🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Bismillahir rahmanur rahim Page 1-5 part two (2) Aiban yana fita da Najma kai tsaye hospital dinshi ya wuce da ita,fadin tsantsar tashin hankalin da yake ciki ma b'ata lokaci ne,gaba d'aya ya rasa me yakeyi masa dadi a rayuwa ya rasa gane shin sama yake ko k'asa,miyan bakinsa ya k'are bayajin zai iya furta ko da kalma d'aya karanto duk wata addu'ar da tazo bakinsa yakeyi,ga kukan Nani da yakeji har cikin ranshi dan shikan baya san kukan mace balle babbar mata irin Nani.ko daidaita parking beyi ba ya fito da sauri tare da daukar Najma yayi ciki da sauri Nani na biye dashi kai tsaye Emergency ya wuce da ita,nurses ne suka bisa baya tare da abokinsa Dr Auwal,d'aya daga cikinsu ne ta rike Nani tace"kiyi hakuri malama bazaki iya shiga ba"janye k'ofar tayi tare da rufewa,wani kukanne ya Kuma kwacewa Nani ta zauna a chair bakin wurin ta rasa abun yi,addu'arta kawai Najma ta samu lafiya,dan idan ta rasa tasan tabbas bazata kumayin rayuwa mai dadi ba. Duk'ufa Dr Aiban da Dr Auwal sukayi akan Najma amma ba wani labari,dafe kai Aiban yayi yace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"dafasa Dr Auwal yayi yace"kayi hakuri abokina,ae munyo sa'a da allurai bata gama cika kwanankinta ba kaga akwai yiwuwar bata gama shiga jikinta ba,insha Allah zamu gwada wata hanyar yanzu"cikin sauri Aiban yace"Dr Naman,bara n Kira shi yanzu"Dr Naman zaune yake a k'asar India,shine farkon malamin Aiban lokacin da yake k'asar India yin karatun likitanci,babban likita ne da akeji dashi a k'asar,yana matuk'ar son Aiban saboda maida hankalinshi da kuma kwazo a wurin karatu.bugu d'aya ya dauka tare da fara magana cikin harshen turanci yace"Dr Aiban ya aeki da k'ok'ari?".shima cikin harshen turanci ya ansa da "Alhmddlh sir,dama na kiraka ne akan wata matsala"natsuwa Dr Naman yayi kamar Aiban na a gabanshi yace"ina jinka ".sosai Aiban yayi masa bayanin abunda ke faruwa da Najma .jinjina kai Dr Naman yayi sannan yace"kada ka damu komai zaiyi daidai,ae anci sa'a da allurar bata gama bin jikinta ba,zan fad'a maka alluran da zakayi mata zai tsaida gubar alluran ne,ya zama dole ka taho da ita nan da zuwa gobe kada ka yarda a wuce goben,sai ka kula da fuskar nata ,nasan kasan me zakayi"godiya yayiwa Dr Naman sannan sukayi sallama,cikin sauri ya fita neman alluran balle wahala takeyi yasha wahala sosai sannan ya samota lokacin da yazo Dr Auwal harya gama gyaran fuskar Najma ya rufeta da bandeji ruf baka ganin komai sai farin abu.cikin ikon Allah sukayi mata alluran,sannan ya fita nema masu yarda za'ayi suyi tafiya ba tare da b'ata lokaci ba. A hankali Ahaad ya soma bud'e rinannun idanuwansa wanda suka sauya kala zuwa ja,bin mutanan dake wurin yayi da kallo,sannu kawai su Mummy suke jera masa amma ya kasa ansawa koda mutun d'aya a cikinsu,dafe kansa yayi da yake barazanar tarwatsewa,lumshe ido yayi da k'yar Mama ta lallab'ashi yasha magani sannan ya koma barci,"daga ina kike ke Kuma"Mummy ta jefawa Fadila tambaya.turo baki Fadila tayi tace"Wai Mummy ni kamar wata k'aramar yarinya zaki sakani gaba da tambayar ina naje"share maganar Mummy tayi kawai tace"Wai baki San meya faru da y'ar uwarki bane?"yatsina fuska Fadila tayi da nuna alamun k'osawa da magana tace"naji waye a garin nan da Wanda ma baya cikinsa zaice be sani ba,an tab'a yarinya mai tashe da dukiya daji da kyau,ae ko ina ya dauka an watsa mata acid an Kuma kasheta an sace gawar,ni zanje ciki na huta".bata jira cewar Mummy ba tayi ciki abunta tana kunshe dariyar muguntar da takeyi. Aiban kam be koma gida ba sai wurin 11 sai da ya tabbatar ya had'a komai na tafiya,Kuma be wani sha wahala ba kasancewar da marar lafiya za'a bar k'asar,da shi da Nani da Dr Auwal ya tsara tafiyan,yana shigowa Hajiya Sadiya ta jefo masa tambayar da yasa y'an cikinsa juyawa"ina fatan bakai ka dauke Najma ba?,bazan tab'a yarda wata alak'a ta kullu tsakaninka da wannan shed'aniyar ba"Hajiya ta Kuma maimaita tambayan,a tsarinshi baya yiwa Hajiya k'arya komai yana k'ok'arin fad'a mata Amma wannan karon saiya tsinci kanshi da fadin "ko kusa Ummana,ni tun da mukaje da Shuhada d'azu gidan to ban sake komawa ba ae,Allah ya tsare gaba ae naji abunda ya faru"tab'e baki Hajiya tayi tare da wucewa d'akinta bata bashi amsa ba.shafa kanshi yayi ya mike tare da nufar part din shi a hanya ya had'u da Muslin ,kallon Muslin yayi fuskarsa dauke da damuwa ,"wai lafiya kuwa?,me yake damunka ne?"Aiban ya tambayi Muslim,had'iye yawu Muslim yayi yace"bari bro ina cikin tashin hankali,shi wancan uban zuciyar yayi saki cikin fushi,gashi yanzu Kuma yazo ya damu da acid din da aka zubawa yarinyar abun d'aga hankalin shine ko gawarta ba'a gani ba,Kuma babu wanda yasan Wanda yayi mata haka,ga Shuhada can na rasa ya zanyi da ita,ni kaina inajin babu dad'i dan inajin Najma tamkar yarda nakejin su Islam a raina"."Allah sarki sai hakuri kayi k'ok'arin shawo kan Ahaad insha Allah zan kula da Shuhada ita Kuma Kuma Najma Allah ya bayyana mana ita,nima dauriya kawai nakeyi.yana tura k'ofar d'akinshi ya hango Shuhada zaune ta had'a kai da gwaiwa sai rafsar kuka takeyi,da sauri ya k'arasa ciki yace"haba haba mana my sweet sis,meye abun kukan Kuma?,ina Ahaad din ya saki matar da aka daura masa a gabanki ?meye Kuma na kuka irin haka?"Aiban ya fad'a,cikin muryar kuka tace"haba Yaya ni yanzu bata wannan nakeyi ba,kaji zalincin da aka aekatawa Najma amma kai kamar baka wani damu ba,nu ina Santa har'a Raina ina jinta kamar ya yarda nake jinku ,duk yarda akayi wannan bak'in zslincin nasan makirci ne"."ya isa haka bana sonji,kiyi hakuri kiyi mata addu'a insha Allah komai zaiyi daidai bana son kuka irin haka"da irin wannan kalaman Aiban ya kwantarwa da Shuhada hankali har ya samu ta daina kuka Kuma ta tafi ta kwanta. Tunda asubar fari Aiban yayi sallama k'ofar d'akin Hajiya,ansawa tayi tana fadin"shigo mana Muhammad aena tashi",shiga yayi samunta yayi zaune a bakin bed tana sanye da hijab da alamaun sallah ta gama,duk'awa yayi har k'asa yace"Hajiya ina kwana?,an tashi lafiya?".cikin sakin fuska da tsananin soyayyar d'an nata tace"lafiya qlau Muhammad,lafiya na ganka da sassafen nan?".sun kuyar da kai yayi cikin jinjina maganan da yakeson yi mata can k'asan mak'oshi yace"Hajiya zan tafi wani aeki India yanzu da safen nan"."Muhammad yanzu kuwa ,tafiya har India ba shiryawa tafiya"."Hajiya tun jiya nasan da tafiyar to ganin ban dawo da wuri ba shiyasa ban sanar maki ba,aekin na gaggawa ne,kuma munyi magana da Abba a masallaci yanzu ,zanyi kusan sati biyu a can"jinjina kai Hajiya tayi tace"to shikenan ae da yake sha'anin aekin ceton rai ne,Allah ya bada sa'a ya kuma tsare"da Ameen kawai yake ansawa sannan ya taso ya fito domin shiryawa.zuwa k'arfe takwas ya gama shiri har breakfast yayi dan Hajiya tsareshi tayi,sallama yayi da mutan gidan sannan ya fita,adaidaita yahau ta k'arasa dashi asibitin,kai tsaye Emergency ya wuce ya samu Najma tana nan yarda ya barta sai dai an shiryata shi kawai ake jira su wuce airport,shafa kan Najma yayi cike da matuk'ar tausayi yayi magana a hankali yace"Allah ya baki lafiya Khadija,Allah Kuma yasa fitarki k'asarnan ya zama warakar dukkanin wani abu dake damunki,Allah yasa ki samu sabuwar rayuwa ki mance da burikan daukar fansa dake ranki dan ba'a gyara b'arna da b'arna".guntun hawayen dake idonsa ya goge aka tura gadon da take aka sakata a motar asibiti sannan suka dauki hanyar airport,lokacin da suka isa kusan jirginsu na haramar tashi dan haka basu wani b'ata lokaci ba suka shiga cikin mintoci jirgin nasu ya lula cikin sararin samaniya suka doshi k'asar India. Tunda ya tashi ya soma had'a kayanshi a akwati ,duk wani abunda yake buk'ata sai da ya had'ashi sannan ya dauki wayarsa daketa faman ruri murya can ciki yace"ya akayi ne?",lumshe ido Muslim yayi yace"haba Sulaiman yanzu bazaka d'aga tafiyar nan ba?,ka duba jikinka ko kwari babu Kuma bamu k'arasa abunda ya kawo mu ba"."kaga malan idan zaka je ka shirya in Kuma baka zuwa ni yanzu zan Kama hanya"be jira ansar Muslim ba ya kashe wayarshi,akwatinshi ya janyo daidai na matafiya ya fito yakoyi sa'a duk suna dining suna break ,ciki ciki ya gaishesu sai kuma yayi shiru daga duken da yake,Mummy tasan y'an mishkilancin suna saman kai idan za'a shekara a haka bazai ce komai ba shiyasa tace masa"Ahaad tafiya zakayi ne?"kai kawai ya iya d'aga mata alamar eh,"haba ka zauna ka idasa warkewa mana"girgiza mata kai yayi alamar a'a ya mik'e tare da d'aga masu hannu yasa kai ya fice,yaransa suka karb'i kayan dake hannunsa ,sannan suka jera motocinsu suka fice a hanya suka d'auki Muslim dan haka suka dau hanyar Niger Delta". Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe. Kamar kullun majidadi ta dawo,ina fatan yarda muka fara lafiya Allah yasa mu gama lafiya,sannan Kuma inji ruwan comments kamar yarda aka saba mu farantawa juna rai. Stylish star Jorderh majidadi Page 6-10 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Ga mai neman bayani akan sabon book dina*DIKKO AHMAD* mai fita gobe ya tuntubi 07033636337 Birnin India Jirginsu ya sauka a garin Mumbai ,juye juye yakeyi yaga ta ina zai hango Umti motar asibiti ta k'araso lokacin da ake fitowa da bed din da Najma take kwance tamkar gawa,can ya hango Dr Naman da Umti,murmushi Umti ta sakar masa sannan sukayo inda yake,rungumeta yayi tare da sakin ajiyar zuciya cikin muryar dake son sakin kuka yace"Umti kinga yarda suka mayarmun da ita ko?"bubbuga bayansa tayi tace"ni dai Aiban dina jarumi ne,dan Allah ya daure komai zaiyi daidai insha Allah"(Umti itace Aunty Maryam k'anwar Aunty Sadiya ,Kuma mahaifiya ga Shuhada da Muslim).risinawa yayi tare da gaishe da Dr Naman shima murmushi yayi sanann ya rungumo Aiban zuwa jikinshi,Umti gaisawa sukayi da Nani ta Kuma jajanta mata,tun a nan Nani ta gazgata tsananin kirkin Aunty Maryam,mota suka shiga tare dabin bayan motar asibitin ,kai tsaye asibitin Dr Naman aka kaita Wanda suke had'in gwaine da Aunty Maryam,d'aki na musamman aka kai Najma cikinsa duk injina da na'urori na gwaje gwaje.office din Umti aka kai Nani ,sannan su Kuma suka duk'ufa akan Najma da take k'afa d'aya duniya d'aya lahira,sosai manya manyan likitoci suka duk'ufa a kanta dan ceto ranta,ajiyar zuciya Umti ta sauke tace"Alhmdllh,nasara ta farko da muka samu shine allurar ko kad'an bata tab'a cikin dake jikinta ba"gyad'a kai kawai Aiban yayi yace "Umti what about her?",dafa kafad'arsa wani baturen Dr yayi yace "soon komai zaiyi daidai"wannan maganar da sukeyi duk a harshen turanci ne.wata allura Dr Naman yayi mata suka tsaya jiran tsammani tare da mak'ala mata wata na'u'ra mai danjoji,addu'a Aiban ya somayi yana a matuk'ar tsorace dan wannan ne lokaci na k'arshe in bata farka ba sai dai ayi hak'uri da ita.ganin danjar jikin na'u'rar zata kawo yayi saurin rintse idonsa ya rike Umti sosai yana karanto duk addu'ar da tazo ransa dan nesan wacce kala ce zata kawo ba,dit dit haka na'u'rar ke k'ara tare da halba tsanwar danja,"Alhmdllh ya Allah,Alhmdllh"abunda Umti ta fad'a kenan,godews Allah Aiban yaci gaba dayi cikin tsananin farin ciki da jin dad'i,ganin Najma ta farfad'o har k'afarta na motsawa.sosai Drs din sukaji dadin nasarar da suka samu,kula ta musamman suka bata sannan aka saka Nurses kula da ita office din Dr Naman sukaje hannu ya bawa Aiban yace"congratulations,na tayaka murnar dawowar y'ar uwarka,insha Allah nan da kwana biyu za'a iya bud'e mata fuska Kuma allurar barcin da aka mata zata saketa,sanann Kuma sai muga wacce hanya zamu b'ullowa fuskar tata"godiya sosai Aiban yayi sanann yayi transfer din kudin da ake buk'ata na aekin yau dan yacewa Umti baya son komai a kyauta ayi mashi kamar kowa.Nani da taji labarin tashin Najma saida ta taka rawar murna,taita zubawa Drs din godiya ,ansha daga da ita sannan aka jata zuwa gida. Tun daga waje Nani ke kallon gidan dukda ba yau bane rana ta farko da ta fara fita waje ba da Kuma zuwa gidaje irin wa'annan,amma ta jinjina kyawu da tsari na gidan,babban gida ne sosai komai a tsare yake