💛 HAJAR 💛 by Nafeesah Yusuf Nagoda....✍️ A.K.A ~~(Feenerh_feeche)~~ BISMILLAH.. Dukkan godiya ga Allah ma ɗaukakin sarki da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi, kuma ina roƙonsa ya bani ikon hattamashi lafiya, ɗumbin gaisuwa zuwa ga mahaifiyata Haj Anty, My sisto Hajiya kema ina miƙo gaisuwa, my little sister Mancy and my little brother Aliyu kuma na gaisheku da gudummuwar ku wajen disturbing ɗina idan ina update, my fans kuma bazan manta daku ba a duk inda kuke Feenerh_feeche na gaisheku. Let's connect.... _Facebook account @ Feenerh feeche _Facebook page @ Feenerh feeche Novels _Facebook group @ Feenerh feeche Novels _Arewabooks @Feenerhfeeche02 ~~~~~~ {1..} wane mahalukin ne da yake lungun ƙunshi a unguwar Dala bai san gidan gini ba, aiko unguwar ka shigo sai ka san gidan gini ballanta ƴan unguwa, gida ne wanda yayi fice yayi shura a fannin hargitsi da rashin zaman lafiya, hakan ya samo asaline daga iyalan gidan da suka kasance ƴan bala'i da jaraba, Magidancin gidan da ya kasance wani soloɓiyo matansa biyu suke juyasa tamkar waina a tanda yadda sukaga dama, Allah ya azurtasa da ƴaƴa mata har guda biyar da maza uku, matarsa ta farko ƴaƴanta biyar ta biyun kuma guda uku, kullum a gidan gini sai anyi hatsaniya tsakanin matan gidan domin tamkar suna ganin hajin junansu, kwata-kwata basa jituwa kullum cikin tashin hankali suke, ƴaƴansu mata ko wacce ta shigewa uwarta, wataran idan faɗa ya kacame har saita kai ga maƙota suna shigowa rabasu saboda wataran har dambe suke idan cacar baki tayi zafii, tin maƙota na shigowa rabasu har ta kai ga an watsar dasu ana barinsu suyi faɗansu iya iyawarsu su rabu dan kansu, kai wataran idan abu yayi tsamari har sai an raunata wasu, idan akai wannan gagarumin dambe haka gidan yake yin kaca kaca, filin tsakar gidan da ko daɓe babu sai burjin ƙasa ya koma tamkar gidan mahaukata da shirgin da akai jefe-jefe da doke-doke wajen dambe, haka Magidancin nan zai shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin rabasu amma faɗa yaƙi ƙarewa daga matan har ƴaƴan nasa basa saduda sai ya yanke jiki ya faɗi wanda a sanadin haka ya haɗu da hawan jini, Malam Adamu mai gini shine magidancin wannan ɗan bala'in gida. da matansa biyu ta farko Rabi'atu wacca ake kira Maama saita biyu Fatima wacca ake kira Umma. ★Wani irin gyatsine take tana hura ɗan siririn hancinta ta fito tsakar gidan da yake duk cakwalkwali saboda ruwan da aka sheƙa daren jiya, hannuta riƙe da brush dinta da ta matso tooth paste akai, can wajen da suke tara ruwa cikin manyan tukanen ƙarfe irin wanda ake abincin gidan biki ta dosa, ta ajiye brush din hannunta akan wata murguɗaɗɗiyar kujera, ta ɗauki buta ta buɗe tukunya ɗaya ta kantami ruwa ta wuce hanyar banɗaki dake cikin wani lungu da wata siririyar kwata wacca ta ɓulla har cikin banɗakin tayi waje, ƙofar banɗakin ta langa-langa ta bubbuga, daga banɗakin aka yi mata gyaran murya, a hasale tace "koma waye aciki yayi sauri ya fito a matse nake!!!", wajen minti biyar tana jira amma ba a buɗe ƙofar banɗakin ba, ta sake bugawa da ƙarfi tace "wai wace shegiyar ce aciki ne??, dalla malama ki fito", daga cikin banɗakin aka ja wani dogon tsaki, a hasale ta banka ƙofar daman bata da sakata bare mukulli, turo ƙofar kawai ake sai a tokareta da wani mulmulen dutse da yake cikin banɗakin, Maimuna da take cikin banɗakin riƙe da buta a hannu ta kalli Hajar sama da ƙasa ta daka tsaki ta fito daga ciki, daman ta gama amfani da bayin amma da ta ji Hajar tana jiranta shine taƙi fitowa, Hajar ta karkaɗa kai ta dubeta tace "zaki sani ne??" ta shiga bayin tayi uzirinta ta fito, ta tsugunna gaban rariya tayi brush ta wanke fuskarta, ta miƙe ta shiga ɗakin umma wacca itace mahaifiyarta, umma da take zaune kan darduna tana irga cinikin kulelen da tayi jiya da yamma tace "makaranta zaki tafi Hajara?, toh wane zai auno min wake ya siyo min manja?", Hajar ta buɗe wardrobe ɗin da ta gama fatattakewa gata wata old modern gaba ɗaya ƙofofinta sun cire saidai a jingine su, ta zaro ironed uniform ɗinta tace "toh bari na shirya saina je na auno miki waken", umma tace "dama haƙura kikai da zuwa makarantar nan gashi kin makara kuma anyi ruwan sama nasan ajinku ma ya cika da ruwa", Hajar tace "A'a nidaii umma zani kinsan shirye-shiryen jarabawa muke, yau za ai mana thumb print wanda za muyi amfani dashi wajen rubuta NECO", Umma ta lalo kuɗi ta miƙa mata tace "wake kwano ɗaya sai manja rabin kwalba", Hajar ta karɓi kuɗin ta ajiye kan shirgin ƙullin kaya tace "ita Sabra ba zata makarantar ba??", Umma tace "Eh babu inda zata gaskiya, makarantarsu tafi taku lalacewa ko taje ma nasan dawowa zatai aii duk ranar da akai ruwa ba ayi", Hajar tace "tom", umma ta ƙulle ragowar kuɗinta a haɓar zani ta fita, Hajar ta janyo uniform ɗinta ta saka wanda sukay mata kyau duk da cewa ba wasu kayan ado bane, ta ɗauki kuɗin ta ɗakko slipers dinta a bayan ƙofa ta saka ta fita tsakar gida, umma ta gani tana wanke gwangwanayen kulele can bakin rariya, suka haɗa ido da Maimuna da take faman haska madubi a fuskarta tana mulka wani sabulu, Hajar tace "Banza mai bleeching", umma ta juya ta daka mata harara ta nuna mata ƙofa tace "akul zoki fita aiken da nayi miki", Maimuna ta ɗaga murya tace "uwar kice mai bleeching shiyasa ta haifeki fara", Maimuna ta cigaba da shafe fuskarta da take tamkar ta larabawa amma ƙafar nan da hannu baƙi ƙirin sai kace tayi dilke da gawayi, Sa'adatu ce ta fito daga ɗakin Maama itama dai fuskar nan taci bleeching daidai gwargwado tace "wai me naji mara kunyar yarinyar nan take faɗa miki ne??", Maimuna tace "aina gwaɓa mata maganar da ta dace da ita shegiya nunar rana", Nabila ma ta fito daga ɗaki tace "aii ni haushi kike bani Maimuna, ki zauna kina takun saƙa da waccan ƴar tatsitsiyar yarinyar har tana gwaɓa miki magana", Sa'adatu ta dungurewa Maimuna kai tace "shashasha kawai" ta koma ɗaki, umma duk tana jinsu bata ce musu komai ba kawai wankin gwangwanayenta take, Nabila ta ɗauki buta ta shiga bayi, Maimuna ta cigaba da ɗashe fuska da sabulu. Hajar tana fita daga gida ta kama hanyar shagon iliya mai awo, duk arean shine mai awon da yake fitowa da wuri, wani ɗan madaidaicin shago ne da ake siyar da kayan awo na masarufi da dai sauran ƴan tarkace, wasu maza ne a bakin shagon ɗaya yana kan benci ya kara rediyo a kunnensa ɗayan kuma yana ɗura manja a kwalba a kan wani tebur da yayi daƙal-ɗaƙal da mai da ƙura, Hajar ta tsaya a bakin shagon tace "salamu alaikum", mai ɗura manjan wanda shine mai shagon wato iliya yace "wa'alaikumus salam", Hajar tace "mal iliya a bani wake kwano ɗaya manja rabin kwalba", iliya ya shiga shago ya auno wake ya fito waje ya zuba manja a farar leda ya haɗesu a babbar leɗa ya miƙa mata, ta ciro kuɗinsa ta basa tace "Allah yasa dai manjan mai kyaune, ba irin na jiya mai warin mushe ba", iliya yace "idan an samu wata matsalar a dawomin da kayana saina baku kuɗinku", ƙasa ƙasa Hajar tace "uhmm sai kace gaske.." ta kama hanya zata bar bakin shagon mutumin da yake kan benci ya cire rediyon kunnensa yace "ke hajara akwai kulele??", ta juya tace "ka cire ke ɗin mana ka bar hajara, babu kulele sai anjima", ya kaɗa kai irin ai halinki ne yace "toh idan an gama ki kawomin ta ɗari biyu nan sai na baki kuɗin", ta yamutsa fuska tace "saidai ka tura yaro ya siyo maka" tayi gaba abunta, iliya ya koma kan benci ya zauna yace "ita da sauƙi fa", munkaila yace "inafa sauƙi, kasan maƙotanmu ne mun haɗa katanga dasu ta fuskar baya, wallahi shekaran jiya suna hatsaniyar nan tasu da suka saba iyalina ta shiga yi musu sulhu, wannan ja'irar yarinyar ce ta kwaɗa mata bokitin ƙarfe a hannu tazo kwaɗawa ƴar uwarta. harfa saida ta fitar mata da jini", iliya yace "aii mal Adamu bashi da iko da gidansa ace bazaka iya tsawatarwa matanka ba, abinda sukaga dama za suyi, ni ban taɓa ganin lusarin namiji kamarsa ba, sai kace wanda suka shanyesa", munkaila yace "ai a shanye yake, kai kana ganin wannan mutumin kasan shanyayye ne ainun, yanzu fa ƴaƴan nan nasa shafe-shafen nan na zamani suke, ni jiya da naga wata ma acikinsu ban ganeta ba saida naga tukubar hancin", iliya ya kyalkyale da dariya yace "ai jiya wata tazo nan siyan shinkafa wallahi data miƙomin kuɗi na ɗauka wani ne ya zuro hannu ta bayanta ya miƙomin kudin ba ita ba", munkaila yace "Allah dai ya kyauta ya shirya mana zuri'a". iliya ya tashi zai bawa wani yaro da yazo aunar masara, munkaila ya kara rediyonsa a kunne ya lumshe ido yana karkaɗa kai. Hajar na komawa gida ta tarar da umma tana tashin wuta a kurfotu, ta wuce ɗaki ta ajiye aiken ta fito ta kalli umma tace "ni zan tafi bazan daɗe ba inayin thumb print zan dawo", umma tace "bazaki jira na dama kunu ba??, haka zaki tafi makarantar ciki kwalam", Hajar ta kalli gawayin da umma take ƙoƙarin cinna masa wuta taga akwai lema ajikinsa tace "idan na dawo nasha, bari na gaida Baba". ta shiga ɗakin Baba da ƴar sallama, yana zaune gefen katifa yana jan wata doguwar cazbaha, ta tsugunna tace "barka da safiya Baba, an tashi lafiya??", Baba ya dubeta da wani irin yanayi, duk cikin ƴaƴansa mata yafi jinta a zuciyarsa, yace "lafiya lau Hajara, makaranta za a tafi?", tace "eh Baba, zanje ayi mana thumb print na jarabawar NECO da zamu zana", yace "Toh Allah ya bada sa'a" ya ciro ɗari biyu a aljihun wandonsa ya miƙa mata, ta sa hannu biyu ta ƙarba tace "nagode Allah ya saka da alkhairy". ta miƙe ta fita, a bakin ƙofa suka kusan yin karo da Mu'azzam wanda shine babban yayanta da suka haɗa uwa da uba ɗaya, Mu'azzam ya ɓalla mata harara ya haɗe rai yace "bani hanya..", da sauri ta matsa masa hanya ya shiga ita kuma ta kama hanyar soro. ★A hankali yake murza steering ɗin ɗumemiyar motar da yake driving, wayarsa da take gefensa ta hau tsuwwa, looking at the road ya kai hannu yayi picking ya kara a kunne yace "Salam Mami, har yanzu dai ban gane street ɗin ba, i thought Dala kika ce koh??", ya ɗanyi shiru sai kuma yace "ohk nagane, inajin nabi wrong way ne", wayar ya katse ya fara juya motar a ɗan tsukun layin da kwaltarsa ta gama ragargajewa, da yake expert ne wajen lailaya mota ya juyata cikin sauƙi ya koma ɗayan side ɗin kwarɓaɓɓen titin, yana fara tafiya wani mai mashin ya yanko gabansa tamkar an wurgosa, da sauri ya ɗauke kan motar yayi gefe da ita, motar ta faɗa cikin wani ruwan kwatami na ruwan sama da kwatocin gidajen mutane da suka ɓulla cikinsa, ruwan kwatar da jar ƙasa ya feshe Hajar da take tsaye a bakin wajen tana jiran napep, gaba ɗaya uniform ɗinta suka ɓaci da jar ƙasa, ga wani wari da ruwan yake na kwata, Hajar tabi jikinta da kallo ta hangame baki, a matuƙar zafafe ta dubi motar da tayi mata wannan aika aikar lokacin da mutumin ciki ya buɗe ƙofar driver......✍️ 💛 HAJAR💛 by Feenerh_feeche {2...} Fitowa yayi daga motar yana hangen mai mashin ɗin da ya shigo masa har ya bulale tsukun layin da hayaƙi ya fece, cikakken gashin kansa ya shafa yana ƙanƙance ido sai kuma ya kalli motar tasa da take cikin kwatami tsamo-tsamo, gefenta ya karkace wajen driver ne kawai bai shiga kwatamin ba, tsirarun mutanen da akai abun a kan idansu suka taso, Hajar da zuciyarta take tafasa tana kallon uniform ɗinta da bazasu taɓa tafiyuwa a wajenta a haka ba, wani ƙululu ne ya tsaya mata, what the heck isn't he going to apologise, a hankali ta taka tana tsantsamin kanta ta isa gabansa inda yake ƙoƙarin buɗe motar zai shiga, ya kai hannu kenan zai buɗe ƙofar motar ta riƙe handle ɗin tace "malam ba kaga abinda kayi bane??", da wani irin salo ta juya fararen idonta ta nuna masa uniform ɗin jikinta dasu, kallo ɗaya tak yayi mata yace "ohk sorry it was not my fault", up and down ta kallesa ta tsugunna ta kwarfo ruwan dattin a duka hannayenta ta shaɓune masa a farar Tshirt ɗin jikinsa, ta kama hanya fagam-fagam zata bar wajen, wani mutum ne ya kalleta yace "amma wallahi ke dai baki da kirki..", ta juya ta kallesa sai taga da ɗan girmansa zai iya kaiwa sa'an babanta hakan yasa ta mayar da asalin abin tayi niyyar fada tace "oh shi bakuga rashin kirkinsa da ya feshe ni da kwatami ba", mutumin yace "amma ai ba sa'an ki bane kuma ya baki hakuri yarinya", cike da tsiwa Hajar tace "banga zan iya hakura ba gaskiya" tayi gaba abunta, wani ne ya taso yace "au baka ganeta ba aii ƴar gidan gini ce zata iya aikata abinda yafi haka ma". kawai gaban Tshirt ɗin jikinsa yabi da kallo lokacin da kunnensa yaji (au baka ganeta ba, ai ƴar gidan gini ce zata aikata abinda yafi haka ma). Hajar na shiga gida tin daga soro ta rushe da kuka, ita duk wannan tsiwar ta ta kuka baya mata wuya, daga zarar zuciyarta ta ɓaci tom sai tayi kuka take jin daɗi, da Sa'adatu ta fara cin karo hannunta riƙe da bokitin ruwa da kwandon soso da sabulu zata shiga bayi, Sa'adatu ta daka wani uban tsaki tace "da murya sai kace ta gardawa an cikawa mutane gidan uba", Hajar ta sharce hawayen idonta tace "saiki nuna wanda ya diro daga sama jahila" ta ƙarasa shiga ciki, Sa'adatu ta mulmulo wata ashariya tace "ni yarinyar nan zata kira jahila" ta dire bokitin da kwandon ta biyota da gudu, kafin ma ta cimmata harta shige ɗakin umma, Mu'azzam da yake bakin ƙofa ya kalleta sama da ƙasa yace "ina makarantar??", Hajar tace "ba ina tsaye a bakin titi ina jiran napep ba wani mai mota ya fesa min cakwalkwali", ta cigaba da kukanta, Mu'azzam yace "A'a kinga malama ki rufewa mutane baki, ki canza wasu kayan ki tafi makaranta", Hajar na shessheƙar Kuka tace "toh aii banida wasu uniform ɗin kuma ance kowa da kayan makaranta za ai masa online registration", umma tace "Mu'azzam dan Allah daure ka rakata makarantar nan tinda kace yau bazaka aiki ba, ke kuma maza kije ki ɗauraye jikinki kizo ki canza kaya", Mu'azzam yace "karki ɓatamin lokaci ina ƙofar gida", ya fita daga ɗakin, Hajar ta wuce bakin rariya ta cire hijab ɗin jikinta ta ɗebi ruwa a buta ta fara ɗauraye inda cakwalkwali ya ɓata ta, cikin sanɗa Sa'adatu ta taho ta cakumo wuyanta tace "yanzu sai ki gayamin wace ce jahilar??", Hajar tace "dalla malama sake ni..", Sa'adatu tace "anƙi a sake kin, me zaki iya??", Maama ta yaye labule ta leƙo tace "naɗi ƴar iska, ki canza mata kamanni", Sa'adatu ta sake maƙure wuyan Hajar har saida idonta suka firfito amma baki nan bai mutu ba cewa take "Allah ya isa, muguwa azzaluma mai bleeching", mai bleeching ɗin nan shi yafi ƙonawa Sa'adatu rai don haka ta kamata da kokawa, Hajar da take ganin bazata ɓata lokacinta a nan wajen ba ta daddage ta danna mata wani mugun cizo a damtse, Sa'adatu da zafin cizo ya ratsa mata kwakwalwa da sauri ta saketa ta lailayo ashar tana kallon damtsenta da haƙoran Hajar suka fito ainun, cizon ya shigeta sosai domin ƙiris ya rage wajen bai fashe ba domin kuwa jeka huda yayi, Hajar ta manna aguje ta shige ɗakin umma tana waiwayen Sa'adatu. ★Sanye take cikin fararen kaya riga da wando sai wani ɗan ƙaramin hijab V-shape, ta ɗora kimono a saman kayan, hannunta riƙe da mug mai ɗauke da coffee, a hankali take tafiya har tazo ƙofar office ɗin tayi knocking a hankali, daga ciki akace "come in..", ta murɗa handle ta shiga ciki da ƴar sallama, secretary ta amsa tace "welcome Nurse Ruqayyah..", tace "yawwa Halima Doctor bai ƙaraso ba ne??", Halima tace "yes i think he is on his way", Ruqayyah tace "Ohk, bari na jirasa aciki", Halima tace "ohk then", Ruqayyah ta shiga babban office ɗin da ya gama ƙawatuwa, ga wani ƙamshi da sanyin Ac da yake tashi a cikinsa, Mug ɗin hannunta ta ajiye kan table ta ɗauki hoton da yake dirke a gefen table ɗin wanda ya haska fuskar wani mutum wanda yake sanye da lab coat ya rataya stethoscope a wuyansa, hannayensa zube a pocket ga kuma wani murmushi da yake shimfiɗe a fuskarsa, Ruqayyah ta zauna kan chair still looking at the picture, 20mins passed amma bata gaji da kallon picturen ba, ƙofa aka murɗa mutumin da yake cikin picturen ne ya shigo, hannunsa riƙe da briefcase, a hankali ya mayar da ƙofar ya ƙaraso ciki yana kallon Ruqayyah da take riƙe da hotonsa, briefcase ɗin ya ajiye akan table sannan ya cire lab coat din jikinsa ya ratayeta ajikin kujerar zamansa kana ya zauna, ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace "good morning babe.. tinda yau ba za a gaishen ba", ta kallesa a fakaice ta zumɓuro baki tace "Dr yau mesa ka makara?, kuma nasan kanada surgery scheduled yau at 12pm", with a soft smile on his face yace "really akan surgery nan kika damu ko kuma mai yin surgeryn?", wani irin cuno baki tayi tace "of course not i care for the surgery not the surgeon", murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa yayi yace "My coffee ko yau rowa za ai min?", ta mayar da hoton mazauninsa ta ɗauki Mug ɗin da ta ajiye ta miƙa masa tace "Here", ya amsa yace "thanks", one sip yayi ya ajiye yace "ya huce aii", tace "tinda ka makara yau mai sanyi zaka sha, now tell me, mene ya makarar da kai?", yace "ohh Mami ce ta turani na amso mata wani saƙo shine nabi wrong way, har car na ya samu matsala, you know yesterday anyi ruwa toh wani ruwa na faɗa a street ɗin, i wasted my time there looking for a solution", tace "ohk, Allah ya kiyaye", yace "Ameen, har yanzun ma coffee mai sanyi zan sha?", juya idanunta tayi ta miƙe ta duba wrist watch ɗinta tace "Byee, zan shiga surgery da Doctor Mansoor, see you later after the surgery.." ta fita ta rufe ƙofa. wasa ya farayi da yatsun hannunsa yana juyi a kan kujera idonsa a lumshe yana tunanin the girl he encounter with this morning, her face look so innocent but she's stubborn, ƴar gidan gini.........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {3...} Ƙarfe sha biyu na rana Dr Uthman ya shiga surgery with his well trained team, shi ƙwararren likita ne da ya karanci ɓangaren thorax da duk wani abu that is located in the chest region, alhmdllh surgeryn da Dr Uthman yayi was successful, yana dressing room yana cire kayan da yayi surgery dasu Dr Marwan ya shigo wanda shine yayi masa first assistance, Dr Marwan ya buɗe lockern kayansa yace "gaskiya Dr surgery nan yayi kyau, gashi patient ɗin ya daɗe da ciwon amma kuma komai yayi kyau", Dr Uthman yace "everything goes well saboda aikinku mai kyau my team members, idan babu ku ai komai bazai yi daɗi ba", Dr Marwan yayi murmushi yace "still dai kaine 70 percent na success ragowar percent ɗin aka raba mana", Dr Uthman yace "Marwan next week inada surgery amma bazan samu damar zuwa ba, kaine za kayi heading sai Khaleel yayi first assistance", Dr Marwan yace "sure Allah ya kaimu", Dr Uthman ya mayar da lab coat ɗinsa ya wuce office, Halima tace "welcome Dr akwai patient da yake jiranka, zan iya shigo dashi??", tsadadden wrist watch ɗinsa ya kalle yace "am off amma ki shigo dashi tinda ya riga yazo", tace "yes sir" ta ɗauki landline ta kira reception tace "hello patient ɗin da yake jiran Dr Uthman ya shigo yanzu" ta katse kiran. babu jimawa patient ɗin ya shigo office ɗin, Dr Uthman ya kallesa yace "referral ne??", patient din yace "Eh" ya miƙa masa wata takarda cikin envelope, glasses dinsa ya ɗauka ya kwamawa idanunsa kana ya karanta takardar tas yace "mal shu'aibu jeka ka kwanta a wancan gadon" yayi masa nuni da gadon da yake a can edge of the office, mal shu'aibu ya kwanta a gadon, Dr Uthman ya ɗauki stethoscope ya isa bakin gadon ya fara dubasa, bugun zuciyarsa ya fara ji sannan yace "mal shu'aibu kaja dogon numfashi", mal shu'aibu yayi yadda aka umarce sa, bayan Dr ya gama duk wani gwaje-gwaje ya koma mazauninsa yayi rubutu ya basa yace "tests ne guda biyu, ayi su kafin nan da sati mai zuwa sai a kawomin", mal shu'aibu yace "nagode likita" ya karɓi takardar ya fita. Dr Uthman ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern Nurse Ruqayyah wacca yayi saving da Love, ya jingina da kujera ya kara wayar a kunne. Nurse Ruqayyah tana zaune a nurse station taji wayarta na vibrating cikin aljihun rigarta, da sauri ta zarota ganin mai kiran tayi murmushi ta kara a kunne tace "my Dr badai harka fito ba??", daga ɗayan side din Dr Uthman yace "yeh na fito, yanzu ma zan wuce, yaushe zaki wuce gida?", tace "ohk, zan yiwa wata da za'a yiwa CS Anesthesia ne kafin na wuce gida", yace "ohk, byee Love", tayi murmushi tace "byee" ta katse kiran, Nurse Jidda da take kallonta tace "gaskiya Ruqayyah kin afka, yanzu fa shekara biyu kenan kuna tare da Dr Uthman, wai yaushe za muga cigaban wannan soyayyar ne??", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ta taɓe baki tace "kwana nan zamu girbi soyayyarmu inshallah, kinsan dai cewa iyayena sun san dashi tinda ya tura magabatansa sunje nema masa izinin zance, toh tin lokacin suka so su bada kuɗin aure, amma Daddy yaƙi amincewa yace sai mun fahimci juna tukun, toh dai tin daga lokacin ba a sake maganar kai kuɗi ba, daman bai gama shiryawa ba yana so ya ƙarasa gidansa kuma ya zama rigid a business ɗinsa, to alhmdllh komai dai ya zama settle gida ma har an saka masa padlock ya gama komai, and his business shima alhmdllh, last week yake gayamin cewa zai turo magabatansa a kawo kuɗi sannan asaka rana, though shi baya so asaka sama da three months, amma nasan Daddy bazai amince ba saboda he is not ready, toh kinji yadda muke ciki", Jidda ta jinjina kai tace "ohk mashallah, Allah ya tabbatar da Alkhairy", Ruqayyah tayi murmushi tace "Ameen". ★Umma na zaune akan kujera tana zuba ƙullun kulele cikin fafaffun gwangwanayen da aka shafesu da Manja, Sa'adatu ce ta fito daga ɗakin Maama taci kwalliya, wata riga da skirt ta saka na material mai rawa, kayan sun ɗameta sosai da kyar take tafiya ga takalmi mai uban tsini a ƙafarta, mayafin da ta saka dashi gara babu, fuskar nan ɗaɗau tasha hoda da mai, Baba ya fito daga ɗakinsa ya kalleta sama da ƙasa yace "ina za kije Sa'adatu?", Sa'adatu ta zumɓuri baki tace "Baba daman bikin wata ƙawarmu ake, yau ne ɗaurin aure", yace "toh wa kika tambaya da zaki fita a haka?", Sa'adatu ta yamutsa fuska tace "na gayawa Maama ai", Baba ya sake kallon shigar jikinta yace "koma ɗaki babu inda zaki", ta tsaya tana ƙunkuni da murguɗe-murguɗe, ya zabga mata carbin hannunsa a baya, ya sake ɗaga hannu zai zabga mata ta ruga da gudu tana gurɗewa ta afka ɗakin Maama, Nabilah da take laɓe a jikin labule ta tuntsure da dariya tace "Baba ya matsa lamba", Maama ta miƙe ta fita waje daman kaf tana jin abinda ya faru, Baba ya juya zai koma ɗaki Maama tace "haba mal ya za ai ka daddage ka daki yarinya budurwa haka, inaji dai ta gaya maka na bata izinin fita shine kake mata wannan dukan", ya juya ya kalleta yace "indai ni na haifi Sa'adatu to ban amince ta fita a haka ba", Maama ta ɗaga murya tace "Toh ai ba kai kaɗai ka haifeta ba malam, nice nan uwar Sa'adatu kuma ta samu amincewa ta", da karfi Maama tace "ke Sa'adatu maza fito ki kama gabanki, Allah ya tsare", Sa'adatu daga ƙuryar ɗaki tace "Tom Maama gani nan fitowa", Baba yace "Rabi ki cigaba da ɓata tarbiyyar ƴaƴanki, yaran nan ko makaranta sunƙi zuwa, ba arabi ba boko, wallahi muddun baki canza ba wataran zakiyi kuka da idanunki", Maama ta zabga uban salati tana tafa hannaye tace "Malam da sanyin safiyar nan kake ƙoƙarin yimin baki, kana kiramin kalmar kuka da idanuna, na shiga uku ni Rabi yau na gamu da jafa'i", Baba ya girgiza kai yace "ƴaƴanki bazasu taɓa koyi da ƴar uwarsu Hajara ba, yarinya mai son karatu", da gudu Nabilah ta antayo daga ɗaki tace "Baba Allah ya tsaremu muyi koyi da wannan tabbatacciyar shegiyar yarinyar", sai a lokacin Umma ta tanka tace "ke karki sake kiran ƴata tabbatacciyar shegiya na gaya miki", Maama ta rangaɗa wata shegiyar guɗa tace "ahayye, da Mu'azzam da Hajara duk shegu ne, da tsohon cikin Hajara da Mu'azzam yayayye kika zo gidan nan", Umma tace "ga ubansu nan, kuma shi yasan ƴaƴansa ne", Maama ta tafa hannaye tace "laha'ila ha illallahu, kuji fa wai Adamu ne uban Hajara da Mu'azzam, yau naga inda ake liƙawa mutum ɗan shege ta ƙarfin tsiya, wallahi ƙarya kike faɗima Sabra ce kaɗai ƴar Malam amma wallahi Hajara da Mu'azzam saidai ki nemo musu uba", Baba ya nuna Umma yace "faɗima karki sake cewa komai, koma ɗakinki", Umma ta rufe ƙullun kulelenta ta shiga ɗakinta, Sa'adatu kam tunda taji tsakar gida ya fara ɗaukar harami ta rungume cogen takalminta ta fita sum-sum tamkar munafuka tayi soro, Baba ya kalli Maama yace "Allah ya shiryeki Rabi idan kinada rabo" ya koma ɗakinsa, ai Maama saida ta gama kumfar bala'i ita kaɗai sannan ta koma ɗaki, Nabilah tace "Maama kinga har yanzu Maimuna bata dawo ba sai kace wacca aka aika wata duniyar", Maama ta zabga tsaki tace "inajin ta tafi sabgar gabanta". ★Washe gari da misalin ƙarfe biyu da Rabi na rana, Hajar ce ta fito tsakar gida sanye da uniform ɗinta na islamiyya, daga bakin rariya ta hango Naseer yana goge kaushi tace "yaya ina wuni", yace "lafiya Hajar makaranta za'a tafi", tace "Eh, Sabra nake jira", yace "toh Allah ya bada sa'a", sai kuma ya miƙe ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin Maama ya kwalawa Maimuna kira, saida ya sake kiranta sau biyu sannan ta fito tace "yaya gani", yace "ke bazaki fito ki tafi makarantar ba", tace "yaya wace makaranta kuma??", ya daka mata tsawa har saida ta firgita yace "islamiyya mana", ta fara inda-inda tana mutsuttsuka hannaye tace "daman yau bazan je ba, Maama bata nan, Nabilah da Sa'adatu suma duk sun fita, wa zan barwa ɗakin Maaman??", yace "shiga ki sako kayan makaranta ki wuce ki tafi", tace "toh yaya wai wa zan barwa ɗakin..", kwalla mata mari yayi har saida ta bugu da bango yace "duk abinda kuke agidan nan kawai kallonku nake, yaushe rabon da kije makaranta, zaki wuce ko saina tattaka ki", a guje Maimuna ta afka ɗakin Maama tana gursheƙen kuka, ta buɗe Ghana most go ta ɗakko zumbulelen hijab ɗin islamiyya wanda rabonta dashi wajen wata huɗu, yaci uban squeezing yana warin ajiya, ta lalubi inda Maama take ajiye padlock ta ɗauka ta fito, Naseer yana tsaye a bakin ƙofar bai tafi ba ya kalleta ganin squeezing ɗin da hijab ɗinta yayi yace "ƙazama", Maimuna ta kulle ɗakin ta rufe fuskarta da hijab ta cigaba da kuka, Naseer yasa ƙafa ya kwarfeta ta baje a ƙasa yace "miƙe munafuka, ai Maama ce ta kyaleku kuke yin abinda kukaga dama, wallahi daga yau kika sake fashin makaranta saina tattaka ki mara kunya", da gudu tayi waje tana kuka, Hajar ta rufe fuskarta da hijab tana tiƙar dariya a zuciyarta tace (Allah shi ƙara), Sabra ta fito suka kama hanyar islamiyya. Hajar tana zuwa ajinsu Abubakar Siddiq wanda shine ajin sauka ta tarar har an fara bitar Al'qurani tinda sunyi sauka, saida aka gama bitar sannan Zainab ta taɓo Hajar tace "me yasa jiya bakizo ba?", Hajar tace "kinsan shirye-shiryen NECO muke, to jiya akai mana online registration", Zainab tace "nima ai naje registration ɗin kuma nazo islamiyya", Hajar tace "nida na kusa samun matsala, ai ina gaya miki saura ƙiris ayi NECOn bana ba ni", Zainab tace "A saboda me??", Hajar ta kwashe kaf abinda ya faru ta gaya mata, Zainab ta zabga mata harara tace "dalla malama gafara can, wai da kika ƙi haƙura kika shafa masa kwatamin mene ribarka?", Hajar tace "zuciyata tayi sanyi aii", Zainab tace "ki ringa haƙuri ƙawata dan Allah", Hajar tace "uhmm nidai akai min saina rama wallahi", Zainab tayi murmushi tace "mutuminki fa ya shigo ajin nan yafi sau ashirin jiya", Hajar ta yamutsa fuska tace "wa kenan??", Zainab tace "wa kika sani bayan ya sayyadi Nura..", Hajar ta juyar da fuskarta tana murmushi..........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {4...} Biyar da rabi na yamma ya sayyadi Nura ya shigo ajin yi musu kiran suna, idonsa akan Hajar ya fara sauka wacca ta sunkuyar da kanta tana duba abinda babu a jaka, Addu'a ya fara yi musu kana ya fara kiran suna, duk wanda aka kira sunansa sai ya tashi ya tafi gida idan kuma kasan kayi fashi sai ka jira ai maka hukuncii, ajin ya ɗaɗe ya rage daga Hajar sai ya sayyadi Nura, register ya rufe ya maida hankalinsa gareta, a hankali yace "Hajara mai yasa jiya kika yi fashi", Hajar ta haɗiyi wani yawu ba tare da ta kallesa ba tana wasa da hannunta cikin hijab tace "ya sayyadi online registration naje na NECO kuma ban dawo da wuri ba", ya sauke ajiyar zuciya yace "toh saiki dage da karatu kinji??", tace "Insha Allah", yace "har yanzu dai Nursing ɗin kike son karanta", a karo na farko da ta ɗago fararen idanunta sai kuma tayi sauri ta mayar dasu ƙasa tace "Eh", yace "toh shknn, indai kin ɓaro marks Insha Allah zaki tafi Nursing School", tace "insha Allah zanyi ƙoƙari", ya ringa kallonta sai kuma ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yace "lokaci nake jira na nemi izini wajen Baba na ringa zuwa wajenki a gida, iya ganin da nake miki a makaranta yayimin kaɗan gaskiya, ace kullum idona baya ci ya ƙoshi", ta janyo hijab ɗinta ta rufe fuska murya can ƙasan maƙoshi tace "ni gida zan tafi", yayi murmushi mai sauti yace "toh taso ki tafi", a hankali ta tashi ta ɗauki jakarta ta fita a ajin ba tare da ta bari ta kalli wajen da yake ba. a gate ta tarar da zainab da take jiranta suka rankaya suka tafi gida. da daddare Hajar na zaune akan tabarma tana cin tuwo, umma ta fito daga ɗaki da mafici a hannunta itama ta samu guri ta zauna tace "kai gaskiya yau akwai zafi inajin hadari ne a garin", Hajar tace "ɗazu ma naga ana walƙiya, ina sabra ita bazata fito tasha iska ba sai sanƙarau ya kamata?", umma tace "tayi bacci kinsan daga anyi sallar isha'i take kwanciya". Maama tana daga can ƙofar ɗakinta tare da Maimuna wacca ta kawo mata ƙorafi akan Naseer. garin zafi ake shiyasa suka firfito tsakar gida shan iska, Hajar ta miƙe ta kai kwanon da ta gama cin abinci wajen wanke-wanke ta ɗebi ruwa tana wanke hannunta, Sallamar Baba ta janyo hankalin kowa garesa, Hajar tace "sannu da zuwa Baba", ya amsa yana miƙa mata ɗaya daga cikin ledar da ya shigo dasu, Maimuna tana ganin ya miƙawa Hajar leda ta miƙe zaune daga kan cinyar Maama tace "Baba sannu da zuwa", yace "yawwa zoki karɓar muku naku", Maimuna ta taso da sauri ya bata leda ɗaya ya wuce ɗakinsa da guda tinda ledojin uku ne. Hajar ta kaiwa umma ledar ta samu guri ta zauna ta tanƙwashe ƙafa, Umma ta buɗe leda, karfashe ne mai zafi ga kuma yaji a gefe, umma tace "kai Allah ya saka da alkhairy ya ƙara buɗi, sako hannu muce Hajara", a hankali Hajar take ƙurmushe karfashen saboda tana sonshi. Maimuna kam tana buɗe ledar ta kalli Maama tace "Chaɓ, daman tinda naji ƙarni nasan wannan abun ne", Maama ta warce ledar tace "idan bazaki ci ba ki barshi" ta ɗauki guda ɗaya ta luƙa a baki ta ƙurmushe, Nabilah ta fito daga ɗaki da fitilar wayarta rakani toilet ta haska kifin hannun Maama tace "me kuke ci ne naji ƙayau ƙayau ana tauna?", Maama tace "karfashe ne idan zaki ci, yanzu babanku ya shigo dashi", Nabilah ta taɓe baki tace "ni kam bazan ci ya farfasan baki ba, kina ganin abu sai kace ƙanzo, Sa'adatu nake jira nasan bazata shigo gidan nan hannu rabbana ba", Maimuna tace "wallahi nima ita nake jira", Maimuna tana rufe baki saiga sallamar Sa'adatu, hannunta riƙi-riƙi da ledoji, da sauri Maimuna ta tarota ta amso ledojin, Sa'adatu ta zauna kan tabarma ta fige ɗankwalin kanta tace "wash nagaji, Maama yau kam ai banyi dare ba ko??", Maama ta kawar da ledar karfashen da take ci ta suɗe hannu tace "Eh yau ba kiyi dare ba ƴar albarka", Sa'adatu ta warce ledojin hannun Maimuna tace "cewa nayi ki buɗe, ai kya bari na buɗe da kaina", Sa'adatu ta ciro takardar tsire da ƙatuwar robar ice cream tace "Maama ga naki", ta ciro wata takardar da kuma robar ice cream ta miƙawa Nabilah tace "keda Maimu". ta kwashi ragowar ledojin ta shiga ɗaki. hannu baka hannu kwarya sai kace mayatattu suke cin tsiren nan suna yaɓa ice cream a baki, Maama sai habaici take zubawa faɗi take "haihuwa tayi min rana, ina zaune akawomin tsire da ƙanƙara mai madara na more, wasu kam sunyi asara kullum saidai a kawo musu takarda ace anyi ƙoƙari a jarabawa", Nabilah ta danna tsire a baki tace "yo daman shege yanada wani amfani ne, ai amfanin shege bai wuce baƙin fenti ba". Hajar ta miƙe ta zazzagi omo ta wanke hannunta ta shiga ɗaki, muddin ta zauna a tsakar gidan nan to kwa tabbas za a iya tashin hankali domin kwa ba haƙuri ne da ita ba musamman ma aka taɓo mata uwa. Washe gari da wuri Hajar ta dawo daga school saboda ranar juma'a ce, umma ta tarar tayi shirin fita, Hajar ta ajiye jakarta tace "Umma fita zakiyi ne??", Umma tace "ta dole ce Hajara, gidan Jamila zanje na duba jikin Hafsa, kar abin ya zama shiririta na shiga wata sabgar ban dubata ba", Hajar tace "to bari nayi sauri na shirya saimu tafi tare", Umma ta girgiza kai tace "da ke nayi niyyar zuwa amma hakan bazai yiwu ba, inada ragowar kulele da ban siyar ba wajen ta dubu, daman ranar juma'a sai bayan masallaci akafi ciniki, ga Sabra nan ta tayaki zama bazan daɗe ba Insha Allah", Umma ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace "Hajara karki biyewa kowa ayi tashin hankali dake kinji", Hajar ta jinjina kai tace "Allah ya tsare sai kin dawo..". Hajar tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa roba-roba, ta dasa kujera a tsagar gida tana yankewa Sabra farce, Sabra ta zille ƙafa tace "dan Allah Adda karki yanke ni", Hajar ta ɓalla mata harara ta fuzgo ƙafar tace "da can da nake yanke miki na taɓa yankar ki ne??". wani yaro ne yayi sallama siyar kulele, Sabra taje ta amso kuɗin Hajar ta zuba masa a kwanon da ya kawo, Hajar ta shiga ɗaki ta ɗakko canji ta bata ta kai masa tare da kulelen, saida yaron ya tafi ta tina cewa bata zuba masa yaji ba, tasan aiken iliya mai awo ne tinda taga kwanonsa ne, indai shine sai ya dawo yace a zuba masa yaji, ta zauna ta ƙarasawa Sabra yankar farcenta, tana gama mata ta fita wasa ita kuma ta shiga bayi, tana toilet ta jiyo yaron ya dawo yanata ɓurari wai a zuba yaji a kulele. Sa'adatu ta fito tsakar gida da kayanta haɗin bauta, zani jaka a tsaye sai wata tsohuwar riga Tshirt duk ta jeme, gyatsine tayi ta mulmulo ashar tace "kai me za a baka kake mana ihu??", yaron yace "yaji za'a zuba min a kulele", Sa'adatu taja wani dogon tsaki tamkar tsohuwar tsaka tace "kawo na zuba maka", ya miƙa mata kwanon, ta buɗe tana kallon kulelen da aka shanana masa manja gwanin sha'awa, ta taɓe baki ta tsugunna ta duntsi ƙasa cikin hannu ta barbaɗe kulelen da ita tas, ta rufe ta miƙa masa tace "jeka an zuba yajin", yaro yayi kasaƙe yana kallonta da mamaki, taja tsaki ta fara kwashe kayan shanyarta akan igiya, Hajar ta fito daga bayi taga yaro tsaye da kwano a hannunsa tace "yaji za'a zuba ko??", ya nuna Sa'adatu da hannu yace "waccan ce ta zuba ƙasa a ciki", Hajar ta zaro ido waje tace "ƙasa?" ta karɓi kwanon ta buɗe, ai kam dai kulelen nan bazata ciyu ba saboda tasha ƙasa harda tsakuwa, wani ƙululu ne ya tsaya mata a maƙoshi gashi umma ta mata gargaɗi, dole ta hakura ta zubo masa wata sabuwar kulelen ta juye waccan, ta koma kan kujera ta cigaba da yanke farce, gani tai bazata iya yin shiru ba kawai anyiwa baabarta asara ta ɗari biyu, ta kalli Sa'adatu da take kwashe kaya jikin igiya tana bigesu saita linke ta ɗora a kai tace "Sama fanta ƙasa coca cola, fuska fara ƙafa baƙa", Sa'adatu ta ƙyalƙyale da dariya amma a zuciyarta ji take kamar ana zuba mata dalma, Hajar kam kamar ta sani harma kamar waƙa take haka ta cigaba da cewa "Sama fanta ƙasa coca cola, fuska fara ƙafa baƙa", Sa'adatu da haushi ya gama turnuƙeta gashi Hajar ko kallonta ba tay ballantana tace da ita take ta shiga ɗaki tamkar zata tashi sama. ★Zaune take cikin wani jugunannen palour wanda ya ƙure lambar haɗuwa, hannunta riƙe da wani tsadadden bowl tana shan fruit salad, damɓasheshiyar Tvn palour sai aikinta take, wata ƴar budurwa ce ta sakko daga kan stairs ɗin da ya kewaye makeken palour, ta zauna kan sofa tace "Mami yaya Nurain bai dawo ba har yanzu??", Mami ta shanye fruit ɗin bakinta tace "Eh bai dawo ba", Noor ta taƙune fuska ta kalli agogo sai kuma ta jingina da kujera ta fara latsa tsaleliyar wayarta, Mami ta kalleta tace "is there any problem dear??", Noor ta ajiye wayar tace "No Mami", Mami tace "ohk" ta cigaba da shan fruit salad ɗinta tana kallon Tv, few Minutes after that wani sassanyar ƙamshi ya fara karaɗe palourn da yake ƙamshin breath taking freshner, Noor ta kalli door jin ƙamshin na yayanta ne, ai kam dai shi ɗin ne, yayi sallama ya tako a hankali hannunsa riƙe da briefcase, Mami ta ajiye bowl ɗin hannunta a hannun kujera bayan ta amsa sallamarsa, a kan soft carpet ɗin dake malale a palourn ya zauna yace "Mami barka da gida", Mami tayi murmushi tace "An dawo lafiya Nurain", yace "lafiya alhmdllh" ya koma kan kujera ya zauna. Noor tace "yaya sannu da dawowa", ya kalleta yace "yawwa Lil sis", Mami tace "a kawo maka abinci ko sai anjima", yace "amm yanzu zanci, Noor ta shirya min kafin na dawo", ya ɗauki briefcase ɗinsa yabi stairs, saida yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya ƴan ubansu sannan ya sakko down stairs, already Noor ta gama shirya masa lunch, zama yayi yana ci peacefully, Mami tace "yauma kayi surgery ne Nurain??", ya ajiye spoon ɗin hannusa yace "yeah Mami, amma banje hospital da nufin yin surgery ba, wata patient aka kawo emergency tana buƙatar aiki in not less than 24hours, a rayuwar nan ta yanzu nothing goes without money, gashi asibiti sun buƙaci su kawo kuɗi mai yawa kuma basu da hali ga surgeon ɗin da zaiyi aikin yace sai an biya sa, ni kuma naga aikin is inside my field shine nayi surgeryn free", Mami ta jinjina kai tace "Allah ya saka maka da alkhairy, i know baka zama likita saboda neman kuɗi ba sai don temakon al'umma". yace "Mami akwai rashin temako a ƙasar mu sosai, masu temako basu da yawa". Mami tace "idan ka temaki wani Allah zai temake ka, Nurain Allah kaima ya dafa ma cikin lammuranka", yace "Ameen". glass cup ya ɗauka da lemon kwali, har zai buɗe lemon sai kuma ya fasa ya kalli Noor yace "plxx change it with chivita orange", ta miƙe ta amsa ta shiga kitchen ta buɗe damfareren fridge ta ɗakko masa chivita orange, ta dawo ta ajiye masa a gabansa sai kuma ta tsaya tana kallon rigar jikinsa fara tass, tsuke ido tayi tana nuna rigar tace "yaya wai rigar nan ta rannan da ka shafo taɓo ajiki yauma itace ka saka??", Nurain ya kalli rigar jikinsa yace "hey get out" ya saita mata hanya........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche { 5...} Noor ta koma kan kujera tana murmushi tace "Allah kam sai naga kamar rigar ce", shiru yayi mata ya buɗe lemonsa ya zuba a glass cup ya fara sipping, Noor ta tashi ta haye stairs ta kara wayarta a kunne tana murmushi. Mami ta kallesa tace "Nurain", ya ɗago yace "na'am Mami", Mami ta sauke ajiyar zuciya ta mayar da hankalinta kacokan akansa tace "you have to move on dear, me ake ciki ne maganarka da Ruqayyah??, ka riga da ka gama gini to mai kake jira, gaskiya ya kamata ka motsa kar iyayenta su ɗauka playing daughtern su kake", Nurain ya sauke sassanyar ajiyar zuciya ya dire cup ɗin hannunsa yace "yeah Mami daman ina so na gaya miki ki sanar da Abba, I'm ready a kai kuɗin, kuma..." sai yayi shiru yana shafa lallausar sumarsa, Mami tace "kuma me??", yace "kar a saka lokaci mai tsaho tinda dai mun gama fahimtar juna, kuma maganar lefe shima ba wata matsala Insha Allah", Mami tayi murmushi tace "idan kai a shirye kake toh iyayenta fa, nima kaina ban shirya ba", yace "Amma nasan kafin lokacin kin shirya aii", tace "maganar lefe mai za a ƙara nasan dai akwai wasu kayan wajen zulaiha, abinda ya rage bashi da yawa", yace "yeah munyi maganar da ita tace 2million sun isa a cike ragowar kayan", Mami tace "toh shknn zan sanar da Abbanku idan ya dawo", Nurain yace "ohk, bari na fita masallaci", ya miƙe ya fita daga palourn. Da daddare Mami ta tari Abba da maganar ta sanar dashi komai, Abba yana zaune a palournsa ya kalli Mami yace "ohk, kika ce yace he is ready??", tace "uhmm haka yace", yace "ohk then, bawai na rabu da Nurain yayi komai na aurensa yana nufin bana sonsa bane, abinda yasa ina son ya martaba matarsa ne kuma ya kula da ita, nafi so yayi aure da dukiyarsa yadda zaifi kula da matar da haƙƙoƙinta, though banida doubt akan Nurain amma i have to do this", tace "na fahimceka my prof". Abba ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern Nurain ya kara a kune, Nurain a lokacin yana balcony yana waya da Ruqayyah, ganin kiran da yake shigowa wayarsa yasa yace "ina zuwa bari na ɗauki kiran Abba zan kiraki if I'm done", Ruqayyah tace "ohk" ta katse kiran, yayi picking kiran Abba, ba tare da ɓata wani lokaci ba Abba yace masa ya samesa a palourn sa ya katse kiran, Nurain ya sakko down stairs ya wuce part ɗin Abba, ya murɗa tsadadden handle ɗin ƙofar palourn ya shiga da sallama, Mami ce ta amsa ya ƙaraso ciki ya zauna kan carpet yace "Abba gani", Abba ya nuna masa sofa yace "zauna", ba musu ya koma ya zauna inda Abba ya nuna masa, Abba yace "naji saƙonka wajen Maminku, naji daɗin hakan, kace kar a saka lokaci mai tsaho amma baka tunanin ɓangaren ita yarinyar zasu iya cewa lokacin ya musu ƙaranci, kamar month nawa kake so ayi fixing date??", Nurain yace "Amm kamar three months haka", Abba ya jinjina kai yace "ohk, kaine ai me aure shiyasa nake tambayarka, amma bazan yi assuring dinka three months ba idan sun nemi a ƙara musu lokaci za a mayar five months, idan kuma basu nema ba za a barshi a three months din da kake so, Insha Allah gobe zan samu uncles ɗinka next tommorow sai aje gidan nasu", Nurain yace "okay", Abba yace "ka iya tafiyarka". ★Umma na fita bakin titi ta tari napep ya kaita har ƙofar gidan Anty Jamila dake a unguwar Goron dutse, Umma ta shiga ɗan madaidaicin gidan mai ɗan ƙaramin gate da wajen parking mota ɗaya matsayin tsakar gida, Anty Jamila baki har kunne ta tarbi ƴar uwarta cike da murna, suka zauna a ɗan matsakaicin palourn Anty Jamila da yasha ado ba laifi, Hafsa ce ta shigo wacca itace second born ɗin Anty Jamila da jug mai ɗauke da zoɓo mai sanyi da ruwa ta ajiye a gaban umma, Umma tace "kai alhmdllh jiki yayi sauƙi, Allah ya ƙara afuwa", Hafsa tace "umma ina wuni, ya baki tahomin da Hajar ba?", Umma tace "lafiya lou, Hajar tana nan tafe zata zo aii", Hafsa tace "tom Allah ya kawota" ta fita ta basu waje. Anty Jamila tace "wllh Adda dama baki wahalar da kanki ba ai na gaya miki Hafsa taji sauƙi, amma naji daɗin zuwanki", Umma ta tsiyayi zoɓon a cup ta ajiye gefenta tace "akwai wani dalilin da ya kawoni bayan duba Hafsa aii", Anty Jamila ta gyara zamanta ta ɗauki remote ta kashe ƙarar Tv tace "ai da kin gaya min sai nazo can ɗin ma Adda ba sai kin wahalar da kanki ba", Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "babu komai nan ɗin yafi", Anty Jamila tace "toh Adda Allah yasa dai lafiya", Umma tayi sipping zoɓo tace "Jamila babu abinda baki sani ba akan rayuwar gidan da nake, toh a da dai abin bai fiya damuna ba sai yanzu da Hajara ta fara mallakar hankalinta, yanzu fa gidan kullum cikin tashin hankali ake, ga Hajara ba zata taɓa gani ta kyale ba, in ƙarƙare miki zance har dambe ake yi dani", Anty Jamila ta riƙe baki ta zabga salati tace "Adda dambe..", Umma tace "da zarar sun tsokani Hajara saita rama, to sai su haɗu su lakaɗa mata duka, ni kuma idan naga zasu kassaramin ƴa saina shigar mata a haka abin yake zama dambe, babu irin faɗan da ban yiwa Hajara ba akan ta dena biye musu amma kuma taƙi ji saboda na lura da ita tanada zuciya kuma bata son wargi, toh yanzu gaba ɗaya lungun mu an riga da an canfa mana gida wai mu ƴan bala'i ne kullum cikin dambe muke, kinsan mutane wallahi harda nasu gishiri da magin suke ƙarawa, ni dai yanzu na yanke shawara zan mayar da Hajara wajen Iya ko a samu sauƙi, jira nake suyi sauka a islamiyya saita koma gaban Iya, ko ya kika gani??", Anty Jamila tace "Eh toh me zai hana ki kawomin ita nan saina haɗasu da Hafsa", Umma ta girgiza kai tace "gara dai na kaita wajen Iya kinga ta ringa taimaka mata da wasu abubuwan, amma kuma bansan ta yadda zan shawo kan Mal ba kinsan yadda yake jin Hajara duk cikin ƴaƴansa", Anty Jamila tace "indai kikai masa bayani ai zai gane". Umma bata baro gidan Anty Jamila ba sai bayan sallar la'asar. ★Wata numfasasshiyar Mota ce tayi parking a daidai lungun ƙunshi, saida motar tayi minti ashirin da tsayuwa sannan Sa'adatu ta buɗe ƙofar mai zaman banza ta fito, hannunta riƙe da ledoji ta fara tafiya tana rangwaɗa ta shiga lungunsu, Naseer na zaune akan benci gaban shagon Iliya kuma akan idonsa aka sauketa daga mota tazo ta wuce, iliya da Munkaila suka haɗa ido suka kasa cewa komai saboda kasancewar Naseer a wajen, ita kam Sa'adatu bata ma lura da yayan nata ba saboda duhun dare na damuna, saida Naseer ya bari tayi nisa sannan ya biyo bayanta, tana shiga soro shima ya shiga ya sakawa ƙofa sakata, ya saka ƙafa ya kwarfeta ta zube a ƙasa har saida bayanta ya amsa, beyi wata-wata ba ya zuge belt ɗin wandonsa ya fara zabga mata ta ko'ina, Sa'adatu ihu take tana neman ceto gashi ta kasa tashi ƙugunta ya riƙe, da iya ƙarfinsa yake sauke mata ruwan belt ajiki. Maama da Maimuna da kuma Nabilah da suke tsakar gida suka jiyo ihu a soro, Maama ta miƙe da sauri tana gyara zaninta da yake shirin kwancewa tace "ke Sa'adatu ce fa" tayi hanyar soro cikin sauri Maimuna ta bita a baya, Nabilah kuma ta rarumo wayarta keypad tana ƙoƙarin kunna fitila wayar ta suɓuce daga hannunta ta tawarwatse a ƙasa. soron duhu dunɗum Maama cewa take "Nasiru ka rabu da ita nace maka", Naseer kam dukan Sa'adatu yake da iya ƙarfinsa yana cewa "uban waye wancan da ya ajiyeki a mota??", Sa'adatu da azaba ta hanata magana sai gunji take, Maama ta kwalawa Nabilah kira tace "ki ɗakko min kyandir a ɗaki", kafin Nabila ta kawo kyandir ai Sa'adatu ta faɗawa ƴan garinsu, a matuƙar fusace Naseer ya wuce cikin gida Maimuna da take kan hanya itama saida ta samu rabonta, domin kuwa saida ya cije ya zabga mata belt ɗin hannunsa ta ɗaureta ya zuge mata ita ajiki tayi mata wankan jego, da mugun gudu Maimuna ta kyalla cikin gida tana soshe-soshe, batama san lokacin da ta bangaje Nabilah ba kyandir ɗin hannunta ya liƙe mata a wuya har saida fatar wajen ta kwaile, Nabilah da zafin wuta ya ratsata ta mulmulo ashar ta danƙara mata, a banza dan Maimuna batama san me ta aikata ba ji take tamkar an zuba mata tafasasshen ruwan zafi a fatar baya. Maama ta tallafi Sa'adatu ta shiga da ita cikin gida, gaba ɗaya jikinta yayi ruɗu-ruɗu da shatin belt, ga wani shaɗi da yayi mata a fuska wajen har ya kwaile, Nabilah ce ta tsaya ɗakko ledojin da Sa'adatu tayi wurgi dasu tin lokacin da Naseer ya kwarfeta, shawarma ce da pizza gaba ɗaya sun gama baɗewa da ƙasa babu ta yadda za ai su ciyu, ice cream kam kifewa yayi a ƙasa. Maama ta shiga ɗakinsu Naseer tace "Nasiru banyi maka gargaɗi akan dukar min ƴaƴa ba?", Naseer ya dafe kai yace "Maama dan Allah ki barni da yaran nan, wllh a wata ƙwatuwar mota aka sauketa, ki duba fa irin suturar jikinta sai kace ƴar arna", Maama tace "nima tashi ka dakeni Nasiru tinda har agaban idona kake kiran ƴata arniya", Naseer ya fice ya bar ɗakin yayi soro da sauri. Washe gari tinda Hajar tayi sallar asuba bata koma bacci ba, tana zaune tana tilawar Al'qurani har saida gari ya fara washewa sannan ta rufe karatun ta matsi toothpaste a brush ɗinta ta fita tsakar gida, saida ta kusan wurgi da brush din hannunta ganin Sa'adatu da take fitowa daga ɗakin Maama da ɗingishi, fuskarta ta kumbura idonta na hagu ya lume da taruwar jini a gefensa, gefen kumatunta ya kumbura suntum sai kace ta ajiye kwallon goruba a baki, duk da irin saɓanin da suke samu saida ta tausaya mata, jiya da daddare tana jin lokacin da Naseer ya lakaɗa mata na jaki, Hajar ta taɓe baki ta saka slipers dinta ta wuce gaban tukwanen ruwa, ta ɗebi ruwa a buta ta saka kujera ta zauna ta fara goge bakinta, kamar daga sama taji saukar wani mugun ɗaɗe a gadon bayanta, ta gantsare saboda azaba brush ɗinta ya suɓuce daga hannunta..........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {6...} Da sauri Hajar ta miƙe daga kan kujera ta juya taga wane ne yayi mata wannan azababben ɗaɗen na rashin imani, Maama ta gani tana mata wani kallo mai cike da tsantsar tsana, Hajar ta ja da baya idonta na kawo ruwa tace "me nayi miki??", Maama tace "uwarki kikay min, uban waye yace ki zauna min a kujera?, ko so kike ki shafamin baƙin fentin da ke tare dake", Hajar bata ce komai ba darajar Naseer da Huzaifa yasa take ragawa Maama, Sa'adatu ta ɗingiso tana ƙoƙarin buɗe idonta na hagu da ya kanne tace "chaɓ wannan ɗan dukan, ai da kin sani dundu kikay mata wanda shegiyar za tay aman wahala", Hajar ta tsotse kumfar bakinta ta tofar ta zabgawa Sa'adatu harara tace "ke dalla malama ja can da ruɓaɓɓen bakinki, wllh kika sake magana saina naushi ɗayan idon kinyi duka babu", umma daga cikin ɗaki ta jiyo muryar Hajar ai kam ta fito da sauri, tana ganin Hajar tsaye ta riƙe ƙugu ga Maama da Sa'adatu tasan ba lafiya, daga bakin ƙofa ta tsaya tace "Hajara zo nan yanzun nan", Hajar ta ɗauki buta ta kuskure bakinta ta ɓallawa Sa'adatu harara ta shiga ɗakin umma. Maama ta kalli fuskar Sa'adatu tace "keda nace karki fito, me za kiyi a wajen?", Sa'adatu tace "bayi zan shiga ne", Maama tace "toh ina Maimuna da nace ta taimaka miki kafin anjima a karɓo miki magani a chemist", Sa'adatu tace "uhmm Maimunan ce zata temaka min" ta ɗingisa ta ɗauki butar da Hajar ta ajiye mai ruwa ta shiga bayii. Maama ta bita da kallo sai kuma ta nufi ƙofar ɗakin su Naseer, bubbugawa ta shiga yi da ƙarfi, Mu'azzam ya buɗe, ta ɓalla masa harara tace "ban hanya", ba musu ya matsa mata ta tura kai ɗakin, Naseer da yake kwance a katifarsa ya rufa har ka ta tsaya tana kalla, ta yaye rufar tace "Nasiru tashi", ya buɗe idonsa da kyar ya miƙe zaune yace "Maama lafiya??", tace "ka gaida babanku kuwa?", ya juyar da kai yace "Tin asuba muka gaisa aii", tace "toh maza yanzu ka fito ka sameni a tsakar gida karka ɓata lokaci" ta fita a ɗakin. Umma ta kalli Hajar tace "waike Hajara mai yasa kike da kunnen ƙashi ne iyee, ba nace ki dena shiga sabgar su ba", Hajar tace "Allah umma ban shiga harkar su ba, kawai fa ina zaune ina goge baki shine Maama tayi min ɗaɗe a baya wai na zauna mata a kujera", ta kwashe rigarta tace "kinga wajen", Umma ta zabga wani uban salati ganin yatsu biyar cif raɗa-raɗa a bayan ƴarta, wajen yayi Jajur tamkar ka taɓa jini ya fito abinka da farar fata, Umma tace "wllh Allah ya isa ban yafe ba", Sabra da take shafa Vaseline a ƙafafuwanta ta miƙe da sauri tace "Adda nagani", Sabra ta zaro ido tace "lalala chaɓ", Hajar ta sauke rigarta ta kalli umma tace "Umma ki bani kuɗi na siyo brush nawa ya faɗi a gefen kwata", Umma tace "kije wajen babanku ki karɓa", Hajar tace "tom, daman yanzu zanje na gaishesa" ta fita waje, a ƙofar ɗakin Baba ta tsaya tayi sallama sannan ta yaye labule ta shiga, ta durƙusa tace "Baba barka da safiya, an tashi lafiya??", Baba yace "lafiya ƙalou Hajara Allah yayi albarka", tace "Ameen Baba", yace "yaushe zaku fara jarabawar??", tace "banda wannan satin wani mai zuwa zamu fara", yace "toh Allah yasa a fara a sa'a, saiki dage da karatu", tace "Tom Baba" sai kuma ta fara murza hannunta tace "Baba dan Allah ka tahomin da brush idan ka fita aiki nawa ya lalace", ya karkace ya ciro ɗari biyar daga aljihunsa yace "gashi ki sayi brush ɗin, ragowar canjin kuma kiyi kuɗin makaranta dasu na gobe", tasa hannu biyu ta karɓa tace "nagode" ta miƙe zata fita daga ɗakin, Naseer ne ya yaye labule ya shigo fuskarsa duk kumburin bacci, Maama ce ta kunno kai ta wani rirriƙo Sa'adatu, Hajar dai ta koma gefe tana kallon ikon Allah sai kuma tace "yaya ina kwana??", Naseer yana murje fuskarsa yace "lafiya" ya samu guri ya zauna, Maama ce ta tattagosa wai tana buƙatar ganinsa a ɗakin Baba, ita dai Hajar ta kama gabanta ta samfe a ɗakin, Maama ta zaunar da Sa'adatu itama ta zauna tana kallon Baba tace "barka da safiya mal, yaudai ga ɗanka nan na kawo maka shi kayi masa katangar ƙarfe da dukar min ƴaƴa, ni nayi masa magana yaƙi ji, kalli kaga yadda ya sauyawa Sa'adatu kamanni, Maimuna ma tana ɗaki ya kwaile mata baya, toh gashi nan dai kayi masa magana wataƙila kai yaji maganarka, nidai nan gaba idan ya sake dukar min ƴaƴa kamar haka to wllh saina kwashe masa albarka kaf ehee", Baba ya kalli Sa'adatu ya juya ya kalli Naseer yace "kai ka daketa ??", Maama ta ɗaga murya tace "yo ƙarya zan masa kake tambayarsa, kayi masa gargaɗi kawai mal", Baba yace "dakata Rabi ki bari na gama magana, Naseer ina jinka me ya faru", Naseer ya gyara zama yace "Baba yarinyar nan kullum akan hanyar fita take daga gidan nan da shigar da bata dace ba, da dare sai kaga an ajiyeta a wata ƙatuwar mota, kuma motar da take kawota daban-daban ce, nayi mata kashedi amma taƙi ji shine jiya na zaneta", Sa'adatu ta fashe da kuka tace "Baba wllh ƙarya yake min, ai Maama tasan inda nake zuwa wajen ƙawata kuma ni ba a taɓa sauke ni a mota ba a napep nake dawowa", Naseer yace "ni nake miki ƙarya?", Maama tace "yo yarinya da bakinta kana ƙoƙarin yi mata sharri ai dole ta ƙaryata ka, mal nidae daga yau sai yau kar Nasiru ya sake taɓa min ƴaƴa, tashi muje", Maama ta miƙar da Sa'adatu suka fice daga ɗakin, Naseer yace "Baba, Maama tana sakaci da tarbiyyar yaran nan, wllh yarinyar nan a mota ake ajiyeta kuma namiji ne ba mace ba, ai ko macen ce a zargeta duniya ta lalace", Baba yace "na yarda da kai Naseer, abinda nake so da kai duk wani hukunci da za kai ka fara sanar dani kafin ka wanzar dashi, tashi kayi tafiyarka Allah ya shiryesu". ★Nurain ya sakko down stairs yana gyara zaman rantsatten agogon hannunsa, bai samu kowa a main palour ba don haka ya wuce part din Mami, da sallama ya murɗa handle ɗin palourn Mami ya tarar bata nan sai ya nufi ƙofar bedroom ɗinta, a hankali yayi knocking, daga ciki Mami tace "come in", ya buɗe door ya shiga, Mami na zaune bisa prayer mat ta idar da sallar walha, ta kallesa tace "A'a fita za kai, yau ai ba aiki ko??", yace "yeah, wajen Anty Zulaiha zani, tace tana son gani na, and i have another appointment", tace "ohk, anjima Abba da su Salisu zasu je gidansu Ruqayyah aii", ya jinjina kai yace "ammm Mami kin yiwa Anty Zulaiha maganar ne??", tace "eh na sanar da ita jiya da daddare", yace "ohk i think that was the reason take nema na, Noor fa?", tace "ta fita Grocery shopping wai girki zata ma friends ɗinta zasu zo", yace "ohk, na wuce", Mami tace "wait" ta miƙe ta buɗe huge press ɗinta ta ɗakko wata paper bag ta miƙa masa tace "ka kaiwa zuhaiha", ya karɓa ya fice daga part ɗin, katafaren compound din gidan ya fito mai ɗauke da shuke-shuke masu kyau da parking lots na motoci ƴan ubansu, Garba ne ya taho da sauri ya russuna yace "barka da fitowa alhj ƙarami", Nurain yace "yawwa, an gama wanke motar", Garba na washe haƙora yace "Eh an gama alhj" ya ciro key daga aljihun rigarsa ya miƙa masa, Nurain ya karɓi key ɗin ya zura hannu a trouser pocket dinsa ya ciro wallet ya buɗe ya fello dubu goma ya miƙa masa, hannu bibbiyu Garba ya amsa yana washe haƙora yace "Alhj harda hidima haka, to nagode Allah ya saka da alkhairy yasa afi haka", Nurain ya nufi wajen wata dunƙulalliyar mota a parking lot ya buɗe ya shiga, yayi warming sannan ya mirgina ya fita daga gidan bayan mai gadi ya buɗe masa damfareren gate. Slowly yake driving yana waya da Ruqayyah, wani murmushi ya sake speaking calmly yace "why are you doing this babe?, mesa bazan zo yau ba?", from the other side Ruqayyah tace "haba dearest nidae kunya nakeji, ka bari sai gobe kazo", yace "naji cewa sai gobe amma mesa zakiji kunya bayan da kanki kika kaini gidanku kikace kina sona kuma zaki aureni...", ƙit yaji ta katse kiran yayi murmushi ya sake dialing amma taƙi picking, a hankali yace "shy girl". A daidai gate din wani gida Bungalow ya danna horn, Gate man ya buɗe masa ya shiga da Motar yayi parking ya buɗe ya ɗauki paper bag din da ya ajiye a kujerar mai zaman banza ya fito, direct Main building din gidan ya dosa, ya tsaya a ƙofar shiga ya ciro wayarsa daga pocket ya kira Antyn nasa, tana yin picking yace "I'm here Aunt", Anty Zulaiha tace "toh me kake jira come in mana", Nurain ya shiga palourn da ya ƙawatu ba ƙarya bayan yayi sallama ya zauna akan kujera ya ajiye bag din hannunsa a gefe, wata ƴar budurwa ce da bazata wuce 20yrs ba ta fito daga kitchen hannunta riƙe da serving spoon, zaro ido tayi ta ƙaraso cikin palourn tace "yaya Nurain sannu da zuwa", yace "yawwa Khausar, ina Anty?", tace "bari nayi mata magana" tabi wani corridor, tare suka fito da Anty Zulaiha, Khausar ta koma kitchen Anty Zulaiha ta zauna kan kujerar dake kusa da nashi tace "na taso Dr da sassafe", ya shafa sumar kansa yace "ai mun saba da fitar safe, ya gida Anty?", tace "lafiya, ya Noor ta dai ƙi zaman gidan nan", yace "ai Noor Mami's tail ce" ya ɗauki paper bag din ya miƙa mata yace "inji Mami", tace "toh me na samu haka wajen yayata haka" ta buɗe taga perfumes ne kala uku, Khausar ta fito daga kitchen da trayn mai ɗauke da drink da kuma snacks ta ajiye masa, ta buɗe lemon ta tsiyaya masa a glass cup sannan ta koma kitchen, ya ɗauki lemon yayi one sip ya ajiye, Anty Zulaiha tace "jiya Mami take gayamin abin arziƙi, ashe yau za a kai kuɗi da sa rana, toh Allah ya tabbatar da Alkhairy, Ruqayyahn ce dai koh??", yace "yeah", tace "tom, maganar lefe na gaya maka balance dai koh??", yace "yea, yanzu zan miki transfer ba 2m ba??", tace "Eh haka yake, Insha Allah zasu isa a gama harhaɗo abubuwan da suka rage..", yace "idan ma basu isa ba just Ping me". Khausar da take rakuɓe a ƙofar kitchen kaf hirarsu a kunnenta ta lumshe ido a hankali tace "what kuɗin Auren yaya Nurain za a kai".............✍️ 💛 HAJAR💛 by Feenerh_feeche {7...} A wannan rana aka kai kuɗin auren Nurain da Ruqayyah, tsakanin ɓangaren ango da na amarya aka taƙaice sa rana wata huɗu cif, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Nurain ba cause he is eager to have her as his wife, on Monday Ruqayyah na zaune a Nurse station, Nurse Jidda tace "an yiwa shuka bar ruwa tasha taki ranar girbi ya kusan ƙaratowa nanda 4months", Ruqayyah tayi murmushi a taƙaice tace "ni kam abin yayi min wuri, i thought Daddy zai saka 1year haka amma wai da suka ce wata uku shine ya ƙara wata ɗaya", Jidda tace "A'a shi Daddy da zai aurar dake ɗin ai ya shirya, toh ke mene dalilin ki da zaki ce yayi wuri??", keenly Ruqayyah tace "my own schedule, anyway nothing is going to change, i can deal with it", Jidda tace "hey i don't get you me kike cewa ne??", Ruqayyah tayi murmushi tace "zaki gane ne", Jidda ta ringa kallonta sai tace "think wise kafin kice za kiyi wani abun", Ruqayyah har ta buɗe baki sai kuma tayi shiru sakamakon wayarta da ta fara ringing, the ringing tone yasa tayi murmushi ta ciro wayar daga handbag ɗinta, ta haskawa Jiddah screen ɗin wayar tace "kin gani my Dr ne yake kira, he loves me so much duk abinda zanyi zai min uziri", har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa sannan Ruqayyah tayi picking ta kara a kunne tace "slm dearest, ka ƙaraso ne??", daga ɗayan ɓangaren Nurain yace "yeah", tace "ohk yanzu zan kawo maka coffeen nasan sai kasha zaka shiga surgery", wayar kare a kunnenta ta miƙe ta dubi Jidda tace "plxx ki kulamin da ward A kafin na dawo", Jidda ta galla mata harara tace "A nawa??", Ruqayyah tace "zan taya ki Night" ta wuce gaba. Nurain yana zaune a office ɗinsa yana duba tsirarun patients ɗin da zasu gansa a yau, Dr Marwan da Khaleel ne suka shigo a tare, Nurain ya ɗago ya kallesu ganin yanayin fuskokinsu yace "what??", Khaleel yace "Allah ya sanya Alkhairy Boss", Dr Marwan saida ya zauna kan kujera yace "fatan alkhairy", Nurain ya taɓe baki ya jingina da chair yana wasa da yatsunsa ya kallesu duka yace "tnx, ƙarfe 11am zamu shiga surgery, get ready", Khaleel yace "yes bari nayi gathering team ɗin", Nurain yace "good", Khaleel ya fita daga Office ɗin, Dr Marwan yace "who will anesthesetice the patient, our anesthesetic is absent", Nurain yace "that is not a problem i have one", Dr Marwan yace "ohk then", Ruqayyah ce ta shigo hannunta riƙe da Mug, Dr Marwan ya miƙe daga kujera yace "tom Dr sai mun haɗu a surgery room", saida yazo fita ya kalli Ruqayyah da take gefe yace "toh Allah ya sanya alkhairy A Nurse, naga tin yanzu ma ana kula mana da Dr ballanta an samu full license", Ruqayyah tayi murmushi tace "ya Amarya??", Dr Marwan yace "tana nan lafiya" ya buɗe door ya fita, ta taka a hankali ta zauna kan chair tana facing Nurain, gani tay ya wani haɗe rai yana latsa wayarsa, Mug ɗin da ta shigo dashi ta tura masa tace "dearest ga coffeen fa", ba tare da ya kalleta ba yace "take it with you", ajiyar zuciya ta sauke tace "sorry ai a faɗan laifina dai ko?", wayar ya ajiye ya zuba mata idanunsa da suke tamkar madara yace "daman kin iya murmushi haka??", dariya ce ta kusan kufce mata tace "jealousy sorry bazan sake ba", keenly yace "good". tace "happy tinda an saka lokaci kaɗan yadda kake so", yace "kefa ba kya farin ciki ne??", shiru tayi ta fara wasa da hannunta, yayi ajiyar zuciya yace "help me", ta ɗago da kanta tace "how?", yayi mata wani narkakken murmushi yace "zanyi surgery anjima zaki min anesthesia", ta juya idonta tace "sure my Dr". ★Maama daga bakin murhu tana kwashe abinci, kwanon Baba ta fara zubawa sai na sauran ƴaƴanta, bayan ta gama ta miƙe tana sharce gumin da ya tsattsafo mata a goshi saboda zafin wuta ta shiga ɗakinta, Sa'adatu tana kwance akan wani ruɓaɓɓen gado daga gani ba a rasa kuɗin cizo a cikinsa ba, Maimuna kuma tana shafa man bleeching ɗinta a fuska da ɗaurin ƙirji ajikinta sakamakon wankan da bata daɗe da fitowa ba, Maama ta kalli Maimuna tace "tin safe nake ce dake kiyi wanke-wanke amma kin ƙi, yanzu ga abinci can na gama amma babu kwanon da zan zuba muku", Sa'adatu tace "Maama mai aka dafa??", Maama tace "wake da shinkafa ne", Sa'adatu tace "dame kuma??", Maama tace "da manja da yaji", Sa'adatu tace "haka tsura ko ɗan salak babu" ta miƙe a hankali ta ɗingisa saboda har yanzu ƙugunta bai gama saki ba, ta ɗakko jakarta ta buɗe ta fello duba ɗaya, Maama ta zaro ido tace "Sa'adatu ina kika samu kuɗi haka", Sa'adatu ta yamutsa fuska ta miƙawa Maimuna kuɗin tace "ki siyo min kifi na ɗari biyar, balangu na ɗari uku saiki siyomin maltina ta gwangwani guda ɗaya", Maimuna tace "chaɓ gaskiya bazanje ba", Sa'adatu tace "ke dalla malama zan sammiki fa", Maimuna tayi gyatsine ta warce kuɗin, Maama tace "Sa'adatu magana fa nake miki", Sa'adatu tace "toh ai kece Maama wllh kin fiya maida hannun agogo baya, na gaya miki ƙawata ce fa take bani", Maama tace "Allah sarki, toh Allah ya biya ta". Maimuna ta zari hijab ta fita. Sa'adatu ta doka wani uban tsaki tace "Maama saida nace fa ki tuna min yau za a siyo piya-piya a yiwa ɗakin nan feshi ko ma samu sauƙin cizon kuɗin cizon nan, wallahi jiya kasa bacci nayi, ina kallon Maimuna da Nabilah ma sunata bige-bige cikin bacci", Maama tace "wai aikam na manta", Sa'adatu tace "shikenan nasan Maimuna ba sake fita za tay ba". Hajar ta fito daga ɗakin Umma da kwandon soso da sabulu a hannunta, bokiti ta ɗauka ta ɗebi ruwa ta shiga wanka, saida ta gama wanka ta fito ta shirya tsaf cikin uniform ɗin islamiyya, Sabra kam tayi gaba tinda ita da wuri ta dawo daga boko, Umma na linke kayan wanki tace "to Allah ya bada sa'a", Hajar ta ɗauki jakarta tace "Ameen". ★Kwanci tashi Hajar ta kammala rubuta jarabawar NECO, yanzu result kawai take jira saita fahimci wace alƙibla zata fuskanta, lokacin jarabawar kam tayi karatu ba ƙarya ga kuma wanda take yi tin fil azal, bayan sati biyu da kammala NECO a islamiyya ma aka fara yi musu screening ɗin sauka, daman sun shafe wata takwas da hattamawa suka tsaya ƙarasa littafai, yanzu kam satinsu uku da fara yin screening, A yammacin wannan rana Hajar ce zaune a kan kujera a bakin rariya tana wanke gwangwanayen kulele, Sabra na yi mata ɗauraya, takun takalma ƙwas ƙwas daga soro yana doso cikin gida yasa Hajar kallon ƙofa, Sa'adatu ce ta shigo cikin wata shiga half naked, ga wani uban kitson attachment da ta yarfa har mazaunai, fuskar nan ɗaɗau harda hujen hanci tayi tana taunar chewing gum ƙass ƙass tamkar cikakkiyar ƴar bariki, yanzu karenta take ci babu babbaka iskanci ya linka na da Maama na goya mata baya, dodon nata Naseer yanzu baya zama a gida tinda ya samu aikin direban tirelar Ɗangote dake jigila tsakanin kano da Lagos shikenan yayi wuyar gani, Hajar ta taɓe baki ta cigaba da sha'anin gabanta, sai kuma ta sake ɗagowa ganin wasu mata wanda suka amsa sunan cikakkun ƴan duniya su biyu a tare da Sa'adatun. Maama na rawar jiki ta shimfiɗa musu tabarma a tsakar gida, Sa'adatu ta nuna ɗaya daga ciki matan tace "Maama wannan itace zeenatu amma anfi kiranta da zeen" ta nuna ɗayar tace "wannan kuma mabaruka amma anfi kiranta da mabruk", Maama ta washe baki tace "Allah sarki, sannunku da ƙoƙari ƴaƴan nan, ai Sa'adatu tayi dacen samunku matsayin abokai", zeenatu tana taunar chewing gum tace "muma haka" cike da rashin ɗa'a da tarbiyya, Sa'adatu ta wage murya tace "ke Maimuna kina ji nazo bazaki fito ba", Maama tace "laaa ai bata nan", Sa'adatu tace "Nabilah fa?", Maama tace "tana ɗaki, ke Nabila ki fito ga ƴar uwarki nan tazo kina ji", Nabilah ta yaye labule ta ƙarewa su zeenatu da Mabaruka kallo tace "Sannunku" sai kuma ta kalli Sa'adatu tace "ɗan shigo daga ciki mana mu gaisa", Nabilah ta koma ɗaki Sa'adatu tabi bayanta, sama da ƙasa Nabilah ta ƙare mata kallo tace "kinga Sa'adatu ki dawo gida ki zauna, waɗannan kuma su waye haka kika kawosu marasa kyan ganii", Sa'adatu tace "nasan zaki zarge ni ai amma wllh kinji dai na rantse ko??, wllh bana kula maza bare takai da abinda kike tunani, rayuwa nake agidansu zeenatu da Mabaruka irin ta wayayyun mata masu ji da kansu", Nabilah tace "wayayyun mata??", Sa'adatu tace "Eh mana ko baki gani ba", Nabilah ta zabga uban tsaki tace "ni ban gani ba, kwata-kwata ma baku ɗauki hanyar zama wayayyun mata ba wllh, ai....", muryar Baba ce ta katse maganarta, a tare suka antayo waje, Baba ya kalli Maama yace "waɗannan su waye??", Maama tace "ƙawayen Sa'adatu ne fa", Baba ya nuna hanyar soro yace "ku tashi ku fitar min daga gida", Mabaruka ta kalli Sa'adatu tace "au daman Babanki bashi da mutunci Sa'adat", zeenatu ta figi jakarta tace "waini ake kora cikin wannan kuturun ruɓaɓɓen gidan sai kace kango, gidanda ko kiwon tumaki bazan yi ba, haba dattijo kai baka ji kunyar kiran wannan kangon da gida ba saboda tsiyar zuci". wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya takore maƙoshin Hajar da take zaune bakin rariya, da sauri ta ɗauraye kumfar hannunta ta gyara wuyan rigarta ta miƙe tsaye a fusace, Zeenatu da ta yo hanyar fita cikin sauri ta tsaya tana kallo, saida ta bari tazo gaf da ita zata wuce ta saka mata ƙafa, wani irin hantsilawa Zeenatu tayi ta kifa da ka, fuskarta ta faɗa cikin kwata, jikinta kuma ya afka kan gwangwanaye, warwas tayi a ƙasa cikin cakwalkwalin ruwan wanke-wanke mai datti da maiƙon manja, gaba ɗaya guiwoyinta da hannunta sun kwaile, da kyar zeenatu ta dafe hannunta ta miƙe bakinta da goshinta sun fashe, fuskarta dama-dama da kwata, Hajar ta gyara wuyan rigarta da wani irin rainin hankali tace "Baiwar Allah ki iya bakinki, kuma kisan a inda za kiyi zagi kici bulus, ke kin isa ki kalli mahaifina ki gaya masa magana akan idona, shiyasa na gurje bakin fitsarar da ruwan kwata, wllh kaɗan ma kika gani", waɗannan kalaman su suka dawo da Maama Sa'adatu Nabilah da Mabaruka daga duniyar daskarewa, zeenatu ta sharce kwatar da ta mamaye mata baki dake fitar da jini tana kallon Hajar cike da mamaki, Sa'adatu ta mulmulo wata ashariya tayo kan Hajar a fusace..........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {8...} Da sauri Hajar ta tuntsurar da ruwan ɗaurayar wanke-wanken, ta ɗauki bokitin ƙarfen ta nuna Sa'adatu da ta yo kanta tace "na rantse da girman Allah kika taɓani saina rotsa miki kai", Sabra tana ganin haka ta fita a guje kiran Umma da ta shiga makwabta barka, turus Sa'adatu tayi saboda tasan tsaf zata aikata, maimakon kan Hajar da tayi nufin yi saita juya akalarta zuwa ga zeenatu da take ta faman sharce kwatar fuskarta, Mabaruka ma ta taho da sauri ta kalli fuskar zeenatu tace "chab an tsokano sama da kara", Nabilah ta shiga tafa hannaye tana faɗin "mun shiga uku yau ga ƴar daba a gida tana dabanci", Maama tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mal kana ganin abinda shegiyar ƴar da kake iƙirarin takace ta aikata ko??, tafa fitarwa da ƴar mutane jini", Baba ya nuna Maama da hannunsa mai carbi yace "karki sake kiramin ƴa shegiya na gaya miki, Hajara ƴata ce", Maama ta tsaya tana kallon Baba galala tamkar wawuya sai kuma ta hura tukubar hancinta tace "wllh idan zaka shekara dubu kana kiran Hajara ƴarka saina ƙaryata", Hajar ta riƙe bokitin ƙarfen ta gam tana kallon kowa sama da ƙasa, Sa'adatu da Mabaruka suka temaki zeenatu ta wanke fuskarta da hannayenta, Mabaruka ta cire yalolon mayafin jikinta taci ɗammara ta kalli Nabilah tace "naji kin kirata da ƴar daba ko??, to ga wacca ta dameta ta shanyeta tas a iya dabanci", Baba ya ɗaga murya yace "Sa'adatu!!, ki kwashi ƙawayenki ki barmin gida", Mabaruka ta kaiwa Hajar wata damƙa, babu tausayi Hajar ta kwaɗa mata bokitin ƙarfe a hannu, azaba tasa Mabaruka durƙushewa tana yarfa hannu, da gudu Sa'adatu taje ta rarumo taɓarya zata jirga mata, Hajar ta kufce, da sauri Baba ya shiga tsakani hakan kuma yazo daidai da shigowar Umma gidan cikin sauri Sabra biye da ita, salati ta fara zabgawa ganin Hajar na huci hannunta riƙe da bokitin ƙarfe ga Sa'adatu itama da taɓarya, Maama tace "kin haifi bala'i da masifa wllh faɗima, ga shi nan shegiyar ƴarki ta kassara ƴaƴan mutane a gidan nan", Sa'adatu tsalle take tana hargowa tana ƙoƙarin bangaje Baba da ya shiga tsakaninta da Hajar faɗi take "kin san kwa su waye waɗannan, wllh yau sai kinyi nadamar zuwa gidan duniya", Hajar ta daka shewa tace "ahayye wllh sune za suyi nadamar zuwa gidan nan, dubeki dabba jahila daƙiƙiya kin tsaya kina hura hanci da ƙoƙarin bawa hammata iska akan jakunan da suka zagi mahaifinki, asararriya mara mafaɗi da tarbiyya....", Umma ta fizgi Hajar tana ƙoƙarin dannata a ɗaki, Sa'adatu ta yunƙuro tana ɓaɓɓarkawa Hajar zagi irin na cikakkun marasa tarbiyya, Hajar da Umma ta kusan cusata a ɗaki tace "tirr da halinki Sa'adatu, ki ɗauki tsummokaran jakunan ƙawayenki daga nan ku wuce chemist, gaba ɗayansu idan suka ji zugin shanshanbale na ratsasu suka ɗanɗana azaba zasu gane inda ya kamata su nuna rashin tarbiyyarsu", Sa'adatu tace "zaki gani ne ba dai zeen da Mabruk kika taɓa ba", Hajar tace "babu abinda zan gani sai alkhairy, sara da sassaƙa basa hana gamji tofo, jaka kawai". Umma tayi nasarar danna Hajar a ɗaki ta rufe ƙofa, wani irin huci Hajar takeyi tana sauke numfashi, Umma ta kalleta cike da takaici tace "ba kya jin magana Hajara, Insha Allah gobe goben nan zaki bar gidan nan", Hajar ta koma gefen gado ta zauna tana huci zuciyarta wasai. Washe gari Umma ta haɗawa Baba karin kumallo, ɗumamen tuwa da kunun tsamiya, zama tayi har saida ya gama cin abincin sannan tace "yawwa mal daman ina so Hajara ta koma wajen iya da zama tinda zamanta anan gidan ya ƙi daɗi, idan babu damuwa ta koma gaban iya", Baba ya zuba ruwa a kofin da ya gama shan kunu ya girgije yace "faɗima ina ne gidansu Hajara?", Umma tace "nan ne", yace "yawwa, to Hajara babu inda zata agidansu zata zauna", Umma tace "amma mal...", ya ɗaga mata hannu yace "ya isa haka, kirawo min Hajarar", tace "tom" ta fita a ɗakin ta shiga nata, Hajar da take gyara gado ta kalla tace "kije inji Babanku", Hajar ta ajiye bedsheet din hannunta ta fita, ɗakin Baba ta shiga da sallama ta tsugunna tace "Baba gani", ya kalleta yace "Hajara banji daɗi da kika biyewa fitsararrun nan ba jiya, kin saɓa alƙawarin da kikai min kwanaki cewa bazaki sake shiga sabgarsu ba, yanzu jiya me kika yi..", ta buɗe baki za tay magana ya ɗaga mata hannu yace "duk nasan abinda ya faru kuma nasan me yasa kika shiga sabgar su, da kinyi haƙuri saiki samu riba, karki sake aikata hakan kinji", tace "tom Baba", yace "tashi ki tafi Allah shiryeki". ta miƙe a sanyaye ta fita, gyaran gadon da take ta ƙarasa snn ta share ɗakin. ta fito tsakar gida tana kallon Umma da ke bakin rariya, kallo ɗaya umma tayi mata ta ɗauke kai ta cigaba da wanke waken kulele da za a kai markaɗe, Umma ta ɗauki zafi fishi take da Hajar ainun yau ko gaisuwarta bata amsa ba da asuba, Hajar ta tsugunna a gabanta tace "Umma dan Allah kiyi haƙuri, nadena bazan sake ba", ba tare da ta dubeta ba tace "ai daman kin iya tuban muzuru, ki matsa min a nan wajen", idon Hajar ya ciko tace "dan Allah Ummana ki yafemin nadena bazan sake ba", Umma ta ja tsaki tace "sau nawa akai hakan Hajara, tinda dai kinƙi jin maganata ai sai kiyi abinda kika ga dama, duk abinda haƙuri bai samar ba rashinsa bazai yi ba", Hajar tace "wllh Umma nifa bana shiga harkarsu tinda kikai min magana, sau nawa suna takalata bana kulasu, jiya ma fa ƙawayen Sa'adatu ne suka yiwa Baba rashin ɗa'a", Umma tace "uhmm ai kina ganinsu kinsan basu da tarbiyya dan me yasa zaki tanka masu", Hajar tace "bazan sake ba", Umma tace "da ya fi dai". Maimuna ce ta fito daga ɗakin Maama tana rangwaɗa, ta saka wasu matsattsun kaya riga da skirt na atamfa, saboda ɗamewar da skirt ɗin yayi mata har shatin panties ɗinta ana gani, itama ta tsiri fita yanzu kuma bata dawowa gida sai dare da ƴan ledojinta na kwaɗayi mabuɗin wahala, ko kallon inda take Umma da Hajar ba suyi ba tazo ta gama barbaɗesu da Harara kana ta fita. Hajar tace "umma dan Allah da yamma zanje gidansu zainab muyi karatu", Umma tace "toh shknn Allah ya kaimu". Bayan Sallahr la'asar Hajar tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa, ta kashe maiƙon fuskarta da farar huda ta murza lipstick a lips ɗinta, ta saka hijab da ya zarce mata guiwa, tayi kyau sosai sai kace wacca ta caɓa kwalliya, wani flat shoe ta ɗakko ta saka ta yiwa Umma sallama ta ƙara gaba, da yake gidansu Zainab ɗin akwai ƴar tazara daga gidansu, ta tsaya a bakin gate tana knocking a hankali, Zainab ce ta buɗe ƙofar ta haɗe rai tace "haba Hajar tin ɗazu fa nake jiranki amma sai yanzu zaki zo", Hajar tace "ke dalla malama Umma na taya aikin kulele", Zainab ta matsa gefe tace "Shigo mana", a ɗan matsakaicin compound ɗin gidan suka tsaya, Hajar ta kalleta da kyau tace "ke kuma ina zuwa??, naga kinyi shiga sai kace mai shirin fita", Zainab ta gyara yafen mayafinta tace "fita zanyi mana, tinda Allah ya kawoki saiki rakani Ummi ce ta aiken", Hajar tace "ban tambayi Umma ba iya nan kawai nace mata zanzo", Zainab tace "muje ki gaisa da Ummi saina kira Umma a waya mu tambayeta ko?", Hajar tace "Eh hakan dai yafi". cikin gidan suka shiga, Mamansu Zainab tana zaune a palour, Hajar ta tsugunna tace "Ummi ina wuni", Ummi tace "ina gajiya, ya Maman taku", Hajar tace "lafiya alhmdllh", Ummi tace "masha Allah", Zainab tace "Ummi ɗan aramin wayarki plxx", Ummi ta lalubi gefe da gefenta taji wayam tace "duba ɗakina", Zainab ta shiga ɗakin Ummi ta fito da wayar a hannunta ta kalli Hajar tace "taso muje", ɗakinsu Zainab suka shiga, Zainab ta miƙawa Hajar wayar tace "saka numbern Umma", bayan Hajar ta ɗura numbern tayi dialing, anayin picking Hajar taji muryar Sabra, Hajar tace "game kike mata ko?, maza ki kay mata wayarta", tana jiyo muryar Sabra tana cewa Adda ta bugo waya, Umma tayi sallama ta kara wayar a kunne, Hajar tace "Umma nice". da kyar Umma ta amince kuma tace mata kar ta kai magariba. bakin titi suka fito suka tari napep, unguwar da suka je ta masu hali ce haka ma gidan da suka amso saƙo wajen ƙawar Ummi, a clean and silent street ɗin suka tsaya suna jiran abin hawa. ★Noor na zaune a main palour tare da Khausar da yau kwananta biyu a gidan, wata spicy noodle mai shegen daɗi suke ci, gaba ɗaya hankalin Noor yana ga TV da ake haska wani Kdrama, Khausar ta ajiye fork ɗin hannunta tace "Noor what is the name of the drama??", ba tare da ta kalleta ba tace "Alchemy of souls", Khausar ta taɓe baki tace "ni kam nafi kallon Cdrama, ina yaya Nurain ne?", Noor bata amsata ba her mind was fully on screen, Khausar ta ɗala mata duka a cinya tace "hey I'm talking to you", Noor ta zabura tace "ouchh kadan ba saina rama ba" ta mayar da idonta Tv, Khausar tace "wai bazaki ci ba saita sandare", Noor idonta ƙur kan Tv tace "kashe AC", Khausar ta janyo wayarta tace "I'm not your servant". atmosphere ɗin living room ɗin ce ta fara canzawa zuwa wani breath taking scent mai daɗi, Khausar ta ɗago kanta suka haɗa ido da Nurain, murmushi yayi mata ya kalli Noor da bata ma san da shigowarsa ba yace "Noor.. Noor.. Noor.." ya kirata sau uku, saida Khausar ta zungureta sannan ta juya tace "what, wai mene??", da ido Khausar tayi mata nuni da Nurain tace "yaya na magana", yace "juicy fruit salad zaki hada min", Noor tace "ohk, amma babu fruit fa, apple and berries ne kawai ya rage", juyawa yayi ya fita daga palourn Khausar ta bisa da kallo, compound ya fita yana neman Garba ya bashi ya siyo masa fruits ɗin amma ya tarar baya nan, lallausar sumarsa ya shafa yace "shittt", ya shafa pocket ɗin wandonsa yaji key ɗin motarsa yace "good", motarsa ya dosa dake parking lot ya buɗe bayan ya gama warming ya mirgina ya bar compound ɗin, a hankali yake murza steering ɗin motar amma kuma ya take accelerator. Almost 20mis Hajar da Zainab na jiran napep, wasu yara su uku suna wasa da ball daga cikin wani ɗan fili, guda ɗaya ne ya buga ball ɗin da ƙarfi tayo kan road, da gudu yaron ya biyota a lokacin kuma wata dunƙulalliyar mota ta yanko cikin street ɗin with minimum speed, saura ƙiris motar ta bige yaron taci wani uban burki ƙiiii ta tsaya gaf da yaron da tsoro yasa ya ƙame, Hajar ta runtse idonta tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", Zainab kam juya baya tayi ta toshe kunnuwanta da hannayenta, a hankali Hajar ta buɗe idonta ta dubi yaron da ya zama froze a gaban motar, da sauri ta isa gabansa ta fara shafa kansa a hankali tace "wake up kiddo babu abinda ya sameka", ajiyar zuciya yaron ya sauke. Tinda ya tabbatar bai bige yaron ba ya kifa kansa ga steering, calming kansa yake yana addu'a a zuci, ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago kansa a hankali, ta front glass yake kallon yaron da kuma ƴar budurwar da take tare dashi wacca tayi backing dinsa bega face ɗinta ba. tamkar wacca aka umarta haka ta juya ta kalli glass ɗin motar da wani irin yanayi, in one sight ƙwaƙwalwarsa tayi booting on ya gane wannan fuskar, one thing came to his mind which is ƴar gidan gini.........