[10/1, 9:36 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 1 Nimcyluv Bright pens.... second batch *Marubuciyar....❤‍🔥* *Mijin malama* *Munafukin miji* *Moon* *Idan ba ke* ..... E.t.c and now *MUTALLAB* *🔞for some reasons.... Akwai copywrite kar a haɗa mini ducoment, banda YouTube a bar mini kayana haƙƙina ne* Jami'an tsaro ne ta ko'ina cikin kayan kaki ma bambanta, duk da cewa yammacin ranar lahadi ne a watan Fabrairu bai hana ta gane fuskarsa ba. Cikin tashin hankali jikinta na rawa da kyarma ta nufe shi tare da ƙoƙarin cakomo wuyan babbar rigarsa tana furta cewa "Shi ne, wallahi shi ne, daman na ce zan gano shi" a gigice mutumin dake ƙoƙarin shiga motarsa da aka buɗe masa ya yi baya yana mai ƙarewa matar kallo sosai sai dai ya kasa gano ko wace ita? Daga ina me kuma take buƙata. "Wace ita?" Ya furta yana tambayar zuciyarsa tare da kallon gefe. "Wallahi shi ne, mugu azzalumi sai ka yi kuka, ka wulaƙanta " Jin furucinta ya saka ƴan'jarida dawowa kan ta, suka fara tambayar "Kin san shine? Mene haɗinki da shi?" Kafin ta yi magana wani ya ce "Arrest her, ku kamata" A hankali ya jingina da jikin motar can ya numfasa yana kallon yaronsa ya ce "Wace ce? Na santa ne? To me ya sa take abu kamar ta sanni?" "Sir da gaske ta sanka bana jin ko mutuwa ta yi ta dawo zata manta fuskarka, kuma zamanta a raye yana nufin abubuwan da yawa dole a yi wa tufkar hanci, kar a bari ƴan'jarida su samu ganawa da ita, even your securites, wannan matsalar kai da kai ce kuma zata shafi kimarka" cike da mamaki ya yi ta kallon yaron nasa na tsayin sacanni da ƙyar ya cije leɓe ya ce "To ina na santa? Me ya sa zata zama damuwata?" "Sir ita ce wacce ka saka aka kawo maka ita, wacce ka yi wa fyaɗe a lokacin.....," "Ya isa!" Ya ce yana jin jiri na neman ɗauke shi, ya dubi tarin jama'ar da suke wajan can ya yi murmushi yana ɗauke fuska sai kuma ya ƙurawa yaron idanu ya juya ya kalli matar ya gyatsine fuska ya ce "kuma ta kasance a raye ya haka? To a yi hanzarin toshe wannan ɓarnar ya zama kamar ba a yi ba" "Amma me ya kamata a yi mata?" "A yi mata allurar hauka, wacce ake yi duk shekara da wata wata kana a kaita gidan yari, life in prison har ta mutu. Bayan haukan zata mance komai, su ƴanƴan talakawa wama ya damu da su mutu ko su yi rai bata da wani mai tsaya mata kai mutuwa ma za ta yi" yana faɗin hakan ya shige mota. Tana takure a jikin ƙofar ɗakin da aka ajjiyeta idanunta ƙur a kan photonsa zuciyarta sai zafi take mata wani abu ya tsaya mata. Da sauri ta juya jin an buɗe ƙofa wani mutum ne sanye da farar riga ya rufe fuskarsa hannunsa riƙe da ƙaton sirinji iya ruwan allurar da ya yi ja abin tsoro ne, ta fara ja da baya amma a haka ya fincikota tare da yin cilli da ita,ta faɗi saman carpet bai tsaya jiran komai ba ya caka mata allurar a ƙashin bayanta wajan spinal cord ihu ta fara da birgima idanunta ya shiga ƙaƙƙafewa jikinta na sandarewa ta dinga buga kanta da jikin bango tana buge-buge a hankali jini ya fara fitowa ta cikin hanci da bakinta tabbacin allurar ta amshe ta za kuma ta yi aikin da ake buƙata a jiki da ƙwaƙwalwarta. ****** Cikin sauri suke tafiya a wani ɗan dogon lungu mai duhun gaske tsarin wajan gabaɗaya a ƙuntacce yake kamar zunubin gidan yari. Magana suke ƙasa-ƙasa ɗaya daga cikin su kuma yana duba agogon dake hannunsa tare da duba cikar lokacin fuskarsa a haɗe take sosai. Sai da suka kawo ƙarshen ginin suka tsaya ya ɗaga kai a hankali ya dubi saman da kansa ke taɓowa ya ɗan rusuna sai kuma ya dubi jami'in tsaron dake wajan ya yi masa nuni daya buɗe ƙofar. "Yes sir!" Bayan ya sara ya ƙame ya buɗe ƙaton kwaɗon yana toshe hanci saboda wari da zarnin wajan. SP Gali ya kalli team ɗin nasa cikin bada umarni ya ce "Ku jira nan, idan akwai damuwa zan muku alama na san dai he can't do anything, ba zai iya komai ba" gabaɗaya suka jinjina masa kai tare da zagaye ƙofar fuskar kowannen su manne da baƙin gilas. A hankali Sp Gali ya tura ƙofar ya shiga yana durƙosawa saboda rashin girman wajan. Tunda kafin su ƙarasu wajan ya san da zuwan nasu har aka buɗe ƙofar tare da shigowa, yana durƙushe inda yake ya kifa kansa a ƙasa hannunsa dunƙule ya damƙe abu wanda tun kafin a kawo shi gidan abu yake a hannunsa, yin duniya yaƙi buɗe abun balle a san menene shi. "Hey you!" Sp Gali ya ce yana saka ƙafa tare da buge ƙafarsa ganin yaƙi motsawa, tamkar gunki haka yaƙi motsi ya kuma ƙi ɗago kansa Sp Gali ya shiga kallon wajan ya rasa wanne irin hali ne da wannan yaron mai baƙar zuciya da taurin kai ya sauke numfashi cikin kwantar da murya ya ce "Ni idan na ce maka ina da tausayi na yi maka ƙarya, amma ka saka zuciyata karaya kana bawa kanka wahala kana bawa jami'anmu wahala. Me zai hana ka sauƙaƙa mana wahalar nan ka faɗa mana gaskiyar abin da ya faru a wannan rana kuma a wannan daren? Me ya sa ka aika abin da ka aikata? Ka kashe matarka, ka kashe ta har lahira kuma kaƙi magana shekara uku kenan kana wajanmu ka rainawa hukuma hankali da kotu, kai baka da zuciya ne dame kake taƙama saboda kana da tsari a jikinka ƙarfe ba zai ratsa naman jikinka ba, muna da kalolin azaba nau'i-nau'i amma gaskiya muke buƙata, ka amsa cewa ka kashe matarka a zaman kotu na yau shikenan sai a yanke maka hukunci daidai da zaluncin da ka aikata" Har Sp Gali ya kammala maganarsa bai motsa ba, babu alamun zai ɗago kai balle ya tanka. Sp ya miƙa hannu zuwa hannun mutumin dake dunƙule da abu zai amsa a firgice ya ɗago kansa yana buɗe dara-daran idanuwansa akan Sp Gali sai da zuciyarsa Sp ta motsa saboda wani mugun jaa da idanunsa ya yi. Fuska ɗaure ya yi wa Sp kallon warning har lokacin bai yi magana ba dukkan naman jikinsa rawa yake kamar zai kaiwa Sp damƙa fuskarsa baibaye da gashi kansa ma cunkus yake ba'a gane kamanninsa sosai saboda cikar gashi. Sp ya duba lokaci sai kuma ya shafa kai ya ce "SCORPIO" nan ma ya sake ɗago kai da sauri ya zubawa Sp idanu "Idan ka bari na gano cewa kai ne Scorpio...." Ya cije baki yana miƙewa tsaye ya furta "Zan addabi rayuwarka, gwara ka zauna a iya wanda ya kashe matarsa da dai ka kasance kai ne Scorpio. Mene asalin sunan naka?" Ya tambaya yana juyawa kamar zai fita saukar gurnanin da ya ji ya saka ya yi saurin juyawa idanunsa ya sauka wanda ake zargi da kashe matar tasa yaga ya dafe kai da hannu bibbiyu yana jujjuyawa ya dinga haɗa kansa da bango cikin sauri Sp Gali ya ce "Team" a guje suka shigo hakan ya saka ɗan ƙaramin ɗakin cika fuskar Sp ba wasa ya ce "Ku danne shi a karɓo abin hannunsa dole mu san mene babu mamaki zamu samu hujja a ciki" yana cewa haka ya fita yana amsa kira. Ganin sunyo kansa ya yunƙura gabaɗaya ya fisu faɗin ƙirji da damtse amma suka rufar masa sanin cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi ya saka shi damƙe hannunsa da kyau yana ɓoye abun da suka karɓa, kokawa suke da shi ya dinga haɗa su da bango ya kama hannun ɗayan ya karya bisa dole suka fice a wahale. Sp ya saka wasu manyan mutane fito da shi suka ɗaure shi da ankwa tare da sarƙa tun daga ƙafa har zuwa kansa. A harabar Criminal Investigation department CID aka tsaya dashi domin tafiya zuwa kuto a rana ta ƙarshe wanda ke nuna ko a sake shi, ko a kashe shi ko kuma ya tafi gidan ɗan'kande. Team guda ne masu matuƙar basira da ƙwarewa akan aikinsu team ɗin ya haɗa da wanda yake ɓangaren Legal section, Anti-human trafficking, Medical Staff, Legal services, NDLEA, FID Federal investigation department. Gabaɗaya idanunsu yana kansa kowanne yana karantar yanayinsa amma shi ko a jikinsa banda faratansa na hannu dana ƙafa da aka ciccire wajan gana masa azaba babu wani rauni a tattare da shi sai matsanancin baƙi da ya yi ya zama kamar mahaukaci saboda shekarun daya ɗauka a kulle daga kuto zuwa state cid zuwa Fid amma har tsayin shekarun bai buɗe baki ya yi magana da kowa ba, babu kuma wanda ya damu daya tsaya masa. Suna ta surutai ƙasa-ƙasa duk yana jinsu har sanda wani yake cewa "Babu hanyar da za a tilasta shi ya yi magana ne? Muna buƙatar muryarsa" Sp Gali ya ce "Ina zargin wani abu game da matarsa daya kashe" "Wanne abu? A binciken da mukai a wajan iyayen yarinyar tun farko ita ta nuna tana son shi, shi da ita class mate ne kuma age mate, tun suna shekaru 15 a secondary school suke soyayya. Me ya sa ya zaɓi ya kashe ta? Sun ɗauki shekaru tare bai taɓa yunƙurin rabata da duniya ba sai ranar da aka ɗaura musu aure? This is complicated" C.i.d Research ya jinjina kai ya ce "Duk binciken da aka yi shine a ruwa, gwajin hannu, yatsun hannu da sahun tafin ƙafa da CCTV camera na kan titin unguwar da aka kai amaryar tasa duk bincika shine" Shiru sukai suna tunanin gabaɗaya kansu ya ɗauki zafi. Yana da can inda yake ya ja idanunsa ya lumshe yana fesar da iska daga cikin hancin wacce hucinta ya sauka har saman fuskarsa “BESTIE” haka ya ji saukar muryarta a kunnensa kamar yanzu ne suke tare da ita. Ya sake lumshe idanunsa yana jin saukar dariyarta sosai ya tuna lokacin yana zaune shi kaɗai a cikin class ranar aka dawo hutun makaranta shi kaɗai ne zaune ciki yana sanye da farar riga sai wando blue black ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman benci tare da yin baya. A hankali ta shigo cikin class ɗin hannunta riƙe da lunchbox da textbook sai school bag data goya, hijab ɗinta daidai da ƙirjinta ita ce ta fara shigowa da mamaki take kallonsa zuciyarta na bugawa ta je ga zauna inda yake ta zuba masa idanu sai kuma ta ce "Ka yi holiday assignment?" Ya buɗe manyan idanunsa bai ce komai ba ta sake ƙasa da murya ta ce "Na san bama ka yi ba ka daina haɗe mini fuska, ka naso a yi ta faɗa da kai da teachers" nan ma bai kula ta ba a hankali taci sautin da cikinsa yake yi sai ta jawo lunchbox ɗinta ta buɗe tare da tura masa gabansa ta ce "Your breakfast, ka ci kafin a shigo na san baka karya ba" sai a lokacin ya buɗe idanu ya juya gabaɗaya yana kallonta sosai ta yi ƙasa da murya kamar zai yi faɗa sai kuma a hankali ya ce "Kuma ga mayunwaci ko?" Ta yi murmushi ta ce "Da ƙyar na jure ban biyoka gida ba, na yi kewar ka sosai bestie" ya yi mata shiru sai kuma ya haɗe fuska sosai yana janyo abincin yaga dankali ne aka soya da ƙwai ya yi ɗan tsaki ya ajjiye spoon ɗin ya damƙa ya kai bakinsa ta yi saurin kama hannunsa ta ce "Kai baka iya komai bane? Sai a yi maka dariya cin abinci da hannu" ya ware idanu sai kuma ya murtuke fuska ya ture hannunta a hankali duk da muryarsa a kumbure take ya ce "Ki daina kusanta kan ki dani, ni fa ba ɗan iska bane" "Laaa Allah Ya baka haƙuri kai duk abin soyayya baka iya ba" a taƙaice ya ce "Ke kika santa" ta ja baya tana ɗaga hannu ta ce "Lalala to shikenan ni dai ƙaddararka ce, na faɗa a gida a yi mini aure, ka san me na ce?" Ya girgiza mata kai kawai yana sake damƙo dankalin yana dannawa cikin bakinsa saboda yunwa ko gani baya yi sosai ta buɗe gorar ruwa ta miƙa masa a hankali ta ce "Na ce su yi mini aure wallahi bana son karatun nan, na ji aure nake so kuma na faɗa musu kai nake so, amma wai ban isa ba karatu ya zama dole kuma shekaruna sun yi kaɗan amma ai ma girma shekararmu 15 years fa, ko kai baka isa aure bane?" Ya yi mata shiru sai ta fashe da kuka sosai ta ce "I love you so much Bestie, don Allah ka aure ni zan zauna dakai a duk yadda kake ka taimakawa rayuwata" ya zame hannunsa tas ta miƙa masa tissue ya goge ya ja baya yana lumshe idanunsa har yanzu students basu fara shigowa ba, ta ɗan yi gaba kamar za ta shige masa ya cikin tsawa ya ce "Zan kwaɗe ki kuwa" "But what if i told you i love bestie? You mean the world to me, wallahi aure nake so ba karatu ba" ta faɗa tana shassheƙar kuka sai a lokacin ya kalleta fuska babu walwala ya dubi yadda take kukan sosai ya ce "Ke, babanki ne ya mutu? Ko uwarki ce?" Ta girgiza masa kai ya sake haɗe fuska yana rarraba idanu a cikin ajin kamar mai neman wani abu can ya ce "To kece za ki mutu kenan?" Ta girgiza kai sai kuma ta ce "A'a" "Kukan fa?" "Na soyayyarka ne bestie taɓa ƙirjina ka ji wallahi ni ce ƙaddararka ba zaka gane hakan a yanzu ba, da ina da ikon cire abin da nake ji a ƙirjina da na yi hakan ina jin dama na mutu na huta kuma idan ban aure ka ba zuciyata zata iya bugawa" "To gwara ta buga na huta da na ci, shekaruna 15 za ki lalata ni da batun aure, ke tashi ki ware daga nan ɗauki kwananki kar ki ƙara kawo mini abinci" ta miƙe jiki a sanyaye zata bar wajan ya nuna mata lunchbox ɗin daya cinye komai "Ko daɗi bai yi ba abincin" Sai a lokacin ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ta yi kukan ba, dimples ɗinta na lomawa ta ajjiye masa 500 ta yi waje tana cewa "You're my darling jarumina, i love you Mai dawa da jeji" ta faɗa tana sake yin dariya tare da yin waje....... Ya yi saurin dafe kansa jikinsa na rawa yana jin dariyar nata na yi masa amasa kuwwa a kunne kamar yanzu ne take yi jikinsa ya ɗauki rawa sosai daidai lokacin aka tura shi cikin motar shiga babu biya, aka nufi kuto. Tun kafin a shigar da shi suka ci karo da wani saƙo daya basu mamaki ainun suka tsaya suna kallon juna sosai cike da tsoro da shakku musamman Sp Gali ya juya ya kalli wanda ake zargin a karo na farko yaga ya yi wani irin murmushin kefen baki wanda ya bada sauti kamat na tsaki yana murza kai gefe. Cikin sauri Sp Gali ya ce "Amma wane ya yi hakan? Bayan ba a gama bincike an tabbatar da hakan ba, mene matsayin ran yarinyar daya kashe ina matsayin iyayenta" "Sp Ghali ka yi abin da aka ce, kuto ta wanke shi daga zargin da ake yi masa ku sake shi ya tafi gida baku da ikon riƙe shi" Sp Gali ya girgiza kai cike da damuwa ya ce "Sir kana nufin bashi ya kashe ta ba" cikin tsawa ya ce "Ko shine ya zaka yi? Ka yi abin da ya dace a matsayinka na jami'i Sp Ghali karka matsa" jiki a matuƙar sanyaye Sp Ghali ya kunce shi tas ya ce "Congratulations. Ka sani shari'a saɓanin hankali ce" shi dai bai ce komai ba ya ciri biron gaban rigar Sp Gali ya fara yi masa rubutu a tafin hannunsa dam zuciyar Sp ta buga ganin ya rubuta kalmar SCORPIO kafin ya yi magana tuni ya juya ya fara tafiya cikin sauri duk da rashin kuzarin da yake dashi yana jin inda iskar ƴanci ke ratsa jikinsa yana shaƙa tare da kaiwa hunhunsa. Kano/Birget Dambe suke yi a tsakiyar tsakar gidan mata wajan uku ne kowacce da ɗaurin ƙirji ga tukunyar abincin dake saman murhu. Banda sautin hayaniyarsu babu abin da ake ji hatta Malam dake waje da Almajirai yana jin yadda suke aibata juna da zagin juna hakan ya saka ya miƙe riƙe da bulala yana ajjiye allon hannunsu da yake rubutu ya yi cikin gidan. "Ke har kin isa ki ce za ki hana Mufeederh abinci a gidan nan? Wace ke?" Cikin ɗagawa Inna Binta ta ce "Ni Binta matar malam ki faɗa mini nawa Mufee ta bayar aka haɗa wajan yin abincin nan? Ke uban yaran nan bai bada kuɗin abinci ba, ba zai yiwuwa yara su haɗa kuɗi kuɗi a siyo dusar awara a yi dambun nan ki ce wai na zubawa Mufee ba ƴar banzar yarinyar da bata da kunya, kina kallo sauran ƴan'uwanta suka fita nemo kuɗi ita ta yi kwanciyarta tunda ƴar mai ce ai yanzu sai ta ci hantar ubanta Malam gashi can yana zaman banza ba fuss" Mama dake ƙoƙarin ganin ta wafcin dambun a kwano ta ce "Daɗin abin dai ba yaranki kawai suka haɗa kuɗin ba, hadda Saudat ko Zaituna?" "A'a ba ruwan Zaituna tun jiya nake ganin hazo-hazo a idanuna cikina banda salati ba abin da yake, Saudat da ciwon ciki ta kwana Olser ta buge ta saboda yunwa ki yi ta kan ki kawai wannan rayuwa Allah dai ya fisshe mu, amma yunwa za ta yi ajalin rabin jama'a a wannan zamanin" Mama Zaituna ta faɗa tana turo kwanan Saudat da nufin a zuba mata ta ɗan tsakura a ciki ta yafa a nata cikin. Inna Binta ta shammafe ce ta yi sama da tukunyar kasancewar ta sharifiya ta ce "Wallahi sai Mufee ta ci abincin nan" Mama Zaituna ta ce "To Allah Ya isa daman kun saba cin kayan Allah Ya isa in sha Allah sai ta yi aman shi" Inna Binta ta ji an cauɗa mata bulala a ɗuwawu ta yi saurin dire tukunyar ta ce "Kan uba wanne mai tsautsayin ne haka?...," shiru ta yi ganin Malam ya ce "Kina sake magana ina ƙara cauɗa muku shasha kawai mara kan gado" Ya juya wajansu ya ce "Mayu marasa godiyar Ubangiji kawai akan abinci duk maƙota da unguwa sai anjiku" Inna Binta ta ce "Yaushe rabon da muga sisi taka banda masifar tsiya kana bamu za mu yi haka ne?" Kan ta ya yi da bulala ta yi saurin waftar dambun a hannu ta yi ɗaki tana "Ohho dai na ɗiba na mai da mugun miyau" Haushin karnuka suka ji wanda rabon da su ji shekaru uku kenan gabaɗaya suka juya wani ihu Mama Zaituna ta yi tare da fatali da dambun da ake ta yin masifa akan shi har zaninta na kuncewa zuwa ƙasa ta yi saurin juyawa zata ɗakko ta zame da ɓawan albasa ta faɗi dif a ƙasa Kasancewar ƙatuwa ce sosai ta fasa ƙara da jan ɗuwawu ta shige ɗakinta hankali tashe. Shi kansa Malam sai da zuciyarsa ta motsa saboda tsoro ya dinga kallon karnukan da idanu yadda suke ɗaga jela tare da zaro harshe waje jibga-jibga dasu sai zagaye wanda ya shigo suke yi. Da ƙyar Malam ya ja numfashi ya ce "Muɗallabi Ɗanmalam nake gani haka? Ya suka sake ka basu kashe ka ba, ni na ɗauka ma tuni ka mutu wallahi, ikon Allah" sosai kansa ke masa ciwo kamar zai rabe ga wani ciwo da jikinsa yake yana jin fatarsa na rawa, ya yi baƙi sosai amma manyan idanunsa na nan kayan jikinsa duk a yage ya zubawa Malam idanu. "Kai Muɗallabi ba da kai nake magana ba? Yanzu da suka sake ka me suke nufi ka kashe ƴar mutane a banza kenan? Ba zan goyi bayan gaskiya ba dole na je wajan jami'an tsaron yanzu na bi ba'asi" Cikin sauri Ammo ta fito daga ɗakinta jin sunan wanda aka kira zuciyarta har rawa take tana fitowa suka haɗa idanu dashi ya kafe jikin bango a hankali yaran gidan suka fara fitowa ya dinga bin guntattakin yaran da kallo wasu duk bai san su ba. Ya nufi Ammo ta yi saurin ɗaga masa hannu ta ce. "Ina jin tsoron kiran ka a matsayin ɗana na ji na yi dana sanin haihuwarka wallahi" Ya buɗe manyan idanunsa sai kawai ya ja ya lumshe yana ƙara yunƙurin zuwa wajanta kenan ya ji ihu a waje kafin ya motsa Goje ya shigo da sauri yana cewa "Mai dawa ƴan unguwa ne ɗauke da makamai wai za su ɗauki fansar....." Da sauri MOH ya ɗagawa Goje hannu baya son ma a kira sunanta a kusa da shi zuciyarsa buɗewa take sosai. Goje ya sake cewa "Ba ƴan unguwa kaɗai ba har da gajoji da cinnakun layi" kafin Goje ya ƙarasa sun ji ana cewa "Ba iya Mai dawa ba har Malam da babarsa yau sai sun mutu da duka mutanen gidan sai mun ɗauki fansar yarinyar daka kashe tunda jami'ai sun sake shi a banza" Mutallab ya kalli karnukansa ya musu inkiya Tiger ne ya fara zuwa ƙofar ɗakin Ammo ya tsaya Rainbow ya je ƙofar gidan ya tsaya, Spider kuma ya tsaya yana kewaye Malam. Goje ya ce "Kai ƙarfe baya cinka tsine baya ratsa jikinka su Malam sune matsalar" bai magana ba kai tsaye ya nufi waje gaban Ammo ya faɗi ganin ba makami a hannun Mutallab. Inna Binta ta fito tana zunduma ihu tana jama'a su kawo musu ɗauki tana leƙa ƴar ƙaramar katangar gidan ganin tarin matasan da suke waje ɗauke da makamai ya saka Inna Binta kurma ihu tana faɗin "Ya gafilan zanbi waya kashifal gammi...." Bata gama ba aka raɗa mata gora aka ta faɗo ɗaga saman katangar ta baje wanwar a ƙasa Mufee ta fasa ihu tana yin wajan Inna Binta ganin haka sauran mutanen gidan suka shige ɗaki banda Ammo da Malam. Moh na fita suka yi masa ƙawanya kasancewar akwai shafi a hannunsa duk wanda ya daka sai ya baje a wajan, suna da yawa sosai cike da rashin sanin cewa tsarin jikinsa ya karye ya shiga tsakiyar su ɗaya ya ɗauki dutse ya buga masa aka nan take ya fashe, wani ya ɗaga wuƙa ya soka masa a ciki nan take wuƙar ta shige Goje ya zaro idanu ganin sun yi nasara ya saka suka zagaye Moh suna kai masa sarawa, baya faɗa da makami bai san kuma ya ake yi ba, kafin wani lokaci sun kai shi kasa ko'ina na jikinsa jini ke fitarwa daidai lokacin tawagar mafarauta suka ƙarasu wajan tare da zugar karnuka faɗan ya koma tsakanin ƴan unguwa da mafarauta cikin mawuyacin hali Moh ya ja jikinsa a hankali jin wani yana waya da ƴan'sanda ji ya yi dama layya zana na wajansa a yanzu haka? Ya dinga tafiya yana jan jiki har ya bar unguwar ya shiga cikin wani waje mai kama da gonaki kuma jeji-jeji. Tana zaune cikin bukkar hannunta riƙe da ƙwaryar nono ta ji an faɗo cikin bukkar a gigice ta miƙe tsaye... *To ga dai shi nan ban san ya zaku amshe shi ba, amma tabbas zai zama daidai da ra'ayinku musamman iyayenmu mata da maza 😭da suke wasa akan yaransu. MUTALLAB zai zo da sabon salo in sha Allah za a yi kuka sosai kuma za a yi dariya fatana kar ku yi mini zagin da kukai a MIJIN MALAMA 😭ku amshi labarin da hannu bibbiyu ku tayani isar da saƙon zuwa ga manya ta hanyar yin sharing saboda Allah* 08164069385 WhatsApp only [10/2, 8:40 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 2 Nimcyluv Bright pens..... Second batch *🔞 Warning... For criminal issues* Cikin bukkar ya faɗa jikinsa jina-jina da jini sara ta ko'ina da ƙyar yake iya fidda numfashi, ya zube a gabanta idanuwansa a lumshe har yanzu yana jiyu sautin ihu da kukanta, ya kasa ceton ta, ta sake mutuwa, yaushe zata ci-gaba da rayuwa tana sake macewa akan idanuwansa? Ya cije jajayen laɓɓansa wanda jini ya ɓata sam bai damu da yadda yake shanye jinin yana koma masa ciki ba, a matuƙar fisge ya yi maganar mai sautin gurnani ya ce "Na amince, da gaske na amince Abbasa, zan zama mata maza, ki mayar dani jinsin mace ina tunanin zama macen ya yi daidai da tafiyar ƙaddarata! Zan zama mata maza, bana iya kwanaki ba, bana iya wa'adin sa'a ba, ba kuma iya na tafiyar sakwanni ba, ba kuma iya na gilmawar kwanaki ko shuɗewar watanni da nisan shekaru ba, a'a Abbasa, a'a Abbasa ina son zama mata maza ne na daidai da tafiyar agogo da adadin shekarun da zan yi a duniya" Yadda furucin ke fitar da kan su, da yadda yake magana idanuwansa na fiddowa waje duka jikinsa rawa yake da ɓari yana wani irin tsuma bakinsa har wani hayaƙi yake yi jijiyoyin kansa tamkar zasu ratsa fata bakwai su keto, ganin halin daya shiga ya saka Abbasa cewa. "Iya zubin tunanin naka kenan? Iya jarumtar kenan? Mayar da suffarka zuwa abi mafi nakasu a rayuwarka? Ka zama mace shin ko ka mace da......" "Abbasa!" Ya kira sunanta a karo na farko a tsawa ce, domin baya son tuna abinda take ƙoƙarin cewa "Shikenan shikenan, zaka zama jinsi biyu, mai halitti biyu" ya girgiza mata kai yana jin amo da sautin muryarta cikin wutar da suka babbaka ta ciki "Kawai ki nakasta ni" "Tabbas zaka nakasa, zaka zama kamar jaririn da aka haifa yau, zaka zama riƙaƙƙe zaka gagara, ubanka zai alfaharin haihuwarka duk da tsinuwarsa na tattare da kai, zaka sake yi rashi, rashi irin wanda baka taɓa yin irinsa ba, zaka samu dukkan wata shahara da ɗaukaka da kake buƙata, amma zaka dauwama a matsayin mata maza" Ihu ya fasa yana ƙoƙarin miƙewa tsaye da ya yunƙura gefen cikinsa yake sake buɗewa saboda shafcecen saran da aka yi masa, jikinsa bashi da wani gurbin da babu sara.Abbasa ta miƙe ta ɗakko wani farin abu a hannunta tana zuwa kan shi ta danne shi da duka ƙarfin daya zo mata, ta ɗauki garin abun ta fara shaƙa masa a hanci yana shaƙa da ƙyar da sauri ya damƙi hannunta ya kifa fuskarsa da hancinsa gabaɗaya, yana ihu da gurnani jikinsa na rawa ya fara sambatu, Abbasa ta ce "A me ka zo waje na?" "Taya" ya bata amsa a raunace idanunsa na lumshewa. "Wasu sun biyo ka ne?" Ya girgiza kai can ya ce "Cinnaku, Cinnaku na fi ƙarfin su" ya dinga juyya kansa can ya ce "Akwai Kimini a tattare dani, ya faɗawa ƙashi wani abu, sun nemi asawa da Tsohuwa....!" Ya kasa cewa komai idanuwansa har yanzu na hango yadda gangar jikinta take ci a wuta. Ita dai Abbasa ta kasa cewa komai ta zuba masa idanu, ta dinga kallon yadda jikinsa je rawa a hankali kuma ya fara saki idanunsa ƙur a saman bukkar cikin fitar hayyaci da yanayi irin na maye yake sambatu tare da kiran sunayen da ita kanta mata sani ba. A hankali ta ce "Mutallab" bai amsa ba sai zuciyarsa kawai dake rawa ta hango hakan ne a yanayin yadda ƙirjinsa ke ɗagawa. Ganin ya zama kamar matacce tsoro ya kama Abbasa ta tuna ashe bai taɓa shaƙar abin da ta bashi ba a yanzu, maganin ƙarfe dana tauri kawai yake sha gashi kuma zaman da ya yi na shekara uku a hannun jami'an tsaro ya sa tsarin ya karye. Ƙwarya ta ɗakko ta jiƙon wani magani tare da ruwa mai zafi ta fara danna goge masa jinin jikinsa sai a lokacin ta lura da gabaɗaya farcen yatsun ƙafafuwansa dana hannu babu ga jikinsa duk alamar an jona masa shokin akan tilasta masa amsa laifin da babu wanda yake da masaniyar komai akai, sun yi masa haka ne da nufin ya amsa laifin kashe matarsa da ya yi. Ta sauke numfashi tare da kallon bakinsa a hankali ta kara kunnenta a tausashe yake cewa. "Ina son ta, ina son ta zuciyata zata fito ita ce wajan ta uku me ya sa.... Ina jinta a ƙasan zuciyata" Tunda suke bai taɓa yi mata zance ɗiya mace ba, haka bai taɓa magana mai tsayin da ya yi a yanzu ba, duk abin da ya saka Mutallab magantuwa ba ƙaramin abu bane ba. Miƙewa ta yi ganin kamar ya samu yin bacci ta fita waje zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Unguwar ta yi shiru saboda zuwan ƴan'sanda wanda da ƙyar suka raba tsakanin mafarauta da jama'ar da suka zo ɗaukar fansan wacce aka kashe zai ya zama kamar an saka kafiyo ne kasancewar babu wanda bai san labarin kisan rashin mutuncin da aka yi wa yarinyar ba. Tiger, spider, rainbow sune suke ta kai kawo a ƙofar gidan Malam saboda basu tsaro kamar yadda Moh ya saba musu ya raine su tamkar mutane hatta mara gaskiya suna ganewa. Da sauri suke tafiya hankali tashe gabaɗaya basa cikin nutsuwa ɗaya sai ɗaga hannu sama take ba'a jin maganarta sai sautin murya. "Ki yi haƙuri" Sa'adah ta ce tana shafa hannunta a ƙirji alamar ban haƙuri da yaran kuramen da zata gane ta girgiza kai tare da sunkuyawa tana buga ƙasa ta ɗaga yatsa sama alamar rantsuwa. "Allah Ya kyauta, da kin bari mun ƙarasa gani ai ya kori ji Bafullatana" daidai nan suka ƙarasu ƙofar gidan ba kowa a rumfar Almajiran sai allonansu da rubar tadawa da ƴan rubobi na bara. Tiger ya ƙare musu kallo yana shinshina su sai kuma ya ja da baya yana ɗaga ƙafa ya basu hanya suka shige cikin gidan. Da Inna Binta dake yashe a ƙasa suka fara cin karo jini na zuba a gefen goshinta ɗan tofinta a bankaɗe Allah Ya sa ba yara a wajan cikin hanzari Sa'adah ta nufeta tana girgizata ta juya ta yi wa Bafullatana alama data bata ruwa bata fahimci komai sai kawai ta kinkimo ruwa bokici guda ta kwarawa Inna Binta ajjiyar zuwa ta sauke a firgice ta miƙe zaune tana furta "Dambun Mufee, a kawo ɗauki jama'a dambun Mufee ƴan ta'adda za su kashe ni" ta ƙanƙame hannunta jikinta ya jiƙe jagab amma har yanzu dambun na hannunta ta miƙe ganin Sa'adah da Bafullatana sai kuma ta ja tsaki "Irin bala'i wallahi Ammo ta haifawa unguwar Birget masifa ɗai-ɗai da ɗai-ɗai zai dinga kashe mu yana zuƙe jininmu ku duba wannan yarinyar ma ya kashe ta kari na uku" Idanun Sa'adah ya cika da hawaye amma ta ɗauke kai ba tare data tanka Inna Binta ba. Inna Binta ta watsawa Bafullatana harara wacce ke ta ihu tana taɓo Sa'adah ta ja tsaki "Kurman banza da wofi gayya masifar, daga haihuwar kurma sai ta ɗan jagaliya" tana kaiwa nan ta shige daƙinta ta samu Mufee tana bacci ta yi maza ta tashe ta, tura mata ɗan guntun dambun ta yi a baki bayan ta cinye ta ce "to sha ruwa kiji abin da kika samu sai kuma gobe, ki yi addu'a ki goge Allah ki gode Muhammadur Rasulullah. Banda ina buɗe ido a gidan nan kema mutuwa za ki yi saboda yunwa kamar taki ƴar'uwar" sai kuma saka dariya sosai "Inna mene?" "Tukunyar dambu ta kife dan ubanki da tuni ba ki lasa ba kema" Mufee dai ta buɗe manyan idanunta irin na Mutallab tana kallon Inna Binta. Ammo ta dinga bin Sa'adah da idanu ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, Bafullatana kuma ta haɗe rai sai girgiza kai take "Ammo don Allah ina Mutallab yake? Da gaske ya dawo an sake shi? Sun wanke shi daga zargin da ake masa, yana ina?" Ammo ta ɗauke idanunta zuwa can gefe tana kallon wani waje daban a ɗakin nata can ta ce "Ki daina kira mini sunansa sallamamman yaron nan a kunnena Sa'adah, ki yi hankali watarana zai iya kashe ki" "Ba zai taɓa kashe ni ba, duk lalacewar shi jinina ne ɗan'uwana ne a wannan halin da yake ciki na ɗauka za ki yi murna Ammo? Za ki ja yaronki jikinki ki nuna masa kulawa gudun kar ya sake lalacewa, kar ki ce za ki yi abin da kikai a baya duk lalacewar Mutallab kece wacce kika haife shi, tun yana ƙaramin kin san zuciyarsa yadda yake da zafin nama taurin kai. Kin san yadda yake da ƙulafucin uwa kodayaushe yana manne dake, me ya sa za ki yi haka?" Miƙewa Ammo ta yi ta nunawa Sa'adah hanya ta ce "Tashi ki tafi gidan mijinki, banga dalilin zuwanku ba ni bani da wani ɗa Mutallab kuma na sani kuskurena ya saka na haifeshi. Wallahi kika sake yi mini maganar tsinannen yaron nan sai na daina amsa gaisuwar ki har abada" tana kaiwa nan ta fice ta bar musu ɗakin, fuuu Bafullatana ta fice daga ɗakin zuciyarta na yi mata zafi Sa'adah ta yi shiru ita dai tana mugun son ƙannin nata ai da ba haka yake ba, ya kamata su amshi hakan matsayin ƙaddara! Washegari Malam na zaune a rumfa yana sauraren karatun wani sabon almajirin shi. Ɗanyaro ne zauna gefe kusa da Malam yana lissafa sabbin kuɗin hannunsa ƴan dubu-dubu sai sheƙi yake ya duba yaga dubu biyar cif ya mayar aljihu ya zaro baƙar leda mai cike da gurasa da nama ya ya fara ci yana ajjiye lemo fanta a gefe. Ajjiye bulalar Malam ya yi ya ce "Ɗanyaro ina ka samu kuɗi da nama haka?" "Bani aka yi Malam" kafin Malam ya sake magana Ɗanyaro ya miƙawa Malam baƙar leda guda mai ɗauke da gurasa a ciki da nama ya haɗa masa da dubu biyu ya ce "A yiwa su Mufee girki Malam" Jiki na rawa ya amsa yana buɗe bakinsa "Da kyau yaron arziƙi, ina ka samu kuɗi fal haka sana'ar me ka fara?" Ɗanyaro ya girgiza kai kawai can kuma ya kalli Malam ya ce "Bana yin sana'a, kyauta ake bani kullum, bani kaɗai ba har Muhajeed da Iro" Malam ya yi sak tunani fal ransa ya sake kallon Ɗanyaro shekarunsa goma rak a duniya a hankali ya miƙe ya yi cikin gida. **** A kusan tare manyan motoci biyun suka tunkaro babban gate ɗin ganin ya rigata kai hancin motarsa ya saka ta rage ta fiya, hannunta ɗaya a saman sitiyarin motar ɗayan kuma ta ɗan riƙe fuskarta a hankali ta lumshe idanunta gajiya ce a jikinta sosai da ƙyar take buɗe tuƙa motar don dai bata san wahalar driver ne. "Fiyya" Ya kira sunanta a hankali cikin muryarsa mai cike da nutsuwa ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi ta kalli wayarta ta manta video call suke yi ma suna haɗa idanu da shi ta ɗauke kan ta gefe tana ya motsa fuska "Fiyya na miki wani laifi ne? Kin sauya" "I am sorry ina driving we'll make a call later" ya zuba mata idanu cike da so da ƙauna yana jin ina ma a janyo ranar aurensu da Fiyya a ce gobe ne? Ya sauke numfashi zuciyarsa na buɗe a hankali ya ce “I adore you Fiyya" ta buɗe idanu ta kalli cikin idanunsa sai kuma ta murguɗa masa baki ya buɗe idanu sosai sai ya girgiza kai yana dariya ya matso da fuskarsa dab da camerar "Na ji kamar ina shaƙar numfashinki...." Ya yi shiru jin ana knocking ƙofar motar da take ciki, itama ta juya ganin wanda yake tsaye ya saka ta ɗan yi murmushi baya ganinta saboda duhun gilas ɗin motar amma murmushi mai kyau ne a fuskarsa. Ta cikin wayar ya ce "Waye?" Tana ɗaukar jakarta a taƙaice ta ce "Yaya Junaid ne" "Ok" ya yi sai kuma ya ce "Fiyya" ta ɗago idanunta da sukai laushi ta kalle shi dasu can ƙasan maƙoshi ya ce “I love you Fiyya" da sauri ta kashe call ɗin tana haɗe fuska ta ɗauki wayar ta fita daga motar. "Yaya J" yana murmushi ya ce "Manager" ta ɗan yi murmushi kawai ya amshi jakar hannunta "Me kika zo da shi" "Ba kyau bincike J" ya jinjina kai suka nufi shiga gate J ya kalli driver ya ce "Ka shigo mata da motar, she left the key inside the car" Fiyya ta marairai ce fuska tana mannewa jikin J ta ce "Yaya J na gaji sosai" "Sannu Manager, ko goyaki zan yi?" Ta buɗe idanu sannu yake ta yi mata har suka shiga babban parlon gidan ƴan samari wajan biyar a zaune a parlon duk dawowar su daga aiki kenan. Wajan tare suka dinga cewa "Sannu Manager" ta shige tsakiyar su tana kwanciya a cinyar Marafa ta ce "Thank you brothers, ku yi mini tausa akwai labari" "Gulma dai ba labari ba, daka dawowa ko wanka ba ki yi ba kin zaunawa mutane a jiki ƙazamar banza" Shiru ta yi masa don basu fiye shiri ba sosai ta juya idanunta rufe, tana jin yadda Marafa ke ta danna mata farar ƙafarta. Yaya J kallonta kawai yake with different thinking running on his mind. Gabaɗaya suka juya jin tafiya cikin sauri ana sakkowa daga saman bene shiru duk sukai suna binsa da idanu domin basu san ya dawo gidan ba, hannunsa ɗaya zube cikin aljihu farar riga ce a jikinsa ta kakin sojoji a gaban rigar wajan gefe an rubuta A.A MARAFA. "Kee!" Ya faɗa a tsawace da sauri Fiyya ta buɗe idanunta lokaci ɗaya kanta ta sara sosai tsawar ta ratsa kanta, ta miƙe zaune fuskarsa babu walwala kamar yadda itama ta yi kicin kicin da rai "Tashi a nan, stupid kawai" ta miƙe tsaye tana murguɗa baki ko inda yake bata kalla ba ta nufi saman bene kai tsaye daƙinta ta nufa idanunta cike da bacci ta faɗa saman gado cikin ƙaramin lokaci bacci ya ɗauke ta. Firgigit ta farka jin sautin labaran ɗ da ake faɗa a gidan rediyo wacce take cikin ɗakin nata, ta miƙe tsaye ta ɗauki rediyon ta ƙanƙame a jikinta tare da lumshe idanunta wasu hawaye masu zafi suna shiga bin idanunta. Ta cikin idanunta take hango fuskarsa a lokacin da rigima ta haɗa su da ita sai take ganin kamar yanzu ne komai yake faruwa. Students ne an cika sosai saboda class partyn da ake yi na kammala exam maza da mata babu teacher ko ɗaya tunda ta shigo hall ɗin makarantar tasu take duban inda zata ganshi. Cikin sa'a ta ganshi yana zaune saman window sanye da gajeren wando fari tas sai armless ɗin riga wacce duk aka yanke hannunta gashin kansa rabi a aske ya zubawa wani tafkeken gidan masu kuɗi idanu ta waje baya ko ƙiftawa kamar an ce ya juya ya ganta tsaye ta zuba masa idanu yaja tsaki kafin ta yi magana an shigo an ce "Mutallab, principal yana nemanka an kai ƙarar ka wai kana son Fiyya" Ya ware idanu abin da bai taɓa zuwa tunaninsa ba kenan sai kuma ya cije baki "Shi principal ɗin ubana ne Malam Abdullahi kenan?" Ya juya ya kalleta sosai ya ce "Sai godiya, ni? Kuma ke hauka kenan" "Kai ne mahaukaci" furucin ya fita daga bakin Fiyya "Kuma na yi maka nisa, kasan yadda nake da masoya a makarantar nan amma ni ubana ba soyayya ya kawo ni ba, karatu zan yi ina da buri mai faɗi da zan cimma" Ya miƙe tsaye yana kallonta daga sama har ƙasa a ransa yana ƙissima abu "Shi uban naki can ta matse masa, karatun banza kawai ka zama mai iko shine" "Ba dai ubana sai dai....." Ya buɗe idanu sai kuma ya fasa abin da ya yi niyya ganin hawaye a idanunta abin da bai taɓa gani ba. Da sauri ta fice daga hall ɗin ta zaga baya ta durƙushe a wajan tana fashewa da wani irin kuka kamar zata haɗiye zuciya "Daddy na shiga uku ina son Mutallab" Ƙanƙame redion ta yi tana sake fashewa da kuka jikinta har jijiiga yake ta ce "Na shiga uku Daddy, ba zan iya ba I can't do it ina son shi. Kamar daga sama haka ya faɗo cikin gidan, jikinsa duk liƙe da bandeji jini na ɗiga kaɗan-kaɗan kwana biyu yana jinyar raunin bai san waye ya yi masa ɗinki ba. Idanunsa jajur har lokacin saboda bai gama dawowa daidai ba sai muzurai yake yi ya ja ya tsaya yana kallon murhun da aka sauke abinci akai ya juya ya kalli ɗanwaken dawar da Inna Binta ta yi ta shiga daƙi ɗakko magi ta barbaɗa ko arziƙin yaji bai samu ba, yaja kwanon da hurɗu-hurɗu yake tura ɗanwaken kafin wani lokaci ya kammala cinyewa tas ya zube a wajan ya kwanta ya rufe idanu, wata nutsuwa yake jin daya kwanta a tsakar gidan mahaifin nasa. Ya yi kamar bacci yake yana jin Inna Binta ta lailayo ashar ta ƙunduma ta ce "Wanne ɗan abu takazar ne ya cinye mini abinci Mufee wanne mayunwacin ne mara godiyar Ubangiji" tsit ta yi ganin Moh kwance hannunsa duk manja taja baki ta tsuke ta ɗauke kwanan tana suɗewa a zuciyarta tana jan Allah Ya isa. Har ya shiga ɗakin Ammo ta bankaɗa labule ta ce "Wallahi abincin da ɗan ta'addar ɗanki ya cinye mini Allah Ya isa, kawai kin haifa mana jaraba ko ɗanɗana ɗanwaken ban yi bafa ya cinye" ta dinga zagin Ammo ta uwa ta uba ta shige ɗaki tana sake suɗe kwanon da ƙyar ta samu rancen ɗari biyu ta yi cefane da ledoji ta dafa. Tana shiga ɗaki ba jimawa ta ji an bankaɗo labule sai ta zuciyarta ta buga ganin shi tsaye hannunsa riƙe da gora ya suke askara a gefen ƙugunsa ga gori a hannunsa, ya juya ya kalli Mufee da hannu ya yi mata alama data fita cikin sauri ta fice tana fita muryarsa a daƙushe kamar dole ya ce "Tiger spider a yi mata aiki" manyan karnukan suka faɗa cikin ɗakin Inna Binta ta fara ihu tana maƙale jikin sif "Nafsi nafsi jama'a na shiga uku ya Allahu Ya Rahmanu, don Allah ka yi haƙuri Muɗallabi zan bawa Ammo haƙuri ka rufa mini asiri kar Mufee ta zama marainiyya" Haushi kawai karnukan suke Tiger na kai mata cafka Inna Binta ta fashe da kuka fitsari na bin ƙafarta ta ce "Hal'àtaka hadisul gashiya ni Binta na shiga uku" Moh ya ce "Sai godiya" gabaɗaya karnukan suka tsaya cak Inna Binta na haki ta jiƙe gabaɗaya da fitsari har lokacin tana maƙale jikin sif kamar ba zai magana ba ya ce "Bani ƙudin nan" jiki na rawa ta miƙa masa ɗari biyar ɗin hannunta ya amshe ya yi waje ta sake sif ɗin ta fashe da kuka tana faɗin "Tsinannen yaro manta ganin yaron dake son uwarsa kamar mutuwa ba irin shi" Moh na fita ya leƙa ɗakin Ammo ta ɗaga kai tana ganinsa ta ɗauke fuska ya yi ta kallonta ya jima tsage kafin ya sauke labulan ya juya. Yana fita wani babur na tsayawa a gabansa aka cillo masa takarda da gudu aka ja babur ɗin tare da barin wajan. Ya ɗauki takardar ya buɗe rubutu ne bai fi layi biyu ba a hankali ya fara karantawa. _Mai dawa baka gajiya? Sau dubu zaka kula mace sau dubu zamu kashe ta. Karo na uku kenan ga misali akan matarka nan_ da jan biro akai rubutun ya juya da sauri amma tuni babur ɗin ya ɓace ɓat waye wannan? Su duka shi ne silar mutuwar su kenan? Waya ya amsa hannun wani Almajiri ya kira wata number ana ɗaga aka ce "Sai godiya" Ya numfasha "Duk inda ƴan daba suke ka haɗa mini su" ta cikin wayar aka ce "Mene haɗinka da daba ko dai ka fara shaye-shaye a state cid ɗin?" Moh ya cije baki ya ce "Zan fitini mutane, na ji daɗin zama can" "To me za su yi maka?" Wannan yaran da suka sare ni iyayensu za su ɗauki sabbin ciki yau, ƴan cikin gari ne a yi mini kan me uwa jawabi" yana faɗin hakan ya kashe kiran ya goge number tas ya lumshe idanunsa ya buɗe sai kuma ya cije leɓe zuciyarsa zafi take sosai ji yake dama ya yi kuka, amma ba a haife shi don ya zubar da hawaye ba ya ɗaga idanu sama ya ce "Da gaske ni na kashe ta amma ba zaku taɓa sani ba" daidai lokacin mafarauta suka kawo kai suna busa ƙaho da buga gangaga suka zagaye Moh ana "Sai Mai dawa ina uban wasu ga namu wuya a ina wuya a daji, kai ne mai Tiger kai ne mai gadon tawada" Jikinsa ya hau ɓari da karkarwa tsumin shi ya motsa idanunsa na ƙaƙƙafewa ya yi kururuwa tare da ɗaga gora sama ya ja ya ƙame sai jikinsa dake rawa ya fara "La'ilahaillahu, sai ni ɗan babana Malam Abdullahi ɗan malam ɗan gatan Ammo ƙanin Sa'adah ƙanin Bafullatana waye ce bani ba Muɗallabi sarki Mai dawa da jeji" gabaɗaya suka zagaye shi suna sake zuga shi daidai lokacin kuma suka ganta kamar daga sama..... *In sha Allah za ku ji abin da baku taɓa ji ba 😘* 08164069385 WhatsApp only [10/4, 9:17 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 3 Nimcyluv Bright pens....Second batch Da sauri ya nufe ta kamar zai kai mata cafka, ta yi saurin ja baya idanunta cikin nasa. Yana tangaɗi ya ja ya tsaya a gabanta tare da ƙura mata idanunsa da suke lumshewa, har yanzu jikinsa ɓari yake domin basu daina buga ganga da ƙahon da suke busawa ba kamar masu yin gangi. Hannunsa ya ɗaga musu cikin sauri suka daina abin da suke, cikin izza da gadara ya basu umarnin tafiya har lokacin idanunsa yana kanta ganin yadda take kallon shi kamar ya ta saba ganin halittarsa. "Ban yi zaton a haka zan ganka ba, autan Ammo me ya sa?" Ya ɗauke kansa yana haɗe fuska sosai ba wargi banda cewa ita ce ba zai taɓa tsayawa ba. Cikin raunin murya kamar za ta yi kuka ta ce "Me za ka yi da wuƙa haka?" Ya buɗe ido sosai sai bai magana ba, a hankali ma ya bi gefen ta zai huce ta yi saurin riƙe masa hannunsa tana faɗin "Ni ɗin ma? Yau za a ji kan mu da kai, kar ka faɗa mini sauyin da ka yi ya zagayo har kai na?" Ya ɗago kai ya kalle ta ya kalli hannun data riƙe shi da shi, hannunta fari tas saɓanin nasa da yake mai kauri kuma baƙi irin na majiya ƙarfin nan wanda suke tashe akan shekarunsu. "Don Allah ka tsaya mu yi magana, ni ko gidan ba zan shiga ba wajanka na zo" ya cije bakinsa ya mai da kai gefe cikin muryar mai kauri ya ce "Kin ci darajar Ɗan Amina, mene sakin?" Ta girgiza kai kawai tana duban gefe dakalin dake wajan ta gani ta je ta zauna akai, ta yi masa alama ya zauna amma ko motsi bai yi ba, ta san cewa yana jinta amma hankalinsa na kan hanya sai waige-waige "Mutallab ka kalle ni bafa wani zai kawo maka farmaki ba" ta nisa idanunta cike da ƙwalla ta ce "Don Allah kai ne ka kashe ta? Ba zargin ka nake ba Autan Ammo ni me iya rufa maka asiri ce idan ya zama kana da laifi ka faɗa mini gaskiya na maka alƙawarin ko Ammo ba zan faɗawa ba, ka kashe matarka ko ba kai bane?" Ya juya da wani irin sauri yana kallon fuskarta da take kallon shi cike da damuwa, idanunsa ya yi jajur naman jikinsa na motsawa ya kasa furta komai. Miƙewa Anty Hameeda ta yi tana girgiza kai kuka na cin ƙarfinta "Ko minti ashirin ba mu yi da kai maka matarka ba, sai labarin mutuwar ta muka ji da kisan wulaƙancin da aka yi mata. Mutallab