai. Wasa kuma sai mace ta gyara kanta take samun yadda take so a wurin miji. Kada ki sake matsoni a lokacin da nake Kunshe da damuwa.� Yaja filo ya kwanta kawai. Karfin turarenta da ta yi amfani da shi suka hade da warin jikinta suna bayar da wani irin tsami. Ji ya yi gaba daya ya tsani kansa, yana matukar kokari wajen yi mata kawaici. Dole ya yi alwala domin yin Sallah ya mika godiyarsa ga Allah, ya fice zuwa falo. Har asuba idanunsa biyu, yana karatun AlKur’ani domin ya sani yaKin da yake shirin tunkara ba abu bane mai sauki. Shiri yake na tonawa dukkan wanda yake da alhakin shigar masa gida asiri, ko waye shi. Ana kiran Sallar asuba ya fito zai je Masallaci ya sami ‘yan sandansa sun farka har sauran sun yi masu bayanin komai. A nan suke cewa su ba su ji motsi ba, sai farin fauda da suka gani ya bade ko’ina. Wasu ‘yan sandan suka yi masa jagora zuwa Masallaci, yana dawowa ya yi wanka a gurguje ya yi shirin zuwa office. Da isarsa ya kira Ashmaan a waya ya kira Mahbub da Khamis duk suka hadu a Office dinsa. Ya gaya masu dukkan abubuwan da suke faru ya Kara da cewa, “Akan case din nan ba zan bari rayuwata ta zama a cikin hatsari ba, bai � kamata in ci gaba da boye su bayan su rayuwata suke nema data iyayena ba. Don haka Ashmaan za ka iya zuwa ‘yan sanda su matse mutumin da na harba a Kafa, sai ya gaya mana wadanda suka turo su, ku buga a cikin Jaridarku daga ta hausar har ta turancin. Ba zan sake yin gangancin da nayi, har aka shigo gidana ana neman rayuwata ba. Na dauki hakKkin Umma da Hafsat, hatta Nasreen da ke can London sai da ta sha kuka har ta gode Allah, kalamanta sun bani tausayi, gani take yi na tura ta can ne saboda zan mutu. Don haka sai sun biya tashin hankalin da suka sa iyalina ta hanyar fanshe abinda suka shuka.�Khamis ya yi shiru can ya ce, “Sultan ka ba ni case din nan mana ya dawo hannun sojoji, ta yadda za mu kakkarya kayayyakin banza mu sake hade su.� . Ashmaan yace, “Ba za a yi haka ba, a dai tona masu asiri kawai.� Mahbub ya saki ajiyar zuciya, “Wai kai ma kenan da kake sama da ni. Na tsani aikin dan sanda sosai, wasun mu‘su suke jawo mana zagi a duniya, ake hada mu ana cewa ba mu da mutunci. A yi yadda ya kamata din.� Cikin hukuncin Allah Ashmaan ya sami yin hira da mai laifin ya kuma samu abinda yake so, sunayen wasu manya ya kirawo daga ciki har da Alhaji Sulaiman da aka yi zaman meeting da shi, da kuma sunan Ogansa. Don haka kafin fitowar jarida Sultan ya kira Meeting da dukkan manyansu meeting din gaggawa. Ogansa yana ganin Sultan gabansa ya dinga faduwa. Sultan ya tsaya a tsaye bayan ba su girma da ya yi ya fara magana cikin bacin rai, “Ku yi hakuri na kira wannan tattaunawan ne saboda in gaya maku abinda ke faruwa a tsakanina da Oga.� Sultan ya kwashe komai ya gaya masu, ya Kara da cewa, “Kai ba ka isa ka hada baki da wasu a nemi rayuwata ba, baka isa ka sani inci hanci dole ba, idan kai za ka iya amsar kudi a kan rayukan ‘ya’yanmu da suke cikin matsala, ni . ba zan iya ba. Na kuma gaya maka a baya ba siyan kwalina na yi ba, a’a da Karfina.na shiga � aikin.� Ya juya wajen babbansu ya sara masa ya ce, “Sir! Barin wadannan a cikin Kasa tare da kakin mu a jikin su tamkar Kara ruguza Kasar ce. Bayan Sultan ya gama jawabinsa ya zauna, a nan take aka yi ta tattaunawa cikin natsuwa babu wani kace nace aka ce a rufe shi, a cire masa kakin jikinsa, har sai an kammala bincike.� Sultan ya dawo gida cike da farin ciki, domin a ranar aka tura akamo su Alhaji 6/29/22, 18:05 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Sultan ya tsaya a tsaye bayan ba su girma da ya yi ya fara magana cikin bacin rai, “Ku yi hakuri na kira wannan tattaunawan ne saboda in gaya maku abinda ke faruwa a tsakanina da Oga.� Sultan ya kwashe komai ya gaya masu, ya Kara da cewa, “Kai ba ka isa ka hada baki da wasu a nemi rayuwata ba, baka isa ka sani inci hanci dole ba, idan kai za ka iya amsar kudi a kan rayukan ‘ya’yanmu da suke cikin matsala, ni . ba zan iya ba. Na kuma gaya maka a baya ba siyan kwalina na yi ba, a’a da Karfina.na shiga � aikin.� Ya juya wajen babbansu ya sara masa ya ce, “Sir! Barin wadannan a cikin Kasa tare da kakin mu a jikin su tamkar Kara ruguza Kasar ce. Bayan Sultan ya gama jawabinsa ya zauna, a nan take aka yi ta tattaunawa cikin natsuwa babu wani kace nace aka ce a rufe shi, a cire masa kakin jikinsa, har sai an kammala bincike.� Sultan ya dawo gida cike da farin ciki, domin a ranar aka tura akamo su Alhaji ZAMU TASHI Sulaiman. Talakawan da Sultan ya taimaka masu suna ta neman ‘Sultan domin su yi masa godiya, amma ganinsa ya zame masu wahala. Yana can kwanaki biyu ya zama sai a hankali baya zama, ita kuma Nasreen har an fara duba idanun, haka sun sanya ranar aikin. A lokacin ta yi Kokarin ganin ta yi waya da Sultan ya kirata yake lallashinta akan yana wani bincike ne. Al-amcen ya karbi wayar suka tattauna, ya Kara yi masa godiya akan irin dawainiyar da yake yi da Nasreen da Naufal ya ce babu komai. A zaman Nasreen da Jidda Nasreen ta Karu da ilimi kala-kala ta ji dadin wannan zaman, haka hankalinta ya kara kwanciya tunda ta fahimei Jidda macece mai ban dariya da saukin kai, a lokaci guda ta shiga cikin jerin mutanen da take son ganin fuskarsu. Hankalin Sultan bai dawo jikinsa ba, sai da aka yanke masu hukunci, duk da Alhaji Sulaiman bai fada masu asalin wanda yake aikata wannan aikin ba. Yanzu yana jin kansa kamar an sauke masa wani nauyi. Yau Umma ta dage tana son zuwa gida, tana yawan yin mugayen mafarkai. Dole ya shirya ‘yan sanda ya ce su kaita gida ya kuma, ce zai zo gobe. Su Umma suka tafi, gidan ya sake yi masa fadi gabansa yana fadiwa akan abinda zai faru a garin Kaduna, gani yake kamar ya shirya ya bi su, sai dai idan ya bi su abin zai fi kwabcewa. Yana zaune Zakiyya ta fito ta zauna kusa da shi tace, “Ka yi hakuri idan nayi maka laifi.� Sultan yana son mace mai bada hakuri a lokacin da ta san ta yi kuskure, sai dai bai taba zaton Zakiyya za ta kasance daga cikin ‘irin matan nan ba. Babu musu ya ce babu komai, a ranar dole ya biye mata, yana mai jin Kunci a zuciyarsa. Yanzu tunanin zuwa London kawai yake yi, domin Al-amcen ya tabbatar masa da anyi aikin idanun suna sa ran za a bude idonun ko wani irin lokaci. Don haka ya fara shiri kawai ba tare da ya gayawa Zakiyya ba. Da gaske yake jin gidansa ya yi masa girma ya saba da hayaniyar gidan. A gefe guda gabansa yana faduwa akan mahaifiyarsa. Umma tana isa Kaduna ta ce wa Driver ya wuce da ita gidan Hajiya Ladidi, babu musu ya wuce da ita. A gida ta sameta tana shirin fita Umma ta zabga mata harara, “Kin bani mamaki butulu. Ba ni Salma za a yi wa haka ba. Kin kai sunan Sultan gidan malamai saboda baki da kirki, kika zugo ‘yarki ta yi min rashin kunya ko? Zan nuna maki baki isaba in dai da gaske ni na haifi Sultan zan nuna maki Karfin ikon a hannuna yake. Zakiyya kamar ta bar gidan dana ta gama. Ke Hafsat juya mu tafi.� Hajiya Ladidi ta kamo hannunta ta marairaice, “Haba Hajiya idan aka gaya maki zan sa Zakiyya ta yi rashin kunya za ki yarda? Kuma ni ban kai sunan Sultan wurin boka ba, gani nayi yadda yake wulakantata yana maki ciwo shiyasa nace bari intaimaka maki inrage maki wahala kin san dan yau ka haife shi ne baka haifi hali ba. Ai ba zan mance karamcinki ba.�Umma ta yi Kwafa ta ce, ‘Me yasa ba ki daukar wayata?�Ta sake marairaicewa, “Wallahi saboda zancen mijinki da na fada maki ne na san ki da kishi shiyasa.�Umma ta saki ajiyar zuciya, “Shi kenan babu damuwa, yanzu zan je gida idan na huta zan leKo� Hajiya Ladidi tace, “Naso kuwa muyi maganar yadda ya kamata ayi da Nasreen dinnan naji ance har waje ya turata aikin idanu. Yarinyar nan tana neman ta zame mana masifa.� Umma ta dawo da baya, “Wannan maganar sai mun zauna, da bakin cikin hakan na dawo Duk da ita ma Zakiyya ta Bata min rai sosai.� Hajiya Ladidi ta ce, “Ai ba ta gaya min ba, ta san halina sai in yi tattaki inci mata mutunci.� Umma ta ji dadin kalaman Hajiya Ladidi don haka ta tafi tana murmushi. Tana wucewa Hajiya Ladidi ta harare ta tace, “An gaya maki bari zan yi ki rabo ‘yata da gidan mijinta? Sai dai ke in raba ki da danki rabuwa ta har abada, muje zuwa.� A mota Hafsat take cewa, “Umma ni ban yarda da matar nan ba, Karya take yi tace bata san abinda Zakiyya take aikatawa ba.� Umma ta yi shiru, bata san dalilin da yasa gabanta ke faduwa ba. Suna isowa gidan aka shiga kwasan kaya ana kaiwa ciki. Ta sa kai ta shiga falon. Mairo ta samu tana matsawa Abba Kafafu shi kuma yana duba Jarida. Umma ta shigo tana zare idanu, ita kuwa Mairo tana ganin Hajiya ta mike jikinta yana Bari. A natse ya ajiye jaridar yana Karewa Hajiya Salma kallo babu wata damuwa a fuskarsa, shi kansa bai san zai iya irin wannan jarumtar ba. “Salma saukan yaushe?� Sa’a daya ya ci yana matsayin mijinta, da babu abinda zai hana ta liliyo ashar ta dura masa. Hawaye suka fara gudu a fuskarta, Hafsat ma ta fasa kuka tana cewa, “Mairo kin cuce mu kinci amanar mu. Yanzu Abbanmu kike irin wannan zaman da shi?� Umma ta saki jakar hannunta tana duban Abba, domin ya fi ba ta mamaki. Ta yi magana cikin sanyin jiki, “Yanzu wannan ne yardar da kake nema a wurina? Ka cuce ni ka cuce ni da har na hada zuri’a da kai. Mazinaci wanda baya tsoron Allah.� Jikinsa na rawa ya mike yana nunata da hannu, “Kada ki sake kirana da mazinaci. Matsayinku daya da Maryama don haka nake sake neman tsari da aikata zina. Ai nasan kin tafi kin bar ni ne saboda in aikata abinda kike fada, sai dai Allah ya nesanta zuciyata ma da wannan tunanin, domin mutuncin ‘ya’yana nake ji ba mutuncinki ba.� Hafsat ta yi cikin daki da gudu tana rusan kuka. Umma ta yi kukan kura ta yi kan Mairo tana cewa, “Yau sai kin bar duniyar nan, sai kin daina cin amana daga kaina. Ni Mairo? In maidoki mutum ki ci amanata? Mijina za ki aura kina Kazamarki da ke? har kin isa in hada miji da ke?�Abba ya samu ya raba ta da jikin Mairo da Kyar. Jikinta yana kyarma ta shako wuyan rigar Abba, “Kai kuma shugaban munafukai! Idan baka sake ni ba yau gidan nan babu mai yin barci. Ka sake ni ko kuma dukkanku indauki mafi munin mataki akanku. Ni za ka yi wa kishiya? Kishiyar ma mai aikina? Duk matan duniyar nan baka ga-mace bane sai Mairo? Ka sake ni nace bakin munafuki.� Tana maganar tana huci kamar zakanya. Abba dai bai ce mata komai ba, ya dubi Mairo ya ce, “Ke Mairo wuce dakinki.� Mairo ta raba gefenta za ta wuce ta saki wuyan rigar Abba ta koma ta fizgo Mairo ta hau duka babu ji babu gani, tana cewa “Babu inda za ki je makira, sai kin gaya min wanda ya baki shawarar aure min miji daga zuwa Unguwa indawo. Fada min dan ubanki, dama kuna neman juna ne? Ba za ki gaya min ba sai na kashe kayan banza?� Abba ya dago ta ya dora mata mahaukacin mari wanda ya yi sanadiyyar fashewan gefen bakinta, amma bakinta bai mutu ba, gaba daya ta zama mahaukaciya. Marin da ya yi mata ya tsaya masa a rai, danasani ya shige shi a lokaci guda. Sannan ya dubi Mairo da ke kuka kamar ranta zai fita ya ce, “Maryama zo ki wuce. Idan kin cika mahaukaciya ki sake taba min mata, za ki ga irin wulaKancin da zan yi maki. Na yi auren ‘nan ne don inbata maki kamar yadda kika bijirewa umarnina, kuma burina ya cika. Idan takardarki kike buKata ki je dakinki zan kawo maki yanzu, domin ni daman na gaji da halayyarki.� Umma ta fasa wani kuka mai ban tausayi a lokaci guda tasa hannu tana goge hawayenta, “Ban yi mamaki ba, sunanka namiji ne babu abinda ba zaka yi ba. Kaddarar namiji waccece bamu sani ba? Cin amana agun maza wannene bakon mu? Don haka ina son a yanzu ka furta da bakinka ka sake ni ba zan zauna a gidanka ba, na gama zama da kai, ba zan sake yarda da da namiji ba, tunda kai Lukman kayi min haka. Allah ya isa tsakanina da kai mugu azzalumi.� Abba ya ce, “Duk naji kuma na amince, nima ban ce maki zan ci gaba da zama da ke ba. A hakan kuma namiji ya yi maki rana don haka ki fice min a falo.� Yana son ya lallasheta zuciyarsa tana gaya masa kada ya kuskura, domin lallashin nan zai sake jawo wata matsalar ce Karshe ma tayi masa Illa, Ta dube shi cikin bacin rai tace, “Me ka taba yi min? Juyo ka gaya min meka taba yi min?� (Ku yi haKuri ‘yan uwa mata, ina son jan hankalinku a kan wannan kalma ta me ka taba yi min? Namiji ya yi maki komai tunda ya raboki da gidan iyayenki, ya kuma dauki nauyin ci da sha dinki, ya hana duniya ta zage ki. Ashe kuwa baki da wata gata da ta wuce ta miyinki? Ashe mijinki ya yi maki abubuwa kala-kala. Baya yuwuwa ace ki zauna da namiji shekaru talatin da wani abu, rana guda ki ce me ya taba yi maki? Sai kace mana zamanin jahiliyya? Idan ran mu ya baci don Allah mu yi shiru kada mu yi magana, domin a yayin yin maganar bamu muke yin maganar ba, shaidan ke yi. Maza suna jin zafin Kalmar me ka taba yi min? Kai ba namiji ba, hatta ke dinnan mai fadin hakan idan watarana aka gaya maki ba za ki ji dadi ba. Ko me namiji ya yi maki ‘yar’uwa ki zauna ki yi tunani kafin furta masa mayana). Abba ya zakuda kafada, “Babu abinda na taba yi maki Salma. Bana fatan ki tuna alkhairi daya da na taba yi maki.� Ya koma ya zauna yana jujjuya Kalmar nan, haka da alamun kalaman sun zauna masa a zuciya ta yadda goge su za su zama abu mai matukar wahala. Dakinta ta shiga da ninyar kwaso kayanta ya lallaba ya rufeta. Ta yi ta bugun Kofar tana kuka, gaba daya ta zama mahaukaciya. � Gabadaya “dabara ta Kare masa. Dakin Hafsat ya shiga ya dade yana lallashinta da bata baki, sannan ta tsagaita da kukan.Washegart da sassafe ya kamo_ hanyar Kaduna, saboda Abbansa ya gaya masa komai. Ga shi jibi jirginsa zai daga zuwa London. Yana hanya ya kira Al-ameen yake gaya masa akwai matsala a gida, da wahala ya sami zuwa ganin Nasreen. Al-ameen ya jinjina kai, “Lallai akwai rikici sosal, kafin a shiga da ita ta sake jaddada min innemeka ko me kake ka iso gareta.