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {9...} Da yake glass din motar tint ne yasa Hajar bata ga drivern ciki ba. hannun yaron ta riƙe still dai tana kallon glass din motar, kawai jira take drivern ciki ya fito, few seconds passed amma babu alamar wanda yaso aikata ta'asar zai fito, Zainab da ta toshe kunnuwanta har tayi jarumtar juyowa ta hango Hajar tsakiyar titi tare da yaron, Hajar taja hannun yaron ta tsaya bakin ƙofar driver ta shiga knocking glass, a hankali glass din yayi ƙasa ya zuge gaba ɗaya, wani sanyi da ƙamshi suka fara sirnanowa suna dukan fuskar Hajar da ta yaron. ta haɗe gira tana kallonsa tace "malam wai baka san darajar rai bane iyeee?, ya za ai ka kusan bige yaro amma ka wani hakimce a mota bazaka fito ka dubasa ba", Zainab ce ta tsallako kan titin itama tace "zo mu tafi ai Allah ya kiyaye tinda dai bai bigesa ba", Hajar tace "ke kinga mutumin nan fa ko a jikinsa, idan da ace ya bige yaron nan fa sai fa yadda Allah yayi", shi kam Nurain mamaki da firgicin da ya ziyarcesa ne ya hanasa magana, Hajar ta sake kallon cikin motar tace "Allah ya isan sa kuma a ringa sanin darajar ɗan Adam", Zainab ta zaro ido tace "Hajar mene haka?", Hajar taja hannun yaron ta tsallar dashi titi tace "maza gida kaji", yaron ya kyalla da gudu ƴan uwansa suka take masa baya. wajen da suke jiran napep ta koma ta tsaya fuska a haɗe, mutanen yanzu basu da kirki ace ka kusan aika yaro lahira amma ka zauna ko a jikinka sai kace wanda ya kusan bige akuya yo ko akuyar ce aika fito ka duba idan kasan darajar rai, Zainab ta dawo gefenta ta tsaya tace "Hajar yanzu me kika aikata haka, Allah ya isa fa kikai masa, dubi fa har yanzu bai tafi ba", Hajar ta kalli motar da har yanzu take tsakiyar titi ta yamutsa fuska tace "me kwa na aikata, ya shekara a wajen kar ya tashi". a hankali ya juya kan motar ya gyara parking a gefen titi, Zainab ta damƙi hannun Hajar ta fara janta ganin ya fito daga motar ya tunkarosu, Zainab tana janta tace "Hajar kizo mu gudu kar yayi mana wani abun", Hajar ta fuzge hannunta tace "wllh bazan gudu ba", Zainab tayi tsam ganin har ya iso gabansu yayinda wani ƙamshi mai daɗi ya fara busowa a hancinsu, yana kallon Zainab speaking calmly yace "Assalamu alaikum young lady", a ɗarare ta amsa kana tace "bawan Allah kayi haƙuri dan Allah", Hajar da ta juyar da fuskarta ta juyo ta ɓalla mata harara jin abinda tace, girgiza kai yayi yace "ba komai, tell your friend itama tasan darajar ɗan Adam cause ba tayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan mutum ba", da sauri Hajar ta juyo ta kallesa, and that look makes her brain to boot on, she saw this calm and charming face familiar, but where and when??, walking fast ya koma ya shiga motarsa ya kunna ya fita daga street ɗin da reverse. gida ya koma sbd wannan incidence ɗin da ya faru yasa yama manta da wani batun fruit salad, yana parking motar Garba ya taho wajensa, ko kashe motar baiyi ba ya fito cikin sauri ya shiga cikin gida, Garba ne ya shiga motar ya kashe sannan ya zare key ya fito. har lokacin Noor da Khausar suna zaune a palour, Noor tana kallonsa tace "yaya ina fruit din ko basu ka fita nema ba", shiru yayi mata ya haye stairs, Khausar ta taɓota tace "he is weird", Noor ta sauke ajiyar zuciya tace "ina jin an ɓata masa rai ne", she knows her brother in and out kuma she is very sure rai aka ɓata masa. ★Hajar ta shiga gida sai gunguni take, Mu'azzam da yake alwala a bakin rariya yace "toh jarababbiya", ta zumɓuri baki tayi ɗakin umma, Maama da take talgen tuwo Nabila na mata tankaɗe tace "kin ji ba ɗan uwanta ma yasan jarababbiya ce", Nabila ta doka tsaki ta cigaba da tankaɗenta, Umma ta kalli Hajar da take ƙoƙarin cire hijab tace "ke kuma lafiya kike wani cin mur..?", Hajar tace "wai a duniyar nan Umma mutane basa son gaskiya, wai wani mutum ne ya kusan kaɗe wani yaro a titi amma ko a jikinsa, wllh ko fitowa ya duba yaron ƙi yayi", Umma tace "Allah ya kyauta bai dai bigesa ba ko??", Hajar tace "saura ƙiris fa, amma wllh mutumin nan yadda kika san gunki haka ya zauna a mota yaƙi fitowa ya duba yaron", Umma tace "ke kuma shine kike kumbura akan hakan", Hajar tayi shiru kawai tuno abinda yacewa Zainab take wai batayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan ɗan Adam ba. kiran sallar magrib ne ya fitar da ita tsakar gida tayo alwala ta dawo ɗaki tayi sallah, bayan ta idar da Sallahr isha'i tana zaune akan darduma Sabra ta ajiye littafi a gabanta tace "Adda ki koyamin", Hajar ta janyo littafin ta duba kana ta fara gaya mata abinda zata rubuta. Umma ta shigo da wata warmer ta abincin da tayi tazarce ta ajiye a gefe guda, Hajar na kallon Sabra tace "yanzu ke Sabra mosquito din ne baki iya spelling ba, ƙwaƙwalwar dusa ne dake ko me??" ta zuba mata rankwashi aka, Sabra ta riƙe kai tace "ashhh Adda fa na iya", Hajar tace "to rubuta mana", Umma tace "kiyi mata a hankali dan Allah". washe gari Hajar taje islamiyya tayi screening dinta na ƙarshe, kuma a yau ne aka fayyace musu kuɗin sauka da walima, kwanaki uku bayan haka ranar Alhamis da yamma, Baba bai jima da dawowa daga wajen aiki ba yana zaune a ƙofar ɗakinsa yana cin abinci, wani yaro ne ya shigo gidan yace "wai ana sallama da mal Adamu", Hajar da take shanya kayan da ta gama wankewa tayi wuf ta shiga ɗaki, jikinta ne ya bata cewa ya sayyadi Nura ne yau yazo wajen Baba daman ya gaya mata zaizo, Baba ya ɗauki kofin ruwa ya sha sannan ya rufe ragowar abincin ya miƙe ya saka takalmi yayi soro, yana zuwa ya tarar da wasu mutane su uku, biyu zasu kai sa'anninsa ɗayan kuma matashi ne, matashin ne ya russuna yace "Baba barka da fitowa", Baba ya kallesa ya amsa, shi dai bai shaida su ba, Baba ya miƙa musu hannu su kay musabaha, ɗaya daga cikin manyan yace "daman munzo da wata magana ne", Baba yace "toh" ya koma cikin gida ya amso tabarma a wajen Umma, tinda Maama taga ya fita soro da tabarma taji hankalinta bai kwanta ba, ta kalli Maimuna da take zaune akan dokin ƙofa tana shan rake ita da Nabila tace "Maimuna leƙo mana su waye suka zo wajen Babanku", Maimuna ta ɗauki rakenta ta ɓalla sai kace sabuwar kamu ta wuce ƙofar soro ta laɓe, leƙawa ta farayi ta hango su a zazzaune, da sauri ta dawo da kanta tace "ya sayyadi Nura" sai kuma ta kasa kunne, kaf abinda suka zanta karaf a kunnuwanta tana naɗa, taɓe baki tayi ta dawo cikin gida tana zabga tsaki, Maama ta dakata da sharar da take tace "su waye??", Maimuna ta zauna dokin ƙofa ta ɓalli rage tace "wai neman izini suka zo yi a wajen Baba na neman waccan shegiyar", Maama ta saki tsintsiyar hannunta tace "neman izini kamar ya??", Maimuna ta hura buɗaɗɗen hancinta tace "ni dai a yadda na fahimta sunzo nemawa ɗansu auren shegiya ne", Maama ta zaro ido tace "aure??", Nabila ta zubar da tuƙar raken bakinta tace "Hajarar??", Maimuna ta kallesu duka tace "meye naga kun wani firgita ne??, bafa wani mai arziƙin ne yake nemanta ba, Nabila kin tuna ya sayyadi Nura??", Nabila tace "kwarai ma kuwa", Maimuna tace "toh shine fa yazo tare da iyayensa", Nabila ta daka wata shewa tace "waii tsiya ta ɗakko tsiya, da wannan ruɓaɓɓen shagon nasa zai riƙeta", Maama tace "kun sansa ne??", Nabila tace "farin sani ma kuwa, ya sayyadin islamiyyar mu da muka dena zuwa ne, wllh bashi da komai, matsolo ne ainun", Maama ta gasa mata harara tace "dalla gafara can, da bashi da komai ɗin ke kin taɓa kawo kamarsa ne eyee ko wanda bai kaishi matsolontaka ba?, wllh kun bani kunya duk irin samarin da kuka tara babu wanda ya taɓa zuwa gidan nan da maganar arziƙi, kuna zaune sai kace tsumammun kayan wanki waccan shegiyar zata cigaba", Maimuna tace "chaɓ, ina wani cigaba wajen Nura, wllh ci baya daii", Maama tace "ja can amma dai ta fi ku ko??", Maimuna tace "wllh bata fini ba nida nake da Alhaj, kuma yace aurena zaiyi, lokacin zuwa wajen Baba ne kawai bai samu ba". Baba ne ya dawo ciki ya naɗo tabarma a hannunsa, kan dardumarsa ya koma ya zauna ya kirawo Umma, Umma ta fito ta tsugunna tace "mal gani". Baba ya wassafa mata kaf abinda ya faru ya ƙarƙare da cewa "da har kuɗin aure suka ce zasu bayar na dakatar dasu sbd inaso na binciki yaron kuma a tabbatar da yarinya itama tana so", Umma tace "to mal Allah ya tabbatar da alkhairy". Maama da tayi karaf da kunnenta ta rangaɗa wata shegiyar guɗa ta cigaba da shararta. ★Nurain zaune a farar kujera a compound ɗin gidansu Ruqayyah yana jiran fitowarta, wayarsa yake latsawa a hankali, saida ya jingine 20mins amma bata fito ba abinda bai taɓa faruwa ba, dialing numbernta yayi, tana yin picking speaking keenly tace "ina zuwa dearest" ta katse kiran, after like 5mins ta fito sanye da hijab da riga da skirt na atamfa, taja kujera ta zauna tana facing ɗinsa tace "sorry na saka jira", wayarsa ya kashe ya saka a pocket yace "na ɗauka ma kwalliya aka tsaya tsara min", murmushin gefen baki tayi tace "ka jira lokaci, kwalliya har saika gaji da ita", ya ringa kallonta sai kuma yace "ehen ina jinki you said you want to talk to me", wasa ta farayi da fingers ɗinta tace "kana ji dearest", yace "all ears", ta sunkuyar da kanta tace "ina so a ɗaga lokacin bikin mu"............✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {10...} With a weird facial expression Nurain ya kalli Ruqayyah, kallonta ya ringa yi ya kasa cewa komai, shirun da taji yayi ne yasa ta ɗago kanta sukay ido huɗu, tayi sauri ta sunkuyar da kanta tace "ina maka magana fa", keenly yace "naji ai, why Ruqayyah?, mesa kike so a ɗaga lokaci?", without looking at him tace "sai naga kamar za a matse maka hidima, dearest banaso ka matsawa kanka akan aurenmu, kabi komai a hankali, a maida lokacin nan da 10months kaga zaka fi balancing..", ido ya zaro yace "10 what?, Ruqayyah are you kidding me?", tace "no dearest i am not kidding", ajiyar zuciya ya sauke yace "look Ruqayyah ba dai damuwanki karna takura kaina ba, babe just relax Insha Allah komai zaizo cikin sauƙi, karki wani damu i planned for it", ajiyar zuciya ta sauke tace "alright", yace "good, yanzu wane shirye-shirye kika fara?", tace "ni ban fara shirin komai ba amma yanzu zan fara", yace "ohk, all the expenses on me", tace "Ohk". da haka kuma suka koma firarsu ta masoya mai daɗi. A kwana a tashi, bikin Nurain da Ruqayyah yau saura 3weeks cif kuma a yau ne aka shirya kai lefe, Anty Zulaiha da Sakeena step sis din Nurain da suke same father da Anty Mardiyya ƙanwar Abba sune jigajigai sai sauran ƴan uwa su biyar aka kai lefe. gaskiya an zuba bajinta, both sides sunyi ƙoƙari sosai, ammafa Ruqayyah ta samu lefe na gani na faɗa ba ƙarya. Nurain yana zaune a kan kujerar balconyn ɗakinsa dake up stairs yana jiran yaga motocin da aka tafi kai lefe dasu sun fara dawowa, ai kam yana ganin dawowar tasu ya sakko down stairs ya fita balcony, Anty Zulaiha da sauran suka wuce cikin gida, Nurain ya amshi baby boy ɗin hannun Sakeena yace "yawwa ƴar uwata fatan dai basu ƙara mana lokaci ba?", Sakeena ta kallesa up and down tace "Nurain ni ka raina kenan ko?, nice baka jin kunya ba?, mesa baka tambayi anty Mardiyya ko Zuhaiha ba saini karkatacciya bishiyarka mai daɗin hawa ko?", yace "ohh wllh kin fiya son girma", handbag ɗinta ta ɗauka ta rufe motar tayi gaba tace "zaka ga son girma alhaji". yana kallonta ta shiga ciki ya shafa kansa shima ya shiga. A palour ya tarar dasu sun baje haja suna mayar da yadda akai, Mami ma na tare dasu suna wassafa mata yadda akai, Noor ta zazzaro ido tana dashare tooth a cikinsu, Allah kaɗai yasan yadda ta tamawa bikin nan, Nurain ya zaga ta bayan kujerar da Sakeena take ya ɗora mata Ayman a laps, ta juya ta kallesa tace "Au bazaka riƙemin shi ba, yanzu daga hidimarka na dawo kuma nagaji", yace "zan je Hospital ne akwai wani urgent patient da zan duba ne", tace "in this Noon?", yace "yeah, naso ma na makara fa na tsaya naga dawowarku ne", tace "Ohk saika dawo saika mayar dani gida banzo da Mota ba", yace "Ohk". ★Alhmdll acikin wannan taƙin result ɗin Hajar na NECO ya fito kuma taci sosai, Nura ne ya amshi takardun ya shiga fafutukar nema mata school of Nursing tinda shine burinta a karatu, Soyayya tsaftatacciyar mara algus Hajar da Nura suka yiwa junansu, a yanzu kam sun buɗe sabon shafi a soyayyarsu tinda sun samu lasisi mai kyau, Hajar na zaune a tsakar gida akan kujera tana buga game a sabuwar wayarta Android da Nura ya kawo mata shekaran jiya, Umma ta leƙo daga ɗaki tayi kiranta, tarar da ita tayi tana ƙoƙarin zura hijab tace "yanzu zaki tafi?", Umma tace "shirya mu tafi", Hajar tace "tom, amma Sabra fa idan ta dawo daga islamiyya", Umma tace "da wuri zamu dawo ai, wllh banyi niyyar zuwa dake ba amma ina tsoro na barki ke kaɗai a gidan nan ga Sa'adatu ma naga tazo", Hajar tace "Umma nifa na dena shiga sabgarsu, na miki alƙawari fa kuma Baba ma nayi masa", Umma tace "A'a shirya dai mu tafi, haƙurinki siƙewa yake". Hajar ta canza kayan jikinta na tsakar gida zuwa wata riga da skirt na atamfa Maroon da zanen manyan flowers pink wacca ta fito da hasken fatarta, mayafi mai ɗan girma pink ta yafa, Umma ta kalleta tace "sai kace zaki gidan biki, asibiti fa zamu", Hajar tace "Umma bafa kwalliya nayi ba, kaya kawai na canza, dan kuma zani asibiti sai nayi shiga hajaran majaran", Umma ta sake kallonta taga dai eh yanayin jikinta ne mai amsa. Hajar ta saka wayarta a handbag ɗin Umma ta ɗauki padlock a kan window, Huzaifa ne ya shigo wanda yazo hutun session daga FUD, cike da ladabi ya gaishe da Umma, Hajar tana gama rufe ɗaki da padlock ta gyara mayafinta ta gaishesa, Hajar da Umma suka wuce, Maama ta yaye labulen ɗakinta tace "uwarka ce ita kake gaisheta?, nace Uwarka ce iyee?, wllh kai da Nasiru da badan a gida na haifeku ba da na rantse na kuma rantsewa canje akaimin a asibiti", ya girgiza kai ya shiga ɗakinsu. Hajar da Umma suna isa Hospital suka bi dogon corridorn da zai kaisu ward A, Umma ta murɗa ƙofa ta shiga da sallama, masu jinyar patient dinda take gadon farko suka amsa mata, tayi musu ya me jiki kana ta fara duba gadon mara lafiyar da suka zo dubawa, Hajar da take biye da ita ta hango Anty Jamila daga can gefen gadon ƙarshe na ward din, Hajar tace "umma ga su can", bayan sun gaisa ne suka duba Wasila wacca take matsayin cousin ɗinsu Umma, Hajar dai gefe ta koma suka jone da Hafsa, Umma ta kalli Anty Jamila tace "waye a wajenta", Anty Jamila tace "Amina ce, tin ɗazu take sintiri zuwa wajen Nurse ɗinda tace ta ringa bibiyarta sbd likitan da zai dubata tin safe ake jiransa baizo ba", Umma ta kalli Wasila da take jin jiki tace "yanzu tin safe likitan baizo ba, wannan wane irin rashin tausayi ne, kai Allah ya gyara mana ƙasar mu", Anty Jamila tace "Ameen", Nurse Jidda ce ta shigo ta duba Wasila tace "ya ƙirjin har yanzu yana miki zafin?", Wasila ta jinjina kai alamar eh, Nurse Jidda tace "Sorry, insha Allah yanzu doctorn da zai dubaki zaizo" ta fita daga ward din, Hafsa ta kalli Hajar tace "wllh Nurse ɗin nan tanada kirki, a yadda Nurses suke zabga rashin mutunci ga patient ita dai banga tayi haka ba", Hajar tace "naji Anty ɗazu tana cewa wai likita baizo ya dubata tin safe ake jiransa?", Hafsa tace "eh muma wajen 1hour kenan da zuwan mu ana jiransa", Hajar ta taɓe baki tace "uhmm wannan rashin sanin darajar ɗan Adam ne...", wani ƙamshi wanda ba baƙonta bane ta shaƙa wanda ya katse sauran maganar bakinta daga fita, Nurse Jidda na leading dinsa har ya iso gaban gadon ya kalli Wasila with care, few minutes ya gama aikinsa, Hajar da ta gama fahimta shine likitan da ake jira tin safe ta juya idanunta akansa tana so ta tuno inda tasan wannan fuskar, coily hair dinsa da kuma ƙamshin da ta fuskanci nasa ne yasa kwanyarta ta amsa, a take ta ganesa a zuciyarta tace (no wonder, wllh an cuci doctors), kasa ɗauke idonta tayi daga kansa tana yamutsa fuska, Dr Uthman ya kalli Nurse Jidda yayi alama da hannu, tace "yess doctor". ya juya zai bar wajen sai kuma ya juyo ya kalli wajen da tin shigowarsa yaji kamar an zuba masa arwa, a take idanunsu suka sarƙe, ya ƙanƙance nasa, yayi wani slight smirk ya juya da tafiyarsa, Hajar taji cewa itama yanzu ne ya kamata ta rama abinda yace mata rannan, da sauri ta miƙe ta wurgawa Hafsa wayarta a cinya ta zura takalmi, Umma tace "ina zaki?", tana tafiya tace "yanzu zan dawo" ta fita daga ward din da sauri sbd karya ɓace mata, long corridorn ta tsaya tana kallo, ta kalli hagu taga bata hangosa ba, tana kallon right taga har ya kusan fita daga block din, ta daka tsaki tace "sauri sai kace lantarki" ta bisa da sauri-sauri gudu-gudu, ai kam har ya fita daga block ta cimmasa, railern stairs ta riƙe tace "ɗan dakata Doctor", the voice sound familiar and the name inkiyarsa ce a hospital, these two reason make him to turn around, kallon 1sec yayi mata ya zuba hannayensa a pocket ya juya zai cigaba da tafiyarsa tace "Fake doctor, i think the name fit you, wanda baisan darajan ɗan Adam ba bazai zama real doctor ba saidai Fake", tinda yake bai taɓa encounter da trouble maker irin wannan little girl din ba, kuma ko kaɗan baiji zafin maganar da ta gaya masa ba saima ya tsinci kansa da yin murmushin gefen baki sai kuma ya juya da nufin kallonta, amma tini har tayi nisa da barin wajen tana tafiyarta cikin nutsuwa. ★Biki bidiri bireɗeɗe, saura 1week cif aka fara gudanar da shagali, Ruqayyah dai ba tay wani event ba duk tace bata buƙata, Nurain kam ya sakar mata bakin aljihu duk abinda ta tambayesa sai yace gashi indai money ne, ranar juma'a ne ɗaurin aure, ranar Alhamis aka daki mother's Eve tare da kamun amarya, Ruqayyah ta fito daga toilet bayan tayi wanka ta wanke nude make-up din da aka mata ta mother's Eve, friends ɗinta su huɗu ne a ɗakin, Meema ce ta miƙo mata wayarta tace "it has been ringing for a while", Ruqayyah ta goge hannunta da yaji jan ƙunshi a jikin farin towel ɗin data ɗaura sannan ta karɓi wayar, wani kiran ne ya sake shigowa da ringing tone ɗinda tayi setting musamman sbd Nurain, murmushi tayi ta kara wayar a kunne, ajiyar zuciya taji ya sauke kana yace "ina kika shiga ne?", tayi wasa da kwayar idonta tace "ina kam zan shiga", yace "Ohk, sleep tight for today, tomorrow in my arms", ƙit ta kashe wayar ta harareta, ta dannata a silent sbd tasan definitely sai ya sake kira, kolacca mai sanyi ƙamshi ta ɗakko ta murza a jikinta sannan ta ɗela gado ta rufa da duvet, wayarta ta danna taga message from dearest, da sauri ta mayar masa da reply, few minutes saiga wani saƙon nan ya sake shigowa, ta mayar da reply, a haka dai sukay ta tura text message har basu san dare yayi sosai ba, text ɗinda ya shigo na ƙarshe hopping daga Nurain yake sai taga akasin haka. minti goma ta ɗauka tana karanta message din, a hankali ta tashi zaune ta kalli agogon wayarta, 3:00am passed, Meema da sauran friend ɗinta duk sun sheme. a hankali ta sakko daga kan gadon ta kunna fitilar wayarta sbd idan ta kunna ta ɗakin haske zai iya farkar da wani wanda a halin yanzu bata son kowa yasan abinda take shirin aikatawa sai zuwa gobe da safe tinda dole a sani. press din kayanta ta buɗe, gaba ɗaya kayanta masu kyau an riga an shirya mata su a box, waɗanda suka rage duk wanda bata buƙata ne na bayarwa, gashi box ɗin tana ɗakin Momy. sleeping gown din jikinta ta cire ta saka wata Abaya wacca ta Meema ce, cikin sanɗa ta fita a ɗakin ta wuce na Momy, a hankali ta murɗa handle ta shiga cikin sanɗa, ta haska fitilar wayarta ta buɗe box ɗin da kayanta suke, 5sets ta ɗiba ta zazzage jakar kayan Kulsum elder sister ɗinta ta zuba a ciki, ta ɗauki jakar ta fita, A palour ta ajiye jakar a kan kujera sai kuma ta juyo ta koma ɗakin Momy, bedside ta janyo a hankali ta ɗakko Jotter da biro tayi rubutu, ta yage papern ta soketa ajikin lamp sannan ta mayar da Jottern, Momy ta motsa tace "waye a nan?", Ruqayyah tayi tsam sai kuma tace "Momy nice, nazo neman paracetamol ne zan sha kaina ne yake ciwo", Momy ta fara ƙoƙarin miƙewa daman bata daɗe da kwanciya ba kuma tin shigowar Ruqayyah ta farko taji ɓuruntu, Ruqayyah tace "Momy ki koma ki kwanta na samu a jakar Kulsum" ta miƙe ta fita a ɗakin jikinta na rawa. ajiyar zuciya ta sauke ta ɗauki jakarta ta fita compound, iyakarta kenan domin daga nan bazata iya yin gaba ba sbd gate a garƙame yake, can bayan wani ƙaton drum da ake tara shara ta koma ta raɓe, she spent almost 2 and half hours there kafin abinda tayi fako ya wanzu, a kan idonta Daddy ya buɗe gate ya fita Masallaci Sallahr asuba, and she used that as an opportunity to fulfilled her mission...........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {11...} ★Da misalin ƙarfe bakwai da arba'in na safe, Hajar ce zaune a gaban rariya tana rege waken kulele, a hankali take humming song tana aikinta, Naseer ne ya shigo hannunsa riƙe da damin doyar da ya siyo a Zaria, Hajar ta amsa sallamarsa tace "yaya sunnu da dawowa ya hanya?", yace "lafiya hajara" ya ƙarasa ciki, damin doyar ya ajiye a ƙofar ɗakin Baba kana ya shiga ciki, Naseer ya kalli Baba ganin yadda ya rame sosai, ya samu waje ya zauna suka gaisa, Baba yace "har kun juyo?", Naseer yace "Eh, sai gobe Insha Allah zanyi lodin Lagos", Baba yace "to Allah ya taimaka", Naseer yace "ga doya nan na shigo da ita", Baba ya saka masa albarka tare da addu'ar Allah ya ruɓanya masa, Naseer yace "Ameen, bari na shiga na gaida Maama" ya miƙe ya fita daga ɗakin, a ƙofar ɗakin Maama ya tsaya yayi sallama, shiru yaji ba a amsa ba ya sake yin wata sallamar nanma dai shiru, ya ɗan yaye labule ya leƙa, Maama tana zaune ta miƙe ƙafa tana karkaɗata, Nabilah tana kwance a kan gado tana bacci kamar mushe don ko sallar asuba ba tay ba, Maimuna kuma tana shafa man bleeching a fuska ta dauɗe kunnuwanta da earpiece, ido huɗu Naseer sukay da Maama wacca take kallon ƙofar kuma tana jinsa tayi burus, takalminsa ya cire ya shigo ya samu waje ya zauna yace "Maama barka da safiya", ta kawar da kanta kamar bazata amsa ba tace "lafiya, ai da yake shi kaɗai ya haifeka dole ka fara zuwa wajensa", tin lokacin da ya shigo ta hangosa ta shatin labule, ya shafa kansa yace "ya gida Maama?", ta galla masa harara tace "saika tambayi gidan kaji ya yake, ni ka tambayeni wani gida, nice nan uwarka Nasiru, wato duk abinda ka shigo dashi saika nufi ɗakin mahaifinka ko, ni banida mutuncin da zaka fara zuwa wajena ko, kaida Huzaifa saidai nayi muku addu'ar Allah ya dawo muku da hankalinku da tunani, an riga an shanyemin ku wllh, ƴaƴana mata kam sai san barka ta ko'ina alheri nake samu dasu", shi dai ya sunkuyar da kai yace "ayi hakuri Maama", Maimuna kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da jin waƙarta tana sabgar gabanta, tashi yayi zai fita suka haɗa ido da Maimuna ta zumɓuri baki ta ɗauke kai, yana fita ta daka tsaki tace "masifa, jaraba ya dawo, Allah yasa dai yau zai koma", Maama ta kalleta tace "leƙa kiga akwai doya a tsakar gida", Maimuna ta leƙa ta dawo tace "Eh naga Baba yana rabawa", Maama ta miƙe ta gyara haɓar zaninta tace "rabawa kuma?" ta fita tsakar gida, Baba har ya gama kasafta doyar gida biyu dai-dai, ya ɗauki guda uku cikin kaso ɗaya ya ƙara a ɗaya, Maama dai ta bishi da kallo tana jiran taga abinda zai yi, ya dubi Maama ya nuna mata kason da yafi yawa yace "ɗauki wannan, Nasiru ne ya kawo mana", Maama ta harari kason doyar bata ce komai ba, Baba ya kira Umma ta fito daga ɗakinta itama ya nuna mata ƙaramin kason yace ta ɗauka Naseer ne ya kawo, Umma tace "toh masha Allah, Allah yayi albarka an gode", ta sunkuya ta fara ɗiban doyar, Maama ta daka wata tsawa tace "wllh ba a isa ba, idan na yadda kwarankwatsa dubu ta waɗo a kaina", Baba ya tsaya yana mata kallon mahaukaciya, Maama ta buga ƙafa har zaninta yana ƙoƙarin kuncewa ta nuna Umma tace "kaji matsiyaciya kwaɗayayyiya, yanzu ke baki ji kunyar ɗaukar doyar nan ba, ɗanki ne ya kawo ko ubanki, keda haihuwa ba tay miki rana ba shine zaki raɓo kice zakici arziƙina, wllh ki ajiye doyar nan tin kafin ranki yayi mugun ɓaci", Umma ta mayar da doyar da ta fara ɗiba ta ajiye ta juya zata koma ɗakinta, Baba ya dakatar da ita yace "Faɗima dawo ki ɗebi doyarki, ai ni Nasiru ya kawowa kuma inada iko akan wanda zan bawa", Maama ta rangaɗa Shewa tace "toh banda nan mal, iko ko?, to baka dashi anan, wllh wannan shegiyar da shegun ƴaƴanta bazasu ci doyar nan ba, haramiya ce a garesu", tana gama bambaminta ta kwalawa Maimuna kira, Maimuna bata ji ba sbd earpiece dake kunnenta, Maama ta leƙa ɗakin ta window ta ɗauki warin slipers ta jefa mata, Maimuna ta fizge earpiece ɗin kunnenta a hasale tace "wane ɗan iskan ne ya wurgomin takalmi", Maama tayi mata daƙuwa tace "fito", kafin Maama ta ankara har Umma ta shiga da wata doyar ɗaki tinda Baba ya umarceta da ta ɗauka dole, Maama ta barƙa ashar tace "wllh saikin fito dasu" ta kalli Maimuna tace "shiga ɗakinta ki ɗakko min doyar da ɗana ya siyo, ni bazan shiga na ɗebo bala'i ba", Maimuna tace "chab kenan ni bala'in ya shafeni", Maama tace "tofe jikinki da addu'a ki shiga ki ɗakko min gumin ɗana", Baba ya nuna Maimuna da yatsa yace "karki kuskura ki shiga ɗakin nan", Maimuna tace "yo Baba kanafa gani Maama ce ta sakani" ta doshi ƙofar ɗakin, Hajar daman tana laɓe a jikin labule zuciyarta na tafasa, ai kam ta ɗauki doyar da Umma ta zube a bakin ƙofa, Maimuna tana kunno kai ta wurga mata ita a fuska, daman doyar guda huɗu ce kuma saida ta jefe Maimuna dasu tas a ƴan sakanni, Maimuna ta riƙe hancinta da doyar ƙarshe ta sauka akai tana jin kamar zai gutsire sbd azaba, Hajar tace "ga tsiyarku nan" ta banke ƙofa ta saka sakata, hannu biyu tasa ta rufe duka kunnuwanta tana bubbugasu sbd karma taji muryar Umma ko Baba. ★Da safiyar ranar ɗaurin aure, Meema friend ɗin Ruqayyah kuma cousin ɗinta ce ta fita palour neman amarya, gidansu Ruqayyah acike yake da ƴan uwa da abokan arziki, Kulsum ta hango akan kujera tana breakfast, Meema ta matsa kusa da ita tace "amm yaya ko kinga Ruqayyah", Kulsum ta ajiye mug ɗin hannunta a gefen kujera tace "A'a bata wajenku ne?, nima tin ɗazu nake nemanta ta ɗauki kayan da zata saka yanzu", Meema tace "Ohk, nima tinda na tashi ban ganta a room ɗin mu ba, to i thought tana wajen Momy ne", Kulsum tace "ping her on phone", Meema tace "switched off, tin ɗazu nake kira amma bari na sake kiran", Meema ta kunna wayarta dake hannunta tayi dialing numbern Ruqayyah ta saka a handsfree, switched off suka ji, Kulsum ta amshe wayar daga hannun Meema ta sake kira, same thing dai aka ce mata wato switched off, keenly Kulsum tace "where could she be?", ta miƙawa Meema mug ɗin hannunta da bata gama shan shayin ciki ba, direct ɗakin Momy ta wuce, ai kam dai tayi sa'a ba kowa a ɗakin sai Momy, kayanta tagani wargaje akan carpet a nannaɗe gefe ɗaya, ta kalli Momy tace "Momy wane ya fitomin da kaya daga cikin jaka??", Momy ta juya hannu tace "ni kam bansani ba, ai saida nace kisa a wardrobe", Kulsum ta fara mita ta tsugunna ta fara kwashe kayan sai kuma tace "to ina jakar kuma??", Momy tace "toh kodai ɓarawo ne ya shigo ɗakin nan, kinga yanzu ma naga box ɗin kayan Ruqayyah a buɗe", Kulsum tace "yawwa Ruqayyah ta gaya miki zata fita ne??", Momy ta buɗe wardrobe tace "A'a, me zai kaita fita yau", Kulsum tace "toh ina ta shiga, Meema ma tace bata wajensu", Momy ta dakata da abinda take cikin wardrobe ta juya tace "An kira wayarta", Kulsum tace "yess", Aisha ce ta shigo babbar ƴa agidan, ta wuce hanyar toilet tace "gwara nayi wankana da wuri kafin na shiga sabga, a matsayina na second mother", Kulsum tace "yaya ko kinga Ruqayyah", Aisha ta riƙe handle ɗin ƙofar toilet tace "A'a rabona da ita tin jiya wajen mother's Eve, me ya faru?", Kulsum tace "yo nemanta fa ake tazo ta shirya", Aisha tace "ko wajen make-up ta tafi?", Momy ta sauke ajiyar zuciya domin har hankalinta ya fara tashi, Kulsum tace "Eh kam haka ne, wajen make-up ta tafi, amma da wuri haka kuma bata gayawa kowa ba", Aisha tayi slight hiss tace "yaran yanzu rawar kaine dasu akan aure" ta shige toilet. Kulsum dai bataga jakar kayanta ba kawai ta saka kayan a press din Momy ta koma palour don ta ƙarasa shan shayinta, ta zauna a position ɗin data tashi ɗazu ta amshi shayin daga hannun Meema tace "toh ai Ruqayyahn wajen make-up ta tafi", Meema tace "wajen make-up, mai kwalliyar fa har gida zatazo tayi mata, kuma mafa kawai gyara mata fuska za tay da ɗauri ba wata kwalliya ta azo mugani za ay mata ba, kinsan Ruqayyah da maintaining natural beauty, aikam bari na kira makeup artist din". Meema ta takune gira bayan ta gama waya da mai kwalliya ta tabbatar mata Ruqayyah bata zo wajenta ba. secretly Meema da Kulsum suka fara neman Ruqayyah a gidan, ko ina saida suka duba kuma suka tambayi waɗanda suka dace, daga ƙarshe Kulsum ta koma ɗakin Momy, this time ƙannen Momy su biyu suna nan da ita kanta Momyn, Aisha kuma tana gefe tana rubbing lotion, Momy fuskar Kulsum kawai ta kalla tasan akwai damuwa don haka tace "mene ne??", Kulsum tace "Momy bafa a ga Ruqayyah ba?", Aisha ta dakata da shafa man da take tace "bata wajen make-up din", Kulsum tace "yess, mun duba ko ina a gidan nan, kuma mun tambayi waɗanda muke tunanin tana tare dasu amma bata nan, and her phone is switched off", hankalin kowa yayi kan Kulsum da ta gama magana, Momy ta zauna a kan bedside thinking of another thing, haj Safiyya tace "Kulsum ku nutsu dai ku dubata sosai, yo ina zata?", Kulsum tace "Aunt wllh bata nan, baki ga duban da mukai nida Meema ba", Momy tayi wani tunani tace "kun duba part din Daddy", Kulsum tace "nan ne kawai bamu shiga ba", Momy zata miƙe hook ɗin zip ɗin rigarta ya riƙo wani ɗan siririn plastic dake kewaye da bedside lamp, tana miƙewa lamp ɗin ta biyota, saura ƙiris ta faɗi, Momy ta mayar da ita sai kuma ta tsaya tana kallon papern data faɗi a kan tiles maimakon fitilar, bata san dalili ba amma tana kallon papern zuciyarta ta buga, ta sunkuya ta ɗauka a zatonta zata ga electricity bill da tayi misplacing jiya, saɓanin electricity bill sai taga rubutun ƴarta Ruqayyah wanda kalaman ciki suka sa ta koma ta zauna a kan bedside babu shiri, Sosai hankalin mutanen ɗakin yayo kanta, Aisha ce ta fara yo kanta tace "Momy lafiya" sai kuma ta zare takardar hannunta wacca ta lura itace ta jefata a wannan hali, Aisha ta zabga salati bayan ta gama karance takardar itama tace "jama'a Ruqayyah ta gudu". iya su da suke cikin ɗakin ne suka san abinda yake faruwa sai Meema wacca bata san cewa Ruqayyah gudawa tayi ba amma tasan ba a ganta ba. Kulsum ta sakawa ɗaki lock gudun kar wani ya shigo, bayan ƙura ta lafa na firgici da tsantsanin mamakin abinda Ruqayyah ta aikata ɗakin yayi tsit, Momy ta zabga uban tagumi tana kallon takardar, haj Safiyya tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, ya kamata ki sanar da Daddy", Aisha tace "chab wannan wane irin abin kunya ne?", Momy ta sauke ajiyar zuciya, wato jiya da taga Ruqayyah da daddare wato ƙoƙarin guduwa take. ta ɗauki papern ta fita daga ɗakin, ƴan biki na gidan sai hada-hada suke wasu ma har sun fesa wanka sbd baifi saura awa ɗaya lokacin ɗaura aure yayi ba, haka Momy ta ringa ƙetaresu tana yaƙe harta wuce part ɗin Daddy, tin daga palour taji ƙamshin turarensa na tashi, Momy ta haɗiyi yawu tana son ƙwallon da ya tsaya mata a maƙoshi ya wuce, a hankali ta shiga bedroom ɗin Daddy da sallama, ta tarar dashi har ya shirya yana waya, ji tayi yace "Eh yau ne ɗaurin auren, ana idar da sallar Juma'a za a ɗaura Inshallah", ta koma gefen gado ta zauna tana jiran ya gama wayar, bai jima ba ya kammala ya juyo ya kalleta yace "me ya faru?" yana gyara hular kansa, bata basa amsa ba kawai ta miƙa masa takarda, karɓa yayi ya saka glasses a idonsa, ya buɗe takardar ya karanta yana ƙanƙance ido yace "meye wannan", Momy tace "Ruqayyah ce ta ajiye", ya cire hular kansa zanna bukar ya ajiye akan mirror, malum-malum ɗin jikinsa da ta sha ado na ɗinkin hannu da zare mai tsada itama ya cireta yayi hanging yace "Shikenan ta yiwa kanta". Daddy ya kira ƴan uwansa maza su huɗu ya sanar dasu abinda ake ciki kuma yace suje su sanar da dangin Ango. suma duk sun sha kwalliyar ɗaurin aure suka hau Mota suka nufi gidansu Ango. A Great room ɗin Abba aka saukesu, shima Abba he was ready duk da dai ya bawa ƙaninsa walicci. bayan sun gaisa babban cikinsu ya sanar da Abba komai, Abba ya sauke ajiyar zuciya bayan ya gama saurarensa yace "Allah ka shirya mana zuri'a", daga haka bai sake cewa komai ba. numbern Mami yayi dialing bayan sun tafi, after wayar tayi ringing sau huɗu Mami ta ɗauka, keenly Abba yace mata yana bukatar ganinta yanzu a part ɗinsa, Mami ta shigo palour cikin wani dakakken lace ɗan ubansu wanda yasha stones da samfalwa mai rawa, fuskarta cike da walwala amma tana ganin fuskar Abba zuciyarta ta buga, kusa dashi ta zauna a kujera 2seater, yana kallon fuskarta sai yaga kamarta da Nurain ainun wanda zai samu karayar zuciya nanda wani lokaci mai ƙaratowa, Abba yace "Khadeeja", Mami tace "Na'am", ya ɗaga kansa ya kalli ceiling yana wasa da yatsun hannunsa yace "ki bawa Nurain haƙuri", ya gaya mata kaf abinda ƙannen Daddy suka gaya masa, tabbas Mami ta girgiza amma Nurain shi yafi tsaya mata a rai, ita uwace wacca tasan ciki da waje na ƴaƴanta, ta san ɗanta yana son Ruqayyah sosai ma kuwa, a hankali tace "shikenan, Allah ya basa wacca ta fita", Abba yana kallon ceiling yace "Ameen, kiyi azamar sanar dashi". Mami ta miƙe ta fita duk jikinta yayi sanyi, tana shiga main palour Noor da itama tasha lace irin nata tace "Mami na kai snacks ɗin ɗakinki, Anty Zulaiha kuma tana nemanki", Mami tace "Ohk, Nurain ya sakko?", Sakeena tace "No, ai duk nan shi muke jira ya sakko muga kwalliyar Ango". Mami ta kalli stairs ɗin da zai kaita ɗakin Nurain, a hankali ta fara hawa stairs ɗin harta kai ƙarshe, sau biyu tayi knocking ƙofar ɗakinsa ya buɗe, he was already dressed up, ta tsaya tana kallonsa da shigar da bata taɓa ganin yayi irinta ba, yayi kyau wanda bai taɓa irinsa ba, caramel skin ɗinsa tayi wani luf-luf, ga wani ƙamshi da yake tashi a jikinsa wanda bata taɓa jin irinsa a tare dashi ba, murmushin da yayi mata shima bata taɓa ganin irinsa ba, calmly tace "Son are you ready?", yace "almost", ta shiga ɗakin tace "i need to talk to you"..........✍️ 💛 HAJAR💛 by Feenerh_feeche {12...} Nurain ya mayar da ƙofa ya rufe, Mami ta riƙo hannunsa ta zaunar dashi a gefen bed kusa da gogaggiyar malum-malumsa da hula waɗanda yake shirin sakawa, da wani irin expressions yake kallonta, ta zaunar dashi sbd gudun kar ya faɗi idan yaji abinda zata faɗa duk da tasan shi mai tawakkali ne, a hankali tace "Uthman" tana shafa kansa, yace "na'am Mami na", tace "kasan duk wani abu da yake faruwa ko kuma zai faru nufi ne na Allah, kuma nasan cewa ka yadda da ƙaddara", ya lumshe idonsa yana jin yadda take shafa kansa kamar tana rarrashinsa, tinda yaji waɗannan kalaman yasan cewa something was odd, yace "Mami me kike so ki gayamin ne?", kusa dashi ta zauna kana ta fara magana a hankali tace "Ruqayyah yarinyar da zaka aura...", ta wassafa masa kaf abinda ya faru, wata irin aradu ce ta doka a zuciyarsa idonsa ya kaɗa yay jaa, ya kasa cewa komai sbd karayar zuci, ba ƙarya Ruqayyah broke his heart into million pieces, sama-sama yaji muryar Mami tana cewa "pray my Son, Addu'a itace maganin duk wata musiba, i know your in agony but plxx don't let it slaughter you", ya ɗago idanunsa da suke farare ƙal-ƙal amma a yanzu sun canja launi, ya buɗe baki kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, ya miƙe da sauri ya zubar da links ɗin rigarsa da yake dunƙule a hannunsa, wayarsa da take kan mirror ya ɗauka, yayi dialing numbern Ruqayyah ya kara a kunne, bashi da shakku ko ɗigo akan maganar da Maminsa ta gaya masa, yana so ya tuhumi Ruqayyah ne ya tambayeta Why him?.., me yasa sai shi a duk faɗin mazan duniya zata yaudara?, me yasa ta zaɓi ta ragargaza masa zuciya?, wannan shine sakayyar da zata yiwa soyayyarsa agareta, All love dinda take nuna masa was it a pretence all those years, Mami tace "who are you calling?", ya sake dialing for the fifths times, Mami ta sake zaunar dashi a gefen gado tace "Uthman, plxx relax, ban sanka da haka ba", ya sauke ajiyar zuciya yace "Mami, I'm okay" sai ya dafe kansa, knocking door akay Noor ta shigo tace "Mami tin ɗazu Anty Zulaiha take jiranki", Mami tace "Ohk, muje", Noor ta kalli Nurain da ya dafe kansa sannan ta fita a ɗakin, Mami ta miƙe a hankali ta dubi Nurain sai kuma ta sunkuya ta kwashe links din da ya zubar ta ɗora akan mirror tabi bayan Noor, zuciyarsa tafasa take, akwai ciwo sosai ace wanda ka yarda dashi ya yaudareka, yaudarar ma me zafi irin wnn, wayarsa ce ta fara ringing, ko kallonta beyi ba at this time he don't want to talk to anybody, he don't want to see anybody, all what he want is an explanation from Ruqayyah, wayar ya fuzgo da niyyar dannata a jirgi wani kiran ya sake shigowa from Dr Marwan, ya haɗiyi wani abu yayi picking kana ya kara wayar a kunnensa, Dr Marwa yace "wai ina ka saka wayarka ne tin ɗazu nake kira baka picking, ka gama ne muzo mu ɗauke ka, everyone is there Ango kawai muke jira", Nurain yace "Marwan cancel everything", Marwa yace "Dr what do you mean?", da kyar Nurain yace "yeah, plxx cancel the reception, ka bawa kowa haƙuri" ya katse kiran, ya janyo curtain ɗin wayar zai sakata a jirgi message ya shigo, saida ya saka wayar a jirgi sannan ya dawo ya fara karanta message din da ya shigo from Ruqayyah.. ( 😭 Sorry dearest, i want you to know that i madly love and i will be back to be with you, plxx wait for me.), yana gama karantawa yaji soyayyar Ruqayyah tana juyewa zuwa ƙiyayya, yayi wurgi da wayar ta daki bango sannan ta faɗi ƙasa ta tawarwatse. wnn text din babu abinda yayi masa saima ƙara masa raɗaɗi a zuciya, shi Ruqayyah zata yayyankawa zuciya da wuƙa mai kaifi kuma ta dawo ta bayan fage tana barbaɗa mata gishiri, dama bata turo masa wnn text ɗin ba da maybe some percent na son da yake mata zai ragu koda 3 ne, amma yanzu zero, zeron ma behind decimal point, ƙarƙat an yiwa mai dami ɗaya sata soyayyar Ruqayyah ta faɗi a ƙasa warwas, babu abinda yake ji sai tsanarta. Ruqayyah ta rushe da kuka bayan ta gama tura text message din, ta rungume wayar a ƙirjinta tana kuka sosai, few mutanen da suke kusa da ita a waiting chairs suka dubeta, saida taci kukanta ta more ta ciro barimar kunnenta, ta buɗe wajen sim card ta zare sims dinta ta zubasu a jaka, wayar ma ta wurgata a jaka, a lokacin aka fara announcing jirginsu zai boarding, ta miƙe tabi queue akay checking dinta sannan ta shiga Flight, ta zauna a seat dake kusa da window ta jinginar da kanta ta lumshe ido, wata mata da take gefenta ce ta taɓota jin anata cewa kowa ya saka belt dinsa jirgi zai tashi amma bata motsa ba, Ruqayyah ta buɗe idonta da sukay jajur ta kalli matar, matar tayi mata murmushi tace "fasten your seat belt lady", Ruqayyah tace "thank you" da dasasshiyar muryarta, ta janyo belt ɗin ta ɗaura, Jirginsu ya sharara gudu akan runway kana ya ɗaga zuwa sararin samaniya. ★Da wani irin expression Anty Zulaiha ta kalli Mami jin abinda ta gama faɗa tace "innalillahi wa'inna ilayhirraji'un, yanzu yarinyar da Nurain zai aura ce ta gudu", Mami tayi ajiyar zuciya tace "wai neman me kike min ne tin ɗazu?", Anty Zulaiha tace "ai magana ma ta wuce, yanzu where is my Son", Mami tace "yana ɗakinsa, Allah yasa ma bai fita ba, he will be okay", Sakeena ta shigo tare da Noor, Noor ta kalli Mami tace "wai me yake damun yaya ne, kamar naga bashi da lfy lokacin da nazo kiranki?", Mami ta kalli Sakeena tace "ina abincin Abba da nace ki ajiye?", Sakeena tace "yana nan", Mami tace "toh ki kai masa yanzu", Sakeena tace "ai sun tafi wajen ɗaurin Aure", Mami tace "ai ba wani ɗaurin Aure da za ai an fasa" ta miƙe ta fita, Sakeena da Noor suka bi bayanta da kallo domin suna buƙatar concrete explanation ne akan maganarta, tana fita sai suka juya a tare suka kalli Anty Zulaiha da ta wayance da buɗe foil papern da aka rufe peppered chicken da ita, Na reception din Nurain ne wanda za a ƙara akan wanda akay order, Sakeena tace "Anty nifa bangane me Mami take nufi ba", Anty Zulaiha tace "Eh an fasa auren", Noor tace "but why?", Anty Zulaiha ta gaya musu komai. Sakeena taji zafi sosai, her only brother wanda take jinsa tamkar shaƙiƙinta, ita har mantawa take ba mahaifiyarsu ɗaya ba, indai Nurain zai kaiwa Ruqayyah wata kyauta kamar Ramadan basket da sallah gift ko kuma dai wani abin haka itace take shirya masa, ko jiya da ta ganshi da daddare a balcony yana waya da Ruqayyah saida ta tsokanesa, duk irin crush dinsa da ƴan mata suke amma ita ɗin dai yake so kuma bai haɗata da ko wace mace ba yana dating, shin her brother yayi deserving irin wnn yaudarar daga Ruqayyah. Biki dai ya mutu ƙurmus, ƴan biki da ɓaki kowa ya ɗaɗe gida ya koma sai ƴar cikinsa daga Anty Zulaiha sai Sakeena ne suka rage, Nurain all this while yana room ɗinsa bai sakko ba kuma Anty Zulaiha ta hana kowa yaje gunsa tace abarsa zuciyarsa ta huta, sai dare da misalin ƙarfe goma sannan Sakeena ta zuba abinci da drinks ta ɗora akan tray zata kai masa, Noor da Khausar ne kawai a main palour, Sakeena tazo zata wuce da abincin Noor tace "amm na yaya Nurain ne?", Sakeena tace "Eh", Noor ta miƙe tace "wait a minute" ta shiga kitchen, few minutes ta jona coffee maker ta haɗa wani yummy coffee ta tsiyaye a Mug, ta fito da Mug ɗin mai ɗauke da coffeen ta ɗora akan trayn hannun Sakeena tace "idan ma bai ci abincin ba I'm very sure zai sha coffeen ko yaya ne", Sakeena tabi stairs zuwa room ɗinsa, a hankali tayi knocking sai kuma ta kara bakinta jikin ƙofar tace "brother nice" ta murɗa handle ɗin ƙofar, half expected ta jita a ƙulle amma sai taji ta a buɗe, ɗakin dulum dunɗum duk an kashe light, ta wawaki bango ta danna switch ɗin fitilu, a take haske ya mamaye ɗakin, yana kwance akan gado yayi rigingine, farar T-shirt da brown trouser ne ajikinsa ya cire na ɗaurin Auren da basu gama daidaita ajikinsa ba, ga nan wayarsa a tarwatse ko sake bin takanta beyi ba, Sakeena ta kallesa kana ta ajiye trayn akan rest chair tace "brother ga abinci na kawo maka, plxx eat", ya ɗago ya kalleta yace "thank you", tace "ga coffee ma Noory ta haɗa maka", kalmar coffeen da ta ambata tasa yaji wata suya a zuciyarsa yace "sister off the lights", bata ce komai ba ta kashe fitilar sannan ta fita a ɗakin. Bayan kwanaki Biyu Momy da haj Safiyya da kuma Kulsum da Aysha suka zo gidansu Nurain, tamkar babu wani abu da ya faru Mami ta saukesu, bayan sun zazzauna ne saiga Garba nan ya fara shigo da akwatuna, Mami ta kalli akwatin na lefen Nurain ne, Momy ita dai duk kunya ta dameta, saida Garba ya gama shigo da akwatuna sannan Momy ta shigar da abinda ya kawosu, takanas suka zo bada haƙuri akan abinda ƴarsu tayi, Momy ta kalli akwatunan da suke tuli guda kuma shaƙure da kaya tace "ga kayan yaron nan, akwai waɗanda aka ɗinka Insha Allah suma za'a ciko su, dan Allah hajiya a bawa yaron nan haƙuri", Mami tayi murmushin yaƙe tace "ba komai ba sai an ciko ba, anga ita Ruqayyahn kuwa?", Momy tace "da kanta ta fita kuma dan kanta zata dawo, babu wani nemanta da zamu tsaya yi", Mami tace "Aa ai baza ai haka ba, hannunka baya taɓa ruɓewa ka gutsire ka yar, ya kamata a nemeta ai macace", Haj Safiyya ta ciro bunch of keys ta miƙawa Mami tace "mukullin gida ne da yake gurinmu, ai ba kaya ma muka zuba aciki ba ɗan albarkar yaron nan ya zuba komai a gidansa", Mami ta karɓi keys ɗin tana jin daɗi ɗanta ya samu shaida mai kyau, kuma ta godewa Allah da bashi bane ya kawo tangarɗa, basu wani jima ba suka yi sallama suka wuce. ★Da dare bayan Sallahr isha'i Hajar ta gyara fuskarta da oil control powder ta shafa colourless lipgloss a lips ɗinta, ta zauna a gefen gado tana jiran isowar Nura sbd yau ranar zuwansa ce, babu jimawa sai ga kiransa nan ya shigo wayarta ta ɗauka tace gata nan fitowa amma kuma tana zaune daram babu niyyar tashi, saida ta kwashi minti biyar sannan ta miƙe ta sake kallon kanta a mirror tana murza lips dinta ta saka hijab, darduma ta ɗauka guda biyu sannan ta fito tsakar gida, Umma da take bakin murhu ta kalla tace "Umma na fita soro", Umma tace "tom saikin dawo", Hajar ta nufi hanyar soro, tin kafin ta kai soron taji ƙamshin turarensa, ta isa da sallama ba tare da ta dubesa ba ta fara shimfiɗa dardumar, ya karɓi ɗayar yace "bari na taya ki" ya shimfiɗa ɗan nesa kaɗan da ta ta, ya zauna ya tanƙwashe ƙafarsa, itama ta zauna tana wasa da ƙasan hijab dinta suka gaisa, yace "kin taho da takardun naki kuwa?", tace "A'a zan shiga na ɗakko maka idan zaka wuce", ya ɗauki wayarsa da yake haska musu fitilarta, gallery ya shiga ya buɗo wani uncompleted building, ya haska mata screen ɗin wayar yace "kinga abinda ya wahalar miki dani", ta kalli hoton tace "har an zuba dakin?", yace "eh Allah ya bada iko" sai kuma yayi gaba ya buɗo wani hoton shi kuma na windows ne sliding da door irin na gida da ake ƙerasu da inganci, yace "kinga suma waɗan nan na gama da babinsu", ya sake buɗo wani hoton na kayan bathroom masu kyau har set biyu yace "kinga 2 bedroom toilets suma na gama dasu", Hajar sai murmushi take suna tsara yadda gidansu zai kasance tare da tanadi mai kyau na futuren su. da wata iriyar tafiya irinta mata ƴan duniya Sa'adatu ta shigo, har ta wucesu sai kuma ta dawo tana yamutsa fuska, Hajar da Nura ko ɗaga kansu su kalleta basuyi ba suka cigaba da kallonsu, Sa'adatu ta zuge handbag ɗinta ta ciro tsaleliyar wayarta da mabaruka ta siya mata, fitilar wayar mai haske ta kunna ta dallare su da ita tana jan dogon tsaki, Hajar ta ɗago kanta tana micincina ido sbd yadda hasken ya kashe mata ido, Sa'adatu ta hura kwai da chewing gum din bakinta sai kuma ta taunesa ya bada sautin ƙass, ta buga wani uban tsaki tace "ke ashe naki iskancin haka yake, wato ke ƴar iska shine kike kawo mana ƙattin banza har cikin gida ko?", Hajar ta ɗauke kanta sbd bata so ta tanka mata a wnn lokacin, Sa'adatu kuma already tayi noticing dinta dan haka ta sake ɗaura ɗammarar ci mata fuska a gaban Nura, ta sake dallare fuskokinsu tace "dalla malam tashi ka fitar mana daga gida, ka bari ta biyoka shago mana, amma bazaku yi mana sheɗanci a soron gida ba", Hajar was burning inside kuma she can't take it anymore, ta miƙe tamkar wacca aka tsikarawa allura tana huci..........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {13...} Sa'adatu ta dallare Hajar da ta miƙe da fitilar wayarta, Hajar tayi mata wani irin kallo sai kuma ta wuce cikin gida ta shiga ɗaki, umma tana ganin yanayinta saita bita ɗakin, wardrobe ta buɗe inda take ajiye muhimman takardunta tana dube-dube, umma ta kalleta tace "lafiyarki kuwa hajara?, Nuran ya tafi ne?", Hajar ta cigaba da ɗaɗɗaga takardu hawaye ya cika mata ido tace "umma wnn wane irin masifa da bala'i ne?, Maama da ƴaƴanta wllh annobane, ni kam nagaji da haƙuri dasu, na rantse da girman Allah daga yau duk wacca ta sake shiga harkata saina raunata ta, anƙi ayi haƙurin dasu, idan zaman lfy toh za'a zauna lfy ɗin, idan kuma zaman tashin hankali toh za'a tashi hankalin fiye da kima.....", umma ta katseta tace "toh maza ki ɗauki harama tinda ke kika haifi kanki, yanzu me ya faru?, naga dai zaune kike a soro da Nura", Hajar ta ɗauki envelop ɗin credentials ɗinta ta zauna a gefen gado ta share hawayen da ya zubo mata tace "Sa'adatu ce", umma tace "me Sa'adatun tayi?", Hajar ta gaya mata abinda tayi musu a soro, Umma tace "shknn, dafatan dai biki tanka mata ba?", Hajar ta girgiza kai tace "bance mata komai ba kawai tasowa nayi na dawo gida, wllh nasan idan na zauna za'a iya haifar ɗa mara ido", umma ta zabga mata harara tace "wato har wani cewa kike za'a haifi ɗa mara ido ko?, Hajara ki ringa sanyaya zuciyarki, ki dena ɗaukar komai da zafi, yanzu waɗan nan takardun su kuma me sukay miki da kika birkito su?", Hajar tace "shine yace na kai masa", Umma tace "A'a naga ai kin basa takardun naki kwanaki?", Hajar tace "Eh, ai na secondary na basa, yanzu kuma primary certificate da testimonial zan basa", umma tace "toh, tashi ki kai masa saiki dawo gida gobe kwa ƙarasa". Hajar ta miƙe ta fita da envelope a hannunta, kasa kallonsa tayi tace "ga takardun", ya miƙe ya amsa sai kuma ya nannaɗe dardumar da ya tashi daga kai ya naɗe ta Hajar ɗinma, ita dai kawai wasa take da fingers ɗinta tace "dama ka barshi zanyi ai", yace "na hutar dake", ya miƙa mata darduman tare da wayarta da ta ajiye a wajen yace "toh seda safe", ta karɓa kanta a ƙasa tace "seda safe", ya tsaya yana kallonta yace "toh shiga gida", ta juya a hankali ta shiga gida shi kuma yayi tafiyarsa, Hajar ta tsaya daga bakin rariya ta kunna wayarta tana murmushin mugunta tace "idan kinci bulus shegiya nake", ta shiga contact ta lalubo numbern Naseer tayi dialing, bata daɗe da fara ringing ba ya ɗaga, ta sauke ajiyar zuciya tace "Yaya ina wuni", daga ɗayan ɓangaren Naseer yace "lafiya lou Hajar", tace "yaya daman Sa'adatu ce tazo, gata can sai rashin kunya takewa Maama sbd tace karta sake barin gida..", Naseer ya katse kiran ba tare da ya ce komai ba, Hajar ta kalli screen ɗin wayar tayi murmushi, tasan yanzu haka gida zai taho, daman tasan yana neman Sa'adatu tinda duk zuwan da yake takan ji yana tambayar Nabila ko Maama ina take wani sa'in. ta wuce tsakar gida ta tsaya tana kallon ɗakin Maama da ake jiyo muryoyinsu daga ciki suna hira da shewa, muryar Sa'adatu tafi ta kowa tashi, Hajar ta yamutsa fuska tace "zaki ɗanɗana ne jaka" tayi wucewarta ɗaki. Nabilah ta juya tsaleliyar wayar hannunta tace "yanzu Sa'adatu wnn wayar ta mazajen kuɗi itace a hannunki", Sa'adatu tace "rass ma kuwa ya son ranki, masoyiya Mabruk ce ta siya min", Maama ta karɓi wayar daga hannun Nabilah tace "gaskiya yaran nan suna sonki da arziƙi, nawa ma kika ce kuɗin ta?", Sa'adatu tayi kwai da chewing gum ɗin bakinta tace "dubu ɗari biyar", Maama tace "caɓɗijam", Maimuna da take kan gado ta sakko tace "yawwa Sa'adatu kince zaki faɗamin sunan man da kika koma shafawa wanda yasa kika koma fara gaba ɗayanki", Sa'adatu ta harareta tace "wane irin mai, yarinya wasa ma kike, ni na dena shafa mai sbd ɓata lokaci ne, allura ake min", Maimuna tace "Allura..??", Sa'adatu tace "rass, har fatar kaina da mazaunai na sun koma farare yanzu", Maimuna tace "chab gaskiya bazan iya allura ba", Sa'adatu tace "yo shknn kiyi ta shafa mai yana miki glass a fuska, yanzu ma kalli fuskarki kamar an watsa fitsari duk tayi wani jirwaye, ga wani map of Africa a kumatunki", Maimuna tace "naji, a haka Alhaj ɗina yake so", Sa'adatu ta warce wayarta da take hannun Maama ta duba lokaci, ta ɗauki handbag ɗinta ta ciro maƙudan kuɗi ta lalo dubu ashirin ta miƙawa Maama tace "toh da haka da haka baƙo zaiyi halinsa", Maama ta soke kuɗin a kirjinta tace "Au ƴar nan tafiya zaki yi baza ki kwana ba", Sa'adatu ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta sai kace wacca ta zauna a sahara tace "la la la bazan kwana ba wllh, kuɗin cizo da sauro suyi min illah", Nabilah tace "Sa'adatu naga kin mayar da kuɗin jaka, ni kuma fa ba ki ɗusheni ba", Sa'adatu ta yamutsa fuska tace "ai kece kinƙi ki waye, yanzu Maimu ba gashi nan ba kullum da ƴan canjinta a ƙugu, miƙomin jakar", Nabilah gaba take da Sa'adatu amma haka ta ɗauki jaka ta miƙa mata da hannu biyu, dubu biyar Sa'adatu ta lalo ta mannawa Nabilah a ƙirji tace "gashi dai mai kai a tukunya", Nabilah ta dafe kuɗin ta linkesu ta cusa a bra. Sa'adatu tace "toh na tafi Maama", Maama tace "karki daɗe baki zo ba kinji", Sa'adatu tace "toh zan duba na gani" ta fito tsakar gida ta saka takalmi ta fita. A soro sukay kaciɓus da Naseer wanda ya shigo a fusace, zuciyarta ta buga da ƙarfi ta juya zata koma ciki, wani gigitaccen marii ya sauke mata a fuska, tayi taga-taga tamkar zata waɗi ta bugu da bango, tsaleliyar wayarta saura ƙiris ta faɗi daga hannunta, tana dawowa hayyacinta ta ruga cikin gida ya biyota da sauri, takalmin da yake ƙafarta mai tsini ya gurɗeta aikam tayi mummunar faduwa a ƙasa daɓas, wayar hannunta kamar wacca aka fuzge haka tayi tsalle ta daki bango, Sa'adatu ta ɗora hannu a ka ta kurma ihu tace "wayyo wayata", Baba ya fito daga ɗakinsa da sauri yace "Nasiru zane min ita, zaneta nace", Maama ta fito jin abinda yake faruwa tana hura hanci tace "wllh karka kuskura ka taɓa ta", Baba zuciyarsa na masa zafi yace "Rabi idan kika sake magana anan wajen na rantse da girman Allah saina tsinke jemammiyar igiyar aurenki guda ɗaya da ta rage", Maama ta dafe ƙirji ta zaro ido amma ta kasa cewa komai, Saki kuma da girmanta da gemunta ace za'a saketa, dama igiyoyin auren saura ɗaya ce ta rage, Baba yace "Nasiru ka zane min ita", Sa'adatu ta wawaki ƙasa zata miƙe ta afka ɗakin Maama amma ina tini Naseer ya fuzgota. wani mabirki mai kauri na icce wanda ake kaɗa miyar yauƙi dashi ya ɗauka, Naseer ya ringa rankwala mata shi a jiki, saida ya kakkafe mata tsoka tass, ƴan yatsenta kam kamar zasu zube sbd yafi rankwala mata anan, Maama dai kawai kumbura take tana sacewa ita kaɗai, saida Sa'adatu ta faɗawa ƴan garinsu sannan Baba yace "ya isa haka, kullemin ita a can" yayi nuni da kitchen wanda basa amfani dashi sai tara shirgi, gaba ɗaya kitchen ɗin ya mutu, Naseer ya figi Sa'adatu ya dannata aciki ya banko mushiyar ƙofar langa-langar, Baba ya numfasa yace "ka gaji ko kuma da sauran ƙarfinka?", Naseer baice komai ba, Baba ya ɗaga murya da kanaji kasan a ɓace ransa yake yace "Maimuna!!, Maimuna!!", wani irin juyawa ƴan hanjin Maimuna da take laɓe jikin labule sukay, daga ita har Nabila sai suka fara neman gurin ɓuya, Baba yace "Shiga ka zanemin ita itama", wayyo daman Naseer duk kansu yanada cikinsu, ai Maimuna a ɗaki akay mata nata walmukalafatun, itama tasha mabirki daidai gwargwado, Baba yace itama a haɗata da Sa'adatu a rufe, Nabilah ma ta amshi rabonta saidai bai kai nasu ba, ita akai aka rarrankwala mata mabirkin sannan ta amshi maruka biyu zafafa, zuciyar Maama ta soyu iya soyuwa, tanaji tana gani aka zane mata ƴaƴa, Baba ya bawa Naseer padlock yace ya kulle kitchen ɗin anan zasu kwana. Hajar da take jikin window tana hangen duk abinda yake wakana tayi murmushi zuciyarta fess, ai ita dukan da akay wa Sa'adatu da kuma yadda wayarta ta daki bango shi yafi mata daɗi, wayar da aka wulaƙanta ta da ita a soro gashi nan ta fashe. washe gari da safe Hajar ta fito tsakar gida da kayanta da zata wanke, ta deɓi ruwa a bucket ta zazzaga omo ta sunkuya ta fara wankinta tana humming song, a fakaici ta kalli ƙofar langa-langar kitchen da take a garƙame da kwaɗo, har yanzu Sa'adatu da Maimuna suna ciki sunyi bugun sunyi kukan har sun gaji, muryar Maimuna taji tana kuka tana cewa "dan girman Allah Baba kayi haƙuri wllh bazan sake ba, wayyo Maamana, na shiga uku na lalace, wllh kunama ta harbeni dan Allah a buɗe mu, Sa'adatu ta yanke da ƙarfen langa-langa", Hajar ta kyalkyale da dariya tana wankinta, Maama ta fito daga ɗakinta zuciyarta busu-busu ta shiga ɗakin Baba, Baba ya gama shiryawa tass zai fita aiki, Maama tace "mal fita za kay?, yaran nan fa har yanzu ba a buɗesu ba", Baba ya gyara wuyan rigarsa yace "sai aka yi yaya da ba a buɗesu ba?", tace "daman naga ko sallar asuba basu yi ba gashi rana ta fito", yace "Au daman kina damuwa idan basuyi sallah ba?", ta fara ƙinƙina tace "dan girman Allah mal kayi haƙuri, a yi musu afuwa", Baba ya gyaɗa kai yace "za a yi musu, amma in tambayeki mana?", tace "toh mal", yace "waye uban Sa'adatu da Maimuna?", ta saki baki sai kuma tace "kaine mana mal", yace "ni mijinki ne ko A'a?", tace "kai mijina ne mana", yace "idan kina so igiyar aurenki ta cigaba da rayuwa to ki gyara tarbiyyar ƴaƴanki, idan kina son ƴaƴanki to ki gyara tarbiyyarsu, kar Sa'adatu ta sake barin gidan nan, Maimuna karta sake fita da daddare, Nabilah ta fito da miji na aurar da ita", Maama ta gyaɗa kai tamkar tsohuwar ƙadangaruwa tace "tom", ya ciro muƙulli daga aljihunsa ya bata yace "ki buɗesu idan na dawo ina son ganinsu", Maama ta karɓi muƙullin tana harararsa ƙasa-ƙasa tace "toh" ta fita a ɗakin, ruɓaɓɓen kichen ɗin ta buɗe Sa'adatu da Maimuna suka fito wujiga-wujiga, zafi ya dakasa ga kuma jikinsu da yayi tsami. ★Nurain ya fita masallaci sallar la'asar, bayan ya dawo ya tsaya suna gaisawa da Garba da yake bawa flowers ruwa, Nurain yace "wace motar ka wanke min?", Garba yace "farar na wanke maka", Nurain yace "Ohk, ka amso min takalmana daga wajen polish", Garba ya dukar da kai yace "toh alhaji ƙarami", Nurain ya wuce ciki, har zai zauna a balcony sai ya fasa dai ya shiga main palour ya zauna a kujera, remote ya ɗauka ya canza channel, bayan few minutes ya miƙe ya shiga kitchen ya buɗe fridge ya ɗauki Apple guda uku ya ɗora akan plate ya dawo palour ya zauna yana ci, Noor ta shigo palourn tace "Yaya Mami is calling", yace "Ohk", ya miƙe ya ɗauki plate ɗin Apple ɗinsa ya shiga part ɗin Mami, Mami ta ringa kallonsa har ya zauna a kujerar kusa da ita, ya ɗan rame kaɗan amma kuma fuskarsa babu wata damuwa, Mami tace "where is your phone?", ya shafa kansa yace "Ta fashe ne", tace "Ohk, toh dan ta fashe shine ba za ai amfani da ita ba, saika zauna haka ba waya", yace "zan siyo wata ne", tace "good do that fast", yace "yeah" tace "when are you resuming work?", yace "next week, daman na ɗauki leave na two weeks", ta gyaɗa kai tace "Son, why not go towards Khausar", yace "Khausar?", tace "yess Khausar"..........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {14...} Nurain ya ajiye Apple ɗin hannunsa yace "Mami i don't get you", Mami ta ɗauki remote ta danna mute tace "Nurain, ga Khausar nan ƴar uwarka, me zai hana ka nemi aurenta, kasan yarinyar nan kuma kasan iyayenta, duk wani qualities da ake so a wajen mace Khausar na dashi, asali, ilimi, home training and what majority of men are after to, beauty right?, she's beautiful..", ya sauke ajiyar zuciya yace "but Mami I don't have such feeling for her, i only see her as my lil sister", tace "Alright, tinda kace haka shknn, you may leave", ta ɗauki remote ta canza channel snn ta buɗe volume, Nurain dai bai sake cewa komai ba yana nan zaune ya cigaba da cin Apple ɗinsa, bayan 20minutes ya miƙe yana jan shirt ɗinsa ya nufi door, har ya murɗa handle Mami ta kira sunansa, ya juyo yace "Na'am", ta nuna masa plate ɗin da ya shigo dashi, ga apple nan guda daya da bai cinyeba akai, ya shafa kansa ya dawo ya ɗauki plate ɗin ya fita, Mami ta bisa da kallon gefen ido. room ɗinsa ya wuce yayi abinda zai yi snn ya sakko down stairs hannunsa riƙe da car key, compound ya fita ya wuce parking space, farar motarsa ya buɗe ya shiga, saida yayi warming snn ya gangara ya fita daga compound ɗin bayan mai gadi ya buɗe masa gate, a daidai wani katafaren wajen siyar da waya yayi parking, ya kashe motar ya buɗe door ya fita, ya shiga building din da akay molding ɗinsa da kirar waya, few minutes ya fito hannunsa riƙe da ƴar leda, yana komawa gida aka kira sallar magrib, yayi using tap din compound yayi alwala ya wuce mosque, bayan ya dawo daga masallaci ya bude car ya ɗauki ledar ya wuce ciki, direct a room ɗinsa yayi branching, ya ɗauki wayarsa da ta tashi daga aiki akan mirror, sim cards dinsa ya cire snn ya farke sabuwar wayar da ya siyo, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon wayar tana booting bayan ya danne switch dinta, bai ɗaukesa wani lokaci ba ya gama setting wayar, kira ne ya shigo wayar, Nurain yayi murmushi ganin me kiran nasa video call ya ɗauka, Farooq ne cousin dinsa da yake Russia, Nurain yace "why the call dude?", daga ɗayen ɓangaren Farooq da ya sha wata jibgegiyar sweater yace "I can't reach you since last week, what was the problem?", Nurain ya jingina da allon gado yace "look, wnn wintern ta garin ku ai bazata bari kayi reaching mutane ba", Farooq ya ɗaga gira yace "decline, look for another way", Nurain yace "Ohk", Farooq yace "ya Mutan 9ja?, ya su Mami?", Nurain yace "All lafiya", Farooq yace "looks like you lost some weight Dr, ko dai Ruqayyah bata iya girki ba, i forgot to asked about her, how is she?", Nurain yace "she is great", Farooq yace "good", Nurain yace "when are you coming?", Farooq yace "nanda 2weeks insha Allah, kuma a gidanka zan fara sauka naci girkin Amarya Ruqayyah", calmly Nurain yace "Ruqayyah is not my wife and she will never be, i don't think ma zaka tarar dani a Nigeria", yadda yayi maganar without joke yasa Farooq fahimtar something has happened, Farooq yace "bro what...", Nurain ya katsesa yace "don't ask me, zan gaya maka later, after my heart healed", Farooq yace "Ohk, amma ina zaka da kace bazan sameka a Nigeria ba?", Nurain yace "India", Farooq yace "Ohk, ynxu ka yarda zaka koma ka ƙaro karatun kenen", Nurain yace "yeah", Farooq yace "Ohk, i understand, i gotta go, good night", Nurain yace "Ohk, good night" ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya. ★Da daddare Baba yana zaune a ɗakinsa Maama tayi sallama ta shigo, tana daga bakin ƙofa tace "mal kace kana son ganin yaran nan?, toh su shigo yanzu ko sai anjima?", Baba yace "ki kirasu yanzu nan, kema kizo", Maama tace "tom" ta juya ta fita, ɗakinta ta shiga tana kallon ƴaƴan nata tace "kuzo inji Babanku", Maimuna ta tashi daga kan kayan wanki tace "na shiga uku na, Maama dan girman Allah kice nayi bacci, wllh har yanzu harbin kunamar nan bai bar jikina ba", Maama tace "A'a dole ki taso, ko baccin ma ki kai tashinki zanyi", ta kalli Sa'adatu da Nabilah tace "kunji dai me nace ko?, ku taso", Sa'adatu ta miƙe tana gunguni ta fita tsakar gida, Maama tabi bayanta, ɗakin Baba suka shiga suka zauna, suna zama Nabilah ma ta shigo, Maimuna ce ta shigo a ƙarshe, tana ƙoƙarin zama Baba yace "karki zauna Shiga wajen Umma ki kiramin ita da kuma Hajara", Maimuna ta kalli Maama, Maama ta ɗauke kanta, haka Maimuna ta fita ta tsaya a ƙofar ɗakin Umma tace "Baba yace kizo keda Hajara", bata jira cewarsu ba ta koma ɗakin Baba ta zauna kusa da Nabilah tace "na kirasu", Maama ta haɗe rai tace "mal naji kace a kira waccar matar da ƴarta, to mene dalili?, mene haɗinsu da zamanka da ƴaƴanka?", Baba yace "Toh haka dai nace a kirasu", Maama bata sake cewa komai ba, Umma ce tayi sallama ta shigo Hajar biye da ita, suka haɗa ido da Maama wacca take harararta ƙasa-ƙasa, Umma ta zauna tace "mal gani", Hajar ta zauna kusa da Umma, Baba ya ƙare musu kallo duka yace "Nabilah!!", Nabilah tace "Na'am", Baba yace "acikin samarinki ki fitar da wanda yayi miki kice masa ya fito, aurar dake zanyi, idan kuma baki da wanda kike so toh zaɓi yana wajena, na baki nanda sati biyu..", Nabilah ta marairaice fuska tace "Baba aure fa..", ya katseta yace "Ba cewa nayi kiyi magana ba, tashi ki ban waje", Nabilah ta miƙe ta fita zuciyarta na zafi, Baba ya juya kan Sa'adatu yace "Sa'adatu!!, Sa'adatu!!, Sa'adatu!!", Sa'adatu ta haɗe gira tace "Na'am", Baba yace "sau nawa na kiraki?", tace "Uku", ya gyaɗa kai yace "gargaɗi na ƙarshe kenan da zan miki, zunubin ki mai kauri ne, wllh wllh wllh tsattsauran mataki zan ɗauka akanki, tashi ki bani waje", Sa'adatu ta miƙe ta fita zuciyarta na tafarfasa, Baba yana gamawa da Sa'adatu ya juya kan Maimuna yace "ke kuma duk abinda Sa'adatu tayi shi kike yi ko?, kin ƙi makaranta kin zaɓi yawon dare ko?, toh ranar Litinin Mu'azzam zai mayar dake makaranta, ɓacemin daga gani", Maimuna ta miƙe ta fita ranta na soyewa, wai makaranta za'a mayar da ita. Baba ya dubi Hajar da take zaune kusa da Umma yace "saura ke Hajara, uwar rashin haƙuri, Nabilah, Sa'adatu duk yayyenki ne, Maimuna ce sakuwarki kuma itama ɗin gaba take dake, karki sake yi musu rashin kunya", Hajar tace "toh Baba", yace "toh tashi ki tafi, Allah yayi miki albarka". Maama ta hura tukubar hancinta tace "suma Allah yayi musu Albarka su da ba ƴaƴan so ba", ɗakin ya rage daga Baba sai Maama sai kuma Umma, Baba yace "Rabii", Maama ta miƙe tace "Allah ya tashemu lfy, ba sai kace komai ba mal, ai naji abinda kace da safe" ta fice a ɗakin tamkar zata tashi sama. Rayuwar gidan ce ta canza zuwa wani fannin daban, babu ruwan kowa da kowa, yau sati guda kenan ba ai hargitsi ba, sosai Maama tayi ladaf ta hana ƴaƴanta fita, daman suma sun tsorata da Baba shiyasa ko ƙoƙarin fitar ma basuyi ba. Sa'adatu ta leƙa kwanon ɗumamen tuwon da Maimuna ta shigo musu dashi matsayin breakfast tace "chab wllh bazan ci tuwo ba", Maimuna tace "ga koko nan", Sa'adatu ta zabga tsaki ta ɗauki jakarta ta ciro kuɗi ta saka hijab ta fita tsakar gida, Maama da take riƙe da kofin koko tace "ina zaki Sa'adatu", Sa'adatu tace "ba nisa zanyi ba, wajen mai shayi zanje na siyo biredi da shayi, ni bazan ci tuwo ba", Maama ta zaro ido tace "kin san dai Babanku ya hanaki fita ko?", Sa'adatu tace "ai ba ko wace fitar yake nufi ba, nifa nan nan wajen mai shayi zani ba wata uwa duniyar ba", Maama ta girgiza kai tace "A'a, kawo kuɗin na leƙa waje idan na samu yaro sai ya siyo miki", Sa'adatu ta miƙawa Maama duba ɗayar data rage mata, Maama ta bata kofin hannunta tace "shigarmin dashi ciki, bari na aika yaron", Sa'adatu ta amshi kofin ta koma ɗaki, Maama tayi hanyar soro kamar da gaske, tana zuwa soro ta laɓe a bayan ƙofa ta ɗaure kuɗin a haɓar zaninta ta koma ciki, Sa'adatu tace "Maama har an samu yaron", Maama tace "Eh yanzu zai kawo miki, ɗan gidan Munkaila ne", Sa'adatu tace "yawwa, ga kokon ki". Maama ta zauna tana kurɓar kokonta tana kallon Maimuna da Nabilah da suke kwarfa lomar tuwo. Shiru-shiru yaro zai kawo Shayi da biredi amma maƙatau ba labari, yunwa sai kartar ƴar hanjin Sa'adatu take, Sa'adatu ta leƙa soro a karo na bakwai ta dawo ciki tana gunguni ta kalli Maama dake bakin murhu tace "har yanzu fa yaron bai kawo ba, yunwa nake ji", Maama ta tura mata kwanon tuwon data rage tace "ki rage hanya da wnn kafin ya dawo", Sa'adatu tace "tuwon ne fa bazan ci ba", Maama ta gyaɗa kai tace "yo ba yunwar kike ji ba, shknn saiki jira shayin". ƙarfe sha biyu da rabi Sa'adatu ta fito ta wafci kwanon tuwon da Maama ta bata ɗazu tace bazata ci ba, loma huɗu tayi masa ta tashi dashi, ta ringa suɗe hannu tana muzurai don ko tsarga mata beyi ba. ★Momy ta Shiga palourn Daddy hannunta riƙe da tray, sallama tayi, Daddy dake zaune kan kujera shallow in thoughts ya amsa mata, ta ajiye trayn akan center table kana ta shiga making tea, thick tea ta haɗa cikin Mug ta dire a gaban Daddy, ta buɗe warmer da ta shigo da ita mai ɗauke da chips, plate ta ɗauka ta zuba chips ɗin with omelette egg a gefe, ta matsa ketchup a wani ƙaramin bowl, ta jera in front of Daddy kana ta koma kusa dashi ta zauna, a hankali ya fara cakar chips din da fork yana dangwalar ketchup yana ci, kaɗan yaci ya ajiye fork ya ɗauki tean ya fara sipping, keenly yace "have you eaten?", tace "I'm not hungry", yace "Tom", calmly tace "Alhaji yarinyar nanfa bamu san inda take ba har yanzu, yaufa kwana sha biyu babu ita babu dalilinta..", yace "so", tace "do something", yace "something like what?", Momy was speechless kawai kallonsa take, ya ajiye Mug din hannunsa yace "lokacin da Ruqayyah ta saka ƙafa ta fita na sani ne?, ajikin lettern da ta ajiye ma tace kar mu nemeta zata dawo, to kinga kuwa me zai sa na ɓata golden time ɗina wajen nemanta..", Momy tayi ajiyar zuciya tace "har yanzu fa ba a samun wayarta, ai dole hankalina ya tashi", yace "toh maza ki ɗauki haramar saka damuwa a ranki, wai yarinya nan ba da kanta ta fita ba, dan ba a sameta a waya ba ai ba wata matsalar bace, tana sane ta kashe wayar, what Ruqayyah did really hurts me, idan tanada wata damuwar why not ta sameki ta gaya miki, and she can talk to me if there was any problem, am i not a free Father?, plxx don't ruin my mood this morning akan maganar Ruqayyah", da haka Daddy ya miƙe ya shiga bedroom ɗinsa, Momy tabi bayansa da kallo sai kuma ta tashi ta fita a palourn, bedroom ɗinta ta shiga ta ɗauki wayarta tayi dialing numbern Kulsoom, saida ta kusan yankewa snn tayi picking, Momy tace "saiki ringa nesa da wayarki", Kulsoom tace "Momy ina kitchen ne", Momy tace "toh kina jina Daddy yaƙi saurarata, anjima da yamma sai muje police station mu shigar da report", Kulsoom tace "toh Momy, har yanzu babu wanda ta kira", Momy tace "Eh", Kulsoom tace "toh ina gama abinda nake zan shirya na taho", Momy tace "toh shknn saikin zo" ta datse kiran. ★Hajar ce zaune a ɗakin Umma tare da Zainab, Zainab tace "kefa ƴar rainin hankali ce wllh, yanzu saida kika tattagoni, ƙiri ƙiri kin ƙi hawa online", Hajar tace "kuma inada data isasshiya wllh, duk sati ya sayyadina sai ya sakomin credit da data", Zainab ta taɓe baki tace "toh ai kin kyauta da kike masa asara, idan baki yi amfani da ita ba ai tayi expire a wofi", Hajar tace "ya mutan gida?", Zainab tace "lfy wllh, kin san kwa me ya kawoni", Hajar tace "inafa zan sani, ai sai kin shaƙamin", Zainab tayi ƙasa da murya tace "kin tuna wnn katafaren gidan da kika rakani?", Hajar tace "katafaren gida?", Zainab tace "Eh mna, wanda muka je har kika yiwa wani mai mota rashin kunya..", Hajar tace "Au, wnn mutumin da bai san darajar ɗan Adam ba, kinsan kwa na sake ganinsa?", Zainab tace "A ina?", Hajar tace "A hospital, likitane", Zainab tace "okay, yanzu dai kina jina?, ɗan gidan ne yace na bashi digits ɗinki, wllh ya takuramin, ni kuma naƙi bashi nace saina sanar dake..", Hajar tace "yawwa gwara da baki basa ba..", Zainab tace "sbd me?", Hajar tace "toh meya haɗana dashi da zaki bashi digits ɗina?", Zainab ta harareta tace "malama karki raina min hankali, kinfa gane me nake nufi", Hajar ta langwaɓar da kai calmly tace "So, kinsan dai akwai wanda muke tare dashi, kuma har yazo gida", Zainab tace "yess nasani, toh ai ba baiko akai muku ba", Hajar ta juyar da kanta tace "kya yi kuma". can dai Zainab ta miƙe tace "toh zan tafi", suka fito tare da Hajar zata rakata ƙofar gida, Zainab ta yiwa Umma sallama suka wuce hanyar soro tare da Hajar, Sa'adatu ta fito daga bayi ta tsaya tana kallon Hajar da Zainab da suka nufo hanyar fita, Sa'adatu ta dire butar hannunta, daman yau ranta a ɓace yake neman wanda zata huce akansa take, Zainab ta marairaice tace "dan Allah Hajar ki sauraresa, zan bashi numbern..", Hajar tace "zanyi tunani.", Hajar ko kallon inda Sa'adatu take ba tay ba, Zainab tana zuwa wucewa Sa'adatu ta saka mata ƙafa. Zainab ta faɗi a ƙasa, Sa'adatu ta nuna Hajar da yatsa tace "kema baki isa ki kawo ƙawayenki gidan nan ba su fita lfy", Hajar da zuciyarta take tafarfasa ta durƙusa ta kamo Zainab ta taimaka mata ta miƙe tsaye, Hajar ta tsugunna kamar zata ɗakko jakar zainab dake ƙasa, ta saka iya ƙarfinta ta kwashi ƙafafuwan Sa'adatu ta nakata da ƙasa, a lokacin Baba yayi sallama ya shigo gidan, ya tsaya yana kallon Hajar.......✍️ 💛 HAJAR 💛 by ~Feenerh_feeche~ {15....} Wani ihu Sa'adatu ta kurma tace "Hajar kashe ni za kiyi?, nifa ƴar uwarki ce", Hajar ta kasa cewa komai sbd kallon da Baba yake mata, Sa'adatu ta miƙe tana dafe bayanta tace "wllh ta karya min ƙashin baya", Baba baice komai ba ya wuce cikin gida, Umma ce tayo hanyar soro sbd ihun da ta jiyo, kaciɓus sukay da Baba tace "sannu da zuwa Malam", Baba yace "yawwa", ya wuce ƙofar ɗakinsa, ya ciro keys a aljihunsa, ya buɗe padlock ɗin ya shiga, Sa'adatu ta cafki wuyar Hajar tana ƙunduma mata ashar, Hajar tace "wllh badai nawa ba, dalla malama sakeni niba jaka bace da zan haɗa ƙashi dake", Sa'adatu tace "keee anƙi a sake kin, kiyi abinda za kiyi", zainab dai sai raba idanu take tana cewa Hajar kyaleta dan Allah, Umma tana zuwa ta tarar da Sa'adatu ta cakumi Hajar, ta fara ƙoƙarin ɓanɓare hannun Sa'adatu dake wuyan Hajar tace "me ya haɗaku?", Sa'adatu ta cakumo Umma sannan ta danna ihu da ƙarfi tace "Maama ku fito, gasu nan sunyi min rubdugu zasu hallakani", Nabilah ce ta fito tana wuwwurga idanu sai kuma ta riƙe baki tace "Maama fito ki gani", Maama tana fitowa ta ɗauki takalmin roba ta rufe Umma da duka, Nabilah da Maimuna kuma suka taru akan Hajar, Sa'adatu kam har lokacin tana riƙe da Umma gam, Hajar ta kufce daga riƙon da Maimuna tayi mata ta gallarawa Sa'adatu cizo a hannun, Sa'adatu ta saki Umma tana lailayo ashar, Zainab dai jikinta sai rawa yake tana kallon ikon Allah, Sabra ta shigo da ɗan gudunta jikinta sanye da Kayan islamiyya, gefe ta koma ta rushe da kuka, hayaniyar da taƙi tsayawa ce tasa Baba ya fito, tsaye yayi yana kallonsu zuciyarsa na tafarfasa, Maimuna da Nabilah suna ganinsa suka saki Hajar suna huci, Baba ya rungume hannu yana kallon yadda Maama ke laftawa Umma takalmi, Maama tana ankara da Baba ta wurgar da takalmin tace "mal baka ga yadda muka fito muka tarar da faɗima da ƴarta sun rufarwa Sa'adatu ba", Umma ta juya ta tsinkawa Hajar marii, Hajar ta riƙe kuncinta ta fashe da kuka, Umma ta daka mata tsawa tace "wuce ɗaki", da sauri Hajar ta shiga ɗaki tana shessheƙa, Sabra tabi bayanta itama tana kukan, Zainab dai ta ɗauki jakarta ta fita daga gidan. Umma ta shiga ɗakinta zuciyarta na tafarfasa, har lokacin Hajar bata dena kuka ba, Umma bata ce mata uffan ba sai haushinta da take ji. kiran sallar magrib akai Hajar ta miƙe da lulu eyes ɗinta da sukay jajur, ta fita tsakar gida tayi alwala ta dawo tayi sallah, bayan ta idar da sallar ta jingina da jikin wardrobe, Umma na zaune kan darduna bayan ta idar da sallah, Mu'azzam yayi sallama ya shigo, ya durƙusa a gaban Umma yace "Umma ina yini", tace "lafiya, an taso lafiya", yace "eh lafiya alhmdllh", tace "toh Allah ya temaka", yace "Ameen", Hajar da dasasshiyar muryarta tace "yaya sannu da dawowa", ya ringa kallonta snn yace "yawwa", ya ciro biscuits daga pocket ɗinsa ya bawa Sabra da take homework, Umma ta kallesa tace "idan ka fita Sallahr isha'i ka tahomin da Ghana most go", yace "tohm, wane size?", tace "medium", yace "tom" ya tashi ya fita. ƙarfe takwas da rabi Mu'azzam ya dawo da Ghana most go a hannunsa, ya miƙawa Umma yace "wnn tayi?", ta karɓa tace "Eh, ga abincinka", ya ɗauki medium warmern abincinsa ya fita, Umma ta ɗauki Ghana most go ɗin ta wurgawa Hajar tace "haɗa kayanki", Hajar ta ringa kallonta bata dai ɗauka ba, a hasale Umma tace "ba kiji me nace miki ba?", Hajar ta janyo Ghana most gon tace "Umma kayan me zan haɗa?", Umma tace "kayan sawarki zaki haɗa", a sanyaye Hajar tace "tom", ta tashi ta buɗe wardrobe side ɗin da kayanta yake, ta ringa ciro kayan tana ɗorawa akan gado, sai kuma ta dawo ta zuba su a Ghana most go, tana gama zubawa ta zuge zip ɗin, Umma ta taso ta kalli wardrobe din tace "waɗan nan kuma fa?", Hajar ta kwaso su ta zuge zip ta zuba, Umma duk tana kallonta, Sabra tace "Umma ina Adda zata?", Umma tace "ba kin gama homewark ɗinki ba, maza hau gado ki kwanta, karna sake jin bakinki", Sabra ta haye gado bata sake magana ba. Hajar dai tayi ta sa ran kiran Baba amma har bacci ɓarawo ya ɗauketa bai kirata ba. ƙarfe bakwai na safe Hajar ta fita tsakar gida tayi brush, tana so ta shiga ta gaishe da Baba amma kuma shakkar hakan take, ɗaki ta koma taga Umma tana shafawa Sabra Vaseline, tana gama shafa mata ta saka uniform ɗinta, Umma tace "ki shiga ki gaishe da Baba kafin ki tafi makarantar", Sabra ta goya jakarta tace "tom" ta fita, sai kuma gata ta dawo tace "Baban bacci yake", Umma dai tayi mamaki sbd da wuya ne kaga Baba yana baccin safe, Umma tace "toh maza ki tafi karki makara". Sabra tayi tafiyarta makaranta, Hajar tace "Umma ina wake yake zan tsince", Umma tace "A'a ba tsintar wake za kiyi ba, zoki shirya fita za muyi", Hajar dai zuciyarta bata yarda da fitar nan ba, haka ta shirya a sanyaye, Umma ta zauna gefen gado bayan ta saka Hijab dinta tace "kiyi sauri kar ki ɓatamin lokaci", Umma ta ɗauki wayarta tayi kira, wayar kare a kunnenta tace "Jamila insha Allah gani nan zuwa gidanki", bayan few seconds Umma ta katse kiran tana kallon Hajar da ta taƙune fuska, Umma ta miƙe ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace "wuce muje", Hajar tace "tom" ta wuce zata fita, Umma ta dakatar da ita tace "zo ki ɗauki kayanki da kika haɗa", Hajar ta kalli Umma ganin babu sauƙi a fuskarta ta fara jan Ghana most go ɗin data fi ƙarfinta, Umma ta rufe ɗakin da padlock, ruwa ya cicciko idanun Hajar, Umma na ankare da ita tace "muje mana", ta goge hawayen da ya zubo mata tace "Umma ban gaisa da Baba ba", Umma tace "bacci yake, ko baki ji abinda Sabra ta faɗa ba, ki ɗauki kayanki ki wuce malama, kina ɓatamin lokaci", Hajar ta fara kuka a hankali tace "bazan iya ɗauka ba", Umma ta haɗe rai tace "ƙoƙarta ki kaisu soro", ta fara jan kayan a hankali, Nabilah da ta fito bayi ta bita da harara tana taɓe baki. bayan Hajar ta kai kayan soro Umma ta saka almajiri ya ɗauka ya fitar musu dasu bakin titi, Umma ta tari Napep, ta kalli Hajar tace "shiga", bayan me napep ya saka Ghana most gon a boot Umma ma ta shiga, few minutes suka isa gidan Anty Jamila, Hajar ta ɗan ji relief ganin inda suka zo, Bayan sun shiga gidan, Hajar ta ajiye kayanta a ƙofar palour, Umma ta zauna akan kujera suna gaisawa da Anty Jamila, Hajar ta zauna kan carpet tace "Anty ina kwana", Anty Jamila tace "lafiya lou Hajar", Umma tace "yara sun tafi makaranta ko?", Anty tace "Eh suna makaranta", Umma tace "Jamila dan Allah wata alfarma nake nema a wajenki", Anty tace "tom Adda", Umma tace "dan Allah ina son Hajara ta zauna a wajenki na ɗan lokaci", Anty tace "Adda wnn ai ba damuwa bace ni me riƙe Hajara ce", Hajar dai duk tana jinsu, Anty ta kalli Hajar tace "tashi ki shigo da kayanki ki kai ɗakinsu Hafsa", Hajar ta miƙe a sanyaye wani kuka yana taho mata, yanzu anan Umma zata barta knn, tasan dai Anty bata da wata damuwa, amma ita tanada kwakwar Uwa, ko kaɗan bata so tayi nesa da Umma shiyasa ma babu inda take zuwa. Anty tabi Hajar da kallo, Umma tace "tashin hankali akai jiya a gidan, kuma Hajar ce a gaba gaba wajen assasa hakan", Anty tace "garin yaya?", Umma ta taɓe baki ta gaya ma Anty iya abinda ta sani, Anty tace "Subhanallah, gaskiya Adda haƙurin ki yayi yawa, shine kika tsaya kishiya ta ringa dukanki da takalmi", Umma tayi ajiyar zuciya tace "duk Hajara ce ta jawo, nayi nayi da ita ta dena shiga harkar yaran can amma taƙi ji", Anty tace "toh ai baki san me ya haɗasu ba da har ta biye mata, kika sani cutar da ita tazo yi ita kuma tayi ƙoƙarin kare kanta", Umma ta miƙe tace "da tayi haƙuri ai da yafi, ba zama zanyi ba, daman cewa nai bari na kawota da kaina", Anty ta raka Umma har ƙofar gida, Hajar na fitowa daga ɗakinsu Hafsa taga babu kowa a palour, ai kam ta fita waje da Sauri, har Umma ta tsare nepep tana shirin shiga, Hajar ta riƙe ƙarfen Napep ɗin tace "Umma dan girman Allah kiyi haƙuri..", Umma ta harɗe rai sai kace bata jin zafin rabuwa da ƴar tata tace "ai bakya son zama dani Hajara", Umma na faɗin haka ta shige napep ɗin, mai nepep ya burgi babur ɗinsa, Hajar ta rufe fuskarta da hijab tana kuka ta koma gida, Anty da take bakin gate ta bata hanya ta wuce snn ta rufe ƙofa. Anty dai bata ce mata komai ba, Hajar taci kukanta ta more snn tayi shiru, Anty ta fito daga ɗakinta tace "kinci abinci ma kuwa?", Hajar ta girgiza kai tace "na ƙoshi", Anty tace "shknn" ta shiga kitchen. Umma tana komawa gida ta leƙa ɗakin Baba, a kwance ta ganshi har lokacin, ta tsaya tana kallonsa na 5second snn ta juya, keys ta ciro daga ƴar purse ɗinta ta buɗe ɗakinta, Hijab kawai ta cire ta fito tsakar gida ta fara aikace-aikace, da Hajar tana nan da tuni ta gama, Umma ta dasa kujera a tsakar gida ta zauna tana tsince wake, Maama ta fito da ɗaurin ƙirji da doya guda ɗaya hannunta, zama tayi ta fara yanka doyar, tana yankawa taga doyar gaba ɗayanta ta ruɓe, ta ja wani dogon tsaki ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗakko wata, itama dai tana yankawa ta ganta ta ruɓe, Maama tayi wurgi da wuƙar hannunta ta miƙe ta shiga ɗaki, Umma dai tabi ruɓaɓɓiyar doyar da ke zube anan tsakar gida da kallo ta girgiza kai, Umma tana ta kallon ɗakin Baba taga ya fito amma shiru, a hankali tace "A'a wai yau malam lfy yake wnn baccin", ta janyo latsinetarta ta duba lokaci taga har tara da rabi ta gota, miƙewa tayi ta shiga ɗakin Baba, tayi sallama yafi sau uku amma shiru, ta ƙarasa inda yake kwance, sai taga nunfashinsa ya canza, ta taɓa goshin taji kamar tasa akan wuta sbd zafi, ta ɗan jijjigasa tace "malam!!, malam!, malam".............✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {16...} Umma ganin Baba bai amsa ba, ga kuma yadda numfashinsa yake fita sama sama yasa ta fita tsakar gida da sauri, salati da sallallami ta zabga snn tace "Rabi ku fito malam ba lafiya", Maama tana ɗaki tana jinta amma tayi mursisi, ita baƙin cikin doyarta da ta ruɓe ne ya turnuƙeta, ƴaƴanta kam suna kwance suna baccin asara, Nabilah ce kawai tayi sallar asuba itama da rana gatsal-gatsal, Umma ta matsa bakin ƙofar ɗakin Maama tace "ku fito mu kai malam asibiti, bashi da lfy", Maama ta gyara ɗaurin ƙirjinta ta fito ta yiwa Umma kallon hadarin kaji tace "Malama lfy kike mana ihu sai kace daga dawanau", Umma dai a rikice take tace "malam nefa ba lafiya", Maama ta tafa hannaye tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, kika ce kin kashe malam", sai kuma ta rushe da kuka, Umma da take a rikice saida tayi sak jin abinda Maama ta faɗa, Maama ta koma ɗaki cikin sauri ta shiga ɗalawa ƴaƴanta duka a cinya, faɗi take "ƴaƴan nan ku tashi, faɗima ta kashe muku uba", Nabilah da ita baccin nata beyi nauyi ba ta miƙe tana zabga hamma, Maama tace "tashi ƴan uwanki, faɗima ta kashe malam", Nabilah ta zaro ido ta dafe ƙirji tace "Baba". Umma dai tinda taga haukan da Maama take shirin ƙullawa bata sake bi takanta ba, wayarta ta ɗauka ta kira Mu'azzam, tana fara ringing ya ɗauka, Umma tace "Mu'azzam kana ina?", yace "ina wajen mai shayi", tace "taho gida yanzun nan", yace "Tom", ta katse wayar ta ɗauki hijab ɗinta ta fita, bayan minti biyar ta dawo tare da Munkaila makwabcinsu, Umma ta nuna ɗakin Baba tace "Bismillah". Munkaila ya shiga ɗakin tabi bayansa. Maama da ƴaƴanta sun rufa akan Baba sai kuka suke, Nabilah tace "wllh ai na gansu da sassafe da wata ƙatuwar bakko zasu gudu", Maama ta fyace majina tace "Ta kashe min miji", Umma ta harɗe rai tace "kiga mutuwa akanki, ni ba ce miki nayi ya mutu ba, dan Allah ku fita kun cika masa kunne da haushi, karku ƙara masa zafin ciwo", Maama ta wangale baki tace "haushi fa kika ce faɗima?", Umma ta bawa shara ajiyarta ta dubi Munkaila tace "dan Allah Munkaila temaka min mu fita dashi", Munkaila da Umma suka fito da Baba tsakar gida, a lokacin kuma Mu'azzam ya shigo, Umma tace masa ya taro napep, Ta uwa ta uba Maama ta ringa zage Umma tamkar zogale, Umma dai bata biye mata ba, da taimakon Munkaila aka fita da Baba aka sakasa a Napep ɗinda Mu'azzam ya taro, Munkaila da Mu'azzam ne riƙe da Baba, Umma ta tari wani Napep din tabi bayansu zuwa asibiti, da yake ranar Monday ne akwai doctors, Emergency aka wuce da Baba, doctor yana dubasa ya rubuta allurai da za a masa a takarda, Mu'azzam ya amshi takardar yaje ya siyo da ƴan kuɗin da suke aljihunsa, Saida Baba ya zama stable snn aka basa gado sbd kwantar dashi akai, blood pressure dinsa ne yayi mugun high gashi kuma akwai heart attack da ake zargin ya samu, Umma dai bata kira kowa daga dangin Baba ba sbd ba ƴan Kano bane, ainahin garinsu Baba Yola, Umma tana zaune gefen gadon Baba da yake bacci sbd alluran da akay masa Mu'azzam ya matso kusa da ita da takarda a hannunsa, a hankali yace "Umma kinga likita ya rubuta tests da drugs da kuma allurai, kuɗin hannuna bazasu isa ba", tace "tom, ka kira Naseer ka gaya masa", yace "bari na kira saina baki wayar kiyi masa magana", ta gyaɗa kai, ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Naseer, Naseer na ɗagawa Mu'azzam yace "Yaya ga Umma za kuyi magana", Umma ta karɓi wayar ta kara a kunne, Naseer yace "ina kwana Umma", tace "lafiya lou, ya aiki?", yace "alhmdllh", tace "toh Allah ya temaka, Baba ne aka kawosa asibiti ba lfy, toh kuɗin hannun mu sun yanke, gashi kuma ba a gama siyan drugs ba", yace "me yake damunsa?", tace "jininsa ne ya hau", yace "toh Allah ya basa lafiya, Insha Allah gobe zan dawo, yanzu dai Mu'azzam ya turomin da account number ɗinsa saina turo muku kuɗi", tace "toh shknn". Mu'azzam ya turawa Naseer account number ɗinsa, babu jimawa saiga alert ya shigo wayar na kudin da Naseer ya turo. Munkaila ne ya shigo ward ɗin ya yiwa Umma sallama, Umma tayi masa godiya Sosai. ★Through out the day Hajar was so Moody, har saida su Hafsa suka dawo daga schl snn ta ɗan sake, Hafsa ta fige hijab ɗin jikinta na uniform tana kallon Hajar tace "yau sai ga ki a gidan nan", Hajar tace "Eh mna", Hafsa tace "kice ƴan ziyarar sun motsa ta kanmu", Hajar ta nasa mata harara tace "kya ji dashi, naga kema ba zumuncin kike ba", Hafsa tace "Tahfeez", Hajar tace "Tahfeez ɗin ce ta hanaki fita knn?", Hafsa tace "yesso, bari na cire uniform" da haka ta shiga ɗakinsu, saida tayi wanka snn ta fito, Hajar ta ɗaga kai ta kalleta, Hafsa tace "ina Anty ne?", Hajar tace "tana ɗakinta", Hafsa tace "kinci abinci?", Hajar ta girgiza mata kai, Hafsa ta wuce hanyar kitchen tace "bari na zubo mana", ta zubo musu abincin a plate ɗaya, ta kawo ta ajiye akan carpet ta koma kitchen ta ɗakko musu pure water da gaseous drink, ta zauna ta janyo plate ɗin abincin ta saka spoon tace "toh sakko hajiya ta", Hajar ta zamo daga kan kujerar da take ta ɗauki spoon ta fara cin abincin, Anty ce ta fito daga corridorn ɗakinta, zama tayi a palourn tace "yanzu kinga damar cin abincin knn?", Hajar tace "daman Hafsa nake jira". suna gama cin abincin Hajar ta ɗauki plate ɗin ta kai kitchen ta dawo ta zauna tana shan drink. da yamma Anty ta shiga room ɗinsu Hafsa, Hafsa na latsa wayarta, Hajar kuma na durƙushe gaban Ghana most go ɗin kayanta, Anty tace "Hafsa ki bata space a press ɗinku ta jera kayanta", Hafsa tace "tom, wai daman da gaske kwana za tay?", Anty tace "kun shigo ɗaki kunyi gurgumi sai kace wasu ƴan matan Amarya, wa zai girka muku abincin dare?", Hafsa tace "wai da sai daren sai muyi jollof spaghetti", Anty tace "A'a tuwo zaku yi, Hajar tayi tuwo ke kiyi dry okra soup", Hafsa tace "tom, semovita ko?", Anty tace "Eh" ta fita ɗakin. Hajar ce ta haɗa duka tayi, da tuwan da miyar duk ita tayi su, kuma kafin a kira Sallahr magrib ta gama, Hafsa aikin fito mata da ingredients da jajjage kawai tayi, bayan sun idar da sallahr magrib sukay zamansu a palour, Abdallah ne ya shigo palourn first born ɗin Anty, ya kalli Hafsa da take bawa Hajar lbri yace "an gama dinner?", Hafsa tace "Eh", ya shiga kitchen, sai kuma ya fito empty hand, ya haɗe rai yace "wai tuwo aka dafa?", Hafsa tace "Eh", yayi slight hiss ya ɗauki remote ya canza channel daga American zuwa channel ɗin da ake ball, ya zauna kan kujera, Hafsa ta kallesa tace "ka turo min 2GB, yanzu na tashi na dafa maka indomie sharp sharp", yace "toh sleepy thief, saidai 1GB", tace "Eh naji, turo min naga dahir", ya ciro wayarsa ya tura mata Data 1GB, ta kalli wayarta da ke hannun kujera tace "yawwa sun shigo, Hajar ina zuwa", ta miƙe ta shiga kitchen da wayarta a hannu, Abdallah yace "Hajar ki koyamin yadda ake dafa abar nan mna, waccan muguwar taƙi koyan kullum sai taci kuɗina kafin ta dafamin", Hajar tayi murmushi tace "tom shknn, karka damu, kafin nabar gidan nan saika zama expert wajen dahuwar indomie", yace "yawwa, ina autar Umma?". tace "Sabra, tana nan lfy". Anty ta fito daga ɗakinta itama ta zauna tana kallon TV tace "meye wnn?, Abdallah idan za kayi kallon Ball dinka ka ringa tafiya can ɗakinka, kazo nan ka cika mu da hayaniya", yace "toh" sai kuma ya miƙe ya shiga kitchen, Hafsa ta jingina da cabinet sai latsa waya take, ga tukunya nan akan gas wacca take dafa indomien, yace "ai daman na sani, kiyi sauri malama, kin tsaya danna waya, I'm hungry", tace "tafa dahu, yanzu zan kawo maka", ya miƙa mata plate yace "juye min haka", ta amshi plate ɗin ta kashe gas, ta kama plastic handle ɗin tukunyar ta juye masa, wayarta ta ɗauka ta fita, saida ya ɗauki drink a fridge snn ya fita da plate ɗinsa na indomie, room ɗinsa ya wuce direct. Humaira ce ta rugo da gudu ta miƙawa Anty wayar hannunta tace "Ana kira", Anty tayi saurin ɗagawa ganin wacca take kiran nata, Hajar ta ringa kallonta sbd ta fahimci da wa take waya, Anty tace "toh Allah ya basa lfy, ya sa kaffara ne" ta katse kiran tana kallon Hajar da ta kura mata na mujiya, washe gari da misalin ƙarfe 11 na safe Hajar ta fito wanka, ta shafa man da ta gani kan mirror snn ta saka doguwar rigar atamfa, tana fita palour ta ga Anty ta fito daga kitchen da basket mai ɗauke da warmers, daman tin ɗazu suka gaisa, Hajar tace "Anty me za ai?", Anty tace "ba komai Hajar, ki ɗakko gyalenki fita za muyi, za muje asibiti mu duba Baba", zuciyarta ce buga da ƙarfi tace "Baban ne bashi da lfy, dan Allah Anty me yake damunsa?", Anty tace "yafa ji sauƙi, kawai dai jininsa ne ya hau, kuma yanzu ma sallamarsa za aii", Hajar ta sauke ajiyar zuciya ta shiga ɗaki, Ghana most go ɗinta ta buɗe ta ɗakko ironed Hijab maroon, tare da wayarta da tin jiya da bata bi takanta ba, hijab ɗin ta zumbula ta fito palour ta zauna tana jiran Anty, babu jimawa saiga Antyn nan ta fito daga room ɗinta. Hajar ta miƙe da sauri, Anty ta kalleta tace "toh ɗauki abincin muje", Hajar ta ɗauki basket ɗin ta fita compound, saida Anty ta rufe ko ina snn ta fito, Anty ta rufe ƙofar gate bayan sun fito ta zuba keys ɗin a hand bag, Hajar dai ta ƙagu kafin ma Anty ta gama rufe gida harta tsare Napep. Anty ta gayawa mai Napep asibitin da zai kaisu snn ta shiga, Hajar ma ta shiga. hankalin Hajar bai kwanta ba saida taga sun iso asibitin, Anty ta kira Umma a waya tayi mata kwatancen ward ɗin da aka kwantar da Baba, Anty ce ta fara shiga ward ɗin snn Hajar dake biye da ita, gadon da yake kusa da ƙofa anan Baba yake, Umma Maama sai Nabilah ne a asibitin, Anty ko kallon direction dinda Maama take ba tayi ba ta matsa kusa da Umma da take bawa Baba Youghurt, Hajar ta ajiye basket ɗin hannunta ta isa kusa da Baba da yake jingine da allon gado, a sanyaye tace "Baba sannu, Allah ya baka lafiya", Baba ya gyaɗa mata kai yace "Ameen Hajara", Hajar ta kalli Umma tace "Umma ina kwana, ya me jiki?", keenly Umma tace "lfy, jiki da sauqi", Anty ma suka gaisa da Baba da kuma Umma, saida Anty ta zauna snn tace "sannu Rabii, ya me jiki?", Maama ta taɓe baki ta juyar da kai tana girgiza ƙafa, Anty a zuciyarta tace kinyi da ƴar halak, Umma ta kalli Hajar tace "Hajara idan kika fita ɗakin nan saiki bi hannun hagu, idan kika bi hagu saiki tambayi Nurse station, saiki tambayi Nurse ɗin wajen ya baki takardar test ki kawomin, tin ɗazu yace aje a ƙarba sbd dashi za mu ga likita anjima", Hajar ta miƙe tace "tom", walking slowly ta fita daga ward ɗin. perfectly tabi kwatance da Umma tay mata ta isa Nurse station, Sallama ta yiwa Nurse ɗin dake zaune kan white plastic chair tace "nazo amsar test ne", yace "name?", Hajar tace "Adam Muhd Gini", Nurse ɗin yace "Okay" ya buɗe wata drawer ya ciro paper ya miƙa mata, Hajar ta amshi paper snn ta juya tabar wajen da papern riƙe a hannunta. ★ƙarfe tara da rabi Nurain ya fito daga room ɗinsa, car key da briefcase ne riƙe a hannunsa, down stairs ya sauka, Noor ya tarar a kan dining tana breakfast, ta yi shirin fita schl shine ta tsaya yin breakfast, Noor ta kallesa tace "good morning", yace "morning lil sis", tace "ga breakfast", yace "enjoy it alone, idan kin gama help me with a cup of coffee", tace "Tom", yace "zan shiga wajen Abba, make it kafin na dawo", ya ajiye briefcase ɗin hannunsa a kan kujera snn ya wuce part ɗin Abbansa, da sallama Nurain ya murɗa tsadadden handle ɗin ƙofar palourn kana ya shiga, ya ji daɗin ganin Mami itama a palourn tare da Abba, kan carpet ya zauna ya gaishesu, Abba ya amsa yana nuna masa kujara yace "sit", Nurain ya koma kan kujera ya zauna yana shafa kansa, a zuciyarsa addu'a yake Allah yasa parent ɗinsa su yarda da maganar da yazo musu da ita yanzu, Abba yace "is there any problem Uthman?", Nurain yace "yeah, but it is not a problem", Abba yace "then?", Mami ta ringa kallon Nurain tana jiran taji abinda zai ce, Calmly Nurain ya fara magana yace "Akan maganar course ɗin da 1yr back nace zanyi a India sai kuma na canza decision, yanzu kuma am ready to take it if i get your approval", Abba yace "for how long?", Nurain yace "six to eight months", da wani expression Mami ta kalli Nurain sai kuma ta girgiza kai tace "No", Abba ya kalleta yace "why ?", Mami tace "sai ya bar aikinsa da business ɗinsa da ya fara kafasa yanzu ya tafi wani karatu, gaskiya nidae bada yawuna ba", Abba yace "wnn ma ai zaiyi boosting qualifications ɗinsa snn kuma he need a rest, kinsan da hakan ko?", Mami ta kalli Nurain tace "tom shknn Allah ya bada sa'a", Nurain yace "Ameen, nagode Mami", Abba yace "saika fara shirye-shirye", Nurain yace "yeah, idan komai ya tafi normal ina jin ma ranar Friday zan tafi", Mami tace "this Friday?", Nurain yace "yeah", Abba yace "Ohk, Allah ya bada sa'a", Nurain yace "Ameen, yanzu ma zan wuce hospital nayi signing". Abba ya gyaɗa kai, Nurain yayi musu sallama ya fita. Main palour ya koma, a lokacin Noor ta fito da Mug ɗin coffeen da ta haɗa masa, tace "in time?" ta miƙa masa, ya karɓa yace "thank you" ya zauna kan kujera kusa da briefcase ɗinsa ya fara sipping, Noor ta rataya jakarta zata fita dan already driver na jiranta, yace "muga wayarki", tayi sak sai kuma ta zuge bag ɗinta ta ɗakko wayarta ta miƙa masa, jujjuyata kawai yayi bai kunna ba ya mayar mata da kayarta. ta mayar da ita bag snn tayi masa sallama ta fita. saida ya gama shan coffeen snn ya ɗauki car key da briefcase ɗinsa ya fita compound, parking space ya nufa ya buɗe motarsa, bayan yayi warming ya fita daga compound ɗin ya hau kwaltar street ɗin gidansu dake a mulmule, with a minimum speed ya isa Hospital, wajen da aka tanada dominsa na parking anan ya paka motarsa, ya kashe motar ya fito hannunsa riƙe da briefcase, Majestically yake tafiya har yaje office ɗinsa, secretaryn sa Halima ta miƙe cike da girmamawa tace "welcome Dr, good morning", yace "Morning" ya wuce katafaren office ɗinsa, ajiyar zuciya ya sauke yana ƙarewa Office ɗin kallo sai kuma ya buɗe briefcase ɗin da ya shigo da ita ya ɗakko wani file, da file ɗin a hannunsa ya fito, Haleema ta miƙe da sauri tace "Sir aike ne?", yace "No, continue what you're doing", ya fita. wani corridor yabi yana shan kwana sukay karo da juna, kanta ya bugu da ƙirjinsa ta shaƙi ƙamshisa, hannunta kuma mai riƙe da papern da ta kwarɓo wajen Nurse ya bige file ɗin hannunsa, a take takardun file ɗin suka baje a ƙasa, itama takardar hannunta ta faɗa cikin takardun, Hajar ta ɗago da nufin basa haƙuri amma suna yin ido huɗu saita murtuke fuska taja da baya..........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {17..} Da wani irin expression Nurain ya kalli Hajar da ta wani murtuke fuska, ya kalli file ɗin da papers ɗin ciki suka baje a ƙasa, Hajar ta yamutsa fuska sbd scent ɗinsa da ya gama bulale corridorn, ta tsugunna ta fara laluben papern ta, tana ɗaukar papern ta miƙe ta zagayesa zata wuce, yayi mata side look yace "rashin sanin darajar mutanen naki har ya kai haka?, ki bige mutum kuma bazaki basa haƙuri ba", Hajar tayi jim sai kuma ta juyo ta kallesa da lulu eyes ɗinta, ta nunasa da papern hannunta tace "mu bawa juna haƙuri daii", ta juya ta cigaba da tafiya, taku uku tayi taji anyi sama da papern hannunta, kafin ta waigo har ya sunkuya ya fara packing papers ɗinsa, ya zubasu a file ɗin ya miƙe, ta haɗe gira tace "ka bani takarda ta", ko dubanta beyi ba yayi wucewarsa bayan ya saka papern tata a pocket, galala tabi bayansa da kallo kafin ta fara tafiya da sauri following him, zumbulelen hijab ɗinta har taɗeta yake, tana zuwa kusa dashi ta rage speed amma duk da hka sauri take following him tace "ka bani paper na", idan corridorn da suke bi yayi magana to tabbas Nurain ya tanka, he was just walking Majestically without minding her, ta naɗe hijab ɗinta tayi blocking front ɗinsa tace "bani paper na", wani kallo da yayi mata and how huge he is in front of her yasa tayi gefe tana juya lulu eyes ɗinta, yayi gaba abunsa, ta tsaya tana daidaita heart racing ɗinta kafin brain ɗinta tayi booting on, yanzu fa result ɗin gwajin Baba ya tafi dashi, toh taya Baba zaiga Doctor babu test ɗin, juyowa tayi taga har ya ɓace mata, yama fita daga block ɗin, a guje ta kwasa ta fito daga block ɗin itama, ta ringa kalle-kalle da waige-waige a compound ɗin asibitin sai kace mara gaskiya, a fili tace "wai nida lantarki", wani worker ta gani yana watering flowers ta isa gabansa tace "Assalamu alaikum, Malam barka dai", ya ajiye watering can ɗin yace "wa'alaykissam, yawwa barka", duk a daburce take tace "dan Allah kaga wani mutum da ya fito yanzun nan?", yace "ai mutane da yawa ke shige da fice ta ƙofar nan, gaskiya bazan iya tantancesa ba, amma ko zaki fasalta minshi wataƙila na ganesa", Hajar ba ta da wani option than to describe him, wani ƙulluto ne ya tsaya mata a wuya, how can she describe him?, toh tace me?, workern ganin ba tace komai ba yace "ko baki sansa bane?", ta gyaɗa kai tace "Eh bansan sa ba, amma dogo ne, shi ba fari ba kuma ba baƙi ba", worker ya ƙanƙance ido yace "topa", tace "gashin kansa me nannaɗewa kuma yana sanye da ƙananan kaya" ta runtse idonta sai kace wacca ta faɗi wani mugun abu, yace "Au Dakta wai?", Hajar tayi wani tunani tace "Eh shi", ya nuna mata wani direction yace "nan yayi", ta kalli direction ɗin tace "nagode", ta nufi direction ɗin da sauri, tsayawa tayi tana ƙarewa wajen kallo, ga wani entrance nan yana facing ɗinta, direct ta shiga entrance ɗin, wani sanyin AC ya daki fuskarta, gashi wajen so quiet and calm, few mutanen wajen ta tambaya, kuma amsa ɗaya suka bata wai bai shigo ba, ta fito duk guiwa babu ƙwari, ta ringa kallon makeken compound ɗin asibitin da mutanen da suke ta hada-hada, daga ƙarshe dai da ta gaji da dubansa ga rana sai kashe mata ido take kawai ta nufi hanyar ward ɗin da Baba yake, babu abinda zuciyarta take sai tafarfasa, sai kace wacca kwai ya fashewa a ciki haka ta shiga ward ɗin, sukay ido huɗu da Umma dake zaune kan darduma tana cin abincin da suka zo dashi, daga ita sai Anty Jamila, Maama da Nabilah sun tafi daman ba wani daɗewa sukay ba. Hajar ta ƙarasa gefen gado ta zaune kusa da ƙafar Baba da yake bacci, Umma tace "da baki gane wajen ba ai sai ki dawo, ba kije kiyi ta bulayi ba", Anty tace "yana ganki duk wani iri ne?", Hajar tace "takardar ce fa ta ɓata", Umma ta ajiye spoon ɗin hannunta tace "kamar ya ta ɓata?", Hajar ta fara jan fingers ɗinta tace "dana karɓo takardar a wajen Nurse kamar yadda kika gayamin shine a hanyar dawowa na kasa ganewa, shine na fita waje, a wajen ne iska ta ɗauke takardar ta shiga cikin silap ɗin kwata", Umma ta taɓe baki ta ɗauki spoon ta cigaba da cin abincinta ba tace komai ba, Anty tace "amma shine baki dawo da wuri kin sanar ba", Umma ta ɗago ta kalli Hajar tace "ƙarya take yi, da ita dai za a duba mahaifinki, idan kin salwantar da ita ke kika sani", wani takaici ya sake balbale Hajar kamar ta fashe da kuka haka take ji, Anty tace "Hajar da gaske kike ?", Hajar ta gyaɗa kai da sauri, wata matron ce ta shigo ta sanar da kowa ya fita za a bayar da magani, Anty tace "toh Adda Allah ya basa lfy, ni dai idan na fita wucewa zanyi", Umma tace "toh Jamila nagode, ku gaida gida", Anty tace "saina bar miki Hajar anan ko sbd wani temakon", Umma tace "A'a karki barmin ita, nima bazan daɗe ba zan koma gida, Naseer da Mu'azzam suna zuwa zan tafi", Anty tace "toh shknn, sune suke kwana dashi?", Umma tace "Eh", Anty ta ɗauki handbag ɗinta ta miƙe tana kallon Hajar tace "tashi mu tafi", Hajar ta tashi tace "Umma sai gobe, Allah ya basa lfy", Umma bata dubeta ba tace "Ameen". da suka fita farfajiyar asibitin Hajar ba abinda take sai faman baza idanu, ko kallon gabanta ma bayi take sosai ba, wani me motorbike ne ya kusan bigeta, Anty ta janyota gefe tace "ki kalli gabanki mana, kalle-kallen me kike haka?", sai a sannan Hajar ta maida hankalinta ga tafiyar da take. suna komawa gida Hajar ta shiga kichen ta fara preparing lunch, jollof rice ta dafa wacca taji attaruhu, a hankali take yanka cabbage ɗin gabanta a kan chopping board bayan ta gama goga carrots, time to time saita ja dogon tsaki tace "lallai ma mutumin nan", ƙarfe ɗaya da minti hamsin ta gama abinda za tay ta wuce ɗakinsu Hafsa, ta shiga toilet tayo alwala ta fito, darduma ta shimfiɗa tayi sallar azahar, tana idarwa ta miƙe ta linke darduman ta ajiye gefe, wayarta ta ɗauka taga missed call da two messages from Nura, karantawa tayi tana murmushi kafin ta shiga tura masa reply, tana tura masa message ɗin babu jimawa sai gashi yana kira, taɓe baki tayi ta kara wayar a kunne bayan ta ɗaga, Calmly tace "Salamu alayyykumm", Nura yayi slight voice smile yace "wa'alay kumussalam babe", tayi shiru ba tace komai ba, yace "ina kika saka wayarki tin jiya ina nemanki?", Hajar ta turo baki kamar tana gabansa tace "toh aii banida chaji", yace "toh yanzu kam anyi chajin ko?", tace "Eh", yace "gobe zanzo, kinga jiya ban samu nazo ba, gashi yauma inada appointment", tace "tom", yayi ƙasa da murya yace "saina tambaya ko?", tace "me?", yace "me yake damunki?, ki faɗa min?", Hajar taji kamar ta fashe da kuka daman tin ɗazu take cijewa, ga Umma na fishi da ita har yanzu bata huce ba, ga Baba ba lafiya, ga kuma baƙin cikin abinda wnn mutumin yayi mata, sosai ya ƙona mata rai, ko mene nashi na tafiya da papern oho, a hankali tace "Baba ne bashi da lafiya, an kwantar dashi a asibiti...", sai kuma ta fara kuka a hankali, Nura yayi ajiyar zuciya yace "me yake damunsa", tace "BP ɗinsa ne yayi high", yace "ki dena kuka kinji, zai samu lafiya Insha Allah", ta goge hawayen da ya zubo mata tace "tom", ta ɗago idanunta da suka fara canza launi ta kalli ƙofa, Hafsa ce ta shigo wacca ta dawo daga schl, Hafsa ta ajiye schl bag ɗin ta tana kallon Hajar, Hajar da waya kare a kunnenta tace "kun dawo?", Hafsa tace "yess, naga ana tsinkar flowers ai", Hajar ta harareta ta kwanta a gado tana sauraron abinda Nura yake faɗa mata. Hafsa tace "Eh lallai" ta fara cire uniform ɗinta ta ɗaura towel ta shiga toilet. harta fito daga wanka Hajar na maƙale da waya, ta buɗe press ta ɗauki kayan da zata saka tana satar kallon Hajar, Hafsa ta zauna akan stool tana rubbing lotion a fatarta. Hajar ta ajiye wayarta tana sauke ajiyar zuciya, ta miƙe zaune tana kallon Hafsa tace "wai har kin fito wanka?", Hafsa tace "Eh mana", Hajar tace "nida jiƙa-jiƙa", Hafsa ta cigaba da rubbing lotion tace "ai dole kice haka sbd lokaci ya miki ƙaranci na tsinkar flowers". Hajar tace "ke kika sani, ina Humaira?", Hafsa tace "tayi wajen Anty", Hajar ta gyaɗa kai ba tace komai ba. Hafsa ta ɗauki kayanta ta saka, ta kalli Ghana most gon kayan Hajar tace "Au baki shirya kayan a wardrobe ɗin ba", Hajar tace "nida ba daɗewa zanyi ba", Hafsa tace "oho miki, Anty ce dai tace na baki space, don haka muci abinci saina temaka miki ki shirya kayan a press". ★Nurain bai baro hospital ba saida ya gama komai da ya dace, ya ajiye aikinsa na good 8months, yayi submitting komai da ya dace, Office ɗinsa ya koma after that, ya tsaya wajen secretary Haleema yace ta kira masa Dr Marwan, Khaleel da sauran team members ɗinsa, with due respect tace "okay sir", Nurain ya wuce cikin Office ɗin, A kan kujera ya zauna wasu moments suna dawo masa a brain, ya kalli kujerar da Ruqayyah take zama, ya ɗauke idonsa daga wajen cause he don't want to think about her, lumshe idonsa yayi yana juyi kan kujerar da yake kai, a bazata yaji zuciyarsa ta sarƙe da tunaninta, a hankali yace "stubborn girl, ashe dai tana tsoro", ya zura hannunsa a pocket ya ciro papern, ya ringa kallon papern da take folded, yanayin papern ne yasa yayi unfolding ɗinta a hankali, kasancewar result ɗin dake rubuce a papern is inside his field ya fahimci komai, ya mayar da papern yadda take bayan ya linketa. Khaleel ne ya fara shigowa ya zauna kan soft sofas da suke hakimce gefe guda a Office ɗin, Khaleel yace "Gani Boss", Nurain na kallon wani makaken picturen heart dake office ɗin yace "Ohk, bari su Marwan su ƙaraso", Khaleel yace "Neh", few minutes kam Office ɗin ya cika da well trained team members of thoracic surgeon Dr Uthman, Nurain ya ringa kallonsu kafin yace "zanyi tafiya na 8 months, so i have to tell you this sbd we work together, kamar yadda idan wani uzirin ya kamani nake barin Dr Marwan incharge, to this time around ma shine, follow by Khaleel, i wish you people all the best", a hankali suka fara daɗewa bayan sunyi masa sallama da fatan Allah ya bada abinda za a tafi nema, Dr Marwan ne ƙarshen fita, har ya miƙe zai fita Nurain yace "Dr wait", Marwan ya dawo ya zauna kujerar dake facing ta Nurain, Nurain ya ɗauki papern gabansa ya miƙa masa yace "plxx, ka duba wnn patient ɗin", Marwan ya karɓa ya buɗe ya karanta, yana gama karantawa ya rufe yace "it is a cardiac arrest?", Nurain ya gyaɗa kai yace "yeah", Marwan yace "toh yana ina?", Nurain yace "yana cikin hospital ɗin nan, plxx kasa a nemo maka shi", Marwan yace "sure" ya miƙe ya fita da papern a hannunsa. ƙarfe uku da ƴan mintina Nurain ya koma gida, direct room ɗinsa ya wuce, after taking his bath ya shirya cikin ƙananan kaya ya fito sallar la'asar, bayan ya dawo salla ya wuce wajen Mami, saida ya dangana da bedroom snn ya tarar da ita tana sallah, palour ya dawo ya zauna yana latsa wayarsa, sai after 20minutes Mami ta fito sanye da hijab ɗin da tayi sallah ta zauna kan kujera three seater, Mami tace "ka dawo?", Nurain ya ajiye wayar da yake latsawa yace "Eh, tin ɗazu ma na shigo", Mami tace "Ohk, kaci abinci?", Nurain yace "A'a yanzu nake jiran Noor ta shigo saita kawo min", Mami tace "Noor bata dawo schl ba, saidai Laure ta kawo maka", Nurain ya shafa kansa yace "No, bari Noor ɗin dai ta dawo", Mami ta taɓe baki tace "toh ai shknn", ta gama rafko jirginsa, ya raina tsaftar Laure. Nurain yace "Mami daga yau bazan sake zuwa Hospital ba har saina dawo daga tafiya, na gama komai da zanyi a can, insha Allah ina sa ran ranar Friday zan tafi", Mood ɗin Mami ya canza, ta ƙurawa TV ido ba tace komai ba, Nurain ya ringa kallonta........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {18..} After the silence of about 5mins Mami tace "kuma kai hakan shi yafi yi maka?", Nurain ya kalleta yaga har lokacin idonta na kan TV, ya shafa kansa ya kwantar da voice yace "yeah Mami hakan shi yafi min", tace "Ohk shknn, Allah ya bada sa'a", yace "Ameen". Mami ta tashi ta fita ɗakin, bata daɗe ba ta dawo da tray a hannunta, akan carpet ta ajiye ta koma position ɗinta ta zauna, ta kalli Nurain tace "saika sauka kaci abincin", ya kalli trayn snn ya ajiye wayarsa akan hannun kujera ya sauka kan carpet, wamers ɗin ya fara buɗewa snn ya ɗauki plate ya zuba abincin, yana fara cin abinci akay knocking door, Mami tace "shigo" cause tasan waye, Laure ce ta shigo hannunta riƙe da tray mai ɗauke da bottle water sai lemon kwali da cup, Mami ta nuna mata Centre table tace "ajiye anan", a hankali ta ajiye kana ta juya ta fita, a hankali Nurain yake cin abincinsa har ya gama, ya ɗauki bottle water ya tsiyaya a cup ya sha, Mami tace "karka yi tafiyar nan ba tare da kaje kunyi sallama da Hajiya ba", yace "insha Allah Mami, zanje muyi sallama". tace "yawwa", ya tashi ya ɗauki wayarsa yace "zan ɗan fita", tace "wajen Hajiyar zaka?", yace "No", tace "Okay, ka taho min da counter", yace "tom" snn ya wuce ƙofa ya murɗa handle ya fita, room ɗinsa ya wuce ya ɗakko muƙullin Mota, daga nan ya fita compound ya shiga motarsa, slowly yake driving listing to the qira'a of Sheikh Husary, A wani annakakken wajen siyar da wayoyi yayi parking, same wajen da ya siyi sabuwar wayar hannunsa, bayan ya shiga building din da akay molding dinsa da pattern ɗin cell phone, tsayawa yayi yana tunanin wace wayar zai siyawa Noor, taɓe baki yayi ya nufi ɓangaren iPhone cause yasan sune ake yayi, ko wace ƴan mata tafi son iPhone, Shi kam waya indai ba Samsung bace ba toh a barta, iPhone mai kyau da tsada ya siya full series, credit card ɗinsa ya miƙawa cashier ta cire kuɗin snn ta miƙa masa with due respect, yana gamawa ya fito ya shiga motarsa, A junction yaga mai counter ya siyi guda uku mai haɗe da agogo, lokacin da ya koma gida har Magrib tayi, saida yayi sallah snn ya shiga ciki, Noor ta amsa sallamarsa, tayi wani dafa'an tana kallon stuff dinta na Kdrama, tace "yaya ina yini", yace "lfy lou", zama yayi akan kujera duk da ba hakan yaso ba, with stern Voice yace "zo nan", ta matsa gabansa ta zauna daga ƙasan carpet, ledar da ya shigo da ita ya ajiye mata akan cinya yace "your birthday presence", Noor tayi murmushi snn ta buɗe ledar, ai tana ganin abinda yake ciki ta daka tsalle ta rungumesa tace "thank you so much, nagode Allah ya saka da alkhairy yayana", yace "you know the rules right?, kuma kinsan warning ɗin da nayi miki ko?", ta gyaɗa kai da sauri all her white tooth out, ya shiga part din Mami ya kai mata counter, ya fito ya haura room ɗinsa cause yana so ya gama duk wani shirye-shirye kafin nanda Wednesday. ★Hajar na zaune a palour tare da Hafsa da Humaira suna kallon wani film a MBC 2 mai suna IT, Humaira duk ta ruɗe sbd film ɗin akwai abin tsoro, Hajar kam kwata kwata mind ɗinta was somewhere else, ita bata ma san me akeyi a film ɗinba, time to time kuma saita ja long hiss, Hafsa ta kalleta tace "wai me ya faru ne tin ɗazu kike mana tsaki?", Hajar ta sake yin wani tsakin tace "uhmm bazaki gane yadda nake jin haushi ba ne", Hafsa ta taɓe baki tace "toh ki gayamin mana, me ya baki haushin?", Hajar tace "wllh wani ɗan rainin hankali ne ya haɗamin zafi ɗazu a asibiti", Hafsa ta tare hammar da ta yanko mata tace "ni kam bangane wane rainin hankalin kike magana akai ba?", Hajar tace "ai shiyasa nace bazaki gane ba", Hafsa tace "taya za kice bazan gane ba bayan baki yimin yadda zan gane ɗin ba", Hajar tace "forget it kawai, Allah ya kaimu gobe, ai zan koma asibitin, wllh sai ya bani takardar test ɗin Babana", Hafsa ta koma tayi resting a jikin kujera tace "uhmm, ke kika sani dai", Anty ce ta fito daga ƙofar part ɗin mijinta, ta ƙare musu kallo snn tace "la'ila ƙarfe nawa har yanzu baki kwanta ba Humaira?", Humaira ta turo baki tace "ai su yaya ne sunƙi zuwa mu kwanta, kuma ni tsoro nake ji", Anty ta zauna ta kalli Hafsa da take ta faman hamma tace "toh kuje ku kwanta mana, sai zabga hamma kike, gobe da schl kinsan da hakan aii", Hafsa tace "Hajar nake jira", Anty tace "Ina ruwanki da ita, ita ba schl take zuwa ba don haka anytime zata iya kwanciya abinta", Hafsa tace "toh saina gama kallon film ɗin nan", Humaira tace "Anty ni tsoro nake ji, kuma bacci zanyi", Hafsa ta nasa mata harara tace "keee, wuce ki kwanta, tin ɗazu nayi miki shimfiɗa", Humaira ta noƙe kafaɗa ta koma cinyar Anty ta kwanta, Anty ta kalli Hajar tace "An sallami Baba", Hajar tace "yaushe?", Anty tace "ɗazu", Hajar ta gyaɗa kai tace "toh yaga likitan?", Anty tace "Eh, Adda tace har daƙi likita yazo ya dubasa, kuma likitan ne yazo da takardar test ɗin", Hajar was speechless sbd mamaki, how comes?, a ina doctorn ya samu test ɗin?, ko dai result ɗin biyu ne?, ganin bata da amsar waɗan nan questions ɗin saita ɓige da jinjina kai, sai kuma tace "gobe da safe zasu tafi gida knn?", Anty tace "Eh". Washe gari da wuri Hajar ta gama gyara gida, ta shiga toilet tayi wanka, ta fito ta ɗauki mai ta shafa, wardrobe ta buɗe ta ɗakko kaya ta saka, Hafsa dai saida ta jere mata kayan nan a press snn ranta yayi sanyi, wani material ta saka mai kyau, Anty ce ma ta bata shi ita da Sabra waccan sallar da ta wuce. gaban mirror ta tsaya tana kallon gashin kanta mai cika, yaushe rabon da ta taɓa sa, gashi nan kam duk ya cukurkuɗe alamar ba a untangling ɗinsa frequently amma kuma babu datti, cause tana wankesa akai akai amma fa tajewa ne yake mata wahala sbd cikarsa, most of the time ma Umma ce take taje mata, roban hair oil ta buɗe ta zauna akan stool, she spent almost 30mins making her black silky hair tide, a ƙeya tayi parking ta ɗaure da ribbon, ta tufke jelar wacca ta saukar mata har midback. ta mayar da comb ɗin cikin drawer snn ta rufe roban hair oil ɗin, ta ɗaura dan kwali ta fita palour, kitchen ta shiga ta tsiyayi ruwan Lipton a cup, ta haɗa tea snn ta ɗauki 4slice of bread ta koma ɗakinsu Hafsa. tana cikin ci wayarta ta fara ringing, sosai tayi mamakin wane yake kiranta at this time, cup ɗin tean ta ajiye ta miƙe ta ɗakko wayar, kallon screen ɗin wayar ta tsaya yi ganin bata son numbern dake kiranta ba, har kiran ya yanke wani ya sake shigowa, slim finger ɗinta ta kai tayi picking snn ta kara wayar a right ear ɗinta haɗe da yin sallama with her cool voice, ɓoyayyen ajiyar zuciya taji an sauke snn aka amsa mata sallamar, ta yamutsa fuska jin muryar namiji, ta ciro wayar daga kunnen dama ta mayar da ita na hagu tace "Ahmm bangane mai magana ba?", yace "Eh, am Ahmad, na samu numbern ki a wajen friend ɗinki", ta taɓe baki sbd ta fahimci shine wanda Zainab tace zata basa digit dinta, tace "okay, but how can I help you?", yace "i want to talk to you", tace "Sorry, ba sai kayi magana ba ma, ina fatan dai Zainab tayi maka bayani", yace "wane bayanin?", tace "akwai baiko a kaina", daga haka ta katse kiran ta cigaba da shan shayinta, tana ajiye wayar saiga wani kiran nan yana shigowa, saida tayi ringing twice kafin ta ɗauka, yace "why did you hanged up?", ta juya lulu eyes ɗinta tace "ina aiki ne", yace "Okay, a gama lfy, zan kira later plxx pick up", tace "tom" ta katse. ★Ƙarfe goma da rabi na safe Naseer da Mu'azzam da kuma Huzaifa wanda ya baro lectures ɗinsa ya dawo gida suka shigo gida tare da mahaifinsu, Baba duk ya faɗa ya rame sosai, Umma ta fito ɗakinta tana musu barka da dawowa, ta wuce ƙofar ɗakin Baba ta buɗe padlock, Huzaifa ya tallafi Baba ya shiga ɗakinsa, ɗakin a gyara yake fes fes sai ƙamshin turaren tsinke yake, Umma ce ta gyara sa da sassafe tinda a gida take kwana. Mu'azzam ya shigo da ledar drugs ɗin Baba ya ajiye gefe, Umma ta fita tana kallon ɗakin Maama ta shiga nata, flask ɗin da ta dama kunun gyaɗa ta ɗauka da cup ta fita, ta kalli Mu'azzam da yake ƙoƙarin fitowa daga ɗakin tace "zaka sha kunu na zuba maka?", ya gyaɗa kai yace "Eh zan sha", ta ƙarasa shiga ɗakin Baba, ta ajiye flask din gefe, Huzaifa ya jingina pillow a bayan Baba snn yace "sannu Baba, Allah ya baka lfy", Baba yace "Ameen, Allah yayi muku albarka", Huzaifa da Umma suka ce Ameen, Umma tace "Huzaifa ina Naseer?", yace "ya shiga ɗaki", tace "ga kunu idan zaku sha na zuba muku?", Huzaifa yace "tom". cup guda uku Umma ta cika da groundnut pap, Huzaifa ya ɗauki nasa dana Naseer ya shigar musu dashi ɗakinsu, Umma ta rufewa Mu'azzam nasa da ya shiga toilet, Baba ya kalli Umma yace "ina Hajara?", tace "tana nan", yace "kirowamin Rabi", Umma ta waro ido amma ba tace komai ba ta tashi ta fito tsakar gida, A ƙofar ɗakinsu Naseer ta tsaya ta kira Huzaifa, ya fito hannunsa riƙe da kofin kununsa da har ya kusa shanyewa yace "na'am", tace "ka kira Maamanku tazo inji Malam", yace "tom" ya shiga ɗaki ya ajiye kofin kunun snn ya fito ya wuce ɗakin Maama, Umma tana ganin ya shiga wajen Maama ta koma ɗakin Baba tace masa gata nan zuwa. Huzaifa ya ringa kallon Maama wacca take zaune dafa'an akan ƙullin kayan wanki, ya durƙusa yace "Maama barka da safiya", tana karkaɗa ƙafa tace "ba yawwa ba, tinda kwanten gaisuwa zaka jefeni da ita, wai har waccar mayyar matar ta fini daraja a idanunku kai da Nasiru, ƙiri ƙiri bakwa kallona a matsayin mahaifiyarku, ace miƙiyyata itace wacca zaku fifita, koda yake ba laifin ku bane tinda an zuba a kunu an baku kun tanɗe..", Huzaifa dai ya shafa kai yace "Baba yana kiranki", ta taɓe baki tace "toh me zan masa da yake kirani, ince dai ga mayyar matarsa nan a tare dashi koh", shiru Huzaifa yayi baice komai ba. Maimuna da take kan gado rashe rashe itada Nabilah ce ta miƙe zaune tana hamma, wani irin wage baki tayi babu addu'ar neman tsari ga shaiɗan bare ta kai ga rufe wawakeken bakinta, buɗe idonta tayi tana soshe soshe snn ta zabga tsaki tace "Allah ya isa wllh, Sauro da kuɗin cizo sun suburbuɗe ni yasin, shiyasa Sa'adatu ta tsani gidan nan wllh, nima dai daf nake da barin kangon nan alkur'an...", dakatawa tayi da tijarar tana micincina idanu ganin Huzaifa, ta sakko daga gadon tace "Laa yaya ina kwana", tsaki yayi ya miƙe ya fita a ɗakin. Maimuna ta taɓe baki tace "ni kam Maama sai naga kamar yaya Huzaifa yana juyewa kamar yaya Naseer", Maama tayi kwafa tace "uhmm shima ai an shanyesa, har kunu fa ake damawa a basa, kinga kam bayan shanyewa har damesa akai". Maimuna ta cigaba da soshe soshe kafin tace "ni kam Maama wai ina ragowar piya-piyan nan yake yau na fesa a katifa?, kuɗin cizon nan yayi yawa", Maama ta ɗauke kanta tace "ya ƙare, daman Sa'adatu ce mai siya kuma kinga tin shekaran jiya rabonta da gidan nan, itace mai zuciyar siyar piya piya ayi feshi, ke kam tsimilmila da maƙo bazasu barki kiyi abin arziƙi ba, koni nan uwarki ba morarki nake ba, ko kuɗin kika samo saidai ki cinye ke kaɗai sbd rowar masifa, nasan yanzu haka kinada uban kuɗi a ƙugunki amma bazaki iya fitar da ɗari biyar a siyi piya piyan ba kin gwammace kuɗin cizon suyi ta cizonki....", Maimuna tace "kaiiii Maama", Maama ta harareta tace "gafara can za wani kicemin kaiiii, aa ba kaii ba hannu ko ƙafa, sakarya kawai, ki kira Sa'adatu yanzun nan kice mata ta dawo gida an sallamo malam, jiya naga kunyi waya da ita kuma nasan ƴan albarkar ƙawayenta har sun mayar mata da tsaleliyar wayar da ta rasa", Maimuna ta ringa ƙunƙuni snn ta ɗauki wayarta a ƙarƙashin pillow ta shiga dokawa Sa'adatu kira, sau uku ta kira wayar na ta ringing amma ba a ɗauka ba, ta zabga tsaki tace "Maama kinga dai bata ɗauka ba ko?, ni dai ba ruwana idan yaya Naseer ya sake lakaɗa mata na jaki", Maama ta harareta tace "sake kira", Maimuna tace "bafa ɗauka za tayi ba don nasan bacci ma take yanxu" ta shiga kiran Sa'adatu for the fourth time. daf kiran zai tsinke aka ɗaga, Maimuna tace "ke Sa'adatu toh ki taho gida inji Maama an sallamo Baba daga asibiti kuma yaya Naseer yana nan..". ƙit aka kashe wayar bayan wani dogon tsaki, Maimuna ta kalli screen ɗin wayar ta mulmulo ashar tace "Alfarmar Annabi da Alkur'ani sai Yaya Naseer ya lakaɗa miki duka"......✍️ 💛 HAJAR💛 by Feenerh_feeche {19..} Maama ta hangame baki tana kallon Maimuna tace "A'a kaji mun muguwar yarinya, ya zaki ringa mata mugun fata kina wani cewa Naseer ya lakaɗa mata duka iyee?, akan me kike mata wnn fatan sbd ƙeta?", Maimuna ta hade gira tace "toh daga temako shine zata wulaƙantani?, kawai saita yimin tsaki ta kashemin waya daga temako", Maama tace "sake kiramin ita ki bani wayar nida kaina nayi mata magana", Maimuna tace "ba dai da katin wayata ba wllh" ta miƙe ta saka wayar a wardrobe. Maama tayi ƙwafa ta miƙe ta fita a ɗakin ta shiga na Baba, sallama tayi ta ƙarasa shiga ciki, Baba da yake jingine da pillow ya amsa mata, ta kalli Umma da take zuba kunu a cup ta taɓe baki snn ta koma gefe ta zauna tace "ya kufan jikin mal?", Baba na kallonta da kyau yace "da sauƙi alhmdllh, ina Sa'adatu da Maimuna sune ban gani ba a asibiti", Maama ta dubi Umma tace "Baiwar Allah saiki tashi ki fita ko, zanyi magana da uban ƴaƴana", Umma ta cigaba da abinda take ko dubanta ba tay ba, Maama tace "Keee magana nake miki fa, ko kurma ce?", Umma ta rufe flask din kunun ta ɗauki wanda ta zuba a cup ta kai gaban Baba tace "gashi, bari naje na ɗora faten accar", Maama ta buɗe ƙananan idanunta tamkar an kwantali ɗata tace "kai jama'a ki fita nace kike reto sai kace mai maula", Umma ta ɗauki flask ɗin snn ta fita ɗakin, da wata muguwar harara Maama ta bita sai kuma ta kalli Baba tace "ka gani ko?, ina mata magana tayi banza dani sbd wulaƙanci", Baba ya ɗauki kofin kunun ya kurɓa snn yace "wllh duk ranar da keda ƴaƴanki kuka kasheni kin shiga uku Rabii", tace "na shiga uku a ina?, sai kace wata mara madogara", wani tari ne ya sarƙe sa ya nunata da yatsa yace "fita Rabii", ya cigaba ta tarin a hankali, ta taɓe baki tace "Sannu, mura ce ta kamaka kenan?". da kyar Baba ya samu tarin ya lafa masa, ya lumshe idonsa ƙirjinsa na suya, Maama ta miƙe tana gyara haɓar zaninta tace "to bari na baka guri ka huta mal, tinda daga magana sai tarii kar ace ni na tayar maka da ciwo" da haka ta fice a ɗakin. Naseer da ya fito a ɗakinsu ta kalla tace "biyoni" ta shiga ɗakinta, Naseer ya shafa kai snn yabi bayanta, ya zauna kan ruɓaɓɓiyar ledar ɗakin, Maama dake gafen gado zaune kusa da Nabilah da take baccin asara ta dubesa tace "wai me yake damun mal ne?", yace "hawan jininsa ne ya tashi snn kuma ya kamu da ciwon zuciya", Maama ta gwalo micimicin idanunta waje ta dafe ƙirji tace "ciwon zuciya mal ɗin, Nasiru me kake cewa ne?". Nabilah ta zaburo ƙasa ashe ba bacci take ba tace "Baban ne ciwon zuciya ta kamasa" ta figi hijab tayi waje da sauri, Naseer da zuciyarsa duk ba daɗi ya dubi mahaifiyar tasa yace "Abinda Baba yake buƙata addu'a snn kuma kar a ringa ɓata masa rai, duk wani abu dai da zai daki zuciyarsa toh zai iya tayar masa da cutar, kuma daman ga hawan jini, ya kamata a kiyaye Maama". kallonsa Maama ta ringa yi kafin tace "A'a Nasiru ai ba ni zaka gayawa a kiyaye ba, waɗancan gayyar shegun zaka gayawa sbd nayi imani da Allah sune suka saka masa ciwon zuciya, ba kaga duk sunfi damuwa ba sbd sunsan abinda suka aikata, tsoro suke ji kar ya mutu ta sanadinsu, tin ranar da shegiyar yarinyar nan da uwarta suka yiwa Sa'adatu ƴar albarka rubdugu toh shknn mal ya kwanta rashin lfy, to Allah dai ya kyauta ai zama da shegu ba kanta sbd tsinannu ne....", Naseer ya katseta da cewa "ni zan shirya na koma wajen aiki, zan ringa zuwa duk bayan kwana uku tinda lodin Lagos zuwa kano nake yi", Maama ta gyaɗa kai tace "toh shknn, amma kuma gidan bamu da komai, mai fita ya kawo ya kwanta rashin lfy, kasan ba abincin ne a jibge ba kullum sai an auno wanda za a sa a bakin salati, ruwan amfani ma sai mun siya", yace "ba komai insha Allah zan ringa yo aike, snn kuma ga wnn" ya karkace ya ciro kuɗi masu ɗan kauri ya miƙa mata. wuff ta amshe snn ta shiga ɓaɓɓaka masa albarka da godiya, ya shafa kansa yace "ba komai Maama" snn ya miƙe ya fita. yana fita Nabilah ta shigo, Maama ta fara ƙoƙarin ɓoye kuɗin a ƙirjinta amma sbd suna da kauri sai suka fito, Nabila ta taɓe baki tace "A'a Maama dama kin dena ɓoyewa ai na gani kuma nasan ya Naseer ne ya baki", ta cire hijab ɗin jikinta snn ta zauna a ƙasa tana fifita dashi tace "Baba na shiga na duba kuma naga jikin da sauƙi, nawa yayan namu ya bayar ne?", Maama ta ciro kuɗin ta ƙulle a haɓar zaninta tace "na gida ne, ina Maimuna tazo ta kira Sa'adatu a waya", Nabilah tace "wanka take", Maama tace "wanka?, amma dai ba fita za tayi ba ko?", Nabilah tace "can ta matse mata, ni bansani ba". Bayan minti goma Maimuna ta shigo ɗakin da ɗaurin ƙirji, ta ajiye kwandon soso da sabulu akan window, wardrobe ta buɗe ta ɗakko kaya da jakar kayan kwalliya ta zauna ta fara shafa mai, tana gama shiryawa tass cikin wasu matsattsun kaya wanda rabin ƙirjinta a waje yake ta ɗauki hijab har ƙasa ta saka. Maama tace "Amma dai ba fita za kiyi ba dai ko?", Maimuna ta dakata da ɗaukar wayarta dake gefen gado tace "bangane ba, nafa gaya miki tin jiya", Maama tace "ehh kin gayamin amma yanzu kinga an sallamo babanku, kin manta dokar da ya kafa muku ne, toh babu inda zaki kuma ki kira Sa'adatu ta dawo.." tana gama faɗin haka ta miƙe ta fita tana cewa "ja'ira idan ma kin samo kuɗin ba alheri kike ba". ★Bayan sallar azahar Hajar ta shiga ɗakin Anty sbd kiranta da take, sallama tayi a hankali, Anty ta amsa mata snn ta shiga ɗakin. Hajar ta nemi guri zata zauna a kan carpet Anty ta nuni mata gefen gado tace "zauna anan", ba musu ta zauna a wajen da ta nuna mata, Anty ta ƙarasa abinda take jikin press ta zauna kan stool tana kallonta tace "kin cire kayanki daga Ghana most go dai ko?", Hajar tace "Eh Hafsa ta saka min a wardrobe", Anty ta gyaɗa kai tace "Okay, idan kina buƙatar wani abun saiki gaya min", Hajar tace "toh", Anty ta kalli fatar ƙafarta da dogon wuyanta tace "wane cream kike using?", Hajar tayi murmushi tace "duk wanda ya sawwaƙa ko petroleum jelly ko mai gurguwa ko kuma Habiba", Anty tace "Okay, kinci abinci?", Hajar ta girgiza kai tace "sai su Hafsa sun dawo", Anty ta kalli agogon da yake maƙale da bango tace "yanzu ma zaki gansu, ita Hafsan ce tace ki ringa jiranta?", Hajar ta girgiza kai tace "A'a Anty", Anty tace "toh shknn, je ki soyamin kajin dana sulala ɗazu", Hajar tace "tom" ta miƙe ta fita Anty ta bita da kallo. Anty dai tinda Hajar tazo gidan bata taɓa ganin wani aibunta ba or something bad akanta, kwata kwata ba ta da wata matsala, gata da tsafta kamar me, kafin ma ta tashi da safe ta gama gyara gidan tass, amma kuma ƴar uwarta na complain da ita. wai bata da haƙuri to gsky in rashin haƙurin ne ga dukkan alamu sai an taɓota. Hajar na fita ɗakin ta wuce kitchen ta ɗauki frying pan ta tuttuli vegetable oil ta ɗora akan gas, bayan oil ɗin yayi zafi ta fara soya naman. tana gama soyawa ta fita kitchen ɗin ta gayawa Anty snn ta wuce ɗakinsu Hafsa. wayarta ta ɗauka ta shiga kiran umma, Umma na ɗauka Hajar ta gaisheta tace "ya jikin Baba?", Umma tace "da sauƙi, mun dawo gida", Hajar tace "Allah ya ƙara afuwa", Umma tace "Ameen", Hajar tayi gathering courage tace "Umma yaushe to zan dawo gida?", Umma tace "wani abun ake miki anan ɗin ne?", Hajar ta girgiza kai tace "ni ba abinda ake min, nafi son gida wllh, dan Allah umma kiyi haƙuri", Umma tace "laifin me kika min da kike bani haƙuri, gwara ma ki saba da zama anan sbd gsky bazaki dawo gida yanzu ba", hawaye ya ciko idanun Hajar tace "dan Allah Ummana", Umma ta sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya tace "kiyi haƙuri kinji, sai anjima", ta katse kiran. Hajar ta ringa kallon screen ɗin wayar tace "na shiga ukuna". palour ta fita ta zauna, tana zama Anty ta fito daga room ɗinta ta shiga kitchen ta fito da plate din abinci da soyayyen naman kaza a kai ta zauna a palourn tana ci, Anty tace "kee tashi ki zuba abinci ki ci ba wani sai Hafsa ta dawo", Hajar tace "Allah Anty bana jin yunwa", Anty ta cigaba da cin abinta bata sake cewa komai ba, few minutes kam saiga su Hafsa nan sun dawo. Bayan Hajar da Hafsa sun gama cin abinci Anty ta kalli Hafsa dake gyara wajen da suka ɓata tace "da yamma zan aike ku supermarket, idan kin kai plate din kitchen sai ki kawomin jotter da biro nayi list din abinda zaku siyo", Hafsa tace "toh" ta shiga kitchen. tana fitowa ta wuce ɗakinsu ta ɗakko jottern da pen ta kaiwa Anty. Bayan Sallahr la'asar rana tayi sanyi Hafsa da Hajar suka shirya zuwa supermarket. dukkansu dogon hijab suka saka. a tare suka fito palour, Anty dake palourn tace "yawwa karku kai magrib and go to the nearest", Hafsa tace "tom" ta amshi list ɗin da kuma Atm card ɗin da Anty take miƙa mata. Hajar tace "sai mun dawo". suka fita Anty na jadda musu cewa kar su kai magrib. suna fita road kam suka samu Napep, Hafsa tace "wellcare", mai Napep yace "Haɗeja Road?", Hafsa tace "Eh". ya faɗa musu bill. Hafsa ta shiga snn Hajar. saida suka hau saman titi snn Hajar tace "Anty fa tace muje na kusa shine zamu tafi Haɗeja Road". Hafsa tace "kinga supermarket ɗin da suke kusa ba komai ake samu a nan ba, kinga gwara muje wanda zamu samu komai mu dawo da wuri". Hajar dai ta gyaɗa kai ba tace komai ba. 20minutes of a ride suka isa supermarket ɗin. bayan sun sauka daga Napep ɗin Hafsa ta basa kuɗinsa snn suka nufi entrance. suna shiga ciki Hafsa ta ɗauki shopping basket ta miƙawa Hajar. ta ciro list ɗin ta fara ɗaukan abinda ke rubuce tana sakawa a basket ɗin hannun Hajar. bayan Hafsa ta gama ɗaukan komai dake rubuce a list ɗin tace "yawwa, saura man ki", Hajar tace "mai na kuma?", Hafsa tace "yess Anty tace a siya miki mai da turare, na ɗaukar miki turaren man ne dai bansan wanda zai miki ba", Hajar tace "ɗaukar min mai gurguwa", Hafsa tace "wane irin mai gurguwa?, bari na ɗaukar miki irin wanda nake shafawa", Hajar tace "A'a nifa man nan naki be min ba sai kace ka shafa ruwa gashi kuma kayi ta gumi kamar kuturu", Hafsa tayi murmushi tace "toh shknn bari na duba miki wani amma banda mai gurguwa", Hafsa ta juya wajen creams ɗin, a tsanake take dubawa cause Hajar is fair in complexion, haskenta irin me pink ɗin nan ne bata so ta ɗaukar mata wanda zai ɓata mata complexion. Tinda suka shigo harabar supermarket ɗin yake kallonta ta cikin tinted glass ɗin motarsa dake parking space, da sauri ya buɗe motar ya fito yabi bayansu, wani yadi ne ajikinsa sky blue mai mugun kyau, kai kana ganinsa kasan kuɗi sunyi kuka, tinda ya shiga wajen shopping ɗin yake nemansu sbd sun ɓace masa. ya ƙanƙance ido yana tuna fuskarta da ya taɓa gani sau ɗaya. tabbas itace. Hafsa ta ɗauki wani cream mai kyau ta saka a basket tace "yawwa mun gama mu tafi". Hajar na juyawa shi kuma ya iso wajen. kallon aisle ɗin da suke yayi. kallonta ya ringa yi ba ƙiftawa. a hankali Hajar da Hafsa suka fito daga aisle ɗin suka nufi counter. suna zuwa aka lissafa kayan aka zuba a ledoji biyu. Hafsa ta ciro card ta miƙawa cashiern wajen. cashier tace "ai ya biya kuɗin" ta faɗa tana miƙawa wani gentleman dake gefensu card ɗinsa......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche { 20..} Idonsa akan Hajar ya karɓi card ɗin ya zura a aljihun gaban rigarsa yace "thanks", Hafsa ta kalli cashier tace "an biya kuma, waye ya biya?", cashier ta nuna mutumin da har lokacin yake tsaye a wajen tace "sir", a tare Hafsa da Hajar suka juyo suna dubansa, ido huɗu sukay da Hajar, Hafsah tace "but why?", baice komai ba ya ɗauki ledojin guda biyu yace "plxx let's talk outside" da haka ya nufi exit way. Hafsa ta dubi mutanen dake bayansu suna jiran su basu space suma a irga musu kayansu. hannun Hajar ta riƙe suka fita harabar supermarket ɗin. adaidai exist door ɗin suka gansa, Hafsa tace "bawan Allah bamu ledojin kayanmu", wani soft smile wanda ya sake feso da kyansa yayi yace "tom, gashi" ya miƙa mata ledojin. kin karɓa tayi ta miƙa masa Atm card tace "muje POS ka cire kuɗin ka", yace "No ba kyau mayar da hannun kyauta", Hafsa tace "toh sbd me zaka biya mana kuɗin shopping ba tare da sanin mu ba?", yace "plxx accept it, yanzu ai kun sani", Hafsa tace "malam kana ɓata mana lokaci, dan Allah ka bani account No ɗinka na dawo maka da kuɗin ka". murmushi yayi yace "A'a", Hajar da take jin duk abinda suke cewa ta yamutsa fuska tace "kinga bar masa kayan sai mu koma ciki mu ɗauki wasu" da haka ta riƙo hannun Hafsa suka nufi entrance, da sauri ya biyosu a baya with cool voice yace "Hajar". dakatawa Hajar tayi da tafiya a lokaci guda ta saki hannun Hafsa snn ta juyo ta zuba masa lulu eyes ɗinta. ya ciro ƴar ubansun wayarsa daga pocket ya danna kira. ƙarar waya ya fara fitowa daga jakar dake hannun Hafsa. Hafsa ta kalli Hajar snn ta ciro wayar ta miƙa mata. Hajar ta ringa kallon numbern dake kiranta wacca ɗazu da safe aka kirata da ita. a hankali ya katse kiran ya shafa kansa yana kallon fuskar Hajar yace "am Ahmad...", Hafsa ta kalli Hajar cike da mamaki tace "au daman kin san sa?", Hajar na kallon cikin idonsa tace "not at all, yanxu ma na fara ganinsa a rayuwa", jin zazzaƙar muryarta tayi beating eardrum ɗinsa ya lumshe ido, a zuciyarsa yace woww beautiful and tasty. Hajar ta juya ta cigaba da tafiya while her heart is palpitating rapidly. Hafsa ta juya zata bita, ya dakatar da ita da faɗin "alright muje a biya kudin kar na wahalar da ku, amma sure they will be next time". Hafsa ta dakatar da Hajar da take gaf da shiga wajen shopping ɗin tace "jirani anan bari ayi refunding kuɗinsa". Hajar ba tace komai ba ta cake a wajen ba tare da tayi kuskuren kallon inda take jin arwa akanta ba, tare dashi Hafsa ta koma ciki akai masa refunding kuɗinsa, ta amshi ledojin hannunsa tace "nagode". yace "is she your sister?", tace "sure, she's my maternal cousin", ya shafa kansa yace "ohk, amma dai ba baiko akanta ko?", Hafsa tayi shiru tana kallonsa kafin ta gyaɗa masa kai ta juya ta fita. bayanta yabi da kallo kafin shima ya fita, Hajar ta karɓi leda ɗaya a hannun Hafsa snn suka fita daga harabar supermarket ɗin. suna fita kam suka samu napep suka shiga. Ahmad ya shiga motarsa yana sauke ajiyar zuciya kafin ya zura key a ignition ya kunnata, bayan adaidaitan da ya ɗaukesu ya ringa bi har suka je inda zasu. a gaban idonsa suka sauka daga Napep, Hafsa ta biya kuɗin napep snn suka shiga gida. wani murmushi yayi ya daki steering motar snn ya lailayasa gami da juya kan motar. ya gammace ya haƙura da appointment ɗinsa da yayi loosing wnn babban opportunityn, he won't let go of this hot cake again. su Hajar suna shiga gida aka kira sallar magrib, Anty da take kitchen tana kwashe tuwo ta fito tace "saida dai ku kai magrib ko?", Hajar tace "abin hawa ne suke wahala Anty?", Hafsa ta ƙarasa cikin palour ta ajiye ledar hannunta. Hajar ma ta ajiye ledar hannunta snn ta shige ɗaki domin yin alwala. tana fitowa daga toilet ta shimfiɗa darduma ta kabbara sallah, Hafsa ce ta shigo itama ta shiga toilet tayo alwala ta fito. a gefen gado ta zauna tana kallon Hajar har ta idar da sallah. Hafsa tace "kin sansa ko?", Hajar ta cigaba da azkar ɗinta bata tanka ta ba, Hafsa tace "gashi nan yanada numbern ki". Hajar ta shafa addu'ar da ta gama snn ta kalli Hafsa tace "yaushe kika zama journalist ne?", Hafsa tace "dan Allah ki bani amsa". Hajar tace "alright, Eh na sansa amma ban taɓa ganinsa ba sai yau, Zainab ce ta bashi numbern ta, ɗazu da safe ya kirani ni kuma na saita masa hanya sbd nasan bazai taɓa samun abinda yake so daga gareni ba", Hafsa ta gyara zama tace "toh sbd me?", Hajar tace "inada wanda nake so", Hafsa tayi tsaki tace "au sbd kinada wanda kike so shine kike ƙoƙarin rejecting dinsa, wllh kinada matsala Hajar, ai ni dai a shawarce ba a riƙon saurayi ɗaya sbd may be ba shine zai zama mijinka ba, kuma suma samarin ba sa zama da girlfriend ɗaya wllh", Hajar ta miƙe daga kan dardumar tace "i won't double date gsky", Hafsa ta buɗe baki za tay magana Hajar ta katseta da faɗin "ki tsaya zance lokacin sallah ya wuce ki". da misalin karfe tara da ƴar mintina na dare kowa na gidan na zaune a palour, wayar Hajar ta fara ringing. ignoring call ɗin ta ringa yi sbd ta sha Ahmad ne, Anty tace "wai wayar waye wnn?", sai a lokacin Hajar ta kalli wayarta ta, ganin mai kiran yasa tayi saurin ɗaukar wayar a hannunta amma kuma ba tay picking ba. kiran na yankewa ta miƙe daga palourn ta nufi ɗakinsu Hafsa, Anty da Hafsa suka bi bayanta da kallo. Hafsa ta kalli Abdallah da yake jujjuya abincin gabansa, wato yau maƙiyinsa akai wato tuwo, ga Anty ta hana a dafa wata indomie, a hankali Hafsa ta fara dariya, Abdallah ya juyo ya kalleta ya haɗe jira yace "kee, meye haka?", ai kam ta sake tuntsurewa da dariya tace "ba komai yaya gani nai miyar taji busasshen kifi", tsaki yayi snn ya miƙe ya ɗauki kwanon abincin da bai ci ba ya wuce kitchen, Anty tace "ina zaka da abinci Abdallah?", yace "na ƙoshi", Anty ta ɗaga kafaɗa tace "shknn, wllh ka fiya tsirfa, naga da kana cin tuwon ai, Hafsa dafa masa indomien, sai yayi ta tsaho kamar wani zalɓe tinda haka ya zaɓa, amma mutum zai kwanta ba zai ci abu mai nauyi ba sai wata shegiyar indomie", Hafsa tace "tom" ta tashi ta nufi hanyar kitchen, tana zuwa kusa da Abdallah ta rage murya tace "ka turo 2GB ko nai maka mai uban yaji kuma na dafe ta", harara ya galla mata ya miƙa mata plate ɗin tuwon yace "ƙarasa dashi, zan turo miki 500MB in yayi miki, idan kuma bakya so shknn", Hafsa tace "Eh, turo amma zan gumbuɗa yaji" ta shige kitchen. Hajar na shiga ɗaki da sauri ta amsa kiran Nura da ya sake shigowa. tace "Assalamu alaikum" fuskarta ƙunshe da murmushi, yace "wa'alaykissam salam gimbiyata", tayi murmushi tace "ina yini", yace "lfy alhmdllh, ykk?", tayi twinking lulu eyes ɗinta gami da sukuwa kan gado tana rungume pillow a ƙirjinta tace "ina lfy alhmdllh, kaima ykk, ya aiki?", yace "alhmdllh, mun gode Allah", shiru tay bata ce komai ba, yace "ya jikin Baba?", tace "da sauƙi", yace "to masha Allah, Allah ya ƙara afuwa, insha Allah gobe zan shigo na dubasa", tace "tom, Allah ya kaimu goben", yace "Ameen, snn bayan isha'i kema zanzo", tace "ai yanzu bana gida", yace "kamarya bakya gida?, to ina kika je?", tace "ina gidan Anty Jamilah zan zaune a wajenta for the mean time", yace "okay, dole kam na biyo ki nan". tayi murmushi ba tace komai ba. ★Sa'adatu ce rakuɓe a soro ta ɓuya a bayan ƙofa, a hankali ta cire takalmanta ta rungumesu a ƙirji ta leƙa cikin gida, zaro ido tay waje ganin Huzaifa a bakin tukwanen ruwa yana ɗiba, ƙirji ta dafe tace "na shiga duba daman ya Naseer bai tafi ba", ta sake leƙawa sukay ido huɗu, Huzaifa yace "waye a nan?", wani relief taji da ta fahimci ba dodonta bane, tayi sauri ta ajiye takalmanta snn ta saka ta shiga ciki, karo suka kusa yi da shi. ya kalleta sama da ƙasa yace "ke daga ina kike?", tace "Maama ce ta aiken", ya kalli cikin idonta yace "nace daga ina kike?", ta murguɗa baki tace "to nace maka Maama ce ta aikeni gidan Balaraba..", gwaɓe mata bakin yayi har saida yayi jini yace "tin muna shaida juna ki gayamin daga gidan uban wa kike kafin na sumar dake", daddagewa tayi ta buɗe murya ta fara kiran Maama, afujajan Maama ta fito daga ɗakinta jin muryar shalelen ƴarta, Maama tace "Sa'adatun Maama kin dawo?", Sa'adatu ta ruga gabanta tace "Huzaifa ne", Maama ta kalli Huzaifa snn ta kalli Sa'adatu tace "me yayi miki?", Sa'adatu ta buga ƙafa a ƙasa tace "dukana yayi a baki, kuma Allah ya isana", Maama tace "duka kuma?, Akul Huzaifa karka sake taɓata", yace "ke ni kikewa Allah ya isa?, wllh saina kifar dake", Sa'adatu ta rakuɓe bayan Maama tace "Eh, mugu kawai". Maama tace "A'a Sa'adatun Maama yayanki ne fa banda rashin kunya", Sa'adatu ta cokalo baki snn ta shige ɗaki. Huzaifa ya sauke numfashi a hankali zuciyarsa na zafii. Maama tace "karka ɗauki halin Nasiru, ku ringa ririta ƴan ƙannenku, amma indai kuka haɗu dasu sai duka, haba don Allah..." ta juya ta koma ɗakinta. Washe gari tin ƙarfe takwas Huzaifa ya shirya komawa schl. ɗakin Baba ya shiga da ƴar jakarsa goye a baya yayi masa sallama, Baba yace "toh Allah ya kiyaye hanya, Allah yayi maka albarka", Huzaifa yace "Ameen Baba", Huzaifa ya fito daga ɗakin ya doshi na mahaifiyarsa, yana ƙoƙarin shiga ɗakin sai gata nan ta fito, ya durƙusa ya gaisheta yace "Maama ni zan koma", tace "Au kaima tafiya za kayi, jiya fa Naseer ya tafi", yace "lecture ta kankama ne", tace "toh, wai saura shekara nawa ne ka gama wnn jarababbiyar makarantar?", yace "saura shekara ɗaya insha Allah", tace "toh Allah ya bada Sa'a", yace "Ameen". Umma ta fito ɗakinta hannunta riƙe da tsintsiya da abin kwashe shara da ta share ɗaki, Huzaifa ya russunar da kai yace "Umma zan wuce", Umma tayi murmushi tace "Allah ya kiyaye hanya", yace "Ameen". Maama ta ƙunduma masa wani zagi tace "dalla malam fita". Huzaifa ya gyara zaman jakar bayansa snn ya fita. da yamma Umma ta fito ɗakinta tana zubawa wata yarinya da tazo siyan kulele, ta gama zuba kulelen a leda ta bawa yarinyar ta shiga ɗaki ɗakko mata canji, tana fitowa ta bawa yarinyar canji saiga dan Munkaila makwabcinsu nan ya shigo yace wai ana sallama a waje, Nabilah da take zaune tsakar gida tayi caraf tace "inji wa?", yaron yace "bari na tambayo" ya fita da gudu, ba jimawa sai gashi ya dawo yace "wai Nura ne". Nabilah tace "kace masa me za a basa", yaron ya juya kenan zai fita Mu'azzam ya fito daga ɗakinsu yace "tafi wasanka kaji", da sauri yaron ya fita Mu'azzam kuma yayi hanyar soro, Umma dai ta koma ɗaki. tare da Nura Mu'azzam ya dawo gidan, ɗakin Baba suka nufa. Nabilah ta taɓe baki tana kallon Nura sama da ƙasa. a hankali Nura ya cire takalmansa ya shiga ɗakin Baba da Mu'azzam ya yaye masa labule. ya durƙusa cike da ladabi kansa a ƙasa yace "Baba barka da yamma", Baba yace "barka dai samari", Nura yace "ya kufan jiki?", Baba yace "Alhmdllh", Nura yace "Allah ya ƙara afuwa", Baba yace "Ameen", Nura bai jima ba ya yiwa Baba sallama. wasu manyan ledoji da ya shigo dasu ya ajiye snn ya fita. tare da Mu'azzam suka fito. a soro suka tsaya Nura yace "Mu'azzam ka ƙi juyowa hadda ko?", Mu'azzam ya shafa kansa yace "A'a ya sayyadi haddar nan fa bazata shiga ba", Nura yayi murmushi yace "Allah ya ƙarawa Baba lfy", Mu'azzam yace "Ameen Ameen", Nura yace "toh sai anjima", Mu'azzam yace "A sauka lfy ya sayyadi". Nura ya wuce Mu'azzam kuma ya dawo gida. Maama da take rakuɓe jikin labulen ɗaki ta fito ta kalli Nabilah tace "wane wnn da naga ya shigo da manyan ledoji?", Nabilah tace "matsolon Hajara ne", Maama tace "ban gane ba?, wnn shine malamin naku?", Nabilah tace "malaminsu daii", Maama tace "Amma ku ka ce min faƙiri ne?, ji fa manyan ledojin da ya shigo dasu snn kuma ji suturar jikinsa", Nabilah tace "wllh faƙiri ne wani kuturun shagon chajin waya ne dashi fa, tsabar ƙanƙantar shagon mutum ɗaya yake ci, gashi kuma na katako, katakon ma duk ya ruɓe gara ta cinyesa tasss, gidansu ma ba kanta wllh, Babarsa ma ɗan wake take siyarwa", Maama ta sauke ajiyar zuciya har cikin ranta taji daɗi tace "Eh lallai uwarsa me siyar da ɗan wake ga uwar wacca zai aura me siyar da alalar gwangwani abincin yan wahala". Nabilah ta sheƙe da dariya tace "kai Maama", Maama ta gyaɗa kai tace "Allah kuwa". Sa'adatu ce ta fito tana latsa wayarta tace "Maama wai baki san Opay ba?", Maama tace "meye kuma Opay?", Sa'adatu tace "kayan haya mana, wnn kayan fa da kika ga ya saka ba nasa bane na aro ne, zuwa yayi aka ara masa don yazo yayi fafa, tin daga kan agogo takalmi hula da tsadaddiyar shaddar jikinsa wllh duk na aro ne", Maama ta sake sauke ajiyar zuciyar daɗi tace "nifa ince, ai daga gani ma kasan kayan na aro ne, ke har turaren ma da ya tsayamin a maƙogaro na aro ne koh?", Sa'adatu tace "kwarai ma kuwa". Maama tayi hanyar ɗakin Baba tace "bari naga wace tsiyar aka lafto a manyan ledojin", Sa'adatu tace "yawwa gano mana tsiyar". ba ko sallama Maama ta afka ɗakin, kallo ɗaya Baba yayi mata ya kauda kai. tamkar shege a rabon gado haka ta ringa kwalala ido har ta hango ledojin a gefe guda, a wulaƙance ta waftosu ta bankaɗa ta fara duba abinda yake ciki, saida numfashinta ya ɗauke ganin uban kayan, leda ɗaya fruits ne aciki harda Apple da pear, ɗayar ledar kuma kayan shayi. Baba baice mata komai ba ta gama bincika kayan snn ta miƙe ta fita zuciyarta na tafarfasa. Nabilah tace "Maama wace tsiyar ce aciki?", Maama tayi mata wani mugun kallo ta shige ɗakinta. ★A yammacin wannan rana Nurain ya fito daga room ɗinsa ya sakko down stairs zuwa part ɗin Mami, wata jumfa ya sanya coffee mai shegen kyau sai zuba ƙamshi yake, murɗa door handle yayi snn yayi sallama ya shiga, Mami na zaune tana shan red watermelon ita da Noor, Nurain yace "Mami zan je wajen Hajiya", Mami tace "Ohk, ka gaidamin ita da sauran mutan gidan", yace "tomm", Noor tace "yaya ka gaida Iron Lady", yace "Ohk". ya fita palour. katafaren compound ɗin gidansu ya fita, ya doshi parking space ya shiga motarsa, few minutes ya gama warming ya fita daga gidan bayan mai gadi ya buɗe masa gate yana ɗaga masa hannu. Slowly yake driving as usual yana sauraron qira'ar Sheikh Abdul Baseet. A ride of 15minutes ya isa gidan uncle ɗinsa Salisu, a bakin gate ya danna horn, parking motarsa yayi a harabar gidan snn ya nufi main building ɗin kansa tsaye. hannu ya kai ya danna bell ɗin door, babu jimawa mai aikin gidan ta buɗe masa, har ƙasa ta tsugunna ta gaishe sa, ya amsa ba tare da ya dubeta ba. da sauri ta shiga wata ƙofa dake palourn don sanar da ƴan gida. palourn ba kowa sai sanyin Ac da ƙamshin freshner mai daɗi. Nurain ya zauna a kan kujera ya ciro wayarsa a aljihu yana latsawa. few minutes kam saiga wata kyakkyawar mace nan ta fito sanye ta hijab har ƙasa, murmushi ne shimfiɗe a fuskarta tace "Nurain", Nurain ya mayar da wayarsa pocket ya russuna yace "ina yini Ummi", Ummi tace "lfy lou, yasu Maami da Noory?", yace "suna nan lfy", tace "toh madallah", yace "daman zuwa nayi na muku sallama jibi zan tafi India", tace "Au kuma ɗan uwanka na shirin dawowa next week kai kuma zaka tafi, toh Allah ya temaka ya bada abinda akaje nema", yace "Ameen, Hajiya fa?", Ummi tace "tana part ɗinta", yace "Ohk bari na shiga wajenta". ya tashi ya nufi ɗakin Hajiya........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche { 21..} A hankali Nurain yayi knocking ƙofar ɗakin Hajiya, da ga cike akace "waye ne?". Nurain ya haɗe gira snn ya murɗa ya shiga. tinda ya shigo Hajiya da ke zaune bisa lallausar rug ɗin ɗakin take kallonsa har ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin. Hajiya ta gwalo ido cikin ƙwamemen glasses ɗinta tace "O oho ashe Usuman ne, ai daman tinda naga abu kamar fel waya nasan kaine, angona ba sangameme bane irinka, ni ko yaushe ma zai dawo daga ƙasar can mai ƙanƙanra karfa ya daskare na shiga uku....", Nurain yace "su duk mutanen da suke rayuwa a ƙasar basu daskare ba sai shi", tace "A'a bar wannan zance ai su daman can ƙanƙarar ta gama musu illa sun saba", yace "shima ya saba aii", tace "inafa zai saba, shi da ba jinsin su ba, mutane kamar an bursuna musu garin filawa, angona da yake baƙi ai sam ba gami tsakaninsu, da zan samu jirgin da zai kai masa saƙo ai da na bada maganin sanyi an kai masa..", Nurain yace "toh ki kwantar da hankalin ki next week zai dawo", ta kallesa ta saman glasses ɗinta tace "Au shi Umarun ne zai dawo?, eh ai gara ya dawo kar ya daskare gsky, to kai wa ya gaya maka zai dawo?", Nurain yace "A waya mu kay magana", tace "Oh ni, babu yadda banyi da yarinyar nan Shatu akan ta kira min shi ba amma ta ƙi, yaufa wajen wata guda kenan ina fama da ja'irar yarinyar nan, yanzu kam tinda kazo maza kamo min shi na gansa..", yace "ki bari nan da mako mai zuwa zaki gansa a zahiri yanzu dare ne a can", kafa masa dattijan idanunta tayi ta saman glasses tace "Auu, kaima ja'irin ne kenan?", hade gira yayi yana pointing kansa yace "nine ja'iri Hajiya?", tace "yo ba gashi na gani ba, nace ka kiramin mijina kace min wai dare yayi sbd ka iya lafto ƙarya, ga rana gatsal-gatsal amma kana kiran dare..", gyada kai yayi yace "toh shknn, ni daman zuwa nayi muyi sallama jibi zan bar ƙasar", zaro ido tayi tace "zaka bar ƙasar kamar ya?, kaima garin arnan zaka koma?", yace "Eh", tace "amma dai ban taɓa sanin notin kan Muntari ya kunce ba sai yanzu, shine ya barka ka koma ƙasar arnan, har itama Khadijan notin kanta ya kwance wllh. kamar abin arziƙi ka doshi hanyar zama cikakken mutum sai kuma ka koma baya, da tini kaima da iyalinka dan ma yarinyar ta kasa ka, au koda yake ba jikana ta kasa ba wllh kanta ta kasa, eh shegiya ita taga duhu wllh dan har abada ta rasa nagartacce kamar jikana....", Nurain ya haɗiyi wani yawu cause his wound is still fresh yace "bari na kira miki angon naki", wayarsa ya ciro daga pocket ya kunna data ya shiga kiran Farooq video call. ba ta daɗe tana ringing ba Farooq ya ɗaga. Nurain yayi waving hannunsa a screen ɗin wayar yace "ba fa na ganinka, ka kunna haske Iron Lady ke son magana da kai", Farooq yace "Ohh really, seee yaah My bride" ya miƙe daga kan table ɗin karatunsa ya kunna Light, fuskarsa ta bayyana raɗau sbd haske, yau ma dai jibgegiyar sweater ce ajikinsa, Farooq yace "tana ina?", Nurain ya haska masa fuskar Hajiya, Hajiya na ganin Farooq tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un me ya kumbura ka haka sai kace wanda aka buga masa iska?", Farooq yayi murmushi sbd ba abinda yake gani sai fuskarta da kantamemen glasses ɗinta sun cika screen ɗin wayar. Hajiya tace "ka yiwa Allah da manzon sa ka dawo gida", Farooq yace "next week zan dawo amaryata", tace "Atoh ya dai kamata wnn kumburi haka..", Farooq yace "ba fa kumbura nayi ba rigar sanyi ce, bari na cire ki ga", da sauri ta katsesa tace "A'a karka cire ka daskare, tinda dai baka kumbura ba shknn", Farooq yace "toh shknn". tace "kaga wnn fel wayar wai shima ƙasar arnan zai koma sbd shegiyar yarinyar da zai aura ta gudu ta barsa shine ba zai nemi wata ba", Farooq was shocked da abinda ta faɗa amma yace "ni kam ina dawowa zan miki kishiya", tace "Eh maza ka dawo kayi min ai kishiya alheri ce indai ta gari ce..", yace "Au ba kya kishi na kenan?", tace "kaji wani zance yo wnn ai shine kishin", Farooq ya murtuke fuska kamar gaske yace "ni bani ɗan uwana", Nurain ya karɓi wayar don yanajin komai da suke faɗa. Farooq yace "so that's why you said until your heart heal?", Nurain ya gyaɗa kai yace "sure, and now it's healing..", Farooq yace "wish you all the best bro", Nurain yace "thank you i will call you tomorrow" ya katse kiran. ganin magrib na dosowa yasa Nurain ya yiwa grandmother ɗin tasa sallama, Hajiya tace "toh yanzu sai yaushe Usuman?, kaima shekarun zaka ɗauka kamar Umaru ko?", yace "A'a Hajiya, wata takwas zan yi insha Allah na dawo gida", tace "O oho har wata takwas ɗan nan, Allah ya tsare...", ta miƙe tana dogara sandarta ta shiga bedroom ɗinta, bayan wani lokaci ta fito da ƴar leda tace "ungo na kane kai kaɗai, karka tsamma kowa", ya karbi ledar yana leƙa cikinta yace "wai har takwarar taki?", tace "A'a ni ba takwarata bace, ni ba sunana Noor ba", yace "ai ɓoyewa akai, to Hajiyarmu khairan", Hajiya ta fara matsar kwalla tace "to Usuman ka kula da addininka don Allah", yace "insha Allah" da haka ya nufi door ya fita, saida sukay sallama da Ummi snn ya wuce. ★Tin safe Hajar take neman hanyar da zata sanar da Anty zuwan Nura, sau biyu tana attempting amma saita kasa, a zaune take akan stairs ɗin varendern palour, wayarta ce ta fara ringing, yamutsa fuska tayi ganin numbern dake kiranta, a fili tace "na shiga uku wai wnn wane irin naci ne", tana kallon wayar har kiran ya katse wani ya sake shigowa, 20+ missed call yayi mata daga safe zuwa yanxu, da kyar ta ɗauka ta wani sha kunu, daga ɗaya ɓangaren Ahmad yace "Assalamu alaikum", a wani daƙile tace "wslm", yace "how are you?", tace "fine", yace "alhmdllh, Hajar plxx just give me a chance to show my feelings", tayi gathering courage tace "don't you have anything else better to do?, I'll pretend that I didn't hear that", ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "you heard everything, you can't pretend that you didn't", ta ciji lower lip ɗinta painlessly dan sosai maganarsa ta shigeta, tace "i have to hang up....", pleadingly yace "plxx answer me before you hang up", kasa cewa komai tayi, shiru ne ya dauka har hakan yasa su ke jin breathing din juna, tayi twinking lulu eyes dinta tace "aiki nake yi", after few seconds yace "alright...", da sauri ta katse kiran ba ta jira sauran cewarsa ba. blocking numbernsa tayi snn ta goge call log ɗinsa gaba ɗaya, murya can ciki tace "Allah ya baka gaba Ahmad". bata da wani space a zuciyarta, Nura has already filled everywhere. knocking gate aka yi ta miƙe ta buɗe, su Hafsa ne suka dawo daga school, Hajar ta matsa musu hanya tace "barka da dawowa yan bokoko", Hafsa tace "na dai kusa gamawa", ƴar autar Anty kam tini ta wuce ciki tana fige hijab ɗinta. bayan Sallahr la'asar Hafsa ta shiga ɗakinsu tana dafe kai, Hajar da ke nannaɗe darduman da tayi sallah tace "lafiya?", Hafsa ta yamutsa fuska tace "kaina ke ciwo", Hajar tace "sannu kinsha magani?", Hafsa tace "A'a yanzu dai zan je wajen Anty na amso paracetamol", Hajar tace "okay, zauna na kama miki kan sai kuma kisha magana za kiji sauƙi sosai", Hafsa tace "tom" ta zaune gefen gado, gefenta Hajar ta tsaya snn ta fara kama mata kan tana hura mata addu'a, tana gamawa ta matsa thick vein ɗin goshin ta yarfe tace "toh ya kika ji?", Hafsa tace "wllh har ya lafa sosai" ta mike zata fita a ɗakin, Hajar tace "wajen Antyn zaki amso magani?", Hafsa ta gyaɗa mata kai, Hajar tace "dan Allah kice mata anjima zanyi baƙo", Hafsa tace "Au haba mutumin jiya ne zai zo?", Hajar tace "kinji ki da wani zance wai mutumin jiya toh bashi bane", Hafsa tace "toh waye?", twinking eyes Hajar tayi tace "Ya sayyadi na ne zai zo", Hafsa tace "wai daman har yanzu kuna tare da Nura?", Hajar tace "Eh, ai iyayensa ma sunje wajen Baba", Hafsa tace "kaiii amma shine baki fadamin ba, da yaushe zai zo?", Hajar tace "da yamma", Hafsa ta fita daga ɗakin ta shiga kitchen ta ɗauki pure water snn ta shiga room ɗin Anty, motsin ruwa taji a toilet, bedside drawer ta janyo ta fara neman Panadol tinda anan suke ajiye first aid drugs, ta dauke panadol ta ɓalli two tablets ta mayar da sachet ɗin. da kyar ta haɗiye maganin tana yamutsa fuska, Anty ta fito daga toilet tana gyara hular kanta tace "ku shirya ke da Hajar muje barkar Fauziyya", Hafsa tace "yanzu zamu?", Anty tace "Eh", Hafsa ta ɗaga ragowar pure watern da ta sha drug tace "Anty wllh kaina ke ciwo yanzu ma nasha magani, ko na bari ranar suna naje da yamma", Anty tace "tom shknn, kyaje ranar suna dama ba zuwa zanyi ba", Hafsa tace "tom, Hajar tace anjima za tay baƙo", Anty ta ciro kayan da zata saka daga wardrobe tace "ke ta aiko knn?", Hafsa tace "A'a wai bazata iya gaya miki ba", Anty tace "toh shknn, sai ta saukesa a sitting room, akwai semosa a fridge", Hafsa tace "tom" ta miƙe ta fita. Anty tana gama shiryawa ta ɗauki handbag dinta ta fita, ɗakinsu Hafsa ta shiga tace "toh sai Allah ya dawo dani", Hajar tace "Allah ya tsare", Hafsa tace "sai kin dawo". Biyar da rabi na yamma Hajar ta fito daga wanka, ta shafe jikinta da sabon cream ɗinta mai daɗin ƙamshi, riga da skirt ta saka na atamfa ta tsaya gaban mirror tana cakare ɗauri, Hafsa ta shigo tace "uhmm kinyi kyau, na gama soya semosan", Hajar na zizara kwalli a fatar manyan idanunta farare ƙal tamkar madara tace "nagode". wayarta dake tsuwwa ta ɗauka ganin me kira tayi murmushi tace "ina jin ma ya iso", kara wayar tayi a kunne tace "okay, gani nan fitowa", mayafin da ta fitar ta ɗauka ta yafa, Hafsa tace "laa ya naga kinsa mayafi ba Hijab ba, ko ba ustaz bane?", Hajar ta zabga mata harara tace "chab wai dan yana malamin islamiyya shine zai zama ustaz, wllh ba ruwansa indai zaki saka abinda zai rufe miki jiki to shi bashi da damuwa", Hafsa ta kalleta sama da ƙasa taga dai ruf mayafin da ta saka ya rufe mata jiki kuma ba shara shara bane, Hafsa tace "Eh, kinsan mazan ma kowa da ra'ayinsa, wani yafi son Hijab wani kuma mayafi wani kuma duka, wani kuma babu ruwansa indai za kiyi decent dressing is okay", Hajar tace "that's my Man shima decent kawai yake so", Hafsa tace "yana fa jira", Hajar tayi wasa da kwayar idonta tace "ai ya saba" ta ɗauki turare ta fesa sama sama. slowly Hajar ta fito compound ta nufi gate, ta bude ƙofa ta fita, yana tsaye jikin fillelen sabon motorbike dinsa yana danna wayarsa, yana ganinta yayi murmushi ya mayar da wayar aljihu, kallonta ya ringa yi ba ƙiftawa har ta ƙaraso, sosai silent kwalliyar da tayi da kuma decent dressing ɗinta ya tafi da imaninsa, sunkuyar da kanta tayi tace "sannu da zuwa", baice komai ba kawai kallonta yake, shirun da taji ne yasa ta ɗago kanta ai kam sukay ido huɗu, tayi sauri ta sunkuyar da nata tace "Bismillah ka shigo", yace "A'a nidae bazan shiga gidan mutane ba", tace "toh nan fa kan hanya ne", ya dubi street ɗin yaga akwai mutane yace "toh amma dai ansan da zuwa na dai ko?", childishly ta hararesa tace "Bismillah" ta juya ta koma ciki ba tare da ta jira cewarsa ba. bayanta yabi har suka shiga gidan tayi leading ɗinsa har sitting room. a kujera one seater ya zauna ita kuma ta zauna a two seater dake gefensa, Calmly tace "ina yini", ya ringa kallonta, ɗago kanta tayi jin bai amsa ba sukay ido huɗu, tayi pouting lips ta rufe fuskarta da palms ɗinta tace "dan Allah ka barii", murmushi mai sauti yayi yace "me fa?", tace "why are you staring at me?", yace "because i missed you so much and you look beautiful", murmushi tayi tana wasa da yatsun ƙafarta, yace "ba ki rubuta Jamb ba ko?", ta gyaɗa masa kai tace "Eh neco kawai na zana", yace "Ohk, suma yanxu school of Nursing suna amfani da jamb, gashi baki rubuta ba amma ba damuwa saiki rubuta next year ko?", tace "Admission din bazai samu ba saida Jamb result knn?", yace "Eh, ai da nasan sun canja tsari da sai kin zana jamb, kamar yanxu ne zaki ji an fara registration, and you're still young kinada enough time", tace "Ahh I'm not young", yace "ohk sai ki gayawa wanda bai sanki ba to me you're a little girl kuma you know akwai certificate of birth ɗinki a wajena", sallama akai a bakin ƙofa Hajar ta amsa, Hafsa ce ta shigo tana sanye da hijab hannunta riƙe da tray mai dauke da bottle water da drinks sai kuma plate ɗin semosa, a hankali ta ajiye trayn akan Centre table ta zauna kusa da Hajar, Hafsa tace "sannu da zuwa, ina yini", Nura yace "mun yini lfy?", tace "alhmdllh", yace "masha Allah, ya karatu?", Hafsa tace "alhmdllh", a hankali Hafsa ta miƙe ta basu waje tana fita ɗakin akay knocking gate, bakin gate ɗin ta wuce ta buɗe ƙofa, ita tasha ma Humaira ce ta dawo daga islamiyya amma me sai taga wani yaro, tace "ya akai?", yaron yace "wani mutum ne yace wai ana sallama da Hajar", tace "yana ina?", yaron yayi nuni da wata jugunanniyar mota dake gefen titi a parke, Hafsa ta kalli mutumin da ya fito daga cikin motar, zaro ido tayi sbd ta ganesa, shine mutumin da suka hadu jiya a supermarket, Ahmad ya ƙaraso bakin gate ɗin yana kallon Hafsa da itama take kallonsa cike da mamaki.......