kai ne fa muka gani tsaye akan gawarta, kai ne fa riƙe da wuƙar da aka kashe ta da ita jikinka duk jinin matarka innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na kasa yadda ka kashe ta, daman soyayyar da ka nuna mata na iya fatar baki ne?" Wani irin ihu Anty Hameeda ta yi tana kaiwa jikin bango ganin ya ɗaga hannunsa ya yo kanta sai kuma ya tsaya cak, a hankali da baya da baya ya dinga ja yana ƙare mata kallo sai kuma ya taune bakinsa idanunsa kamar zasu zazzago don girma kallo ɗaya idan ya yi dasu sai an razana da ƙyar ya iya ware laɓɓansa biyu da sukai masa nauyi sosai ƙasan zuciyarsa na ta fasa banda cewa Anty Hameeda ce tabbas da sai ya karya ta gida huɗu. "Ni na kashe ta, ta cancanci haka ne" ya juya da sauri Tiger da spider da rainbow suka bi bayansa kamar zai tashi sama haka ya sha kwana. Zubewa Anty Hameeda ta yi a wajan tana rushewa da kukan baƙin ciki, su waye suke da saka hannu wajan lalacewar Mutallab? Ba komai ta sani ba ita ba ma'abociyar zaman garin bace ita da mijinta ta dinga kuka da ƙyar ta rarrashi kan ta, ta miƙe tsaye kamar zata shiga gidan nasu sai kuma ta fasa tana ƙoƙarin barin wajan ta ji Malam ya ce "Hameedatu me kike anan ina mijin da yaran naki?" Kanta a ƙasa ta ce "Suna gida, ina yini Malam?" Ya jujjuya yana kallon hannunta ganin babu komai ya ce "Ba za ki shiga bane?" Ta girgiza masa "Zan juya wajan Mutallab na zo" ya jinjina kai domin ba wannan ne a gabansa ba. "Ba wata mutalla da zan iya samu a wajanki na siyo wainar rogo?" Ta buɗe jakarta ta zaro kuɗi tana irgawa ya yi maza ya fisge ya ce "Mene na lissafi? Maza jeki wajan yaranki kuma na ja kunnenki babu ke babu yaron nan idan ba su kike watarana ya ja miki masifar da za ki ƙare rayuwarki a gidan ɗan kande ba" bata ce komai ba sai data juya zata tafi ta ce "Duk lalacewar Mutallab kai ne ka haife shi, jininka na wanzuwa a nasa" tana kaiwa nan ta yi gaba abinta saboda ɓacin rai da damuwa ko gabanta bata gani sosai. Moh na kwance a saman wani dutse idanunsa a rufe tun bayan barin shi wajan Anty Hameeda ya zo wajan ya kwanta, zuciyarsa a cunkushe take babu gurbin samun sauƙi a cikinta duk yadda ya ke son tuna waye shi me ya sa ya zama haka sai ƙwaƙwalwarsa ta yi hooking, ya ɗauki zafi sosai ta yi ta processing ya ji Ammo ɗinsa kawai yake son kasancewa da ita yanzu. Ya motsa kaɗan zazzaɓi ne sosai a jikinsa saboda saran da aka yi masa bai gama warkewa ba, baya kuma shan magani wacce zata iya kula da shi baya jin zai iya zuwa wajanta. Ya ƙanƙame jikinsa sosai abubuwa da yawa baya son tunawa sai ya cimma muradin zuciyarsa sai ya ɗauki fansa na abin da aka aika, sai ya bayyana abubuwa da dama tunda har suka bari ya shiga cikin gidan yari ya kuma yi shekaru uku a Cid ya rayuwa cikin masu aikata manyan laifuka. A sama ya ji an kira sunansa "Mai dawa, sarki mai jeji" bai buɗe idanunsa ba, bai kuma ɗauki murya ba haka baya buƙatar sanin waye don hakan babu abin da zai ƙare shi da shi. Ya nemi waje ya zauna yana furta "Ka saɓe Mai dawa ka basar, fansa kake buƙata ba raunin zuciya ba, ka ajjiye tunanin baya ka fuskanci burinka ka zama abin da kake muradi kafin aga bayanka" har lokacin bai buɗe idanu ba, ko inuwarsa bata motsa ba. Mangal ya ɗaga kai yana busawa samaniya hayaƙin sigari "Idan kana son yin bacci cikin nutsuwa ka manta komai ya kamata ka sha wannan" ya zaro abu a aljihu yana kalle-kalle sai a lokacin Mai dawa ya buɗe rinannun idanunsa ya juya ya kalli mai maganar irin kallon waye kai? Mangal ya ce "Ka dake musulmi akul musulmu, zuwa na yi na taimaka maka" "Riƙe wannan tiramol ce, ko doki ya sha sai ya gane barno gabas take kana afawa za ka ji zam-zam komai ya zama labari" Mai dawa zubawa ƙwayar idanu shi bai taɓa shan ta ba, bai taɓa shaye-shaye ba ya juya ya kalli Mangal "Da gaske zan yi bacci?" "Darr ne ai aikin wannan kamar yankan wuƙa ne, mai ƙirin ce da ƙyar aka bani ita ina karɓa na doƙu nan" jikin Mai dawa na rawa ya amshi ƙwayar guda ɗaya ya cilla cikin bakinsa, yana runtse idanu ya yi shiru. Mangal ya zubawa Moh idanu a ransa yana jin wani daɗi da kuma farinciki bai taɓa yin aikin da za a bashi kuɗi masu yawan da aka ce ba irin na yau, gashi ya yi nasara Moh ya sha ƙwayar. Jikin Moh ya ɗauki rawar zafin zazzaɓi duk da irin dariyar da yake da ita, gashi duk inda ya motsa ciwon shi jini yake babu wani wanda zai iya duba lamarinsa sannu a hankali ya fara dafe kan shi da wani irin gurnani yaga sama na jujjuya masa ya ɗaga hannu da niyyar ya tare sama ya faɗo daga saman dutsen sai saka hannu yake yana tare sama a hankali kuma jikinsa ya fara saki yana jin wani shuu a tsakiyar kansa yana game jikinsa gabaɗaya zuciyarsa da tunaninsa suka dinga kissima masa kawai ya kashe kansa ko ya cinnawa gidansu huta gabaɗaya kowa ya mutu har shi. Ganin laɓɓansa na motsawa alamar yana magana ba'a ji sosai ya saka Mangal matsawa tare da kafa kunnensa a bakin Mai dawa cikin mawuyacin hali yake furta "Safiyyerh... Safiyyerh...Safiyyerh" Mangal ya maimaita sunan a fili “Safiyya?” wace haka? Ko ita ce wacce ta mutun wacce aka kashe? Ya miƙe tsaye ya ɗauki wayarsa wata number daya haddace ya saka ya kira ana ɗagawa Mangal ya ce "Sakin nan ya kammalu, yanzu zan zo a taya na amshi fararen" shiru ya yi yana sauraren mai maganar kafin ya ce "Jira jira jira nifa cikin uwata aka haifan ba ɗan zina ba, na maka al'ƙawarin dole zan bawa Mai dawa ƙwayar kuma da sannu zai zama namu. Sai dai na ji yana kiran sunan wata ɗawa wai Safinu ko Safiya?" Ya ƙara yin shiru ya numfasa ya kalli Moh dake kwance a wajan ya ce "A'a Oga ni bana sabga da masu ɗan kwalin nan. Da ƙirin ka oga kanka baya kullewa a fice kake sai na doƙu yanzu" Kashe wayar Mangal ya yi kuma ya goge kiran cikin sauri kuma ya bar wajan. Baya tantance halin da yake ciki, sai dai yanayin na yi masa daɗi sosai shi ba'a sama ba shi ba'a ƙasa yana fatan ya dauwama har ƙarshen rayuwarsa. Duk da a cikin giyar maye yake bai hana shi gano fararen kyawawan idanunta masu matuƙar ɗaukan hankali ba, a lokacin da take masa wannan duban ji yake kamar ba zai taɓa aikata abu makamancin haka ba amma ƙuruciya da wawta ya saka komai ya wakana a lokacin da duk su biyun basu ankara ba. Gani ranar yake kamar yanzu a cikin idanunsa ya juya da ƙyar yana buɗe idanu zuwa gefe guda sai fara hango kansu su biyun a shekarun da suka huce suna tsaye tana jifansa da wani irin kallo. Suna tsaye za su shiga practical a lokacin, ya jingina da jikin bango ƙafarsa ɗaya a jikin bangon ɗaya a ƙasa ya harɗe hannayensa duka biyun a ƙirji students ɗin yake kallo yana mamakin abin da ya saka ƴan mata ke burge wasu mazan, as a man kuma good man kawai ka nemi kuɗi ka yi arziƙi ka shahara a duniya shi ya fi, ka zama mai iƙo da faɗa a ji, ka zama wanda zai iya samun abincin da zai ci da safe kuma ya ci da rana ya ci kuma da dare ya bawa ƴan'uwasa da duk mai jin yunwa ya zamana kuma ka kasance mutumin da ake shakka duniya ta san da zamansa bawai kana namiji ka ƙare a wajan wata yarinya ba. Yana cikin wannan tunanin ya ji an ja mugun tsaki ya buɗe idanu ya ganta sosai ya buɗe idanunsa da suke a rufe kodayaushe cike da gashin idanu masu tsayi. "Kai ai babu macen da zata soka a school ɗin nan, sai dai kaga ana soyayya" bai taɓa tsayawa ya tanka ta ba sai lokacin har zai mata shiru sai ya ce "Ok" ta haɗe fuska "Saboda macen abinci ce ko iskar shaƙa daya zama dole Mutallab ya amfana dasu?" Ta yi masa sheƙeƙe tana nuna masa ɗaliban makarantar da kana ganinsu zaka san iyayensu nada arziƙi sosai kowanne a students ƙuruciya da tashen balaga na ɗawainiyya da su. Ta ce "Mata ai sune jin daɗin maza, kai fa mace ko kiss bata taɓa yi maka ba a school ɗin nan" Mutallab ya yi ta kallonta daga sama har ƙasa "Matar Moh zata zama mai irin halin MOH" har ya juya sai yaga bata ci bulus ba ya tako har inda take ya zuba idanunsa cikin nata kamar yadda take kallon tsakiyar nasa idanun yana sake matso da fuskarta "About the kiss, ƙilan Moh ya ji ƙan ki ya yi miki don naga shi kike buƙata" Tsoro ya kamata amma ta dake ta fara ja baya ya yi saurin saka ƙata ya falleta kamar zata kita ya saka hannu ya cafko gaban wandon uniform ɗinta ya dawo da ita dab dashi yana sauke mata numfashi a hankali kuma ya ɗora fuskarsa..... "Mai dawa" kiran da aka yi masa ya saka bidiyon abin da ya faru a baya saurin gogewa a idanunsa har lokacin idanunsa na kafe waje guda sosai yake son sake tuna abin da ya faru a lokacin ya gagara. Goje ya ce "Nan ka auno kenan, na samo sha ɗayan gayen nan. Ya naga kamar a buge kake?" Goje ya faɗa yana tattaɓa jikin Moh ya ji zafi sosai idanunsa kuma ya kaɗa ya yi ja ya san babu abin da zai fahimta koda ya yi masa bayani "Mene haɗin mafarauci da shaye-shaye?" Shi dai ya yi shiru kawai zumbur kuma ya miƙe tsaye kamar wanda ya tuna wani abu ya juya idanu wuƙar da ya gani a jikin Goge ya fusga duk yadda Goje ya yi da shi amma ya kasa amsar wuƙar cikin sauri kuma ya mara masa domin ganin me zai aikata? Tafiya suka dinga yi har suka kawo titi ya tsayar da mai napep ya faɗa shima Goje ya faɗa ciki. Shi kansa bai san ina za a kaisa ba. Tafiya suka sosai har suka ƙarasu daidai wajan wani ƙaton kamfani wanda kaf Kano babu wanda bai san zaman wannan kamfanin ba. Iya haɗuwa ya haɗu ginin kamfanin ma abin sha'awa ne ga masu tsaro ta ko'ina. Ya tsayar da mai napep ɗin ya sauka "Kuɗi na?" Ya buɗe ido sai ya share "Malam haƙƙina na daƙƙoka daka waje mai nisa ina da wajan zuwa" Goje ya ce "An cinye" "Kut, ni da haƙƙina daman tunda na daƙƙo ku na ji kuna warin wiwi na san cewa ɓarayi ne ku, cikakken ɗan zamani ne nima ku bani kuɗina yanzu ku na daki kuɗin" Goje ya ce "dan babarka zo ka daka idan ka haifu" mai napep ɗin ya share shi, ganin Mai dawa ya yi shiru yana kallo kamfanin ya nufi inda yake ya damƙi wuyansa ya ce "Kai ka tsare ni ai....," kafin ya ƙarasa maganar Mai dawa ya damƙi hannunsa ya matse ya bada sauti ƙass har lokacin ya kafe kamfanin da idanu. Mai napep ɗin na ihu yana neman ɗauki Goje ya zaro wuƙa yana bubbuɗe jajayen idanu hakan ya saka ba wanda ya zo wajan kowa saurin barin hanyar yake gudun kar tsautsayi ya faɗa masa. Mai dawa ya saki karyayyen hannun mai napep ɗin ya ƙara damƙar ɗayan zuciyarsa na tafasa har yanzu ba komai yake ganewa ba, ya sake karya hannun daman ba tare daya sake shi ba ya ce "Goje" "Mai dawa sarki mai jeji, sai godiya" "Kamfanin meye wannan? Na waye kuma?" Goje ya kalli tafkeken kamfanin da manyan motoci ke ya shiga da fita kafin ya ce "Sai godiya, ciki ne a kan sabgar nan bani da ilimi akan wannan massarafar" Mai dawa ya saki mai napep ɗin da ya karya masa duka hannunsa biyu yana ja da baya a hankali ya ce "Ina son shi, ina son ya zama mallakina" cikin sauri Goje ya ce "Me kake so?" "Kamfanin" Tana zaune akan kujerar dake haɗɗan office ɗin, cikin nutsuwa dake danna system ɗin gabanta files da yawa cike saman table ɗin hankalinta na kan aiki sosai kana kallon fuskarta zaka san serious ce ita akan aikinta bata da wasa ko kaɗan. Brown suit ce a jikinta mai riga da wando ta yi rolling kanta da mayafi zagayayyiyar fuskar ta fito sosai ta saka wani shade a idanunta baƙi. Wayarta ta fara ƙara alamar kiran ta san tunda ya fara ba zai daina ba, cikin nutsuwa ta murja kujerar ta yi ba, suu kuma ta kujerar zuwa inda wayar take ta ɗaga kiran tana sawa a hands free "My manager" ta ɗan buɗe idanu ta cikin glasses ɗin ta yi shiru tana ta danna system a hankali ya ce "Maamah" ya kira ta kamar yadda suka ce mata ta sake yin shiru domin bama ta jinsa sosai "Fiyya ina miki magana?" "Yaya J yaushe zaka fara ɗaukan aikinka very serious, ina kan aiki fa" ya yi murmushi mai kyau tana jin sautin shi a kunnenta "Sanda kika so na zama Mamaa" "Uhm kiran fa?" "Kin ci abinci, nina manta Captain ya saka na kira na tambaye ki" cak Fiyya ta tsaya da abin da take ko dai bata ji daidai ba "what?" Ya ce "Kin ji ai" a taƙaice ta ce "Na ci" ya ce "Good, ƙarfe nawa za ki tashi?" "Ina da meeting Yaya J ka biyo ka ɗauke ni i can't drive cikina ciwo" cikin sauri ya ce "Subuhanallahi! Bari na zo na duba ki ko kawai mu tafi gida" kashe wayar ta yi domin ba wani ciwon ciki da take so take ta saka kanta busy sosai ko zata manta da wasu abubuwan. Knocking aka fara tana ji ta yi shiru can ta ce "In" ya buɗe ya shigo idanunsa ya sauka a jikin sunanta dake manne a table ɗin “SAFIYYERH A. MARAFA” ya ɗauke idanunsa yana rusunawa ya ce "Good day Maa" Da hannu ta yi masa nuni ya zauna bayan ya zauna, still idanunta akan system tana danna keyboard ta miƙo masa file ya ɗauka ya ce "Wannan fa?" A nutse ta ce "I have to ask, daga ina file ɗin nan? Wanne kaya aka fitar aka samu ruɓanyar kuɗi kashi wajan goma cikin awa guda Accounter?" Ya ɗan shafa kai ya ce "Maa ni ma haka na gani, kawai aka ce na kawo ki saka hannu" "To ba zan ba" ta ce a taƙaice. "Maa ya zama dole fa" A hankali ta ɗago idanunta sai kuma ta cire glasses ɗin idanunta manyan fararen idanunta tas a kan shi ya yi saurin ɗauke nasa idanun saboda kwarjin da ta yi masa "Ni ce Manager, ka faɗawa duk wanda ya turo ka cewa ba zan ba, ina buƙatar explanation me aka siyar a kamfanina nan har aka samu shigowar kuɗi kimanin 5.1B cikin awa guda, ba details na abin da aka siya sai file na zuwan kuɗin kuma yanzu ana buƙatar fitar dasu daka account ɗin kamfani? This is complicated" zai yi magana cikin tsawa ta ce "Out of my office accouter" cikin saurin ya miƙe tsaye yana ficewa daga officer ɗin. Numfashi Fiyya ta sauke ta rufe idanunta da sauri kuma ta buɗe jin an shigo ba tare data bada umarnin a shigo mata officer ba. Cikin sauri ta miƙe tsaye tana ɗan ja baya ta shiga ƙare masa kallo daga sama har ƙasa ta yi mamaki to babu security a ƙofar office ɗin nata ne? Da ƙyar ta ja numfashi tana saukewa ta ce. "Who are you? Waye kai. For more information 08164069385 WhatsApp only.[10/6, 9:07 AM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 4 Nimcyluv *Bright pens....Second batch* Ƙarewa office ɗin kallo ya yi yana buɗe idanunsa akan Fiyya wacce ta ɗan ja da baya tana ɗauke kanta gefe. "Ya Allah i really missed her, Safiyya A. Marafa" ya furta yana kallon makaken photon Fiyya dake cikin office ɗin kafin ya ƙarasa ciki murya a hankali ya ce "Wa kike tunanin zai zo banda mijinki Fiyya? You're enjoying teasing me" sai a lokacin ta sauke ajjiyar zuciya a ɓoye tare da ɗan yin murmushi mai kyau wanda ya saka shi lumshe idanunsa ya buɗe "Like this.... I missed you completely Fiyya ba shiri na dawo gida fa" "Ina yini ya hanya?" Ashraf na kallon files ɗin gabanta ya ce "Allahamdulilah. Ya naki aikin Manager?" Ta ce "Lafiya, me ka zo yi a kamfanin ko kana da business damu ne?" "Eh, babban business ma" tana kallon system ba yabo babu fallasa ta ce "Ohh" kallon ta ya dinga yi yadda take operating system ɗin cike da nutsuwa fuskarta a kame ba wargi hakan bai hana kyan fuskarta bayyana ba ya ja numfashi ya sauke yana jin wani abu sosai na fuskarsa a kan Fiyya ya kalli agogon hannunsa ya ce "Ko gida ban je ba, ina son na samu nutsuwa da kallon fuskarki dear" kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta ce "Ok" mamakin halinta na ko ina kula yana damunsa cikin damuwa yana sassauta murya ya ce "Fiyya" ta ɗago ta kalle shi sai kuma ta zame idanunta. "Na kasa fahimtar me kike nufi dani Fiyya anya kina so na kamar yadda nima nake son ki? I told you na dawo saboda ke amma ki ce mini wani ok? To hell with the ok ɗin na tsani irin wannan ɗabi'un naki, da na yi miki uzurin rashin sabo ne amma for good 5years muna abu ɗaya dake? Idan customers ne kya musu fara'a ki yi welcoming nasu, amma ni da zan zama mijinki kwana kwana nan kike ma haka, ko wanne gardi ya zo office naki kin zama wata kamar jerry abar kallon kowa" ya girgiza kai cikin damuwa da ƙunci yana zare gilas ɗin idanunsa tare da buga table ɗin gabanta ya ce "A cikin abu biyu dole ne a yi guda" Kallon Ashraf kawai take ta tabbatar yana da anger issues tama rasa me za ta ce masa don takaici ya zo har office ɗin ta kuma yana yi mata hayaniya, yana ƙoƙarin tara mata jama'a. Ko motsi ba ta yi ba, tana juya kujerar da take kai a hankali idanunta zube a kansa. "Ina ji Ashraf" bata taɓa kiran sunansa ba sai yau hakan ya saka ya kalleta da sauri ransa ya ƙara ɓaci. "Aure ko aiki, ya zama dole ki zaɓi guda ɗaya a ciki" "Ok" ta sake cewa tana miƙewa tsaye tare da ɗaukar jakarta da wayarta da makullin mota ta zaga a hankali zata shige shi ya yi saurin saka hannu ya riƙo nata hannun cikin sauri ta kalle shi tare da jefa masa wata iriyar harara sakinta ya yi ya matsa dab da ita yana sauke mata hucin numfashin ɓacin ransa dake fitowa tun daga ƙasan zuciyarsa. "Ki bani amsar abin da na buƙata kafin ki fita, aikin ki ko aure" Ta taune leɓenta tana ware masa manyan idanunta sai kuma ta kalli wayarta tare da buɗewa ta shiga wajan photos pictures ɗinsa ta nemo wanda ya yi kyau sosai ya saka ƙananun kaya lokacin bashi da lafiya ta je duba shi ya fito harabar gidan tana murmushi ta ce "My patient, bari na ɗauki photo as evidence karka mutu bani photon nunawa yarana masoyin da ya tafi ya bar Fiyya" a lokacin juyawa ya yi ya kalleta daga kwancan da yake ya wurga mata harara sai kuma ya miƙe tsaye yana nufar inda take ta yi saurin yin baya tana masa wani irin murmushi ya tsaya yana kallon ta sai kuma ya ce "To make you clear, ba ki da wasu yara sai na Ashraf, ba ki da wani miji sai Ashraf ba wanda za ki yi wa takaba sai Ashraf.... Ashraf na Fiyya ne Fiyya kuma ta Ashraf ce in sha Allah" murmushi kawai ta yi bata ce komai ba ta ɗauke shi photon yana langwaɓe kai gefe. Fiyya ta shafa screen ɗin wayarta tana kallon photon kamar yanzu ta ɗauka cikin muryar mara hayaniya idan tasu ta ce "Ya ce wai na zaɓa aiki ko shi, kar ya buƙaci jin amsar daga bakin Fiyya" fisge wayar ya yi "Dole ki bani amsa yanzu ba sai anjima ba" ta gyara tsaiwa tana fuskantar shi da kyau a hankali ta matsa dab da shi ta ce "Allah Ya baka wacce ta fi Fiyya" Ashraf ya yi sak can ya ce "Me kike nufi?" "Ina nufin na haƙura da auren, na zaɓi aikin" tana kaiwa nan ta fisge wayarta cikin sauri ta yi waje ya bita da kallo zuciyarsa na ta fasa. Tana fita ta kalli security ta ce "Idan ya fito a rufe mini office" waje ta yi ko Elevator bata tsaya shiga ba ta sakko ta bene dake a wajan 5 floor office ɗin nata yake. Sai gaisheta ake yi amma ba wanda ta saurara idanunta har dishi-dishi yake saboda ɓacin rai. Misalin 1:43 dare ya nutsa ana samawa zuciya nutsuwa ya yinda kowa yake bacci a lokacin ne safiyarsa ta waye. Ya tsaya a ƙofar gidan yana kallon gate sosai ya jima a wajan kafin ya juya ya kalli Goge da Darma cikin hanzari Goje ya shiga buga gate ɗin gidan kamar zai cire shi, sun jima kafin daga bakin ƙofar suji an ce "Waye?" "Buɗe" Goje ya ce yana zare wuƙa tare da matsawa jikin ƙofar mai gadin a ruɗe yake sosai ya ce "Kamarya na buɗe a wannan zamanin da muke cikin insecurity na sani ma ko ƴan fashi ne?" "Sune" Darma ya ce yana yin muzurai shi kaɗai ne a cikin su yake a buge shi Moh abin da Mangal ya bashi har yanzu bai gama sakin shi ba, shi ya sa ba komai yake ganewa ba. "Wallahi ba zan buɗe ba, babu mamaki kun ji Alhaji Wada ya dawo gari shine za ku yi masa fashi" "Ko ka buɗe gidan nan na rantse da Ɗan Amina na shigo sai na yi maka ɓalli-ɓalli" ai kowa mai gadin ya ce "Ka yi mini ɗari-ɗari ma amma babu abin da zai saka na buɗe daman ƙasa babu lafiya ga yaron can daya dawo abin tsoro ana ta surutu a unguwa ya kashe matarsa kuma ya shigo cikin al'umma zai lalata jama'a..." Kafin ya ƙarasa faɗa Moh ya saka ƙafa ya daki ƙaramar ƙofar nan take ta ɓalle ya faɗa cikin gidan, da sauri mai gadi ya ja baya ba wani sanin Moh ya yi ba kawai zancen ya dawo kunnensa da labarin kisan daya game ko'ina a shekaru uku da suka shige. Goje ya daƙo mai gadin ya falle shi ya faɗi "Kai har ana cewa ka buɗe ƙofa kana ƙi?" "Goje" "Sai godiya" Moh ya numfasa yana durƙosawa daidai fuskar mai gadin "Me ya ce a yi masa?" "Sai godiya ɗari-ɗari ya ce yana buƙatar tsini" ihu mai gadin ya saka ya ce "Wallahi tallahi ƙarya nake" "Zaɓi ɗaya" cewar Moh yana fito da askira ya ajjiye gefe ya sake fito da wata wuƙar ya ajjiye ya jima a duƙe kamar mai tunani sai ya ce "Ko ɓalli-ɓalli ko ƴan uku ko na jaki" "Ɓalli-ɓalli" mai gadin ya ce da sauri ya ɗauka wani abun za a ɓalle da idanu ya kalli Goje da Darma suka riƙe mai gadin tare da juya shi yana ihu da komai Moh ya ɗauki ankarar ya dinga tsaga masa a baya jini na fitowa shi kansa zuciyarsa ce kawai ke ingiza shi ya yi hakan kuma daidai gani yake yanzu daidai yake da tsarar kowanne mutum haka ƙwaƙwalwarsa ke karantar da zuciyarsa. Tun mai gadin na kuka har ya yi laƙwas sai nishi yake fitarwa, suka yar da shi a wajan cike da tafiyar taƙama yana taku ɗaiɗai jikinsa na buɗewa cikakken namiji a tsaye matashi dake kan lokacinsa. Cikin sa'a ya samu ƙofar shiga babban parlon gidan a buɗe ya kutsa kai yana kallon tangamemen parlon ya dinga kallon komai, iya haɗuwa ya haɗu sai ƙarar a.c ya lumshe idanunsa ya buɗe ya jima kafin ya ƙara shiga cikin ɗaya parlon su Goje na biye dashi. Alhaji Wada na zaune shi da iyalansa basu da jima da sauka daga ƙasar ba. Yana saman kujera matarsa na gefe sai yaransa guda biyu mace da namiji kayan ciye-ciye fal a gabansu bama su damu da cin abincin ba sai ice-cream dake hannunsu suna sha. Da sauri Alhaji Wada ya miƙe tsaye yana kallon matasan da suka shigo ya juya ya kalli matarsa da yaran ya ce "Su waye ku? Me kuka zo yi mini a gidana a irin wannan lokacin?" Moh bai ce komai ya zaga ya zauna saman kujera ya jingina ya ɗora ƙafarsa a saman table ɗin yana kallon abincin Goje da Darma na tsaye sai muzurai suke yi cikin sauri Alhaji Wada ya ɗauki wayarsa zai kira ƴan'sanda "Ba wani abu da zai bani tsoro, yadda aka fara dakai dole a ƙare da kai Alhaji Wada" "Waye kai? Me aka fara dani" fuskar Moh a rufe ya saka hannu ya zame abin da ya rufe fuskar da shi "Idan maye ya ci ya manta ai uwa ba zata manta ba, idan kare na yawo zabo na yawo za a haɗe ya ranar" ƙirjin Alhaji Wada ya buga ya yi baya da sauri ya ce "Kai ne? Me na yi maka" "Ba labari na zo baka ba, ba fansa na zo ɗauka ba na zo ka ganni kasan ina raye ina numfashi ka san cewa na cika ɗan babata Ammo Mai dawa nake sarki mai jeji, na gode Ɗan Amina da ka zama kai ne silar da ya saka na gano wasu abubuwan" Alhaji Wada jikinsa rawa kawai yake ya ce "Don Allah kar ka yi mini komai kar ka taɓa yarana basu san abin da ya faru ba" "Idan zan yi mana jira, idan na yi sai ta ɓaci. Ina je store ɗin gidan nan?" Da hannu Alhaji Wada ya nuna masa hanya ita kam matar ta kasa motsi saboda tashin hankali bata taɓa ganin fuska mai ban tsoro irin wannan ba, yaran sai takurewa waje guda suke yi ko haɗa idanu da Moh basa son yi" ganin har lokacin Moh bai tashi ba ya saka Alhaji Wada cewa "kar ka ce zaka mini komai" shi dai Moh kallon Alhaji Wada kawai yake zuciyarsa na tuna masa irin zaluncin da ya yi masa da hannu ya nuna masa yaran cikin kakkausar murya ya ce "Ko dan waɗan nan, ba zan so su zama abin da na zama ba" ya juya ya kalli Goje ya yi masa fito da inkiya suka nufi store ɗin kayan abinci kamar hauka haka suka dinga fito da buhun shinkafa katon na taliya da maroni su magi da galan na mai suka jide waje guda. Yana bada faɗi ya miƙe tsaye ya nuna kayan abincin "Ka raba a masallaci ka haɗawa mutane da haushin kare guda goma-goma, ka kai har gidanmu" Ya juya zai fita sai ya tsaya ya saka hannu a aljihu ya zaro kunama ƙatuwa baƙa ƙirin da ita ta ɗaga ƙari sama ya damƙi hannun Alhaji Wada ba tare da yaran sun gani ba, ya cilla kunamar ciki ya damƙe hannun. Azaɓa ta saka Alhaji Wada zubar da hawaye zufa na yanko masa sosai da sosai a hankali cikin ƙasa da murya ya ce "Ka kira cinnaku ƴan'sanda kenan ka faɗa musu an yi maka fashi, idan sun tambayi waye karka yadda ka ce Mai dawa, ka ce SCORPIO" yana kaiwa nan ya kashe kunamar ya soke jikin bango da sauri ya fice kamar walƙiya, su Goje suka mara masa baya. Fiyya na durƙushe a gabansa kanta a ƙasa ji take dama tana da ƙarfin yin kuka a yanzu, ta kasa fahimtar sai yaushe ne komai zai daidaita ya tafi daidai? Tana haɗiye abubuwa da dama ba tare da kowa ya sani ba bata bari a san rauninta amma yau ita aka saka gaba akan abin da sam bai kai ya kawo ba? Ita zaiwa haka?. "Safiyyerh A. Marafa" Ya kira sunanta a karo na uku sai a lokacin ta ɗago kai ta kalli Daddy dake zaune saman kujera hannunsa riƙe da carɓi fuska ba wasa ya lura sai ya dage sosai akan Safiyyerh. "Ya kuka yi da Ashraf me neman auren ki?" A hankali ta ce "Ba komai Daddy" "Ba komai Daddy, na gaji da jin wannan daga bakin ki Safiyyerh ke kina nuna mini ke mai wayo ce kuma kin girma kin isa ki yi handling dukkan wasu matsalolinki ko? Ke jaruma mai experience akan aikinta Managern FS WORLD INVESTMENT COMPANY? na yarda kina da wayo tunda na kasa sanin damuwarki tsayin shekaru na yarda kina da experience hakan ya sa cikin ƙaramin lokaci kika zama Manager but amma.." ya yi shiru yana kallon ta sai kuma ya ce "Safiyyerh kina buƙatar aure shine cika da ƙimar kowacce mace, me kike buƙata a rayuwa da ba a yi miki ba, wanne gata ban yi miki ba da kika ce kin fasa auren Ashraf?" "Daddy ya ce na zaɓi aiki ko aure" "Sai kika zaɓi me?" "Aiki" Daddy ya dinga kallon ƴar tasa shi ya rasa gane wani mataki zai ɗauka a kanta. "Ba za ki yi auren ba kenan, baƙin cikin jikoki kike mimi Maama? Sai na faɗi na mutu za ki yi auren me ya sa kika kasance stubborn ne, ko don kinga ina biye miki?" Fashewa ta yi da kuka sosai ita kanta bata san kukan ya ƙwace ba, kalmar mutuwar da Daddy ya faɗa ya firgitar da ita sosai idan Daddy ya mutu ta shiga uku. "Daddy gasu Yaya J, su Marafa, su Captain Daddy me ya sa sai ni za a yi aure ne? Ni ce ƙarama fa nawa nake gabaɗaya ko aure za ka mini ka ƙara mini lokaci Ashraf zafin zuciya ne dashi baya fahimta ta a kodayaushe" "Maama kuma taurin kai, ji da kai while zafin zuciya, Safiyyerh dole za ki yi aure" runtse idanunta sosai kenan duk abin da take ya tashi a banza? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me ya sa Ashraf zai yi mata haka me ya sa zai haɗata da mahaifinta? Ta kasa cigaba da kukan abu ya tsaya mata a wuya sosai. Har Daddy ya je bakin ƙofar shiga sashinsa ya tsaya ba tare daya juya ba ya ce "Cikin satin nan zan ɗaura miki aure da Ashraf in sha Allah" Dum! Haka ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi har tsakiyar kanta kuma ta ji hakan, ta runtse idanunta sosai take ƙoƙarin jan numfashi ta kasa ta yi saurin riƙe wuyanta da take jin kamar an soka mata abu a ciki saboda zafin da yake. Cikin sauri J ya ƙarasu parlon daman ya shigo da nufin yiwa Daddy sai da safe ya nufeta yana riƙo hannunta ya ce "Manager lafiya? Mene?" Kafin ta bashi amsa Marafa shima ya shigo ya nufe ta, haka Dr Hash gabaɗaya suka zagaye ta suna tambayarta lafiya kasancewar suna mugun son ƙanwar tasu kamar rai. Hannun J ta riƙe gam tana nishi hawaye na zubu mata sosai ta kasa magana hakan ya saka Dr Hash miƙewa ya ɗakko ruwa mai sanyi ya yiwa J alamar ya ɗago ta, a hankali ya dinga bata ruwan tana sha ya zame rubar ruwan. "Junaid kwantar da ita saman kujera ko ka kai ta ɗaki" "Bari ta ƙara jin dama dama a dai ƙaro gudun acn ta fi shaƙar iska da kyau" cikin sauri Marafa ya nufi wajan ƙaro a.c a hankali suka ji an ce "Kar ka ƙaro" ya juya ya kalli Captain dake zaune kan kujera abin shi yana dannawa, yana zaune Daddy ya kira Fiyya duk maganganun da sukai yana zaune har halin data shiga. "Captain daman kana ciki kana kallo Maama ba lafiya?" "Ni na ɗora mata?" "Amma baka ce mata sannu ba, she's our little sis our favourite" kallon da Captain ya yi wa Marafa ya saka dole ya yi shiru dukkan su ba wanda ya iya cewa Captain komai domin sun san hali basa shiri da Fiyya bai shiga sabgarta ba, duk abin da ya shafe ta babu ruwansa da shi. Ko magana bai fiya yi ba ana ganinsa kowa ke nutsuwa domin shine babba a cikin su Fiyya kuma Auta. Fiyya ta yi lamo jikin J tana sauke numfashi Dr Hash na riƙe da hannunta jin jikinta ya fara ɗaukan zafi sosai. Da ƙyar ta lallaɓa J na riƙe da ita suka haura sama duka sauran mazan suka bi bayansu banda Captain da yake harkar gabansa. Wajejen 2:30 Daddy ya sauke numfashi yana kallon yadda take sauke numfashi a hankali ko a baccin bata da walwala ya juya ya kalli Captain dake tsaye hannunsa zube cikin aljihu "Aliyu me na ragi Maama da shi a duniya dana kasa fahimtar meke damunta? Ita ɗaya ce mace ƴata laifi ne don na so ta yi aure?" Captain dai ya yi shiru idanunsa a saman fuskar Fiyya Daddy ya miƙa hannu ya taɓa goshinta ya ji har lokacin da zafi daman ya fi ƙarfin awa guda zaune a wajan, yana cikin Captain ya buɗe ƙofa ya shigo da tunanin babu kowa cikin ganin Daddy ya saka dole ya tsaya. "Maama ki yi mini alfama ki yi auren nan, shi ne abin da za ki yi ki faranta rai na" ya gyara mata hannunta daya lanƙwashe kana ya miƙe tsaye zai fita "Aliyu mu je" "After you daddy" Daddy ya jinjina kai ya fita yana janyo ƙofar. A hankali Captain ya nemi waje ya zauna a gefen gadon ya zuba mata idanu sosai, a nutse a kamo hannunta ya riƙe cikin nasa jin jikinta zafi sosai ya saka ya saki hannun ya ɗakko towel da ruwa ya dinga goga mata a goshi har lokacin yana riƙe da hannunta har sai da zafin ya ragu, bai tashi ba yana zaune aka fara kiran sallar farko cikin sauri saki hannunta ya miƙe tsaye yana haɗe fuska J ne ya shigo a hankali ya bi Captain da idanu har ya fice daga cikin bedroom ɗin na Fiyya. ***** Cikin gidan ya faɗo babu ko sallama Inna Binta na zaune har za ta yi magana ganinsa tsaye ya saka ta yi shiru da bakinta. Yau ranta fari tas an yi musu rabon abinci Malam ya basu ya ɓoye sauran. Ɗakin Ammo ya nufa yana ɗaga labulan ɗakin ya ganta zaune tana ɗaura kuɓewa tun kan ya shigo jikinta ya bata yana hanya saboda gabanta daya tsananta faɗuwa. Ya shiga ɗakin ya zauna ita dai bata kalle shi ba, sai kallon ta ya ke yi can ƙasa da murya kamar ba shi ba ya ce "Ina yini Ammo?" Miƙewa ta yi maimakon ta amsa masa, ya cije bakinsa yana rufe idanu kwanon abinci ya jenyo ya buɗe yaga taliya ce jallof ta ji albasa nan da nan yawunsa ya tsinke ya tuna rabon shi da abinci har ya manta. "Alhaji Wada ya bawa Malam, idan da zuciya ai ba za ka ci abincin daya bamu ba" cak ya tsaya yana kallon abincin kamar zai tashi sai kuma ya nutsa hannunsa ciki ya ɗebo lauma zai kai bakinsa cikin sauri aka ce "Allah Ya isa ban baka ba ida ka ci abincin nan" Malam ya kalli Ammo ya ce "Bana ce kar ki yarda ya shigo gidan nan ba? Wato har abinci kika bashi ko?" Ta girgiza kai ta ce "Ɗauka ya yi" Jiki a sanyaye Moh ya miƙe ya fice daga cikin ɗakin yana saka ƙafa ya banko ƙofar da ƙarfin gaske yana zuwa daidai inda Inna Binta ke gyara shinkafa ya saka ƙafa ya yi fatali da farantin shinkafar ta tarwatse ya yi waje kamar zai tashi sama. Ta dafe ƙirji tana rafka salati "Ƴar gwamnati ce fa Allah ya isa wallahi". Goje ya dubu Mangal ya ce "Me ka bashi wai? Yake wannan sambatu da mimmiƙar haka?" "Sha fara kaga aljan ce, ita za ta yi aiki a jikinsa, daga sama aka bani ita" Goje ya juya ya kalli Mai dawa ya sauke numfashi cikin damuwa ya ce "Dole sai ka koya masa shan waɗannan abubuwan ne?" "A'a ina zaune ya zo mini kamar an koro shi yana huci ya ce na bashi irin abin da na bashi kwanaki saboda damuwar zuciyarsa ta kau ya manta da komai ni kuma na bashi sha fara kaga aljan" "To gashi nan yana ganin aljanin ai" da ƙyar ya samu ya yi bacci a wajan. Bayan ya farka Mangal ya bashi abinci ya girgiza kai "Mai dawa idan kuɗi kake so ina da hanyar da zan yi maka ka dinga samun kuɗi sosai cikin sauƙi har ma ka taimaki wasu" tunda ya farka sai lokacin ya ɗaga kai ya kalli Mangal alamar ina ne? "Bangar siyasa kasan yanzu muna gab da fara shiga sabgogin siyasa uban gidana cikakken ɗan siyasa ne, shima yana da uban gida kuɗi zaka samu sosai a sabgar nan ina faɗa maka" "Kai ni" kawai ya iya cewa yana miƙewa tsaye. Suna zaune a wani haɗaɗɗan parlo inda suke karɓe wa su yi meeting na sirri. Gabaɗaya suka kalli MUTALLAB TAHHB SCORPIO ɗaya daga cikin su ne ya ce. "Mene sunanka" "Mai dawa" "Kai mafarauci ne?" Ba tare daya kalli mutumin ba ya ce "Darr" babban mutumin ya jinjina kai sosai ya zaro wani photo a aljihu ya ce "Kafin mu yi maka bayanin su waye mu, me muke buƙata da kai, fara ganin wannan ka saka dai a ranka mu ƴan siyasa ne" Shi dai Mai dawa bai ce komai ba, aka ajjiye masa photon a gabansa "Ɗauki ka buɗe ka gani mana" Wani daga cikin mutanen ya ce "Manager ce a FS WORLD INVESTMENT COMPANY aiki za ka yi mana a kanta kafin mu faɗa maka aikin mene ka fara ɗaukan photon kaga wacece" a sanyaye ya ɗauki photon kafin ya kai idanunsa kai.... 08164069385 For more information WhatsApp only [10/8, 7:59 AM] null: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 5 "Safiyyerh Abdu Marafa Manager ce a Kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY kuma ƴa a wajan tsohon leccara, muna buƙatar ka yi mana kidnaping ɗin ta" Moh Kallo ɗaya ya yi wa photon da suka bashi ya ɗauke kai "Ka santa?" Shi dai bai ce komai ba. Eng Ali wali ya dinga kallon Moh yana tunanin abubuwa da yawa a ransa kafin ya ce "baka gama ganin photon bane, ko da yake yana da kyau da ƙare mata kallo maybe ka zama silar mutuwar ta ko ka kashe ta da hannunka, ka ya zama dole ka gane kamamminta" Goje ne ya ɗago kai da sauri yana kallon Eng Ali wali kafin "Sai da kai mai gida wannan aikin ai ko ni zan iya yin shi ba sai Mai dawa ba, ka huta ka sarara mai gida" Eng Ali wali ya yi murmushi yana jingina da kujera ya ɗauki ƙafarsa ya ɗora akan ɗaya ya kalli Mai dawa wanda ko motsi bai yi ba sai jujjuya photon da aka bashi yake. "Ko Mangal ba zai iya aikin nan ba da ya fika wayo a sabgar balle kai da na sani yanzu, shi wannan Mai dawan idanunsa na kalla na san zuciyarsa za ta iya aikata komai" Ya yi shiru sai kuma ya ce "Ni ɗan siyasa ne babu mamaki ka taɓa ganin poster na ko bana, shekaruna takwas ina riƙe muƙamin Ɗan majalisa na tarayya a jam'iyyar da nake ta kara, bani da ra'ayin haƙura da kujerata kamar yadda ake yi mini kirarin idan na yi na gama na karya kujerar. Siyasa jinina ce Mai dawa, bana jin akwai wani dalili da zai zo ya saka na haƙura da kujerar na amma wannan karon na yi karo da muruci wanda yake shirin yi mini wahalar dafawa ko ta halin yaya ne dole na sake hawa kujerar nan a karo na huɗu. Hon Maɗatai yana tare da manya wanda suka san kan siyasa ciki da bai dole mu fito da salo na musamman wanda zai kai su ƙasa. Hon Maɗatai shine ɗan takarar jam'iyyar hamayya kuma yana da ƙarfi har yanzu ba'a san mene rauni ko aibun shi ba amma akwai jita-jitar data zo kunne na domin tabbatar da gaskiyar al'amari ya saka na kawowa cikin jama'ata" Sai a lokacin Mai dawa ya ɗago kansa ya ɗan kalli Eng Ali wali kamar ba zai ce komai ba sai ya cije baki yana karkatar da kai gefe ya haɗa hannayensa biyu suka bada sauti mai ƙara cikin wata murya ta izza ya ce "Mene haɗin ta da maganar yawar ku?" Eng Ali wali ya ce "Wa kake magana" "Ita ɗawar mai ɗan kwalin?" Cikin rashin fahimta Eng Ali wali ya ce "Meye ɗawa da ɗan kwali kuma?" Mangal ya yi murmushi yana "Ka fice Mai gida, ɗawa da mai ɗan kwali mace kenan ake kwafa maka zancen" Ya ce "Yaran naku sai ku" Miƙewa Mai dawa ya yi tsaye yana ɗora ƙafarsa a saman farar kujerar dake parlon kallonsa kawai Eng Ali wali ya yi bai ce komai ba. Sai wani ya ce "Mai dawa farar kujera ce fa?" "Ko takaddar jikinka zan ɗora ƙafa akai" wanda ya yi maganar ya yi saurin kallon farar shaddar dake jikinsa fara tas da ita sai ya ja bakinsa ya yi shiru. Moh ya kalli gefe yana furzar da iska daga bakinsa ya ce "Me ya sa ka neman, bayan kana da gajojinka?" "Saboda kai ne baƙuwar fuska a cikin wannan sabgar tamu, ba wanda zai gano cewa a tsagina kake za ka yi aiki mai kyau hankalina ya kwanta da kai Mutallab" wani irin kallo Mutallab ya jefa masa idanunsa sun sauya kala ya yi murmushi ya ce "Oh Mai dawa da jeji, ya batun yarinyar ka santa ne ko ka taɓa ganin fuskarta?" "Na santa ko ban santa ba ina jin bashi kake buƙata ba. Yaushe kake so a kawo maka ita?" Girgiza kai Eng Ali wali ya yi ya ɗauki ruwa ya kurɓa ya ajjiye kana ya miƙe tsaye yana zagaye parlon hannunsa a baya "Ka jira umarni na, kawai ka zama cikin shiri a koyaushe zaka iya jin kira. Akwai gidan dana samu a bayan gari zan baka makullin ko ka ɗakko ta can zaka ajjiyeta kai ne zaka dinga kula da ita har yanzu lokacin da muka shirya abin da mukai niya, a cikin gidan akwai kayan aiki irin naku wanda za su sama muku nutsuwa" Goje ya jinjina kai cike da jin daɗi kafin ya ce "Mai gida za a siya mana mota mai iska kamar yadda muke ƴaƴan iska?" "Za a yi muku komai, ku riƙe amana. Sai dai kawai sharaɗi ko da wasa kar ku nuna kun sanni idan ina buƙatar ganin ku a wannan gidan zamu dinga haɗuwa, ku buɗewa kowa idanu kar ku ji tsoro da shakkar komai ni zan tsaya muku har zuwa ci zaɓe" Moh ya ce "Bayan cin zaɓan fa?" "Kamarya?" Ya buɗe manyan idanunsa sosai a kan Eng Ali wali a karo na farko ya ƙare masa kallo "Mene farashin aikina?" "Nawa kake so?" Ya yi shiru yana tunani can ya ce "Zan sanar" Eng Ali wali ya ɗakko ƙatuwar bana da fastoci ya bawa Goje da yawa ya ce "Kuje ku fara da aikin liƙawa wannan a unguwanni da saƙo da lungu ya zamana babu wanda ake ganin sai Eng Ali wali, bayan wannan akwai wani dattijo da yake zuwa gidan rediyo yana yi sojan baka kuma duk ni yake kushewa yana son jiƙa mini aiki a tabbatar an saka shi yin shiru da baki da kowacce hanya" kuɗi ya ciro daga cikin Aljihu ya miƙawa Goje ya ce "Aje a yi caji a huta" har Moh zai juya sai kuma ya tsaya ya cake waje guda kamar saƙago ya ce "Me ya sa kuke son a kamata?" "Aiki ne kawai naka wani abu ba sai ka sani ba, mune shuwagabanni ku dai a baku kuɗi da kayan sararawa shine" kai tsaye Moh ya ce "To nemi wani" Eng Ali wali ya ce "Me ya sa? Bayan kai ka cancanta?" "Ba zan ba" "Shikenan na gane, Safiyya Abdu Marafa na faɗa maka ƴa ce wajan tsohon leccara, yana kawo mini barazana a sabgar siyasa tare da nuna rashin cancanta a fili. Matasa na jin maganarsa abin da ya zaɓa kuma da shi suke yin aiki a yau ɗin da muke ciki matasa sune siyasa ina so a sa shi yin mubaya'a dole. Kasan da yawan lokaci Malamai suna kawo mana cikas" Mai dawa ya jinjina kansa alamar ya ji sai dai bai yi magana ba a hankali ya duƙa yana buɗe hannu ya ce "Sai godiya" "Sai godiya" Mangal da Goje suka faɗa suna zagaye shi. Cikin sauri kuma ya fice daga cikin parlon suna mara mishi baya. Eng Ali wali ya dubi wanda ke zaune sai kuma ya yi dariya sosai ya ce "Amfanin su kenan fa babu wani aiki da ɗan daba zai iya yi maka banda bangar siyasa kashe kashe da sare-sare mu kuma sai mu jefe su da abin da sukewa" Fiyya na tsaye gaban madubu tana gyara rolling mayafin kanta yau ma suit ce a jikinta ta mata riga da wando blue black ta amshe ta sosai ta kalli kanta a madubin she missed the old Safiyyerh komai nata sabo take jin shi, ta ji kamar ta rasa wani abu mai amfani a tattare da ita amma mene? Shi ne abin da sam ta gaza fahimta ko a cikin bacci. Ta sauke numfashi tare da ɗaukan wayarta da jakarta tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fita Ummi na shigowa cikin ɗakin Fiyya ta yi baya tana bata hanya kafin ta ce "Good morning Ummi" daga sama har ƙasa Ummi ta kalle ta sai kuma ta je can bakin gado ta zauna tana sake kallon Fiyya "Ina za ki?" "Ummi Company" "Junaid told me ba ki da lafiya, na yi bacci da wuri" a hankali ta ce "Lafiya lou nake Ummi ga alama kin gani zani aiki" "Fiyya bana son irin wannan shigar taki, kuma ki haƙura da aikin nan yau za a kawo kayan auren ki" da sauri ta ce "Aure kuma Ummi? Ba sai nan da watanni ba?" "To Daddynku ya ce cikin satin nan" "Shikenan zan je aiki" "A'a ki haƙura yau" marairai ce fuska ta yi sosai kamar za ta yi kuka ta ce "Ummi akwai buƙatar na je, ina da meeting da ma'aikata ba zan jima ba" Ummi bata san damuwar Fiyya dole a hankali ta ce "Allah Ya tsare ki dinga kula ke dai macace ba namiji ba, kina lura da abubuwa da kike yi" Fiyya ta yi dariya tana yin waje ta ce "Kuma ki saka tsoron Allah a ran ki Fiyya ban da wulaƙanta jama'a, al'umma ta Annabi ce" Ummi ta girgiza kai kawai ta ce "Wato kin haddace kenan" "Dole na Ummi" Cak ta tsaya tana riƙe kan ta Ummi ta ce "Subuhanallahi Fiyya kina lafiya? Ba za ki haƙura da zuwa aikin nan ba?" Ta ɗan ya tsuna fuska da nuna alamar ba komai ta ce "Kawai na ji kaina kamar an saka mini shocking" gaban Ummi ya faɗi sosai sai bata nuna ba ta kama hannun Fiyya suka sakko ƙasa. Dr Hash ne ya fito shima sanye da farar riga ta likitoci Fiyya na kallonta ta ce "Likita bokan ture, kuma fiɗe ku ɗinke" "Kamar wasu mahauta" ta yi murmushinta mai kyau tana lumshe idanu "Barka da safiya Dr" ya yi mata murmushi "The whole Manager in the world" Ta buɗe ido shima ya buɗe kafin su ce komai J ya fito shima yana cewa "In the world mana, wannan kamfanin nan ku ina ne basu da reshe ni dai watarana zan zauna ki bani labarin kamfanin sosai na ji ai na yin wanda yake da shi" "Kai Yaya J nima ban san ko na waye" ya buɗe ido ya ce "Ban gane ba?" "Da gaske nake Yaya ban san asalin me shi ba, kawai dai na san ni Manager ce" "Ji nake Ashraf's father is the owner of the company" Ta tura baki gama tana harar shi "Kuma ka sani kake tambayata" ya ɗaga mata gira ya ce "Zan zo ki nema mini alfarma wajan surukin naki nima ya bani ko messenger ne" bata kula shi ba. Ɗago kai ta yi suka haɗa idanu da shi yana zaune ya watsa mata harara yana ɗauke kan shi gefe "Aliyu ba yau zaka tafi bane" ya yi shiru a hankali kuma ba tare daya ɗago kai ba ya ce "A'a" "Ok na ɗauka yau ne, ni wallahi duk firgitar dani kake mutum ba walwala kamar a filin yaƙi nan fa gida ne, amma kodayaushe kamar an yi maka dariya ko yaya ne ka dinga murmushi" "Ban iya ba Ummi" "Murmushin ne baka iya ba Aliyu? Ka gwada zaka iya" ya miƙe tsaye yana yin waje "Ban san yadda zan ba" "Ina kwana Captain?" Fiyya ta faɗa tana haɗe fuska ko inda take bai kalla ba ya yi waje abin shi. Shi dai J murmushi kawai yake yi halin Captain na bashi malam sosai suka jera shi da Fiyya suka fita. Mota ta shiga yana ɗaga mata hannu shima ya shiga tasa motar kowa ya kama hanyar wajan aikin shi. Fiyya na driving a nutse ta hangi wata mota na bin duk inda ta yi sai ta taɓe fuska ko a jikinta a fili ta ce "Ɗan wahala ko waye" Daddy dake zaune bayan shigowar Ummi cikin parlon sama ya kalleta ya ce "Me kike cewa Ummi?" Ta damuwa ta ce "Kwana biyu ba a amshi maganin Fiyya ba, kuma kamar ciwon zai tashi" ya ajjiye littafin hannunsu yana saka glasses ya ce "Wani abin ya faru?" Ta numfasa yana faɗin "Irin abin da ya faru kwana ki tana jin kamar ana mata shocking a kanta, ni wallahi bana son ma ta dawo daidai bana fatan ubangiji ya ƙara gwada mini tashin hankali dana gani shekarun baya" Daddy ya jinjina kai "Nima addu'ar da nake a raina shi ya sa ma na matsu kawai a yi ai maganar auren nan, wallahi bana son Maama ta dawo old Safiyyerh" "In sha Allah hakan ba zai kasance ba" Meeting hall ɗin ya yi shiru sai muryarta dake tashi cikin faɗa tana ɗan buɗe hannayenta tare da yin baya ta ce "Wanne irin rainin wayo da hankali ne, file ɗin dana ajjiye shi a office ɗina ina jiran a kawo mini proof hujjar abin da aka fitar aka samu shigowar kuɗi zuwa asusun kamfani kamar yadda Accounter ya faɗa mini shine za a ce wai na yi signature a file aljana ce ni da zan taso da gida na zo kamfani na saka hannu, idan zan saka me ya sa ban yi ba tun da file ɗin ya zo table ɗina?" Ta miƙe tsaye tana kallon su gabaɗaya duka maza ne ita kaɗai ce mace ta koma ta zauna tana juyi a kan kujerar "I need to find out the truth, meke faruwa a wannan kanfanin. Md da kai da secretary za ku kai ni na duba ko'ina a wannan kamfanin yau ɗin nan, kai kuma Director ka kawo mini record ɗin komai daga watan daya shige zuwa yau ɗin nan, ina buƙatar statement yanzu a office nawa" ta sauke numfashi fuska a haɗe sosai "An gama" secretary ne ya kalleta kamar a tsora ce yake ya ce "Manager akwai baƙi da suke jiran ki" File ta ɗauka ta miƙe tare da ficewa daga cikin meeting hall ɗin. Bata nufi office ɗin ta ba inda suke ganawa da baƙi ta nufa ta tura office ɗin a hankali a hankali ta yi sallama ta shiga. Manyan mutane ta gani su biyu zaune a kan kujera kana ganin su ba sai an yi magana ba ta zauna kan kujera mai cin mutum biyu a ladabce ta ce "Ina kwanan ku? Welcome to FS WORLD INVESTMENT COMPANY i am Safiyya A. Marafa how can i help you?" Wani rushehen mutum ne daya Hakim ce a kan kujera ya dinga kallon ta kamar zai haɗiye ta idanunta dai na kan system tana ta dannawa da aikin tura saƙo can ta ɗago kai suka haɗa idanu ta sake kame fuska ta ce "How can I you? Ta ya ya zan iya taimaka muku" "Ba ki gane ni ba" Sarai ta gane ko waye ta ce "Yau na taɓa ganinka" "To ma sha Allah. Sunana Hon Maɗatai zan saka hannun jari ne a cikin wannan Company" "Ok, me kake buƙata?" Ya gyara zama sosai ya ce "Za a dinga bani shinkafa, suger, wake a kan farashin yadda Company yake siyarwa ni kuma zan ɗora kaso 50 domin cin riba amma daga lokacin Company ba zai sake siyarwa da kowa kaya ba sai ni" Fiyya ta dinga kallon shi sosai a ranta tana mamakin son zuciyar wasu ya suke so talakawa su yi da ran su ne? Burin shuwagabanni talaka ya faɗi ya mutu saboda yunwa? Ta yi jim sai kuma ta ce "Da wata ce matsayin Manager ba Safiyya A. Marafa ba do wataƙila ka samu wannan damar a yanzu ina maka murna da cewar we're not interesting anymore, da wannan zai fi kyau ka buɗe naka masana'antar ka nemi matasa marasa aikin yi wanda suke lalacewa ka basu abin yi" ya dinga kallon ta can ya ce "Kin san waye ni? Ƴan'mata ki bi a hankali fa" "Ai ba a yi wa Fiyya maimaici Hon Maɗatai ba zamu baka hannun jari ba You can leave" ya miƙe tsaye yana jin ba'a taɓa yi masa wulaƙancin da yarinyar ta yi masa ba "Safiyyerh ko? Ki bi a hankali haɗuwar farko ce wannan, zan tafi amma zan dawo" Ficewa ya yi rai ɓace zuciyarsa na zafi. Fiyya ta ɗauki kayanta ta nufi office. A hankali take bin bayan Md da Secretary ɓangaren kayan abinci aka kaita kana da mai daga can baya wajan shara inda ake ajjiye bukar kamfanin ta dinga jiyo wari da sauri ta nufi wajan Md ya ce "Manager sharar kamfani ce nan" bata kula shi ta nufi wajan sharar tana rufe hanci da f facemask kamar an ce ta juya idanunta ya sauka akan yatsun hannu guda huɗu da suke a leda ƙuda na bin su. Tunda ya nufu layin su tiger na biye masa baya hannunsa riƙe da gora yara suke watsewa sai waje ake bashi hatta almajirin Malam sai da wasu suka bar wajan banda Ɗanyaro dake zaune yana danna sabuwar wayar daya siya sosai Malam yake ji da shi yanzu lokaci zuwa lokaci yake yi malam alheri na kuɗi ga nama da yake kawo masa, sai dai cikin dare Ɗanyaro zai lallaɓa ya gudu ba zai dawo ba sai safiya. Moh na ƙoƙarin shiga gidan Malam ya tare ƙofar ya ce "Na haifi yaro sunan shi Muɗallabi amma yanzu bani da wannan yaron na bar wa ƴan iska shi da ƴaƴan banza tunda ya zama shaiɗani ba zaka ja mini masifar da zan mutu a gidan ɗan kande ba" Moh zuciyarsa ta fara tafasa har wani hayaƙi ke fita ta cikin bakinsa ya dinga kallon asawan nasa ya kasa cewa komai ya leƙa surar gidan ko zai ga Ammo amma sai Inna Binta dake suɗe tukunya tana faɗin "Matsalata ɗaya a duniyar nan abinci idan na ci na ƙoshi Mufee ta ci ni fa ko a jikina" Juyawa Moh ya yi kamar zai yafi sai kuma ya nufi saman katanga ya kama ya dire ta cikin gidan Inna Binta ta zabura tana faɗin "ƙulna naru ƙulni bar dan wasalamun Allah Ibrahim, auzubillahi" jikinta sai rawa yake masifar tsoron Mai dawa take kamar ran ta sauran jama'ar gidan duk suka shige ɗaki banda Mufee da ta yi tsaye tana kallon shi sosai idanunsu yake iri shi bai san wace ita a gidan ba, bai damu daya sani ba yara ne kamar yaƙi wasu iyayensu basa cikin gidan. Labulan ɗakin Ammo ya ɗaga ya ganta zaune tana ninke kaya ya fi minti goma tsaye kamar zai juya sai kuma ya shiga cikin ɗakin idanunsa akan kwanon abinci sosai yake jin yunwa idanunsa na rufewa ya miƙa hannu zai ɗauki abincin Malam ya ce "Kana ci zan maka Allah Ya isa ka tashi ka bar mini gida tsinannen yaro" da sauri Ammo ta kalli Malam sai kuma ta ɗauke kai. Jikin Moh ya fara rawa jijiyoyin kansa na mimmiƙewa jin uban daya kawo shi duniya na yi masa Allah Ya isa ya yi ƙasa da kansa idanunsa kamar za su fito waje ya ji babu abin da yake buƙata sai ƙwayar da Mangal ya bashi ya sha, ita kawai zata sauke masa abin da yake ji ya manta da komai, yaushe ne zai zama daidai kamar kowanne mai rai an ci zalin shi an lalata masa rayuwa. Ya miƙe da sauri yana banko ƙofar ya yi waje "Sallamammen yaro Allah dai ya rabani da ƙaddara na huta" Kai tsaye Moh dabarsu ya nufa yana zuwa suka mimmiƙe Darma na faɗin "sai godiya Mai dawa sarki mai jeji, wani ya ce ba kai ba yanzu mu fito mu yi farfesun hanjinsa" Yanayin fuskar Mai dawa a bar tsoro ce ya takure waje guda yana jin kamar zuciyata zata fito waje don baƙin ciki. "A sama yake ku bashi sha fara kaga aljan" cewar Darma Mangal ya girgiza kai ya ce "Ba za ta yi masa ba, kawai a yi masa allurar fenta" "A'a ta yi masa girma yaushe ya faɗo sabgar kar ka luda masa ya yi mana na jakuna yanzu" zaro sirinjin ya yi Moh ya ƙurawa siririn idanu ganin yadda Mangal ke zuƙo ruwan ciki ya fara girgiza kai da ƙyar ya ce "Kar ka yi mini Ka bar ni da tunanin bana son mantawa" kokawa suka fara yi da shi ya ɗauki Darma ya buga da ƙasa Mangal ya faki idanunsa ya caka masa allurar a gadon baya. Jinjiga ya fara sosai cikin ƙaramin lokaci ya yi shiru yana jin shi kamar a samaniya yana yawo yanayin ya yi masa daɗi sosai ya ji zuciyarsa wasai a wannan yanayin bacci ya ɗauke shi. Can cikin dare ya farka kam shi ya yi masa nauyi har yanzu bai dawo daidai ba, babu komai a cikinsa ya miƙe tsaye yana layi kamar zai faɗi Mangal ya ce "Mai dawa" Ya yi masa shiru yana ɗaukar wuƙa ya soke ya ɗauki fitila ya riƙe "Dare ya yi ba, kana fita waɗancan ɗankokin za su iya kama ka gashi babu da goge a hannu ka zauna, kasan kuma ƴan cikin gari sun shigo sun samu labarin mun yage musu poster bama wannan ba ɗazo an ga gawar wani to ana tunanin mu ne kuma yaron ɗan cikin garin ne fansa suka zo ɗauka,na bibiyi abun shi yaron ƙwacan abar magana ya yi jama'a kuma sun fara ɗaukan doka a hannunsu suka rufe yaron da duka har ya mutu. Su Cokali kuma ba za su haƙura ba kar muna zaune su ci mu da yaƙi" "Sai godiya" Ya furta da ƙyar daga nan sake yin shiru yana shirin barin wajan kamar zai kifa "Ina zaka ne? Ka dawo ka kwanta" "Kai fa ba Malam zan haɗaka da Rainbow" "Shikenan ina zaka yanzu" ya cije leɓe zuciyarsa na ayyana masa abin da zai yi shi ne daidai allurar sai gaibu take faɗa masa a hankali ya ce "Zan kashe Malam ya baza lahira" For more information 08164069385 WhatsApp only [10/9, 5:16 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 6 *Bright pens... 2nd batch* *🔞for the adults and criminal side please 🔥 just take it as a lessons* Goje daya farka daga bacci ya yi saurin miƙewa yana furta "Malam ɗin zaka kashe mahaifin naka?" Ya yi shiru bai yi magana ba, yana sake riƙe wuƙar a hannunsa da kyau duk jikinsa rawa yake, ga wani irin ciwo da kansa yake yi masa sosai, idan ya tuna abubuwan da aka aikata masa sai ya ji zuciyarsa ta bushe ta kuma ƙeƙashewa. Ya saka ƙafa ya banga je Mangal dake tsaye zai shige Goje ya yi saurin shan gabansa yana ɗaure fuska sosai ya ce "Saboda kana jin kanka a sama ta bakwai kake jin komai za ka iya yi? Me ya sa ba zaka yarda sarki sammai ke yin komai ba, mu fa ba haihuwar ta zubar bane ko yaya ne mun san abin da ya dace kashe mahaifinka ba shi ne mafita ba Mai dawa" ya ɗaga jajayen idanunsa kamar zai ci babu yadda ƙwaƙwalwarsa take faɗa masa ba daidai haka komai na duniyar yake yi masa babu daɗi maƙoshinsa na yi masa zafi da raɗaɗi wani abu ya tsaya masa da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce "Ya zan yi?" Kai tsaye Goje ya ce "haƙuri, ka bi komai a sannu mai dawa ita gaggawa aikin ƴan annaru ce. Kashe Malam a yanzu ba zai rage maka kashi goma a cikin ɗari na damuwar da kake ciki ba, iya wuya iyaye ne su" "Ba iyaye na bane, ka bari ko ɓalli-ɓalli na yi masa" ganin da gaske shirin tafiya ya ke yi ya ce "Idan kaga ka bar wajan nan sai dai ni za ka fara kashewa" Ya ƙuri da idanu yana kallon Goje har wani hayaƙi ke fita ta cikin bakinsa ya wani cije gefen baki yana karkatar da kai gefe. Kamar wasa Goje ya ga Moh ya nufe shi da wuƙar shima yaƙi matsawa yana ganin kamar wasa ne yana ƙoƙarin kawai Goje sara su kaga mutane kamar daga sama sun zagaye su. Moh yaƙi motsawa sai Goje da ya yi baya ya cake yana zazzaro idanu tare da ɗaga gora sama. A kallon farko Mai dawa ya gane cinnaku ne ƴan'sanda sai ya ɗauke kai shi Goje bai faɗa da labarin ba saboda shigar fararen kaya suka yi. "Eng Ali wali ya aiko mu wajan ku kawo muku kaya" sai a lokacin Mangal ya ƙarasu yana tale ƙafa ya ce "Kaya sun sauka da zafin su kenan yallaɓai, amma eh kun razana mu shigowa ba notice sai mu ɗauka dire aka yi mana" ɗan'sandan ya yi murmushi kawai ya ce "Kuna da kamar Ali wali za ku ji tsoro? Kune matasan da yake ji daku a yanzu musamman wannan da naga ko kallo bamu ishe shi ba" Goje ya juya ya kalli Mai dawa da yake kallon wani sashi daban alamar baya ma jin me suke cewa "Mai dawa sarki me jeji wajanka aka aiko mu domin aikin bana yara bane" "Faɗi" Moh ya ce yana bada faɗi ba tare daya kalli da ɗan'sandan ba. Abu ya fito da shi a jaka ya miƙawa Mangal ya amsa ya ce "Ka a dana kada a je a yi ta sha ana ɓarna, Eng Ali wali ya ce akwai fita ta musamman kuma ƙauyen da za shi basu da kirki dole tafiyar sai daku a ranar zaku cake ku bawa samaniya yazo ta yi hadari" Mangal ya buɗa ya ce "Dar hakan ya yi mana, sai Eng Ali wali ko ana su ko ba'a su ya zama dole don uwatar" Police ɗin ya juya kan Mai dawa a hankali cikin magana mai muƙamin ya ce "Ka taɓa jin mai suna Scorpio?" "Wa?" Goje ya ce da sauri yana kallon Mai dawa da sai a lokacin ya juyo ya kalli Jafar shima Jafar ya kalle shi da kyau ya ce "Akwai matsala ne babba, Scorpio yana yi wa Eng Ali wali barazana, yana da babbar hujjar da zai iya kawo masa matsala a mulkinsa kuma babu shakka ko waye Scorpio akwai alamar ya shirya fito na fito da Eng Ali wali, to muna jami'ai ba zamu bari ba tunda a jikin shugabannin da ƴan dabarun mu muke samun namu rabon. Ali wali yana buƙatar ka taya shi gano waye wannan Scorpio da sunan shi kawai ake ji ba kamanni" "Kamarya kenan?" Mai dawa ya tambaya a taƙaice yana jin ƙirjinsa na buɗewa saƙo ya fara isa kenan a fili kuma ya sha kunu sosai. Jafar ya dafa kafaɗar Mai dawa ya ce "Kamar kai yanzu kowa ya san sunanka Mutallab inkiya Mai dawa saɓanin shi da sunan Scorpio kawai muka sani, babu wanda Eng Ali wali ya yarda da shi sai jami'an Dss ka baza jama'arka su tayaka binciko asalin waye Scorpio akwai kyauta mai yawa idan hakan ya tabbata, kuma ya ce ka faɗi kome kake so zai baka" Wani irin kallo Moh ya dinga yi wa Jafar na kan kaga biri, biri ya ganka kifi na ganinka mai jar koma sai kuma ya ɗaga kai sama yana kallo sama cikin kumburarriyar murya ya ce "Bayan Dss da shi uban gidan naku waye ka ji yana neman SCORPIO?" Jafar ya ce "Me ya sa kake tambaya?" "To kuje ku yi aikin da kan ku" ya faɗa yana juyawa cikin sauri Jafar ya riƙo shi ya ce "ka dinga sassautawa zuciyarka da fushi. Bayan Dss akwai jami'ai mafi hatsari da suke neman shi idanu rufe FID Federal investigation department, basu da imani wannan mutanen jami'ai ne da ba zaka taɓa tunanin ta ina zasu cimmaka ba, suna iya zuwa a suffar mahaukata ma ko mai neman taimako, su kakkarya mutum ko su kashe shi ko haukata shi ba wani abu bane a wajan su" "Suka kasa kama Scorpio?" Jafar ya watsa hannu ya ce "Sannu sannu da zarar sun gane kamanmin su, babu mamaki su ɓullo ta wata hanyar kafin hakan ta fara ka ruga su kai hari,mun gama magana da kai Mai jeji" ya yi shiru bai ƙara cewa komai ba "Ka yi shiru?" "Ka bada sha ɗayanka, zamu jauwalo ka idan akwai sagi" cewar Goje Jafar ya girgiza kai "Ka bar shi ya yi magana" Moh ya sake kame fuska babu wasa kuma yaƙi cewa komai sai ma fito daya fara yi yana kallon bindigar dake hannun ɗaya ɗan'sandan. Bisa dole suka juya suka tafi ba tare daya tanka su ba,daman Goje ya san ba maganar zai yi ba. Goje ya juya ya kalli Mangal da yake zuƙar wiwi a hankali ya ce "Ka raina musu hankali waye Mai dawa waye Scorpio" "Ni ne, MUTALLAB TAHHB SCORPIO" Mai dawa ya ce yana zare idanu waje manya gwanin tsoro da razani har sai da Goje ya ja da baya don bai taɓa ganin halittar idanu kamar ta Moh ba ƙwayar ta juye kamar bata mutane ba kuma sai ƙara ware manyan idanun yake yi. "Akwai matsala Moh idan suka gano cewa kai ne Scorpio, za su yi maka illa gwara ka ɓace kawai daga yankin kafin komai ya sarara" "Gawata za su iya gani su haƙura da nema na" Ya furzar da iska daga cikin bakinsa kansa ya yi masa nauyi "Goje an yi sake tunda aka bari na je state cid,ba san komai ba amma a fitar dani. Zan iya haƙura da komai banda abin da yake damuna a zuciya ni da kai na zan bayyana cewa nine Mutallab Tahhb Scorpio da zarar na cika muradina na abin da na yi niyya" "Mai dawa" "Sai godiya" "Ina tunanin ka haƙura ka bar wa Allah komai duk zamu baza mu je gare shi ya yi mana eh hisabi" Moh ya taune harshe yana kaɗa leɓe tare da saka harshe ya kashe wuƙar dake hannunsa "Zafin nake ji a zuciyata zan yi ɓarna, zan sha jini" "Kamar wani maye? Shi Ali wali ɗin me ka yi masa ne?" Mai dawa ya ja idanunsa ya lumshe ko yaya idan ya yi shiru sautin kuka biyu yaje ji a kunnen shi, tare da jiyo ƙarar wutar dake cinye jikin nata hakan ya saka baya iya runtsawa idan ba wani abu ya afa ba haukwata shi ake son yi. "Na yarda da kai Goje, ka ci amanata askira zan saka maka a maƙoshi" "Ni ɗan halak ne. Yanzu ya batun Manager ɗin? Ka santa ne na ji baka bashi amsa ba" jin ya yi shiru ya saka shi cewa "Ko dai ka san Managern kamfanin?" "Karka ka daman" ***** Fiyya na zaune a saman gadonta tunda ta dawo take kwace tunani ne fal a cikin zuriyarta ga wani irin tsoro da bata taɓa jin shi ba, a karo na farko ta ji tana son sanin komai da komai na Kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, da duk mutanen da suka saka hannun jari a ciki data rufe idanunta yatsun hannun take ganin da aka yanka aka zuba cikin leda sosai taga rubutu jikin ledar amma ta manta bata duba ba. Ta juya a hankali tana kallon wayarta kamar mai tunanin wani abu kuma sai ta ɗauki wayar tana dannawa numbersa ta kira aka danna line busy. Har zata ajjiye wayar sai ta ji an kira ta zubawa sunan idanun kafin ta ce. "Ashraf..." Kiran ta ɗaga ta kara a kunne ta yi shiru ta cikin wayar ya sauke numfashi da ƙyar muryarsa a hankali. "Na ji tsoro Fiyya" ta ɗan tura bakinta gaba kamar yana kallonta muryarta mai daɗi ta ce "He said he was scared" ya ƙara fidda numfashi kamar tana gabansa "Maama kina wahalar dani da kika zaɓi aikin nan na kusa mutuwa, na ji ba zan iya barin ki ba kuma ke ce dai wacce nake so Fiyyar nan tawa" "Ba na ce ka daina ce mini Maama, why not Fiyya kawai?" Kamar mai raɗa a hankali Ashraf ya ce "I am sorry bestie me" Dum! Haka ta ji kan ta ya yi masifar sarawa da sauri ta dafe kan nata tana jin kamar wani abu na janta a gigice cikin faɗa ta ce "Karka sake kira na da wannan sunan" ta cikin wayar ya ce "Ba zan sake ba amma lafiya kike? Yanzu kike mini magana cikin soyayya Fiyya me ya sa sometimes kike abu kamar bake ba? Are You okay?" "Kai na ke ciwo" Tana cewa haka ta kashe kiran ta cillar da wayar nata zuwa gefe guda. Da sauri ta miƙe babu ko hula a kan gashinta yana tashi sama tana dafe da kanta bata ganin ko gabanta duhu ne a cikin idanunta haka ta dinga sauka akan matattakalar benen. Karo ta yi da mutum cikin sauri ta kama hannunsa tana ɗorawa a kanta "Yaya J kai na zai cire wani abu nake ji, ciwo yake mini kamar ana jana" gabaɗaya ta rikice ta ƙanƙame shi har zufa ke tsattsafo mata. Kama hannunta ya yi ya jata saman kujera taƙi sakin shi ya zauna a hankali tare da zaunar da ita ta yi saurin ɗora kanta a cinyarsa ya riƙe mata kan yana murza goshinta nata very careful kar ta ji zafi. Sun jima kana ta shiga sauke ajjiyar zuciya numfashinta na sauka ya ɗan leƙa fuskantarta yaga bacci take ya saka hannu ya juyo da fuskarsa yana zuba mata idanu ya riƙe hannunta har lokacin bai ce komai ba. "Aliyu" Da sauri ya saki hannun nata yana zame ta ya miƙe tsaye Ummi ta kalli Fiyya ta kalle shi ta ce "Ita kuma lafiya take bacci a nan? Yaushe ta shigo gidan ai lokacin tashi bai ba?" Captain dai ya yi shiru ta juya ta kalle shi sosai ta ce "Lafiya take?" "Ban sani ba" "To ya naga kana haɗe rai duka zaka kawo mini me kai komai naka babu walwala Aliyu ka dubi girman Allah ka dinga murmushi shifa yin murmushi sunna ne ta ma'aiki" ya shafa kan shi yana zuba hannu a aljihu cikin gaskiyarsa ya ce "Ban iya ba wallahi Ummi ki koyan" "Shi murmushin? Allah ya rufa asiri to wannan matarka ta shiga uku" yana dai tsaye bai ce komai ba. "Maama?" "Ummi" "Maama ta shi yammaci za ki yi ƙunci ko ciwon kai idan kikai bacci" ta buɗe fararen idanunta suka haɗa idanu ta sha kunu sosai tana tura baki ya zabga mata uwar harara ta yi baya zata koma baccin. "Kee" ya kira sunanta ta buɗe idanu "Tashi kafin na yi balle da wannan silar ƙafafuwan" miƙewa tsaye ta yi ta murguɗa masa baki bata ce komai ba shi kuma ya yi kamar zai juya ya damƙo hannunta ta ƙwalla ihu daidai nan Daddy ya shigo parlon cikin sauri ya sake ta. "Da kyau Soja gwara ka nuna ƙarfinka akan ɗiyata, yanzu zaka tattara ka koma inda ka fito" Captain ya juya ya bar parlon gabaɗaya yarinyar haushi take bashi har zuciyarsa. Daddy ya kalli Fiyya ya ce "Maama, yaushe za ki girma ina ganin wawtar wanda ya ɗauki muƙa min Manager ya ba ki wallahi" "Daddy kune kuke raina ni wallahi, na girma am matured enough" ya girgiza kai kawai kasancewar t.v. na kunne aka fara karato taƙaitattun labarai. Sunan Scorpio aka fara ambata matsayin wanda jami'an tsaro na hukumar FID Federal investigation department suke nema idanu rufe. Dake t.v a hankali ta juya ta kalli mai karanto labaran matashin ɗan jarida dake aiki a gidan t.v na VOA juyawa ta yi ta ce "Daddy ɗan bani aron wayarka" "Ki yi me da ita?" "Wayata zan kira, ina son fita ne wajan Kinal" ya miƙa mata wayar ta ɗan jim tana ɗaga hannunta tare da copy na wasu numbersa sai kuma ta miƙa masa bayan ta yi deleting tana murmushi "La la la na tuna inda na sata" Ya kalli t.v ya kalleta ya kuma kalli wayarsa, ya dai amsa a ransa yana mai jin tsoro da mamakin kaifin tunanin Maama. Ummi kuma ta ce "Ayi ta neman mutum kamar kiyashi shi kuma ya rasa sunan da zai sawa kan shi sai kunama?" Daddy bai yi magana ba Ummi da abin ke ta cinta ta kalli Fiyya dake shirin haurawa sama ta ce "Maama ta shi me ya yi ne?" "Ummi ina zan sani, idan kika ɗauke yadda ake juya biyar ta zama goma ba abin da Fiyya ta sani" tana cewa haka ta haura cikin sauri tana nanata numbersa dake kanta cikin sauri ta yi wanka ta shirya cikin abaya ta yi rolling tare da fesa turare sauri-sauri take a haka ta sakko hannunta riƙe da waya ko jaka bata ɗauka ba. Daddy ya dube ta ya kalli lokaci "Wai zuwa wajan Kinal baya tashi sai yamma? Ita Kinal ɗin nan ta dinga zuwa mana zai fi" "Daddy ba jimawa zan yi ba, na jima ban je ba mun gaisa ba" "Maama bani da nutsuwa haka kawai idan kika fita gari ya hargitse bani number Kinal ɗin nan na kira ta" kafin ta yi magana J ya yi saurin ƙwace wayar Fiyya ya ce "Bari na kira maka ita Daddy" babu sunan Kinal a jerin wanda ta yi waya dasu yau cikin sauri ta amsa ta ce "Number Kinal a kashe yaje fa J wai ni yarinya ce na san yadda zan kare kai na no body can come and hit me" Ta kalli Daddy da Ummi ta juya ta kalli J ta ce "To tsoran na mene ni Safiyya A Marafa?" "Allah Ya tsare Maama jeki" amsawa ta yi da amin ta raɗawa J kunne "J akwai gulma yau bari na je na dawo" tana fita harabar gidan mota ta shiga ta yi mata key cikin nutsuwa dake driving har ta fita ganin ta hau kan titi ta dubi bayan motarta ta cikin gilas wata ajjiyar ta sauke mau nauyi ta rufe idanunta ta buɗe sai kuma ta ɗauke hanyar ta nufi wani titin daban a zuciyarta addu'a take yi sosai. ***** Eng Ali wali na zaune a parlo cikin wani gidansa da yake ganawa da ƴan siyasa masu mara masa baya a kujerar shi. Ya dubi CSP chief Superintendent of Police ya ce "Ina son ku ɗauke idanunku akan yarana, ko me kuke buƙata zan baku idan ɓarna sukai zan ji da komai" Csp ya ce "Hon yaushe za mu cigaba da zuba idanu ƴan dabarka suna yin yadda su kaga dama a garin nan musamman a unguwar Birget gashi lamarin na shirin haddasa faɗa tsakanin ƴan cikin gari da su ƴan Birget, mu jami'ai ne mun san gaskiya muke take ta" "Ku cigaba da takewar su wannan yaran suna da wa'adi dana samu na ci zaɓe ko inuwata babu mai gani a cikin su. Don haka ku rufe idanunku a toshe kunnuwa, zuwa gaba har matsayi zan saka a ƙara maka mu yi ƴan dabaru" CSP ya jinjina kai Eng Ali wali ya ɗakko kuɗi mai yawa ya miƙa masa yana cewa "Idan kun kama masu dilar ƙwayoyi da kayan maye na san ana miƙa su hannun NDLEA ko? Ka tabbatar ƙwayoyin na zuwa wajan Jafar shi kuma zai bawa yarana, kar ka sake sunana ya fito daman ai ƴaƴan asara ne ko an kama su ba za su taɓa furta ni suke yi wa aiki ba, lastly magana akan Scorpio ɗin nan yana neman bani ciwon kai bana son ya zama damuwata, idan F.i.d suka riga ku kama shi akwai matsala" "Karka damu hon mun zuba yaran mu ta ko'ina" Eng Ali wali ya ce "Lallai Scorpio ya zo hannu kafin zaɓe" Cikin sauri Fiyya ta fito daga cikin motarta tana shiga cikin wajan data zo a reception ta tsaya na wasu mintina tana zaune ta fito tana murmushi ta ce "Ikon Allah kamar tare kuke?" Fiyya ta buɗe idanunta sosai ta ce "Wa?" "Captain yayanki" Gabanta ya faɗi ta kasa cewa komai Kinal ta zauna ta ce "Wallahi zuwan shi biyu fa, nima dai na yi mamaki amma ya ce aiki yake dubawa shi ne ya leƙo mu gaisa har ma na tambaye shi ke sai bai bani amsa. Amarya ya kike ya sabgogi" "Good. Yanzu lokacin ku ne Kinal siyasa ta matso ana ta fama da habaice-habaice" "Kamarya habaici?" Fiyya ta cire gilas ɗin idanunta ta ce "babu abin da mawaƙa suka iya sai habaici wallahi ku zagi wanda kuke so kuma ku yabi wanda ku kaga dama" Kinal ta yi murmushi ta ce "A'a ni ba ruwana idan an kira ni dai waƙa ina yi amma ai ni ta soyayya nake yi tunda a nan na fi kauri, ina nan ina shirya miki ke da Ashraf" Fiyya ta sauke numfashi ta ce "Ina cikin matsala Kinal ban so faɗawa kowa ba wallahi" "Subuhanallahi matsala wacce kuma? A kamfanin ko gida ko wani wajan?" "Kema kin san a gida ba wanda zai mini komai sai mai baƙin halin nan, tunda ya dawo ya uzzura mini ko parlo bana fitowa mutum sai baƙar zuciya ɗan wahala kawai aikin kawai" Kinal dai ta zuba mata idanu kafin ta ce "Mene damuwar?" "Kwana biyu da suka shige ana bibiyata kullum idan na fita, harta nan wajan da na zo sai da aka biyo ni, ni ba damuwata kai na ina tsoron su Daddy su sani kin san abu idan ya same ni tashin hankali suke shiga. Kinal ban san su waye ba me kuma suke buƙata saboda bani da issues akan kowa wallahi na ji kawai ina son sanin wanda ke following nawa duk inda na je gwara mu yi fito na fito da shi, da na ce ko na yi hayar ƴan daba nima suna take mini baya?" Kinal ta buɗe idanunta sosai ta ce "Daman na fara zargin kina da taɓin hankali Fiyya, ke yanzu ina kika san inda ƴan daba suke bare ki je? Bakya tsoro ko shakka ai matsalarki police ne wannan ina ganin a gayawa Captain kawai" tsaki Fiyya ta yi tana miƙewa tsaye "gwara duk abin da zai same ni ya zaman da dai na faɗawa Captain ni ina da abin yi" "Ƴan daban za ki yi haya yanzu kenan?" "E" sai kuma ta koma ta zauna cikin nutsuwa ta kalli Kinal ta ce "Akwai abubuwan da bana ganewa kwana biyu kamfaninmu ina son na yi bincike duk abin da na samu ba daidai ba wallahi sai na kaiwa hukuma Kinal yatsun hannun mutum na gani a cikin kamfanin fa?" Kinal ta zare idanu waje ta ce "A'a ki fara samun mai kamfanin ku yi magana dashi tunda ke ce Manager" "Sai yanzu na fara tunani, i wonder aka bani Manager a kamfanina bayan akwai maza da yawa sosai da na yi tunanin ko experience ɗina ne yanzu kawai na ji ina zargi" "Zargin me?" Ta ɗaga kafaɗa ta ce "I don't know, na fara bincike dole zan gano gaskiya" Kinal ta ce "To ki bi a hankali Please Fiyya we care about you ni ma zani anniversary na makarantarmu FGC dana shigo Kamfanin gobe, har waƙa na yi mana yanzu haka wani Eng Ali wali na yi wa waƙar da aka saka ni" shiru Fiyya ta yi tana nanata sunan FGC a ranta "Na ji kamar na san makarantar nan fa" "Ke da ba ita kika yi ba ina za ki sami, ni a can na yi secondary school kinga" "Haka ne bari na je" "To ki kula Please kar ki saka kan ki cikin matsala don Allah Fiyya" murmushi kawai Fiyya ta yi tana ficewa daga cikin studio ɗin. ***** Kamar an cillo shi haka yaga Mai dawa ya faɗo masa cikin office ɗin nasa da yake tare da manyan mutane sosai tun kafin ya yi magana ya ce "Kowa zai iya tafiya" duk suka fice ya ɗaga kai ya kalli Mai dawa ya ce "Ka daina zuwa ina nake ni zan dinga neman ka" "Ka yi ƙarya" "Ni nake maka ƙarya Mai dawa?" Ya wani haɗe fuska tamau fuskarsa ɗauke da sabon yankan da aka yi masa jiya har yanzu ba'a gyara ba. "Kai ai ba Malam Abdullahi bane da ba zan ce kana ƙarya ba" Eng Ali wali ya jinjina kai ya ce "Me ya kawo ka yanzu? Har cikin office nawa" "Ka saka ni aiki har biyu, da kamo maka ɗawar can da nemo Scorpio" ya shagiɗar da baki gefe ya yi fito wanda ya cika office ɗin sosai "Na je gidan asawanta jiya" "Kana nufin gidan Abdu Marafa?" Ali wali ya ce yana miƙewa tsaye cike da tsoro Mai dawa ya ɗaga ƙafa ya ɗora a saman table ɗin gaban Ali wali "sharaɗin kawo maka ita barewar shi ne mallaka mini kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, aikin Scorpio kuma ka saka cinnakunka cire hannu daga sabgar ka bar mini ni zan nemo maka shi, bana haɗa aiki da wasu" Ali wali ya ce "Mene haɗina da kamfanin nan? Karka saka ni rigimar da tafi ƙarfina da ka san ma'anar abin da FS WORLD INVESTMENT COMPANY yake nufi ba zaka haɗa kan da shi ba, wannan Kamfanin ciwon idanu ne" Mai dawa ya ce "Ni Mutallab Tahhb ɗan babana Abdullahi da inkiya Mai dawa bana harin abu na haƙura, wannan kamfanin shi ne burina" Ali wali ya goge zufa ya ce "baka san kamfanin ba shi ya sa a ba ki yake maka wahalar faɗa ni Ali wali sabgar siyasa na sani na saka gaba, ka bar ni a haka ba zaka saka ni a masifa ba" "Waye mai kamfanin?" "Sannin hakan daidai yake da tunuwar asirin manyan mutane da dama, ka bar komai yadda ka sani" jinjina kai Mai dawa ya yi ya ce "Zan maka jahilanci ne, ka riƙe amana ka bi sharuɗan da na ce zan maka komai ni ɗan daba ne kai mai neman iko da muƙa mi ni na sare na kashe mu bauta maka shi ne. Batun kamfanin zan yi bincike da kai na, kar ka zama butu don wallahi sai na yi maka daƙiƙanci" "In sha Allah, daga nan har bayan zan yi maka komai" "Dar zan doƙa yanzu sai godiya" Yana fita Eng Ali wali ya ɗauki waya ya kira Csp ya ce "Waye Mutallab yaron da ya fito daga wajan state cid kwanan nan bayan ya yi shekaru uku a wajan su" ta cikin wayar Csp ya ce "Sunan shi dai Mutallab ya kashe matarsa aka aka kama shi, daga baya kotu ta sake shi a zama na ƙarshe ba wanda ya san dalili" Ali wali ya kashe wayar yana sauke numfashi a fili ya ce "waye MUTALLAB?" For more information 08164069385 WhatsApp only.[10/11, 9:21 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 7 *Bright pens... 2nd batch🔞* The door is open... Ga masu buƙatar ayi musu tallah. Na hango wasu ƙwailaye a conversation group da Mikiya writers 😛Maman Sayed ta ce a faɗa muku akwai maganin gargajiya cikin sati guda komai zai kankama haɗaɗɗan maganin da Fiyyar Ashraf ke amfani da su ta ce a baku numberta ba... 08063114606 Washegari da safe Fiyya na ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fito da nufin zuwa office ya rigata buɗe ƙofar, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kan ta zuwa gefe a hankali kuma can ta ce "Ina kwana?" bai amsa ba sai cewa da ya yi "You told Abba za ki wajan wata, amma kin yi ƙarya ina kika je?" Manyan idanunta ta ɗago ta kalle shi ta ce "Ƙarya kuma?" Ya rufe ƙofar ya tsaya "Idan kina yi mini kamar ba ki gane ba, kwaɗa miki mari zan yi maybe it will help you to understand it very well" ita mamakin shi take yi "Ni fa Manager ce business zai iya fitar dani ko'ina" ya buɗe mata manyan idanunsa sosai sai kuma ya ce "ina kika je" ta tura baki gaba sosai ta yi gefensa za ta shige ya saka hannu ya fisgota kafin ta yi motsi ya ɗago fuskarta ya wanka mata mari ƙwayar idanunsa tamkar zata fito waje yana ihu a saman kan ta ya ce "Idan na sake maimaita miki tambayar sai na tabbatar yatsun hannuna sun kwanta fuskarki" "Sai dai ka kashe ni" ta yi maganar ko gezau gefen fuskarta ya yi jajur dakakkiyar zuciyarta kuma ya saka ta nuna ko a jikin ta, ƙasan zuciyarta kuma wani zafi da raɗaɗi take ji "ni kike cewa na kashe ki?" Hannu ta saka zata ƙwace nata hannu idanunta cikin nasa ba tsoro ta ce "Me kake so na yi maka? Ka shigo kana tambayata abin da ban sani ba, ka saka hannu ka mari fuskar da kullum nake shafa mata mayuka masu tsada, ni ka mara ban maka komai ba, tunda ka tsane ni ka kashe ni kawai" da ƙyar ta iya ƙare maganar saboda muryarta dake rawa Captain ya saka hannu ya sake ɗauke fuskar Fiyya da mari yana huci ya ƙara ɗaga hannu zai mare ta cikin sauri ya tsayar da hannun nasa ganin hancinta na fitar da jini sosai kuma yaƙi tsayawa. Ta yi masa ƙuri da idanunta da ruwa ya kwanta a ciki, jinin kuma bai fasa zuba ba daidai nan aka buɗe ƙofar tare da shigowa ciki da sauri Fiyya ta nufi wajan Daddy ta riƙe shi tana fashewa da kukan dake cin ran ta jikinta har wani irin rawa yake yi da ɓari jinin dake fita a hancinta kuma ya shiga ɓata masa farar rigar jikinsa. Daddy ya juya ya kalli Captain daya haɗe fuskarsa "Aliyu me ka yi mata?" "Ni kuma?" Ya tambayi daddy irin bai ma san me ya faru ba "To ita da waye haka ji bi yadda take kuka hancinta na jini kuma kai na gani a ɗakin, dole kasan mene ya faru" cikin damuwa daddy ya yi maganar wacce sai da ta bayyana saman fuskarsa ya ɗago Fiyya yana duban ta sosai ya ƙara kallon Captain "Maama wannan jinin fa? Daman kina yin haɓo ne wani abun Aliyu ya yi miki?" Ita dai Fiyya taƙi cewa komai sai shassheƙar kuka take yi numfashinta na yin sama, Daddy duk ya rikice baya wasa da al'amarin daya shafi Maama ko kaɗan a ƙasan zuciyarsa yake jin soyayyarta ya kuma tabbatar ita ce rauninsa Fiyya kawai za a taɓa a iya nakasta rayuwarsa. "Ya isa daina kukan haka nan, Allah Ya nuna mini sati mai kamawa ki tafi gidan mijinki ni ma zan fi samun nutsuwa da hakan zan fi samu nutsuwa idan kikai auren nan Safiyyerh" "I love you daddy" Fiyya ta ce a hankali tana rungume daddy ya shafa kan ta cike da soyayya "daddy love Safiyyerh" tuni Captain ya fice daga cikin parlon. Anty Turai da zuwan ta gidan kenan ta ce "Ikon Allah. Yaya kai ne kake ɗaurewar yarinyar nan gindi wallahi ka lalata da soyayya take yin abin data ga dama, ko Aliyu baka tambaya abin da ta yi masa ba ta wannan figaggiyar yarinyar kake" "Fita daga ɗakin nan Turai" rai ɓace Anty Turai ta fice tana zabgawa Fiyya harara ranta duk a ɓace. Daddy ya kalli Fiyya sosai kamar zai yi magana sai kuma ya ce "jeki wanke fuskarki I'll drop you" "Daddy daman i missed your drive wallahi" murmushi ya yi mata a duk santa zai kalli Fiyya sai gabansa ya faɗi ya juya a hankali ya dubi picture ɗinta dake gaban madubi sanye da kayan graduation ta yi wani kyakkyawan murmushi ta rungume hannunta tana kallon gefe guda. Ya ƙarasa ya ɗauki photon ya shafa a hankali "Maama na ni kamar na yi ba daidai ba, bani da wani zaɓi ne i am sorry Safiyyerh Abdu Marafa" ya lumshe idanu ya buɗe a kan photon "kina tunanin kin yi girman da za ki iya kula da kan ki, ki kuma yankewa kan ki hukunci? Maama ba kin san komai ba a rayuwa you're nothing but a stubborn girl" Ya ajjiya photon ya ɗauki wayarta babu wani password a kai dudduba abu ya fara a nutse yana yi yana kallon ƙofar banɗaki can ya sauke ajjiyar zuciya ya ajjiyar wayar daidai nan ta fito. Ya yi waje yana "Ki same ni a ƙasa" Suna tafe a hanya daddy na driving a nutse ta ce "Daddy" bai kalleta ba yana dai sauraren ta domin program ɗin da ake yi da Eng Ali wali a redio shi ne ya ɗauke masa hankali. "Zan raka Kinal FGC" Wani burki ya ja a kusan tsakiyar titin Fiyya ta dafe kai tana "Subuhanallahi" "Mene haɗin ki da FGC Maama?" "Daddy Kinal zan raka suna yin taro na makarantar zan bita idan na tashi aiki" zufa har fitowa daddy take a saman goshi sunan FGC ba ƙaramin gigita masa lissafi ya yi ba. "ba za ki ba" shagwaɓe fuska ta yi "don Allah daddy wallahi na ji ina son zuwa" "Wallahi mistakenly kika je shegiyar makarantar nan sai ranki ya ɓaci kuma sai kin daina fita hatta aikin sai kin ajjiye. Wallahi Safiyyerh Abdu Marafa idan kika je za ki san waye Abdu sai na zane miki jiki da carbi ko bulala" ta yi ƙasa da kanta zuciyarta duk babu daɗi idanunta na cika da hawaye tun tana ƙarama take yin biyaya a komai akan abin da ya yi crossing da buƙatar daddy. Hannunta riƙe da jakarta ɗaya hannun wayarta data kara a kunne suna magana da Kinal, duguwa ce hakan yasa bata fiya saka takalmi mai tsayi ba suit ce jikinta as always fara tas mai riga da wando ta yi rolling da black ɗin mayafi idanunta sanye cikin wani shade glasses mai kyau a hankali take tafiya tana ɗan jinjinawa mutanen kamfanin kai with so much respect tana da girmama mutane kawai rainin hankali ne bata ɗauka "Kinal ki je kawai idan na koma gida za mu yi magana, daddy ya hana" yadda ta yi furucin ya bayyana ainihin abin da take jin a zuciyarta. "To shikenan nima na zo studio ne zan yi waƙa idan na koma gida zan shirya za mu yi video call na nuna miki cikin FGC ɗin" Fiyya ta ɗan taɓe baki daidai lokacin da take isa bakin ƙofar office nata security ya matsa ta buɗe ta shiga ta buɗe idanu ganin Ashraf zaune a office ɗin "Kinal mu yi magana anjima" ta cire wayar tana kallon Ashraf daya miƙe tsaye yana mata murmushi "Kuma da permission ɗin wa ka shigo?" "Wake neman permission idan ana batun ganin mata, na zo ganin matata ne" ta ajjiye jakar hannunta tana zama saman duguwar kujera "Sannu mai mata" ya miƙe ya dawo kan kujerar yana leƙa fuskarta "Miji ɗaya gare ki a duniya kuma nine" cikin wasa ta ce "Ai kowa ba zan aure ka don ka ji" "Funny Fiyya" a yanayinta na rashin damuwa da soyayyar ta ce "How are you?" Yana kallonta yana ji wani abu sosai game da ita "Fiyya na yi kuskure wallahi bana sanin ina shige limit ɗina sai na yi wani abu. Ni na san ba wani sona kike ba amma idan kika yi haƙuri watarana za ki ji son nan ko yaya ne kullum kina ƙara nesanta kan ki dani yayinta zuciyata ke ƙara kusanto kanta gare ki. Komai da lokacin shi idan mukai aure muka rayuwa inuwa guda I'll definitely be honest to you, ina jin kishin ki a ƙirjina ne a nan nake ji kina mini motsi Fiyya" ya nuna ƙirjinsa saitin zuciyarsa sai ya ɗan juya gwanin tausayi "Amma bakya so na" "Who told you that?" Ashraf ya buɗe idanunsa "When are you gonna tell me you love me?" Tana kallon shi tana murmushi ita tana son shi sosai kawai bata san ya zata nuna bane sometimes rigimarsa ke sawa ta bijire itama ta miƙe tsaye tana danna kiran number messenger bayan ya ɗaga ta ce "Call Md for me, ka kira mini Md da Secretary hadda accouter" ta ajjiye ta ce ta haɗa shayi a cup guda biyu ta saka cokali tana miƙawa Ashraf ɗaya idanunta cikin nasa ta ce "San da aka kai ni gidanka matsayin mata" ya lumshe idanu ya buɗe "I'll wait as far as you're with me. Abin da kawai nake buƙata shine ki so ni. Ki so ni ko da kaɗan cikin yadda nake sonki ne" ***** Anty Hameeda na sunkuye a madaidaicin parlon gidanta tana duba jarkokin lemon ginger ɗin da take siyarwa ta ji hucin mutum da sauri ta miƙe sai kuma ta yi baya a razane ganinsa tsaye a gabanta yana waige-waige kamar wanda aka biyo ga wani irin yanka a ƙarƙashin wuyansa da alama yanzu akai masa jini ja zuba, ya yi zuru-zuru sai huci yake yi naman jikinsa musamman na ƙirjinsa na motsawa "Ɗan autan Ammo wannan hucin fa kamar an biyoka wani abun ka yi? Wane ya yanke ka haka me ka yi masa?" Bai kula ta ba ya juya ta bi bayan shi kitchen taga ya nufa ba jimawa ya fito da kwanon abinci daidai nan wata mata ta fito tana ganin Mai dawa ta yi saurin sakin butar hannunta ta ce "Wannan tantirin ƙanin naki uban ne ya zo yi mana a gida? Yaushe ma aka sake shi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un mugun ji da mugun gani Ubangiji ya kare Allah wadaran ƴan daba ya tsine musu albarka ya saka su fita a cikin ajalin su" matar ta faɗa hawaye ya cika idanun Anty Hameeda ta ce "Baba ina laifin ki ce Allah ya shirya ɗa fa na kowa ne bawa kuma sai me shi, ciki ne mai haife-haife baka san me Ubangiji ya ɓoye ba suma fa ƙaddara ce ba wanda ya zaɓi yadda rayuwarsa zata kasance" "Ai duk wani ɗan daba ƙarshe wulaƙantacciyar mutuwa ce ko idan sun sha ta faɗa musu babu daɗi su kashe kan su, ko kuma su haukace garin shaye-shaye ko garin faɗan daban su a kashe su. Allah wadai" Moh dai bai yi magana ba abinci kawai yake ci hannunsa ko wankewa bai ba duk jini Anty Hameeda ta shige ɗaki bayan ta share hawayen idanunta lemo ta ɗakko masa da ruwa ta ajjiye tana kallon yadda kusan rabin fuskarsa ya yi tabo da yanka yaro ba ya kalle shi ihu zai yi ba annuri a fuskar nan. Duk yawan abincin ya cinye ta sha ruwa ya shanye lemon tas "Na Ammo yanzu kana jin abin da ka zaɓawa rayuwarka shine daidai ka ji tausayin mu don girman Allah. Wallahi daka kasance cikin wannan rayuwar gwara ka dinga aikata abubuwan da kake a baya, jibi yadda ka yi muni ka zama ƙazami sai warin dauɗa kake yi. Na je gida sun ce sun fi sati uku ko gilmawar ka basa gani wai malam aure zai ƙara kuma da ƙyar idan ba Ammo zai saka ba, na rasa wake bashi kuɗi ya fi son ya yi ta auri saki ana haifa masa yara yana kasa kulawa da tarbiyyar su" Tamkar bada shi take ba haka ya yi ko gezau can ya miƙe tsaye ta ciro kuɗi dubu ɗaya ta bashi ya kalle ta ya kalli kuɗin idanun nasa a rine kamar gauta yaƙi amsar kuɗi ganin inda ya nufa hannunsa riƙe da wuƙa ya saka Anty Hameeda ihu ta ce "Me za ka yi ka rufa mini asiri kar ka kashe mini aure na shiga uku" ko kallon ta bai yi ba, ya ɗaga labulan ɗakin Baba tana sujjada ya same ta. Tsartuwa ya yi ya fito da kunama ya cilla mata a cikin hijabi kafin ta ankare ta ɗago jin abu na bin bayanta kamar kunamar tsafi ta shige mata riga ya zaro askira ya daidaici ɗuwawunta ya lafta mana wani uban yanka, baba ta saki ihu tana ta shiga uku ya yi saurin fita askirar na zubar da jini da. Yana fita su spider suka rufa masa baya. A cikin wani kango ya kwanta ya yi shiru cikinsa zafi saboda faɗan da sukai da ƴan cikin gari akan fita wajan kamfel da sukai kilashin. Ya rufe idanu zuciyarsa na buɗewa wani irin ɗaci yake ji a cikin maƙoshinsa wani a ya tokare masa kamar yanzu komai ke faruwa haka yaga magic ɗin idanunsa ke hasko masa bidiyon komai ta ciki inda take tsaye. Yana zaune a gida a lokacin yana jin yadda karatun Almajirai ya cika masa kunne ya yi kicin-kicin da fuska. Ammo ta kalle shi ta ce "Yau kuma waya taɓa jarumin Ammo?" Ya yi mata