kwanin ban sha'awa ko ina ga filawoyi suna kad'awa.tunda suka shiga takebin wani makeken pic da kallo a parlon na wani Dattijo mai tsananin kyau,amma sam ta rasa ina ta tab'a ganin wannan fuskar sai kawai ta share ta wuce d'akin da masu aekin suka nuna mata,wanka ta shiga lokacin da ta fito har an jera mata abinci a madaidaicin table na d'akinta dan haka taci ta kwanta danta d'an huta. Har k'asa Aiban ya d'uka tare da gaishe da Abba,cikin sakin fuska Abba ya ansa yace"watanni da yawa malan Muhammad,sai yau har nayi cigiya na gaji"sunkuyar da kai Aiban yayi yace"Abba ayyukane keyin yawa"."to Allah ya taimaka,naji abunda ya faru Allah ya bata lafiya ya kuma tsare gaba,jibi zanje na dubata insha Allah"Abba ya fad'a,godiya sosai Aiban yayi masa sannan ya wuce d'akinsa ya shirya ya koma asibitin,haka Aiban yaketa d'awainiya da Najma ba dare babu rana ko yaushe yana hanyar asibiti da Kuma kashe mata kud'ad'e. 3days later A hankali Dr Naman yake warware bandage din dake rufe da fuskarta,yayinda take zaune ko hadiye miyau ta kasayi sai fargaba da tsoro,Aiban kam kasa shigowa d'akin yayi,zaro ido Umti tayi tare dayin baya tasa hannu ta rufe bakinta,a hankali Najma ta d'aga idanuwanta Wanda suka zama kalar ja,ta kalli mirror din dake gefenta k'arami,zaro ido tayi tasa hannu a hankali ta shafi gefen hagun fuskarta,wata irin razana tayi ta fasa wata irin razananniyar k'ara ta zube k'asa akan gwaiwowinta,ta fitar da sautin kuka mecin rai. Wani irin zabura Ahaad yayi amma ya kasa furta komai,zuciyarsa sai ambaton sunan Najma takeyi amma saboda tsabar mishkilanci ya kasa furta koda kalma d'aya. "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"shine kawai abunda Najma ke maimaitawa tana sake hararo yarda taga fuskarta gaba d'aya rabin fuskarta ya toye ya jagule ya lalace ta tashi daga Najmarta kyakyawar budurwa,hawayene suka soma zarya a kuncinta,daga Window Aiban yana hangen komai beyi aune ba saijin siraran hawaye nabin fuskarshi yaji. Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 11-15 Shigowar Daddy mijin Aunty Maryam yasa Najma saurin mik'ewa wani irin bugawa k'irjinta yayi da k'arfi ta tsare mutumin da ido,shima ba k'aramar fad'uwa gabansa yayi ba,kallon yadda aka b'ata fuskar yarinyar yakeyi,k'arasowa yayi inda take yace"kefa musulma ce,kiyi hak'uri ki rungumi kaddararki ki zauna kinji ko"ji tayi wani irin nauyin mutumin takeji da ganin girmansa dan haka babu musu ta zauna,tare da sunkuyar da kanta k'asa.d'agowa yayi yace"Dr yanzu meye abunyi game da fuskar nata?"nisawa Dr Naman yayi ya kalli y'an uwan Drs y'an uwansa dake wurin Dr Ishani ne yace"fuskan ya b'aci da yawa bama da wata mafita daya wuce a canza mata fuska"wani irin razana Najma tayi ta d'ago tace"yanzu hazan dawo da kamanni na na asali ba?"gyad'a mata kai yayi alamar eh, innalillahi wa'inna ilaihir raju'un shine abunda take maimaita hawaye na Kuma wanke mata fuska,da sauri Aiban ya shigo d'akin ya Kama hannuwanta yana girgizata ganin tana neman fita hayyacinta sai da yaga tad'an dawo daidai yace"ki kalleni"d'ago idanuwanta tayi ta zuba mashi su,goge mata hawayen fuskarta yayi yace"ki daina wannan kukan,ur d must strongest women I have ever seen,so karki bani kunya,wannan ma wani matakin nasaran ne,ki bari ayi maki aekin nan,cikin kwanaki kad'an zaki warke,ina so kiyi karatu sosai ki dogara da kanki ki haife abunda ke cikin ki,sannan kiyi k'ok'arin had'a kan Family dinki,ki sani ba'a rama cuta da cuta"shiru tayi can tace"to kayimun alk'awari zaka barni na cika mafarkina ina so in zama soja"girgiza kai yayi tare da shafa gefen fuskarta yace"ga iyayena su zama shaida bazan tab'a hanaki cikar burin ki ba".murmushi ta saki tana zancen zuci."to Alhmdllh hakan yayi kyau,ni Kuma na dauki nauyin karatunta da aekin canjin fuskar da za'ayi mata"Daddy ya fad'a.har k'asa Najma ta d'uko tana zubawa Daddy godiya,hannuwa yasa ya d'ago kafadunta yace"kada ki damu,abunda nake so dai karki bani kunya,ki mai da komai ba komai ba kiyi rayuwa kamar kowa,ki dauka mun zama iyayenki karkiyi fargaba a kanmu"har cikin ransa yakejin kaunar yarinyar kallo d'aya da Daddy yayi mata yaji ta gama zama wani b'are na jikinsa,kallon Dr Naman yayi yace"a fara shirya kayan aekin".gyad'a Kai Dr yayi yace"to wanne suna za'a saka mata a rasid'in da takardunta?".kafin kowa yayi magana Najma tace"yarda Kama ya canza dole komai ya canza,ka samun SHUZNA BASHIR"ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.shafa kanta Daddy yayi yace "na gode kwarai da kara Shuzna,kinga yanzu y'an matana biyu Shuzna da Shuhada"dariya Umti tayi tace "baban y'an biyu kenan. Duk yarda Nani taso ganin fuskar Najma hanata sukayi sunsan ba k'aramin tashin hankali zata shiga ba,dan haka sai dai suka ce mata za'a canza saboda wani b'are ya toye sosai,Nani tasha kuka marar misaltuwa amma haka dai ta hak'ura ta zubawa sarautar Allah ido. After 3 days Sanye aka fito da ita da kayan aeki a jikinta fuskarta lullub'e da bandeji,kwance take a bed tamkar gawa ,turata akayi zuwa d'akin da za'a kwance fuskar,kowa addu'arsa Allah yasa anyi aekin a sa'a.Aiban ne ya fara warware mata fuskar sannan ta mik'e zaune amma idanuwanta a rufe tana tsoron ganin yadda ta koma,Daddy,Umti Nani duka suna wurin,"Alhmdllh ,Masha Allah "abunda duk suka fad'a kenan,sab'anin Nani da taketa faman wangale baki tana dariyar farin ciki ga hawaye na zubo mata na dadi, mirror Aiban ya dauko ya kara mata a gaban fuskarta ,a hankali ta soma bud'e idonta wanda yalwataccen gashi ya k'awatashi duk da yadda ta kaga fuskarta kamar ba'a toyata ba Kuma tabbas fuskar da aka saka mata mai matuk'ar kyau ce,lallai Umti tayi mata zab'i na gari sai dai fatanta kada hakan ya janyo wata matsalar Kuma.hawaye Umti ta fara da sauri tazo ta rungume Najma tace"Shuzna basan iya misalta maki irin farin cikin da nake ciki ba,kece kika dawomun da fuskar yarinya mafi soyuwa a gareni,wanann fuskar dana bada aka saka maki fuskar yarinyar da Yayanku Muslim yaso ne wato Zinatu,a daren daurin aurensu ta rasu,y'ar aminiyata tace ita,garinya mai ladabi da biyayyah da sanin ya kamata ,fatana dai Allah yasa ki daukemu tamkar iyayenki".hannu Shuzna tasa ta gogewa Umti hawayenta tace"insha Allah bazan baku wata matsala ba,ni dinnan y'arku ce,Zan bada dukkanin biyayyata gareku kun taimakeni lokacin da nawa y'an uwan suka gujeni"sosai sukaji dadin bayanin nata ,kallonsu Daddy yayi yace"wannan ya zama sirri a tsakaninmu,kada Wanda yasan asalin yarinyar nan Kuma daga yau sunanta Shuzna ta tashi daga Najma,gobe Shuhada zata dawo ina so ku gabatar mata da Najma a matsayin Shuzna Kuma y'ar uwata,nasan zata dauka Kuma tayi tunanin kamace kawai sukeyi da Zeenatu"sai da suka daukar masa alk'awarin rufe sirrin har Drs din da sukayi aekin Wanda Aunty Maryam na cikin sannan ya k'arb'i magungunanta da ita kanta suka wuce gida.harta takardun makarantarta sun koma Shuzna Bashir dan haka aka fara neman mata scul danta dage ba zata bari ta haihu ba,ga ciki harya soma d'an nunawa a jikinta,saukinta d'aya bata laulayi mai wahala bazaka tab'a gane a lokacin tana da ciki ba. Girke girke aketayi a gidan fitowar Shuzna kenan daga d'akin da aka bata ta safko kitchen ta nufa ta samu Umti suna aeki tare da masu aeki,sirrinawa tayi tace"Umti barka da safiya,sannu da aeki"murmushi Umti ta sakar mata tace"yauwa y'ata Shuzna sannu da tashi"d'aukar rova da Shuzna tayi yasa Umti k'arb'a tace "a'a y'ata jeki zauna ki huta yanzu jikin naki ya fara nauyi,ae munma gama rigimar Shuhada ne yasa aka yi aekin nan da yawa".jin ihun murnar Shuhada yasa suka gane har Aiban ya dawo daga d'aukota daga airport kenan,Umti kawai take kwalawa kira,ta shigo kitchen din da gudu turus ta tsaya tana kallon Shuzna tace"wow Masha Allah ,Umti ina kika samo mai Kama da Aunty Zeenat?"ta k'arashe maganar tana rungume Umti,dariya Umti tayi tace"y'ar uwar Baffanku ce tazo daga Canada y'ar Auntynku data rasu"hannu Shuhada ta mikawa Shuzna tace"am Shuhada nice to meet u"dan a tinaninta Shuzna batajin hausa ma.fara'a Shuzna ta fad'ad'a duk da sarai ta gane Shuhada amma ta wayence tare da mika hannu itama tace"naji dadin haduwa dake Shuhada,sunana Shuzna "zaro ido Shuhada tayi tace"la ashe kinajin hausa,Allah nayi tunanin bakiji dan wannan kyau ae sai a dauka balarabiya ce ke"dariya duka suka saka sannan ta janyo hannun Shuzna da sauri wai su fita da sauri Umti tace"ke malama kiriniya kiyi a hankali tana da juna biyu"turus Shuhada ta tsaya tace"u mean matar aurece Umti?"."eh amma sun rabu da mijin shiyasa ta dawo zata zauna damu"cike da matuk'ar tausayi Shuhada tace "Allah sarki Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi".da ameen suka ansa sannan suka fito,Shuhada sai zubawa Shuzna labarin garin lagos takeyi,cikin rai Shuzna tace lallai rayuwa wai mahaifata ake bani labari irin haka.kafin kace me har Shuhada ta Kira Muslim ta fad'a masa y'ar uwarsu mai Kama da Aunty Zeenat tazo,shikam bancin aeki yasha kanshi niya yayi ya gudo yazo yaga mai Kama da zeenart dinshi. Bayan wata hud'u. A yanzu rayuwa kam ta matuk'ar camzawa Shuzna ga wata irin Shak'uwa da sukayi da Shuhada komai tare sukeyi sun zama kamar y'an biyu,a dole Shuzna ta hak'ura da school saita haihu saboda tun wata biyar cikinta yayi wani irin nauyi ya fara girma sosai ga kumburin k'afa data fara fama dashi,sai dai computer scul da taketa zuwa danta k'ara gogewa kafin ta koma makaranta,Shuhada ma tsaida karatun tayi duk da ita Law take son karanta sai dai ta koma zuwa computer scul din itama.sanye ta fito da doguwar riga batayi wani k'iba ba sai dai jikinta ya canza ga ciki ya fito mata sai dai tayi wani irin haske da kyau,wani irin fad'uwa gabanta yakeyi tunda ta tashi yau,da k'yar take janyo k'afarta harta safko daga stairs da sauri Shuhada ta k'araso tare da riko hannunta tana mata sannu dariya Shuzna tayi tace"sai kace wacce take dauke da wasu uwayen kaya?","ae yanzu kinfi ma koma fama da nauyi,Allah dai ya raba lafiya"ta rikota ta taimaka mata suka zauna a chair d'agowar da zatayi sukayi ido biyu da Ahaad kallan kallo aka shiga yi tsakaninsu,kauda Kai Shuzna tayi tare da tab'e baki wata irin tsantsar tsanar Ahaad takeji a kanta da k'yar take had'a yawu har wani d'aci d'aci takeji a mak'oshinta maganar Shuhada ta dawo da ita daga tunanin data tafi ta d'ago tana kallonsu wannan shine"Yaya Muslim sai wannan Yaya Ahaad ,shima kamar d'an gidan nan yane,duk in sukazo garin nan anan suke zama"gyad'a Kai tayi ganin su Umti sun tsareta da ido yasa tace"sannunku da zuwa ,ina wuni".da "lafiya "kawai Ahaad ya ansa ya wuce ciki abunsa.shikam Muslim zama yayi yana kallonta yana jinjina tsananin Kama tsakaninta da Zeenat ji yayi ciwansa ya zama sabo Amma a haka ya daure ya ansa gaisuwar sannan shima ya wuce ciki. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe. Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 16-20 Sosai Umti ta fahimci halin da Shuzna take ciki dan haka ta matso kusa da ita tace "taso muje d'aki ina son muyi magana"yunk'urawa Shuzna tayi Umti na rik'e da hannunta sai jera mata sannu Nani takeyi ,suna shiga d'akin Umti a gefen gado suka zauna duka hannuwanta Umti ta Kama tace"Khadija ki tattaro duka hankalinki ki bani,naga yanayin da kika shiga Kuma na fahimta lokacin da kika ga Sulaiman,Sulaiman dai anan yayi karatu gidan nan tamkar gidansu yake,baya da maraba da d'ana Muslim,ni ina da tabbacin Sulaiman bazai wani kulaki a gidan nan ba,to kema ki share kada ki sake ki bashi k'ofar dazai gane kece Najma,ki bari harya safko da kanshi ya nuna soyayyarki sannan ki bashi kai"a matuk'ar razane Shuzna ta d'ago dara daran idanuwanta tana kallon Umti cikin k'asa da murya tace"Umti har abada,har abada bazan tab'a iya komawa gareshi ba"murmushi Umti tayi tace"y'ata kada fushin yayi yawa,kici gaba da addu'a insha Allah komai zaiyi daidai,Ahaad ba mugu bane kawai kun samu matsalan fahimta ne". "Wallahi ki taso in yi tafiyata ni kad'ai ,bana so ruwa ya samemu a waje,yau tafiyan bamai nisa zamuyi ba"Shuzna ta fad'a tana k'ara kallon bubun dake jikinta na atamfa,murmushi tayi ,hannu Shuhada ta karkad'a akan fuskar tata tace"yadai uwar biyu,ko sirikin nawa yayo waya a sasanta ne kike ta cika fuska da fara'a haka"yunk'urawa tayi zata kamo Shuhada,aeko ta kauce tana babbaka dariya"wallahi zanyi maganinki a gidan nan,inawa kaina dariya ganin nasa atamfa,inaga tun ina yarinya na yarda saka Kaya haka ko da nayi auren bana sakawa"."Kuma kinsan kinyi bala'in Kyau sosai,fatana dai Allah ya saukeki lafiya mu koma school".haka suka fito suna tattaunawa gwanin birgewa suka Umti da Nani sallama suka fita a k'afa dan Shuzna ta samu ta motsa jikinta.fitarsu ba dad'ewa sama tayi bak'inkirin hadari ya soma cida iskar damuna mai sanyin dad'i ta fara kad'awa ko da wanne lokaci ruwa zai iya tsugewa,kamar Shuzna zatayi kuka ta k'ara k'ank'ame d'an k'aramin gyale dake jikinta tace"wayyo Allah,bana son ruwan nan ya tab'ani".kallonta Shuhada tayi tace"aeko to inmun tsaya bamu san yaushe ruwannan zai Kai ba,gashi babu abun hawa,ki daure mu k'arasa".Jan k'afa kawai Shuzna takeyi dan takai k'arshe ji takeyi kamar zata fad'i a wurin ga sanyi da takeji har k'arma ta soma,jin ruwan ya fara sauka yasa Shuzna lunshe idanuwanta tanajin safkar ruwan har cikin ranta,kafin wani lokaci sunyi sharkab da ruwa har d'igan ruwa sukeyi. Motace ta gittasu sai dai baka iya gane waye yake ciki,tsayuwa Shuzna tayi tana mayarda numfashi.motarce ta dawo gabansu ta tsaya,lek'owa driver din yayi wanda yake zaune da kayan sojoji yace"madam ".dariya Shuhada tayi tace"la Samuel"haba bata tsaya komai ba tayi gaban motar tace"Shuzna ki shiga baya zakifi sakewa".da k'yar Shuzna ta shiga k'araso gaban motar,gabant ne yayi mugun fad'uwa,ga k'amshin turarenshi daya addabi hancinta bata da wani zab'i haka yasa ta k'arasa shiga kawai ta zauna.d'ukowa yayi saitin kunnenta yace"y'ar lukuta idan kika fasamun laptop sai dai mijinki ya biyani kayata"ya Kuma juya tamkar bashine yayi maganar ba.dan d'agawa tayi ta zaro laptop din ta daura masa bisa cinyarsa,,hannunta yad'an shafi jikinshi yarrr suka ji gaba d'ayansu,amma ko da wasa bai nuna yaji wani abu ba, kallonta yayi yace"kinji dadi kin tab'ani Kuma kinsan saina rama,idan so kikeyi maza su tab'aki to ki komawa mijinki danmu gidan nan ba y'an iska".sake da baki haka Shuzna ta bishi da Kallo ,ji takeyi ae yama gama da ita,kafin tace wani abu motar ta tsaya kawai sai ta saki kuka ,lokacin har Shuhada tayi cikin gida,shima fitowa yayi ya zagayo inda take yace"malama a fito mana daga mota,dan bama tai maka maki zanyi ba gara ki fito da kanki". k'ok'arin fitowa tayi amma k'afarta ta rike sai kawai ta Kuma rushewa da kuka ta rumtse ido sosai tana yarfa hannu tana fad'in"wayyo Allahna,wayyo Nani ,Ummuna k'afana bazan iya fitowa ba Allah"sosai tayi masa kyau ya saki baki yana kallonta ganin zata bude ido yasa yace"Dallah malama rufemu baki Shagwab'a na yara ne ba tsofi jawarawa irinku ba".maganar ta shigeta sosai ,hannu yasa ya kamota kawai sai ta saki murmushi mai wuyar fassaruwa. Suna shiga parlon tana k'ok'arin kwace hannunta daga rik'on dayayi mata amma sam yaki bata dama.da sauri Umti da Nani sukazo suka kamata suna mata sannu,Umti tace"tun d'azu naketa faman zullimi gashi dai sai da ruwan ya tab'aki,ga Yayanku Aiban can ma yazo tun d'azu yake zaryar nemanki.sai lokacin Aiban ya d'ago yace"Babyn Aiban kije ki canza kaya bana son sanyi ya kamamun ke"dakuwa Umti tayi masa tace"ungo wannan yaushe ka zama marar kunya haka?"sosa k'eya yayi yana dariya,Bayan Nani Shuzna tabi da take cewa"Maza kizo kiyi wanka da ruwan dumi ko zaki daina jin sanyin nan".Ahaad kam bin bayanta yayi da Kallo yadda rigar ta d'ame a jikinta yana kallon yarda hips dinta suke juyawa jin yana neman fad'awa wani yanayi yasa yayi saurin kawar da kanshi suka gaisa da Aiban ya wuce part dinsu,yana shiga ya Samu Muslim yana aekin danna waya,be kulashi ba ya soma zare rigar dake jikin shi,"Wai dan Iskanci mutun ya shigo d'aki amma be iya ko kallon Wanda yake a d'akin ina amfanin bak'in hali wacce ma macace zata iya zama da kai a haka mugu kawai"wani irin duka Ahaad ya kawowa Muslim cikin sauri ya goce ya fice da sauri yana dariya tare da rufo d'akin.kwafa Ahaad yayi ya fad'a toilet. Lokaci na tafiya,kwanaki suna karewa,mintina na tafiya hakan ne ya faru a rayuwar su Shuzna ,cikinta harya shiga watan haihuwa,zaune take a compound din gidan tayi d'ai d'aya akan tabarma tayi wani irin girman ciki ga k'afarta data kumbure ,yau tunda ta tashi takejin wani irin matsanancin cikin mara saboda dauriya ta shanye ciwan taki fad'awa kowa,Aiban ne gefenta yana yanyanka mata apple tana ci,d'ukar da kanta k'asa tayi tana taunar lips dinta kamar zata huda "ciwanne ko?,tun safe ina lura da ke amma kin wani gardama ki tashi muje asibiti"Aiban ya fad'a yana niyar mik'ewa,isowar Ahaad wurin kenan zai dauki wayar Umti data bari a wajen yana d'ukawa yaji an ruko hannunsa ,batasan ta rike hannun Ahaad ba ta k'wallah k'ara tace"wayyo Allah marana,Yaya zata fashe,ku taimakeni dan Allah".a kidime Aiban yace"Ahaad ka sakata mota bara na kira Nani"be jira ansar Ahaad ba yayi cikin gidan da sauri,shikam kallonta yakeyi yadda ta jike da gumi sai siraran hawaye dakebin kuncinta ga lips dinta data taune sukayi jajir dasu,tayi matuk'ar bashi tausayi da sauri ya sab'eta dukda nauyin da tayi haka ya daure ya sakata mota hakan yayi daidai da fitowar Umti da Nani ,Aiban kasa yin komai yayi dan dole Ahaad yaja motar zuwa asibitin. Dr Naman ne da Umti ke kanta,Aiban kasa shiga d'akinma yayi,tasha bak'ar wahala Wanda harsun fidda ran zata iya haihuwa da kanta sai kawai ga kan baby ya taho,yana fitowa kuma wani ya biyo baya,sai kuma ga wani,suka saki kuka a tare Alhmdllh kawai Umti ke fad'a. Bayan minti talatin Umti ta fito ita da wata nurse Ahaad ne kawai a wurin Umti ta saki gud'a tace"yau na zama kaka,kaka Kuma harta y'an ukku,yau bansan wanne irin farin ciki nakeyi ba"ta k'arasa wurin Ahaad tare da daura masa yaro na farko tace"ga Hassan"sannan ta daura na biyu tace"ga Hussain"sai Kuma jikata ta k'arshen mace wato "gambonsu".wani irin Kallo Ahaad yake binsu dashi ganin tsantsar kamarsa da yaran babu abunda suka baro nasa,yayi matuk'ar kidima da ganin wannan kamar,dariya Umti tayi tace"kana kallon kamarku ne ko?,kada ka damu Allah yana iya halitta haka,ina Aiban ne?"kafin ya bata ansa sai ga Nani da Aiban sun iso cike da farin ciki suka k'araso garesa tare da d'aukar yaran suna zumudi dajin dadi,da sauri Nani ta shiga d'akin da aka kai Shuzna ta rungumeta tare da sakin kuka.itama Shuzna kukan ta saki tare da rungume Nani,shigowa Umti tayi ta daura duka yaran akan cinyar Shuzna tace"kibar kukan nan ki kalli abunda kika haifa"a razane take kallon yaran taba kallon Ahaad dake tsaye gabanta. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 21-25 *Wanna page din sadaukarwa ne ga daukacin members na Ruhin fansa Fan,ina matuk'ar jin dadin comments dinku* Wani tunanin ne yazo mata a zuciya tace me hakan yake nufi?,hakan na nufin Ahaad ne yayi rapping dina?,das das gabanta ya fad'i ,no no sun Kama dashi ne kawai dan yana Yayana bayan wannan Babu wani abu Kuma,Aiban ne ya katse mata tunanin sakamakon shigowarsa yana fad'a fara'arsa cikin sigar tsokana yace"sannu da k'ok'ari uwar y'an ukku,haba mutun dama ya zama rusheshe yana cinye tiyan shinkafa a rana ae da walaki"k'ulli Umti tayi masa a baya yace"washh Allah Umti yanzu fa na girma da dukannan,nifa uban yara ukku ne"dariya dukansu suka saka ya kwashi yaran ya tsura masu ido sosai yana jin soyayyar yaran na ratsa shi ta ko ina,addu'a yayi masu,sannan ya bawa su Shuhada da Muslim da suka shigo yanzu, Shuhada sai surutu takeyi ta rike y'ay'a ita a dole itace mamansu.kwanan Shuzna biyu a asibiti aka sallamesu ,Tasha mamaki da suka koma gida siyayyah jibge ta iske a d'aki d'aya Wai dukna yaran ne,Daddy da Umti sunyi nasu,gana Ahaad da Aiban Muslim ma ba'a barsa a baya ba,Shuzna tayi kukan murna tayi godiya kamar zata cire bakinta bata tab'a zatan yaranta zasu samu soyayyah irin haka ba. "Kije inji Daddy yana parlo"Shuhada ta fad'a.mikewa Shuzna tayi tare da sako Hijab dinta ta wuce parlon Daddy,anan ta samu Umti da Nani sai Kuma Aiban.har k'asa ta duk'a ta gaishe da Daddy,ya ansa cikin sakin fuska yana rike da Baby d'aya cike da kulawa ya tambayeta lafiyarta sannan ya daura da cewa"kin zab'awa yaran sunan da kikeso ayi masu hud'uba dashi?"sunkuyar da kanta k'asa tayi cikin natsuwa tace"Daddy duk Wanda aka saka masu yayi"murmushi kawai yayi ya juya ga Aiban yace"Baban yara kayi masu hud'uba da sunan da kaga ya dace"sosa Kai Aiban yayi sannan ya matso kusa da Daddy ya dauki hassan yayi masa hud'uba a kunne ya mik'awa Umti shi yace"Sunansa JAFAR zamuna kiransa(Fayyad)",sannan ya k'arb'i Hussain shima yayi masa hud'uba ya mik'awa Nani yace" Sunansa KABIR zamuna kiransa(Fayyam)",sannan ya k'arb'i mace yayi mata hud'uwa ya mik'awa Daddy yace "Allah ya raya Sha'awanatu zamuna kiranta(Faida)"wani irin bugawa gaban Daddy yayi da matuk'ar k'arfi sanadiyar jin sunan Sha'awatu da yayi amma yayi shiru baice komai ba sai faman Allah ya raya suke fad'a,sanarwar gasar da aka sabayi akan computer duk shekara a k'asar India ne akeyi a television dake kunne,masu kud'i daga garuruwa sukan saka kud'ad'e masu matuk'ar yawo domin a bawa wanda yaci,d'agowa Shuzna tayi tana kallon sanarwar hakanan taji tana sonyi ,kallon yanayinta Aiban yayi yace"zakiyi gasar ne?,tunda naga ke baiwarki a computer yake"murmushi tayi ta d'aga kai alamar eh,daga nan Kuma bai sake cewa komai ba. Yaune suna ansha shagali sosai,sanuwa Daddy ya yanka da raguna Kuma ba wani taro akayi ba kasancewar ba gida bane Nigeria sai dai abokan Umti ne da suka zo yi mata murna,ba laifi Shuzna ta samu kyaututtuka ita da yaranta,sunsha gayu sunsha hotuna ,anyi komai cikin aminci da jin dadi.sai dai muce Allah ya raya mana Fayyad ,Fayyam da Kuma Faida. Bari mu lek'a gida Nigeria. Kishingid'e Mama take a jikin kujera tana kallon Fadila dake zaune da k'atoton ciki a gabanta sai ruzgar kuka takeyi tace"Ae Mama duk laifinki ne,kece kika gayawa Yaya Ahaad ,gashi ya hana a zubar ga dukan tsiya da yayimun wata nawa ina jinya,ki duba kiga duk yarda na fige na lalace"."ohni Khadija naga abunda ya isheni a gaskiya Fadila na gaji da wannan iskancin surutun naki,ni meye had'ina da ke,bancin Kabir daya haifo mani bala'i aeda tuni na koreki daga gidannan ciki Kuma saikin haifa,ko da ubanki kike yawa a ka"Mama ta fad'a tana hararen Fadila,sai Kuma kawai ta fashe da kuka tace"nan nan aka kashemun jikata na rasa gano gaskiya gara ma mutuwar y'an uwanta naga gawar amma ita kamar diyar Baby ace ba'a ganta ba,bazan tab'a yafewa Wanda yasa naci amanar da Jafaru ya barmun ba".wani irin ihu Fadila ta saki ta dafe ciki tana "wayyo Allah Mama mutuwa zanyi cikina,wayyo Allah na Mummy na)da gudu Mummy ta shigo d'akin tana rike Fadila ganin nak'uda ce takeyi yasa sukayiwa Dr Jamil waya yazo gidan.cikin awa d'aya ta haihu y'arta mace kyakyawa da ita ,gyarasu akayi sannan suka fito sai dai Kuma ba zaka iya gane farin ciki sukeyi ba ko akasin haka,ranar suna yarinya taci Bilkisu suna kiranta(Nasirah),sosai Aliyu yayiwa y'arsa sayayyah dan ya k'arb'i cikin,sai dai daga wurin iyayensa ne keda matsalar.ansha shagali sosai . Bayan suna da kwana ukku Ahaad ya diro gari,Fadila na hangoshi tayi d'akin Mama da gudu tana ihun ceto tace"Mama na shiga ukku ga Yaya Ahaad nan,wallahi ya dawo dama yace bazai kuma zuwaba harsai na haihu,kuma ae Aliyun ya k'arb'i cikin yarinyar Mama ki taimaka mun"."ae da yake sadda zaki yawan ta zubar dinki na taimaka maki dole a yanzu ma na taimaka maki"Mama ta fad'a ta gutsirar goron dake hannunta.kai tsaye Ahaad d'akin Mama yayi fuskar nan babu alamun annuri ya dawo Ahaad dinsa na asali,zama yayi a chair ba arziki Fadila ta had'iye kukanta tana k'yarma duk'ar da kansa yayi wanda tun d'azu yake barazanar tsarwatsewa wani wawan Kallo yayiwa Fadila yace"Dan uwarki zonan"sai da numfashinta ya dauke na wucin gadi tace"Yaya