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche { 22..} Ahmad ya shafa kansa yana kallon Hafsa yace "Assalamu alaikum", har lokacin mamaki bai bar face dinta ba tace "wslm, ina yini", yace "lfy lou, kinyi mamakin gani na ko?", tace "dole, ince dai lfy bawan Allah?", numfashi ya sauke a sauƙaƙe yace "Ammm lfy", tace "Ohk" ta juya zata koma gida, da sauri yace "amm Hajar fa?" ya fada yana shafa kwantaccen beard ɗinsa, ta juyo tace "what about her?", yace "i came for her, help me by informing her", hannunta na riƙe da ƙofa tace "ohh, amma Hajar ba ta nan", mood ɗinsa ne ya canza lokaci guda yace "bata nan?", Hafsa ta gyaɗa masa kai cause that was the only way, yace "I'm sorry to invade her privacy, tana ina?", ta saukar da kanta ƙasa tana tunanin abinda za ta faɗa, few seconds passed amma ba tace komai ba, ya ringa kallon fuskarta with his cool voice yace "girl.., where is your sister?", ta ɗago ta kallesa sbd yadda yayi pronouncing girl ɗin tace "amm sunje unguwa da Babarmu", yace "Okay thank you, ai naga yamma ma tayi sosai, bari kawai na jirata...", ta katsesa tace "A'a karka jirata, ba yanxu zasu dawo ba", yace "toh sai yaushe?" yana kallon cikin idonta da rashin gaskiya ya bayyana ainun, hade gira tayi tace "A'a, nace fa ba yanxu zasu dawo ba, may be ma acan zasu kwana", Humaira ce ta ɓullo ta layin dake gefen gidan ta dawo daga islamiyya, sosai gaban Hafsa ya faɗi ganinta da tayi, Humaira ta tsaya tana kallonsu ko ƙiftawa babu sai kuma ta ƙaraso ta shiga gida, Hafsa ta sauke ajiyar zuciya tabi bayanta da kallo, rediyo me jini knn, tasan tabbas saita zayyanawa Anty abinda ta gani, Hafsa tace "sai dai ka dawo gobe", yace "No zan dawo anjima dai", tace "toh idan kuma basu dawo ba fa sun kwana acan", yace "No problem sai na dawo gobe, she worth it", tace "alright" ta juya zata shiga gida yace "wait", ta tsaya ba tare da ta juyo ba, yace "kinga kwa Cousin dinki tana bani wahala kema kina tayata ko?", tace "kamar ya?", yayi slight smirk yace "kin ƙi faɗamin whereabout ɗinta, and my heart keep saying that my Hajar is inside the house", Hafsa can't help it dole tayi slight smile ta juyo tace "really", ya gyaɗa kai yace "sure, young lady do you believe in fate?", sosai tambayarsa ta bata mamaki tace "Yess Noo", yace "hmmm, toh yess ne or No?", ta karyar da kai gefe tace "toh nidae a nawa view ɗin is No, a view din wasu kuma zance yess", yace "toh a ajiye naki view din a gefe a dauki na wasun, kema nasan bazaki so ki zama silar datse fate ba", kallonsa tay tace "sure bazan so hakan ba, abu guda ɗaya i promise you ni da kaina zan fito maka da Hajar amma not today, zanyi hakan ne dan na nuna maka cewa bazan datse fate ba..", kallonta ya ringa yi kafin yace "then when?", tace "sooner or later", ya gyaɗa kai yace "amma taya zan san lokacin?", tace "where is your phone?", wayarsa ya ciro a aljihu, a hankali ta fara karanto masa number yana lodawa, tana gama gaya masa tace "sau ɗaya zaka kira, idan lokacin yayi zan kiraka..." da haka ta shige gida ta rufe ba ta jira cewarsa ba. Ahmad yayi murmushi yana sauke ajiyar zuciya ya shiga motarsa, saida ya kira layin Hajar wajen sau uku amma bata shiga, tin ɗazu abinda ake ce masa knn. ƙarfe shida da minti sha biyar Nura ya miƙe daga kan kujera, ya ciro bandir ɗin ƴan 200 ya ajiye a hannun kujera, Hajar na ganin haka tace "kaga ka ɗauki kuɗinka", yace "toh ai ba ke na bawa ba, na Hafsa ne", ya fita a ɗakin tabi bayansa, a bakin gate ya tsaya yana kallonta yace "toh sai munyi waya", ta gyaɗa kai tace "toh", yace "toh shiga gida", ta juya ta shiga gida a hankali ta rufe ƙofa, sitting room ta shiga ta ɗauki kuɗin da tray ta fita, kitchen ta fara shiga ta ajiye trayn ta ɗauki glass cup mai ɗauke da ragowar lemon da ya rage tana murmushi, a hankali ta kafa kai ta moɗe lemon snn ta fito ta shiga ɗakinsu Hafsa, rafar kuɗin ta ajiye akan cinyar Hafsa dake gefen gado tana operating wayarta, ga Humaira a gefenta sai zaro idanu take tamkar ɓera a buta, Hafsa ta dubi Hajar da mamaki tace "meye wnn?", Hajar na warware ɗaurin dankwali tace "cewa yayi na baki", Hafsa ta zaro ido tace "na shiga uku Hajar shine kuma kika amsa", Hajar tace "tinda yayi niyya wllh ba yadda na iya", Hafsa ta ɗauki kuɗin tana juyasu tace "amma sunyi yawa wllh, ni ya zanyi dasu?", Hajar tace "nima ban sani ba", Hafsa ta kalli Humaira ta galla mata harara tace "na dai gaya miki, wllh kika kuskura kikai wata magana a gaban Anty sai na kira miki IT, yadda ya cinye wnn yaron acikin kwata kema haka zai miki", a rikice Humaira tace "dan Allah kiyi haƙuri wllh bazan ce komai ba", Hafsa ta hade gira tace "yawwa kin temaki kanki yarinya, tashi ki tafi palour ki kunna cartoon", a hankali Humaira ta miƙe tana murza ido ta fita, Hajar tace "ji muguwa, me yasa kike threatening dinta?", Hafsa tace "guess what?", Hajar tace "what?", Hafsa tace "wnn mutumin da muka hadu a supermarket ne yazo", Hajar tace "ban gane ba", Hafsa tace "ɗazu ne kina tare da Nura, bayan na fito daga wajenku naji ana knocking gate, ina buɗe gate na tarar dashi a ƙofar gida, ke ba kiga dagar da mukay dashi ba kafin ya tafi, toh shine Humaira ta ganni dashi a ƙofar gida, kinsan rediyo me jini ce yanxu saita rattaɓawa Anty a yimin wata fassarar ta daban", Hajar ta taɓe baki tace "toh taya ya san gidan nan?", Hafsa tace "ke zan tambaya", Hajar ba tace komai ba ta canza kayan jikinta ta fita ɗakin zuwa kitchen ta ɗora dinner. ★Washe gari da safe Umma ta hadawa Baba breakfast ɗinsa, tana zaune gefensa yana cin abincin a hankali tana masa fifita, ledar drugs ɗinsa ta janyo ta ɓalli wanda zai sha ta basa, Baba yace "Allah yayi albarka", tayi murmushi tace "Ameen", ya jinginar da kansa ga bango yace "wai ina Hajara ne?", Umma ta ajiye maficin hannunta tace "tana gidan Jamila", ya gyaɗa kai yace "toh ta dawo gida haka nan", Umma ta gyara zama tace "malam na fi son ta cigaba da zama a can, wllh yanxu gidan nan kunnenmu ƙanƙanra ba hatsaniya, Hajara ba hakuri gareta ba, kamar dage take indai aka taɓata saita rama, zamanta acan shine zaman lfy", Baba ya ajiye numfashi a hankali yace "a wnn marrar bazaka ɗauki nauyinka ka rataya a wuyan wani ba, ai a rayuwar nan zama inda Allah ya ajiyeka da kuma ƙarƙashin wnda Allah ya ɗaurawa nauyinka shine daidai, idan kana so ka zauna lfy da mutane to ka guji abin hannunsu. Hajar ta dawo gida yau ɗin nan", Umma tace "amma malam...", katseta yayi yace "kiyi abinda nace", a hankali tace "toh, insha Allah zata dawo", Maama ce ta bankaɗo labule da ƙarfi ba ko sallama ta antayo ɗakin, hannunta riƙe da wani kantamemen kofi da cokali, daga tsayen da take tace "malam ya kufan jiki?", ba tare da ya dubeta ba yace "alhmdllh", ta gallawa Umma harara tace "madara zan ɗiba zamu karya kumallo nida yara", Baba yace "toh ina kika ga madarar?", Maama ta geɓare baki tace "Auu malam jiya fa naga an kawo maka manya manyan gwangwanaye na madara da milo, kayan marmarin ma sai sun ruɓe ba za a kasafta ba, ya kamata a raba a bawa kowa rabonsa", Baba yace "anƙi a raba", hangame baki Maama tayi tace "toh ai shknn, toh a bamu madarar mu karya kumallo", yace "suma an hana, mai neman auren Hajara ne ya kawo, ita kuma da kike kira da shegiya toh wnn arziƙinta ne....", Maama ta gyara hular kanta da ta wani waskace gefe tace "toh shknn.." ta fita fuuu a ɗakin sai kace wata kububuwa. ɗakinta ta shiga tana hucii, Maimuna da take tsefe kitson attachment tace "Maama ina madarar?", Maama ta wurga mata ƙaton kofin hannunta a fusace tace "madarar gidanku, malama ki cire kuɗi a ƙugunki ki siya, uwar tsimilmila kawai", Maimuna ta taɓe baki ta cigaba da tsefe kitsonta, Nabilah dake haɗa kayanta masu datti da zata wanke tace "toh Maama ina kuɗin da yaya Naseer ya baki ne?, ki bayar a siyo mana ƙosai da gasara", Maama tace "baki da hankali, toh ƙosan ɗari biyar ma yayi mana kaɗan", Nabilah tace "toh wainar gero fa?", Maama tace "wllh an wulaƙanta ni, ina Sa'adatu na?", Maimuna tace "ta fita", Nabilah tace "wane ɗan abu kazan kasan ne ya wulaƙantaki Maama?", Maama ta sauke ajiyar zuciya tace "wai akan wata mushiyar madara ake min gori", Nabilah ta yamutsa fuska tace "daman ai saida nace miki kar kije amma kika biyewa Maimuna ƴar san banza, ai ga irinta nan", Maama tace "ke Maimuna wai ina Alhaj ɗin naki ne shi bazai kawowa mahaifin naki kayan dubiya ba?, ko baki gaya masa ba?", Maimuna tace "chab na gaya masa mana amma bana son yazo ruɓaɓɓen gidan nan gaskiya, da ace ma har yanxu Baban na asibiti da sai yazo, ko da yake baya nan ma ya tafi Abuja", Maama ta wangale baki tace "Allah, wato har Habuja yana zuwa?", Maimuna na taje figaggen gashinta wanda ya gama tsiyacewa tass sbd yawan saka attachment tace "uhmm ai yace idan ya aureni acan zamu zauna", Nabilah ta kwashi kayan wankinta tayi waje tana cewa "bamu gani a ƙasa ba". Maimuna ta ɗaga murya tace "oho miki dai, ƴar ciki baƙi kawai", Maama tace "muna fatan Allah ya mayar da ƙoƙo masaki". Maimuna ta miƙe ta tattara gashin attach ɗin da ta gama tsefewa tace "Ameen". Umma na fitowa ɗakin Baba ta shiga nata, wayarta ta ɗauka ta fara kiran ƴar uwarta, bayan sun gaisa Umma tace "ya yaran ya ɗawainiya?", Anty tace "alhmdllh Adda", Umma tace "Hajara ta shirya ta taho gida..", Anty tace "to sbd me Adda?", Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "wllh malam ne yace lallai lallai yau ta dawo gida, ba yadda banyi ba akan ya haƙura amma ya kasa fahimta, kuma wllh ni wani abun ma sbd shi nake, yanzu fa ba isasshiyar lfy garesa ba, idan Hajara ta dawo gidan nan sai anyi hatsaniya, ita fa ba a mata ta kyale, ga muƙarrabanta nan suma duk suna nan", Anty tace "toh shknn Adda, nida kaina zan dawo da ita, kuma zan ja mata kunne, amma dai nidae tinda tazo gidan da nake banga wata matsalar ba", Umma tace "uhmm ai hakuri ne yayi mata ƙaranci", Anty tace "ba damuwa zan mata nasiha, insha Allah da yamma zan kawota tinda mahaifinta yace ta dawo gida", Umma tace "toh sai kinzo Allah yayi albarka, a yiwa Kabiru godiya da ɗawainiya", Anty tace "laa ba komai Adda muma fa masu riƙe Hajar ne, sai anjima" ta katse kiran. ★Da misalin sha biyu da minti uku Anty na zaune palour Hajar ta fito daga ɗakinsu Hafsa ta shiga kitchen, fridge ta buɗe ta ɗauki ruwa ta sha snn ta fito, har zata koma ɗaki Anty ta kirata, dawowa tay ta zaune kan carpet tace "Anty gani", Anty ta ɗakko sababbin ƴan ɗari biyu dake gefenta ta miƙa mata tace "toh kema ga naki", Hajar ta ɗaga kai ta kalli kuɗin ta girgiza kai tace "A'a na Hafsa ne", Anty tace "ba zaki amsa ba", Hajar ta sunkuyar da kanta tace "ai Hafsa ya bawa", Anty tace "Eh naji Hafsa ya bawa, ita kuma Hafsa ta baki, ki amsa tin kafin rai na ya ɓaci", a hankali Hajar ta sa hannu ta amshi kuɗin ta ajiye kan cinyarta tana ganin aukinsu, kamar ma gida biyu aka raba su aka bata rabi, Anty ta gyara zama tana kallonta da kyau tace "Hajar", Hajar ta ɗago kai tace "Na'am", Anty tayi softening voice tace "Haƙuri shine babbar ribar zama da mutane, duk wani mai haƙuri yana tare da waraka da kuma wadata shiyasa hausawa suka ce mahaƙurci mawadaci, akwai laifin da za ai maka ka rama akwai kuma wanda za ai maka ka haƙura, ammafa wanda za kayi haƙurin ya fi riba, Hajar ki zama mai haƙuri daidai mitsali ba wai wanda zaki zauna a cutar dake ba, kinsan me yasa nace ki zama mai haƙuri", a hankali Hajar ta girgiza kai, Anty tace "yawwa, nasan kinada haƙuri daidai naki amma ina so ki ƙara akai, ɗazu mukay waya da Adda tace Babanki yace ki koma gida yau ɗin nan, toh anjima da yamma zan mayar dake, kinsan dalilin da yasa mahaifiyarki ta haƙura da zama dake ta kawo ki nan dai ko?, ki ringa jin duk abinda mahaifiyarki ta gaya miki, tin kina ƴar tatsitsiya take haƙuri da kishiyarta a haka dai rayuwa take gara mata cikin zaman doya da manja, babu abinda ya cita dan tayi haƙuri, amma ke kin ƙi haƙuri ki zauna lfy, kimin alƙawarin cewa bazaki shiga gonar ƴan uwanki ba, kuma bazaki biye musu ayi tashin hankali dake ba..", da kyar Hajar tace "toh Anty, wllh abinda suke min ne yayi yawa nida Umma...." nan ta shiga gayawa Anty irin abubuwan da siblings ɗinta suke mata. Anty ta sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya tace "Allah ya kyauta, haƙurin dai da nace shi zaki yi, ba abinda yake dawamamme wata rana sai labari, Wataqila ma ba zaki ƙara shekara ba a gidan zaki tafi naki tinda Allah ya baki manema sai dai fatan zaɓi na gari", Hajar tace "Toh Anty, nagode", Anty tace "yawwa, Allah ya yi miki albarka, tashi ki haɗa kayanki". Hajar ta kwashi kuɗin da suke kan cinyarta ta miƙe ta wuce ɗakinsu Hafsa, bata wani daɗe ba ta gama shirya kayanta tass, komai da komai ta haɗa, a ƙasan zuciyarta kam wani irin daɗi take ji zata koma gidansu wajen Ummanta. Da yamma kam suka shirya duk kansu harda Hafsa da Humaira, Hafsa dai bata ji daɗin wnn lamari ba, tinda mai Napep ya saukesu a daidai lungun ƙunshi Hajar take murmushi, Hafsa ce ta fara shiga gidan snn Humaira da Anty sai Hajar tare da almajirin da ya ɗakko jakar kayanta, da sauri Umma ta fito daga ɗaki tana musu brka da zuwa, Anty ta tsaya a tsakar gida suka gaisa da Baba dake zaune bisa darduma a ƙofar ɗakinsa, su Hafsa ma suka gaisa snn suka shiga wajen Umma. Hajar ta sunkuya gaban mahaifin nata tace "Baba barka da yamma", yace "ywwa Hajara", tace "ya kufan jiki?" yace "alhmdllh", tace "Allah ya ƙara afuwa" tayi zamanta nan kusa dashi. Sa'adatu ta leƙo ta ruɓaɓɓiyar windown ɗakin Maama tana yamutsa fuska tace "gayyar tsiya knn". Su Anty basu wani jima ba suka wuce gida, har bakin Titi Hajar da Sabra suka rakasu, Hajar ta kamo hannun Humaira ta damƙa mata rabin kuɗin da Antyn ta bata ɗazu tace karta gayawa kowa, bayan su Anty sun hau Napep sun wuce Hajar da Sabra suka koma gida. ★Washe gari Friday, a hankali Nurain yake sakkowa daga stairs, hannunsa riƙe da ƴar ƙaramar trolley da ya zuba kayansa, yayi matuƙar kyau cikin shigar ƙananan kayan da yayi all back, hakan sai ya sake haska caramel skin ɗinsa sosai, wata shegiyar Pcap black ya ɗora akan cikakkiyar sumarsa and that makes him to look younger than his age, Mami Noor sai Khausar da ta zo jiya ne zaune a main palourn, daman Noor da Khausar ƴan rakiyar airport ne, duk kansu Abaya suka saka ta Noor black ta khausar kuma maroon, Mami ta dubi ɗan nata tace "har ka fito Uthman?", a hankali ya ƙaraso kusa da ita yace "yeah Mami", Mami tace "toh ka yiwa Abba sallama naga time ya ja tinda jirgin 9am ne, yanxu gashi eight har ta gota". Majestically Nurain ya wuce palourn Abba, Abba ya fito daga bedroom ɗinsa yace "za ka wuce knn?", Nurain ya durƙusa yace "Eh Abba", Abba yace "wane zai kaika airport?", Nurain yace "Driver", Abba yace "toh Allah ya kiyaye, you call me right away after landing..", Nurain yace "insha Allah Abba" ya miƙe ya fita dan already takwas da minti goma ta gota, yana fitowa daga palourn Mami ta miƙe ta nufi part ɗinta, Nurain yace "Mami" sai kuma ya cire Pcap ɗin kansa ya ƙarasa gabanta, murmushi tayi ta shafa kansa tace "Allah ya tsare Son", baice komai ba ya rungumeta yana lumshe ido. har compound Mami ta raka sa, Noor da Khausar suka shiga back seats, Nurain ya kalli drivern da zai tuƙasu yace "bani key", ba musu drivern ya miƙa masa, ya san drivern baya gudu tinda dokar Abba yake bi, shi kuma yanxu sauri yake kar yayi missing flight, driver seat Nurain ya shiga drivern kuma ya shiga kujerar mai zaman banza, Garba da sauran ma'aikatan gidan na ɗaga masa hannu ya fita daga gidan, suna hawa saman titi Nurain ya take accelerator, ai kam few minutes of a ride suka isa airport, 9:05 dot jirginsu Nurain yayi take off, driver ne ya mayar da su Noor gida. Bayan minti goma da take off ɗin jirgin da zai tafi India jirgin da yazo daga Egypt yayi landing. a hankali passengers ɗin suke sakkowa daga matattakalar jirgin. wani murmushi Ruqayyah tayi bayan ta shaƙi iskar 9ja, a hankali ta ƙarasa fitowa daga airport ɗin bayan ta gama bin duk wasu procedures, wayarta ta ciro daga handbag ta kira bolt dake within her location. after 15minutes bolt ɗin ta ƙaraso, a boot drivern bolt din ya saka mata jakarta snn ya buɗe mata back seat ta shiga. location ɗin da ta gaya masa nan ya ringa bi, wani irin bugawa zuciyar Ruqayyah tayi da taga sun shiga street ɗin gidansu. a ƙofar gidansu tace ma mai bolt ɗin yayi parking, a hankali ta sakko daga motar, tayi masa transfer ɗin kuɗinsa, ya ciro mata jakarta daga boot snn ya shiga motarsa ya juya ya fita daga street ɗin. Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon gate ɗin gidansu, har lokacin wani irin bugu zuciyarta take tamkar zata bulluƙo, da kyar ta kai hannu tayi knocking a hankali.........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche { 23..} Har wajen minti biyar tana knocking amma ba wani respond, da ɗan karfi ta buga tana karanto duk addu'ar da tazo mata baki, mai gadi ne ya buɗe, idonsa duk a kumbure alamar bacci, bake bake yayi a hanya yace "wai waye ne?", Ruqayyah da bugun zuciyarta ya ƙaru tace "sallau bani hanya na wuce", zaro kumburarrun idanunsa yayi ya saki baki yana kallonta, lokacin guda kuma ya saki kabbara yace "alhmdllh, Allah mun gode maka da ka bayyana Hajiya ƙarama....", Ruqayyah ta yamutsa fuska tace "ba ɓata nayi ba sallau ƙasar waje naje", yace "barka da dawowa hajiya", da sauri ya matsa mata hanya, sai kace wacca take taka rurutaccen garwashin wuta haka take tafiya a ɗan madaidaicin compound ɗin gidan nasu, mai gadi biye da ita da jakar kayanta, ajiyar zuciya ta shiga jerawa da idonta ya kyallaro motar Daddy dake parking space, knn bai fita work ba, a bakin ƙofar shiga main building ɗin ta tsaya, mai gadi ya ajiye mata jakarta ya ƙara gaba. a hankali ta kai hannu ta murɗa handle ɗin ƙofar snn ta shiga ciki sai kace wata ɓarauniya, palourn ta tsaya ƙarewa kallo sai kace wani baƙonta, babu kowa sai motsin da take jiyowa daga kitchen. murya na rawa tace "Assalamu alaikum..." tana raba idanu. Momy ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe da Mug, wani irin kamewa tayi tana kallon ƴarta ta da wani weird expression, Ruqayyah tace "Mommyy.." sai kuma ta nufi Mahaifiyar ta ta da sauri da nufin rungumeta, Momy tana ganin haka ta juya ta koma kitchen fuskarta ba yabo ba fallasa, a take Ruqayyah ta fara shan jinin jikinta, kitchen ɗin ta bita ta tarar da ita tana kaɗa kwai, hawaye har ya ciko idonta ta ƙarasa gaban Momy tace "Momy... Please let me explain", banza Momy tayi da ita ta kunna gas ta ɗora kasko ta fara frying omelette, kusa da ita Ruqayyah ta matsa tana ƙoƙarin riƙo hannunta, da wani irin zafin nama Momy ta hankaɗa ta, Ruqayyah ta afka can jikin cabinet ragowar tafarfasasshen ruwan zafi a kettle ya kwararo mata a hannu, ƙara ta fasa sbd zafin ruwan ta shiga sosa wajen a gigice. Momy ko a jikinta ta cigaba da juya kwan da take soyawa a kasko. sink Ruqayyah ta nufa da sauri ta buɗe famfo ta shiga zuba ruwan sanyi a wajen da ta ƙone, ai kam ta ƙone sosai domin kwa wajen yayi jajur har fatar ma ta tattare. Ruqayyah ba ta sake gigin zuwa kusa da Momy ba, sai yanxu take ganin girman laifin da tayi, ita ta sha abun ba zai kai haka ba, wai Momyn ta ce ta ƙonata da ruwan zafi amma ko a jikinta, lallai akwai lukutar masifa, Momy ta gama haɗa komai na breakfast ta jera a tray snn ta fita kitchen ɗin. Bayanta Ruqayyah tabi ta zube a gabanta lokacin da ta ƙarasa palour, duk ka ƙafafuwan Momy Ruqayyah ta riƙe ta fara kuka tace "dan girman Allah Momy ki saurareni, wllh ban aikata hakan wai don bana son auren ba, ina son auren wllh, ki tsaya nayi miki bayani dan Allah...", Momy ta ajiye trayn hannunta akan kujerar da ke kusa da ita. Ruqayyah na ɗago kai ta ɗauketa da wani gigitaccen marii a kuncin dama, bata gama dawowa hayyacinta ba ta sauke mata wani a kuncin hagu har saida ta kifa, Ruqayyah da ke ganin wasu white stars na haskawa a idonta ta rushe da matsanancin kuka tace "na shiga uku Momyyy kin tsiyayar min da ruwan ido", Momy na huci tace "shut up Ruqayyah, dabba ma ya fiki tunani, are you mad da zaki zo kina cemin na tsaya kimin bayani?, bayanin uban me zaki min nonsense, wllh kika sake magana saina sumar dake Coward..." da haka Momy ta ɗauki trayn ta wuce part ɗin Daddy, Ruqayyah kuka take kamar ranta zai fita, ba ta taɓa tunanin abin zai dagule haka ba, ta ɗauka faɗa kawai za ai mata amma shine harda mugayen maruka, toh Momy ma knn inaga Daddy, da sallama Momy ta shiga palourn Daddy, Daddy da ke kallon news ya amsa sallamar yana nazarin expression ɗin fuskarta, Momy daurewa kawai take har ta gama serving ɗinsa abinci, Daddy yayi sipping tea yana kallon fuskarta yace "what happened?", remote control ta ɗauka ta ƙara volume tace "A'a, ba komai", yace "alright indai akan Ruqayyah ne ai jiya naje police station na shigar da report, yau ma zan koma naji ya ake ciki", Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk idan ka koma sai kasa ayi closing case ɗin cause Ruqayyah tana gidan nan yanzu haka..", bread ɗin hannunsa ya ajiye yace "Ruqayyah na gidan nan?", Momy tayi resting a jikin kujera tace "Eh, ba ta daɗe da shigowa ba, she's perfectly fine..", gyaɗa kai Daddy yayi ya cigaba da cin abincinsa yace "daman na gaya miki don't stress yourself about Ruqayyah's missing, gashi nan ta dawo aii..", Momy ta sauke numfashi a hankali har lokacin zuciyarta zafii take. saida Ruqayyah taci kukanta ta ƙoshi snn ta ja jiki ta shiga room ɗinta, toilet ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta tsaya a gaban mirror tana kallon fuskar, a hankali ta kai hannu ta shafa kuncinta inda ya kumbura da shatin yatsun Momy biyar ciff. fita tayi daga ɗakin ta kama hanyar part ɗin Daddy, da sallama ta murɗa handle ta shiga kanta a ƙasa, kallo ɗaya Daddy yayi mata ya kawar da kai, Ruqayyah ta zube nan kan carpet kusa da ƙafarsa tace "Daddy ina kwana..", without looking at her yace "lfy Ruqayyah, kinga dama kin dawo knn", shiru tai ba tace komai ba, Momy dake karkaɗa legs tace "fita malama, ban san ganinki...", Daddy ya ɗaga mata hannu yace "No leave her, Ruqayyah kin dawo ko?, toh shknn sannu da zuwa", hawaye ne ya zubo idon Ruqayyah ta ɗago kai tace "Daddy I'm very sorry...", yace "No Ruqayyah sorry for yourself, ke kikai loosing.." da haka ya miƙe ya shiga bedroom ɗinsa, Momy tabi bayansa da kallo snn ta miƙe ta fita palourn, da kyar Ruqayyah ta miƙe itama ta fita daga palourn, duk wani hope da karsashinta ya tsiyaye, sosai reaction ɗin Daddy ya dagargaza mata zuciya, toh da wnn action ɗin ai gara shima ya falla mata mari kamar Momy, jakar kayanta ta ɗauka ta shiga room ɗinta sai kace wacca kwai ya fashewa a ciki. ★Hajar ce tsaye gaban wardrobe tana jera kayanta, tana gama jera kayan ta linke Ghana most gon ta ɗaga katifar gado ta saka, tsintsiyar laushi ta ɗauka a bayan ƙofa ta fara share ledar ɗakin, tass ta share ta gyara ko ina, ta kunna turaren tsinke, zanin wanka ta ɗaura a ƙirji snn ta cire kayan jikinta, ta saka dogon hijab ta ɗauki kwandon soso da sabulu ta fita. Umma na yanka albasa cikin ƙullun alale, Hajar tace "Umma nazo na shafa miki manja a gwanayen?, tin ɗazu na wanke yanxu nasan sun bushe", Umma ta kalleta tace "ba wanka za kiyi ba?", Hajar tace "Eh wanka zanyi", Umma tace "toh jeki kiyi wankanki na karasa", Hajar tace "tom" ta wuce gaban tukwanen ruwa, bokiti ta ɗauka ta fara kanfatar ruwan tana zubawa. tana gama cika bokitin ta ɗauka ta wuce hanyar toilet, da gudu Nabilah da ta fito daga ɗaki tazo ta bangajeta ta shige banɗakin, Hajar tayi ƴar ƙara sbd bokitin ruwan da ya saukar mata a ƙafa, a fusace Hajar ta buɗe baki za tay magana sai kuma tayi shiru ta tsaya tana kallon ƙofar banɗakin, juyawa tayi ta dawo tsakar gida ta ɗauki kwandon da ta kife gwangwanaye ta ajiye kusa da Umma, ta koma ta ɗakko tasar manja da audiga suma ta kai gaban Umma ta ajiye, durƙusawa tayi ta fara shafa Manjan jikin tin, Umma tace "yawwa Hajara haka nake so, ko sun takaleki dan Allah karki kulasu", Hajar tayi murmushi tace "insha Allah Umma..", Umma tace "yawwa Allah ya yi miki albarka". sai bayan minti ashirin snn Nabilah ta fito daga toilet tana yatsine, ta kalli Umma da Hajar ta buga uban tsaki tace "annoba" ta shige ɗaki. Hajar ta miƙe ta sake ɗiban wani ruwan ta shiga wanka. Nabilah da ta shiga ɗaki ta dubi Sa'adatu tace "banza, wai ke Sa'adatu wane irin gigin bacci kike ne?, sai ki ringa tattaɓa jikin mutum sai kace wata ƴar yaye, wllh jiya da kyar nayi bacci duk kin ƙadabaibaiye ni sai kace wata ƙadandoniya, mtswww", wani shu'umin kallo Sa'adatu tayi mata tace "ina Maama?", Nabilah tace "ta tafi gidan Balaraba ita da Maimuna", Sa'adatu tayi wani murmushi mai ma'ana daban daban tace "Nabilah kina so ki samu mazajen kuɗi?", Nabilah ta zaro ido tace "so kai", Sa'adatu ta dafa kafaɗarta tace "wllh kizo na haɗaki da zeenatu da Mabaruka, zaki samu kuɗin a wajensu wllh tallahi..", Nabilah tace "Allah, aikatau zan musu?", Sa'adatu tace "lah lah lah ko ɗaya babu aikin da za ki musu, rayuwa irin ta wayayyun mata kawai zaku ringa yi, kiji daɗi ina gaya miki malam, kici mai kyau ki sha mai, ki kwanta a lafiyayyen gado fatarki ta sha raɓa, ga kuma uban kuɗi a aljihunki", Nabilah tace "toh wai mene rayuwar wayayyun matan?", Sa'adatu tace "rayuwar ƴanci knn ba ruwan mu da maza mu kaɗai mun ishi kan mu", Nabilah ta taɓe baki tace "mtswww, dalla malama ni ban fahimta ba", Sa'adatu ta hura hanci tace "idan kin yarda gobe zani gidansu saiki rakani kiga irin rayuwar da nake nufii", Nabilah ta gyaɗa kai tace "zanyi tunani". Bayan an sakko daga masallaci sallar juma'a Baba ya shigo gida tare da Mu'azzam, nan tsakar gida Baba ya zauna daga jikin inuwa. Mu'azzam ya durƙusa gabansa yace "Baba zan wuce aiki", Baba yace "har yanzu baku gama sakawa gidan tiles ba?", Mu'azzam yace "mun gama tarazo mukewa farfajiyar gidan", Baba yace "toh Allah ya temaka, ka kai Maimuna makarantar da nace ka mayar da ita?", Mu'azzam ya shafa kai yace "A'a Baba, ai ranar Litinin ɗin muna asibiti", Baba ya gyaɗa kai yace "toh jibi saika kaita", Mu'azzam yace "tom" ya miƙe ya leƙa ɗakin Umma yayi mata sallama snn ya fita. Baba ya ringa kwalawa Maimuna kira amma shiru, Nabilah ce ta fito tace "Bata nan sun fita da Maama", yace "ina Sa'adatu?", tace "tana ɗaki", yace "kira min ita", tace "tom" ta koma ɗaki, Sa'adatu sai gyatsine take tinda taji komai, Nabilah tace "Eh ai kinji dai ko?, saiki je". Sa'adatu ta fice fuu ta sha kunu, can gefen Baba ta koma ta rakuɓe tana zumɓuro baki, Baba yace "toh kema ki shirya jibi Mu'azzam zai mayar dake makaranta ke da Maimuna..", zaro ido tayi tace "Baba makaranta fa kace", yace "Eh, idan kuma ba kya son karatun saiki fito da miji na aurar da ke, itama Nabilah na bata lokacii..", Sa'adatu ta girgiza kai tace "wllh ni bana son aure, gwara na koma makaranta", Baba ya ringa kallonta kafin yace "tashi ki ban waje, saiki shirya ranar litinin...", bazar bazar ta koma ɗaki tana taɓe baki wai ita shagwaɓaɓɓiya. ★Raqayyah ta sake dialing numbern da tayi saving da dearest a wajen karo na ashirin tin dawowarta gida, abu ɗaya dai ake ta nanata mata wato the number you dial is switched off, wurgi tayi da wayar akan gado tana jin wani zafi a zuciyarta, she madly missed his stern voice, sound of his deep breathe out, komai nashi tayi missing sosai. lumshe ido tayi tana jin tsantsar kewarsa a duka sassan jikinta, maganarsa ta ƙarshe da tayi hitting eardrums ɗinta wacca she'll never forget ( sleep tight for today tomorrow in my arms), a fili tace "Soon dearest". towel ta ɗora a jikinta ta shiga wanka, ɗaure da towel ta fito tana tsane fresh fair skin ɗinta da hand towel, ta buɗe press ɗinta, ganin babu kaya aciki ta mayar ta rufe, ta tina ashe fa kayanta na ɗakin Momy acikin ɗaya daga cikin boxes ɗin lefenta, Abayar da ta cire ta mayar snn ta fita zuwa ɗakin Momy, a hankali tayi knocking ta shiga, ta tarar Momy ba ta nan don haka ta fara surveying ɗakin da idonta tana neman boxes ɗin lefenta. har press ta buɗe amma ba taga alamar akwatunan lefe ba, tana rufe press Momy ta shigo, Momy ta kalleta sama da ƙasa tace "kee me kike yimin a ɗaki?", Ruqayyah tayi gathering courage tace "amm Boxes ɗin lefe nake nema zan ɗauki kaya", wata muguwar harara Momy ta galla mata ta nuna mata wata box dake kusa da shoe shelf tace "ga kayan ki can, ba ki ma da hankali da kike neman wasu akwatunan lefe, toh kwananki biyu da guduwa muka mayarwa da Nurain kayansa..", da ƙarfi zuciyar Ruqayyah ta buga, ji tayi kamar ta fita daga ƙirjinta ta koma ciki sbd anan take jin bugunta, a lokacin idan akace mata ta haɗiyi zuciyarta ne to fa ba za tayi musu ba. lips ɗinta na zikiri tace "Momyy... wllh banji me kika ce ba, me aka mayar?".......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {24..} Momy ta ringa kallonta kafin tace "Au maimaita miki zanyi knn, kada Allah yasa kiji, take your belongings and leave my room idiot", Ruqayyah da har lokacin bata gama recover ba tace "Momy call me anything amma dan Allah ba a mayar da lefena ba ko?", tsaki Momy tayi ta janyo box ɗin kayan ta dire mata tace "hmmm, ƙarya zan miki, ko na taɓa miki ƙarya ne?", wani kuka ne ya kwace mata tace "A'a Momy, wllh baki taɓa min ƙarya ba", Momy ta haɗe girar sama da ƙasa tace "toh sai kuma me?, ba dai auren ne bakya so ba har da su guduwa?, toh everything was cancelled, ba wata maganar aure, tinda kin fi son ki zauna a gida nida ke muna haɗa kafaɗa toh shknn ai ga fili ga mai doki, waccan ɗakin dai kwalli ɗaya tak da shi kaɗai zaki tsira...", Ruqayyah ta sake rushewa da kuka tace "na shiga uku na lalace, Momy kun karanta lettern da na bari kuwa?", Momy tace "ai lettern taki ce tasa akay cancelling komai, ki ɗauki kayanki ki fita, mu dosa zama nida ke a gidan nan tinda haka kike so", da gudu Ruqayyah ta fice a ɗakin tana kuka sosai, Momy tace "Au kayan fa.", Ruqayyah na shiga ɗakinta ta zube a kan gado, kuka ta ringa yi kamar ranta zai fita, wai an mayar da kayan lefenta kuma anyi cancelling aurenta da dearest, sharce hawayen da ya jiƙa mata cheeks tayi ta janyo wayarta, dialing numbernsa ta sake yi, ai tasan dearest ɗinta bazai fasa aurenta ba, Momy da Daddy ne kawai suke zancensu, tinda tayi masa message tace ya jirata tana nan dawowa garesa ai end of discussion, kuma she's very sure ya yarda da ita, wasu twin tears ne suka zubo a cheeks ɗinta jin wanda take da hope a kansa har yanzu wayarsa switched off, sister ɗinta Kulsoom ta shiga kira, Kulsoom na ɗagawa Ruqayyah ta fashe mata da kuka tace "na mutu na lalace sister..", a rikice Kulsoom tace "Ruqayyah kina ina?", Ruqayyah tace "am home sister, ina gida, ina cikin lukutar masifa da bala'i", Kulsoom ta sauke ajiyar zuciya don ba ƙaramar firgita tayi ba tace "toh wace masifa kuma?, tinda kinga dama kin dawo gida ai shknn", da muryar kuka Ruqayyah tace "mayarmin fa da kayan lefena sukai kuma wai anyi cancelling aurena da dearest..", tsaki Kulsoom tayi tace "ke dalla malama kin cika min kunne, uban wa yace kice ba kya son auren, ai abinda kike so akai miki", Ruqayyah ta zaro ido tace "billahillazi la'ilaha illa huwa ni bance bana son auren ba, wllh bance haka ba..", katseta Kulsoom tayi tace "dakata malama, kinsan irin baƙin fenti da kikai mana kuwa?, kin san irin kunyar da kika bamu kuwa, har yanzu tabon abinda kika aikata bai goge ba, dan wulaƙanci kuma kika kashe wayarki, da farko ma dai ina kika je?", Ruqayyah ta haɗiyi wani ɗaci tace "Egypt naje", Kulsoom tace "au ƙasar ma kika bari, toh me ya kaiki Egypt?", Ruqayyah tace "later zan miki bayani sister, ni yanzu so nake ki tayani bawa Momy da Daddy haƙuri don Allah su bar maganar cancelling auren nan", ta rushe da matsanancin kuka tace "wllh i can't imagine me loosing Nurain, na shiga uku na lalace, help me sister..", Kulsoom tayi tsaki tace "lallai Ruqayyah surely you need a Psychiatrist don kwakwalwarki ta taɓu..", Ruqayyah tace "naji ko ma me zaki ce kice nidai ki temakamin", Kulsoom tace "ehmm toh ki kira ya Aysha wataqila ta taimaka miki nikam I can't face our parent da maganarki, sai anjima girki nakewa mijina..", ƙif ta kashe wayarta, Ruqayyah ta ringa kallon screen ɗin wayar baki buɗe. kamar wata marainiya haka ta koma ta kwanta tana hawaye, saida akay Sallahr magrib snn ta tashi tayo alwala tayi sallah, zaune tayi kan prayer mat ta rasa abinda ke mata daɗi, ƙarfe tara da rabi na dare ta tashi ta fito palour, kitchen ta shiga sbd ta samu wani abun ta zuba a cikinta, tin abincin jirgi babu abinda ta sake ci ko ruwa ba ta sha ba, kwata kwata ma bata da wani appetite, fridge ta buɗe tana neman koda fruit ne, ai kam dai babu fruit, glass cup ta ɗauka ta bude fresh milk, rabin cup ta zuba snn ta mayar da bottle din madarar fridge, sai kace mai shan maganin haka ta ɗaga ta kwankwaɗe tana yamutsa fuska, har wani amai ne ke taho mata. room ɗinta ta koma ta kwanta tana jin kanta na juya mata, har dare ya raba babu alamar bacci a idonta, kawai tunanin moment ɗinta da Nurain take, idan ta tuna cewa wai an mayar da lefe kuma an fasa aure sai hankalinta ya ɗugunzuma. sai wajajen Asuba snn bacci ɓarawo ya figeta. ★Washe gari Sa'adatu ta cakare kwalliya cikin matsattsun kayan da ta saba snn ta zumbula hijab har ƙasa, ta dubi Nabilah dake saka riga tace "wllh kin fiya nawa Nabilah, tin ɗazu baki shirya ba", Nabilah tace "ke Malama sauri fa nake yi", Maimuna tace "Sa'adatu nima na shirya mu tafi tare.." haɗe gira Sa'adatu tayi tace "A'a yi zamanki ban gayyace ki ba", Maimuna ta taɓe baki tace "ku kuka ga duhu da kunje dani da ni zan biya kuɗin Napep zuwa da dawowa", Sa'adatu ta yatsine fuska tana mata kallon hadarin kaji tace "ji faƙiriyar talaka, ni za kice zaki biyawa kuɗin Napep, mtsww dalla can riƙe tsiyarki, ke daman ba cin arziƙinki ake ba uwar mammaƙo kawai...", Maimuna tace "A'a kinga malama karki gayan ba daɗi mana, tinda kince dai ba zaki dani ba ai shknn magana ta ƙare". Sa'adatu tace "kin samawa kanki salama kuwa". Maama ce ta shigo da kwanon abinci tace "kai jama'a har sai rana tayi zafi baku tafi ba", Sa'adatu taja dogon tsaki tace "wllh Nabilah ce, sai kace ba ƙaruwarta ba, tayi abu da jiki sai wani salalo-salalo take kamar dodon koɗi", Nabilah tace "kai jaraba nagama mu tafi" ta zaro takalminta daga karkashin gado tana kwamawa, Maama tace "ke Nabilah dan Allah ki tsaya ki musu abinda suke so kema ai kya fito gari, ɗan kuɗin nan ki ringa samu muma ki tsammana, karki musu kauyanci da gidahumanci da sakarci", Nabilah tace "idan abin baifi ƙarfina ba zanyi", Maama tace "yawwa ku salallaɓa ku fita karku bari malam yaji motsinku". tamkar munafukai haka suka fita ɗakin suna tafiya a hankali. Hajar da ke tsakar gida tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kai ta cigaba da abinda take. bakin titi suka fita suka tsarar da Napep, Sa'adatu ta faɗi unguwar da zai kaisu, mai Napep yana cewa zashi ba wani ciniki Sa'adatu ta shiga, Nabilah tabi bayanta tace "ba kuyi ciniki ba", mai Napep yace "kuɗin ku dubu ɗaya ne", Nabilah ta zaro ido za tay magana Sa'adatu tace "Allah ya kaimu lfy", suna hawa saman titi Sa'adatu tace "sai munje zaki fahimci me nake nufi..", Nabilah dai tace "uhmm". tafiya mai nisa sukay suka isa unguwar da zasu, a bakin wani annakakken gida suka sauka, Sa'adatu ta fello duba ɗayar mai Napep ta basa. wani lafiyayyen gida suka shiga, Nabilah sai kalle kalle take, Sa'adatu ta riƙe hannunta har suka shiga cikin gidan. direct wata ƙofa Sa'adatu ta murɗa sai gasu a wani katafaren palour. Zeenatu da ke zaune kan sofa tana cin cake ta juyo jin ƙarar ƙofa, zaro ido tayi ganin Sa'adatu, ta taso da sauri ta rumgumeta tace "nayi masifar kewarki baby", Sa'adatu tace "nima haka, ina baby Mabruk?", Zeenatu tace "tana ɗaki tare da Teema", Sa'adatu tace "hegiyar kati yaushe tazo?", Zeenatu tace "jiya, wace wnn?" ta nuna Nabilah, Sa'adatu tace "mu shiga daga ciki nayi miki bayani". Zeenatu ta nunawa Nabilah kujera tace "zauna ga guri", Nabilah ta zauna tana kallon damfareriyar TVn dake palourn, kitchen Sa'adatu ta shiga ta jibgo kayan ciye ciye tray guda, a gaban Nabilah ta girke tana mata wani shegen murmushi. Nabilah ta ringa kallon kayan ciye ciye yawunta na tsinkewa. kusa da Zeenatu Sa'adatu ta zauna ta ɗauki cake ɗin da take ci ta kai baki, Zeenatu ta rage murya tace "itama ƴar hannu ce?", Sa'adatu tace "ke ƴar uwata ce fa, sabuwa ce fil a leda", Zeenatu tace "Allah itama ta amince ta shiga ƙungiyar tamu?..", Sa'adatu ta dubi Nabilah tace "Eh, ta amince", Zeenatu tayi wani makirin murmushi tace "gaskiya ni zan buɗeta daga kwali, bari na jarabata", Sa'adatu tace "toh", Zeenatu ta miƙe tana gyara kwalar rigar da ta bayyana rabi da kwatan ƙirjinta tace "baiwar Allah ya sunanki?", Nabilah da ke yagar naman kaza tace "Nabilah", Zeenatu tace "wow sunanki yayi min daɗi, taso muje", Nabilah ta ajiye naman hannunta tace "ina?", Sa'adatu tace "wai me Maama ta gaya miki ne, bafa cinyeki za tayi ba aikinki zata nuna miki". Nabilah ta miƙe tabi bayan Zeenatu suka shiga wani ɗaki. ko minti goma ba suyi da shiga ba Nabilah ta fito a fusace hannunta riƙe da gyalenta, Sa'adatu ta saki cake ɗin da take ci ta miƙe tsaye ganin Zeenatu ta fito itama a fusace, a hasale Zeenatu tace "ki fita da wnn bagidajiyar daga gidan nan Sa'adat idan ba haka ba nasa karnuka na su yagalgala namanta", Sa'adatu ta dubi Nabilah da ke huci jikinta na kyarma a hankali tace "mene haka Nabilah?", a hasale Nabilah ta ɓarka mata ashar snn ta wuce fuu ta fita daga palourn. da sauri Sa'adatu tabi bayanta, wani uban sauri Nabilah take zabgawa har ta doshi gate, tana fita waje tabi layin tana tafiya zuwa bakin titi, Sa'adatu biye da ita har suka ƙarasa main road. babu wanda yace da wani uffan har aka saukesu a bakin lungunsu, Nabilah na fita ta shiga lungunsu da sauri, Sa'adatu ta biya kuɗi snn ta biyota, adaidai ƙofar gida Sa'adatu tace "kin san bazaki iya ba shine kika zubar min da mutunci da kima", a karo na farko Nabilah tace "mutuncinki da kimarki duk sunci abu ta kaza kazan su, da ke da ƙawayen naki duk mahaukata ne ƴan iska tsinannu, dabbobi kawai, jakai marasa ilimin addini bare na boko..", Sa'adatu ta mulmulo ashar tace "jar bala'i daga temako shine kike zagina", Nabilah tace "an zage kin kiyi abinda zaki.." ta wuce cikin gida a fusace. da gudu Sa'adatu ta bita ta cakumota a tsakar gida, Nabilah ta juyo ta wanka mata wani mari na bazata, habawa ai hannun Nabilah bai gama leveling ba Sa'adatu ta ɗaga nata itama ta wanke ta da mari, lokaci guda suka kaure da dambe, Umma da tin shigowarsu take kallonsu tana daga tsaye inda take kwashe kaya akan igiya tace "kai ku bari mana..", Maama ta fito da sauri tana tafa hannaye ta shiga raba su, dambe kawai suke ba ji ba gani, Hajar dai na tsaye daga bakin ƙofar ɗakin Umma tana kallon ikon Allah, saida zanin Maama ya kwance garin raba faɗa amma basu saduda ba, Maama faɗi take "ba zaku bari ba, ke Sa'adatu bari mana, Nabilah ba magana nake miki ba, ku bari nace, ku wuce ɗaki kuyi acan cikin sirri...", Maimuna ma dai ƴar kallon ta zama tana dariya ƙasa ƙasa, ba wai su ƴan uwa ba aka wareta aka ƙi tafiya da ita ai gashi ba aje ko ina ba ta jagwale musu. da kyar Maama ta ɓamɓaresu tace "hauka kuke, mene haka?", sai huci suke suna kallo juna sai kace wasu maƙiya ba waɗanda suka fito ciki ɗaya ba, Sa'adatu ta goge bakinta da ke fitar da jini tace "wllh saina rama", Nabilah tace "idan kin fasa baki haifu ba", bangaje Maama Sa'adatu tayi ta cakumo Nabilah, damben da yaci uwar na farko suka ɓarke dashi, har ƙasa Nabilah ta yaga zumbulelen hijab ɗin Sa'adatu, takaici yasa Sa'adatu ta kama doguwar rigar Nabilah ta dire mata ita har ƙasa, cikin bacci Baba ya jiyo hanyaniya, fitowa yayi ya tsaya yana kallonsu. ɗakinsa ya koma ya ɗakko carbi, yana fitowa ya nufesu ya shiga tsula musu a jiki, ai dole suka rabu sbd zafin carbin, da hannu Baba ya nuna su yana so yayi magana amma wani tari ya sarƙesa, tamkar zai fitar da ruhinsa haka yake tarii, Umma tazo ta janyesa ta shiga dashi ɗaki. Maama da takaicin ƴaƴan nata ya turnuƙeta tace "abinda ku ka tarka knn?, ciwon zuciya za ku samin iyee?, dambe sai kace karnuka, me ya haɗa ku?", Nabilah da ta cukuikuiyo rigarta da ta ɓarke tace "wai wnn mahaukaciyar yarinyar shine ta kaini wajen tumakan ƙawayenta har suna ƙoƙarin taɓamin jiki...", Sa'adatu tace "ƙarya take munafuka, mai kai a tukunya kawai, wai fa aikinta za a nuna mata shine ta fara hauka da ballagazanci", Maama ta riƙe haɓa tace "mu shiga ɗaki karku tonawa kanku asiri a bainan nasi a tambara min ku, ku wuce ɗaki", Maama ta haɗa kawunansu ta turasu ɗaki. ★A hankali Hajar take cin abincin da ke gabanta, yamutsa fuska take cike da rashin jin daɗi sbd lower abdominal cramp da ke damunta, tin safe ta tashi da ciwon gashi har dare bai dena ba saidai yana lafa mata time to time, abincin ta ture ta sha ruwa ta haye gado ta kwanta gefen Sabra, Umma ce ta shigo ɗakin, ganin Hajar ta kwanta ga ragowar abincinta nan bata cinye ba ta kira sunanta, Hajar ta miƙe zaune tinda ba bacci take ba tace "Na'am..", Umma tace "ya baki cinye abincin ba?", Hajar na yamutsa fuska tace "na ƙoshi", Umma tace "ya ciwon yayi sauƙi?", girgiza kai Hajar tayi tace "A'a", Umma tace "toh taso muje chemist tinda yaƙi lafawa gwara ayi miki allura kawai", zaro ido Hajar tayi tace "Allah bana son allura, magani zan sha", Umma ta ringa kallonta kafin tace "toh bari na kira Mu'azzam sai ya taho miki da magani" ta ɗauki wayarta ta kira Mu'azzam, yana ɗagawa tace "kafin ka shigo gida ka biya ta chemist ka siyowa Hajara magani", yace "wane iri?", Umma ta kalli Hajar snn ta mika mata wayar tace "fada masa sunan maganin da kike sha ɗin", Hajar ta amshi wayar ta gaya masa. bayan kamar minti sha bakwai sai gashi nan ya shigo da maganin, tinda Hajar tasha magani ta samu relief, daman duk month sai ta samu cramp though ba ta flowing heavily amma dai abin na wahalar da ita. washe gari kam sumul ta miƙe ta fara harkokinta, yau dai kam Baba ya fita aiki, Umma kuma ta shirya zuwa Wajen Iya don haka Hajar ta bari a gida, Hajar na zaune tsakar gida akan kujera tana cin gyaɗa, Sabra ta shigo tace "Adda zan ci abinci", Hajar ta tashi ta zuba mata taliyar hausa da manja da yaji tinda ita ta dafa, Sabra ta amshi abincin ta wanko hannunta ta zauna tana ci. Hajar tace "ki yi sauri lokacin islamiyya ya kusa", Sabra tace "toh" ta cigaba da zuƙar taliyarta cike da yarinta. Maimuna ce ta fito daga ɗaki da ɗaurin ƙirji sai kace wata tsohuwar guzuma, kan Sabra da ke cin abinci ta tsaya tace "ke je ki wajen Iliya mai awo ki aunomin shinkafa ƴar hausa gwangwani huɗu" ta faɗa tana miƙa mata kuɗin hannunta, Sabra tace "toh bari na ƙarasa cin abinci", fatali Maimuna tayi da kwanon abincin tace "kee ni sa'ar kice ko sa'ar uwarki da zan aikeki kice sai kin gama cin abinci", Sabra ta sunkuyar da kai tana hawaye ta ƙi amsar kuɗin, damƙota Maimuna tayi ta miƙar da ita tsaye ta kifa mata mari tace "ba magana nake miki ba", ɗaure fuska Hajar tayi tamkar wacca bata taɓa murmushi ba tayi wurgi da gyaɗar da take ci. gam ta riƙe hannun Maimuna da ta ɗaga zata sake saukesa akan fuskar little sister ɗinta......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {25..} Maimuna ta wancakalar da hannunta tace "dalla malama cikani", Hajar bata tanka mata ba ta fizge ƙanwarta da ke kuka sosai, hawaye ta share mata tace "je ki wanke fuskarki, zan zuba miki wata taliyar, yi sauri kinji yarinyar kirki kar ayi miki dukan makara a islamiyya", a hankali Sabra ta wuce bakin rariya, Hajar ta ɗauki ledar gyaɗarta ta zauna ta cigaba da ci, baki buɗe Maimuna ke kallonta kafin ta mulmulo ashar tace "kut melesi, ke shegiya Hajara ina ruwanki dani, ina yiwa ƙanwata hukunci za ki shiga, ke asu wa iyee?, shegiya da ke kawai ƴar gaba da fatiha..", Hajar da zuciyarta ke tafarfasa hundred degree celsius ta mike tana kallon Maimuna, ji take kamar ta fizge tsumman zanin da tayi ɗaurin ƙirji dashi saita nuna mata aikin shegantaka da hujja, da sauri ta shige ɗaki zuciyarta na zafi don tabbas in ta tsaya zata iya waskatarwa da Maimuna mummuƙe. Maimuna ta koma bakin ƙofar ɗakin tace "ashe dai tsoro ne, da ki tsaya mana ki ga yadda zan yagalgala ki, da saina waskace miki ƙugun nan mai zubin na ƴar duniya, shegiya nunar rana...", Hajar kam zama tayi kan leda ta dafe kanta, calming kanta kawai take cause tana so tayi keeping promise ɗin da tayi, wllh ba daban promise din ba da sai ta gayawa Maimuna maganar da har ta mutu bazata manta da ita ba. wai itace shegiya nunar rana mai ƙugun ƴan duniya duk ita kaɗai, shiyasa bahaushe yace muni tudu ne ka taka naka ka hango na wani, wai har Maimuna ce za tace mata nunar rana ita ba taga kanta bane ai tafi kama da nunar rana tinda itace me bleeching irin na ƴan tasha iya fuska, kuma ƙugu ta godewa Allah yafi nata da yake flat sai kace an ɗaurawa muciya zani, gsky ita fa an mata katsalandan a al'amura, itafa haƙurinta bai kai nan ba wllh, bai kai gejin da za ayi mata rashin mutunci ko a gaya mata magana ta haƙura ba, amma dai yau Maimuna taci darajar masu daraja, ita kaɗai ta ringa sauke ajiyar zuciya tana huci, har Sabra ta shigo tayi shirin islamiyya tace "Adda zan tafi", Hajar ta ciro 20naira a bayan wayarta ta miƙa mata tace "toh ga kuɗin makaranta", Sabra ta amsa tace "na tafi" ta ɗau jakarta ta fita. Hajar ba ta sake fita tsakar gida ba, wayarta ta janyo ta buɗe data ta shiga whatsapp, yaushe rabon da ta shiga ita chatting bai dameta ba, saida tayi upgrading Whatsapp ɗin sbd ya zama outdated, ai kam ga unread messages nan rututu daga friends ɗinta na islamiyya da boko, message ɗin Zainab ta gani a sama ƙasansa kuma na Hafsa, tana gama karanta message ɗin Zainab ta taɓe baki ta shiga mayar mata da reply tinda online take, Zainab tayi mata reply da "Hajar kiji tsoron Allah daga tambayarki mutum sai kice kin saita masa hanya", Hajar ta yamutsa fuska bayan ta karanta ta rubuta mata "uhmm ke nifa ban ma basa fuska ba, na gaya miki ya sayyadi ya maye ko ina". Zainab ta turo da steaker ta duka. murmushi Hajar tayi ta rubuta "ban jin duka, malama ki canza topic, bana son wnn zancen", Zainab ta turo "Allah ya bawa mai sonki haƙuri", Hajar ta tura mata "Ameeennnn.." sosai chatting ɗinta da Zainab ya sanyaya mata zuciya, sai bayan sallar la'asar Umma ta dawo gida, Hajar ta mata sannu da zuwa tace "ya hajiya Iyalluwa", Umma ta mata daƙuwa tace "in kinje kya kirata da Iyalluwa, me kika dafa da rana", Hajar tace "taliyar hausa da manja", Umma ta cire hijab ɗinta tace "waii wnn ba cimar malam bace, tashi ki tankaɗen gari na ɗora tuwo", mikewa Hajar tayi tace "maƙiyin Abdallah knn, ya tsani tuwo, duk ranar da akay tuwo bazai ci ba saidai a dafa masa indomie", garin tuwo dake cikin buhu ta ɗauka ta fita, saida ta hura mangal ta ɗora ruwa snn ta zauna tankaɗen, tana gama tankaɗen already ruwan ya tafasa tayi talge. Maama ta fito toilet ta ajiye butar hannunta bakin rariya, har zata shiga ɗaki sai kuma ta fasa ta tsaya akan Hajar tace "kee sbd baki da kunya da mutunci har ni zan aiki Sabra ki hanata zuwa", Hajar ta cigaba da gyara kayan miyar da za tay miya tace "ni ba hanata nayi ba", Maama ta lafto ashar ta danƙara mata tace "za kimin shiru ko saina kifa kanki a talgen tuwan nan", Hajar ta turo baki ta miƙe zata bar wajen, fuzgota Maama tayi ta daki bakin tace "nace rashin kunya zaki min kike turomin baki sai kace an mari kare", Hajar ta kalli ƙasa tana jin kamar ta kurma ihu sbd takaici, rankwashi Maama ta zuba mata a kai snn ta hankaɗeta, saura ƙiris ta faɗa kan tukunyar dake kan wuta tana zaɓalɓala da talgen tuwa, Maama tace "saina miki ƙafa ɗaya idan kika sake shiga gonata", da sauri Hajar ta shiga ɗaki sbd kukan da ya cicciyota, a ƙasa ta zube ta rushe da kuka, Umma ta kashe rediyon da take ji jikin waya tace "lfy Hajara?", Hajar dai ta kasa cewa komai kawai kuka take zuciyarta na tafarfasa, ita babban takaicinta da aka hanata ramawa, sosai hankalin Umma ya tashi tace "ciwon marar ne?", Hajar na shessheƙar kuka tace "ba waccar matar bace da ƴaƴanta", Umma ta kunna rediyonta tace "ai kam aiki ya sameki, ruwan idonki daf yake da tsiyayewa, kin gama haɗa miyar?", Hajar ta girgiza kai tace "A'a, kayan miyar fa nake gyarawa waccar matar ta takura min", Umma ta miƙe tace "bari kiga na ƙarasa kar magariba tayi ba a gama abincin dare ba" ta fita. washe gari Monday Mu'azzam ya fito tsakar gida da kuftarsa hartin da wando, agogon wayarsa ya duba yaga ƙarfe takwas harta gota, tsaki yayi ya jingina da bango, shi kam yaga ta kansa Baba ya haɗasa da ƴaƴan Maama marasa ta ido, shi ko kallo ma basu ishesa ba, ba ruwansa da su tinda ya lura ba mutunci suka cika ba, tasa ƙanwarma da suke uwa ɗaya da yaga tana shiga sabgarsu magana ya dena mata, har takwas da rabi yana tsaye wajen, ɗakin Baba ya leƙa yace "Baba har yanzu fa basu fito ba", Baba yace "har yanzu" ya tashi ya fito, ƙofar ɗakin Maama ya buga, Maama ta fito tace "A'a malam lfy?", yace "Sa'adatu da Maimuna su fito a mayar dasu makaranta", Maama ta gwalo micimicin idanunta tace "makaranta mal, wace irin makaranta ana zaune ƙalau?", yace "su fito su wuce lokacin na ƙurewa gashi kuma suna ɓatawa wnda zai kaisu lokaci", Maama ta riƙe baki tace "Eh ba shakka, toh waye wanda zai kai sun?, naga duk yayyen nasu basa gari", kai tsaye yace "Mu'azzam ne zai kaisu su fito yanzu", taɓe baki tayi tace "ai kwa dai bacci suke", Baba yace "tashe su, nan da minti biyar na gansu a waje" ya juya ya koma ɗakinsa, Maama ta hura hanci tace "toh idan ma na tashen su haka zasu tafi makarantar ciki kwalam, sai dai shi mai kaisun ya tsaya su karya kumallo nanda awa biyu ehe", da gayya ta faɗi hakan tana yiwa Mu'azzam mugun kallo ta shige ɗaki, da kyar Maama ta tashi Sa'adatu da Maimuna da suke bacci tamkar mushe, saida suka daɗe suna diminiya snn suka fito, lokacin kam har tara tayi, fuskar Mu'azzam kamar ta bujumin sa yayi hanyar soro, suka bi bayansa. ƙarfe sha ɗaya da rabi suka dawo gida, Mu'azzam ya yiwa Baba bayanin komai, Maimuna jss3 aka kaita, Sa'adatu kam dilhu dankali da makani knn daman ƙwaƙwalwar fanko ce da kyar aka barta a jss2. ★Ƙarfe takwas da rabi na safe Ruqayyah ta fito daga wanka, box ɗin kayanta da ta ɗakko jiya daga room ɗin Momy ta buɗe, daman ta kwafe a ranta bazata mayar da kayanta wardrobe ba har sai an ɗaura mata aure da dearest snn zata jera a press ɗinta ta gidan Nurain, ga kayanta ga nasa, sassanyan ƙamshinsa ya ratsa nata kayan, uniform ɗinta na Nurses ta saka, ta ɗora black Abaya a saman uniform ɗin, gaban mirror ta tsaya tana kallon fuskarta, sai kace wata taɓaɓɓiya haka ta ringa gwada yadda zata bawa Nurain haƙuri da irin kalaman da zata gaya masa, chapette mai strawberry ta shafa a pink lips ɗinta, tasa pinky finger ta kwantar da eyebrows ɗinta, ta sake gyara zaman V-shapped hijab ɗinta da kyau, perfume mai sanyin ƙamshi ta fesa sama sama, takalmi black ta sanya sandals ta ɗauki jaka ta fita palour, direct kitchen ta wuce dan ta jiyo motsin Momy a nan, ganin Momy ta kunna gas tana girki Ruqayyah tace "Momy na fa dafa breakfast, na ajiye muku a warmer...", Momy ta ajiye serving ɗin da take juya sauce tace "So, ai bance zanci ba, kinsan bana son high carbohydrate da zaki dafa doya da kwai tsura ba vegetables", Ruqayyah tace "nayi tomato sauce aii", yamutsa fuska Momy tayi tace "too much Acid knn". Ruqayyah dai ta fahimci cewa har yanxu Momyn ta bata gama hucewa ba, a ƙasan ranta tayi alƙawarin sai ta goge stain ɗin da tayi musu a zuciya, daga ta rarrashi dearest mgana ta ƙare. tace "Momy zan wuce aiki", Momy ta cigaba da aikinta tace "Ohk, kin sanar da Baban ki?", Ruqayyah tace "No, kafin na fita zan gaya masa", Momy ta taɓe baki ba tace komai ba, bayan Ruqayyah tabi da kallo tana girgiza kai tace "Allah ya baki dama kinsa ƙafa kinyi fatali da ita". Da sallama Ruqayyah ta murɗa door handle ɗin palourn Daddy, durƙusawa tayi ta gaishesa, Daddy ya amsa ba yabo ba fallasa yana duban dress ɗin jikinta, tace "Daddy zan fita aiki", his piercing eyes fixed on her yace "Okay, sai ki rubuta resignation letter ki submitting kafin ki dawo gida", a razane ta gwalo ido waje, gashi with seriousness on his voice ya fadi hakan, har ruwa ya ciko idonta tace "resignation letter?", yace "are you questioning me?", yarfe hannu tayi tace "No Daddy, i won't dare", ya daka mata tsawa yace "get lost my friend". da sauri ta miƙe ta zabga tuntuɓe da jikin kujera, saida tayi karo da bango har kanta ya sara snn ta lalubi ƙofa ta fita, tana zuwa palour ta sulale ƙasa tana yarfe hannu ta fashe da matsanancin kuka, Momy ta fito kitchen ta ringa kallonta cike da mamaki, har ƙoƙarin birgima Ruqayyah take sbd raɗaɗin da zuciyarta ke mata, Momy ta haɗe gira tace "meye haka?", Ruqayyah ta taso da gudu ta rumgumeta ta cigaba da kuka, Momy tace "ba tambayarki nake ba", Ruqayyah ta ɗago kanta daga shoulder ɗin Momy tace "Daddy ne yace nayi resigning from work..", Momy ta buɗe baki tace "ban gane ki bar aikinki ba", Ruqayyah na shessheƙar kuka tace "haka yace idan naje aiki yau sai na rubuta resignation letter na kai, na shiga uku Momyyy, wllh i love my job", Momy ta zameta daga jikinta ta shiga wajen Daddy, malamala Ruqayyah tayi a ƙasa tana hawaye, after 10mins Momy ta fito fuskarta a haɗe, Ruqayyah ta ɗago idanunta da suka rine tana kallonta, Momy tace "tashi ki tafi, ki rubuta resignation lettern ki dawo gida da ita", Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya tace "tom, kar nayi submitting?", Momy tayi tsaki tace "ai kinji me nace" ta nufi room ɗinta. saida Ruqayyah ta koma ɗakinta ta wanke fuska snn ta fita daga gidan, har ta isa Hospital tunani kawai take, ai abun sai yayi mata yawa ga rashin dearest ga kuma rashin aiki, tsaf zuciyarta za tayi bombing idan ta rasa these two valuable things. a hankali take tafiya cikin babban compound din, wajen da ake parking motoci ta tsaya tana kallo, idonta ya sauka a parking space din thoracic surgeon Dr Uthman, babu mota a parking space din nasa, tayi murmushin ƙarfin hali tace "dearest bai ƙaraso ba". Nurse station ta wuce, gaisawa sukay da colleague ɗin nata su biyu dake zaune wajen, Ruqayyah tace "ina Jiddah?", ɗaya daga cikin Nurses din tace "ai kam ina jin ta tafi gida da yake jiya night tayi", Ruqayyah tace "Ohk". wani room da suke ajiye ƴan kayansu na Nurses ta shiga, kettle ɗin ruwan zafi ta nufa ta kunna, ta buɗe locker dinta ta ɗakko mug da coffee powder, coffee mai rai da lafiya ta haɗa snn ta fito daga room ɗin. barin Nurse station ɗin tayi ta wuce Office ɗin Dr Uthman zuciyarta na harbawa, a garƙame ta tarar da office ɗin, kan silver chair da ke wajen Office ɗin inda patient ke jira ta zauna, almost 1hour babu alamar wnda take jira zai zo, har secretarynsa ma bata zo ba, Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya deeply in thoughts ta dubi Mug ɗin hannunta da coffeen ciki ya gama hucewa, ta duba agogon dake wrist dinta taga har 11am ta wuce, murya can ƙasan maƙoshi tace "Dearest". ta ciro wayarta daga pocket ta shiga kiran layinsa, saida ta kira sau goma amma switched off, hankalinta ne ya kuma tashi, Sha daya da rabi na cika ta tashi ta nufi Office din Dr Marwan, patient ta tarar yana dubawa don haka ta samu space ta zauna, Dr Marwan ya gyara zaman glasses dinsa yana rubutu jikin card, patient din ya miƙawa card ɗin yace "sai next week", patient ta amshi card ɗinta snn ta fita, Ruqayyah da hankalinta ba a jikinta yake ba tace "barka da safiya Dr", Dr Marwan da ke mata wani weird look yace "yawwa A Nurse", tace "ya aikin?", yace "Alhmdllh, wai ina kika shiga ne A Nurse?, har mun fara samun matsala wajen anesthesia", murmushin yaƙe Ruqayyah tayi tace "Egypt naje, yanxu kam ba ku da matsala tinda na dawo", yace "great, Khaleel ma ya gama complain ɗinsa", tace "yau ba ku da surgery ne naga Dr baizo ba har yanzu?", file ɗin dake kan table ya shiga buɗewa like he don't care yace "Boss yana India, this Friday ya tafi". tamkar wata statue in human form haka ta ringa kallonsa, shirun da yaji tayi ne yasa ya ɗago idanunsa ya kalleta, kallonsa yaga tana yi yace "A Nurse, kinyi shiru?".......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {26..} Wannan time ɗin ma dai Ruqayyah a ciki ta ji bugun zuciyarta, har wani darkness ne ya rufe mata sight, sama sama taji muryar Dr Marwan, a firgice tace "Dr, kamar dai banji me kace ba..", yace "i said kinyi shiru..." da sauri ta katsesa tace "No ba wnn ba", kallonta ya ringa yi ganin she isn't herself yace "ohk, which one?", tace "you said something like Boss yana India, this Friday ya tafi", he can't help it dole yayi blushing yace "Ohh you heard it, am jet serious baya nan, sai nanda 8months insha Allah zamu gansa", ƙirjinta ta dafe tace "8months..", katseta yayi yace "A Nurse i thought you are here for something serious, but i have patients waiting outside", tamkar wacca aka zarewa spine haka ta miƙe tace "Alright, thank you for the little time" da haka ta nufi door ta buɗe ta fita, da kyar ta isa Nurse station cause har yanzu darkness ɗin da yayi mending sight ɗinta bai gama fading ba. room ɗin dake station ɗin ta shiga, tsaye tayi tamkar wata statue, a tare ƙafafuwanta da hannayenta suka fara karkarwa sai kace wnda aka jona musu shocking machine, ta dubi Mug ɗin hannunta mai ɗauke da coffeen da ya zama tap water tsabar hucewar da yayi, tasss Cup din ya faɗi ya tawarwatse, two seconds da faɗuwarsa itama ta bisa ƙasan. kuka take son yi amma ta kasa, tears sun ƙafe a idanunta, kawai mgnar Dr Marwan ce take amsa ƙuwwa a kwanyarta, she spent 15 good minutes durƙushe tana kukan zuci, ta lumshe idonta da ƙarfi, she wish this is nothing but a nightmare, ita kanta tasan she was just fooling herself babu wani nightmare. wata colleague ɗinta ce ta shigo, kallonta ta tsaya yi kafin ta dubi broken cup ɗin dake ƙasa tace "Ruqayyah are you okay", Ruqayyah ta miƙe tana murje idonta wanda take fatan hawaye ya cikosa tace "partially, kai na ke ciwo Amina", Amina tace "ohh sorry bari na kawo miki drug", tsugunnawa Ruqayyah tayi ta fara picking pieces ɗin broken cup ɗin tace "don't burder I'm going home", Amina tace "Okay lemmi help you", Ruqayyah ta tashi ta dafe kanta tace "thank you", tarkacenta ta ɗauka ta bar asibitin da ya zame mata one living hell, a wani book shop ta tsaya ta siyi plain sheet da envelope snn ta fito ta tari Napep ta wuce gida, kafin taje gida ciwon kan da ta kirawa kanta ya lulluɓeta, a ɗan madaidaicin compound ɗin gidan nasu ta tsaya, ta zauna akan dakalin shiga main building ɗin, jakarta ta buɗe ta ɗakko pen da plain sheet ɗin da ta siya ta ɗora akan jotter, tana ɗora pen kan papern hannunta ya ringa rawa, da kyar ta gama rubuta umarnin da Daddy ya bata, tayi folding papern ta saka cikin envelope amma bata liƙe ba, tashi tayi ta shiga ciki da sallama, Momy dake zaune palour ta amsa, Ruqayyah da kanta ya fara juya mata tace "Momy barka da gida, na dawo", Momy ta kalli agogon dake palourn tace "da wuri haka", Ruqayyah ba tace komai ba, Momy ta taɓe baki tace "ina resignation lettern?", Ruqayyah ta miƙe mata white envelope dake hannunta, amsa Momy tayi ta ajiye hannun kujera, Ruqayyah tace "Momy na shiga ciki" ta wuce room ɗinta, da ido Momy ta bita ganin yadda ta dawo odd, she looks disturb and weak. wunin yau Ruqayyah bata ji daɗinsa ba, tama rasa meke damunta, gaba ɗaya ta kasa figuring out what is happening to her, abinci ma saida Momy ta kirata tace mata taci snn taci kaɗan, that was bayan sallar la'asar, tinda taci ta koma ɗakinta har akay sallar magrib da isha bata fito ba, tana kwance kan tiles tana juye juye Momy ta shigo, kallonta ta ringa yi kafin tace "ke me yake damunki ne waii?", zaune Ruqayyah ta miƙe tace "ba komai Momy", ai ko karen hauka ne ya cijeta bazata iya faɗin damuwarta ba, daman Momy ba haƙura ta gama yi ba tasan tsaf za tace mata Allah shi ƙara or something that will add salt to her fresh wound. Momy tace "ki sameni a palourn Daddy yanxun nan, kuma in kinje karki ce komai haquri kawai zaki basa", Ruqayyah ta gyaɗa kai, Momy ta juya ta fita. Ruqayyah ta ɗauki hijab ɗin da tayi sallah ta saka ta fita, zuciyarta na lugude ta shiga palourn Daddy, rakuɓewa tayi gefe saman carpet ta zauna, Daddy ya ɗauki envelope da ke gefensa ya wurga mata yace "ni zaki kawowa ko ni na baki aikin?", Ruqayyah dai kanta a ƙasa tace "sorry Daddy, dan girman Allah kayi haƙuri, wllh i learn my mistakes", keenly yace "wane mistake?", kuka ta ringa yi kamar ranta zai fita tace "kayi haƙuri dan Allah..", wani ɓoyayyen ajiyar zuciya yayi baice komai ba, sai a lokacin Momy dake zaune palour itama tace "ayi mata afuwa Alhaji, wnn shine first time da tayi wronging namu amma kuma she won't go free ayi mata wani hukuncin dan Allah", shiru Daddy yayi na wani lokaci kafin yace "da farko ma dai ina yarinyar taje?", Momy ta kalli Ruqayyah tace "talk", Ruqayyah ta sharce hawayen idonta tace "Egypt naje", baki buɗe Momy tace "Ruqayyah me ya kaiki Egypt?", Ruqayyah tace "kuyi haƙuri dan Allah..", wani tsawa Momy ta daka mata tace "wnn ba zancen haƙuri bane magana za kiyi malama", Ruqayyah ta kwantar da murya tana shessheƙa tace "wani aiki naje nema amma ban samu ba...", Momy tace "karki bari na sake tambayarki Ruqayyah, I'm giving you this last warning, ki gaya min komai", Ruqayyah ta share zufar dake keto mata tace "few months kafin a kawo kuɗin aurena na cike wani form online na wani aiki da ƙasar Egypt take bayarwa na waɗan da suke da karatu a fannin lafiya, aikine na shekara ɗaya mai kyau, bayan na tura musu form ɗin suka turomin da saƙon cewa zasu nemeni domin yin interview, ban sake samun wani message ba har sai ranar wata alhamis ranar mother's eve ɗina, tsakar dare na ga message cewa anyi hiring ɗina don haka kafin ranar Monday na kasance a garin Cairo, ban tafi haka ba saida na ajiye muku latter ai kuma shima Nurain na tura masa saƙon cewa ya jirani zan dawo, ranar juma'a na hau jirgi zuwa Abuja kamar yadda suka ce nan ne meeting point ɗin da zamu taru kafin mu wuce Egypt, A Cairo Monday ta riskeni, akay mana interview amma ni banci ba, don haka suka ce na ƙara gaba baza a ɗaukeni ba, da kyar na samu aikin da nayi na samu kuɗin ticket din jirgi na dawo Nigeria, Momy Daddy wnn shine gaskiyar dan Allah kuyi haƙuri na ɓoye muku da nayi, ina tsoron ku hanani shiyasa ban gaya muku ba...", Daddy ya jinjina kai ya kalli Momy yace "barin aikin shine hukuncin da ya dace da ita...", Momy dai tayi tagumi takaicin ƴarta ta ya gama cikata, ajiyar zuciya tayi tace "get out Ruqayyah", Ruqayyah na sharɓe hawaye ta miƙe ta fita, Momy tace "Alhaji karka yanke hukunci cikin fishi, ka tsaya kayi nazari dan Allah, yaran yanxu sai a hankali idan ka biye musu sai ka bata musu rayuwa da baki ko kuma ka tagayyara su da wani action ɗin, Allah ya huci zuciyarka, plxx think twice kafin ka zartar da hukunci...". ajiyar zuciya yayi yace "toh aurar da ita zanyi daman har yanzu Dauda na ciki", Momy tace "Eh ba damuwa gara ayi mata auren" da haka ta tashi ta fita. ★Tinda aka mayar da Sa'adatu da Maimuna makaranta shegun suka samu babban lasisin tsula tsiyarsu, yau sati uku kenan sau ɗaya suka taɓa zuwa, a kullum zasu shirya cikin uniform harda jaka snn su fita, daga sun fita sai ko wacca ta kama hanyarta, Maimuna ta wuce yawonta daga wnn hotel ɗin zuwa wani, Sa'adatu kam gidansu Mabaruka take wucewarta su sheƙa ayarsu san ransu, daga lokacin tashi daga makaranta yayi sai su dawo gida, hakan ba ƙaramin daɗi yake musu ba, su a ganinsu da baƙi ƙirin gwara baƙi baƙi. A fanin Hajar kam babu abinda ya shalleta dasu, a kwandon shara ta wurga su, ita gani take ma kamar babu su a gidan, koda sun takaleta saidai ta yamutsa fuska tayi banza dasu ko kuma ta shige ɗaki. ta kwantar da hankalinta ta zubawa idonta toka bama ta gani ba bare ta tanka, ta tushe kunnenta bama ta ji ba bare ta tanka, ranar Alhamis da daddare Hajar na zaune a soro tare da Nura, firar su suke cike da shauƙi da kaunar juna, rufe fuskarta tayi da hijab tana tiƙar dariya sbd abin dariyar da ya fada, shima dariyar yake yace "insha Allah gobe zasu kawo min kuɗina wajen Baba..", ta bude fuskarta tace "kuɗin me?", yace "kuɗin da zan ɗauki hanyar mallakarki..", turo baki tayi tace "kaji ka ko, toh wai haka ake yi, nifa har yanzu ba sanka nake ba, kuma ni ƴar yarinya ce ban isa aure ba" ta murguɗa masa baki childishly, murmushi mai sauti yayi yace "Ohh really, ai naga alama shiyasa yau kika takura sai naxo kin ganni hakan ma ai duk cikin rashin so ne, snn kuma very soon zaki zama mother kinga ba maganar yarinta..", ta juya manyan idanunta tace "Au nice ma nace maka kaxo ko?", kafaɗa ya ɗaga yace "Eh mana, kin ga you inform your parent kinji", wani gwalo ido waje tayi tace "chabb ai kwa ba za a kawo kuɗin ba indai ni zan gaya musu", dariya ta basa sosai na expression dinta yace "toh meye aciki?", yana kwaikwayon muryarta yace "haka fa kawai zaki ce, Umma Baba gobe za a kawo kuɗin", turo baki tayi tace "ni gida zan shiga", ya kalli agogon wayarsa yace "Okay, sai munyi waya don ban gaji da jin muryarki ba", ledar da yazo da ita ya miƙa mata, ƙin amsa tayi tace "A'a nagode", haɗe gira yayi yace "amshi mana ko so kike mu ɓata", a hankali ta amsa tace "nagode", ya tashi ya nannaɗe darduman da ya zauna ya naɗe wacca Hajar ta zauna ma, amsar darduman tayi tace "nace maka fa ka ringa bar min zan naɗe fa", yace "naƙi ɗin..", ya ringa kallonta har saida ta gaji ta juya masa baya tana turo baki tace "Allah nace maka fa banaso", yace "toh me nayi miki", tace "saida safe" ta shige gida. tinda ta shigo Maama da Sa'adatu dake zaune bakin ƙofar ɗaki suke binta dana mujiya, Maama tayi tsaki tana kallon ledar hannunta, Sa'adatu tace "kullum sai a shigo da wata mitsiyaciyar leda, uhmm Maama za kiji zuwan da dawowar wllh, a banza ake zaman soro harda su leda, ai nasha ganin blue film na zahiri a soron nan...", Maama tace "barewa tayi gudu ɗanta yayi rarrafe, ai muna ganin jalala a wnn gidan...", Hajar dai ta wuce ɗaki abinta. washe gari Juma'a, bayan Sallahr la'asar aka kawo kuɗin Hajar, Baba ya shigo gida da uban kuɗin a hannunsa yana kabbara yace "alhmdllh", yaye labule Maama tayi tace "wnn kabbara haka malam sai kace wanda akay wa bushara da gidan aljanna..", yace "ki fito ki saka albarka kuɗin auren Hajara aka kawo", Maama ta buga wata shegiyar guɗa ta fito tace "Au haba, ƙwandala nawa aka kawo?", ƙanƙance ido yayi yace "wace irin ƙwandala kuma Rabii?, ke me yasa ba a abin arziƙi ne dake", tace "ai gani nai ƙwandalar ce ta dace da ita", Baba ya girgiza kai yace "kiyi fatan Allah ya bawa ƴaƴanki ko da rabin nata ne..", da sauri Sa'adatu da Maimuna suka matso jikin window suka kasa kunne suji nawa aka kawo, Nabilah kam taɓe baki tayi, Maama tace "nawa ne", Baba baice komai ba ya kunce ledar uwar kuɗin ya fito dasu, zaro ido Maama tayi ganin yawansu, tinda take bata taɓa ganin kuɗi masu kaurin haka ba, Baba ya mayar da kuɗin yace "ƙwandala goma ne" ya wuce ɗakinsa ya barta nan tsaye da sakakken baki, wani tuƙuƙin baƙin ciki da hassada ne ya turnuƙeta, tamkar kububu haka ta afka ɗakinta, ta dubi Maimuna da ke jikin window tace "wai mahaukaciya kuka mayar dani ko me?", Maimuna ta turɓune fuska cike da rashin ɗa'a tace "toh wai ke Maama me mukay miki ne?", wata muguwar ashariya Maama ta lafta mata tace "uban ki kikai min, ji nake cemin kukai faƙiri ne ke neman auren Hajara, toh ba kuga uban kuɗin da aka kawo ba na aure", Sa'adatu tace "wai uban kuɗi naji fa Baba yace ƙwandala goma", Maama da zuciyarta ke tafarfasa tace "toh wasu dunƙulallun kuɗi ne ƴan dubu dubu, kaurinsu da aukinsu inajin sun doshi miliyan...", baki suka haɗa sukace "Aaaaaa Maama haba dai", cike da takaici ta shiga kutuntuma musu ashar tace "ƙarya nake knn?", Nabilah ta fashe da dariya tace "A haba dai Maama ya zai kiyi ƙarya ai saidai ki faɗa ba daidai ba ko Maimu", Maimuna tace "kwarai kuwa, Maama na rasa me yasa kika ɗaga hankalinki a kan wanda waccar matsiyaciyar zata aura", Maama ta gasa mata harara tace "yo ba dole hankalina ya tashi ba, ha kurum sai taci gaba kuna zaune jaɓar kuna kallonta..", Sa'adatu tace "Maama nifa kinsan ba aure zanyi ba, indai cigaba na aure kike magana toh na yarda Hajara ta fini a wnn fannin", Maama ta saki baki tana kallonta tace "Au haka zaki zauna a gidan ba xaki gidan mijinki ba...", Nabilah ta taɓe baki tace "Ayyah Maama ai ki saka Sa'adatu a addu'ar ki ta koda yaushe, dan na gaya miki irin alfashar da nake tunanin suna aikatawa da tumakan ƙawayenta amma kin ƙi yarda", Sa'adatu tace "dalla malama ban kasafta dake ba bare ki dauka..", Nabilah tace "kinyi kaɗan bari kiji in gaya miki, toh baki kai nan....", Maama tace "ya ishesku, zaku fara raba halin naku knn", Maimuna tace "dama kin rabu dasu yauma nasha kallo, ai sun iya bawa hammata iska" ta fashe dariya. Da misalin tara da rabi na dare wayar Hajar tay ringing, yamutsa fuska tayi snn ta sakata a silent, yau dai baza tay picking ba, gado ta hau tayi kwanciyarta zuciyarta wasai, an kawo kuɗin aurenta da ya sayyadi, washe gari ta tashi ta gama komai na gyaran gida da ta saba, har waken kulele saida ta wanke, bayan ta gama komai ta shiga wanka, tana shafa mai Umma ta shigo ɗakin, gaban wardrobe ta tsaya ta ciro kuɗi snn ta koma gefen gado ta zauna tace "idan kin shirya zan aikeki gidan Jamila", Hajar tace "tom" ta cigaba da rubbing cream a fatarta, doguwar rigar atamfa ta saka, ta sanya hijab da ya tsaya mata a guiwa tace "Umma na gama", Umma ta miƙa mata kuɗin hannunta tace "ki kai mata wnn, za muyi waya da ita", Hajar ta amshi kuɗin ta saka a jakarta tace "na tafi", Umma tace "karki kai yamma", tace "tom" ta ɗauki flat shoe a ƙarƙashin gado ta fita, a soro ta tarar da Naseer da yazo jiya, ta sunkuya tace "yaya ina yini", yana kallonta yace "lfy lou, ina zaki haka?", tace "Umma ce ta aiken gidan Anty Jamilah", gyaɗa kai yayi yace "Okay" ya wuce ciki ita kuma ta fita, cike da nutsuwa take tafiya har ta isa bakin titi, cikin sa'a kam ta samu Napep da wuri, tana zuwa gidan ta tsaya bakin gate tayi knocking, Hafsa ce ta buɗe tana ganinta ta zaro ido tace "the bride to be wnn bazata hka", Hajar ta shiga gidan tace "ina Tahfeez din, yau naga asabar..", Hafsa tace "ba nida lafiya". da haka suka shiga ciki, Hajar ta durƙusa ta gaida Anty, Anty tace "lfy lou, ya mutan gidan", Hajar tace "suna lfy", Anty tace "madallah", Hajar ta zuge jakarta ta ciro aiken ta mikawa Anty tace "gashi inji Umma".......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {27..} Da mamaki a fuskar Anty ta amshi kuɗin tace "toh, na mene?", Hajar ta girgiza kai tace "bansani ba amma tace za kuyi waya", Anty ta gyaɗa kai tace "Okay". Hafsa ta tashi ta nufi ɗakinsu, wayarta da ke kan mirror ta ɗauka, call log ta shiga ta nemo wata number ta shiga dialing, tana fara ringing akay rejecting few seconds kira ya shiga daga same numbern, ta kara a kunne tace "Assalamu alaikum", from the other side Ahmad yace "Wa'alaykissam salam, young lady", tace "yawwa, nace ba, yau idan babu damuwa zaka iya zuwa na cika alkawarin da nayi maka", keenly yace "Okay, na ɗauka ma kin manta ashe ba haka bane", tace "yap, sai kazo immediately after Asr prayer", yace "insha Allah", kashe wayar tayi tace "kar alƙawari ya zarbaɗo ƙafata ranar lahira ya hanani gudun famfalaƙi..", palour ta fito ta zauna, Anty ta kwashe kuɗin da ta ajiye hannun kujera ta shiga room ɗinta, wayarta ta dauka, missed call ta gani daga ƴar uwarta, zama tayi gefen gado ta shiga kiranta, Umma na dauka suka gaisa, Anty tace "Hajar taxo da saƙo, Adda kuɗin na mene?", Umma tace "kinsan jiya aka kawo kuɗin auren Hajara, Jamila ba a fafe gora ranar tafiya, wnn kuɗin wnda nake ɗan tarawa ne tin tini, shine nace bari na turo miki su sai a fara mata ƴan tsince tsince sha'anin aure da yawa..", Anty tace "gaskiya haka ne ba a fafe gora ranar tafiya, toh mai za a tsinto da wadan nan kuɗin?", Umma tace "abinda kika ga ya dace Jamila, koma mene asiya a ajiye", Anty tace "wata shida suka sa ko?", Umma tace "Eh, kinga kwa ba lokaci, yanxu sai kiga abin yaxo kusa, idan na sake tara wasu saina turo miki kafin lokacin muga abinda za muyi", Anty tace "gsky kam, toh wnn kuɗin dai saidai na siya mata decorants, kayan kitchen nawa ne ni zan mata", Umma tace "Kaii Jamila abun fa da yawa", Anty tace "she's my daughter fa, insha Allah zan mata duk wani abu da ya danganci kitchen, cikin rufin asiri zamu kaita insha Allah babu me rainata a dangin miji ko kuma a goranta mata". Umma ta ajiye numfashi tace "toh Ameen, Allah ya tabbatar mana da alkhairy", Anty tace "Ameen". Hafsa ta kalli Hajar tace "gsky fa zanyi amarancin a bikinki, daman nice ƙirjin biki kuma babbar aminiyar amarya", Hajar tayi murmushi tace "yayi kyau..", Hafsa tace "anko kala uku zan fitar mana na ƙawayen amarya snn kuma zan shiga na ƴan gida, ga wanda zanyi iri ɗaya da amarya ranar yini, kai abinfa ba a cewa komai gsky zan zuba amaranci", Hajar dai ta ringa binta da ido tana murmushi, wai itace wacca ake maganar bikinta, bikin ma da rabin zuciyarta Nura. Hafsa tace "amma dai ba yau zaki tafi ba ko?", harararta Hajar tayi tace "chab ana yin sallar la'asar zan samfe..", Hafsa tace "kaiii dan Allah ki kwana", Hajar tace "yau naga jalala daga zuwa kuma sai kwana, A'a wllh tafiya zanyi", Hafsa ta haɗe gira ta tashi tace "sai ki ta tafiya" ta wuce kitchen, Hajar tace "ai daman tafiyar zanyi", Abinci ta zubo musu ta kawo ta ajiye, ta koma kitchen ta ɗakko gaseous drink da pure water ta kawo ta ajiye, tana hararar Hajar ƙasa ƙasa tace "saiki matso muci", salon ta sake bata haushi tace "na ƙoshi", Hafsa ta ajiye spoon ɗin hannunta tace "ke kin isa, kadan ba sai kinci ba", Hajar ta tashi ta cire hijab ɗinta snn ta zauna ta ɗauki spoon, Hafsa ta kai spoon baki tace "toh ki bari ƙarfe biyar da rabi ko shida saiki tafi", Hajar ta noƙe kafaɗa ta cigaba da cin abincinta, suna gama ci Hafsa ta tattare plate da empty bottle na drink ɗin ta wuce kitchen dasu, ganin ta daɗe bata fito ba Hajar ta bi bayanta, tarar da ita tayi tana wanke wanke bakin sink, Hajar tace "Au wanke wanke kika tsaya", Hafsa tace "harda left over na safe da banyi ba". Hajar ta tattare hannun rigarta ta matsa gaban sink ɗin ta fara temaka mata da ɗauraya, Hafsa tace "kina fa da kirki amma kaɗan" Hajar tace "point of correction bani dashi". wata small pot Hafsa ta ringa gurzawa soson ƙarfe tace "Abdallah ne ya babbaka indomie da safe", Hajar ta leƙa cikin tukunyar ganin yadda tayi baƙi ta fashe da dariya tace "amma dai Indomien ba tada maraba da gawayi", Hafsa tace "uhmm gobara ya kusan tayarwa fa, ba kiga faɗan da yasha ba kuwa wajen Abba, har suka fita kasuwa Abba na faɗa", Hajar tace "wai Allah ya kiyaye". Ana yin sallar la'asar Hajar ta fara shirin tafiya, ta tsaya gaban mirror tana gyara ɗaurin dankwali, hijab ɗinta ta janyo zata saka Hafsa tayi wuf ta amshe tace "ki bari ba yanzu ba", Hajar ta riƙe ƙugu tace "ka jimu da mata, toh wai me zan miki?", Hafsa tayi serious face ta nuna mata kusa da ita tace "dan Allah zauna kiji", Hajar ta zauna tana kallonta tace "what..?", Hafsa ta marairaice fuska tace "tin kina nan gidan nayi masa alƙawari", Hajar da ta ƙosa taji mene tace "wa knn?", Hafsa tace "wnn mutumin da muka haɗu a supermarket", Hajar ta ƙanƙance ido tana nazari, lokaci guda ta gwalo ido waje tace "alƙawarin me kikai masa", kaf Hafsa ta gaya mata abinda ya faru, Hajar tace "toh yanxu ya kike so ayi?", Hafsa tace "so nake idan yazo ki fita, ni ko biki masa magana ba hakan ya wadatar", Hajar tace "da baikon a kaina zan tsaya da wni namijin", Hafsa tace "ai manufar abin zaki duba, bawai zaki tsaya dashi bane a matsayin saurayi, dan Allah don't turn me down just say Hi shknn", Hajar ta dafe kanta tace "wllh kin tafka wauta, idan ya wuce huɗu da arba'in tafiya zanyi wllh", Hafsa tace "bazai ma kai haka ba..." ko gama rufe baki ba tayi ba saiga kira nan yana shigowa wayarta, numbern kawai ta gani tayi ajiyar zuciya ta ɗauka, kara wayar tayi a kunne, yace "nazo", tace "Alright, wait a minute". ta kashe wayar ta kalli Hajar dake kallonta tace "yazo", gyaɗa kai Hajar tayi tace "toh sai muje ko", Hafsa ta gwalo ido waje tace "wai tare zamu, kefa kaɗai zaki", Hajar ta gyara zama tace "kince kar naje knn", Hafsa tace "toh sai ki yiwa Anty sallama daga nan ki wuce kinga na samu hanya sai nace rakaki zanyi", Hafsa ta saka hijab dinta, dakin Anty Hajar ta shiga tayi mata sallama, Anty ta bata 1k kuɗin mota, Hafsa tace "Anty na fita rakata", tare suka fita gate, Hajar ta matsa gefe tace "fara fita", buɗe ƙofar gate ɗin Hafsa tayi snn ta fita, yau ma dai a wata jugunanniyar motar yazo saɓanin ta ranan, yana hangota ta tint glass ɗin ya buɗe motar ya fito, mayar da door yayi ya rufe snn ya ƙaraso wajenta yayi sallama, tace "wslm, ina yini", yace "lfy lou, ykk?", tace "alhmdllh am great", juyawa tayi da nufi mgana da Hajar ai kam taga wayam, tace "lemme get her" ta shiga gida, a tsaye ta ganta da wani expression bisa fuskarta, Hafsa tace "toh muje", Hajar tace "wllh ban san me zance masa ba", Hafsa ta ja hannunta tace "anything" saida ta kaita har gabansa snn ta cikata, Hajar ta ja baya making some distance between them, Hafsa tace "As promised", waje ta basu ta shiga maƙotansu, gefe Hajar ta kalla tace "ina yini", bai amsa ba ya jefa mata tambaya "you blocked my number right?", kanta a ƙasa tace "yess", kallon fuskarta kawai yake yace "why?", tace "sorry you ask for a chance da bazan iya baka ba, kayi haƙuri dan Allah, wllh a lokacin inada manemi wnda yaje wajen iyayena, bana so na ɓata maka lokaci shiyasa", wani iri ya ji har cikin zuciyarsa yace "Alright, ynxu fa?", tace "ynxu kam an riga an min baiko, kayi haƙuri..", wani deep breathe ya sauke yace "ba damuwa Hajar, loosing you is one of my destiny, may Allah choose the best for us", a karo na farko da ta ɗago ta dubesa, ta mayar da kanta da sauri tace "Ameen, nagode", gidan da Hafsa ta shiga ta nufa ta fara knocking, Hafsa ce ta buɗe ganinta ta fito tace "har ya tafi..." shiru tayi ganinsa a tsaye yana kallonsu, ta ƙarasa inda yake tace "then ynxu dai na fita daga jerin masu yanke fate, na cika alkawari", yace "thank you", tace "don't mention, sai anjima", yayi waving ɗinta slightly snn ya juya ya shiga motarsa zuciyarsa a dagargaje, wani irin cin taya yayi ya juya kan motar, da gudu yabar unguwar tamkar zai tashi sama, Hajar tabi ƙurar da ya tayar da kallo snn ta matsa kusa da Hafsa suka sauka kan titi, Hajar tace "ya bani tausayi wllh", Hafsa tace "Allah ya basa wata". da haka Hajar ta tsari Napep ta wuce gida. ★A kwana a tashi lokaci bashi da wuya wajen shuɗewa a wajen Ubangijin talikai, mu shagalallun bayi mu muke ganin jimawarsa harda ɗokin cika burikan rayuwa ( yau HAJAR ya ɗakko wani daga cikin scene na littafina SOHANA), A wannan rana ta laraba saura wata ɗaya bikin Hajar, kuma a wnn rana aka kawo lefe, manya manyan tabarmi har guda biyu aka baje a tsakar gida da yamma ana jiran ƴan kawo lefe, Maama da ƴaƴanta sai shige da fice suke suna yaɓa baƙaƙen maganganu, tin Anty Jamilah na sharesu har ta fara mayar musu da wacca tafi tasu zafi da ciwo. an zuba bajinta gsky, lefen Hajar san kowa ƙin wanda ya rasa, dangin Ango suna gama sauke kayan lefe suka ce suna buƙatar a ƙara musu wata ɗaya domin ango ya gama shirye-shiryen sa, kai tsaye aka amsa musu dan Anty da Umma suma suna son su gwangwaje ƴarsu, tray tray su Anty da wasila da sauran ƴan uwan Umma suka ringa fitarwa na kayan motsa baki da kaji da kuma steak suka bawa ƴan kawo lefe, ga kuma kuɗin tukuici mai tsoka da aka basu, sunji daɗin karamcin da iyayen Hajar sukay musu, nan fa aka baje kaya ana musu ɗaɗɗai kowa na sanya albarka, maƙwabta da abokar arziƙi kowa shigowa yake yana kashe kwarkwatar idonsa, a duk wnn zazzafar wainar da ake toyawa Maama da ƴaƴanta sun ƙule ɗaki saidai fa komai akan micimicin idanunsu tinda laɓewa sukay jikin labule da window suna leƙe. baƙin ciki da hassada ainun suke nunawa, Anty sai ɗaɗɗaga kaya take tana saka albarka, wasila kuma na rangaɗa guɗa, da baƙin ciki ya ishi Maama da sauri ta bar bakin labule ta zauna ƙasa daɓas ta dafe kai, Sa'adatu kam tsaki tayi ta koma gado tayi kwanciyarta tace "ko sha'awa", Maama tace "ƙarya kike munafuka, wane mai zuciyar ne zaiga uban kayan nan yace basu birgesa ba..", Nabilah ta rage murya tace "haba Maama kiyi magana a hankali kar ace baƙin ciki muke", da ƙarfi Maama tace "Eh aji ɗin mna" sai kuma ta miƙe ta gyara ɗaurin zaninta ta saɓi hijab tayi waje, da sauri Maama ta fice daga gidan zuciyarta na tafarfasa ta saɓi hanya........