� Hankalin Sultan ya sake tashi, ya gaya masa halin da ake ciki a gida, don haka shima ya jajanta ya kuma yi addu’ar samun sassauci akan komaiTafiyar awa biyu ya iso da _ shi garin Kaduna. Yana isowa ya shigo cikin damuwa. Ya dubi Abbansa da duk ya rame a lokaci guda. “Abba ina Umman take?� Da hannu ya nuna masa dakinta, babu bata lokaci ya karbi makullin ya budeta. Tana jin alamun budewa ta mike. Ido hudu suka yi, duk ta rame ta zama abar tausayi. A lokaci guda tausayin mahaifiyarsa ya yi tasiri a zuciyarsa. Tunani yake yi da mata ne aka halartawa yi wa maza kishiya, da babu abinda zai hana mazajen duniya basu zama masu kisa ba. Mata suna haKuri matuKa. Umma ta taso da wuri tana zuwa ta dauke Sultan da wani irin mari, kafin ya wartsake ta sake dauke shi da mari, sannan ta ci kwalarsa, “Ban taba ganin mara kishi irinka ba, da kai za a hada baki a cuceni? Har in turo ka ka duba min abinda ke faruwa amma ka gaya min babu komai? Ka fada min da saninka aka yi wannan auren kokuwa? Nayi alKawarin duk wanda ya tsaya tsayin daka aka yi min kishiya da ‘yar aikina sai na hukunta shi.� Abba da yake tsaye a bayansu ya ce, “Za ki dauki hakkinsa bai san da komai ba.� Umma ta juyo tana duban Sultan ido jajir, idan har da saninka akayi min kishiya Allah ya tsi..Sultan da yaji tsigan jikinsa yana tashi ya rike Umma da Karfi jikinsa yana rawa ya ce, “Umma kada ki tsine min, da ni aka je aka daura auren Abba. Umma Sunnar Ann…� Bai Karasa ba ta sake dauke shi da mari, sai dai na wannan karon yafi sauran zafi. Saboda ta gigice jin da danta na cikinta aka hada baki aka yi mata kishiya da ‘yar aiki. “Ka cuci kanka, ka kawo abinda zai raba_ mahaifiyarka da mahaifinka rabuwa na har abada. Ba zan sake _~ zama kusa da ku ba, bana son watarana ka tuna a zuciyarka ni Salma ni na haife ka, na yafewa Mairo. Na jima da ji a zuciyata ba ni na haife ka ba, ban tabbatar da hakan ba, sai yanzu. Zan je duniya in fada da babban murya dan cikina ne ya sa ayi min kishiya da ‘yar aikina. Kai Sultan ba zan taba yafe maka ba, ka jima kana cutar da ni, ka kawo min mazinata gidana, ka kawo min ‘ya’yan arna gidana, ka kawo min _ kishiya gidana? Idan na ce na yafe maka kai kanka sai kayi shakkar kasancewata uwarka, wacce tasha wahala kafin ta haifeka. Da nasan wahalar da zaka jawo min kenan Sultan da na danne ka a lokacin da nake naKudanka ka mutu, da nasan tuggun da kake son ka girma ka hada min kenan, babu ko shakka da a lokacin da likita ya sanar da ni ina da ciki da na sha magani na watsoka kana matacce. Allah ya isa tsakanina da kai Sultan ban yafe maka ba.� Hankula fa sun Kara tashi, danasani ya sake shigarsa, bai taba tunanin abin zai kai haka zafi ba. Sultan ya riKe kansa da Karfi yana ganin mutanen wurin bibbiyu. Ya yi magana cikin dauriya da cijewa. “Na yi asara a rayuwata, nayi mugun asara tunda har mahaifiyata take danasanin haihuwata, na yi tirr da rayuwar da nayi. Yau ni ce uwar da ta haife ni take cewa ta yi danasanin tsawon rayuwata a matsayin dan cikinta. Umma saboda mahaifina ya raya Sunnar ma’aiki shiyasa kike tsine min? Raboda mahaifina ya raba kansa da muguwar cutar nan da ke damun wasu ya kiyaye kansa daga fadawa halaka shiyasa kike tsinewa danki? Yau da waje ya fita ya aikata ba dai-dai ba, na 6/29/22, 20:32 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Zan je duniya in fada da babban murya dan cikina ne ya sa ayi min kishiya da ‘yar aikina. Kai Sultan ba zan taba yafe maka ba, ka jima kana cutar da ni, ka kawo min mazinata gidana, ka kawo min ‘ya’yan arna gidana, ka kawo min _ kishiya gidana? Idan na ce na yafe maka kai kanka sai kayi shakkar kasancewata uwarka, wacce tasha wahala kafin ta haifeka. Da nasan wahalar da zaka jawo min kenan Sultan da na danne ka a lokacin da nake naKudanka ka mutu, da nasan tuggun da kake son ka girma ka hada min kenan, babu ko shakka da a lokacin da likita ya sanar da ni ina da ciki da na sha magani na watsoka kana matacce. Allah ya isa tsakanina da kai Sultan ban yafe maka ba.� Hankula fa sun Kara tashi, danasani ya sake shigarsa, bai taba tunanin abin zai kai haka zafi ba. Sultan ya riKe kansa da Karfi yana ganin mutanen wurin bibbiyu. Ya yi magana cikin dauriya da cijewa. “Na yi asara a rayuwata, nayi mugun asara tunda har mahaifiyata take danasanin haihuwata, na yi tirr da rayuwar da nayi. Yau ni ce uwar da ta haife ni take cewa ta yi danasanin tsawon rayuwata a matsayin dan cikinta. Umma saboda mahaifina ya raya Sunnar ma’aiki shiyasa kike tsine min? Raboda mahaifina ya raba kansa da muguwar cutar nan da ke damun wasu ya kiyaye kansa daga fadawa halaka shiyasa kike tsinewa danki? Yau da waje ya fita ya aikata ba dai-dai ba, na ZAMU TASHI tabbata ba za ki yi mana wannan kalaman ba. Kishiyar waje ita ce abar Kyama ba matar halak ba. Bana danasanin abinda nayi, amma ina danasanin isowa gareki a yau dinnan da naji kalaman da har in mutu ba zasu taba bace min ba. Umma na jima da sanin_ baki sona, kina rowan sa min albarka a dukkan abubuwan da . nayi, na alkhairi ko akasinsa. Yau zan barku zan tafi, bana tunanin zan sake waiwayo gidan nan, domin ba zan mance ba, a cikin gidan nan mahaifiyata ta tsine min.Juyawa ya yi da ninyar tafiya, jirI ya kwashe shi ya zube Kasa. Abba ya rugo da sauri ya riKe shi yana jijjigawa. � Umma ta Karaso cikin kuka mai tsanani tana danasanin furucin da ta jefi danta da mijinta akan abinda suka aikata wanda ba haramun bane, sai dai cin fuska ne. Za ta taba shi Abba ya daga mata hannu. “Kada ki kuskura ki taba min da. Kuma akan wannan abun da kika aikata ki tafi na sake ki saki daya. Kin lalata min rayuwar yaro, tun yana Karami yake fuskantar matsala a dalilinki. Ya kamata Sultan ya fi haka, amma saboda mugayen addu’ar da kike jifarsa da shi, yana nan adankwafe a wuri guda. Ina fatan za kije ki auri_mara mata, wanda ba zai taBa yi maki kishiya ba?Umma. ta girgiza da sakin da Abba ya yi mata ta sake sa kuka, tana fadin “Na shiga uku. Sultan ka tashi na yafe maka, na janye tsinuwar da nayi maka. Insha Allahu albarkata tana tare da kai, don Allah kada ka mutu ka barnI. Kada ka tafi ko ina. Lukman yau ni ka saka saboda wata? Ni ka wulaKanta saboda ‘yar aikina?�� Abba ya dube ta cikin jajayen idanu ya ce, “Da zan sake ki saboda Ita, da tun jIya da kika rufeta da duka zan sallame ki, amma na cije. Haka kika babu zagin da baki yi min ba, amma na daure na Kyale ki a zatona za ki yi hankali daga jiya zuwa yau, sai dai zuciyar kafiran da ke manne da jikinki taki sakinki bare ta baki shawarar Kwarai. Kuma Wallahi idan dana ya rasa rayuwarsa babu shakka sai nayi shari’a da ke.� Hafsat ya Kwalawa kira, ta kawo ruwa jikinta yana rawa, aka watsa masa. Abba ya dade da shi anan kwance sannan ya farfado, ba tare da ya iya furta komai ba. Idanunsa sun sauya. Ana hakane Alhaji Mu’azzam yayi sallama ya shigo. Kallo daya yayi wa Umma ta shiga taitayinta, suka kama Sultan suka kai dogon kujera a falo. Abba ya dubi Alhaji Mu’azzam ya mayar masa da komai. Duban Umma yake yi yana ganin kamar ba za ta iya aikata hakan ba, ““Amma Salma kin bani mamaki. Wannan ba tarbiyyata bace, ki shake wuyan rigar mijinki? Mijinki fa?? Kinsan girman miji kuwa? Hauka da jahilci su suke aikatawa, ba aikin addini ba. Aure ba a aure ne aka aure ki? Iyayenmu kafin su bar gidan duniya matansu nawa? Kuma saboda rashin hankali a gaban ‘ya’yanki? Ki ji tsoron Allah Salma ki nemi afuwan mijinki tun kafin lokacin nadamar da babu amfani ta zo maki. Ki guji cin fuskar mijinki don yafi ni daraja a gunki nesa ba kusa ba. Kuma idan bai mayar da sakin da yayi maki ba, ki san gidan ubanda za ki koma ba gidana ba, ba kuma gidan dan da kika tsine masa ba. Kin lalata rayuwar danki da kanki, saboda son zuciya.� Kallo daya za ka yi wa Umma ka tabbatar ba wai ta hakura bane, amma sai ta nuna ita tayi nadama, ta roki Abba tana kuka. Abba ya yi ajiyar zuciya yace, “Idan har kin daina wannan abinda kikeyi ni na hakura. Kuma na mayar da ke dakinki, fatana ki hada kai da ‘yar uwar zamanki ki kuma kama girmanki.� Umma ta dube shi duba na tsanake ta sunkuyar da kai ba tare da ta iya furta komai ba. ********? A can kasar London kuwa yau za a bude idanun Nasreen, dow haka tasa masu rigima ita sai Deedinta ya zo. Al-ameen ya Karaso yace, “Nastcon yace haba ki hakuri wani abu mai mahimmanci ya hana shi zuwa, ki yi hakuri ba zamu dade ba zamu koma Kasarmu har sai kin ji ya isheki.� Nasreen ta girgiza kai ta ce, “Uncle ba zan iya ba, shi nake so infara gani, shi nake mafarkin ya zama mutum na farko da zan dora idanuna akansa inhar Allah yasa sun bude. Don Allah Uncle ka taimaka min a fasa bude idanuna a tsaya a jira shi.�Dr Sadiq ya Karaso yana murmushi, ya yi mata magana cikin harshen turanci, “Ki yi hakuri dole zamu bude idanunki. Idan mun bude sai ki kalli Kasa idan kin tabbatar mana kina gani shikenan sai ki mayar da idanunki ki rufe har sai ya iso. Hakan ya yi maki?�Nasreen babu yadda za tayi dole ta amince. Ana warware bandejin gabanta yana tsananta fadi. Sannu a hankali aka gama _ warware bandejin. Yana kallonta taki dago kan haka taki budewa. Dr din ya yi magana a hankali, “Bude idanunki ki kalli saitin Kofa a hankali idan kin tabbatar kina gani sai ki mayar da idanun ki rufe, bana son ki kalle ni.� Nasreen ta ware idanunta tana duban Kofa, sai dai dishi-dishi take gani, don haka tace, “Dr, ina ganin dishi-dishi. Yauwa ina ganin wasu fararen abu kamar farar riga.� Dr ya yi murmushi, “Ci gaba da ware idanun a hankall1. Babu musu taci gaba kamar yadda yace. Fes ta dora idanunta masu girma a kan wanda take fatan fara gani kafin kowa. Tsurawa juna idanu suka yi, ya Kara kyau da haske, sai dai da alamun rama a jikinsa, kamar wanda ya yi jinya ko kuma yake cikin halin rashin lafiya. Ta kasa kauda idanunta, ta kasa daina kallonsa, bata san akwai ranar da Allah zai amsa addu’arta ba, na sake kallon Dee dinta mai kyau da kwarjini. Shi kansa idanunta yake kallo yana jin wani farin ciki yana ratsa shi, ji yake kamar ba a taba halittar damuwa a zuciyarsa ba. Yana harde cikin fararen kayansa da suka sake haskaka fatarsa. Murmushi kawai yake . zubawa yana jin kamar ana sake sa masa soyayyarta. Tana son yin kuka ya girgiza mata kai, ya taka cikin tafiyarsa ta isa ya iso har gaban gadonta. Sai a sannan ta sake ganinsa da kyau. Waiwayawa ta yi kamar mai neman wani abu, sai kuwa ga Naufal. Ya zama Kato ya fita girma har da wani gemu. Farin ciki ya sa ta bude hakora tana dariya. “Deena, Naufal Allah na.gode maka da ka amsa addu’ata.� Dukkan su suka zauna akan gadonta suka � kamo hannaeyanta suna ci gaba da kallonta. Sultan yace, -“Alhamdulillahi. Al-ameen shigo ka ga idanun Nasreen dita fes da su.� Ya kai hannu kamar zai tsokane idanun, ta rike yatsan tana dariya. Jidda da Al-ameen suka shigo a tare. Farin cikin ganin Jidda ya sake kama zuciyarta. Tabbas Jidda da Alameen kyawawa ne na _ ~bugawa a jarida.Nasreen ta rungumeta tana fadin “Allah ya saka da alkhairi ya sa zumuncinmu har abada. Ba zan gaji da roKa maku Aljannah ba.� Nasreen ta sake waiwayawa tana neman likitan da ya yi mata aiki. Yana tsaye yana ta murmushi tace, “Dr mun gode.�Ya Karaso yana murmushi, “Kukan kiran Dee ya Kare ko? Yanzu babu wata damuwa ko? Daga yanzu Dee shi zai zauna da ke har mu sallameki, tunda dai mu bamu iya jinya ba, Dee shi kadai ne ya iya.� Nasreen ta sunne kanta a jikin Sultan tana dariya Kasa-Kasa. Sun burge shi sosai don haka yace, “Allah ya dorar da zaman �* lafiya a tsakanin ku, Allah ya nesantaku da dukkan abin Ki. Ina fatan zaka taimaka ka * dan zauna da patient din mu domin samun natsuwarta da kuma kasancewarta cikin farin ciki?� Sultan ya shafi fuskarta yace, “Dr, Kafata Kafar matata, nasha wahala da babu ita a cikin gidana, gaba daya sai gidan ya yi min girma bana jin dadin komai. A yanzu haka na dauki hutu ina son cin amarcina yadda ya kamata ko Babyna?� Naufal ya shafi kansa yana dariya KasaKasa Al-amecn ya nuna masa naufal da baki, Sultan ya tabe bakinsa alamun bai damu ba. Naufal ya mike yana dubanta, “‘Ku gama hira da Deedi, sandarki tana nan, ko kuma in ce maki dan jagoranki yana waje yana jiranki. Na huta da shan kira. Abu kadan Naufal! Zo ka yi min kaza, Naufal! Meya sa kayi kaza? Naufal ka tafi ka barni. Oh sunana ya kusan Karewa a bakinki.� Sultan ya kai masa duka ya kauce yana kwasar dariya. Nasreen ta marairaice kamar za ta yi kuka, “Dee ka ganshi ko? Yana � tsokana ta.� Sultan ya mayar da kanta a bisa kafadarsa. ““Kyale shi zan rama maki, kuma dole yaci gaba da yi maki wanki har ki warke. Zan bashi wahala akan abinda ya yi maki.� Ta sake dagowa tana dariyar jin dadi, ta tsura masa idanu, shi ma ita yake duba. A hankali duk aka watse aka barshi da matarsa. Ya dan waiwaya ya ga babu kowa, don haka ya jawota gaba daya jikinsa yace, “Ashe zan sake ganin wadannan idanun masu haske da kyau? Allah na gode maka.� Nasreen ta kwanta tana kallon bayansa, “‘Deeena, me yasa aka yi min Karyar ba zaka zo ba?� Hannunsa yana bisa kanta ya ce, “Da gaske da ba zan sami zuwa ba. Bani da lafiya Baby, hakannan ban warke ba na taso. Matsala tana ta faruwa a cikin gida, Umma ta koma ta sami Mairo a matsayin matar Abba. Babu tashin hankalin da ba ayi ba, daga Karshe ta tsine min.� Ya yi shiru abinda yana ci gaba da cin zuciyarsa, yana mamakin ta -. inda mata suke KoKarin haramta halas. Nasreen tace, “Hasbunallahu Wa n1’imal wakil.