shiru don bai fiya cewa komai ba idan ran shi ya ɓaci kafin ta sake magana wani yaro ya yi sallama ya ce "Wai bestie ya zo in ji bestie" "Waye bestie? Injiwa jeka tambayo" Mutallab a lokacin bai motsa ba ya hakimce kamar sarki kansa a ƙasa yaron ya dawo ya ce "Wai in ji Safiyyerh matar Mutallab bestie" Baki buɗe Ammo ke kallon Mutallab ta ce "Na Ammo yaushe ka yi aure bani da labari yau naga abin da ya fi ƙarfina, yara ƙananu daku wacece Safiyya" ya miƙe tsaye daga shi sai gajeren wando ta wata riga ƙarama "ban san ta ba" "Ikon Allah" Fita ya yi yana shan kunu ganinta tsaye suna haɗa idanu ta yi ƙasa da kan ta. Ya dinga kallon ta yana jiran ya ji mene "meye ne?" Ya tambaya. Hawaye ya gani a idanunta fal "Ni a gidanku zan kwana" tar ya gama buɗe shanyayyun idanunsa a kanta "wanne gidan?" Ta nuna masa gidan "sai ki ce ke wa?" Tana masa shagwaɓa wacce daman ya san hali "Matar Mutallab, baka zo makaranta ba yau ba kyau fashi" da wani irin ƙarfi ya ce "Safiyyerh!" Gani an yi kanta. *** “Safiyyerh” ya ƙwalla kiran sunanta yana zabura kamar yanzu ne abin ke faruwa jikinsa duk rawa yake ganinsa shi kaɗai a kangon ya saka ya kifa kansa zuciyarsa na wani irin tsalle tana huci jijiyin kansa sun fito sun yi kwance saman kan shi. Ƙwayar Rohypnol ya ɓalle ya haɗiye har huɗu ya yi shiru jikinsa ya yi weak yana ganin kangon na jujjuya masa lokacin gudu yadda idanunsa suka gane masa cikin jini kwance saman gado ya sake faɗo masa, ya dinga jujjuya kansa ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak kamar wacce ta yi hooking da sauri ya zaro takardar daga cikin aljihu tsoron ƙara kalla yake ya yi saurin damƙe ta cikin hannunsa sai kuma Ammo ta faɗo masa a rai bai damu da jinin dake fita a wuyansa ba ya yi kwance a ƙasa shi kaɗai kamar maraya. Yammaci liƙis yana zaune gaban ta, ya kalleta a karo na farko ya ce "Me ya sa kika buƙaci na ce ina son company?" Abbasa ta ajjiye abin hannunta ta kalli cikin bukkar ta ce "Sanda ka faɗa mini waye Mutallab, ka bani labarinka zan faɗa maka hujjata tare da dalilin cewa ka cewa Ali wali kana son kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY" "Bakya tsoro na kashe ki?" Ta dube shi ta saka hannu tana goge masa wajan ciwon "ba zaka iya kashe ni ba babu abin da zaka iya yi wa Abbasa. Ya batun zama mata mazan? Mene dalilin daya saka kake so ka zama?" "Bana son haɗa danganta da kowacce kurciyya, ba idan aka yi baru aure kenan ana wani abu ba, to bana so ba wacce za ta yi sha'awar zama dani mata uku kenan babu su saboda ni ki mayar dani mata mazan" "baka watarana zaka iya buƙatar lafiya ko kasancewa da mace" "Sai godiya kafin lokacin na cika muradaina na baza ƙiyama ki mayar dani" ta dinga kallon shi ta ce "Ka tabbata ka yi tunani" "Ki aikata kawai" "An gama, riƙe wannan" abu ta bashi ya amsa ya sha ba jimawa bacci ya ɗauke shi. Bai san lokacin daya shafe ba sai farkawa ya yi ya gan shi an wanke masa ciwon an saka audiga ya yi shiru yana jin he just missed something very important. Message ɗin Eng Ali wali ya gani kan yana son ganinsa da gaggawa ya tura masa address ɗin wajan. Mai dawa na tsaye yana kallon Eng Ali wali da ya yi badda kama ya zame facemask ɗin fuskarsa yana kallon Mai dawa ya ce "Mai dawa" bai magana ba sai fito yake yi. "Abdu Marafa ya shiga gidan rediyo yau da safe ya sake jaddada ra'ayinsa akan ƙin takara ta yana kuma janyo hankalin matasa da su farka a daina amfani da su, domin yanzu matasa sunw siyasar wannan mazanin. Gwara youth su haɗa ƙungiya suna fitar da wanda suke ganin ya cancanta ya zana shugaba ba irina ni Eng Ali wali ba. Mutallab a fara shirin ɗakko yarinyar nan yadda zamu saka harshen Abdu Marafa ya yi laushi dole zai kawo kasa ya yi mubaya'a a gare ni Eng Ali wali" Mutallab dai ya yi shiru abin shi. "Mutallab ina magana ka yi shiru?" "Yau kake so a kawo ta ko gobe? Kai yanzu tukun mene ra'ayin naka akan matasa?" "Bangane ba" "Ka gane mana, ka zama ɗan halak cikin gyatuma idan ka ƙi cika mini alƙawari bayan cin zaɓe zan maka jahilci. Jinin malam Abdullahi ke guna a jikina idan na so dole na janyo maka farinjini amma na daina wannan sabgar yanzu. Na rantse da ɗan Amina ka yi mini ba daidai ba za kaga ba daidai ba ɗan malam nake ka daina ganina haka" Ali wali yace "Ai kai ƙanina ne, amma waye kai? Zan so jin tarihinka ka faɗa mini waye kai Mutallab?" Nan da nan Mutallab ya sake haɗe fuska tamau ya yi shiru. "Shikenan zan maka komai ka tabbatar ka sato mini yarinyar nan babu lokaci ban san me Hon Maɗatai yake shiryawar ba amma shirun da ya yi yana nufin komai. Sai batun nemo Scorpion" "Zan tafi zan aiko Mangal anjima" yana faɗin hakan ya fice kamar walƙiya. Kwana biyu da faruwar abin da Captain ya yi bata ta ɗauke walwala daga gidan kodayaushe tana sama, tun lokacin bata sake jin motsin shi ba. Abubuwa da yawa ke damunta yadda ciwon kai ke damunta tana jin kamar ana jona mata wani abu, bata iya bacci. Ga matsalar kamfani da kullum manyan kuɗaɗe ke shigowa cikin asoson kamfanin an rasa daga ina? Ta yi duk binciken daya kamata ta kasa gano bakin zare masu gadi sun tabbatar mata da cikin dare manyan motoci na zarya a kamfanin hakan ya saka ta ɗauki niyyar dole yau zata saci hanya ko wajan ƙarfe ɗaya na dare ta fita tana jin hakƙin kula da kamfanin yana kanta ne. Ta ƙara adding number cikin jerin numbersa ɗin abubuwan da take buƙatar sanin abu kai ma'ana hadda hujjar daddy na hanata yin wasu abubuwan. Miƙewa ta yi tare da yin wanka ta tare da alwala ta gabatar da sallar issha ta yi addu'a sosai da azkar wanda ke sanya mata nutsuwa tare da kusantata ga Ubangiji. Fiyya ta dinga kallon kanta cikin madubi sometimes tana jin kamar ba ita ba, she missed the old Safiyyerh. Buɗe ƙofar akai tare da shigowa "Zaman ɗaki manager ta fara kenan?" Murmushi kawai ta yi tana juyawa ta saka hijabi "Yaya J, how are you?" Ya yi murmushi "Nothing without manager, ki fito daddy na kira an kawo invitation card" ta haɗe fuska ya yi baya yana ɗaga hannu ya ce "cut me out Fiyya da kan shi ya saka akai yi komai" "wai dole sai an yi mini aure ko me daddy ke tsoro?" Shiru J ya yi sukai waje ta samu Dr Hash zaune ta ce "Dr good day, ina gefen kan mutum na ciwo yana ganin reflection na wasu abubuwa what was the problem?" Dr Hash ya ɗago kai haka J da kuma Marafa Ummi ma kallo Safiyyerh take daddy na zaune yana ji bai ɗago ba. Ta buɗe musu manyan idanunta Dr Hash ya ce "Me kike gani?" Kawai ta haɗe fuska ta ce "babu" wajan daddy ta ƙarasa ta durƙusa har ƙasa ta kashe shi ya miƙo mata waya Ummi ta ce "Ki zaɓi furnitures ɗin da kike so" ta yi sak tana kallon su dai daddy ya Aman wayar ya ce "Babu buƙata, zuciyata ta kasa nutsuwa zan yi requesting da an ɗaura auren kawai Ashraf ya bar ƙasar dake" da sauri ta kalli daddy "Daddy aikina fa?" "Za ki bar aikin" ta girgiza kai ta ce "ba zan maka musu ba daddy kai mahaifina ne ina yin biyayya a komai, amma don girman Allah ka bar ni daddy akwai binciken da nake yi a kamfani da zarar na kammala zan je duk ƙasar da kake so idan ma ƙare rayuwata ne a can zan yi" daddy bai kulata ba ya miƙe ya bar wajan J yana jin babu daɗi Ummi ma ta yi shiru babu yadda za ta yi da daddy idan abu akan Maama ne sai dai a kalle shi ta jawo Fiyya jikinta ta dinga bata haƙuri tana kwantar mata da hankali, Fiyya ta rungume Ummi tana kuka. Kamar kullum J Kalla ne yake sanar da an samu gawar wani babban mutum mai suna Alhaji Haladu da aka shiga aka kashe har gidan shi ana kuma zargin Scorpion ne saboda shaidar daya bari na sunan Scorpion a jikin bango. Ta dinga kallon screen ɗin t.v sai kuma ta miƙe "kin ci abinci?" Ta girgiza kai "na ƙoshi an yi mini formatted folder a wayata Yaya J" "Formatted kuma ko dai kin shiga wani wajan ne" ta ɗaga masa kafaɗa ranta duk a ɓaci. Kwanciya ta yi sukai waya da Ashraf yana ta mata maganganun masu daɗi har ta yi bacci. **** Idanunta ya kalla muryarsa a hankali ya ce "There's something about you that make me feel like you actually use magic about me, many things I do because you, many things I don't even know or remembered when I started doing them. The love I have for you is so real baby. Yet, ban san me ya sa zuciyata take yawan bijiromin da kokwanton yiwuwar samunki a rayuwata ba. I love you Safiyyerh" “I love you Safiyyerh” A gigice ta farka daga baccin tana ihu da ƙanƙame pillow jikinta na rawa sosai da ɓari da sauri Daddy ya buɗe ƙofa ya shigo haka Ummi da Yaya J wajan karfe biyu na dare "Fiyya mene? Maama mene?" Ta sakko daga kan gadon a gigice ta nufi wajan daddy bakinta na rawa ta kama hannun daddy ta ce "Mutallab daddy, Mutallab who is Mutallab?" For more information akan littafin MUTALLAB. Via 08164069385 WhatsApp only Na'ima Sulaiman Sarauta Assalama alaikum Hajiya muna da ingantaccen maganin gyaran nono wadda ya amsa sunansa magani Maganinmu ingantaccen maganine da yake tada jijiyon nonon da suka saki y'ar uwa breast dinki ko yakai silifas saboda kwanciya kikai amfani dashi in sha Allah zakiga amfaninshi acikin 1week maganinmu powder ne yana ciko da breast y gyarasu bashi da illa ajikin mutum munyi amfani da saiwoyi da magunguna gargajiya domin gyaran breast 08063114606 ina garin kano karki sanya y'ar uwa nono yana karawa mace martaba a gurin mai gida maganinmu kowa zai iya sha wadda zatai yaye ko gyara budurwa duk zasu iya sha breast dinki ya ciko yayi bull -bull [10/13, 10:53 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 8 *Bright pens... 2nd batch* "Daddy na ji kamar gangar jikina ta wanzu da wannan mai sunan, na ji ƙirjina ya mini nauyi numfashina ya taɓa gauraya da nashi daddy ina jina kamar bani ba, daddy who is Safiyyerh? Daddy tell me something about me, don Allah wallahi zuciyata bugawa take i missed something very important... Daddy!" Ganin duk sun yi mata shiru ya saka ta girgiza daddy da hannunta biyu "waye Mutallab daddy?" Duk suka sake yi mata shiru kamar basu fahimci me take nufi ba Dr Hash da bai jima da shigowa gidan ba saboda aikin kwana ya yi a asibiti ya nufi inda Fiyya take tsaye yana leƙa fuskarta ya ce "Mutallab kuma?" Ta kasa magana sai bin su take da idanu daddy ya yi namijin ƙoƙarin wajan kama kafaɗun Fiyya ya ce "Maama waye haka? Kinga irin abin da nake faɗa miki akan muhimmanci da ƙarfin addu'a kina sake da gaske kina wasa da azkar" Sakin daddy ta yi ta nufi wajan Ummi ta ce "daddy na san ke za ki faɗa mini" nan ma Ummi ta kama hannun Fiyya ta ce "Mamaa ban san me kike nufi kowa kike magana akai ba, kamar mai iskokai ki farka kina surutai mene haka kike safiyyerh?" Da sauri ta saki Ummi ta nufi wajan Yaya J ganin ta nufu shi ya yi saurin juyawa ya fita da sauri yana dafe kan shi. Fiyya ta sake juyawa wajan daddy jikinta duka rawa yake da ɓari kamar mazari ta kama hannun daddy ta ɗora a saitin ƙirjinta idanunta na cika da hawaye bakinta na rawa da ƙyar ta ce "Ni ban buƙaci sanin wani abu bayan hakan ba, ban ce dole na san wani abu ba ka yi mini alfarma ka faɗa mini waye shi waye Mutallab? Daddy please...!" Kasa magana ta yi jin an tsira mata sirijin allura ta runtse idanunta ta saki daddy ta juya a hankali ta kalli Dr Hash ta sake nutsa ganinta cikin idanunsa ta kalli allurar hannunsa sai kuma ta yi murmushi ta sake juyawa ta kalli photon daddy dake gefen gadonta "why? Me ya sa ake mini allura daddy i love you" sai kuma ta lumshe idanunta jikinta ya saki ta ji kanta ya mata nauyi tunaninta na ruɓanya gudun zuciyarta na ƙaruwa, kamar wacce ake yi wa updating haka take jin ƙwaƙwalwarta ganinta zata faɗi ya saka daddy ya riƙota ya jima bai ji tausayin abu ko wata halitta a duniya irin Fiyyarsa ya dinga kallon fuskarsa cike da so da ƙauna a hankali ya kwantar da ita saman gado ya ɗora kan ta a saman cinyarsa ya dubi Dr Hash ya ce "Hashim ya zan yi da Fiyya ta fahimta me zan yi Hashim, Awais ya ya zan yi da Maama?" Ya faɗa yana kallon Marafa duk suka kasa magana Ummi idanunta ya yi jajur baccin da basu koma ba kenan sukai spending sauran lokacin wajan Fiyya sai addu'a yake yi mata. Dab da asuba ya miƙe ya fice daman shi ya yi saura ya kulle ƙofar. Duk da nauyin da kanta ke mata bai hana ta motsa ba saboda kiran sallah wanda hakan alama ce ta cewa kai musulmi ne da zarar lokacin asuba ya yi dukkan wani rai a duniya daya kasance musulmi sai ya motsa, bakinta ɗauke da addu'a ta ce ” ﺍﻟﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬِﻱ ﺃﺣْﻴَﺎﻧﺎ ﺑَﻌْﺪَ ﻣَﺎ ﺃﻣَﺎﺗَﻨَﺎ ﻭﺇﻟَﻴْﻪِ ﺍﻟﻨَﺸُﻮﺭ" muryarta da ƙyar take fita a hankali ta ji an ɗan matsa hannunta, ta motsa yatsun hannun ta ji shi sarƙe dana wani ta rufe ido ta san cewa Yaya J "ni ka cika mini hannu" Ya buɗe ido ganin yadda ta murguɗa masa baki bai motsa ba a hankali ya zare yatsun shi ganin tana ƙoƙarin juyo da fuska zuwa ina yake ya miƙa hannu da sauri ya kashe hasken ɗaki the same time ya miƙe ya fice yana rufe ƙofa ta bi door way ɗin da kallo. **** Ammo na zaune a cikin ɗaki kamar yadda ta saba kodayaushe Malam ya ɗaga labule yana daga tsaye ya kalli Ammo ya ce "Ba dai tunanin wancan gantalallan kike ba? Kamar wacce aka ce na mutu kike takama ki yi ni ɗaki kwana ɗaki, to idan ma shine ki sawa zuciyarki ruwan sanyi da salama ki sallama shi, yanzu ke ba kifi samun nutsuwa ba da bakya ganin gilmawarsa yana saka miki faɗuwar gaba" ita dai bata tanka shi ba ta cigaba da aikin da take yi. Ya sake duban ta da kyau yana furta "Aure zan ƙara na hango wata ƴar duma-dumar bazawara fara tas sakin wawa ku yanke shawara a cikin ku wa zan saka" a sanyaye ta ce "Allah ya sanya alheri, duk wacce ka saka babu komai ko ni ɗin ce" Malam ya juya zai fita Anty Hameeda ta shigo idanunta zuru-zuru alamar ta yi kuka gaban malam ya faɗi ya ce "mene kuma Hameeda?" "Malam wajanka na zo da Ammo don Allah ku saurare ni" ya yi jim sai kuma ya yi ɗakin Ammo ta bi bayansa gaishe su ta yi kafin cikin sanyin murya ta ce "Ammo ke uwa ce kin ɗauki cikin Mutallab watanni wajan 11 ɗaya yake zaune kafin ki haishe shi, kin ji zafi da raɗaɗin naƙida wajan haihuwarsa, kin shayar da shi kin goya shi a bayanki, kin bashi abinci, kin ƙaunaci Mutallab sai dai ƙaunar da yake miki kamar har ta ninka wacce kike masa, idan bashi da lafiya baya yadda kowa ya taɓa shi sai ke ban san yaushe ne ko yaya ne ya zama haka ba, labarin da nake da shi akan Mutallab ba cikakke bane, zamana a Lagos ya saka ban san wasu abubuwan ba, kin ƙi faɗa mini yadda ya zama haka kin hana a faɗa mini, shin bakya jin rauni irin na uwa? Ƙauna irin ta uwa da ɗanta, duka bakya jin hakan kike barranta kan ki da autanki Ammo, hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar kar ki manta kalmar da ake cewa idan ka ƙi naka duniya ta so shi, idan ka so naka duniya ta ƙi shi, Ammo ga duniya da bakin jama'a na rige-rige kai Mutallab kabari idan kyautata zaton watarana za a kashe shi ko ya je inda ba zai taɓa fitowa ba..," "Allahamdulilah da zai mutum ai da ya sawwaƙa mini da ƴan'sanda Mutallab masifa ya zame mini ni na gode Allah da bana ganinsa cikin idanuna" kallo malam kawai Anty Hameeda ke yi da ƙyar tana haɗiye abu mai ɗaci a maƙoshi ta ce "Dukkan iyaye suna saka hannu cikin abin da ya fi gaban sanin mutane.Kowannen su yana ba da kaɗan daga jikinsa. Ta haka, abin da ya yi girma a cikin uwa ya zama mutum. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne, sa’adda da aka haifi jariri, mutane sukan ce _mu’ujizar haihuwa_ , haƙiƙa, haihuwar yara ita ce hakƙin iyaye na farko. Da farko, jarirai suna dogara ƙwarai ga iyayensu, amma sa’adda da suke girma, suna buƙatar fiye da a mai da hankali ga abincinsu kawai. Suna bukatar taimako domin su yi girma a tunaninsu, a motsin rai, a ɗabi’a, da kuma a ruhaniya. Domin su yi girma da kyau, yara musamman suna bukatar iyayensu su yi ƙaunarsu. Ko da yake yana da muhimmanci a furta kalami na ƙauna, ya kamata ayyuka su tokara hakan. Haƙiƙa, yara suna bukatar misali mai kyau daga iyayensu. Suna bukatar ja-gora a ɗabi’a, mizanai da za su bi a rayuwa. Kuma suna bukatar wannan tun suna ƙanƙanana zuwa gaba. Abubuwa masu ɓata rai suna iya faruwa kuma suna faruwa sa’adda da ba a taimaki yara ba har sai da ya makara" kukan da take dannewa ya ci ƙarfinta "Ammo idan Malam bai fuskanta ba ki daure ki gane don girman Allah, shi kaɗai autanki ɗanki tilo ɗaya namiji da Allah Ya ba ki idan babu ranku shi ne zamu kira da sunan uba, zai mana walicci a ko'ina bai kyautu don ƙaddarar Ubangiji ta kitta a rayuwarsa ku ce za ku juya masa baya ko wofitar da rayuwarsa har haka ba, akwai hakƙin iyaye akan yara haka akwai hakƙin yara akan iyaye shin kina buƙatar Ubangiji ya tuhume ki da hakƙin Mutallab? Allah da kan shi cikin hadisi mai girma ya ce; ƴaƴanku amana ce kuma kiwo ne a gare ku, lallai za mu tambaye ku wannan amanar da kiwon idan an ce ki faɗi inda yake a yanzu ba za ki faɗa ba wannan abun da kuke kun bashi dama da lasisin ƙara lalacewa ne idan yaro ya ɗaƙko hanyar kangara jawo shi aje jiki a nuna masa ƙauna da soyayya" Miƙewa ta yi tsaye tana share idanunta "ya zo mini jikinsa duk sara kamar korarre mara iyaye a duniyar nan har na yi na gama magana bai tanka wani kuskuren iyaye ke haddasa shi" Tana kaiwa nan ta fice abin ta inda ta shige Inna Binta da Mama Zaituna na kokawa akan wani ƙanzon tuwon da aka baza ya bushe sai ya yi gwanin sha'awa tana ɓantara da kaiwa baki ta ce "eh, kya yi kya gama wannan ƙanzon sai na bawa Mufee ke ni fa akan abinci ba wani kirki gare ni ba, ba zan zauna yunwa ta yi ajalina a gidan nan ba, tunda mai gidan zuciyarsa a mace take bai san fus na hakƙin iyali ba sai auri saki da tare yara kamar ƴaƴan ɓeraye kowanne kana kallonsa yunwa zata fara maka sallama a jikinsa haba me ake da hali na..." Da sauri ta yi shiru ganin malam tsaye ta yi mamaki da bai tanka mata ba ya shige. Safiyyerh ta sakko daga saman bene tana yi tana duba wayarta ganin saƙon da Ashraf ya tura mata cewa ya ɗan yi tafiya ba ta yi reply ba ta riƙe wayar. Yaya J ta gani zaune ta juya masa manyan idanunta da suka sake fitowa farare tas ta ce "Office ɗin kenan?" "Ina ni ina zuwa office banga yadda little sis ta farka daddy's favourite" ta girgiza kai tana ɗan murmushi iya leɓe ta ce "Yaya J kenan, good morning" "Kin tashi lafiya sai ina?" "Office, ina da meeting kuma Yaya J ka yi mini addu'a Please da wannan kyakkyawan harshen naka, zan baka labari mai daɗi" ya ware hannunsa ya ce "To ina jira ko na kai ki office ɗin?" Ta girgiza kai ta juya tana nufar sashin daddy dake ƙasa. Fiyya tuni ta manta abin da ya faru ta manta wani Mutallab fresh take jin kan ta, tana ƴar waƙarta ta turanci tama manta ta shigo parlon daddy dake zaune ya zuba mata idanu ta yi saurin rufe ba ki ta ce "Ka yi haƙuri daddy i enjoying when i sing a song, don Allah ka yafe wa Maama" "Sai an yi magana idan kin yi laifi kina buɗe manyan idanunki kinawa jama'a turancin yaran zamani ke ba kowa naki da yake bature" "To babana babban laccara ne wanda ake alfahari da shi dukkan matasa ke son shi saboda ƙoƙari da iyawar shi" Fiyya ta ce tana zaman ƙasan ƙafafun daddy "Tiger" sak ta yi jin sunan da ya kira ta da shi, lallai an taɓa donganta ta sa wannan sunan na Tiger ta share kana ta gai da daddy. Ya amsa cikin kulawa duk motsin da take akan idanunsa Fiyya na da mugun wayo dana da wani experience da Qualities bata yin abun da za a iya following footsteps ɗin ta, she is a clever girl faɗanta har tsoro yake bashi ga taurin kai da miskilanci har addu'a yake Allah ya sassauta mata sai gashi Ubangiji ya gyara komai a lokacin da bai zato ba. Ya ɗauke kai yana kallon wani gefen "Aliyu yaushe ka dawo?" Idanunsa a kan waya yana dannawa, wandon uniform na sojoji ne jikinsa sai fara t.shirt tas wacce ta kama damtsen hannunsa ya saka p.cap ta sojoji fuskarsa kamar ya ce ya shiga uku can ya ce "Da daddare" "Dare da yaushe? Aliyu kai kana son shigowar dare kamar mara gaskiya?" Captain ya ɗan kalli daddy ya ce "Tun 12" "Kuma baka shigo ba me ya sa?" "Kawai daddy" ficewa ya yi yana cilla wayar a aljihu yana jin Fiyya na gaishe shi ko inda take bai kalla ba. "daddy ni ba zan iya ɗaukan wannan halin ba wallahi bai ishe ni kallo ba zan daina ko gaishe shi ina dalili, Safiyyerh Abdu Marafa na da class babu mai ɗaga mini shoulder, duk wannan abun da ya yi aure a waje ne yake soja" Ranta duk a ɓace ta miƙe tana cewa daddy ta tafi ya ce "Allah Ya tsare Manager ya shirya safiyyerh Abdu Marafa". Kasancewar sauri take yi ta saka ta yi driving kamar zata tashi saman bata wasa idan tana kan titi, tana isa ta buɗe office ta shiga fahimtar da sabuwar envelope a table ɗin ya saka ta sa hannu ta ɗauka tare da buɗewa taƙaitaccen rubutu ne mai ɗauke da jan biro wanda ke nuna rayuwarta na cikin matsala. A hankali ta fara duba consent ɗin da takardar ke ɗauke da shi tana ajjiye waya. “Jarumtarki bai kai ki tsaya bincike akan FS WORLD INVESTMENT COMPANY ba, kina iya ɗaukan rubutun matsayin wasa amma gargaɗi ne da jan kunne ga yara masu rawar kai irin ki. Ki tsaya da binciken da kike you're nothing but a manager” Ta dinga juya takardar a hannu tana jin confidence nata na ƙara hakan kamar wata dama ce aka haska mata na nuna cewa lallai akwai ƙullalliyya a wannan kamfanin, kuma ta shirya buɗe faifai ko da za su yi zubaibai ƙwarya ne, ko da gaskiyar da take ƙoƙarin bayyanawa zai yi silar barin ta numfashinta daga ƙirjinta. Ta yi Addison na cikin abubuwan da take ƙarawa a binciken za ta yi komai ko hakan na nufin fito na fito da surukinta ne. Zama ta yi ta fara duba files na sabbin kayan da aka kawo can ta saka aka kira mata accouter bayan ya shigo ba tare data kalle shi ba ta ce "Accouter kana buƙatar wani abu ne?" "Allah Ya taimaki manager kamarya fa?" Still bata kalle shi ba ta yi baya tana duba maganar da aka turo mata yanzu a waya ta ce "kawai kuɗi idan kana so na buƙatun rayuwa" "Ina jiran lokacin albashi ya yi ai nasan za a sallame mu da wuri" ta ɗago idanunta masu sanyi ta zuba a kan shi sai ta cillo masa ƙaramin file ta ce "na saka hannu ka yi signature as a accouter ka cire 1m a asusun kamfani na baka" da mamaki ya ce "Ni kika bawa kuɗin?" "E, ko baka so?" "To na ga ban yi wani aikin da na cancanci 1m ba kin sa na fara jin tsoro ba zan iya cin abin da ba haƙƙina ba" ta ɗan yi murmushi ta janyo files ɗin ta yaga ta ce "meye cikakken sunanka ma?" Rainin hankalin Manager mamaki yake bashi sai kawai ya ce Wazeer" da hannu ta ce ya je yana fita ta saka aka kira mata MD abin da ta yi wa Accouter shi ta yi wa Md cikin sauri ya ce "Yanzu kika ɗakko hanya manager da za ki haƙa ramin da za ki iya binne kan ki ciki ai duk sai na raina wayonki wallahi da ajin nan naki ko mene a ƙasa ba ruwanki mind your own business rayuwar nan kana kallon wasu abubuwan kake yi kamar baka sani ba, to a haka cibiya ta rai ne mu kuma yanzu hankalin jama'a da yawa na kan siyasa, matasa na neman hanyar karatu, wasu na can suna bautawa ƴan siyasa, wasu sojan baka wasu rayuwar social media wasu bangar siyasa wasu kasuwanci. Safiyyerh da yawa ana yin abin da ya samu ne ko yazo hannu ba wanda kake ganin cancnatar shi ba, ba a duba capacity na abu ko a siyasa kana ji kana ganin wanda ya dace amma kake rufe idanu ka ɗauki baragurbi saboda yana watsa maka hatsi mu ɗin kamar ka ji suka ɗauke mu, think big Fiyya ke macace babu mai ce miki don me, akwai kuɗin da shi kan shi Alhaji Baihaƙi bai sani" "Kana son siyasa" Md ya yi murmushi ya ce "Safiyyerh siyasa yanzu ai kusan a jinin kowanne matashi take, kinga muna da jam'iyyu uku ɗaya ce mai ƙarfi saboda ita ke riƙe da muƙami ma'ana ƙasar a nan Hon Maɗatai yake neman takarar kujera, sai jam'iyyar su Eng Ali wali sai last jam'iyya wacce mutumin cikin ta ya fi kowanne nagarta kuɗi masu dame shi ba, da ƙyar aka taushi zuciyarsa yake muƙamin kusan matashi ne matasa na son shi amma kasancewar yana cikin jam'iyya ƙarama kusan sabuwa ya sa ba a yin maganar shi ma kuma da ba musulmi bane" Safiyyerh ta jinjina masa kai ta ce "Ka bawa accouter ya yi signature a baka 2m, enjoy yourself MD, but sunan wanda kake bani bayani yanzu?" Ya washe bakinsa ba ƙaramin jin daɗi ya yi ba ya ce "Abraham Denial David, shine ɗan takarar" "Yana da hannun jari a nan ne?" "A'a, i don't think zai saka hannun jari a nan gaskiya" a hankali ta ce "Me ya sa?" "Kar ki zurfafa a bar maganar, za mu yi aiki tare" sallamar shi ta yi tana jin zata yi amfani da Md da accouter Md zai taimaka wajan sanyawa ta san sirrin kamfanin cikin sauƙi accouter zai taimaka wajan bayyana komai. A gefe guda tana jin kamar ta shiga batun siyasar Abraham ɗin kawai ta ji ya yi mata she just want to help him. **** Su da kan su sun kwana biyu basu saka shi a idanunsu ba, ba kuma su samu labarin inda yake ba sai yanzu da suka ganshi kamar walƙiya kwance a ƙasa idanunsa buɗe yana kallon sama Darma ya ce "Sai godiya wanda ya ce zai bi sawunka ya wahala, ɗan malam yaƙi halin malam dafinka ƙarinka masifa ne idan ka taɓa mutum da shi" "Darma" "Ka dake Mai dawa ka jima ka yi lastin irin na dabino, wa kake so a taka a kashe ko a yi masa fiɗa" Darma ya ce yana buɗe hannu sama tare da karkatar da baki hannunsa riƙe da ledar pure water ya nannaɗe a hannu yana kaiwa baki tare da zuƙa. Mutallab ya sake buɗe idanu a sama ya kasa cewa komai tunaninsa ya tafi wani wajan. Goje ya ce "Sai godiya matsalar goge ce ko wato ka kayan lantarki" "Zaman gidan yari ba daɗi,amma na ji daɗi" "Ka ce ka tuna na jakuna nan cinnaku tsakaninmu da su sai ƙarfe ba ma'ana ka tuna na jakin da suka haɗa maka kenan" "Ina jin zafi a ƙirjina farcuna na da suka cire mini sun ƙi fitowa, zan ɗauki fansa Goje" Kafin su yi magana an yi sallama an ƙarasu cikin sauri Mutallab ya rufe idanunsa jin muryar zabuwa. Goje ya dinga kallon wacce take tsaye "Bayin Allah sallama nake muku fa" Mangal ne ya kalleta sosai ya ce "Yi batu" ta ɗan rausayar da kai gefe ta ce "Amma dai ku musulmai ne amsa sallama wajibi ce" "To alaiki, mene sagin aiki kike so a yi miki?" Kinal ta fito da littafi da biro ta ce "Sunana Kinal ni mawaƙiya ce, har zan shige na hango ku na ji ina son tambayarku na ji ina son na yi waƙa akan ku kasan mu da mu da marubuta kusan aikin mu ɗaya muna da son bin ƙwaƙƙwafi" Goje ya ce "To ina ruwan mu? Fece kafin na yi miki lahani" "Ku ba ƴan shaye-shaye bane? To akan shaye-shayen zan muku tambaya ina yin waƙar zan kawo muku ku ji, idan kun yi shaye-shayen me kuke ji mene dalilin daya saka kuka fara shaye-shaye kuma kuke harkar daba" Moh na jin su ya juya musu baya zaka ɗauka bacci yake, ransa duk a ɓace saboda jin muryar mace da ya ji ya san daya juyo zai iya kashe ta tsaf don bashi da wani business da mata. Darma ya ce "Yanzu yadda muke ji za mu faɗa miki kenan?" Kinal ta yi saurin cewa "E, wallahi na iya waƙa ina da murya sosai babu mamaki idan na yi waƙar na saka a YouTube ta je viral na saka a tiktok ta yi trending" Darma ya ce "To ni dai tun daga sanda a gida na yi...,"Da sauri Goje ya tsayar da shi yana cewa "Kai amma ɗan tsinanniya ne kai, ba haka ake bayani ba" Miƙewa ya yi ya ce "bari na faɗa miki" wuƙa ya zaro a ƙugunsa Kinal ta zare idanu tana yin baya cikin sauri Mangal ya tare bayan jikinta na rawa ta fasa ihu jin yadda Goje ya yanke ta da wuƙa a fuska,ya danna mata ledan wiwin a baki ta fara zare ido tana ihu. Sai a lokacin Moh ya juyo yana kallon yarinyar ya cije bakinsa tare da juyawa exactly irin ihun da Safiyya ta yi lokacin zata mutu. "Gani ya kore ji, idan kin rero waƙar muna dakon ki a nan sata ƴar munafuka" Darma ya dinga tuntsira dariya sosai yana riƙe ciki "Amma Goje baka da imani kamar fa fitsari ta yi a wando gaskiyar kurciyar nan akwai jan ido ga bayani nan kin gani ganin idanunki ai" ya juya ya kalli Moh ya leƙa ga wata cukurkuɗaɗdiyya takarda yake karantawa shi ba wani karatu ya yi ba "Wai wannan takardar mece kamar ta asiri kodayaushe tana wajanka, kamar numfashin shaƙa ka faɗa mana ta mece" cikin sauri ya ɓoye yana damƙe ta a hannu Goje ya ce "Nima sai fakon farar nake na mata karatun makarantar allo, na rasa wacce tsiyar ce a ciki" "Goje" "Sai godiya" "Zan saka maka tsini idan ka taɓa takardar nan ko na saka su tiger cinye ka ɗanye, wallahi zan iya kashe ka akan takardar nan" Kafin su yi magana an zo da babur an cillo wata takarda da sauri mai babur ɗin ya juya, Mangal ya miƙe tsaye ya ɗakko ya buɗe cikin sauri ya kalli Mai dawa dai kuma ya miƙa masa amsa ya yi ya duba, photo na gudu biyu ne ɗaya zanen fuskar wata kamar dai mahaukaciya sai kuma photo jira-jirai, photo me mai magana ga wanda yake da cikakken lissafi a gefe an rubuta FS WORLD INVESTMENT COMPANY. **** Kwana biyu Safiyyerh ta yi busy duk wani family sun zo saboda gobe ne ake ɗaura auren, kamar auren munafurci ba wata gayya ko shagali ɗaurin aure ne kawai ana yi kuma Ashraf zai ɗauki matarsa su tafi. A daren ranar Safiyyerh ta riga data gama accepting auren Ashraf ta yarda bata da wani miji sai shi zata sawa zuciyarta yadda zata zauna da shi tunda tana son shi ko ba can ba. Waya suka yi da Ashraf ya dinga tsokanarta "Har na hango idanun Maama a ɗakin miji, mijin na kuma Ashraf ta yi nasarar samun kyakkyawan saurayi" ta murguɗa masa baki ta ce "Zan fasa" ya yi saurin cewa "Idan ki kaga ba ki auri Ashraf to mutuwa na yi ko ke kika mutu, da gaske Fiyya ina son ki Allah shine shaida duk da ina dalilin auren ki ko saka ni akai na yi hakan amma na yi you're my life partner har janna in sha Allah" "Kamarya? Mene dalilin auren?" "Ke ba ki da wani favourite words ne sai kamarya, zan faɗa miki komai a daren ranar da kika zama halaliyyar Ashraf zan faɗa miki, zan sauƙaƙa miki binciken da kike akan Company" a ruɗe ta ce "Ta ya ya kasan ina bincike akan Company" "Safiyyerh kenan, that's is the difference between man and woman, ina da baƙi sai goben idan na zo ganin matata a wannan lokacin dole na rungume ki halal runguma zan miki Safiyyerh" hankalinta duk a tashe waye Ashraf ne me ya sa daddy ya amince da auren shi? Ta kasa magana har ya kashe kiran sai ya ƙara kiranta video call ƙura mata idanu ya yi taga yana shiri cikin sauri ta ce "Kuma sai ina?" "Inda kika aike ni" ta buɗe idanu "Kamarya?" "I miss you Fiyya shine abin da na manta na ce miki, a nan nake jin motsin ki" ya nuna mata saitin ƙirjinsa, daga nan ya kashe wayar. Daga ƙarshe ta yi zamanta cikin bedroom Awais har bedroom ya shigo ya dinga mata shira "Yaya Aiwas ka ɗan yanke mini farce" "to ban taɓa ganin amarya irin ba tunda nake a duniya" ya jawo ƙafar ya fara yanke mata farce ta rufe idanu. Washegari da sassafe Fiyya na bacci daddy da kan shi ya tashe ta, ta farka da ƙyar saboda kan ta dake ciwo mamaki ta yi ganin kusan family a ɗakin ya kalleta ya ce "Kin dai yi sallah ko?" Ta ɗaga masa kai "Daddy lafiya?" Ya yi shiru ya ce "Junaid je ku fara yin gaba, Captain an kira shi yanzu daga can headquarter, Ummi ɗakko mini hijabin Maama" Hijab ya karɓa ya saka mata ya riƙe hannunta Anty Turai ta yi gaba tana zabgawa Fiyya harara har harabar gidan suka je, abin mamaki gidan shiru ta rasa meke faruwa a motar daddy suka shiga yana baya riƙe da ita Awais na jan motar da Ummi. Motar Fiyya kuma da ita Captain ya yi using wajan fita saboda shi bai Fiyya ɗaukan tashi ba. Fiyya ta yi shiru kan ta a ƙasa,har suka ƙarasu cikin babban gidan mai tarin jama'a daidai lokacin aka fito da shi daddy na riƙe da hannunta ya ce "Mamana je ki masa addu'a" "Addu'a? Daddy waye?" Ta furta muryarta na rawa ta juya ta kalli makarar da aka ajjiye gabanta ɗauke da gawa, ya sake riƙe hannunta da kyau ya jata zuwa gaban makarar ya duƙa tare da yin namijin ƙoƙarin buɗewa. Fiyya numfashinta ta ji ya ɗauke lokacin da idanunta ya yi arba da gawar Ashraf dake kwance cikin makara, jira ya fara ɗaukar gangar jikinta da gaske Ashraf ne kwance ba yau aka ce za a ɗaura musu aure ba shine zai mutu anya gawar Ashraf ce numfashinta ya tsaya cak tana daga tsayen suka ji ta yi wani irin ajjiyar zuciya tare da yin baya cikin sauri a tare daddy da J suka tare ta, ta ƙarasa suma a jikinsu. Bayan sallatar gawar Ashraf da binne shi duk ana zaune ana addu'a daddy ya ce yana neman alfarma don Allah suka ce tame "Kar a tambayan hujja ko dalili a yanzu ina son a ɗaura auren Safiyyerh da Aliyu". *🫠for now na san a ranku za ku yi ta wasu wasu, wasu ma su ce ba su gane inda labarin ya nufa ba😛ku dai nutsu tafiyar kura ce mai tsarƙaƙƙiyya har nishaɗi kuke bani idan ana comment tafiyar da hasashe ku lissafi ba zai taɓa kawowa tunanin mutum ba, kar ku ji kun karaya domin na san dole a gaba zaku buƙaci labarin, har yanzu shimfiɗa muke yi iya shafi 8 mukai* Littafin MUTALLAB na kuɗi ne kuma za a ke yin posting kullum. An fara biya yau domin shiga paid group na MUTALLAB. MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S.... A tura shaidar biya ta nan 08164069385 ku yi ku biya a sati uku mu kammala 🫠 Domin gyaran nono ❤‍🔥🔥💃 Assalama alaikum Hajiya muna da ingantaccen maganin gyaran nono wadda ya amsa sunansa magani Maganinmu ingantaccen maganine da yake tada jijiyon nonon da suka saki y'ar uwa breast dinki ko yakai silifas saboda kwanciya kikai amfani dashi in sha Allah zakiga amfaninshi acikin 1week maganinmu powder ne yana ciko da breast y gyarasu bashi da illa ajikin mutum munyi amfani da saiwoyi da magunguna gargajiya domin gyaran breast 08063114606 ina garin kano karki sanya y'ar uwa nono yana karawa mace martaba a gurin mai gida maganinmu kowa zai iya sha wadda zatai yaye ko gyara budurwa duk zasu iya sha breast dinki ya ciko yayi bull -bull [10/15, 2:30 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 9 *Bright pens..2nd batch* "Bani da wani zaɓi sai na hakan, haɗa auren Aliyu da Safiyyerh kar ku tambayan dalili kar a tambayan cikin Safiyyerh da Aliyu waye ba ƙwayar halittata bace ta yi sanadin zuwan shi duniya, hankalina zai fi kwanciya kafin Ashraf ya kwana cikin kabari ya zamana Safiyyerh nada igiyar aure a kan ta" ajjiyar zuciya Sharfaɗi ya yi idanunsa a kan Prof Abdu Marafa ya ce "Me kake jin tsoro da kake so dole ka aurar da ita, Allah Ya gani amintar mu ya saka muka yanke hukuncin haɗa yaran nan aure saboda ƙarfafa zumunci, to kana taka Ubangijin talikai na tashi nasa kuma shine gaskiya, Ashraf ya rasu baya duniya ina tunanin ka bar yarinyar nan ta samu nutsuwa ta duba wanda take so yake son ta sai a yi mata aure, kar a ƙuntata rayuwar yarinya" "Sharfaɗi ba zaka fahimta ba, ka yi mini wannan alfarma ka wakilci Aliyu ni zan wakilci Safiyyerh ga jama'a su shaida Please sai a haɗa a yi addu'a har ta Ashraf" J zufa har yanko masa take yi na tsananin mamaki mene haɗin Captain da Safiyyerh da za a yi musu aure? Baya son zuciyarsa ta gasgata abin da yake jin tsoro ko wassafo shi cikin kan shi, Safiyyerh fa and Aliyu? Ya Allah! Shi dai Awais kan shi a ƙasa Dr Hash daman baya wajan yana can duba Fiyya tunda ta faɗi wajan ya yi shiru can daddy ya ce "Kawai alfarma nake nema zan ji daɗin hakan idan ka yi mini" "To shikenan, waye maɗaurin auren?" Daddy ya nuna wani abokinsa, Sharfaɗi ya ciro kuɗi mai yawa a cikin aljihu ya dire ya ce "Ni Sharfaɗi ina nemawa ɗana Aliyu Abdu Marafa auren Safiyyerh Abdu Marafa a wajan waliyi na wannan yarinya" daddy ya saka hannu ya ɗauki kuɗin ya ce "Ni Abdu Marafa uba a wajan Safiyyerh Abdu Marafa na bawa Aliyu Abdu Marafa auren yarinyar wajena Allah Ya sanya musu albarka" addu'a aka yi nan take kuma aka ɗaura auren a gaban shaidu ma ɗaurin ya ce "Aure ya ɗauro a kan sadakin da Sharfaɗi ya bawa dubu ɗari biyu, Allah Ya sanya albarka tsakanin Aliyu da Safiyyerh ya kuma kaɗe fitinar da kan iya wanzuwa a tsakaninsu" duk aka amsa da amin. Daddy ya lumshe idanunsa yana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya nutsuwar ta saukar masa, bashi da sauran fargaba a yanzu Safiyyerh ta zama matar wani. Kasancewar rasuwar ɗan babban mutum ce kamar Sharfaɗi ya saka manyan mutane zuwa gaisuwa, ƴan kasuwa da ƴan siyasa da wanda dai suke jin kansu wasu ne a garin. Kallo kallo aka shiga yi tsakanin Hon Maɗatai da Eng Ali wali dukkan su cikin shiga ta alfarma, ga mutane da take musu baya kowanne da tarin ƴan jagaliya da ƴan daba gudun kota kwana. Hon Maɗatai ya yi murmushi yana miƙawa Ali wali hannu ya ce "Kwana da yawa Ali wali?" Ali wali ya ɗauke hannu sai kuma ya juya ya ce "Ba yanzu ba ka jira na wani lokaci komai zai haska, za a yi tsawa walƙiya ta bayyana munafukan da suke ɓoye cikin duhun ciyayi" murmushi Hon Maɗatai ya yi kawai yana furta "Allah Ya nuna mana" gaisuwa duk sukai sai dai daddy tsakaninsu kawai addu'a ya miƙewa daga wajan. Bayan yin ta'aziyya Hon Maɗatai ya ce "Allah Ya yi wa Ashraf Rahama, ya taƙaita iya kan shi" Sharfaɗi ya juya ya kalli Hon Maɗatai kana ya kalli Eng Ali wali sai kuma ya ce "Amin, yanzu ba gashi ba gwanin sha'awa a dinga siyasa bada gaba ba sai an fi samun nutsuwar zuciya data ƙwaƙwalwa duk wanda zai samu wannan kujerar Ubangiji ya gama rubutawa kawai dai lalube ake yi cikin duhu ku haɗa kai da hannu kowa ya yi kamfel nasa babban jin daɗin ba jam'iyyarku ɗaya ba" Cikin jinjina kai Hon Maɗatai ya yi murmushi daman shi bashi da wata matsala da Eng Ali wali shi yake haukan shi hankalinsa na kan wanda ya yi shiru, shirun nasa kuma yana nufin babbar barazana a gare shi "Siyasa ai ba zata haɗa musulmi irina faɗa da wani ba, munga jiya mun ga yau muna da tabbacin za muga gobe mai kyau, ni fatana na samu gurbin saka hannun jari a kamfaninka idan aka bani dama an yi mini komai Sharfaɗi" daddy na jin su can aka kira shi waya da sauri ya miƙe tsaye yana neman uzurin tafiya Eng Ali wali ya bisa da idanu. Cikin dare Fiyya ta farka da wani irin ciwon kai na ɓari guda, ta kasa buɗe idanunta a hankali ta saka hannu ta dafe kan ta duk da halin cewa bai hanata yin addu'a ya yi tashi a baccin ba domin tabbatarwa da kanta ba a cikin kabari ta farka ba. "Sannu Maama" shine abin da Ummi ta iya cewa tana hamdala a ranta domin shirun ya yi yawa ta damƙe hannunta sosai "Ummi kai na ciwo, ciwo nake ji a gefen kaina" jikinta har rawa yake na tsananin ciwo Ummi ta ce "Maama zai daina in sha Allah, bari a kira likita" "Ummi daddy fa?" "Yanzu ya fita, ki yi ta addu'a komai ya yi farko yana da ƙarshe, wannan ciwon kan zai daina miki watarana buɗe idon ki kalle ni" a hankali ta buɗe idanun ganin yadda idanun ya yi jajir ya saka Ummi cewa "Subuhanallahi wannan jan kuma na magani da mene?" "Ummi jimawar da ta yi a kwance da ciwon kan shine ya saka idanun ja yanzu daddy zai shigo Fiyya zata ji sauƙi ki kwantar da hankali" daidai nan daddy ya buɗe ƙofa ya shigo J na bin shi a baya da Dr Hash, ganinsu kuma ya saka komai ya dawo tunanin Fiyya ta runtse idanunta tana jin fargaba na saukar mata. "Da gaske Ashraf ya mutu daddy? Da gaske an binne Ashraf babu Ashraf ya mutu yanzu haka yana kwance cikin kabari mijin da zan aura ranar ɗaurin aurena ya mutu daddy na shiga uku" daddy ya kama hannun Fiyya cikin nutsuwa ya ce "Laa, sam ba ki shiga uku ba tana iya yiyuwa ya shige iyakar shi ne, kuma mutuwa a hannun Ubangiji take idan lokacin ya yi kota wacce siga ce dole wannan rai ya koma wajan wanda ya samar dashi, Maama da gaske mijin da za ki aura mutu ki sawa ranki haƙuri ki yi masa addu'a ki saka salama ki ɗauka bashi ne zaɓinki ko alheri gare ki ba, Ubangiji na yin komai a lokacin ya yi niyya babu mai tuhumarsa hujjar hakan domin shi ishasshe ne ki yi addu'a Safiyyerh Ashraf is no longer alive pray for him" juyawa Fiyya ta yi ta zubawa daddy manyan idanunta wanda yake cike da hawaye da ƙyar ta ce "Ashraf ya mutu ya bar ni cikin zullumi daddy, inama tuntuni aka ɗaura mini aure da shi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wayyo ni Safiyyerh" "Zullumi na me kuma Safiyyerh kin ga abubuwa da yawa a rayuwa sai mutuwar Ashraf zai tsaya miki? Ba za ki yi addu'a ki sawa zuciyarki sallama, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne kamar yadda aka sanar yau ɗaurin auren ki da Ashraf Allah bai yi ba, haka kuma alƙawarin Allah gaskiya ne igiyar auren wani ta hau kan ki Maama" ta yi shiru don ta tabbatar daddy ba zai fahimce ta ba, ba zai gane me take nufi ba, ta yi missed Ashraf tun ba'a je ko'ina ba ta ji inama ita Ubangiji ya ɗauki rayuwarta ya bar Ashraf ko da bai aure ta ba, babu mamaki ta dalilinsa wani ya san abin da yake ɓoye gashi ta mutu ya barta da wani irin damuwa ba tare daya bar mata ƙofa ko ɗaya da zata gane ba komai ba. "Daddy me ya sa ka haɗa aure na da Ashraf tun fari?" Daddy ya kalli Fiyya cikin kwantar da hankali "Saboda ya cancanta kuma ya dace Maama ki yi shiru da wannan maganganun duk zafin ciwo ne yake sawa kike furta su kamar saukar ruwan sama ki yi addu'a" ta jinjina masa kai a hankali ta zare hannunta daga cikin nasa idanunta rufe sai sauke numfashi take yi ba tare da ta ce komai ba ta juya ta kwanta maganganun Ashraf na dawo ba, a ranta ta dinga masa addu'a ita bata taɓa sanin bashi da lafiya ba, he never told her he was sick innalillahi. Dr ne ya shigo zai yi magana daddy ya yi saurin girgiza masa kai alamar kada ya ce wani abu serious Dr ɗin ya zubawa Safiyyerh idanu ya ce "za'a sallame ta yau kamar yadda ka buƙaci baka son kwana zan mata allura amma before" "Thank you Dr" Dr Hash ya miƙe ya ce "daddy zan je asibiti ina da aikin dare Awais zai yi dropping nawa bana jin daɗi" Ummi ta ce "Kuma baka jin daɗin zaka tafi kamar dole ka yi kwanan tsaye ba'a ɗaukan uzuri ne" ya ɗan yi murmushi kawai ya ce "Ummi ai ba zai yiwu na amshi kuɗi na ƙi aiki ba, sai Ubangiji ya kama ni da wannan hakƙin ki yi addu'a zan iya" ta ce "To Allah ya sauwaƙe ya bada sa'a ya kuma kare" "Amin Ummi" Dr ɗin ya yi wa Fiyya allura ta samu bacci mai nauyi, Ummi dai kallon daddy take jin ya kira