✍️ 🔔*WEDDING BELL*🔔 Ehen it's ringing...... ƙalalannnn 🔔 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche. {28..} Can cikin lungunsu ta shiga, bayan tayi tafiya ba mai nisa ba tazo ƙarshen lungun, ta gangara can ciki, wani tsukun layi ta shiga mai wawakekiyar kwata, ƙudaje da ƙwari sai shawagi suke, wari kam ba a cewa komai sbd kwatar ta Engine markaɗe ce kuma mara gudana, wani kuturun gida na laka Maama ta shiga ta zabga sallama daga soro, ta kutsa kai ciki, wata mata ce ta fito wacca za su kai shekaru ɗaya da Maaman daga wani ɗaki, ganin Maama ta riƙe baki tace "lale lale maraba da baƙuwar yamma", Maama tace "bani ruwa na sha maƙoshina a bushe yake", wata randa dake can gefe matar ta buɗe ta kantamo ruwa a cup ta kawo mata, daga tsaye Maama ta moɗe ruwan, tayi ajiyar zuciya tana hura tukubar hanci ta miƙawa matar kofin tace "yawwa Balaraba, da zance nazo", Balaraba tace "Atoh mu shiga ɗaki ko mu zauna nan waje tinda ba kowa, duk basa gidan", Maama tace "mu zauna nan tsakar gida yafi iska", Balaraba ta shiga ɗaki ta ɗakko wata yagulamun tabarma duk ta zare ta shimfiɗa musu, suka zauna, Balaraba tace "lfy dai Aminiya", Maama ta sharce zufar da ta tsattsafo mata da ƙasan hijab tace "Balaraba ƴaƴana gaba ɗayansu sun wurgar da zuciyoyinsu a ƙasa kare ya lashe". Balaraba tace "me ya faru?, shaƙamin mana", Maama tace "kinsan dai ina zaune bazan bari ƴaƴan faɗima sufi nawa ba, wai wnn shegiyar ƴar Hajara itace yau aka kawowa lefe", tayi shiru ta riƙe baki tace "ke baki ga uwar dukiyar da aka lafto ba", Balaraba tace "babbar magana, toh su kuma yara meye haɗin su da wnn lamari kika ce kare ya lashe musu zuciya?", Maama tace "kwanwar su ce fa duka, gaba ɗayansu gaba suke da ita, ni bama wnn ba wnda shegiyar zata aura ne matsalata", Balaraba ta taɓe baki tace "ɗan gidan waye?", Maama ta juya hannu tace "oho ni bansani ba, amma dai wai malamin makarantarsu ne, yaran nan da yake sun sansa shine suka ce min wai faƙiri ne bashi da komai, wai ƙaramin shagon chajin waya yake dashi, uwarsa ɗan wake take jefawa a ruwa, kin san me?", Balaraba tace "yo ina zan sani ai sai kin gayamin", da wani irin takaici Maama tace "hmmm arziƙi da rashinsa ai basa ɓuya, wllh in gaya miki lokacin da malam ya kwanta a asibiti ke baki ga uban kayan da ya kawo masa ba na dubiya, tin daga lokacin zuciyata ta fara wasiwasi akansa, wai sai Sa'adatu tace min kayan haya ne, wai shi Opay, in gaya miki aka zo aka kawo kuɗin aure, nidai tinda nake ban taɓa ganin kuɗi masu aukinsu ba, to sai wnn kayan na lefe da aka kawo, shknn fa akasa muƙeƙiyar sanda aka bajar dani a ƙasa, kinji fa lukutar masifar da nake ciki..", Balaraba ta jinjina kai ta riƙe haɓa tace "amma baki taɓa sanar dani ba Rabi", Maama tace "ai yaran nan ne sukai ta juyar min da kai da tunani, suka ringa cewa matsolo ne kuma faƙiri shiyasa ban damu ba, nidai yanxu ki bani shawara me zanyi?", Balaraba tace "ai kwa dai bazaki zauna ba kina ji kina gani ƴar faɗima tafi naki ƴaƴan, yanxu dai yaushe ne bikin?", Maama tace "naji ɗaxu dangin mijin suna cewa saura wata biyu", Balaraba ta washe haƙoranta da suka gama dafewa sbd cin goro tace "yo wnn ai me sauƙi ne, munada lokaci isasshe, wata biyu ai da yawa", Maama tace "kar dai muyi sake, ta ina zamu fara?", Balaraba tace "toh wai me kike so ayi ne?", Maama tace "A'a haba ke kuwa Balaraba ai kinsan me nake so", Balaraba ta ɓarke da dariya tace "Azzaluma Rabii", Maama tace "har na kaiki", Balaraba tace "gidansu yaron zamu fara nemowa, ai bazai wuce unguwar Dala ba tinda kince malamin islamiyya ne", Maama tace "to wa zai nemo gidan nasu?", Balaraba tace "haba Rabii sai kace baki san ko ni wace ce ba, nice larabe uwar kwakkwafi da bin diddiƙi", Maama tayi ajiyar zuciya tace "yawwa, na bar komai a hannunki, sai zuwa yaushe zan ji ki?", Balaraba tace "har gida zanzo na sameki ai wnn abu nima ya shafeni, bazan bari kiji kunya ba Rabii", sai ynxu zuciyar Maama ta sake, taji daɗi har cikin ranta tace "to bari na saɓa, wai ƴar tafiyar nan da nayi ba kiji yadda ƙirjina ya riƙe ba sai kace wata wacca ta tara kitse, yo Allah na tuba ina naga maiƙon", Balaraba tace "ai da anci maiƙon, yanzu ne dai babu, amma da gidan Malam Adamu ai baya rabo da maiƙo, ke kanki maiƙon kika gani kika liƙe masa..", Maama tace "gsky dai sai bayan da aka haifi autar gidan arziƙi ya yanke mana, malam yana riƙon gida sosai, yanxun ma yana bamu daidai ƙarfinsa, kin san ni ba ruwana in mutum yayi abin arziƙi bazan kushesa ba, shiyasa nima nayi masa halacci na zauna dashi a babu", da haka Maama ta miƙe, soro Balaraba ta rakata, sukay sallama Maama ta wuce, har ta koma gida jama'a basu baje ba, ynxu ne suka fara shigowa, abinka da unguwar tsuku wato gheto, wnn gayawa wnn haka suka cika gida suna kallon abin arziƙi, sai bayan Sallahr magrib aka samu masaka tsinke, Anty ta riƙe haɓa tana kallon Umma tace "Adda mutane akwai gulma", Umma tace "uhmm bare ƴan lungun nan", Anty ta kalli boxes ɗin da Mu'azzam ke jigilar shigowa dasu tace "Alhmdllh gsky kaya sunyi kyau sai san barka Allah yaci da ƴan baya", Umma tace "Ameen, zan tambayi mal nanda kwana biyu sai a kai kayan gidan ki", Anty tace "toh shknn, wnn tururuwar jama'a haka ai ba a rasa mai dogon hannu ba, yanxu sai ki ga kaya na ɓata, haka kurum su cuci yarinya mutanen yanxu ba imani", sai takwas da ƴan mintina Anty ta tafi gida. ★Washe gari Umma ta saka Mu'azzam ya kai lefen ɗakin Baba don ya gani, ko gama buɗe box ɗin atamfofi Umma ba tay ba ya dakatar da ita yace Allah ya saka albarka yasa rabonta ne, Umma tace "Ameen" ta rufe kayan, bayan Sallahr la'asar Hajar ta dawo gida, daman gidan Iya taje ta kwana abinta don haka bata san wainar da aka toya jiya ba, tasan dai za a kawo lefe, koda ta shiga ɗaki taga boxes ɗin lefen murmushi kawai tayi ta kawar da kai, ammafa sun burgeta, nace uhmm hajiya Hajar don ma ba kiga abin arziƙin dake ciki ba da sai bakinki ya yage. da yammacin ranar Naseer yazo sbd kiransa da Baba yayi, ya durƙusa ya gaida mahaifin nasa, Baba ya amsa yace "Naseer akan filina dake unguwar Ring road, kasan na sakasa a kasuwa?", Naseer ya shafa kai yace "Eh Baba na sani", Baba yace "toh yawwa, an samu mai siya, anyi ciniki anyi komai, kuma an samu riba sosai, kasan filin yanada girma kuma na daɗe da siyarsa", Naseer yace "Eh", Baba ya gaya masa adadin kuɗin, mazajen kuɗi Baba ya ambata, Naseer ya jinjina kai, Baba yace "yawwa, gida huɗu za'a raba kuɗin, kaso ɗaya na Hajara ne dashi za ai mata kayan ɗaki, ragowar kaso ukun kuma na Nabilah da Sa'adatu da Maimuna ne, suma duk ranar da Allah ya kawo musu mazaje sai ayi musu kayan ɗaki", Naseer ya gyaɗa kai yace "hakan yayi Baba, Allah ya ƙara girma", Baba yace "A Bank account ɗinka za a tura kuɗin", Naseer yace "toh Baba", Baba yace "idan aka ɗauki na Hajara sai kuma a nemi wani filin can wajen gari a siya da kuɗin su Nabilah", Naseer yace "nima ai akwai tawa gudummawar da zan bayar, zan siya mata katifu", Baba ya jinjina kai yace "Masha Allah, Allah yayi abarka ya yauƙaƙa maka hanyar samu, Allah ya baka ikon kula da ƙannenka ko bayan raina", Naseer yace "Ameen", Baba ya ciro wata paper daga aljihu ya miƙa masa yace "gashi lambar mai siyan filin ce, ka kirasa sai ka tura masa da account numbern", Naseer yace "tom" yasa hannu biyu ya amshi papern, tashi yayi ya fita, har karo suka kusa yi da Maama dake musu laɓe, zuciyarsa ce ta buga ganinta tsaye a ƙofar ɗakin, tayi masa wani mugun kallo tayi ƙasa da murya tace "biyoni Nasiru" ta shiga ɗakinta, dole ya bita ɗakin, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, wani huci tayi tace "sbd kai sakarai ne wai zaka mata katifu, A'a ba katifu ba kamfanin Royal foam zaka siyar mata, toh wllh bada yawuna ba karka kuskura ko ficika ka bayar a bikin Hajara, idan kuma ka bayar to ban yafe ba wllh, kaji dai na gaya maka", murtuke fuska yayi yace "kiyi haƙuri Maama na riga na siya ai", hangame baki tayi tace "saika mayar kamfanin a baka kuɗinka, ai ba a ciniki dole, idan kuma bazaka mayar ba ni ka kawomin daman tawa ta ruɓe, kannenka duk sun lotse ta", baice komai ba ya miƙe ya fita zuciyarsa duk a dagule. Bayan sati biyu Umma na bakin rariya tana alwala, Balaraba ta zabga sallama a gidan, Umma ta amsa bayan tayi mata kallo ɗaya, Balaraba ta yatsine fuska tace "wai ina mutan gidan ne inata sallama bare na amsawa", da jin muryarta Maama ta fito tace "ai gamu nan, muna miki lale maraba", Balaraba tace "toh daga sallama sai bare su amsa", Maama tace "kedai mu shiga daga ciki", Maama ta yaye mata labule ta shiga snn itama ta shiga, Nabilah ce kawai a ɗakin, sauran kam sun tafi makarantar gogi, Maama tace "Nabilatuwa bamu waje kinji", Nabilah ta yatsine fuska tace "toh ni kuma inje ina?", Maama tace "tsakar gida zaki fita", sakkowa tayi daga ruɓaɓɓen gadon tace "tsakar gida akwai rana wllh", Maama tace "ki zauna can kusa da banɗaki ba rana anan", tace "Maama warin kwata fa?", fuskar Shanu Maama tayi tace "ke dalla malama fitarmin daga ɗaki don ma kinga ana lallaɓaki, fita malama", Nabilah ta zumɓuri baki ta zumbula hijab ta fita, Balaraba dake kallonsu tace "gsky Rabii kin sangarta ƴaƴan nan naki", Maama tace "nasan akwai magana tinda naga kin fito rana gatsal-gatsal", Balaraba tace "uhmm, ai bazan iya bari rana tayi sanyi ba maganar cina take", Maama ta samu waje ta zauna tace "toh ya muke ciki ƴar uwa?", Balaraba ta riƙe haɓa tace "uhmm, ai ƴaƴanki basu miki ƙarya ba Rabii, Nura ai shagon chaji ne dashi ammafa a da, dan yanxu a babbar kasuwar saida wayoyi ya mallaki babban shago, uwarsa ma tayi sana'ar sayar da ɗan wake ammafa banda yanzu, tashi ɗaya Allah ya azurtashi daman ance akwai shi da ƙoƙari da neman na kai, yanxu dai babu maganar matsolontaka ko faƙiranci a tattare dashi, Mahaifinsa ya mutu shine yake kula da ƙannensa mata biyu da mahaifiyarsa cikin yalwa da wadata", Maama ta sharce zufar da ta keto mata ta tashin hankali tace "na shiga uku, ynxu ya za ai Balaraba?".........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {29..} Wani mugun murmushi Balaraba tayi tace "wnn ai bai kai abinda zaki shiga uku ba ƙawata, karki damu..", Maama ta katseta da faɗin "ya za kice kar na damu.., nace miki fa bana son yarinyar da uwarta su cigaba", Balaraba tayi tsaki tace "ai bazasu cigaban ba, me kike so ayi?", Maama tace "kar ayi auren nan ko ta halin ƙaƙa ne", Balaraba tace "kinxo ta gidan sauƙi, malamin tsamiya shi zai zartar miki da aiki kina zaune hankali kwance, wllh aikinsa kamar yankan wuƙa", Maama tace "yo ai idan ana neman ruwan kashe gobara har na kwata ɗiba ake, sai muje wajen nasa", Balaraba tace "hmm matsalarsa kuɗi, baya aiki sai yaji dumuss", Maama tace "wnn ba matsala bane, kamar nawa zan tanada?", Balaraba tace "Aƙalla ki riƙe dubu hamsin a hannunki", Maama ta gwalo ido tace "dubu hamsin, jar bala'i ina naga dubu hamsin", Balaraba tace "dole kam kiyo kashinsu in kina son burinki ya cika", Maama ta zabga tagumi tana tinanin a ina zata samo waɗannan kuɗi, Balaraba tace "uhmm idan so samu ne ma ace yanxu haka kinada kuɗin, in ban manta ba dududu saura wata ɗaya da sati biyu bikin ko?", Maama tace "haka yake", Balaraba tace "gsky dai ya kamata ki farga, ki nemo kuɗin nan fa", Maama tace "bani kwana uku zan nemosu kuwa", Balaraba tace "A toh kika tsaya bacci dai kwaɗo ne zai miki ƙafa", Maama tace "ke an ma samu fa an gama waɗannan kuɗi", Balaraba ta miƙe tace "to nidai nabi ta nan, daman cewa nayi bari nayi maza na ankarar dake", Maama tace "sai kin jini", Balaraba ta fito tsakar gida Maama biye da ita, a lokacin Hajar ta fito daga bayi knn, ta gefen ido Balaraba ke kallonta snn tayi soro, ta juya ta dubi Maama tace "itace ko?", Maama tace "itace shegiyar..", Balaraba ta jinjina kai sukay sallama da Maama ta tafi. Washe gari Hajar ta haɗa ƴan kayanta a Jaka zata wuce gidan Anty Jamila, tin ranar da aka kawo lefe Anty taso ta bita gidan amma Umma tace malam bazai bari ba, yanxun ma dai da kyar Baban ya amince, da yamma ta tafi bayan ta gama shirinta, murna wajen Hafsa ba'a cewa komai tace "yanzu fa shknn, ba zuwa gidan nan zaki ringa yi kina kwana ba", Hajar ta juya idonta tace "kin san me?", Hafsa tace "A'a saikin faɗa", Hajar tace "nifa banga lefen ba, ranar da aka kawo bana nan ina gidan Iya, kuma dana dawo ban bi takansu ba kar Umma tace min mara kunya", Hafsa tace "toh yanxu ya za ai?, gani za kiyi ne?, sai Anty tace miki mara kunyar", Hajar tace "A'a ke ni ba gani zanyi ba, ki gayamin mene ne aciki", Hafsa tace "chabbbb ai ki gani da idonki yafi, gsky fa ya sayyadinki ya zuba miki kaya", murmushi Hajar tayi tace "Allah..", Hafsa tace "Anty ta kira wacca za ta ringa yi miki gyaran jiki, ina jin ma jibi zata fara zuwa", Hajar ta gwalo lulu eyes ɗinta tana kallon jikinta tace "Me za a gyara", harararta Hafsa tayi tace "zaki gani ne aii". Humaira ce ta shigo tace "yaya Hajar wai kixo inji Anty", Hajar ta tashi tace "toh", suka fita tare da Humaira, room ɗin Anty suka shiga, Anty na zaune gefen gado ga boxes nan sun cika sararin ɗakin, Anty ta kalli Hajar tace "ki ma kwa ga kayan?", gyaɗa kai Hajar tayi tace "Eh", Anty tace "toh daman kiran da nay miki knn, tinda kin gani shknn", Hajar ta juya ta fita ta koma wajen Hafsa, tace "kiran da tay min tambayata tai naga kaya, ni kuma nace mata Eh", Hafsa tace "kinga kwantar da hankalinki, nasan Anty a wnn week ɗin ma saita fita, tinda bana zuwa schl an mana hutu mu bari idan ta fita sai muje kiga lefenki a tsanake". ★Da daddare Maama ta tarfa Sa'adatu da Maimuna a ɗaki, Sa'adatu tace "wllh Maama ni ba nida kuɗi, ina naga wata dubu talatin, ina ma laifin dubu goma amma shine za kice na baki dubu talatin, wllh ban dasu ba nida dalilinsu...", Maimuna da ta tamke fuska tamkar tsohon baƙin hadari tace "yo kema knn, bare ni, wai dubu ashirin", Maama tayi kwafa tace "duk za kuci gidan ku, dani kuke zancen, toh wllh ko kunƙi ko kun so sai kun bani kuɗin nan, yanxun nan ma kuwa", Maimuna tace "nidai Maama saidai ki yanka ni amma ban dasu eheee", Nabilah dake sauraron su tace "anayi ina cin indomie, ni kam ko ta kaina ba a bi sbd ansan babu, Hajjajai maza ku buɗe lalita hajiya Maama na jiran dumuss", Sa'adatu tace "ai kam dai baxa ta ji wani dumuss ba, Maama nidai kin san in ina dashi zan baki", Maimuna tace "nima dai in ina dashi zan.....", katseta Maama tayi da faɗin "ƙarya kike uwar mammaƙo, a gidan ubanwa kike ban iyee?, toh bari kuji in gaya muku karku zata ban sani ba, sarai nasan cewa ba makaranta kuke zuwa ba daga zarar kun fita sai ko waccen ku ta wuce shu'uninta, ko ku bani kuɗi ko na gayawa Babanku, kuma kun san cewa Nasiru na gida, babu abinda ya shalleni haka zan bada fuska ya zane muku jiki, kai wllh har ziga mal zan ringa yi dan jikinku ya gaya muku, ni zaku mayar yarinya kucemin wai baku da kuɗi..", Sa'adatu tace "to ki faɗa mana ai nace miki banda su...", Maama tace "haka kika ce ko?", Maimuna tace "Maama ai gaskiyar knn", gyaɗa kai Maama tayi ta isa bakin ƙofa ta ɗaga murya tace "Malammm", da wani mugun zafin nama Sa'adatu ta rufe mata baki, Maimuna kuma ta kama zaninta sai muzurai take, habawa ai Nabilah kifowa tayi daga kan gado sbd dariya, Maama ta kwace bakinta tace "zaku bayar ko a'a?", haɗa baki sukay su kace "zamu bayar", Maama ta hura tukubar hanci tace "jikinku ya huta" ta fizge zaninta daga hannun Maimuna. daga waje Baba ke neman ba'asin kiransa da akay, Maama ta sake ɗaga murya tace "daman cewa nayi barka da hutawa". A take Maimuna ta buɗe jakarta ta lalo duba ashiri ta miƙa mata a wulaƙance, Sa'adatu kuma ta kira Zeenatu tana mata wata maganar ƙirsa tace ta turo mata mutsabbai, da kyar Sa'adatu ta lusar da Maama cewa gobe da safe zata fita Pos ta ciro mata kuɗin. Da sassafe kam Maama ta tayar mata da mandiran zuciya, haka ta fita tasha wahala harta nemo pos ta ciro kuɗin ta kawo mata, tinda Maama taga dubu hamsin dumuss a hannunta ta fara shirin zuwa gidan Balaraba, ƙarfe goma na safe ta fice don saida ta bari Baba ya fita, tana isa gidan abokiyar cin mushen nata ta azalzale ta, sharp sharp Balaraba ta shirya suka saɓi hanya, tin ƙarfe sha ɗaya suka fita amma basu dawo ba sai yamma liƙis, gidan Balaraba Maama ta tsaya ta huta snn kuma ta amsa mata tambayoyin da take ta riƙonsu tin bayan fitowarsu daga wajen malamin tsamiya, ruwa kawai tasha ta hau surfa mata tambaya, Balaraba tace "kai Jama'a tinda fa yace aiki ya kammala to mgana ta ƙare", Maama da idanunta sukay jajur tsabar wahala ta tafiyar mota da ƙafa tace "da farko fa cewa yayi tabbas yaga ana biki, kuma aure sai an ɗaurasa", Balaraba tace "ai kece kika ringa cewa ga abinda kike so ayi, kinga kin ce masa a sawa yaron tsanar yarinyar kuma da ya duba allon bokancinsa yace miki hakan bazai yiwu ba sbd yaron akwai addini, ba za a iya samun galaba dashi cikin sauƙi ba, idan kwa aka matsa to lokaci zai ƙure har ranar auren tazo ba a samu galabar ba, shine yace ya sami lagon yaron wanda dashi zaiyi amfani, kuma ma yace aiki ya kammala kawai ki jira lokaci", Maama ta sauke wata gauruwar ajiyar zuciya tace "yanzu dai ba matsala knn?", Balaraba tace "kwarai kuwa, ki saki jikinki ki shiga bidirin biki, daga gefe kuma ki zubawa sarautar Allah ido kiga ta inda ɓaraka zata ɓullo", tin daga wnn moment Maama ta samu peace of mind, daga gefe guda kuma tana jiran ranar da faɗima da shegiyar ƴarta za suji kunya. ★Wani irin fresh Hajar tayi, fatarta tayi luwai luwai har wani sheƙi take sbd gyaran jikin da akai mata na sati biyar, ga wani sassanyar kamshi da yake tashi ajikinta, duk inda ta gifta sai ƙamshi, ko a waje ta zauna sai ya ɗauki lokaci ƙamshin bai baje ba, ilahirin jikinta kamshi yake, gashinta kam tamkar gonar furanni masu ƙamshi, babu inda take zuwa, ba ta shiga rana shiyasa gyaran yayi armashi, ko kitchen Anty ta hanata shiga, idan ma aikin za tayi iyakacinta palour da ɗakuna amma banda gaban wuta da rana, Nura kam kullum yana kan hanyar zuwa, ɗaiɗaikun ranaku ne kawai baya zuwa, ji yake tamkar ya janyo lokacin akay masa ita kawai, wata shaƙuwa ce ta shiga tsakaninsu a wnn taƙin, Yau ma dai mai gyaran jiki tazo tayi mata ta gama ta tafi, toilet ta shiga tayi wanka, ta fito tana wani ƙamshi na daban wadan ya gauraya da wanda take zubawa kafin shigarta wankan, zama tayi kan stool ta janyo sabon man da take shafawa na gyara fata da saka glowing, a tsanake take tattale fatarta da tayi wani laushi da santsi, ita kanta yaba kyan da tayi take a zuciya, Hafsa ce ta shigo hannunta riƙe da cup, ajiye cup ɗin tayi kan mirror tace "ki shanye yanxu ki bani kofin na mayar mata", Hajar ta ɗauki kofin ta kwankwaɗe ta miƙa mata empty, ( Ehen ba fa maganin mata bane, it's not good a bawa budurwa, maganin infection ne da cire dattin golden organs of a woman). doguwar riga ta material ta saka snn ta fita palour, zama tayi kan kujera tana latsa wayarta, tanan suke magana da zainab akan bikin musamman ma walimar da zatay, Anty ta fito da shirin fita da jaka a hannunta tace "ina Hafsa?", Hajar tace "tana kitchen", kitchen ɗin Anty ta shiga, bayan few seconds ta fito tace "na tafi", Hajar tace "A dawo lfy", tace "Ameen", snn ta fita, su Anty an shiga ruruma don yanxu bikin saura 1week, sha'anin jera gidan amarya suka karkata. A hankali Hajar ta dafe kanta tace "subhanallah innalillah wa'inna ilayhirraji'un" sakamakon gabanta da ya yanke ya faɗi ba gaira ba dalili, sau huɗu yana mata haka bayan zamanta a palourn, wayar ta ajiye ta miƙe ta tafi kitchen wajen Hafsa, Hafsa tace "Abu zaki ɗauka ne?", girgiza kai Hajar tayi tace "nope nagaji da zama ni kaɗai", Hafsa tace "kinga ki fita ynxu zan fito bari na gama zuba seasoning a miyar", Hajar tace "kawo na ɓare miki maggin", Hafsa tace "A'a zanyi da kaina, Anty fa tace ki dena shiga kitchen", turo baki tayi ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa ta fita, tana ƙoƙarin zama gaban nata ya sake faɗuwa, nan ma dai Addu'ar tayi, har bayan Sallahr isha'i abinda take fama dashi knn, a hankali ta tashi daga kan dardumar da tayi sallah ta nannaɗe, wayar tace tayi ƙara wanda ya razanata tsabar rashin sukunin da ya risketa a bazata, ta ɗauki wayar tana kallon mai kiranta, ( ya sayyadi na) haka tayi saving, picking tayi ta kara wayar a kunne, ajiyar zuciya taji ya sauke snn yace "Hajar", tace "Na'am", yace "dan Allah fito na ganki, gani nan a ƙofar gida".......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {30..} Shiru tayi na some seconds kafin tace "tom" ta katse kiran, da dogon hijab din da tayi sallah ta fita, Humaira da Hafsa ne zaune palour, Abdallah ya fita masallaci salla, Hajar tace "Hafsa zan fita ƙofar gida", Hafsa tace "okay zuwa yayi knn?", gyaɗa mata kai kawai tayi ta nufi ƙofa, ta ƙetare small compound ɗin gidan ta buɗe ƙofar gate ta fita, jingine ta gansa da jikin gate ɗin, street light ta haska masa fuskarta, yayi ajiyar zuciya yana kallonta sosai, jinginar da kanta tayi jikin gate ɗin itama tace "ina yini", tini hancinsa ya cika da scent ɗinta, da cool voice ɗinsa yace "lfy alhmdllh, ykk?", tace "am fine", ya juyo sosai yana kallon yace "Hajar", kanta a ƙasa tace "Na'am", yace "karki bari azkar ya fita a bakinki, kinga dai ynxu zaki shiga ruruma, ki dage da Addu'a kinji", gyaɗa masa kai tay tace "insha Allah", ta ɗago ta kallesa tace "amma dai lafiya ko?", yayi ajiyar zuciya yace "alhmdllh", tace "ni kuma sai naga kamar you're not okay", keenly yace "partially", tace "me yake damunka?", murmushi yayi yace "ai tinda na ganki komai ya wuce, na dawo normal", tace "da gaske?", yace "uhmm", shiru ne ya ɗauka na wasu ƴan sakanni, ya katse shirun da faɗin "toh me kika shirya a bikin?", ta girgiza kai tace "ba komai", yace "ba komai, babu abinda za kiyi?", ta gyaɗa kai, murmushi yayi ya zaro envelope daga pocket ɗinsa, miƙa mata yayi yace "take", tace "meye wnn ɗin?", hade gira yayi yace "i said take", tasa hannu ta amsa tace "nagode", yace "good girl, toh shiga gida saida safe", tace "Allah ya tashemu lfy", har ta juya zata shiga sai kuma ta fasa ta juyo ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta, murmushi yay mata ta mayar masa snn ta shige. Ranar talata da yamma Hafsa ta rakata wajen salon, Anty tace tayi amfani da kuɗin da ya bata, wankin kai na musamman akay mata, natural aka bar mata gashin, steaming kawai aka ƙara mata bayan wash and set, sai kyalli gashin yake da sheƙi, daman baƙi ne siɗik shiyasa sheƙin yay yawa, Hafsa ma aka wanke mata nata, kafin magrib suka dawo gida, da wuri Hajar ta kwanta sbd ciwon kan da ya dameta uwa uba faɗuwar gaban da take fama da ita, washe gari da sassafe wacca za tay mata lalle tazo, saida tayi breakfast wanda kawai turawa take snn ta zauna aka fara shaɗana mata lallen, jan lalle kawai akay mata banda baƙi, inda za ai baƙin akay mata shi da ja, waoh lalle ya samu inda yake so wato farar fata ga kuma jiki yaji gyara, duk da yadda kanta ke ciwo haka ta jure aka rangaɗa mata kunshinta, mai lallen ce ta yarfa mata kitso sirara mai kyau two steps, sha biyu na rana angama mata komai, tayi kyau harta gaji kamar a sace ta, kaf suka shirya suka wuce ainahin gidan biki sbd a ranar akwai ƴar gaɗa da ƙawayenta suka shirya. lfy ƙalau aka gudanar da shagalin gaɗa a wani kango da aka gyara tsaf dake bayan gidansu, washe gari Alhamis saura kwana ɗaya ɗaurin aure wato ranar Juma'a, a ranar akay walima wacca ta ƙawatu matuƙa daidai gwargwado, Hajar tasha kyau har ta gaji. Maama kam bata tsoma hannunta akan komai ba haka ƴan ci ku bamunta, saidai fa zuciyar nan baƙi ƙirin tamkar ta iblus. ★Baba ne zaune bisa bencin mai siyar da dankali da doya a bakin titi, mai dankali dake cin banɗashen gurasa yace "mal Adamu gobe ne ko?", Baba yace "insha Allah, bayan Sallahr Juma'a za'a ɗaura", mai dankali yace "anan ƙofar gidan naka?", Baba yace "Eh", mai dankali ya luƙa wata ƙatuwar yankan gurasa baki yace "so samu ayi a masallacin juma'a na unguwar nan, yafi sarari kuma ga albarkar mutane", Baba yace "Eh saidai nafi son a ɗaura a ƙofar gidana, ƙofar gidansu yarinya", mai dankali ya jinjina kai yace "hakan ma yafi wllh, Allah ya kaimu goben", Baba yace "Ameen". wata shimfiɗeɗiyar mota mai numfashi ce tazo ta wuce, har tayi nisa sai kuma ta dakata kafin ta dawo da reverse, adaidai saitin benci da Baba da mai dankali ke zaune ta tsaya, tsayuwar motar a wajen ya katse musu firarsu, mai dankali ya suɗe hannu ya miƙe ya isa gaban motar sbd a zatonsa siyar dankalinsa ko doya za ai, tsaye yayi bakin motar yana gwalo ido yana jiran a buɗe ayi masa ciniki, da yake glass din motar tint ne don haka ba'a ganin wnda ke cikinta, back seat aka buɗe a hankali, wani mutum ne ya fito wnda yake sanye cikin wata shegiyar shadda, kawai kallon Baba yake kamar yadda Baban shima ya ƙura masa ido, mutumin ya saɓa babbar rigar jikinsa yana micincina idanu, miƙewa Baba yayi daga kan bencin, mutumin ya tako har kusa da Baba yace "Adam", Baba da shima ya ganesa ainun yace "Muktar", Alhj Muktar ya miƙawa Baba hannu sukay musabaha yace "duniya mai yalwa, Adam daman kana garin nan?", Baba yayi murmushin manya yace "Muktar ai kai zan tambaya daman kana garin nan, tinda nidae a sanina ai kana Abuja", Alhj Muktar yace "shekara ta sha biyar da baro Abuja na dawo Kano", Baba yace "ba masaniya", Alhj Muktar ya gyara babbar rigarsa ya samu waje ya zauna kan benci, Baba ma ya koma ya zauna, Alhj Muktar da yake jin wani daɗi na ganin aminin nasa da ya jima yana nema yace "ya bayan saduwa, ya iyali?", Baba yace "bayan saduwa sai alkhairy, iyali lfy alhmdllh an gode Allah, ya naka iyalin Muktar?", Alhj Muktar yace "Alhmdllh, amma dai ba'a kano kake zaune ba?", Baba yace "kano nake zaune Muktar", Alhj Muktar yace "baka koma Yola ba knn?", Baba yace "Eh, nan nake rayuwa da iyalina saidai dangina na can Yola", Alhj Muktar yace "masha Allah" ya faɗi hakan yana duba tsadadden wrist watch ɗin hannunsa, Baba yace "shekara da yawa Muktar, ban taɓa tunanin zan sake ganinka ba", Alhj Muktar yace "ikon Allah....", bai ƙarasa maganar ba drivern sa ya fito hannunsa riƙe da waya dake tsuwwa, russuna yayi ya miƙa masa hannu bibbiyu cike da girmamawa yace "ranka shi daɗe ana kira", Alhj Muktar ya amshi wayar snn ya ɗaga kiran, maganar da bata wuce ta minti ɗaya ba yayi ya katse yana kallon Baba yace "Adam, zan sameka gobe a nan wajen", Baba yace "Eh to, ba damuwa zaka samen", Alhj Muktar yace "ko dai anan unguwar kake da zama?", Baba ya gyaɗa kai yace "a nan nake", Alhj Muktar ya jinjina kai yace "to ko bayan nan akwai wani wajen da zan iya samunka, insha Allah gobe fa zan dawo Adam", Baba yace "idan ma baka sameni anan ba, kana tambayar gidan gini shknn", Alhj Muktar yayi ajiyar zuciya ya miƙe, ya bawa Baba hannu sukay sallama snn ya doshi motarsa da driver ya buɗe masa ƙofa, mai dankali da ke daskare tin ɗaxu yaja baya gudun kar a markaɗe masa ƙafa, saida motar ta ɓace snn ya juyo ya kalli Baba, ya ƙaraso ya zauna yace "mal Adamu, wnn mutumin fa?", Baba yace "mutumin arziƙi wanda ya gaji ainihin arziƙi ba ƴan tashi firgigit ba, Muktar knn", mai dankali ya kasa kunne yace "yo Mal Adamu aini a duhu ka sake dulmiyani, ai ban gane me kake nufi ba", Baba ya dubesa yace "hmmmm, Idi knn" daga haka bai sake cewa komai ba. ★Ranar ta yau itace fa Juma'a, ranar ɗaurin auren Hajar, tin bayan sallar asuba ƴan uwan Umma suka ɗora sanwa, tuwo suka mulluƙa aka ɗaɗɗaura shi a leda aka zuba a ƙatuwar warmer, dabgen miyar taushe da taji tantakwashi itama aka juye ta a warmer, bayan nan aka shiga tuyar wainar shinkafa da sinasir, ga kuma gurasa da Mu'azzam ya kawo buhu guda. kai Hajar dai mai ƙashin arziƙi ce, tinda aka fara shagalin bikinta ba ai abu na ƙaranta ba duba da cewa gidansu ba masu hannu da shuni bane, komai an yisa cikin wadata, wnn magana ake ta masu arziki da yalwar zuci bata masu kuɗin banza da basu ciyuwa ba saidai a fito daga gida ana ƙombo, yo wasu masu kudin ma ai gidan su living hell ne. da gyatsine Balaraba ta shigo tsakar gida, duk wanda ke tsakar gidan nan kallon hadarin kaji tayi masa kafin ta faɗa ɗakin Maama, a karo na farko da Maama ta washe haƙora tin wayewar gari, Balaraba tace "wai haka aka mayar miki da gida sai kace na mahaukata Rabii", Maama ta taɓe baki tace "uhmm, baƙin cikin da nake shaƙa yafi ƙarfin kwatance", Balaraba ta ƙarewa Sa'adatu da Maimuna dake bacci kallo tace "su kuma basu tashi ba", Maama tace "ai jiya ba a barmu munyi baccin kirki ba a gidan nan", Nabilah da ke malelewa ƙasan siminti tace "Anty Balaraba ina kwana", Balaraba tace "yawwa". Maama ta matso kusa da Balaraba ta rage murya can ƙasa tace "kinga dai babu wani cigaba, anya kwa aikin malamin nan yayi?", Balaraba tayi yadda Maama tayi tace "hmm ai zuwa nayi na tayaki farin ciki, snn nima nasha kallo, don tinda malamin tsamiya yace ba aure to magana ta ƙare, kedai kawai mu zuba ido", Maama tayi ajiyar zuciya ta gyaɗa kai tamkar tsohuwar ƙadangaruwa. Tin daga soro har zuwa ƙarshen lungun ƙunshi aciki yake taf da jama'a, maza wanda suka zo halartar ɗaurin aure, ƴan uwan Baba na Yola da abokan arziki, ga dangin umma. daga soro kuma waliyyin Amarya da sauransu ne zaune suna jiran dangin Ango, lokacin ɗaura aure harya gota amma har yanzu dangin Ango basu hallara ba. Naseer da ke zaune soron ya dubi agogon hannunsa, yayi kyau sosai cikin farar shaddar da ya saka ta ankon da sukay shi da Huzaifa da Mu'azzam da kuma mahaifinsu, Naseer yace "lfy kuwa, ya har yanxu basu iso ba", Bappa ƙanin Baba wanda shi ne waliyyi yace "Baka da lambar wani daga cikin dangin Angon?", Naseer yace "ba nida ita Bappa", Mu'azzam ya shafa aljihun wandonsa yace "bari ni na kira Bappa", Bappa yace "yawwa, marmaza kira su, jama'a na jira", Mu'azzam ya ciro wayarsa daga pocket ya shiga kiran Nura Ango tinda lambarsa yake da ita, sau uku ya kira tanata ringing amma ba'a ɗaga ba. tsayawa yayi yana kallon uncle din nasa, Bappa yace "ya akay?", Mu'azzam yace "ba'a ɗauka ba"..........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {31..} A tare Baba da Bappa suka dubi Mu'azzam, Naseer yace "ka sake kira", Mu'azzam yace "tom" snn ya sake dialing numbern Nura, respond din dai daya ne, Baba da hankalinsa ya fara tashi yace "A ɗan jinkirta zuwa nan da minti goma sha biyar, ko wani uzirin ne ya riƙesu..", Bappa ya gyaɗa kai yace "ai ba jiran bane damuwa, jama'ar da suka taru kuma ba a rasa masu wani appointment din bayan wnn ba", Naseer yace "insha Allah yanxu zasu ƙaraso". Bappa yace "toh Allah yasa kar abar mutane a tsaye", kai har minti sha biyar da Baba ya ambata babu alamar dangin ango, tuni mutane suka fara canza fuska harda masu cewa su sauri suke, a yanxu kam hankalin Baba ya kai maƙura wajen tashi, Mu'azzam kam tinda ya koma gefe yake kiran lambar Nura. Naseer yanata duba agogon wayarsa, Bappa ya sharce zufar da ta wanke masa fuska sbd zafi, soron a cike yake da mutane gashi kuma ba a aiwatar da abinda ya tara jama'ar ba. kai abu fa ya fara wuce jira domin har an fara sidetalks, Huzaifa ne ya fito daga cikin gida ya durƙusa gaban Bappa yace "ko muje gidan nasu a jiyo lfy tinda nan gangare ne bamu da nisa", Bappa ya karkaɗa ɗan yatsansa yace "samm, ba zamu zubarwa da kanmu mutunci ba, a cigaba da jiran nasu, ai idan matsala ce waya zasu bugo", Huzaifa ya tashi ya koma kusa da Mu'azzam yana tambayarsa ko ya samu lambar. Daga ta cikin gida kam gidan biki ya ɗau harami, Umma sai warkajaminta take cikin riga da zani na atamfa mai shegen kyau, ta kashe ɗaurinta ture kaga tsiya, Hajar kam tana ɗakin Baba tare da ƙawayenta, kai kana kallonta kasan itace Amarya, tayi kyau harta gaji, abinda yafi birgeni da kwalliyarta shine yadda tayi maintaining natural beautyn ta, ba wata make-up da akay mata, Hafsa ce ta gyara mata fuska, powder mai tsane gumi kawai ta shafa mata sai zizaren kwalli da kuma colourless lip gloss wanda yasa pink lips ɗinta shining matuƙa, sassanyar kyau tayi kam ba ƙarya, ko nanda shekara ashirin ba a kalli hoton bikinta ayi dariya ba, dan wnn make-up ɗin ta zamani canja kamanni take ainun. Zainab ta kalli agogon wayarta tace "uhmm yaci ace an ɗaura fa, Hajar ta kusa zama matar ya sayyadi Nura", murmushi Hajar tayi tana jin wani daɗi har cikin ranta, hannunta da yaji zanen ƙunshi ta saka ta janyo wayarta, mesaage din da ya turo mata yau da safe ta binciko, ta karanta fuskarta ƙunshe da murmushi sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana juya lulu eyes ɗinta da yayi wani fari sol tamkar madara sbd kwallin da aka zizara masa, Hafsa tace "ko na zubo mana abinci ne?", Zainab tace "Eh kam gwara muci yanxu don nasan bayan ɗaurin aure sha'anin yini zamu shiga", Hafsa ta fita tsakar gida ta fara neman Anty tinda itace incharge of abinci, a ɗakin Umma ta sameta tana zuba tuwo sinasir wainar shinkafa da gurasa a mabanbantan warmers, Hafsa tace "Anty zan zuba mana abinci", Anty tace "tom ga plates can, idan kin gama zuba muku ki fita ki kiramin Mu'azzam ko Abdallah su fitar da na ƴan daurin aure gashi nan na fitar musu da nasu", Hafsa tace "tom", ta dauki plate ta zuba musu waina da sinasir, wani plate ɗin ta ɗauka ta zuba miyar taushe da isasshen tantakwashi, saida ta kai abincin ɗakin da suke snn ta fito ta doshi soro, leƙawa tayi waiko zata hango Mu'azzam amma bata ganshi ba, juyawa tayi kawai zata koma gida sai kuma ta tsaya tana sauraron wasu maganganu, cikin gida ta koma ta tarar da Anty ta fito tsakar gida, wajenta ta isa ta rage murya tace "Anty, kinji wai har yanxu dangin Angon basu zo ba", Anty tace "kamarya basu zo ba ai na ɗauka ma an gama ɗaura aure shiyasa nace ki fita kira Mu'azzam", Hafsa tace "A'a wllh ba a ɗaura ba", Anty tace "ikon Allah ko mene ya makarar dasu". Hafsa tace "bari naje muci abinci" da haka ta shige wajensu Hajar. wata shegiyar dariya Maama ta ɓarke da ita ta miƙawa Balaraba hannu suka kashe, Maama tace "ga dukkan alamu aiki yayi kyau, kinga har yanzu mirsisi banji maroƙi ya ambaci cewa an ɗaura aure ba", Balaraba tace "hmm ke dai bari, yanxu kawai tashi mu fita tsakar gida yadda zamu sha kallo muga ƴan bori", Maama ta tuntsure da dariya zuciyarta wasai tace "wllh kam ƴan bori, dan wllh tllh idan aka fasa auren nan tsaf faɗima za tayi bori", su Nabilah dai kawai binsu suke da kallo don basu rafko jirgin ba, miƙewa Maama tayi ta fita tsakar gida Balaraba biye da ita, kawai kallon Umma take tana yamutsa fuska cike da tsantsar tsana. A hankali yake shigowa cikin lungun yana ratsa mutane da suke basa hanya da kansu sbd shigarsa ta kamala, hehehe akace kuɗi ƙumbar susa, yana zuwa ƙofar gidan nan ma aka bashi hanya, ido huɗu sukay da Baba da ya kafe ƙofa da ido yana fatan dangin ango su shigo, Baba ya goge fuskarsa da handkerchief ya miƙe tsaye yace "Muktar, barka da isowa", Alhj Muktar yace "Amma Adam jiya fa muka haɗu da kai amma baka sanar min da abin arziƙin nan ba", Baba dai baice komai ba sbd hankalinsa baya jikinsa, Alhj Muktar ya gaggaisa da mutanen soron snn ya samu waje ya zauna. ★Wata zufa ce mai shegen yawa take tsattsafowa Nura, tamkar ƙaramin yaro haka yayi dafa'an gaban Hajiyarsa, fuskarta a murtuke tamkar baƙin hadari, Nura da zuciyarsa ke wani irin tafarfasa gami da dagargajewa yace "dan girman Allah Hajiyarmu kar ki min haka, kiyi haƙuri dan Allah", Hajiya dake zaune bisa kujera ta wani harɗe ƙafa tace "Nuraddeen", yace "na'am Hajiyarmu", with seriousness in her tone tace "matuƙar ni na kawoka duniya, matuƙar ni na ɗauki cikinka na wata tara, matuƙar ni na shayar da kai, matuƙar ni na raineka, matuƙar ina da daraja da kima a idonka to nace bana son auren nan, nace a fasa yin sa bazaka auri yarinyar ba", wata gudumar tashin hankali ce ta doka a kwanyarsa, kansa ya ɗau zafin da ya saka jinin jikinsa tafarfasa wanda ya linka tsiyayar gumi a sassan jikinsa, tamkar wanda aka sharawa ruwa haka gumi ya jiƙasa, farar Sabuwa shaddar jikinsa mai kyalli ta jiƙe sharkaf, idonsa da ya rine yayi jajur ya ɗago yace "Hajiyata, karki min haka dan Allah, me yasa.....", tsawa ta daka masa tace "tambayata kake Nuraddeen, akan wata zaka zo ka titsiyeni kana min tambaya sai kace sa'arka, wllh tllh indai baka tashi daga gabana ba yanzun nan saina tsine maka, kaji mu da mara kunyar yaro, daman an haifi wata yarinya a duniyar nan da zaka zauna a gabana ina fada kana fada akanta, to wllh kar a kuskura a ɗaura auren nan na gaya maka", shi dai kawai kallonta yake sbd canzawar da tayi, kamar ba Hajiyarsa ba, wacca bata masa tsawa, wacca kullum cikin saka masa albarka take, sai kace wacca aljanu suka shafa, sai ranar ɗaurin aure za tace a fasa, to me yake faruwa ne, kamar ba ita bace ta daɗe tana jiran wnn rana, guiwa a sace ya miƙe ya fita daga palourn nata, Babban palourn gidan ya shiga inda Uncles da kuma Aunties ɗinsa ke jiransa, tin ɗazu da Hajiya ta tubure aka kasa shawo kanta shine yace zaije da kansa ya bata haƙuri, shimfiɗar fuskarsa ma kaɗai amsa ce, kallonsa suka ringa yi kafin Uncle ɗinsa Saminu yace "ta haƙura Nuraddeen", Nura ya haɗiyi wani yawu wanda ya gagara wuce maƙogoronsa yace "A'a, tace tsine min za tayi", baki buɗe Saminu yace "A haba dai, ina zuwa", ya miƙe ya shiga palourn Hajiyar, haj Yahanasu ƙanwar Hajiya ta miƙe itama ta shiga palourn Hajiyar, Nura da kansa ke juya masa ya koma da baya ya tsaya a bakin palourn, duk abinda suke cewa yana ji a inda yake tsaye daga bakin ƙofa, Hajiya har ƙwarewa tayi tana kumfar bala'i ita Nura ba zaiyi aure ba, haj Yahanasu ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tace "Haba dan Allah yaya ki yiwa yaron nan adalci mana, mene dalilinki da zaki ce ba zai yi aure ba?, ki dubi Allah kuma kiji tsoronsa karki ɗauki haƙƙin yaron nan dan kina matsayin mahaifiyarsa", Hajiya tace "dakata Yahanasu karki min wata maganar banza a nan, cewa nayi kar yayi aure, ni ban hana Nuraddeen aure ba, abinda nace shine ba zai auri yarinyar can ba", haj Yahanasu tace "Yaya karki datse soyayyar dake tsakanin yaran nan dan girman Allah...", a matukar hasale Hajiya tace "Yahanasu karki kaini bango, dan wllh tllh zan iya zazzabga miki marii, kuma zan tsinewa Nuraddeen Albarka", sai a yanxu Saminu ya tanka yace "Hajiya ayi haƙuri, Nura fa ba yaro bane, tinda har yace aure zaiyi to ayi masa...", hannu Hajiya ta ɗaga masa tana karkaɗa ƙafa tace "wai ku me yasa baku da hankali ne, nifa ban hana Nuraddeen aure ba, amma tinda har kun ɗauki haramar fassarani baibai, bari na kashe bakin tsanya, ka aura masa ƴar wajenka Maryam yanzun nan, ai yarinyar na sonsa shine ya ƙi yace wai ƴar gidan gini yake so, ai aure dai aure ne ko wane iri ne, na yarda a aura masa Maryam a maimakon ƴar gidan gini", Nura ya jinginar da kansa a bango ya lumshe idanunsa da suke masa zugi, a zuciyarsa ya furta "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", wai shine zai rasa Hajar ɗinsa, wnn wace irin mummunar ƙaddara ce, shekara sama da goma ya rayu da soyayyar Hajar ɗinsa, tin tana ƴar yarinya yake sonta har lokacin da ta mallaki hankalinta ta gane kuma Allah ya haɗa zuciyoyinsu, ya sake furta kalmar "innalillah wa'inna ilayhirraji'un" a fili. Saminu ya shafa tsigaggen gemunsa yace "anyi haka kuwa Hajiya, karfa ayi abinda zai ɓata zumunci", Hajiya tace "wnn abu ai saidai ya gyara zumunci Saminu, idan ka amince ka bayar da Maryam magana ta ƙare, na gaya maka Maryam tana sonsa, tin tini nasan da hakan har maganarta nayi masa kwanaki", Saminu ya sauke ajiyar zuciya don sosai ya aminta da hakan, barin ma da yaga Nura ya fara tara abin duniya. cikin mintinan da basu wuce ashirin ba aka ɗaura auren Nura da Maryam a babban palourn gidan, Nura da already ya fara ganin baƙi baƙi ya tashi yana haɗa hanya ya shige ɗakinsa. daga nan kuma wani ƙanin Hajiya ya bada shawarar cewa aje gidansu Hajar a sanar musu cewa an fasa auren, su uku ne suka shirya suka nufi gidan. wajen da aka bubbuɗa musu a soron suka zauna, wani sanyi Baba yaji a zuciyarsa, Bappa kam kallonsu yake ganin hannunsu siƙam babu goron ɗaurin aure, ƙanin Hajiya wanda shine Babba a cikinsu ya fara koro bayani, rufa rufa yayi ya musu bayani mai cike da nutsuwa ta hanyar da bai bayyana ainahin abinda ya faru ba, sarawa kan Baba yayi ya miƙe yace "ku dai ba mutanen kwarai bane wllh, baku san darajar alƙawari ba, kunsan baku shirya aurar da dan naku ba kuka nemi da a basa auren yarinya....", sarƙewa maganar tayi ya fara tari, da sauri Naseer ya miƙe ya riƙosa yana ƙoƙarin zaunar dashi, Bappa ya gyaɗa kai cike da takaici yace "Allah ubangijj ya musanya mata da wanda yafi ɗan ku Alkhairy a gareta, muma mun fasa aura muku ƴar mu", Saminu yace "Ayi haƙuri, dan Allah idan an nutsu kuje ku kwashe kayanku da ku ka zuba a gidan yaron mu, muma wanda muka kawo muku ku dawo mana da abin mu, ai da sulhu muka zo", Bappa yace "karku damu za a dawo muku da komai tsinke ba za a bari ba". Saminu yace "Allah ya haɗa kowa da rabonsa", da haka suka bar soron, ƴan ɗaurin aure suka fara tashi da nufin tafiya, wasu na jajantawa yayinda wasu suka samu abin gulma, tamkar saukar wahayi daga sama haka soron ya amsa ƙuwwa da kalmomi shida da suka fita daga bakinsa "ina nemawa ɗana auren wnn yarinya", Bappa ya dubi Alhj Muktar da yayi wnn furuci, Baba ma da yake cikin tashin hankali ya dubesa, mutanen da suka fara tashi da sauri suka koma suka zauna, Alhj Muktar ya miƙe ya isa gaban Baba yace "Adam ina nemawa ɗana auren ƴar wajenka da aka fasa aura yanxu", wani ɗaci ne ya kauraye bakin Baba wanda yake jin tamkar an musanya masa miyau da ruwan maɗaci, expression ɗin fuskarsa bazai misaltu ba, kasa cewa komai yayi, Bappa ya girgiza kai yace "A'a, ba zan iya aura mata wanda bansan koshi waye ba, ban san komai a kansa da ya kamata na sani kafin aure ba...", Alhj Muktar yace "nine mahaifinsa, amma nasan bana daga cikin jerin mutanen da za a tambaya shaida a kansa, koda ba za a tambayeni ba amma zan faɗa cewa ɗana nagartacce ne, halayensa masu kyau ne saidai kuma ko wane ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, a matsayina na uba kuma mahaifi wanda bazan so abinda zai cutar da ƴaƴana ba toh haka zalika bazan cutar da ƴaƴan wasu ba, ba nida wata manufa na nemawa ɗana auren wnn yarinya face manufar alkhairy". Bappa ya sake girgiza kai, Naseer ma dai girgiza kan yayi kuma har cikin ransa bai aminta ba, Baba ya dubi fuskar aminin nasa Alhj Muktar snn ya dubi ta ƙaninsa Bappa, ajiyar zuciya yayi yace "Muktar na amince maka, Bappa a ɗaurawa Hajara aure da ɗan gidan Muktar".........✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {32..} Bappa ya ringa kallon Baba kafin yace "kace na daurawa Hajara aure da yaron da ba musan waye shiba?", Alhj Muktar yayi murmushin manya yace "naji daɗin wnn furuci naka, tabbas kanada gsky sosai, nima hkan zanyi idan na samu kaina a matsayinka na yanzu, kuma nima na taɓa shiga irin wnn yanayin da Adam ya shiga yanzu, na sake faɗa cewa ɗana nagartacce ne, amma idan zuciyarka ba ta aminta ba shknn ba damuwa", Baba ya dubi Bappa yace "A ɗaura mata aure da ɗan gidan Muktar, ba nida shakku ko kaɗan a kalamansa, na yarda dashi...", Bappa yayi ajiyar zuciya yace "tom, Allah ubangiji ya tabbatar da Alkairi" sai kuma ya dubi Alhj Muktar yace "fatan dai akwai sadaki a kusa", Alhj Muktar da walwala ta bayyana ƙarara a fuskarsa yace "akwai, bani minti uku", wayarsa ya ciro daga aljihu ya kira drivernsa, da sauri driver ya ɗauka, Alhj Muktar ya umarcesa da ya ɗakko masa kuɗi a mota, bayan minti bakwai driver ya bayyana a soron, ya durƙusa gaban Boss dinsa ya ciro wasu maƙudan kuɗi daga pocket ya ajiye, Alhj Muktar yace "zauna ka zama shaida", ba musu ya zauna ya tankwashe ƙafa, Alhj Muktar ya ɗauki uwar kuɗin ya ajiye gaban Bappa, Bappa ya dubi kuɗin ya girgiza kai yace "wnn kuɗin sunyi yawa", Alhj Muktar yace "ba suyi yawa ba, sadaki ai baya yawa saidai yayi kaɗan", ( Ehennnn a zamanin nan sai kaji mutane suna cewa wai ba a tsawwala sadaki ai ba siyar da yarinya za ai ba, to ga point of correction ba wani siyar da yarinya, shi fa sadakin aure baya yawa a musulunce, matuƙar kanada ikon bawa matarka zunzurutun dukiya mai yawa matsayin sadaki toh ba matsala, tauye sa shine matsala, wllh idan ma kanada arziƙin raba kano gida biyu ka bata rabi matsayin sadaki hakan daidai ne). An ɗaura auren Hajar da ɗan gidan Alhj Muktar bisa sadaki mai tsoka, ɗaurin auren ya samu shaidu masu yawa, Baba ya lumshe idonsa ya furta "alhmdllh", maroƙi ya ɗaga murya yana sanar da jama'a cewa ɗaurin aure ya kammala, muryarsa har cikin gida ta ratsa, wani mugun bugu zuciyar Maama tayi jin muryar maroƙi ta daki dodon kunnenta, ta juya ta kalli Balaraba da ta hangame baki har ƙuda na ƙoƙarin afkawa ciki, Wasila ta ɗaga zureren hancinta sama ta rangaɗa guɗa, murmushi mai kyau Umma tayi. Maama da idonta ya kisfe tsabar takaici tace "wllh sai malamin nan ya biya ni kuɗi na, kadan ba sai ya biya ba", Balaraba tace "abin fa da mamaki, tinda nake dashi bai taɓamin aiki baici ba, wllh a tarihin aikinsa ma baya faɗuwa, gaskiya akai abinda ya faru Rabii", Maama tace "Eh ai kam ga aiki nan na gani", Balaraba ta dafe kai tace "Rabii akwai lauje cikin naɗi, mu tsaya dai muyi kallo". Mu'azzam ne da Huzaifa suka ringa firfita da abinci, walima aka baje a soro ana kwasar dabge. Alhj Muktar da Baba suka fita daga soron zuwa can inda babu taron jama'a, godiya Alhj Muktar ya ringa yiwa Baba, shima Baban godiya yake masa domin kwa ya fitar dashi kunya, Alhj Muktar yace "insha Allah da yamma zasu zo", Baba yace "bana ganin ɗaukar yarinyar nan zai yiwu a yau, a bari zuwa gobe, kaga dai yadda lamarin ya jirkita, shima yaro ai sai an sanar dashi...", Alhj Muktar yace "toh ba damuwa da yau da gobe ai duk ɗaya ne, karka damu yaro a shirye yake", Baba yace "nagode fa, kaxo domin mu gana sai kuma wnn batu ya gifta bamu samu lokacin ganawarba", Alhj Muktar yace "daman nazo ne domin naga inda kake Adam", Baba yace "Allah sarki", Alhj Muktar ya miƙa masa hannu sukay sallama snn ya tafi. saida rurumar ƴar ɗaurin aure ta tsagaita snn Baba ya samu shiga gidan nasa, nan fa akay masa caa da gaisuwa da kuma fatan alkhairy, da sakakkiyar fuska ya ringa amsawa yana neman Umma da idanu, daga ɗakinta ta fito fuskarta ƙunshe da walwala, Baba ya dubeta yace "ɗakinsu Nasiru a buɗe yake?", tace "bari na duba", ta wuce ƙofar ɗakin ta tura taga a buɗe take, tace "Eh a buɗe take", ya ƙarasa ƙofar ɗakin yace "ina son ganinki" ya shiga ciki. afujajan Maama ta fito daga ɗakinta jin muryar Baba, wuwwurga idanu ta fara yi duk ta jiƙe da gumi, hangosa tayi lokacin da ya shiga ɗakinsu Huzaifa, da sauri ta wuce har tana ƙoƙarin bangaje Umma ta shiga ɗakin, kallonta Baba da yake shirin zama yayi, Umma dai ta shigo ta samu waje ta zauna, daga tsaye Maama tace "tin safe ka hana mu kudin abinci a gidan nan mal", yace "kuɗin abinci kuma Rabii?, ga abinci nan ku zuba kuci", tace "a ina yake abincin?, ni bangani ba", ya ciro 1k daga aljihun gaban rigarsa ya miƙa mata yace "gashi", amshewa tayi tace "yo da an barni da yunwa nida ƴaƴana", ta juya zata fita sai kuma ta dubi Umma tana yamutsa fuska, dawowa tayi ta zauna ta wani sha kunu, Baba yace "ba na baki kuɗin abincin ba", gefe ta kalla tace "Eh anan zan zauna", Baba yayi ajiyar zuciya baice komai ba, shiru ɗakin ya ɗauka babu wanda ya sake magana, bayan wani lokaci Umma tace "mal ko na tafi ne akwai baƙi da suke jirana", Baba ya girgiza kai yana kallonta yace "Faɗima", tace "na'am". kaf ya wassafa mata abinda ya faru akan auren ƴarta. wata katafariyar shewa Maama ta daka, ta miƙe da sauri ta fice tana gyara haɓar zaninta, saida ta shiga tsakiyar ƴan biki tace "ahayye riiiiiii, an yanka ta tashi, kowa ya baje an gama biki", ta afka ɗakinta domin ta sheƙawa Balaraba nasarar da suka samu, murna suka shiga ɓarkawa a ɗaki tamkar waɗanda akay wa bushara da gidan aljanna, sosai suka saki baki suna zance sbd su Nabilah sun fice daga gidan. Umma ta tuge ture kaga tsiyar kanta ta share zufar da ta tsattsafo mata tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mal dama baka ɗaura mata aure da wani ba...", katseta yayi yace "karki ɗaga hankalinki Faɗima, kiyi mata addu'a Allah yasa hakan shine alkhairy a gareta", tace "amma mal...", yace "idan kika ɗaga hankalinki waye zai kwantarwa da Hajara nata, itace wacca ya kamata a duba, idan kika samu nutsuwa itama hankalinta ba zai tashi sosaii ba, ƙaddararta ce, ko wane dan Adam da irin tasa, Allah ya rubuta ba Nura ne mijinta ba, ni kuma na gaya miki mutumin da na bawa auren Hajara bashi da matsala", Umma ta ajiye deep breathe tace "Allah yasa hakan shine alkhairy, amma taya ya zan sanar da ita?", Baba yace "she's your daughter fa, ki kiramin ita", ta gyara daurin dankwalinta ta miƙe ta fita da wani facial expression a fuskarta. ɗakin Baba ta nufa inda Hajar da muƙarrabanta ke zauna, a bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsu, Umma ta dubi Hajar da tayi wani kyau wanda bata taɓa irinsa ba a rayuwa tace "kije inji Babanku yana ɗakinsu Mu'azzam", Hajar tace "tom", ta saka wayarta acikin handbag dinta, gyara yafen mayafinta da yake fitar da ainahin ƙamshin kabbasa tayi, ta saka takalminta flat mai kyau snn ta fita. Umma kam ɗakinta ta shige, ta matsar da kayan dake gefen gado ta zauna ta dafe kanta, a haka Anty ta shigo ta sameta tace "Adda, lfy kuwa?, ya da tagumi haka a lokacin farin ciki", Umma ta ajiye numfashi a hankali tace "Jamila", Anty ta samu guri ta zauna sbd yanayin ƴar uwarta ta, Umma tace "kin san kwa bada Nura aka ɗaurawa Hajara aure ba", Anty ta gwalo ido tace "ban fahimce ki ba Adda", Umma tace "uhmmm" ta labarta mata abinda Baba ya sanar da ita, shiru Anty tayi tana kallonta, kasa cewa komai tay kawai juya lamarin take a kwanyarta, can tace "kiyi haƙuri Adda amma sai naga kamar kun yiwa Hajar gaggawa, wai har nawa take har yanxu fa bata cike shekara 18 ba, dan ma tanada garun jiki amma wllh bata isa aure ba...", Umma tace "ba haka bane Jamila, muma ai bamu kaita ba aka kaimu gidan miji, kuma muka zauna", Anty tace "haka ne Adda, duk yadda zamani ya juya haka za a tafi dashi, a wnn zamanin aure yafi kyau idan yarinya ta kai shekaru 20, ta mallaki hankalinta...", Umma dai tayi shiru, Anty tace "Hajar ɗin ta sani?", Umma tace "Eh nasan yanzu ta sani, Mal ya sanar da ita". Hajar ta fito daga ɗakinsu Mu'azzam ƙafarta na harɗewa, da gudu ta shige ɗakin Umma ta zube a ƙasa snn ta fashe da wani matsanancin kuka mai ban tausayi, runtse ido Umma tayi tana jin itama kamar tayi kukan, Anty ta taso ta ɗagota ta rufe mata baki tace "shhhh, kiyi haƙuri kinji", kuka take kamar ranta zai fita. ★Mami ta murɗa handle ɗin ƙofar part ɗin Abba, da sallama ta shiga, Abba dake zaune kan kujera two sitter ya amsa mata, a gefensa ta zauna, ta ɗauke hularsa dake hannun kujerar ta ajiye bisa huge Centre table dake palourn, tace "gani yallabai, amma dai ba'a masallacin sarki kayi juma'a ba?", Abba ya sosa forehead dinsa yace "Eh, a can Masallacin Abubakar Siddiq nayi", tace "Ohk", yace "yau ce ranar da Uthman zai dawo ko?", tace "insha Allah, ɗazu na gama waya dashi sun ma taso, 9pm za suyi landing", ya gyaɗa kai yace "Alright, a yau da na fita ban dawo gida ba saida na ɗaurawa Nurain aure", cike da mamaki Mami ta dubesa har tana haɗe gira tace "aure kuma yallaɓai?", yace "yess, so start all the necessary preparations tommorow insha Allah za aje a ɗakko masa matarsa", Mami was speechless na kusan 1minute kafin tace "but without his consent aka ɗaura", yace "Do i need his consent, he is my son, he most respect my decision", Mami tace "this is a different case...", yace "i know, a da fa haka ake daura maka aure ba tare da kasan waye ka aura ba, iyaye ne kawai suke haɗinsu", Maami exhale heavily tace "wa ka aura masa?", yace "sunanta Hajar, ƴar wajen abokina ce", tace "Allah ya basu zaman lfy", yace "Ameen, key din gidansa na wajenki ko?", tace "Eh suna wajena", yace "ohk, sai a duba gidan nasa kafin Allah ya kaimu gobe", tace "sure, za ai komai". Mami na fitowa daga wajen Abba ta shiga kiran ƴar uwarta Zulaiha, tana picking Mami tace "idan ba damuwa ina son ganinki Zulaiha", Anty Zulaiha tace "ohk, when?", Mami tace "idan ma zaki taho yanxu to nafi son haka", Anty Zulaiha tace "is everything ok?", Mami tace "sure, komai lfy urgent abu ne ya taso", Anty Zulaiha tace "Shknn I'll be there right away", da haka Mami ta katse kiran thinking of another thing to do, After 40mins Anty Zulaiha ta iso tare da Khausar, direct palourn Mami suka wuce, Khausar ta sunkuya ta gaida Mami, amsawa Mami tayi tana tambayarta school, Noor ce ta fito daga bedroom din Mami sanye da english wears, gaisawa sukay da Anty Zulaiha snn taja hannun Khausar suka fita daga part din zuwa huge room ɗinta, Anty Zulaiha ta cire gyalenta ta gyara zama sosai bisa executive sofar palourn tace "wai mene ne abinda ya taso urgent?", Mami tace "ɗaxu Abba da ya dawo daga masallaci yake gayamin cewa wai ya ɗaurawa Nurain aure da ƴar abokinsa", Anty Zulaiha tace "ikon Allah, daman har yanzu ana irin wnn haɗin", Mami tace "nima dai haka nagani, saidai fatan alkhairy, wai sai gobe za a kawo amaryar, yanzu dai gidan Nurain din nake so aje a duba, an riga anyi furnishing dinsa amma kuma almost 8months ba shigesa ba, kinga za aje a dudduba abinda yayi damage, komai dai ya zama intact", Anty Zulaiha tace "toh ai wnn ba aikin mu bane, na dangin Amarya ne", Mami tace "yess nasu ne, Abba ne yace a buɗe gidan a gyara", Anty Zulaiha tace "toh shknn, ai sai a tura ma'aikata su gyara, su firfito da abinda yayi damage, mu kuma in Allah ya kaimu goben sai muje mu gani", Mami tace "nima haka nake tunani, kawai a tura masu aiki", Anty Zulaiha tace "toh kuma haka za a ajiye yarinyar a gidan babu mijinta", Mami tace "No, ai yau Nurain ɗin zai dawo", Anty Zulaiha tace "toh masha Allah abu yayi kyau kinga yana dawowa sai yayi Settling down, Allah yasa ta zame masa babban tukuici na abinda Ruqayyah tayi masa", Mami tace "Ameen". labourers aka tura katafaren gidan Nurain, tin daga sama har ƙasa aka shiga tsaftacesa, babu wani datti sai dust da dry falling leaves. ★Da misalin ƙarfe takwas da minti hamsin na dare ya parker luntsumemiyar motarsa a parking space da ke babban international airport na garin kano, waiting area ya nufa ya zauna yana kallon wajen da matafiya suke ɓullowa, yana jin announcement na saukar jirgin da ya iso daga India ya miƙe tsaye, few minutes kam suka fara fitowa, shine na biyar, sanye yake cikin ƙananan kaya da Pcap saman kansa kamar yadda ya bar 9ja, hannunsa daya na riƙe da trolley da yake ja yayinda ɗaya yake maƙale cikin sweet black pant nasa, Farooq na hango brother din nasa ya fara tafiya towards him, Nurain ya ciro hannunsa daga pocket ya dunƙulesa, shima Farooq dunƙule hannun nasa yayi, suna haɗewa suka haɗa hannayen nasu, Nurain yayi murmushi yace "hey dude", Farooq yayi masa side hug yace "barka da zuwa punk". saida aka gama checking luggage ɗin Nurain snn suka baro airport din, Farooq dake driving da mininum speed yace "ko dai wajen amaryata zamu wuce", Nurain yace "No, iron lady ban shirya facing dinta ba", slight smirk Farooq yayi yace "tsohuwa mai ran ƙarfe", Nurain yace "oh God look at how you're driving, ka take accelerator", Farooq yace "as in how na take accelerator, wai naga fa Doctors suna lallaɓa lafiyarsa amma look at you kana so ayi risking taka", Nurain yayi resting jikin kujera can ƙasan maƙoshi yace "hurry up". Farooq ya ƙara gudun motar kaɗan, slow down yayi kafin ya juya kan motar ya shiga street din gidan uncle ɗinsa, a bakin huge gate ɗin gidan ya danna horn, da sauri mai gadi ya zuge gate, ya danna motar ciki, parking lots ya isa yayi parking snn ya kashe motar, yana ciro key daga Ignition yace "did you just take a nap?", Nurain ya buɗe idonsa yana kallon environment ɗin ya yake ciki, buɗe motar yayi ya fita, yayi ajiyar zuciya yana stretching kansa yace "home sweet slum".......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {33..} Farooq ya buɗe back seat ya ciro bag da trolley, ya kalli Nurain da ya gama stretching kansa yace "wai ka gaji ne?", Nurain yayi ƙass ƙass da fingers ɗinsa yace "yeah, am exhausted". da sauri Garba ya taho wajen, har ƙasa ya durƙusa yace "sannu da zuwa Alhj ƙarami, an dawo lfy", Nurain yace "yauwa Garba, ya ƙasa?", Garba yace "ƙasa tana nan yadda ka barta", tashi yayi ya gaida Farooq ma snn ya amshi bag da trolley. huge luxury main building ɗin gidan suka nufa, suna isa balcony Nurain ya danna bell, few seconds Noor ta buɗe, ta daka tsalle tace "oyoyo Yaya" sai kuma ta koma cikin palourn tana cewa "the groom is here Mami", sosai abinda ta faɗa yayi hitting eardrums dinsa, wai the groom, ya juya ya dubi Farooq yace "you", Farooq ya girgiza kai yace "nope", ai tini Noor ta shige part din Mami, Farooq ya zauna a daya daga cikin executive sofar dake babban palourn, Garba ya ajiye kayan da ya shigo dasu yayi waje, Nurain kam part din Mamin sa ya nufa, Mami ta fito daga bedroom ɗinta knn ya shigo, Pcap ɗin kansa ya cire ya zo ya rungumeta yace "i missed you Mami", Mami tace "Nurain...", Noor da ke murmushi all her white tooth out tace "Yaya sannu da zuwa", yace "lil iron lady, how are you doing", tace "am great alhmdllh", Mami tace "ina Umar ɗin?", yace "yana palour", tace "Ohk, muje can", main palourn suka fito, Mami ta zauna tace "mijin Hajiya", Farooq yayi murmushi yana shafa kansa ya zamo ƙasa ya gaidata, Mami ta amsa tace "ka ɗakko brother ɗinka knn?", yayi murmushi yace "Eh", Nurain ya zauna bisa lallausar rug din palourn ya gaisheta shima, ta amsa tana saka masa albarka, Kitchen Noor ta shiga ta ɗakko ruwa da drinks with glass goblet ta fito, kusa da Farooq ta ajiye tace "ina yina ya Farooq", yace "lfy lou Noory", tace "yasu Ummi da Aysha?", yace "suna nan lfy". Nurain yace "Abba fa?", Mami tace "yana ciki", yace "ohk bari naje wajensa", ya dubi Farooq yace "muje dude", a tare suka shiga part din Abba, Mami ta dubi Noor dake operating waya tace "ohh kin fara jarabar danna wayar ko?", tace "No Mami, course mate ɗita ce ta turomin da question na assignment", Mami tace "toh tashi ki shirya musu dining kafin su fito", tace "tom", ta ajiye wayar ta gyara hular kanta ta shiga kitchen. Abba ya kawar da system da yake operating ya daga kai yana kallon zaratan samarinsa, da Farooq suka fara gaisawa kana Nurain, Abba yace "ya aiki Engineer?", Farooq ya shafa kansa yace "alhmdllh Abba", Abba yace "toh madallah Allah ya temaka", Farooq yace "Ameen", Abba yace "Uthman..", Nurain yace "na'am", Abba yace "ya karatun, an gama lfy?", Nurain yace "Eh alhmdllh, an samu abinda aka je nema", Abba yayi ajiyar zuciya yace "masha Allah, Allah yasa ya amfana", tare suka amsa da Ameen snn suka fito. already Noor ta gama setting table, Mami tace "ga abinci kan dining", Farooq ya dubi tsadadden agogon wrist dinsa yace "wllh Alhmdllh, am full, zan wuce yanxu", yayi musu sallama ya tafi, har compound Nurain ya rakasa snn ya dawo, Noor ya saka ta kawo masa abincin nan palour ya ci don shi he don't like it eating on table, ba laifi yaci abincin cause yaji taste en abincin na Mami ne, ya ture plate din daga gabansa ya buɗe bottle water ya zuba a cup ya sha, stretching kansa yayi yana lumshe ido, duk gajiya ce ajikinsa, duk lokacin da yayi tafiya a jirgi sai yaji kamar nerves ɗinsa sunyi freezing, shiyasa yake yawan yin miƙa, Mami tace "ka je ka huta Nurain", yayi ajiyar zuciya yace "yeah", ya tashi yana massaging neck dinsa, trolleynsa ya janyo yace "ga stuff na India", Noor tace "Yaya a New Delhi ka zauna?", yace "yap, that's where my school is", da haka ya ɗauki bag ɗinsa ya haye stairs still massaging his thick neck, ya tarar da room ɗinsa a gyare tsaf tsaf komai tide, ƙamshin freshner da traditional scent mai dadi ne yake tashi, ga sanyin Ac, huge Chinese comfortable bed ɗinsa malale da white bedding. wayarsa ya ɗakko daga bag yayi powering dinta, ya cire Sim card ɗin ciki ya musanya da ainahin nasa na Nigeria, ya ajiye wayar akan mirror ya shiga bathroom domin ya sakarwa kansa warm water, ko 1min beyi ba da shiga wayarsa ta fara tsuwwa, kiran na yankewa wani ya sake shigowa, shima yana katsewa wani ya biyo baya, haka kiran yayi ta shigowa ba ƙaƙƙautawa, da sauri ya gama abinda zai ya fito, yayi wrapping kansa da bathrobe, gefen kunnensa duk kumfa sbd saurin da yayi ya fito don yaga wane yake masa wnn mummunar kiran daga kunna waya, ɗaukar wayar yayi wacca take ringing har lokacin, ya tattare gira gami da tsuke piercing eyes ɗinsa yana kallon screen ɗin wayar, sunan da yake jiki da kuma numbern ba baƙinsa bane, tabbas beyi blocking numbern ta ba amma kuma bai sake kira ba, wani ɗaci yaji a throat ensa, ya dangwarar da wayar yace "Damn it.." ★Kaf waɗanda suka zo biki sun ɗaɗe, mutanen Yola kam ana gama ɗaurin aure suka saɓi hanya, Anty Jamila sai Hafsa wacca aka bari domin ta ɗebeba Hajar kewa ne kawai suke rage a gidan, Wasila kuma ta tafi da zummar insha Allah gobe da sassafe zata dawo. da hijab ɗin da tayi sallar isha'i ta ƙudunduna ta takure waje ɗaya, a kwance take kan dardumar da ta idar da sallah, hawaye na zuba daga manyan lulu eyes ɗinta waɗanda suka ƙanƙance tsabar kukan da ta sha, ƙirjinta da maƙoranta har zafi suke sbd shessheƙar kuka, Anty ta tsaya a kanta tace "hasbunallah, Hajar ba zaki dena kukan nan ba ko?", da dasasshiyar murya tace "ba kuka nake ba", Anty tace "toh tashi zaune", a hankali Hajar ta miƙe zaune ta jingina da bango, sosai ta bawa Anty tausayi tace "za kici abinci?", ta girgiza kai tana goge kumatunta tace "na ƙoshi, bazan iya ci ba ƙirjina ciwo yake", Anty tace "sannu, ai baza ki kwanta da yunwa ba bari a siyo miki yoghurt" da haka ta fita daga ɗakin. Hafsa ta matsa kusa da Hajar tace "sannu sister", Hajar tace "wllh ji nake kamar zuciyata zata fashe, wai ba ya sayyadina na aura ba, na shiga uku Hafsa", ta rufe fuskarta da hijab ta sake rushewa da kuka, Hafsa tace "Allah ya ƙaddara ba shine mijinki ba, kiyi addu'a Allah yasa hakan alkhairy ne a gareki", Hajar na shessheƙar kuka tace "ban san fa wanda aka aura min ba, ban san wane irin mutum bane". Hafsa tace "koma waye insha Allah alkhairy ne", jinginar da kanta tayi a bango ta lumshe idonta, hawayen da suka taru suka fara zarya a kuncinta. Sallama aka rangaɗa daga soro, Anty dake tsakar gida tana waya da Mu'azzam da take basa saƙon siyo yoghurt, kashe wayar tayi ta amsa sallamar da akay, Umma ta fito daga ɗakin Baba tace "waye?", matar da tayi sallama ce ta shigo tace "Larai ce", Umma ta tsaya tana kallonta da taimakon hasken kwan lantarki sbd akwai nepa, Umma ta shimfiɗa tabarma tace "Bismillah" duk da dai bata shaida wace ce ba, dattijuwar da ta kira kanta da Larai ta zauna akan tabarmar da Umma ta shimfiɗa, gaisawa sukay, Anty ma ta gaisheta, ta dubi Umma tace "baiwar Allah kece mahaifiyar Hajara", Umma tace "Eh nice", tace "Alhmdllh, wllh tllh nice nayi muku laifi, dan girman Allah kuyi haƙuri", Umma tace "Allah sarki, laifin me kika min baiwar Allah?, ai ni ban ma shaida ki ba", tace "mahaifiyar Nuraddeen ce wanda za a ɗaura masa aure da ƴarku", tini Umma ta canza fuska, Anty da ke zaune kan ƙaramar kujera ta ɗaure fuska, Umma tace "oho, to ince dai lfy?, ai an mayar muku da kayanku", Hajiya tace "ba wnn bace ta kawoni, dan girman Allah kuyi haƙuri akan abinda mu kayi muku, wllh laifina ne shiyasa na taso takanas nazo domin na baku haƙuri", Umma tayi murmushin yaƙe tace "ba komai mun haƙura, muma Allah ya yafe mana", Hajiya tayi ajiyar zuciya tace "Alhmdllh, Allah yayi albarka, auren da aka fasa ɗaurawa da rana sai a ɗaurasa yanxu da daddare", Umma ta ajiye numfashi tace "bari nayi miki magana da baban yarinyar" da haka ta miƙe ta shiga ɗakin Baba, kaf yaji abinda ya faru don haka bai bata damar magana ba ya fito tsakar gidan, Anty ta tashi ta shiga ɗaki. Baba ya gaisa da Hajiya wacca ta shiga basa haƙuri, yace "Allah sarki, ai komai muƙaddari ne..", Hajiya tace "haka ne, amma wllh nice nan silar wnn babbar ɓarna, dan girman Allah ku yafe min, a ɗaurawa ɗana Auren da yarinyar ku", Baba yayi ajiyar zuciya yana jujjuya wnn lamari, Maama ta fito da ɗauri ƙirji da mafici a hannunta tace "haba don Allah, wllh kun fiya gutsittsira zance, kawai ku gaya mata cewa an ɗaurawa Hajara aure da wani a maimakon ɗanta", da matuƙar mamaki Hajiya ta dubeta sai kuma ta kalli Baba tace "wai haka ne?", Maama tace "Yo ya faɗa miki da bakinsa kiji, shi ya aura mata wani da ɗanki yace ya fasa", Hajiya ta fara matsar kwalla tace "wllh babu ruwan Nuraddeen, nice me laifi, ni nace a fasa auren, wllh lokacin da nake faɗa ma ban san inda kaina yake ba, dan Allah dan darajar alƙur'ani mai girma karku hana ɗana auren ƴarku", Baba yayi ajiyar zuciya gami da yin gyaran murya yace "Hajiya ai bakin alƙalami ya bushe sai dai ɗanki ya nemi wata, yanzu maganar da nake miki na aurar da Hajara", Maama na fifita da mafici tace "Atoh ai yafi dai ka gaya mata gaskiya", Hajiya ta zabga wani uban salati sai kuma ta ɗaga murya tace "Nuraddeen...", Nura ne ya shigo da sallama, daman yana soro a tsaye shine ma ya rako Hajiyar. wata iriyar zabura Hajar tayi ta miƙe tsaye jin muryarsa, ta tsaya a jikin window tana leƙen tsakar gida, wani shauƙin kuka ne taho mata da taga fuskarsa, Hajiya tace "Nuraddeen, basu haƙuri da kanka, ni kam sun ƙi amsar nawa", Nura da har fuskarsa ta faɗa na wuni ɗaya ya durƙusa, ya gaishe da Baba kana Umma da hankalinta ya fara tashi, fuska babu yabo ba fallasa Baba yace "ba ƙin haƙura mukay ba, ai haƙurin ne ma yasa na saurare ki, kuma haƙurin za kuyi Hajara matar wani ce", Nura ya zuba guiwoyinsa a ƙasa yace "Baba, dan Allah kar a rabani da Hajar, ku yafe min...", Umma ta tashi ta shiga ɗaki, Baba ya girgiza kai yace "kayi haƙuri Nura wllh an riga an ɗaurawa Hajara aure...", Hajiya ta ɓarke da kuka tace "wllh nice sila, Nuraddeen ka yafe min, ban kyauta maka ba, ban yi maka adalci ba, duk abinda nake so shi kake min, ni kuma na datse maka farin ciki, wllh ban san na aikata maka hakan ba, na ɗauka mafarki nake ashe a zahiri na aikata...", Nura kam ko fahimta me take cewa beyi ba sbd juyawar da kansa yake masa, ga wani raɗaɗi da zuciyarsa ke masa, Baba ya kawar da kai yana jujjuya wnn lamari a kwanyarsa, abu sai kace a film. Nura ya tashi yana layi ya taimaki mahaifiyarsa ta tashi itama yace "Allahumma ajirni fi musibati wa aklufuli khairan nimha", shi wnn babbar musiba ce a wajensa, ya juya yay hanyar soro, Hajar ta sulale ƙasa ta cigaba da rusa kuka da dashasshiyar murya, a ƙofar gida Nura ya haɗu da Mu'azzam da yake shirin shiga gida, cike da mamaki Mu'azzam ya dubesa yace "ya sayyadi..", Nura ya kallesa da jan ido yace "Mu'azzam" da haka yayi gaba ya fara tafiya da sauri tamkar zai tashi sama, gida Mu'azzam ya shiga, yabi Hajiya da ido wacca take ƙoƙarin fita tana matsar kwalla. yayi sallama a bakin ƙofar ɗakin Umma ya bawa Anty saƙon yoghurt da ya siyo. da kyar Hajar ta sha quartern yoghurt din, ta sha panadol sbd kanta da yake mugun ciwo. wnn night shine worst night a rayuwarta, she couldn't sleep at all even a nap. ★Washe gari da safe, Nurain na zaune a balcony perceiving the morning blessings, wayarsa yake latsawa time to tima kuma yana sipping black coffee, last night da kira aka addabesa har saida yayi silencing wayar ya samu yay bacci, da safe kam missed calls da ya shallake expectation nasa ya gani, sai kuma ta ɗora da text message, a ƙalla daga asuba zuwa yanzu da ake maganar ƙarfe bakwai da rabi ta turo masa da messages sama da goma, kuma ko ɗaya bai karanta ba, daga message ɗinta ya shigo yake wipping notifications ɗin wayar, shifa indai ya bar abu to ya barshi kenan no going back, yanada zuciya sosai saidai kuma kafin yayi zuciyar sai ransa ya ɓaci. wayarsa tay vibrating, yana dubawa yaga Abba ke kiransa, picking yayi ya kara a kunne, Abba yace "ka sameni a great room now", Nurain yace "yeah", da haka Abba ya katse kiran, ya ɗaga coffeen sa ya shanye snn ya tashi ya shiga ciki da cup ɗin a hannunsa, kitchen ya wuce ya ajiye cup din snn ya fito ya nufi great room din Abban sa. ya cire soft slippers dake clean legs ɗinsa ya shiga great room din, yana shiga Abba yayi pointing kujera yace "sit", Nurain ya zauna looking at his Father. Abba yace "Uthman, tin jiya naso nayi informing ɗinka amma na bari sai yau", Nurain dai baice komai ba kawai kallon Abban nasa yake, Abba exhale heavily yace "na ɗaura maka aure da ƴar wajen abokina...", with a weird facial expression Nurain ya dubesa, peach lips dinsa ya motsa a hankali yace "marriage..", direct Abba yace "yess, jiya aka ɗaura auren, and insha Allah today za a kai maka matarka gidanka, get ready to settle down Son".....✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {34..} Nurain was speechless at that moment, he was shocked and confused, marriage shine plan dinsa na ƙarshe a yanzu, Abba ya katse silence din da faɗin "don't you have anything to say?", Nurain ya shafa cikakkiyar sumarsa yace "Abba, kawai i don't expect this, beside ma i think am not ready..", Abba yace "wane ready kuma Nurain?, ai komai an gama, shirin da ya rage maka shine settling down, kanada gida, kanada Sana'ar da zaka riƙe even four wives, you're rigid enough, sai dai in auren da nayi maka ne baka so", Nurain yayi ajiyar zuciya yace "No Abba, i like it, sai dai akwai consequences..", Abba yace "no matter what the consequences might be you most settle down, kamar duk wani abu mai merit to definitely yanada demerit, abinda nake so da kai shine, ka amshi auren nan ka zauna da matarka lfy, Allah ya bka ladan biyyar da kay min...", Nurain yace "ba komai Abba, nagode sosai..", Abba yace "madallah, Allah yay albarka..", Nurain yace "Ameen, if you excuse me?", Abba yace "fine, you may leave", tashi Nurain yayi ya fita, shi dai bashi da wni feeling akan mattern, shi ba mai farin ciki ba kuma ba mai baƙin ciki ba, Mami ta fito kitchen hannunta rike da wani royal tea flask, ganin Nurain na fitowa daga great room din Abba ta tsaya kallon expression en fuskarsa, tasan Abba ya gaya masa maganar auren, ya zuba hannayensa a pocket walking towards her yace "i just talk with Abba", tace "ka sani knn?", yace "sure, are you happy with the marriage..", Mami tace "Eh mna, am very happy, Allah ya sanya alkhairy.." da hka ta wucesa ta shiga great room din Abba. ƙarfe sha ɗaya Sakeena ta iso gidan da kids dinta guda biyu, Aymana da kuma Ayman wanda take goyo, a part din Mami tayi branching, Mami ta dauki Ayman tana masa wasa, Sakeena ta cire veil dinta ta zauna tace "ina kwana Mami..", Mami tace "lfy lou, ya kids", Sakeena tace "suna lfy, ai Abba ma ya kusa zuwa yaye..", Mami ta shafa kan Ayman dake cinyarta tace "A'a Sakeena, wnn ɗan ne ya isa yaye?..", Sakeena tace "laa ya isa, watansa 11 fa", Mami ta haɗe gira tace "A'a gsky bai isa ba..", Sakeena tayi ƴar dariya tace "kamar haka na yaye Aymana ma..", Mami tace "ai dan an gansu ƴan lukutaye shi yasa ake ɗaukar alhakinsu..", Sakeena ta gyara zama tace "kuma a yau za a ɗakko amaryar?", Mami tayi ajiyar zuciya tace "Eh, yau da yamma ba", Sakeena tace "ƴar Abokin Abba ce ko?", Mami tace "Eh, but I don't know which one...", Sakeena tace "Alright, Allah yasa dai mai kirki ce", Mami tace "Ameen". Anty Zulaiha ma ta hallara da misalin ƙarfe ɗaya da ƴan mintina, ba ta jima ba saiga Mama Mardiyya ƙanwar Abba da kuma Umminsu Farooq, Mami tasa aka firfito da lefen Nurain na bikinsa da Ruqayyah, tace "yawwa da cewa nayi kawai sai a basu lefen idan an kawo amaryar...", Mama Mardiyya tace "Shknn kam, kinga an wuce wajen", Mami tace "to ku duba ko akwai abinda za a ƙara...", Ummi tace "wai lefen Nurain ne, ai a yadda nasan lefen nan baya buƙatar ƙari..", ai kam dai boxes ɗin nan basu da masaka tsinke acike suke ɗam ɗam, Sakeena tace "Ai da aka kaiwa Ruqayyah sun taɓasa..", Mami tace "Atampa da lace kawai suka ɗauka, kuma nayi replacing da wasu..", Anty Zulaiha tace "A wnn abu yayi, kawai miƙa musu za ai", Mama Mardiyya tace "Nurain ya bani tausayi a lokacin da aka fasa aurensa na farko, Allah yasa wnn shine mafi alkhairy", kowa ya amsa da Ameen, Ummi tace "Hajiya ma da cewa tayi zata biyoni sai kuma ciwon ƙafa ya hanata, ba mamaki idan taji dama dama tazo anjima, dan cewa tay ita zata riƙo matar Nurain", Anty Zulaiha tace "Allah sarki, ai Hajiya na ji da jikokinta..", Sakeena tace "Iron Ladyn mu akwai rigima...", Mama Mardiyya tace "gidanku, bazaku dena ce mata iron lady ba ko?", Sakeena tace "Allah ba ruwana Mama, Noory da Aysha ne suke ce mata iron lady...", Anty Zulaiha tace "toh yanzu dai da kayan lefen zamu tafi ɗakko ta knn?", Mami tace "wai da cewa nayi akai lefen can gidan Nurain, idan aka kaita can ɗin sai a basu lefen a can..", Ummi tace "Eh, hakan yayi, ba nan za a kawota ba knn?", Mami tace "gwara ta fara shiga gidanta in yaso Nurain ya kawota mu gaisa daga baya..". Haka kuwa akay ana idar da Sallar la'asar Ummi Anty Zulaiha da Mama Mardiyya suka tafi ɗakko Amarya, mota uku sukay, drivern Abba da yasan gidan shine yake musu jagoranci. Abba ya kira Baba ya sanar dashi don daman sunyi exchanging phone number. Sakeena Noory Aysha da kuma Khausar aka haɗasu da kayan lefe suka wuce gidan Nurain. ★Taci kuka harta gaji ta zubawa sarautar Allah ido, tin ɗan yoghurt din da ta sha daren jiya bata sake cin komai ba sai bayan Sallahr azahar taci awara kaɗan, Baba yana dawowa daga masallaci sallar la'asar ya sami Umma ya sanar da ita cewa su shirya yanxu za a zo ɗaukar Hajara, wani yanayi Umma ta shiga amma haka ta jure ta sanar da Anty, Anty tasa Hajar tayi wanka, babu musu ta tashi tayi, ita ta riga da ta saddaƙar tana jiran sakamakonta, asalin kayan da aka tanadar mata na zuwa gidan miji ta saka, atampa black mai manyan flowers red, da mayafi red mai stone na shuwariski mai walwali, sai handbag da flat shoe black colour, Hajar tayi kyau sosai duk da dai babu walwala a fuskarta, aihanin ƙamshinta na gyaran jiki da kuma na kayan da akay musu kabbasa ga kuma perfume sai tashi yake daga jikinta, a gefen gado ta zauna tana wasa da slim fingera dinta da suka sha zanen jan ƙunshi wanda a yanxu ya koma maroon, Hafsa ce a kusa da ita itama ta shirya abinda, Sabra na tsaye daga jikin wardrobe ta zubawa yayarta ido, Hajar ta dubi little sister ɗinta tace "zo Sabra", da sauri ta matsa kusa da ita, Hajar ta riƙo hannunta, Sabra tace "Adda me yasa ki kai ta kuka jiya?", Hajar tace "kuka nake yi sbd zan rabu da ku, ke da Umma da Baba da yaya..", Sabra ta zaro ido tace "tafiya zaki ki barmu", Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh, zaki bini?", ta gyaɗa kai da sauri tace "Eh zan biki..", Sallama ce ta ratsa tsakar gida tare da ƴar ruruma, Hajar ta runtse idonta snn ta damƙe hannun Sabra dake cikin nata, tabbas tasan cewa masu ɗaukarta ne suka hallara. Hafsa ta miƙe ta janyo mayafin Hajar ta rufe mata fuska. Shimfiɗar fuska da ta tabarma su Anty sukay wa baƙinsu, su Mama Mardiyya suka zazzauna, aka fara exchanging greetings ga juna, bayan nan Wasila ta kawo drinks da snacks da aka tanadar ta ajiye musu. Maama ta fito daga ɗaki tana ƙarewa baƙin kallo, sosai gabanta ya faɗi sbd yanayinsu, sam ba suyi kama da ƴan wahala ko yaku bayi ba, hutu ne kawai yake haskawa a jikinsu, ta shiga muhawara da zuciyarta, shin wane ne wnn abokin na Baba da aka ɗaurawa Hajara aure da ɗansa, tin safe take jiran taga su waye zasu zo ɗaukar Hajar, ta yamutsa fuska ta koma ɗaki ta hau canza kayan jikinta zuwa masu ɗan dama dama, Nabilah tace "Maama fita za kiyi?", Maama tace "zuwa zanyi naga kangon da za a kai Hajara". Mama Mardiyya ta ɗaga kai tana kallon Maimuna da ta fito daga wanka, ɗaurin ƙirji ne ajikinta, ga fuskarta ɗaɗau tasha man bleeching jiki kuma baƙi ƙirin, ko kallon inda suke Maimuna ba tay ba ta tsugunna gaban rariya ta fara goge baki. Mama Mardiyya suka haɗa ido da Anty Zulaiha. Ummi tayi ajiyar zuciya don itama taga Maimuna tace "ba zama za muyi ba ina ƴar tamu?", Anty tace "tana ciki, wai yau zaku tafi da ƴar taku?, sai kuma naga ba a gyara mata ɗaki ba", Anty Zulaiha tace "ai ɗakinta a gyare yake, jiranta kawai yake", Anty tayi murmushi ta tashi ta shiga ɗakin Umma, ta tsaya tana kallon Hajar tace "to taso Hajar", hannunta riƙe da na Sabra ta tashi tana jin bugun zuciyarta a maƙoshi, kawai dagewa take amma jikinta duk yayi sanyi, Hafsa ma ta miƙe, Anty tace "toh cikata mana, kin riƙe yarinya", da cracking voice tace "da ita zan tafi..", baki buɗe Anty tace "Au da ita zaki tafi..", ta gyaɗa kai don da gaske take. Anty ta riƙe ɗayan hannunta wanda ta saƙalo small handbag dinta ta fito da ita tsakar gida, Mama Mardiyya tace "masha Allah" sai kuma ta miƙe tace "toh mu tashi ko", ta shatin veil dinta da ya rufe mata fuska take kallon Umma, ta saki hannun Sabra taje ta rumgumeta, sai alokacin ta saki kukan da take ta dannewa, idon Umma yayi rau rau don itama yaƙe kawai take, da kyar ta yaficeta daga jikinta ta shige ɗaki, Hajar ta kuma rushewa da kuka tamkar zata shiɗe, Ummi ta riƙota tace "yi haquri ko wace mace yar haka ce". Maama ta kirma wani uban hijab tana kallon Nabilah tace "ki taso muje muga kangon da za a kai Hajara", Nabilah tace "A'a nidae ba inda zani", Maimuna tace "ni bari na saka kaya mu tafi", Maama ta leƙa window tace "yi da jiki naga sun tashi..", shap shap Maimuna ta gama saka kaya, suna fita already anyi soro da Hajar dake gursheken kuka. da yake mota uku suka zo da ita akwai space sosai, Amarya Mama Mardiyya da Anty suka shiga mota guda, sai Hafsa a front seat, Ummi da Anty Zulaiha da wasila suka shiga mota daya, Maama da taga an barta a waje ta shiga buga windown motar Amarya, Mama Mardiyya ta buɗe glass tace "lfy?", Maama tace "ban gane lfy ba, ai harda ni za a kai amaryar", Mama Mardiyya tace "Ohk, ga wani motar can ai saiki shiga.." da haka ta zuge glass dinta, wani takaici ne ya turnuƙe Anty, idon baƙi ne zai hana ta tatawa Maama rashin mutunci, ɗayar Motar da ta rage Maama ta shiga tana zare ido, jikinta har rawa yake tana fatan waɗan nan motocin duk na haya ne wato Opay, Maimuna tayi kwam a gaban Mota, tafiyar minti talatin ce ta kaisu unguwar da zasu, motarsu Maama ce a front don haka itace ta fara shan kwanar street din gida, Maimuna sai cizon lips take tana kallon tsala tsalan gidajen da ke layin, a bakin gate din gidan da yafi ko wanne gida ƙawatuwa a layin motar ta tsaya, Maama ta ɗaga murya tana kallon driver tace "kai malam ya zaka ajiyemu a ƙofar gidan ƴan yankan kai, ba wancan ne gidan ba?..." ta nuna wani gida da duk yafi ƙanƙanta da rashin kyau a layin, driver ya danna horn yace "A'a ba nan bane, wnn wanda zamu shiga shine gidan", wani irin sakin baki Maama tayi har yawu na zuba. lokacin da suka shiga harabar gidan kam suman zaune tayi, motar Amarya da tasu Ummi ma ta shigo, Hajar Amarya ta fito a hankali tamkar wacca kwai ya fashewa aciki, idonta sai zugi yake tana shessheƙa a hankali. Mama Mardiyya da Ummi sukay main building da ita, Ummi tace "toh shiga da ƙafar dama da Bismillah"......