� Muryarta ta soma rawa, a lokacin da ta dago tana taba jikin Sultan. Zafi ne rau, haka har yanzu zazzabin bai sake shi ba. Sultan ya zame hannunta yana girgiza mata kai, “Idan kika yi kuka zan koma in Kyaleki. Kin dai san aiki aka yi maki, gara ki bi idanun nan a hankali har su Karasa warkewa, bana son kukan nan.� Dole Nasreen ta shanye hawayenta tana sake dubansa. “Yanzu da tsinuwan Umma ka hau jirgi ka taho nan?� Girgiza kai ya yi “Baba Mu’azzam ya Zo, ta janye tsinuwanta har ta Kara da sa min albarka. Amma ina tabbaiar maki ba za ayi zaman lafiya a gidan Abba ba, saboda har yanzu Umma tana cike da tsanar Mairo akan aure mata miji da tayi. Nasreen ina danasanin wannan aure, ina jin zuciyata tana tuhumata da rashin kyautawa Umma. Duk da ko wata ce can Abba ya aura sai Umma ta aikata fiye da abinda ta aikata a cikin gidan mu. Amma babu komai babu abinda ya gagari Allah. Ya Karfin jikin?�� Ya Karashe da tambayarta yadda jikinta yake. Bata iya bashi amsa ba, zuciyarta tana tausayawa Umma, domin abin akwai zafi da cin rai Kwana biyu kawai Nasreen ta Kara a cikin asibitin, wanda suka yi shi cikin wasa da dariya, haka taga tattali agun Sultan kamar ta koma cikinsa ya boyeta. Ko da aka Sallameta, Sultan ya hana su dawowa Najeriya ya tabbatar masu sai ya more kudinsa zai bar Kasar. Babu wanda ya musa, domin su kansu ba su son komawa gida. Yau tana kwance a Kafafunsa suna dan taba hira tace masa, “Dee kana waya da Anti Zakiyya kuwa?�Ya daga kai, “Eh muna waya wani abu ne?� Girgiza kan ta yi, “Babu komai na dai tambaya ne kawai.� Ta tashi zaune ta tsurawa yatsun Kafarsa ido, kamar mai nazari. Hakan yasa ya tsargu ya dube ta, “Lafiya ° ki ke min irin kallon nan?� Idanunta ta dago ta dora a bisa nasa, ya� yi saurin janye idanunsa yana duban Kafar. Ta ce “Gani na yi Kafafunka iri daya da na Naufal.� Murmushi ya sakar mata, “To menene abin mamaki? Na fada maki ke jinina ce, ke ce kawai baki gamsu da bayanina ba.� Nasreen ta dan langwabe, “To na yarda da kai Dee, amma ka gaya min su waye iyayena? Ka gayamin ina son insan ni wacece?� Sultan ya dake, ya shafi kumatunta ya matso da ita jikinsa sosai, “Ke rubutacciya ce. Ina fatan shikenan kin fahimci ke wacece ko? Oya tashi mu je mu kwanta ko kuma in zane dan bakin nan da bulala.�Nasreen ta yi murmushi tace, “Lahh ai ba a zane baki Deena.� A kunne ya rada mata wata magana ta sunkuyar da kai kunyarsa ta kama ta, ta ruga da gudu tana KyalKyaltar dariya. Sultan ya saki ajiyar zuciya da Karfi ya mayar da kai ya jinginar a jikin bangon yana nazarin ta hanyar da ya kamata ya biyo wa Nasreen. A ganinsa lokacin boye-boye ya wuce, yana ganin fada mata gaskiyar za tafi, domin lokacin da zai sada ta da danginta ya yi. Yana tunanin lokacin da zai mayar da hankalinsa akan matsalolin Nasreen ya yi. Ko babu komai a yanzu ya riga ya gama da matsalar idanunta, tana iya ganin kowa. Yana nan zaune bai tashi ba, ya ji hannaye masu taushi suka rufe masa idanu, sannan aka sumbace shi a goshi, “Nasreen kin Kware a wasa ko? Idan na kama ki ba zan 6/29/22, 20:41 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Sultan ya dake, ya shafi kumatunta ya matso da ita jikinsa sosai, “Ke rubutacciya ce. Ina fatan shikenan kin fahimci ke wacece ko? Oya tashi mu je mu kwanta ko kuma in zane dan bakin nan da bulala.�Nasreen ta yi murmushi tace, “Lahh ai ba a zane baki Deena.� A kunne ya rada mata wata magana ta sunkuyar da kai kunyarsa ta kama ta, ta ruga da gudu tana KyalKyaltar dariya. Sultan ya saki ajiyar zuciya da Karfi ya mayar da kai ya jinginar a jikin bangon yana nazarin ta hanyar da ya kamata ya biyo wa Nasreen. A ganinsa lokacin boye-boye ya wuce, yana ganin fada mata gaskiyar za tafi, domin lokacin da zai sada ta da danginta ya yi. Yana tunanin lokacin da zai mayar da hankalinsa akan matsalolin Nasreen ya yi. Ko babu komai a yanzu ya riga ya gama da matsalar idanunta, tana iya ganin kowa. Yana nan zaune bai tashi ba, ya ji hannaye masu taushi suka rufe masa idanu, sannan aka sumbace shi a goshi, “Nasreen kin Kware a wasa ko? Idan na kama ki ba zan ZAMU TASHI yi maki da kyau ba.� Dai-dai saitin kunnensa ta yi masa magana, wanda ya haddasawa tsigan jikinsa tashi, “Idan ka kama ni zaka yi min da kyau, hasalima tarairayata zaka dinga yi kana tattalina, bana tunanin zaka iya barin dai-dai da kuda ya taba ni. Kayi min duk yadda kake so Dee.� Hannunsa ya sa ya jawota ta zauna a jikinsa. “Nasreen komai naki mai kyau ne, naso a ce kowa yana ganin muninki ni daya nake da ikon � ganin kyawun matata har intasata a gaba in yi ta kallonta kamar zanen hoto a gabana. Mu je ciki sanyi nake ji sosai.� Suna shiga ciki wasan ya fara sauyawa, don haka na tattara `yan takarduna na koma dakin su Jidda, su kansu abin ba a cewa komai, na juya wurin Naufal da ya nausa cikin dogon tunani. Tambayoyi ne cike da cikinsa, amma Sultan yaqi bashi fuskar da zai aiwatar da wannan tambayar Kansa yana sake daurewa ganin dangin Abba ne kawai suka damu da su. Ya sha alwashin suna dawowa zai bi diddigin gaskiyar lamari. Cikin ikon Allah suka dawo kasarmu Najeriya, basu yi yungurin dawowa Abuja ba, sai da suka kwana a Lagos sannan suka dawo cike da gajiya. Zakiyya suka samu a falon tana shan kida abinta. Sultan ya zauna yana rike kansa. Nasreen kuwa kafe Zakiyya tayi da idanunta tana mamakin yadda take. Duk a zatonta wata kyakkyawa ce ta nunawa duniya ce, bata taba ganinta ba, ko can tana da idanunta. Kallo daya ta yi mata ta ji ko alama bata sonta, don haka ta kawar da kanta ta zauna tana lumshe dare-daran idanunta. Zakiyya ta dago suka hada ido a karo na farko gaban Zakiyya ya fadi Bata taba sanin haka idanun Nasreen suke da kyau da daukar hankali ba, da babu abinda zai sa ta bari a bude su. Kowannen su da abinda ke zuciyarsa, ta so ta yi magana ganin Jidda a wurin ya sa ta yi shiru, dan tana tsoron Jidda. Jidda ta dubi Nasreen ta ce, “Tashi mu shiga kitchen mu samar masu abinda za su ci, kinsan Abban Muhsin baya cin abincin masu aiki.� Babu musu suka mike. Sultan ya bi bayan matarsa da kallo, yana ayyanawa kansa abubuwa. Zakiyya ta sake cika ta yi fam. Ya dubeta yace “Ke baki iya sannu da zuwa bane?� Ta turo baki tana magana ciki-ciki, “Ba a koya min ba.Ya zaro ido kamar yaji me take cewa, yace, “Me kika ce?� Ta dan Kara murya tace, “Sannun ku da zuwa. Al-ameen ya kauda kansa ba tare da ya tanka ba, haka ya yi kamar bai san suna yi ba, daga Karshe yasa waya a kunne ya fice. Sultan yana kula da Al-ameen idan yana waya ko da Ashmaan ko Mahbub, baya son yi a gabansa, idan kuwa aka Kira suna tare ya dosa kame-kame kenan� har su fahimci yana tare da Sultan su kashe wayar. Abin yana damun Sultan gani yake ko sun cire shi a cikin abokai ne? Ya rasa gane irin wannan abin. Haka yayi wa kansa alKawarin ba zai komai ba tukun, sai yaga iya gudun ruwansu. Zakiyya ta dawo kusa da shi ta manne masa, bai ce komai ba ya kauda hancinsa yana duban gefe. Ta kama hannunsa ta mayar bayanta tana magana, “Ba ka damu da ni ba ko?� Ya dan dube ta ya ce, “Namiji yana ajiye matar da bai damu da ita ba ne?� A lokacin Nasreen ta shigo falon daukarwa Jidda wayarta. Ganinsa yasa ta gigice, ta rasa hanyar da za ta bi ta koma. lokacin ya dago kai suka yi ido hudu, jikinsa ya yi sanyi ya kuma karanci damuwa a kwayar idanunta. Juyawa ta yi kawai ta koma kitchen din. Yadda ta yi shiru yasa Jidda wanke hannunta ta karaso kusa da ita, “Menene kuma Nasreen?� Ta dago idanunta cike da hawaye ta ce, “Jidda me yasa maza basa da kunya ne? Yanzu namiji zai gaya maki duk duniya ke kadai yake so, da za ki leka dayan dakin za ki sha mamakin irin kalaman da zai yi mata. Ni duk soyayyar da zai yi da matarsa ban hana shi ba, amma kada ya yi a gabana. Baki gansu a falo ba, Wallahi zuciyata ta sosu. Dama in zauna da makanta ta, da na fi samun sauki tunda ban gani ba. Jidda ta ce. “Subhanafillahi. Haba Nasreen, ke fa malama ce bai kamata kishi yasa ki mance matsayinki na Musulma ba. Kuma idan kika ce gara kina makanta kamar baki gode wa Allah ba kenan. Kin ganni nan? Har Anti Bintu ta bar gidan duniya ban san wani kishinta ba, ni lokacin yaushe rashin hankalina ma ya bami nasan kaina bare wani kishi? Na ji dadi a raina da Allah ya haneni da inn wannan kishin, gashi mun rabu lafiya. Kada ki soma ki ce za ki sa damuwar wata a ranki bare ki kasa samun natsuwar zaman aure. Kuma su maza haka sake, ko ina suka je za su gayawa matansu suna son su, amma ke kinsan wacece yake so. Ba sai an tambaya ba, kina kallon kwayar idanunsa kinsan Nasreen dinsa ce kadai a cikin zuciyarsa ba wata banza wai ita Zakiyya ba.� Nasreen ta dan sami natsuwa, amma kuma yanayin da ta Gansu ya ki goge mata a zuciya, tana jin zafinsa da gaske, da bata iya boye irin wannan abin a gaban ko waye. Tana jin ba za ta iya zama a falon ba, ba za ta iya ci gaba da kallon Zakiyya a jikin mijinta ba. Haka suka karasa aikin jikinta a sanyaye. Shi kuwa tashi ya yi ya shiga ciki ya watsa ruwa sannan ya sauya kaya zuwa kanana. Yana fitowa falon ya sami Al-ameen ya dawo suka ci gaba da maganarsu. A lokacin su Jidda suka shigo da abinci. Kowa ya zauna suna ci ana hira amma Nasreen ta kasa ci sai danna cokalin take a cikin abinci amma ta kasa ci. Duk suna kula da ita, Naufal da shigowarsa kenan ya dube ta cike da kulawa ya ce, “Menene Nasreen?� Sultan ya dago habarta, yana murmushi. “Ashe haka Babyna take da kishi?� Nasreen ta yi iya bakin kokarinta don ta danne abin ya faskara, sai hawaye. Ya jawo ta gaba daya jikinsa yana bubbuga bayanta, “Ki yi hakuri kin ji? Na tuba ba zan sake ba. Ci abincin mu gama muje yawo abin mu.� Tayi shiru tana goge hawayenta, sannan ta janye jikinta tana cin abincin. Jidda ta dubi mijinta suka yi murmushi. Bayan sun kintsa ne suka fito zuwa gida FAtima Doctor Yummah, Nasreen ta dubi Yumnah cike da farin cikin ganinta a fuska. Suka rungume juna Nasreen ta ce, “Masha Allah. Jaruman ‘Yar Borno dukkansu Masha Allah. Na ji dadin ganinki fiye da tunanin mutum Yumnah ta yi dariya ta ce, “Na ji dadin samun lafiyar idanunki.allah kara tsarewa.� Suka saki juna, suka shige suka bar mazajen a falo. A nan suka sake zama suna hira. Jidda ta zage Yumnah tsaf akan yadda take boye mata abubuwa akan kayan kamshi Yumnah ta mike ta ce bari inbaku wani abu ku ji. Ta dauko wani humra ta dan fesa masu duk suka shaki kamshin suna dubanta, “Wannan kuma fa Yumnah? A ina kika samu?� Yumnah ta miko masu Humran ta ce ku karanta da kanku. Dukkan su suka kafa kai, “HUMRA. Uwargida kafarki kafata. Tana sanya kamshin fata ta zauna a jikinki, tana kuma kara jawo hankalin mai gida ya kasa barin kusa da ke.� Dubanta suka yi idanu a waje. Ta yi dariya ta zauna tana dubansu, “Wannan humrar daban ne, yadda kika san da Suratul Yusuf aka hada shi. Duk yadda zan gaga maki haduwarsa ya wuce nan, sai kin kwatanta.� Jidda ta sake matsowa ta ce, “Yumma Aminu ina zan sami Humran nan? Kuma haka sake a gore?� Ta gyada kai, “A shagon Jafar dinnan zaki samu, Bashi da tsada. Boye boyeta yake yi baya siyarwa kowa sai idan kinsan sirrinsa ka tambaye shi, shi ne yake daukowa. Kina zuwa shagon ki ce masa Uwargida (kafata Rafarki kike nema wato Humra. Ni saboda zalama, kwalin na siya gaba daya. guda Boma she biyu ne a ciki. Bari in baku dai-dai ku kwatanta za ku ba ni labari.� Jidda ta ce, “Kin san Allah:? Tunda ta Zaria zamu bi sai Uncle ya kaini her shagon nayi siyhyyana. Harda sabulan gyaran fata duk zan siya a wurinsa. Bani lambarsa don Allah.� Yumnah tana dariya ta ayyano lambar, 07038882560. Suka ci gaba da hirar su. Su Jidda dai sun koma gidan su, don haka gidan yayi shiru Jidda ta gyara bangarenta sai tashin karnshi yake yi, ta shiga baYi ta wanke jikinta da sabulan shagon Jafar, ita kanta ta gamsu da irin kamshin da ke fita a jikinta, ta shafe jikinta da humra mai sanyi wanda Yummah ta bata. Ta haye gado ta yi kwanciyarta. Shi kam tunda ya fita har aka kira Magriba bai dawo ba. Saida ta idar da Sallar isha’i ta sake tsala jwalika, ta shafe Humran ta gyara gashinta yana ta tashin kamshi, sannan ta koma ta kwanta. Sultan yana shigowa gidan ya shigo hannunsa dauke da kaji da abubuwan sha kala-kala ya shiga dakin Zakiyya ya mika mata ledanta zai fito tasha gabansa, “Kamata ya yi yau ka kwana a wurina, tunda dai kunje London. tare.� Dubanta yayi da wani irin duba sannan ya fice abinsa. Dakin Nasreen ya wuce hakan yasa Zakiyya bin baYansa ba tare da ya sani ba. Labe ta yi tana hangensu ta cikin makulli. Kan gadon ya bita ya mata sumba, sun jima a irin yanayin nan sannan ta zare kanta, ta rintse idanunta ta fara magana cikin wani yanayi, “Bai kama ta kana wahalar da karamar kwakwalwa kamar tawa ba. ina jin ka ba zan iya amsar wadannan bayanan naka ba sun yi min girma.� Dubanta ya yi idanunsa sun sauya, ya dubi kafafunta farare tas masu kyau da su, ya kai bakinsa ya yi kissing kafafun, ta yi saurin janyewa tana fadin, “Babu kyau fa,� Murmushi ya sakar mata, ya mika mata hannu ta rike suka sauko. A baki ya dinga bata naman tana ci ta � ture hannunsa tana kaiwa bakinsa, wai dole sai shima yaci. Haka suka Gama yaje ya wanko hannunsa ya sake yin brush ya daga ta cak sai bandaki ya wanke mata baki suka dawo kan gado. A hankali ya rada mata, “Baby wani kamshi nakejia jikin ki maisa kasala a ina kika samu. Yummah ko?� Yana maganar tare da zuge mata zif din rigar wanda gabansa dogon zif ne. Hannunsa ta rike tan girgiza kai. Wutar dakin ya kashe gaba daya. Zakiyya ta nemi ta kurma ihu, cikin ikon Allah ta toshe bakinta. Mamaki ya kashe ta, dama haka Sultan ya iya soyayya yake kin yi mata Ta gigice iya gigicewa kamar za ta yi hauka haka take ji. Ta ci alwashin bai isa ya aikata wani abu da Nasreen a wannan daren ba, don haka ta 6/29/22, 20:48 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Murmushi ya sakar mata, ya mika mata hannu ta rike suka sauko. A baki ya dinga bata naman tana ci ta � ture hannunsa tana kaiwa bakinsa, wai dole sai shima yaci. Haka suka Gama yaje ya wanko hannunsa ya sake yin brush ya daga ta cak sai bandaki ya wanke mata baki suka dawo kan gado. A hankali ya rada mata, “Baby wani kamshi nakejia jikin ki maisa kasala a ina kika samu. Yummah ko?