kayimun rai,ka tausaya mani kodan y'ar dazan raina y'anzu,wallahi Yaya tsautsayi ne".jin maganar Fadila yasa Mummy da Amaan harda Abba shigowa part din Maman,zama Abba yayi yace"Babana lafiya kuwa?".kasa magana Ahaad yayi ya daura kansa saman cinyar Abba kawai yana sauke ajiyar zuciya."to wallahi kaji da iskancinka Sulaiman,Dan nazaka dakarmun y'aba,cikin shege aeba kanta farau ba,kafin tayi ae wata ta fara lokacin da Najma tayi ae bata fuskanci tsangwama irin haka ba,rubuce yake a kaddararta dama zata haifi Nasirah bata hanyar aure bane". murmushi Amaan yayi yace"Mummy ae ita Najma abun soce shiyasa da taje tayo karuwancin t...."kasa k'ara magana Amaan yayi sakamakon wasu gigitattun maruka da Ahaad ya wankesa dasu,kafin ya idasa dawowa daidai Ahaad ya Kuma shakareshi cikin kausashiyar murya yace"don't u ever say something bad against her,cos i will not tolerate it,Najma ta haihu ne da aure,kuma cikin jikinta nawane,nine wanda yayi rapping dinta,kaga yarana ba shegu bane,Kuma Najma tana nan da ranta bata mutuba kuma ta haihu cikin aminci",sosai idanuwan Amaan suka firfito ko motsin kirki ya kasayi ,kuka Mama ta saka tace"kuna kallowannan bayahuden zai kashemun jika da zuciyarsa irinta arna".da k'yar Mummy ta k'arbe Amaan daga hannun Ahaad, Amaan kam numfashi ya soma daukewa ya rarumi kwalbar ruwan sanyi ya soma kwankwad'a yana maida numfashi.cikin sigar rikidewa Mummy ta kalli Ahaad tace"yaushe ka fara shaye shaye ban sani ba?,yaushe ma ka keb'e da Najmar balle har kayi mata ciki,ina ka ganta kasan tana raye?".dafe kansa yayi alamar gajiyawa yace"ki tambayi wancan makirar yarinyar da yanzu zanwa bugun mutuwa sannan zaki gane".hannu Fadila ta daura a Kai tace "na shiga ukku Yaya,ka rufamun asiri".murmushin takaici Ahaad yayi yace"Alhmdlh Fadila aeni godiya ya kamata nayi maki,duk tsananin kiyayyarku da Najma gashi harta haifaman yan ukku,kinga hanyace kika sharemun tana dawo da auren dake tsakaninmu Kuma ta zauna cikinku,kinci arzikin taimakon da kika yimun da wancan yarinyar da kika haifa wallahi da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba"juyawa yayi zai wuce da gudu Mummy ta cakumo wuyan rigarsa tace"kayi hauka ne?,wallahi indai ina raye jinin Sha'awa bai isa ya kusanto inda nake ba,duk ranar daka maida aurenka da wannan yarinyar a ranar zan tsine maka na Kuma sallamaka gareta,Najma ta mutu karya kakeyi wata ka gani kamar ita"tamkar Mummy ta zare haka takeyin surutai sai da Abba ya kamata yayi d'aki da ita.Fadila kam y'arta ta sab'a tayi d'aki da gudu ta danna Key,dariya Mama ta saka tare da sakin gud'a tace"tace Najma gadon arziki yarinya mai nasara a rayuwa kainuwa dashen Allah,duk lokacin da akaso aga bayanshi sai ki dawo da nasarorinki,tabbas ke jinin Jafaruce sai yau na k'ara tabbarwa. Ahaad kam yana shiga d'aki ya sakawa k'ofar key ya daura kansa bisa gado saijin hawaye nabin gefan fuskarsa yayi. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan karshe Stylish star JORDERH MAJIDADI 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 26-30 Birnin indiya Kamar yarda Shuzna ta nuna ra'ayin ta akan gasar haka Daddy da Aiban suka shiga suka fita tare da saya mata form din suka yi mata komai da ake buk'ata.lokacin da Aiban ya kawo mata takardun ba k'aramin farin ciki tayi ba tayi masu godiya kamar ta ari baki Nani ma ta tayata. A kwana a tashi ba wahala wurin Allah inda rayuwa ke canzawa,ya Kama yaune su Shuzna suke gama wanka,Kuma tun washe garin suna da Ahaad yabar India bai sake waiwayarta ba,hakan yayi daidai da Kuma washe gari zasu gabatarwa da wannan gasar data shiga,tuni an samowa su Fayyad mai aeki sunyi tana kula dasu sunyi wayau sosai.Shuzna kam ta mayar da hankalinta ga bitar gasar da zatayi. Next day. Fitowa tayi sanye cikin shigar farin wando sai top bak'a ta tattare gashin kanta ta saka shoe toms bak'ak'e,sai tashin kamshi takeyi,kallonta Umti tayi tare da sakar mata murmushi tace"kinyi kyau y'ata,amma hakan zaki fita?".kallon jikinta tayi tayi murmushin itama ta koma kusa da Umti ta zauna tace"Umti wannan shine shigar dana saba da ita,hasalima inba da wannan cikin ba bana saka kaya irin namu na hausawa,amma Umti kada kiji komai insha Allah zanci gaba da kare mutuncina kamar a da"shafa gefen fuskarta Umti tayi tace"amma y'ata yanzu kefa uwace".k'asa Shuzna tayi da kanta sannan tace"Umti zama uwa bashi zaisa na canza burikan rayuwata ba,ko Kuma na fasa bin hakkina a wurin azzaluman can ba,na rayu ne cikin burin d'aukar Fansa duk da ba hakan yana nufin nima na zalincesu ba,sai dai kuma bazan tab'a iya yafe masu ba"."Allah ya bada sa'a kije idan kin dawo zan fad'a maki abunda baki tambayeni ba,zan gaya maki dalilin baki fuskar nan da nayi"fitowar Aiban yasa batace komai ba ta tashi suka wuce,tunda suka fito take kallon garin yana matuk'ar burgeta,addu'a kawai takeyi a ranta da neman nasarar abunda zatayi ,holl din cike yake tun a hanyar k'arasowa wurin zaka gane ana babban tarone na k'asashe.wurin da aka tanadarwa wad'anda zasuyi gasar taje ta zauna mutun 10 ne kacal a wurin,bayan bayanai aka soma fara gasar Shuzna itace ta 6 dan haka ta shiga wurin canza kaya ta saka rigarta mai tambatin tutar Nigeria da Kuma number dinta a jiki,ko wacce daga cikinsu wurin computer din da aka tanada ta nufa,kallon abun Shuzna takeyi kud'i ne aka saka wurare daban daban tare da matakan tsaro na na'u'rori duk wanda yayi nasarar had'esu a account d'aya cikin awanni biyar ta shine Wanda yazo na d'aya a gasar,umarnin farawa aka basu dan haka Shuzna tayi Bismillah tare da fara sarrafa computer din ta yadda take ganin zata fi Mata sauki.Aiban ma addu'a kawai yakeyi mata,cikin ikon Allah Shuzna tana ta sarrafa computer bataga wani wahala akan aekin ba amma saiya kasance kai k'warone akanta ita dama ta kasance hakan tun tasowarta babu na'u'rar da bata iya shiga ta lalata ko Kuma tayi abunda take so ta fito,ko da akaje hutun rabin lokaci ita bata bar wurin ba ,dan bata da wani malami Wanda zai k'ara bata haske akan abun.cikin awa hud'u cib ta samu nasarar had'e kud'in a babban account na k'ungiyar sunkuyar da kai tayi tare da fadin "Alhmdllh "sannan ta mik'e,ta mik'a sauran takardun dake wurinta,ba k'aramin mamaki mahukuntan wurin sukayi ba Wai a awa hud'u ta gama wannan aekin,zuwa awa biyar din kowa ya fito daga.sannan kowa ya wuce gida zuwa gobe zasu fad'i sakamako a babban taron da suke shiryawa sannan Kuma su bada kyaututtukan da suka tanada,tana dawowa Kuma ta iske takardun makarantarta Wanda har registration an gama masu ita zata karanci Computer ita Kuma Shuhada Law kowa gidan da fatan alkhairi suke bin Shuzna da mata addu'ar Allah yasa taci gasar,yaran Nani ta kawo mata tace "duk yau kinbar yara da madara kawai yanzu saiki basu abincinsu".turo baki tayi tace"Nani ni dan Allah ki barsu ,na gaji yanzu fa"ta k'are maganar tana shagwab'e fuska ."a'a baza'ayi hakan ba,maza kije ki watsa ruwa ki fito ki karb'i yaran ki dubasu".mik'ewa tayi ta wuce hanyar d'akinsu ji tayi ta bige da mutun ta yo baya tare da fadin"washhh"kallonta yayi sama da k'asa yace"daga Ina kike haka ?"murgud'a d'an k'aramin bakinta tayi tace"inda ka aekeni".zaro ido yayi ya mik'a hannu zai tamk'ota ta shige d'aki da gudu tana masa gwalo.k'wafa yayi sannan ya sauko k'asa,kai tsaye wurin Nani ya k'arasa ya d'auki Fayyam dake ta neman fara kuka,d'agashi yayi yace"no baby boy,meyasa zakayi kuka?"kamar yaji me yace yakoyi shiru yana kallon Ahaad,shikam Ahaad kallon da yakeyiwa yaran na ganin yadda suke k'ara rikidewa ne suna komawa shi yakeyi,sosai ya rungume yaron a jikinshi yana k'arajin soyayyarsu a ranshi.Shuzna kam tana gama wanka ta saka k'aramar riga kawai tayi kwanciyarta ta soma lumshe ido alamun bacci.jin ta dade bata fitoba Nani ta fara fad'a"Allah yarinyar nan taurin kanta ke niyar fara aeki akan yaran nan,ace duk lokacin da akace ki bawa yara mama sai anyi rigima dake,ita aeba haka aka reneta ba,shin me madara zata k'ara yaran nan dashi?".mik'ewa Ahaad yayi yace"Nani bani yaran dolenta ta basu abincinsu kuwa"Fayyad ya dauka mai renonsu ta dauko Faida suka nufi d'akin,be lura da ita ba,hakan yasa ya daurasu saman bed sannan ya juyo ya karb'i Faida,yana juyowa idanuwansa suka sauka akan Shuzna wacce tayi d'ai d'aya a bed iskan AC yana ratsata rigarta ba wani kaurine da ita ba musassaman wurin breast din, idanuwansa suka sauka akan santaleliyar cinyarta fara tas sai shek'i takeyi,idonsa yakai a sauran jikinta ji yayi ya fara k'yarma da sauri ya tauna lips dinsa kamar zai huda, breast dinta yake Kallo Wanda suke tsaye g'yam kamar zasu huda rigai har sawun nipples dinta yana gani ,ganin tana motse motse yasa yayi k'ok'arin daidaita kansa,cikin kausashiyar murya yace"ke,ke"juyowa Shuzna tayi tana binsa da Kallo da sauri ta mike tace"malan me kakeyi a d'akina?"ganin yayi shiru yana kallonta yasa ta kalli jikinta,ihu take da niyar yi da sauri ya rufe mata bakinta da hannunsa,wani irin yarr sukaji su duka biyun,basarwa yayi ya rankwafo daidai saitin fuskarta yace"ke ki rufe mana wannan b'areran bakin nak'i mai Kama da k'ofar tukunya mumuna kawai,meye kike wani neman Hijab?,ni ae banga komai a jikinki da zaki boyeba,shi kanshi mijinki na tausaya masa daya auri kwaila,inma rasa abun Kallo sai bsjawara kwantan wani?Ina saurayi sabon jini?".duk da maganar ta matuk'ar shiga Shuzna haka ta daure tare da ture hannunsa a bakinta tace"Dallah malan daina tab'ani da wannan mugun turaren naka mai saka mutane amai,Allah sai ya rik'a sakawa kanayin wari"ta k'arashe maganar tare da shiga toilet ta wanko bakinta.mutuwar tsaye Ahaad yayi sai Kuma ya saki murmushi yace"kina nan yarda kike,yarana na kawo a basu Nono "wani kallon banza tayi masa tace"hmmm to sannu da k'ok'ari nikam barci zanyi na gaji bana da lokacin wasu yara anan"ta juya da niyar hayewa bed fizgota yayi ta fad'o a kirjinshi sai da ta tsorata da ganin fuskarshi danya koma Ahaad dinshi na asali yace"kada kiyi wasa dani Najma inba haka ba ranki zaiyi matuk'ar b'aci,wallahi ko ki basu ko Kuma ni da kaina na basu",tasan sarai zai iya,a zuciyarta tace kardai ace ya ganeni,a fili Kuma tace"ni wallahi ba y'ar iska bace bare ka tab'amun jiki,Kuma ban bada..."bata k'arasa maganar ba tayi saurin d'aukar Faida ta zaro breast din ta saka a bakinta ganin Ahaad yayo kanta, murmushi yayi yana jinjina k'arfin hali irin na Najma,Faida na kamawa Shuzna ta rumtse ido ta saki siririyar k'ara cikin Shagwab'ar da bata San tayi ba tace"wallahi Yaya da zafi,ni bana iyawa duka ukku fa"ya k'are maganar hawaye na gangarowa akan fuskarta,taci gaba da cewa"ni karka k'ara cemun wata ko Najma,ni ba sunana kenan ba"murmushi kawai yayi ya fita daga d'akin. Washe gari da la'asar suka shirya dan zuwa wajen karb'ar sakamako,duka gidan sukayi Mota biyu suka tafi,Shuzna ansha kwalliya cikin gown purple colour sosai ta matuk'ar yi Mata kyau ga net data yafa a sakan rigar bayan kanta ya sha gyara. Tunda aka fara jawabi babu abunda Ahaad yakeyi sai kallon Shuzna tayi makukar yi masa kyau musassaman da take rike da yaran nata tana sakar masu murmushi,jin an ambaci sunanta yasa ta d'ago a matuk'ar mamaki kowa ita yake kallo yayinda yayinda camerori da dama suke ta faman daukarta hoto,jinjina kai tayi tace"Alhmdllh ya Allah,yau nice nazo ta d'aya a wannan gasar ta k'arashen duniya,a matsayina na y'ar Nigeria"mik'awa Umti yaran tayi ta mik'e tana tafiya kwanin ban Sha'awa ga kowa ta hau step ta k'arasa inda zata k'arb'i lambar yabon tata,wasu hawayen farin ciki ne suka zubo mata,ta soma d'aga abun tana d'aga hannunta,sai wata y'ar China tazo ta biyu sai y'ar nan k'asar India tazo ta ukku,anan take aka bata ATM da komai na account din da aka tanadarwa wacce tazo na d'aya zunzurutun kud'i ne a ciki Wanda anan Nigeria zasu kai kimanin milyan D'ari ukku da makullin Mantions(manyan gidaje)guda biyu d'aya anan indiya sai d'aya a America ga dank'areriyar motar hawa,sai masu tsaronta har mutum hudu ,sai kuma wad'anda suka bata kyauta na mamakin tana y'an Nigeria taci wannan gasa nan fa