✍️ 💛 HAJAR💛 by Feenerh_feeche {35..} A hankali Hajar ta saka ƙafarta ta dama ta shiga gidanta bayan tayi Bismillah a zuciya, wani irin sanyi ne ya tsarga mata a jijiyoyin jiki, su Sakeena dake zaune a katafaren palourn suka fara musu sannu da zuwa, upstairs aka wuce da Hajar domin kaita ainahin ɗakinta, the room was in woah ba a cewa komai, it's very huge and luxury, aka ajiyeta a makeken italian bed dake ɗakin wanda a halin yanxu ya zama nata. Anty dake biye dasu tanata zabga murmushi tace "masha Allah", Hafsa ta shigo tana jan box din kayan Hajar, ta zauna gefenta tana ƙarewa ɗakin kallo, wnn ai daula aka kawo ƴar uwarta, wani hanin ga Allah baiwa ne, Allah ya bata zaman lfy da mijinta shine fatanta agareta, Anty ta fita tana bin ɗakunan dake saman ɗaya bayan ɗaya, bedroom biyu ne extra bayan wanda aka kai Hajar, saidai basu kai nata girma ba, wata sliding glass door ta hango wacca ko ba a gaya mata ba tasan turakar mai gidan ce, don haka ba tay hanyar ba kuma daman ma a rufe yake. da kyar Maama ta iya fitowa daga mota sbd jin ƙafafuwanta take tamkar ba zasu ɗauketa ba, Maimuna kam tini ta shige tana kashe kwarkwatar idonta, tamkar an wurgota haka ta shiga palourn tana zazzare ido, duk da sanyin Ac amma zufa take, Noor ta yamutsa fuska tace "wnn kuma daga ina?..", Aysha tace "who knows..", babu inda Maama bata shiga ba a ɗakunan ƙasa, kuma duk wanda ta shiga sai numfashinta ya ɗauke, nadama kam tayi yafi cikin kwando, duk ɗakin da ta shiga saita fito a gigice, tuntuɓe kam tayi wajen sau ashirin sbd kallon fitilu na jikin roof, tin jama'a basu lura ba har suka fara fahimta, a sama suka haɗu da Maimuna wacca ta maƙale a bedroom ɗaya tana fatan dama nata ne, Maama tace "kinga abinda Babanku ya aikata ko, ya siyar da Hajara, wnn ai gidan yankan kai ne", "ki ga yankan kai a kanki, wnn gidan auren Hajar ne..", Anty ce ta furta hakan tana shigowa dakin, Maama tace "ke Jamila ki shiga taitayinki..", Anty ta taɓe baki tace "dalla malamai ku fita karka saka mata ƙazanta a ɗaki, sa'a ma ku ka ci da akazo da ku..", Maama ta buɗe baki za tay magana Anty ta turata waje tace "ki fita nace Rabii", Maimuna ta buɗe baki za tay mgana Anty ta daka mata tsawa itama ta hankaɗata waje ta rufe ɗakin tace "da so samu ne ma ku fita, ko mala'ikun rahama sun shigo" da haka ta bar wajen ta sauka ƙasa. Maimuna ta mulmulo ashar tace "ni za'a wulaƙanta akan wnn kuturun gidan, wllh gidan da Alhaj ɗina zai sakani yafi wnn sau dubu", Maama ta gasa mata wata shegiyar harara tace "zan ɗuɗɗura miki ashar wllh, Alhaj ɗin banza Alhaj ɗin wofi, yana ina shi Alhaj ɗin", Maimuna ta tsuke ido tace "Maama fa zaginsa kikai?", Maama da take neman gurin huce takaici tace "na zaga ɗin", Maimuna tayi kwafa tace "kin dena cin ƙwandala daga kudinsa wllh, ni na tafi gida bazan zauna ana min gori ba", Maama tace "tsayani mu tafi kar zuciyata ta fashe..", a hankali Maimuna take sauka daga kan stairs din da yasha mable, Maama na biye da ita, fitilun da ke jikin bangon stairs din da kuma na sama suka ja hankalin Maama, ai kam baifi saura stairs shida ba bayan Maimuna ta kai ƙasa ji kake timm Maama ta faɗo, goshinta ya daki tsinin tiles na ƙarshen stairs din, a take jini ya ɓalle, hankalin Jama'ar dake palour suna gabatar da kayan lefe yayo kanta, a gigice ta miƙe ta saka duƙunƙunannen hijab dinta ta dafe goshin, Mama Mardiyya tace "ya salam, taji ciwo ko?", Aysha da ta fito daga guest room da ƙaramar kit ta jewelry na lefe tace "taji ciwo, ga stain din jini a floor", Anty ta taɓe baki ta kawar da kai, kowa na palourn saida yayi mata sannu banda Anty da wasila, Maama ta kyallaro idonta ɗaya wanda yake a buɗe tana kallon akwatunan da suke baje a tsakiyar hamshaƙin palourn, Anty Zulaiha tace "ya kamata a kaita Hospital, naga kamar she's bleeding, Noor yi ma driver magana", Noor da takewa Maama kallon wata psycho tace "ohk" ta tashi ta fita. Mama Mardiyya tace "ga lefen yarinya", Maama ta zaro ido jin an ambaci kalmar lefe, chab wnn ne lefe sai kace na budurwa uku, ya linka wanda aka kawo mata na Nura, Maimuna da ta tsaya gulma ta hura hanci tace "Maama ni kam na tafi sai kiyi ta tsayuwa", Maama bata san lokacin da ta ɓarke da kuka ba, hannunta dafe da goshinta ido ɗaya a rufe ta wuce Maimuna ta fita, Maimuna tabi bayanta da sauri, Mama Mardiyya da daman bata taking shit tace "who is that woman?", Anty tace "kishiyar Babar Hajar ce", Mama Mardiyya tace "Allah ya kyauta, sai kace mai junnu..", Noor ta shigo tace "Ammi (Anty Zulaiha) na gaya masa yace ta fito", Anty Zulaiha tace "ai sun tafi ma..", Noor ta tsaya kusa da Aysha da Khausar tace "mu tafi wajen Amarya..". suka wuce upstairs. bayan su Anty sun gama ganin lefe Mama Mardiyya tace "Alhmdllh, mu dai fatan mu Allah ya basu zaman lafiya", Anty tace "Ameen". da haka suka miƙe domin tafiya don basa son sukay magrib, a lokacin ne kam suka hau sama domin suga fuskar amarya, tinda su Noor suka shigo suka bude mata fuska, Hajar tayi sauri zata rufe fuska ganin su Ummi na shigowa, Anty Zulaiha tayi murmushi tace "ƴar fillo", Mama Mardiyya tace "to ai shknn wataran ma gani" da haka suka fice daga ɗakin. Anty ta keɓe ta sanar da Umma abinda ya faru a waya, ta tambayeta ya za ai da lefen, Umma tace a barsu anan kar a taho dasu. Anty ta shiga wajen Hajar domin mata sallama, Hajar ta riƙe mayafinta ta ringa kuka kamar zata shiɗe, da kyar Anty ta rarrasheta ta samu tayi shiru, Hafsa tayi mata sallama da cewar gobe zata dawo, kowa ya tafi aka bar su Noor da ita, Sakeena ma tabi su Ummi. ★Through out the day Nurain na room ɗinsa, bacci ma yayi abunsa, lokacin sallah ne kawai yake fito dashi, yana dawowa daga sallar magrib ya tarar da su sun dawo kenan, wajen motocin ya dosa yana musu barka da zuwa, suka ringa sa masa albarka tare da fatan Allah ya bada zaman lfy, shi dai baice komai ba saidai ya shafa kai. bayan sun shiga ciki Sakeena tace "So.. ashe kai a angonce ka dawo 9ja, Abba ya kyauta", ya zura hannayensa a pocket yana kallonta da kyau yace "And shknn.. nima na huta da surutun ku, that bla bla bla Nurain kayi aure you're not getting younger..", tace "Sure kuma fa ka huta, am telling you wllh tafi Ruqayyah kyau nesa ba kusa ba, she's beautiful and young bana jin ma ta kai sa'ar Noory", ya ja pointed nose ɗinsa yace "really.. toh yayi kyau", tace "brother harna tausaya maka wllh zaka sha shagwaɓa don shagwaɓaɓɓiya ce, tin fa da aka kawota take kuka har muka taho bata dena ba, ya kamata ka tafi da wuri kaje kayi aikin rarrashi kar ƴar mutane ta haɗiyi zuciya..", yayi ajiyar zuciya yace "wai ke baki san ba auren soyayya bane wnn", tayi hitting ɗinsa lightly tace "that doesn't change the fact that she's your wife, arranged marriage ko kuma auren soyayya ai duk ɗaya ne tinda dai an zama miji da mata, and kar kayi using that bullshit think of you kayi maltreating yarinya..", ya zaro ido yayi pointing kansa yace "Nah?", tace "Yess you", yace "ai kinsan ba halina bane", tace "yeah, i know brother, naji kana wani zance ne daga nace kayi consoling yarinya..", murmushi yayi yace "uhmm ai ba sai kin koya min yadda zan kula da baby wife dina ba", wucewarta tayi ta barsa a wajen tana cewa "shine ka tsaya kana ɓatan lokaci.." ta shiga ciki. ƙarfe takwas da rabi na dare Nurain na tsaye gaban Mirror, buttoning rigar dake jikinsa yake, dakakkiyar shadda ce mai tsadar gaske, sabuwa fil wacca ya ɗinka a lokacin bikinsa da Ruqayyah kuma ya tanade ta ne sbd shiga gidansa na farko wajen matarsa, ashe dai ba Ruqayyah bace, wata ce daban, sai a yanxu ma ya fara tambayar kansa shin ya wacca aka aura masa take, yana gama buttoning ya kafa hula samar cikakkiyar baƙar sumarsa, ya fito a well dressed gentleman, wata ƙaramar trolley da ya haɗa few belongings nasa ya ja ya fito daga room ɗin nasa, ya rufe ya saka key din a pocket, down stairs ya sauka yana zuba ƙamshi, Farooq da ke zaune main palour yana latsa wayarsa ya ɗaga kai ya dubesa, Nurain ya ajiye trolleyn ya wuce part din Mami sukay sallama, tare suka fito da Sakeena, ya shiga part din Abba ita kuma ta ƙarasa wajen Farooq, ta miƙa masa key din motarta tace "plxx brother ka taho min da car na tana can gidan..", yace "what about mine?", tace "ai yanxu a ta Nurain zaku tafi, idan ku ka je sai ka taho da tawa ka bar masa tasa, idan ka dawo saika dauki taka", yace "Ohk, you wet my work fa, banyi niyyar dawowa ba..", tace "sorry, ai daman ma saika dawo tinda zaka ɗakko su Noory..", ya amshi key ɗin ya zura a pocket. Nurain yay sallama da Abbansa snn yace "amm naga alert daga wajenka, what about the money?", Abba yace "ka yi amfani dasu ko wajen siyan foodstuffs ne", Nurain yace "ngd Allah ya saka da alkhairy" da haka ya bar room din, yana fita main palour Farooq ya miƙe yace "let's go..", Nurain ya tsaya yana kallonsa yace "muje zuwa ina?..", Farooq yace "zuwa gidanka mna, amarya na jira", trolleyn kayansa ya ɗauka ya fita compound, parking space ya dosa ya buɗe black ride dinsa, ya bude back seat ya ajiye trolleyn snn ya shiga driver seat, Farooq ya shiga front seat yana cewa "wai rakiyar ce baka so?", direct yace "yap" ya kunna motar yana warming, Farooq yace "i guess right, Mami ce tace nazo ai, you know I can't say no to her", Nurain yace "that's right..", ya fita daga parking lot din da reverse snn ya juya suka bar gidan. A wani babban supermarket yayi parking, yace "zanyi shopping, do you mind going in?", Farooq yace "nope saika fito", Nurain bai kashe motar ba ya barta a kunne sbd AC tinda Farooq na ciki, wajen shopping din ya shiga, after 20min ya gama, shopping yayi sosai da kudin da Abba yay masa transfer kuma a hakan ma ko quarter bai taɓa ba, saida back seat ya cika da ledoji, bayan ya gama ya shiga mota suka bar harabar supermarket din, Nurain yace "i never thought arranged marriage za a min, my wish is to marry someone that I love and she loves me too...", Farooq yace "Allah planned the best for us, wish kuma wani abu ne na rayuwa wasu nasu fulfill wasu kuma unfulfill, in your case ba zamu ce naka unfulfill bane cause you have another three chances", Nurain yace "kuma ba nida niyyar auren mace sama da ɗaya", Farooq yace "Ohk, saika ajiye niyyar kayi fulfilling wish dinka", Nurain yayi ajiyar zuciya baice komai ba, ganin sun wuce wani wajen suya da gashin kaji Farooq yace "kayi mantuwa fa punk", Nurain na murza steering his eye fixed on the road yace "mantuwar me?", Farooq yace "baka siyi roasted chicken ba", yayi slowing down yace "damn it, yanxu kuma naga mun wuce suya..", Farooq yace "sai ka koma ka siyo..", Allah yaso ba suyi nisa sosai ba tinda yau baya gudu, da reverse ya koma wajen Suyar, Kaji guda uku da tsinken tsire shida akay masa wrapping, ya biya bill ya bude back seat ya ajiye, saida suka hau saman titi yace "Allah bashi ka ɗauka dude, wai kana ganin inata wahala bazaka temaka ba ko..", Farooq yayi wani murmushi mai sauti yace "hmmm, toh ai naga kamar u don't need a help, rakiyar ma baka so ba..", Nurain yayi ajiyar zuciya baice komai ba, After 15mins yay parking a gaban gidansa da fitilunsa suka ƙara hasken layin, ya miƙawa Farooq muƙulli yace "buɗe gate", ya amsa ya fita daga motar ya buɗe gidan snn ya shiga ya zuge gate ɗin that's soft in sliding, Nurain ya shigar da motar ciki yay parking. Farooq ya rufe gate en snn ya ƙarasa ciki. Ta jikin window Aysha taga shigowarsu ta dubi su Noor tace "Yaya ya ƙaraso, tare suke da ya Farooq", wani irin nervousness ne ya lulluɓe Hajar, shin da wane irin mutum za tay tozali matsayin mijinta, Khausar tace "gashi can suna knocking", da sauri Aysha ta fita ta sauka ƙasa ta buɗe ƙofa, Farooq yace "ina sauran suke, fetch them now karku ɓata min lokaci", tace "tom", da sauri ta haura sama ta sanar dasu Noor, ai kam da sauri suka haɗa kayansu sbd sun san halin Farooq, yanxu sai ransu ya ɓaci, sukay wa Hajar sallama suka fita, a hankali ta gyara zamanta a gefen gado, ta janyo mayafinta ta ɗora a kai har yana rufe mata goshi, wani irin feeling take ji, zuciyarta na lugude. suna sauka down Farooq da ya shigo da ledoji a hannunsa yace "ku jirani a waje", ba musu sum sum suka fita, Nurain ne ya shiga da ledojin ƙarshe wanda sune na kaji ya ajiye a palour, Farooq ya miƙa masa hannu yace "toh brother, wish you Happy marriage life..", sukay shaking hands Nurain yace "thank you", compound suka fita tare, Farooq ya shiga driver seat na motar Sakeena, Noor a front seat Khausar da Aysha suka shiga back seat. saida suka fita daga gidan snn Nurain ya rufe gate da padlock, ya duba ko ina a compound din yaga dai ba matsala snn ya shiga ciki, ya sakawa ƙofar lock yana sauke ajiyar zuciya, trolleyn kayansa ya ɗauka ya haura sama, ya kalli doors ɗin ɗakunan yana jin wani irin feeling, definitely his wedded wife tana ɗaya daga ciki. part dinsa ya wuce ya ciro key ya buɗe ya shiga, ya lalubi bango ya danna switch, a take haske ya gauraye makaken palourn nasa, kai palourn nan fa ya naɗi pulus, ya wuce master bedroom wanda yafi ko wane ɗaki girma a gidan, tsabar girman dakin daga can nesa zaka hango makeken bed din ɗakin, ya ajiye trolleyn a kusa da closet ya juya ya fita daga part din, a long corridor dake ɗauke da three bedrooms din ya tsaya, ya saki ajiyar zuciya mai karfi kafin ya buɗe room na farko, da sallama ya shiga ya tarar ba anan aka ajiye masa matarsa ba, room na biyu ma haka, yana taɓa door handle na room na uku yaji iced shock, ya murɗa handle din gami ta tura ƙofar ya shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe a hankali yace "Assalamu alaikum...", da cracking voice wacca ta dashe ta amsa ciki ciki, ta sunkuyar da kanta tana kallon slim fingers ɗinta da take wasa dasu, his piercing eyes landed on her slim fingers da suka ji zanen ƙunshi, a hankali ta ajiye numfashi ta lumshe idonta perceiving his pure men scent da rairayin sanyin Ac ya kwaso, takowa ya farayi towards her, yayinda ita kuma taji tamkar an ɗago fuskarta, idonta ya faɗa cikin nasa, ya dakata da tafiyar yana kallon innocent face ɗinta wacca tasa brain ɗinsa ta amsa, sosai idanunsu suka sarƙe, he automatically get froze bayan ya gane wnn fuskar, tamkar robot da aka kunna da remote control haka ta miƙe zumbur, ta zaro lulu eyes ɗinta waje, mayafinta ya zamo daga kanta zuwa shoulders ɗinta kafin ya zame ƙasa gaba ɗaya, ta kurma wani uban ihu kafin ta sulale ƙasa tabi mayafinta.....✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh _feeche {36..} At first tsayawa yayi yana kallonta kafin ya ƙara one step, tsananin shock da abinda bata fatan haka ne yasa ta sulale ƙasa, Hajar ta yayibi mayafinta ta miƙe nan ma sai kace robot, ta lulluɓe jikinta gami da kallon mutumin front dinta wanda shima yake analysis me ya kawo wnn yarinyar nan, Hajar da take shivering as a result of shock din da tayi ta nunasa da yatsa tace "me kake yi anan?", da wani irin expression yake kallonta cause he will never accept what his mind is thinking, ta zuba masa lulu eyes ɗinta kawai amsa take jira ya bata, After few seconds of silence ta sake cewa "nace me kake yi anan...", da stern voice yace "that question goes to you young lady, what are you doing in my house...?", shivering da jikinta yake har saida ya ratsa zuwa lips dinta snn yayi birki a muryarta tace "your house..?" kafin ta sake sulalewa ƙasa a karo na biyu, maimakon ƙara da ta fasa wancan karon yanxu kuma saita rushe da kuka, what wnn mutumin da ta ƙi jini, mutumin da bai san darajar ɗan Adam ba, ko 10sec bai ƙara a tsaye ba ya juya ya bar ɗakin, gaba ɗaya brain ɗinsa ta kulle, he can't think otherwise, downstairs ya sauka ya nufi main door, har ya fara murza key sai kuma ya kalli agogon wrist ensa wanda yake nuni da sha ɗaya na dare saura few minutes, fasa buɗe ƙofar yayi ya koma ya zauna akan ɗaya daga cikin exclusive sofa dake palourn, yayi resting jikin kujerar gami da lumshe ido, bayan minti goma ya buɗe idonsa, ya ciro wayarsa daga pocket snn ya tashi ya koma upstairs, part dinsa ya shiga ya zauna a palour, kunna wayar yayi ya fara ƙoƙarin dialing numbern Abbansa, kiran ko shiga beyi ba saiga kiran wacca ta takura masa nan yana shigowa, ya tsaya yana jiran kiran ya katse, yana katsewa wani ya sake shigowa, sau biyar yana attempting kiran Abba amma kiranta ya hana nasa shiga, shi kam bashi da lokacin blocking numberta cause she didn't worth it, idan ma yayi blocking layinta ai ta samu matsayi, daga dawowarsa jiya zuwa yau gaba ɗaya ta hanasa operating wayarsa lfy, daga text messages sai uban kira, fasa kiran Abban yayi ya ajiye wayar gefe guda, yana jin sai vibrating take, yayi ajiyar zuciya ya cire hular kansa ya ajiye kan huge center table dake palourn, shafa cikakkiyar sumarsa yayi yana nazarin demon din dake gabansa. The girl... ya tuna encounter dinsa da ita.. na farko lokacin da ta shafa masa cakwalkwali, cike da tsiwa take magana "malam ba kaga abinda kayi bane??, oh shi bakuga rashin kirkinsa da ya feshe ni da kwatami ba, banga zan iya hakura ba gaskiya". na biyu lokacin da ya kusan bige wani yaro da mota... "malam wai baka san darajar rai bane iyeee?, ya za ai ka kusan bige yaro amma ka wani hakimce a mota bazaka fito ka dubasa ba, ke kinga mutumin nan fa ko a jikinsa, idan da ace ya bige yaron nan fa sai yadda Allah yayi, to Allah ya isan sa kuma a ringa sanin darajar ɗan Adam". encounter na uku... "Fake doctor, i think the name fit you, wanda baisan darajan ɗan Adam ba bazai zama real doctor ba saidai Fake", sai kuma na ƙarshe... "mu bawa juna haƙuri daii". not her gaskiya, da dai ace wata ce daban da zai haqura yayi accepting marriage din nan amma wnn yarinyar mara ta ido, bama ta ido ba bata da manners. tunani kawai yake yana nemawa kansa solution, idan ya saƙa wancan sai ya kwance wancan, after 40mins dai ya samu solution ɗaya, ya tashi ya shiga huge bedroom nasa ya wuce bathroom, alwala yay ya fito yana jan hannun rigarsa da ya tattare, nafila ya shiga jerowa, nap na few hours ya samu kafin sallar asuba, ya sake wata alwala yay sallah, ƙarfe shida da minti hamsin na safe ya fito hannunsa riƙe da car key, ko kallon ƙofar room din da take beyi ba ya gangara downstairs, ya dubi ledojin da ke palourn wanda bai sake bi takansu ba, compound ya fita bayan ya rufe main door din da key, ya wuce wajen motarsa ya bude ya shiga ya kunnata, a kunne ya bar motar tana warming ya fito ya nufi gate ya bude, dawowa yayi ya shiga motar snn ya fito daga gidan, ya sauka ya rufe gate din shima da mukulli snn ya koma mota ya fara driving, ƙarfe bakwai da minti sha biyar ya danna horn a ƙofar gidansu, mai gadi ya bude masa, ya shiga wawakeken compound din gida yayi parking ya kashe motar ya fito, ya danna door bell, babu jimawa Laure mai aiki ta buɗe masa, bai saurari gaisuwar da take masa ba ya wuce great room din Abba, Noor ta fito daga kitchen da Apron a jikinta tace "wane yake knocking?", Laura tace "Alhj ƙarami ne..", Noor ta zaro ido tace "Yaya na?", Laure tace "Eh hajiya..", Noor tabi palourn da kallo tace "ina ya shiga?..", Laure tace "ɓangaren Alhj", Noor ba tace komai ba ta koma kitchen ta cigaba da suyar plantain da take. Nurain na shiga great room din Abba ya ciro wayarsa daga pocket ya fara kiran Abban, tana daf da katsewa Abba ya ɗaga yayi sallama yace "Uthman..", Nurain yace "na'am, am so sorry for disturbing you, barka da safiya Abba..", Abba yace "lfy lou..", Nurain yace "dan Allah i need to talk to you Abba, gani nan a palourn ka..", Abba yace "Alright" da haka ya katse kiran, bayan minti biyu ya bayyana a great room din da coffee color jallabiya a jikinsa, Nurain ya sauka kan carpet ya sake gaishesa, Abba yace "me ya faru Son?, what's the matter?", Nurain yayi gathering courage yace "am sorry Abba, wllh i can't accept this marriage, zan datse sa", Abba ya ringa kallonsa kafin yace "what happened all of a sudden Nurain?", Nurain ya shafa kansa yayi ajiyar zuciya yace "bazan iya zaman aure da yarinyar ba Abba", Abba exhale heavily yace "why?, musaka ce, ko akwai tawaya ajikinta ko wani abun?", Nurain ya kasa cewa komai, Abba yace "answer me..", ɗago kansa yayi yace "no one, kawai dai i will never accept her as my wife", Abba yayi shiru na some seconds kafin yace "toh ya kake so ayi Nurain, an riga an ɗaura auren?..", Nurain yace "plxx father ina neman yardar ka dan sakinta zanyi..", Abba yace "toh me yasa zaka nemi yarda ta Nurain, ai wuƙa da nama na hannunka, na gama role dina, ra'ayin ka ne ka zauna da ita snn kuma ra'ayin ka ne ka rabu da ita, kai ne mai saki a hannu...", Nurain yace "am very sorry to turn you down father..", Abba ya gyaɗa kai yace "ba komai, bazan tilasta maka ba Nurain, amma ka tabbatar bka son auren?", Nurain yace "yeah", Abba yace "i will find another way, ka rubuta takardar sakin ka kawomin...", buɗe ƙofa akay, suka juya suna kallon mai shigowa, Hajjaju Hajiya ta shigo tana dogara sandarta, ta kalli Abba ta cikin kantamemen glasses dinta tace "Muntari, ya naji kana cewa yaro ya kawo takardar saki, takardar saki kamar ya?, karfa ina ganin kayi abin arziƙi ka ɓige da tsiya Muntari...", Abba yace "sannu da zuwa Hajiya", ba ta amsa ba kawai dai ta kafesa da idanu ta cikin glasses tana lasar wawulon bakinta, Nurain ya miƙe yace "sannu da zuwa", ta ɗaga kai tana kallonsa tace "wai Usuman, ince dai kai ma garin ƙanƙara kaje don naga ka ƙara haske", yace "babu ƙanƙara a ƙasar da naje" ya riƙo hannunta ya ƙarasa shigowa da ita palourn, Nurain ya koma position dinsa ya zauna, saida ta zauna akan kujera ta kalli Abba da ke shirin gaisheta tace "tin jiya naso zuwa naje na rungumo matar Usuman na kai masa ɗaki, to ciwon ƙafa ya hanani, ai dole tayi ciwo na azabtar da ita lokacin ƙuruciya, tinda aka idar da Sallar asuba nake neman wanda zai kai ni gidan Usuman, shi Umaru bacci yake kuma gsky bazan tashi mai gida ba, ita kuma Shatu ba a maganarta maƙiwaciya ce..", Abba yace "Allah sarki", ya russuna yace "Hajiya barka da safiya..", tace "A'a bar barka da safiyar nan tukunna, wace takardar saki za a kawo?, wa za a saki?, waye zai yi saki?, kasan na tsani kalmar saki Muntari...", Abba ya kalli Nurain yace "Nurain ne zai saki matarsa..", Hajiya ta buɗe bakinta mai wawulo tace "wai Usuman, wace matar zai saka kuma?", Abba ya dubi Nurain yace "talk my friend..", Nurain ya sha kunu baice komai ba, Hajiya tace "Usuman a sbd wani dalilin za ka saki matar da aka aura ma jiya?, notin kanka ya kunce", Nurain yace "ba dalili, kawai bazan zauna da ita ba", Hajiya ta buga sandarta a kan carpet tace "haka fa, wato sbd ka mayar da mu ƙananan mutane a idon duniya ko, sbd ka zubarwa da Muntari kima ko, sbd ka zubar mana da mutunci ko, zaɓin mahaifin naka ne bai maka ba ko me?, naga hakan ne ya dace da kai tinda zaɓin naka da ka kawo guduwa tayi ta barka, shine daga aura maka yarinya jiya jiyan nan kace zaka saketa, toh ai ba akuya ko tinkiyar turke bace da za a saketa sakaka, sam ban amince da hakan ba, ai wnn ƙaranta ce...", Abba yayi ajiyar zuciya yace "Hajiya ayi haƙuri, nima Uthman ya bani mamaki wllh ban taɓa tunanin hakan daga garesa ba, tinda dai yace baya so ina ganin kawai ya saketan..", Hajiya ta fara matsar kwalla tace "Au Muntari isa zaka nuna min akan ɗanka, wato abinda yake so za muyi sbd gashi uban mu, toh wllh bai isa yayi sakin nan ba, wnn ai mugunta ce da cin zali an auro yarinya jiya jiyan nan sai a saketa yau sbd rashin imani..", Abba ya rage murya yace "an janye maganar sakin, dan Allah Hajiya kiyi haƙuri..", ta janyo lulluɓin da ke kanta na atamfa ta cire glasses ta goge hawayen tace "Muntari na tsani kalmar saki", Abba yace "na sani Hajiya", ta mayar da glasses din ta dubi Nurain tace "Usuman na tsani kalmar saki", Nurain da zuciyarsa ke ƙoƙarin bombing ya shafa fuskarsa snn ya miƙe ya fita. ★Maama ce a tsakar gida sai zance take mara kan gado, goshi a kumbure yayi lemon tsami, ta gyara haɓar zaninta tace "tin jiya nake magana a gidan nan amma anƙi saurara ta, kawai an ɗau yarinya an kaita gidan yankan kai sai kace mara galihu iyee, naga dai da gatanta a duniya..", Baba ya fito daga ɗakinsa da shirin fita wajen aiki, yana zura takalmi Maama ta matsa kusa dashi tace "mal kana ji ina magana fa, wllh abinda kayi bai dace ba, ya zaka ɗauki ƴarka ka miƙata ga halaka ka kaita gidan yankan kai..", Baba ya kalleta yace "Au haba, ashe kin san Hajara ƴata ce ko Rabi?", Maama tace "yo ai ana ganin Hajara an san kaika haifeta mal, ni dai ina baka shawara wllh kaje ka ɗakko ƴarka daga wnn gidan tin kafin ayi layya da ita, toh ni dae na faɗa gidan yankan kai aka kaita..", Baba yayi wani murmushi na manya yace "tinda dai ba Nabilah ko Sa'adatu ko Maimuna na siyar ba ai shknn, ki zuba ruwa a ƙasa ki sha", da haka ya kira Umma da ke ɗakinta, fitowa tayi tace "gani mal", yace "na fita", tace "Allah ya tsare mal", yace "Ameen" ya saka kai ya fita daga gidan, Umma ta juya zata shiga ɗaki Maama tace "faɗima..", Umma ta haɗe gira ta juyo ta kalleta tace "dani kike?", Maama da ta koma wata psycho tace "akwai wata faɗimar ne bayan ke, dake nake..", Umma tace "Au", Maama har dasu gyara tsayuwa tace "idan mal baiji ba ina fatan ke kiji, wllh shawara nake baki, karki bari ayi layya da ƴarki, marmaza ki rugungunta kije ki ɗakko ƴarki..", Umma tayi wani murmushi tana kallon Maama sama da ƙasa tace "kashh baiwar Allah aini bana ɗaukan shawara dama dai basir ne wataƙila na ɗauka.." da haka ta bankaɗa labule ta shige ɗakinta ta bar Maama da sakakken baki, Maama ta ɗaga murya tace "in Allah ya yarda sai kunyi nadama keda mal, tinda kunnen ƙashi ne daku, a kwali za a kawo muku gunduguilar kan Hajara anyi layya da ita..", Sa'adatu ta fito tace "haba Maama ya zaki tashi da safiyar Allah ki ringa mana ihu a gida", Maama tace "Sa'adatu wai Maimuna ba ta gaya miki cewa mal ya siyar da Hajara ba, ai ita taga gidan, wllh na ƴan yankan kai ne", Sa'adatu ta yamutsa fuska tace "toh wai ina ruwanki Maama, ko gidan yankan kai aka kaita meye naki aciki..", Maama tace "wllh kuwa ba nawa a ciki, kawai dai shawara nake bawa mal yaje ya ɗakko ƴarsa a raba auren..", Sa'adatu tayi tsaki ta koma ɗaki. Maama tabi bayanta tana cewa "kamo min Balaraba a wayarki", Sa'adatu tace "ni bani da lambarta, Nabilah ce mai ita..", Maama ta ɗauki wayar Nabilah ta lalubo lambar Balaraba, tayi dialing saidai kuma babu kuɗi a wayar, da kyar Sa'adatu ta kira mata ita a tata wayar, tsabar rashin nutsuwa a waskace Maama ta riƙe wayar ta kara a kunne, Balaraba na ɗauka Maama tace "an yanka ta tashi, sai an biyani kuɗina", Balaraba tace "lfy ƙawata?", Maama tace "ina fa lfy, ai ko ƙamshin lfy babu a tare dani, gani nan zuwa gidan ki..", ba ta ƙarasa magana ba Sa'adatu ta warce wayar ta kashe tace "daman minti ɗaya nace", Maama ta bita da kallo. ★Noor ta shiga part din Mami ta sanar da ita cewar ta gama haɗa breakfast da za a kai gidan Nurain, Mami tace "good, an shirya a basket ko?", Noor tace "na bar Laure na shiryawa", Mami tace "Ohk, to kiyi sauri ki shirya a kai musu", Noor tace "tom, ai Yaya ma yazo", Mami tace "Nurain din, tin yaushe?", Noor tace "almost 20minutes, Hajiya ma is here tana part din Abba", Mami tace "okay, je ki shirya". Noor ta fita zuwa room dinta, Mami kuma ta fita zuwa part din Abba, Mami na shiga Hajiya ta miƙe kenan tayi support da sandarta, Mami ta gaisheta cike da ladabi, Hajiya ta amsa tace "ina Usuman din yazo ya kaini gidansa", Abba yace "call him for her", Mami tace "yana nan ne", Yace "yanxu ya fita daga nan", Mami tace "tom" da haka ta juya ta fita, upstairs ta haura zuwa room ɗinsa, ta ringa knocking amma no respond, murɗa handle din ƙofar tayi don taji a rufe yake ko a buɗe, ai kam tana murɗawa ta buɗe, Mami ta shiga, yana kwance kan bed yayi rigingine, kallon 5sec Mami tayi masa trying to figure out me yake damunsa, ta kirasa bai amsa ba, ta sake kiransa nan ma bai amsa ba, da alama ya lume cikin tunanin da yake, gefen bed din tayi taping tace "Nurain are you Okay?", ya tashi yana goge fuskarsa da palm yace "Sure, am okay", ta ringa kallonsa kafin tace "Alright, ka taso ka kai Hajiya gidanka", shiru yayi baice komai ba, Mami tace "kaji me nace?", yace "yeah", tace "toh yi da jiki gata can tana jiranka a palour", ta fita a ɗakin, saida yayi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa ƙanana snn ya fito, a hankali yake sakkowa daga stairs, thick eyebrows dinsa a haɗe, tini Hajiya da ke zaune main palour ta dogara sandarta tayi hanyar fita, Mami tace "tare da Noor za ku tafi zata kai breakfast", yace "tom" yabi bayan Hajiya, Noor ta fito daga kitchen da basket a hannunta Laure biye da ita itama da wani basket din a hannunta, Hajiya ta hakimce a gaban mota rungume da sandarta, Noor ta saka basket din abincin a boot snn ta shiga back seat, shi dai Nurain baice komai ba kawai ya kunna qira'ar Sheikh Abdul Baseet yana sauraro, har suka je gidan ba wanda yayi magana, ya sauka ya buɗe gate snn ya dawo ya shigar da motar compound, yana parking ya fita yaje ya buɗe ƙofar shiga main building, Hajiya ta dashare tooth tana kallon flowers tace "kaii gida zakwai", Hajiya na zuwa balcony Nurain ya buɗe mata ƙofar ta shiga shi kuma ya bar wajen, Noor na gama sauke basket yaja motarsa ya bar gidan daman bai rufe gate ba da suka shigo, saida ya zuge gate din amma bai sa masa key ba snn ya bar unguwar, da ɗaɗɗaya Noor ta shiga da kayan Abincin, Hajiya na tsaye ƙiƙam a palour tana ƙarewa ko ina kallo, Hajiya tace "kinga sai sallama nake ba amsa", Noor ta dubi tulin ledojin dake yashe a palourn tace "tana sama Hajiya, bari na kirata", Hajiya tace "A'a ina ke ina hawa sama, mijinta yazo ya kirata", Noor tace "ai ya fita", Hajiya ta hangame baki tace "ban san me yasa Usuman ya zama mai baƙar zuciya ba, kina gani fa zaman kurame mukay dashi a mota", Noor tace "mood ne ironlady..", Hajiya tace "meye kuma mood?", Noor tace "ina zuwa", ta haye stairs, ta kwankwasa ɗakin da Hajar take, bayan kamar minti uku tana knocking kawai ta murɗa ta shiga, surveying ɗakin ta ringa yi da idonta, daga can gefen gado ƙasan tiles ta hangota a kwance, ta ƙarasa kusa da ita ta tsugunna tace "Hajar.. Hajar.. Hajar..", ko motsi Hajar ba tay ba, Noor tayi taping ɗinta nan ma dai bata motsa ba, saida Noor ta nutsu snn taga yadda take breathing a hankali kamar zai ɗauke, ta taɓa goshinta taji zafi ɗau tamkar tasa akan wuta......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {37..} Noor ta sake taping dinta a hankali gami da kiran sunanta, da kyar Hajar ta buɗe idonta da sukay mata nauyi, tana buɗewa ta mayar ta rufe, Noor ta taɓa wuyanta taji shima yayi zafi ɗau amma bai kai kanta ba, Noor tace "Hajar are you Okay?", Hajar ta sake buɗe idonta da kyar tana jin yadda kanta ke sarawa kamar zai tsage, dishi dishi take ganin Noor, tace "Umma.. Umma.." kafin ta kuma lumshe idon, Noor dai ta fara firgita cause Hajar was so weak, ta tashi da sauri ta fita a ɗakin, downstairs ta sauka ta nufi inda ta ajiye handbag dinta, Hajiya da ke zaune kan sofa tace "ina matar gidan take?", Noor na ƙoƙarin ciro wayarta daga jaka tace "ina jin ba tada lfy ne, bari na kira yaya", tayi dialing numbern Nurain, no respond, ta kuma kira nan ma same thing, Hajiya tace "kai jama'a, ƴar nan kiyi min magana yadda zan gane mana waye kuma ba lfy?", Noor tace "Amaryar ce, jikinta zafi, ko motsi bata yi", Hajiya tace "ba kanta, sbd Usuman ya zama mai baƙin hali daga nace kar ya saki yarinya shine ya ƙullaceni, ya kawoni gidansa ya yasar sai kace bola, da badan ni na haifi mahaifinsa ba da yau sai ya iya kwakkwalla min mari, don yadda ya fusata ɗin nan ƙiris ya rage ya zargeni ɗaxu a palourn Muntari..", Noor dai bata tanka ba kawai kiran layin yayan ta take, sau wajen goma tana kira, ta sauke wayar daga kunnenta tace "Hajiya kinga bai ɗauka ba yanxu ya zanyi?, ba fa ta motsi", Hajiya ta gwalo ido tace "mun shiga uku, tana numfashi?", Noor ta haura sama da sauri da wayarta a hannunta, Hajiya dai ta bita da ido don ba ƙafar hawa bene, yadda Noor ta barta haka ta sake tarar da ita, ta ajiye wayarta gefen gado ta durƙusa gabanta ta kira sunanta don taga dai is she concious, yess she is concious amma daf take da zama unconscious, Noor ta fara ƙoƙarin ɗagata daga kan tiles, Hajar ta saka last strength dinta tayi ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa, ƙafarta ta lankwashe za tayi collapsing a ƙasa Noor tayi saurin tarota ta turata kan gado, sosai hankalin Noor ya tashi ta ɗauki waya ta kira Mami, Mami na ɗagawa Noor tace "Mami, Hajar ce ba tada lfy, I don't think she is concious..", Mami tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un mai ya sameta?", Noor tace "i don't know wllh a haka na sameta", Mami tace "ina Nurain din?", Noor tace "he is not around tinda ya sauke mu ya fita, na kira wayarsa beyi picking ba..", Mami tace "seak for help outside, gani nan zuwa.." da haka ta katse kiran, Noor ta ringa kallon fuskar Hajar da pity eyes sai kuma ta juya ta fita, compound ta fita tana jin Hajiya na watso mata tambaya, ta buɗe gate ta fita, ta ringa bin layin da kallo wai ko zata ga wani, tsit har bayan minti goma da fitowarta ba taga wani ba, tayi deciding ko ta shiga wajen neighbors, gidan dake very close to the house ta fara knocking da dutse, almost 5mins amma ba a buɗe ba, wani tunani ne yazo mata don haka ta koma gida, ta maƙale jamlock ta yadda ƙofar ba zata garƙame ba, tana shiga palourn taga Hajiya sai jinjina take tana ƙoƙarin hawa stairs, ta riƙe railer gam da hannun dama hannu hagu kuma sandarta, Noor tace "Hajiya ki koma ki zauna bafa zaki iya hawa ba", Hajiya ta koma gefe tana haki tace "hankalina yaƙi ya kwanta wllh, naji kince batada lfy kuma naga kin fita kin barta ita kaɗai shine nace bari naje na zauna da ita ba a barin mara lfy shi kaɗai", Noor tace "ga Mami nan zuwa ai", taimako gaggawa Noor ta bawa Hajar ta hanyar jiƙa towel ta ɗora mata a forehead sbd zazzaɓin ya sauka. Babu daɗewa Mami da iso gidan tare da driver, Hajiya tace "Dije, a tsakani ga Allah mai Usuman yake shirin zama ne, tinda ya kawomu ya yasar ya saka kai ya fita, ga yarinya can a ƙololuwar samaniya sai suma teke tana farfaɗowa, mijinta likita amma bashi da wani amfani..", Mami tace "Noor na sama da ita knn?", Hajiya ta gyaɗa kai tace "takwarata keta wahala wllh", Mami ta haura saman, ƙofar da ta gani a buɗe ta shiga, Noor ta miƙe daga gefen bed tace "Mami you're here already..", Mami tana kallon innocent face din Hajat tace "how is she?", Noor tayi ajiyar zuciya tace "A bit okay", Mami ta matsa kusa da gadon tana kallon kyakkyawar fuskar Hajar, indeed she is beautiful and young, Mami tace "Bacci take?", Noor tace "A'a ta zama very weak ne", Mami tace "gyara mata ɗankwali sai mu wuce hospital en Dr Mansoor", Noor tace "tin ɗazu nake gyara mata sai ya kuma zamewa, bari nasa mata hula kawai" ta cire hular kanta ta rufewa Hajar black silky hair dinta da aka yarfawa siraran kitso. Babban private hospital aka kai Hajar, tini doctors suka amsheta, a Amenity room aka kwantar da ita aka saka mata drip, cikin mintinan da basu wuce uku ba ta zama stable, fever din ta sauka, akai mata allurar bacci sbd ta huta, Mami ta fita reception ta cigaba da kiran Nurain da tin ɗazu take kira baya picking, wajen Hajiya da ke zaune kan silver chair ta nufa tace "Hajiya, driver zai mayar dake gida...", Hajiya tace "ina fa zan koma gida ga ƴar mutane rai a hannun Allah, yanxu wnn kyakkyawar yarinya ɗanya shagaf Usuman zaice baya so, kyan fuska dai ya samu Allah yasa zuciyar ma me kyau ce, ni babu inda zani sai ƴar mutane ta farfaɗo", Mami tace "ai ta samu lfy, bacci take zata huta daga ta farka shkn. zata tashi sumul", da kyar Mami tayi convincing Hajiya ta yarda zata koma gida, Hajiya na tafiya tare da driver Mami ta kira Anty Zulaiha ta gaya mata abinda ya faru, bayan ta gama waya da Anty Zulaiha ta sake kiran Nurain, ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba da baya picking. ★Nurain kam daman kai tsaye gidansu Farooq ya wuce, yana parking motarsa ya zagaya ta bayan gidan inda zai shiga part ɗin Hajiya direct ba sai yabi ta main door ba, anan kusa da part din Hajiya ɗakin Farooq yake, Nurain yayi knocking ƙofar ɗakin Farooq, Farooq ya buɗe ƙofa ya kallesa da sleepy eyes ɗinsa sai kuma ya ƙanƙance ido yace "brother, me ya fito da sabon ango this early morning?..", Nurain da yake moody yace "move", Farooq ya basa hanya ya wuce, yana shiga Farooq ya rufe ƙofar ya bisa da kallo, Nurain ya zaune kan executive coach dake ɗakin gami da lumshe ido, Farooq ya zaune gefen gado yana facing dinsa yace "what's up..?", Nurain bai tanka masa ba saima ya kwanta kan coach din yayi pillow da hannunsa, Farooq yayi kwanciyarsa don bacci bai ishesa ba, weekends ne kawai yake samun hutu ba fitar sassafe zuwa work, Nurain kam gaba ɗaya mind dinsa a cunkushe take, meyasa bashi da sa'a ne wajen aure, Ruqayyah betrayed him and now an aura masa mara manners, tashi yayi ya zauna ya dafe kansa, Farooq ya miƙe ya zuro ƙafafuwansa ƙasa yana kallon brother din nasa yace "wai me yake damunka ne Nurain?, aren't you here to tell me..", Nurain yace "auren da akay min ne banaso wllh, am not happy with it..", Farooq yace "why?, naga dai jiya lfy na maka rakiya, and it seems like you were happy that time..", Nurain yayi ajiyar zuciya yace "damn it, ko a lokacin bana farin ciki kawai dai i was calm to accept it as my destiny, but now bazan hakura ba gsky, ban taɓa tunanin akwai ranar da zan turning Abba down ba sai wnn karon, turning din kwa shine wllh sakinta zanyi, waccar rigimammiyar tsohuwar ce ta mayarmin da agogo anticlockwise, wllh da tini na wuce wajen..", Farooq da bai fahimci brother din nasa sosai ba yace "wai kana nufin kace sakin matar da aka aura maka jiya za kayi?", Nurain ya shafa fuska yace "yeah, sakinta zanyi sbd bazan zauna da ita a matsayin mata ta ba...", Farooq yace "ban san mene dalilinka ba amma kana ganin sakinta shine solution, what about Abba..", Nurain ya katsesa da fadin "Abba babu abinda yace infact ma cewa yayi ai ya gama role dinsa ynxu option ya rage nawa, ruwana ne na zauna da ita ruwana ne na saketa, so na gama yanke decision zan rubuta takardar sakin na kaiwa Abba tinda ya amince..", Farooq yayi murmushi yace "shi Abban ne ya baka damar ka saketa?", Nurain yace "Sure", Farooq ya sake yin wani murmushin yana jujjuya kai, Nurain ya hade gira yace "meye haka..", Farooq yace "uhmm, are you a kid?, toh wllh Abba testing naka yake, am telling you gwada ka yake punk, taya ya zai baka go ahead direct ka saki ƴar mutane", Nurain yace "Allah ko, toh kwa zanyi failing don bazan ci test dinsa ba..", Farooq ya tashi yace "nidai ga piece of Advice zan baka, indai dalilinka bai kai wanda zaka saki ƴar mutane ba toh ka janye batun nan, ko don reputation din Abba ya ɗaure a idon iyayen yarinyar..", Nurain ya wani galla masa harara yace "oh really, i don't want your Advice ka rike abinka", Farooq ya ɗaga kafaɗa ya buɗe huge wardrobe ensa ya ɗauki button down shirt and dark blue jeans trouser ya shiga bathroom, bayan minti goma ya fito da kayan da ya shiga dasu ajikinsa, Farooq ya tsaya jikin mirror yana goge kansa da hand towel, yayi combing hair din da brush snn ya shafa mai a palm da legs, Farooq ya dubi Nurain yace "am coming" da haka ya buɗe door ya fita, after like 5mins ya dawo dakin da rufaffen plate a hannunsa, ya ajiye plate din akan bedside, mini fridge dinsa dake ɗakin ya buɗe ya ɗakko lemon kwali na raspberry, gefen gado ya zauna ya ɗauki plate en da ya shigo dashi ya buɗe, chips ne da kwai sai satchet ketchup, Farooq yace "ga breakfast", Nurain yace "No, thanks..", Farooq yaci abinci yayi nak abinsa, ya zuba juice yasha daman shi baya shan tea da safe sai dare, Nurain ya tsiyayi lemon yana sipping, wayar Farooq ce tayi ringing, Farooq yayi unplugging dinta daga charge da take, ganin mai kiransa ya dubi Nurain kafin yayi picking ya kara a kunne yace "Na'am Mami..", yay shiru na second uku sai kuma yace "eh yana nan", yana kallon Nurain da shima yake kallonsa yace "okay" ya sauke wayar daga kunnensa, Farooq yace "Mami ce take tambayarka, tin ɗazu take kiran wayarka baka picking", Nurain ya ajiye cup din lemon da yake sha ya tashi ya fita, compound ya fita wajen motarsa, ya buɗe ya ɗauki wayarsa da ya manta kan dashboard, 40 missed calls ya gani daga different people, na Mami duk yafi yawa sai na Noor ga kuma na Abba ma guda uku, sai kuma na wacca tasa ya tsani wayar, ya kare hasken rana dake haske masa ido da hannu, numbern Mami yayi dialing, tana shiga tayi picking, ya lumshe ido yana jin yadda muryarta ta canza tana masa faɗa, Calmly yace "am sorry Mami". ★Anty Zulaiha na kallon Hajar dake bacci tace "wai me yake damunta Mami, lafiya lou fa jiya muka barta tare dasu Khausar..?", Mami tayi ajiyar zuciya tace "sai doctor yazo zai faɗi abinda suka gani, ba kiga a yadda muka kawota nan ba, Noor kam cewa tayi lokacin da ta ganta ko numfashi ba ta yi sosai..?", Anty Zulaiha tace "innalillah, Allah ya rufa asiri, shi kuma Nurain ina ya shiga har yarinyar mutane ta shiga wani hali", Mami tace "wa ya sanar masa, da sassafe dai yazo gida wajen Abba, daman Hajiya ta zabga sammako tazo tace a kaita taga Amarya shine ya ɗauketa ita da Noor zata kai musu breakfast zuwa gidan nasa, wai ashe yana ajiyesu ya juya yabar gidan, Noor ta kirani take gayamin wai Hajar en ba lfy, saida naje gidan snn muka ɗakkota muka taho nan, tin ina gida nake kiran Nurain amma bai ɗauki kirana ba, saida na kira Farooq na tambayesa, shine yake gayamin wai yana gidansu, Nurain bai taɓa ɓatamin rai kamar na yau ba, zaizo ya sameni aii", knocking ƙofa akay Dr ya shigo tare da Nurse biye dashi, ya gaisa dasu Mami snn ya wuce gadon patient yana magana da Nurse din, yace "for now kar ay mata amfani da normal saline..", Nurse tace "yess dr", ya duba ruwan da ake ƙara mata snn yayi feeling temperaturen ta, discharging Nurse en yayi ta fita, ya juya yana kallon su Mami yace "me ya faru da ita haka har bp nata yayi high?", Anty Zulaiha ta kalli Mami da weird expression, Mami tace "Bp doctor?", Dr ya gyaɗa kai yace "yess, jininta ne ya hau sosai, Allah yaso kunyi rushing zuwa hospital da ba haka ba zuciyarta zata iya exploding cause jinin ya hau sosai..", Mami ta miƙe tace "what's her condition now?", yace "Alhmdllh everything has been taken care of, ba matsala insha Allah she is stable", Mami tace "Alhmdllh", yace "i will send a prescription right away, a siyo drugs en a bata idan ta farka taci abinci" da haka ya fita daga ɗakin, Mami ta dubi Noor tace "bisa ki amso prescription din", Noor tace "tom" ta tashi tabi bayan doctor, Anty Zulaiha tace "an kwa sanar da iyayenta?", Mami ta girgiza kai tace "A'a, bamu da contact dinsu..", Anty Zulaiha tace "ya kamata a gaya musu kwa, kinga ma a tambayesu akan Bpn nata ko tuntuni tana dashi", Mami tayi ajiyar zuciya ba tace komai ba, knocking akay kafin aka buɗe ƙofar aka shigo, Nurain ne ya shigo shi da Farooq, Mami ta ɗauke kanta ta haɗe gira, tini Nurain ya sha jinin jikinsa, suka gaisa da Anty Zulaiha, Farooq ma haka snn ya juya ya gaida Mami ta amsa masa, Farooq yace "ya me jiki?", Mami tace "alhmdllh da sauƙi", yace "Allah ya ƙara lfy ya mayar kaffara" da haka ya matsa kusa da gadon da Hajar ke kwance, Nurain ya shafa kai yace "Mami how is...", Mami ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu, Anty Zulaiha tace "kiyi haƙuri don Allah..", Mami tace "meye dalilinsa da har yarinya ta zama unconscious amma be sani ba, da safiyar Allah ya kama ƙafa ya fita ya barta ita kaɗai duk bance masa komai ba, snn ma da ya kaisu Noor gidan me yasa ya tafi ya barsu haka nan, gashi wayarsa ba tada amfani ko emergency ya taso ba za'a sami taimako daga wajensa ba..", ta kalli Nurain da kansa ke ƙasa zuciyarsa na tafarfasa tace "Uthman, wllh Allah idan wani abun ya samu yarinyar nan you are going to see the other side of me, ai Abba ya gaya min abinda ka tarka mara tushe da kan gado" da serious note ta faɗi hakan, Noor ta shigo da prescription paper a hannunta ta miƙawa Mami, without looking at him Mami tace "bashi ya siyo drugs en", Noor ta miƙa masa takardar, ya warce kafin ya fita daga ɗakin da speed, Farooq ya ja kujera ya zauna, a hankali Hajar ta fara motsi da hannunta kafin ta kaisa ta dafe goshinta, ta buɗe idonta tana ƙarewa environment ɗin da take ciki kallo, Farooq da yayi noticing yace "ta farka". Mami ta taso ta zauna gefen gadon tace "sorry dear", Hajar ta haɗiyi wani yawu wanda da kyar ta samesa sbd bakinta a ƙafe yake, support tayi da hannunta ta miƙe zaune, ta kalli hannunta mai canular da ake mata ƙarin ruwa, sai kuma ta ɗaga kai tana kallon drip stand din da akay connecting da hannunta, tass ta fahimci a inda take amma bata san mutanen da ke wajen ba, Noor kawai ta shaida, ta lumshe idanunta ta kuma buɗesu murya a dashe tace "Umma.. Umma.. Ummata".....✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {38..} Kawai Ummata Hajar take kira, Mami tace "Umman ki za'a kira miki?", ta gyaɗa kai a hankali, Mami tace "alright, insha Allah za'a kira miki ita, how are you feeling now?", Hajar tace "alhmdllh", Anty Zulaiha ta taso ta tsaya gaban gadon tace "sannu ko", a hankali ta jinjina kai sai kuma ta koma ta kwanta ta lumshe ido, few seconds bacci mai nauyi ya sake figarta cause allurar baccin bata gama sakinta ba... Nurain na fita ya buɗe prescription paper en ya karanta content en ciki, he was totally confused bayan yayi realizing drugs en dake rubuce, murya can ciki yace "too young, may be inheritable..", wani near by pharmacy ya shiga ya siyo drug en, ya dawo asibitin da ledar magungunan a hannunsa, duk iya ƙoƙarin sa na ganin ya saki fuskarsa kafin ya shiga Amenity room en kasawa yayi, cause da gasken gaske zuciyarsa ba dadi, ya murɗa ƙofa ya shiga kafin yay sallama ciki ciki, Anty Zulaiha ta amsa, nan kan kujera ya ajiye ledan yace "gashi", without looking at him Mami tace "saura abinda za taci idan ta tashi", still yay na few seconds kafin yace "i thought daga gida za'a kawo abincin..", tace "right, amma ita bashi zata ci ba, so ka samo mata nata kafin ta farka", yace "yeah" zuciyarsa kamar zata fashe, ya juya ya fita, Farooq dake zaune kan plastic chair ya tashi yabi bayansa, Anty Zulaiha tace "Mami that was too tough", Mami tace "No Zulaiha, abinda ba halinsa bane yake so ya tarka, ba zai yiwu ba wllh, bazan bari yayi abinda bai dace ba gsky, ko baki lura da reaction ensa bane, bayan ya kulle yarinya a gida harta shiga wani halin, nifa I'm not in support Nurain ya bagarar da yarinya in the name of aura masa ita akay, bazan so ayi ma nawa yayan haka ba don haka nima bazan bari ayima yayan wasu ba..", Anty Zulaiha tace "kin san arranged marriage akan samu irin haka Mami..", Mami tace "ai irin hakan ne banaso..", Anty Zulaiha ba ta sake cewa komai ba. bayan 40mins Farooq ya shigo with bags a hannunsa, ya ajiye snn ya juya ya fita, Mami tace "check.. kiga mene aciki", Anty Zulaiha ta janyo ledojin gabanta ta duba, grilled fish ne na manyan tilaphia with potatoes, sai ƙatuwar bottle of fresh milk da kuma leda guda ta fruits, Mami dai combination na abincin bai mata ba, kifi da madara, kawai dai tayi shiru tinda dai ya siyo. Farooq ya ringa kallon kujerar da ya bar Nurain akay nan reception ganin empty baya nan, toh ina yaje, cewa fa yayi zai jira shi anan ya fito sai su wuce Chinese restaurant suci seafood. Nurain yayi knocking consultation room kafin ya murɗa ya shiga, ya zauna ɗaya daga kujeru biyu da suke gaban huge table da ke ɗauke da nameplate da sauran tarkace na doctor, gaisawa sukay da Doctorn, Dr yace "Dr Uthman right?", Nurain yace "yeah", Dr yace "ya aiki..?", Nurain yace "Alhmdllh ya naku?..", Dr yace "same alhmdllh", Nurain yace "Dr Mansoor bai ƙaraso ba knn?", Dr yace "Eh, sai qarfe biyar zai shigo", Nurain yace "Ohk, amm akwai wata patient da aka kawo.." sai kuma yayi shiru cause bai san sunan da zaice ba, tunawa yayi da numbern room din yace "wacca take Amenity room 2", Dr yace "Ohh, what about her?", Nurain ya sauke numfashi yace "how's her condition, za'a iya dischaging nata kafin dare..", Dr yace "No, her condition is totally not enough for discharge, za'a ɗan riƙeta na some days sbd kula da yanayin Bpn..", Nurain ya jinjina kai yace "Alright, ba damuwa kawai ayi dischaging nata akwai family doctor da zai kula da ita a gida", Dr yayi shiru yana kallonsa sai kuma yace "is she part of your family?", Nurain yace "No", Dr yay jim jin yadda ya basa amsa with repartee, Nurain yace "look, she's the daughter of my father's friend, rashin zuwan family doctor en ne yasa aka kawota nan toh yanzu doctor yazo, he will take over insha Allah...", Dr yace "Ohk", nan ya shiga yiwa Nurain bayanin komai, treatment en da aka fara mata ta yadda kawai Dr ɗorawa zaiyi, da yake shine ya duba Hajar din a take ya rubuta referral letter ya bada amma sai yamma za sallameta under cewar wani dr zai taking over, Nurain ya basa hannu sukay sallama kafin ya ɗauki referral papern ya fita a office en, wnn shine kawai option ensa to get rid of Mami's anger, yasan mene a zaman asibiti ai, ganin dr da gwaje gwaje, All Bp stuffs yana dasu a gida. sai ƙarfe biyu na rana Hajar ta farka, ba kamar ɗazu ba yanxu jikin yafi kwari, sai kace wata qaramar yarinya ta fara kiran ummata, Anty Zulaiha ce kawai a dakin Mami bata dade da fita ba wajen Dr, Noor kuma ta wuce gida Mami ce tace ta tafi sbd Hajiya na can kar tayi zugum ita kaɗai, Anty Zulaiha tace "toh fadi numbern umman taki sai a kirata", ai kam da sauri ta fara karanto numbern Umma dake haddace akanta, Anty Zulaiha ta rubuta snn tayi dialing, har ta katse ba a dauka ba ta sake kira, tana daf da katsewa aka daga, cikin dabara kuma a nutse Anty Zulaiha ta fara yiwa Umma bayani, don haka Umma bata wani firgita sosai ba, daga ƙarshe Anty Zulaiha ta kwatanta mata asibitin tace idan zata zo amma dai ba wata matsala Hajar ta samu lfy, sai a lokacin Hajar ta dan ji relief, ta fara ƙoƙarin sakkowa daga gado, Anty Zulaiha tace "mene ne, akwai inda ke miki ciwo ne?", ta girgiza kai tace "A'a sallah zanyi" tana kallon wall clock dake ɗakin, Anty Zulaiha "Ohk, zaki iya tafiya da kanki", ta gyaɗa kai tace "zan iya", a hankali Hajar ta sakko daga gado ta ɗane hannun da aka saka mata canular, ruwa leda biyu aka saka mata, tana bacci aka cire na biyun ba a saka wani ba sai kuma dare sbd kar tayi swelling tinda ba tada rashin ruwa a jiki kawai na kwarin jiki ne, Anty Zulaiha ta nuna mata door din toilet dake dakin, Hajar ta shiga toilet en tana bin bango tayo alwala ta fito, hannu a ɗane ta fito tana riritasa sai kace wani babban ciwo, Anty Zulaiha ta bata prayer mat da Nurse ta ara musu ita babu jimawa za suyi sallah, mayafinta ta ɗauka ta yafa tinda babba ne snn kuma kayan jikinta was more than decent, ta hau kan prayer mat din ta tayar da sallah, kafin ta idar Mami ta shigo, ba ƙaramin daɗi taji ba ganin Hajar harta samu kwarin sallah, Anty Zulaiha tace "na kira Mamanta na gaya mata..", Mami tace "Ohk, Dr ma yace insha Allah zuwa yamma zai iya dischaging enta, toh kinga kwa Alhmdllh jiki da sauƙi", Hajar na idar da sallah ta koma ta jingina da wall, Mami ta dubeta da sakakkiyar fuska tace "ya jikin naki?", Hajar tace "da sauƙi" tana kallon hannunta da ta ɗane sa, Mami tace "toh koma kan bed ki kwanta", ba musu ta miƙe ta koma kan gadon ta zauna, Anty Zulaiha ta ɗakko robar grilled fish ta bata, da rubber fork Hajar ta ringa cakar dankalin tana ci, kaɗan taci kifin tace ta ƙoshi, tasha ruwa da already shima Anty Zulaiha ta ajiye mata, Mami ta buɗe ledar drug dinta ta duba dose kafin ta ɓalla ta bata, wani irin yamutsa fuska Hajar tayi don idan akwai abinda ta tsana bayan allura to magani ne, da ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya ta haɗiye three tablets din. da misalin uku da minti hamsin Umma ta iso asibitin ita da Anty Jamilah, wata staff ce mai shara ta rakosu room din da suka gaya mata sunansa da Anty Zulaiha ta sanar musu ta waya, Hajar na ganin Ummanta ta sakko daga kan gadon tabi bango taje ta rumgumeta hawaye na zuba idonta, Umma tayi yaƙe ta shafa bayanta, Anty Jamilah ta zauna sukay exchanging gaisuwa dasu Mami, Anty Zulaiha ce ta sanar da Mami wace ce Anty Jamilah, Umma kan ba sai an gaya mata ba cause Hajar ta sanar da ita, Umma ta janyeta daga jikinta ta ƙarasa kusa da Anty Jamilah ta zauna, suka gaisa da su Mami, Hajar ta rakuɓe nan gafe guda hannu a ɗane tama faman riritasa, Anty Zulaiha tace "dan dai ta damu da sai an kira mata Ummanta ai da sai mun koma gida za a gaya muku, tinda da yammar nan za a sallameta", Anty Jamilah tayi murmushi tace "gashi dai kam ai lafiya ta samu, ai ƴar uwarta ma taje gidan tanata tsaye a waje ashe ba kowa ana asibiti", Anty Zulaiha tace "Allah sarki, ai tin safe muke nan da yake ciwon da safe ya tasar mata..", Umma ta ɗan tattare fuska, ciwon ya tasar mata, idan fa akace ciwo ya tashi to ana nufin daman tin tini mutum na ɗauke dashi, toh me yake damun ƴarta don ita dai tasan batada wani ciwo. Dr ne ya shigo wanda yayi taking over tinda wanda ta gani da safe ya tafi, kallon gado yayi ganin wayam yace "where is the patient", Hajar ta turo baki ta tashi tana layi kaɗan ta koma kan gadon, few questions yayi mata kafin ya fita yace zai dawo nan da 1 hour, su Umma basu wani jima ba suka tashi tafiya, nan hankalin Hajar ya kuma ɗagawa, Anty Jamilah na kallon fuskarta da hawaye ya cika tam a idonta tasan kuka za tay, ta isa gefen gadon ta zauna kusa da ita ta fara mata magana a hankali, Hajar ta gyaɗa kai tana controlling kukan da yke shirin kwace mata, da kyar tace "tom, na dena wllh kuma zan kwantar da hankalina", Anty tace "good, to sai nazo" da haka ta miƙe ta sake yiwa su Mami sallama, Umma ta dubi Hajar da take daf da rushewa da kuka tayi mata murmushi snn ta buɗe ƙofa ta fita Anty Zulaiha tabi bayanta. Hajar tayi sauri ta kwanta ta tsiyayar da ruwan hawayen da ya cika mata idanu, After 1 hour din kam Doctorn ya dawo a lokacin biyar saura, kai tsaye sallama ya basu daman sunyi magana da waccan Drn. ƙofa akay knocking kafin aka shigo, Nurain ne, ido huɗu sukay da Hajar, yay saurin ɗauke kansa ya hade gira, Mami na kallon Dr tace "A cire mata canular", with a repartee Nurain yace "No, kar a cire", Mami ta dubesa ba tace komai ba, Dr yay musu sallama kafin ya fita. Anty Zulaiha na riƙe da hannun Hajar suka fita harabar Hospital en, Farooq dake zaune a under tree ya taso, Nurain ya shiga front seat ya bawa Farooq key din Mota don haka ya shiga driver seat, Mami Anty Zulaiha da Hajar kuma suka shiga baya, Farooq ya kunna motar ya fara driving suka fita daga asibitin, direct daman hanyar gidan Abba ya ɗauka. ★Maama ta rantse ta kuma rantsewa ta buga cinya tace "billahillazi la'ilaha illa huwa sai malamin tsamiya ya biyani kudina dubu arba'in, tinda aikinsa bai ci ba wllh sai ya biyani kuɗina", Balaraba da ke kallonta baki a hangame tace "ai kwa kya yi kya gama Rabii, wane cin kike magana a kai, naga dai auren da ba kya so a ɗaura naga dai ba a ɗaura ba, bata auri malamin makarantar ba ehee, kinga kwa malamin tsamiya yaci kuɗinsa wllh", Maama ta fige ɗan kwalin kanta da ya rufawa kanta asiri, don wani irin tsohon kitso ne a kanta wanda zai kai wata huɗu, ta sosa kan wanda nasan babu shakka kwarkwata ce ta mintsileta, tace "Balaraba malamin nan dan abu kaza kaza ne, me yasa bai hango wanda zata aura ba iyee, wllh da nasan haka zata faru wllh tllh bazan yi asarar kudina ba, ai gwara ta auri malamin makarantar....", Balaraba tace "Wai a sbd me kike faɗin haka?", Maama ta dafe goshinta mai lemon tsami tace "dana sanin da nayi yafi cikin kwando Balaraba, wato ina gaya miki, malamin makarantar nan ba komai bane akan wanda Hajara ta aura...", Balaraba ta kuma hangame baki har ƙudaje suka fara shawagi, Maama ta sharce zufar dake keto mata tace "ke kinga gidan da aka kaita kuwa gari guda, lefen da aka bata kam ya linka na malamin makaranta sau shida..", Balaraba ta kore ƙudajen da suke shawagi kusa da bakinta tace "an shiga ƙuryar ɗaka ba'a tsira ba, Rabi kimin bayani yadda zan gane..", nan Maama ta gyara zama ta shiga fesawa Balaraba zance, ta ƙarashe tana sharce zufa tace "kinga lukutar masifar dana jibgowa kaina", Balaraba ta gyaɗa kai cike mamaki ta kasa cewa komai, Maama ta hauta da masifa tace "dalla malama ya zaki min shiru na zo ki bani hanyar ɓullewa, kin wani hangame baki wari duk ya cikamin hanci ciki ya kumbura, kiyi magana na shaƙi warin da hujja tinda dai na rage zafi amma kinyi shiru inata shaƙar ɗoyi a banza", Balaraba tace "Au haka fa, kinsan gwano baya jin warin kansa, ni da kika buɗe wnn tsumman kan naki sai kace hammatar ɗan iskan sabon gari mai ɗoyin tsiya bance komai ba sai ke, toh kafin cikin ki ya kumbura nawa ya gama cika dammm da samamin kanki..", Maama tayi kwafa tace "haka kika ce ko?", Balaraba tayi tsaki tace "Ahap ai kinji mai nace", Maama ta ɗaura ɗan kwalinta tace "biyani dubu biyar ɗita..", Baraba tace "wace dubu biyar?", Maama ta miƙe tsaye a fusace tace "wacca kika ce sai na baki zaki rakani wajen malami..", Balaraba ta miƙe itama tace "bazan biya ba, akan me zan biya bayan na miki aiki kin samu", Maama ta yayibi duƙunnanen hijab dinta mai warin dauɗa ta saka ta fice fuuu daga gidan kamar zata tashi sama, Balaraba ta buga cinya tace "Allah raka taki gona, ni nan da kike ganina ɗuwaiwai ce ko dan zama a nemeni". daf da magrib Maama ta koma gida a fusace, Baba da ke alwala nan bakin rariya ya ringa kallonta kafin yace "daga ina kike?", ta hura hanci tace "nan nan maƙota na shiga an yiwa ɗan gidan shayi", Baba bai sake ce mata komai ba ya cigaba da alwalarsa, Umma ta fito daga ɗakinta itama za tay alwalar, ta ɗau buta ta buɗe tukunya ta ɗebi ruwa, Baba da ke wanke ƙafa yace "ya jikin Hajaran?", Umma tace "Ahh da sauƙi sosai..", Maama da bata ƙarasa shigewa ɗakinta ba ta juyo tana tafa hannaye tace "za kiga sauƙi, wato har an fara tsotse jininta, wllh duk wanda ya hau motar kwaɗayi babu inda zata ajiyesa sai a tashar wulaƙanci, kuɗi ƙumbar susa sun hanaku amso ƴarku ko, toh wllh ku ka bari aka tsotse mata jini har ta mutu ranar gobe qiyama sai an muku hisabi da ita, wnn ai cin zali ne da tauye haƙƙi, ƙiri ƙiri kuɗi sun ruɗeku kun wurga yarinya a halaka, kun kaita gidan yankan kai za ai layya da ita..." Baba ya tashi yayi ficewarsa cause har an kira sallah, Umma tayi shigewar ta bayi, Maama ta gyaɗa kai tace "hmmm, a banza an yakushi kakkausa, wllh kanku kuka wulaƙanta" da haka ta afka ɗakinta, ta kalli Nabilah tace "Su Sa'adatu basu dawo ba ko?", Nabilah tace "Eh, dan Allah Maama wai ina ruwanki da auren Hajara ne", Maama ta zabga wani uban tsaki tace "shknn, tinda nace kar su kai dare amma saida suka kai wllh ba ruwana idan mal ya gansu, kar ma shegiyar da ta ambaci suna na". ★Wani extra room dake part din Mami aka gyarawa Hajar, Noor ta kawo mata kaya set biyu da kuma sleeping gown, bayan tayi wanka ta ɗauki guda ɗaya ta saka, Hajiya har nan tazo ta dubata tana rafsa salati da godiya, ai gwara da ta warke kar ace a gidan jikanta ne, Hajar ta durƙusa har ƙasa ta gaida Hajiya, bata amsa ba ta tsaya tana kallon hannun Hajar din da take maƙalesa tsabar san jiki, Hajiya tace "meye wnn en kuma ya sandarar mata da hannu?", Noor da itama ke ɗakin tace "Canular ce iron lady, abin ƙarin ruwa..", Hajiya tace "toh me yasa basu cire mata ba a can asibitin suka barta da wahala?", Noor tace "nima ban sani ba", Hajiya ta kalleta ta saman kantamemen glasses dinta tace "tafi kira Usuman yazo ya cire mata, ji fa yadda hannu ya sandare", Noor tace "ya fita masallaci", Hajiya ta danne sandarta ta mike daga gefen gado da ta zauna tace "nima bari naje nayi sallar" da haka ta dogara sandarta ta fita, Noor tayi ajiyar zuciya tace "Ohh, Hajiya iron lady", Hajar tayi murmushi, Noor tace "kiyi sallah, yanxu zan kawo miki abinci", ta fita, Hajar tayi sallah, tana idarwa ba jimawa saiga mai aiki da tray na abinci, ta ajiye kan couch kafin ta fita, Hajar na idar da sallah ta jingina da jikin gado ta lumshe ido, jiri ne yake ɗan ɗibanta kaɗan, Mami ta shigo, ganinta a haka tace "are you okay dear?, idan akwai inda ke miki ciwo say it out", Hajar tace "bana jin komai", Mami tace "Alhmdllh, ga abinci ki ci sai ki sha drugs ki kwanta ki huta ko", tace "tom nagode", saida tayi sallar isha'i wacca da kyar ta iya yinta a tsaye sbd jiri snn ta buɗe abincin, aroma na abincin ne ya ɗebeta har ta ɗan ci kaɗan, ta sha ruwa, daga haka ta malale kan carpet, (that question goes to you young lady, what are you doing in my house) shine abinda ya amsa a brain dinta, ta lumshe idanunta hawaye na zubowa a cheeks dinta... Nurain ya shigo palourn Mami da leda a hannunsa, Mami na shan fruits Salad while watching news, kujerar da ke facing ɗinta ya samu ya zauna, ya ringa kallonta ganin ko kallon inda yake ba tay ba her eyes fixed on TV, calmly yace "Mami zan dubata", tace "ohk" tana shan fruits Salad dinta, yayi ajiyar zuciya yace "zan sa mata drip ne, na mata injection..", tace "toh..", shiru palourn ya ɗauka sai ƙarar TV, shi bai sake cewa komai ba kuma bai tashi yayi abinda yace zaiyi ɗin ba, Noor ta shigo tana dariya tace "wnn aboniki naki iron lady ina zan kai yajinsa, dole Aysha ta gudu idan kika ce ta shafa miki..", hanyar room din da Hajar take ta wuce, Nurain yace "Noor", ta juyo tana kallonsa tace "Na'am", yace "tana ina?", tace "waa?", ya tsuke piercing eyes ɗinsa, Mami dai ba tace komai ba, Noor tayi tsaye tana jiran yace wani abun, a dan hasale yace "ina patient din?", tace "tana ciki" tayi masa nuni da ƙofar ɗakin da Hajar take, miƙewa yayi da ledar a hannunsa ya shiga ɗakin, Mami ta bisa da kallo, Noor ta shiga ɗakin itama, a bakin door ta gansa ta wucesa ta durƙusa gaban Hajar dake kwance kan carpet, taping dinta tayi a hankali tace "Hajar are you okay?", Hajar ta miƙe a hankali tana kallon ɗakin sbd scent din da tayi perceiving, jajayen idanunta suka faɗa cikin nasa, da sauri ta sauke kanta ƙasa tana yamutsa fuska, yace "Noor help her to bed", Noor ta tashi ta riƙe hannunta ta temaka mata ta koma kan bed, Nurain ya ajiye ledar hannunsa kan chest of drawers ya fara haɗa ruwan injection, ya fito da ruwan da zai ƙara mata ya ciro empty syringe ya zuƙi ruwan kafin ya isa gefen gadon, koda wasa bai dubeta ba, hannun da take maƙewa yake kallo don tanan zai mata allurar ya sa mata ruwa, Noor ta tashi zata basa waje yace "no, ɗago min hannun", Noor ta dauki pillow ta ɗora hannun Hajar mai canular a kai ta matsa gefe, ya kwance Canularn making sure bai taɓata ba, ruwan da ya zuƙa cikin syringe ya fara ɗura mata sbd yayi flushing vein en kafin ya zuba ainahin ruwan allurar, wani zafi Hajar taji a hannun da take riritawa, a zabure ta janye hannunta ta kwala ihu.....✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {39..} Still Nurain yayi yana kallon syring en da ta bar masa a hannu, Hajar ta zaro ido tana yarfe hannunta da already jini ya gama wankesa cause Canularn a buɗe take, da sauri Noor ta isa gaban mirror ta dakko kwalin tissue, ta zauna gefen gadon ta kamo hannun Hajar tana goge mata jinin, Mami ce ta shigo da sauri cause taji ihun Hajar tinda door a buɗe take, Mami tana kallon Nurain tace "what is happening here?", Noor tace "amm flushing vein en ake mata za'a mata allura", Mami ta ƙaraso gefen gadon tana kallon Nurain da ke riƙe da syringe tace "ka mata a hankali mna, you know it's hurting...", baice komai ba ya bar wajen ya ajiye syringe en cikin ledar dake kan chest of drawers snn ya nufi door, Mami tace "Nurain...", ya juyo yace "na'am Mami", tace "ina kuma zaka?, ka gama mata injection din ne?", yace "No, kawai tasha drugs.." da haka ya fice mai gaba ɗaya, Mami ta dubi Hajar da hawaye ya ciko idanunta tace "Sorry" sai kuma ta dubi Noor tace "take that thing off her vein kawai" ta fita a ɗakin, a hankali Noor ta zare mata canularn daga hannun, ta bata tissue ta danne wajen, wani sakayau Hajar taji hannun yayi mata, bayan kamar 2minutes Mami ta dawo ɗakin da ledar drugs da bottle water an rufa mata disposable cup, da kyar Hajar ta iya haɗiyar maganin tana yamutsa fuska, Noor ta gyara mata pillow ta kwanta, Mami tace "Noor saiki kwana anan ko?", Noor tace "tom, bari naje room dina na dawo". ko minti biyar ba ai da fitar Mami da Noor ba bacci ya kwashe Hajar, luntsum tayi cikin duvet tana baccin da ba daban rashin lfy ba bazata iya yinsa ba, Noor na gama uzirinta a room ɗinta ta dawo ɗakin da Hajar take ta kwanta. tsakar dare Hajar ta farka sbd kanta da take jin tamkar zai tsage, ga wani azababben jiri da take jin tamkar ana hajijiya da ita daga kwance, sideways take jujjuya kanta ba tare da tasan tana aikata hakan ba, slight movement da take yi ne ya farkar da Noor wacca sam sam ba tada nauyin bacci, Noor ta kunna bedside lamp kafin ta yaye duvet da ta rufa ta miƙe zaune, saida vision dinta ya daidaita ta lura da yadda Hajar take motsi involuntarily, da sauri ta sakko daga gadon ta kunna lights sosai, with compassion Noor ta taɓa forehead dinta, her temperature was very high at that moment, direct Noor ta fita a ɗakin, after like 5minutes ta dawo tare da Mami, sosai hankalin Mami ya tashi, amma kuma da ta fahimci cewa Hajar na cikin hayyacinta sai damuwar ta ragu, complain ɗin da Hajar tay kawai shine kaii sbd shi yafi takura mata, har Mami zata bata panadol sai kuma ta fasa, Noor da idonta ke cike da bacci tace "kamar ma anyi dischaging enta da wuri fa", Mami tayi ajiyar zuciya tace "nima dai haka na gani, what says the time?", Noor ta duba lokaci a wayarta tace "biyu da minti sha uku..", Mami ba tace komai ba ta tashi ta fita, Hajar dai na jingine da allon gado idonta a lumshe. Mami na fita kai tsaye room din Nurain ta wuce, knocking door tayi, ko 1minute ba tay da fara knocking ba ya bude, ya zaro sleepy eyes dinsa yace "Mami..", tace "kazo ka duba Hajar jikin ya tashi", yace "tom ina zuwa" ya koma cikin ɗakin nasa domin ɗaukar wasu abubuwan, definitely yasan haka saita faru tinda taƙi bari yay mata allura, yana gama ɗaukar abinda zai ɗauka ya fito, yabi bayan Mami suka wuce part enta, yana shiga ɗakin ya ɗauki ledar da ya bari kan chest of drawers, ya zuƙi injection dose en da zai mata a syringe, ya isa inda take jingine da gado yana kallon hannunta da yaji zanen ƙunshi, Mami ta ringa kallonsa ganin yayi tsaye bashi da niyyar yi mata allurar, har ya kai hannu zai riƙe hannunta sai kuma ya fasa, ya farke ledar hands gloves da ya shigo da ita ya saka gloves en a hannunsa, Mami da Noor dai suka bisa da ido, ita kam baiwar Allah Hajar ko iya buɗe idonta ba tayi sbd haske linka mata ciwon kan yake, a damtse yayi mata allurar, ta motsa kaɗan lokacin da ya zare empty syringe en daga muscle enta, ya saka mata drip da bai sa mata ɗazu ba, deeply in his mind saida yayi dana sanin da yasa akay dischaging enta, wai shi gudun liability na asibiti yayi, sai gashi bai tsira ba, yana gama mata duk wani abin da ya dace yace "Mami you should get back to sleep, itama bacci za tay", Mami na kallon Hajar tace "gobe da sassafe sai mu koma asibiti gsky", yace "No, insha Allah she'll be fine", Mami tace "toh Allah yasa, Allah yay albarka", yace "Ameen" kafin ya fita, bayan minti goma da fitarsa Mami taga jikin nata har yay sauqi, ta koma baccinta kuma babu zazzaɓi a jikinta, Mami ta kashe musu fitila kafin ta bar room din, washe gari kam jikin Hajar saidai nace alhmdllh cause kamar ba ita bace ta cikin dare jiya, har ɗaki aka kawo mata breakfast, daga wayewar gari zuwa yanxu da ake maganar 10 na safe Mami ta shigo dubata sau uku, Noor kuma ta wuce school tinda ranar Monday ne. ★Hakima Ruqayyah ta ajiye wayarta a kan mirror bayan ta gama tura text message, ta gyara wuyan rigar kayan baccin jikinta wando da riga kafin ta fita daga ɗakin nata, kitchen ta shiga ta fara preparing breakfast, omelette roll da toasted bread saita tafasa black tea mai kayan ƙamshi, tana gama haɗa breakfast din ta ɗakko Oat meal ta damawa kanta, ta zuba isasshen powdered milk da sugar kaɗan, ta zuba 4pieces na omelette roll ta ɗauki oat meal din ta fita, a palour ta zauna ta ci abincin, tana gama ci ta kai plate da cup en kitchen ta wanke, ta koma room enta ta shiga wanka, ta fito ta tsaya gaban mirror ta gama shafe shafenta tana humming song da tayi setting enta matsayin ringtone na dearest, well ironed uniform ɗinta ta ɗakko ta saka, as usual ta ɗora black Abaya saman uniform en, tsaf ta shirya snn ta ɗauki wayarta ta zura a jaka ta fita ta rufo ɗakin, room din Momy ta shiga don ta sanar da ita ta fita, Momy ta amsa gaisuwar da ta mata tace "kuma kika ce yau night ne dake?", Ruqayyah tace "Eh, exchanging nayi da wata collegue dita ita tanada abinda za tay da safe", Momy tace "ohk, toh sai kin dawo", Ruqayyah tace "uhmm, nayi breakfast na ajiye muku a kitchen", Momy tace "Okay", Ruqayyah ta miƙe zata fita, har ta kai ƙofa Momy ta kirata, dawowa tayi ta zauna, Momy tace "kinsan dai lokacin da Daddy ya ɗebar miki ya kusa ƙarewa ko, ya maganar Dr tinda kince kun sasanta idan ya dawo daga tafiyar komai zai daidaita, ya ake ciki ya dawo en ko bai dawo ba, don na gaji da kareki a wajen Daddy zanyi shiru na zuba idanu ya aura miki Daudan tinda dai bashi da wata matsala...", Ruqayyah ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tace "Momy, har yanzu bai dawo bane, daga ya dawo shknn, dan Allah ki cigaba da bawa Daddy haƙuri, wllh bana son Dauda bayan mata biyu da yake dasu gashi gajere kamar a kife da kwando, kuma fa ɗingishi yake wllh sai a zata gurgune..", tini idonta ya kawo ruwa, Momy ta taɓe baki tace "Au lallai Ruqayyah har kinada bakin kushe wani ko, toh ke da kike ba nakasasshiya ba ai ba finsa kikai wajen Allah ba, toh kwa ki san inda dare yayi miki wllh, haba kin bi kin nace sai Dr, Doctorn da kika tozarta kika gudu kika barsa ranar ɗaurin aure, daman ni jinki kawai nake da kike cewa ai kun sasanta, ai ba zuciyar kare ne dashi ba da zai yarda dake bayan cin amanar da kikai masa, wani chance en sau ɗaya yke zuwa a rayuwa, ki tsaida hankalinki ki fuskanci reality, ki na dai da manema ba babu ba...", Ruqayyah dai gaba ɗaya guiwarta ta saki, ta goge kwallar da ta zubo mata, Momy tace "you may leave na gama dake", Ruqayyah ta tashi tana goge idonta tace "zan biya gidan ya Kulsoom", Momy tace "kar kiyi dare", tace "tom" kafin ta buɗe ƙofa ta fita, slowly take tafiya a street en gidansu tana saƙa da warwara a zuciyarta har ta fita babban titi, ta tsayar da Napep ta gaya masa inda zai kaita, har cikin asibitin ya shigar da ita, ta sauka ta buɗe jaka ta bawa mai napep kuɗinsa, a hankali take tafiya tana kallon parking spaces, wani irin harbawa zuciyarta tayi, hope din da take dashi ya zagwanye gami da tsiyayewa ta guiwarta ganin babu motar Dr Uthman a wajen parking ensa, direct hanyar office ensa ta nufa, tayi zaman jira kan silver chair dake ƙofar office en nasa, nace wasa farin girki hakima Rukky, almost one hour tana jira amma babu alamarsa, ta shiga aikin da ta saba na kiransa da tura masa text message, ta ciro handkerchief ta fara share hawayen dake sauka idonta, ji tayi ance "A Nurse are you okay?", ta ɗago kanta sukay ido huɗu da Khaleel, tayi fake smile tace "Oh Dr am fine..", ya tsuke ido yace "are you sure?", tace "sure", ya kalli ƙofar office en Dr Uthman yace "but what are you doing here all alone?, aren't you suppose to be in nurse station?", ta sake yin wani fake murmushin tace "yeah, yanzu nake shirin tafiya can en", yace "ohk see you later.." da haka ya bar wajen ya barta zaune, ta dafe kanta a hankali tana tunanin what next, ga dukkan alamu dai wanda tazo Hospital en dominsa bazai zo ba, daman yau sai dare take da duty amma sbd shi ta ƙuma uban sammako, gashi kuma bai zo ba, tamkar wacca aka zarewa spine haka ta tashi ta bar bakin office en, wani irin nauyi zuciyarta tayi mata, haka ta sake saɓa ta fito daga asibitin, ta tsari napep zuwa gidan Kulsoom. ★Sosai Hajar ta ware, she really appreciate yadda mutanen gidan suke they were so humble and caring, duk abinda take buƙata an mata shi, lunch ma har ɗaki mai aiki ta kawo mata, ga Mami wacca take dubata akai akai, da daddare Hajar ta idar da sallahr magrib knn tana wrapping prayer mat Noor ta shigo, tace "Alhmdllh jiki yay sauqi, ai zaki iya fitowa ko?..", Hajar ta ajiye darduman kan stool ta girgiza kai a hankali, Noor ta jingina da jikin ƙofa tace "na shi gangaɗe...", da farko kamar Hajar ba zata tambaya ba sai kuma tace "me ya faru?", Noor ta shafa forehead dinta tace "wllh iron lady ce, nace mata kin samu lfy amma duk bayan minti talatin saita ce nazo naga ya kike, wai ƙafarta ke ciwo bazata iya tafiya sosai ba, ta hanani ma kallon stuff ena gashi i hate watching it on phone or computer, i prepare watching it on TV...", Hajar dai ba tace komai ba, Noor tace "dan Allah kizo muje ta ganki in yaso saiki dawo, Allah bazata barni na huta ba", Hajar dai tayi shiru ba ta san me za tace ba, ita kam bata son ma ta ɗara ko ina, kawai dai dagewa take tana so ta zama comfortable which was very hard on her, ta kalli expression en fuskar Noor wacca take kallonta da pleading eyes tana jiran amsa, da kyar ta iya cewa "tomm", Noor tayi clapping hands enta wanda hkan ya bada sound kaɗan tace "thank you, muje ko, tana ganin dai you are fine saiki dawo abinki, rigimar tsufa ne..." da haka ta buɗe ƙofa, Hajar ta gyara wuyan dogon hijab din da ta idar da sallah kafin tabi bayanta, ba kowa a huge palourn Mami, itama Mamin ta shiga bedroom enta daman idan ta shiga sallar magrib bata fitowa sai after isha'i, Hajar tayi surveying palourn da idanunta tana biye da Noor, Noor ta buɗe ƙofar fita daga part en kafin suka wuce long corridor suka fita main palour, nan ma dai saida Hajar tayi surveying ensa, wani nervousness ne ya rufe ta, ta fara tambayar kanta to wane ne wnn abokin na Baba ita dai bata sansa ba, tinda take bata taɓa ganin palour mai girma da ƙawatu kamarsa ba, ita bata tsaya ƙarewa gidan kallo ba jiya da aka kawota, ko lokacin sallah da agogon room enda take ciki take amfani cause bata gane dare da rana sbd komai na gidan equal yake, safe rana dare duk akwai wuta, Noor ta wuce hanyar da zai leading zuwa part en Hajiya, Hajar dai was following her like one living statue, buɗe ƙofan part en Hajiya Noor tayi da sallama, Hajiya dake zauna kan lallausan carpet ta miƙe ƙafafuwa ta kalli door tace "waye anan?", Noor ta matsa gefe Hajar ta shigo da sallama, Hajiya ta sake cewa "nace waye anan...", Noor ta tsugunna gabanta ta ɗauki glasses enta ta saka mata tace "da me yasa kika cire glasses dinki..?", Hajiya tace "yo idon ne yake min ƙaiƙaiyi shine na cire zan sosa, ban kai ga sosawar ba naga inuwa akaina", Noor ta dubi Hajar tace "ƙaraso mana", Hajar ta ƙarasa shiga cikin palourn ta zauna can ƙarshen carpet, Hajiya ta bita da ido, Hajar tace "ina yini..", Hajiya tace "wace ce wnn?", Noor tace "Au keda glasses din ma idon naki sai a slow, wacca fa kika takura naje na dubo miki ce fa", Hajiya tace "O oho matar Usuman din ce?", Noor tace "daman nace miki taji sauqi, toh gashi dai yanxu idonki ya gani", Hajiya tace "matso kusa mana ƴar nan saiki raɓe can ƙarshen buzu sai kace wata bare ba ƴar gida ba", Hajar ta matso a hankali ta shigo kan carpet en sosai ta sake tisa gaisuwar da tayi mata, Hajiya ta amsa tana dashare wawulon bakinta tace "tubarkallah masha Allah, yarinya ta saɓe jiki yayi kyau alhmdllh", Noor tace "ai na gaya miki", Hajiya tace "ita ta zaunar dani a gidan nan, yo inba larura ba mai zaisa na baro mijina na zo nan na zauna, hankalina ne yaƙi ya kwanta wllh tin jiya da naga yadda muka kaita asibiti, ace ana kawo mna yarinya sai kawai ta kwanta ciwo sai kace an kawota wajen mayu, kinga kwa gobe in Allah ya kaimu saina kira Umaru yazo ya ɗaukeni na koma gidan tsamiya..", Noor ta haɗe gira tace "nan ma ai gidan tsamiya ne", Hajiya tace "nan fa ɗaya, ba miji a gida ta ina ya zama gidan tsamiya", Noor ta miƙe tana kallon Hajar tace "bari nayi leading enki ki koma ko..?", Hajar ta gyaɗa kai, Hajiya tace "ta koma ina kuma, rabu da ita anan tayi zamanta tinda ba tace ta gaji ba, haka kurum ki ƙugata a ɗaki", Noor ta koma kan kujera two sitter ta zauna, remote ta janyo ta canza channel, tayi murmushi don yanxu ne ake taken next Cdrama da take so, ta fara cin coconut macaroons da ta ajiye nan tare da popcorn, Hajiya ta micincina idanu tana kallon Tvn tace "ji mutane sai kace aljanu, fuska kamar anyi ɓarin filawa, anya ma kwa akwai jini a jikinsu?", Noor dai an riga da an bada amanna ba ta ji ma sosai, a hankali Hajar dake wasa da laushin carpet ta ɗaga kai ta kalli TV, ko minti goma ba ai da fara film en ba ta ji ya ɗan birgeta sbd margic da ake zubawa, Hajiya sai mita take a mayar mata da makka, Noor kam tayi mata shiru tinda ita ta nace saita zauna a wajenta don haka sai ta gama kallonta kuwa, Hajiya ta saƙa hannunta ƙarƙashin kujerar da ta jingina da ita ta ciro kwalbar man zafi (Aboniki), ta buɗe kwalbar ta shiga lakuta tana laftawa a sangalale, tini Noor ta toshe hanci sbd har yaji ya bulale palourn, saida ta lafce ƙafufuwanta tasss da Aboniki, sai shining suke da sheƙi, can wajen yatsun ƙafar ne kawai bata shafawa ba sbd hannunta bazai kai ba kuma bata iya tankwashe ƙafar, ta lakuto wani lafcece kafin ta dubi Hajar da already idonta ya kawo ruwa sbd yaji tinda tafi kusa da ita tace "shafa min daga nan saman makyangyamar..", ba musu Hajar ta miƙa hannu Hajiya ta lakuce mata uban man Aboniki a tafin hannu, a hankali Hajar tayi rubbing dinsa a palm kafin ta fara shafesa a toes en Hajiya da suke a yamushe kuma a tattare sbd tsufa. juyowar da Noor za tay kenan taga Hajar na aikin da ita da Aysha ke gudu, Noor tayi murmushi ta kuma toshe hancinta ta cigaba da kallonta, door aka buɗe aka shigo, scent ensa ne ya mamaye palourn, yay sallama yana ƙarasa shigowa sai kuma ya tsaya cak, Hajar ta ɗauke hannunta daga legs en Hajiya gami da mayar dashi cikin hijab ta juya ta cigaba da kallonta, and that gave him the full access to saw her face completely, and he realized her, automatically ya juya ya fita a palourn tare da banging door......