Aliyu ya zo ya ɗauki Fiyya nan da 20 minutes shi zai tafi tare da Ummi har lokacin Aliyu bai san da batun auren ba kamar yadda Fiyya bata ɗauki maganar daddy serious ba. Ya gyara mata kwanciya ya miƙe Ummi ta miƙe tana shafa kan Safiyyerh a haka suka fita. Har wajan ƙarfe 1:30 Fiyya na kwance tana bacci lokaci zuwa lokaci wata nurse ke shigowa duba ta. Yana tsaye hannunsa biyu zube cikin aljihu ba zai ce ga abin da yake tunani ba, amma fuskarta kawai yake kallo ganin yadda a bacci ma take ɓata rai ta sauke ajjiyar zuciya, ƙofa aka buɗe ya yi saurin yin baya yana kame fuska sosai. Dr ya kalli Captain ya ce "Sai yanzu na ɗauka ma ko a nan zata kwana" Aliyu dai ya yi shiru ya zaro waya ya fara dannawa "ga maganganun nata wannan za a yi amfani da shi lokacin...," "Ka kira su, sai ka musu bayani" shi daya tsaya tunanin yadda zai tashe ta yake ga daddy sai kiran shi yake banda haka da ba zai zo bama, ya saka ƙafa ya fara zungurun gadon dr ya ce "Allurar da aka yi mata nada ƙarfi sai dai ka ɗauke ta" siririn tsaki ya yi "to ɗauke ta kai" ganin fuskar Aliyu cikin serious ya sa dr ya nufi Fiyya zai ɗauke ta zuwa waje kafin ya ƙarasa kawai yaga Captain ya saka hannu da drip ɗin da mayafin nata ya ɗaga sama ta zabura ta yi saurin riƙe shi Idan ba kuskuren ji ya yi ba ya ji kamar ta ce "TAHHB" ya sata gaban mota ya kwantar da kujera kamar wanda ake bi haka yake jan motar. **** Yana durƙushe ya tsattsare mutumin da jajayen idanunsa wanda suka shige ciki alamar a buge hannunsa riƙe da askira gefe kuma jibgegen karan shi Tiger ne da duk a cikin karnukan ya fi son shi. Ya saka askira ɗin a cinyar mutumin ya nutsa jini ya fara fita sosai yana ihu da kururuwa cikin tsakiyar daren ga duhu ko'ina ya ce "Wai me ya sa baka da imani ne, zaka raba mini cinya biyu" Duk da cewa a buge yake amma tar ya buɗe idanunsa, cikin muryarsa da kana ji ka san shi ba ma'abocin magana bane da wani kalar sautin mai kama da gurnanin zaki ya ce "Ka gane ni yanzu?" Ya jinjina kai yana wani irin nishi da kakari kamar na mutuwa ya ce "Na gane na gane, wallahi na gane ka" "Good" ya sake nutsa askirar ya yi feshi kunama ta faɗo ta shige cikin wandon birnin ya ce "Sanda aka yi mini baru ma'ana aure, da nazo kai na ganin bakin ƙofar gidana, haka ne?" Ya sake faɗa yana ƙara cilla masa wata kunamar baƙa ƙirin ta sake shigewa cikin wandon mutumin, Darma da Goje sun tale shi kowanne ya take hannu ɗaya mutumin ya yi shiru hakan kuma ya sake fusata Moh ainun "Idan aka bani ciwon kai hauka nake yi ba zaka ka ji daɗi ba, a yunwa ce nake, yi batu" kamar zai mutu cikin kakarin mutuwa ya ce "Zan yi, zan yi magana" suka sake shi suna kallon shi. "Mutane kala biyu ne suka shigo a wannan daren da aka kawo ta, na farko sun bani kuɗi fuskar su a rufe take na biyun ma sun sake bani kuɗi suma fuskar su a rufe take amma sun bani saƙo na baka tun a wannan lokacin, bayan an kama ka na rasa wa zan bawa na dinga bulayi kawai na haƙura, daga baya kuma aka zo aka sake cewa na bada wannan saƙon na ce a'a sai sukai mini tagoma shi da kuɗi har miliyan ɗaya kawai na basu ai kan ƙasar nan yadda muke fama da babu da yunwa ga iyalai ina dasu kawai na amsa na bashi" Darma ya ce "ka ji kimini ƴan yankin nan ba za ku gama da duniya lafiya ba, da ƙyar kusha ruwan alkausara" Moh ya zubawa mutumin jajayen idanunsa sai kuma ya miƙe tsaye magana yake son yi amma ta maƙale a harshen shi da ƙyar ya ce "Ku yi masa ɓalli-ɓalli" yana cewa haka ya juya. "Baka ji ba, ai na haddace abin da aka rubuta harafi uku ne a jiki. A.M.A, sai wani suna nada ban kamar sunan asibiti kamar sunan unguwa idan na tuna zan zo na faɗa maka amma don Allah kar ku yi mini komai a tausaya mini sabuwar amarya ce dani" "Ni tawa matar ko kwana ban yi ɗakinta ba, duk irin gwagwarmayar dana sha, uhmmm" ya yi shiru a lokacin sautin muryarta yake ji na kakarin mutuwa a kunnensa can ya miƙe kawai ya yi gaba. Goje ya ce "Zan dinga zuwa lokaci lokaci domin kana cikin taskar Moh" Da sauri suka bi bayansa ganin har ya yi nisa sosai "Mai dawa daman ka iya yaran nasara na ji ka ce Good" "Na yi kala da wanda iya turanci ko mota ko amfani da waya ne?" Kallon tsaf sukai masa Darma ya ce "Ciki ne kai yasin sai fama kake da kan ka ba wannan maganar a basar kawai ya maganar ɗawan nan?" Kamar zai yi shiru sai ya ce "Bana son sabga da mace zan iya kashe ta kamar yadda itama ɗayar na kashe ta" Darma ya fashe da dariya sosai yana kaɗa kan shi ya ce "ba wannan ba wallahi wata figigiya da ita, suma dai basu da man kai wai ita ce manja" Goje ya ce "matsalar kai daƙiƙi ne ajawo sam ciki ne kai, manager ake cewa dake mayen garau garau ne kai wai manja ai uwar manja gaja kawai" Darma dai bai kuma Goje ba ya ce "Maganar gaskiya wannan za a iya karya mata ƙugu a wajan ɗakko ta ma sille kenan, Mai dawa ko kai baka ganta bane" Ya yi musu shiru yana jinsu dai "Sai godiya, ina magana baka ganta ba wata ƴar shila da ita?" "Ita wa?" "Manja ɗin" "Idan ka ƙara ce mana manja a wajan nan za kaga manja ganin idanunka, ɗan wahalar yaro kawai" Mutallab dai idanunsa a lumshe tunanin da yake yi daban, kalmomin da mutumin ya faɗa masa nata yawo a cikin kan shi. A.M.A Ya kasa fahimtar kowanne harafi me yake nufi sai kawai ya taune bakinsa ƙirjinsa na buɗewa duk jikinsa tsami yake masa ya buɗe idanunsa ya kalli sama yana ganin yadda gajimare ke gudu yana haɗewa tare da warewa muryarsa bata wani fito sosai can ƙasa ya furta kalmar. "her eyes look alike, tiger". Washegari misalin 12 na rana Safiyyerh na saman bene cikin ɗakinta ta dinga kallon Kinal bata da nutsuwa sosai da babu abin da zai hanata yin dariya. Kinal ta share hawayenta tana ɓata fuska cikin sanyin murya ta ce "Kalli yadda sukai mini da fuska daga tambaya na ɗauka za su faɗa mini ashe ƴan wahala, ni bada wata munufar na je wajan su ba wallahi kawai su bani amsa na ƙara gaba" "To ga amsar nan ai" "Maama fuska ita ce kyan mace fa, yanzu idan tawa ta lalace waye zai aure ni haka? Sun kusa tsaga mini baki gashi yanzu ina da aiki a ƙasa sosai har Hon Maɗatai zan yi wa waƙa" Safiyyerh ta yi shiru tana tunani so take ta fice daga cikin gidan secretly amma no way "wai ina magana kina ji ba zan shariyar nan naki damuna yake, na zo ɗebe miki damuwa da kewa na rashin Ashraf kamar yadda Ummi ta buƙata duk da ciwon da bakina yake mini ina da zuba ke kina ignoring nawa for God sake" "Idan ba ƙi auro ba sai ki auri ɗan daban kawai" Kinal ta yi tsaki ta ce "Kuma zan iya, mene a ciki" "Shi auren ɗan daban?" Fiyya ta buƙaci amsa tana kallon Kinal. Kinal ta ce "Deal, nama yi miki alƙawarin in dai ina da numfashi wallahi wallahi sai na auri ɗaya daga cikin ƴan daban nan, kamar ni mawaƙiya za su yi wa haka? Uhm" Fiyya ta lumshe idanu ta buɗe deep down ƙirjinta na bugawa sai ta ce "You most like them ma, ƴan daban ai sun iya soyayya" "Ke ta ya kika san sun iya?" Shoulders kawai Fiyya ta ɗaga ba tare da ta ce komai can ta sauke numfashi tana kallon Kinal ta ce "Kinal Ashraf ya rasu, mijin da zan aura ya bar ni Kinal ina cikin damuwa ina jin da old Safiyyerh ce ba zan ce ina cikin damuwa ba, gwara ta kashe ni haka nake ji" Kinal ta jinjina kai "Fiyya something is over doesn't mean your life is over, ki yi haƙuri mu ɗauki ƙaddara ki yi wa Ashraf addu'a Please kar ki saka damuwa wani abun ya zo yana damun ki daman ke idan kika birki ce kamar mai ƴar mero a ka, ƙaddararmu zata zama mai kyau muna tare da addu'ar iyaye ai" sun jima tare da Kinal har yamma kana ta tafi gida tana jin dole ta sake komawa wajan ƴan kodin ɗin nan. Da ƙyar da daddare Fiyya ta sakko ƙasa bayan tayi sallar issha tana sanye da hijabi har ƙasa, fuskarsa looking ok ba yabo ba fallasa sai dai ta faɗa idanunta ya fito akwai damuwa a tattare da ita. Inda ta yangi su J ta nufa ta shiga tsakiyar ƴan mazan ta zauna a nutse ta ce "Sannun ku" Awais ya ɗago ya kalleta ya ce "Yawwa Manager ya ƙarin haƙuri?" Idanunta ya juya ta cije baki ta ce "Allahamdulilah,thank you" daddy dake kallon ta cike da tausayi ya ce "tashi a nan wajan Safiyyerh" "Daddy me ya sa?" "Ki dai tashi na ce ko?" A sanyaye ta miƙe sai kawai ta yi sama ya bita da idanu a hankali ta ce "Sai yaushe zaka faɗa mata batun auren?" Daddy ya ce "Da sai an kammala Visa ɗin ta, na san wacce take da ita a baya ta yi expired, to Safiyyerh stubborn girl ce da na yi maganar visa zata kalli cikin idanuna ta fara mini turanci wayonta tsoro yake bani, kuma yanzu i feel very comfortable da Aliyu matsayin mijinta duk da basa shiri amma ba zai ɗaga mata ƙafa bana son dai ta yi rayuwa a wajan shi kamar Prisoner, za ta yi shakkar yi masa abu" "Kana ganin zata amince da auren?" Ya miƙe tsaye yana haurawa sama ya ce "In sha Allah" daman daga sallah ya dawo shine ya zauna. J dai baya uhm baya uhm'uhm abubuwa da yawa ke yawo a ƙasa wanda baya rasa nasaba da tunanin wace Safiyyerh waye Aliyu? Ummi ta kalli yadda ya shigo ba wanda ya kula kamar bai ga kowa ba ta ce "Aliyu tun safe ina ka je ne?" Ya buɗe ido ya yi shiru ta ce "Kuma ka ci abinci ne? Kodayake ba'a tambayar soja ko ya ci abu da za'a buɗe cikin ka duk ganye ne" kallon Ummi kawai yake kuma ya yi shiru "Yaushe zaka tafi goben?" "A'a, night Ummi" ya ce yana shigewa cikin ɗakin shi dake part ɗin mazan. Fiyya ta ci kuka a ɗaki kamar rai da sauri ta buɗe system ɗinta taga saƙo a e-mail nata tun sanda sukai last called da Ashraf bayan hakan ta minti ashirin da wajan biyar. Maganar daya tura mata ya saka ta buɗe idanu sosai. _Safiyyerh daddy ya zo ya fita yanzu, ko ma dai menene ki tabbatar ba ki bawa wani damar mallakar FS WORLD INVESTMENT COMPANY ba Fiyya mutane biyar sune mamallakan wannan kamfanin mutane masu haɗari ko ni ban san su ba, da ina da yadda zan yi a yanzu zan faɗa miki komai domin sauƙaƙa miki, ki fara nemo ma'anar FS shine key ɗin binciken, don't cry when you miss me i love you"_ Safiyyerh was shocked, thinking me ya saka Ashraf ya yi mentioned sunan daddy a lokacin, meke shirin faruwa ne gabaɗaya kan ta ya ɗauki zafi da gaske ta yi rashin Ashraf sai yanzu ne take jin gudun zuciyarta na ruɓanya aikinta a kan Ashraf ɗin. Ta kwanta tana rufe idanunta ƙarar notification na wayarta ta saka ta buɗe idanu tana janyo wayar a hankali, rubutu a taƙaice mai ɗauke da azanci da ɓoye manufar abin da ake so a bayyana. _“laifi akan laifi again? Kodayake shi laifi tudu ne Safiyyerh ke inuwar wani ce ki yi ƙoƙari kar a saka ki shiga wuta”_ A gigice ta ce "Na shiga uku ni Safiyyerh" **** Cikin dare ne wajan biyu da arba'in motarsa na gefen titi cikin duhun daren ya saka facemask ya rufe fuskarsa tsoro da fargaba ya gaba gitta masa zuciya a hankali ya zuge glasses ɗin motar babu mai cewa shine a ciki, yana buɗewa ya faɗo cikin motar ya ce "Kira cikin dare? Ban fiya son ina tsaka da wani aikin kuma ana kira na wani ba, ya akai?" Photo ya fito masa da shi na wani kyakkyawan yaro fari tas da shi idanunsa buɗe ya shagwaɓe fuska tare da miƙa hannu alamar a bashi wani abu, yana sanye cikin wasu ƙananun kaya baƙaƙe. "Na gani photon waye? Wannan yaron fa?" "Ɗan gidan Safiyyerh ne" ya furta yana lumshe idanu tare da yin baya ya jingina da kujerar zuciyarsa na buɗewa sosai tsoro da fargaba na cika shi "What! Safiyyerh yaronta kuma?" "E, idan kaga Safiyyerh ka gan shi kamar an yi kaki ban san ko ta san da yaron ba a tabbatar an gano mini inda sa Safiyyerh take" Kwanakin wajan biyar da rasuwar Ashraf daddy bai faɗawa Fiyya batun auren ba, haka ma Aliyu Fiyya kullum sai ta fita wajan aiki ba kuma ta dawowa da wuri. Yamma wajan magariba take driving a gajiye take sosai fahimtar ana bin bayanta ya saka ta ƙarawa motar giyar da sauri ta ɗakko waya number J ta fara kira amma bai ɗauka ba, ta shiga kiran ta daddy amma a kashe duk wanda take tunanin kiran number shi a gidan ta kira bata samu ba, ta kalli madubin taga har yanzu motar na biye da ita, tare da wasu babura biyu bata iya hango fuskar mutanen amma kallo guda ta yi musu ta san ƴan daba ne, ko dai masu satar mota ne ko satar waya ta shiga uku. Baburan guda biyu suka cimma ta ɗaya ya saka hannu ya daki glasses motar nata, ta yi gefe tare da ƙarawa motar gudu suma suka take mata baya a lokacin tsoron da ya yi mata yawa ya saka ta fara gani dishi dishi kan motar na neman kwace mata, cikin sauri tana ƙanƙame steering ta shiga lalubar numbersa bata da tabbacin ko tana da ita cikin sa'a ta gani ta danna kiran sai da ta yi kiran biyar bai ɗauka ba, gashi hanya babu mutane a kira na shida ya ɗaga cikin ɗaga murya da fitar hayyaci ta ce "Yaya na shiga uku Captain wasu ne" Ya yi mata shiru can ya ce "Who are you?" "Yaya Safiyyerh ce wasu ƴan daba suka biyo ni gashi titi babu kowa, Captain suna da yawa wasu a babur wasu a mota na kira number kowa a gida basu ɗauka ba gashi ciwon kaina kamar zai tashi bana ganin hanya sosai kan motar ƙwace mini yake" ta cikin wayar Captain ya yin siririn tsaki can ya ce "Ina ruwana?" "Captain kashe ni fa za su yi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" "Allah Ya ji ƙan ki" littafin MUTALLAB Na kuɗi ne we're still on free pages. Ka biya a yi adding naka a paid book before mu yi cutting free pages ɗin. MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S. A tura shaidar biya ta nan 08164069385[10/17, 8:12 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 10 *Bright pens..2nd batch* "Kamarya Allah Ya ji ƙai na, Captain ina faɗa maka biyo ni ake yi za'a kashe ni, kana cewa Allah Ya ji ƙai na, i called you saboda na rasa wanda zan kira Please help me" ta cikin wayar Captain ya yi tsaki ya ce "Kee, ina ruwana idan sun kashe ki who cares about your life, zan kira daddy a ɗauki gawarki ok" kashe wayar ya yi. Safiyyerh wani irin zafi ta ji a zuciyarta da raɗaɗi bata san ma wanne gurbi zata saka Aliyu ciki ba idanunta ya kawo hawaye baƙin cikin kiran da ta yi masa tana zargin kanta da laifinta ne. Ta cikin madubin motar take sake kallon motar dake bib bayanta da kuma sauran baburan ta runtse idanunta a fili ta ce "Ya Allahu Ya Rahmanu ka dubi Safiyyerh ka kawo mata ɗauki..Daddy!" Ta kira sunan daddy a gigice tana sakin steering motar bata sake sanin abin da ya faru bayan nan ba. Yana tsaye fitowar shi daga motar kenan ya dubi yadda ta yi flat kwance a ƙasa gefen kanta da jini ya kalli sauran jami'an tsaron da suke wajan "Is she ok? Tana numfashi?" "She is, buguwa ne kuma Allah Ya rufa asiri motar ta tsaya da kanta, ba'a yi nasarar kama ko mutum ɗaya ba, yarinyar ce dai bamu san wace ita ba za mu duba id card nata sai a kira iyayenta a shaida musu ko asibiti ne a tafi da ita" ya yi maganar cikin girmama kan shi a ƙasa, wanda ke tambayar ko Fiyya na raye ya yi baya rungume da hannunsa can ya duba a gogo sai bai ce komai ba "Sir meeting ɗin naka? Ina tunanin ka je kawai za mu kula da komai tunda shugaban jam'iyya da secretary na jam'iyya na jiran zuwan naka" kafin ya yi magana cikin sauri wata mota ta ƙarasu wajan kamar zata tashi sama ko gama daidaita tsaiwar motar bai yi ba ya fito idanunsa a kan Safiyyerh, mutumin ya dubi fuskarta shima a hankali kuma ya ce. "Easy Captain, ka kira ni sanda muke kan titin da take ta kuɓuta Allahamdulilah" jinjina kai Aliyu ya yi cikin girmamawa ya ce "thank you" "Anything for you Aliyu, amma ku kula tana da harshe zuciyar nan tata irin take ce, Allah Ya bata lafiya" Aliyu dai na tsaye idanunsa akan fuskarta ya kasa magana har mutumin ya shiga motarsa driver ya ja, jami'an tsaron suma suka shiga motar suka marasa masa baya cikin tafiyar sirri. Ya jima yana kallon ta hannunsa riƙe da wayarsa tunanin yadda zai yi da ita, ƴar mitsitsiyar yarinya ta fito da shi, banda darajar daddy da babu abin da ya yi masa zafi sanin cewa idan Fiyya ta mutu hakan na nufin tsayawar numfashi daddy ya saka ya lallashi zuciyarsa. Cak ya ɗauke ta ya saka ta a gaban mota yana yin baya da kujerar a ransa ya ji ba zai zama drivernta ba, ya ɗauki wayarta ya rufe motar yana shiga ya tare da zama ya sake juyawa ya kalle ta da kyau sosai jinin ke fita a goshin nata ya taɓe bakinsa kawai a hankali kuma yana ɗora mata tissue ya furta “Fitinanniyya... Safiii” Farar safiya ce gari ya yi shiru amma shi idanunsa biyu, yadda ya ga dare haka ya ga rana idanunsa tarwai a sararin subuhana yana kallon sama da abubuwan da Ubangiji ya wanzar a cikinta, a hankali ya juya ya kalli Darma da Goje sai kuma Mangal dake can gefe guda ya sha ta gaya masa babu daɗi sai lilo yake da ƙafarsa a sama. Mangal ne ya buɗe idanunsa da sauri ya miƙe zaune yana murza idanunsa alamar bai gama wastsakewa ba. "Jeji naka dawa taka ka huta mai dawa, ba dai gaba da gaba ko ta baya ƙaryar mutum dan uwatar ya aka yi ba ka yi kasa bane ka raya daren da gadin mu?" Moh ya yi shiru ƙirjinsa sai ɗagawa yake. "Ina tsoron shirun nan naka don ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ka tara dafi a cikinka jira kake ka samu inda zaka sauke ƙarin dake damun jikinka ka sarara a kaiwa mai duka lillahi kukan kawai" sai a lokacin ya juyo da gajiyayyun idanunsa da suka shige ciki duk girman da suke da shi, sun yi wani bala'in ja ya zubawa Mangal ido "Talk da turanci kenan da hausa na goga maka yi magana sarkin jeji" "Mangal" "Yes inji masu jajayen kunnuwa bi ma'ana na'am" muryar Moh bata fita sosai a lokacin duk wanda ya nutsu zai hango wani irin sanyin murya da yake da shi da sauti maraya hayaniya. "Wacce cuta aka taɓa yi maka a rayuwa wacce ba zaka iya yafewa ba?" "Kan uban nan, ni ai ka sani a kusurwa kaina ya kulle wanda sukai mini kuma tuni sun girbe abin da suka shuka bana yafiya bana cuta bana bari a cutan" cije baki kawai Moh ya yi yana lumshe idanunsa da sauri ya buɗe su tar saboda yadda yake jin kakari da numfashin fitar ranta yana yi masa amo a kunne, ya mirgina kaɗan ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora akan ɗaya yana girgiza wa ya zubawa zara-zaran yatsun ƙafarsa idanu tare da rungume hannayensa a ƙirji. "Wai what happened Mai dawa?" "Ka dai na yi mini turanci don uwarka" "Ɗan tsinanniya ba, ba uban da ya iya kuma ya san ai duk bama ji shima a Legas ya koya" cewar Goje yana farkawa tare da zama dukkan su babu wanda yake da niyyar miƙewa domin yin sallah. Goje ya kalli Mutallab ya ce "Yaushe za a kwalo berewar nan ne? Ka yi shiru karfa ka jiƙa masa aiki" Da sauri Mutallab ya kalli Goje jin sunan daya kira na barewa ya lumshe idanu ya buɗe zuciyarsa na bugawa sosai sai bai ce komai ba can dai ya miƙe zaune a hankali kuma ya tashi tsaye ya zaga bayan katanga ya daɗe kafin ya dawo wajan Darma ya kalli hannun Mai dawa ya buɗe idanu ya ce "Bura... Wannan ƙwayar ka shanye to kwarankwasa ka shirya zama mahaukaci, ƙwayar doki ce fa? Wai kashe kanka za ka yi akan wasu ƴanƴan jakuna ka fito musu gaba da gaba mana, a yi komai duk abin da zai faru ya jima bai faru ba, ƙarshe dai gidan ɗan kande ne kuma mu ba wai baƙin ta bane" Mutallab ya tsaya cak a tsakiyar wajan naman jikinsa na motsawa musamman kakkauran ƙirjinsa mai faɗi sai kawai ya shagiɗe bakinsa gefe kamar zai yi murmushi da sauri ya tsuke fuska zuciyarsa na tuna masa shekarun da suka shige a fusge ya furta "Sai godiya" gabaɗaya suka miƙe tsaye suna maimaita "Sai godiya" Basu fargaba sai ganin tarin wasu ƴan daba suka gani suna fitowa daga wasu lunguna a ƙalla sun fi su ashirin ɗauke da gorori wasu wuƙaƙe. "Dara ta ci gida lallai an raina mu, mu wasu daƙiƙai zasu kawowa farmaki har lukanmu?" Cewar Darma Mangal ya kalle su ya ce "Kuma suwaye ku yara?" Wani daga cikin su ya fito ya tsaya a gaba ya ce "Sanin sunana ko waye ni bashi da wata fa'ida a gare ka, da zaka tambayi wanne kalar kisa zan maka zai fi maka, amma saboda gudun tilawa ko tafiya ƙiyama da tunanin wanda ya kashe ka lallai zan goga maka sunan nawa". Ya zaro wuƙa daga cikin ƙugunsa idanunsa akan Moh da bai ma kalle su ba sama kawai yake kallo yana jin yanayin na yi masa daɗi ya ɗora da "Uban ƴan daba nake maganin ƙananun yara masu ɓoyewa a saƙo, to cut you short sunana Lauje, ban duƙo dan na saka muku makami ba, na zo na tafi da uban gidan naku salin alin akasin hakan wajan bijire mini zai saka an samu kwacewar lissafi dar kenan" wanda ke kusa da Lauje mai suna Modara ya ce "Ka saɓo shi a wuya mana sai ka tsaya ɓata yawun da Ubangiji ya halitta a bakinka Oga?" "Ban zo don rigima ba, bisa umarnin Hon na zo wannan shine" Darma ya matsa gefe yana nuna musu Mai dawa Moh kenan ya ce "Bisimillah gashi nan kuje da shi kuna da hannu na san" Moh ya sake juya musu baya maganganunsu da gaske ciwon kai da zafin zuciya suke ƙara masa hannunsa kawai yake dunƙulewa yana hura iska sama ko yaushe ya zama sa'annin yara irin su Lauje? "Ji mana" Mutallab ya juyo yana gyara tsaiwa idanunsa a birkice Lauje ya dinga kallon Mai dawa, shi bai ya yi tunanin haka yake ba yaji ana Mai dawa da Mutallab sai ya ji sunan Mutallab kamar na ƙananun yaran ganin Mutallab cikakken namiji a tsaye mai kakkauran hannu da buɗaɗɗan ƙirji gabaɗaya jikinsa a murɗe yake musamman damtsen hannun ya basar ya ce "Shige muje" Da hannu Mutallab ya yi masa alama da ya zo ya tafi dashi, Lauje ya nufi wajan Mutallab ba tare da sanin cewa akwai shafin hannu a jikinsa ba ganin ba wani makamani hannunsa ya saka ya nufe shi. Yana miƙa hannu da sunan kama shi Mutallab ya yi masa wani naushi a gefen ƙirji, nan take Lauje ya fara fari da idanu ƙashin gefen ƙirjinsa ya yi ƙara ya sulale a wajan ba numfashi. Ganin hakan ya saka su Modara ja baya a tsora ce ya ce "Kut ya bazar dashi ba, wannan mahaukaci ne" "Bai mutu ba tafiyar zango ƙalilan ya yi kawai ya samu karaya a ƙirji, kar dai ku manta da Mai dawa kuke magana masu jeji da namomin jejin da kansu matsalar gajanci kenan kun tari mutumin dake da shafi a hannunsa duka ɗaya ka sume gwara ya saka maka kaifi daya saka hannu, ya zame muku hadda. Yi batu waye ya aiko ku?" "Hon Maɗatai" "Wani abu ne haka? Me za a yi masa?" Modara ya ce "Bamu sani ba, ya ce yana buƙatar ganinsa shi kaɗai kuma a sirrince" "To ba zan zo ba" Cewar Moh yana cije bakinsa hannunsa har yanzu rawa yake baya son yin kisa, idan ya riƙe wuƙa bai san me zai iya yi ba kuma sam. Da mamaki Modara ya ce "Kasan waye hon Maɗatai kowa? Wallahi taimako zai baka shine kawai yake jin tausayin ƴan daba irin mu" "Ɗan daba irin ka dai, shi Malam Abdullahi ne balle ya yi mini baki, ko Malam Abdullahi can ta matse masa" Modara ya buɗe baki da nufin sake magana "Kana kira mini sunansa sai na yi maka sabuwar kaciya" ba shiri ya tsuke bakinsa suka ja Lauje tare da barin wajan cike da takaici. Safiyyerh na kwance tana bacci tun bayan sallar asuba da ta yi, Dr Hash ya sake ɗaura mata ruwa a hankali kuma ya ji tana surutai ƙasa-ƙasa ya kasa kunne da kyau ko zai ji mene take cewa "Ashraf ka taimaka ka dawo ka faɗa mini ma'anar FS, ka faɗa mini suwaye mutane biyar ɗin da kake magana akai, Ashraf the company is belong to your father,ko a mafarki ne ka faɗa mini ko a fatalwa ne ka zo mini bazan ji tsoro ba, Ashraf i really really need your help, don ka dawo" Dr Hash ya juya ya kalli daddy da ya yi ƙasa da kan shi "Daddy akwai damuwa fa, meke faruwa da Fiyya ne? Me take buƙata wajan matacce ne Ashraf zai fito daga kabarinsa kuma ya yi mata, daddy Ashraf ya rasu fa ranar da za a ɗaura musu aure da Fiyya me ya sa ba za ta yi tawakakkali ba, me ya sa wai?" "She loves him so much, tana son Ashraf ne shi ne dalili" cewar daddy yana sake matsawa tare da zama a bakin gadon ya kama hannun Fiyya ya riƙe cikin nasa da kyau "wannan zafin hannun fa? Her temperature is too high, bana son zazzaɓi a jikin Maama ka yi wani abu Dr Hashim" Dr Hash ya ce "Ciwon kanta da bugawar ne ya saka mata zazzaɓi, na yi mata allura zuwa anjima zai sauka ai" Maimakon Fiyya ta yi shiru sai ta cigaba da surutan sosai tana furta "Ni ba Tiger ba ce Tahhb, why are you decided to call me Tiger?" Kamar a gaske kamar kuma yanzu ne ta ji saukar muryarsa a tsakiyar kanta, sautin ya sauka a ƙirjinta "Saboda ke matar Moh ce Tiger, zama matar Moh is not easy we most fight together halinki irin na tiger ne, matar Moh" tar da buɗe idanunta a gigice a kuma sauti na ruɗani ta ce "Motar Moh" Daddy da Dr Hash suka kalli juna jin abin da ta furta kafin su yi magana Safiyyerh ta juyo ta kalli daddy sai ta yi murmushi mai kyau wanda suka jima basu gani a saman fuskarta ba, ainahin murmushi da kyawun Safiyyerh daya shuɗe ya dawo fil ta riƙe hannun daddy a nutse ta ce "His voice daddy, muryarsa ce" "Shi wa?" "Tahhb" daddy ya yi murmushi yana shafa sumar kanta ya ce "ai kuwa na ji nima, ki yi bacci Maama za ki samu sauƙi in sha Allah" ta jinjina masa kai tana riƙe da hannunsa har lokacin ta ce "In sha Allah daddy, in sha Allah daddy" jikinta ya saki ta koma bacci daddy ya sauke numfashi ko samun sukunin karyawa bai yi ba, ya dubi Dr Hash ya sake duban Fiyya ya ce "Ka yi mata allura kafin ta farka" "Daddy ka duba Maama tana cikin damuwa ba, baka jin allurar zai saka ta dawo da ɗabi'unta na baya daddy yin allurar ba mafita ba musamman ga lafiyarta, tsayin shekaru na daddy har yaushe ne ka duba Safiyyerh don Allah" miƙewa tsaye daddy ya yi ya ce "Ka yi hakan Dr Hashim Abdu Marafa, completely tsayin rayuwa haka nake son ganin Safiyyerh" jinjina kai Dr Hash ya yi sai ya haɗa allurar har guda biyu ya juya bayanta ya caka mata cikin sauri ta ƙanƙame jikinta wani irin azaba da raɗaɗi take ji a duk sanda aka yi mata allurar. Yana yi mata ya fice ba tare daya sake kallon daddy ba. Ya zubawa photonta idanu yana juya mata baya a hankali ya ce "Ki yafe mini Safiyyerh ki fahimce ni ki fahimci mahaifinki, i am sorry Safiyyerh" fita ya yi ya rufo ƙofar ya nufi parlonsa a zaune ya tarar da Ummi tana kallon shi ta ce "Ya jikin nata? Ta farka ne?" Ya zauna yana numfasawa "Ta sake yin bacci, ina Aliyu?" "Kasan sai ya yi niyya yake shigowa" daddy ya ɗauki wayarsa ya kira number Aliyu yana ɗagawa ya ce Aliyu zo mana ya ajjiye ya kalli Ummi cikin kulawa ya ce "Ina jin kamar haɗa auren Aliyu da Safiyyerh na yi kuskure ina jin kuma hakan shine mafita, ina jin tsoron tambayar da dukkan su za su yi mini wacce bani da amsar su, da gaske bani da wannan amsar tasu Ummi, ba komai Safiyyerh take ganewa tana jin ta isa ta yankewa kanta hukunci ita ba kowa face yarinya mai wayon gaske da tunani Safiyyerh bata san komai ba ita kawai yarinya ce" "Ka san dole zaka jira amsar wannan tambayar da kake tsoro, amma sanar dasu auren shine zai fi maka a raina ina jin Maama ba zata yi maka gardama ba" kafin ya ce wani abu Aliyu ya buɗe ƙofar ya shigo da izinin daddy kamar kodayaushe wandon sojoji ne a jijinsa da farar riga tas ya ɗora hula p.cap a kan shi ya zauna kansa a ƙasa yana furta "barkan ku da safiya" "Aliyu ya aiki, baka san Maama ba lafiya bane naga baka shigo ba?" "Na sani" ya ce kawai a taƙaice yana danna wayarsa "Ka sani kuma? Shine ba ka yi mata sannu ba me ya sa kake haka ne Gadanga, me ya sa kai zuciyarka bata motsawa sai akan Maama meke damun tunaninka baka ɗaukan responsibility ɗinka as a brother" "Idan bai ɗauki responsibility nasa matsayin yaya ba, yanzu zan ɗauki responsibility Safiyyerh a matsayin mijinta" da wani irin yanayi Aliyu ya juya ya kalli daddy yana son sake tabbatar da abin da ya faɗa masa a zuciyarsa wani irin fargaba ne ya wanzu ciki a fili kuma ko gezau ya dai zubawa daddy idanu can ya ce "kamarya?" "Da kai da Safiyyerh baku da wata kalma da za ku replying mutum ko responding maganarsa sai kamarya? To kamarya dai yadda ka ji ai aikin da ka yi na soja bai saka ka daina jin Hausa ba, har gwara Safiyyerh ma" daddy ya gyara zama Aliyu dai kallon mahaifin nasa kawai yake da wani irin yanayi mai ɗauke da zallar mamaki. "Aliyu ni ban isa na saka dole ba, ban kuma isa na tilasta rayuwarka yin abin da ka yi niyya ko baka so ba, Aliyu ni dai mahaifinka ne ka saka hakan a zuciyarka. Bani da wanda zai mini wannan rufin asirin kaf family, ka manta da batun Junaid da Awais da kuma Dr, kar ka tambayi mai ya saka na zaɓe ka na ji a raina zaka kula da Safiyyerh ko bayan bana numfashi ko bayan ƙasa ta rufe mini idanu na zaɓi aura maka ita saboda dalili mai ƙarfi, na yarda da ingancinka" Ya yi shiru Ummi kuma Aliyun take kallo shi kuma yana kallon daddy da duk nutsuwarsa. "Ranar da Ashraf ya rasu a ranar aka ɗaura maka aure da Safiyyerh, don Allah don girman Allah karka tambayan tsakaninka da Safiyyerh waye ba jinina ba, wannan tambayar shine abu mafi girman laifi a gare ni, ka taimaka ka yi mini alfarma ka riƙe Maama ka amshe ta matsayin matarka" Captain ya kasa motsi balle magana bai ma san mene zai ce ba. Daddy ya matsa hannunsa "Don Allah Aliyu" "Ita ta sani?" "A'a, kai na fara sanarwa Safiyyerh bata da wata matsala ga umarni na" Aliyu ya sake yin shiru idanunsa a ƙasa har ya juya baya ya sake juyawa ya kalli daddy a hankali ya ce "tell her first, ko bana son ta zan yi ƙoƙarin ganin na fara son Safii in sha Allah" "Ba zan tambaye ka ni ne ba ɗanka ba ko ita, zan bar tambayar a raina har sanda ka shirya faɗa mana gaskiya ni da ita, zan rayuwa da fargabar sanin amsa, da gaske daddy zan so Safii iya tsayin numfashi tunda kai ka zaɓa mini ita" Daga Ummi har daddy kallon Aliyu suke musamman daddy bai yi tunanin jin wannan amsar ba ya dinga kallon Aliyu ba ko ƙiftawa "da gaske zaka so Safiyyerh? Ka san Safiyyan da nake nufi Aliyu?" Aliyu ya buɗe idanunsa wanda hula ta ɗan rufe masa su "Safiyyerh Abdu Marafa ko ba ita ba?" "Ita, zaka so ta ka ce?" Daddy ya sake faɗa da mamaki "Bata da Qualities ɗin da za a sota ne?" "Haka ne tana da shi, na shirya tafiyar ku za ku bar ƙasar nan nan da kwana biyu bana buƙatar ku gabaɗaya a yanzu domin nutsuwar zuciya" Aliyu ya sake duban daddy ya ce "Kuma? Ka bar tafiyar nan daddy" sai kuma ya juya gabaɗaya ya kalli Ummi da daddy "Aliyu soja ne, so i will be with her always" Yana cewa haka ya fita da ƙyar ya yi jarumtar kai kansa ɗaki ya cire p.cap ɗin kansa ya shiru ba auran ke damun shi ba, tunani ya fara wa daddy ya haifa tsakanin shi da Safii? Da yamma Safiyyerh ta ɗakko ƙasa bayan tafiyar Kinal daga ita sai duguwar rigar bacci kanta ba hula sosai ƙuruciyar nan tata ya bayyana, ta zauna saman kujera ta lumshe idanunta ta zama wata ira tun bayan tashin ta daga bacci jikinta ba ƙwari. I dake kallonta ya ce "Sannu Manager, ya jikin yanzu?" "Bayana ke mini ciwo Yaya J, ina jin Dr Hash ya mini allura, bana son allurar nan Yaya J bana jin daɗin ta watarana zata kashe ni don Allah ka cewa daddy ya daina sawa Dr ya yi mini" idanunta ya shiga kawo ruwa ta yi lamo da kanta saman hannun kujera. Daman yana bakin ƙofa jin abin da take cewa sai kawai ya juya shi kuma Yaya J ya ce "Ki yi haƙuri Maama za a daina miki in sha Allah" ta yi shiru kawai. Dr Hash na zaune a lambun gidan yana waya kasancewar baya da wani aiki a asibiti hutawa yake kashe wayar ya yi ganin Captain tsaye a kan shi. "Babban yaya barka da fitowa" kamar ba zai zauna ba sai kuma ya nemi waje ya zauna fuskarsa kamar kodayaushe babu walwala ya jima a haka kana ya ɗaga kai ya kalli Dr Hash "Akwai wani abu da kake son faɗa ne Captain?" "Ka daina yi mata allurar da kake mata" "Me ya sa?" "Haka dai na ce, idan kuma ka yi zaka sha mamaki" Dr Hash ya ce "Wannan kam ai daddy zaka faɗawa shine ke bada umarni" "Wa kake da suna, ka da ka sake ka kuma yi mata idan ba haka ba kuma wallahi zaka kwana ɗakin duhu" yana cewa haka ya miƙe tare da barin wajan. ***** Hon Maɗatai na zaune gabansa zube da fastocinsa yana magana da wani yaronsa wajan keɓantacce ne kamar lambu haka yake bai san da zuwan mutum ba sai huci da ya ji ta bayansa ya juya da sauri sau kuma ya buɗe idanu waje kafin ya ce "Ya zaka faɗo mini kamar ɓarawo?" "Da ɗan siyasa da ɓarawo uwa ɗaya ta haife su, waye kai?" "Baka san waye ni ba a garin kake nufi?" "Ba'a haife ni da na sanka ba, ka aika akawo ni ina fatan saƙona ya iske ka?" Hon Maɗatai ya kalli mutumin gabansa da wani ya ce "Waƙa ta yi, da ita za'a fara fita yawon kamfel a biya a dinga sawa a gidajen rediyo" ya ciro kuɗi miliyan biyu ya bawa mawaƙin ya ce "Ga sadakin ka, ina fatan waƙar gaba tafi wannan akwai wata zabiya wai ita Kinal A Awaya" cikin jin daɗi mawaƙin ya amshi kuɗin ya ce "Na san Kinal ai ta iya waƙa, ba dai ta shahara sosai bane" "To sai mu saka ta shahara na ji ta yi Ali wali waƙa, ta yi sosai ta zuba kalamai na fikira harshen nata akwai zaƙi dani kuma kawai ya dace a nemo mini ita" "zan kawo ta in sha Allah hon, ka yi ka gama ka karya kujerar dambu mai hawa uku Allah Ya kare ka ɗan Majilisa kai ne da nasara Hon" "zaka iya tafiya sai na jika" "Akwai taliya da atamfa da su Omo suger, a tabbata duk local government ɗin da aka je kamfel an basu, a kuma ɗauki photo da bidiyo za a bawa ƴan social media su baza shi ko'ina. Sai sauran magana na siyan ƙuri'u za ku yi da p.a you can leave Musbah" Musbah ya miƙe tsaye ya fice sai a lokacin ya juya ya kalli Moh dake tsaye fuskarsa duk rauni "Nan ai ba jeji bane, ni kuma ba naman jeji bane ba have a seat" "Bana zama" "Saboda me?" "Tsaro, yi magana" "Shi wanda kakewa aikin baya kula da lafiyarka ne dubi fuskarka Mutallab" "Ka kira ni da Moh ko Mai dawa sai mu yi magana" Hon Maɗatai ya jinjina kai ya ce "Ina son sanar maka na haɗa hannu da Dr Abraham, ta yiyuwa ya janye muƙamin da yake nema ƙarƙashin jam'iyyarsa idan haka ta gaske zamu kai Ali wali ƙasa ne, ka haɗa hannu dani lallai za ka ji daɗi" "Me ka shirya yi wa matasa idan kaci zaɓen?" Hon Maɗatai ya ɗaga kai ya kalli Moh sai kuma ya yi murmushi ya ce "Inganta ilimin su, rage musu kuɗin makaranta samar musu da ayyukan yi cusa musu ra'ayin noma da muhimmanci yinta" "Su kuma ƴan daba fa? Wanda kuke anfani da su wajan cimma burikan ku, bayan yaran ku na keɓe kuna tattalin tarbiyar su ba ruwansu da sabgar siyasa sai mu ƴaƴan talakawa ƴan wahala kuma ƴan daba mashaya mune ƴan bangar siyasar ku a yau, a gobe a manta damu jibi kuma a neme mu shine ko?" Hon Maɗatai ya yi murmushi ya ce "Mutallab kenan, duk wata nasara da muka samu ai daku zamu rabata ni mulki da siyasa tamkar don su ne aka haifan, ina da kyakkyawan tanadi akan ku ba za a bar rayuwarku haka ba" "Me kake buƙata" "An saka ka kamo Manager ta kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY ko?" "Wanne kiminin ya faɗa maka?" Hon Maɗatai ya miƙe tsaye yana zagayawa ya ɗauki fasta ɗinsa ya dinga kallon kansa ta ciki can ya ce "kai yin aikin ne a gabanka, mu ƴan siyasa da idanu ɗaya muke bacci mun raba kunnuwanmu ko'ina, ka dai sani a siyasa babu masoyi na dindin haka ma maƙiyi, iya ruwa je fidda kai kowa ya iya allonsa ya ce wanke kuma ni da Ali wali ai sahun qiwa ne ya take na raƙumi kowa da abin da yake buƙata, idan ka yi kidnaping yarinyar ka tilasata maka ta saka mini hannu domin na saka hannun jari a wannan kamfanin shine abin da nake buƙata" Jin Mutallab ya yi shiru ya saka ya ce "Ko baka ji ba?" "Na ji" "Mene alaƙar ka da makarantar FGC?" "Ban sani ba, maganar kuɗin aikinka sai na yi aikin zai sanar. Sai godiya" yana cewa haka ya bar wajan. Kasancewar Monday ce Safiyyerh ta shirya da wuri zuwa office har yanzu jikinta bai warware ba dole amma ya zama sai taje. Ba jimawa Md ya shigo bayan sun gaisa fuskarta dai a kame ya shafa kai ya ce "Manager gari ya ci wuta fa" idanunta akan wani ducoment tana juya kujera a hankali kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce "Nawa kake buƙata Md?" "Ko dubu ɗari biyar ne zan yi maleji" "Zan saka accouter ya baka miliyan ɗaya" ya dinga mata godiya sosai ta yi murmushi kawai ta ce "Mene ma'anar FS ni kam Md?" Tsam ya yi da ransa sai kuma ya ce "Ba zan iya ba ki wannan amsar ba Safiyyerh, zan dai faɗa miki abin da ba ki sani ba" ta sake juya kujerar hannunta a haɓarta tana murmushi mai kyau "Ina ji Md" "Yatsun da kika gani kwanaki gaskiya ne, ana siyar da ƙodar mutane a wannan kanfanin tare da jarirai, ana kuma dillacin ƙwayoyi, sauran abun ki yi bincike da kan ki za ki iya dacewa" yana cewa haka ya fita. Kasa motsi Safiyyerh ta yi numfashinta ya tsaya cak da ƙyar ta miƙe ta ɗauki ruwa ta sha ta dawo saman duguwar kujera ta zauna zufa ta dinga yanko mata a hankali ta ware rolling na kanta ta rufe idanu tana kiran sunan Allah. Knocking aka yi da ƙyar ta ce "In" Ta buɗe idanu da mamakin ganin wanda ya shigo, ya ƙarasu cikin office ɗin "Ba dole ki buɗe idanu ba Safiyyerh, idanunki kenan?" Ta yi murmushi tana gyara zamanta "I. Qasim kai ne" "Ni ne Safiyyerh" Ya nemi waje ya gaisa ta ce "Yaushe gari kuma?" Ya yi murmushi ya ce "Zama likita a garin nan is not easy Fiyya, ya batun ciwon kan ki kowa?" Ta ce "Yana nan" "Ayya sorry, akwai maganganu da zan ba ki in sha Allah da allura, gudun kar ki dinga sha ba daidai ba zan dinga zuwa dasu kina sha a gabana na yi miki allurar, za ki samu sauƙi in sha Allah" "Thank you I. Qasim na gode sosai" wayarsa aka kira ya kalleta sai kuma ya miƙe tsaye tare da yi mata alama da yana zuwa. Ta bishi da idanu har ya fita. ***** Safiyyerh ta dinga kallon daddy kamar mahaukaciya saboda rashin fahimta ta ce "Daddy, aure da Yaya Aliyu ka ce dani kuma Safiyyerh, mu duka ƴaƴanka ne fa" hawaye ya fara suntiri a saman fuskarta ta saka hannunta ta toshe kunnuwata tana girgiza kanta gabaɗaya ta jiƙa hijabin da ta yi sallah da shi da hawaye "ruɗanin da kake sani a kullum yana shirin haukatar dani daddy, ba auren ne ban yi na'am da shi ba na kasa fahimta ne dani da Captain waye wanda ka haifa waye ba ɗanka ba" "Ku duka yarana ne Maama, idan har kin yarda ni uba ne a gare ki kuma kina so na da ƙaunar farincikina ki amince da auren Maama, ba zan taɓa cutar dake ba ni ubana ne, uban ƙwarai kuma yana zaɓawa yaransa abun ƙwarai ne ki yi mini biyayya Safiyyerh, kin ji ko?" "Na amince daddy zan amince da abin da ya fi wannan ma, Allah Ya sa shine mafi alheri a gare ni" ta faɗa tana rushewa da kuka da sauri kuma ta yi waje ta nufi ɗakinta ta faɗa saman gado ta dinga wani irin kunjin kukan kamar ranta zai fita wai wanne irin abu ne haka? Ta shiga uku meke faruwa aure fa, auren ma da Captain innalillahi wa'inna ilaihirraji'un addu'a take Allah ya yafe mata komai ta fahimta da ƙyar bacci ya ɗauke ta ko abinci bata ci ba. Cikin dare ta farka ganinta ta yi rufe da bargo ta yi saurin buɗe ido don bata san kwanciya a duhu gashi an kashe mata hasken ɗakin babu mamaki Yaya J ne. Gani ta yi wajan ɗaya da rabi ta miƙe ta ɗauki ɗan makullin mota da wayarta ta saka hijabi har ƙasa, ƙofa ta buɗe ta sauka downstairs ba kowa ta buɗe ƙofa ta fita mota ta shiga mai gadi ya buɗe mata cikin sauri ta nufi kamfani gari shiru sai hasken fitilo na titi ta dinga duban hanya ba wanda ke biye da ita a haka ta isa kamfanin ta ajjiye motar a waje, ciki ta shiga wajan mai gadi sun jima suna magana ya ce "Ana shigo da mata cikin dare ana kuma fita da su, na yi bincike abin da ya saka ke iya ɓangaren abinci kika sani to akwai asibiti a cikin wannan kamfanin" ta ce "Ka ɗauki number motar ko haddacewa?" "A'a ranki ya daɗe" "To shikenan na gode Baba, ga wannan" ta ɗauki kuɗi ta bashi a cikin aljihun rigarta. Tana ƙoƙarin buɗe gate ɗin kamfanin ta fita kawai ta ji ƙarar dingowar mutane, ta juya da sauri suka haɗa idanu da Darma da kuma Goje da Mangal wani irin mummunan faduwar gaba ne ya sameta lokacin da idanunta ya shige cikin nasa shi bai kai ga dingowar ba yana zaune saman katangar shima ɗin ita yake kallo babu ƙiftawa... MUTALLAB PAID BOOK ne a jerin littafan bright pens. We're still on free pages kar ki bari a yi bake. MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 via WhatsApp only. DOMIN INGANTA NONO🔥 Assalama alaikum Hajiya muna da ingantaccen maganin gyaran nono wadda ya amsa sunansa magani Maganinmu ingantaccen maganine da yake tada jijiyon nonon da suka saki y'ar uwa breast dinki ko yakai silifas saboda kwanciya kikai amfani dashi in sha Allah zakiga amfaninshi acikin 1week maganinmu powder ne yana ciko da breast y gyarasu bashi da illa ajikin mutum munyi amfani da saiwoyi da magunguna gargajiya domin gyaran breast 08063114606 ina garin kano karki sanya y'ar uwa nono yana karawa mace martaba a gurin mai gida maganinmu kowa zai iya sha wadda zatai yaye ko gyara budurwa duk zasu iya sha breast dinki ya ciko yayi bull -bull [10/18, 9:23 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 11 *Bright pens.. 2nd batch* Ya ƙura mata idanu yana daga zaune saman katangar a hankali yake girgiza ƙafarsa, fuskarsa rufe da baƙin ƙyalle a lokacin duniyar ya ji tana masa daɗi yana jinsa kamar a cikin jirgi ana juyawa dashi, shi ya sa yaƙi sakkowa ƙasa daga katangar, shi kansa bai san wacce irin ƙwaya Mangal ya kawo masa ba. Fiyya ma shi take kallo ganin shi kaɗai ne ya rufe fuskarsa Goje da Darma da Mangal suka zagaye ta, ta juya ta kalli securityn da yake on duty ranar ta nuna masa Goje "Su kuma waɗannan fa security?" Kai tsaye ya bata amsa da "Ban san su ba, amma Hajiya akwai hatsari bamu san me suka zo nema ba" Goje ya matsa kusa da ita yana kallon ta "Mai dawa wannan ce ƙuruciyar? A hotun kamar bata kai haka girma ba, ƴar firit da ita kamar benu, nan kuma an ci kuɗin jama'a an sha madara da milo an yi ɓulɓul" sai ƙarewa Fiyya kallo yake ita kuma ta yi tsaye tana jin yadda warin wiwi ke dukan hancinta kamar za ta yi amai amma taƙi matasa saboda taurin kai irin na Safiyyerh Abdu Marafa da rashin tsoro. Tsaki ta yi kawai ƙasan zuciyarta kuma tsoro ne fal ga ƙirjinta dake bugawa kamar zai fito waje sai buɗe manyan idanu waje take yi. "And what is my business with you? Me kuke nema a wannan kamfanin kun zo sai warin ganye kuke mini" Mutallab ya sake buɗe manyan idanunsa jin sautin muryarta zaƙwai a cikin kansa ya kalli bakinta