companoni da dama suka fara kawo mata hari tun a wurin,amma taki sauraran kowa a lokacin,a kai tsaye aka fara haskata a gidajen television da social media kota ina hotunan Shuzna ke yawo ,anyi mata karramawa sosai harda shugaban k'asar Nigeria sai da ya bata kyauta ,tayi hotuna da y'an uwanta Wanda kowa murna yake tayata da fatan alkhairi,a hankali ta taka zuwa gaban Aiban dake tafa mata hannu ,hawaye nabin fuskarta zatayi magana yayi mata alama da tayi shiru yace"ki godewa Allah,ni kawai d'an aeke ne"da haka aka tashi taron suka dawo gida kowa murna fal a ranshi, Shuhada kam ae bakinta baya rufuwa itace ke ansa ma Shuzna murna ma.a gajiye Shuzna take dan haka key ta sakawa d'akinta ta fara farar bacci abunta. *Sai muce ni da Ruhin Fansa Fan muna taya uwarsu Fayyad murna ,Allah ya k'ara arzik'i mai amfani* "Ki shirya kije meeting din gobe,nayi masu alk'awari zakije,kinga Kuma gobe zaki fara zuwa scul"cewar Daddy dake kallon Shuzna. Lallai Daddy ya wuce ya roka wani abu a wurinta,tun bayan wannan gasar take b'oyewa daga duk wasu taruruka amma yau kam tunda Daddy ya rok'a tabbas zataje,kanta a k'asa tace"to Daddy insha Allah zanyi k'ok'arin zuwa". Washe gari tunda wuri ta shirya cikin suit bak'a rigar ciki fara tayi matuk'ar kyau hills ta saka suka bak'ak'e sannan ta d'auki hand bang jelar gashin kanta ta tattare ta daure ta fito rike da key din motarta,kai tsaye wurin Umti ta nufa ta gaisheta sannan ta gaishe da Nani tare dasu Muslim kowa ya ansa a tsaitsaye tasha tea ta sumbaci yaranta ta fita da sauri ganin lokacin ya tafi,babban wurin taron ta nufa,driver na Jan motar da take ciki,sai motar bayanta masu tsaronta su hud'u ,tayi parking inda aka tanada sannan ta wuce ciki,kowa ya taru ita kad'ai ake jira cikin takun k'asaita ta shiga wurin gabanta yayi mugun fad'uwa ganin Ahaad a wurin ,kauda idonta tayi ta wuce inda aka tanadar mata ta zauna ,suka fara gabatar da taron,bata tab'a tunanin Ahaad yana kasuwanci ba sai yau.duka taron ya gudana yarda ake so sai bai wuce kowa dake kawo mata hari akan taje tayi aeki a company dinsu ba,duka ta fad'a masu makaranta takeyi yanzu gaskiya Kuma ita bata sha'awar yin aeki amma zata saka hannun jarinta a wani company na America sai d'aya anan india sai d'aya a istanbul.kuma tace idan suna buk'atar wani abun na b'angaren computer din zatazo ta tai maka,dan ita data gama karatu k'asarta Nigeria zata koma,ba yarda suka iya a dole suka yarda da hakan sannan aka tashi kowa yana k'ara tayata murna,da sauri masu tsaronta suka k'araso tare da sakata tsakiya ta wuce abunta,tana tunanin ashe Ahaad babba ne haka a kasuwanci yana da hannuwan jari a campanoni amma ita bata da wani labari Ashe shiyasa baya zama Kuma ayyuka keyi masa yawa ga aekin soji Kuma yana fama. Lokaci mai tayi baya jira inya wuce ya wuce kenan a kwana a tashi yau gashi Najma ta kammala Digree dinta akan Computer science ta fito da sakamako mai kyau tayi matuk'ar farin ciki sosai, a lokacin yaranta na da shekara 3 ,ga kasuwancinta ta ko ina nasara take samu dukiya sai habb'aka takeyi ta kwanta Naira.abunda ke matuk'ar bama Shuzna mamaki shine Fayyam ,ko kad'an baya jin magana baya da tsoro ga d'an banzan wayau da k'iriniya,ga zuciya baya d'agawa kowa Koda wasa Babu mai iya tank'warashi itama wani lokacin sai tayi da gaske,baya son hayaniya ko magana saika shekara kanayi sai ya ga dama yake maida maka ansa,a tak'aice dai Babu abunda ya baro daga halin Ahaad kamar shine aka sake daukowa aka ajiye yana yaro.a lokacinne ta shiga neman aekin soji bata sha wahala ba ta samu kuwa Navy dan haka ta wuce training na tsawan wata shidda cikin ikon Allah tayi ta gama ta zama cikakkiyar soja Kuma suka dauketa da Digree dinta dan sunan da tayi yasa bata wani wahala ba ta fito a matsayin Captain.bayan samun horon soji da tayi,abubuwa da yawa sun faru a lokacin. *Note zakuga nan page din yawanci labarin yazo a gaggauce to ina so in shiga cikin aenahin labarin ne,ina so na gama book din kafin azumi,na gode da soyayyarku gareni* Allah ka gafartawa iyayenmu kayi manakyakyawan karshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 31-35 Tafiya takeyi cikin nutsuwa sanye take da uniform na kakin soji tayi matuk'ar kyau a cikinsu,gashin kanta a nannade ta rike cap din a hannu ba zaka tab'a cewa wai Shuzna tayi aure ba ,bare Kuma kace ta haihi su Faida,babban wurin taron ta doso da d'an gudu gudunta ta shigo wurin tabi layi cikin sabbin ma'ae katan da aka dauka sannan ta sanya hular dake hannunta tayi,kamar yarda aka tsara taron yayi kyau sosai kuma anyi jawabai,manyan sojoji aka gabatar ciki harda Ahaad Wanda yanzu yake rik'e matsayin General Muslim ma haka,lokacin da aka gabatar da Shuzna a matsayin Captain ta gidan soji wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta,ta d'aga kanta sama tayi magana a hankali tace"Allah na gode maka,Ina nan zuwa gareku iyalan Kabir Bindawa,wasan yanzu aka fara",tana fitowa daga wurin Nani ta rungume tace"y'ata Allah yayi albarka,wannan ma wani matakin nasara ne a rayuwarki,na tayaki murna sosai y'ata"haka y'an gidan suka koma gida cike da farin ciki ga Shuhada ta zama cikakkiyar lawyer itama ta cika burin nata. "Ki tashi,ba lokacin baccinki bane wannan,lokaci yayi da zaki cika alk'awarin da kikawa Ruhina ,ki tashi Najma ,ki tashi". firgigit Shuzna ta farka daga baccin da ya d'an dauketa bakinta dauke da addu'ar bacci,duk lokacin data kwanta bacci takanyi mafar amma na yau ya banbanta da ko yaushe,lallai Najwa tana tunanin kamar ta manta da burin d'aukar Fansa dake cikin ranta Wanda ko yaushe yake cin Ruhin ta,"a'a Shuzna lafiya dai ko?"Umti ta fad'a tana kallon yarda Shuzna ta jik'e da zufa,da gudu Fayyad ya k'araso ya rumgumeta cikin kwarancinsa yace"Aunty kice ya daina",Fayyam ne ya rugo wurin shima yana cewa"bani abuna"b'oye abun wasan Fayyad yayi,kallonsa Shuzna tayi tace"my boy kaga Yayanka ne Fayyad ,ka daina binsa haka da gudu sai kunje kun fad'i?".tsalle Fayyam ya daka tare da kwala ihu ya fad'i akan tayil yana kururuwa,wata zuciya tazowa Shuzna ta fizgoshi ta dalla masa mari tare da sakar masa dundu.bai fasa abunda yakeyi ba,cikin Sauri Ahaad ya safko daga bene yace"karki k'ara dukanshi haka,yaron zaki wa duka kamar kina filin daga?,ke waye ya dakeki?". murgud'a baki Shuzna tayi cikin zuciya tace"shi yaro ba'a da ikon masa magana?,Babu abunda ya ajiye sai dukan y'an uwansa,nan jiya sai da ya fashewa Faida goshi yanzu kuma ya biyo Fayyad wallahi bazan dauki wannan iskancin nashi ba"ta d'auki Fayyad tayi wucewarta,k'wafa Ahaad yayi ya d'auki Fayyam yayi ciki dashi. "Bazai yiwuba Muslim,wannan ba abunda zan iya yarda dashi bane,kayi hakuri bawa Shuzna fuskar Zeenart ba shi yake nuna kazo kace kana sonta ba Kuma,Shuzna tana da miji Kuma gidan uban y'ay'anta zata koma da yardar Allah"Umti ta fad'a. Dafe kai Muslim yayi yace"Umti kada kiyi mun haka dan Allah,na tsaya tsawan shekaru ina kallonta kamar Zeenat na bari ta haihu ne kafin na bayyana mata soyayyata,Umti ki taimaki d'anki Wanda tsawan Shekara 5 kenan aka kashe masa masoyiya ya shiga tashin hankali har yanzu ya kasa samun wacce zata maye gurbinta".d'aga masa hannu Umti tayi tace"ya isa haka Muslim bawai bana tausayinka bane ko wani abu ba a'a ,kasan zanfi kowa san ganin farin cikinka,amma kaddara bata zo da Shuzna gidan nan danka aureta ba,na gama magana Kuma kada in k'ara jin kayi maganar da wani".duk'ar da kansa yayi cikin ladabi yace"to Umti insha Allah zanyi kamar yarda kike so,amma ki sani babu ranar da zan iya yin aure ko naga wata da kaina nace ina santa".yana gama fad'an haka ya tashi ya fice daga wurin.tashi Umti tayi ta wuce d'akin Shuzna samunta tayi kwance tayi rubda ciki ,jin an bud'e kofa yasa Shuzna juyowa ganin Umti yasa ta tashi tace"a'a Umti aeda kin aeko sai nazo basai kin taso da kanki ba"kallon Faida tayi yarinyar kyakyawar gaske gata fara tas tace"kije wurin Ummanku(Nani)Ina zuwa kinji".da gudu Faida ta gice daga d'akin.gefan gado Umti ta zauna tace"Shuzna yau zan sauke alk'awarin dana dauka kanki,kinga komawarki nan Nigeria ina tsoronsa sai dai babu yarda zanyi tunda aeki ya kaiki can(zataje yin wani aeki Nigeria),Kuma ko ba aeki nasan tabbas zaki koma gida,wannan fuskar dana baki Wanda nasan kinsan fuskar Zeenart ne y'ar aminiyata,Kuma itace wacce D'ana Muslim zai aura,wannan fuskar bata cancanta a badata ga kowa ba,saboda ba kalar kowa bace,lokacin da aka kawoki,duk da kina a sume amma naga idanuwanki suna fitar da hawaye,naga kina da San k'ara rayuwa,baki da wani muradi daya wuce wannan,shine dalilin da yasa na dage wajen neman mafita a kanki cikin yardar Allah kuma muka samu nasara,Ina so ki sani Zeenart kasheta akayi ba mutuwa tayi ba,yankan rago akayi mata saboda sanin wani sirri da tayi,zan gaya maki Wanda yayi mata haka,amma ko da wasa kiyi mun alk'awarin bazaki tab'a fad'awa kowa ba".jinjina Kai Shuzna tayi tace"Umti basai kin rok'eni ba,zan iyayin komai a kanki". murmushi Umti tayi taci gaba da cewa"Amaan shine Wanda ya kashe Zeenart"a matuk'ar firgice Shuzna ta kalli Umti baki na rawa tace"dama ya santa ne?"."dalilin mutuwarta ne yasa ta gitta a rayuwarsa,tabbas zaki fuskanci k'alubalan da yawa daga wurin Amaan,amma insha Allah zaki tsallake Kuma duk wani sirrin da yasa ya kasheta Zeenart ta gama bayyanamun komai insha Allah idan lokaci yayi zan baki,ke dai ki kula da kanki".Umti bata jira cewarta ba tayi waje abunta.jujuya Kai Shuzna takeyi a tsawace yace"Wai kai wanne irin mutunne Amaan?,tabbas ka kasance azzalumi mai rusa farin cikin kowa,tabbas ka shirya ina zuwa gareka,ba Kuma zan tab'a tunanin kai D'an uwana bane".wayarta data soma ruri ta dauka ganin Barista Abbas yasa ta dauka da sauri tace"Ina zuwa yanzu"kashe wayar tayi bata jira komai ba tayo waje kawai,masu tsaronta suka taso tare da bud'e mata mota ta shiga ,kamar kullun da mota biyu suka fita .ba wani nisan tafiya sukayi ba ta k'arasa inda zasu had'u da Barista Abbas zama tayi a d'ayar kujerar dake kusa dashi tace"barka da zuwa Barista, harka huta daka fito haka da wuri?". murmushi yayi yace"ae dole nayi abunda ya kawoni k'asarnan,balle Kuma aeki daku manya ranki ya dade,nasan zaki shiga rud'ani dajin abunda zan fad'a maki amma karki wani damu kaddara ne yazo da haka,Fadila itace wacce tayi niyar sakawa ayi maki Fyad'e a Kuma ranar da Dr Jamil yayi maki wannan allurar,ta ajiye lemu a firij dinki shine Ahaad ya taka sawun b'arawo ko ince Allah yana sanki ya kub'utar dake daga tarkon Fadila,Ahaad yasha lemun da Fadila ta ajiyene kuma shine Wanda yayi maki Fyad'e a wancan lokacin a tak'aice dai shine uban y'ay'anki".jefar da glass Cup din hannunta tayi a matuk'ar razane ta mik'e tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,ni ,ni Shuzna Ahaad shine Wanda yamun wannan abun?"take kalamansa da yake kiranta da Dabba,mazinaciya,dak'ik'iya suka soma dawo mata radau a kunne kamar yanzu yake fad'a mata haka,ihu ta saki Allah ya taimaka wurin rufe yake da glass Babu Wanda zai iyajin sautin muryarta,hannu tasa ta dod'e kunnuwanta tace"a'a,a'a hakan Sam bazai yiwuba,na tsane shi,na tsane shi,meyasa duk wani farin cikina Ahalina suke k'ok'arin rabani dashi".dafata Aiban yayi yace"meye haka kikeyi?sai kace wata warda aka fad'awa mutuwa?meye da Ahaad din?Wanda yanzu zaki godewa Allah kin haifi yaranki da aurene,ba shegu bane da ubansu".lokaci d'aya fuskarta tayi jawur harda k'asan idonta had'e fuska tayi kamar an saukar mata da mutu ta kalli Aiban da idanuwanta Wanda suka firfito waje alamun tsananin b'acin rai cikin kausashiyar murya tace"na tsane shi,na tsane shi,har abada bazan tab'a sassautawa wani daga cikinsu ba,sun tarwatsamun rayuwata"."duka abunda aka yi maki ke shaidace Babu saka hannun Ahaad a ciki,wannan ma kaddara ce kawai,Ina so ki sani zafin kiyayyah baya canza komai Shuzna"."haka zalika bazan tab'a bari suyi nasa a kaina ba wannan karon,yanzu ne zan fuskancesu,meye amfanin rayuwa idan har za'a rayu babu martaba?,zalinci kawai suka saka gaba,suyi farin ciki yau Baba Kabir ya zama Governor a garin katsina ,dan zuwa gobe tunaninsu zai hargitse ne gaba d'aya"files din da Barista Abbas ya ajiye mata ta dauka ta fice daga wurin suka bita da ido. Tunda ta shiga mota take kuka harta k'arasa gida,goge fuskarta tayi ta fito cikin izza tana tafiya shan gabanta yayi yace"Najma daga Ina kike?".a hassale tace"daga inda ka aekeni malan".sosai ran Ahaad ya b'aci da ansar data bashi ya daure fuska ya nunata da hannu"yake ki kiyayeni,niba tsaranki bane da zakina fad'amun duk abunda yazo bakinki,sake maki da nakeyi baya nufin ki rainani kuma,ki rika shiga yarda kike so kina fita Kuma ki dawo lokacin da kike so". murmushi tayi tace"kasan Dabba abunda yazo kanta kawai takeyi ,yawan kasuwancin Dana saba na tafi".ji kakeyi tas tas tas ya daiketa da kyawawan maruka.ko gezau batayi ba bare Kuma ta nuna masa Marin ya shigeta ta nunashi da hannu tace"wannan ya zama na k'arshe da wannan k'azamin hannun naka zai sake tab'a wani b'angare na jikina,bazanyi mamaki ba tunda gadon zalinci kayi,Ahaad na tsaneka ,na tsaneka ,na tsaneka bana son sake ganin fuskarka ina Dana sanin kasancewa a cikin zuri'arku"wata irin zuciyace kecin Ahaad ya rud'e gaba d'aya tunda yake a rayuwa ba'a tab'a gaya masa ba'a sanshi ba,ko wacce macce burinta ya kulata,amma yau shi ake gayawa haka,dandanan idonsa ya canxa yace"ni kike gayawa haka"."ka sani bazan tab'a yafe maka kusantata da kayi ba,ni yarana ba yaranka bane,kada ka k'ara nuna wata alak'a a tsakaninku,ka fita daga rayuwata dan Allah". 