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_ feeche {40..} Hajiya tabi ƙofar da Nurain yayi banging da kallo tace "ikon mai duka, cewa nayi fa zanyi magana da kai shine zaka zo ka nunamin wata fuskarka da na rasa dalilin sauyawarta ka fita", Hajar ta runtse idonta tana haɗiyar wani kwallo da ya tsaya mata a throat, ta wutsiyar ido ta gansa shine ta maze, gaba ɗaya taji ta tsani zaman nan en so take ta koma inda ta fito, a hankali ta miƙe tana jan fingers, Hajiya ta dena sababin da take ta ɗaga kai tana kallon Hajar tace "lafiya kika miƙe sai kace wacca aka zubawa mugun mintsili?..", Hajar tayi kasa da idonta tace "zanyi sallah ne..", Hajiya ta nuna mata qibla tace "buzun tsaftatacce ne, kiyi sallar ki", Hajar dai tayi shiru don ba haka taso ba, ita so take ta bar nan din kawai, Hajiya tayi kasaƙe tana kallonta ganin bata kalli qiblar ba kuma ba tada niyyar kabbara sallar da tace za tay, Hajiya ta dubi Noor tace "ƴar nan, kee", ina Noor sai blushing take tana tura coconut macaroons a baki, gaba ɗaya mind dinta na kan TV, Hajiya ta ɗauki trow pillow ta wurga mata, sai a snn Noor ta juyo tana wuri wuri da ido tace "mene ne iron lady?", Hajiya ta mata daƙuwa tace "wnn wane irin masifar kallo kike ne, nayi ta miki magana amma kin saki baki da hanci kin zubawa wasu kodaddu idanuwa a talabijin", Noor ta ajiye coconut macaroons da take ci tayi folding hands tace "Allah ya baki haƙuri, banji bane", Hajiya tayi tsaki tace "kinga ƴar nan matar Usuman tace zatay sallah nace tayi anan tinda buzun tsaftatacce ne amma taƙi yi, toh inajin dai tsaftarsa ba tay mata ba, ki tashi ki ɗakko mata wani acikin ɗaka sai ta ɗora akan wnn tayi sallar", Hajar tayi ƙasa da murya kanta a ƙasa tace "A'a zan koma can din ne sai nayi sallar a can", Noor ta tashi tace "alright muje na rakaki..", da haka Noor ta nufi door Hajar tabi bayanta walking slowly, Hajiya ta bisu da kallo tana taɓe baki tace "Au wnn aka aurawa Usuman, da gani bata son mutane, ta zauna a cikin mutane amma taƙi ta gwammace ta ƙursum sa a ɗaki, Allah dai ya kyauta...". har sun kama hanyar part din Mami sai kuma Noor ta dakata, ta juyo tana ƙarewa main palourn kallo, taji scent dinsa amma kuma bata gansa ba, yana zaune a edge of executive two seater yana operating Mac phone, Noor ta buɗewa Hajar ƙofar shiga part en Mami tace "go ahead am coming", Hajar ta shige ciki, Noor ta koma main palourn ta isa kusa dashi ta tsaya daga gefen kujerar tace "Yaya ina yini?", ciki ciki ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba kawai danne dannesa yake jikin Mac phone, tace "Yaya don Allah zan turo maka da project dina ka duba min kafin nayi submitting na gama..", sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalleta kafin ya mayar da idonsa kan abinda yake yace "Ohk, Allah yasa ba shirme kike rubuta ba, don naga yanzu ba kya karatu sai kallon shirme kika iya, keep this in front of your mind idan shirme kika rubuta am going to punish you", ta sosa forehead dinta tace "shknn ma, yaya Farooq zan turawa ma kar nayi stressing dinka", yace "kafin 9pm naga mail dinki in my inbox Noory", ta gyaɗa kai a hankali tace "Sure Yaya" ta bar wajen ƙirjinta na bugawa, tasan dai bata rubuta shirme ba cause saida tayi research kafin ta rubuta komai, amma dai dole sai an mata gyara, ta shiga part en Mami, a tsaye ta tarar da Hajar a corridor ta jigina da bango, Hajar tayi saurin juyar da kanta gefe tana goge cheeks dinta, Noor taso ta fahimci cewa kuka take amma kuma demon en gabanta shine ya kwashe mata tunani, har ɗaki ta raka Hajar kafin ta fito, direct kuma room dinta ta wuce tayi plugging Lap top dinta a charge. Hajar ta idar da sallah, kwanciya tayi kan carpet ta lulluɓe da babban hijab din da tayi sallar, tara da rabi Mami ta shigo dubata, Mami ta dafa forehead dinta to feel her temperature, Hajar ta buɗe idonta don ba bacci take ba, tunani ne iri iri ya cunkushe mata a brain, Mami tace "ki dena kwanciya kan carpet ga bed nan, ko headache en ne?", Hajar ta tashi zaune tana girgiza kai tace "A'a ya dena ciwo", Mami tace "toh alhmdllh, ya baki ci abincin da aka kawo miki ba, ko ba kya son sa?", Hajar tace "na ƙoshi, naci da yamma", Mami tace "Okay, toh kisha drugs enki sai ki kwanta ko, if you need anything just let me know kinji", Hajar ta gyaɗa kai a hankali, Mami na fita Hajar ta shiga bathroom, tayi wanka ta fito ta saka kayan baccin da Noor ta bata, like yesterday night wnn ma ba tayi bacci ba, saidai wnn daren lafiyar ta lou kawai dai ta kasa rintsawa. ★Hajiya ce zaune bisa 3 sitter a great room din Abba, tayi shirinta tsaf da shigar asun da asun na atamfa, ga ɗaurin kallabi irin na tsofaffin nan mai santi, ta zubawa Abba dattijon idanunta da suka sha farin kwalli tace "Muntari nidai ban fahimci zaman Usuman a gidan nan ba, ya ɗauki matarsa su koma gidansu tinda ta warke sumul abinta, tinda dai waraka ta sauka to banga amfanin zama a nan ba, su koma gidan su kar aje a ƙuma musu sata, don wnn uwar dukiyar da aka laftawa gidan ɓarayi sai su shigar musu tinda banga alamar mai gadi ba, amma kuma dai naga wayar shokin zagaye da gidan, ɓarayi ba zasu iya shiga ba gsky..", Abba yace "insha Allah this week zasu koma..", Hajiya ta katsesa da fadin "toh mai zai hana yau su tattara su tafi, nifa yau zan rugungunta na tafi, kamata yayi ma mu fita gidan nan tare dasu, nasan yanzu ma Umaru yana kan hanyar zuwa ɗaukata", da taushin murya Abba yace "Hajiya ku dan sake zama mana zuwa wani lokaci ko sati fa ba kiyi ba..", Hajiya ta girgiza kai tace "A'a A'a Muntari kasan dai ni adala ce, shekarata biyu a gidan nan banje gidan Salisusu ba ina nan, shima saina jingine masa shekaru biyu kafin na juyo nan idan Allah ya ara min lokacin". knocking door akay kafin aka buɗe aka shigo, Mami ta shigo da sallama, ta sanar da Hajiya cewa breakfast dinta is ready, Hajiya tace a kawo mata abincin nan anan zata ci, Mami ta juya ta fita, babu jimawa ta dawo da tray a hannunta, tayi serving Hajiya creamy groundnut pap with yummy beans cake. Mami na gama serving dinta ta tashi zata fita, Hajiya ta ajiye cup en pap tace "Khadijah...", Mami ta juyo tace "Na'am Hajiya", Hajiya tace "naga jikin ƴar taki da sauƙi toh shine nace me zai hana yau su tattara su koma gidansu..", Mami tace "Eh Alhmdllh ta samu sauqi sosai, amma dai bata gama shan drugs dinta ba, da sai nan da sati mai zuwa sai a mayar da ita ɗakinta lokacin insha Allah ta gama shan drugs en, amma yadda kika ce ai haka za ai Hajiya", Hajiya ta rausayar da kai tana cin ƙosai tace "ai shknn tinda kin kawo batun magani, shima mijin naki haka yace sai sati mai zuwa da yake bakinku ɗaya". kwanan Hajar hudu a gidansu Nurain, tin ranar da suka je wajen Hajiya bata sake fita daga part en Mami ba, everytime tana ɗakin da aka ajiyeta, tana dai fita palourn Mami ta gaisheta sai kuma ta koma ɗaki, Sosai suka saba da Noor sbd tare suke kwana, da rana kuma ta zauna ita kadai idan Noor ta tafi schl, ƙarfe biyar da minti huɗu Noor ta shiga ɗakin da Hajar take, dawowarta daga schl knn, wanka kawai tayi ta canza kaya, Noor tayi murmushi tace "masha Allah, waoh gsky kayan nan sun miki kyau", Hajar ta dubi kanta, straight skirt ne na english wears da shirt dinsa masu kyau, Noor din ce ta kawo mata su tinda daman kayanta take sawa, duk yawancin kayan da ta bata ƙanana ne amma decent, don Noor ta fi son su sbd tafi zama comfortable dasu, Noor ta ringa yaba kyan Hajar da kayan, sun fi yiwa Hajar din ma kyau don ita data saka sau ɗaya basu mata kyan haka ba, Hajar tayi murmushi tace "an dawo schl lfy?", Noor tace "lfy alhmdllh, za kici Noodles?'', Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh zan ci", daman kaɗan taci lunch da aka kawo mata, Noor tace "Ohk, let's prepare it together", Hajar tace "together?", Noor tace "yhap", ƙin yarda Hajar tayi wai ita bazata fita ba, daga ƙarshe ma tace ta ƙoshi, da kyar Noor tayi convincing dinta ta yarda, zumbulelan Hijab din da take sallah ta kirma, Noor ta bita da kallo tace "keda zaki kitchen meye kuma na saka hijab", Hajar tace "in ba dashi ba na fasa zuwa", tare suka fito main palour suka shiga huge luxury kitchen din gidan mai shegen kyau, kitchen island ma wani irin makeke, ga cupboards da drawers suma manya wanda suka zagaye girman kitchen din, Noor ta ɗakko pot kafin ta fara harhaɗo ingredients, Hajar daga gefe ta tsaya tana kallonta, within 15mins Noor ta gama dafa wata shaɗananniyar Noodles, ga fried egg with sausage, A babban plate ta juyo musu, Noor ta buɗe fridge ta ɗakko lemon kwali da ruwa ta bawa Hajar ta riƙe musu ita kuma ta ɗakko plate en Noodles en, a Main palour suka zauna wanda Hajar ba taso hakan ba, Still Hajar tayi tana kallon Noor ganin abinda ta ajiye musu a maimakon fork, Hajar ta ringa kallon tsinkayen tace "meye kuma wnn?", Noor ta ɗauki chopsticks din ta fara ci dashi, sosai ta iya amfani da Chopsticks, saida Noor taci loma uku amma Hajar ko attempting ɗaukar sticks en ma ba tay ba, Noor tace "ya naga ba kya ci?", Hajar ta ɗauki Chopsticks en gabanta ta fara ƙoƙarin ɗebo Noodles din, daga ta ɗiba sai ta zame, Noor ta ringa mata dariya kafin ta tashi ta shiga kitchen ta ɗakko mata fork, Hajar tace "tayi daɗi sosai", Noor tace "really, da fatan dai kin riƙe recipe din cause it's one of yaya Nurain's favorite", suna gama ci Hajar ta ɗauki plate din ta shiga kitchen dashi, Noor ta juya tana kallon stairs jin footsteps, tini ta ajiye cup din lemon da take sha ta tashi da sauri ta ruga ɗakinta, tsoron haɗuwarsu take sbd wata red cancel ya turo mata akan project dinta da ta tura masa hakan yana nufin shirme tayi kenan, gashi yace sai yayi punishing dinta idan shirme tayi, shiyasa take avoiding dinsa kar ya kamata, Nurain ya ƙarasa sakkowa downstairs yana kallon ƙofar part din Mami, kitchen ya nufa da cup din Coffee da ya gama sha, yana shirin murɗa handle kawai yaji an murɗa ta ciki kafin aka buɗe ƙofar, kanta a ƙasa tana tattare ƙasan hijab dinta da yake sharar floor, ji tay tayi karo da abu, ta ja baya da sauri ta ɗago kanta, girarsa a matuƙar haɗe yake kallonta, Hajar ta zuba masa lulu eyes dinta zuciyarta na bugawa, ita tsorata ma tayi shiyasa take masa wnn kallon, da sauri ta janye idonta tabi ta gefensa zata wuce tinda akwai space sosai da yake ƙofar babba ce, ( mu bawa juna haƙuri daii ) shine abinda ya amsa a brain din Nurain within 1sec, this time around din ma junan zasu bawa haƙuri ko kuma ita zata basa, hannu yasa ya fixgota baya ya mayar da ita kitchen din, yace "kee are you mad?, dutse kika bige ne?..", Hajar ta yamutsa fuska tace "wa ya sani ko dutsen ne".......✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {41..} Nurain was more than shocked jin abinda ta faɗa, wnn ƴar kucular yarinyar ce zata gaya masa haka, nawa take a wajensa, with hatred yake kallonta, itama Hajar da hatred din take kallonsa har wani zugii take ji a zuciyarta, da mugun sauri ta sake kewayesa zata wuce, hijab dinta ya taɗeta saura ƙiris ta baje a ƙasa tayi saurin dafa handle, a fusace Nurain ya juyo da nufi koya mata hankali, a ransa ya ji dama faɗuwar tayi ta dauje guiwa, Mami da ta fito daga part din Abba a daidai lokacin da Hajar ta taɗe snn kuma lokacin da Nurain ya juyo a fusace sai taga kamar Nurain din ne ya hankaɗota, Hajar da bata lura da presence din Mami a palour ba tayi sauri ta zagaya ta bayan kujeru ta shiga part din Mami, Mami ta bita da kallo kafin ta fara tafiya towards Nurain daya daskare a tsaye, tace "daman ka na gidan nan Nurain..?", don gaba ɗaya ya ƙauracewa part dinta, kwana biyar knn bai shiga part en ba, saidai ya gaisheta a main palour ko kuma part en Abba idan sun haɗu a can, Nurain yace "yeah, shirye shiryen kowama work nake so am busy in my room.." da haka ya shige kitchen, Mami ta bisa cikin kitchen din, ya ajiye cup din dake hannunsa a sink yana sauke ajiyar zuciya, Mami tace "i saw what you did Nurain", ya juyo ya zuba mata idanunsa da kana gani kasan ransa a ɓace yake ba tare da yace komai ba don bai fahimci me take nufi ba, tace "why did you pushed her..?", Nurain was confused don brain dinsa ma ta kasa basa hadin kai yayi thinking, bai ma san me zai ce ba sbd bai gane me take cewa ba, da kyar ya samu kansa da cewa "Mami i don't get you", sosai ran Mami ya fara ɓaci kawai ta juya tabar kitchen din. Hajar na shiga ɗakin da take ta kafa goshinta a bango tana jin suya a ƙahon zuciyarta, hawaye ne suka fara bin cheeks dinta kafin ta fashe da kuka gaba ɗaya, a haka Mami ta shigo ɗakin ta tarar da ita, har harɗewa ƙafafuwan Mami suke ta iso wajenta ta riƙe both shoulders dinta tana tambayarta me ya faru, Hajar ta girgiza kai alamar ba komai tana ƙoƙarin danne kukan, Mami da hankalin ta ya tashi sosai tace "talk to me my dear what happened..?", kawai girgiza kai Hajar take taƙi tace komai, gashi kuma ta kasa haɗiye kukan sbd zuciyarta a raunane take, da kyar Mami tayi consoling dinta duk da taƙi gaya mata damuwarta. Hajar ta shiga toilet ta wanke fuska ta fito, wani irin fige hijab ɗin jikinta tayi sbd ƙamshin Nurain da ta fahimci akwai ajiki, kodai hancinta ne ke jin hakan, tayi wurgi da hijab ɗin a tsakar ɗakin, ta juyar da kanta gefe tana kallon damtsenta inda ya rutsa ya fuzgota baya, cike da takaici tayi kwafa tace "Allah ya saka min da ka taɓa ni..." ★Maama ta saki tsintsiya da abin kwasar sharar da ta sharo uban dattin dakinta wanda ke ɗauke da mushen kuɗin cizo da aka zubawa piya piya daren jiya tana kallon ƙattin da suke shigowa da buhunhunan shinkafa, da catoon na spaghetti Macaroni da Indomie, ga kuma manya mayan jarkokin Mai biyu, Baba ne ya shigo yana nuna musu inda zasu ajiye kayan, har suka gama shigar da kayan ɗakin Baba Maama bata dena kallonsu ba, Nabilah ma dake zaune gaban murhu tana jefa ɗan wake sakin baki tay tana bin kayan abincin da ido, har kumfar ɗan waken da ta zuba a tukunya ta fara zuba bata sani ba, Baba ya sallami yaran da suka shigo da kayan kafin ya ja ƙofar ɗakin nasa ya saka mata kwaɗo, Maama ta washe yalayen haƙoranta tace "sannu da ƙoƙari mal, wnn irin uban kayan abinci haka, ai ma shekara muna ci wllh, Allah ya biya buƙatu ya bunƙasa hanyar nema, shine nace dama ba ɗakinka aka kai ba ga kitchen nan da ba a amfani dashi sai a ciro shirgin ciki a kai bola a zuba kayan abincin anan, kaga ba a ringa takura maka ba idan zamu ɗiba, wllh tllh dama a kitchen aka ajiye...", Baba dai kawai jinta yake, ta sake cewa "idan ka yarda yanzu sai na ci ɗammara na fara fiddo shirgin kitchen din, ina da ma piya piya saina feshe sa da shi gudun ƙananan ƙwari..", direct Baba yace "Ai ba namu bane garar Hajara ce", Maama ta zaro mici micin idanunta tamkar an kwantali ɗata tace "kam bala'i da masifa, me kake nufi mal, wai kanaso kace min wnn uban kayan Hajara za a kaiwa da sunan gara?", yace "Eh Rabii, kayan garar Hajara ne", Maama tayi wani murmushin takaici tace "wasa ma knn, nan da kake gani na ba karen hauka ne ya cijeni da zan zauna inaji ina gani a ɗebi kayan nan akaiwa Hajara ba, idan kai da matarka kun makance to ni garau nake, muna fama da yar Hausa Mai da yaji da tuwan dawa shine za a kwaso yar gwamnati da abincin kwali a kaiwa yar so ko, ni ban taɓa ganin inda ake haka ba wllh, ai wnn ƙarawa mai kuɗi ƙarfi ne, ce muku akay babu abinci a gidan nata ne, koda yake ashe baku je kunga gidan ƴan yankan kan ba..", Baba yace "sai kuma kiyi, gara dai sai an kai mata, babu ruwana da cewar masu kuɗi ne, mutuncin ƴata zan kare..", Maama ta fara fyace majina tana sharar kwalla don sosai maganar tayi mata ciwo tace "wllh Allah sai ya saka min nida ƴaƴana yadda ake mana cin kashi a gidan nan...", Baba ya haɗe rai yace "Da Hajara da su Maimuna duk ɗaya suke a wajena, idan kina ganin rashin adalci nake yi akan su to kwa kin yaudari kanki, dukka abinda na yiwa Hajara insha Allah irinsa zan maimaita idan Allah ya kawo lokacin auren su Maimuna" da haka ya barta a wajen ya matsa kusa da ɗakin Umma ya kirata, Umma ta amsa ta fito tace "gani mal", duk tana jin abinda ya faru daga ɗaki, Baba yace "Jamilah ce zata amso kayan zaƙin ko?", Umma tace "Eh, in Allah ya yarda ranar juma'a za a kawo", yace "yawwa gobe knn, zuwa ranar asabar ko lahadi sai a kai mata garar ta", Umma tace "toh Allah ya nuna mana da rai da lfy, Allah ya saka da alkhairy", yace "Ameen" ya fita daga gidan, Nabilah da take jefa ɗan wake ta ɗago kai ta dubi Maama tace "dan Allah Maama ki ringa ragawa Babanmu, nifa yanzu na zama ƴar ba ruwana wllh, idan ma bai mana irin na Hajara ba ai Allah na gani..", Maama ta rausayar da kai tace "idan bai muku ba ni zan muku da yardar Allah, kuma sai Allah ya kawo muku mazaje wanda suka kere dan yankan kan da waccar shegiyar ta aura, ai tin yanzu ma na fara gani tinda Alhaj ɗin Maimuna a Habuja yake, kinga kuwa ai yanada kuɗi". Umma na komawa ɗaki tayi dialing numbern Anty Jamilah, tana ɗagawa bayan sun gaisa Umma tace "Jamilah ya maganar mai dubulan da alkakin nan ne..?, da ƙarfe nawa zata bayar goben..?", Anty Jamilah tace "da safe tace wajen ƙarfe goma", Umma tace "tom, ga su shinkafa da taliyar har an kawo, kin san mal da karfin hali tinda yaji cewa ba a jerawa Hajara kayan ɗaki ba ya dage akan sai an mata gara, yace bazai bari mutumcin ƴarsa ya zube ba ace ba a kaita da ko tsinke ba, kuɗin kayan ɗakinta da aka siyar dasu yayi amfani wajen siyayyar garar snn kuma yace ragowar nata ne", Anty Jamilah tace "Alhmdllh, Allah ya saka da alkhairy, ai hakan shine dai dai wllh", Umma tace "wai ya ƴar taki kuwa? ni kam bana samun wayarta...", Anty Jamilah tace "nima haka Adda, ashe ma tana gidan su mijin, da naji bana samunta a waya shine na kira numbern wacca nake zaton kwanwar mother in law dinta ce wacca na amsa a wajenki ranar da muka dubota a hospital, shine fa take gayamin cewa ai Hajar na gidan surkanta", Umma tace "tofa ashe haka akay", daga haka sukay sallama. ★Da daddare da misalin tara da rabi, da ɗan sauri Nurain yake sakkowa daga stairs ya zura right hand dinsa a pocket na dark brown sweat pant dake jikinsa, left hand din kuma yana shafa tsakiyar cikakkiyar sumar kansa, hanyar part din Abba ya nufa, ya murɗa door handle na great room din kafin ya shiga da sallama, ya cire soft room slippers dinsa ya ƙarasa ciki, har zai zauna kan carpet Abba ya nuna masa sofa don haka ya zauna a sofar, Mami ta gama zubawa Abba Moringa tea ta miƙa masa, ya amsa yana murmushi yace "thank you..", tace "ur welcome dear..", Mami ta ɗago sukay ido huɗu da Nurain, ɗauke kanta tayi ta tashi ta shiga bedroom din Abba, Abba ya ɗauki tean yayi sipping, sip uku yayi snn ya ajiye Mug din, ya rage volume din TV, Abba ya dubi Nurain da yake jiran kiran da ake masa yace "ya project din Mamana tace ta turo maka zaka duba mata...?", Nurain yace "Yeah she try", Abba ya gyaɗa kai yace "good", after like 5secs Abba ya nisa yace "Uthmaan kasan me yasa na kiraka nan..?", Nurain dai kawai kallon Abba yake ya girgiza kai yace "A'a..", Abba yace "lokacin da Allah ya yiwa first wife dina rasuwa the mother of Sakeena, Sakeena was just 3months old lokacin da mamanta ta rasu, duk wanda yaga Sakeena sai yaji tausayinta sosai, dangin mahaifiyarta sun so su amsheta su riƙeta ni kuma nace bazan basu ba sbd tana ɗebemin kewar mahaifiyarta, a koda yaushe Sakeena na wajena sai idan zan fita aiki ne nake kaita wajen Hajiya idan na taso kuma na ɗakkota mu koma gida, Hajiya tayi min mgna akan na ƙara aure amma ni kuma sam aure ya fita a raina, a haka har Sakeena ta cika wata bakwai a lokacin ne kuma na tafi Abuja wani aiki", Abba yayi murmushin manya snn ya cigaba da magana yace "ai sai dawowa nayi daga Abuja na tarar da gidana a buɗe an kawo min mata, aikin Hajiya ne, itace ta shiga ta fita ta haɗa aurena da Maminku tinda ƴar Aminiyarta ce, Hajiya tayi kicin kicin ta ɗaure fuska da ta ganni kawai warkajaminta take, ban kai ga mata magana ba tace min ai Uwa ta yiwa Sakeena, ai kam dai Hajiya gave Sakeena the best Mother ever domin kuwa hannu bibbiyu Mami ta riƙeta tamkar ƴar cikinta, ni kuma Allah ya musanya min ita da Marigayiyar mata ta, sosai na samu peace of mind wllh, your Mother is a good woman..", Abba ya dakata yana sauke ajiyar zuciya yace "kaga biyayyar da nayi ma Hajiya a tashar da ta ajiyeni, nine na kasance a farin ciki da kwanciyar hankali, don good wife ita ke riƙon gida ba kuɗi da kyale kyale ba, kasan me yasa na baka brief storyn nan??", Nurain yace "No Father", Abba yace "sbd kaima ka shiga irin halin da na shiga Son, saidai nawa da naka akwai bambancin amma kuma suna kamanceceniya, hankalinka da nutsuwarka da sanin kai din waye da kuma iko yasa na aura maka yarinyar nan", nan Abba ya shiga labarta masa yadda komai ya wanzu har ya aura masa Hajar, Abba yayi sipping tea yace "ina da babban hope akanka Son shiyasa na tafi kai tsaye na amso maka auren yarinyar nan, amma look at what happened you are trying to do something da ban taɓa tsammani ba, Uthmaan wllh da nasan za kace sakin yarinyar nan za kai bazan aura maka ita ba, wai ni nan gata na gwada maka snn kuma na haɗa da taimako, ranar nan da Hajiya tace a bar maganar saki kawai shiru nayi sbd bana so ranta ya ɓaci, amma yanxu mu ɗora daga inda muka tsaya Uthman, ka amince zaka zauna da yarinyar ko kuma kana kan bakarka na sakinta...?", Nurain ya ɗago kansa yana kallon Abba ya kasa cewa komai, ya shafa kansa har yanzu baice komai ba, Abba ya ƙura masa ido yana jiran amsa, Nurain ya kalli fuskar Abba kafin ya runtse idonsa ya buɗesu, a lokaci ƙanƙani suka rune, da kyar ya motsa peach lips dinsa maganar ma bata fita sosai yace "Abba na amince zan zauna da ita..", Abba yayi ajiyar zuciya yace "Allah yayi maka albarka, zaka iya aurar wacca kake so a ko wani lokaci, zaka girbi iri mai kyau for your obedient", Nurain dai ya dena fahimta sakamako tsittsinkewar da zuciyarsa take, Abba yace "toh yaushe zaka ɗauki matarka ku koma gida...?", Nurain da throat dinsa ya bushe yace "i think on Saturday insha Allah...", Abba yace "jibi knn?", Nurain yace "Yeah", Abba ya gyaɗa kai ya cigaba da sipping tea, Nurain ya miƙe yana jan farar T-shirt dake jikinsa yace "can i excuse myself", Abba yace "sure", Nurain ya masa saida safe ya nufi ƙofa, room slippers dinsa ya zura zai fita Abba yace "gobe in Allah ya kaimu zamu fita bayan sallar Juma'a", Nurain yace "Ohk" da haka ya buɗe ƙofar ya fita Abba ya bisa da kallo, Mami ta fito daga bedroom din Abba ta zauna side dinsa ta dafa hannunsa tace "hakan ai yafi gwara musan road din da zamu bi kafin abu ya tabarbare...", yace "haka ne, All thanks to you Mami". ★Washe gari da ta kasance juma'a, ƙarfe sha biyu Nurain ya fito huge compound din gidansu ya isa parking spaces, ya buɗe motarsa da ya fita da ita jiya da yamma ya shiga, wayarsa dake kan dashboard ya ƙurawa ido, gaba ɗaya ya dena amfani da ita saidai yayi using Mac phone, haka yake baya son takura, ya kwantar da hand brake ya tada motar, after warming for few minutes yaja motar ya fita daga gidan, tunani iri iri ke kawowa brain dinsa amma sai ya kawar dasu ta hanyar bin karatun Alkur'ani dake tashi a motar, wayarsa ce ta fara ringing, da kamar bazai ɗauka ba sai kuma yabi gefen titi ya ɗauki wayar ya duba wake kiransa, Farooq ne, Nurain ya saka wayar a handsfree ya cigaba da driving slowly, complain Farooq ya fara masa akan baya ɗaga wayarsa, Nurain yace "Hey punk nafa gaya maka ka dena kira idan zaka ajiye mail da yafi maka", Farooq yace "i won't, kira naga dama", Nurain ya ɗaga kafaɗa yace "Alright..", Farooq yace "ni idan ba ma iron lady da ta takura na kiraka ba me zaisa na kira unavailable person", Nurain yayi murmushi yace "kai har kayi mgana anan punk..", Farooq yace "are you coming daman iron lady ce take son ganinka..?", a hankali Nurain yace "yeah, idan na dawo daga mosque zan shigo", Farooq yace "fine" da hka ya katse wayarsa, saida Nurain yaje masallacin da ya saba zuwa sallar Juma'a snn ya wuce gidansu Farooq, suka gaisa da Ummi kafin ya wuce part din Hajiya, bai jima da zama ba saiga drink da ruwa Aysha ta shigo masa dasu harda abinci, Aysha ta tashi zata fita Hajiya tace "tin ɗazu nake fama dake Shatu akan ki shafamin man zafi a saman makyangyama amma kinyi burus dani, jifa yadda ƙafafuwan suka sussuntuma sai kace an buga musu iska, da kyar na iya yin sallah fa", Aysha tayi fuskar mage tace "iron lady, ina zuwa yanzu zan dawo, kinga abinci nake kawowa yaya ai bai kamata na taɓa man zafi ba", Hajiya ta ɗaga kai sama tana kallon Nurain ta ƙasan glasses tace "ke da Allah rabu dashi kizo ki shafamin mai na, yo ina ruwanki dashi shi da yake da aure, zukumin cikinsa na wajen matarsa, kai matar Usuman yar aljanna ce yarinyar nan, wllh ta iya shafa man zafi, tinda nake ba a taɓa shafamin wanda naji daɗinsa kamar nata ba, ni idan ma naga ina ƙoƙarin rasa ƙafafuwan babu abinda zai hanani tarewa gidan Usuman..", Nurain dai kawai latsa wayarsa yake like he was not existed there, sai a lokacin yace "toh taso mu tafi", Hajiya tace "mu tafi ina kuma, ai cewa nayi sai naga ina ƙoƙarin rasa ƙafafuwan...", Nurain ya miƙe tsaye yana kallon hajiya yace "na tafi, idan Farooq ya dawo masallaci kuce masa na tafi", Aysha tace "Yaya what about the food", ko amsa bai bata ba ya nufi door, Hajiya kam kasa magana tai sbd abinda ma ta kirasa ta gaya masa bata kai ga fada ba, da sauri Nurain ya shiga motarsa ya bar gidan, shaf ya manta cewa Abba yace zasu fita yau, hold off ne ya riƙesa a wani round about, almost 20mins hold off din bai ware ba, Nurain ya daki steering motar murya ƙasan throat yace "damn it", kiran Abba ne ya shigo wayarsa, yayi picking, Abba ya tambayesa whereabouts dinsa, yace hold off ne ya tsaresa bayan ya fito daga masallaci, Abba yace "Okay, ni na riga na wuca ma amma zan turo maka inda zaka sameni sai ka tafi can din", Nurain yace "Aha". Nurain ya buɗe google map a wayarsa yana bin direction din da zai kaisa unguwar da Abba ke jiransa bayan ya samu ya fito daga hold off din, ya ringa kallon screen ɗin wayar ganin inda arrorn map din ke masa pointing, ya ɗago kansa yana kallon street din a zahiri wanda ya karya kwanarsa yanxu, street din ba baƙonsa bane kuma zamm ya ganesa tinda ya ajiye memory a nan din, Slowly yake driving a street din sbd ruɓewar kwalta da kuma shagiɗaɗɗun jakin baban gida, opposite inda Incidence din memoryn sa ya faru yaga motar Abba, drivern Abba ya fito yana ɗaga masa hannu, Nurain ya samu gefe yayi parking motar ya buɗe ya fito, koda ya fito sai ya tsaya yana kallon daidai wajen da motarsa ta taɓa ruftawa, anan ne kuma first encounter dinsa da mara kunyar yarinyar nan wacca a yanxu ta amsa sunan matarsa.....✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh_feeche {42..} Tsallaka titin Nurain yayi ya isa wajen Motar Abba, driver ya buɗewa Abba motar ya fito, Abba ya ringa kallon Nurain da ya ƙurawa street din ido yace "wajen mahaifin Hajar na kawoka ka gaishesa, ya kamata ya sanka..", Nurain ya kare hasken rana da yake haske masa ido yana tunanin wace ce kuma Hajar, sunan ya ringa yawo a brain dinsa amma ya kasa gane wace, ganin bai fahimta ba Abba yace "your wife, ko baka san sunanta ba..?", Calmly Nurain yace "Ohk, amm nan ne unguwar...?", Abba yace "yess, ga layin gidan can" ya nuna kwarɓaɓɓen lungun gidansu Hajar, with disgusting look Nurain ya kalli layin, how mutane suka rayuwa a nan wajen, Abba ya ciro wayarsa daga pocket yayi making call na minti biyu, yana gama wayar yace "muje" da haka ya fara tafiya ya shiga layin, Nurain yabi bayansa, Nurain dai kawai bin Abba yake suna surƙumawa cikin lungun, wani irin nisa yaga tafiyar ta masa duk da cewa gidan bashi da nisa da titi, Abba ya tsaya a daidai ƙofar gidan, Baba da already yana soro ya fito waje sukay musabaha da Abba, Baba yace "Bismillah", Abba ya bisa suka shiga soron gidan ya zauna kan tabarma da ke shimfiɗe a soron, saida Nurain ya rage tsaho snn ya shiga, ya zauna daga gefe yana kallon Baba yace "barka da rana", da fara'a Baba ya amsa, Abba yayi murmushi yace "he is my second born Uthman, dashi aka ɗaura auren...", Baba yayi ajiyar zuciya yana kallon Nurain yace "masha Allah..", Nurain ya ɗaga kansa yana kallon roof din soron wanda spider web ta cikasa har tana zazzagowa, Abba da Baba sai taɗinsu suke, past dinsu suke tunawa suna mgana akai, after 5mins Nurain ya duba agogon wrist dinsa, Abba ya dubesa ta gefen ido kafin yace "Nurain you can go idan Kanada wani appointment din", cike da girmamawa Nurain ya yiwa Baba sallama kafin ya tashi ya bar soron, Nurain na fita daga lungun ya ciro handkerchief ya goge fuskarsa, titi ya tsallaka ya shiga motarsa, zaune yayi cikin motar bayan ya kunna ya ware Ac, So a nan Abba ya masa aure, Ghetto area, shi ba wnn ne damuwarsa ba ma, bayan ƴar Ghetto da aka aura masa kuma mara manners, da reverse ya fita daga street din, yana hawa main road ya take accelerator, hanyar gidansa ya ɗiba, few minutes ya isa unguwar duk da cewa akwai nisa cause ya take motar ba ƙarya, a ƙofar gida yayi parking ya fito, Garba dake tsaye bakin gate tare da wani mutumi ya taso yana yiwa Nurain barka da zuwa, Nurain ya amsa yana kallon mutumin dake tare da Garba, Garba ya dubi mutumin yace "ga uban gidan nawa fa..", da sauri mutumin ya russuna yace "barka da zuwa Alhj..", Nurain yace "an yini lfy...?", mutumin yace "lfy alhmdllh an gode Allah...", Nurain na kallon Garba yace "shine ko?", Garba ya shafa kai yana ɗan russunawa yace "Eh alhj ƙarami, shine wllh, ɗan uwa na ne na jini, da Babansa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya..", Nurain ya jinjina kai yace "Ohk, hakan yayi" da haka ya ƙarasa bakin gate din ya buɗe, ya koma cikin motar Garba ya zuge masa gate ya shigar da ita huge parking space dake gidan nasa, saida Garba ya bari mutumin da suke tare ya shigo snn ya mayar da gate din ya rufe, Nurain ya fito daga mota bayan ya gama parking, ya ringa kallon compound din, kiran Garba yayi wanda ya taho da sauri, Nurain yace "ka gaya masa aikinsa ko?", Garba yace "Eh na gaya masa komai, gadi da bar ruwan shuka sai share tsakar gida", Nurain yace "Yawwa, kira min shi", Garba ya tafi ya kira mutumin suka taho tare, Nurain yace "Garba ya maka bayani ai", mutumin kansa a ƙasa yace "Eh alhj..", Nurain yace "yawwa, bar ruwan shuka da share tsakar gida na wani lokacin ne kafin a samu me yi naka dai shine gadi", mutumin yace "insha Allah komai bazai gagara ba..", Nurain ya gyaɗa kai yace "suna fa..?", mutumin yace "Inuwa..", Nurain ya jinjina kai kafin ya wuce ya bar wajen ya nufi main entrance din shiga gidan. Garba ya dashe haƙora yace "Allah kuwa Inuwa ka kwashi dami a akala don wllh tllh kirki dai a wajen bawan Allahn nan har ya masa yawa, ni dai na gaya maka ka zama mai gsky da amana, idan ka riƙesa da kyau tabbas zaka samu alkhairy bana wasa ba, wllh don ma dai kai ne amma in ba haka ba wani huhulahun zan nemawa wnn gangariyar aiki...", Inuwa yayi murmushi har cikin ransa yaji daɗi yace "ai Allah ne zai biyaka Garbati da wnn taimako da ka min", Garba yace "wnn fa aikin nawa ne na sadaukar maka..", Inuwa yace "ai shiyasa nake ta gode maka...", bayan minti sha biyu Nurain ya fito bayan ya rufe ko ina, keys guda biyu ya bawa Inuwa yace "key din ɗakinka ne da kuma gate, gobe da safe saika zo kayi abinda za kai ka buɗe ɗakinka, amma yau dai ka tsaya tare da Garba", hannu biyu Inuwa yasa ya amshi keys din, Garba ne ya masa nuni da ɗakin nasa wanda ke kusa da gate, Nurain ya ciro kuɗi daga pocket ya bawa Garba yace "saiku koma can gidan..", godiya Garba yayi masa sosai. sai bayan Sallahr la'asar wajen ƙarfe biyar snn Nurain ya koma gida, don sai yau ne ya samu yaje wuraren da yake son zuwa tin dawowarsa 9ja. ★Hajar ta saka Hijab dinta tabi bayan Noor data isar mata da saƙon kiran da Mami ke mata, Mami na zaune palourn ta tare da Tailor wacca ta saba musu ɗinki, Noor ta koma inda ta tashi ta cigaba da latsa wayarta, Hajar ta zauna kan carpet tace "gani", Mami ta dubi Tailorn tace "ga mai kayan nan", Tailorn tace "Okay tom bari na aunata..", bai ɗauketa wani lokaci ba ta gama auna Hajar tass, Mami tace "gobe fa nake son kayan nan Salmah", Salmah tayi murmushi tace "Mami kar kiji komai insha Allah gobe sha biyu na rana a gidan nan zata yiwa kayan nan..", Mami tace "toh Allah yasa", Salmah ta yafa mayafin Abayarta, ta ɗauki wata Babban leda dake kusa da ita tace "toh Mami na wuce, Noor sai anjima..", Noor ta ɗago kanta daga kallon waya tace "da wuri haka...", Salmah tace "gwara na tafi yanzu na fara aiki, bana so naƙi cikawa Mami alƙawari", Mami tace "dan kwa faɗa zanyi wllh idan kayan nan basu samu gobe da wuri ba", Salmah tace "insha Allah baza aji kanmu ba Mami.." da haka ta musu sallama ta tafi, Hajar bata koma ɗaki ba tayi zamanta anan, buɗe ƙofa akay Nurain ya shigo, hannunsa riƙe da handle ya ƙarewa ɗakin kallo, har yayi wanka ya canza kayan jikinsa daga manya zuwa ƙanana da yke zaman gida dasu, wani irin zaro ido Noor tayi ganinsa unexpected, da sauri ta kara wayarta a kunne ta fara wayar ƙarya, ta tashi zata shige bedroom din Mami, ƙarasa shigowa palourn yayi yace "idan kika shiga har nan zan biyoki na zaneki", Noor ta yarfe hannunta tace "yaya ka tsaya kaji don Allah...", yatsansa ya ɗora a lips yace "shhhh na tambayeki ne...?" ya samu Sofa ya zauna, yana zama Hajar ta miƙe ta nufi hayar ɗakin da take, Mami ta kirata tace "ina zaki...?", Hajar ta juyo a hankali tace "ciki zan koma..", Mami tace "dawo ki zauna nifa na kiraki kuma bance ki tafi ba..", ba yadda Hajar ta iya haka ta dawo ta zauna, koda wasa bata dubi position din da Nurain yake ba, shima tinda ya kalli inda tke sau ɗaya bai sake kallon wajen ba, Nurain ya dubi Noor da tay tsaye sai wurwurga idanu take, murya ƙasan maƙoshi yace "je ki kawomin abinci, surely we will meet later..", a ɗarare Noor tace "tom", har ta kai bakin ƙofa Mami ta kirata, ta dawo da baya tana kallon Mami, Mami tace "je ki kunna burners ki zuba turaren wuta..", Noor ta dubi Nurain kafin tace "tom" ta dawo ta shiga bedroom din Mami, Mami ta kalli Hajar da ta zubawa Tv ido, kawai Tv take kallo duk da ba wani abun arziƙi ake haskawa ba amma ta gwammace ta kalli Tv sbd kar idonta yaje inda zuciyarta zata sosu, Mami tace "Hajar..", Hajar ta kalli Mami tace "Na'am", Mami tace "tashi kije kitchen za kiga wasu silver warmers guda uku akan cabinet ki ɗakko min su, idan kin kawo sai ki koma ki ɗakko min ruwa da drink a fridge", Hajar tace "tom" ta tashi ta fita daga palourn, Nurain yayi kamar baiji me Mami ta faɗa ba ya fara duba Mac phone, Mami dake kallonsa tace "misplacing phone dinka kayi ne..?", yace "A'a, a ɗaki na barta", Mami tace "alright then", Hajar ta shigo da tray a hannunta mai ɗauke da warmers, ta ajiye nan kan carpet kafin ta juya ta sake fita, babu jiwa ta dawo da wani tray din na ruwa da lemo da Cup da kuma plate with spoon, ta ajiye kusa da warmers din, a hankali tace "zan koma ciki", ba ta bari ta kalli Mami ba ta faɗi hakan, Mami tace "toh", Hajar ta tafi a hankali tana zuwa ƙofar ɗakin ta buɗe ta shige da sauri har dasu tuntuɓe, jingina tay da jikin ƙofar ta lumshe idanunta. Ganin har wajen minti talatin da ajiye masa abincin amma bai taɓa ba yasa Mami tace "Nurain ba Abincin zaka ci ba kasa aka kawo maka..?", ya ajiye Mac phone din a gefensa yace "A'a ni ba ci zanyi ba, i thought ke zaki ci ma", da mamaki Mami ta ringa kallonsa, after looking at him for few seconds tace "zuba abinci kaci malam", ya shafa kansa yace "nifa am full bance zanci ba", Mami ta haɗe gira tace "nace ka zuba abinci", bai sake mata musu ba ya ɗebi abincin kaɗan wanda bai wuce loma biyar ba, duk da irin yunwar da yake ji amma samm yaji baya sha'awar abincin, gaba ɗaya ya fitar masa a raii, ya ringa juya spoon ɗin hannunsa, Mami dai ta ringa kallonsa ta gefen ido har ya gama caccakar abincin wanda ko kusa da baki be kai ba ya ajiye, ruwa da lemon ma bai sha ba haka ya tashi ya fita, Mami ta bisa da kallo, girgiza kai tayi a ranta tana addu'ar Allah yasa dai wnn abu mai ɗorewa ne kar ya zama fitina. washe gari wani irin odd Hajar ta ringa jin kanta, tinda aka kawota gidan yau ne ta wayi gari taji hakan, ita ba mai rashin lfy ba kuma bazata kira kanta da mai lfy kai tsaye ba, breakfast da aka kawo mata ma kaɗan taci, Noor ma saida ta tambayeta lafiyar ta kuwa sbd sauyin nata, Hajar tace "bacci ne bai isheni ba inajin", Noor tace "toh ki koma ki kwanta kawai..", Kwanciyar da Hajar tayi sam bata samu bacci ko na 1sec ba, kawai juye juye ta ringa yi sai kace ƙadondoniya, wajen ɗaya saura ta tashi ta shiga bathroom ta ɗora alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ta sake kwanciya, kamar wasa sai bacci ya ɗauketa, ba ita ta farka ba sai daf da sallahr la'asar, Noor ce ta shigo ganin ta farka ta fita a ɗakin, babu jimawa sai gata ta dawo tare da Mami, Noor ta ajiye kayan da suke hannunta a gefen bed kafin ta juya ta fita, Mami tace "har kin tashi dear..?", Hajar ta gyaɗa, Mami tace "Sallah za kiyi ne..", Hajar tace "Eh", Mami tace "idan kinyi Sallahr sai kiyi wanka ki saka waɗan nan kayan kinji", Hajar tayi shiru tana kallon kayan dake gefen gado kafin ta gyaɗa kai tace "tom", saida tayi sallah taci Lunch da Noor ta kawo mata snn ta shiga wanka kamar yadda Mami tace tayi, ta fito ɗaure da towel ta zumbula hijab, mai ta shafa kafin ta dawo gefen gadon ta zauna ta fara warware gogaggun kayan, wani sassanyan ƙamshi ne yake tashi daga jikinsu, Atampa ce mai laushin gaske kai kana ganinta kasan mai tsada ce, Hajar ta ringa shafa kayan kafin dai ta warware ta saka a jikinta, sosai sukay mata kyau dass dass, riga da skirt sosai yake fito da ainahin shafe dinta, ɗan kwali da mayafi sai pendant necklace da ear rings ne kawai bata saka ba, da sauri ta fara ƙoƙarin rufe kanta ganin Mami ta shigo, ɗan kwalin ta yafa a kanta ta rufe gashinta, Mami ta zauna gefen gadon itama ta riƙo hannunta tace "Yau kuma sai gidanki insha Allah", wani darammm Hajar taji a ƙirjinta, Mami tace "Allah yayi miki albarka tare da zaman lafiya madauwami, maza ki ƙarasa shiriyawa...", hawayen da suka cika idanunta suka fara zarya bisa kuncinta wanda bata shiryawa hakan ba, Mami that was very surprised da ganin tears ɗinta tace "what happened Hajar...?, akwai abinda yake damunki..?", Hajar tasa bayan hannu ta goge hawayen ta girgiza kai a hankali tace "A'a, kawai dai ni bansan waye wanda aka aura min ba, ni dai nasan Baba na yace yamin aure amma ban san waye ya aura min ba..", ta fara kuka a hankali, Mami tayi ajiyar zuciya ta tausasa murya tace "dear he is my son wanda aka aura miki, yayan Noor ai kin ganesa ko", Hajar na kallon Mami da jajayen eyes ɗinta ta gyaɗa kai, knn dai shi ɗin ne ko, Mami tace "Stop crying kinji, he will not harm you i promise..", Hajar dai ta rasa a wani position zata ajiye zuciyarta don ji take tamkar an tsireta da tsinken tsire ana gasawa a tukuba, Noor ce ta shigo, ganin yadda idanun Hajar suka kumbura tace "subhanallah kuka kike..", Mami ta tashi tace "she is not, gyara mata fuskarta ina zuwa" da haka ta buɗe ƙofa ta fita, Noor ta saka mata ear rings da necklace snn ta mata ɗauri mai kyau, saida ta ɗauki kwalbar turare dake kan mirror ta sake baƙaƙa mata ajiki duk da irin ƙamshin da kayan suke, biyar da ƴan mintina Hajar na zaune main palourn tare da Noor, Mami ta fito daga part din Abba ta kama hannun Hajar suka shiga part din, 5minutes da shigarsu suka fito bayan Hajar ta gaida Abba, don daman bai taɓa ganinta ba sai yau. Mami na kallon Noor dake zaune main palour tace "Nurain din bai fito ba har yanzu..?", Noor tace "Eh bai sakko ba", Mami ta kalli stairs kafin ta wuce ta fara hawa, knocking door ɗin ɗakinsa tayi, ya buɗe ƙofar yana kallonta, tace "baka gama bane..?", yace "yanzu zan sauko" da haka ya mayar da ƙofarsa ya rufe, yayi ajiyar zuciya, ya ƙarasa buttoning rigarsa ya saka links, shi kaɗai yasan abinda yake ji a zuciyarsa kawai jurewa yake, down stairs ya sauka bayan ya kulle ɗakin nasa, part din Abba ya shiga ya masa sallama, ya yiwa Mami ma dake zaune main palour daga haka ya fita compound, packing space ya isa ya buɗe motarsa ya shiga, Noor riƙe da tagomishin kayan arziƙin da Mami ta haɗawa Hajar na turaruka ta fita compound, Noor ta saka turarukan a back seat, ta dawo ta riƙe hannun Hajar zuwa wajen motar, front seat ta buɗe mata, a hankali Hajar ta shiga motar, Noor tace "sai nazo sister" da haka ta rufe motar taja baya, Nurain ya ƙurawa steering ido bai bari ya kalli inda take ba, saida ya gama warming motar snn ya fara driving a hankali ya fita daga gidan, tinda suka hau babban titi Hajar ta juyar da kanta side glass din ƙofa kawai kallon waje take, sanyin Ac ya ringa shigarta ga kuma abinda yafi tsaya mata a maƙogoro scent dinsa, ita dai bata san ma ina suka bi ba kawai gani tai sun tsaya a bakin gate ɗin wani katafaren gida, Nurain ya danna horn, mai gadi ya buɗe gate da sauri, Nurain ya parker motar a parking space kafin ya kashe ya zare key daga Ignition, buɗe murfin motar yayi ya fita, a hankali Hajar ta buɗe motar ta fito, ya buɗe back seat ya ciro ledar da Noor ta ajiye ya rufe motarsa, dire ledar yayi nan bakin motar yayi wucewarsa ciki, a karo na farko data ɗaga kai ta kallesa, ta taɓe baki ta sunkuya ta ɗauki ledar tayi hanyar da ta ga yabi, tsaye tayi bayan ta shiga palour, ta ajiye ledar hannunta, ta ƙarewa palourn kallo tass, direct Nurain upstairs ya haura ya shiga ɗakinsa bayan ya kunna Solar, trolleyn kayansa tin wacca ya kawo last week ya buɗe, arranging kayan ciki ya fara yi awajen da yake so, duk yawanci ma kayan aikinsa ne aciki ba sutura ba don on Monday yake da shirin rusuming work, yana gama arranging kayan yaji ana kiran sallah, huge bathroom dinsa ya shiga yayo alwala, da sauri ya gama ya fito, fita yayi ya sauka down stairs, Hajar na rakuɓe daga bayan kujera har ta gaji da tsayuwa ta samu guri ta zauna, kallo ɗaya yayi mata ya fita zuwa masallaci wanda akwai tazara kaɗan tsakaninsa da gidan, Hajar ta miƙe tsaye tana tunanin ina ne alqibla don da alwalarta sallah kawai za tay, kallon stairs tai wani tunani yazo mata, bayan ta gane gabas tayi sallar ta, har sallar isha'i Nurain yayi kafin ya dawo gida wajen takwas da ƴan mintina, muƙullin motarsa ya ɗauka ya fita, eatery ya fita ya siyo abinci ya dawo, wai yau shine da siyar abinci a waje, abinda bai taɓa sha'awa ba knn, kan Centre table ya ajiye ledojin da ya shigo dasu kafin ya haura sama, Hajar da bacci ya fara kwasarta ba tama san ya shigo ba, Sha ɗaya da rabi ya sakko with Pajamas mai sweat pant, ledojin dake kan Centre table ya ɗauka ya bar guda ɗaya, har ya fara hawa stairs sai kuma ya dawo baya, tsayawa yayi yana kallonta, jingine take da kujera bacci yayi awan gaba da ita, maganar Abba ce tayi hitting brain dinsa, kallonta ma da yake wani maƙaƙi ya ringa ji a zuciyarsa, ya taka a hankali ya tsaya gaban kujerar da ta jingina da ita, kujerar ya bubbuga yace "hey"......✍️ Arewa book @feenerhfeeche02 💛 HAJAR 💛 by Feenerh feeche {43..} Saida ya sake buga kujerar snn ta motsa, daman ba wani daɗin baccin take ji ba, buɗe idanunta tayi, yana ganin haka ya bada distance a tsakaninsu yace "hey, you better find a place to sleep, nan ba wajen bacci bane", ta buɗe idanunta tarwal ta mutsuttsukasu da hannu, taɓe baki tayi tace "what concern you da wajen dana kwanta..", ta mayar da kanta jikin kujerar ta lumshe ido, sake bubbuga kujerar yayi this time around da ƙarfi yace "you are not serious, ki tafi wani wajen malama amma banda nan", miƙewa tayi tsaye ta gyara yafen mayafinta, ledar data rage akan Centre table ya ɗauka yace "follow me...", ɗauke kanta tayi kamar ba taji me yace ba, yayi controlling tempern dake taso masa yace "i said follow me", ta sake juyar da kanta tayi folding both hands dinta tace "kayi mgana da yaren da zan gane..", yace "haka ne fa, ohk, duba da irin localityn da kika taso bai kamata a miki magana ta masu ilimi ba, cewa nayi ki biyo ni", bai jira cewarta ba ya fara hawa stairs, bin bayansa tay da kallo kafin ta haura saman, a daidai ƙofar ɗakin dake matsayin nata ya dakata, ya murɗa door handle ya buɗe, ajiye mata ledar yayi a gefenta ya koma ƙasa, ta yiwa ledar wani kallon hadarin kaji ta shiga ɗakin ta barta a nan, Nurain ya kashe duk bulbs dake kunne palourn, ya haura sama da ledar abincinsa a hannu, tsayawa yayi yana kallon ledar da ta bari inda ya ajiye, ya ɗaga kafaɗa ya wuce part ɗinsa, a palour ya zauna ya buɗe ledar, abinci ne mai rai da lafiya jollof rice da taji kayan lambu sai quartern kaza da soyayyen plaintain, spoon ya ɗauka ya ɗebi rice din ya kai baki, ajiye spoon din yayi yana kallon abincin, ya koma yayi resting da kujera don taste din bai masa ba, kwata kwata baya son abincin waje, rufe abincin yayi ya buɗe bottle water ya sha, daga ƙarshe dai ya tashi daga palourn ya shiga bedroom, ya rage hasken fitulu ya bar dim ta bedside, ya ɗauki Mac phone dinsa dake kan bedside ya kunna. Hajar ta gama ƙarewa ɗakin kallo kafin ta taɓe baki, da sauri ta isa gaban gado ganin handbag dinta, ta ɗauki handbag din ta buɗe, wayarta ta fara cirowa tana jujjuyata, kunnawa za tay taga ta mutu, acikin hand bag din ta zaro charge tayi plugging wayar a socket da ta gani a room din, zama tayi kusa da wayar har saida tayi 10% ta kunnata, bayan wayar ta gama booting taga missed call da yawa wanda sune ma suka sa wayar ta mutu tinda ba wani charge ne da ita ba lokacin da aka kawota gidan, call log ta shiga ta kira Ummanta, ba tama damu da dare yayi ba, don a lokacin sha biyu na dare ake magana, har kiran ya katse Umma bata ɗaga ba, Sake kira Hajar tayi, daf da kiran zai katse aka ɗaga, wani ajiyar zuciya Hajar ta saki tace "Umma na..", Umma ta tashi zaune don bacci take kiran wayar ya farkar da ita, Umma tace "Hajara..", tini hawaye ya ciko idanun Hajar tace "Na'am Umma", Umma tace "ina kika saka wayarki anata kira ba a samu..?", Hajar tace "a gida na barta kuma babu chaji..", Umma tace "Okay, toh ykk ya zaman sabon waje?", Hajar da already hawayen idonta sun fara tsiyaya tace "Ya Baba da Sabra da Yaya...?", Umma tace "kowa lfy alhmdllh..", Shiru Hajar tayi ba tace komai ba don wata ball ce ta tsaya mata a throat, jin tayi shiru Umma tace "ya jikin naki..?", da kyar tace "naji sauƙi sosai..", tayi shiru kafin tace "Umma..." sai kuma ta kasa cewa komai don ta rasa me zata ce, daga ƙarshe dai tace "Umma seda safe nasan ma kin fara bacci na tashe ki" da haka ta kashe wayar ta fashe da kuka, har cikin ƙasan zuciyarta bata san auren nan, saida taci kukan mai isarta har kanta ya fara ciwo, ta goge hawayen da ya jiƙa mata cheeks kafin ta tashi daga tiles da ta zauna, bathroom ta shiga ta wanke fuskarta ta fito, pillow ta ɗakko daga kan gado ta wurgar kan lallausan carpet dake room din, ta kware duvet din gado shima, tayi kwanciyarta kan carpet ta rufa har ka da duvet din don wani irin sanyi ne yake ratsata na Ac, har uku na dare idonta biyu ta kasa bacci sai juye juye take, babu kalar tunanin da ba tay ba a zuciyarta, sai wajen huɗu da ƴan mintina bacci ɓarawo ya kwasheta, alarm din wayarta ne ya tasheta wanda tintini take dashi wanda yake tashinta da asuba sbd ɓatan rana, kafin ma ya tasheta take tashi, da kyar ta yunƙura ta miƙe zaune ta dafe kanta sbd faskarawar da yayi, ta tashi ta kashe alarm din, a hankali ta fara jiyo kiraye kiaryen sallar asuba, ta dai samu ta daddafa ta shiga toilet tayo alwala tayi sallah, tana idar da sallah ta koma ta kwanta don da gaske kanta ciwo yake. Washe gari ƙarfe takwas da rabi na safe Nurain ya sauko down stairs da key din motarsa a hannunsa, saida ya rufe main door din shiga gidan kafin ya wuce parking spaces, Inuwa mai gadi da ke goge motar da soft duster ya gaishesa da ladabi, Nurain ya amsa yace "zan fita amma ba jimawa zanyi ba..", Inuwa yace "toh Alhj Allah ya tsare", Nurain yace "Ameen" ya buɗe motar ya shiga, da sauri Inuwa yaje ya buɗe gate, da reverse ya fitar da motar daga parking space kafin ya juyata ya fita daga gidan, Inuwa ya mayar da gate din ya rufe ya ɗauki watering can yana bawa flowers ruwa, Supermarket Nurain ya tafi, duk wani kayan abinci saida ya siya na tsaba da kuma masarufi, ruwa da lemo ma bai barsu ba saida ya siyo, har da perishable food ya siyo, sai 11 ya gama siyayyan ya wuce gida, yana parker motar ya zaga backyard ya buɗe wata glass door wacca zata kaika kitchen, ya shiga kitchen din, ya buɗe store dake cikin kitchen din, gas ya kunna wanda cylinder dinsa ke can bayan gidan anyi connecting pipes zuwa kitchen, ranar Thursday da yazo giran yasa aka masa refilling babar cylindern, daga haka kuma ya sake fita compound wajen motarsa ya buɗe booth, Inuwa ya saka ya ringa jigilar kai kayan da ya siyo yana libgewa a store, wanda za a ajiye a freezer kamar meat da chicken suma aka zuba a freezer, lemo da ruwa kuma a store aka ajiyesu bayan an zuba wasu a babban fridge dake kitchen din, a section na biyu na fridge din kuma aka zuba kayan miya, kitchen dai ya cika tsaf, bayan an gama shigar da komai Nurain ya buɗe cupboard ya ajiye Coffee powder da ya siyo ma kansa, daga haka ya buɗe ƙofar palour ya shiga, upstairs ya haura zuwa part dinsa, after like 10mins ya fito ya bar gidan mai gaba ɗaya a motarsa. ★Anty Jamilah ta yafa gyalenta tana kallon Umma tace "toh bari mu wuce kar muyi yamma tinda an gama fita da kayan", Umma tace "Amma kina ganin abin nan bazai zama gulma ba bafa wanda aka gayyata kai garar", Anty tace "babu gulmar da za ai wllh, toh Allah na tuba wanda ma yayi gulmar ai shi yaga zai iya yawunsa ne zai ƙafe a banza, yaushe aka gama bikin da zamu sake jajiɓowa kanmu jama'a wani kai gara, yarinya fa za a yiwa ba wani abun kallo bane, ai na ɗebar miki dubulan da Alkaki da gireba da chin chin saiki ƙuƙƙulla a leda a rabawa maƙota da abokan arziki", Umma tace "toh ai shknn, ince dai dangin mijin sun sani..?", Anty tace "mu dai namu kaiwa, ita Hajarar ta gaya musu da kanta..", Umma tace "hakan ma yayi", Anty ta miƙawa Hafsah dake zaune ɗakin hand bag dinta tace "tashi muje..", Hafsah ta amshi jakar ta tashi ta fita ta tsaya bakin ƙofa, Anty ta fito tana kwalawa Mu'azzam kira don dashi za a tafi, ya fito daga ɗakinsu yace "Anty gani", tace "ko ka fasa zuwa kaga ƙanwar taka ne..?", ya girgiza kai yace "A'a zani", Shi dai so yake yaje yaga halin da ƙanwarsa take duba da irin auren da akay mata, gaba ɗaya ya kasa nutsuwa tin bayan auren, gashi kuma lokaci da dama ya kira wayarta switched off, Anty tace "toh muje ko" da haka tayi soro Hafsah tabi bayanta, Mu'azzam ya saka takalmansa ya fita shima, a soro suka kusa yin karo da Maimuna dake ƙoƙarin shigowa ta ɓoye wani abu a hijab, ko kallonta beyi ba ya wuceta ya cigaba da tafiya, Maimuna ta taɓe baki ta zabga masa harara ta shiga cikin gida da gudu, ɗakin Maama ta shiga tana zazzare ido ta fito da abinda take ɓoyewa cikin hijab, Maama dake tsaye da ɗaurin ƙirji tace "amma Maimuna Ala wadaran nawarki, daga siyo shinkafar ɓera shine kika je kikai zamanki sai kace an aiki bawa garinsu, wllh kin cuce ni, har an gama fita da kayan..", gwalo ido Maimuna tayi tace "mun shiga uku, har an gama fita dasu..", Umma tace "tin ɗazu ma, ai bakya abu da jiki daman baki so aiken ba..", cikin ɗaga murya Maimuna ta dakawa Maama tsawa tace "wai ke dalla Maama kin san da ya akai na samo bom din ɓeran nan kuwa, saida na fita daga unguwar nan sannan na samo sa fa", Maama ta saki baki jin yadda ƴar cikinta ke mata magana na rashin ɗa'a, Maimuna ta zabga tsaki tace "kuma wllh bazan yi asarar ɗari shida ta ba sai kin biya ni..", Maama tace "toh ai saiki bisu can gidan ki zazzaga bomm din da kanki don ni babu yadda zanyi tinda har sun fita", Maimuna tace "A jarkar mai zan zuba ko?", Maama tace "Eh shine yafi sauƙi tinda dai ba zaki iya farke buhun shinkafa ba amma idan kika ɓalle jarkar mai kika zazzaga saiki rufe kawai", Maimuna tace "bari na bisu kuwa don wllh sai Hajara tayi nadamar cin abincin nan", Maama tace "maza ƴar albarka ki tafi kar su ɓace miki", da gudu Maimuna ta fita daga gidan, Maama ta rafsa wata shegiyar guɗa ta buga cinya tace "sai a koma asibiti kuma bayan an take tumbi da abinci", Maimuna na fita bakin titi ta tarar har an gama saka kayan a ƴar ƙurƙura, Mu'azzam ya shiga gaban ƙurƙurar Anty da Hafsah kuma sun tari napep suna ciniki, Maimuna ta matsa kusa da napep din ta wani haɗe rai, Anty ta kalleta ba tace mata komai ba ta cigaba da kwatantawa mai napep unguwar da zai kaisu, Hafsah tace "Anty muje kawai zan gane gidan", Anty ta shiga napep din Hafsah ma ta shiga, ba kunya ba tsoron Allah Maimuna ta riƙe ƙarfen napep ta fara shirin hawa, Hafsah ta leƙo tace "ke malama ina zaki...?", Maimuna tace "kin fini kusanci ne da gidan wacca zaki..?, dalla malama dakatamin ki tsaya iya matsayinki, ke asuwa banza karan kaɗa miya a jefa bayan gida", Hafsah ta jefa hand bag din Anty dake hannunta a booth din napep, tasa hannu biyu ta hankaɗa Maimuna da ta turo buttocks zata zauna, saura ƙiris Maimuna ta baje a ƙasa, ta kasa yiwa Hafsah komai sbd bomb din ɓeran da take ƙunshewa a hijab, Maimuna tasa hannu ɗaya ta riƙe karfen napep din tana ɓarkawa Hafsah zagi, Hafsah ta taɓe baki tace "ban iya ba wllh, zagi ko toh ni ban iya ba, mai daidaita sahu kawai bi takanta muje", Kawai Maimuna ganin Mu'azzam tayi a gabanta, yace "ke dan uwarki ban nan wajen kafin na ɓarar dake...", Maimuna ta saki ƙarfen napep din ta matsa baya, Mu'azzam yayi kwafa ya koma ya shiga ƴar ƙurƙurar, mai napep yaja napep dinsa suka hau saman titi, bayansu su Mu'azzam suka bi tinda su za su musu jagora, Maimuna ta kalli kuɗin dake hannunta ɗari tara, tsayar da mai napep din da yazo wucewa tayi, da sauri ta shiga ta nuna masa motar su Mu'azzam wacca tayi nisa tace "yi sauri malam ƴar ƙurƙurar can zaka bi karsu ɓacemin", mai napep yace "tom" ya bawa babur ɗinsa wuta daman kuma sabo ne, Maimuna ta ringa azalzalal mai napep kar ya bari su ɓace masa don idan suka ɓace babu yadda zatay, gashi dai ta taɓa zuwa gidan amma kuma bazata gane ba sbd dulhu dankali ce, daga farkon layin Maimuna tasa mai napep ya ajiyeta tinda zata iya gane gidan daga nan, bill dinsa ta tambayesa, direct yace "dubu ɗaya zaki bayar hajiya", zaro ido tayi tace "duba ɗaya kuma, gsky ɗari biyu da hamsin zan baka..", yace "ɗari biyu da hamsin taɓɗi", Maimuna tace "nidae haka zan baka..", yace "haba malama duk wnn tafiyar, Shata fa kika ɗauka don baki bari na ɗauki wani pasinjan ba..", mai napep da yaga tana ƙoƙarin ɓata masa lokaci tini ya kashe babur din ya fito, yace "ko ki bani kuɗina ko na haɗa miki jini da majina, ce miki akay ruwa na zubawa babur din, ko baki san yadda fetur yayi tsada ba..", tini jikin Maimuna ya hau zikiri don kwa layin tsit babu kowa, hannunta na rawa ta fito da ɗari tarar data rage mata tace "dan girman Allah yi haƙuri ka amshi wnn, wllh su kenan a hannuna", da magiya da komai ya haƙura ya amshi ɗari tarar bayan ya mata Allah ya isan ɗarinsa ya burga mashin dinsa ya tafi. mai gadi ya buɗe gate da ake knocking ya tsaya yana kallon su Anty, gaisheta yayi ya bata hanya ta wuce, Hafsah tabi bayan Anty zuwa cikin gidan, mai gadi da mai ƴar ƙurƙura sai Mu'azzam ne suka sauke kayan suka shigar dasu ciki, Mu'azzam yayi mamakin ganin gidan da aka kawo ƙanwarsa, Inuwa sai duban kayan yake yana gyaɗa kai, da ake cewa babu kuɗi a gari ashe dai kuɗi suna nan inda suke, Hafsah ta danna bell ɗin main door ta shiga gidan bayan knocking da tayi, Anty ta ciro wayarta ta shiga kiran layin Hajar, tana dai ringing amma no respond, Anty tace "ikon Allah, ko basa nan ne, munyi waya fa da ita ɗazu tace min tana nan", Hafsah tace "toh bari a tambayi mutumin da ya buɗe mana ƙofa", Hafsah ta ƙarasa wajen da Inuwa ya koma kan white plastic chair ya zauna, tace "mutanen gidan basa nan ne...?", mai gadi yace "Alhj ne kawai ya fita", Hafsah tace "mu gashi nan sai bubbuga ƙofa muke amma shiru", mai gadi ya tashi yace "bari na nuna muku ta baya sai ku shiga" ya wuce gaba Hafsah tabi bayansa, har ƙofar kitchen dake backyard ya rakasu kafin ya koma bakin aikinsa, Anty ta murɗa ƙofar tashiga taga ashe kitchen ne, ta kalli Mu'azzam tace "a shigo dasu nan kawai, ba a barsu yashe a tsakar gida ba", har sukay minti goma da shiga palourn basu ga alamar Hajar ba, daga karshe dai Hafsah ta tashi ta haura sama, a hankali tayi knocking ƙofar ɗakin da tasan an kai Hajar, murɗa ƙofar tayi ta shiga, ba taga kowa ba saidai taji ƙarar ruwa daga toilet, tsaye Hafsah tayi tana jiran fitowarta, few minutes kam sai gata nan ta fito tana tafiya a hankali......✍️ follow my account on Arewa book to stay connected @ feenerhfeeche02 💛 HAJAR 💛 by Feenerh feeche {44..} Tamkar wata munafuka haka Mainuna ta ƙarasa bakin gate din gidan ta bubbuga, mai gadi ya buɗe ƙofar, tsayawa yayi yana kallonta, Maimuna tace "zan wuce ko", mai gadi yace "hajiya daga ina...?", tace "tare muke da mutanen da suka shigo yanzu, na tsaya ne akan hanya na amshi saƙo..", mai gadi ya sake kallonta sama da ƙasa don sam ba tayi kama da mutanen ba, fuskarta sai kace horror duk ta ɗashe sbd azabar shafa mai, ga kuma uban ƙuraje da barni da mugu, kayan jikinta ma ba kanta don wani yagulamun hijab ne sanye ajikinta duk ya ƙoƙƙone ya farke, matsa mata yayi ta shiga ya rufe gidan, wani kallon baƙin ciki Maimuna take bin compound din dashi, tsaye tayi ta rasa ina ma zata dosa, Inuwa da har ya koma ya zauna ya sake tashi ganinta a tsaye, yace "bari na nuna miki ta baya tinda naga tanan a rufe take..", gyaɗa masa kai kawai tayi don tsoro ya fara shigarta, wai ta yaya ma zata iya zuba shinkafar ɓeran, haka tabi mai gadi har ya nuna mata hanyar baya, kasa shiga tayi don tsoro ya kamata fa ainun, shi dai mai gadi tinda ya gwada mata ƙofar ya koma bakin aikinsa, shahada kawai tayi ta tura ƙofar a hankali, tinda dai ta riga da tazo babu yadda za suyi da ita, saɗaf saɗaf ta shiga da wani suɗaɗɗen takalminta, cak ta tsaya tana kallon kitchen din ganin kayan garar zube a nan, wani daɗi ne ya tsarga mata a zuciya, da sauri ta fito da ledar da take ƙunshewa a hijab. Tare da Hafsah Hajar suka sauko ƙasa, Hafsah ce ma ta riƙota don da kyar take tafiya sbd ciwon kan, ga kuma yunwa da ta mata illa don rabonta da abinci tin jiya da yamma, sosai Hajar taji daɗin ganin Anty da Mu'azzam, saida suka gaisa gaba ɗaya snn ta samu waje ta zauna ta jingina da kujera, Mu'azzam na kallonta yace "ke lafiyar ki kuwa..?", Hafsah tace "kanta ne yake ciwo..", yace "Sannu, Allah ya sauwaƙe", Anty tace "Ayya sannu kinsha magani..?", Hajar ta girgiza kai tace "babu maganin ai", Anty tace "tin yaushe kan naki ke ciwon..?", Hajar tace "tin safe", Anty tace "akwai panadol a jakata, Hafsah buɗe ki ɗakko mata", Mu'azzam ya tashi yana ciro wayarsa da tay vibrate daga aljihu, ƙofar kitchen ya murɗa ya shiga, a gigice Maimuna dake tsugunne gaban jarkar mai ta ɓalle murfin tana shirin zazzaga shinkafar ɓeran data buɗe ta ɗago kanta, wani irin juyawa ƴan hanjinta sukay ganin Mu'azzam, tsabar gigicewa sai ta saki ledar shinkafar ɓeran a ƙasa, daɓas ta zube a ƙasa tana raba ido tamkar ɓera a buta, da mamaki Mu'azzam yake kallonta, mayar da wayar yayi aljihu ya fasa ɗaga kiran, ledar da ta wurgar ya ɗauka, ƙurawa ledar ido yayi, ya dubi Maimuna da tayi tsilli tsilli, wata mummunar zuciya ce ta ɗebesa ya haɗa kanta da cooking gas, wata razananniyar ƙara ta fasa sbd ji tai kamar raba mata kan gida biyu yayi, tini zufa ta fara tsattsafo masa a goshi, Anty ce ta shigo kitchen din, still tay tana kallon Maimuna da goshinta ya wanke da jini, Mu'azzam ya goge zufar goshinsa yana kallon Anty yace "Why, ƙoƙarin kashe min ƙanwa take Anty" ya juya yana nuna Maimuna da yatsa yace "so take ta kashe min ƙanwa...", Anty ta ringa kallon Maimuna sai kuma ta dubi Mu'azzam, bata kai ga cewa komai ba ya nuna mata ledar bomb din ɓeran hannunsa har rawa yake yace "kamata nayi tana ƙoƙarin zubawa a cikin mai", Anty da mamakin ganin Maimuna a nan ya gama cikata tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mun shiga uku, yanzu Shayin ɓera ka kamata zata zuba a mai", Anty ta sakawa ƙofar kitchen ɗin lock sbd bata son Hajar ko Hafsah su shigo ta juya tana kallon Mu'azzam tace "dan girman Allah fitar mana da ita daga nan, marmaza ka fita da ita wnn ai gara annoba da ita, yanxu ke har zuciyarki tayi baƙin da zaki cutar da mutum da bomb din ɓera", Mu'azzam ya iza ƙeyar Maimuna suka fita daga kitchen din, Anty tabi bayansa tace "ka tabbatar bata zuba ba...?", yace "Eh bata kai ga zubawar ba na kamata..", Anty ta koma cikin gidan hankalinta duk a tashe, banzatar da Hafsah dake tambayarta me ya faru tayi, bayan ta nunawa Hajar kayan ta shirya tace tafiya za tay, don gaba ɗaya hankalinta ya ɗugunzuma gwara taje ta zauna da ƴar uwarta, wnn abu ai ba na wasa bane, a nan ta bar Hafsah zata tafi gida daga baya bayan tace mata karta kai dare, sosai Hajar taji daɗin bar mata Hafsah da akai, Hafsah ta shiga kitchen ta dafa mata Noodles, ta ringa mita bayan ta kawo mata Noodles din tace "ga abinci ba zaki dafa kici ba saiki ta zama da yunwa", Hajar na tura Noodles din tace "bana jin daɗi ne", Hafsah tace "yunwa ce fa..", Hajar na gama cin Noodles din da zata iya tasha panadol da Anty ta bari, sosai taji dama dama kan ya dena ciwo, Hafsah taje kitchen ta ɗakko ledar da suka zo da ita wacca ke ɗauke da turaren wuta da sauran tarkace da Anty ta haɗawa Hajar, Hafsah tace "bari na rage miki aiki", upstairs suka haura again zuwa ɗakin Hajar, Hafsah ta buɗe box din kayan Hajar ta jera mata su a wardrobe, kayan lefenta ma saida Hafsah ta buɗe ta mata tsince tsince, kayan bacci da mayuka da perfumes, mirror kam saida ya cika damm da kayan shafe shafe don Hafsah bata barsa haka nan ba, ita dai Hajar kawai kallonta take tana yamutsa fuska, ita sam babu abinda ya birgeta na daga gidan ko kuma kayan cikinsa, garar da Baban ta yayi mata ya fiye mata komai na gidan, daga ƙarshe Hafsah ta shiga bathroom tayi masa jerensa shima, Shower gel Shampoo da conditioner duk ta jera su a cupboard dake toilet din, saida Hafsah ta gajiyar da kanta don har shara tayi ta goge ko ina ta bisa da turaren wuta a burners, da joke Hafsah tace "da fatan dai kin ɗauki course, haka zaki ringa yi kullum", Hajar ta taɓe baki tace "uhmm", Hafsah tayi ajiyar zuciya ta saka serious face tace "Sister i understand your feelings, nasan yadda kike ji, amma ki ajiye komai ki riƙe hakan as one out of your destiny, ke naki ƙaddarar knn, Allah ya rubuta wnn da aka aura miki shine mijinki, nothing can change that, don Allah ki kwantar da hankalinki ki amshi ƙaddarar ki hannu biyu, forget about the past and face the future ehmmm", Hajar tace "idan da ban haƙura na amshi ƙaddarar ba ai bazan zauna ba Hafsah, wllh tllh Baba nake dubawa shiyasa na zauna amma baya ga haka babu abinda zai zaunar dani", Hafsah tace "Eh hkan ma yayi, komai na rayuwa ai sila ne, in Allah ya yarda wnn auren sai ya zame miki jin daɗi da kwanciyar hankali...", Hajar ta rausayar da kai ba tace komai ba, ƙarfe biyar Hafsah ta fara shirin tafiya, tini mood din Hajar yana canza, Hafsah tayi kamar bata fahimta ba ta cigaba da shirinta, tana gama shiryawa ta ɗauki jakarta, har bakin gate Hajar ta rakata, bayan ta tafi ta koma ciki. Hafsah tsaye bakin road tana jiran napep bayan tayi ƴar tafiya ta fito daga layin gidan, napep biyar ta tare kuma duk basu ɗauketa ba wai ba za suyi hanyar ba, har ta fara gajiya da tsayuwa, wata lafiyayyiyar Mota ce taci taya a gabanta, ganin motar ta kare mata titi ta matsa daga wajen, driver seat aka buɗe, wani gentleman ya fito his eyes covered with shade, ta cikin shade din ya ringa kallonta kafin ya rufe murfin motar ya isa inda take, Calmly yace "Assalamu alaikum...", Hafsah ta juyo tana kallonsa ba tare da ta amsa sallamar ba, sake matsawa tayi ta haɗe gira, cire shade din yayi yana kallon side view din face ɗinta yace "Young Lady", juyowa tayi ta ƙura masa ido, tsuke ido tayi bata kai ga magana ba ya rigata yace "it is me Ahmad..", ta zaro ido tace "ohh Sannu ai ban gane ba da farko", yayi murmushi yana shafa kwantaccen beard dinsa yace "how are you...?", tace "am fine alhmdllh", yace "masha Allah..", ya kalli road din da yake tamkar an sharesa babu motoci sosai ma bare kuma napep yace "where are you heading to...?", tace "Gida zani", yace "toh bari na ajiyeki ko", a fakaice ta dubesa sai kuma ta girgiza kai tace "No thank you...", yace "me yasa ba zakizo na ajiye ki ba..?, zafa ki iya kai Magrib anan tricycle basu wucewa sosai tanan", ta sake girgiza kai tace "i can wait....", da kyar yayi convincing dinta ta yarda bayan dai taga tabbas zata iya kai magrib don tin zuwansa wajen babu napep din da ya sake wucewa, da kansa ya buɗe mata front seat ta shiga a hankali ya mayar da ƙofar ya rufe kafin ya zaga ya buɗe driver seat ya shiga, ita dai ta maƙale daga jin window, gaba ɗaya she isn't comfortable ta takure waje ɗaya, Ahmad ya kunna motar ya fara driving da minimum speed, Silence ne ya ɗauka a motar, bayan sun fita daga unguwar Ahmad yayi breaking silence ɗin da faɗin "ya school...?", tana kallon handbag dinta dake kan laps ɗinta tace "alhmdllh ai mun kusa gamawa..", yace "University fa", tace "No secondary ne..", ya jinjina kai yace "as expected you are a teenager", zaro ido tayi tace "A'a fah", his eyes fixed on the road a hankali yace "how is she..?", ɗaga kanta tayi ta kallesa, a lokaci guda ya juyo sukay ido huɗu, da sauri ta ɗauke kanta ta kalli window tace "tana lfy alhmdllh...", yayi ajiyar zuciya yace "Ohk" da haka bai sake cewa komai ba, ita dai tana jiran taji ya tambayeta hanyar unguwar tasu don sai take ganin kamar ya manta, amma sai taga beyi hakan ba kuma tiryan tiryan hanyar unguwar yake bi, Hafsah tana ganin sun shigo unguwarsu zuciyarta ta buga, basu ƙarasa gidansu ba tayi saurin cewa "amm drop me here zan ƙarasa", slowing down yayi yabi gefen titi ya tsaya, tace "nagode" ta fara ƙoƙarin buɗe motar taji a ƙulle don bai buɗe lock ba, ta juya za tace masa ya buɗe taga ashe kallonta yake, da wani irin expression bisa fuskarsa yace "Sorry, one minute please", ta sauke hannunta dake riƙe da handle din ƙofar tace "Okay", yayi ajiyar zuciya still looking at her yace "the last time i met her ta gayamin cewa she is getting marry soon, at that time na yarda amma bayan wani lokaci sai mind dina taƙi yarda..", yayi shiru na 3secs kafin ya ɗora "i want you to tell me the truth..", ta ɗago kanta ta kallesa kafin ta mayar ƙasa tana wasa da ƙasan mayafinta tace "me yasa kake tambayata wnn...?", yace "bcox i need to confirm it ko na samu rest of mind..", kai tsaye tace "Alright, the truth is since last week Friday akay bikinta, yanxu ma daga gidanta nake...", Ahmad was very shocked and dump founded, yama kasa cewa komai, zuciyarsa ce ta ringa confusing nasa tana ce masa ai Hajar kawai tace masa haka ne to get rid of him amma ba hakan bane, Hafsah dai ganin baice komai ba tace "please open the door one minute has passed..", buɗe lock din yayi da kyar yace "sai anjima..", tace "thank you..", ya gyaɗa kai yace "you're welcome", ta buɗe motar ta fita ta rufe masa ƙofar, ta ƙarewa street din nasu kallo wai ko za taga wani wanda yaga fitowarta daga motar kuma wanda ta sani, Sosai taji daɗi da ta lura babu kowa, tana ƙarasawa ƙofar gida ta juyo, sosai tayi mamakin ganin motarsa bai tafi ba har lokacin, ita dai ta ɗakko keys daga jaka ta buɗe gida ta shiga. ★Umma ta ɗora hannu bibbiyu aka ta zabga wani uban salati tana kallon Anty tace "Jamilah na shiga uku na lalace shayin ɓera fa kika ce", Anty tace "ai ba ɗora hannu a ka za kiyi ba, kuma biki shiga uku ba Adda, wllh tllh zama bai kamace ki ba, idan haƙuri yayi yawa toh cutarwa ma yawa take, abu ne wanda ba yanxu aka fara ba an ɗebi shekaru anayi, ace har an fara farautar raii, gsky ya kamata ki farga cutar tayi yawa, idan da ace Mu'azzam bai ganta ba da shknn sai yadda Allah yayi, wa yasan halin da Hajar da Mijinta zasu shiga idan sukaci oil din nan, gani nai bazan iya shiru ba shine nace bari na dawo na tasheki daga barcin da kike..", Umma da kuka ya kwace mata tace "Jamilah yanzu ya zanyi dan Allah wnn wane irin masifa da bala'i ne, ace yarinyar nan tayi aure ta bar maku gida amma ku bita har gidanta da bita da ƙulli, da tana gida ma baku barta zaman lfy ba ita da gidan ubanta gashi gidan mijin ma an bita, wnn wace irin rayuwa ce..", Anty tace "Ahapp ki dena ɓaɓatu kina ƙarar da yawun bakin ki Adda, tashi tsaye za kiyi ki nemawa kanki salama, ki buga ƴan iska ga hukuma, wnn lamari ai ba na wasa bane, ƙoƙarin kisa fa..", Umma ta sharce hawayenta tace "bari mal ya dawo..", Anty tace "A'a Adda mal ai ba hukuma bane, idan nice ke yanzu ba sai anjima ba zan wanke ƙafa na tafi inda za a nemamin haƙƙina", tini Umma ta zari hijab ta saka ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace "a ina zan buga matsiyatan..?", Anty ta tashi tace "muje", da sauri Umma ta fita tsakar gida Anty na biye da ita, banke ƙofar ɗakin nata kawai tayi babu wani batun padlock, tin daga soro kake jin muryar Baba yana kwalawa Maimuna kira, da iya volume din muryarsa yake kiranta har yana ƙoƙarin ƙwarewa, da mugun gudu Maama ta fito daga toilet, har tana fyarɗe hannu da ƙarfen langa langar ƙofar banɗakin, banga banga tayi a ƙofar ɗakinta tana zaro ido, a matuƙar fusace Baba da ya shigo gidan shi da Mu'azzam yace "ina Maimuna..?", Maama da hannunta yake azabar raɗaɗi da zugi tace "wace Maimuna kuma mal, yarinyar dake kwance tin shekaran jiya tana fama da masassara, yau kuma ta tashi cikinta ya tsuru wuni tayi tana fatattaka gudawa, gaba ɗaya ta fita daga hayyacinta ido ya zuzzurma...", Umma dake tsaye tsakar gidan ta daka mata wata gagarumar tsawa tace "wllh ko kashin ƴan hanjinta take saita ɗanɗana kuɗarta a yau, na gaji da abinda ake min a gidan nan yau an kaini bango, billahillazi la'ilaha illa huwa bazan haƙura ba..", galala Maama take kallon Umma ta hura tukubar hanci tace "toh ai sai kizo kisa ta ɗanɗana kuɗarata ta, ke kin isa ma ki ɗora hannunki akan ƴata", Baba da tari yake ƙoƙarin sarƙe masa numfashi yace "Rabii ki faɗamin inda Maimuna take ko na sake ki..", Maama ta dafe ƙirjinta ta gwalo idanu waje tace "da girmana da gemuna mal kake cewa zaka sakeni a bainan nasi, toh Maimuna dai ƴarka ce kuma gata can kwance tana makyarkyata...", Baba yace "So nake ta fito nan yanzu yanzun nan..", kasaƙe Maama tayi sai kuma ta rausayar da kai ta shiga ɗakinta, Maimuna da ke rakuɓe can ƙarshen gado ta haɗa hannayenta waje guda tace "Maama dan girman Allah ki rufa min asiri, na shiga uku na lalace..", Maama tace "A'a Maimuna a gaskiya tashi za kiyi ki fita, kina jifa sakina yace zaiyi idan ya sakeni ina na dosa..", Nabilah dake ɗakin itama tace "wanda baiji bari ba ai yaji hoho, saida nace ki bari Maimuna amma saida kika biyewa Maama, tinda dai baku rasa ci da sha ba ina ruwanku da garar Hajara, ga dai irin ƙarangiyar da kika jajiɓowa kanki...", Maimuna ta rushe da kuka ga goshi yayi suntumm, tini Maama ta figi ƙafar Maimuna ta fara janta ƙiyyy jin Baba na sake jaddada mata zai saketa, Maimuna ta riƙe gado ta daƙile tana kurma ihu, ta ƙarfi da yaji Maama ta fitar da ita, daga ita har Maimunan haki suka ringa yi, Maama tace "ƴarka ce daii", Anty dai tinda ta jingina da bango tana kallon ikon Allah ba tace komai ba, Baba kawai kallon Maimuna yake da wani irin takaici, shi ba ya mata baki rayuwarta taɓarɓarce ba. Maimuna ta faɗawa ƴan garinsu da shaɗin carbi, daga tazo guduwa Mu'azzam zai tarota ya dawo da ita don ji yake kamar ya taya Baba dukan ƴar banza, Maimuna da taji azaba iya azaba tace "na rantse da Allah Maama ce ta sani, itace tace na zuba wllh" tana soshe soshe, saura ƙiris Baba yayi collapsing Mu'azzam ya riƙosa ya kaisa ɗakinsa, wnn dalilin ne yasa Umma ta fasa fita, maganin Baban dake wajenta ta ɗakko da ruwa ta shiga ta kai masa, Wani irin tari mai ƙarfin gaske Baba yake, idanunsa sun firfito waje, da kyar aka sami kansa, Maimuna dai ta samu ta arce ɗaki tana soshe soshe, Maama ta bita ɗakin tana sababi tace "Shine kika fita bainan nasi kikai yama ɗiɗi dani..", a gigice Maimuna tace "Allah ya isa na bazan taɓa yafewa ba, munafiki azzalumi mugu..", Nabilah tace "kan bala'i Maimuna wa kikewa Allah ya isa...?", Maimuna tace "waccan Shegen Mu'azzam ai shine yazo ya ƙalamin sharri, kuma na rantse da izu sittin sai yasan ni aka daka ta dalilinsa, wllh tllh saina biya ƴan daba kuɗi sun sassara shi, idan yaci buluss shegiya nake, shi ya isa yasa a dakeni kuma ya fasamin goshi a banza, wllh Allah sai nasa ƴan daba sun sassara shi...". ★Nurain ne zaune main palourn gidansu, plate din abinci da Noor ta zubo masa ne a gabansa yana ci, Mami ta fito daga part dinta, shigowa palourn tayi tana kallonsa sai kuma ta kalli plate din abincin tace "har yanzu baka tafi gida ba Nurain...?", ya ajiye spoon din hannunsa yace "yeah na tsaya yin dinner ne", tace "Ohk hurry up ka gama dare yayi fa 9 ya wuce tin ɗazu..", yace "Ohk", Mami ta zauna kan kujera, kaɗan ya rage abincin ya tashi ya shiga da plate din kitchen, ya fito da bottle water a hannunsa, Mami ta tashi tace "toh good night zan sawa door lock", kallonta ya ringa yi da mamaki sai kuma yace "am spending the night here", with facial expression take kallonsa tace "baka isa ba kuma wnn", ya girgiza kansa don yana sane ya faɗi hakan don yaji view ɗinta, upstairs ya haura zuwa room ɗinsa, bayan few minutes ya sakko da wata medium bag a hannunsa wacca ya zubo kayan sawa, ya yiwa Mami sallama wacca har lokacin bata bar palourn ba ya fita, yana fita Mami ta sakawa door lock, Nurain ya girgiza kansa don yaji lokacin da ta saka lock din, wato dai Mami harda kora, motarsa ya shiga ya bar gidan, yana zuwa gida bayan yayi parking ya fito daga motar, Inuwa mai gadi ya masa sannu da zuwa, Nurain ya wuce hanyar shiga gidan, keys ya ciro ya buɗe ƙofar ya shiga, tsayawa yayi yana kallon palourn da yake tsaf tsaf sai ƙamshi ke tashi, tsaki yayi ya taɓe baki ya haura sama with his bag, bayan yayi wanka ya shirya cikin Pajamas ya ɗauki jakar Laptop dinsa ya sake sakkowa downstairs, ajiye bag din Laptop din yayi kan kujera ya shiga kitchen, shima dai kitchen din tass yake komai a mazauninsa, daga can gefe yaga foodstuffs, still yayi yana kallon foodstuffs din, ga kuma bucket guda huɗu kusa da foodstuffs din, ya buɗe bucket ɗaya wanda yake cike damm da dubulan, ya sake buɗe wani shi kuma yaga Alkaki shima acike damm, bai buɗe ragowar ba sbd ya gane na mene, Coffee maker ya jona jikin socket kafin ya buɗe cupboard da ya ajiye Coffee powder ciki, within few minutes ya gama haɗa black coffee ya bar kitchen din, saida ya kashe dukka fitulun palourn snn ya zauna a kujera ya kunna Laptop dinsa, operating system din yake at same time kuma yana sipping Coffee, ɗago kansa yayi ya kalli stairs jin footsteps, a hankali Hajar take sakkowa daga benen, harta fara bacci wata azababbiyar yunwa ta farkar da ita, tamkar an yashe mata kayan ciki haka take ji tsabar yunwa, tunawa da kayan garar da aka kawo mata ne yasa ta fito domin ta ɗiba taci kar yunwa ta halaka ta, kafin ma ta ƙarasa sakkowa ƙasa ta hango duhun palourn, Allah yaso da wayarta a hannu, tana gama sakkowa ta kunna fitilar wayar, rays ɗin hasken fitilar wayar da ta kunna ya dallare masa ido......