dake motsawa cike da masifa duhun dare ne amma kamfanin haske tar tar ko'ina. Mangal ya lailayo ashar ya dannawa Safiyyerh "ke dan ƙaniyarki mune muke warin ganyen, su waye sila idan baku ba, ƴar wahalar yarinya idan ban bawa tiger namanki ɗanye ya cinye ba" Safiyyerh ta juya ta kalli tiger daya hauro ya zauna kusa da Moh, yana zaro harshe waje ta nuna karan da hannu ta ce "abin da ya fi namana ɗanye, banda rainin hankali jikin nawa zaka ɗauka ka bawa shegen karan naku, idan kuɗi kuke buƙata na baku don nasa na yin caji kuke nema, stupid" Goje ya juya ya kalli Mai dawa ya ce "ba zamu rage wa yarinyar nan tsayin harshe ba kuwa? Kauɗinta ya yi over, ka je ka zauna matsalar idan ka sha wannan ƙwayar baka gane komai yanzu babu mamaki jinka kake a saudia" Moh ya lumshe idanunsa ya sake buɗe su a kan Fiyya duk motsin da take yi a kan idanunsa sai dai ba wani fahimta yake ba muryarsa a cunkushe mai ban tsoro ya shafa kan tiger ya ce "shiit" Tiger ya diro shima ya diro ya tsaya a kan ƙafafuwansa hannunsa ɗaya yana murza gashin kansa wanda ya zama wani iri ba kyan gani na shegun shahararrun ƴan daba ɗin nan. "Mai jeji ƙirit ka ankare ba lokaci ka ɗaƙkota a kafaɗa mu fece kafin kwalawa su kawo kai dan akwai kimini a nan wancan mai fararen kayan" ya nuna securityn wajan wanda shi kaɗai ne kawai ya rage. Safiyyerh ta ja baya tana juya idanunta ta ce "ban gane ya saɓo ni kafaɗa ba kamar wata ƴar iska ko mara gata, kai naga alamar kai ne shugabansu ko? To wallahi ba wuƙa ba ko bindiga ce bana tsoro kana taɓa ni sai na raba ai an ce ba wani ƙwari ne daku ba" ta ƙare maganar tana kallon cikin idanun Mutallab wanda tun ɗazo shi take kallo shi kuma yaƙi furta komai. "Ki iya harshenki ƴar kanzagi ko na fitar miki da jini yanzu na shata miki bille a wannan fuskar kamar gwada" juyawa ta yi ta ce "Baba wai where are the securities? Where are the rest ka kira su yanzu" kafin baban ya motsa Mangal ya saka ƙafa ya kwarfe shi zuwa ƙasa, ya sake saka ƙafa ya danne masa baki. Darma ya zaro wuƙa ya ce "Ke fitsararriya ce ko? Ba wata uwar muke nema ba ke muka zo ɗauka, don ke muka cikin wannan kamfanin ke za mu yi kidnaping yanzu kin fahimta kin gane ko, ki shige salin alin ko na ɗauke ki yanzu na haura dake wallahi" Fiyya ta buɗe idanu tana kallon wuƙar dashi kansa Darma ɗin ta yi murmushi zuciyarta kuma bugawa tsoro ya shige ta, ƙoƙarin danna recoding take a wayarta hannunta ya shiga rawa ta dake a ƙasan zuciyarta tana kiran sunan Allah da ƙyar ta furta "kidnaping kuma ni, ni Safiyyerh Abdu Marafa za ku sace, ni Safiyyerh matar soja guda kuna hauka ne ko kuna tunanin mijina zai bari hakan ta kasance?" Jin furucin Safiyyerh ya saka Moh sake kallonta da sauri yana hana zuciyarsa abin da yake ji, haka kawai ya dinga jin tafasar zuciya ya nufi wajan Safiyyerh jikinsa na rawa idanunsa suka fito waje kamar zasu faɗo da muryar mai ban tsoro mafi muni ba muryar ba ita kanta fuskarsa abar tsoro ce tsaf mutum zai dinga mafarkin ta. Hannunsa riƙe da wuƙa yana kallon cikin idanunta da kyau dab da ita ya ce "Ba mijinki ba ko ubanki Abdu Marafa aka bani umarnin daƙƙowa ko kashewa sai na yi balle ke" ya cije bakinsa ya feshi ya cilla mata ƙatuwar baƙar kunama ta shige ƙirjinta kai tsaye, zufa ta dinga yanko mata saboda tsananin azaba ta kasa ihu ko kuka ga warin da yake yi yana neman kashe ta, idanunta ya juye ya yi ja ta zuba masa idanu tana kallon fuskarsa data yaye,ta miƙa hannu da nufin shafo fuskarsa ta ji ya caka mata wuƙar a gefen cikinta ta yi wata ƙara tana buɗe idanu duk yadda jikinta ke rawa ga jini na zuba mai hanata sake kai hannunta ta shafo fuskarsa ba, daidai nan ya yunƙura zai saɓata a kafaɗa suka ji shigowar motoci na jami'an tsaro, bai niyyar barinta ba yadda Goje ke jan shi da ƙarfi ya saka kawai ya sake ta a wajan yana furta “Mutallab” Ɗaya bayan ɗaya suka kama katangar suka haure daman kuma kaf kamfanin ita ce ƙaramar katanga wacce babu kwalabe jikinta. Securities kala biyu ne dana fararen kaya da masu uniform sai shi da yake sanye da wando three qauter da farin takalmi da riga baƙa ko p.cap ɗin kansa babu, ya nufe ta sauran suka nufi wajan baba suka fara ɗaukan statement "Baba kwantar da hankalinka babu abin da zai sameka in sha Allah, bayan waɗannan ƴan daban da suka zo, an bamu tabbacin a daidai yanzu Scorpion ma yana wajan nan ko kuma ya zo" a hankali Aliyu ya juya ya kalli baban jin tambayar da ake masa, sai kuma ya ɗauke kai ya saka hannu ya ɗauki Fiyya zuwa cikin mota bayan ya kwantar da ita ya tsaya yana kallon wanda ke ɗaya motar a tsaye da yake ce masa "Ya akai kuka barta ta fito cikin dare haka? Macace ita fa" "Sir ƙuruciya, thanks for the call" "Anything for you Captain Aliyu" suka shiga mota duk suka bar wajan ya rage sai jami'an F.i.d kawai da suke tambayar baba. Su Goje cikin kwalabati suka shige suka ɓoye suna zare idanu da muzurai a hankali ya ce "Akwai matsala jami'an tsaro ne fal yasin, baka dai bar sheda ba kuma me ya saka ka caka mata wuƙa idan ta mutu fa?" Moh ya yi shiru can ya ce "Ba zata mutu ba" "A ciki ka soka mata wuƙar fa? Baka kalli yadda jini ke zuba bane da zaka ce wai ba zata mutu ba?" Kai tsaye Moh ya ce "ba zata mutu ba" "A buge kake shi ya sa, askira ka caka mata fa na ɗauka tsoratar da ita kawai za ta yi" A firgice ya kalli Goje idanunsa kamar za su faɗo "Goje, idan ka sake maimaita mini cewa na saka mata wuƙa zan maka jahilci yanzu wallahi zan iya kashe ka" "Kashe ni mana daman ai daba babu wata amana a ciki dole na faɗa, ɗaƙkota aka ce kawai ka yi ba kashe ta ba" Mutallab ya wani juya cikin zafin nama ya damƙo wuyan Goje cikin sauri Darma ya shiga tsakiya ya ce "Sai godiya kar a yi haka akwai amana, kai Goje ka iya bakinka idan ba farkawa kake so ka yi ka ganka a ƙiyama ba" Moh ya cije bakinsa kansa na wani irin sara masa yana girgiza kansa ya kalli sama "duk sanda na sake ganinta sai na kashe ta don uwarka" duk sukai masa shiru sun daɗe a wajan kafin jami'an tsaron su bar wajan suka fito tare da barin wajan suma kallo ɗaya za ka yi wa Moh ka ɗauke kai saboda yadda yake huci ya fiddo da ƙarin jikinsa neman inda zai sauke kawai yake. The following days. I. Qasim ya ce "Tunda ta bar I.c.u ai Allahamdulilah, she will soon recovering" "Dr Qasim ba dai abin ku kuke mana na likitoci ba, ya jikin Maama don Allah ita ce kawai last hope ɗina" Dr Qasim ya yi murmushi ya ce "Safiyyerh zata ji sauƙi in sha Allah, ba'a caka mata wuƙar inda za ta yi mata illa ba ta zubar da jini sosai ne sai kuma zuriyarta data ninka gudun da take yi, ka yi mata addu'a" "Shikenan Allah Ya bawa Maama lafiya,zan iya shiga ai kwana biyu ba'a barin mu shiga sai na ji kamar har yanzu bata dawo hayyacinta ba" I. Qasim ya girgiza kai ya ce "Daddy kana son Safiyyerh da yawa, shiga ka ganta" har bakin room ɗin da take ciki ya shiga ya shiga sanye da kayan daya dace a shiga aga mara lafiya. I. Qasim ya juya ya fita daddy ya zubawa Safiyyerh idanu tana ƙwace ta sake yin fari a barka da farar mace ta ɗan faɗa an ja mata rigar marasa lafiya zuwa saman ƙirjinta duk da baya kaya a jikin sai iya rigar an buɗe wajan ciwon da akai mata aiki a wajan ya zuba mata idanu ya matsa a hankali yana kama hannunta addu'a ya shiga yi mata sosai ta samu sauƙi zuciyarsa duk babu daɗi idan ya rasa Maama bai san yaya zai yi ba kuma. "Allah Ya baki lafiya Maama, don Allah ki rage wa kan ki fitina da zaƙewa cikin wasu al'amuran kalli yadda za ki saka rayuwarki ta lalace, Safiyyerh ban shirya ba ban shirya ba Safiyyerh" ya damƙe hannunta yaga bakinta na motsawa amma sam baya jin me take cewa. Ta shi ya yi ya fita yana sake yi mata addu'a a ransa na samun sauƙi da rangwame. Bayan ya fito waya ya saka ya kira Aliyu yana ɗagawa ya ce "Aliyu kana ina ne, an fito ita daga i.c.u amma babu kai a wajan bana son haka fa, da baya da yanzu ba ɗaya bane matsayin Safiyyerh ya jima da sauyawa" "Allah Ya sauwaƙe" Kawai Aliyu ya furta ta cikin wayar daga nan ya yi shiru ran daddy ya sake ɓaci yana jin kamar ya yi kuskure na aurawa Aliyu Safiyyerh na damƙa masa dukkan ragamar rayuwarta da tunanin zai kula da lamarin Safiyyerh amma ba lallai hakan ta kasance ba, sosai abubuwa da yawa ke damun zuciyarsa yana hana shi sukuni tare da rashin isasshen bacci, idan Safiyyerh ta tare a gidan mijinta dole ne ya amshi responsibility da Ubangiji ya ɗora masa na mijinta. Ummi na kallon daddy da jajayen idanunta ta ce "Ina ta zuba idanu rayuwar yarinyarta na neman lalacewa, ka yi abubuwa da yawa Professor na ja baki na yi shiru da tunanin duk abin da ka yi daidai ne, zuciyata ba zata ɗauka ba Safiyyerh gabaɗaya nawa take ni kawai ta haƙura da aikin wannan Companyn da bana gane masa ai shekarunta bai kai ya kawo ba, ban shirya rasata ba" daddy ya yi shiru yana kallon yadda Ummi ke kuka. "Ki tashi muje dare na yi" da sauri ta kalle shi tana share hawaye ta ce "Kuma ban gane muje ba zuwa ina?" "Ai kin san majinyata basa kwana a wannan hospital ɗin, patient ne kawai yake da alhakin kwana" tun kafin ya kammala magana take girgiza masa kai "i don't think zan iya barin wannan asibitin da Safiyyerh ita kaɗai, ni bana ma ganewa irin haka ka yi musu magana ko a nan zan iya kwana I'll manage" Daddy ya yi gaba yana furta "Kar na sake maimaita miki" dole ta miƙe bayan ta sake leƙa Fiyya ta yi waje. Kafin a rufe shigowar masu ziyara Yaya J ya daɗe zaune gaban Fiyya yana kallon fuskarta, da kwanakin baya ne zai riƙe hannunta cikin nasa yana ta mata sannu da addu'a yanzu kallon ta kawai ya kasa koda yin addu'ar ma, can ya miƙe ya fice haka Awais da Dr Hash duk suka shigo basu da tabbacin bacci take ko farkowa ne ba ta yi ba. Wajajen 2 na dare ya buɗe ƙofar ya shigo bayan I. Qasim ya bashi damar hakan daman aikin kwana zai yi idanunsa a kanta har ya shigo ya rufe ƙofar a hankali ya tsaya gabanta hannunsa biyun zube cikin aljihu ya ɗauki minti a ƙalla ashirin kafin ya ƙarasa ya zauna bakin gadon har yanzu bacci take ya dubi hannun da ruwa yake shiga ya dubi ɗaya hannun da jini ke shiga a hankali ya kama hannun drip ɗin da yake ɗan mitsi-mitsi ya riƙe cikin nasa a hankali yake murza yatsunta can ya ji ta riƙe hannunsa ya ɗaga kai yaga tana jujjuya kanta sai a lokacin ya lura da sauyin ƙarar da na'urar ke yi. Safiyyerh tana buɗe idanu ta rufe saboda wani fau ɗin haske daya shige mata ciki sai kuma hawaye ya fara bin idanunta ya ɗan sunkuya yana kallon fuskarta. Ta sake buɗe ido ta kalle shi ta dudduba taga ba kowa ta rufe idon still ta buɗe har lokacin jujjuya kanta take yi "Yaya" ya yi mata shiru ya sake cewa "Me na yi musu?" Still shiru ya yi mata ta buɗe idanu ta kalle sai ta fashe da kuka sosai ƙirjinta na ɗagawa ya damƙe hannunta "Yaya" "Safii..." Ya kira sunanta a hankali ta ce "Kai na zai cire ƙirjina ciwo cikina ciwo yaya mutuwa zan yi" "Allah Ya yi miki Rahma" sai kuma ya matsa dab da kan nata ta saka hannu ta riƙe nashi ta yi shiru a hankali ta sake cewa "Captain" "Manager" "Na ce musu mijina soja ne, wai ko sojan zasu kashe balle ni" ta yi shiru ta sake cewa "Ka riƙe mini kai na ciwo yake mini sosai na shiga uku daddy wayyo" maimakon ya riƙe kan nata sai ya ɗora goshinsa saman nata, ta buɗe idanu ta kalli fuskar Captain kamar zau haɗe da data a nutse ya ce "sun kashe kin?" Ta girgiza kai "Me ya sa?" "Ban sani ba" ya ɗan murza mata goshinsa yana kallon cikin idanunta ya ce "Saboda ke matar soja ce" ta yi shiru kawai tana kallon shi can ya matsa yana sauka ya zauna saman kujera. Washegari da sassafe ƴan sanda suka shigo room ɗin lokacin tana zaune ta ɗan jingina da jikin gado, statement na abin da ya faru suke tambaya. Sp Ghali ya kalli Safiyyerh data sunkuyar da kanta ƙasa ya ce "Da suka zo sun faɗa miki abin da suke buƙata?" Ta girgiza musu kai. "Za ki iya gane wani daga cikin su? Suna ko kammani?" Ta ɗago ta kalli Sp Ghali dake tsaye ta ce "Idan na gane kamannin sai me za'a yi to?" "Zamu kira a zana mana fuskar wanda kika gane ne" "To ban gane ba" Duk suka tsora mata idanu musamman daddy ta buɗe idanunta itama ta ce "Kamarya? To na gane ne?" Daddy ya ce "Maama wa kija ji ya ce wani abu?" Sp Ghali ya dinga kallon Safiyyerh yana jin wani irin abu a ransa na motsa masa sai ya yi murmushi ya ce "dear kin ce basu nemi komai ba, ba wanda kika gane ba suna amma haka kawai sai su caka miki wuƙa think Safiyyerh" sarai Safiyyerh ta tuna sunan da ta ji ya ambata na Mutallab sai ta yi shiru a hankali kuma ta ce "Sp kasan matsalar da ƙasar nan take ciki musamman Jiharmu akan ƙwacan waya, wayata zasu ƙwace ni kuma na hana saboda ina da abubuwa a ciki shine sukai mini haka" ya jinjina kai ya ce "Haka ne dear za mu yi bincike zan gano kowaye za mu hukunta shi ƙarƙashin hukuma bisa kundin da aka wanzar, get well soon dear" ya sake faɗa yana murmushi kan ta dai a ƙasa yake. Sallama sukai dasu daddy suka tafi. Captain na zaune ko tari bai yi ba wayarsa kawai yake dannawa can ya miƙe ya fita daddy ya bisa da kallo haka Yaya J ganin ko sannu bai yi Fiyya ba daman bai jima da zuwa ba. Eng Ali wali ya dinga kaiwa yana kawowa ransa duka a ɓace ya kalli Mai dawa ya ce "Yanzu daka kashe ta fa? Wai me kake nufi da wannan abin da ka yi ne Mutallab?" "Ka dai na yi mini ihu kamar Malam Abdullahi" Ali wali ya jinjina kai kawai ya ce "Kasan ka raina ya ɓaci kake cewa haka? Ya zan aike ka ka yi sato yarinya kuma ka caka mata wuƙa salon ka ɓata mini aiki da sanyin safe ake kama fara ba mai dawa" "To na fasa" Ali wali ya buɗe idanu ya ce "Meka fasa ɗin? Ba dai ɗakko yarinyar ba kake nufi?" A taƙaice ya ce "Shi" "Haba uban mafarauta, kai baka san wasa ba kai kamar ɗa kake a wajena fa" sai a lokacin Moh ya buɗe idanu ya kalli Ali wali yanzu dai normal yake ba'a buge ba "baka haifan ba, san da aka haifan baka da labari" ya yi fito yana miƙar da ƙafa ya ce "To ka kira ɗan naka ya yi maka aikin, mu fa kuke sawa a wahala har a yi zaɓe aci a cinye ka hau kujerar ba lallai yaranka suna ƙasar ba, ba'a rainawa Moh hankali ka bar mu matsayin ƴan daban kawai" Ali wali ya ce "Ya batun yarinyar?" "Na ji" ya ce yana miƙewa tsaye har zai shige ya dawo ya ɗauki bandir ɗin kuɗi ƴan dubu-dubu ya watsa cikin aljihu. Sautin daya ji kamar gurnani kamar kuka kuma ya sa ya nufi ƙofar da yaje jin hakan ya murɗa handle zai buɗe cikin sauri Eng Ali wali ya riga shi ya ce "Haba Mutallab idan iyalina ne a ciki fa?" Moh ya zubawa Ali wali ido ya kalli ƙofar sai kawai ya fice yabar wajan. "Ɗan wahalar yaro ɗan jaraba Allah Ya nufa na lashe kujerar ganina sai ya yi maka wahala" Hon Maɗatai yana zaune ya kalli Sp Ghali ya ce "Ka lemo record ɗin nasa?" "Na samu Hon amma cin dai amana ne irin namu na jami'an tsaro amma fidda record ɗin wani criminal ya saɓawa kudin tsarin ƙasa" Hon Maɗatai ya ce "Waye Mutallab?" Sp Ghali ya ce "Nothing serious about him hon, shekaru uku da suka shige an kama shi da laifin kashe matarsa ranar da aka kai masa ita matsayin amarya, kafin nan yana da record na zama gidan yari na watanni sai kuma taɓa guduwa Legas, a baya kuma kafin hakan shi mafarauci ne ma'abocin shiga jeji ya yi farauta" "Hon akwai matsala ne? Na ga ka yi shiru?" "Batun Scorpion ba, case ɗin yarinyar nan Manager a ranar ance shima Scorpion ya je wajan" Sp Ghali ya ce "Hon Scorpion da ƴan siyasa irin ku yake da matsala fa, ko mutumin daya kashe last yana da za hujjar kisan mune dai bamu sani ba, waye Scorpion ba wanda ya sani jami'an mu na neman shi haka F.i.d Federal investigation department wallahi suna kama shi wannan kisa ne nan take ko su yi masa allurar hauka" "Al'amarin Scorpion ya yi kama da ɗaukan fansa fa, za mu zuba ido ya kashe mu ne? Ku hanzarta nemo ko waye Sp Ghali" "In sha Allah Hon" Aliyu na zaune saman kujera daddy ya ce "Kaji ai ko?" Ya jinjina kai kawai "Zuwa dare sai ka ɗauke ta ku tafi can part ɗin dake gidan daman tuni an zuba komai empty dai yake to ɗazo an kaiwa Safiyyerh kayanta, Aliyu Safiyyerh amana ce idan ka ci amana ba zan yafe maka ba, na yi haƙuri na rabu da kai amma na so kun bar ƙasar gabaɗaya" addu'a daddy ya yi musu sosai duk da Fiyya bata wajan. Aliyu ya tashi ya fita. A daren ranar ƴan jarida suka shigo saboda hirar da za su da daddy. Sosai aka yi hirar inda yake cewa. "har kullum ni Professor Abdu Marafa bana goyan mutumin da bashi da wata nagarta wanda baya duba rayuwar yaranmu matsa wanda kuma zuwa gaba sune zasu gaje mu, duk wanda ya buƙaci ku zaɓe shi ku fara duba nagartar shi waye shi, bane background na rayuwarsa waye shi tun farko? kar a yi amfani da talauci da rashin iliminku a saka ku yi zaɓan tumun dare a wannan lokacin matasa yana da kyau ku yi gangami ku magana da murya ku saka iyaye na gida ƙanne da yan'uwa su zaɓi cancanta, wannan masu gamu taliya gishiri ko masu siyan ƙuri'ar mu basu ne wanda suka dace ba, ƙuri'armu ita ce ƴa'cinmu kana siyarwa baka da damar yin zaɓe ku kalli yadda ake mayar da ƙananan yaran ƴan daba masu bangar siyasa ana basu ƙwaya suna aikata zunubi suna kai kansu inda za'a kashe su, ku faɗa mini ko sau kun taɓa ganin ɗan wani daga cikin ƴan takarkarun nan? no! Sai yaran talakawa wanda basu da ilimi ko basu da sana'a sai a yi amfani da wannan damar a janyo su a kurɓata musu rayuwa a ƙarshe kuma ko gidan yari yaro ya tafi wallahi sai dai iyayensa su yi fafutuka duk da cewa har da laifin wasu iyayen a lalacewar yaran, matasa ku haɗa ƙungiya da za ku dinga taimakon juna kar ku yadda da mulkin kama karya kuna kallon shekaru huɗu da suka shige yadda zaɓe ya kasance" "Professor Abdu Marafa kenan a yayin da yake bawa matasa shawara akan su miƙe tsaye domin ƙwatuwa jiha ƴan'cinta. Professor mai ya sa duk maganar da zaka yi akan matasa ne? Da batun shaye-shaye ko daba?" Daddy ya rantse idanunsa yana jin zuciyarsa na yi masa zafi can ya ce "Ɗan jarida kenan baki abin magana, saboda matasa sune yau, sune gobe haka jibi matasa sune cigaban ƙasan idan har aka tsaya musu aka fitar da iri mai kyau, shaye-shaye kuma....," sai kawai ya yi shiru. Yakasai ya ce "Gabaɗaya abin da zamu iya naɗa kenan a wannan satin, zamu cigaba da bibiyar professor Abdu Marafa domin ganin haƙar tasa zata cimma ruwa ko yaya ne? Ni Khalid A Yakasai nake cewa a huta lafiya" **** Numfashi Mutallab ke fitarwa a hankali jikinsa duk yanka saboda faɗan da suka yi da ƴan cikin gari bai san adadin mutanen daya sara ya fitarwa da jini ba, bashi da tabbacin ko bai yi kisa bama rabin fuskarsa duk yanka ne wani wajan har ya zame masa tabo. Goje shima cikinsa rauni ne da ƙyar yake fidda numfashi a hankali ya ce "Sun kashe Darma fa, ni ban ɗauka haka zuwa kamfel ɗin yake ba, wallahi sun kashe Darma na yi ƙoƙarin kai masa ɗauki amma ta kai nake" "Goje" "Na'am, Sarki" "Nemi maɓoya" ya ce "Idan na ɓoye kai fa? Naga ba zaka iya tashi ba gwara ni ma kai ma da tuni sun kai ka kushewa, gashi wannan ɗan jakar Mangal ban san inda yake ba, balle a jira Ali wali a faɗa masa koda taimakon da zai mana" "Wai baka jina idan ba ƙiyama kake shirin zuwa ba ka tashi ka face Goje" da sauri Goje ya miƙe ya yi kwana saboda ƙarar motar kwalawa da ya ji, Moh ya saka hannunsa a aljihu ya danna laya tuni ya ɓace a wajan. Abbasa ta dinga kallon Mutallab kamar baya numfashi ta girgiza kawai ta kalli mai yi masa treatment ɗin bayan ya gama ya miƙe ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai ya fice kawai. Ta yi shiru tana sake kallon Ɗan'malam. Kamar yadda daddy ya buƙata Safiyyerh ta tare cikin part guda da yake gidan daga can baya, ita dai da to kawai take binsa sai kuma idanu ta yarda ba zai zaɓa mata abin da bai dace da rayuwarta ba, ta amince zata zauna da Captain Aliyu zata koyi son shi. Cikin sauri yake gudanar da komai kamar mai tsoran wani abu. A harabar gidan Aliyu na tsaye yana kallon Awais da yake cewa "Yaya ban gane tambayar da kake mini ba" "Ya sunanka ma?" Da mamaki Awais ya ce "Ikon Allah Yaya ni fa ƙaninka ne tsayin shekaru baka san sunana ba?" Aliyu ya haɗe fuska ba wasa ya ce "Kuma dole akai na haddace, seriously bana iya tunawa" "To kai ne Baba captain Aliyu sai Junaid sai Dr Hash sai ni Awais sai Maama" "Ok, shi likitan wanne allura ya ke yi mata ban damu na san ba a baya yanzu ina so" "Wai Dr Hash da ya kewa Fiyya? Ban sani ba gaskiya Yaya why not ka tambaye shi?" Wata tsawa ya dakawa Awais yana cewa "Get lost mumu" fita ya yi daga cikin gidan gabaɗaya. Har ɗaya saura Safiyyerh na kwance a bedroom ta yi shiru tana jin ciwon na yi mata zafi ta yi kuka sosai na rashin sanin dalili har bacci ya ɗauke ta. Cikin bacci ta ji an buɗe ƙofar an shigo ta yi saurin rufe idanu yana sanye da kayan bacci farare ya ƙarasu ya duba magungunan yaga ko ɗaya bata sha ba, ya ƙarasa bakin gadon ya zauna shi gabadaya ya manta cikakken sunanta na gaskiya rashin sanin ne zai ce kawai ya saka hannu ya janyo ƙafafuwanta zuwa ƙasa ta matso dab da shi da sauri ta buɗe idanu, suna haɗa idanu ta tura baki tana juya fuska "Zan saka bindiga na harbe ki a iska kina juyawa" ta kalle shi ta ce "To yaya ciwona ka fama mini" kallon da yake mata ya saka ta miƙe zaune "kin accepting auren?" Ta jinjina kai ta ce "Na yi kamar yadda ka yi na san daddy yana da nasa dalilin damuwata ɗaya na rashin sanin gaskiyar ni ce ƴar daddy ko kai, amma aure tun kafin na zo duniya Allah Ya rubuta wanda zai zamo miji gare ni ina da sani daidai gwargwado zan zauna ƙarƙashinka duk da baka so na, ko kana so na?" Ya girgiza mata kai alamar "A'a" "Ni ma,sai mu koyi son juna" ya kalleta kawai sai ya ce "Muga ciwon" "Yaya a wajan ƙirjina ciwon yake fa" da rashin fahimta ya kalli ƙirjin ya kalleta kuma ya nisa ya ce "Kuma mene a ƙirjin?" Ya faɗa yana yaye rigar. WE'LL SOON END OF THE FREE PAGES. Ku hanzarta biyan 500 domin karanta Mutallab posting za mu babu ɓata lokacin ba lallai ku fahimta a yanzu wanda suka shiga paid group sune da batu ko rabin book 1 babu shiga ba. Tsakiyar labarin akwai muke, mene ya faru a farko me zai faru tsakiya ba zaku taɓa sani ba ko a sashe. MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 [10/21, 2:10 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 12 *Bright pens..2nd batch* Hannunsa ta cire da sauri ta ce "ciwon fa a wajan ƙirjin yake yaya" da mamaki Captain ya kalleta ya kalli ƙirjin, da gaske bai san mene matsalarta da hakan ba. Ya ɗauki lokaci kafin ya ce "kuma mene special a ƙirjin?" "Baka sani ba?" Fiyya ta buƙaci jin amsa ganin har lokacin kallon ta yake da alama processing ƙwaƙwalwarsa take yi shi dai ya san wajan da aka caka mata wuƙar kawai zai gani. Bai sake cewa komai ya miƙe tsaye ya nufi fita, Fiyya ta bisa da idanu tana jinjina rainin wayon Captain yana abu kamar baya fahimta. Ta yi shiru bayan fitar tasa, ta ɗan jingina da jikin gadon thinking me ya sa abubuwa suke juyawa tare da faruwa ne? Ba wani tsanar Captain ne a zuciyarta sosai ba, kawai yadda yake abubuwansa ke ƙular da ita amma kaf yayyanta tana matuƙar so da ƙaunar su. Damuwar bai shige dalilin daddy na aura mata Captain ba, bayan shi blood brother ɗinta ne. Yanzu ita ce ba jinin daddy ba ko Aliyu? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Da sauri ta riƙe ƙirjinta jin zuciyarta na harbawa, duk yadda take ƙoƙarin ko a cikin bacci ta sake ganin gilmar reflection ɗin shi ta gagara, ko sautin muryar tasa ma ta mata sai kuma tunanin mahaukacin daya caka mata wuƙa ya faɗo cikin ranta wai shi Mutallab? Who is he? "Who is he?" Muryarta ta sauka a tsakar kanta tana nanata mata tambayar da zuciyarta ta yi mata a fili. "To ya ɗauke ni ya yi mini me? Safiyyerh Abdu Marafa ai ba sa'ar yara bace, bata zama teddy ba, the whole manager anya ya san me yake ce mini? Ba sai ya sake ganin ko inuwar fiyya ba balle ya aiwatar da abin da ya yi niyya a kaina, aikin banza aikin wofi don ma dai ban san ya zaro wuƙar bane zuwa gaba Captain zan lallaɓa ya ara mini bindigarsa problem solved" Ita kaɗai take ta yin mita ta zubawa madubi idanu bayan ta miƙe tsaye. Wanka ta yi tare da alwala bayan ta idar da sallah ta ɗauki skin products mai kyau dake sa fatarta laushi ta yi ta ƙyalli, tana son amfani da kayan Aisha s bayero skin care nd herbal medice, ta ɗauki riga mara nauyi saboda ciwon jikin nata. Kasa bacci ta yi ta ɗauki system ɗinta ta fara dannawa hannunta riƙe da ruwan zafi ta jima suna tattaunawa da Md da Secretary ta email kafin ta rufe system ta yi addu'ar bacci ta kwanta sai dai ciwon ya dameta da zafi har zazzaɓi ya saka ta. Washegari da ƙyar ta yi sallar asuba don bata yarda ta shige ta, ta rufe jikinta da duvet ta girgiza kai da ƙyar baccin ya sake ɗauke ta. Har 12 bata fito ba, sanin abin da ya faru da ita ya saka ba'a nemi ba'asin rashin zuwan nata kamfani ba. Wajejen ƙarfe biyu ta buɗe idanunta dalilin ƙamshin da ta ji da kuma goshinta da ake murzawa a hankali, ta juya ta kalle shi taga waya ya ke yi muryarsa ƙasa tana jin yadda yake magana one by one jin ana kallon shi cikin sauri ya ce "i will call you later" Ya juya suka haɗa ido a hankali ta ce "Ina yini?" Ya yi mata shiru yana kallon kanta da sauri itama ta kalla sai yanzu ta lura kan nata yana cinyarsa ne shi kuma hannunsa na gefen fuskarta "ɗaga ni" "Yaya bani lafiya fa" ya harareta kawai ya yi shiru shima ya ji zazzaɓin ta juya masa baya tana sauke kanta idanunta rufe zafin zazzaɓin na ƙaruwa ji tayi ya ɗago ta zaune kamar wacce zai zaunar a cinyarsa ya faki idanunta ya damƙe gefen cikinta ta yi ƙara tana riƙe shi "Ki dai na yi mini sauti haka, za ki je zaman barrack lazy" ta haɗe fuska tana ji yana taɓa cikinta yaga wajan ciwon na jini ya saka hannu ya shafi ciwon ya taɓo jinin da hannu can ya miƙe yana juyawa. "Captain jini wajan yake yi ka fama mini na shiga uku" idan ba kuskuren ji ta yi ba, muryarsa ta ji ya furta "Allah Ya ƙara" Cikin dare ne yana tsaye ya fito daga cikin motarsa sanye da manyan kaya na alfarma da fuskarsa rufe da facemask ya dubi yaran da suke gabansa ya ce "Ina buƙatar aiki cikin gaggawa bana son wani mistake idan aka samu akasi ina cikin taraddi, kuna kallo abu ya taho lokacin na neman cimmana" Ya buɗe idanu yana sake dudduba inda yake tsaye gani yake kamar ana ganinsa za kuma a iya gane wanene shi. "Mai gida wanne kalar aiki ne ya fito da kai cikin duhuwar nan, faɗa taka cikawa tamu sai da kai iya wuya ba wani shege a baya wallahi" ya ɗan yi murmushin jin daɗi yana kallon mai maganar da kana ganin shi zaka san a buge yake cikin maye kamar kullum "Idanun mutane nake so, maza uku mata uku" ya ce yana kallon wanda yake faɗawa maganar ganin yadda ya yi shiru kamar dai ban fahimta ba. "Aiki ja idanun bama na mutum ɗaya ba? Akwai kuskure fa" "Yanzu akwai wani aiki da zan iya sakawa ka yi mini da zai fi ƙarfinka? Kai ɗin amintacce nane na kuma yarda da ƙwarewarka ina jin daɗin business da kai wallahi" ya zaro kuɗi masu yawan gaske ya miƙa masa, ya sake zaro wata ƙwaya kala daban-daban masu kyan gaske da tsada kana gani kasan manya ne ke shan irin ta. "Ka fara riƙe wannan kuɗin nasan kana buƙatar caji a kanka kafi yin aiki yadda ya kamata, idan ka kammala ka sanar mini zan faɗa maka inda zaka ajjiye ko?". "Ka yi ƙarko irin na dabino sai da kai wallahi yau zam dani, ko kan mutum ka ce na kawo maka a yadda ƙwayar nan ke buɗe mini tunani kawowa zan, ba ƙaramin ilimi ne dani ba da tuni fa ni zan yi ministan kuɗi nace na fasa, kaf ƙasar waye bai sanni ba don uwar mutum" sambatu kawai yake na maye ya bugu ƙarshen buguwa, shi mutumin dariya kawai yake basa hakan kuma na yi masa daɗi ainun. Mota ya shiga ya bar wajan shi kuma ya gangara ya shiga lungun titin da suke. Tunda ya tafi ya zauna cikin yan'uwansa mashaya yake tunanin ta ina zai fara? Ina zai samu mutane har ya ƙwaƙwule idanunsu hankali kwance? Ya yi shiru yana kallon sama yana ta furzar da iska mai ɗauke da warin sholi dana bakin gabaɗaya. ***** Mutallab ya tanƙwashe ƙafafuwansa kamar wani sarki ya kuma ɗora hannunsa saman cinyarsa cikin kowacce ƙafa, kallon Abbasa yake tun ɗazo take magana yaƙi cewa komai ko tari kuma bai yi ba, raunukan jikinsa ya kame sai saura, ido biyu za ka yi da shi ba zaka ƙara marmarin kallon nasa ba, babu rahama a fuskarsa nan zaka ɗauka tunda Ammo ta kawo shi duniya bai taɓa yin murmushi ba, ko haɗa hanya da inda fara'a take. "Kalli nan" Ya dubi abin da take nuna masa, zanen kamfanin ne da photon jariran sai kuma kalmar A.M.A "Da fari mu fara gano ma'anar kalmar A.M.A, photon jariran kuma mai sauƙi ne ana nuna maka har jarirai da aka haifa yau ana siyar da shi a kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, abu biyu ne wanda dole za ka yi ko kusan ukun, da fari sato ita wannan yarinyar ta yiwu a samu wani haske tattare da ita, na biyu kasan yadda duk ka yi ka mallake wannan kamfanin cikin sauƙi, na uku....," sai kuma ta yi shiru ta dinga kallon Moh ciki da bai "Waye Mutallab, waye kai, dole ka faɗa mini asalin waye kai kana ji na?" "To na haƙura" Ya miƙe tsaye a hankali a lokacin ras yake sai abubuwan da sukai masa tsaye a zuciya da maƙoshi "Dole na san waye kai, ko ka faɗa mini ko ba ka faɗa ba, abu na uku sai ranar da asalin naka ya zo kunnuwana zan furta maka shi" bai dai yi magana ba, hannunsa zube cikin alijun kayan da Abbasa ta basa ya sauya da ƙyar yafi ƙarfin minti ashirin a tsayen yana harhaɗa kalmomin abin da zai ce mata ransa duk a jagole. "Lalacewar Moh bai kai ya sato yarinya ba" "Kuma dole a yi hakan fa" Ya yi waje abinsa yana yana ƙoƙarin ficewa daga cikin bukkar ta ce "Baka da lokaci fa Mutallab, kuma baka da ikon taɓa ta a waje idan ba kana shirin komawa gidan yari bane, kasan yadda za ka yi dai wish you all the Mutallab" Bai ƙara bi ta kanta ba, ya dinga ɗora ƙafafuwansa a ƙasa kamar mai tsoron taka ƙasa sai haɗe fuska yake yana kwaɓewa duniyar ya ji ta yi maza zafi ta ko'ina, ya rasa ina zai je me kuma zai yi sai ɗaga yatsun ƙafarsa yake wanda suke zara-zara matar nan Abbasa ta fara takura masa ko waye ya ce ta yi masa gyaran farce? Yama a ka yi ta samu mai yin aski ya wani kwashe masa suma? Bakin bishiya ya samu ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa, zufa ta shiga tsattsafo masa ta tsakiyar goshi ya sa yatsa ɗaya yana gogewa ya shafa jikinsa ba kayan garawa ko ɗaya yana buƙatar fita daga yanayin da yake ciki, baya son tunawa ko da wasa. _“One day i will leave you, duk son nan da nake maka”_ Ya ji saukar muryarta a kansa ta sauka har ƙasan zuciyarsa a ɗan lumshe idanunsa da ya yi, ya juya zuwa gefe sai yake ganin bidiyon abin da ya faru bayan kammala assembly, at that time yana can baya zaune ya yi shiru yana kallon students bai san da zuwanta ba sai ganinta ya yi ta baya kamar zata shige jikinsa ya fiddo manyan idanunsa waje yana miƙewa tsaye hannunsa ɗaya zube a aljihu ya dinga kallon ta da ƙyar ya furta "And what is this Safiyyerh?" "Bestie shi ake cewa love mana" ta langwaɓar da kai gefe yana sake kallon yaluwar fuskarta kamar zabiya. "To iskanci za ki mini?" "Iskanci kuma bestie? Me ya sa kake haka ne, son ka kawai nake yi fa why are you doing this to me? Kai ba'a gane maka sam? Ko murmushin masoya ne ka dinga yi mini mana, bafa ni na ɗorawa kai na son ka ba" idanunta ya cika da waye tana jin zuciyarta na yi mata zafi bata ganin komai a idanunta sai fuskar Mutallab. "A love? Shine za a yi wa mutum fyaɗe a soyayyar??" Ta buɗe idanu tana rufe baki jikinta har rawa yake tana jin kamar ta idda abin da zuriyarta ke umartar ta "To ka yi haƙuri idan dai na mutu ka huta, kuma idan baka zo gidanmu yau ba Allah a wajan Ammo zan kwana" fuskar nan a ɗaure ya ja sirirn tsaki ya shige cikin class kafin ya ƙarasa ya ƙara jiyo ta a bayansa tana sake yunƙurin riƙe shi da sauri ta juya sai kuma ta ɗauki school bag ɗinta ta fice daga makarantar tana kuka. *** "i missed the hug" ya furta ƙasan zuciyarsa lokacin da bidiyon abin ya ɗauke daga kusa da shi, ya yi shiru yana tunani har yamma ta yi lis bashi da niyyar tashi daga wajan baya son shiga cikin jama'a yana jin nan ɗin shine daidai da ina ya kamata ya ɓoyewa kwalawa. He feels uncomfortable a cikin jama'a haka nan. Safiyyerh na zaune bayan ta dawo daga kamfani ko ɗaki bata shiga ba idan ta tuna yadda Hon Maɗatai ya sake matsa mata akan hannun jarin da yake son sawa a FS WORLD INVESTMENT COMPANY sai ranta ya sake ɓaci, duk dukiyar da Ubangiji Ya bashi bai gode Allah ba, mutane nawa ne a wannan duniyar da basa ci, idan anci na safe ana fargabar na rana, idan na rana ya samu dare kuma sai dai a yi salatin Annabi a sha ruwa a kwanta, masifar rayuwa ta yi wa talaka dirar mikiya, yunwa na neman illata su ga lalura ga rashin aikin yi? Amma hon Maɗatai shi dukiya yake nema idanu rufe ƴan siyasa da yawa kansu kawai suka sani suke ginawa, mene amfanin talaka ya je ya yi zaɓen? Gabaɗaya sabgogin dimokuraɗiyya ya lalace son zuciya kowa yake bi. Ta yi tsaki tana jin ko zata rasa kujerar Manager ɗin ba zata taɓa bari Hon Maɗatai ya saka hannu a kamfanin ba. Miƙewa ta yi ta nufi bedroom bata ɗauki wani lokaci ba ta fito sanye da wando da riga,wandon iya cinya kanta ko ɗan kwali babu da mamaki take kallon Captain ganin ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna mata system ga wayarta a hannunsa kafin ta ƙarasu ya kashe system ɗin ya ajjiye har wayar. "Yaya me kake nema a system ɗita kuma?" Ya yi mata shiru ta zauna kawai tana buɗewa bata sake kallon shi ba, ta shiga duba dukkan ayyukan da aka fitar yau da sauri ta kira accouter da number da take amfani da shi na kamfanin tana girgiza ƙafa a hankali cikin faɗa ta ce "Accouter me nake gani a haka? Kuɗi fa kimanin miliyan 500m yanzu sun shigo account na kamfani dana gani a bayanai, bayan tafiyata me aka fitar ne shinkafa ko me?" Faɗa take sosai domin ta iya faɗa ajin ƙarshe ce a fannin. "Manager nifa kina tunawa accouter ne kawai, bani ke da alhakin saka hannu a fitar kaya ko shigowar su ba, kawai ni ke saka hannu a duk wani kuɗi da zai shigo ya fita, i am nothing but a Accounter" Miƙewa tsaye ta yi tana riƙe ƙugu ta ce "Rubbish; ka tura mini ducoment na PDF via email na abin da aka siya har miliyan 500m yanzu yanzu accouter" "Ki yi magana da Md ni kawai kuɗin naga shigowar su babu wani file daya zo officer nawa, trust me manager ba zan ɓoye miki, na san dai bayan tafiyarki Professor Abdu Marafa ya shigo kamfanin" "daddy!" Ta furta da ƙarfi "E, mahaifinki shi" "Kamarya to?" "Shine ban sani ba" sai kawai ta kashe wayar ta ajjiye waje guda, ta sauke numfashi da ƙyar ta shiga uku meke shirin faruwa ya ake ƙoƙarin amfani da ita ba tare data sani ba?" "Yaya" bai amsa ba idanunsa a ƙafarta ta ce "Yaya bacci nake ji" "to ina ruwana" Sai kawai yaga ta ɗora kanta a cinyarsa maimakon ta juya masa baya sai ta juyo wajan cikinsa ta yi shiru tana kallon ƙirjinsa dake buɗe. Ta yi shiru tana sauke numfashi shi dai bai yi magana ba, bai ɗauka haka take da masifa ba yana jin ƙirjinta na ɗagawa a hankali kuma bacci ya ɗauke ta. Cikin baccin ta ji hucin numfashi ta buɗe idanu kallonsa ta dinga yi yadda ya kifa fuskarsa a tata hannunsa ɗaya tamƙe cikin nata "Captain" da sauri ya buɗe idanun ya ƙurawa cikin idanunta ido sai kuma ya ɗauke fuska yana haɗe rai. Fiyya bata ce komai ba ta miƙe zaune shi kuma ya shige cikin part ɗinsa yana taku da sauri sai shafa kai yake yi. Notification ta gani kamar wancan lokacin saƙo ne ta dm nata. Ta buɗe ba wani magana mai tsayi bane sai dai maganar dab take da rusa tunaninta ta bi saƙon da kallo inda ake cewa. _“bai ci a ce kin yi mantuwa mai nisan haka ba, ki tuna akwai hakƙin wani kan ki Allah Yana kallon ki TIGER“_ ta dafe kan ta to hakƙin waye a kanta waye mai wannan saƙon kuma? Tsaki ta yi ta miƙe ta bar parlon. Bata sake ganin Captain ba har dare ta yi kwanciyarta. **** Cikin sauri take tafiya tana yi tana juyawa sauri take ta isa chemist amsar maganin ga dare ya raba mijin nata ya fita. Kamar daga sama taga mutane sun tsaya gabanta fuska rufe "Su waye ku? Don Allah ku rufa mini asiri magani zan siyo" muryarta na rawa ta yi maganar. Haɗa idanu sukai sai suka ɗaga ta sama tare da danna ta cikin napep ɗin basu tsaya ko'ina ba sai wani kango a nan taga wasu mutanen kwance kamar basu da rai, kuka take tana duk addu'ar data zo bakinta "Don Allah kar ku cutar dani don Allah ku rufa mini asiri da yarana da rayuwarsu" Tana ji tana gani suka danneta tun tana ihu har ta kasa jini kamar an yanka rago babu imani suka cire ƙwayar idanunta duk biyun tare da watsa su cikin aliju da gudu suka fice daga kangon. Bayan ta dawo daga wajan aiki ta shige gidan Anty Turai saboda kiran da ta yi mata, a parlo ta samu Anty Turai da yaranta da kuma wasu ƴan mata zaune. "Ina yini Anty?" "Sannu matar Captain Aliyu Marafa?" Cewar Anty Turai ita dai Safiyyerh idanunta akan waya bata ce komai ba Waheeda ta ce "Mama wai shi Uncle captain ɗin son ta yake yi ne? Ni banga abin so a jikin wannan zabiyar ba sam sam wallahi" Zahiderh ta yi saurin cewa "Ina fa? Captain ne zai ce yana son Fiyya never wallahi, kawai dai auren dole aka yi masa, wannan fari ko na lalura" Safiyyerh dai jinsu take Anty Turai ta ce "Sannu Safiyyerh, ya kamfanin yanzu ai Aliyun ya bar nan wajan Zahiderh ya zo ki dinga haƙuri da shi ya jaddada mini baya buƙatar ki cikin rayuwarsa bai san me zai yi da zabiya ba" miƙewa Safiyyerh ta yi ta ce "To Anty a ɗaura masa aure da Zahiderh ni bani da wata matsala, zabiya kuma ina jira ku halitto irin kalar idan da sauƙi, so kuma ba abin da ya yi mini zafi da shi zan zauna da mijina haka tunda zaɓin daddy ne, wallahi babu wanda ya kai level ɗin ɗagawa Fiyya hankali" Anty Turai ta miƙe tana nuna Fiyya idanunta ya rufe sam bata kula da shigowar shi ba, balle ankarar da ita da su Waheeda suke ta ɗaga hannu zata mari Fiyya dake tsaye tana juya idanunta ta ji an riƙe hannun. Tun zuwan shi ta ji ƙamshin turaren nasa, ya tsaya a bayanta Anty Turai ta kalli Aliyu ta kasa cewa komai ya saki hannunta yana matsawa bayan Fiyya ya zagaye hannunsa a ƙugunta ya jata jikinsa daga baya yana sake kallon Anty Turai "Shekararki nawa Anty yaushe na zo gidan naki kuma? And who told you bana son ta?" Duk a dagule yake maganar yana sake haɗe Fiyya da ƙirjinsa kasancewarta duguwa sosai so ma sha Allah. "Aliyu ni zaka shigo gida ka faɗawa haka?" Bai kalleta ba sai Fiyya daya kalla wacce take shirin juyawa idanunta cike da hawaye ya yi saurin riƙo hannunta yana "Wait" sai kawai ta kifa kanta a ƙirjinsa tana shassheƙar kukan da bata shirya saboda ganin idanunsa "Anty karki sake mini haka" "Idan na sake me za ka yi Aliyu na ce me za ka yi?" Ya girgiza kai ya rungume Fiyya tsam a jikinsa ya ce "Ban san me zan iya yi ba, kawai dai na faɗa miki, kuma i love my wife" Fiyya ta yi saurin ɗago kai ta kalle shi ya ɗage mata gira "Yes, I Iove You Safii" yana cewa haka ya kama hannunta suka fice. *** Suna zaune a dabarsu ya yi sauri ya miƙe tsaye Goje ya ce "Sai godiya, ina aka nufa don shirwa kake baka jewar banza, ɓauna mai tafiyar ɗaukan rai jeji naka dabbobi naka, a lafiya mai dawa" jikinsa ya ji ya fara kakkarwa tsohon tsuminsa na neman tashi ya yi ƙasa da kansa yana ƙoƙarin hana kansa yin kirari da amsar saƙon Goje, ya bar wannan layin tuni. Da ƙyar yana girgiza kai ya ce "Goje" "Sai godiya, wuya a ina wuya a daji kai ne mai dawa da jeji na Malam Abdu shalelen Ammo, ƙanin Sa'adah da Bafullatana a lafiya aminin Hamida, ɓauna taka mesa taka ba wani bayanka jan biro maganin daƙiƙin yaro Allah Ya ja da ran mai dawa" gabaɗaya jikin Mai dawa ɓari yake yana damƙe hannunsa wajan ganin mai ɗaga su sama ba har can cikin kansa yake jin kirarin. Kawai ya juya ya bar wajan "Wai ina zaka ne kasan yanayin da ake ciki fa akwai cinnaku" "Baka haifan ba balle ka tambayan karka biyo ni" yana cewa haka ya bar wajan ya jima yana tafiya kafin ya ƙarasu gidan sai ya saka maƙulli ya buɗe ya shiga. A ɓangaren su Safiyyerh tunda suka bar gidan Anty Turai suka shiga mota basu ce komai ba ya kuma haɗe fuska itama bata ce komai ba, daidai wani gida a bakin titi taga ya tsaya ya kalle ta "Kar ki fito jira ni nan" ta jinjina masa kai. Fita ya yi ta jingina tana ɗaukan waya, abin da ta fara cin karo da shi a X picture ɗin wani kyakkyawan yaro yana murmushi ya rufe idanunsa saboda hasken da ya yi masa yawa kamar ka taɓa shi jini ya fito, ta dinga kallon picture ɗin sai kawai ta yi skipping zuwa next tweet. A hankali ya buɗe ƙofar ya shiga idanunsa zube a saman tafkeken screen ɗin computer dake jikin bango, gabaɗaya wajan nau'in kayan computer ne kala-kala. Ya ɗan dafa kafaɗar wanda yake zaune akan kujera yana juyawa a hankali, kallo ɗaya zaka yi masa kasan mayen computer ne masanin hakin da duk wani surƙulle. Captain ya ce "Where are you hiding?" Ya ɗaga idanunsa a hankali ya kalli Captain bai ce komai ba kuma ya cigaba da danna wayar, Captain ya saka hannu ya dungure masa kai ya nemi waje ya zauna yana taɓa computer shima. Da sauri ya miƙe kuma jin sautin muryarta da yadda take ƙoƙarin buɗe ƙofar ya yi saurin miƙewa ya nufi ƙofar daidai nan Fiyya ta shigo "Yaya gaskiya yunwa nake ji akwai hadari sosai a gari ina tsoron ruwa" "Muje" Ya yi saurin faɗa yana kama hannunta tare da rufe ta da jikinsa leƙawa take son yi ya saka hannu ya juyar da fuskarta ya jata waje, shima ɗin dake zaune ya juyo a nutse ganin sun fita ya saka ya cigaba da abin da yake yi. Cikin dare Fiyya na bacci ta ji ana buga ƙofar parlon kamar za a cire ta, ta miƙe da sauri riga da wando ne jikinta na bacci wandon iya cinya ta saka slipper ta fito, tana mamakin mai ya sa Captain ya kai dare har haka? Ta buɗe ƙofar "Yaya ka tashe ni daga musulmin bacci da nake..." Shiru ta yi tana yin baya ganin shi tsaye a bakin ƙofa su Goje da Mangal a bayansa "Kai ne me ka zo yi mini har gidan mijina, matar aure ce ni fa" banko ƙofar Moh ya yi ya shiga yana ƙarewa parlon kallo "Mai dawa ɗauke ta mu shige kar a yi ta kwanaki" ta gudu Fiyya ta juya zuwa part ɗin Captain tana kirin sunansa a tsora ce kafin ta ƙarasa Moh ya saka ƙafa ya falleta ta faɗi ƙasan tayal idanunsa ya yi jajur domin ba haka ya zo da su ba, jin ana shirin buɗe ƙofar ɗakin Captain Moh ya kalli Goje da sauri Goje ya laɓe a baya kafin Captain ya fito, cikin sauri ya rufe fuskarsa da ƙyalle. "Safii are you ok? Peanut ihun nan fa wife?" Yana fitowa Goje ya saka gora ya maka masa a ka kasancewar Captain bai shirya ba ya faɗi a wajan da sauri kuma Moh ya ce Goje ya ɗauki Fiyya ko me ya tuna sai ya saka hannu ɗaya ya sunkuceta a kafaɗa yana ɗaga wuƙa sama suka fice daga gidan... MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 Zan yi cutting free a shafi na 15 in sha Allah. Wannan shafin 🥰🥰🔥🔥🔥🔥ku hanzarta yin payment kafin wannan lokacin yanzu kuma na labarin a rufe yake zuwa gaba za ku ce kun shiga uku ashe haka abin yake😂😂ina ƙara tuna muku ba fa farkon labarin muke a tsakiya muke waya san mene ya faru a farkon? Me kuma zai faru a gaba? Just pay 500 naira only.