� Yana maganar tare da zuge mata zif din rigar wanda gabansa dogon zif ne. Hannunsa ta rike tan girgiza kai. Wutar dakin ya kashe gaba daya. Zakiyya ta nemi ta kurma ihu, cikin ikon Allah ta toshe bakinta. Mamaki ya kashe ta, dama haka Sultan ya iya soyayya yake kin yi mata Ta gigice iya gigicewa kamar za ta yi hauka haka take ji. Ta ci alwashin bai isa ya aikata wani abu da Nasreen a wannan daren ba, don haka ta ZAMU TASHI yi falo, ta kurma wani irin ihu, wanda ya shiga har cikin kunnen Nasreen da Sultan yake kokarin rabata da budurcinta, yake son raya wannan dare, yake son mayar da Nasreen cikakkiyar mace. Bai so tashi ba, amma yadda Nasreen ta rude ne yasa ya manneta a kirjinsa yana magana cikin sanyin murya, “Sorry kada ki fito bari inje ingani.� Nasreen ta girgiza kai, dole ya taimaka mata ta mayar da kayanta ya kunna wuta tasa hijabi jikinta yana rawa, suka fito. A falon su ga Zakiyya tana makale da jikinta duk ta hada gumi. Nasreen ta karaso da sauri tana tambayarta, Menene? Lafiya kuwa?� Sultan ya dubeta cike da rashin yarda yace, “Ki yi magana man Ta nuna waje wai ta ga wani ya shigo da bakaken kaya. Haushi ya kara kama Sultan ya yi kamar ya juya abinsa, ya riga yasan halin Nasreen ba za ta bashi hadin kai ba, don haka yanemi waje ya zauna yanajin bakin ciki a ransa Nasreen sarkin tausayi ta dubi Sultan tace, “Dee ka zauna da ita ta riga ta tsorata yanzu haka shaidanun dare ne. Bari induba garin habbatus sauda sai ayi hayakinsa. Sultan ya ji kamar ya kifa wa Nasreen mari, yadda bata damu da damuwarsa ba, sai damuwar wacce ta fi tsanarta fiye da kowa. Banza ya yi mata, ta gama dube-dubenta bata gani ba, ta dawo ta ce masa ya dan tofa mata addu’a. Sultan ya karasa babu abinda yake fadi ya dinga yi mata tofi ba tare da ya karanta komai ba. Ta dinga sakin ajiyar zuciya, haushi ya kara kama shi, bai san me Zakiyya take nufi da shi ba. A nan falon dukkansu suka kwanta, da zarar taga Nasreen ta fara barci sai ta fasa kara, haka za ta tashi a gigice ta tallabota tana yi mata sannu. Nasreen ta ji irin warin da Zakiyya take yi, don haka ta ci alwashin sai ta taimaka mata ta raba ta da wannan warin tunda ta kula abinda keyi mata katangar karfe da mijinta kenan. Tuni Nasreen ta cire komai a ranta ta ci alwashin sai ta daidaita Zakiyya da mijinta, ba za ta so mijinta yana zuwa yana shakar irin wannan warin ba, karshe ya illata shi. Sultan yana son ya yi mata rashin mutunci amma kuma ya kasa yin hakan saboda Nasreen ba za ta bari ba. Abin takaici duk suka yi barci suka barshi yana zaman kunci. Haka ya zuba masu ido takaici yasa duk ya barsu anan ya wuce dakinsa. Da asuba ya fito ya sami duk basu nan, sun koma dakunan su, takaici ya sake kama shi, wato babu ruwansu da yadda ya kwana. Bayan ya dawo Masallaci ne ya fara shiri yana da taron da zai je da misalin karfe takwas na safiya, yana son fita da wuri don wuce wa wani wurin. Shirinsa yake tsaf a can cikin zuciyarsa kuwa kamar ya cinna wuta. Nasreen ta shigo hannunta dauke da plate ta yi Sallama, ya amsa ba tare da ya dago ba. Murmushi ta yi ta fahimci fushi yake yi da ita, bai san ita kanta dadin hakan ta ji ba, saboda tsoron da take ji. Da sauri ta ajiye plate din ta karaso tana sanya masa maballin riga. Suka dubi juna ta hade fuskarsu wuri guda ta dan Bashi fake a baki ta dube shi. “Ka tashi lafiya?� Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, “Eh� Murmushi ya kwace mata, bata sake magana ba, ta ci gaba da shirya shi har ta gama ta kamo hannunsa suka zauna. Tace, “Sai ka saika karya tukun ko ya girgiza kai a,a sauri nakeyi basai na karya ba sumba tayi masa sosai saida ta tabbatar da duk ya saki sannan ta janye jikinta tanajin wani iri a jikinta cikin mutuwar jiki ta dauki flate din ta kai masa kwan bakinsa babu musu ya karba haka ta dinga tura masa tana kai masa kofin shayin bakinsa saida ta tabbatar daya koshi sannan ta nufi turarukansa ta fesa masa kafan tana cewa kada wata taji min kamshin ka A tare suka Tito falon zai zaiyi waje, ta kamo hannunsa suka shiga dakin Zakiyya, shi dai sai dubanta yake yana mamakin irin wannan karfin halin. Barcinta take shaka mai rai da motsi. Dole suka juyo ba tare da sun sake magana ba. A bakin kofa ta tsaya. “To Allahya tsare Me kake son a dafa maka?� Sosai yake dubanta zuciyarsa tana gaya masa Nasreen ta daina sonsa. Zai fita sai ga Naufal yana shigowa. Ya dubi Sultan yace, “Dee barka da safiya. Kace za mu fita tare, Wallahi ko abin karyawa ban gani ba. Ni da irin wannan horon gara a sani a motar kawai inkoma gidanmu, ba. zan iya da horon yunwar da Nasreen take yi min ba.� Sai yanzu Sultan ya yi murmushi ya dafa Naufal yace, “Wato da a gida ne da tuni ka karya ko? Babu motar hayan da zaka hau, tare zamu je Kadunan, ina son Abba ya ga idanun Nasreen.� Nasreen ta dan yi tsalle ta kaiwa kan Naufal ran kwashi tana dariya, “Kana nufin nice ma mai barinka da yunwa ko? Tsaya ka bani minti biyu babu inda zaka je kana jin yunwa.- Da gudunta ta yi ciki Sultan ya rakata da idanu, tana dawowa da plate a hannu ta ajiye a tsakiyar falon, ta jawo hannun Naufal ta ajiye shi gaban Plate din sannan ta tallabi keyarsa, “Maza ka ci Dee yana jiranka.� Ta fago ta daga masa gira ta ce, “Ai zaka dan jira shi ko?- Dawowa ya yi ya zauna a kujera yana latsa wayarsa. Har Naufal ya kammala sannan suka wuce. Nasreen ta fada kitchen tana shirya masa abinda zai ci da rana. Sai wajen sha biyun rana Zakiyya ta farka ta biyo Nasreen kitchen tana hamma. Nasreen ta gaidata sannan ta gabatar mata da abin karywanta. Bahu kunya ta dauka ta yi Palo tasha. sai wajen karfe ukun rani suka dawo a gajiye. gurguje ta hada masa ruwan wanka ya shiga ya yi kafin ya fito har ta gama jera masa abinci, ta wadata falcon da turarukan kamshi. Yana fitowa ya shaki kamshin ya rintse ido, har abada mace mai tsafta daban take. Ya kira Naufal suka zauna zaman cin abincin tare. Abincin ya tafi da hankalinsa, amma sai ya dake yaqi nunawa. Zakiyya ta zo ta zauna da shi, ita kuwa Nasreen ta shige ciki tana karanta littafan da Yumnah ta aiko mata da su, na gyara ne da salon sace zuciyar mai gida. Ta gamsu da dukkan bayanan Anti Rahama Hassan Zaria, da ta yi a cikin littafinta Don Ma’aurata, tabbas duk macen da za ta bi hanyoyin nan babu shakka ta gama mallake zuciyar mijinta. Tana kwance ta rufe fuska da littafin ya karaso ya dauke littafin yana dubawa. A lokacin ta bude idanu aikuwa ta yi tsalle tana son kwacewa amma ya hanata, suka yi ta zagaye dakin, karshe ya fito falo ta biyo shi ta haye bayansa ta fizge littafin. Zakiyya da ta ji kamar anwatsa mata barkono ta ci alwashin sai ta rama wannan cin fuskar. Tana fitowa Nasreen ta kama kanta, domin ta tsani ta yi wa mutum abinda ita idan anyi mata ba za ta ji dadi ba. Ta koma daki domin dauko hijabi, kasancewar hakannan ta fito. Tana dawowa ta sami Zakiyya ta manne masa sosai, gabanta ya fadi da karfi, amma sai ta danne ta yi saurin korar shaidan ta saki fuska sosai ta karaso tana yi masa bayani akan littafin. Ya ture Zakiyya cikin wayau da dabara ya ce mata, “Nasreen ni kike son ki yi wa wayo?� Ta yi dariya kawai tana sosa kai, sannan ta sa kai ta fice. A waje -ta sami Naufal ya nausa cikin tunani. Ta dafa shi tana dubansa, “Naufal meke faruwa ne?� Girgiza kansa ya yi ya kwashe abinda ya ji Sultan suna fadi ranar a Kaduna wajen kasar gada. Nasreen ta yi shiru tana nazari, Anya kuwa maganar ta shafe mu? Kuma kasan wani abu ne? Idan ina kallon kamanninka da Yaya Haidar sai kawai in dinga jin kamar da gaske mu din jininsu ne. Ka dubi idanuna da kyau ka dubi idanun Umma, sai dai ta nuna min tsufa, amma idanun mu iri daya ne. Shiyasa ma na daina damuwa. Kada ka sake zama kana irin wannan tunanin kaji Naufal? Idan kana yi ni ma zaka sanya ni a cikin irin tunanin.� Naufal ya gyada kai. Sultan da ke tsaye a bayansu ya yi shiru yana nazari. Yaci alwashin yana isowa Kaduna zai yi duk yadda zai yi ya samo mahaifin yaran, don ya kula su Mahbub suna yi masa sanya, wanda zai iya jawowa har hutunsa ya kare bai kammala abubuwan da yake yi ba. Yau ma kamar kullum, cikin dare Nasreen din ce da kanta take ta fizge-fizge. Yana zaune ya kafeta da idanu, a ganinsa kawai sun hada baki ne suke son raina masa hankali. Sai da ya ga tana cizge dukkan abinda ke kanta, ta yi waje da gudun gaske. Sultan ya biyo bayanta, tuni ta yi tsakar gida sai zubewa ta yi a wurin. `Yan sanda suka yo kanta suna kokarin dagata, Sultan ya daka masu tsawa wanda yasa kowannensu ja da baya. Yana zuwa ya dagota yana dubanta. Da gaske ba ta numfashi, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi. Naufal ya fito a gigice yana duban Nasreen. Sai dai ya kasa cewa komai gabansa sai faduwa yake yi da karfi. Sultan ya dauketa suka koma ciki. Sun dade akanta suna yi mata karatu, sai a lokacin ta ci gaba da fizge-fizge. Sai wajen karfe ukun dare barci ya kwasheta. wannan lamari ba karamin daga hankalin Sultan da Naufal ya yi ba. Ita kuwa Zakiyya tana jin su ko lekowa bata yi ba, tunda dama uwarta ce tasa akayi mata tore. Da kyar Sultan ya lallashi Naufal ya tafi dakinsa ya kwanta, sai dai ya kasa barci, Salloli ya dinga yi yana rokon Allah, ya aiko mata da sauki. Sultan kuwa akanta ya kwana yana mata tofi. Washegari da kyar ya nufi Masallaci saboda tsabar barci da ke idanunsa. Ita kuwa Nasreen da kyar ta iya yin Sallah ta koma ta kwanta. A hanyar dawowa daga Masallaci ne Sultan yake kwantarwa Naufal hankali akan ta sami sauki sosai. Lamarin Nasreen abin sai ci gaba yake sake yi hakan ya daga hankalin Abba, har ma yaso zuwa ya dubata, Sultan ya hana shi. Dole ya daga waya yake sanar da Aslaf abinda ke faruwa. Aslaf ya gayawa Yummah. Babu bata lokaci suka ce wannan lamarin na Aljanu ne akwai wani wuri a Kano Abin yabo kurmi Market. Ta tabbatar masu idan suka je wurin sun sami maganin matsalar su. Sultan ya zaro wayarsa ya karbi lambar, 08036527328. Babu bata lokaci ya kira su ya yi masu bayanin yadda take yi. Suka ce suna da buKatar ganin mara lafiyar. Ganin yamma ta yi duk suka yanke shawarar gobe za su wuce da sassafe. Haka akayi da Safe Dr Aslaf ya fito da. mota, suka kama hanyar Kano. Cikin hukuncin Allah suka iso da ita, babu bata lokaci aka dubata aka bata magunguna, sannan suka tabbatar masu turen aljanu akayi mata. Dole suna dawowa suka sauka a Kaduna, da nufin kwana gobe sai su wuce Abuja. Nasreen tana ganin Abba ta kafe shi da, idanunta. ~Abba ya Karaso yana dubanta, “Nasreen.� Ya kira sunanta cike da fara’a itama cikin sauri ta Karasa wurinsa ta kama kuka, “Abbana, sai yau nake saka a idanuna,� Sun yi mamakin yadda take magana, bayan bata cewa um bare, um-um. Abba ya dafa kafadanta yace, “Ki, daina kuka Nasreen kin ga ba lafiya gareki ba.�Tare suka Karasa falon, ya yi wa Dr Yummah Godiya akan irin taimakon da sukayi wajen kai Nasreen gun magani. Umma ma sun gaisa babu yabo babu fallasa. Anti Mairo tana dakinta jin muryarsu yasa ta fito, tana kula da irin kallon da Umma take aika mata, sai ta kauda kanta. Abin mamaki ciwon Nasreen bai tashi ba, haka sun fara yi mata amfani da dukka magungunan. Sultan yana son yi wa Mairo magana, yana tsoron Umma, dole ya cire duk wani tsoro ya ce, “Anti Mairo ko ki leko mu.- Mairo ta dan yi dariya kawai, Umma kuwa ta sake cika babu alamun wasa a tare da ita. Kamar an ce ta dubi kafafun Nasreen, ta kafe su da ido babu ko kyaftawa. Gabanta yana ci gaba da fadiwa. Tunani ne kala-kala a cikin kwakwalwarta, tana kuma mamakin ta yadda za ayi kafafun Nasreen ya yi kama da nata. Sai yanzu ta sake karewa yarinyar kallo, tana kama da wata a cikin danginta. Haka suna diban kama da ita kanta Umman. Gabadaya ta gigice tana girgiza kai, “A’a sai dai idan idanuna ne suke yi min gizo.� Zumbur ta mike ta shiga wurin Hafsat ta ce, “Hafsa kin kuwa ga abinda na gani? Nasreen kafafunta iri daya da nawa.� Hafsat ta yi murmushi tana ci gaba da ninke kaya, “Umma sai you kika kula�? Ai hatta idanun Nasreen irin naki ne. Ki dubi Naufal da kyau ki dubi Yaya Haidar kamanninsu ya baci. Abin ya .dade yana bani mamaki, amma da yake zama wuri daya yana sauya kamanni sai ban damu ba.� Umma ta dafe kirji da karfi tana cewa, “Ko dai Abbanku ne yayi cikin yaran nan? Wallahi ban yarda da shi ba.� Hafsat ta dubeta da mamaki, tace, “Umma me ya kawo irin maganar nan kuma? Ai ba da zuri’ar Abba suke kama ba, da zuri’arki suke kama.- Umma ta zazzaro mata manyan idanunta tana dubanta, “Kaf zuri’ata basu san komai ba, in banda Alqur’ani da Hadisai, me yasa za ki ce da zuri’ata suke kama? Kai bana son maganar nan abarta kawai.� Umma ta fada zuciyarta cike da tunani. Washcgari suka tattara suka koma Abuja, suka bar Umma cikin tunani da tarin damuwa. Kwanaki biyar ta dauka tana amfani da magungunan ta ji sauki sosai kamar bata taba yin wata lalura ba. Zakiyya kuwa ta rantse in dai 6/29/22, 20:54 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Hafsat ta yi murmushi tana ci gaba da ninke kaya, “Umma sai you kika kula�? Ai hatta idanun Nasreen irin naki ne. Ki dubi Naufal da kyau ki dubi Yaya Haidar kamanninsu ya baci. Abin ya .dade yana bani mamaki, amma da yake zama wuri daya yana sauya kamanni sai ban damu ba.� Umma ta dafe kirji da karfi tana cewa, “Ko dai Abbanku ne yayi cikin yaran nan? Wallahi ban yarda da shi ba.