7years later Allah ka gafartawa iyayenmu kasa muyi kyakyawan karshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 36-40 7 years later Jirgin ne ya sauka babban filin jirgi a Kano,cikin takun k'asaita ta safko ,sanye take da kakin soji ba kad'an kayan sukayi mata kyau ba,lumshe idonta tayi tana jin wani sanyin dad'i na shigarta ga iskar garinta dake ratsata,lallai yau dole ta godewa Allah,tsawan shekara goma bata garin amma yau gashi ta dawo mahaifarta,bayanta Nani ce da Shuhada sai y'aranta Wanda suka gama Zama samari Faida an Zama y'an mata ko wanne cikinsu fuskarsa dauke da murmushi,cikin yaran dake k'ark'ashinta ne suka zo daukarsu saukar safiya sukayi dan haka suka d'auki hanyar katsina dan nan ne zatayi aekin nata a k'asarta Kuma a garinta,titi kawai take Kallo tana tuna rayuwarta ta baya har suka iso tank'amemen gidanta na katsina batace da kowa komai ba.Fayyam kam sai yatsine fuska yakeyi yace"Ni Mamie ki mayar dani wurin Umti bana son zama garin nan".dafa kafad'arsa tayi tace"Son nan ne fa garinka na asali ,nan ne garin kowa naka".zaro daradaran idonsa yayi yace"Mamie kina nufin su Daddy dinmu nan ne garinsu?"dariya kawai tayi tace"kuje ku huta anjima kayi tambayar naka"Mai aekinsu ta jasu zuwa d'akinsu,sai Nani ta ja Faida dan tayi mata wanka. Da gudu yaran ke riga rigan fitowa jin Muryan Aeban,kowa so yakeyi ya fara rungumeshi,duk'awa yayi ya ware duka hannuwansa ya tungumesu gaba d'aya,dingure kan Faida Fayyad yayi yace"harda wani saurin riga na fitowa".wani mugun Kallo Fayyam ya wurga masa Wanda yake fitowa yanzu cikin takun izza yace"wallahi idan ka k'ara ture mun k'anwa saina karya maka hannun gobe inga da wanne zakayi".ya samu Chair ya zauna sai huci yakeyi,"k'anwarka ce kai kad'ai malan?ko nakaga wasa mukeyi bane ,Fayyam ka fiye neman tsokana"Fayyad ya fad'a.glass cup din dake kusa dashi ya dauka yayi jifa dashi amma ya kasa furta komai da sauri Shuzna ta safko daga sama tana fad'in"subhanallah lafiya?"tsaye tayi turus tana kallon ikon Allah,sakin Fayyad Aiban yayi ya k'arasa ya Kama Faddam yace"haba son kullun ina gaya maka ka daina fad'a da y'an uwanka baka bari,kai kullun sai kayiwa wani duka".cikin d'aga murya yace"to Daddy ae laifinka ne,kaine ka bari Fayyad da Faida suka fara rungumarka kafin inzo,Ni bana son sai wani yayi abu sannan in yi".murmushi kawai Shuzna tayi ta k'arasa shigowa parlon tace"Fayyam ka cika rigima da yawa ,to su ba Yayanka da k'anwarka bace".alama Aiban yayi mata da tayi shiru ya rungumo Fayyam jikinsa yace"am sorry son".Shima Fayyam din rungume Aiban yayi saboda yana matuk'ar sonshi. Bayan sati d'aya da sukayi a Nigeria ,komai ya daidaita Aiban ya saka yaran makaranta boko da islamiyyah makarantu masu kyau ya Kuma d'aukar masu mai lesson komai yana tafiya yarda suke so,yaune kuma plan din Shuzna zai fara aeki dan ta gama shirya komai ,musamman yanzu da Abba(Kabir)ya Zama Governor na garin Katsina.bayan yara sun tafi scul, Shuhada ta yafi wurin aeki tayi wanka ta shirya cikin dogon riga Purple colour sosai tayi mata kyau ta dauko k'aramin bak'in veil ta daure kanta dashi,hand bag ta dauka bak'a sai hills shoe dinta ma bak'ak'e sai fitar da sihirtaccen kamshi takeyi tana fitowa ta rungumi Nani tace"saina fawo Nani,ki kula da kanki".shafa kanta Nani tayi tace"Allah ya tsare hanya y'ata,kinyi matuk'ar kyau sosai".Shuzna tana fitowa masu tsaronta suka taso da mota biyu suka fita kai tsaye wurin shak'atawar da yasan kamar yanzu zata samu Wanda take nema ta nufa,Koda suka isa da aka bud'e mata mota bata fito ba sai da ta tabbar ta hango Wanda take nema,murmushi ta saki sannan ta ziro k'afarta fari tas ta jima kafin ta idasa fitowa gaba d'aya,Masha Allah shine mutanan dake wurin suke fad'a saboda tsananin kyan halittar Shuzna da suka gani.kallon Islam Fadila tayi tace"Islam waccan ba itace wacce taci gasar nan a k'asar India ba?".kallon Shuzna Islam tayi sosai tace"Masha Allah itace ko,a filima tafi kyau akan a hoto"tsura mata ido sukayi,ita Kuma kai tsaye ta wuce daidai inda suke cikin wata murya mai dadin sauraro tace"zan iya zama?,bana son side dincan".har had'a baki sukeyi wurin fad'in"sure madam". murmushi ta sakar masu ta zauna,order tayi masu na kayan ciye ciye kala kala kafin kace me an cika teburin gabansu,ruwa kawai Shuzna ta kurb'a ta soma aekin latsa waya,amma a bad'ini tana nazartar su ne,cikin felek'e Fadila tace"sis bazakici komai bane?".gyad'a kai Shuzna tayi tace"am owk don't worry".bata dad'e a wurin zaune ba ta mik'e tace"na gode zan wuce"ATM dinta ta mik'a wa d'aya daga cikin yaranta tace"ka biya bill din".cikin girmamawa ya k'arb'a yace "owk Madam".cikin sauri Fadila ta mik'a mata hannu tace"am Fadila Kabir bindawa y'ar Governor ta nan garin".sakin fuska Shuzna tayi ta bata hannu tace"nice to meet u am Shuzna Bashir".Islam ma hannu ta bata tace"Islam Sadeeq,ko zamu iya zama friends".hannu ta bata itama tace"why not?,sure".Jakarta ta bud'e ta fiddo card dinta ta basu ta d'aga masu hannu ta wuce. Da gudu Fadila ta k'arasa shiga parlon Hajiya Sadiya tsakiyar su Mummy ta fad'a tace"albishirinku".da goro Hajiya Sadiya ta ansa tace"yau Kuma wanne kamun y'an matana suka yomun?"washe baki Islam tayi tace"Umma yau babban kamu mukayu,Ina Shuzna Bashir yarinyar nan da taci gasa a k'asar India ta computer?".cikin sauri Mummy tace"eh,eh meya faru?".carab Islam ta ansa da cewa"wallahi yanzu muka rabu da ita,kunga katinta data bamu mun Zama k'awaye".gud'a Hajiya Sadiya ta saki tace"lallai yau babban kamu,kuyi kokari ku janyota jikinku mu dangwali dukiya mu barga inda take,ae ba abun wasa bane wannan".kafin kace me harsun gama tsara yarda zasu janyo hankalin Shuzna zuwa ciki su"."ae insha Allah Mummy kada kuji komai ae mun janyota mun gama kawai".sun dade a gidan kafin Mummy da masu tsaronta suka daukesu tare da Fadila zuwa gida. Cikin k'ank'anin lokaci Shuzna dasu Islam sun gama jonewa kowa k'ok'arisa ya fara janyota cikinsu,yayinda take cike da matuk'ar farin ciki tasan ba zata wani sha wahala ba wurin cinma burinsu,tunda suka had'u ko wacce ke kwakwar Shuzna taje gidansu amma bata maida hankali ba,yau ta kasance babbar rana a wurin Shuzna dan yaune Nani Fammah ta k'arb'i muslunci ta koma da suna Fatima,zaune suke cikin babban Parlonta zaune suke Shuzna ,Islam sai Fadila fira kawai sukeyi,duk tsawon zuwansu gidan ko kad'an basu gane Nani ba dan ta k'ara kyau ta murje bare yanzu da takeyin shigar hausawa duk daukarsu Su Faida kannen Shuzna ne,"ya kamata yau dai ki cika alk'awarin ki Shuzna,yau kikace zakije gidanmu,daga nan mu wuce gidansu Islam"."yes of course ina sane fa,zanje na shirya yanzu".tayi matuk'ar kyau cikin shigar farin wando da blue din riga yau toms ta saka ta ja jakarta wurin Nani taje tayi mata sallama tare da yaranta sannan ta fito yau bata fita da masu tsaronta ba,ita ke driving sai Fadila a front seat sai Islam a baya,fira kawai sukeyi har suka isa k'ofar gidan su Fadila , Shuzna ta fara danna Horn aka bud'e suka shiga,kallon get man din tayi shine dai tun nasu na da,sai dai yanzu a gidan akwai tsaro sosai saboda gidan gwamna ne,basu da wani nisa tsakanin gidan Shuzna da gidansu Fadila,jin komai takeyi kamar a mafarki Wai yau itace a cikin Family dinta bayan tsawan shekara goma,a hankali ta fito da k'afarta suka wuce cikin tankak'amemen gidan,a ranta tace lallai Mummy ta samu abunda take so,tunda suka shiga Fadila ke kwallah Kiran "Mummy Mummy Ina kika shige?",part din Mummy suka shiga ,zaune a chair suka sameta tasha wanka ga jikinta duk zinarai,fad'ad'a fara'arta tayi tace"a'a sannunku da zuwa ,tun d'azu nake tsimayen isowarku"ta k'arashe maganar tana mik'ewa ta nufosu,sun kai minti d'aya suna kallan Kallo tsakanin Mummy da Shuzna sannan Shuzna ta wayence tare da rungume Mummy tace"barka Mummyna".rungumta Mummyn tayi tace"lafiya qlau y'ata ,Allah yayi maki albarka sannu da dawowa k'asar haihuwa".dariya Shuzna tayi sannan Mummy ta rike mata hannu suka zauna a chair kafin kace me tuni an cika gaban Shuzna da abubuwa iri iri,Mummy sai rawar kai takeyi tace"ki gama ku gaisa da Governor da kuma Hajiya Mama". Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan karshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 41-45 Da fara'arsu suka k'arasa akan milisar da Mama ke zaune,kallonta Shuzna takeyi cike da matuk'ar kewarta,Babu laifi Mama ta k'ara tsufa babu laifi,cikin d'oki Shuzna ta k'arasa gabanta ta duk'a tare da rungumeta ta baya ta sark'o kanta dai dai wuyanta,da sauri Mama ta d'ago fuska a hankali tace"Najma",da yake suna hayaniya babu Wanda yaji me tace sai ita Shuznar,murmushi kawai tayi tace"Mama barka da hutawa".k'ara kura mata ido Mama tayi jin muryar Shuzna sharewa tayi ganin ba fuskarta bace tace"yauwa yarinya"labari sukeyi amma kab hankalin Mama yana kan Shuzna yarda takeyin abubuwa da matsa k'afa yasa take ganin kamar Najma ce zaune a wurin,a b'oye sai share hawaye takeyi.shigowar Amaan yasa Shuzna mik'ewa tsaye tana kallonsa,wani irin zaro ido yayi bakinsa na k'yarma ya d'aga hannu yana nuna Shuzna yace"ke..e..ke...Zee...na...t"da sauri ya dafe kanshi ya fice da gudu yana k'ok'arin sakin ihu yana bubbuga kanshi yana so ya gane ko dai yana da hankali.Daddy suka gaisar sannan suka isa gidansu Islam,anan da taga Shuzn yi tayi kamar bata Santa ba,anan suka had'a kawancen yarda babu Wanda zai zargesu.sosai Hajiya Sadiya ta k'arbeta.ta jima sosai a gidan kafin tayi masu bankwana tace su zauna zataje gida ga Driver dinta nan yazo,tun da suka fita ,Amaan kam baya ya bisu dan yana so ya tabbatar da abunda ya gani,da sauri tasa Driver ya taka burki daidai wani super market,har kusan Faduwa takeyi data fito tayi kan wata kyakyawar mata dake shirin shiga mota hawaye suka wanke fuskarta tace"Ummu,Ummu"juyowa matar tayi ta kalleta kawai ta shiga mota kafin Shuzna tayi wani yunkuri tuni Driver din yaja motar yabar wurin,hawaye suka Kuma zubo mata da k'yar ta k'arasa mota ta shiga,Amaan ko ihu ya saki a cikin motar yace"menene haka yake neman zautar dani?,ni da hannuna na kashe Zeenart ,haka Ummu amma meya sa sukemun gizo a idona?,wannan ba abunda zai tab'a yiwuwa bane"da gudu ya taka mota ganin tasu Shuzna tayi masa nisa har suka iso bakin gate dinsu yaga gidan sannan ya koma gida a matuk'ar rude. Har yanzu Shuzna hawaye sun kasa tsayawa akan idonta,ga k'afarta da takejin kamar bazata dauketa ba tunda ta shigo parlon tayi wurki da Jakarta hannu tasa ta b'aro glasses din dake wurin ta cusa hannuwanta cikin yalwatacciyar sumar gashin kanta ta