[10/23, 5:43 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 13 *Bright pens..2nd batch* Safiyyerh na durƙushe a ɗan ƙaramin ɗakin da suka ajjiye ta ciki, warin sigari ya cika ɗakin sai yunƙurin amai take yi ta kasa, ta shiga tashin hankali da tunanin suwaye waɗannan da suka je har gidan mijinta suka dake shi tare da yin kidnapped ɗinta? Me suke buƙata a wajanta waya saka su yin hakan? Da alama ba kuɗi suke nema ba wani muradi ne a ran su da suke son cikawa manufar da bata san ta mece ce ba. Ta ɗago kanta da ƙyar tana buɗe kumburarrun idanunta saboda kukan da ta yi da hanzari ta fara buga ƙofar da hannunta tana girgizawa tare da faɗin. "Wai baku da imani ne me na yi muku idan kuɗi kuke buƙata ku bani waya na kira daddyna zai biya duk abin da kuka buƙata na fansa ta, macace ni fa a gidan mijina kuka je har gabansa kuka sato ni, don Allah ku buɗe mini wallahi wari zai kashe ni babu iska a ɗakin ku tausaya mini" abin da take faɗa tana dukan ƙofar da hannu, amma ko tari ba ta ji sun yi ba, kuma tana da tabbacin suna jinta ta sake ɗaga murya ta ce "For the sake of Allah, da girman iyayenku ku mayar dani gida gaban iyayena me na yi da za a yi garkuwa dani,ku barni da raina kar ku kashe ni zan muku kwatancen gidanmu ku je wajan daddyna a baku dukkan kuɗin da kuke buƙata, idan ba ku yarda ba ku a cikin kuɗina zan baku wallahi mahaifina ya ji abin da ya same ni mutuwa zai yi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me na yi muku ne kukai garkuwa dani na shiga uku ni Safiyyerh Allah ka kawo mini ɗauki" ta sake durƙushewa a bakin ƙofar ta tura kanta cikin cinyoyinta saboda warin sholi daya gama hautsina mata ciki kamar kayan cikinta zai fito haka Safiyyerh ke ji, duk girman idanunta sai da ya yi mitsi-mitsi abin ka da zabiya da ƙyar take buɗe idanun nan, ba sunan wanda bata kira ba hadda Anty Turai akan su kawo mata ɗauki Yaya J ya sha kira. Ta sauke ajjiyar zuciya tana karanta addu'ar neman tsari da kuɓuta daga magauta ta yi zumbur ta miƙe saboda fitsarin dake mintsinin mararta. A can wajan ɗakin a cikin gidan da su Goje basu san da shi ba, duk suna zaune suna busa kayan shaye-shayensu hayaƙi ya cika wajan, wani na shan sigari wani na shan sholi wani wiwi sun hautsina sai surutai suke yi. Moh na gefe ɗaya ƙwance ƙafarsa ya ɗora akan ɗaya idan yana acting ka ɗauka jinin sarauta ne ko wanda yake da aljanu sarakai a kansa, duk ihun da Fiyya take yi da surutai yana jinta. Goje ya kalle shi ya ce "Wannan yarinyar tafa dame mu wallahi, ka kira ka faɗa masa tunjiya mun ɗakko ta ya san abin yi" Shiru ya yi yana sake kaɗa ƙafarsa a hankali har lokacin idanunsa a rufe yake. Goje ya kalli ƙofar ɗakin da Fiyya ke ciki ya sake kallon Moh kafin ya miƙe tsaye ya ce "Ina da matsala da jin kuka gaskiya, ko dai a rufe mata bakin ko a ɓara bakin biyu yanzu da askira" "Mangal" Da sauri Mangal ya kalli Moh jin ya kira shi domin tunjiya da suka ɗakko Fiyya ko tari bai sake yi ba, bai runtsa ba har gari ya hawaye ba wanda kuma ya kula a cikin su. "Ankar sarki, faɗa taka cikawa tamu akwai wani sagi a ƙasa ne?" "Bana son hayaƙin nan" lokaci guda suka kalle shi a take suka cillar da sigarin tare da saka ƙafa suka murje "Angama sai mene na gaba?" Bai magana ba ya juya musu baya a hankali ya buɗe idanunsa ya zaro takardar da yake faman ajjiya kamar rai, kusan kullum yana karantawa sama da sau wajan biyar a rana abu ɗaya ne amma sai ya ji baya fahimta,baya kuma ganewa, ya zubawa rubutun idanu Goje shima ya leƙo kai yana kallo ganin ya ninke ya ɓoye ya saka ya yi siririn tsaki "Na ji takaicin rashin makarantar da ban, shi ilimi ko yaya yana da rana" "Ina zargin wannan takardar bata tsafi bace, kamar ita ce ransa ko iskar dake shaƙa ya manta da komai amma banda ita, watarana sai na sace ta yasin" dariya Goje kawai ya yi ya san Mangal faɗa kawai yake yi. "Mai dawa kasan a yankinmu an sace mutane har biyu, yau da sakaliya anga gawar ɗaya ba idanu" ya juyo a hankali ya zubawa Goje idanu kamar mai tunani sai kawai ya miƙe yana taku ɗaiɗai ya fice daga cikin gidan, suka bisa da idanu ganin yau ya zama wani so silence kamar ba Moh ba. Safiyyerh ta ji an turo ƙofar da sauri ta miƙe tsaye tare da ja baya, mutum biyu take gani Goje da Mangal shi kuwa tunda ya cillar da ita a ɗakin bata ƙara ganin shi ba. Abincin hannunsa ya cilla mata da ledar ruwa pure water ta kalli takeaway ɗin da ruwan, ta ɗauke kai a hankali tana sake ja baya "Saura ki ƙi ci kamar na ɗazo, idan kuma kika sake yi mana amai a nan sai kin lashe abin ki tas" ta ƙurawa wajan ido ta ce "Ba zan iya cin abinci a nan ba, ni bana shan ruwan leda abincin ma ba irin wannan nake so ba, ko nama babu akai" "Kuma a ina kike tunanin ganin nama? Don ma kin samu an kawo miki dar yarinya saboda kina Manager kun saba cin mai kyau a sha mai kyau, a saka suttura a shiga mota a kwana cikin a.c ga naru a gida 24/7, a ci shinkafa basmati da ruwan gora dole ki ce haka, ɗiyar ƙaruna" Girgiza masa kai ta yi muryarta na rawa ta ce "Da gaske nake maka, ni kawai a bani ruwan jakar da lemo ko snacks" Goje ya dinga kallon ta ganin she is serious juyawa ya yi zai bar wajan ta yi saurin cewa "Don Allah ku bani waya na kira daddy na maka alƙawarin yanzu za a kawo kuɗin da kuke buƙata wajan nan akwai sauro headache da fever zai kamani" ta langwaɓar da kai gefe alamar neman alfama. "Ki jira Mai dawa ya zo, sai ki tambaya bani da ikon haka. Da kike maganar kuɗi kin ji mun ce muna buƙata ne? Ba kidnapped ɗin ki mukai domin a bamu kuɗin fansa ba, mun sato ki saboda a koyawa asawa hankali a rage masa tsayin harshensa da yake da kauɗi kin gane? Daga yanzu ki cire rai da samun ƴanci" "Daddy?" Safiyyerh ta faɗa a gigice tana dafe kan ta idanunta ya cika da hawaye, tausayin kanta dana daddy ya cika mata zuciya babu wani wanda take so a duniya sama da daddy da Ummi me za su yi masa rayuwarta suke son kassarawa tabbas idan suka taɓa kimar mahaifinta. "Me daddy ya yi muki, mene alaƙae sato ni da kukai da mahaifina me kuke nema a wajansa na roƙe ka da girman Allah kar ku cutar da mahaifinsa kar ku illata rayuwarsa, shi ne jin daɗi da farincikin zuciyata, ku duka kuna da iyaye na tabbata ba za ku so rasa su a rayuwarku ba ka ji tausayina Please brother" "Ni ba brother naki bane ni ɗan daba ne sunana Goje kin gane, idan kina buƙatar wani abu kina iya bubbuga ƙofar" kafin Safiyyerh ta yi magana ya yi sauri rufo ƙofar ya fita. Ya je ya samu Moh a wajen gidan zaune ya sake tanƙwashe ƙafafuwansa ya kalle shi sosai kana ya ce "Scorpion" "Kana son faɗar sunan, zan manna maka hauka Goje zan ja maka ruwa". "Me ya sa baka son na dinga faɗa ne? Ai dafinka ma ya fi na kunama ni ina son sunan" Moh ya yi shiru yana sake harɗe hannayensa duka biyun ya zubawa samaniyya idanu. "Idan zan nuna maka asalin kalata a Scorpion ba zaka ɗauka ba, za ka daina haɗa idanuwa dani sauƙin sunan na wajan faɗa ne, ka kalle ni a Moh ko Mai dawa ok" "Yadda ka ce haka za a yi, ya zamu yi da yarinyar nan yanzu? Kwananta ɗaya da wuni fa, kuma bata cin abinci" Cikin rashin fahimta Moh ke kallon Goje su yake ya tambaye shi wacce yarinyar bakinsa kuma ya yi masa nauyi ya dinga juya idanunsa akan fuskar Goje, fahimtar hakan ya saka shima Goje cewa "Manager wacce Ali wali ya saka mu ɗakko yarinyar da muka je gidansu jiya" haɗe fuska sosai Mai dawa ya yi idanunsa ya shige ciki haka kawai ɓacin ransa ya sake ninkuwa ya yi shiru ya datse laɓɓansa kamar zai raba su gida biyu ya yunƙura zai tashi Goje ya ce "Wannan sauyin na yanzu na mene? Na fara jin daɗi a raina kwana biyu baka sha ƙwaya ba, lafiya dai?" "Mutallab" still ya yi shiru Goje ya sake kiran sunansa yana leƙa fuskarsa ganin babu alamar zai kula shi kawai ya miƙe ya fice ya bar wajan. ***Gabaɗaya suna zaune a cikin parlon banda shi dake tsaye, zuwan nasan ake jira amma tunda ya shigo bai kalli kowa ba balle ya yi magana, fuskar nan a murtuke kamar kodayaushe. Yaya J, Awais Dr Hash, Anty Turai Waheeda sai Ummi dake zan gefe bata cewa komai sai goge hawayen da yaƙi tsaya mata take yi. Daddy baya uhm baya uhm'uhm kansa a ƙasa zuciyarsa ta bugawa da ƙarfi yama kasa yarda da abin da ake faɗa har lokacin gani yake wasa ake yi masa da hankali da kuma wahalar da zuciyarsa da ake saboda anga yana ƙaunar Safiyyerh ƙauna mai tarin yawa an fahimci ita ce rauninsa. "Captain Aliyu Abdu Marafa shiru ba naka bane, ba muzo nan da a shiru ba a matsalar kidnapping ba a yi mana wasa" cewar Sp Ghali daya ƙara amsar case ɗin Safiyyerh a karo na biyu ya ɗaga kai ya kalli masu gadin asalin gidan da kuma na part ɗin su Captain sai kuma ya ce "Heyy you man, mene sunanka da aikin da kake yi?" Cikin rawar murya ya ce "Sunana Isma'il ni mai gadi ne Yallaɓai" "Isma'il sanda abin ya faru ƙarfe nawa ne? A daidai lokacin kana ina kuma?" "Ban san ƙarfe nawa bane a lokacin don ban duba a gogo ba, sanda abin ya faru kuma ina bakin gate ne amma kafin nan na miƙe na shiga banɗaki kama ruwa wallahi gaskiya nake faɗa maka Yallaɓai" "To na ƙaryata ka ne? Kenan Isma'il bashi da sani akan waɗanda suka shigo gidan ko? Da ɗauke Safiyyerh?". "Duk abin da na ce maka na yi ƙarya abu ɗaya na sani fitowar su ɗauke da ita, hannunsu riƙe da makamai ɗaya ya ce na buɗe ko ya ɓola mini ciki na ji tsoro haƙiƙa sai na buɗe ashe sun yi parking mota wata ɓaka mai kyau daga can gefe" Murmushi kawai Sp Ghali ya yi yana duban ɗaya ma'aikacin ya ce "Kai kuma fa? Mene information?" Shi wannan jikinsa har ɓari yake don tsoro ya ce "Yadda na gansu Allah Ya sa naga Annabin Rahama, misalin biyu da arba'in ne ina zaune na ji ana dirowa ta katanga kafin na yi magana ɗaya ya make ni yana nuna yatsarsa a baki alamun na yi shiru, ni kuwa na yi shirun don wallahi a lokacin na ɗauka mai gida shi sojan kenan daman shi ke kai wa dare a waje saboda yanayin aikin nasa, suka ɗaure ni ina hango sanda suka nufi part ɗin tunda can babu masu gadi daga nan ban san mene ya faru ciki ba sai gani mukai sun fito da ita a kafaɗa kamar ma a sume take yadda ta langwaɓar da kai" Daddy da Captain suka runtse idanunsu lokaci ɗaya, kowanne tunanin da yake daban a ransa, is he a loser? Captain ke tambayar kansa or he is falled as a husband maybe da yana kwana ɗaki ɗaya da Safii da hakan bai faru ba, idanunsa ya ƙara sauya kala. Daddy ma nasa tunanin dabanne, ko dai ya yi gaggawa ne ba yanzu ya dace ba? Ko mistake ya yi daya aurawa Aliyu Safiyyernsa ne? Is he a loser? Daya kasa tsare rayuwar yarinyarsa mace ɗaya tilo a duniya ko dai da gaske he is falled as a father? Kafin kowa ya yi magana ta shigo cikin gidan a gigice duk da nutsuwar da take da ita, da sauri kuma Daddy ya miƙe tsaye cike da tsoro da mamaki hatta Captain sai da ya ji wani abu mai kama da faɗuwar gaba, who told her? Tun kafin ta yi magana daddy ya yi saurin matsawa kusa da ita ganin yadda take ta zare idanu fararen idanunta fuskar nan nata ya ɗakko rana kamar ta yage don fari "Zahiyerh" Girgizawa daddy kai ta yi a daburce ta ce "Ina Maama?" Ya yi shiru yana ƙoƙarin riƙe hannunta ta ƙwace ta yi baya da ƙarfi kuma ta ce "Ina Maama? Ka bani ita na tafi da ita where is Safiyyerh" "Safiyyerh has been kidnapped" "Kidnapped?" Ta maimaita tana juyawa ta kalli Sp Ghali anya ya san wacece ita da yake furta mata maganar anyi garkuwa da Safiyyerh kai tsaye bai tauna harshe ko ya lissafa maganar ba, Safiyyerh fa? Sp Ghali zai yi magana daddy ya girgiza masa kai yana sake kallon Zahiyerh wacce zuciyarsa ke buɗewa a duk sanda ya kalle ta. "Ummimi please ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa tafiyar nesa kikai jirgi kika hau" "To na ji, ka faɗa mini meke faruwa da Safiyyerh?" Daddy ya sauke numfashi a hankali kuma ya nuna Sp Ghali ya ce "As he said, he told you already Safiyyerh has been kidnapped" "Uhm" "Komai zai daidaita Ummimi" ita dai bata sake magana ba can ta ɗaga kai ta kalli Aliyu da sauri ya zame idanunsa ƙasa ta harɗe hannayenta a ƙirji ta tsaya jikin hawa steps ɗin bene. "Afuwa Sp muje ko?" "Next question ɗin mu akan Captain ne" "Ok ka yi mana" in ji Anty Turai. "Aliyu kafa yi haƙuri kalar aikin ku na sojoji daban, namu daban kowa da nasa iyawa da ƙwarewar a nasa ɓangaren ok. Aliyu kai ne zaka faɗa mana abin da ya faru a cikin gidan su waye suka sace maka mata har cikin gidanka a matsayinka na soja wanda kodayaushe zaka iya samun ƙarin matsayi na aiki, ya akai haka ta faru? Su waye?" "Ban sani ba" Kai tsaye Captain ya bada amsa "Baka sani ba? Har kuma suka ji maka ciwo kada ka saka na fara zarginka na yi tunanin sace Safiyyerh set up ne kuma ne ka yi plans ɗin hakan, ka sace matarka?" Aliyu ya dinga kallon Sp Ghali a hankali kuma ya ce "E". "kana nufin ka sace matarka Safiyyerh?" "E" ya sake cewa "Aliyu!!" Daddy ya kira Aliyu da ƙarfi ya miƙe ya ce "Da gaske ka sace Safiyyerh?" Kamar idanun Captain za su faɗo ƙasa saboda yadda suka fito waje sai kawai ya lumshe ido ya buɗe ya ce "E, na sace ta daddy" yana cewa ya fita daga parlon yana banko ƙofar da ƙarfi kamar ya cire ta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Muryar Ummi ta karaɗe parlon ƴan mazan dai sukai shiru. "Karya yake yi" Ummimi ta ce har yanzu taƙi zama lokaci zuwa lokaci kuma tana duba wayarta kawai sai tabi bayan Aliyu. Daddy har jiri yake gani baya so a fitar da maganar ya fiso a yi komai secretly har Safiyyerh ta dawo gare su amma sai yaushe ne?. Only God knows. ****Ammo na zaune ta yi shiru a ɗakinta kamar kodayaushe ta yi nisa a tunaninta bata ma san Malam ya shigo ba sai muryar Inna Binta da ta ji a sama wajan ƙofar ɗakin tana faɗin "Yanzu don Allah Ammo da rana ma ba za ki daina kwantar miji kina satar kwana ba, wacce irin jaraba da masifa ce haka ni Bintalo jaraba kala-kala Malam ɗin duk da basir ya cinye shi da rana ma ba za a bar mana miji mu dinga ganinsa duk da ba wata tsiyar yake yi mana ba" Ammo ta cira kai ta kalli Inna Binta ta juya ta kalli gefe har yanzu ba taga Malam ba cikin rashin fahimta ta ce "Kamarya?" "Ohho shafa ki ji mace an girma amma sai shegen munafurci da kissa wato kafin ki gama sallama ɗan naki wa duniya kafin ya gama zama ɗan ta'adda ya miki aikin mallake malam ko? Shi ya sa kaf gidan nan kin fi kowa yawan yara" Ammo ta kasa cewa komai da ƙyar ta buɗe baki ta ce "To ina Malam ɗin yake yaushe ya shigo mini?" Ta banka mata harara ta nuna mata malam dake zaune ya yi shiru a hankali ta furta "Ikon Allah ki yi haƙuri ban san ya shigo ba" Malam ya yi gyaran murya ko kallon Inna Binta bai yi ba cikin damuwa ya ce "Ammo ki nutsu ki ji me zan ce miki babu tabbacin abin dai har yanzu, ki yi haƙuri idan har hakan ya kasance gaskiya" Jin haka ya saka Inna Binta neman waje ta zauna a bakin dakalin ɗakin Ammo ita dai wacce ake maganar domin ta shiru ta yi tana bin Malam da kallo gabanta na faɗuwa ba wai yanzu ta saba da faɗuwar gaba ba, ta ji wannan ta musamman ce. "Gawa aka tsinta....," "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na Ammo?" Malam ya ƙura mata idanu bai taɓa zaton tunanin wancan gantalallan yaron mara amfani a duniya zai zo ranta bq, ya girgiza kai kana ya yi shiru caraf Inna Binta ta ce "Idan shine ai gwara ka faɗa ko kuwa? Kai aka cire masa ko wuƙa ce harsashi ne ko rayata ko babbake shi aka yi kasan haka ake yi wa ƴan daba, wallahi wani da aka rutsa shi ƴan unguwar jahilin duka sukai masa, ashe shima dai irin tsinannen yaron naka ne wuƙa bata huda shi, suka dinga rutsa masa dutse aka ina sai da kan ya ya yi dugu-dugu a nan cikin gari akai abin, da iyayen nasa suka je wajan ƴan sanda cewa sukai su yi haƙuri gawar ba zata ɗakko ba ta yi muni yaron nan dai da yake bashi da rabon rahama ko sallah ba a yi masa ba, yana can za a yi gwaje-gwaje da gawar ƴan makaranta daman ƙarshen duk wani ɗan daba kenan" Malam ya yi shiru bai yi zaton haka Inna Binta take ba, Ammo rasa kalmar da za ta yi amfani da ita ta yi wajan yi wa Inna Binta, ta yi shiru tana sunkuyar da kai. "Malam ka faɗa mata kawai sai ta ɗauki don gana" "Wallahi tallahi ko" Mama ta yi caraf ta faɗa ashe itama tana laɓe a jikin taga daga waje. Ya girgiza kai kawai cike da takaici kana ya ce "Gawa aka tsinta ta mace an cire mata idanu biyu kuma an cillar da ita bakin hanya, aka kira ana tunanin kamar gawar" haka kawai ya ji yana jin tsoron kalmar da abin da zai biyo baya Ammo ta ƙura masa idanu a sanyaye ta ce "Sa'adah ce ko Bafullatana ko Hameeda?" "Hameeda" "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Astagafirulla Allah mun tuba jama'a an cire idanun Hameeda gatan na ammo ta shige jama'ar gida Hameeda ta mutu a kawo mana ɗauki" a gigice Inna Binta ta zari mayafi tana ficewa zuwa maƙota. Mama kuma ta yi shiru idan haka ne ba ƙaramin gigita mutuwar Hameeda ya saka ta ba. Ammo bata ce komai ba a ranta tana nanata kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ita kawai ta yi mata saura a cikin baki "Ba a tabbatar bata, saboda haka ki taso muje a gani ƙila ki fini ganewa sosai" kafin Ammo ta yi magana Baba uwar mijin Anty Hameeda ta shigo tare da mijin idanunta ya yi ja cikin sauri Mama ta ce "Yaya lafiya dai Baba?" "Ina lafiya, Hameeda ce daga fita siyo magani da daddare mun neme ta mun rasa kwana biyu kenan wallahi". "Shikenan ta tabbata an kashe Hameeda" kafin ka ce me cikin gidan ya cika Inna Binta sai rusa ihu take yi tana sun shiga uku an kashe musu yarinya. Koda aka kawo gawar Hameeda ba kowa ya iya gani ba kamar dodo har ta fara wari an cire kyakkyawan idanun nan nata. Ammo ta dinga tuna nasihar Hameeda ta ƙarshe da ta yi musu,daga nan bata sake dawowa gidan ba wani abu ya tokare wuyan Ammo ta kasa magana balle kuka sai kallon gawar take cike da sarewa. ****Kamar kullum yau na Goje ya buɗe ƙofar tana durƙushe duk ta fita daga cikin hayyacinta idanunta ya faɗa ba zaka taɓa cewa Safiyyerh bace. Ya dire mata abincin yau dai pure water ɗin hadda sanyin shi "Kar ki sake buga mana ƙofa domin ba wanda zai buɗe miki" "Ka ɗauke bana ci" "Dar kin yi kyan kai ƴar kurciya" ya juya baya ta faki idanunsa ta zare ƙaramar wayar data gani a jikin aljihunsa ta yi saurin ɓoyewa. Goje kuma ya dawo cikin harabar gidan Moh ya gani zaune yana sake karanta takardar sai ya yi murmushi yana dafa kafaɗar Moh ya ce "Ni dai na fara gajiya da siyo abinci gaskiya" banza Moh ya yi yana ninke takardar tun daren da aka kawo Safiyyerh bai sake ganin kamarta ba sai sautin kukanta da yake ji kullum yanzu ma kukan take tana buga musu ƙofa da ƙarfi a fusace ya miƙe tsaye ya nufi ƙofar ɗakin Goje ya bisa da kallo can ya miƙe ya bi bayansa. Da ƙafa ya daki ƙofar ta buɗe da sauri Safiyyerh ta miƙe cak kukan nata ya tsaya a maƙoshi ta tattare ta haɗiye ta mayar zuwa cikinta, fitsarin dake mintsinin mararta ya saki kansa ya fara zuba a gefen ƙafarta, dukkan wata gaɓa ta jikinta ɓari take yi. Ashe da bata san waye ba, bata san waye ya yi kidnapping nata ba sai yanzu cikakkiyar siffarsa ta bayyana zubi da tsarin da halittar da Ubangiji ya yi masa mai firgitarwa bata san waye mafi muni a cikin ƴan daba amma ta san wannan tantirin ne ko daga tsaiwar da ya yi, cikakken namiji a tsaye majiyin ƙarfi matashi kuma mai jini a jika da cikakkiyar lafiya shine matsayin ɗan daba tsaye a gabanta gefen fuskarsa wani zabcecen yanka wanda akai masa ɗinki har ya zama tabo. Salati take ƙoƙarin yi ta kasa ta gama jiƙa wajan da fitsari ƙiris ne babu numfashinta ya yi ƙaura daga ƙirjinta ta yi saurin ƙasa da idanunta. "Ka yi haƙuri kar ka mini komai, don Allah ko nan waje ne ku bar ni na fito kalli skin ɗina zai lalace akwai ants a nan waje" ta tattare hannun rigarta tana nuna masa farar fatarta da ta yi wani irin tabo ritsi-ritsi kamar kwanciyar ji fuskarsa ta kumbura ta yi jaa sai susa take yi saboda ƙaiƙayi. Ta langwaɓar da kai ta ce "Ka gani ko na sake nuna maka har bayana" ta juya bayan tana ƙoƙarin ɗaga rigar ta ji ya daki ƙofar da mahaukacin ƙarfi kafin ta juyo ya bar wajan. Ta sauke ajjiyar zuciya feeling reliver ganin ƙofar a buɗe. Tana fitowa suka haɗa idanu da shi da sauri ta juya kanta na bugewa da jikin bango, anya tana da hankali da lissafi kuwa? Fitsari fa a wando sai ya tsuke fuska. Suna zaune Mangal ya shigo yana hakki da sauri Goje ya zare wuƙa sama tiger ya yi zumbur ya miƙe tsaye yana gurnani Moh kuma kallon Mangal yake yana jiran ya ji suwaye suka biyo shi don yana da yaƙinin ba wanda ya san gidan da suke. "Kai ɗan wahala mene su waye suka biyo ka?" "Daga layin su Mai jeji naje an yi rasuwa kuma a gidansu Moh aka anyata lahira wallahi" duk suka juya suka kalli Moh shima ɗin kallon nasu yake fuskarsa ba wani sauyi kawai ƙarashen maganar yake jiran ji. "Sai aka ce waye ya baza? Iyayen Moh dai akwai sauran rai wannan dar in sha Allah" "Wai ko Hamida ko Hamda, idanu aka ƙwaƙule mata ashe tana cikin mutanen da aka sace ta" Moh tunani yake yi ina ma ya san mai sunan Hameeda tasa Hameedan ba zata taɓa mutuwa a irin wannan halin ba, sam ba zata mutu ba duk da yanzu ba ruwansa da ita. Bayan wasu shuɗewar daƙiƙo zumbur ya miƙe tsaye kansa na sarawa a dagule ya furta "Amini?" Da sauri kuma ya yi wani ɗaki suna shiga suka same shi yana cakawa kasan wata sabuwar allura da Ali wali ya basu da maye, bayan ya zuƙe ruwan a jikinsa ya ƙara ɗakko wata ya sake cakawa kansa sirinjin ana ukun Goje ya yi saurin matsawa ya ce "Easy Mutallab,zaka haukata kanka a banza kasan wacce irin allura ce ko dan baka jin turanci muma bama ji, haukatar da mutane take yi fa?" Sakar masa allurar ya yi ya sake ɗakko wata Goje ya sake riƙe wa ya ce "Wallahi in dai ina nan ba zaka sake yi ba" ya ƙara sakar masa ya ɗakko fenta zai yi Goje ya ƙara riƙe, Moh ya shammaci Goje ya ɗauke shi ya damfara shi da ƙasa ya saka ƙafa ya take hannunsa hannun ya yi ƙara, ganin yana shirin kashe shi ya sa Mangal ya ɗakko abu ya makawa Moh aka, ya ɗauke ƙafarsa ya juya yana kallon Mangal da sauri Mangal ya zare Goje ya fito da shi daga ɗakin da gudu suka fice daga cikin gidan. **The following days. Buɗe ƙofa Captain ya yi ya shiga ɗakin a hankali wanda ya yi wa Aliyu mugun sani shi zai lura da ramewar da ya yi. Idanunsa akan Ummimi dake zaune gefen gado hannunta tsakanin cinyoyinta ta sunkuyar da kanta ƙasa ya ƙarasa ya duƙa gabanta ya ɗora hannunsa a cinyarta a hankali kuma ya leƙa kansa ta ƙasa ya kalli fuskarta suka haɗa idanu ta zabga masa harara lallausan murmushi ya yi mata a hankali ya ce "Love" "Aliyu fita" Ya girgiza mata kai ya yi shiru sai lokacin ta yi shiru tana ƙare masa kallo "Ciwo ka yi ne Gadanga?" "A'a love" "Kuma yaushe ka damu da Maama har haka ka dame?" "Love, Safii is my wife" ta wani buɗe idanunta na rashin fahimta "Waye Safii?" "Safiyyerh, your Maama" da sauri ta miƙe tsaye tana girgiza kai "Yaushe aka yi haka? Tunanin waye hakan decision ɗin waye wannan professor ko?" Gani take sauri take yi amma sai ta cire ƙafa ɗaya take mayar da ɗaya ta fice daga ɗakin a parlo taga duka mutanen gidan hadda police da team na musamman da suka fara bincike akan sace Safiyyerh Abdu Marafa. "Ashe daman baka yarda ba professor za ka iya mini haka? Bana baƙin ciki da auren da ka yi musu amma ina da hakƙi na sanin ka haɗa Safiyyerh da Aliyu aure, Professor burinka ya cika ƙudirinka ya tabbata ka aurawa Safiyyerh Aliyu" masifa Zahiyerh take yi tai Hausa tai turanci ta koma larabci ba wanda ya tanka ta, kan Abba a ƙasa. Da ƙyar Aliyu ya janye ta a ransa ya gode Allah da bata ce a raba auren ba tsaf zata iya. Ta nemi kujira ta zauna sai nishi take yi na rashin lafiya. "Zo Aliyu" ya ƙarasa wajanta ta nuna masa kusa da ita ya zauna, sai kawai ta rufe idanu ta kwanta ta yi shiru a hankali ya fara danna mata kanta Dr Hash shima ya ɗauki ƙafarta data kumbura ya fara danna mata sai a lokacin Daddy ya buɗe idanu ya kalleta ya girgiza kai fatansa kafin ta farka Safiyyerh ta dawo gida. "Sp har yanzu ba wani kira da muka samu akan batun sace Safiyyerh, ina zargin anya issues na kidnapping ne?". "Za su kira ai sun sauya salo ina mai tabbatar maka cewa za a kira Safiyyerh zata dawo gida" daddy ya jinjina kai ya yi shiru. Wayar Aliyu ce ta fara ƙara yana dubawa yaga kamar private number har sai share sai ya yi tunanin ko masu sace Safiyyerh ne? Da sauri ya amsa kiran was the first abin da ya ji daya nemi buɗe masa zuciya sautin kukan Safiyyerh ƙasa ƙasa ya runtse idanu can ya ji ya ce "Yaya Please help ants za su cinye mini fata Yaya za su kashe ni" "Safiyyerh listen" Karo na farko daya kira sunanta "Take a heart peanut, ke matar soja zama jaruma". "Yaya am scared wuƙaƙe" ya buɗe idanu ya ga duk kallonsa suke yi hadda daddy Sp Ghali ya yi masa alama ya saka speaker. "Kina ji na?" Kamar tana gabansa ta ɗaga kai "Be strong Maama, daddy is here for you, Ummi kowa ma hadda ni am here for you ƴan mata, hadda Ummimi" da wani irin sauri ta ce "Ummimi? Ummimita Yaya?" "Sure, ki nutsu wanne waje suka kai ki, za ki iya tuna suna ko wanne abu da zai bamu haske?" "Yaya sun rufe mini idanu ban san komai ba, don Allah ka taimaka mini daddy help me please" idanun daddy ya yi jajur already anyi connecting na wayar an fara bincke da ƙoƙarin tracking daga ina wayar ke zuwa. Shima kuma daga can haɗaɗɗan ɗakinsa da suke zube da kayan na'ura kamar hauka ya saka abu a kunne ya ɗora ƙafa yana girgiza kai a hankali yana jin conversation ɗin Safiyyerh da Aliyu yana yi yana duba time da cije leɓe. Abin da Aliyu bai taɓa yi ba kenan ƙoƙarin jan Safiyyerh da hira da ya ji Ummimi zata motsa zai yi saurin girgiza ƙafarsa "In sha Allah i will save you Safii, ki yi ƙoƙarin gane wani abu ki yi addu'a" tana ƙoƙarin sake magana suka ji ihunta da ƙarar buga wayar da ƙasa "Safiyyerh kina nan kina kan kayi baby?" Aliyu ya jere tambayar. Kafin sun an kare daddy ya sulale a wajan babu numfashi. ****Tunda su Goje suka fita yake abu ɗaya kamar wanda za'a zarewa rai, sai buge buge yake yana fasa komai na gidan kumfa na fita a bakinsa ihun da ya yi da gurnani shi ya saka Safiyyerh sakin ihu tana yin cilli da wayar a gigice ta miƙe har lokacin kayan bacci ne a jikinta, tana fita ta ganshi a tsakar gidan ya yi tumu-tumu wani irin mahaukacin tausayinsa ya ratsa zuciyarta ta duba babu kowa a gidan sai ta yi tunanin wannan opportunity ne da zata bar gidan hankali kwance, bata damu da kayan jikinta ba sai kawai ta nufi ƙofa da gudu tana ƙoƙarin fita ta ji muryarsa cikin mawuyacin hali kamar ana fisgar ransa abin da ta ji ya saka ta tsaya ta yi jim itama kanta na sarawa tana gani bibbiyu ta sake yunƙurin buɗe ƙofar ta ji ya ce "Safiyyerh....!" Ya faɗa da ƙarfi a gigice ta juya taga ita yake kallo yana ƙoƙarin tashi ya kasa yana miƙo mata hannu... *MUTALLAB IS NOT FREE* We'll soon end the free pages. ka yi payment a yi naka a paid group. MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 Ƴan Niger kuma ya gadda tsarin yake. 'Yan Nijar ku turo carte airtel ta 300fcfa saman wannan layin 84506476 [10/25, 11:14 AM] Nanameera: *This is not a love story,but a love that builds a story, and a love that destroys the story.* *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 14 *Bright pens...2nd batch* *Author's books* Munafukin miji Moon Mijin malama Tsintacciya Idan ba ke Sirrinmu E.t.c Follow on Arewabooks Follow on telegram Remain 1 free page Jikinta rawa yake ganin ya kafe ta da idanunsa har lokacin kuma kakkarwa nasa jikin yake yana fesar da numfashi. Ina ya san sunanta? Take tambayar kanta. A hankali Moh ya lumshe idanunsa bayan ya janye su daga gare ta yana ɗan ciccije bakinsa. Safiyyerh ta kasa fita, idan ta bar shi ya mutu alhalin zata iya taimaka masa Ubangiji zai kamata da laifin rashin tausayi da imani, ta salwantar da rai ta hanyar ganganci da son zuciyarta. "Safiyyerh taki rayuwar fa? Kashe ki za su suma fa, ya kamata ki bar wajan nan tunda kin samu dama, shi kinga kamar mahaukaci ne maybe" zuciyarta ta bata shawara cike da gamsuwa ta jinjina kai tare da kama handle ɗin zata fice. Haɗa idanu suka sake sanda ta juyo ya dinga kallon ta rinannun idanunsa sai ta saki hannun ƙofar tana ɗaga ƙafa zata nufe shi. "Run Safiyyerh, run away run Safiyyerh" Ta sautin muryar zuciyarta a cikin kunnenta ta sauka har tsakiyar kanta ƙirjinta ya dinga ɗagawa tana son tafiya bata kuma san meke janta zuwa gare shi ba. Ta girgiza kai "Save him frist" ta furta a iya harshenta. Yana ganin ta nufo inda yake ya rufe idanu kafin ta ƙaraso ya juya baya yadda ba zata ga fuskarsa ba. Jikinta a sanyaye ta durƙusa cike da tsoro ta kasa magana can ta yi ƙarfin halin furta "Ina ke maka ciwo?" Ya mata shiru ba bacci yake ba, domin tana hango yadda ƙirjinsa ke ɗagawa sosai yana ƙoƙarin ganin ya hana kansa yin abin da ƙwaƙwalwarsa ke umarta shi. "To faɗa mini inda maganin yake na ɗakko maka" Jin shirun ya yi yawa ta matsa tana leƙa fuskarsa suka haɗa ido ya zaro mata manyan jajeyen ƙwayar idanun ta yi saurin ɗauke nata idon "Tab kalli idanunka fa, ko asibiti zaka je?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin kai hannu zata taɓa shi ya mirgina gefe yana haɗe fuska kamar ya ce ya shiga uku, da zata gane to tabbas ita ɗin ce baya son gani ko jin muryarta ta kura masa hakan yake yi sosai ya tsuke fuska yana rufe idanu Safiyyerh ta miƙe gabaɗaya hopefully ya buɗe ido ko ya bata amsa ba sarewa ta sake miƙa hannu dukan da ta ji ya kaiwa jikin bango ne ya saka ta yi baya tana zaman ƴan bori,shima ya tashi zaune yana zazzaro idanu daidai lokacin su Goje suka shigo ya kalli Safiyyerh da take yarfe hannu saboda bugewar da ta yi ya dubi Moh daya miƙe tsaye yana tangaɗi ya shige ɗaki yana rufo kansa a ciki. "Ke me kikai masa?" "Ƙato da shi me zan masa?" "Abu a duhu na san matan yanzu ba kunya ce da su ba, idanu rufe suke afkawa maza" da mamaki Safiyyerh take kallon Goje zuciyarta babu daɗi ga takaicin rashin guduwa gana wancan da ko inda take bai kalla ba duk maganar da ta yi masa, ta matsa tana takure jikinta waje guda sai yanzu ma take jin kunyar shigar jikinta sosai, ita Safiyyerh yau ita ce take rayuwa a wajan ƴan daba mashaya kuma ƴan ta'adda hawaye ya cika idanunta sosai mutanen da sam basu suwaye su ba, basu san kansu ba basu da wani amfani a wajan al'umma. "Ke kina ji ko?" "Safiyyerh sunana" "Mene ya daman kuma warning zan miki kar ki kuskure ki sake zuwa wajan shi idan kina son tsira da ranki ba, ba kema ko Abdu Marafa bane a nan wallahi zai iya ganin bayansa, ki yi abin da ya shafe ki kawai ki tsaya iya matsayin ki na wacce akai garkuwa da ita kuma ɓarayin gwamnati". "Shi wa?" Ya nuna mata ƙofa "kin gane ai" "A'a" wuƙa ya zaro yana gwalo idanu waje ya ce "Idan na cire miki yatsa ɗaya za ki gane ai" "Ni mu yi magana ta fahimta daku, me kuke buƙata zan baku koma mene amma ku rabu dani don Allah ina kyakkyawan fata da muradan da nake son cimma a rayuwa naga ku babu inda kuka saka gaba rayukan ku ma sam baku damu dasu, wallahi ina buƙatar rayuwa mai tsayi da zan bar baya mai kyau ba zaku ɓata mini rayuwata ba, kuma warin sigarin nan juya mini kai yake da ƙyar nake shaƙar numfashi, ni macace mai hankali da ilimi wacce iyayena suka bawa tarbiyya daidai gwargwado in da ilimin addini saɓanin ku da ba lallai ko ummul kitahhb kun iya ba, ƴan daba ne ko masu laifi rayuwarku a gurɓace take ba a yi muku tarbiyya ba" hatta Moh dake cikin ɗaki idanunsa a sama yana kallon rufin kwano sai da ya waro ido yana sauraren maganganun da take cewa, Mangal ya yi mata ƙuri da nasa idanun haka Goje "Wuyanki ya isa yanka ba laifinki bane za mu yi maganinki" "To me na ce na ba daidai ba, don Allah ku ba ƴan daba bane ƴan ta'adda kuma ga tantirin can shine shugaban naku da alama asalin daƙiƙi ne ajin ƙarshe sai wari dauɗa dana rana ga na shaye-shaye wallahi...," saurin haɗiye maganar ta yi ganin shi tsaye a kanta yana huci ta miƙe tsaye hannu ya ɗaga kamar zai kwaɗa mata mari ta kurma ihu tana ƙanƙame jikinta "Don Allah ka yi haƙuri ƙarya nake yi wayyo daddy wayyo captain" sai idanunsa suka sake jirkicewa ta buɗe idanu taga ya zuba mata nasa idanun fuskarsa dab da nata sai juya ƙwayar idonsa yake a saman fuskarta kamar mai son tantancewa wani abu. Ta tura baki cike da tsiwa ta ce "Kana kwaɗa mini mari zan rama tunaninka rabuwa zan yi dakai ka ci bulus? Bayan an ce duk wani ɗan shaye-shaye bashi da wani ƙarfi hayaƙi ya cinye shi" Goje ya ce "Wannan yarinyar ƴar wasa ce bayan kuɗi data iya sarrafawa har rashin kunya ta iya Allah kar ka rabu da ita" Shi dai Moh na tsaye yana kallon ta ita kuma ta kasa jure ganin ƙwayar idanunsa ta yi ƙasa da kanta tana murguɗa masa baki, bata ankara ba ta ji ya cilla mata baƙar kunawa cikin riga ta zumduma ihu a gigice ta yi kansa zata riƙe shi ya yi saurin baya yana ficewa daga gidan Goje yana ta dariya da buga ƙafa "Kinga aikin Mai jeji gana Scorpion nan" ****Eng Ali wali yana zaune a gidan wutawarsa yana zantawa da wasu manyan mutane masu taimaka masa a harkar kamfel ya dubi P.a ya ce "P.A ina tunanin iya abin da ake buƙata kenan kuma na bada, ka sani ba kuɗi yanzu a ƙasa kamfen ya cinye komai, you can manage ko?" "Ba damuwa amma muna da raguwar list na local government wajan biyar da bamu je ba yanzu haka, ga ƴan media sun matsa kasan mutane babu amana gwara a fara watsa musu hatsi tun yanzu fa a yi maganin yunwar data addaba musu" Ali wali ya yi murmushi yana juya kai kafin ya ce "Ku je za mu yi magana zuwa dare ina da hira da ƴan zuwa dare we'll talk" P.A ya kalli mutanen ya ce "Don't make any mistakes idan kun shiga gidan rediyon ku tabbatar kun yi abin da ya dace, kar kuma ku nuna wata alaƙa tsakaninmu da ku yadda na faɗa muku haka zaku faɗa" "In sha Allah, ai harma da abin da baku buƙata ba mu indai za a biya mu ai buƙatar maje hajji sallah zamu farfaɗi ayyukan bogi da ya yi kuma ya yi mana" "Nice to hear this, you can leave ku je" Tafiya suka yi suna murnar ƴar dubu biyar biyar ɗin da za a basu akan faɗar abin da ba haka bane. Ali wali na shirin miƙewa ya ji numfashi a bayansa ya juya da sauri, tsaye ya ga Moh fuskarsa rufe sai ƙwayar idanunsa da take a fili ya cake yana muzurai. "ka bani tsoro amma" "Mara gaskiya ko a ruwa zufa yake" "Me na yi na rashin gaskiya?" Ya yi masa shiru yana wani irin fito ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman kujera yana zaro kunama ya ajjiye saman kujerar wajan ta fara yawo tana ɗaga ƙari sama ta kumbura sosai. "Yaushe ka shigo? Na ce ni zan dinga nemanka bawai ka dinga biyo ni duk inda nake ba, bana so a san ina mu'amala da kai" "Saboda annoba ne ni? Tunda ka jawo ni haka zaka shanye duk abin da na dama, na kwalo yarinyar mene next?" Murmushi Ali wali ya yi ya ce "Ai na san kun ɗakko ta, tunda CSP ya yi mini magana akan case ɗin kidnaping sannu namijin duniya" "Zan kawo ta nan" "Ina? A'a ka bar ta nan wajanku zan baka key ɗin wani gida sai ku tafi can kwafi sararawa ni bani da gaske koda zaka dinga huta gajiyarka a wajanta kana rage zafi" Moh ya ɗaga kai ya kalli Ali wali da kyau. "Wacce gajiyar, sanyi ne a jikinta?" "Kana abu kamar ba wayayye ba, mu bar maganar ka yi mini aiki na farko and i appreciate it. Sai batun Scorpion" daidai nan kunamar dake yawo a wajan ta shige hannun Moh ya matse ta ya yar waje guda Ali wali ya cigaba da cewa "Scorpion ba zai bar mu ba, Hon Maɗatai yake hari a yanzu nasan kuma bayan nan ni ne a list, yana neman zame mana masifa yana kawo mana barazana a akan siyasarmu gwara Hon Maɗatai ya samu dukkan abin da yake nema a mulki ya samu nasa rabon ni yaushe na fara? I will never let that happen ba zan bari ya yi galaba akai na ba" "Me za ka yi?" "Zan tabbatar an nemo shi an ɓatar da shi, don ba haka kawai yake yin abin da yake ba akwai abin da ya taka yake taƙama da gadara dashi, ka yi ƙoƙarin nemo mini shi kafin hukumar FID su kama shi zan ruɓanya maka abin da duk na yi niyya" "To kuna da case da shi?" Ali wali yace "Pardon? Kamarya kenan" "Basar" Key ɗin gidan ya basa, hadda na mota Moh yaƙi amsa wai he don't know how to drive ya basa kuɗin abincin Fiyya mai kyau da duk abin da take so. "Kaƙi faɗa mini waye kai dai ban san komai dangane da kai ba Moh, sunanka kawai na sani Mutallab without surname and middle name, whatever shikenan dai" Moh ya ƙara ɗaga ƙafa zai fita Eng Ali wali yace "One more think Mutallab" "Ali wali ka kira ni da ɗan daba ko ɗan ta'adda sai mu yi magana" Ali wali ya yi murmushi ya ce "Sai godiya" ya tsuke fuska Moh. "Professor Abdu Marafa ya mini mummunan tabo a zuciyar matasan jihar nan,ya ɓata mini suna na ji ina son ɗanɗana masa kwatankwacin abin da ya yi mini ta hanyar ramuwar gayya wacce ake cewa tafi ta gayya daɗi, kamar yadda ya ɓata ni shima haka nake so a ɓata tarihin tarbiyyar gidansa da sunan da yake taƙama da shi, a dinga masa kallo a matsayin wanda ya gaza" Ya yi shiru yana sauke numfashi yana duba wayarsa ganin shugaban jam'iyya na kiran shi ya miƙe tsaye. "Bayan sato budurwar ƴarsa da kuka yi har gida, ina son ka yi Safiyyerh Abdu Marafa fyaɗe, ina son ka yi wa Safiyyerh Abdu Marafa ciki kaga tana da auren wani, wani kuma daban ya yi mata ciki wanin ma ɗan daba, ɗan daban da basu san waye shi ba, kaga Safiyyerh zata haifi ɗan zina ko" "Ɗan zina?" Moh ya maimaita a fili Ali wali ya ce "To ɗan mene? Yayinda da wani wanda ba mijin yarinyar ba ya keɓe da yarinya har ta samu ciki wannan cikin ya sunan shi? Cikin shege ba haka lissafin yake, idan na ce wani zan bawa wani aikin lissafin Eng Ali wali bai gama cika ɗari over ɗari ba, dole kai zaka aikata haka Mutallab dole kai zaka yi wa Safiyyerh ciki domin dauɗar gora ciki kan shata" "Wanne zunubi ita yarinyar ta aikata, gyatuminta ne kamar batun nan ba zan ba, shi kuma daman cikin yinsa ake yi? Ba kawai girma yake ba?" "Au baka san yin ciki ake ba? Shekarar nawa?" "Koma mene ba za a yi ba" Ali wali ya yi murmushi ya ce "Dole zaka yi, ka rubuta kuma ka ajjiye sanda za ka yi baka sani ba jeka" bai wani ɗauki maganar Eng Ali wali da muhimmanci ba ya fice daga gidan. ***Safiyyerh ta rufo ƙofar bayan ta gama dubawa ta kalli Goje ta ce "Kawai ku siyo mini kayan abincin na dinga dafawa sai ina san muku?" "Kin iya wato ne?" "Mene wato?" Ya ce "Shi girkin nake batu" ta jinjina masa kai ya miƙe tsaye ya ce "Da kin yi dabara daman ba ki da wani amfani. Ita mamaki ta yi ganin kitchen hadda tukunya plates da spoons ga risho da sauran tarkace. Babu jimawa Goje ya dawo hannunsa riƙe da Indomie guda biyar da ƙwai guda goma hadda kayan miya da magi ya bata ya ce "Ta yi musulmin daɗi kin ji Manager" Ta samu kanta da yin murmushi a ranta kuwa dabara take yi ta samu hanyar guduwa. Suna tsaye ya faɗo cikin gidan sai ya yi turus yana kallon Goje yaƙi yadda ya kalle ta, ta ƙasan idanu ita kuma take binsa da idanu mamakin yadda jikinsa yake a murɗe take har ƙasan zuciyarta ta ji tana shakkarsa. "Barka da antayowa mai jeji ya ƙarin haƙuri" banza ya yi masa ya shige ciki Safiyyerh ta ce "Au rashi ma aka yi masa?" "Yayarsa aka sace sai jiya aka kanta an ƙwaƙwale mata idanu" Safiyyerh ta zare idanu tana dafe ƙirji sai tausayinsa ya kamata a raunace ta ce "Kuma bai je gida ba? Anya yana son yayar tasa kuma kun tabbatar wannan ba mahaukaci bane?" Shi dai tuni Goje ya bar wajan. Ta gama dafa Indomie wacce ta ji azabar Attahiru rabon da ta shiga kitchen a rayuwa ta manta fuskarta ta yi jajir da wani irin roɗi-roɗi idanun sukai micin-micin ta dinga mata ƙaiƙayi fuskar saboda zafin wuta ta nemi kaɗan ta juye musu a faranti. Moh yana kallon yadda ruga lauma kamar mayunwata sai jan yaji suke yi ya kalli Indomien ya kalle su can ya miƙe ta ce "Kai baza ka ci ba? Ni ina son yin sallah fa" duk suka share ta, suna gama ci suka fice tare da rufo ƙofar ya rage sai ita kaɗai ta haɗe kai da qwwia ta dinga kuka kamar ranta zai fita har bacci ya ɗauke ta a wajan. Cikin bacci ta ji an cillo mata abu ta miƙe da buɗe idanu tsaye ta ganshi ya juya baya leda ce ya cillo ta buɗe taga duguwar riga guda biyu da hijabi da takalmi ta yi ta mamakin yadda ya san size ɗinta ta miƙe tsaye yana jin zata zo wajansa ya nufi hanyar fita ta sha gabansa ya yi turus ta dinga kallonsa shima yana kallonta "Wai kai baka yin magana ne, ko ƴar dariya babu kafin na tafi mu ƙulla mu zama abokai" ta miƙo masa hannu ya kalli hannunta mai ɗauke da siririn zobe sai yatsunta zara zara da su "Am Safiyyerh Abdu Marafa You?" Ya sake yin shiru ta langwaɓar da kanta gefe guda ta ce "Ina son zama ƙawarka fa, zan maka labarin daddyna da yadda yake so na, da labarin kamfanin da nake aiki hadda labarin Ashraf wanda zan aura