� Hafsat ta dubeta da mamaki, tace, “Umma me ya kawo irin maganar nan kuma? Ai ba da zuri’ar Abba suke kama ba, da zuri’arki suke kama.- Umma ta zazzaro mata manyan idanunta tana dubanta, “Kaf zuri’ata basu san komai ba, in banda Alqur’ani da Hadisai, me yasa za ki ce da zuri’ata suke kama? Kai bana son maganar nan abarta kawai.� Umma ta fada zuciyarta cike da tunani. Washcgari suka tattara suka koma Abuja, suka bar Umma cikin tunani da tarin damuwa. Kwanaki biyar ta dauka tana amfani da magungunan ta ji sauki sosai kamar bata taba yin wata lalura ba. Zakiyya kuwa ta rantse in dai ZAMU TASHI tana raye ba za ta taba barin Nasreen su kebance da Sultan ba. Shi ma kuma bai sake nemanta ba, yana matuKar jin tausayinta yana son sai ta sake Warwarewa Sosa. A Katon dakin taron wanda yake mallakin Ashmaan ne, a cikin katafaren kamfanin su. Dukka jaruman ne zazzaune, suna Sauraren irin ruwan masifar da Sultan yake zuba masu babu ji babu gani. Sai yanzu ya dan tsagaita tare da sake kallon su daya bayan daya, ya ci gaba da cewa, “Abin ya ishe ni haka! Dukkanku nan hukumomi ne masu zaman kansu, akan me matsalata za ta gayareku fitarwa? Me ya sa za ku ci gaba da jan abin da tsawo? Ina Kara roKonku da ku janye ku bar ni in yi abubuwana da kaina, a kwanaki biyu rak! Zan samo wanda ake nema.� Dukkansu suka dubi juna, = sannan BarristerTajuddeen Abdulsalam yace, “Fushin nan ya yi yawa, duk wurin nan babu wanda bai yi nasa lokacin ba, in dai a kan fushi da zuciya ce. Amma da yayin mu ya Kare dukkanmu nan mata su suka sauya mu daga irin yanayin da muke, kai me yasa ba zaka canzu ba? Soja ma ya canza tasa rayuwar bare wani dan sanda?�� Sultan ya dube shi ido cikin ido ya ce, “Kayi kadan ka raina dan sanda ina wannan wurin.� Muhbub ya hada rai ya ce, “To ya ishe ka Tajjud, ka kama kanka tun wuri, dan sanda ya wuce saninka.� Khamis ya dube su ya tabe baki yana ci gaba da latsa wayarsa. Yace “Kanku ake ji.� Sultan ya fizge wayar hannunsa yana dubansa rai a bace, “Me zai sa ka dinga latsa waya ana magana mai mahimmanci?� Sai a lokacin ya dubi wayar yaga an rubuta Alhaji Na kan titi. Ya jujjuya wayar yana tunanin inda ya taba jin sunan. Khamis ya fizge wayarsa yana aika masa da mugun kallo, “Malam ina ruwanka da wayata? Ni nan aiki aka bani kuma gashi ina yi, amma ka tsaya sai hayaniya kake yi mana. Zafin kanka yana gab da sauka, in dai da ‘yar mutan Borno ka zabi tafiya.� Yamutsa fuska ya yi yi yace, “Ku kuka dauki ‘yar mutan Bornon wata abar yabawa, ni ba ita ke gabana ba, mahaifin Nasreen nake son in hukunta shi.�Ashman da yake ta latse-latsen Laptop ya dago yana dubansa, sannan ya ce, “Ka dai bi a hankali tun kafin tauraronka ya sauka daga gun ‘yar mutan Borno. Wai ma da kake cewa zaka hukunta mahaifin Nasreen, ka mance surukinka ne?� Sultan ya furzar da huci mai zafi, yace, ‘““Nayi rantsuwa ko jinina na kama da laifin nan sai na hukunta shi, dai-dai da laifinsa. Ni cinnaka ne, wanda bai san na gida ba.� Dukkan su suka kafe shi da idanun su kamar masu jin tausayinsa. Shi kansa yasha jinin jikinsa irin kallon da suke yi masa. Duk cikin su aka rasa mai Karfin halin da zai yi masa bayani, dole suka daga tattaunawar zuwa jibi. A gajiye Sultan ya dawo gida, a falo ya sami Nasreen ta ci kuka idanunta sun kumbura. Tana ganinsa ta dago dara-daran idanunta ta sauke su a bisa nasa. Mamaki ya kama shi, ya tabbata babu wanda zai aikata mata hakan sai Zakiyya. Babu tambaya ya mike cikin zafin nama zai wuce dakin Zakiyya. Nasreen ta kamo hannunsa cikin sanyin jiki, wanda yasa dawowa da baya yana dubanta. Wasu sabbin hawaye suka wanke mata fuska. ““Nasreen raina yana baci idan kina Zubar da hawayen nan. Ki daina kuka na gaya maki yana daya daga cikin abinda na tsana in ga kina yi Sharce hawayen fuskarta ta yi ta fara magana cikin rawar baki, “Dee. Su waye iyayena? Ka gaya min da gaske cikin shege mahaifiyata ta yi ta haifeni? Yanzu ni da Naufal ‘ya’yan shegu ne? Baka sona Dee, baka sona! Da har na _ tambayeka~ gaskiyar kasancewar mahaifiyata mara addini, ka Karyata hakan, har kayi min rantsuwa mahaifiyata ta bar gidan duniya tana rike da addinin Allah. Kuma yau dinnan ba sai gobe ba, zan bar maku gidanku, zan bar zuri’arku, zan daina jin gori daga bakunan ‘yan uwanka.�A lokaci guda ta saki hannunsa tare da dire maganarta cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa.� Maganar ta zo masa a bazata, a kuma irin lokacin da bai taba zato ba. Sunkuyawa ya yi kusa da ita yana dubanta cike da mamakin furucinta, ‘““Nasreen kika ce bana sonki? Kin yi gaskiya da kika iya kallon Kwayar idanuna har kika gaya min Kalmar bana sonki. Nasreen na fara sonki ne tun kina cikin mahaifiyarki, a lokacin da baki zo duniya ba, bare kisan wahalar zaman duniyar. A_ sanadiyyar in tsamo mahaifiyarki daga halin da take, har yau dinnan ban sake zama inuwa daya da mahaifiyata ba, a lokacin ne kyakkyawan ginin da mahaifina ya dade yana yi domin inganta rayuwar iyalansa ya wargaje. Ginin da har yau ba a sake tada gininsa ba, domin kuwa gyaransa sai Allah. “Muna rayuwa cikin son juna, wanda har ta kai dangi suna alfahari da mu, suna yaba mana, suna kwatance da hadin kan mutanen gidanmu, rana guda, ranar da na hadu da mahaifiyarki wannan kwatance ya rushe. Tun daga ranar na zama bare a cikin gidanmu, tun daga ranar ‘yan uwana Hafsat da Haidar suka ware ni kamar ba dan uwansu ba. “Haka na taso cikin maraicin ‘yan uwa. Mahaifina kadai ke bani goyon baya. Duk kina nufin hakan ba so ba ne? Tun zuwanku gidanmu ke da dan uwanki, mahaifina da matarsa Umman mu, suka raba hanya, ya kasance mahaifiyata tana yawan saba masa. Duk ni ne sanadi saboda na kawo ku cikin rayuwar gidanmu. Ra’ayina ba aikin dan sanda bane, amma saboda in sami daman aiwatar da bincike akan wanda ya yi sanadin zuwanku duniya, na sauya ra’ayina zuwa aikin dan sanda. Duk kina nufin ba sonki nake ba? Ban taba yi wa iyayena gardama ba, haka sun jima basu ga hawaye a idanun dan su ba, sai a dalilin mahaifiyarki. Har gobe ina kallon Anti Saudat a idanuna, har gobe ban daina kai goshina Kasa ina yi mata addu’a ba, haka na kasa kallon tarin hotunanta da suka jima a hannuna, sai dai na ba abokaina domin su nemo abubuwa akanta. Mahaifiyarki musulunta ta yi, kuma har ta bar gidan duniya tana riKe da addinin gaskiya. Yanzu za ki ji dukkan abinda kike son ji akan rayuwarki.� Ya Karashe maganar cikin raunin murya, wanda za ta iya rantsewa bata taba jinsa da irin muryar ba. . Nasreen ta dago cikin wasu hawaye masu tsananin zafi, tana girgiza kai. Idan da a ce bakinta zai iya furta magana a yanzu, da ta roki Sultan ya yi shiru da labarin da yake son bata, domin wannan ma kadai ya gigitata, ya tafi da dukkan sauran Karfin halin da ya rage mata. Tausayin kanta, tausayin Naufal, tausayin Sultan, su suka fara buga tsere a cikin zuciyarta, suna Kara sa mata damuwa. A yau ta Kara yarda, duk duniya babu mai son su da gaskiya irin Sultan. Kunyarsa ta lullubBeta, saidai kuma me mahaifinta ya yi da har Sultan zai yi aikin dan sanda saboda shi? Tana da buKatar amsoshi masu tarin yawa daga bakinsa. Wannan karon hawaye da majina suke sauka daya idanunta zuwa hancinta, ga wanii irin gumi da ke tsattsafo mata, ta jiKe ta yi sharkaf. Sultan ya mike tsaye ya kwashe yadda aka yi har ya taimaka wa Saudat zuwa haihuwarsu da ta yi, har ya gangaro kan renon su da ya sha cikin wahala. Duk ya yarda ya sadaukar da farin cikinsa saboda nasu farin cikin. .Tun Nasreen tana iya fahimtarsa har ta daina fahimtar komai, numfashinta yana kaiwa yana komowa. Ta tabbata sun gama tozarta a duniya, tunda har ya kasance aka yi wa mahaifiyarsu fyade aka samar da su a duniya. Haka babu wanda ya san waye mahaifin su. Tabbas sun tabbata ‘ya’yan shegu kamar yadda Zakiyya take ta nanata mata a kullum, wanda hakan yasa ta haddace sunan shegu, saboda yawan ambata mata da ake yi. Da Karfi ta riKe kanta, hakan bai taimaka mata da komai ba, domin kuwa a take ta zube a sume. Sultan ya tsaya kawai yana kallonta, ya rasa ma me zai fara yi mata domin bata taimakon gaggawa. Sosai yasa natsuwa a zuciyarsa hakan yasa ya tuna da ruwa, ya je ya dibo yana shafa mata a fuska. Da Karfi ta saki ajiyar zuciya, ta ware idanunta tana dubansa_ dishi-dishi. Hannunsa ta kama ta mayar bisa kanta da ke sara mata. Cak ya dauke ta ya kai cikin dakinta ya kwantar bisa gado. Zakiyya da ta gama leKen su ta saki dariyar jin dadi ta shige abinta. Nasreen tana riKe da hannunsa, ta Ki saki, gani take idan ta saki zai tafi ya barta ne. A hankali take magana, “Dee, na yi mugun � mafarki, wal� Wai� Wai� Mu shegu ne, an yi wa Mamana fyade, ta yi rayuwa a Karkashin mota, ta yi bara a titi, sannan wai, wai kakannina ba musulmai bane.. Mafarkin babu dadi Dee, babu abin sha’awa a cikin rayuwar mu, bana son mafarkin, kayi min addu’a kada in sake yin irinsa.� Wasu surutai take yi tana kuka. Sultan ya yi danasanin gaya mata wadannan maganganun, bai taba tunanin Nasreen za ta tashi hankalinta kamar yadda ta tasa a yanzu ba, bai taba tunanin Nasreen za ta: fita hayyacinta haka ba. Yana nan zaune bai iya cewa komai ba. Kafin yasan abin yi zazzabi mai zafi ya shiga jikinta sai rawar sanyi take yi. Hankalin Sultan ya sake tashi, ya kira Aslaf a waya ya gaya masa duk abinda ya faru, Aslaf ya ce, “Amma da ka sani da ka dinga gaya mata a hankali ne, domin yarinya ce Kwakwalwarta ta yi Karama da daukar irin wannan tashin hankalin. Bari Yumnah ta zo yanzu ta dubata.� Sultan ya sauke wayar yana sake kai dubansa gareta, har yanzu ta Ki sakin hannun, duk da irin karkarwar da jikinta ke yi. Shafo kanta ya yi da dayan hannunsa yana tofa mata addu’a, “Baby za ki ji sauki kin ji? Ki yi hakuri ki rage damuwar nan kin ga kin tada min hankali. Wannan Kaddarar ba a kanki aka fara ta ba, haka agun Allah kin fi wasu wadanda suke cikin musuluncin, amma basu yin aiki da abinda addinin ya fada. Ke baki da laifi, mahaifiyarki ma bata da laifi, mahaifinki shi ne mai laifin. A wurina kinfi wadanda aka Haifa ta hanyar halas. Babu wanda ya isa ya tambayi Allah dalilin aiko da Kaddara. Sai dai ma mu gode masa a dukkan yanayin da muka tsinci kanmu.� Haka ya dinga yi mata kalaman lallashi, kuma yana cin nasarar wargaza dukkan damuwar da suka taru suka hanata zaman lafiya. Yumnah da kanta ta tuko mota ta zo har gidan, ta dubata tare da bata allurai. A falo suka fito suna tattaunawa da Sultan, ta sake tabbatar masa kada ya yi nisa da Nasreen, saboda su samu jininta ya sauka. A zahiri ta yi hakan ne domin ta nesanta Zakiyya da Sultan. Kwanan Nasreen biyu ta wartsake, a lokacin kuma sunan da Sultan ya gani a cikin wayar Khamis ya tsaya masa a rai. Tunani yake yi waye Na kan titi? Domin tabbas ya taba jin sunan amma ya rasa a in da ya ji. Wannan zaman da suka yi shi suka kira da zama na Karshe, sun tabbatar za su yi Kundunbala su gaya masa komai, haka dole ya ba su hadin kai wajen zartar da hukuncin da ya dace. Sai dai fa duk taron su a cikin dakin taron, babu wanda ya iya furta komai. Yadda suka yi shiru haka Sultan ya yi shiru, ya yi alKawarin ba zai ce masu komai ba, don wulakancin ya ishe shi hakannan. Wayarsa yake latsawa, sai ga kiran wayar Alhaji Mu’azzam yayan Umma. Cikin girmamawa ya dauka ba tare da ya nemi izinin kowa daga cikin dakin ba, kamar yadda ya saba. Daga cikin wayar yake magana, “Sultan ina son nemanka, ana son a lalata min suna, kuma antabbatar min masu KoKarin aikata hakan, suna da kusanci da kai, Ashmaaan, wani mara kunyar yaron nan dan jarida, da wasu dai haka. Ina son ganinka gobe insha Allahu.� � Daga kai ya yi yana kallon su Ashmaan, zufa na karyo masa, a lokaci guda mamakin fuskarsa ta Karu da Ashmaan ya amshe wayar ya bude muryar gaba daya sannan ya fara magana, “Ashmaan ba mara kunya ba ne, domin yana girmama na sama da shi, idan suka kasance masu girmama kansu. Ba za ka sami ganin Sultan kamar yadda ka buKata ba, haka kai baka da laifi + ko alama a cikin maganar nan, masu laifin dai suna nan zagaye da kai, wanda kai baka san suna » aikata barna da sunanka bane. Muna fatan zaka yi hakuri ka barmu muyi aiki a kan Alhaji Kabir ba akanka ba. Mun gode.� Sultan ya rasa abin cewa sai kallon-kallo ake yi. Al-ameen ya yi alKawarin zai cire dukkan wata kunya da shakkar yadda maganar za ta iso cikin kunnen Sultan, ya yi maganarsa, ya gaji da yadda ake sa Meeting ana dagawa duk saboda tsoron Sultan yasan komai. Duban Sultan ya yi a lokacin da ya zare farin gilashinsa, wanda ke sake Kawata fuskarsa, “Sultan zauna mu yi magana.� Babu musu ya zauna, tare da kafe idanunsa akan na Al-ameen, da alamun shi kadai yake saurare, yana son sanin dalilin hadin sunan Baba Mu’azzam, da irin maganar nan. Da alama dai basu san wanene suke alaKanta shi da wannan barnar ba. Al-ameen ya sake duban Sultan ya ce, “Sultan Baba Mu’azzam Yayan Umma, wanda yake zaune a garin Kaduna, kuma mai Karya da addini, ina nufin ya shiga rigar addini yana abinda ya gadama, shi ne mutumin da muke ta nema akan matsalar Nasreen, ina nufin shi ne mahaifin Nasreen da Sultan. Shi ne mutumin da ya boye kansa yake ta bamu wahala wajen nemansa.� Sultan ya mike yana duban Al-ameen. Tabbas da a kusa suke da juna da babu abinda zai hana shi shake shi, a kan Kazafin da yake son yi wa Baba Mu’azzam. Sultan ya sake dubansu ya tabbatar da dukkansu sun san da wannan maganar kuma sunyi na’am. Cikjn tashin hankali sultan 6/29/22, 21:01 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA ya gaji da yadda ake sa Meeting ana dagawa duk saboda tsoron Sultan yasan komai. Duban Sultan ya yi a lokacin da ya zare farin gilashinsa, wanda ke sake Kawata fuskarsa, “Sultan zauna mu yi magana.