✍️ Feenerhfeeche02 @ Arewa book 💛 HAJAR 💛 by Feenerh feeche {45..} Da sauri Nurain ya lumshe idonsa tsabar yadda hasken ya kashe masa su, Hajar da tsoro ya sandarar da ita ta kasa wani cikakken motsi, sosai ta razana don ba tayi tunanin akwai mutum a wajen ba, Nurain ya ajiye cup din Coffeen ya kaucewa hasken yace "kee mene haka kuma are you mad...?", da sauri ta janye hasken daga kansa, furiously ya tashi ya kunna bulbs haske ya gauraye palourn, wani irin shan kunu Hajar tayi ta shige kitchen da sigar ko in kula, sarai tasan haske masa ido tayi amma she don't care tinda dai ba intentionally ta aikata hakan ba, wani tuƙuƙi ne ma ya mamaye mata zuciya da taga fuskar tasa, plate ta ɗauka ta zuba dubulan da Alkaki sai chin chin, cup ta ɗauka ta buɗe tap din sink ta cika da ruwa, daga haka ta fita daga kitchen din, direct stairs ta dosa, Nurain ya miƙe daga hannun kujerar da ya zauna ya zuba both hands dinsa a pocket fuskarsa a murtuke yace "hey you stay there", tamke fuskarta tayi ta cigaba da tafiya a hankali sbd kar cup din da ta ciko da ruwa yayi tambal tambal ya zube, yayi blocking front dinta yana binta da wani kallon tsana yace "wnn shine karo na ƙarshe da zaki sake fitowa palourn nan idan ina zaune, daga ƙarfe shida na yamma bana son ko silhouette naki ya gifta ta palourn nan, ko me za kiyi ki yisa kafin wnn time din that is weekdays knn, a weekend kuma you just have 3 hours daga shida na safe zuwa tara, daga nan kuma sai gobe, am i clear...?", ta juya lulu eyes ɗinta ta yamutsa fuska sbd yadda tayi perceiving pure men scent dinsa, ta taɓe baki tace "sorry you can't tell me what to do...", yace "ko, toh ki jini da kyau as far as you are living in my house you must follow my rules, bad attitudes din kike ji dashi toh ki tattarasa ki ajiye gefe, ba dai a nan ba saiki bari lokacin da kika gaji da zama kika sallami kanki ki ɗauki abinki ki ƙara gaba, this is my last warning...", da haka ya barta tsaye ya ɗauki Laptop dinsa da cup of coffeen zai haura sama, wata nannayar ajiyar zuciya Hajar ta sauke, har wani huci take masifar ta motsa, idonta ya kawo ruwa, tana ganin yayi rabin stairs din tace "ji mana malam, karka tsaya wahalar da kanka, ka damƙa min shaida kaga idan ban ƙara gaban ba", ya juyo ya wurga mata wani mugun kallo yace "save the time that you are free to roam in my house..." da haka ya juya ya haura stairs, har wajen 50seconds tana tsaye inda ya barta, gyaɗa kai tayi ta numfasa tace "lallai wnn mutumin bai sanni ba, sanin da yayi min na taɓin gishiri ne, mu zuba ni da kai wanda ya fasa bai haifu ba", ɗakinta ta wuce abinta, akan mirror ta ajiye plate da cup din da ta shigo dasu, ta zauna akan stool dake gaban mirror din tana kallon kanta, kwafa tayi ta girgiza kai ta ja plate din gabanta ta fara cin tarkacen da ta ɗeba, tana gama cin iya yadda zai mata ta sha ruwa, tayi kwanciyarta kan carpet kamar yadda tayi jiya, ta lulluɓe da duvet don wani azabar sanyi ɗakin yake mata sbd Ac gashi bata san ta inda zata kashe ba. Nurain ya gama abinda zai yi jikin Laptop kafin ya kashe ya mayar da ita bag, ya fita da cup din daya gama shan Coffee zuwa Kitchen yana dawowa kuma ya kwanta, da Asuba bayan ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita daga room din nasa, a corridor ya tsaya yana kallon ƙofar ɗakinta, after looking at the for few seconds kawai ya sauka downstairs, bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yayi recitation of the holy book, sai wajen 8 na safe ya rufe karatun, daman already yau Monday yake son komawa work, bathroom ya shiga bayan yayi wanka ya fito da towel a hannunsa yana goge cikakkiyar sumarsa, 9 ya gama shirinsa tsaf ya ɗauki briefcase da ya saka Laptop dinsa ya sauko ƙasa bayan ya rufe part din nasa, bai ga dai alamar ta sakko ba har ya shiga kitchen, ya haɗa tea ya dawo palour yana sha, tsaki yayi don ya saba yin full breakfast kafin ya fita aiki, daga karshe dai ya gama shanye tean ya kai cup din kitchen, daga haka ya fita compound bayan ya rufe main door ya zuba keys din a pocket, da sauri Inuwa dake zaune kan white plastic chair a bakin gate ya taso, ya russuna da kyau ya gaida Nurain, a takaice ya amsa yace "akwai wanda suka zo jiya ne bayan fita ta..?", Inuwa yace "Eh alhj anyi baƙi sunxo nan da kayan abinci..", Nurain ya gyaɗa kai bai ce komai ba ya buɗe motarsa da Inuwa ya gogeta tass ya wanke wheels ɗin kuma, bayan ya gama warming ya ja motar ya bar parking space din ya fita daga gidan dan already mai gadi ya buɗe gate, after a ride of 20mins ya isa hospital, yayi parking motar, kallon yawarsa dake kan dashboard yayi kafin yasa hannu ya ɗauka ya zurata a pocket, ya fito walking majestically ya nufi hanyar office dinsa, securities da sauran ma'aikata suka ringa gaishesa da welcoming dinsa, briefly yake amsa gaisuwar yana tafiya, yana ƙarasawa office din ya buɗe ya shiga, secretaryn sa Haleema da ya turawa saƙo ta email cewa zai shigo on Monday, shiyasa tin ranar friday tasa aka kyara office din, Haleema ta tashi with respect tace "good morning sir", da sakakkiyar fuska ya amsa mata yace "morning, ykk..", tace "alhmdllh sir an dawo lfy..?", yace "fine alhmdllh" da haka ya shige cikin office din, ƙarewa office din kallo yayi kafin ya ajiye briefcase din hannunsa kan huge table dake office din, after surveying the huge office ya zauna kan kujera yana sauke ajiyar zuciya, ya kalli glass nameplate dake gaban table din mai ɗauke da sunansa (Dr Uthman). wayarsa ya ciro ya kunna, saida ta gama booting uban messages da suke pending suka gama shigowa, call log ya shiga yayi dialing numbern Khaleel, tana fara ringing Khaleel yayi picking, Khaleel yace "ba dai ka dawo ba boss..", Nurain yace "gani ma a office", Khaleel ya katse kiran, after like 5minutes ya shigo office din, Khaleel ya zauna kan ɗaya daga biyun kujeru da suke gaban table din, bayan sunyi exchanging greetings Khaleel yace "An dawo lfy..?", Nurain yace "alhmdllh, Dr Marwan ya shigo..?", Khaleel yace "yeah amma ya shiga surgery not too long ago", Nurain yace "Ohk", Khaleel ya ciro wayarsa da tayi ringing daga pocket din labcoat dinsa, few seconds ya katse kiran ya tashi yace "i have to go now ana kirana a E.R". Khaleel na fita office din Nurain ya kira Haleema ta landline, tayi picking tace "yess sir", yace "Patients zasu iya fara shigowa", tace "Okay sir". Nurain ya fara attending first patient da ya shigo, yana yiwa patient din ƴan tambayoyi aka buɗe ƙofa aka shigo, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ya cigaba da attending patient dinsa, jingina Ruqayyah tayi jikin ƙofar tana mayar da numfashi, ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya sai kuma ta buɗe idanun, kamar a yanzu ta fara ganinsa haka ta zuba masa na mujiya, kawai kallonsa take babu ƙiftawa ta jingina da jikin ƙofar, Nurain yayi prescribing patient din with drugs da cewar zai dawo nan da 2weeks follow up, Ruqayyah ta matsa gefe ta bawa patient din hanya ya fita, tamkar wacca kawai ya fashewa acikin haka ta isa gaban table din nasa kanta a ƙasa tana wasa with her fingers, tinda ya mata kallo ɗayan nan bai sake ba, kwata kwata bai nuna yasan ma da shigowarta ba, ya cigaba da rubutu jikin record book, muryarta na rawa kanta a ƙasa tace "Dearest...", next patient ce ta shigo ƴar dattijuwa, ganin haka yasa Ruqayyah ta bata space, sai a lokacin Nurain ya ɗago yayi attending patient dinsa, a haka dai saida yayi attending 5 Patients kuma har lokacin Ruqayyah na tsaye bata fita ba, na biyar din patient na fita, da sauri Ruqayyah taje ta rufe ƙofa, Nurain ya kira landline yace "i need security now", kasaƙe Ruqayyah tayi tana kallonsa sai kuma ta haɗa hannayenta waje ɗaya tace "plxx talk to me, dan Allah kayi haƙuri ka saurareni Dearest...", rubuce rubucen sa ya cigaba da yi, Security man ya buɗe ƙofa ya shigo with respect yace "sir you call", ba tare da ya ɗago kansa ba yace "get her out of my office", security man yace "yess", ya kalli Ruqayyah da Mamaki ya gama daskarar da ita yace "Muje hajiya..", wani kwallo mai uban tauri Ruqayyah ta haɗiya lokaci guda ta fita daga office din with speed hawaye na zuba idonta. Nurse station ta wuce, tana zuwa ta zauna kan kujera ta hade kanta da table din station din ta fashe da kuka, Nurse Jidda da ita kaɗai ce a station din duk sauran sun shiga ward ta ajiye kidney dish din hannunta tace "Ruqayyah lfy...?", Kuka kawai Ruqayyah take taƙi tace komai, da damuwa Jiddah tace "subhanallah dan Allah ki gayamin mene ya faru..?", Ruqayyah ta ɗago kanta tana kallon Jiddah da jajayen idanunta tace "Jiddah ni yanxu ya zanyi, Dr yaƙi saurarata...", Jiddah ta jinjina kai ba tace komai ba, ita ganin ƙarfin halin Ruqayyah take, yo ko itace Dr ai bazata saurareta ba, Ruqayyah ta goge cheeks dinta tace "wai fa security ya kira yace yayi waje dani sai kace wata ɓarauniya..", ta sake fashewa da kuka, Jidda tace "bari na duba patient a ward A" da haka ta saka kidney dish din da ta ajiye a cikin tray ta ɗauka tabar station din. ★Sai goma da rabi Hajar ta farka daga baccin da ta koma bayan ta idar da sallar asuba, bathroom ta shiga tayi brush ta wanke bakinta da mouth wash, tayi wanka, saida ta wanke bathroom din snn ta fito, tsaye tayi bakin mirror tana kallon uban kayan shafe shafen da Hafsah ta jera mata jiya, wani body lotion ta ɗauka tana duba sunansa sbd da shower gel dinsa tayi wanka, ta zauna kan stool ta fara rubbing lotion din, ta ringa kallon gashin kanta da duk kitson ya fara warwarewa da kansa, bai ɗauketa wani minti 20 ba ta gama tsefe ƙananan kitson kanta tass, daga ta kama jelar zugeta kawai take cause gashinta mai laushi da santsi ne na fulani, combing hair din tayi ta shafa masa oil shima da ta gani, tayi parking dinsa a ƙeya ta tufke jelar, daga haka ta tashi daga gaban mirrorn, ta buɗe huge wardrobe tana taɓe baki, ita dama a box Hafsah ta bar mata kayanta, wata doguwar riga ta atamfa ta saka, ta zumbula hijab ta fita a ɗakin ta sauka ƙasa da cup da plate din jiya da taci kayan gara, kayan garar ta sake ɗiba taci a kitchen din tasha ruwanta a famfo kafin ta fito ta koma room dinta, tanata zaune a ɗakin saidai tayi game a wayarta inta gaji ta ajiye har akay sallar Azahar, tana idar da sallah taji wata yunwa ta bijiro mata, kayan garar dai ta kuma ɗurawa cikinta, samm taƙi yin girki sbd gani take knn ma rayuwa mai tsayi zata yi, palour ta fito ta ringa kallon ƙofa kafin ta matsa kusa da ita ta kama handle ta murɗa, a rufe taji ƙofar, ta koma kitchen ta buɗe ƙofar da zata sadaka da backyard din gidan, luckily ta jita a buɗe, ta ringa kallon backyard din tana ɗan zagawa, ta zauna kan wani dakali da ta gani wanda shine chamber na ruwa, sosai zaman wajen yayi mata daɗi don ji tayi kamar an cirota daga maƙabarta, ba tasan iya awannin da ta ɗauka zaune a wajen ba tana tunani iri iri, motsin zubar ruwa ta jiyo daga front din gidan, tashi tayi ta ringa bin inda motsin yake, mai gadi ne ya kunna famfon compound din yana alwala, ɗan russunawa yayi ganinta ya kashe famfon yace "ina wuni Hajiya..", Hajar ta mayar masa da gaisuwar don ta ganesa ranar da suka dawo gidan shi suka tarar, Inuwa ya duƙar da kai yace "wani abin za a amso miki hajiya...?", Hajar ta girgiza kai ta juya ta koma backyard din, ciki ta koma don yin sallah, tana idar da sallah wayarta ta fara ringing, ta ringa kallon screen ɗin wayar ganin number ke kiranta kuma bata san numbern ba har kiran ya katse wani ya sake shigowa, picking tayi ta kara a kunne ba tace komai ba, wani murmushi tayi bayan ta ɗau murya tace "Noor...", Noor tayi dariya tace "ta ya akay kika gane...?", Hajar tayi ƴar dariya tace "your voice mna", Noor tace "toh ykk ya gida...", Hajar tace "lfy lou and you..?", Noor tace "am great wllh..", Hajar tace "good, toh yaushe zaki zo..?", zaro ido Noor tayi tace "not soon..", Hajar ta marairaice murya tace "kefa kika ce zaki zo..", Noor tace "yeah zan zo amma ba yanzu ba..", Hajar tace "toh shknn sai kinxo", sun ɗan jima suna hira da Noor kafin daga karshe Noor tayi mata sallama, Hajar ta tashi ta naɗe darduman da tayi sallah, sai kace wata ƴar kurkuku haka take jin rayuwar gidan, daga ƙarshe dai ta fara gyara ɗakinta wanda babu wani datti ta masa turaren wuta wai dan duk ta ɗan ware, taje kitchen ta ciko plate da kayan garar da ta mayar abinci, da kyar ta iya hawa stairs bayan ta fito daga kitchen sbd ƙullewar da cikinta yayi, ta samu dai ta shiga ɗakinta ta zaune gefen gado ta danne cikin da yake kan murɗa mata, bayan wani lokaci cikin na murɗawa sai ta fara yin ƙalas, maiƙon Alkaki yazo ya tsaya mata a wuya har tana jin kamar za tayi amai. ★ƙarfe biyu da ƴan mintina Nurain ya fito daga office dinsa holding his briefcase, saida yayi attending kaf patient da suka zo shiyasa ya kai wnn time din, acikin doctors da suke aiki a hospital din shine me wnn halin, indai kaga kazo ganinsa bai duba ka ba toh akwai babban dalili amma duk yawan patient yana squeezing ya duba su, Ruqayyah dake zaune bakin office din over three hours tana jiran fitowarsa ta tashi da sauri tabi bayansa, tana zuwa gaf dashi tace "Dr..", dakatawa yayi da tafiyar ya jiyo yana kallonta ba tare da yace komai ba, kallon da yayi nata sai taji gaba ɗaya ɗan guntun courage dinta ya narke gami da tsiyayewa ta guiwarta, ta kasa cewa komai amma lips dinta sai ɓari suke, shi kam da yasan ma itace wllh bazai dakata ba, shi Allah ya masa wani hali na bagarar da lamari indai ya bar abu topa shknn, don yanzu idan nace muku ya manta muryarta ne shiyasa ma har ya juyo data kirasa kar kuyi mamaki, ya haɗe thick eyebrows dinsa ya juya ya cigaba da tafiyarsa, Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ta lumshe idanunta da suke mata zugi tsabar kukan da ta sha, da sauri ta kuma binsa sai kace mayya tace "dan girman Allah Dearest kayi haƙuri, make time for us so that we can discuss about it, i will tell you all what happened...", har suka fito harabar hospital din tana biye dashi tana masa magiya, ganin ba sauraronta zaiyi ba ta tsaya a ƙofar department din gudun kar ta dizga kanta a public, Nurain yana isa parking space ya shiga motarsa, keys ya zura a ignition ya kunna motar, har lokacin girarsa a haɗe take don ba ƙaramin fama masa zuciya waccar psycho din tayi ba, he dislike the sight of her, direct gidansu ya dosa don bazai koma gidansa yaga wani abun da zai sake ɓata masa rai ba, bayan yayi parking motarsa ya shiga ciki. Mami na zaune a main palourn da wasu close friends dinta guda biyu, ya ƙarasa shiga palourn ya gaishesu duka da ladabi, Mami dai tayi mamakin ganinsa a wnn lokacin it seems like daga wajen aiki yake shine ya zarto nan a maimakon gidansa, shidai yana gama gaidasu ya wuce upstairs, Mami ta bisa da kallo, Haj Sadeeya tace "Aaa aha ashe duk munyi furfura don Allah kalli yadda yaron nan ya koma Nurainin Mami, kinga ma ban tambayesa iyalin ba don ina Canada kika gayamin zancen aurensa...", Mami tayi yaƙe tace "matarsa na nan lfy baifi kwana goma da yin auren ba..", Haj Sadeeya tace "kwana goma kuma nifa mganar almost one year nake miki..", Haj Fati tace "ni dai nasan wancan an fasa yinsa, bayan nan ma Nurain din ya koma India, toh dai wnn na kwana goman ne bansan dashi ba.." ta fadi hakan tana kallon Mami, Mami ta kallesu duka tace "wllh auren ne yazo unexpected, nima kaina saida aka ɗaurasa na sani, prof ne ya haɗasa da ƴar abokinsa, shima yaron ba sani yayi ba don lokacin ma bai dawo ƙasar ba..", Haj Sadeeya tace "duk ba labari da fasa wancan din da kuma sabon, toh in banda abinki Mami aiko baza mu zo ba ai kya gaya mana", Mami tayi ajiyar zuciya tace "duk kuyi haƙuri abin ne yazo unexpected shiyasa, ba a nitse nake ba wllh". uku da minti goma Nurain ya sakko har yayi wanka ya sauya kayan jikinsa, yana kallon Mami yace "Noory fa..", Mami tace "bata dawo schl ba..", yace "Okay" yana kallon hanyar kitchen kafin ya wuce can din, kitchen din ya shiga bayan few minutes ya fito da plate din Abinci, dining ya wuce ya zauna ya fara cin abincin, saida ya cinye tass don yunwa yake ji ba kaɗan ba tin tea da yasha da safe bai sake cin komai ba banda water, Nurain bai baro gidansu ba sai ƙarfe takwas na dare, a hakan ma sbd Mami ne dan ya lura da irin kallon da take masa ga dukkan alamu tana so ta fadi wani abun ne amma bata fada ba, yana zuwa gida daman a palourn ƙasa yayi branching, yayi powering TV kafin ya zauna kan exclusive sofa dake palourn, almost 30mins da zamansa aka buɗe ƙofar kitchen, da sauri ya kalli direction din, a hankali ta fito daga kitchen din da cup ta ciko da ruwa, ta juya ta rufe ƙofar, ƙishi ruwa ne yasata fitowa tin ɗazu, shine da tazo kitchen ɗiba ciwon cikin ya murɗa mata ta durƙushe a ƙasan kitchen din tana murƙususu har saida taji dama dama snn ta iya tashi ta ɗebi ruwan ta samu ta fito, wani irin haɗe rai Nurain yayi, wato bata ji warning din da ya mata ba knn, how dare her zata ringa masa taurin kai, who born her with her bad attitudes, dole tayi abinda yace indai tana son cigaba da zama a gidan, furiously ya tashi yace "ke ba kiji warning din da na miki ba knn..", hannunta ɗaya riƙe da cup dayan kuma ta dafe cikinta, da kyar ta iya cewa "daman nace maka naji ne.., na riga na gaya maka you can't tell me what to do malam" tana gama fadin haka ta nufi stairs, bata ankara ba taji an fixgota baya ta bige da hannun kujera.....✍️ 💛 HAJAR 💛 na Nafeesah Yusuf Nagoda A.K.A Feenerh feeche {46..} Nurain was extremely angry at that moment, yana mata wani kallon barazana yace "maimaita abinda kika ce..", ta ja da baya zuciyarta na lugude tace "bazan maimaita din ba, idan baka ji ba kai ka sani...", da sauri ta durƙushe ƙasa ta ajiye cup din ruwan ta damƙe cikinta tana murƙususu, fashewa tayi da kuka tana yarfe hannu tace "na shiga uku cikina", tsuke idanunsa yayi ya matsa daga kusa da ita yana kallonta, after looking at her for few seconds yace "hey get up..", banza tayi dashi ta cigaba da kukanta a hankali, folding hands dinsa yayi yace "ke tashi daga nan...", duk da irin azabar da take ji hakan bai hanata ɗaga kai ta zabga masa harara ba, ya koma kan kujera ya zauna gami da ɗaukan remove ya ƙure volume din Tv don baya son ya cigaba da jin sautin kukanta, saida cikin ya lafa mata bayan kamar minti goma ta tashi tana goge fuskarta, ta ɗauki kofin ruwan ta haura sama tana tafiya a hankali, bayanta yabi da kallo bai san lokacin da wani tsaki ya kufce masa ba, ya tashi ya kashe Tvn gaba ɗaya, kitchen ya shiga yana ƙare masa kallo, ya buɗe store ya duba ko ina, yadda ya ajiye foodstuffs haka ya gansu ba a taɓa ba, carton din Noodles kawai ya gani a bude kuma shima pack ɗaya aka ɗauka, ya fito daga storen ya buɗe fridge shima dai babu abinda aka taɓa, ganin bottle water shima ko ɗaya ba'a taɓa ba murya ƙasan maƙoshi yace "what.. toh wane ruwa take sha..", bottle water ya ɗauka ya rufe fridge din snn ya bar kitchen din, upstairs ya haura zuwa part dinsa, direct bedroom ya shiga ya kunna lights, yayi drawing bedside drawer ya ɗauki wani satchet na drug, tashi yayi ya fito daga bedroom din snn ya fita daga part din, tsaye yayi a corridor yana kallon ƙofar ɗakinta, after standing for few seconds ya haɗe gira ya murɗa handle din ƙofar ya shiga, ƙasa ƙasa yayi sallama wanda ta tsaya iya lips, kwance ya ganta kan carpet ta rufa da duvet har ka, ya ƙarasa cikin ɗakin bayan yabar door a wangale, controlling ɓacin ran dake taso masa yayi, chest of drawers ya bubbuga yace "hey", ta yaye rufar da tayi ta tashi zaune, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta, fuskarsa a haɗe ya ƙara four steps towards her, dungurar da bottle water din yayi a gabanta, ta juyo ta kalli ruwan ta ɗaga kai ta kallesa, ya ajiye satchet din drug din yace "take it..", ta haɗe gira tace "bazan sha ba...", one step ya kara getting even more closer to her, tayi sauri ta muskuta ta bada space a tsakaninsu, taɓe baki yayi yace "an gaya miki nayi hakan ne sbd ke, hmm you don't worth it ba dan ke nayi ba, darajar Abba kika ci, tinda an riga an liƙa min ke babu yadda zan iya and now we are living in the same roof, so listen tinda kema kin nace kina son auren nan toh ga fili ga mai doki, zaki zauna anan amma kuma bazaki jamin matsala ba, na fita haƙƙina na ajiye miki foodstuffs, you are free ki shiga kitchen ki dafa abinda za kici idan kinga dama, don babu wanda zai miki gage, secondly you see this room da downstairs palour and kitchen are the only places da kike da damar shiga daga su kar kiyi gigin shiga wani wajen, and if you need anything bance kimin magana ba, ki nemi pen da jotter ki ajiye duk sanda kike buƙatar wani abu ki rubuta ki ajiye kan center table a palour, i will give that idan baki da shi, am done with you...." da haka ya isa gaban mirror ya ɗauki cup din da ta ajiye, girgiza kai yayi yana kallon ruwan kafin ya juyo ya dubeta yace "for your own heath tap water ba shine ruwan sha a nan ba...", ƙofa ya nufa zai fita yaji tace "malam ka gama, dawo ka ɗauki tarkacen da ka zube min a nan who are you to give me drug, kai tinda aka kawoni wnn ƙaddararran gidan na taɓa mka magana ne da farko da kake cewa wani kar na maka mgana, kaga malam nifa ba mara galihu bace da zaka ringa giggillamin sharuɗa sai kace wata ƴarka, ni nan na fika tsanar wnn jarababben auren wllh, da zaka sauwaƙe mna da ka huta..." ta ƙarashe tana murguɗa baki gami da hura siririn hancinta, bai motsa daga inda yake tsaye yana kallonta ba, tana lura da reaction din fuskarsa zuciyarta ta buga da ƙarfi, tayi sauri ta yaye duvet din da ta lulluɓe jikinta ta miƙe tsaye fuskarta a haɗe, lokaci guda ta dubi kanta, kayan bacci ne a jikinta riga da wando, ai kam da sauri ta durƙusa ta yayibi duvet din ta rufe jikinta, kamar me ƙirga takunsa haka ya fara walking towards her, ganin haka yasa ta fara tafiya da baya tana banka masa harara, da gudu ta shige bathroom tana taɗewa da duvet din, tayi sauri ta saka lock tana sauke numfashi, Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana bin ƙofar bathroom din da kallo kafin ya juya ya fita daga ɗakin, jingina Hajar tayi da jikin ƙofa, ta hura hanci tace "Wllh ka gayamin ajali sai na gaya mka mutuwa, haka kurum ba zaka danƙaramin magana nayi shiru na kyaleka ba zuciyata ta buga, kai da kanka zaka koma wajen wnda ya ƙulla wnn jarababben auren ya kunce sa ehe, dan billahillazi la'ilaha illa huwa yanxu na fara musguna maka a gidan nan, kai ka isa ka aureni kai asuwa...", ita kaɗai ta ringa huci sai kace wata kububuwa, bayan kamar minti goma ta buɗe ƙofar a hankali, ta gama surveying ɗakin da idanunta kafin ta fito, tsaki tayi taje ta rufe ƙofarta, tasa ƙafa tayi fatali da bottle water da satchet din maganin dake kan carpet, ta sake yin wani tsakin tayi kwanciyarta, tsakar dare ciki yace ba sai kiyi baccin na gani ba, duk da sanyin AC gumi ne ya ringa tsattsafo mata a goshi, ganin alamar dai cikin nan ba lafa mata zaiyi ba ta tashi zaune, a gigice ta fara laluben maganin tana rarrafe, taci sa'a kam ta hango sa a karkashin mirror, ta ƙarasa bakin ƙofa ta ɗauki ruwan da ta wurga can, da sauri ta buɗe bottle din ta ɓalli 2tablets ta afa a baki ta bisa da ruwa, within minutes Allah ya taimaketa cikin ya lafa, ta ringa kallon satchet din maganin kafin ta tashi ta ajiye bisa mirror ta koma ta kwanta. washe gari wajen ƙarfe takwas da rabi Hajar ta fito daga ɗakinta bayan tayi wanka ta shirya, downstairs ta sauka zuwa kitchen, tana buɗe ƙofar kitchen sukay ido huɗu da Nurain da ke making coffee, da sauri ta rufe ƙofar ta haura sama, Nurain ya kashe coffee makern bayan ya gama haɗawa, zai ɗau cup din Coffeen knn wayarsa ta fara vibrate, da asuba ya dakkota daga mota bayan ya dawo masallaci, ya duba yaga babu wani missed call kuma luckily wacca tasa ya tsani wayar bata kira ba kuma bata turo message ba, ya ciro wayar daga pocket yayi picking ganin Dr Marwan, fita yayi daga kitchen din still yana wayar, Nurain yace "alright send it now..", Dr Marwan yace "Okay", Nurain yace "when is it going to start..?", Dr Marwan yace "12noon insha Allah...", Nurain yace "Neh, i will be there before then..", Dr Marwan yace "thank you Dr..", Nurain ya katse wayar ya haura sama ya shiga part dinsa, Laptop dinsa dake jone a charge ya ciro ya zauna yayi switching dinta on, tana gama booting ya buɗe WiFi, it connected automatically with the house router, ai kam sai ga mail daga Dr Marwan, Nurain ya bude mail din yana duba hoton jiki, almost 30mins yana examining picturen, it is a human chest diagram, a zuciyarsa wondering yake who is this patient with a damage lungs. Hajar ta sake sakkowa ƙasa don yunwa take ji sosai, plain Noodles ta dafa ta juye a plate, tinda ta shigo kitchen din take kallon Cup din dake cike da Coffee, bayan ta gama tafasa tea ta juye a cup ta zuba sugar da lipton, har zata fita da shayi da Noodles dinta a hannu sai kuma ta dawo da baya, ta ajiyesu kan kitchen island, store ta shiga ta ɗakko ledar gishiri ta fito, farke ledar tayi ta ɗauki spoon ta matsa wajen Coffeen, ta zuba cokali biyar cikakku na gishiri a Coffeen tana murmushi, ta mayar da gishirin store ta fito tana kakkaɓe hannunta tace "Asha shayii lfy.. counting from today..." kafin ta ɗauki plate din Noodles da kofin shayinta ta fita. Nurain ya shigo kitchen din bayan fitar Hajar da minti biyu, direct Coffeen sa ya ɗauka, ya ringa kallon coffeen ganin kamar ya ƙara yawa, gashi kuma it is not hot but warm, tinda it is warm he can take it, Sipping yayi domin yaji temp din dai a bakinsa, guntse wanda ya kurɓa yayi ya yamutsa fuska, lokaci guda ya isa gaban sink ya zubar ya kunna tap ya wanke bakinsa, har lokacin wani irin taste yake ji a bakinsa wanda ya kasa gane masa, ya ringa kallon Coffeen kafin ya sheƙar dashi ya bar kitchen din, yana zuwa ɗakinsa ya wuce bathroom ya shiga wanke bakinsa da mouth wash har saida yaji taste din ya ragu sosai. ★Tin daga soro Sa'adatu ta fara zabga sallama harta shiga cikin gida, wani kallon hadarin kaji ta watsawa Umma dake zaune kan ƙaramar kujera tana shafa manja jikin gwangwanaye, ɗakin Maama ta shiga, Maimuna dake zaune kan gado ta bita da kallo tace "kin dawo..?", Sa'adatu ta saki baki tana kallon Maimuna kafin ta yakice hijab din da ta zumbula a jikinta, wasu irin matsattsun kaya ne jikinta wanda ya bayyana shape din bom bom dinta da ƙirjinta, ta zauna kusa da Maimuna ta sake ƙare mata kallo tace "ke kuma wa ya mayar dake wnn mummunar halittar, babur ne ya bigeki...?", Maimuna ta shafa goshinta tace "idan na gaya miki Allah yasa ki yarda.., wai fa Mu'azzam ne yamin haka..", Sa'adatu ta hangame baki tace "Mu'azzam din ne ya miki haka...?", Maimuna da takaici ya kuma maƙureta tace "shifa..", Sa'adatu tace "chaɓɗi jamm, wato har dasu kaza acin danƙo, ke me ya haɗani da wnn jakin har yayi miki haka...?", Maimuna ta kwashe kaf abinda ya faru ta gaya mata, Sa'adatu ta ringa jinjina kai tana hura bubble da chewing gum din bakinta, Maimuna ta kwashe cinya tace "kinga walmukalafatun da Baba yayi min..", Sa'adatu tace "karki yarda wllh tllh, toh aiko shinkafar ɓeran kika zuba iya abinda za a miki knn, karki haƙura wllh..", Maimuna tace "ke ko ce miki akai zan haƙuri zaki yarda ne, dan na rantse da zabbatin Ubangiji bazan yarda ba..", Sa'adatu ta karyar da kai tace "wllh karki haƙura wannan halittar da ya mayar dake ai ya cuce ki, fuska duk ta suntuma, ji fa yadda idanunki suka koma ciki sai kace fuskar biri bukka, kibi dare idan ya kwanta ki rusa masa taɓarya a ka..", Maimuna tace "A'a ni bazan taɓasa da hannuna ba, dafa kuɗina a ƙugu, ƴan daba zan biya su lakaɗa masa duka su sassara banza su jefar a layii", Sa'adatu ta sheƙe da dariya tace "hakan yayi... wai ina Maama da waccan mai kai a tukunyar...?", Maimuna tace "Maama ta fita bansan inda taje ba, Nabilah kuma ta fita auno shinkafa...". babu jimawa Maama ta shigo gidan bayan ta dawo daga gidan Balaraba, ganin Sa'adatu Maama ta yaƙe haƙora tace "Sa'adatun Maama kin dawo...?", Sa'adatu tace "nadawo Maama..", Maama tace "ai kinga haka yafi kin cika alƙawari, kinga gobe ma sai nasan ƙaryar da zan shiryawa malam idan ya tambayeki, ina ƴan albarkar ƙawayen naki kuwa...?", Sa'adatu tace "suna nan kalau Maama sunce ma na gaisheki..", Maama ta washe haƙora tace "Ahh ina amsawa kuwa..", Nabilah ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda, kallo daya ta yiwa Sa'adatu ta ɗauke kanta, hijab dinta ta cire zata fita Maama tace "haba Annabilatuwa biki ga ƴar uwarki ba", Nabilah ta juyo tace "Au sannunta toh" da haka ta fice a ɗakin, gawayi ta zuba a kurfotu ta tashi wuta, tana fifita wutar Naseer ya shigo, ta masa sannu da zuwa ya amsa a taƙaice, Maama ta leƙo tace "A'a Nasiru sannu da zuwa..", Naseer ya ajiye doyar da ya shigo da ita ya russuna ya gaisheta, Maama tace "lfy lou, ya wajen aikin..?", yace "Alhmdllh an gode Allah..", bai tambayi Baba ba sbd yasan dai a wnn lokacin Baba ya fita aiki, ganin haka yasa Nabilah tace "Yaya Baba yana nan fa..", yace "toh" ya shiga ɗakin Baban da Sallama, Maama ta zabgawa Nabilah wata harara tace "naga ranar da wnn munafikin canjin naki zai ɗore..", bayan Naseer sun gaisa da Baba yace "Baba ko dai jikin ne..?", Baba ya numfasa yace "Nasiru duk ranar da kuka wayi gari bani toh mahaifiyarku ce sila..", Naseer ya kasa cewa komai tsabar ydda mgnar Baba ta dakesa, can dai yace "Ayi haƙuri Baba, Allah ya huci zuciyarku..", Baba yace "haƙuri ai ya zama dole tinda ta gama zubamin virus ta haifeku...", Naseer dai kawai haƙuri ya ringa basa duk da cewa bai san me ya faru ba. ★Kamar yadda Nurain yace kafin 12noon zai iso hospital, 11:40 ya isa hospital din, yana shiga office dinsa yasa Haleema ta kira masa his team members, har zai wuce sai kuma ya dawo yace "exclude A Nurse, call Nurse Amina instead..", Haleema tace "yess sir", ta ɗauki landline ta shiga kiran members din, babu jimawa kam All of them suka hallara a office din, Nurse Amina ce kawai ba tazo ba, briefing dinsu Nurain yayi akan surgeryn da zasu shiga, daga nan suka fita to get ready, Nurain na wanke hannunsa kafin ya shiga surgery room din Khaleel ya da already dressed up in surgeon gown da nose mask a fuskarsa amma bai rufe hancin ba ya iso wajen yace "Boss everyone is here banda Nurse Amina, kuma i informed her tace tana zuwa..", Nurain na cigaba da wanke hannunsa yace "lets wait for her since the surgery is not yet started...", Khaleel yace "sure..", Nurain na gama wanke hands daman already ya sanya surgical Scrub. Surgery room din ya shiga, wani Nurse dake riƙe da surgeon gown ya ƙaraso kusa da shi helping him to wear the gown, Nurain ya saka nose mask da hand gloves kafin ya isa position dinsa na head of the surgery ya tsaya, patient din daman tintini aka masa anesthesia. Ruqayyah na zaune Nurse station duk abin duniya ya isheta, tinda tazo babu wani aikin arziƙi da tayi kawai safa da marwa take tsakanin Nurse station da Office din Nurain, taje office din yafi sau biyar saita tarar baizo ba, Nurse Amina ce ta shigo station din in a hurry tace "please Ruqayyah ki kulamin da ward C ina dawowa..", Ruqayyah tace "ina zaki haka..?", Nurse Amina ta dafe goshinta tace "Dr Uthman ne yake nemana a surgery room..", miƙewa Ruqayyah tayi tace "surgery zaiyi knn..?", Nurse Amina tace "eh..", wani irin ɗaci Ruqayyah taji ya taso mata daga zuciya, she is part of the team toh me yasa ake neman wata Nurse din bayan gata, Nurse Amina tace "Please Rukky..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "A'a gaskiya bazan kula miki da ward ba saidai ke ki zauna in shiga surgeryn", Nurse Amina tace "ai kwa da na fi son hakan ma, nagode sosai..", Ruqayyah tace "don't mention" da haka ta bar station din walking fast, surgery gown ta ɗora kan uniform dinta ta saka nose mask da gloves kafin ta shiga surgery room din kanta a ƙasa, with respect ta ɗan russuna tace "sorry Dr..", Khaleel yace "come closer..", ta ƙarasa ciki tana satan kallon Nurain, surgery tray ta dauka ta tsaya position dinta, ta ɗauki Scalpel ta miƙawa Nurain, da haka aka fara surgeryn, kawai aikinsa yake cike da nutsuwa yayinda Ruqayyah ta kafa masa idanu tamkar zata cinyesa, wani sa'in ma sai yace ta basa instrument snn take basa sbd rashin nutsuwa, a haka dai har suka gama surgeryn, bayan an fita da patient din sauran doctors din ma sun fita Nurain ya cire hands gloves yayi disposing, sauke nose mask din fuskarsa yayi ya wuce zai bar room din, Ruqayyah tace "Dr...", ya juyo yace "yess Nurse Amina...", idonta yayi rau rau ta kai hannu ta zame nose mask dinta....✍️ Arewabooks @ feenerhfeeche02 💛 HAJAR 💛 Feenerh feeche ce {47..} Da mamaki Nurain ya ringa kallonta dan bai taɓa tunanin da ita akay surgeryn ba Nurse Amina ba, Ruqayyah ta sauke idonta ƙasa a hankali tace "the surgery was a success, alhmdllh..", baice mata ƙala ba ya juya ya fita daga surgery room din ya barta tsaye, tabi bayansa da kallo hawayen da suka taru idonta suka fara bin kuncinta, fita tayi daga room din bayan ta gama matsewa, ta cire surgeon gown kafin ta wuce Nurse station, bag dinta ta buɗe ta ɗauki black Abaya ta ɗora saman uniform dinta, daga haka ta saƙala jakarta a shoulder ta yiwa colleagues dinta sallama ta bar hospital din, tana fita titi ta tari napep ta gaya masa unguwar da zai kaita, shiga napep din tayi bayan sun gama ciniki, tafiyar minti ashirin ce ta kaisu unguwar, ya shiga da ita har layin da ta masa kwatance, sauka tayi daga napep din ta buɗe handbag dinta ta ciro kuɗinsa ta basa, ya miƙa mata chanjinta yaja machine dinsa, wani gida mai brown paint da black gate ta dosa ta fara knocking, almajirin gidan ne ya buɗe mata, bayan ta shiga ya gaisheta ta amsa a takaice kafin ta nufi entrance din gidan, ta buɗe ƙofa ta shiga palour da sallama, ƙarewa palourn dake tashi da ƙamshin turaren wuta gauraye da na freshner kallo take sai kace wani baƙonta, ta sake yin wata sallamar kafin ta zauna kan kujera, ƙofar wani room dake palourn aka buɗe, Kulsoom ta fito da 2months old babyn ta goye a baya tana jijjigasa, ganin Ruqayyah tace "Ruqayyatu kece kika ta sallama sai kace wata baƙuwa..", Ruqayyah ta cire ƙaramin hijab dinta tayi resting da kujera tace "ina wuni sister..", Kulsoom ta ƙaraso cikin palourn tana jijjiga babyn dake ƙishi ƙishin kuka tace "mun yini lfy...", Ruqayyah tace "alhmdllh..", Kulsoom na kallon fuskar ƴar uwarta ta da ta lura tayi duhu tace "kin kwaso rana..", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya tace "kawosa naga kamar kuka zaiyi..", Kulsoom ta kwanto babyn ta miƙa mata tace "rigimamme ne wllh.." da haka ta wuce kitchen, Ruqayyah ta ringa kallon Babyn kafin ta lakuce masa hanci tace "shine kake wa sister na kukan banza ko, tubarkallah ga ka dai narkeke sai kace ba watanka biyu ba bare ace yunwa kake ji", ta ringa patting soft cheeks dinsa, deeply in her mind taji dama babyn ta ne, da anyi aurenta da Dearest da tini itama ta kusa haifar baby, Kulsoom ta fito kitchen da tray a hannunta, ajiye trayn tayi kan Centre table tace "toh ga ruwa kisha kafin na gama girki na ga kinyi wani wujiga wujiga...", Ruqayyah tace "na gaji ne, kuma gashi na shiga surgery yau na 3hours", Kulsoom dai ta gyaɗa kai tace "Okay", a ƙasan ranta tasan bayan gajiya akwai damuwa a tattare da Ruqayyah, Ruqayyah ta zuba ruwa tasha tana jin yadda sanyin ruwan ya sanyaya mata maƙoshi, bayan kamar 15mins Kulsoom ta tashi ta shiga kitchen, babu jimawa ta fito da plate da bowl a hannunta, Ruqayyah ta ringa kallon abincin tana jin appetite dinta na dawowa, lafiyayyen dambun shinkafa ne wanda yaji attaruhu da albasa da gyaɗa yana bayar da wani ƙayataccen aroma, sai kuma coleslaw a bowl, Ruqayyah ta janyo abincin tana ci a hankali, kallonta Kulsoom ta ringa yi tana feeding babyn ta, saida taga ta ture plate din alamar ta ƙoshi tace "kin gama....?", Ruqayyah tayi gyatsa tace "alhmdllh, godiya dubu..", Kulsoom na shafa kan babyn ta looking at Ruqayyah tace "now tell me, me yake damunki sister...?", Ruqayyah ta zaro ido tace "Ni.. me kika gani..?", Kulsoom ta saka serious face tace "haba Ruqayyah nifa ƴar uwarki ce na sanki ciki da bai, wllh there most be something troubling you, ji fa yadda kika rame kuma kinyi duhu ai ba haka hasken ki yake ba..", Ruqayyah bata san lokacin da hawaye ya fara zuba cheeks dinta ba, Kulsoom ba tace komai ba kawai kallonta take, Ruqayyah ta share hawayen tace "tin lokacin da na dawo Daddy ya yankamin warning cewa na fito da miji shi aurar dani zaiyi idan kuma banyi hakan ba zai aura min Dauda, Dauda fa wnn mai bacogalar ƙafar, da kyar da maƙyarƙyata na shawo kan Momy ta shigemin a wajen Daddy bayan na shirga mata ƙarya nace ai mun sasanta da Dr, idan ya dawo daga tafiya za a ɗaura mna aure, da haka na samu abubuwa suka lafamin a wajen Daddy, sister wllh na gama sakankancewa ina tutiya da irin son da Dr yake min kawai jira nake ya dawo na basa haƙuri, and now he is back almost 2weeks da dawowarsa, nayi kiran a waya na tura text message amma duk a banza, babu kalar haƙurin da ban rubuta a message na tura masa ba amma he didn't respond to any of it, ke na ƙarƙare miki mgana jiya har office dinsa naje ina basa haƙuri amma yaƙi saurarata, daga ƙarshe ya kiramin security, yau kam he kick me out of the surgery team..", Ruqayyah ta fashe da kuka tace "wllh Allah ina sonsa, i can't live without him Allah kuwa..", Kulsoom ta jinjina kai ta kwantar da Babyn da ta gama feeding tace "gsky kinyi babban kuskure da kika yiwa Momy ƙarya Ruqayyah..", Ruqayyah tace "toh ya zanyi sister dole ce tasa na mata ƙaryar nan, da banyi haka ba da tini an wuce wajen an auramin Dauda bacogala..", Kulsoom tace "ke kika fusata Daddy shiyasa ya kafe sai ya aurar dake, Ruqayyah yau inda ace baki aikata abinda kika yi ba wllh kinji dai har na rantse babu abinda zai sa Daddy ya miki auren dole, zai dauka cewa Allah ne bai kawo lokacin aurenki ba, amma akazo akay komai da komai ranar ɗaurin aure kika kwashi ƙafa kika gudu...", Ruqayyah ta kastseta da faɗin "wllh ba guduwa nayi ba..", Kulsoom ta haɗe gira tace "let me land malama, idan ba guduwar ki kay ba toh uban me ki kai, yanzu dai ina baki shawara kije ki gayawa Momy cewa ƙarya kika shirga mata snn kuma ki haƙura da wani Dr, yo Allah na tuba mazan yanzu har wasu abin so ne, an gaya miki in this era ana yiwa namiji makahon so ne, namiji ya soka ma yaka ƙare da wulaƙancin sa ballantana wanda ya fito ra'ayil aini ya nuna baya sonka, idan Dr ya soki a baya toh yanzu ba hakan bane, ai kin masa narkakken wulaƙanci ba ƙarya duk abinda ya miki ke kika siya da kuɗinki, so wake up malama ki san inda yake miki ciwo, kin zauna kina wani ɓare baki kina kuka shaɓa shaɓe akan wani namiji.... ehen ki ajiyesa a gefe ko shine autan maza", tinda ta fara magana Ruqayyah ta saki baki hanci kunne tana kallonta tamkar wata psycho, idonta har wani wulƙilewa yayi tsabar yadda take kallon Kulsoom cike da ruɗin abinda ta gaya mata, Dearest din zata ajiye a gefe, da kyar ta iya cewa "wai doctorn zan ajiye a gefe..?", Kulsoom tace "yhap shi din mna tinda kinyi loosing opportunity tin farko...", Ruqayyah ba ta sake cewa komai ba ta fara haɗa kayanta, ta saka wayarta a jaka, hijab dinta ta sanya kafin ta miƙe ta fara zura Abaya, Kulsoom ta bita da ido, Ruqayyah na gama saka Abayar ta ɗauki handbag dinta tace "sai anjima", Kulsoom ta taɓe baki tace "mu jima da yawa..", ficewa Ruqayyah tayi daga gidan fuskarta a haɗe, da badan Kulsoom ƴar uwarta bace da babu abinda zai hanata danƙara mata baƙar magana, kuma taci sa'a elder sister dinta ce yau da ace itace gaba da Kulsoom to babu abinda zai dakatar da ita daga kwalla mata marii, wai ta ajiye Dearest a gefe wato ta rabu da shi, never ever babu abinda zai sa ta rabu da shi sai mutuwa, tana isa bakin titi ta tari napep zuwa gida. ★Hajar ta gyara ɗakinta fes bayan ta gama cin Noodles da ta dafa, ta rufe ɗakin ta sauka downstairs zata kai plate da cup din da tayi amfani dasu kitchen, gaban sink ta tsaya tana kallon liquid soap dake wajen, ta kunna pampo ta matsa liquid soap din a plate ta tashi foam, sponge ta dauka ta fara wanke utensils din da ta ɓata, tass ta wankesu ta kife a inda ta ɗauka, duk da kitchen din babu datti amma saida ta sake gyarasa, tayi drying hannunta da towel kafin ta fita daga kitchen din, room dinta ta koma tayi zugum sai kace wata prisoner, can dai ta gaji da zaman daƙin ta tashi ta fita, ta kitchen tabi ta fita daga gidan zuwa backyard, through out the day anan tayi zamanta kamar dai jiya sai idan za tayi sallah ne take komawa ciki, bayan ta idar da sallar la'asar ta birkito kayan da ta saka set biyu sai nities da hijab biyu, toilet ta shiga da kayan ta zazzaga detergent a bucket ta shiga wankesu duk da cewa ba suyi wani datti ba, tana gama wankewa ta ɗauraye toilet din ta fito da kayan cikin bucket, can backyard din ta wuce ta shanya kayan jikin flowers, tana cikin shanyar saiga mai gadi da watering can a hannunsa zai bawa flowers ruwan yamma, dan russunawa yayi ya gaisheta ta amsa kafin ta ɗauki bucket din tabar wajen dan ta gama shanyar, tana shiga palour taji kamar ana buɗe main door din gidan, ta ringa kallon ƙofar har aka buɗeta, Nurain ne ya shigo Farooq biye dashi, suna yin ido huɗu tayi sauri ta ɗauke kanta ta wuce zata haura sama taji ance "Amarya..", dakatawa tayi amma bata juya ba, Nurain ya wurgawa Farooq wani kallo kafin ya wuce ya haye sama, Farooq ya ɗaga shoulder ya ƙarasa cikin palourn, a hankali Hajar tace "ina yini..", Farooq yayi murmushi yace "lfy lou amarya.. how are you..", tace "am fine thank you.." da haka ta nufi stairs ta haura sama, Farooq ya zaune kan kujera ya ciro wayarsa daga pocket yana latsawa, after 20mins yana zaune palourn ya daga kai yana kallon stairs, contact ya shiga yayi dialing numbern Nurain har ta gama ringing bai ɗauka ba, babu jimawa saiga shi nan yana sakkowa, Farooq ya ringa kallonsa har ya ƙaraso palourn yace "muje..", Farooq bai motsa ba yace "daga ɗakko paper saika tsaya wanka kuma..", Nurain ya nufi door yace "c^mon let go..", Farooq na fitowa Nurain ya rufe ƙofar da mukulli, shidai Farooq yana so yace wani abun amma dai ya fasa, a tare suka nufi gate, Inuwa dake zaune nan bakin gate din yayi saurin miƙewa har suka ƙaraso, russunawa yayi ya gaidasu duka, shidai bai san lokacin da suka shigo ba sbd a lokacin ya tafi can backyard, Nurain yace "ba wanda yazo..?", Inuwa yace "Eh Alhj..", Nurain yace "Okay, zan sake fita sai na dawo..", Inuwa yace "Allah ya tsare..", Nurain yace "Ameen" ya buɗe ƙofa suka fita gidan da Farooq, motarsa da ya parker nan waje ya bude ya shiga, Farooq ya shiga front seat, tada Motar Nurain yayi ya fara driving out of the street, suna hawa main road Farooq yace "Allah yasa dai ba rufe yar mutane kake a gida ba..", banza Nurain yayi dashi kamar baiji ba, Farooq ya sake cewa "kaga idan ma rufeta kake to ka dena dan naji Mami tayi complain akan hakan a asibiti..", still Nurain bai tanka masa ba kawai driving dinsa yake, Farooq ya gyara zama yace "if i were you banza zanyi da rayuwa wllh, tini zan saki jikina with my cutie wifey, the girl is so cute...", Nurain ya ƙara speed din motar kafin ya juyo ya dubi Farooq yace "really, tinda she is cute idan kana sonta sai in saketa kawai ka aureta punk...", Farooq ya haɗe gira yace "you're not serious...", Nurain yace "am jet serious..", da wani irin expression Farooq ya ringa kallonsa ya kasa cewa komai, Nurain ya juyo sukay ido huɗu, ganin reaction din fuskarsa Nurain yayi murmushi, Farooq ya fara latsa wayarsa bai sake cewa komai ba har suka je inda zasu, 40mins suka ɗauka a wajen kafin suka gama abinda za suyi suka fito, bayan sun shiga Mota Farooq yace "dude you have to make this thing serious, container nawa ce zata sauka..?", Nurain yace "three.. next month", Farooq yace "Ohk..", Nurain yace "lokacin da nake India naje China nayi order dinsu, you know shipping zasu jima basu zo ba..", suna zuwa wani junction Farooq yace "drop me here..", Nurain yace "bari nayi dropping dinka gida mna..", Farooq yace "i have another appointment..", Nurain yace "Ohk", Farooq ya buɗe motar ya sauka. Nurain na zaune main palourn gidansu bayan ya dawo daga masallaci sallar isha'i, Noor ta shigo palourn da Laptop dinta a hannu, ta zauna a gefensa tace "Yaya please duba min..", keenly yace "Ohk..", kunna Laptop din tayi ta shiga slide din, duba mata ya fara yi inda akwai gyara sai ya nuna mata ta goge ta gyara, resting yayi jikin kujera ya lumshe idonsa, Noor ta gama typing mistake din da ya gyara mata tace "Ya am done..", yace "get me something to eat first..", tace "tom" ta tashi ta shiga kitchen, abincin da aka dafa na dinner ta zubo masa, ta haɗo da ruwa da lemo ta kawo masa a tray, saida ya gama cin abincin snn suka cigaba, Mami ce ta shigo, tayi still tana kallonsa kafin ta dubi wall clock dake palourn da ya nuna 9:20 dot, Mami ta kalli Plate din abincin da ya gama ci, tini taji wani iri a ranta, sau uku knn, Mami ta ƙaraso kusa dasu tace "Nurain me yasa kake dare ne baka tafi gida ba, i thought ka tafi ma since..", ya shafa kansa a hankali yace "ina dubawa Noor project dinta ne...", Noor tayi saurin cewa "we will continue tomorrow then Yaya, thank you..", Nurain ya miƙe yace "Mami saida safe..", without looking at him Mami tace "Ohh Allah ya tashe mu lfy..", Noor tace "Yaya ka gaida Hajar Please..", ya gyaɗa kai kawai da haka ya fita, Mami na kallon Noor tace "wane yaci abinci..?", Noor tace "Yaya ne", Mami ta wuce part din Abba dan daman nan ta fito shiga, Noor ta kwala kiran mai aiki, Laure ta fito daga kitchen tace "gani hajiya ƙarama..", Noor tace "Please gyara nan wajen", Laure ta dauke trayn ta shiga kitchen. ƙarfe tara da minti arba'in a gida ta yiwa Nurain cause gudunsa ya falfala a mota, kuma yana shiga gidan daman Kitchen ya wuce, yaufa gaba ɗaya bai sha coffee ba shiyasa yake jinsa moody, kuma bazai iya bacci bai sha ba, ya buɗe Cupboard ya ɗakko Coffee powder yana sake duba expire date, coffeen da ya sha da safe was the worst coffee ever da ya taɓa sha, shine yake duba expire date wai ko powdern tayi expire shiyasa yaji na safe da ya hada rotten, still dai wani sabon pack din ya buɗe cause bai yarda ba kar yaje daga powdern ne, da sauri ya dubi window ganin kamar mutum ya gifta, ya ƙurawa windown ido yana mamakin abinda ya gani, ƙofar kitchen wacca ta fita ta backyard aka buɗe, rumgume da kayanta da ta wanke ta shigo, ta ɗan firgita ganinsa a kitchen din sai kuma ta haɗe rai ta wuce, ta buɗe ƙofar shiga cikin gidan ta shiga palour, Nurain ya ringa kallon ƙofar backyard din, jinjina kansa yayi ya fita kitchen din, ya haura sama ya shiga part dinsa, drawer da ya ajiye kaff spare keys din gidan ya buɗe ya ɗauki guda ɗaya kafin ya fito ya koma kitchen din, ya gama making coffee ya juye a cup, ya matsa gaban ƙofar backyard din ya zura key din ya kulle, saida ya tabbatar ta rufe gamm snn ya cire key din, ya ɗauki Cup of Coffee dinsa ya bar kitchen din bayan ya kashe lights....✍️ 💛 HAJAR 💛 by Feenerh feeche {48..} Washe gari tinda Hajar ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba sbd da wuri ta kwanta jiya, tana kwance kan carpet ta rufa da duvet da wayarta ta buɗe Alqur'anin tana karantawa, sai ƙarfe bakwai da rabi ta ajiye karatun, linke duvet din tayi ta maida kan bed, shima pillow da ta tada kai ta mayar dashi gado, bathroom ta shiga dan yin wanka, minti ashirin ta ɗauka tana wankan kafin ta fito ɗaure da towel da yazo mata har guiwa, sai ƙamshin tsadadden showel gel da tayi wanka ne ke tashi a ɗakin, gaban mirror ta tsaya kafin taja stool ta zauna, body lotion ta janyo ta fara rubbing a jikinta, a hankali take shafa man tunani iri iri na amsawa a brain dinta, da sauri ta dubi ƙofa jin alamar za a shigo, ido huɗu sukay da Nurain, yana riƙe da handle din ƙofar, Hajar ta zaro ido kafin ta fasa ƙara ta fara kare jikinta, ya ɗauke kansa fuskarsa a murtuke, da wani irin zafin nama ta tashi daga kan stool din ta wafci hijab dinta ta saka, ƙarasa shigowa ɗakin yayi ya ajiye pen da jotter din hannunsa, da haka ya doshi ƙofa zai fita, Hajar da jikinta yake mugun rawa sbd tinda take babu wani namiji da ya taɓa ganinta a haka, har ruwa idonta ya kawo, da kyar tace "malam ka dena shigo min haka nan without notice...", fita yayi daga ɗakin, ta bisa da sauri ta tsaya bakin ƙofa tace "kai da Allah da ka shigo min babu sallama...", tana kallonsa ya shiga part dinsa, ta juya ta koma ɗakinta zuciyarta na tafasa, wani irin yamutsa fuska tayi sbd kawai ƙamshinsa da ya bari ne ke tashi a ɗakin, ƙamshin da sam baya mata daɗi, ta ɗauki freshner ta hau feshe room din amma duk da haka pure men scent dinsa bai disashe ba, Shafa man da bata ƙarasa ba knn ta buɗe wardrobe ta ɗauki kaya ta saka, har ta gama shiryawa zuciyarta ba ta dena tafasa ba, knn yaga bati, a fili tace "shi ya isa yaga bati, wllh Allah ban yafe ba..", gaban mirror ta koma ta ringa kallon jotter da pen din da ya ajiye, ta taɓe baki kafin ta ɗauki biron, rubutun da bai wuce 5lines tayi ba ta yage papern tayi folding dinta, da papern a hannunta ta sauka downstairs, ta wurga takardar kan Centre table tace "wnn kaɗai nake buƙata a wajen ka malam..", kitchen ta shiga dan samawa kanta abinda zata ci, ta buɗe fridge tana kallon fresh vegetables dake ciki, ta rufe fridge din kafin ta buɗe freezer wacca take cike da nama da chicken ga kuma fish duk frozen, shawara ta yanke akan cewa anjima za tayi stew saita ajiye a fridge ta ringa amfani da abarta na ƴan kwanaki, ruwan shayi ta tafasa ta soya kwai guda biyu da haka tabar kitchen din, bata haura sama ba ta zauna nan palour, Centre table da Tv stand da kujerun duk sunyi ƙura, tin ranar da Hafsah ta gyara palourn rabonsa da ganin tsintsiya, taɓe baki Hajar tayi tace "uhmm tinda ba ubana ne ya zuba ba babu abinda ya shalleni..", ta ɗauki kofin shayinta ta fara sha tana gutsirar kwai, tana gama cin abincin ta tashi ta shiga kitchen, ta wanke kwanukan da ta ɓata ta mayar dasu position dinsu, tin kafin ta gama wanke wanken ma take kallon ƙofar backyard, Alla alla take ta gama ta fita can ta ɗan sarara, bakin door din ta isa ta murɗa handle, sake murɗa handle din tayi da ɗan ƙarfi jin ƙofar taƙi buɗewa, lokaci guda ta saki handle din ta kafawa ƙofar ido, shiknn a kulle take, sosai ranta ya ɓaci dan zaman backyard din nan sosai yake rage mata kaɗaici, ranta duk ba daɗi ta bar kitchen din, main door ta ringa attempting buɗewa itama dai a rufe. tinda aka kawota gidan duk wnn ranar tafi mata zafi, baccin rana ma kasawa tayi, babban abinda yafi tsaya mata a rai bai wuce na safe da ya shigo mata ba, bayan tayi sallar la'asar ta kira Umma, gaisawa sukay Umma ta tambayeta ya take, Hajar dai tace lfy amma dai a ƙasan ranta ba haka bane, har Sabra ta tambaya tana cewa yaushe za a kawo mata ita, Umma tace mata ba yanzu ba, da haka suka kashe wayar. ★Nurain na zaune bisa executive kujera dake office dinsa bayan ya gama attending last patient, ƙofar office din aka buɗe aka shigo, ya ajiye plastic heart like da yake wasa da ita ya ɗaga kai ya dubi wanda ya shigo, lokaci guda ya haɗe thick eyebrows dinsa, da sauri Haleema ta shigo office din itama gaba ɗaya a ruɗe take, ta kalli Ruqayyah tace "Maam please get out..", ko kallonta Ruqayyah ba tayi ba ta isa gaban table tana kallon Nurain tace "i can stand any humiliation as far as zaka saurareni Dearest....", Nurain ya maida dubansa ga Haleema yace "amm me na gaya miki ne...?", with due respect Haleema tace "don't let her in..", Calmly as if speaking to himself yace "bayan nan..?", Haleema tace "call security..", ya gyaɗa kai yace "good.." kafin ya ɗauki heart din da ya ajiye ya cigaba da wasa da ita, Haleema ta fita daga office din da sauri, Ruqayyah ta zauna kan ɗaya daga kujeru biyu dake gaban table din, kallonsa ta ringa yi babu ko ƙiftawa, kifa kanta tayi da table din ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "na haɗaka da Allah, na haɗaka da manzon Allah, please talk to me Dearest, ko scolding dina kayi that will be better amma...", ta kasa cigaba da maganar tana kuka sosaii, a hankali yayi baya da kujerarsa ya tashi salum alum ya nufi door ya buɗe ya fita, Ruqayyah ta ɗago kanta ta bisa da kallo da jajayen idanunta, Office din Dr Marwan ya wuce, Dr Marwan na kallonsa yace "is there any problem Dr..?", Nurain yace "not at all, how is the patient..?", Dr Marwan yace "alhmdllh he is recovering gradually..", Nurain ya gyaɗa kai yace "how about his vital..?", Dr Marwan yace "great, Khaleel ya duba not too long ago", Nurain bai sake cewa komai ba yayi resting jikin kujerar, after few minutes of silence Dr Marwan yace "naji ana maganar Seminar wacca za aje Abuja nan da 1month, all thoracic surgeon must be there..", Nurain yace "am not going..", Dr Marwan yace "why..?", Nurain ya ɗaga shoulder yace "kawai.." da haka ya dubi wrist watch dinsa, tashi yayi ya yiwa Dr Marwan sallama, yana fita daga department din ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Haleema, tana picking yace ta kawo masa briefcase dinsa yana parking lot, da haka ya kashe kiran ya cigaba da tafiya zuwa inda ya parker motarsa, buɗe motar yayi ya shiga, babu jimawa saiga Haleema da briefcase din tasa, ya amsa ba yabo ba fallasa yace "thank you..", tace "am so sorry sir about what happened, i tried to stopped her...", ya ɗaga mata hannu yace "it's okay..", tace "thank you sir", murmushi kawai ya mata ya sauke handbrake yaja motar yabar harabar hospital din, driving kawai yake saman titi amma bai san inda ya nufa ba, lokaci guda yayi murmushi yace "ironlady..", yana zuwa wani roundabout ya juya kan motar, yana zuwa gidan ya danna horn, mai gadi ya buɗe masa gate ya shigar da motar, fitowa yayi daga motar bayan ya gama parking, ta baya yabi inda direct nan ne zai kaika part din Hajiya, da sallama ya shiga palourn Hajiya, Hajiya na zaune kan darduma ƴar dattijuwar mai aikinta tana yanka mata papaya, Hajiya ta kalli Nurain ta saman kantamemen glasses dinta tace "ywwa ga likita ma Allah jefomin daga sama, Usuman cikina ne ya ɗaure kwana biyu ban kewaya ba, toh duk ya dameni ji nake kamar anyi min jeren marmaroni a kyuiɓi ko isasshen bacci bana samu, dana gaji da azaba shine nasa Umaru ya kwaso min gwanda kwallo uku, na sha kwallo guda da safe yanzu ma gashi ana yankan wata zan shanye, da daddare in Allah ya kaimu a yanke min gudar da ta rage itama na shanye, ai idan nayi hakan na huta da jarabar basir din nan, ba kaga da yaya na shanye wacca aka yankan da safe ba, cikina har baya kamar zanyi amai amma kuma ai lfy nake nema, yanzu haka har na fara tararrabin yadda zan shanye wnn..", Nurain yayi still yana sauraronta kafin ya samu waje ya zauna yace "karki sake shan wata ta safen is Okay..", Hajiya tace "Allah ko idan na sake sha zan iya tsurewa knn...?", ta dubi mai aikin tace "ke Asabe maza fita da ita duk warinta ya cikan hanci, kije can ki shanye rabonki ce", mai aikin ta ɗauki plate din papayan tayi waje da ita. Hajiya tace "na ganawa kaina azaba har yanxu gyatsar wnn aba nake, kai ina jin ma harna koma ga mahalicca na bazan sake shan gwanda ba duk ta gundureni", Nurain yace "ba kya jin komai daga wnn...?", tace "A'a ƙalau nake Usuman, haka kurum nace maka wani waje na min ciwo ka samu hanyar da zaka fara zuba min allurai..", yace "toh shknn tinda lafiyar ki ƙalau..", Hajiya tace "toh madallah ya gyatumar taka.." sai kuma ta tsuke baki tace "ji wani sakarci nida zan fara tambayarka matarka kuma na tafi wani wajen, Mami ai ba gida ɗaya kuke kwana ba yanzu..", shi dai baice mata komai ba, bayan ƴan mintina yace "bari na gaida Ummi.." da haka ya tashi ya buɗe wata ƙofa ya shiga, luckily ya tarar da Ummi na palour, ya gaisheta with respect, amsawa tayi tana tambayarsa aiki da iyali, shi dai ya shafa kansa ya amsa a takaice kafin ya mata sallama ya bar palourn ya koma na Hajiya, babu jimawa da zamansa saiga Abinci Ummi tasa an kawo masa, sosai Nurain yaji daɗin hakan, plate ya ɗauka zai zuba abincin Hajiya tace "wai ci za kayi kai Usuman na matarka fa..?", yace "shima zanci", ya faɗi hakan ne dan ya huta da surutunta ta barsa lfy yaci abincin kar ya dawo masa ta hanci. tin ɗaya da rabi sai uku da arba'in Nurain ya bar gidan, bai jira Farooq ba sbd baya dawowa aikin da wuri cause na Company ne. gidansu ya wuce, yana gama parking motarsa yaji ana kiran sallah, yayi amfani da tap dake compound yayi alwala ya wuce mosque, bayan ya dawo masallaci ya shiga ciki, part din Mami ya shiga ya gaisheta kafin ya fito ya haura room dinsa. bashi ya sakko ba sai biyar saura shima sbd Noor ne wacca ta takura masa akan project dinsa, saida sukay chapter biyu snn ranta yayi fari tinda saura ɗaya ya rage su gama. ƙarfe bakwai da arba'in Nurain ya shiga wajen Mami, attention dinta ta mayar kansa, Nurain yace "Mami saida safe ni zan wuce..", Mami ta dubi agogo ganin lokaci tace "yawwa toh Allah ya tashemu lfy, ka ringa tafiya gida da wuri ai yafi son..", ya shafa kansa yace "tom Mami", Compound ya fita ya shiga motarsa, ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Noor, tana picking yace "yi sauri malama", tace "Yaya gani nan..", few minutes saiga tanan ta ɓillo ta can baya da basket a hannunta, ta buɗe front seat ta ajiye basket din ta rufe door, Nurain ya gyara zama ya tada motar. saida ya tsaya wajen suya ya siyi kaza snn ya wuce gida, fitowa yayi daga motar yana amsa sannu da zuwan da mai gadi yake masa, ya buɗe front seat ya ɗauki basket din kafin ya nufi main building din gidan, keys ya ciro daga pocket ya buɗe door ya shiga ya mayar ya rufe still da muƙulli, ajiye basket din yayi nan palour kafin ya haura sama, wanka yayi ya saka Pajamas masu sweat pant masu shegen kyau, downstairs ya sakko da room slippers a ƙafarsa, kamar ce masa akay ya kalli wajen, ya ringa kallon papern dake kan Centre table, haɗe gira yayi kafin ya ɗauki papern ya buɗe a wulaƙance, beautiful handwriting din dake jiki ya fara karantawa.... "malam wai an gaya maka inada wata buƙata ne a wajenka in banda guda ɗaya, kawai ka sauwaƙe mana shine buƙatata..", tsaki yayi ya cukuikuiye takardar ya wurgar da ita, wani irin ƙauri ya fara perceiving, da sauri ya nufi kitchen, yana buɗewa yaja da baya ya toshe hancinsa, gaba ɗaya kitchen din ya gumame da hayaƙi da uban yaji, da hannu ɗaya ya rufe hancinsa ɗayan kuma ya ringa kore hayaƙin har ya samu ya shiga kitchen din, gaban cooking gas ya isa yana ƙoƙarin kashe wutar amma da yake hayaƙi yayi yawa baya gani sosai hannunsa ya jogali tukunya, da sauri ya janye hannun ya riƙe da other din, hkan ce tasa yayi perceiving ƙaurin har cikin lungs dinsa, tini ya fara tari at same time yana ƙoƙarin kashe gas din. Hajar ta saki pillow din hannunta bayan brain dinta ta amsa, shaf ta manta da kayan miyar da ta ɗora akan wuta, bata tsaya bi takan wani hijab ba ta gyara hular kanta ta fito daga room din, da sauri ta ringa sauka stairs har tana tuntuɓe, tin daga palour ta fara tari ga uban hayaƙi da ya rufe mata vision, gadan gadan kitchen ta shiga daidai lokacin da Nurain ya kashe gas din, da sauri ta juya kamar zata sa gudu sbd fitowar da tayi ba shiri, Allah yaso ma kayan baccin riga da wando ne kuma rigar ta saukar mata, tana fita daga kitchen din shima ya fito yasa ƙafa ya banke ƙofar, tana shirin hawa stairs taji an fixgo hannunta, figarta yayi zuwa dining area inda babu hayaƙin sosai, haɗe ta yayi da bango still bai sakar mata hannu ba fighting with his breathing, sosai ya shaƙi hayaƙin shiyasa numfashinsa har yanzu bai dawo normal ba, kiciniyar kwace hannunta ta fara yi tana turesa da iya ƙarfinta, sake matseta yayi da bango ta kasa motsi, heavily yake breathing har zuwa lokacin da yaji dama dama, a hankali take mayar da numfashi ta ɓalla masa harara tace "let go off me, ni ka sake ni..", ita babban tashin hankalinta kayan jikinta, muryarsa ma bata fita sosai yace "from today henceforth karna sake ganinki a kitchen, are you mad fire outbreak zaki ja min a gida, koda wasa na sake ganinki a kitchen saina sumar dake nonsense" yana kaiwa nan ya hankaɗeta saura ƙiris ta faɗi. da sauri ya nufi stairs ya haura sama don bazai iya ƙara koda 1minute a wajen ba, Hajar tabi bayansa da kallo zuciyarta ta ringa ƙuna kamar zata kama da wuta, zama tayi kan stairs din hawa dining ta haɗe kai da guiwa, after 10mins ta tashi ta haura sama kamar wacca kwai ya fashewa a ciki. washe gari da safe Nurain ya sauko downstairs, ta main door ya fita ya zaga can backyard ya kashe gas cylinder, cikin gida ya dawo bayan ya kashe gas din, ya shiga kitchen to make a cup of coffee, wani tsaki yayi ganin tukunyar dake kan cooking gas, tayi wani baƙi ƙirin ko kyan gani babu, cikin sink ya saka tukunyar ya sakar mata ruwa saida ta cika damm snn ya kashe pampon, ya jona coffee maker. A hankali Hajar ta ƙarasa sakkowa daga stairs idonta ƙur akan keys din dake jikin ƙofa, ta isa bakin ƙofar a hankali ta zare keys din, tana juyawa sukay ido huɗu dashi ya fito daga kitchen da cup a hannunsa, ta haɗe gira tayi sauri ta kunshe keys din a hijab, garin haka ji kake tass muƙulli sun faɗi a kan tiles, kallon keys din Nurain yayi snn ya kalleta, ta wani haɗe rai, yana kallon main door ita kuma ta samu opportunity ta sunkuya ta ɗauki mukullin ta kwasa a guje sai sama, a hannun kujera ya dungurar da Coffee din yabi bayanta da sauri, tana ƙoƙarin rufe ƙofa yasa ƙafa ya banke ƙofar, zaro ido tayi tace "na shiga uku" ta ruga can edge of the room ta boye hannunta a baya, daga bakin ƙofar ya tsaya yace "give me the keys..", ta murguɗa masa baki tace "wllh bazan bayar ba, ni ba tinkiyarka bace da zaka ringa kulleni", ƙofar bathroom ta kalla sai kuma ta kallesa tana banka masa harara, lokaci guda ta tafi da gudu zata shige bathroom din, ganin haka ya taho da speed ya fixgota ya haɗeta da jikin wardrobe, dunƙule keys din tayi a hannunta ta ɓoye a baya, tini ta ringa shaƙar scent dinsa da bata so, ta ɗaga lulu eyes ɗinta ta kallesa, shima kallon cikin idanunta yake da wani irin expression zuciyarsa na tafasa.......✍️ 💛 HAJAR 💛 {49..} Thick eyebrows dinsa a haɗe while still staring at her yace "i said give me the keys..", ta juyar da kai gefe tana turo baki tace "ni fa bazan bayar ba..", bata ankara ba taji hannunsa akan nata da ta ɓoye a baya yana ƙoƙarin dawo dashi gaba, ta cije iya ƙarfinta ta sake dunƙule keys din a hannunta, partially ya dubi fuskarta kafin ya murɗa hannun nata ya dawo dashi, ƙara ta fasa ta fara ƙoƙarin fixgewa, tana ji tana gani ya ɓamɓare keys din daga hannunta, ya bita da wani shegen kallo ya juya ya fita daga ɗakin, wani mugun takaici ne ya tokare mata a maƙoshi, ta sulale ƙasa ta rushe da kuka tace "wllh sai na maka rashin mutunci mai wasali, ba dai ni ka murɗewa hannu ba, na rantse da Allah saina rama, dala ba gammo ka ɗakkowa kanka idan baka sani ba saika sakeni zaka cigaba da rayuwa mai daɗi..", taci kukanta ta more ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskarta da ruwa ta fito, fita tay daga ɗakin tana cika ta batsewa ƙiris take jira a taɓata ta sauke kwandon bala'i, downstairs ta sauka ta nufi kitchen tana cewa "duk abinda kace kar nayi toh yanzu na fara yinsa a gidan nan, dani da kai naga wanda zai sumar da wani, dan wllh tllh ni kaɗai nasan irin ayar da zan gasa maka a hannu..", plate ta ɗauka ta buɗe bucket din dubulan dana chin chin ta zuba, ta fito daga kitchen din, tsaye tayi tana kallon cup din Coffeen da ya ajiye a hannun kujera, Cup din ta ɗauka tana kallon coffen, ta gyaɗa kai ta haura sama da Kofin, a kan mirror ta ajiye plate da cup din taja stool ta zauna, taci dubulan da chin chin dinta tayi nak tana korawa da coffee, sosai combination din ya mata dadi sbd the coffe is creamy and yummy gashi babu sugar sosai sai hakan ya bada wani armashi. Nurain ya ringa kallon inda ya ajiye Coffeen sa wayarsa a kare kunne yana magana da Farooq, zagaye ya ringa yi yana duba each sofa a palourn, Farooq yace "are you listening..?", Nurain yana sake duba hannun kujeru yace "yeah", Farooq yace "alright" ya cigaba da bayanin da yake masa, after 5minutes suka gama wayar, Nurain ya shafa cikakkiyar sumarsa yace "damn it i misplace my coffee" da haka ya haura sama to get ready for work, dakatawa yayi da zuge glass door da ya fara ya kalli ƙofar ɗakinta da ta buɗe ta fito, idonsa ya sauka akan cup din dake riƙe a hannunta, ya ringa kallonta har ta ɓace masa bayan ta sauka ƙasa, slight hiss yayi ya juya ya shiga room dinsa, ƙarfe tara dot ya fito bayan yayi wanka ya shirya hannunsa riƙe da briefcase, ya sauka downstairs ya shiga kitchen ya ɗauki basket din abinci da yazo dashi jiya, bayan ya rufe main door ya isa parking space, ya shiga motarsa ya kunna, a booth ya saka basket din ya koma ya shiga motar tana gama warming ya fara driving ya fita daga gidan Inuwa na ɗaga masa hannu. sai ƙarfe uku Hajar ta fito ɗakinta zuwa kitchen, duk wnn lokacin ba ta ji yunwa ba sbd breakfast din yau ya riƙe mata ciki, ji take dama zata sake samun wnn creamy coffee din, saida ta gama jajjaga attaruhu da Albasa ta zuba a ƙaramar pot ta ɗora kan gas, ta ɗauki lighter ta kunna gas din amma babu wuta, ta canza wani shima dai wuta ba tazo ba, ta koma ta jingina da jikin cabinet tana tunanin yanxu yaya knn, me zata bawa cikinta, ta ringa kallon gas cooker din sai taga ashe akwai electric head ajiki har guda biyu, ta tuna lokacin da take gidan Anty Jamilah dashi ai take amfani most of the time sbd unguwar akwai nepa sosai, Hajar tayi ajiyar zuciya a bit relief, tana murɗa control knob din electric stove din luckily for her sai gashi ya kama, tinda a jone yake da wuta, wani dadi ne ya ratsa Hajar, tini ta hau yin girkinta, cikin kayan gararta ta farke buhun shinkafa ta ɗebi yadda zai mata ta dafa, bayan ta gama dafa shinkafar da ƴar sauce ta palm oil, gaba ɗaya ta juye a plate ta zuba Sauce din akai, ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa da haka ta fita zuwa palour, da kyar ta iya cinye abincin, ta kai plate din kitchen, saida ta wanke komai da tayi amfani dashi ta mayar mazauninsa snn ta bar kitchen din ta haura sama, cikinta ɗam ɗam dan ji take ita da abinci kam sai gobe kuma. ★Maama na kallon Maimuna da take ƙoƙarin saka hijab tace "wai ina zaki a haka Mainuna.. jifa fuskarki ko gama saɓewa ba tayi ba..", Maimuna da tayi ɗaurin ɗan kwali har goshi tace "kai Maama ba fa daɗewa zanyi ba, nan nan zanje na dawo..", Maama tace "nan nan ina..?", Maimuna tace "kai jaraba" ta ciro wata fatattakakkiyar dari biyu daga bra ta linƙawa Maama a ƙirji tace "yanzun nan zan dawo..", Maama ta dafe ɗari biyun tace "karki daɗe", Maimuna ta ƙarasa saka hijab dinta ta fita, bayan ta saka takalmanta dake bakin ƙofa tayi soro, can ta gangara cikin lugunsa har ta ɓulla wani lungun, daga nan tayi tafiyar da bata wuce ta minti biyar ba sai gata a wani kango wanda aka zagayesa da blocks sai gate na langa langa, tin kafin ma ta ƙarasa cikin kangon ta fara jin warin kayan zuƙe zuƙe, haka nan ta dake ta shiga kangon, su biyar ne a zaune a kangon matasa dasu babu wanda ya haura ashirin da bakwai a cikinsu, wanda ya fara hangota ya cire cigarette da yake zuƙa yace "ke ubanki kika kalla anan...?", Maimuna tace "ƙwage nake nema..", wani daga can gefe wanda ya fisu shekaru bakinsa baƙi ƙirin ya kalleta a wulaƙance, Wiwin dake hannunsa ya yiwa mummunar zuƙa ya fesar da hayaƙin ta hanci da baki tamkar salansar tsohon babur yace "ke yarinya yane... kin kawomin kanki ne dan na tuɓeki..?", Maimuna tace "haba ƙwage ai kasan nafi ƙarfin ka... harƙalla na kawo maka..", Ƙwage ya tashi ya matsa kusa da ita yace "meye..?" yana cigaba da busa wiwi, ta fara lalube cikin hijab dinta ta ciro kuɗi masu ɗan kauri a ƙalla zasu kai 10k ta miƙa masa, wurgar da ragowar wiwin yayi ya murjeta a ƙasa ya amshe kuɗin, Maimuna tace "kasan Mu'azzam ɗan gidan gini..?", Wani ne ya taso yana kallon hannun Ƙwage yace "kai wnn yaron fa nunar rana take nufi, ke ba ƴar gidansu bace ai naga yayanki ne..?", Maimuna tace "Eh ɗan kishiyar Baabarmu ne..", yace "A'a malama baabarki dai ba tamu ba..", Ƙwage yace "kai zan feɗe ka da rai nace ka sako bakinka ne..?", Bisi ƙwale yace "haba gorun goruba naga harkar nan tare muke yinta ai karka mana eh yane faa..", Ƙwage yayi kwafa yace "ina jinki", Maimuna tace "Shi nunar ranar Mu'azzam nake so ku masa dukan tsiya..", Ƙwage yace "Au abin sauƙi, ai ko cewa kikai mu ƙaddamar masa wllh a yau sai yaro ya ziyarci barzahu..", Maimuna tace "ku lakaɗa masa na jaki..", zuciyar Maimuna ba tada maraba da kindirmon nono sbd fari haka ta koma gida, tana shiga ɗaki ta cire hijab ta bage akan gado, Maama ta bita da idanu tace "har kin dawo...?", Maimuna tace "gashi kin gani", Maama tace "sai naji kamar kina warin Wiwi", a hasale Maimuna ta miƙe zaune tace "wiwi kuma Maama..?", Nabilah dake zaune ɗakin tana tsince shinkafa tace "nima naji wllh...", harara Maimuna ta bisu da ita ta koma ta kwanta tana jan dogon tsaki. Da yamma Umma na zaune bakin murhu tana kwasar tuwo, Mu'azzam ya shigo gidan da sallama, ya durƙusa gaban Umma ya gaisheta, da fara'a ta amsa masa tace "an dawo lfy ya aiki..?", yace "Alhmdllh Umma, yau mun gama da gidan ma har an biya mu zuwa jibi zamu tafi Katsina wani aikin..", Umma tace "toh alhmdllh, Allah ya temaka..", yace "Ameen Umma ga wnn.." ya ajiye mata ledar da ya shigo da ita, tace "toh madallah, Allah yayi albarka, ga can abincinka a ɗaki", yace "toh" ya tashi ya shiga ɗakinta ya ɗauki warmern abincinsa, daga nan ya shiga ɗakinsu, Maimuna dake laɓe jikin window tana leƙensa tayi kwafa ta koma ta zauna, Umma ta gama kwashe tuwon ta ɗauka ta kai ɗaki tare da ledar da Mu'azzam ya kawo mata, ta buɗe ledar taga lemo da Ayaba sai kuma ɗan tsire ne ciki, murmushi tayi ta ajiye kan mirror, Sabra ce ta shigo da gudu tana haki tace "Umma Yaya ya dawo...?", Umma tace "ba zaki dena guje gujen nan ba ko dan kinga Addarki ba tanan ne?", Sabra tace "ya haƙuri Umma", Umma ta shafa kanta ta ɗauki lemo ɗaya Ayaba ɗaya ta bata tace "zauna kici". Mu'azzam na alwala bakin rariya zai wuce masallaci dan daf ake da kiran sallar magrib, yana idar da alwalar ya fita daga gidan, bayan Umma ta idar da sallahr Isha'i tana zaune kan darduma tana lazimi, sallama akay daga soro, Maama da ƴaƴanta babu wanda ya amsa Nabilah kuma da ta ɗan fara shiryuwa sallah take, ga Baba ma baya nan ya fita masallaci, Umma ta ajiye carbin da take lazimi ta fita, daga bakin ƙofar soron ta tsaya, bata kai ga magana ba Naseer ya shigo, gaisawa Sukay da Munkaila wanda shine yayi sallamar, Munkaila yace "ina Baban naku..?", Naseer yace "yana masallaci..", Munkaila ya numfasa yace "toh muje da kai, ban san me ya haɗa Mu'azzam da fitinannun yaran nan ba gashi can sun sassara sa, yanzu haka dai an wuce dashi emergency..." ganin Umma kawai sukay a soron tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un.. wane Mu'azzam din.." ★Nurain yayi parking motarsa a wani babban eatery, fitowa yayi daga motar ya shiga eatery din, a vacant table na two sitters ya zauna, tini waitress ta kawo masa food menu, bayan ya gama order abinda yake so waitress din ta tafi kawo masa, dice watermelon da Orange juice aka fara serving dinsa as a starter, gently yake sipping orange juice din yana latsa wayarsa, Tamkar ɓera a buta hka ta shigo Eatery din tana rarraba idanu, tana hangosa ta nufi table din da yake zaune, ta ja kujera ta zauna gami da zuba masa idanu, ajiye glass cup din lemon yayi ya fara shirin miƙewa, da sauri ta riƙo hannunsa tace "dan girma Allah listen to me ko sau ɗaya ne..", fasa tashin yayi da sigar ko in kula murya ƙasan maƙoshi yace "what..?", duk da Ruqayyah taji haushin yadda yayi treating dinta these days amma bata nuna ba, gyara zama tayi tana kallonsa tace "Dr dan Allah don't take grudge against me, ba wai na tafi bane sbd bana son na aureka, ba a fahimce ni bane from the start..", keenly yace "Ohk, then stop following me..", Ruqayyah ta haɗiye kukan da ya taho mata tace "shknn, nasan har yanxu fishi kake dani Dearest..", yana latsa wayarsa yace "not at all..", tace "nagode da ka tsaya, har yanzu ban canza daga Ruqayyahn da ka sanni ba, i still remains your first love and only kuma your wife to be, zan aureka Dearest, a shirye nke ko yanxu ma kaje wajen Daddy za ai mana aure Dearest..", a lokaci na farko da ya ɗago kansa ya kalleta kafin ya dauki orange juice yayi sipping yace "Ruqayyah..", murya na rawa tace "Na'am", yace "a lokacin da nayi dating dinki kinsan duk abinda na bari na barsa knn", ta gyaɗa kai idanunta na ciccikowa, yace "snn kin san banida ra'ayin auren mata sama da ɗaya..", nan ma ta gyaɗa masa kai tace "amma why are you saying that bayan baka da aure..?", ya girgiza kai yace "you are wrong" da haka ya kira waitress yace ai masa packaging abincin da yayi order, Ruqayyah dai ta kasa mgn cause tana buƙatar concrete explanation, wayarsa ya saka a pocket ya tashi zai biya bill, cashier ya nufa ya biya bill din ya amshi ledar abincin ya nufi exist, da sauri Ruqayyah tabi bayansa tace "wllh Allah ban fahimci me kake cewa ba, kuma baka bani enough time na maka bayani ba..", yayi ajiyar zuciya yace "i don't like it idan kina bina hka, please stay away from me, i don't have any feelings for you now, snn kuma i am married.. good luck..", da haka ya nufi motarsa ya shiga ya bar Eatery din, Ruqayyah taga kamar birds ne suke yawo a kanta kafin ta fara ganin harabar Eatery din bibbiyu daga nan kuma bata sake fahimtar halin da take ciki ba. farkawa tayi ta ganta a restroom na Eatery din mutum har huɗu akanta, ta miƙe zaune tana kallonsu kafin ta dafe kanta, wata mata ce tace "Alhmdllh sannu ko..", Ruqayyah ba ta iya cewa komai ba kawai binsu take da idanu, wani mutum wanda shima staff ne a Eateryn yace "ki bamu contact din wani naki a kira a gaya musu halin da kike ciki..", a hankali Ruqayyah ta girgiza masa kai tace "no need ngd sosai..", ta miƙe da kyar kanta na sarawa, waitress din da itama ke wajen ta miƙa mata ragowar bottle water da aka yayyafa mata ta farfaɗo tace "ga ruwa ko zaki sha..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "nagode.." ta nufi ƙofa zata fita, mutumin ya sake cewa "da dai kin jira an kira ƴan uwan naki hajiya", bata tanka masa ba sbd ita kaɗai tasan abinda take ji, da kyar ta kai kanta bakin titi ta tsari napep, ba ta ma gaya masa inda zai kaita ba kawai ta shiga, saida suka fara tafiya snn ta gaya masa inda zata, Ruqayyah na zuwa gida direct hanyar room dinta ta nufa, Momy dake zaune palour ta bita da kallo tace "baki da lfy ne..?", gyaɗa mata kai Ruqayyah tayi, Momy tace "sannu..", room dinta ta wuce zuciyarta kamar an ɗora mata dutse, tayi wurgi da handbag dinta a kan bed kafin itama ta zube akan bed din, Momy ce ta shigo da plate din abinci da ruwa, ganin Ruqayyah a kwance ta ajiye plate din akan mirror ta iso bakin gadon tana feeling body temp dinta, jikin nata zafi ramm, with care Momy tace "zazzaɓi kike ne Ruqayyah..?", Ruqayyah ta yunƙure ta miƙe hawaye na zuba idanunta wani nabin wani, sosai hankalin Momy ya tashi ta zauna gefen gadon, Ruqayyah ta ɗora kanta a kafaɗar Momy ta fashe da kuka mai ƙarfi tace "Momy kiyi haƙuri, am so sorry". ★Ƙarfe takwas da rabi Nurain ya isa gidansa, basket din abinci da ya taho dashi daga gidansu ya ɗauka kafin ya fito daga motar, ya ciro ledar take away na abinci da ya siya baici ba dan tinda ya saka a motar baima bi takansa ba, Inuwa ya bawa ledar abincin ya wuce ciki da basket na abincin gidansu, upstairs ya haura yayi refreshing kansa kafin ya sakko sanye da white pajamas ya shiga kitchen ya ɗakko plate da spoon da drink, saida yayi powering TV snn ya zauna cin abincin, ko rabin abincin bai ci ba ya ajiye spoon din yana kallon stairs, lokaci guda ya miƙe ya haura saman, toh me tasamu taci bayan ya kashe mata gas, har ga Allah mantawa yayi ya bawa Inuwa ya siyo mata Charcoal ko firewood da safe in yaso sai tayi amfani dasu tayi girkin, still yayi a corridor yana kallon ƙofar ɗakinta, ya haɗe gira ya murɗa door handle ya shiga, yayi sallama ƙasa ƙasa, Hajar ta ajiye wayarta kan mirror ta dubi ƙofar, tin ɗazu take kiran Umma amma no respond, suna haɗa ido dashi ta murtuke fuska ta galla masa harara ta ɗauke kai, duk da ya lura da hakan amma he don't care, with a repartee yace "hey..", bata bari taji sauran maganar ba ta katsesa da fadin "can kaje ka nemo hey dinka nan Hajar ce ba Hey ba", Nurain was more than shock jin abinda ta faɗa, furiously yace "young lady, na fahimci kanki na rawa kuma baki da kunya, amma please enough don't try me..", wani irin yamutsa fuska tayi tace "Au haba, so kake na ɗauki mayafi na kirma a ka na rufe fuskata shine zan zama me kunya ko me.." haɗiye sauran maganar tayi ganinsa a gabanta, ita dai bata san lokacin da har ya taho yazo gabanta ba, wani mugun bugu zuciyarta ta fara yi, ta ja baya da sauri tana zare ido, tana ƙoƙarin sake ja da baya ya kama dukka hannayenta ya mayar dasu baya ya rutsasu duka da hannu ɗaya, riƙo bana wasa ya mata ba don ji tayi kamar shoulders ɗinta zasu karye, turo baki tayi tace "malam ni ka sake..", bata gama maganar ba yasa finger ya ɗalle bakin rashin kunyar, tini Hajar tayi shiru tana jin azaba a lips ɗinta, yana ganin ta fara motsa lips alamar za tay magana ya sake ɗalle bakin, gashi ta gagara motsi babban weapon dinta kuma an hanata amfani dashi wato her mouth, motsa lips din ta sake yi nan ma ya ɗallesa, tini lips din kwa sukay jajir, thick eyebrows dinsa a matuƙar haɗe yake kallon fuskarta, wani yunƙuri tayi zata fixge, da sauri ya kuma matseta ya ɗalle lips din a karo na huɗu, lulu eyes ɗinta ya kalla da suka cika taff da hawaye, lokaci guda tears din suka fara zarya kan kuncinta.....✍️