zube a wurin.Ahaad shine Wanda ya fara ganinta kafin Nani ta k'araso gareta shi harya iso da sauri ya rike hannunta dake zubar jini yace"subhanallah,meye haka kikeyi,kin jiwa kanki ciwo"."meye yake samunki y'ata?"Nani ta tambaya.kuka Faida ta saka tace"Aunty ki tashi please".rike hannun Ahaad Shuzna tayi tace"naga Mamana,Allah itace na gani,kafin nayi wani abu ta b'ace ta barni"riketa sosai Ahaad yayi ganin yaran sun rud'e yasa ya dauke Shuzna cak ya wuce sama da ita,Nani kuma ta Kama su Faida zuwa d'akinsu.koda ya kaita d'akin gefen bed ya ajiyeta ya dauko first aid box ya soma gyara mata hannun,duk zafin iodine a ciwo ko motsawa Shuzna batayi ba ,kanta k'asa kawai yake kallo idanuwanta sunyi jajawur.kallonta yayi yace"ki kwantar da hankalinki,wannan ba shine mafita ba,kinsan kina da aeki a yau da dare nan,idan kika kuskure kin fad'i daga amincewar da abokan aekina suka baki".ganin yarda yayi maganar a daure ya koma mata tsab oganta a wurin aeki .mik'ewa tayi tare da Sara masa tace"insha Allah General Ahaad".kallonta kawai Muslim keyi Wanda yake tsaye bakin k'ofa,da hanzari ya k'arasa shigowa ya rike hannuwan Shuzna hawaye na silalowa daga fuskarshi yace"Ashe kece Najma k'anwata,Ashe ke jinina ce?".a razane Najma take kallonsa tana son tuno abubuwan da suka faru a baya,bakinta na rawa tace"tabbas kaine Yayana Wanda Mummy ta kashe d'aya kai Allah yasa ka rayu,sai yau na gane dalilin da yasa nake matuk'ar son Daddy Ashe shine Uncle Bashir dinmu,na dade ina ganin kamarsa da Ummuna amma na share hakan,Ashe a cikin Family dina nayi rayuwa,Allah na gode maka".da gudu ta fad'a jikin Muslim tana sakin kuka,Nani ma kukan takeyi had'e da dariya ,matsowa tayi tana shafa fuskarshi tace"munyi kewarka sosai Muslim,ka yafe mana tabbas dani aka had'a kai aka rabaka da mahaifiyarka,amma munyi hakan ne dan ceton rayuwarka"sunkuyar da kai Ahaad yayi yana jin wata matsananciyar kunya ta rufesa da sauri yabar d'akin yana jin wani iri daban saboda halin Mummy.nan Nani ta basu labarin komai,kwafa Shuzna tayi tace"nikam bazan tab'a iya yafewa wad'annan mutanan ba,ko yaushe su suna kawo hari akan farin cikinane".dafata Muslim yayi yace"ko dan Hallaccin da Aiban yayi maki bai isa ace kin gafartawa k'anwarsa da Ummansa ba?,duk da nasan Islam itace ta kawo shawarar a zuba maki Acid Kuma ita ta siyo ta bawa Fadila kuma ita tasa Fadila tasa ayi maki Fyad'e".murmushi Shuzna tayi tace"Kuma Mamanta harda hadin kanta aka yimun allurar mutuwa ko?,Kuma Islam itace wacce ta gayawa Ahaad nice Shuzna bayan daya saka aka kamo masa ita".zaro ido yayi yace"a ina kika San wannan?"."ina tare daku a India amma ruhina yana nan Babu wasu bincikena da ban gama ba,abunda ya rage shine sora d'aukar hukunci". Da dare ta shirya cikin Uniform dinta na kalan Soji tayi matuk'ar kyau sosai ,sai dai har yanzu idonta akwai alamar ja ja a jiki,sai fidda kamshi takeyi,da gudu Fayyad ya shigo d'akin tare da rungumeta yace"Ummu kije dani bana son Zama anan",k'arasa daure igiyar takalminta tayi tace"haba Super hero ,kasan bazan dad'e ba kuma Ummanku na tare daku,aeki ne na gaggawa yazo mun"ta k'arashe maganar tana janyo hannunsa suka sauko daga bene ,har a ranta tana matuk'ar son Fayyad saboda Shima yarda yake tsananin sonta da nuna kula gareta,a kusa da Nani ta zauna ta rungumota tace"Nani zan tafi"."kai kinyi matuk'ar kyau y'ata,bara muyi photo a tare"wayarta ta d'akko take hotonsu da Shuzna ya bayyana tun bata girma sosai ba,camera ta shiga ta soma daukarsu tare,d'aya ta rungumeta,d'aya ta Mata kiss a kumatu,d'aya Kuma sukayi duka harda yara,mik'ewa tayi ta sumbancesu su duka ta nufi hanyar fita da gudu Fayyad ya k'araso ya rike hannunta Cuo din madara ya bata yace"kinyi mantuwa baki sha madarar ki ba"duk'awa tayi murmushi dauke fuskarta Tasha madaran sannan ta shafa kanshi tace"na gode".kanne Mata ido d'aya yayi tare da sakin murmushi yace"Allah ya tsare,ya Kuma karemun ke Ummina,ki kulamun da kanki,ko yaushe ina alfahari dake,kedin garkuwace ta gari garemu,ko yaushe zaki kasance a zuciyar Fayyad Aiban"sak fuskar Ahaad ya koma mata,duk wani abu nasu yayi kala d'aya,rungume yaron tayi tare da saka masa albarka hannu ya d'aga mata yace"masoyiya am gonna miss u"dariya duka suka saka a parlon,sannan duka yaran sukayi mata Allah ya tsare sannan ta fita daga gidan, Driver yaja motarta zuwa babban barikin soji a katsina,da d'an gudu gudu ta shiga d'akin taron,k'amewa tayi tare da sarawa manyanta irinsu General Ahaad, General Muslim,General Akiyy da dai sauransu duk manyansu sun hallara ,ansa Mata sukayi kafin ta k'arasa jikin wani k'aton allo Wanda Computer ke ajiye a gefansa bisa tebir ta soma masu bayani tiryen tiryen akan yarda akayi aka kwashe kud'in matai Makin shugabansu,sannan ta Kuma fad'a hanyoyin da za'abi a kawar da irin wannan b'annar tasha wahala sosai kafin ta gano Wanda sukayi aekin dan da gani Shima k'warone a computer. Tafa mata sukayi tare da Mata jinjina dan tabbas sun jiniinawa k'ok'arinta ba kad'an ba,hakan ya k'ara Mata kima a wurin aekinta,gabanta ne yayi mugun fad'uwa da sauri ta soma karanto addu'a ta samu taji daidai sannan taci gaba da godiyar kyaututtukan da take samu.ba su suka Kama hanyar gida ba sai bayan sallar asuba,Muslim yaja Ahaad yace"muje idan an ajiye Captain Shuzna gida sai driver dinta ya mikamu kaga Amaan bai bada motar an kawo ba"ba yarda ya iya haka suka shiga motar sai faman had'e rai yakeyi,yayinda Shuzna keta jan siririn tsaki dasun had'a ido ta b'allah masa harara.murmushi kawai yayi ya kawar da kansa yana Mata akamar zaki gane kuranki. Daidai k'ofar layin sukaga motar Ahaad fitowa sukayi tun a nan,Ahaad yace"to Kuma waya kawo motar anan?".jinjina kai Muslim yayi yace"nima ina zan sani".ko kulasu Shuzna batayi ba ta wuce tare da tura k'ofar parlon tanajin gabanta yana dukan ukku ukku kamar zuciyarta zata bud'e kirjinta ya fito,ganin duhu yasa ta matsa wurin makunnin kwan fitilar ta kunna,a hankali ta soma juyowa kamar mai tsoron d'akin baya tayi tana jin jiri na neman kwasarta ,murza idonta tayi ganin kamar dishi dishi take gani,lallai ba mafarki bane,wani irin zananniyar k'ara ta saka wacce ta karad'e duka illahirin gida ta Kuma kwala wata k'arar tace"Nani,Fayyad"jin motsin mutum ta bayanta yana niyar shak'areta yasa ta juya da sauri zaro idonta tayi cikin muryar kuka tace"sai kayi dana sani,sai kayi nadamar zuwanka duniya,Amaan ka tabka babban kuskuren k'ara kashemun farin cikina"duka ya kai Mata a fuska ta goce ta kai masa wani duka a wuya,k'ara ya saki ya nemi hanyar fita,yaransa guda biyu suka rufa masa baya,cikin zafin nama ta rufa masu baya ta zare bindigar dake jikin wandonta ta soma harbi ta ko ina ,da gudu Muslim da Ahaad sukayo cikin gidan jin ihun Shuzna,bangajesu Amaan yayi sukayi waje,itama turesu tayi ta rufa masu baya,cikin sa'a ta harbi Amaan a k'afa,sai yaronsa d'aya akan cinya ,kafin ta k'arasa garesu suka shige mota suka ja da gudu.dafe kai Ahaad yayi yana Kiran"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"Nani da Fayyam ne kwance cikin jini anyi masu yankan rago,gaba d'aya parlon ya b'aci da jini,da gudu Ahaad ya k'arasa ya d'ago gawar Fayyam sai yaji hawaye nabin kuncinsa,yau d'ansa ne a hannunsa Kuma wai k'anensa ya masa yankan rago ya kashesa.jin muryar su Ahaad yasa Faida da Fayyam fitowa da sauri,mak'alk'ale Muslim Faida tayi tace"Uncle suka kashesu ,suka yankasu muna kallo,Uncle a idona,wani ne mai Kama da Papa,muma suna nemanmu Fayyam ne ya buga masa katako a kai ya janyeni ya b'oyeni a bayan k'ofa"nuna gawar su Fayyad kawai takeyi a take ta sulale jikin Muslim sumammiya,shikam Fayyam jikin Ahaad ya kwanta ya kasa cewa komai .girgiza Faida Muslim yakeyi amma shiru,ruwan sanyi ya zuba mata amma ko motsawa batayi ba,sai yanzu tunanin Ahaad yazo masa akan Shuzna janye yaran yayi daga jikinsa ya fito da gudu yana kiranta duk da ji yakeyi kansa tamkar zai tsage,Shuzna kam fad'uwa tayi akan gwaiwowinta tana sakin kuka ,da gudu Aiban ya fito daga mota ya k'araso ya rumgumeta yace"kiyi hakuri,kada ki d'auki doka a hannunki,nayi maki alk'arin zanbi hakkin D'ana a ko wanne yanayi".ganin hakan yasa Ahaad sunkuyar da kai ya koma ciki tare da jingina da bango ya dafe kansa.Aiban yanayin tozali da hawar su Nani,besan ya soma hawaye ba.ruwa da yawa Fayyam ya ebo ya watsawa Faida ya girgizata da k'arfi yace"kema tafiya zakiyi ki barni?,ki tashi kada ku barni ni kad'ai ina sanku sosai"ya k'are maganar tare da sakin kuka mai karfi,wani dogon numfashi Faida ta saki itama tana sakin kuka,ba arziki aka Kira Dr yayiwa yaran allurar bacci su duka biyu dan nema sukayi su zare masu. Cikin awanni kad'an aka gama shirya gawar Nani data Fayyad,Shuzna kam ta koma kurma ko motsi batayi ha daga inda take,har aka fita da gawarsu.ganin Shuhada ta shigo a rude yasa Shuzna sakin kuka ta rungume Shuhada suka saki kuka a tare. Kamar daga sama sukaji magana"yanzu ba lokacin kuka bane,ki Zama jaruma ki share hawayen kije ki gama da makiyanki,ki kawar dasu daga datsewa duk wani bawa farin ciki,ina so yau ki Zama ta k'arshe wacce zasu tarwatsa wa rayuwa Najma"jin muryar Ummu yasa suka juyo da sauri su duka. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe. Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Part 2 ,part 2 ,part 2 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* End A kallon Ummu kawai Shuzna takeyi sannan ta fad'a jikinta cikin dishewar murya tace"Ummuna Ashe zan k'ara ganinki?". Shafa fuskarta Ummu tayi tace"kwarai kuwa y'ata,komai kike ciki ina sani,ina jiran lokaci kawai yayi kafin nazo gareki,saiki godewa Yayanki Kuma Baban yaranki danshi ya dauke maki Ummarki ya kula da ita duk tsawon wannan shekarun yana bata tsaro"sunkuyar da kai Shuzna tayi ta kasa cewa komai,sai dai tana jin dadin yarda Ahaad ya kula da Ummanta duk da Shima tashi ce ita ta rainesa,rasa kalmar da zatayi amfani tayi.matsawa kusa da Ahaad Ummu tayi ta Kama duka hannuwansa ,kansa a k'asa yace"Ummu dan Allah kuyi hakuri,nasan Familyna sun cuta maku da yawa"rufe masa baki Ummu tayi tace"nima Family dina ne ae,kayi hakuri bana nufin Shuzna ta cutar dasu,sai dai ina San a d'auki matakin da irin haka ba zata k'ara faruwa ba".murmushin k'arfin hali yayi cike da kunya amma bece komai ba,shi kanshi tsiyar dasu Amaan suke aekatawa ya ishesu haka.cikin k'an k'anin lokaci ta sauya kayan dake jikinta ta fice daga gidan. Da matuk'ar gudu ya shiga gidan tsaye yayi turus ganin Daddy yana balbale Mummy da bala'i yace"kinyi abunda kika iya,amma ki sani bazanyi maki baki ba,sai dai yau iyalan y'an uwana zasu dawo gida,kin cutar dani Bilkisu,bansan iya wanne abubuwa kika saka na aekata ba,bazan tab'a yafewa kaina ba"ya k'are maganar yana fita daga parlon. Hannu Mummy ta saka a Kai tace"Amaan aekin komai ya bud'e,mun shiga ukku idan Alhaji ya juya mana baya". K'arasowa yayi cikin d'akin yace"ae wannan bakiga komai ba akan abunda ke dosomu,Ummu Sha'awa tana raye Ashe Yaya Ahaad shine Wanda ya dauke Ummu,Shuzna k'awar Fadila Kuma itace Najma"dafe zuciya Mummy tayi tace"Amaan karkasa zuciyana ta buga,na mutu ka huta".sallamar Hajiya Sadiya da Islam ya mai da hankalinsu garesu,fuska daure Hajiya Sadiya ta shigo a hassale ta nuna Mummy tace"Ashe ke baki da mutunci?,yanzu mijin nawa kike tunanin zaki iya sakawa a ture daga Gwamnati?,to wlh kinyi kad'an ke baki kaiba,duk wani abunki bayana kika biyo"."Kai Kai Wai meye kukeyi haka ?,yanzu ya kamata mu nemi mafitar tsiratar da kanmu ne,duk abunda muka dade muna shiryawa zai rushe rana d'aya".murgud'a baki Islam tayi ta soma zagaye Amaan cikin d'aga murya tace"naku dai ya tarwatse maciya amana,koka manta yanzu Kai kaje ka kwanto wata rigimar?,Kaine kaiwa yaran Najma yankan rago,ka kuma kashe Mata Naninta ,bayan a baya kayiwa y'ar uwarta Fyad'e ka kasheta,Kuma ka kashe Mata Babanta,kayi hari akan Ummanta sai dai ita bata mutuba,Zeenart kam daka kashe ta mutu sai dai fuskarta aka bawa mak'iyiyarka,Kuma Najma tasan komai akan abunda ka aekatawa zeenart,abun farin ciki da