� Babu musu ya zauna, tare da kafe idanunsa akan na Al-ameen, da alamun shi kadai yake saurare, yana son sanin dalilin hadin sunan Baba Mu’azzam, da irin maganar nan. Da alama dai basu san wanene suke alaKanta shi da wannan barnar ba. Al-ameen ya sake duban Sultan ya ce, “Sultan Baba Mu’azzam Yayan Umma, wanda yake zaune a garin Kaduna, kuma mai Karya da addini, ina nufin ya shiga rigar addini yana abinda ya gadama, shi ne mutumin da muke ta nema akan matsalar Nasreen, ina nufin shi ne mahaifin Nasreen da Sultan. Shi ne mutumin da ya boye kansa yake ta bamu wahala wajen nemansa.� Sultan ya mike yana duban Al-ameen. Tabbas da a kusa suke da juna da babu abinda zai hana shi shake shi, a kan Kazafin da yake son yi wa Baba Mu’azzam. Sultan ya sake dubansu ya tabbatar da dukkansu sun san da wannan maganar kuma sunyi na’am. Cikjn tashin hankali sultan ZAMU TASHI Sultan ya girgiza kansa ya ce, “Ku fada min sunan wani amma ba Baba Mu’azzam ba. Babu yadda za ayi Baba Mu’azzam ya aikata abinda ake zargi. Me yasa zaku zarge shi? Mene ne hujjarku? Kumaaa..� Cak ya dakata a lokacin da ya tuna kamannin Naufal da Haidar, haka suna kama da ‘yan gidan su Umma. Can kuma ya tuna ai Baba Sani Kanin Umma yana can Kasar waje da iyalansa. Baba Sani biyu ne, akwai a dangin Abba, akwai kuma a dangin Umma. Na kan titi a gabansa wani abokin Alhaji Mu’azzam ya kira shi da sunan. Amma ta yaya Malami kamar Alhaji Mu’azzam zai iya aikata wannan rashin imanin? Kai bai yarda ba, ba zai taba yarda ba, babu hujja mai Karfi a cikin wadannan hasashen. Kansa a daure ya ce, “Amma mene ne hujjarku na cewa Baba Mu’azzam shi ne mahaifin Nasreen?� Barrister Tajjud ya watso masa hotuna, sai a lokacin ya dubi hotunan da suke watse a gabansa. Ga mamakinsa, hoton Baba Sani ne, sai hoton Alhaji Mu’azzam wanda tare da Baba Sani aka dauka, abin mamaki har da shi a cikin hoton yana Karami. Ba zai taba mance lokacin da aka dauki hoton ba, a wata ziyara da Baba Sani ya dauke shi suka kaiwa Baba Mu’azzam, kasancewar Baba Sani shi ne dan gaban goshin Baba Mu’azzam. Hotunan Saudat ya kafe da idanu yana jin zafin rabuwa da ita. Kafin ya samu ya dawo hayyacinsa, Alameen ya mika masa littafin da Saudat ta yi ta rubuce-rubuce da turanci. Shafukan ya dinga budewa duk labaran soyayyarta ce da Baba Sani, sai kuma shafin da ya dauke masa hankali, shi ne shafin da ta rubuta sunan Alhaji Mu’azzam da manyan haruffa. Ya kasa dagowa saboda tashin hankalin da ya tsinci kansa. Wannan karon Ashmaan ne ya ci gaba da magana, “Mun ki bude littafin nan da ka bamu ne, saboda muna son mu yi amfani da Karfin KwdKwalwarmu, domin wannan wani abu ne mai rikitarwa. Dukkan mu =mun_ yarda_ da Kwarewarmu shi yasa muka hada kai babu dare babu rana sai mun gano wanene mahaifin Nasreen. Alhaji Kabir ya bamu wahala, mun kasa gane komai akansa, har sai da muka hada masa tarko kuma ya fada. A lokacin da ya kiran domin ya ci gaba da yi min barazana sai na gaya masa, muna da masaniyar tare da Alhaji Sulaiman suke aiki, don haka zamu zayyano sunan su, sai hakan ya daga masa hankali, wanda a zahiri bamu san suna da alaKa ba, kawai Case din su Alhaji Sulaiman ya yi kama da irin Case din su Nasreen. Da haka muka samu suka yi ta bin mu, Suna son mu gana, sai na yarda da ganawar, ta hanyar hada tafiya a tsakaninmu mu dukka, kuma kowa ya tafi da shirinsa. Cikin ikon -Allah bayan mun hadu mun tattauna, ashe sun bi bayan Mahbub, wanda babu wanda ya ankare sai saukar bindiga a dantsen hannunsa.�Sulta ya dubi Mahbub kansa a daure yadda babu wanda ya taba gaya masa, haka kuma bai taba sani ba. Tajjudeen ya ci gaba da cewa, “Abubuwa sun faru mas� yawa, a dalilin neman shaidar wanda , ya yiwa Anti Saudat fyade. Abin burgewa a ranar Khamis ya bi bayan Alhaji Kabir ya kuma ga ina ne mazaunin su a duk lokacin da suka kwaso yara, domin zuwa yi masu fyade.� Sultan ya riKe kansa da Karfi daga bisani ya dubi Tajjud cike da tashin hankali ya ce, “Kana nufin fyaden Kananan yara? Har da Baba ake yi wa yara Kanana fyade?� Ashmaan ya amshe maganar, “Kwarai kuwa. Baba Mu’azzam shi ne babban wanda ke turawa a samo yara ‘yan shekaru biyar ko sama da hakan. Haka a kowacce rana yana aikata fyade ga Kananan yara sau biyar ko sama da hakan. A ranar da muka gane Baba Mu’azzam ne, mun shiga rudu da tashin hankalin, ta hanyar da zamu iya sanar maka. Haka mun bude littafin mun samu dukkan bayanan da muke nema. Yaran aikinka da ka watsa su anan Kawo, sun samo amsa dai-dai da irin namu, mu muka hana su gaya maka komai. Haka na sami Nora na nuna mata hoton Alhaji Mu’azzam ta tabbatar min da shi ne. Don haka kamannin da kake gani a tare da Haidar da Naufal, da gaske ne, jini daya ne, haduwar jininku shi yasa ka dage sai ka taimaka wa Anti Saudat. Mun yi ta kauce maka ne dan bamu son ka san abinda ke faruwa da wuri. Da fatan a yanzu zaka sami Umma domin ta amshi ‘ya’yan dan uwanta hannu bibbiyu?� Sultan ya koma ya zauna shiru.. Bai samu ya iya magana ba, sai da ya dauki wasu ‘yan mintuna, sannan ya ce, “Mahbub ka tafi Kaduna � gobe, ka shirya min motar ‘yan sanda, zan Karaso gidan mu insha Allahu, akwai abinda zan yi.� Gaba daya suka dube shi, ba su taba tunanin zai amince da hukunta Baba Mu’azzam da wuri haka ba. Sultan ya dube su yace, “Za ku iya biyo ni mu je mu Karasa aikin nan tare. Zan kama Baba Mu’azzam zan kuma tabbatar da kotu ta hukunta shi, ko da kuwa hakan yana nufin rabuwar shi da gidan duniya ce.� Sultan ya dubi abokansa da yake jin su tamkar jininsa. Yana son ya yi masu godiya, sai dai ya san babu wanda zai so hakan. Don haka suka yi Sallama kowa ya shiga motarsa suka kama hanyar gida, a bisa sharadin goben a Kaduna kawai za su hadu. Sultan ya dai-daita muryarsa sannan ya daga waya ya kira Baba Mu’azzam a waya, ya tabbatar masa ya kashe maganar, amma kuma yana son gobe ya je gidansu ya roki mahaifiyarsa ta Kyale shi da matarsa Nasreen kada ta raba su. Babu musu Baba Mu’azzam ya amince da abinda Sultan ya roKa domin yana ganin ya gama rufa masa asiri tunda ya kashe Karar da ake son danganta shi da ita. A ranar Sultan ya kasa barci, ya kasa zaune ya kasa tsaye, a bakin windo ya tsaya yana dogon tunani. Umma ta tsine masu yafi a Kirga, ta ce zuri’arta tsaftatattu ne, na wasu ne banza. Ta ce ta tsani mara addini, bayan mara addinin tafi dan uwanta kamun kai. ‘tace ta tsani mazinaci, sai ga nata mazinacin da yara Kanana yake aikata irin nasa zinan. Umma ta tsananta tsanarta ga zina, ta yi tirr ta yi Allah wadai da mazinaci. Ta Kyamaci Saudat da abinda ta Haifa. Ji yayi an tabashi shi, bai waiwayo ba, ba shi da alamun kuma waiwayowan. Nasreen ta goge hawayenta ta saita muryarta ta ce, “Dee me ya hanaka barci? Ko nice na bata maka?� Juyowa ya yi gaba daya yana jin kunyar hada idanu da ita, kasancewar zuri’arsa ce ta ci mutuncin mahaifiyarta, dukkan halin wahalar da mahaifiyarsu ta shiga, a dalilin dangin Sultan ne, yana duba girman laifin fyade, da kuma kisa. A lokaci guda kuma idan ya tuna Karshen Kiyayyar Nasreen da Umma ya zo Karshe, duk lokacin da za ta ci mutuncinta, za ta tuna da alaka mai girma da ke tsakanin su. � Murmushi ya Kirkiro mata, “Ki je ki kwanta gobe insha Allahu, za mu je Kaduna.� Kwantar da kanta ta yi a Kirjinsa, dole suka shiga dakin tare, suka kwanta. Kowannen su da irin tunanin da yake yi, haka ko da barci yake barawo bai ci nasarar sace su ba. Da sassafe ya dauki Nasreen ba tare da yayi Sallama da Zakiyya ba, suka wuce Kaduna, da ‘yan sandansa. Umma suka samu tana ba masu_aiki umarmmin abubuwan da za su yi. A lokacin Naural yana zaune ya yi tagumi, idan ka Kura masa idanu zaka ga hawaye kwance a_ fuskarsa. Nasreen ta Karaso gabansa da sauri tana tambayarsa, “Me ya faru? Naufal kai da waye?� Umma ta dube ta cike da bacin rai, “Shi da uwarki ce, dan ba zan ce ubanki ba, tunda babu uban. Ni ce nan nace ba zan iya zama da kato a cikin gidana ba, ya tattara ya koma Makaranta da zama, ban ga dalilin zama da ‘ya’yan shegu a wuri guda ba. Kai kuma Sultan ka tabbata. Nasreen ta dawo kenan zan san inda za a sama mata ta zauna. Wallahi na tsani yaran nan, ga su kamar mayu, sun Ki barin mu.� Nasreen tasa kuka, Sultan ya dubeta a lokacin da Abba yake fitowa, domin duk ya ji furucinta. Sultan ya ce, “Ku daina kuka Nasreen, Umma bata tsaneku ba, hasalima ita ce wacce za ta fi son ku fiye da kowa, domin ku din ba dolen Abba ba ne, ba dole na bane, amma dolenta ne.� Umma ta bude baki cike da mamakin furucin Sultan, haka ma Abba ya tsura masa idanu yana kallon damuwa cike da fuskar Sultan. A lokacinne kuma Hafsat ta fito da gudu tana sheKa amai. Duk suka bi ta da kallo. Tana gama aman, Sultan ya karaso kusa da ita yana mata sannu, ya ce Nasrcmeen ta zo su jesu kaita asibiti. Hakan yasa duk suka zauna cikin zulumi, ita dai Umma bata kawo komai a ranta ba, Sultan ya dauketa sai asibiti. Suna nan zaune aka fito da sakamakonta tana dauke da ciki. Nasreen ta dora hannu a kai za ta fara kuka, Sultan ya Harare ta, dole ta ja bakinta, amma duk da hakan sai da hawaye suka wanzu a fuskarta. Hafsat kuwa hannu ta dora a baki tana ja da baya tana kuka. Sultan ya rike hannunta da Karfi ya wuce ya jefa ta a cikin mota. Ji yake kamar zuciyarsa za ta faso Kirji saboda azaban zafin da take masa. Kukan su kawai yake saurare ba tare da ya iya furta komai ba. Suna isa gida suka sami Abba Baba Mu’azzam, Baba Sani da Umma suna zaune suna karyawa. A falon ya watso da Hafsat yana yi mata wani duba. Umma ta dube shi cikin rikicewa ta ce. “Lafiya kuwa? Menene?�� Sultan bai yi magana ba, ya dubi Baba Sani, wanda bai ma san ya dawo Kasar ba. A lokacin Naufal ya shigo yana duban Nasreen da ke kuka. Shi kansa Baba Sani kafe su ya yi da idanunsa yana mamakin = irin� wannan kama. Baba Mu’azzam ma yau dai ya Kare masu kallo ba tare da ya furta komai ba. ‘Umma ta dubi su Naufal tace “Yau naga masifa. Tunda nan babu ubanku ko danginsa, sai ku fice ku bar ‘ya’yan dangi muyi magana ko? Yaya ka dai ga abinda nake gaya maka ko? Da kake cewa in barsu tare, in dai Sultan ya zauna da ‘ya’yan mazinaciyar nan babu ko shakka watarana sai sun shafa mana masifa a cikin dangi.� Abba yai yi magana, Sultan ya dakatar da shi da hannunsa. Yana jin yau zai gaya wa mahaifiyarsa gaskiya sai dai ta tsine masa. Ya waiwayo yana duban naufal da ya kamo.hannun Nasreen suka yi hanyar fita, dukkansu kuka suke yi yace, “Kai Naufal ku dawo, akwai danginku anan, kuma nan gidan gidanku ne, zaku iya sakin Jiki ku y? abinda ‘ya’yan Baba Mu‘azzam za su Umma ta zabura ta ce, “Karya kake yi Abdullahi! Babu yadda zaka hada ‘ya’yan Kwarai da shegu. Na kula rashin kunyarka sake girma yake yi, ni kuma zan sauke maka.� Sultan ya Karaso gaban mahaifiyarsa ya ce, “Umma ki gafarceni, amma su Nasreen ba su da gidan da ya wuce nan. A yau kuma zagin da kike yi masu akan basu da uba, su je su nemi uban su, mun jajirce Kwarai mun nemo masu_uba. Nasreen, Naufal ku zo Baba Mu’azzam shi ne mahaifinku, shi ne wanda ya yi wa mahaifiyarku fyade, shi ne wanda ya tura a_ kashe mahaifiyarku saboda kada asirinsa ya tonu. Baba Sani shi ya so ya auri mahaifiyarku, saboda Kaddara ta sameta ya gujeta a lokacin da ya kamata ya kusanceta, ya nuna mata kulawa, ko dan darajar addininmu da ta shiga. Umma kin jima kina tirr da mazinaci, kin jima kina aibata mazinaci, kina kasa yi masa addu’ar shiriya, saboda Baba Mu’azzam malami ne, shima ya tsani mazinaci. Sai ga ‘ya’yan shegu sun zama jininki, Hafsat kuma ta dauko maki abin kunyar da har mu mutu ba zai daina bin mu ba, Hafsat tana dauke da cikin shege a jikinta.� Baba Sani ya mike zumbur, Abba ma ya mike, haka Baba Mu’azzam shima ya mike. Nasreen da Naufal suka dubi wanda aka kira da mahaifin su duba na tsana, ba su taba jin tsanar mutum kamar mutumin da ke tsaye cikin shigar mutunci da sunan mahaifin su ba. Umma ta daga hannu ta wanke shi da mari, tana dubansa. “Kai har ka isa ka ci mutuncin Yayana uwa daya uba daya? Sultan ka cuceni, ba shi ka ci wa mutunci ba, ni mahaifiyarka ni ka wulaKanta.� A jejjere su Ashmaan suka shigo, fuskarsu babu wata rahama. Sannu a hankali suka warware masu komai Baba Sani ya dubi Baba Mu’azzam ya ce, “Yaya ka cuceni, har gobe da soyayyar Saudat nake rayuwa. Na rabota da kowa nata na kawota cikin addinina, shi ne ka zagaya ka wulaKantata, ni kuma na kasa yi mata uzuri. Sultan baka fadi Karya ba, haka dukkan bayananku ya gamsar da ni. Yanzu ‘ya’yan Saudat ne wadannan? Daman cikin jikinta jinina ya yi mata? Datun lokacin ta gaya min da ban barta ta wulakanta ba.� Abba ya dubi Umma cike da fushi ya ce, “Wallahi kin taba fuskar Sultan na Karshe, idan kika sake Kofarin marinsa, zan nuna maki kuskurenki. Kin ji kunya Salma! Yanzu ne kike girban abubuwan da kika shuka. Mazinaci kika tsana? Ga ‘yarki nan manne da abin kunya. Kin tsani ‘ya’yan shegu? Yayanki ya Haifa maki, sai ki jira haihuwar Hafsaat, domin babu mai zubar da cikin nan. Nasreen da dan uwanta sun sha gori, ashe ke ce kike dauke da abin gorin. Kin wulakanta ‘ya’yanki ba tare da wani daga cikin mu ya tayaki ba. Kin jima kina neman ubansu, to ga uban su nan a gabanki. Malam Mu’azzam ka _bani mamaki. Ban taba tunanin hakan ba, anan har da kai ake haduwa ana zagin mazinaci, a maimakon addu’a da fatan Allah ya shirya. Kun “tsani wadanda suka tuba suka koma addininku, amma baku tsani wanda ya keta haddin wacce ba addininku daya ba. Duniyar nan ina za ki damu? Yau wacce irin rayuwa muke ciki ne? Sultan da ke jin bakin ciki yana cinsa ya duKar da kai yana magana, “Babu yadda ban yi da Umma ba, akan su Nasreen amma taKi saurarena. Akan ‘ya’yanta ta wargaza gidan, ta ce ba zamu zauna lafiya ba. Bansan su Nasreen jinina bane, na damu sai an taimaka masu. Umma kullum maganganun da kike fada akan su 6/29/22, 21:06 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA sai ki jira haihuwar Hafsaat, domin babu mai zubar da cikin nan. Nasreen da dan uwanta sun sha gori, ashe ke ce kike dauke da abin gorin. Kin wulakanta ‘ya’yanki ba tare da wani daga cikin mu ya tayaki ba. Kin jima kina neman ubansu, to ga uban su nan a gabanki. Malam Mu’azzam ka _bani mamaki. Ban taba tunanin hakan ba, anan har da kai ake haduwa ana zagin mazinaci, a maimakon addu’a da fatan Allah ya shirya. Kun “tsani wadanda suka tuba suka koma addininku, amma baku tsani wanda ya keta haddin wacce ba addininku daya ba. Duniyar nan ina za ki damu? Yau wacce irin rayuwa muke ciki ne? Sultan da ke jin bakin ciki yana cinsa ya duKar da kai yana magana, “Babu yadda ban yi da Umma ba, akan su Nasreen amma taKi saurarena. Akan ‘ya’yanta ta wargaza gidan, ta ce ba zamu zauna lafiya ba. Bansan su Nasreen jinina bane, na damu sai an taimaka masu. Umma kullum maganganun da kike fada akan su ZAMU TASHI Nasreen ba masu dadi bane. Sai gashi dukka abubuwan sun taru sun dawo cikin gidanki. Baba Mu’azzam you’re under arrest!