ya mutu aka aura mini captain labarin Ummimi da Kinal ƙawata i will tell you everything, abota Frist?" Ta sake miƙa masa hannun a karo na uku. Gefenta ya bi ya shige yana rufe ƙofar gidan ya bar ta tsaye da hannu a ƙaƙe takaici ya ishe ta shi wannan yana ɗan ta'adda yana jin kansa kamar ɗan gidan ƙaruna saboda faɗin rai ga miskilancin masifa the manager ita Safiyyerh take magana ake sharewa bai san cewa akan dole take yin maganar ba? Ta lumshe idanunta hawaye na cika cikinsu da ƙyar ta yi alwala ta fara jero salloli. Goje ne ya shigo da sauri ya ce "Ke kina ina fito maza taso" ta miƙe za ta yi masa gaddama kawar Moh ya shigo ya damƙi hannunta ta kalli baƙin hannunsa da ɗan mitsitsin nata farin hannun ya jata sukai waje mota ta gani bai tsaya jiran komai ba ya dannata a gaba Goje ya shiga baya Mangal dake tsaye ya ce "Waye zai ja motar yanzu? Ni ban iya ba kuma haka?" Moh dake shirin shiga mazaunin driver ko me ya tuna ya kalli Safiyyerh a karo na farko ta ji muryarsa a sake ya ce "Dawo nan" tsoran shi take ji ta fito ta koma wajan driver ya dawo ita ta tashi, ya cilla mata key ɗin motar "Muje" bisimillah ta yi ta fara driving ta juya ta kalle shi ta ce "Ina?" Ya bata wayar hannunsa wacce yanzu ya shigo da ita ta duba location da ya fara driving cikin sauri har suka bar wajan. Mintuna kaɗan da barin su motoci suka tsaya a ƙofar gidan Captain ya fito jikinsa danye da uniform na sojoji da suka amshe shi sosai ga ƙatuwar bindiga sauran yaransa suka fito a hankali ya dinga bin wajan da kallo har ya shiga cikin gidan abin da ya fara cin karo da shi ya sanya zuciyarsa bugawa ganin rigar baccin Fiyya yashe a ƙasa ya ɗuka ya ɗauki rigar idanunsa ya sauka akan wani busasshen jini ya dinga kallon gidan a nan ya kalli ƙwayoyi kala-kala da wuƙaƙe da gorori ya lumshe idanunsa "Where are you Wife? Ina suka kai mini mata?" "Captain kuma ka tabbatar tracking ɗin nan ya nuna?" Ya jinjina kai don baya jin zai iya magana. "Sun gudu, amma ya akai sukai san an yi tracking location nasu har suka gudu da wuri haka?" Captain ya girgiza kai irin bai sani ba "Ka kwantar da hankalinka matarka zata kuɓuta ko kana tunanin sun yi mata wani abu ne?" Captain ya nuna masa rigar baccin Safiyyerh da jinin dake wajan mutumin ya dafe kai ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, in sha Allah ba abin da muke zato bane muje" fita sukai Captain ya ji a ransa ba zai bar abin haka nan ba. Mutallab wani gida ya kai su madaidaici mai kyau da tsari da yake can bayan gari duk suna zaune Safiyyerh kanta na ƙasa tana mamakin yawan shiriun bawan Allan nan, idan ya yi shiru shi kaɗai sai ya saki ajjiyar zuciya ko ya ƙurawa waje guda ido. ***Wajan sati guda babu labari akan batun sace Safiyyerh ba kiran waya babu komai Daddy ya hana a faɗi maganar ko a social media ko a gidan rediyo ya ce a bar ta tsakaninsu. Yana ƙwace hannunsa maƙale da ruwa muryarsa a hankali ya ce "Aliyu waye ya saka?" "She is my wife daddy" "And? Ɗan sanda ne kai ko soja?" "Zan iya amfani da uniform ɗina ko babu haka ai she is my responsibilities yanzu na kula da haƙƙina zan ji na zama lusari idan ban nemo Safii ba, kar ka dakatar dani daddy police su yi nasu aikin ni na yi nawa" "Ka cire hannunka a ciki Aliyu" "Ok zan jire akan wanne dalili?" "Aliyu yanzu baka tunanin dalilin hakan su yi mata wani abu ne? Baka san su waye mutanen nan ba, duk abin da zaka ji a bayan nawa dana Zahiyerh yake kar ka yi kuskuren da za su salwantar da rayuwar Maama na roƙe ka, mutanen ba mutunci ne da su ba kamar komai hannun Sp Ghali" Aliyu ya miƙe ya nufi ƙofa "I am sorry daddy idan kaga na tsaya to na mutu ne, idan da numfashi a ƙirjina ba zan gusa ba sai na dawo da Safiyyerh cikin rayuwata i am sorry" yana cewa haka ya bar ɗakin. Daddy ya rufe idanunsa daya cika da ƙwalla ya wani irin ramewa ko abinci baya ci Ummi ta ce "Ka san halin Aliyu da baka fito masa ta haka ba, gwara ka saka Ummimi yi masa magana" daddy yaƙi cewa komai. Wayarsa ta fara ƙara number ya gani sai ya yi sauri ya ɗaga yana kaiwa kunne aka ce. "Barka, ina magana da Professor Abdu Marafa na sani ko baka amsa, zan fara da yi maka ya jiki don ina da yaƙinin kana nan zuciyarka na ciwo bari na ɗora maka da wata maganar ban sani ba ko zaka iya jure jin abin da zan faɗa. Yarinyar da kake ji da ita ni na saka a sato mini ita Safiyyerh kenan ina son ka lashe aman da ka yi da kanka. Professor ni ɗan siyasa ne lissafin ɗan siyasa daban yake dana Malami, bana barin kota kwana daman mun saba saka jama'a a uku, wallahi ka shiga komata yanzu nine da wasan ka fara lissafa ranakun mutuwar yarinyarka daga yanzu" da sauri Daddy ya ce "Waye kai?" "Sarai ka ɗauki ne muryarta professor, kana magana da Eng Ali wali mai neman takarar ɗan majalisa, ka hanani bacci yanzu lokaci ne da zaka ji abin da nake ji". "Ali wali me kake buƙata me Safiyyerh ta yi maka karka cutar mini da yarinyar don girman Allah kar ka taɓa ta" "E, ba zan taɓa ta ba muddin ka yi abin da nake so" "Me kake so?" "Ka dawo jam'iyyata kuma tsagina ka lashe aman da ka yi ka kuma gyara ɓarnar da ka mini na rusa mini dukkan shirina, yadda ka ɓata sunana a wajan matasa da al'umma a gidan rediyo da kai da ɗan jaridar da yake mara maka baya ku sake sabon lale wajan wanke ni inma kana buƙatar kuɗi zan bayar hakan ba laifi bane ba" "Uhm Ali wali kenan tun yanzu har ya yi sauri haka? Ni kake cewa idan ina buƙatar kuɗi kaga na yi maka kala da mabuƙaci? Kamar dai ka manta waye Professor kana buƙatar tuni na, laaa la la dama sauran lokaci ai. And da kake batun Safiyyerh tunaninka ita ce raunina ko?" Daddy ya tsige ruwan hannunsa da ake ƙara masa ya sakko daga saman gadonsa daman tuni ya nunawa Ummi ƙofar fita tun kafin ma ya ɗaga kiran. "Ka yi kuskure sosai, Safiyyerh is nothing to me kuma she never be my headache idan ka so ka saka wuƙa ka yankata a yanzu is doesn't matter for me, idan akan Safiyyerh ka kira ka mini warning ka makara Ali wali tunda Safiyyerh ta bar gidan nan ko da dai da rana ban taɓa tunaninta ba siyasa ce kai kuma yaro ne mu zuba mu gani" A ɓangaren Ali wali dariya shima ya yi ya ce "Lallai prof ka cika ɗan siyasa, to wallahi ka shirya ganin gawar Safiyyerh a wannan daren ku tara ƴan jana'izarta". "Idan ka haifo kuma kai cikakken ɗan iska ne idan har ba zina akai ka haifeka ba na roƙeƙa Ali wali don Allah ka kashe Safiyyerh nima fa wani aikin ka rage mini..," ƙit Ali wali ya kashe wayar daddy ya saki dariya yana wani irin murmushi wata number ya kira ana ɗagawa ya shige toilet yana saka key, ya jima ciki kafin ya fito ya zauna saman gado Dr Hash ya shigo da Yaya J ganin daddy zaune ya saka dr cewa "Daddy ya jikin naka?" Hawaye ya cika idanun daddy ya ce "ba abin da zai tafi daidai babu Safiyyerh zuciyata zafi take my innocent Fiyya, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ina tsoran halin da Ummimi zata shiga" ganin hawaye a idon mahaifin nasu ya saka Junaid ficewa dr ya zauna ya dinga lallaɓa daddy da bashi bakin za a ga Safiyyerh in sha Allah. Aliyu yana zaune a ɗakinsa aka buɗe ƙofa tare da shigowa ya ɗaga kai ya kalleta ya miƙe da sauri duk da babu fara'a a fuskarsa amma sai da ya saki ajjiyar zuciya. Ta juya idanunta "Nan ka ɓoye?" Ya girgiza mata kai "Ka cigaba da binciken inda Safiyyerh take Aliyu kar ka saurari mahaifinka ka ji ko?" "in sha Allah Ummimi" ta zuba masa ido sai ta juya ya ce "Tafiya za ki yi?" "Me zan maka?" "Love, ganin ki nake son yi" ta haɗe rai tana cewa "To ɗakko zani na goyaka" ya buɗe idanunsa ya yi wajanta yana rungume ta ya saki ajjiyar zuciya "I love you Ummimi, and I love Safii too" Kan shi ta shafa ta ce "Kawai ka zaɓa ni ko ita" ya lumshe idanunsa ya yi mata shiru, rungume shi ta yi a jikinta ta yi shiru tunani daban daban a ranta sai kuma ta sake shi ta ce "Fito waje" saƙo Aliyu ya samu cikin gaggawa sunansa ya fito a jerin sojojin da za a yi posting nasu wajan aiki ya dinga kallon saƙon yaushe ma ya dawo da za a sake tura shi wani wajan bayan babu shi a sojojin da aka yi list? Sai kawai ya fita da nufin zuwa kiran da ya samu domin bata uzurin yana da wani muhimmin aiki akan nasa iyalin ya manta da batun a tsarin aikin sojoji babu sauyi idan har a zaɓe ka. ****Mafarki ta yi mai ban tsoro ta farka a gigice tana kiran sunan TAHHB sai haki take yi fitila taga an kunna an hasko ta ya zuba mata idanu a ransa yana ƙara mamakin wannan hasken nata gefensa zabtareriyar addace saboda tsaro ya miƙe a hankali ya kunna hasken parlon sai a lokacin Fiyya ta lura da Goje dake cikin kwance cikin jini haka Mangal ga wuƙaƙe a gefen su sai numfarfashi suke yi. Ya taka ya je gabanta ya tsaya can ya duƙa dab da ita baki ta buɗe za ta yi ihu ya saka yatsarsa a bakinsa "Shhhh" ta yi tsit ya cake addar "Mene?" "Ban kira ka ba wallahi" ya zuba mata idanunsa masu kaifi ta janye nata "sunan wa kika kira to?" "Tahhb" "Sunanki ne? Ko na Abdu Marafa?" Ta girgiza kai "Mafarki na yi a mafarkin na ji sunan, amma ban sani ba ni na manta komai na mafarkin ma kai na ciwo yake i have a headache" Ya ɗaga addar ya cake ta tsakanin ƙafafuwanta sai sheƙi take yi ya ce "Ko dai ki faɗa mini waye Tahhb ɗin da kika dame ni da kiran sunansa yanzu ki na ɓula miki cinya" "Don Allah ka yi haƙuri wallahi ban san shi ba" "Ke wace?" Moh ya tambaya "Safiyyerh sunana" ya cije bakinsa sosai ya ce "Matar soja ko?" Ta jinjina masa kai "To ni waye? Kuma ya nake a wajanki?" "Wallahi ban san ka ba, kai ba kuwa bane a wajane" idanunsa har ruwa yake ya daka mata tsawa a gigice ya ce "Waye ni? Waye ni waye tell me.... ❤‍🔥🔥💃1 page remain ba zan taɓa buɗe komai ba shafi 15 is nothing nothing ku biya you'll never regret sai mun yi nutsu za ku fahimci labarin MUTALLAB bai haɗa hanya da kowanne kalar labari ba, idan za ka yi kuka ka fara tun yanzu 😭😂ba kuma zan taɓa sauya labarina a yadda nake ba, you better shut up... MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 'Yan Nijar ku turo carte airtel ta 300fcfa saman wannan layin 84506476 [10/27, 4:07 PM] Nanameera: *The story of a thug husband MUTALLAB, as a good parents za ku bada auren yarinyarki ga ɗan daba ɗan ta'adda? Ban ce ku fara kuka tun yanzu ba,ban ce ku ji soyayyar ciki kamar a ƙirjinku ake wanzar da ita ba.* *The story of TIGER and MOH The destiny of CAPTAIN and FIYYA. Finally the eternal love* *between..The love that separate them and back them together❤‍🔥😭* *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 15 last free episode *Bright pens.. 2nd batch* For more updates follow Mutallab on Arewabooks in sha Allah ❤‍🔥🥰 Page 15 shine last free pages na labarin, kar ka yi tunanin ganin wani page ɗin a waje ka yi payment a yi naka into paid group akan 500 kacal, love ɗin da kuke showing yanzu ne zai yi aiki🫠MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 'Yan Nijar tsarin biyan zai kasance ta *Stock na airtel*. Ku yi wa wannan layin 84506476 magana sai ta ba ku lambar da za ku turo mata stock ɗin. Kafin ɗorawa da inda muka tsaya zamu ɗauki hutun zango na sati ɗaya tal😂 maybe har a yi albashi ko masu mining ta fashe musu. Godiya ga Hajja Aisha Abubakar Khadhfsum data biyawa mutane 8 🥰 ga masu business zaku iya badawa a tallata muku idan kun ɗauki nauyin page in sha Allah. Ba zan manta da BESTIE ba🥰I so much love her wish you all the best Aunty Nazeefah Sabo Nashe ta ce HADARIN GABAS yana hanya. Ina son ta sosai😮😮 Gaisuwa ga haƙarƙarina😂🥰uwar gidan Viper tunda mun amince Nabila ce amarya Ayushercool masoyiya. My beb Zee kumurya sai tallafe ƙirji muke muna sata a addu'a gashi zata fara yi mana ZAYTOON a watan Nuwamba i love them sosai🥰 Conversation bana ce kuci kanku ba, saboda ina ƙaunarku Sarautar's library Mutallab fans, Nimcy paid group my ArewaBooks people. Mikiya writers Association Mikiya fans AUTAR MANYA❤‍🔥 Ubangiji Ya bar ƙauna. Page 15 Last free pages *What if I tell you, I love you?* "kar ki ce ba ki sanni ba, kar ki ce haka dole ma tarihin rayuwarki ba zai taɓa cika ba sai da sunana, dole a same ni a cikin rayuwarki sai dai idan za ki cire wani sashi na cikin tarihin" ya furta yana huci da gwame numfashi Safiyyerh was shocked and speechless at the same time ta kasa kallon shi wani irin tsoro shi take ji mai girma ya ratsa zuciyarta. A hankali ta ɗago kanta zuwa gare shi hawaye na taruwa cikinsu yana sauka akan fuskarta Ta ƙura masa ido da sauri kuma ta girgiza kai ta ce "Wallahi da gaske ban san ka ba, ban taɓa ganin ka ba sai kwanakin nan, i don't even know your name balle kai,me ya sa zan sanka to?" za ta sakar masa kuka ya ɗora yatsarsa a baki ya ce "Shhhh" ba shiri ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya shi dai har lokacin fuskarta yake kallo yana murza tsinin wuƙar a ƙasa. "To kai ka sanni ne? Ni ka cire mini wuƙar nan ka ji ɗan baƙi" ta furta tana juya idanu ta langwaɓar da kanta gefe guda. "Ki daina kiran sunana daga yau" "Sai na dinga ce maka me to? Ka faɗa mini ban ma san sunan ba ai" ƙoƙarin biye mata yake wajan ganin ya samu abin da yake buƙata amma a duk kalma ɗaya daya furta ko kafin ya furta sai ya fama hautsina kan shi kafin ya san me zai furta mata. Wuƙar ya ɗauke ya cilar gefe guda ya juya ya kalli Goje jira ya ke yi safiya ta yi ya fara tunanin yadda zai samu likita ya ji ta ce "Kai ne ka yanke su ko? Ba kyau wallahi ka mutu a haka wuta zaka tafi babu fashi kana kallo za mu shige aljanna muna jiyo ihunka a cikin lazza ko saƙara tunda baka da wani aiki a rayuwarka sai daba da bushe-bushe cikinka ba komai sai ƙwaya da hayaƙi, gabaɗaya gudanawa kake daka zaɓi wannan rayuwar ne ɗan baƙi? Bayan rayuwa akwai mutuwa fa karka bari ka mutu cikin wannan halin ba zaka ji da kyau wajan Mala'iku ba" "Kina da ɗan'uwa mala'ika ne?" "Subuhanallahi, kai ko wa'azin baka so kamar jinin fir'auna ni tausayinka kawai nake ji tunda baka gani shikenan" ta haɗe fuska irin ta ji haushin nan har ƙasan zuciyarta ita ƙyamar shi take yi rayuwarsa a gurɓace take babu wani abu na birgewa ko ban sha'awa a ciki deep down kuma tausayin rayuwar tasu take ji tana jin da tana da iko tabbas ba zata taɓa gazawa ba wajan ganin ta taimaka musu. Ya rufe idanunsa yana daga zaunen saman kujera ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗora akan ɗaya ya fara yin fito wanda ya cika ɗakin a hankali kuma ya zaro sigari zai kunna ta yi saurin cewa. "Matsalar daƙiƙi kenan a rayuwa, shi da kansa bature ya ce tana lalata lafiya dake babu arabi ba boko ba'a gane komai ai shikenan, goodness Safiyyerh what exactly wrong with you, that's not your business" ta faɗa lokaci guda kuma tana miƙewa tsaye sai dai bata kai ga zuwa inda ta yi niyya ba ta gan shi tsaye a gabanta hannunsa riƙe da sigarin yana zuƙa da fesarwa, ta saka zata rufe hancinta ya sa hannu ya tukare jikin bango ya sata a tsakiya sigarin a bakinsa yana binta da jajayen idanu bakinta na rawa ta girgiza kai ta ce "Mene haka wai?" Ya yi shiru yana duƙawa fuskarsa dab da nata har lokacin ita ɗin da yake kallo "Iskanci ne wannan matar aure ce ni fa, saboda ƙwaƙwalwarka bata faɗa maka daidai ko? Idan ka sato ni a gidan mijina shine yake nufin me? Zan barka ka yi yadda ka so ko ƙazamin jikinka ya taɓa fatar Safiyyerh ba zan taɓa yafewa kai na ba, da babbar murya ina faɗa maka ni Safiyyerh matar aure ce ka ji ko? Kana jin Hausa ai?" Ya zare sigari hayaƙin daya zuƙa ta cikin bakinsa ya dinga fesa mata a fuska ta fara tari tana ɗauke kai, ya ƙara zuƙar sigarin a baki ya matsa dab da fuskar tata ya sake fesa mata lokacin ta buɗe baki za ta yi magana gabaɗaya ta haɗiye hayaƙin, a gigice ta fara tari tare da kakarin amai ganin da gaske aman za ta yi,ya matsa a wajan tare da shigewa wani ɗakin. Safiyyerh ta durƙusa tana riƙe ciki saboda wani irin ciwo da yake yi mata ga amai dake ƙara hautsina mata kayan ciki ta rasa yadda za ta yi ta kwanta tana riƙe cikin da dinga rusa kuka. Duk abin da ya fara Goje na jinsu kawai yana cikin wani hali ne tsautsayi ya saka su fita a daren sukai karo da ƴan daban cikin gari sun shigo ɗaukar fansar wani faɗa da aka yi can kwanaki shine suka rufar musu, a cikin ƴan daban cikin garin wanda yake jagorantar su me suna Bakin wuta shine ya sare su shi kuma Moh sai da ya sari wajan mutum goma a yaran Bakin wuta wanda kuma shine faɗan su na farko a rayuwa ba wanda ya san wani, a cikin yaran ba sai da aka buɗewa wani ciki kuma duka aikin Moh ne yana da tabbacin kuma Bakin wuta ba zai bari haka nan a ci bulus akan shi ba. Goje ya juya kaɗan ya kalli Safiyyerh dake kuka sosai kamar ranta zai fita itama yarinyar naci gare ta ga bakin tsiwa da Moh na taɓa mace da tuni Safiyyerh bata duniya ya san ba zai iya kashe ta ba amma zuwa gaba zata gane bata da wayo idan ta cigaba da kai shi bango. Tana kukan a haka bacci ya ɗauke ta bata ji kiran sallah ba amma tunda ta motsa bakinta ɗauke da addu'a ta san asuba ta yi ta miƙe da ƙyar ta nufi banɗaki ta yi alwala ta jima tana azkar kafin ta yi raka'atul fijr kana ta yi sallar asuba. A hankali ta dinga leƙa shi abin da ya bata mamaki bai shige ganinsa durƙushe a kan qwiwinsa ba yana kallon gabas ba kuma sallah ya yi ba, kan shi a ƙasa ya yi shiru kamar zata shiga sai kuma ta fasa ta tsaya cak ta samu kanta da yi masa addu'a samun sauƙi da mafita a rayuwarsa da shiriya idan yana da rabo. "Allah Ya shiryarka idan kana da rabo" Ya ɗago kan shi ya juya kaɗan suka haɗa ido, ba ƙaramin gigita ta yi da ganin idanunsa a haka ba, ya ƙura mata ido a ransa girman nacinta yake ƙara jinjinawa duk da bai yi mamaki bai kuma zama sabon abu ba, bai fiya son takura ba wani lokacin. Safiyyerh ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce "Ko yunwa kake ji na daba maka abinci? Ko shayi?" "To na zo na yi maka shira? Ko waƙa?" "Get out..." Ya ce a hankali muryarsa ƙasa ta buɗe ido jin ya yi turanci ta ce "Wow ashe a ɗan san wani abu, nifa ba zan fita ba bakina ciwo yake na rashin magana gaskiya" kafin ya yi magana ta shiga cikin ɗakin ya yi saurin tashi da ƙyar ya nufi kujera ya kwanta ƙafarsa ɗaya a armchair ɗaya a can saman kujera hannayensa ya harɗe a ƙirji idanunsa rufe. Safiyyerh ta zauna a ƙasa ita kanta bata san me ya sa take son yin magana da shi ba, ta ji kuma tana barin wajansu zata haɗa Kinal da shi ita take son auren ɗan daba a hankali muryarta a nutse ta ce "Sunana Safiyyerh Abdu Marafa, ni ce auta a gidanmu..." Ta ɗan yi shiru bata ga alamar yana ma jinta ba kamar bacci yake yi haka yanayinsa ya nuna bata karaya ba ta sake matsawa ta ɗora da faɗin. "Mahaifina professor ne ya koyar a jami'o'i da yawa a wannan ƙasar cikakken lakcara ne matasa na son shi sosai saboda yana taimaka musu da shawarwari. Ina da yayyi huɗu babban yayenmu sunansa Aliyu muna ce masa Captain shi soja ne, bashi da kirki gabaɗaya baya dariya kamar kai ɗin nan amma shi ba baƙi bane fari tas, yana da ilimi he is educated, sai mai bi masa Dr Hash likita shi a ɓangaren kwakwalwa Neurologist, shi rayuwarsa ba sawa ba hanawa sai my favourite Yaya J sunansa Junaid shi aiki biyu yake yi aikin banki da business, ina son shi sosai kamar yadda yake so na, rayuwarsa abar sha'awa ce wallahi. The last one Awais Shi kuma ɓangaren siyasa yake so amma daddy baya so yanzu dai ya ce yana son zama shahararren ɗan kasuwa ne, sai kuma ni Safiyyerh nima na yi karatu ina aiki yanzu matsayin Manager a FS WORLD INVESTMENT COMPANY, ina da saurayina da nake so kuma yake so na Ashraf sunansa ɗan mai kamfanin da nake aiki ne, akwai wasu abubuwa da bana ganewa a kamfanin..." Shiru ta yi da sauri kuma ta kalle shi taga har yanzu idanunsa rufe yake bai motsa ba "Kodayake shikenan, saura kwana ɗaya auren mu da Ashraf ya rasu, Ashraf died ya mutu ya bar ni cikin tsoro da fargaba, a ranar daya rasu a ranar ne aka aura mini yayana Aliyu, da dai bana jituwa da shi sam amma ƙaddara ta haɗa kuma Ubangiji kaɗai ya san dalilin hakan, wannan shine labarin Safiyyerh Abdu Marafa" Ta leƙa fuskarsa taga idonsa still a rufe ta tura bakinta gaba "Nima sai ka bani labarinka ai muna zaune waje guda bai kamata bamu san juna ba" miƙewa taga ya yi ya nufi ƙofa kafin ta bi bayansa har ya fice daga cikin gidan. ****Eng Ali wali ya dinga kallon Moh da yake tsaye kafin ya ce "Ina wayar daka amsa wajena? Mene amfaninta ina kira baka ɗauka wai?" "Ba gani gabanka ba?" Moh ya ce yana kame fuskarsa kamar kodayaushe. "Yarinyar nan tana wajanka ko Mutallab?" Moh ya yi tsaki a fili da ƙarfi kuma ya ce "Ni a tarihina sau ɗaya ake faɗa mini magana na haddace ka yi batu kawai" ya ƙarasa maganar yana jawo flask ɗin shayi ya tsiyayi ruwan zafi ya saka madara da su milo ya nemi waje ya zauna ya janyo biredi da plate ɗin ƙwai ya fara ci duk zafinsa da taurin kan shi a nutse yake cin abinci sai dai baya laumar wasa "Daman kai aka kawowa abincin karin Mutallab? Ai shikenan magana nake so mu yi very important akan yarinyar nan daka ɗakko" ya yi shiru can ya ce "magana nake maka fa ka yi shiru" "Kunne ke ji" "Professor ya raina mini hankali wai ko kashe yarinyar nan zan yi ko a jikinsa yana nufin bai damu da ita bane ko mene? To wallahi ni Ali wali zan bashi mamaki, yarinyar nan kafin ya ganta sai ikon Allah don haka ka yi yadda na ce a kanta, ka yi mata fyaɗe ka yi yadda ka so da ita har ta samu ciki yadda zamu watsa labaran yarinyar professor Abdu Marafa ta yi cikin shege ya kore ta daga gida ni kuma na ɗauke ta na kula da ita har zuwa haihuwa,kaga daga nan hankalin jama'a zai yi kan Professor Abdu a bar batuna ni kuma na yi amfani da wannan opportunity wajan cin nasara a zaɓen da yake gabatuwa, don this time ba zan taɓa barin Hon Maɗatai ya yi nasara a zaɓe ba zan yi duk abin da zai tabbatar dani ne na ci zaɓe ko a can hukumar zaɓan inec na shirya tsaf ba gudu ba jada baya siyasa sai ɗan siyasa, harkar siyasa da zama wani a harkar ƙasar nan sai ka nuna ba wani shege ka cire tausayi da imani, ba ri ka ji Mutallab duk wani ɗan siyasa kan shi kawai ya sani" ya numfasa yana ɗaukar ruwa ya sha. Moh dai har lokacin shayin yake sha hankali kwance abin shi. Ali wali ya duƙa ya ce "Dole ka yi wa Safiyyerh fyaɗe dole ne ka yi wa yarinyar nan ciki, samun cikinta shine plan ɗina na farko da zai kai ni matakin hawa kujerar ɗan majalisa" "To ya ake cikin?" "Baka san yadda ake yin ciki ba, ciki na haihu fa?" "E, ban sani ba" "Mutallab, da ake cewa ka yi aure a ranar an kashe maka matarka da me za ka yi da auren da ka yi" "Bayan a yi wa mutum girki ya ci ya yi bacci akwai wani abu ne? To ni ban iya yin ciki ba, sara da soka kawai na sani a rayuwa da shiga jeji, ka bar batun hakan bani ba ko waye ba za a yi mata wani abu ba" "Moh" "Ali wali" Mutallab ya ce yana yin kyatsa yana miƙewa tsaye kuma. "Mutallab yadda aka fara aikin nan da kai, to da kai za a ɗora kuma a ƙarashe dole zaka yi wa Safiyyerh fyaɗe i am telling you this, za ka ce na faɗa maka" "To ka fara bani matarka na yi mata ai kana da ita, sai kace Professor ɗinne ya yi mata" Ali wali ya dinga kallon Moh ganin how serious he is da maganar kuma da gaske yake. "Ni zan shige zan na ji kira idan ka shirya bani matar taka tunda yarinyarka Noor bata ƙasar" "Ina kasan ina da yarinyar Noor?" "Ali wali kenan" Hanyar fita ya yi kamar wancan karan ya ƙara jin sauti mai kama da ihu ya dinga kallon ƙofar kafin Ali wali ya ƙarasu har Moh ya buɗe ƙofar ya shiga cak ya tsaya ganin wata mahaukaciya zaune sai ihu take ita kaɗai gashinta ya rufe mata fuska ya juya ya kalli Ali wali ya ƙara kallon matar bai yi magana ba ya saki ƙofar zai fita Ali wali ya ce "Ka manta kaga wannan, sirrina ne" Ko magana Mutallab bai yi ba ya kwashi kuɗi ya yi waje abinsa yana rufe fuskarsa. Bayan ya fita Ali wali ya ɗauki waya ya yi kira ana ɗauka ya ce "an samu matsala P.A yau wani yaga ajjiyata, fitar maganar nan daidai yake da zuwana gidan yari" ta cikin wayar P.A ya ce "Kafin ka je gidan yarin ka fara tura wanda yaga ajjiyar taka can" "Mutallab ne" "Tab, matsala kenan ina ruwan ciwon idanu wannan yana matsala kuna samun akasi za kaga ba daidai ba" Ali wali ya yi murmushi ya ce "Ina da tsari P.A idan na tabbatar na ci wannan kujerar zan yi tuggun da za a yi wa Mai dawa ɗaurin rai da rai a gidan yari, ka zo mu yi magana wai kasan har batun ƴa ta Noor ya sani, uhm sai ka zo dai" Yana gama wayar ya duba interview ɗin da za a yi da dukkan wani ɗan takarar ɗan majalisa daka mabanbanta jam'iyyu wanda BBC ke shiryawa hakan yana nufin za su haɗu waje guda da Hon Maɗatai da Dr Abraham Denial David yana da buƙatar ya zauna ya rubuta dukkan abin da zai faɗa a wajan. ***Yana zaune ya zubawa yaron idanu gabaɗaya ba zai shige shekaru biyu da watanni ba a duniya ya yi wayo gwanin sha'awa duk wanda yaga yaron sai ya burge shi akwai shiga rai da ƙyar yake buɗe idanu saboda farin da yake da shi ya sauke ajjiyar zuciya yaushe zai rabu da damuwar ran shi sai yaushe zai ga Safiyyerh ya nuna mata abin da Ubangiji ya bata, daga samun cikin har haihuwar ba wanda ta sani. A fili ya ce "Come back please Safiyyerh, where are you ina kika shiga haka me ya sa hakan? Jininki fa Safiyyerh haba my innocent Mahmah" "Ka dinga yin addu'a komai zai daidaita ya zama tarihi Ubangiji yana gani kuma yana kallo ba zai bar addu'ar ta tashi a banza ba, zata dawo ta damu ɗan ta, zata dawo a faɗa mata gaskiya, mu ma muna da namu laifin" "I missed Safiyyerh dear, ki bar ni na koka" ya ƙarasa ya ɗauki babyn ya rungume a jikinsa hatta farinsa irin na uwarsa ne sak yaushe zai ga Safiyyerh ne? Wayarsa ya ɗauka ya yi kira ana ɗauka ya ce "Har yanzu ba wani information akai ko?" Ya yi shiru can ya ƙara cewa "Ka san komai ba, ka san yadda na samu na tsira da raina bana sha'awar komawa kuma ni da aikin lauya har abada, komai namu a can muka baro bani da picture ɗin Safiyyerh ko guda wallahi zan yi ƙoƙarin neman ƙwararren mai zane na gani ko za a dace thank you" Kashe kiran ya yi ya ajjiye wayar yana sake rungume yaron da ko ɗomin jikin uwa bai sani ba, balle ya sha nono kamar yadda kowacce uwa ke shayar da nata ɗan. ***Safiyyerh na zaune bayan ta gama musu girki Goje yana ci da sauri yana ƙona harshe ta ce "Kaci a hankali mana akwai zafi" ya yi murmushi ya ce "Allah dai ya ba ki kada Manager" "Amin" Suka yi shiru can ta ce "Wai ba ka ce yayar wannan babban naku ce ta mutu ba? Me ya sa yake zaune a nan wai, ina yayenku suke" Goje ya ce "Babata ta mutu ni haka baba, shi kuma iyayensa suna nan cikin Birget Scorpion ai baya son zuwa gida ko unguwarsu baya son zuwa, tun bayan daya dawo daga gidan yari wajan state cid" "Kai me ya yi haka to? Kwanansa nawa a wajansu" "Shekara uku" Safiyyerh ta jinjina kai har ranta ta ji tana son cin labarinsa waye shi a hankali ta ce "Ai daman naga baya ji shikenan da wuƙa a hannu ya sari wani wacce kalar rayuwa ce haka?" Goje ya ce "Manager kenan, ai yanayi ne ke sanyawa a zama haka babu wanda ke son zama mutumin banza fa, ki gane hakan". "Son zuciya dai, Ubangiji daya halicci bayinsa an ce baya ɗora musu abin da ba za su iya ba, a tsaftace halicci kowa tun daga cikin uwa mahaifiya, a nan son zuciya ne da rashin wadataccen imani a zuciya da kuma yana da ilimi ai ba zai yi hakan ba" Goje ya ce "Ko? Kin san shi ne kin san waye shi? To ki maye masa gurbin abin da ya rasa sai kiga ya dawo daidai idan an yi sa'a" "Me ya rasa shi ɗin?" "Soyayya, ta uwa, ta mahaifi, ta mata" "Ok nan wai a haka yana da mata?" "Ta rasu" Goje ya ce a taƙaice ta yi shiru "Ki gwada cewa kina son kiga ki ce za ki aure shi" da sauri Safiyyerh ta kalli Goje ta ce "Kasan me kake cewa ne? Ina da aure fa ai zunubi ne haka" "Zance kenan, ba ki da wani aure yarinya haka kalar masu auren take kenan?" Safiyyerh ta yi shiru ita dai ko bata aure shi ba kawai za ta yi using opportunityn ɗin nan ya bata labarinsa, ko a lissafin ƙaddarorinta babu batun zama da ɗan daba balle soyayya har ace aure amma idan har zai bata labarinsa lallai za ta yi wani abu. Ta yi murmushi ta ce "Kana da gaskiya ka gano ni, ai kaf ƙawayena ni ce bani da aure to bana son gori shine fa nake cewa ina da aure shi Captain ɗin ai yayana ne don ka ji, amma kana ganin zai so ni? He is such a arrogant, boring person yana da matsala" "Ki gwada mana" "Zan ƙoƙarta, ya sunan shi ok ka ce Scorpion ko?" "Mutallab sunan shi, mantawa na yi" "Wow a nice name, sunan shi ya fi shi kyau shine kuje ce masa mai jeji? Kai ya sunanka?" Ya yi mata shiru kawai sai ta miƙe ta shige ɗaki. ***A karo na biyu Aliyu ya kalli Commander ya ce "Sir ka yi replacing nawa da wani mana" "Aliyu me ya sa kake yin haka, na lura kamar aikin soja ya fara fita daga ranka ko? Ka je ka yi tunanin tun farko wahalar daka sha kafin zama abin da ka zama, ƙiriƙiri an ƙara maka muƙami amma ka nuna baka son ana kiranka da sunan muƙamin sai Captain? Why?" "Sir to a ɗan bani sati guda ok?" "Ba zai yiwu ba, ka je ka fara shiri cikin daren nan da kwana biyu za a poster ku" rai ɓace Aliyu ya miƙe ya fita bai taɓa Jin takaici da kuma dana sanin zama soja ba a rayuwarsa sai wannan lokacin, shekarunsa nawa a duniya sai yaushe zai cigaba da jurewa yaushe zai ta yin haƙuri baya son shiga cikin ko barrack ne balle a nisanta shi da garin, ya samu sauƙi daga matsalar mata ga kuma wannan matsalar he need his wife, seriously he need his Safii yana buƙatar Safiyyerh a gefensa. Daddy ya dinga kallon Aliyu kafin ya ce "Aliyu mene plan ɗinka akan case ɗin nan wai? Sp Ghali yana neman information ka ja baki ka yi shiru na ce ka cire hannunka a wannan matsalar ko, ka san me hakan yake nufi?" "Daddy Safiyyerh fa matata ce hakƙin kare ta yana wajena so allow me to do daddy ka rabu dani" "Allow me to do daddy" daddy ya maimaita ya juya ya kalli Ummimi dake zaune tana kallon Aliyu ya ce "Kin gani ko Zahiyerh idan Aliyu ya saka na rasa Maama zai yi mamakina" murmushi kawai ta yi ta ce "Matarsa ce fa, ta ya ya zai yi wasa da ranta bayan yana buƙatar ta cikin tasa rayuwar, bana son wani magana mai tsayi da bayane babu mai yi wa Safiyyerh kutse a rayuwarta ka sani, su yi nasu binciken shima ya yi" "Aliyu bar wajan nan" Fita ya yi rama rasa wanne kalar tunani zai yi, daddy ya lumshe idanunsa a fili ake ganin bugawar zuciyarsa bai shirya ba sam, baya jin kuma akwai abin da zai iya kawo masa cikas bai yi maganinsa ba. Daddy ya gargaɗi kowa akan kar a fitar da maganar sace Safiyyerh kwatsam zance ya fita a shafin daddyn wanda shi kansa bai san yaya aka yi ba, wayarsa kullum na hannunsa balle ya ce wani ya ɗauka ya yi posting cikin yaran, ya tabbatar kuma ba hacking wayar aka yi ba, aka fara kiran wayarsa domin tabbatar da gaskiyar al'amarin ya rasa ya ya zai yi kawai ya ɗauki wayar ya kashe. ***Mutallab na zaune yana sauraren Goje Safiyyerh ta fito ta saka hijabi har ƙasa bai kalle ta sai haɗe fuska da ya yi ta ce "Abokina Goje barka ya jiki naga an yi maka treatment, ku siyo ka yayyenki na dinga yi muku tunda dai dabar ya zama dole na iya ai" murmushi ya yi "Na ɗauka lissafin kuɗi kawai kike ai? Ashe likita ce" Ta yi murmushi ta ce "Ina yini?" Ta faɗa tana kallon Moh ya yi kicin-kicin da fuska bai amsa ba. "Wallahi kyau kake mini idan kana haɗa fuskar nan, na ji ina son ka kuma zan iya aurenka wallahi" ya juya ya kalleta da sauri ta kashe masa idanu ɗaya ta ce "What if I tell you, I love you?" Ta sake cewa "Idan fa ka amince zan so ka har numfashina na ƙarshe a duniya, kawai dai kar ka wulaƙanta ni" "Ke bar nan" Ya furta a kausashe kamar ya ce ya shiga uku "Na san saboda na ce maka ina da aure ne, wasa nake yi don kar ku yi mini wani abun ne na faɗa fa, trust me i love you kuma na ji zan iya aurenka a yadda kake, zan baka farinciki walwala da jin daɗi ka amince mini ka ji dear" Moh ya dinga kallon ta wani irin kallo wanda bai ma san yana yi ba,sai dai ba'a tantance kallon na mene yanayin fuskarsa bai bada damar hakan ba, kaifin idanunsa ya saka Safiyyerh ƙasa da nata idanun, duk da shaye-shayen da ya ke yi da ɗaukar wuƙa matsayin abokiyar rayuwa da tarin raunukan da suke fuskar bai hana wani irin tsoro da shakkarsa ta gitta a zuciyar Safiyyerh Abdu Marafa ba, wani kwarjinin take hango wa na musamman a fuskar Mutallab Tahhb haibarsa da kwarjininsa mai ban tsoro ga namiji balle ɗiya mace sai yanzu take ji ta yi tsaurin idanu wajan tunkarar shi da wannan maganar mai kama da tatsuniya a gare shi, gare shi kallon kin raina mini wayo ya kewa Safiyyerh da tunanin ko ta samu matsala da nata tunanin tunanin ne? Idan ba matsala ta samu na gushewar tunani ba abu mamaki ne gare shi da jin furucinta ya yunƙura zai tashi ta riga shi miƙewa kanta a ƙasa hawaye na zuba a idanunta. "Don darajar da Allah Ya yiwa Manzon Sallallahu alaihi Wasallama ka saurare ni, ba zan taɓa juya maka baya ko da nasani b a kasancewa ta da kai, kai musulmi ne nima musulma ce babu haramci idan mace ta ƙaunaci namijin daya kwanta a ƙasan zuciyarta, a kullum na ganka sai na ji zuciyata na kiran Safiyyerh wannan shine ƙaddararki zaɓin da kike jira irin namijin da kike fata, idan zuciyata ta kusanci zuciyarka sai na ji tawa zuciyar ta sake buɗewa da tarin tausayinka, kullum mutuwa nake da farfaɗuwa da soyayyarka ta yan kwanakin nan data rutsa da zuciyar Safiyyerh Abdu Marafa, kullum mutuwa nake da son ka, wallahi...," kasa cigaba ta yi saboda kukan daya ƙwace mata da gaske, da ace ita ƴar wasan kwaikwayo ce irin fina finai da ake haskawa sai ta ce a yanzu acting take, duk abin da take faɗa she doesn't mean it, iya laɓɓanta ne kawai ta yi hakanne saboda ta yi kutse cikin rayuwarsa ta san waye shi me ya sa ya zama abin da ya zama, tana son jin labarai mai kama da hikaya ko almara ko na soyayya. "Will you love me?" Ta ce tana marairace masa fuska tare da ɗan turo masa jajayen cute lips ɗinta, ya bi lips ɗin da kallo ta haɗe hannaye waje guda ta langwaɓar da kai "Please, Safiyyerh loves you a nan a cikin nan ɗina" Ta nuna masa saitin ƙirjinta wajan zuciya da yatsarta manuniyya sai ƙifta idanu take. Har lokacin bai ce mata komai ba kamar yadda ta lura yawan magana ba ɗabi'arsa bane yana wanzuwa da shiru da tunanin ya fi masa. A duk maganarta ɗaya ƙare haɗe fuska yake yi ya zaro sigari ya kunna ya saka a baki da ƙarfi ya zuƙi hayaƙin yana jin saukar hayaƙin ƙasan ƙirjinsa ya hura kumatu ya matsa dab ya fesa mata a fuska ya yi gaba abin shi yana taku ɗaiɗai irin he don't care. Safiyyerh ta bisa da idanu ta yi shiru ta ji ta damu sosai a ranta tana Astagafirulla data tuna da gaske ita matar aure ce matar Aliyu Abdu Marafa ce ita halaliyyarsa ta jingina da jikin bango tana lumshe idanunta. Moh bai ƙara dawowa cikin gidan ba, har dare ya nutsa bama shi ɗaya ba kusan dukkan su basa nan ta dinga sallah tana addu'a har girki ta yi musu ta ajjiye amma ya yi sanyi. Tana haka ta ji an buɗe gidan da sauri an shigo ta buɗe ƙofa ba tsoro ta fito Mangal sai nishi yake yana kallon ta, da gudu Goje shima ya shigo yana shigowa kuma ya rufe ƙofar ya zube a ƙasa ta kalle su cikin sigar damuwa ta ce "Ka rufe ƙofar shi kuma fa?" "Bai shigo ba?" Ta jinjina masa kai ya miƙe tsaye ya ce "Jagwal kenan, ai kuwa bama tare" "Innalillahi kamarya like how bakwa tare?" "Ke bafa wani abu saɓe kawai ki je ki yi kasa ko". "A'a don Allah ka je ka nemo shi ka ji ɗan'uwanka ne fa idan wani abu ya same shi ai ba za ka ji daɗi ba, shi ma ba zai bari komai ya same ku ba" ya yi murmushi ta lura yana da fara'a ba kamar sauran ba "Ubangiji nada kyakkyawan tanadi a rayuwar Mai dawa, ba yanzu zai mutu ba kin ji ko?" "Na kawo muku abinci?" "Dar daidai kenan kin taimaki ƴan hanjina jagwalo shi nan a ɓatar da shi a rufawa ciki asiri" abincin ta ɗakko ta kawo musu duk yadda taso su wanke hannu ƙi sukai Kodayake haka ogan nasu shima yake. Har bacci ya ɗauke ta bata saka shi a idanunta ba. Sai da asuba ta fito dafa ruwan wanka kamar jiya haka ta ganshi ya yi shiru yana kallon sama, tunanin maganganun da Abbasa ta yi masa yake da abin da Ali wali ya dinga nanata masa akan Safiyyerh. "Bai kamata gwarzona ya wanzu yana tunanin da zai iya illata masa rayuwarsa da zuciyarsa ba, haba mafaraucina" ya juya ya kalle ta, ta kashe masa idanu ta ce "Yes, ba farautar dabbobi kawai ka iya ba ka yi dacen farautar zuciyar ƴar Professor Abdu Marafa" kamar a buge yake haka ta lura da shi musamman yanayin zaman da ya yi, sai a lokacin ta lura da yankan dake damtsen hannunsa ta ƙarasa ta duƙa ta ce "Subuhanallahi faɗa ka je ka yi haba mai sunan manya, Muhammad Mutallab fa masu sunanku salihan banyi ne" Ya duƙar da kan shi ƙasa ta je ta ɗakko kayan da Goje ya kawo ta zauna dab da shi, ta kamo hannun nasa sarai ya jita amma bai kula ta ba, tunani ne ya addaba masa. Ya shiga hura masa iskar bakinsa ganin yankan na kumfa data saka magani ta gama yi masa treatment ta kalle shi taga ya rufe idanu miƙewa ta yi zata fita kamar daga sama ta ji ya ce "Cikakken sunanki" "Safiyyerh Abdu Marafa" "Cikakke" ya sake maimaitawa "Haka sunan yake fa Jarumi" "Shi Abdu?" "E, sunan daddy kenan Abdu" ya buɗe jajayen idanunsa ya watsa mata su ta yi saurin yin ƙasa da nata idanun ta fidda ran zai yi magana har zata juya ya ce "Ƙarya, idan na tuna miki na kwaɗa miki mari ko?". "Allah ni dai haka na sani babana ne fa" "Uhmm" ganin kamar da magana a bakinsa kuma a buge yake ta matsa ta zauna ta ce "Jarumi, do you want to say something? Say it. Ka ce wani abu Jarumi" "Faɗi mana Jarumi" "Tiger" ya ce a hankali ta ce "Me ka ce? Ban ji ba" "Ammm, hmm kika ce ba ki da aure?" Ta ce "E, bani da shi like a told you" ya buɗe ido ya zura mata idanu yana ta kallon ta da ƙyar ya iya cewa "za ki so ni?" "Zan aure ka na rayu da kai idan ka faɗa mini labarinka waye kai?" Ya sake yi mata shiru "Ina ji" "Zana ba ki labarina idan za ki aure ni" "Ni Safiyyerh na yi maka wannan alƙawarin zan rayu da kai a duk yadda rayuwa ta yi da kai Jarumi" ya miƙa mata tafin hannunsa a hankali kamar mai jin tsoro ta kalli hannun cike da rashin fahimta, jiran ba'asi take shi kuma ya yi shiru sun ɗauki minti biyar da wasu daƙiƙo a hankali ya sake furta "Promise" ta dinga kallon hannun kafin ta yi Astagafirulla da tunanin Ubangiji ya yafe mata saboda igiyar auren wani ce a kanta ta ɗora ɗan ƙaramin hannunta cikin nasa, tana sawa ya damƙe kamar abin da yake jira kenan ya yi shiru ya lumshe idanunsa muryarta na rawa ta ce "I Promise you Jarumi" yana riƙe da hannun bai cika ba bai kuma yi magana ba can ya sake ta, ta fara masa magana sai dai ko tari bai kuma yi ba tunaninta bacci yake yi ta dinga kallon shi tana son hango kyau ko ko muninsa. A daren ranar su Goje basa nan sai shi ɗaya yana busa hayaƙi a sama yake jinsa sosai ya ji an buɗe ƙofa an shigo, maza ne har su huɗu sun rufe fuskokinsu ya damƙi wuƙarsa kafin ya miƙe ɗaya ya cafki wajan yankan da Safiyyerh ta gyara masa ya janyo hadda naman wajan suka fara kokawa yana buga su da ƙasa, cikin sauri Safiyyerh dake bacci ta farka zata fito daga cikin ɗakin ya yi baya da ƙarfi ya tura ta ciki ya rufe ƙofar ta taga ta leƙo tana kiran shi, taga ya ɗaga wuƙa ya sokawa ɗaya a gefen wuya ya ƙara soka masa a ciki ya watsar da shi can gefe yana kakari, Safiyyerh ta zaro idanu tana rufe baki saboda ihu za ta yi ganin yadda aka yi kisan kai akan idanunta, bata san mene ya faru ba taga ɗaya ya zaro sirinjin allura ya zirarawa Moh a damtsen shi, ya sake zaro wani ya yi masa da azama Moh ya ɗaga wuƙar hannunsa ya sari wanda ya yi masa hakan ya goce ganin sun yi masa allurar suka ja wanda yake kwance kamar gawa suka bar gidan, a hankali ya yi baya ya zube saman kujera jini na ɗiga jikinsa Ilahirin jikin Safiyyerh rawa yake cikinta ya ƙulle ta shiga uku, kisan kai aka yi akan idanunta haka dabar take dama? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Moh kuma minti goma ya yi yawa ya ji zufa na yanko masa jikinsa ya yi sanyi wani irin baƙon al'amarin ya fara ziyartar gangar jikinsa yana sauka a mararsa, abin da bai taɓa tunani ba idanunsa ya shige ciki ya ɗauki ƙwaya ya zura a ƙasan harshen shi da tunanin zai daina ji, amma ina kan shi ya hau ciwo ya miƙe da ƙyar ya nufi ɗaki jin tsigar jikinsa na miƙewa da zubewa sanyi na ratsa shi komai na jikinsa ya bubbuɗe al'amarin buƙatuwar wani abu. Ya kwanta ya yi shiru can ya mirgina ya yi rufda ciki ya lumshe idanunsa ya jiƙe shimfiɗar lokacin ɗaya da zufa da jinin da yake zufa a jikinsa, ya rasa ciwon ciki yake ko mara ko zazzaɓi? Jijiyoyin kan shi sun miƙe raɗau lallai ya ji akwai abin da yake buƙata ya dinga juyi ya shanye sigari kwali wajan biyu amma ba abin da ya sauya ba zai ce tsautsayi ne ya kai shi ɗakin Safiyyerh ba saboda kawai tsintar kan shi ya yi a ciki. Safiyyerh na bacci ta ji hucin numfashin mutum a fuskarta ta buɗe idanu da sauri ihu za ta yi ganin fuskarsa kamar zai haɗe da tata ta yunƙura zata tashi ya saka hannu ya mayar da ita kwancan "Dan Allah karka mini komai ka yi haƙuri ba zan sake kula ka ba, innalillahi na shiga uku daddy ka yi na tuba don Allah" bai kulata ba yana daga durƙushen da yake dab da ita ya miƙa hannu ya kashe wutar ɗakin gabaɗaya. LAST FREE PAGES Waye Mutallab? Waye Scorpion? Wace Safiyyerh? Waye Daddy? Mene FS WORLD INVESTMENT COMPANY? Labarin Mutallab da tarihinsa ya fi wannan da muke ciki yanzu ai za ku zo jin wannan soyayyar ta ƙuruciya ba? Mene yake saka a fara daba da shaye-shaye? Wanne ganganci iyaye suke yi akan yara? Mece siyasa da cikakken tarihin dimokuraɗiyya? Za ku su sanin ya ake mulki a ƙasar nan? Har ku yi supporting yaran ku? Soyayya na saka shaye-shaye ne ko daba? Me ya sa Mata har uku suka mutu ta sadanadin MOH me ya sa ya kashe matarsa SAFIYYERH? YAUSHE SAFIYYERH TA HAIFI YARO? maza hanzarta yin payment chat with me on WhatsApp 08164069385 BRIGHT PENS... 2ND BATCH 🔥🔥