zan gaya maku shine Muslim shine yaron Umma da Kuka kashe Mata y'an biyu to D'an uwanta Bashir yaji komai Kuma shiya dauke Muslim ya renesa,yana nan zuwa gareku".Mari Fadila ta katsawa Islam tace "ke marar mutunci yanzu Iyayen nawa kike gayawa haka?,ae duk abunda ake k'ullawa da Uwarki Sadiya aka yishi,hasalima itace mai kawo shawara,banzaye masu bak'ar zuciya kawai"shak'e Fadila Islam tayi tana kiran"ke harkin isa?,wallahi ko uwarki Bilki bata kaini tasha ba balle ke tsohuwar guzuma jaka dake".jin an banko k'ofa da k'arfi yasa suka juyo da sauri,Shuzna ce cikin shigar Uniform dinta na soji,sai yaranta su hudu suma duk a shigar Uniform.ko wannensu rike da bindiga k'arasa shigowa tayi cikin d'akin tana kallonsu da tsantsar tsana tabbas wa'annan mutanan sun cuta mata da yawa bata ma san meye zata iya aekatawa akansu ba inhar ta biyewa zuciyarta.jin an fasa k'ara yasa suka juyo da sauri ganin Fadila na niyar faduwa yasa Shuzna ta k'arasa da sauri ta fad'o a hannunta Islam ce ta caka mata wuk'a a gefen cikinta,girgizata Shuzna keyi tace"Fadila ki tashi" hannu Mummy ta daura saman Kai tace"wallahi yau saina kasheki kema,baza'a tab'a d'aukar gawar y'ata ita kad'ai ba,hakan bazai tab'a yiwuwa ba"kan Islam tayi gadan gadan Hajiya Sadiya ma tayi kanta nan suka had'e kamar mahaukata suna kokuwa da juna,fizgo hannun Islam Amaan yayi ya wanke ta da maruka har hudu ya soma jibgarta,da sauri yaran Shuzna sukayi kansu,hannu ta d'aga masu tace"stay out of this"Shima k'ok'arin jaka masa wuk'ar takeyi tana zage zage,ganin da gaske shima zata illatashi cikin bak'ar zuciya ya saita bindigar dake hannunsa akan Islam ya danna kunamar ,wata irin ihu Hajiya Sadiya ta saki tayo kan Islam ,Islam ta fad'o a saman hannunta ga jini yana zubowa daga kanta,ko shurawa batayi ba ta mutu a wurin.innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kalmar da Hajiya Sadiya ke maimaitawa kawai kenan hawaye na wanke fuskarta yaranta biyu Islam da Aiban Kuma kowa yasan Islam itace rayuwarta yau ga gawar Islam a gabanta ,wani kukan ta kuma rushewa dashi,k'ara kad'an Shuzna ta saki lokacin da Amaan ya janyo yalwataccen gashin kanta take ribom din ya zare gashin ya watsu a fuskarta da bayanta,saurin sakin Fadila tayi ta mik'e ta samu ta kwace kanta tace"kada ka kuskura k'azamin hannunka ya k'ara tab'ani".dariya ya fashe dashi yace"Babu Wanda zaiyi rai a nan daga Ni sai Mummyna Babu wani sarki sai ni a wurin nan"halbi ya soma saki kota ko ina cikin zarin nama Shuzna ta goce ta koma bayansa,rike hannun da keda bindigar tayi suka soma kokowa ,yayi mamakin yarda Shuzna tayi k'arfi haka duk da yasan ko a da can tana da k'arfi ba ragguwa bace amma beyi tunanin a yanzu zai kasa kwace hannunsa gareta ba,a tsawace yace"ki sakeni ko kuwa kiyi ta ranki"Murmushi Shuzna tayi ta kallesa ido a ido tace"aeni Amaan tun daga ranar daka rabani da iyayena,yar uwata,D'ana da Kuma Nanina from that very day u took my life,shiyasa yanzu bana tsoron na mutu,amma sai naga bayan tantiri marar tsoran Allah irinka,saina tabbatar nice ta k'arshe da zaku lalatawa rayuwa a duniya gaba d'aya".murd'eta yayi ta dur'usa k'asa,cikin dabara ta samu ta d'ago ta zare hannunta daga jikinshi ta wanka masa maruka har biyu ta kuma ingijesa yayi baya,juyawa tayi zata dauki waya ta Kira y'an sanda ,cikin sand'a ya daura Mata bindiga a Kai yace"tabbas yau saikin mutu,haka sauran yaranki da tsohon mijinki da Uwarki sai sun mutu kinga duk abunda kika mallaka nawa ne"motocin y'an sanda dana soji ne suka shigo gidan,kafin kace me sun zagaye gidan ,daga ciki harda General Muslim da General Ahaad,sai shugaban Shuzna kuma Wanda take jagorancin team dinsa a yanzu haka,parlon suka shigo harda Aiban,"ku tsaya daga nan idan Kuma har kukayi wani abu marar kyau to tabbas zata mutu yanzu",ganin da gaske yake yasa suka ja baya,kallonsu General Asam yace"dole fa yanzu ayi zab'i na k'arshe ,sai an harbi Amaan"zaro ido Aiban yayi da sauri ya k'arasa wurin Mamanshi tare da riketa jikinsa ta fad'a ta saki kuka tace"Aiban ya kashe mani ita,ya kashe mani Islam,Islam ta tafi ta barni Aiban"juyar da fuska yayi yana share guntun hawayen dake zubo masa rungumeta yayi yace"Hajiya kiyi hakuri,hakan Allah ya rubuta".kamar daga sama sukaji k'arar halbi Wanda basu gani ba harsunyi saranda kowa daukarsa Shuzna ya harba,ganin Ahaad da bindiga a hannu yasa kowa ya kalli inda yake Kallo,k'ara Amaan ya saki ya dafe k'afarsa da Ahaad ya harba ya zube anan wurin,wani kukan Mummy ta Kuma saki tace"Ahaad karka kashe d'an uwanka,dan Allah kabarmun yarona Ahaad"ta wuce gabansa zata duk'a,da sauri ya riketa ya kawar da kansa gefe"daku kamani gara na kashe kaina,bazan tab'a bari na mutu a hannunku ba"kanshi ya saita Mama tana kiran"a'a Amaan karkamun haka".kallonta yayi hawaye na zubowa daga idonsa yace"ki yafemun Mummyna"kafin tayi magana ya harbe kansa a take ya mutu a wurin ko shurawa beyi ba.y'an sanda suka kwashe su sai office dinsu Fadila kam a sume aka kwasheta sai asibiti,har Dr Jamil an kamo tare aka rufesu a office din y'an sanda.duk abunda sukeyi Daddy yana jinsu daga part dinshi be fitoba ,ya rasa meke masa dadi,kwakwaran motsi baya iyayi.cikin sati d'aya aka shirya komai aka Kai ,Mummy ,Hajiya Sadiya da Dr Jamil kotu,Shuhada da barista Abbas sune suka tsayawa Shuzna,ba wani b'ata lokaci suka ansa laifukansu,kotu ta yankewa Mummy da Hajiya Sadiya zaman gidan yari na shekara biyar da tarar dubu d'ari bibiyu,sannan su mayarwa Najma da dukiyarta.Fadila kam Shuzna bata yarda an kaita kotu ba,yarda taga tanata faman kuka da rokon Shuzna gafara ,ga tausayina Nasirah da Shuzna keji yarinyar bata da damuwa,tun kafin ayi wannan rigimar dama aka dauke Mama da Nasirah aka had'asu dasu Ummu dasu Faida.cikin sati biyu aka sallami Fadila suka dawo gidan Shuzna,ga Umti da Daddy Bashir sunzo Family ya hadu sai tattauna sukeyi da sanin abubuwan da suka faru a da.da gudu Shuzna ta shigo rike da wasu takardu ."a'a har yanzu kina nan da wannan shiriritar taki ?"Ummu ta tambaya, murmushi Shuzna tayi ta rungume Mama tace"Hajiya Mama yau jikarki ta koma da sunanta Najma Jafar Bindawa,Komai nawa ya koma da sunansa na da".Alhmdllh Umti ta fad'a ta dafa kafadar Shuzna tace"y'ata Najma kiyi hakuri da rasa fuskarki"rungume Umti Najma tayi tace"ba komai Mamana".tureta Muslim yayi yace"dallah malama tashi anan,zaki karyamun Mama".rigiman hakan suka fara Ummu ta janyoshi tace"barsu suje Sojana ae nima ga y'ata nan"ta fad'a tana janyo Shuhada jikinta ta had'asu ta rungumeta,hannuwansu ta had'a wuri d'aya tace"nima ga ma'auratana na had'a,zanyiwa Muslim da Shuhada aure"kowa dariya ya saka ,Shuhada ta boye fuskarta jikin Ummu,janyo hannunta yayi yace"haba masoyiya kunyata kikeji ne?".dungure masa Kai Mama tayi tace"gaba d'aya baku da kunya Kai da wancan labcecen bayahuden"harara Ahaad ya maka Mata wanda tunda ya zauna saika dauka baya d'akin.shigowar Aiban d'akin yasa suka takaita dariyar sai da ya gaishe da kowa sannan ya zauna kusa da Mama,"kaga yaron kirki mai tarbiya ,sannu da zuwa Aibanu".danna k'afar Mama ya farayi sannan yace"Mamana nazo neman aure fa"."yi sauri gayamun wace mai sa'ar ce?,gaskiya na gaji da zamanku hakanan dama".sunkuyar da kansa yayi alamar kunya sannan ya rad'a Mata a kunne,"Alhmdllh,Alhmdllh,Allah na gode maka,Aiban Allah yayi maka albarka Kuma na maka alk'arin baka abunda kake so Koda hakan zai Zama abu na k'arshe da zanyi,Allah ya shiga lamuranka,na baka Najma duniya da lahira".wani irin bugawa da k'arfi zuciyar Ahaad yayi ,"toshi Papa waye zaku bashi ya aura?"Fayyam ya tambaya."baba ko ubanwa,aeshi wannan fad'in ran nashi bazai barshi yayi aure ba".turo baki Fayyam yayi yaja hannun Nasirah yace"sai kiyi dama ae halinkine"tunda Nasirah ta dawo gidan Fayyam yake kula da ita,baya yarda kowa ya tab'a ko da wasa,"tsohon marar kunya Wanda yayi gadon ubanshi". Bayan sati biyu Ko wanne b'angare Shirin biki sukeyi ba k'akkautawa, yayin da Ahaad tun ciwo yana cinsa a tsaye har yakai gaya kwantar dashi ko fita bayayi kullun yana kwance kawai.ko kad'an Mama ta hana kowa ya kulashi tace a barshi can shiya sani. Kaya Muslim ya ajiye masa yace"ka tashi ka shirya mu tafi,lokaci yana kurewa".Jan pillow yayi ya rufe fuska cikin dishewar murya yace"kuje kawai bazan iya fita ba".sai da Ummu tayi da gaske sannan Ahaad ya shirya cikin blue din shadda suka saka mai matuk'ar tsada sai black din huda da black din takalmi sai fitar da sihirtaccen kamshi sukeyi.haka suka tafi daurin auren.wuri ya cika makil da mutane na nesa dana kusa,baka iya banbance wurinwa wane yazo,dafe Kai Ahaad yayi da yaji yana barazanar tarwatsewa juyawa yayi yaga babu mai kallonshi ya samu ya fito daga cikin masallacin can baya ya koma ya zauna tare da had'e Kai da gwaiwa yana jin jiri,jin hawaye masu dumi yayi suna bin fuskarsa..kamar daga sama yaji ana cewa an daura auren Muslim da Shuhada,Aiban da Fadila sai Ahaad da Najma akan sadaki naira dubu d'ari.a firgice ya d'ago yana jin tabbas mai shelar nan bejiwa kunnensa daidai ba.murmushi Aiban yayi masa lokacin da suka had'a ido yazo ya kamashi ya d'auki babbar rigarsa daya cukurkude ya ajiye a k'asa"ace ango ya b'ata kwalliyarsa haka?,kakkabe rigar yayi ya saka masa ya Kama hannuwansa yace"Congratulations angon Najma Allah ya bada zaman lafiya".tangare k'eyarsa Muslim yayi yace"raggon maza,ashe kasan kana Santa ka saketa"kasa furta komai Ahaad yayi sai murmushi kawai da godewa Allah da yakeyi a ranshi,"kada ka damu,ni bazan raba zuciya biyu ba,ina tabbatar maka itama Najma tana sanka ".Jan hannunsa sukayi zuwa cikin mutane fara'a kawai yakeyi yana gaisawa da mutane haka har suka samu damar komawa gida bayan hotunan da suka sha sunyi kyau kamar y'an ukku.koda suka shiga gidan an tsara wurin sosai anayin y'ar dinner,kujerune ukku inda su Najma suka zauna komai nasu iri d'aya fuskarsu a rufe sunyi masifar kyau.rike hannun Ahaad Umti tayi tace"yarona muje ka fara zab'ar matarka a can"binta kawai yayi a wurin ta tsakiya ya tsaya inda Shuhada take kenan,har zai budeta Kuma ya fasa ya tsaya yana k'are masu Kallo su duk'a,matsawa yayi can hannun dama sannan yasa hannu ya yaye lullubin take fuskar Najma ta bud'e Tasha kwalli,ihu mutanan wurin suka dauka tare da tabi ana masu ruwan nera da turare,sosai abun ya k'ayatar. 5years later. Yarinya kyakyawa ke gudu ta fad'a jikin Ahaad tace Daddy "kacewa Ammi ta kyaleni ni bazan koma gida ba"Farna ta fad'a tana fad'awa jikin Aiban,dariya Ahaad yayi yace"Captain kibar yarinyar nan wurin Babanta,bazata bimu bafa"dariya sukayi Najma tace to"nima zan tafi da little Najma kuwa"ihu Farna ta saka ita bazata yarda ba,fuska Fayyam ya yatsina yace"u idiot keep queit mai bakin parrot kawai"ba musu ta hadiye ihun da takeyi tasan yanzu sai tasha dukan tsiya.. A yanzu Fadila yaranta biyu Little Najma da Mahamud,sai Nasirah da take wurinta, Shuhada kuwa ukku dan Muslim yace saiya ta taddosu yara,Islam itace babba sai Afnan sannan Salim shine auta,Najma kam Faida da Fayyam sai Farna kawai data k'ara.sosai suke kaunar junansu suna zaman lafiya komai ya koma lafiya suna sada zumunci,a cikin satinne Kuma aka saki Hajiya Sadiya da Mama,shikam Jamil shekara Goma zaiyi dan haka yanzu yayi rabi,sosai Mama da Hajiya Sadiya suka canza zaman lafiya sukeyi suna Kuma San jikokinsu da iyakansu gaba d'aya suma ko wacce ta koma d'akin mijinta,Ummu ce kawai taki yarda ta sake aure take zauna da tsohuwa Mama Wanda tsufa ya fara kamata. Fadin irin soyayyar da Najma da Ahaad sukewa junansu b'ata lokacine yanzu kam Babu abunda ke rabasu zaman lafiya sukeyi da nunawa juna matuk'ar soyayyah. *alhmdllh, Alhmdllh,Allah na gode maka daka bani ikon kammala k'arshen littafin nan,Allah ka yafe mana kurakuren dake ciki,Allah kasa kuma a amfana da abunda ke cikinsa* *Sakon godiyata ga masoya Ruhin Fansa,na gode kwarai da nuna kauna a agareni,sanso fisabilillah,wannan littafi sadaukar ne ga masoya labarin Ruhin Fansa* Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe. Stylish star Jorderh majidadi