� Abba ya gyada kai, “Na ba ka izinin ka hukunta duk wani mai laifi. Bana goyon bayan zalunci, Aikinka ne kayi dukkan abinda ka gadama ba zan hanaka ba.� Mahbub ya sarawa Sultan sannan ya nufi Baba Mu’azzam. Shi kuwa ido ya raina fata, sai duban su Nasreen yake yana jinjina Karfin ikon Allah. Nasreen da Naufal suka Karaso gabansa suna dubansa, “‘Kai ba mahaifinmu bane, ba zan taba ambaton sunanka a matsayin ubana ba, ba * zan taba kallonka a matsayin mahaifi ba. Sultan shi ne gatanmu,.a duniya, Abba shi ne uban da muka budi ido muka sani, amma ko da alama ba zamu taba danganta kanmu da kai ba. Wayyo rayuwa! Me ya sa rayuwarmu bata tafi a duhu ba, da in ga wannan mutumin a matsayin uba? Me yasa kuka bari nasan wacece ni?� Nasreen ta zube Kasa kuka ya ci Karfinta ta daya hannu sama tana magana cikin kuka, “Allah na roKeka, ka hukunta wannan bawa naka tun a gidan duniya, ka hana shi kwanciyar hankali, ka aiko masa da masifu iri-iri ka wulakanta…� Sultan yana jinta ya share ta, sai Abba ne ya hanata Karasa addu’ar da take kwararowa mahaifinta. “‘Nasreen! Uba ubane, ba a taba canzawa tuwo suna. Kada ki sake yi wa mahaifinki irin wannan addu’ar kin ji?� Nasreen ta girgiza kai tana tsananta kukanta, “Abba! Abba ka daina cewa wannan mutumin ubana ne, ba zan taba yin alfahari da shi ba. Ya wulakanta uwata, ya barta tana kwana a cikin garejin motoci, cikin kwata, cikin Kazanta. Ta kwana bata ci ba, ta tashi duniya suna yi mata kallon karuwa! Suna aibatata. Tana cikin halin wahala, ga yunwa ga Kishin ruwa, ga ‘ya’ya biyu a cikinta, tana magana da Kyar, amma mutumin nan bai tausaya mata? Zai aiko a sassareta? Insha Allahu, Insha Allahu…� Takasa Karasawa saboda kukan da ya ci Karfinta. Baba Mu’azzam kuka yake yi, ya rasa me ke masa dadi.. Ita kuwa Umma kusan suman tsayé ta-yi: Ta rasa meke yi mata dadi. Nadama ce ta shigéta. Ita dama Mairo tana can dakinta ta nade tana gudun fitowa ta sami dizgi daga Umma. Hafsat kuwa bude baki ta yi tana duban kowa da ke dakin. Naufal sai yanzu ya sami daman yin magana, “Ba ni da uba sai Deedina, shi kadai ne ubana, shi ne wanda ya ganmu a cikin halin matsi da Kazanta ya kusance mu a irin wannan lokacin. Da mahaifiyarmu za ta dawo duniya, babu wanda za ta ba ‘ya’yanta sai Deedinmu. Har in mutu ba zan taba kallonka a matsayin uba ba. Ban taba-jin wata alama a zuciyata da za ta nuna min kai ubana ne ba.� Haka aka tasa Baba Mu’azzam aka fice da shi ba tare da ya samu tausayawan ‘ya’yansa ba. Su Ashamaan gaba daya suka fice bayan sun bada umamin a kamo su Alhaji Kabir. Suna , fita Sultan ya kama Hafsat da wanié irin mahaukacin duka, babu ji babu gani, domin ya fi jin tsanarta fiye da kowa. Umma ta kasa ko daga kai, gaba daya ta muzanta, ta amince laifinta ne, ta kasa yi wa ‘yan uwanta musulmai uzuri, gani take yi duk wanda ya aro addini baya daya daga cikin jerin masu shiga Aljannah, ji take kamar ita ke da ikon sanya mutum a Aljannah ko kuma a wuta, Gaba daya gidan babu dadi haka an rasa wanda zai Kwaci hafsat daga hannun Sultan. Mairo ce ta yi Karfin halin fitowa ta Kwaceta da Kyar. Abba yana zaune ya nuna kamar abin bai dame shi ba, amma acan Kasar zuciyarsa kukan zuci yake yi, yau shi ne ‘yarsa ta cikinsa take dauke da cikin shege. Nasreen kuwa da ita da Naufal suka hada kai suka zauna shiru a waje, ba su cewa um bare um um. Umma tana son yi masu magana tana jin. kunya, ba ta san da wasu idanun za ta kalle su ba. Sultan shi ya kawo masu abinci ya zauna da su, ya tsoma hannun shi, sannan suma suka sanya hannayen su, suna ci fuskar nan babu fara’a kallo daya zaka yi masu baka buKatarn yin na biyu, zaka fahimci ba su jin dadin abinciza. Da daddare Nasreen tana zaune akan dadduma tana roKorwa mahaifiyarta Rahamar Ubangiji, ta ji an turo Kofa. Duba daya ta yi wa Umma ta kauda kanta. Tana jin zafin Umma fiye da kowa, sai dai kuma darajar Sultan ba za ta iya yi mata ko da kallon banza ba. Umma ta Karaso ta zauna kusa da Nasreen Sai kuma tasa kuka. Jikin Nasreen yana rawa ta rarrafo jikin Umma ta kwanta kawai tana ci gaba da kuka. A karo na farko Umma ta rungumeta tana neman afuwanta. Ta kasa magana sai kuka da take yi, Umma tana yi mata nasiha sai daga kanta take yi alamun ta ji. Umma bata bar dakin ba, sai da ta tabbatar Nasreen ta daina kukan, sannan ta koma dakin Hafsat. Hafsat tana ganin Umma ta durKusa Kasa tana sharar hawaye. Ta ce, “Umma ki yafe min na ci mutuncinku, ban kyauta maki ba, Umma ki yafe min don Allah.� Umma ta shafa kanta kawai ta kasa magana, sai bubbuga bayanta take yi.“Na yarda da Kaddarata. Naga ishara akan Nasreen, na tsane su na wahalar da su, da ga Karshe na makantar da Nasreen, nasa aka kwashe su aka bar garin nan da su, saboda kawai bana son zama inuwa daya da mazinata. Kaicona! Da ban tashi ankarewa ba, sai da ya faru da ni. Allah na tuba. Hafsat gaya min yaushe kika yaudare ni k,’ka je aka yi maki ciki? Yaushe kika fara siyar da ;mutuncinki a kasuwa Hafsat? Hafsat tana kuka ta gayawa mahaifiyarta yadda Salim ya yaudareta da sunan zuwa gaida mahaifiyars. yasa mata Kwaya a cikin lemu. Tana kuka tana cewa, “Wallahi Umma bana cikin hayyacina ki yarda da ni,� Sultan ya Karasa shigowa yana duban Umma duba na mamaki. Ya ci alwashin idan ya kama wanda ya aikatawa Nasreen, wadannan abubuwan sai ya dauki mataki, sai dai yanzu ko da shi ne shugabarr masu daukar mataki wannan tafi Karfinsa. Jiki a sanyaye yake duban Ummansa. Ya ce “Umma� Yanzu ke kika aikatawa Nasreen wadannan abubuwan? Wallahi Umma da a ce ba a bakinki na ji ba, ba zan taba yarda ba.� Umma ta sunkuyar da kai, hatta danta kunyarsa take ji sosai. Shi kansa Abba ta kasa~ ganin fuska a wurinsa. Sultan ya nemi? wuri ya zauna, duk suka yi shiru a dakin. Ya dubi Hafsat ya ce, “Zan sa a kama Salim, sai ya dandani irin bakin cikin da yasa mu -ciki. Hafsat har yaushe kika yi wayewar bin saurayi gida? Ina. tunaninki yake? Ina iliminki da wayonki? To sai kin haife cikin kuma dole ya aureki, bayan ya gama shan wahala gidan yari.� Ya mike kawai ya fice ‘yana jinjina wai Umma ce ta makantar da Nasreen saboda tsabar Kiyayya. Washegari Sultan suka wuce Abuja, kasancewar ya sami kiran gaggawa daga office 6/29/22, 21:12 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Umma ta sunkuyar da kai, hatta danta kunyarsa take ji sosai. Shi kansa Abba ta kasa~ ganin fuska a wurinsa. Sultan ya nemi? wuri ya zauna, duk suka yi shiru a dakin. Ya dubi Hafsat ya ce, “Zan sa a kama Salim, sai ya dandani irin bakin cikin da yasa mu -ciki. Hafsat har yaushe kika yi wayewar bin saurayi gida? Ina. tunaninki yake? Ina iliminki da wayonki? To sai kin haife cikin kuma dole ya aureki, bayan ya gama shan wahala gidan yari.� Ya mike kawai ya fice ‘yana jinjina wai Umma ce ta makantar da Nasreen saboda tsabar Kiyayya. Washegari Sultan suka wuce Abuja, kasancewar ya sami kiran gaggawa daga office ZAMU TASHI A gida ya ajiye Nasreen ya wuce abinsa. Tana shiga ciki ta kama gyara ba tare da ta duba bangaren Zakiyya ba, komai ta shirya shi a ma’adaninsa tana jin tunanin mutumin da aka kira a matsayin mahaifinta yana ci gaba da addabanta. Har ta gama abincin bata bar tunaninsa ba. Ta rasa a tsakanin tausayi da tsanarsa wannene yafi tasiri a zuciyarta. Yau shigar Kananan kaya ta yi, kasancewar garin da zafi. Zakiyya ta leKo dakin ta ci burin koma me ke cikin ran Nasreen akan kwana da miji, ita sai ta daKile hakan. Yana dawowa ya fada wanka ya dan kintsa sannan ya shiga bangaren Zakiyya yace ta zauna yana son magana da ita. Babu musu ta zauna ya dubeta duba na tsanake ya ce, “Zakiyya na zo in yi maki magana ta Karshe daga haka kina iya wuce wa gidanku. Kin ganni nan? Bana son fitina, bana son tashin hankali, idan kika sake zagin yarinyar nan, ko! kika sake gaya mata maganar da Za ta sa ta kuka. Wallahi! Za ki tattara ki koma inda kika fito. Da kike yi mata gorin uba, ke waye yasan naki uban? Zan dauki mataki KwaKKwara akanki. Sai da safe.� Ya mike ya fice abinsa. Da shigarsa ta tare shi kamar wacce take jiransa. Rungume juna suka yi, ta saki ajiyar zuciya mai Karfi, “Namiji daya ne a gabana, amma yafi maza dubu. Kana da kima a idanuna, ina sonka, ina yi maka irin son da duk wanda ya tsaya kwatanta shi, bai san girman son ba ne. Yau zan yi barci irin wanda na jima ban yi irinsa ba.� Sultan ya shaki Kamshinta yace, “Allah na gode maka da na samu irin wannan tarbar a gurinki. Ban yi tunanin Kunci zai barki ki tarbe ni ba. Hakan yake nuna min ke matar Kwarai ce, mai danne damuwarta don ta faranta ran mijinta.� Ta ji dadin yabawan miinta, suka koma gado. Anan wasa ya sauya jin kansu, suke yi kamar wadanda suke dauke da Kishir ruwa. Ko da yake dukkan su makoshin su a bushe yake. Sun gama fita hayyacinsu suka ji ihun Zakiyya. Nasreen ta fara mutsu-mutsu za ta Kwace kanta, Sultan ya sake sauya salon wasansa, dole ta mance da wani ihun Zakiyya, a wannan dare Sultan ya tabbata ango, a wannan dare ya bambance budurci., da kuma_ rufa-rufa. A wannan dare ya fahimci dadin aure da yake yawan ji ana fada. Haka a wanann dare ya fahimci ashe lafiyarsa Kalau? Nasreen tasha albarka, hakan ya Kara mata juriya, sannan ta dage bata son duk wani dalili da zai batawa Sultan, ta rasa da me za ta saka masa irin wannan Kauna da ya nuna masu? Da safe ta nemi yin Karfin hali, tana ta mike ta fasa Kara saboda wani irin zafi da ya ziyarce ta. Dole ya hana ta yin komai, ya fita da kansa ya kawo mata abinci, duk abinda ake yi Zakiyya tana nan zaune a falo ta ci kuka idanunta sun kumbura. Amma ko duban inda take bai yi ba. Cikin ikon Allah kafin dare ta fara tafiya da Kafafunta, sai dai jikin babu Karfi. Dole Sultan ya dinga lallaba ta. A falo ya � ajiye su, Zakiyya ta dinga jin kamar ta shaKo Nasreen ta kasheta kowa ya huta. Sultan ya yi jawabi, ya kuma Kara da cewa yanzu ne zai yi kwanaki bakwansa, da tuntuni suka hana shi yi da matarsa, bayan kwana bakwan za su raba girki, kowa kwana bibbiyu. Ya Kara da jawowa Nasreen kunne akan ta rike Zakiyya a matsayin yayarta, duk da ita ce uwargida, yana son su mutunta junan su. Zakiyya ta dube su sosai, kawai ta kada kai ta bar dakin. ‘Nasreen ta dago cikin jin kunya ta dan saci kallonsa, ya aika mata da murmushi, yana sake ware idanunsa akanta, “Wai har yanzu kunyar ce? Ashe ban cireta gaba daya ba, ina zuwa.� Nasreen ta dago cikin nuna tsoro ta ce, “Wallahi babu kyau fa.� Ya yi murmushi yana jin natsuwa tana shigarsa. Hannunsa ya mika. mata ta noKe tana nuna masa-. hanyar dakin Zakiyya. � Murmushi ya yi ya ce. “To mene ne?� . Girgiza kanta ta yi cike da son mijinta ta ce, “A’a idan ni ce na zo naga hakan ai sai na kwana _ ina yi maka kuka. Don�haka ina.amfani da hadisi, ina son wa kaina� abinda nake sowa dan ‘uwana.� Ta mike tana Kokarin guduwa, sai dai ba za ta‘iya ba, har ya cimmata ya dauke ta, tana mutsuU-mutsu, bai dire ta ko’ina ba sai kan gadonsu. Ya hada fuskarsa da nata yana dubanta sosai, sannan yasa hannu ya ja hancinta ya ce, “Haka Allah ke lamarinsa, shi ya hada soyayyar mu tun kafin ki fito duniya. Shi ya nuna min Anti ya ce, ga matarka can a cikin baiwar Allan can, maza jeka ka dauki abinka. Bana danasanin kasancewa da ke, ko da kuwa za ki dinga dibo wuta kina Kona min jiki da shi ne Zan ci gaba da sonki har in koma ga Mahaliccina, Kanwata ta jini kuma matata.� Nasreen ta ware idanunta tana son kallon sa, sai dai kunyarsa ta hana hakan, don haka ta dan lumshe idanunta ta ce, “Ko da zan dauko bakin wuta da ninyar in Konaka bana tunanin zaka ji zafin wutan, domin babu komai a cikinsa sai ruwan sanyi. Bana jin wannan hannayen nawa Za su iya cutar da kai, bana tunanin idanuna za su tsaya kallon maKiyinka basu dauki mataki ba. Na tabbata ka haddace kalaman nan nawa, masu KanKanta amma kuma suna da kaifi, Ina sonka, Ina sonka.� Sai kuma ta rintse idanu� tana jin hawaye suna zuba daga idanunta. Hannunsa yasa a bakinta, “Shiiii� Idan kika yi min kuka sai na fasa dan bakin nan.� Haka suka sake komawa cikin shaukKin soyayyarsu kamar Za su cinye juna. Sultan ya dauki Nasreen da Umma da Naufal ya kaisu har gidan su Saudat. Iyayenta suna nan a raye, bayan sun karbe su né, Umma ta yi masu bayani, kafin su ankare*har mahaifiyar Justina ta shake Umma, “Shegu mugaye! Kun raba mu da ‘yarmu kun jawota cikin musulunci daga Karshe kuka kasheta. Haka addinin naku yake? Kuna cewa kuna da gaskiya kuna da tausayi, ina tausayin yake anan? Kune dukan mata, kune yi wa duk wanda ya musulunta gorin musulunci, ku ne Kyamatar mu, ga shegen saki a wurinku kamar kun mayar da matan riga. Tunda kun kasheta me kuke nema a wurin mu? Ku fita ku bar mana gida.�Baban Justina ya Kwace Umma daga hannun matarsa Rabeka, ya dubi su Umma ya ce, “Me ke tafe da ku?� Umma ta nuna Nasreen da Naufal ta ce, “Wadannan ‘ya’yan sune Saudatu ta Haifa. Ina . nufin jikokinku ne.� Rabeka ta kafe su Nasreen da idanu, a lokaci guda Nasreen ta Karasa kusa da ita hawaye suna zuba, tana jin za ta fi yin alfaharida_ � su, fiye da mahaifinta. Ta rungume Rabeka ta saki kuka. Rabeka ta rungume Nasreen ta hada da Naufal. Gaba daya kuka suke yi. Sai bayan sun zauna ne Umma ta nuna Sultan, sannan ta gaya masu duk yadda aka yi. Sultan yasha albarka, haka sun Karyata maganar da ake fadi akan musulmai, sun tabbata a cikin musulman akwai na Kwarai akwai kuma bata gari. Sun yi alKawarin zuwa suga gidan Nasreen. 6/29/22, 21:17 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 13 KARSHE END BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO MUN TSAYA Baban Justina ya Kwace Umma daga hannun matarsa Rabeka, ya dubi su Umma ya ce, “Me ke tafe da ku?� Umma ta nuna Nasreen da Naufal ta ce, “Wadannan ‘ya’yan sune Saudatu ta Haifa. Ina . nufin jikokinku ne.� Rabeka ta kafe su Nasreen da idanu, a lokaci guda Nasreen ta Karasa kusa da ita hawaye suna zuba, tana jin za ta fi yin alfaharida_ � su, fiye da mahaifinta. Ta rungume Rabeka ta saki kuka. Rabeka ta rungume Nasreen ta hada da Naufal. Gaba daya kuka suke yi. Sai bayan sun zauna ne Umma ta nuna Sultan, sannan ta gaya masu duk yadda aka yi. Sultan yasha albarka, haka sun Karyata maganar da ake fadi akan musulmai, sun tabbata a cikin musulman akwai na Kwarai akwai kuma bata gari. Sun yi alKawarin zuwa suga gidan Nasreen. ZAMU TASHI Nasreen kuwa taKi tafiya tace a tafi a barta, tana son yin hira da Kakanninta, tana son jin labarin mahaifiyarta. Dole Sultan ya tafi ya barta, cike da takaicin rabuwa da ita na kwana daya. Tana kwance a cinyar Kakarta sai zuwa ake ana ganinta, ta ji alamun shigowar saKo ta wayarta. Ta bude tana karantawa, “Baby kin sami su Kaka kin mance da ni ko?� Murmushi ta yi, domin ita kanta tana kewar mijinta. ‘Sorry Deena, kana cikin raina, sai dai kasancewata a cikin dangina ya fiye min komai dadi. Amma kai kasan babu inda zan je in manta ° da kai.� Yana ganin saKon ya yi murmushi yg ce, “Haba yarinya, aronki kawai muka ba su, mune * asalin danginki, da dangin uba ake ado ba dangin uwa ba.� Murmushi ta yi ta ci gaba da sauraron Kaka, kada ya dauke mata hankali ya hanata shan labari Cikin dare daga ita har shi babu wanda ya yi barci, suna manne a waya suna shan hirar su. Washegari da kansa ya zo -ya tafi da ita. Yanzu Nasreen ta zama ‘yar gata agun dangi, kowa ji da ita yake yi. Haka Baba Sani ya tabbatar mata shi ne mahaifinsu su dauke shi matsayin uba. Ita kanta Ummi duk motsi sai ta ji -dalili. Zakiyya kuwa baKin cikinta da take fama da shi, yasa taci burika kala-kala akan Nasreen. Da dawowarsu Nasreen ta fara fama da Infection mai bala’in zafi. Wasa-wasa abu ya fara nisan da ko Sultan bata son gani a kusa da ita, saboda azaba. Hankalin Sultan ya Kara tashi a sakamakon shi ma ya kamu da cutan sanyi. A wannan karon ma Yumniah ce ta sake ba su lambar Abun yabo, winda ya warkar da ita daga cutar jinnu, ta tabbatur masu idan dai maganin sanyi ne, sai dai su ji wasu suna yl, ba dai su ba. Wannan karon ta waya suka yi magana, aka turo da maganin ta mota..raba daya suke amfanr da shi, a sati daya suka nemi ciwo suka rasa. sun warke ras. � Yau ya fita office yana jin natsuwa a ransa idan ya tuna yau Nasreen dinsa ke da girki, haka yana da tabbacin zai sami natsuwar da ya rasa ta a kwanaki biyu. Lokaci zuwa lokaci yakan tuna da case din Baba Mu’azzam wanda gobe za a yanke masu hukunci. Shi kansa yasan_ ko hukuncin kisa ko hukuncin daurin rai da rai Yana kula da yanayin Nasreen kwana biyu tana cikin damuwa gosai. Da isarsa gida ya sami Nasreen tana yashe kamar bata motsi. Hankalinsa ya tashi, ya girgiza ta shiru, kanta yana fitar da jini. Cikin gaggawa ya mike ya shiga dakin Zakiyya a nan ya ji tana waya, “Shegiyar tana can a yashe a falo na kwada mata kwalba. Daga ina mata magana, kawai ta dinga yi min kallon banza ni kuma kinsanni ba ayi min in bari. Dambe sosai muka yi, gudun kada ta kada ni na kwada mata kwalba. Eh ya fita tun dazu hankalinsa yana tashe za a yankewa Mahaifin Nasreen din hukuncin kisa. Suna zagin wasu ashe su sun fi kowa abin kunya� Zakiyya ta dan saurara sannan ta saki shewa tana bayar da labarin yadda aka yi suka turawa Nasreen aljanu, da kuma yadda akayi aka mallake Sultan daga baya ya kubuta, da irin maganin da take sa masa kafin ya sadu da ita. Daga Karshe ta yi maganar da ta gigita shi wato zuwa da ta yi aka yi mata dinki dan ta koma budurwa, da haka ta raina masa hankali. Sultan ya shigo dakin yana dubanta, hakan yasa ta saki wayar a Kasa tana rawar jiki. Fizgo ta ya yi ya shiga duka babu ji babu gani, sai da ya tabbatar da ya sabauta mata kamanni sannan ya jawo hannunta ya watsar da ita waje ya kwalawa Dan sandansa kira, ya ce maza ya kaita tasha ya tabbatar ya sanyata a motar haya, ya hadata da kudin mota. Da sauri ya koma ciki, ya dauki Nasreen yasa a mota aka ja su sai asibiti. Gabadaya ya mance bai hada ta da takardarta ba. Bayan an gama yi mata Dressing ta farfado babu wanda ya iya cewa komai, sai da za su wuce gida ta riko hannunsa cikin sanyi ta ce, “Ka kaini gidan Yumnah in zauna kafin ka sama min wani gidan, ba zan zauna anan gidan ba.� Rungume ta ya yi ya ce, “Kada ki damu mu je gidan.� Bata sake magana ba, suka koma gida., Har ta gama shan magungunanta babu wanda ya ce Kala, haka bata ga Zakiyya ba, tana son� � tambayarsa amma kuma barci yana cin idanunta. ~� Anan ta zube tana barci. Har washegari da Sultan ya matsa mata su je Kotu Nasreen bata san Zakiyya bata gidan ba. Abin mamaki sai ga su Naufal da su Umma, harma da Abba da Anti Mairo. Suna nan zaune har aka yanke masu hukunci, wanda hukuncin daurin rai da rai aka yanke masu.Baba Mu’azzam ya dubi sashen su Nasreen da take kuka kamar ranta zai fita, ta kawar da kanta, Ya tsaya ya dubi su Nasreen ya ce, “Idan baku yafe min ba, na shiga uku. Idan ba ku kirani da Abba ba, bansan yadda zanyi da hakkinku ba.� Sai a lokacin Nasreen ta kula ashe ‘ya’yansa dukka su shidan sun iso wurin har da mahaifiyarsu. Dukkansu suka Karaso suna kukan halin da mahaifinsu ya shiga. Nasreen ta dago tana duban Abba, ya gyada mata kai, ta dubi Sultan shima kai ya gyada mata. Cikin sauri ta Karaso gabansa, a lokacin da Naufal ma ya Karaso kusa da shi, suka hada baki suka ce,� “Abba.� Sai kuka ya goce masu. Nasreen tana girgiza kai ta ce, “Abba ka kashe mana rayuwa, ka mayar da mu marayu. Ka jawo mana abubuwa da yawa. Abba babu wani da da zai ga mahaifinsa a cikin wannan halin ya ce zai juya masa baya. Na jima da yafe maka, albarkacin Deedi. Abba ka sa mana albarka.� Naufal da Nasreen suka durkusa Kasa. Ya dinga sa masu albarka yana gode masu, har aka tafi da shi. ‘Ya’yansa da su Nasreen suka rungume juna suna kuka mai ciwo. Har akayi kwana biyu Nasreen bata daina damuwa ba, sai da Sultan ya yi ta mata nasiha sannan ta dan sarara. Sultan ya kira Umma a waya ya ce mata, “Umma ciwon da kike ta matsawa kina tambayar wanda ya ji wa Nasreen ba kowa ba ce Zakiyya ce. Ban ce maki komai bane saboda matsalar Baba Mu’azzam. Don haka ni na gaji sosai.� Ya kwashe dukkan abinda ya ji ya gaya mata, sannan ya Kare da cewa, “Umma na saki Zakiyya saki daya. Kuma ina sake rokonki ki fita harkar Hajiya Ladidi ba. masoyiyarki ba ce. Ciki kuma da take cewa tana da shi babu komai.�Umma ta gyada kai, “Kayi min dai-dai Sultan kuma ka haifu. Hajiya Ladidi tun ranar da ‘yarta ta dawo ba mu sake shiri ba. Ashe har Babanku ta je tana nema, banda bata ni da ta yi agunsa duk yaki amicewa. Ni yanzu ina lallaba rayuwata ce. Jiya kuma iyayen Salim sun zo gidan nan, sun roki ka saki Salim sun amince za su ci gaba da kulawa da Hafsat har ta haihu, idan ta haihu sai a daura masu aure. Don haka ka sake shi kawai, ko.a haka ai ya horu.� Sultan ya shafi kansa, “Babu damuwa yadda kika ce haka za ayi. Ina Anti Mairo?� Umma ta kwadawa Mairo kira ta mika mata wayar. Sultan ya ji dadin wannan hadin kan, yana da tabbacin yanzu mahaifinsa zai dawo da jikinsa, haka gidansu zai dawo tamkar da. Nasreen tana ji an saki Zakiyya hankalinta ya tashi, za ta yi magana ya hanata, dole ta zuba masa idanu. Ita kanta ciki gareta ba tare da dukkansu sun san da cikin ba. Yau suna kwance tace, “Wai inane asalin su Umma?� Sultan ya ce, “Cewa za ki yi ina ne asalin ku? Mu ‘yan asalin Maiduguri ne, a Karamar hukumar Biu, Umma kuma ‘yan Katsina ne, da yake gaba daya dangi an dawo Kaduna, babu sauran ‘yan uwa na kurkusa a can, sai gaba daya muka koma muka saje da ‘yan Kaduna. Kin ji asalin mijinki kin ji asalinki. Ta jinjina kai ta ce, “Ya maganar su Anti Nova? Wani taimako za a ba su?� Murmushi ya sakar mata ya ce, “Su Ashmaan sun gama komai, har sun _ karbi musulunci, haka su Kaka sun karbi musulunci agun Ashmaan.� Nasreen ta tashi zaune tana dubansa, idanu a waje, “Kana nufin yanzu su Kaka musulmai ne? Me yasa baka gaya min ba Dee?� Kunnuwanta ya kama ya rike, “Tuba nake yi ina son in baki mamaki ne, in dauke ki in kai ki gidan, bansan me yasa bakina ya subuce na gaya maki yanzu ba. Babu abinda zan cewa su Ashmaan, sai fatan Allah ya biya su. Sunyi abinda, naira daya nawa ciwon kai, kowannansa ya ajiye dumbin aikinsa, ya zo ya tallafa min. Yanzu haka na shirya mana dukkan mu zamu fita Kasashe uku domin yawon bude idanu. Daga Karshe zamu dire a Saudiya mu gode wa Allah bisa dora mu da ya yi akan maKiya ya kuma bamu ikon warware komai cikin nasara.� Nasreen ta rintse idanu ta ce, ““Wato dee duk yadda nake ganin muna da hadin kai, ku mazajen mu naku yafi namu Karfi. Ina-rokon Allah ya dauwamar da kwanciyar hankali a cikin wannan zumunta. Ina son in koma Islamityya domin samun daman zuwa Gasar Alqur’anin da ake yi duk shekara.� Gyada kansa ya yi yana jinjina Karfin wayonta. Kamar an tsikare shi ya ce, “Ke wai yaushe rabon da kiyi al’ada a gidan nan?� Ta daga kai sosai sannan ta ce, “Wata biyu kenan.� Murmushi kawai ya yi bai ce komai ba_ a. Cikin hukuncin Allah cikin Hafsat ya zube, bayan ta sami lafiya sosai, aka daura aurer ta da Salim, da yake ta rawar Kafa, wanda dama yana sonta, sal kuma tsoron Yayanta Sultan. Haidar ya samu fitowa a matsayin Soja, mai ji da kansa. Ranar da suka zo gida Sultan yana tsaye yana duban yadda Haidar ya Kara girma da kyau. Haidar ya Karaso yana dariya, ya ce “Wato Yaya Sultan kwarjininka na daban ne. Ya za a yi ina sanye da kakin’sojoji, amma ka firgitani haka?� Sultan ya yi murmushi ya dafa bayansa suka Karasa gun Abba. Hankalin Abba a kwance ya yi kyau da Kiba. Yana ganin ‘ya’yansa ya saki murmushi, “Allah ya yi maku albarka. Allah ya sakawa Khamis da alkhairi. Yanzu saura aure ko?� Haidar ya dubi Naufal da shima yake gaf da dora kakin ‘yan sanda yace, “Abba amma dai a bari Naufal ya fito sai a hada mu dukka ayi mana. auren.� Gabadaya dakin suka yi dariya. Naufal ya ce, “Ai na ga kai Kanwata kake so, da alamun ni zan koma inzama yaya.� Abba ya zaro idanu ya ce, “Ba dai Badiyya yar wajen Alhaji Mu’azzam ba?� Naufal ya gyada kai, “Ita kawa Abbana.� Haidar ya ce “To gara dukkan mu a tona asirin kowa. Shi ma Rufaida yake so ‘yar wajen Baba Sani.� Abba ya yi murmushi ya ce, “Wato dai Hafsat ce kawai ta fita daga cikin dangi ko? To Allah ya nuna mana lokacin yasa ayi komai cikin nasara.� Sultan ya yi murmushi yana satan kallon Nasreen sannan ya ce, “Abba Nasreen fa bata da lafiya.� Nasreen ta kalle shi kamar za ta yi kuka, ta ce, “Ayya Abbana ba gaskiya bane, lafiyata kalau.� A nan duk suka fahimci abinda Sultan yake nufi, aka yi ta mata dariya. Cikin ‘yan kwanaki Ashmaan, Aslaf, Alameen, Barr Tajjud da su Khamis da Mahbub suka shirya da matansu za su fita Kasar, kowannen su cike da farin: ciki, domin ansan sabuwar soyayya za a bude a can. Sai mu ce Allah ya dawo da su lafiya. BAYAN SHEKARU HUDU Nasreen ce zaune tana baiwa Danta Lukman wanda ake kira da Asaad, ya ci sunan Abban Sultan abinci, yaron dan shekaru uku da rabi yi wayo abinsa. Kanwarsa Saudat wacce ake kira da Yesmeen watanta biyar a duniya tana ta sharar barcinta. Sultan ya shigo hannunsa dauke da ledoji. Cikin sauri ta tare shi, ta amshi kayan ta ajiye a Kasa ta rungume shi sosai a jikinta, “Barka da dawowa yallabaina. Tun kana hanya naji Kamshinka ashe da gaske kana tafe.� Kallon Asaad suka yi gaba daya a ya yin da ya shige sakiyarsu yana fadin “Deedina Oyoyo.� Nasreen ta zaro idanu, “Ka ji min yaro da Kwace. Deedinka, ko Deedina. Maza kaje ka . nemo Dee dinka a gidan Babanka Naufal, ko Baba Haidar.� ° Yaron ya noke kafada yana miKawa Sultan hannu. Sultan ya dauke shi yana juya shi, sai KyalKyatan dariya yake yi abinsa. Sannan ya sauke shi yana cewa, “Ina Mamana farin cikina? Don Allah dauko min ita.� Nasreen ta ce, “Ayya Dee barci take yi.� Ya Karaso har in da take kwance ya ce, “Kema kinsan duk barcin da take yi idan na dawo sai na tashe ta. Bana tunanin zan iya zama na minti biyar a gidan nan babu uwata a kusa da ni. Ita fa ta Haifa min matar da nake so fiye da kowacce.� Nasreen ta jawo Asaad ta rungume tsam, ta ce, “Ni kuma ina ji da wannan gwarzon wanda ya Haifa min miji na gari, ya kuma tsaya tsayin daka ya taya mijina renon matarsa. Bana jin ina da abinda zan iya biyanka da shi Abbana.� Gaba daya suka dubi juna suka yi murmushi. ALHAMDULILAH MASHA ALLAH ANAN MUKA KAWO KARSHEN WANNAN KAYATACCEN LITTAFIN MAI SUNA RUBUTACCIYA WANDA MUKA FARA TUN DAGA LITTAFI NA DAYA HAR IZUWA NA HUDU ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKINSA