*RUHIN JIKI!!* *JORDERH MAJIDADI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book,special greetings to my siblings ,cousins and My lvly fans that have waited so long for Majidadi,and now am back da wani saban salon,I know u will luv it,cos I am in luv with it too...abun fa ba wasa,kudai ku biyo muji ya zata k'are salon na dabanne.😘😍😀 BISMILLAH Page 1 Sauti ke tashi da hayaniyar y'an Matan a cikin babban parlon Wanda yaji kayan more rayuwa kallo d'aya zaka masa ka tabbatar an narka dukiya a parlon..Doguwar cikinsu siririya ko kad'an bata da jiki black colour ne skin dinta irin mai silb'in nan tana da long face ,wacce komai na jikin fuskar ya dace da muhallinsa.tsantsar kyau da yarda fuskar ta wadatu da bakin gashi sidik a duk in da ya kamata she's the real Definition of beauty..magana take yayinda gefan kumatunta suka lotsa shiya kara fito da kyawunta white teeth dinta suke anan jere ras take fadin"Muhibba wallahi Anni ta fito zata ci k'aniyarki ne,mukam nan karki janyo mana ita.ki mayar mata da fura"Su ukku ne a parlon sa'annin juna sai dai su farare ne tas wacce aka kira da muhibba ta tsuke bakinta tare da fadin"ke LAYAN haka kike, in ba ke zaki fad'a mata ba to ina zata gane? Kinsan tana gani zata ce Yaya ne ".Duka a cinya Basma tawa Muhibba tana hararenta tare da zaro ido tace"to kisa a kashe mu da ranmu , kinsan halin Yaya a gidan nan amma zaki jawo mana jangwam? To wallahi sai dai kiji ke da shi." Murmushin bosawa Layan tayi tace"lallai yau banga gidan kwana a gidan nan ba ni Layan d'akin Ammi zan gudu ni kam."Dariyan shakiyanci Muhibba tayi tare da cewa"Au yau kuma Layan? Ke da Habibin naki? Farin cikin rayuwan ki?" Da sauri Layan ta yunk'ura tare da rufe bakin Muhibba tana jujuya dara-daran idanuwanta masu matuk'ar girma da haske cikin cool voice tace" please mana "tana kare. Maganan tare da raurau da ido alamun zatayi kuka...kallonsu kawai farar Dattijuwar take tsaye a entrance na parlon farace sosai duk da yanayin tsufan daya bayyana a jikinta amma wanke take tas tasha sabuwan atamfanta ko ina a jikinta k'al-k'al fuska babu fara'a ta k'aro tana bin cup din furan dake hannun Muhibba da kallo cikin mitsi-mitsi da ido tace"Amma wallahi kin cuci kanki Mubabbi,ke da Allah,yanzu furar tawa zaki shanye? Ko da kudin waccan narkekiyar matar na had'a na siya ne? To Wanda yayi na gari yaga na gari dan uban mutun kuma ki sani da Amadu kike kuma a gabanki zai biya kudin tashi barmun d'aki mai kama da zabiya kawai". Had'e fuska Layan tayi tace"Anni meyasa kike haka wai?".. " A kul na haneki ,bansan tsirfa tunda ban kasa da ke ba kina fama zok'ai-zok'ai to kiyi ta kanki"......Daga sama har k'asa Ammi kebin Veer da kallo she was speechless. Cikin sanyin murya kamar mai rad'a yace Am-mi please".kuma daure fuska Ammi tayi"hala na fara wasa da kai Jabeer?, ka daiji abunda na fada" ta k'are maganan tana kai mug din tea a baki ajiye mug din tayi ta dauki handbag dinta d eyeglasses dinta with car key tace "I'm going to office".. Cikin sanyin murya yace" Allah ya tsare".Da gudu Layan ta shigo part din tare da mak'alk'ale Ammi tana turo d'an karamin pink lips dinta gaba" har so nawa zan fad'a maki ki daina yin gudu a gidan nan iyee Layan?"..rau rau tayi da ido kamar wacce zata fasa kuka tace"Ammi..."Bana so naji komai kinji ma na fad'a maki,Sam na hanaki tsokanan fad'a a gidan ,dama wannan ne shirin school din naki?"Ammi ta k'are maganan da alaman tambaya.hawaye ne suka kawo fuskar Layan cikin sanyinta dan duk rigimarta da tsokanarta akwai sanyi tace"Ammi Yaya Jafar ne kuma yasa Driver ya tafi dasu Basma school an barni"..Agogon hannunta ta kalla kafin ta mayar da kallonta ga Layan tace"and I'm late too,bazan iya jiranki ba kije ki karasa shirin Yayanki ya ajiyeki,shima ki masa rawan kai ai kinsan sauran" Ammi bata jira cewarta ba ta juya ga Veer tace"drop her at school" tana zuwa nan ta fice tana gyara lab coat din jikinta dan ta kusa latti na zuwa asibitin...ko kallon in da take Veer beyi ba,hasalima kamar bada shi Ammi tayi magana ba,hankalinsa sosai ya tattara akan waya yana pressing,ganin Haka Layan ta k'arasa a tebur din idanuwanta a k'asa kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki taja chair zata zauna tana fad'in "ina kwana Yaya". Be amsa ba saima d'agowa yai yana watsa mata mugun kallo ganin tana neman zama kallon data fahimci yana mata ne yasa tayi saurin marairaicewa idanuwanta na tara ruwa tace"da break zanyi ban karya ba". Wani wawan tsuka Veer yaja tare da kuma tamke fuska a fusace yace" barnan ko na karya maki wannan sololon k'afar naki ".Da gudu Layan tayi hanyar d'akinta dake part din.haushi da takaicin rawar kan Layan ya kuma kume Veer na sakalci irin nata wanda ko tafiya bata iya yi sai gudu...a daidai corridor Layan tawa kanta masauki kafin ta daidaita tsayuwanta a hankali ta leko Veer dake zaune still yana aikin pressing phone tuni wani murmushi ya kwace mata zara-zaran siraran hannuwanta tasa tare covering long face nata a hankali tana jin wani dadi da sanyi suna ratsata ganin yana kallon agogon hannunsa tasan time ya ibar mata kuma tasan idan ya cika ko zata mutu bazai tab'a kaita school ba.Da hanzari ta fad'a d'akinta ta sanya k'aramin hijabinta na school sannan ta ratayo bag dinta ta fito ,baya parlon saurin zaro ido tayi tare da cewa" Kai Yaya!"sai kuma ta kwasa da gudu a parking space ta same shi yana kokarin bud'e mota beko nuna yasan alaman akwai zuwan mutun a wurin ba....har cikin school ya kaita ,yana kallon malaminsu dake tambayarta "why is she late". Juya ido kawai take without noticing wani abu taji muryar Veer kamar mai rad'a yana fadin" just furnish with some work ko duka gobe ba zata sake ba".ko kad'an Layan bataji mamaki ba dan ba yau ya saba kaita school yasa a mata duka ba.maimakon taji haushi sai kawai ta saki murmushi tana k'arewa Yayan nata kallo kafin cikin sanyi tace"Allah ya tsare Yaya na gode".ko bi ta kanta beyi ba ya juya ...aiko sosai Teachernsu ya bata dama gwani ne a mugunta...parking ya gyara tare da fitowa kai tsaye ya shiga gidan Aunty din nasa babu kowa a parlorhad'u..Maid dinsu daketa faman goge goge a parlor ga kamshi d sanyayan AC na tashi ,sai a lokacin ya samu nutsuwa da farin ciki Dan wani k'unci ke mamaye shi idan yana zama inuwa d'aya da Layan baya son Fadannan na Ammi shiyasa yau kawai ya daure ya kaita school.. Kujera kawai ya samu ya zauna tare da sauke idanuwansa suna anan kamar mai kama da jin bacci yana kuma tauna red lips dinsa a hankali ga kuma hannunsa a cikin tulin gyarariyar sumarsa wacce ke shek'i ta wadatu da kamshi.Gaishesa Maid din tayi tare da wucewa dan Sanar da Ummi kanwar Baban Veer mai rasuwa zuwan shi.a hanya suka had'u ...da Kallo Ummi ta bishi tare da cewa"kai da nace ka kwana ka'ki and now meye na zuwa mun da sassafe?".sai ka kallesa sosai zaka ga alamun sakin fuskarsa alamun murmushi sannan yace"ina kwana".harararsa Ummi tayi tace" ba wannan na tambaya ba".sosa kai Yayi yace"na sauke wacce ugly monster ne a school".without second though Ummi ta kwashi pillows na kusa da ita ta jefa masa su a fuska ,fuskarta tana nan a d'aure tace"iskancin naka yana nan ashe Jabeer? Har yanzu baka daina cewa Layan wannan sunan ba,to wallahi ahir dinka da ni.yanzu zanci k'aniyarka a gidan nan,kai da y'ar uwarka wannan wacce irin bak'ar rayuwa ka dauka wa kanka? To daga Mahaifinka har mahaifiyarka dai ba haka suke ba,kuma Umma da Abba basu cancanci kak'i jininsu haka ba".kallon Ummi kawai yake can dai ya mik'e ko sallama babu cikin tsawa Ummi tace"karna sake ganin k'afarka kuma harsai kayi hankali"ko juyowa beyi ba ya fice yana jin dama be biyo ba...Annie ce zaune a k'atuwar darduman data baxa a tsakar parlon nata ga carbaha a hannunta tana ja ansha gogggen sabon Hijabi ala lazumi ta d'aga kai tana k'arewa Jabeer kallo Wanda ya shigo tare da kwanciya a chair ya lumshe ido.saurin karasa lazumin tayi ta iso wurinsa tana binsa da kallo kafin tace"kai Jabeeru a wurin aikin sojan ne aka kore ka? Naganka haka kamar Wanda aka saukarwa da mutuwa?shiru ba amsa".wani kallo Annie ta jefa masa cikin shaushin shareta da yayi tace" to kaita yi wannan bak'in halin naka ko shi yasa Janar yake ko wa oho maku a maka tsinannan duka a kawo mana kai kaca-kaca muhau jinya da kashin kudi.to wallahi kada ka janyo mana inmu ka raina to can akwai hukunci sai ka kama kanka ah'to".idanuwansa da suka soma canza launi ya bud'e yana bin Annie da kallo bece komai ba ya kuma rufesu.. Comment and share kada Ku bari a wuce Ku mutanena . Oum Aryaaan..... *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* page 2 A gajiye suka shigo daga school din kai tsaye Layan part din Annie ta tafi in da duk yawancin rayuwarta anan take yi,duk yarda Annie keda rigima amma tana tsananin son Layan Wanda asalin sunanta Maryam sunan Annie ne da kuma y'arta wato Ammi mahaifiyar Jabeer taci.kallon Basma Umma tayi tace "ina kuma Layan din ta wuce? ". Zama a d'aya daga cikin Sofa's din parlon tayi tare da cewa " ina fa Umma kinsan ta wuce wurin Annie ne"."oya maza kije ki cire Uniform din lokacin Islamiyya yana k'urewa"....kamar ko yaushe tun daga waje take k'wala kiran "Annie,Annie nikan ina kika shige Annie gani na dawo daga makarantar" she was speechless a tsananin tsorace take waro manmanyan idanuwanta tare da langwab'ar da kai a k'asa.tuni sakakken yalwataccen sumar kanta ta zubo a bayanta tare da bajewa a duka fuskarta .cikin jin zafin fusgarta da Veer yayi cikin shak'ak'en murya tace"wallahi Yaya ban ganka ba,ban kula da kai b..."sauran maganar ta mak'ale sakamakon kyakyawan marin da Veer ya wanke fuskarta da shi.iya k'arfinsa yasa hannu tare da ingijeta daga jikinsa da take shirin fad'owa.a can jikin TV stand kanta ya bugu ta sakin wahalliyan k'ara kad'an dan tasan baya son ihu ko kad'an."innalillahi wa'inna ilaihir raju'een Jabiru,Jabiru kana tsoron Allah kuwa,ni na tabbata ka mutu a haka wuta can Allah zai maka masauki,kashemun y'ar zakayi to wallahi bari maryam ta dawo kai ko darajar sunan da taci ma ba zaka tausayawa yarinyar nan ba? Duka duka nawa Laya din take"sai kuma ta fashe da kuka tana nufo in da Layan ke kokarin tashi..cikin jin jiki take fadin"Annie ki barsa dan Allah,ban gani bane n dora masa jakkan school dina,basai kin fad'awa Ammi ba"."ke rufemun baki yaune Jabiru ya fara cin zalinki a gidan nan?".k'arar bud'e k'ofa yasa duka suka mayar da kallonsu a wurin..Jabeer ne ke barin parlon hankalinsa kwance kamar Wanda beyi komai ba...Annie ta kama Layan zuwa bedroom dinta tana ta sababi..tsuke fuska Layan tayi duk da yarda fuskarta ta haye ga shatin hannun Jabeer kwance a fuskarta sannan tace"wai Annie meye naki a ciki,ina dai ni ya doka bake ba? Kuma nace abar maganar nan dan Allah".sake da baki Annie tabi Layan da kallo ta saki dariyan bosawa tace"tabdi jam.in ke lalacewa ta same ki to banda ni wallahi wallahi kinji na rantse ni banyi gantalewar da zan saka ido ina kallon Jabiru yana abunda yaso a gida ba".Bata ko kula Annie ba ta kwashi bag da hijab nata tayi bedroom tana tura baki,ita ko kad'an bata ga laifi a abunda Yaya Jabeer ya mata ba.....sallama yayi ciki ciki tare da k'arasawa kusa da Ammi ya zauna kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace"Ammi kin kira".banza tayi masa har sai da ta karasa cike paper's din da take dubawa sannan ta cire white eyeglasses dinta tare da ajiye pen din hannunta kafin tace"so nake naji me layan ta maka ka mata wannan dukan harda buga mata kai da bango"waro ido Jabeer yayi kamar zaice wani abu sai kuma yayi shiru."I think ka kurumce anyway let me drop this in your head,na rabaka Layan tunda bakai ka haifeta ba,to banga dalilin treating dinta da kakeyi haka ba,tunda kai baka da kunya da kara,tashi ka bani waje"lumshe idanuwansa yayi cikin cool voice yace"kiyi hakuri Ammi"ko kulasa batayi ba ta kwashe kayanta ta bar masa parlon As if zai gano wani abu a jikinta haka ya bita da kallo..d'akin da Layan take ta tura ta shiga Muhibba ta samu da cup a hannu ga Layan jingine da bed sai tura baki takeyi ..."kin bata maganin?"kallon Ammi Muhibba tayi kafin tace"to Ammi wai bata sha".karasa shigowa tayi cikin d'akin cikin daure fuska tace"bansan iskanci halan na fara wasa da ke?"rau rau tayi da ido kafin ta karb'i maganin tana hawaye tasha da kyar sannan tayi saurin daukar Shayin da Muhibba ta kawo mata tun dazu ta banzatar sai yanzu take sha.tab'e baki Ammi tayi ta fita ta bar masu d'akin....sosai Jafar ke dariya harda rike ciki yana kallon yarda Annie ta dage tana nuna masa yarda Jabeer ya dodoki Layan..."ah to ni lalacewata bata kai nan ba Jahwaru niko jiki har rawa yake na isa sashen maryam da ta dawo aiki na sanar mata abunda wancan yaron yayi na kara da cewa maza tasa ya hada inasa-inasa ya kama hanya ya tafi gidan ubanshi mu bamu gayyar tsiya ko nayi ba daidai ba? Saboda Allah ai zalinci babu kyau ko?,Allah sarki Laminu ni nasan da yana nan duk ba haka ba,yo yana kusa waya isa ya saka Laya kuka?".....Da safe ba laifi zazzabin ya saki Layan har tayi shirin zuwa school da yake tana karantar medicine ne tana shekara ta biyu,Muhibba kuma law in da Basma ke karantar Entrepreneur dan tana sha'awa kasuwanci sosai kuma shine abunda familyn su sukafi yi sai dai da yake gidan y'an boko ne yasa suka tara ma'aikata da makaranta da dama a gidan...kai tsaye tana fitowa main ginin gidan ta nufa in da nan ne Asalin gidan ,gidan Alhaji Ahmad Wanda suke kira da Abba kenan kuma shine yaro na farko a wurin Annie Wanda yake da 2wifes Hajiya Badiyya wacce suke kira da Momy itace ta farko tana da yara hud'u Lamin shine babba Wanda Barrister ne yaje wani course a Uganda shiyasa baya nan sai Hydar shi kuma Dan kasuwa ne sai Faruk yana karatu sai Muhibba Auta,sai Hajiya Aisha wacce suke kira da Aunty Amarya tana da yara ukku Jafar Wanda tare aka haifesu da Hydar shima kuma Dan kasuwa ne dan komai tare suke yi sai Basma sai Ahmad takwaran Daddy Wanda suke kira da khalifa yana JS 2.Sai Alhaji Sadeeq Wanda shi ne ke biwa Abba suna kiransa Daddy matarsa d'aya Hajiya Fatima wato Umma yarinyarsu d'aya wato Layan..Sai Ammi maryam takwarar Annie wacce itace Auta kuma y'a Mace tilo a wurin Annie tayi Aure ta Auri Alhaji Sadeeq Dan gaske hamshakin mai kudi Wanda a garin kano da kewaye suke alfahari da shi,shekararsu sha shidda da aure sannan ta haifi Jabeer .mahaifiyarsa da kanwarsa Hajiya Fatima Ummi su kadai suka rage masa itama tana aure a nan kano Allah yawa mijinta rasuwa tun Jabeer na da Shekara biyar Biyar kuma har yau bata kuma yin aure ba ta dawo gida ta zauna a part din da yayunta suka gina mata a cikin gidan.... A parlo ta samu Mummy da y'an aiki suna had'a dining sunkuyar da kanta tayi k'asa kafin tace"ina Kwana Mummy"sai da Mummy ta kare mata kallo daga sama zuwa k'asa kafin ta tab'e baki tace"lafiya" bata kuma cewa komai ba tayi hanyar stairs a tsawace Mummy tace"kije sama kiyi mene? To Alhajin be tashi ba jiya be shigo da wuri ba,kar Wanda yazo cikinku kuma ya damesa"kallonta kawai Layan keyi amma bata ce komai ba ta fita tana tura baki xuwa part din Ummanta da sallama ta shiga jiki a sanyaye,kallonta Umma tayi kafin tace"lafiya kika shigo mun d'aki a haka ko tun safe halin zaki fara?"..cikin shagwab'a tace"naje ganin Abba shine Mummy..."bata k'arasa ba Umma ta datseta ta cewa"bani wuri da wannan sakalcin naki baya k'arewa har yau naga ranar da zaki girma shi Wanda ya shagwab'aki ya tafi ya barmu da ala k'ak'ai a gida"..tura baki taci gaba da yi ta fito parlo ganin Jabeer yasa tayi saurin k'asa da Kansas cikin in ina tace"ina kwana Yaya"siririn tsaki ya saki har zai koma baya sai Umma ta fito hannunta rike da plate da spoon "a'a Son harka fito,k'araso ka karya dama yanzu nake tunaninka a rai". Kallonta ta mayar kan Layan" kije ki d'auki me zaki d'auki saura a tafi a barki kice kinyi latti".hawaye ne suke son zubowa a idonta da k'yar ta mayar da su ta wuce d'akinta Wanda sai ta mance rabonta da shi dan tafi zama a part din Annie ko Amminta dan mutane da yawa suna dauka Layan ce Ammi ta haifa ba Jabeer ba...sosai ransa ke kunci da kyar yake shan kunun gyad'an da Umma ta zuba masa haka kawai yaji komai ya fita a kansa da kyar yasha kad'an duk da kowa yasan a gidan abincinsa hannun Umma yake ko part din Annie shi mutun ne mai kyankyami ba komai d ya fito daga hannun kowa yake iya ci ba,Sallama yawa Umma ya fita yabar gidan gaba d'aya ko zai samu saukin abunda yake ji... Comment and share Oum Aryaan. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Page 3 Driving yake amma zuciyarsa wani iri take masa har wani tashi tashi takeyi dan tsabar takaici da kuncin ganin Layan da yayi duk lokacin da zaiga yarinyar takan dagula masa lissafi ta tab'arb'arar masa da duk wani farin ciki nasa da take tattali juya kan motarsa yayi zuwa gidan Hajja wato Mahaifiyar Abbansa mai rasuwa..tunda ya shiga gidan ya beko kallon ma'aikatan daketa masa sannu da zuwa kai tsaye ya shiga parlon Hajja bakinsa d'auke da siririyar sallama Wanda ba lallai kowa yajisa ba.farar Dattijuwa ce wacce manyanta ya kamata idonta sanye da farin glass tana duba hisnul Muslim sai da takai k'arshen addu'ar da take yi kafin ta d'ago fuskarta fad'ad'e da fara'a tana kallon Fuskar Jabeer da tayi wasai sai dai alamun k'unci da b'acin rai ne ke kai kawo akan kyakyawar fuskar tasa.Ajiye littafin tayi cikin so da k'auna ta mik'a masa hannu tare da fad'in"meke damun Autana? Waya b'atamun ranka? In ce dai ba Maryama bace dan itama wannan karon hukuncina bazai shallake kanta ba".Lumshe idanuwansa yayi yana kuma jin tsananin soyayyar Hajja na ratsa shi kai tsaye wurin k'afafunta ya zauna tare da d'aura Kansa a k'afarta ya kuma runtse idonsa gam-gam yana jin b'acin ransa na sauka a hankali a hankali. Murmushi Hajja tayi ta soma saka hannunta tana d'an bubbuga bayansa alamar lallashi.Sake da baki Ummi ta bisu da kallo duk da ba yau ta soma ganin lallashin Hajja ga jikan nata ba,k'arasowa tayi cikin parlon ta zauna tare da saka hannu ta dungure keyar Veer tace"oya d'agamun uwa,tunda kai kace ba zaka bar zucitarka ta zauna lafiya ba,kullun ayi mutun fuskarsa a d'aure dinkim ba fara'a? Kullun sai fushi".ringing din wayar Ummi shiya katse mata magana kallon wayan tayi ta kuma kallon Veer da suka had'a ido cikin alamar tambaya tace"me kayiwa Annie?".shiru yayi tare da d'aga kafad'a ya kawar da kansa..Daga wayar Ummi tayi tare da sakawa a speaker tare da cewa "Assalamu alaikum Annie an tashi lafiya ,ina kwana"...." Wa'alaikis salam shima dan ya zama dole na ansa,batun na tashi lafiya ko ban tashi bama duk bata taso ba dan kin jiyewa kunnanki ahto,jiya gigice na kwana Allah ,Allah nake garin Allah ya waye kada na kiraki jiya kuma ace Janar na nan,to gaskiya matsalar babba ce Wanda kab dangi sai kun hallara dan samun maslaha ,jiya jiya nan nake gaya maki akan Laya muka kwana irin wasan kuran da wancan mai bakin halin Jabiru yayi laga-laga da ita baki gani ba,dan ni da farko nasa ma rai zaiyi halinsa,kinga k'ara tun wuri a shiga tsakani to Allah na tuba meya hadasa da laya banda ni dana haifi uwarsa ita kuma na haifi ubanta? Ahto ba ruwana kara asan nayi dan Sam bani so Jabiru ya mutu a haka dan nasan Allah wuta zai saka shi kodan hakki,kuma ai Wanda kake so ya wuce nan." "Adaiyi hakuri Annie insha Allah zan tsawatar hakan bazai kuma faruwa ba,amma gaskiya Veer be kyauta ba,ayi hakuri "Ummi ta fad'a dan bata so ta kuma tono Annie tsab yanzu zata masu tas...kashe wayan tayi tana bin Veer da kallo Wanda ya sunkuyar da kansa k'asa " Abunda kakeyi kana ganin daidai ne ko Jabeer,is this the best gift da zaka sakawa Umma da Abba da soyayyan da suke maka? Kai bakaji kunyar kanka ba? Let me tell u this,Umma ita macen da tun yayenka ta d'aukeka ta rikeka ita da Abban Layan basu tab'a bari kayi kukan rashin mahaifi ba,ko wani abu na bukatan rayuwa har gobe komai naka a hannunsu yake amma ka rasa Wanda zaka tsana sai gudan jininsu d'aya da suka Haifa a duniya Jabeer.one day one time zakayi nadaman da ba ita ake so ba,in ka gyara kanka idan ka kiya shima ruwanka." "Ya isa haka Ummin yara,insha Allah kuma zai daina Layan dai jininsa ce ta har abada kuma k'anwarsa ce ni kinga kuga kuwa babu yarda za'ayi ace baya sonta sai dai wani dalili na daban kuma komai zaiyi daidai kuci gaba da yi masu addu'a" Hajja ta fad'a tana mayar da kallonta ga Jabeer cikin sanyin murya da rarrashi tace"Babana meke had'aka da Maryama k'arama? Kasan yara hakuri ake dasu ka daina yin duk wani abu da kasan zai janyo maka magana ,Babana shifa alkhairi danko ne bibiya yake yi ,duk da bansan dalilinka ko hujjarka ba amma dan Allah a kiyaye danni bazan tirsasaka sai ka fad'a ba abunda kawai nake so shine naga canji".sosai Ummi ta shak'a tace"Hajja lallashinshi fa kike yi? Kuma keda kanki kinji meya aikata,baya da wata hujja data wuce yace maki baya sonta ne kawai,kuma ai bazai kasheta ba tunda bashi ya halicceta ba wallahi wallahi ina mai tabbatar maka ka kusa dawowa gidan nan kabar yarinya ta huta ko ka tattara kayanka ka koma wurin aiki hutun ya isa haka,Allah ya bada lada tunda kai baka San kara da kawaici ba"....sosai Ummi ta masa tas,dan Ummi irin matan nan ne da nasa wasa ko daukar al-amari da sauki kuma tasan sarai irin abunda Jabeer yake yiwa Layan ,maca ce ita mai zafi bata son raini kwata-kwata...kallon Ummi kawai Jabeer yake yi maimakon yaji zuciyarsa tayi sanyi a'a saima zafi da kuma tsanar Layan ke kwarara da ratsa duk wata gab'a,k'ashi da b'arko na jikinsa har wani d'aci d'aci yakeji a makoshinsa saboda tsabar takaici yanzu akan wannan mai kama da y'an ruwan yarinyar ake masa fad'a kamar wani yaro? Ya tambayi kansa sai dai bece komai ba illah"Ayi hakuri Ummi" "sorry for your self Jabeer ,Hajja ni zan wuce sai na shigo jibin insha Allah" Ummi ta fad'a tare da tattara belonging's nata tabar parlon ranta a b'ace.......kwance take akan makeken bed dinta taja white duvet ta lullube duka jikinta banda fuska,yalwatacciyar sumar kanta bak'a sid'ik itace baje ta rufe gaba d'aya fuskarta ta bazu akan lallausan pillon da take kwance tana bacci hankalinta kwance...turo door din Ammi tayi kasancewar yau weekend bata zuwa hospital ta shigo tana kuma kallon agogo 11:20am ta gani k'arasowa tayi a bed din tare da tapping laps din Layan dake sharara bacci,sake juyawa tayi cikin bacci a hankali take fad'in yaya Veer,Yaya Veer sai kuma magana wacce Ammi sam bata tsaya ta saurara ba ta tapping dinta da k'arfi.a firgice Layan ta tashi tare da turo d'an karamin bakinta gaba kamar zatayi kuka tace"Ammmmi"kallon da Ammi ta jefa mata yasa tayi shiru tare dayin k'asa da kanta "bazance ki daina ba kije ki kashe kanki saboda shi,karki focusing akan rayuwanki kullun ki tsaya kina dreaming da b'atawa kanki lokaci ,ki kalli time ina ga zaman jiranki za'a tsaya yi...A hankali ta zuro siririn doguwar k'afarsa tare d Santa bedroom silifas dinta kafin ta mike tana goggoge fuskarta da kallon Ammi ta bita sanye take da White sleeping dress trouser ne Rabin labs dinta sai shirt mai vest hand iya west dinta.bajajjen sumar kanta ta tattare ta saka hula tayi toilet..in minute Ammi ta gyara d'akin tas Wanda Layan ta mayar dashi out of order sannan ta fita tare da janyo mata k'ofan....A k'a'idar gidan duk weekend a parlon Annie kowa ke haduwa anan ake breakfast, lunch even Dinner tare da iyayensu da kowa.....Gyara zama Abba Ahmad ya kumayi yana cin d'umamen tuwan da Annie ta kawo masa yace" nifa har yanzu taron nan ya kasa cikamun banga Mamana ba da Son".tab'e baki Hajiya Badiyya tayi tare da cewa"inafa zakaga y'ay'an milkin ai ba kamar gwanar nasan ana can ana bacci marar amfani."Murmushi Aunty Amarya tayi mace mai kawaici da Hakuri tace"Haba yanzu zakaga yar tawa Mamar masu gida,Veer kam jiya anje gidan Hajja bana da tabbas ko ya dawo,shima Dan neman guda"ta k'are zancan da dariya dan kawar da zancen da Hajiya Badiyya tayi....kafin wani ya sake magana Layan ta shigo cikin shirinta tsab da ita sai tashin kamshi take. Murmushi sosai ya bayyana kan fuskarta da sauri ta iso gaban Abba ta zauna dab da shi,sai kuma tasa hannu ta rike hannunsa sosai cikin nata race"Abbana I missed you so much".."nikan nayi fushi Mamana yau almost to 4days we haven't meet bansan meke hanaki zuwa dubani days din nan ba."....wani takaici ne ya kume Hajiya Badiyya har bata gani da kyau ta tashi ta fice rai a matukar b'ace bata so tayi magana kuma Annie ta daura daga in da ta tsaya dama basa shan inuwa d'aya. Comment and share. Oum Aryaan. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Page 4 Kanta ta kwantar a kafad'an Abba cikin cool voice tace"I'm sorry Abbana,I missed you so much,bazan sake ba".Hannunsa ya daura a kanta tare da cewa"Allah yayi maki albarka Mamana ,Allah ya zama gatanki ya jib'anci lamurranki"Duk Wanda ke a parlon da Ameen kawai yake ansawa banda Veer da zuciyarsa tayi bak'ik'in tsabar takaici da wani irin k'unci dake tokare masa zuciya.lumshe kyawawan idanuwansa yayi Wanda tsabar b'acin rai suka soma canza kala hannu yasa yana shafa tulin sumar kansa dake ta shek'i alamar gyara ya kamata.Daddy ne ya lura da shi fuska cike da fara'a yace"a'a My son k'araso mana,yaushe ka shigo?"b'ude idonsa yayi cikin Dan sakin fuska kadaran kadahan yace"yanzu na shigo Daddyna"sai ka saurara sosai zakaji abunda ya fad'a kafin ya shigo ya gaishe da Abba dasu Aunty Amarya..Umma kam tunda Veer ya shigo ina taka saka taka ajiye ta soma had'a masa abun kari sai tattalinsa takeyi tanaji kamar shi kadaine yaron a wurin..tab'e baki Ammi tayi jin abunda Umma ke fad'a tace "Haba Yaya Fatima ai son kanku yawane da shi yanzu duk girman parlon nan amma ace kin mayar da gandamemen saurayi kamar wani jariri,ai shiyasa yake tab'ara yarda yaga dama ,duk laifinki ne ai"...." Annie ta mele baki kamar taga abun k'i tace"a'a a'a Maryama bansan kuma yaushe kika maida Hassada abincinki ba ,yo in banda haka,gaskiya mutun sai Allah yanzu ki rasa dawa zaku cakud'e sai Dan da kika Haifa a cikin ki? To ke ba abun murna bane,ni bana son haka,karki takura yaro a barshi ya b'ararraje in ba haka ba dai Allah yana kallonki,karkizo ki biyewa son zuciya"...sake da baki Ammi tabi Annie da kallo sai dai bata ce komai ba dan tasan halinta ba kuma dainawa zatayi ba,yanzu yanzu zata gama cashewa da mutun amma anjima babu tamkar shi.A haka akayi Karin cikin jin dadi da ammshuwa kafin su Basma sukayi shirin Islamiyya suka shiga babban masallacin gidan dan bada harda da sauransu dan duk girman yaro a gidan dole kaje islamiyya in har akwai lokacin.....ciki ciki yayi sallama ya shiga cikin parlon ya samu daga daga cikin Sofa's na parlon ya zauna yana sauke ajiyar zuciya ruwa masu saukin sanyi ya daukar akan table Wanda aka ajiyewa Ummi ya b'alle marfin robar ya soma sha a hankali yana sauke ajiyar zuciya.Ummi dake waya ta juyo tana k'are masa kallo sai dai bata ce komai ba har sai da ta k'arasa wayar Wanda da Ammi ne sannan ta sauke tana kallonsa tare da ansa gaisuwar da yake mata.Ummi ta had'a fuska tace"ni Jafar nace a turomun ba kai ba,bazan bika ba so I can drive my self ".Murmushi Jabeer yayi yace" kiyi hakuri"...harararsa Ummi tayi tare da cewa"hala wani abun kayi kuma?".sunkuyar da kansa kawai yayi bece komai ba yana kallon zara-zaran fingers dinsa kamar mai son tuno abu.Dama tasan bazaice komai din ba sanin ko Ladi ta kawo abinci baci zaiyi yasa ta tashi da kanta zuwa kitchen din ta had'o masa abincin da drinks da ruwa duk a tire tazo ta ajiye gabansa tace"kaci bari in shirya kafin yaron nan su shigo daga school sai mu wuce..gyad'a kai kawai yayi sannan ya soma tsakaurar abinci a hankali kamar Wanda akawa dole yaci..beci wani sosai ba ya ture tire din ya jingina da sofa yana latsa waya...runtse idanuwa yayi da k'arfi jin muryarta ta karad'e parlon tun daga k'afarsa har cikin tsakiyar k'walwar kansa yake ansawa dandanan fushinsa ya tashi amma be d'ago ba bare ya kallesu ita da Asma'u da Jalila ne yaran Ummi Wanda suke kai d'aya suketa zuba surutu suna dariya da yake school dinsu d'aya..turus tayi showing her thirty-two waje mad'aukakin farin ciki na ratsa duk wata gab'a ta jikinta wani sanyin dad'i ke ratsata Murmushi kawai take saki da Sauri ta iso gabansa tace"Yaya"bakinta ya kasa rufuwa d'ukawa tayi har k'asa kusa da k'afafunsa ta rike hannunsa cikin nata tace"Yaya yaushe kazo? Amma Ammi cewa tayi Yaya Jafar zaizo daukar Ummi ba kai ba"....kamar Wanda aka jonawa wuta haka Jabeer yaji a jikinsa duka wani zafi ya rufeshi da iya k'arfinsa yasa du biyun hannuwansa ya ingije Layan ,in seconds ta isa da table din da yake wurin ta fad'a a kansa hannunta data bige ta rike hannu tana jin wani tsananin zafi da zugi yana ratsata sai dai idanuwanta akan Jabeer k'yar ta kasa d'aukesu tare da murmushin dake kan fuskarta..zazzaro dara daran idanuwansa yayi cikin tsananin b'acin rai yace"this should be the last Monster, don't you there in your life repeat this mistake,if not wallahi wallahi azeem sai dai a haifo wata ko kuma ki k'are rayuwarki babu hannu,ni sa'anki ne?".ganin kallonsa kawai take yasa ya kwashi pillows ya wurga mata a fuska yace"mayya ba zaki daina kallona da wannan aljannun idanuwan naki ba?" Cikin Sauri Layan ta janye idanuwanta tana fad'in I'm sorry,I'm sorry Yayana,na daina bazan kuma ba ,kada ka b'ata ranka dan Allah I'm sorry"...zazzaro ido Jalila da Asma'u sukayi da Sauri suka zo suka d'aga Layan zuwa d'akinsu....cikin tsawa Asma'u tace"jar ubancan waike Layan kin haukace ko kina da hankali kuwa? Dole sai kina zuwa wurin Yayan ne? Kina so a kashe ki ne? Ni bansan wannan wacce irin tsana bace ,sannan kice wai kada a fad'awa Ummi."Harara Layan ta bakawa Asma'u tace"to meye damuwanki a ciki? Ina ga dai jikina ya daka? To nace kuma na yafe kar a fad'a dan Allah kiyi hakuri abar maganan,ni nasan komai mai wucewa ne ,and even in second bazan tab'a jin zafin abunda Ya Jabeer kemun ba sai ma addu'ar Allah ya cikamun burina a kansa,so u not worry ba yau aka fara ba ,ba kuma za'a k'are yau ba so chill."kallon mamaki kawai suke binta da shi murmushin takaici Jalila ta saki tare da cewa"to Allah ya baki lafiya Layan ina ga jinnul Ashk'i sun kawo maki hari sai an rik'a had'awa da rokin Allah"..shigowan Ummi d'akin yasa duk sukayi shiru"shine kunsan Ku nake jira kuka shigo ban baku da lokacina?,to maza Layan tashi kici abinci ki wuce muje Amminki tace k'afata k'afarki"...Gaishe da Ummi kawai tayi ta tashi cikin sanyin jiki kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki ta wuce kitchen jin cikinta takeyi a toshe gudun kada ta musawa Ummi ne ta gano wani abun yasa tayi shiru .kad'an ta saka abincin bayan ta gaishe dasu Ladi anan ta zauna tana ci ba jimawa ta gama duk da ba ci ta wani yi ba ta fito ta koma ta dauki school bag dinta ta fito parlo wurin Ummi da suke jiranta..kallon sama da k'asa Ummi tayi mata kafin tace"yanzu nan har kinci abinci?to ke kika sani wuce muje."Murmushi kawai tayi batace komai ba kafin suka fito gate da Ummi.kallonsu kawai Jabeer keyi amma bece komai ba ya taso ya bud'e mota ya shiga,Ummi ma ta shiga,Layan tazo zata bi bayan Ummi.Ummi tace "halan shi Jabeer din Driver ne ko? My friend kin wuce gaba ko kuwa". Turo baki kawai Layan tayi ta bud'e motar ta shiga,Jabeer kam bece komai ba ya soma driving suka bar cikin gidan ya doshi unguwarsu..A motan bece komai ba sai dai tsab Ummi ta gama karantar tsananin b'acin ran da yake ciki sai ko kusa yaki nunawa kuma ko da wasa be kalli in da Layan take ba...sosai Ummi ta zurfafa tunani tana jinjina wannan tsananin kiyayyar da Jabeer kema Layan sai dai duk yarda taso lalubo wani abun amma abun ya faskara dan ta kasa samo wata hujja ko madafar da zata rike akan lamarin Addu'ar shiriya kawai tayi masa taci gaba dayin wani tunanin daban. Comment and share Ouhmm Aryaan *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Page 5 Kallonta kawai Ammi keyi lokacin data zauna kusa da ita tana ajiye school bag dinta kafin tace"shine daga labari kika kwasa kika yi can wurin Ummin,da kinsan Wanda xaije d'aukota aida ba kije ba,danna tabba bazai barki haka nan ba."Murmushi kawai Layan tayi tare da cewa"Allah Ammina bemun komai ba"ta k'arashe zancan tana mak'alota sosai a jikinta kamar wasu aminan juna.dungure mata kai Ammi tayi tace"dadai ba Jabeer bane ,to ki adana kalamanki ki fadawa wata danni kinsan nayi hardar karyar da kika saba zubawa a kansa".Tab'e baki Ummi tayi tace"wannan kuma lamarinsu ai sai su.Mikewa kawai Layan tayi ta fice daga part din ta wuce na Umminta da sallama ta shiga Parlon a d'aya daga cikin kujerun d'akin ta hango Umma zaune ta cab'a ado kamar ko yaushe dan Umma badai kwalliya ba,k'aramin azkar me hannunta tana karantawa bata kula Layan ba sai da takai aya sannan tace"wane sabon salone kuma zaki zo kimun tsaye aka kamar wata bishiya".zunb'uro baki Layan tayi kafin tace"nifa kawai zuwa nayi "." To an gode Allah yayi albarka sai ki koma wurin Ammin taki dan kinsan ni bazan dauki wannan sakalcin naki ba yanzu ma sab'a"."to ai Ummi ce tazo sai na basu wuri ko."Layan ta bada ansa Umma bata kuma cewa komai ba taci gaba da karatunta dan tsab ita bata daukar rawan kan Layan yanzu ta kai mata duka...Tura baki Layan tayi kafin ta wuce d'akinta danyin wanka ta canza....kallon Hydar kawai Momy Badiyya keyi zuciyarta cike da tsabar takaici da k'unci cikin fad'a tace"shin wai Hydar Fatima ta Haifa mun kai ko ko uwarme kake nufi?,wallahi wallahi ka fita idona sakarai Wanda besan kishin uwarsa ba kawai,kai yanzu Fatima da wata y'arta har abun sone a wurinku in banda rashin zuciya irin taku,matar da aka fifita ta zama mowa ita da yarta akan karan kanku da mahaifitarku duk da baku had'a komai ba baccin Sadeeq daya jajibo mana,in kyautar ka tashi yi baga Muhibba nan ba,kai kara ka bawa Basma ma daka ba wancan bak'ar yarinyar mai kama da tsinken tsintsiyar kwakwa,sallamamme bani agogon nan".ta daure fuska tare da mik'a masa hannu.Bece komai ba ya d'auka ya mik'a mata ya tashi zaibar parlon Momy ta rakashi da Harara tana jan tsaki zuciyarta na zafi....mayar da kallonta ga khalifa takwaran Daddy tayi tare da cewa"b'ace mun da gani ka baza kunne kaje ka kai rahoto to ka mayarda hankali kaga in banyi maganinka a gidan nan ba"..Aunty Amarya kam dake dining tana shirya culas yi tayi kamar bataji me suke fad'a ba...."Abba dan Allah yaushe Yayan zai dawo,ina kiran wayarsa amma bata tafiya"Basma ta tambaya.Murmushi Abban yayi tare da cewa"gobe insha Allah i war haka Lamin yana nan tare da mu,yace kada a fad'awa Mamana ne sai dai ta ganshi kawai".wani ihun Murna Muhibba da Basma suka saki a tare kowa da abunda yake fad'a.....A hankali take fitowa daga d'akin to make sure batayi wani sound da zaija hankalin Umma ba tace mata bata da natsuwa da hankali sanye take cikin atamfa royal blue da ash riga da sike dinkin yayi daidai da ita d'as ga dan karamin kugunta kamar an zana a cikin siket din scarf dinta a hannu sai ribbon ta taho tana tura baki,sosai tayi kyau dan Layan asalin y'ar gayu ce duk rawar kanta akwai shegen tsabta da iya kwalliya gaban Umma tayi raurau da ido kamar wacce zata fasa kuka har idonta ya tara ruwa tace"Umma please ki daure mun na kasa"from head to toe Umma ta bita da kallo tare da tab'e baki tace"as big as you are Layan kina 22 years kina university amma har yanzu baki iya daure gashinki ba?kin b'acemun a wuri ko sai nayi maganinki yanzu".with out second thought Layan ta b'are baki da sakin kuka,cikin Sauri Hydar dake dining yana cin abinci yana kuma kallon drama ya taso da Sauri ya janye Layan daga dukan da Umma ta kawo mata,aiko tana ganinsa ta kuma shashakwewa tana kiran Yaya hannunta ya kama yana fadin"Afuwan Ummanmu ba zamu sake ba,lallai yau ana so Abba yayi hukunci da kowa a gidan nan an tab'a Annie k'arama".ya k'are zancan yana dariya kafin suka fita daga part din zuwa na Annie acan ya zaunar da Layan yana tubke mata tulin sakalkiyar sumar kanta wacce ta sauka har bayanta yana kuma aikin lallashi...Annie dake kan abun sallah da carbaha a hannunta anata istigfari tayi saurin yaye Hijab din jikinta tare da kai k'arshen lazimunta tace"Kai Aliyu meka mata daga dawowarta makarantar ko hutawa batayi ba,me aka mata?"...."ita da Umma ne tana so ta daure mata gashi "...." Hubuhu duniya ke Laya meya kaiki wurin Fatima? Dama dai kinsan bayi maki zatayi ba,shiyasa nace zanje kauye wurin malaman Allah da Annabi bafa boka ba,danni bana bin la'anannun Allah,kawai dai suyi mana addu'a da bamu k'aik'ayi koma kan mashekiya dan tabbas ba banza ba yarda Fatima take maki kamar ba ita ta haifeki ba ,,,keni duniya ba tsoron Allah ba ruwana bama nufin kowa da sharri amma dole mu tashi mu k'are kanku wannan zamani duniya ba tsoron Allah ba tawakkali sam".......Zaune yake akan sofa ta babban parlon part din su na mazan gidan,sanye yake da farin 3quater sai white singlet k'ar tana nan kamar ba'a tab'a sakawa ba idanuwansa a lumshe sai tashin sanyayyen k'amshi yakeyi,waya ne kare a kunnansa da alama magana yake da wani mutun mai mahimmanci a rayuwarsa,kad'an yad'an saki fuskarsa alamun Murmushi tare da shafa tulin sumar kansa tare da cewa"Owk Allah ya kawo ka lafiya ,nima kai nake jira na wuce hutuna ya k'are"banji me aka ce masa ba sai naga ya ajiye wayar tare da tsurawa silin ido kamar mai son gano wani abu.....Shigowar Daddy parlon Annie yasa duk suka mayar da hankalinsu a kanshi banda Annie data wuce kitchen dan daura girki dan ita Sam bata fasa girki ba,ko yan aiki a sashenta bata so.cike da girmamawa Hydar ya gaishe da Daddy tare da Jafar Wanda yake shigowa yanzu,kallon Layan Daddy yayi tare da cewa "naga motar Yayanki yana gida maza kiramun shi bana so na makara kuma ". Sai da gabanta yayi tsananin bugawa saboda tsorata duk da yarda take cike da zakun da buri da muradin ganin kyakyawar fuskarsa sai dai bata so taje ko dan tattalin farin cikinsa Wanda ta sani yana ganinta komai sai ya dagule,sai dai ko da wasa ba zata tab'a gujewa aiken Daddyn ba,Dama Annie an kusa tasan ba zata tab'a bari taje ba.kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta mik'e tana d'aura dankwalinta ta fice daga d'akin zuwa madaidaicin part din nasu..cike da tsananin tsoro fargaba bawai na dukan da zai iya mata ba a'a sai na bata son taga b'acin ransa wannan shine abu mafi wahalar da zuciyarta ta rasa meyasa tun tana jaririyarta har kawo yau tana rayuwa ne da so da kuma farin cikin Yayan nata a rayuwarta tabbas duk ranar rabuwarta da shi tayi imani cewa a ranar rai zaiyi bankwana da gangar jikinta a ranar duk wata jijiya ta jikinta da zuciyarta zasu gaza su kuma kasa d'aukar d'awainiyar gangar jikin nata.dan haka tuni ta sallama Jabeer shine rayuwarta ko da kuwa zai ringa yankan naman jikinta ne...tura parlon tayi sai dai ba kowa.dib dib dib haka zuciyarta ke bada sautin bugawa a hankali ta soma saka doguwar kyakyawar k'afarta wacce tasha ado da Jan lalle sannan ta taka zuwa kofar d'akinsa Wanda yake jingine Dana Yaya Lamin..A hankali tayi knocking kofar to make sure batayi sound da k'arfi ba gudun kada ya balbaleta da masifa duk da tasan akanta ne kawai zuciyarsa ta fiye hawa,jin ba'a ansa ba yasa ta kuma knocking can ciki ciki yace"come in".hannunta har kyarma yake ta samu ta bud'e tare da shiga ta tsaya a bakin k'ofar sosai ta rike hannuwanta tare da runtse idanuwanta Wanda take kallon k'asa cikin sanyin murya tace"Yaya Daddy yace kazo yana sauri ne"....Jabeer dake kwance rubda ciki ya bada kofa baya ya juyo da wani irin speed bakinsa har rawa yake cikin tsananin tashin hankali yace"you again?".waro dara daran fararen idanuwantayi ta d'agosu suka had'a ido.cikin k'araji Jabeer yace"innalillahi wa'inna ialaihir raju'un,sai dai kici kanki mayya kawai"kafin ya safko daga bed din jikinsa har rawa yake ya k'araso tare da d'auketa da gigitaccwen mari ya bud'e kofa ya ingizota gaba d'aya iya k'arfinsa baya ko tunanin irin fad'uwar da zatayi,jikinsa har rawa yake...Da k'arfi Layan ta runtse ido dan ta riga ta sadak'as yau saita karye k'ugu sai kawai ta jita a jikin mutun ,Aunty Amarya ce ta tareta sosai Layan ta k'ank'ame Aunty Amarya tana karanto duk wata addu'ar da tazo bakinta....kallon Veer kawai Aunty Amarya keyi ko kad'an batayi mamaki ba dan tasan zaiyi fiye da haka ma "ka kyauta Jabeer ka kashe Layan a gidan nan ka huta kawai,tunda kai bakasan kara da kawaici ba". Tana zuwa nan taja hannun Layan suka bar part din... Comment and share Ouhm Aryaan 07033636337 WhatsApp only *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Page 6 Kai tsaye part dinta tayi da Layan ta baya ma suka shiga dan Sam bata son wani yasan abunda yake faruwa Bare a sakata gaba da tambaya.har bedroom ta kai Layan ta zaunar da ita a gefen bed ta tsaya tana k'are mata kallo.k'asa Layan tayi da kanta hawaye masu zafi suka soma rige-rigen sauka a fuskarta duk yarda take k'ok'arin da son ta mayar dasu amma hakan ya faskara,siraran hannuwanta da suka sha ado da Jan lalle da bangles ta daga tare da k'are fuskarta duka dasu tana sakin kuka Marar sauti..Basma ce ta shigo d'akin tana k'wala Aunty Amarya kira sororo ta tsaya tana k'arewa Aunty kallo da kuma Layan dake kuka cikin sauri ta yunk'ura zatayi kan Layan Aunty tace"don't you try that,maza fice mun a d'aki,idan kin fita kuma naji labari a gaba"sunburar baki Basma tayi tare da cewa"Amma Aunty"."au bakiji mena fad'a ba kenan,in maimaita kaina?".Aunty ta katseta .shiru tayi ta fita tabar d'akin ...zaman kusa da Layan Aunty Amarya tayi tace"ya isa kukan haka Daughter bana son Amminki ta gane kinyi kuka kinsan hankalinta zai tashi ,shawara d'aya zan baki ki guji duk abunda zai had'aki da Jabeer batun yanzu baki Layan tun kina zanin goyonki kinsan manufar Jabeer a kanki to ki taimaki rayuwarki ki nisanta kanki da shi,kuma hakan baya nufin ki daina ganinsa a matsayin Yayanki a'a sai dan ki guje masa fad'awa fushin iyaye sanin kanki ne duk ranar daya maki duka to Ammi tana fushi dashi ke kuma nasan ba zaki so hakan ba.dan Allah Layan ki guji duk abunda zai had'aki dashi ,mu had'u mita masa addu'a Allah ya sassauta masa wannan tsanar da yake maki wacce bata da makama bare tushe babu kuma Wanda yasan dalilinta bare muce ga k'arshenta"....Layan kasa fadin komai tayi sai kai kawai data girgizawa Aunty tare da k'ak'aro Murmushi tana zancan zuci taya mutanan gidan su zasu San ba zata tab'a iya nesanta kanta da Jabeer ba,ilahirin rayuwarta ta ginu ne a tsananin son Jabeer da bautatawa sonsa ko da ace a kullun yankan naman jikinta yake yi bata tab'a jin zata bar sonsa kamar yarda yake jin har abada bazai tab'a daina nuna tsana da kyara gareta ba,ta tabbatar duk ranar data rabu da Jabeer to ranar ne ranar mutuwarta ko tantama batayi ranar rai da ruhi zasuyi bankwana da gangar jikinta,firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula sanadin tab'ata da Aunty Amarya tayi murmushin ta kuma yi mata tasa hannunta tare da shafar fuskarta da tayi sakayau bak'inta sai k'yalli yake da sulb'u kafin ta shiga toilet ta wanke fuskarta kamar yarda Auntyn ta umarceta sannan ta samu damar fitowa daga part din zuwa babban parlo.Da gudu Khalifa yaso ya rungumeta cike da tsananin so da k'auna da yakews yayar tasa dan duk gidan babu Wanda khalifa yake matuk'ar so kamar Layan da Jabeer yace"Yaya Layan ina kika shige duk gidan nan bakya nan har Daddy da Yaya Jabeer sun fita tare,Yaya yace zai siyamun chocolate ".Murmushi ta sakar masa kafin tayi magana kuma Momy Badiyya ta rigata da fad'in 'kai Khalifa bana son surutun banza da wofi maza zoka nemi wuri ka zauna,ke kuma ki shiga kitchen ki taya su Ladi aiki kina mace har kinje university ace baki iya komai ba harkar kitchen sai zaman banza da neman magana ,da daukar rahoton gulma"... Kwab'e fuska Layan tayi kamar zata saki kuka tace" Momy kin manta ne? Kinsan bana iya shiga kitchen bana iya yin aiki".'rufemun baki amma aikin iya gulma ba? To maza tashi mai Asthma karya kije maza,in an maki aure ubanwa zai na maki aikin? Cavage da su carrots zaki yanka mun kota nan a k'aru da ke"...sakin hannun Khalifa tayi ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen tana aikin turar baki......Tunda tayi sallar asuba ta koma ta kwanta bata cewa komai ta zurfafa dogon tunani Wanda ita kanta bata San iya lokacin data d'auka tana yinsa ba tun tanajin hayaniyar y'an gidan da suketa kai kawo a ko wanne part girke-girke da gyaran gidan kawai akeyi sai kace zasuyi bak'i har ta daina jinsu ,Muhibba ce ta shigo d'akin da Annie tare da tapping long legs na Layan tace"ke madam bacci ba zaki tashi ba? Ko irin ma ki tambaya meke faruwa da gidan amma ke ko a jikinki sai bacci da tunani marar amfani".tura baki Layan tayi tare da kuma Jan Duvet ta duk'unk'une kanta kamar zata saka kuka dan duk jikinta ciwo yake yi saboda tsaiwanda tasha jiya na yanka Cavage ga hannuwanta duk sun d'ura ruwa cikin cool Voice tace"please Muhibba allow me dan Allah"...."to ki zauna kyayi takaici ke kad'ai a d'aki"...Annie dake jikin k'ofa tsaye ta k'washe labile tace"Amma in nace zanyi maganinku aga kamar cin zalinku zanyi.Mahibba na hanaku shigo mun d'aki idan nayi gyara,kuna da d'akin nan naga kuma waccan Narkekiyar tana da nata d'akin itama to bansan me kika manta ba da kika tahoman kika tile kamar shirgin doya,to wallahi zakuga tsiya tashi fita tunda ba gadona kikeyi ba".kyab'e baki Muhibba tayi tace"shi mutun sai rakad'i in banzo nan ba ina zanje,daga na shigo d'aki ki sanyani gaba."kanne ido Annie tayi tare da cewa "hmmm huuumm ni da d'akina? Nace ko d'akin Amadune kona Badiyya?" Ki tsaya ni da ubanki zanyi Ku baku isheni kallo ba". Ganin Annie na neman fita yasa Muhibba rigata ficewa tana kwashewa da dariya dan tasan sarai tana fita to wurin Abba zatayi kuma tsab zaiyi maganinta ta sani.....Gaba d'aya Ahalin gidan marigayi Alhaji Sulaiman Bulasawa dattijon Arziki Wanda ya mutu yabar tarin alkhairai da zuri'a a doron k'asa.jere suke reras a babban compound na gidan tun daga kan Anni har zuwa kan Khalifa Layan ce kawai babu a wurin...kowa ka gani fuskarsa dauke take da madaukakin Murmushi tsananin farin cikin da suke ciki ya kasa b'oyuwa kowa ya cab'a Ado musamman Momy Badiyya wacce tayi shiga cikin wani dangan les daga hannuwanta zuwa wuya da kunne ko ina yaji d'anyan gold sai fitar da sihirtaccen kamshi take yi tana ta ware hakoranta Wanda hokorin makka ya masu ado....Jabeer da Jafar,Hydar da Faruk su sukaje taro Lamin a filin jirgi.get din gidan aka wangale take wasu ratsa ratsab rides guda biyu suka sako kai na gaban Faruk ne a mazaunin driver sai Jafar a gefansa sai Hydar a baya.mai bi masu kuwa Jabeer ne a matsayin driver sai gefansa wani matashin saurayine da zasuyi agemate da Jabeer din...A tare zaratan samarin suka taho sai d'aukar ido sukeyi..wani kyakyawan farin dogon saurayi Wanda kusan komai nasu d'aya da Jabeer ya sako k'afarsa daga cikin motar kafin ya fito gaba d'aya sosai naga tsananin kamarsu da Jabeer sai dai yafi Jabeer haske ,Jabeer kam ya fisa kyau,sanye yake black suit sai inner fara yayi matuk'ar kyau da haskawa kamar shiya halitta kansa.Jabeer kam sanye yake cikin long black trouser sai long sleeveless black colour itama da bakin takalmi velt da jacket dinsa duk brown sai fitar da sihirtaccen kamshin nan nasa mai wuyar barin zuciya yakeyi gashin kansa sai d'aukar ido yake yi saboda tsananin gyaran da kulan da yake samu a kullun,tsadaddan Gucci agogon hannunsa ya kalla tare da dan waro idanuwansa da yada'an lumshe yana kuma rike briefcase din da Lamin ya kefo masa,"au ni zan maka daukar jakkan ma"..Dariya Lamin ya saki tare da cewa "to mene amfaninku badan kumin haka kukaje d'auko ni ba".. Tab'e baki Jabeer yayi tare da cewa" sure Papa"sosai Lamin ya saki dariya tare da zagayowa ya rungume Jabeer sosai a jikinsa cikin tsananin k'auna yace"I missed you so much Buddy".bige masa hannu Jabeer yayi tare da hararansa kafin yaja hannunsa suka nufi y'an gidan...da gudu Basma da Muhibba sukayo Kansu tare da ruk'unk'uke Yaya Lamin fuskarsu ta gagara daina sakin Murmushi.sakin Hannun Lamin Jabeer yayi tare da k'arasawa wurin su Daddy yana gaishe su Dan harya fita basu had'uba...tare dasu Basma ya k'araso wurin ya duka ya gaishe da Abba da Daddy a tare suka d'agosa tare da rungumesa suna welcoming nasa,Annie ya fara gaisarwa ta washe baki tana fad'in "yauni Maryama saina taka rawa,jikana na Allah da Annabi Wanda baya cin zali ya dawo,maza ka gaishe su Dan bangarena nan ne masaukin baki".. Ta k'are maganar tana kallon Jabeer kyab'e fuska yayi duk da yasan da shi take sai yayi kamar besan ma tana yi ba.Ammi ya fara gaisawar ,sosai ta rike hannunsa tana masa sannu d zuwa kafin ya gaishe da Momy wacce tuni fara'ar fuskarta ta gushe ganin ba wurinta ya fara zuwa ba shikan gani yayi Ammi CE kusa dashi ,ciki ciki Mommy ta ansa kafin ya juya ya gaishe da Umma da Aunty Amarya yana rike da hannun Ahmad yace" nikan da sake banga Lil sis ba"..."komu nan ba mutane bane bari muyi saurin tafiya sai ka nemi wacce kaga tafi dacewa ta tareka"Mommy ta fad'a tare da juyawa ta nufi part dinta.... Comment and share Ouhm Aryaan *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Page 7 K'asa da kai Lamin yayi yana tunani jiya i yau dai kenan,har yanzu gidan nasu na nan yarda ya barshi kenan tsawon lokaci,wannan yana d'aya daga cikin abunda yasa yake son barin k'asar kodon ya samu kwanciyar hankali da sukuni a zuciyarsa...A cikin bacci kamar ance ta tashi ta mik'e tsaye tare da yaye labulayen window na bayan d'akin Annie sosai ta waro manya-manyan idanuwanta Wanda bacci ya kuma k'ara masu girma,hannu tasa ta shafi tulin uwar sumar dake cikuikuye cikin ribbon kafin wani kyakyawan Murmushi ya sub'uce a fuskarta ji tayi ta nemi duk wani ciwo na jikinta ta rasa without second though tayi wajen bedroom din da gudu cikin sauri ta tura k'ofar part din Annie Lamin kawai idanuwanta suke gano mata tseye sukayi kowa yana kallonta cikin sauri ta rungume Lamin tana sakin wani sanyayyan murmushi cikin farin ciki tace"I missed you so much Yayana,shine baka fad'a...."sauran maganar nata ya mak'ale idanuwanta suna saukan akan kyakyawar farar fuskar Veer duk yacce yayi kicin kicin da fuska hakan be hanata hango sanyayen kyau da yayi ba,his nose,his brown shining eyes,his white teeth dake zagaye da cute lips the way he stand ,the best of all his cool walking and body structure cikin sakanni duk ta kare masa kallon nan kasancewar siririn tsakin daya saki ya wuce part dinsu zuciyarsa na cunkushewa da wani irin tsabar takaici har wani d'aci d'aci yakeji a makoshinsa yarda kasan ya soma dukan Layan haka zuciyarsa ke raya masa har sai ta daina numfashi yasan idan ya tsaya wurin komai zai iya faruwa yasa ya wuce kawai Dan yarda kasan Monster haka yake bin duk mumunar fuskarta da kallo.da sauri ya rintse idanuwansa Wanda suka soma canza launi ajiyar zuciya ya soma saukewa lokacin daya shiga d'aki yanajin all the world na masa wani irin zafi.....Da kallo Umma kebin jikin Layan da kallo takaici da kunya duk sun gama rufeta har gobe Layan batajin magana ba zata daina shiga a haka ba,kasa hakuri Umma tayi tace"ke har gobe yaushe zakiyi hankali Layan? Kin wuce kinbar wurin nan ko saina rufeki da duka a wajen nan sakarya kawai har abada banga ranar da zaki daina shirme ba a haka kullun girma kike k'ara yi,look at your body"....k'ank'ance ido Annie tayi tare da cewa"A'a Fatima inma na maki Allah ya isa to tsab ta zauna,wannan wacce irin rayuwa ce? Ace y'ar daka haifa ma ba zakayi mata magana cikin salama da kwanciyar hankali ba? A'a tunda nake wallahi,dole na tashi tsaye na shiga malamai badai boka ba danni ba ruwana da sabon Allah wallahi,amma dole a nemo kaikayi koma kan mashekiya ko kin sawa ranki salama ki daina gantalewa ki rike y'arki da zuciya d'aya".tura baki gaba Layan tayi tana k'arewa jikinta kallo,long robber trouser ne a jikinta sai rigar har rabin cinyarta mai hannun vest amma shine Umma take complain akan shigarta to itakam batasan me zana sakawa ba ,kallon da Umma ta kuma binta dashi yasa ta juya zata bar wujen.Abba yace"zo mamana! "Sannan ya juya ga Umma yace" Ayi hakuri Hajiya faty nasan bata San da dawowar Yayanta ba aida ta shirya tunda wuri"k'asa Umma tayi da kanga sai yanzu kuma wata irin kunya ta rufeta takaicin Layan ne ta kasa d'auka har ya sakata yin magana,a hankali ta zame tabar wurin.Mommy Badiyya dake can gaban Apartment dinsu tayi mutuwar tsaye ganin irin rungumar da Layan tayiwa Lamin takaici kunci duk sun gama kasheta a wurin.she's just helpless kawai taja tsaki kamar zata tsinke harshenta ta shige ciki kamar zata tashi sama......b'ararrajewa yayi a parlor yana kwasar hadaddiyar miyar zogale da Masan da Annie tayi masa da kanta wacce tasha manshanu sai zuba kamshi takeyi,tare sukeci da Layan yayin da Annie ke gefe hannunta rike da robar man shanun tana kora masa bayani na komai ke faruwa a gidan ko abu d'aya bata iya ta b'oye ba...tura baki Layan tayi tace"ke Annie duk yaushe Yaya Veer din yamin haka? Ke komai yayi ni gaskiya bana son kina mun wannan abun,in ma ya daka ai ni dolensa ce kuma komai zai mun ba Wanda zaice danmi"...wani kallo Annie ta bita dashi sannan cikin takaici tace"tashi ki fita,in dai Jabiru ne gaki gashi,ina nan zaki zo ki sameni,yarinya kamar kun had'a dangi da mayu,ina amfanin duniya ka so Wanda baya sonka? Ranar da zai maki dukan mutuwa ki dawo babu ruwan Mairo ,in dai na haihu na gama shiga tsakaninki da wancan labcecen marar imanin tashi tashi kada nima zunubi ya shafeni kibar gidan nan,tunda ba waccan figaggiyar ta ginamun shi ba,gaki nan kin kwaso rashin auki kina tafiya kamar iska zai kwashe"...sosai Lamin ya fad'ad'a fuskarsa da fara'a yace"a'a Annie ba ayi haka ba,in dai Layan ce ke da kanki zakije biko".."meye wata Laya? Na had'a me da ita banda na haifi Abubakar".murgud'a baki Layan tayi yare da mikewa ta fice tabar d'akin...k'asa k'asa Annie tayi da murya tace"to ko ni fa,na samu na korata da kyar kullun saita shanyemun fura yanzu meye amfanin haka."Dariya kawai Lamin yayi ya tashi ya tafi part dinsu,da sallama ya shiga parlon Mama Badiyya ba kowa sai Muhibba da Ahmad dake game a tab.Da gudu Ahmad yaje ya rungumesa yana kuma masa oyoyo,shafa kansa yayi yana jin dadin samun kowa da yayi lafiya kafin ya kalli Muhibna tare da ansa sannun da take masa yace "ina Mommy?" "Tana bedroom yanzu ta dawo daga wurin Abba"... Bece komai ba ya wuce tura k'ofan yayi tare da sallama ya shiga ya zauna a gefen bed,sai da ta gama wayan da take yi sannan ta juyo ta kallesa cikin tsabar takaici tace"sai yanzu kayi lokacinmu Alhaji? Na dauka ai kana can wurin ita uwar taka,ko ka taba ganin Jabeer yayi tafiya ya sauka a bangaren nan,sai kai da baka San kishin mahaifiyarka ba anya Lamin,anya dai rayuwa zataje a haka,to bari kaji wannan karon a shirye nake da kai duk wani abu da kasan kanayi billah wannan karon bazan dauka ba ,ka gama daukata y'ar banza ,kaji yarda ka tsaya yarinyar can sauran cuta ta wani makalkaleka ko kunya bakaji ba,to inma kana da intention na wani abu na fada maka tun wuri ka tsayar dashi dan zanyi mugun sab'a maka wallahi zanga ko Fatiman ko Maryam ciki idan akwai Wanda yamun goyon cikinka ko nak'udarka". K'asa da kai Lamin yayi yasan komai zai fad'a mata ba zata tab'a yarda dashi ba, in fact ya gaji da duk wannan issue's din yana son hutu da kwanciyar hankali cikin cool voice yace"kiyi hakuri Mommy insha Allah zan kiyaye"."yadai fi maka,zakaci abinci ko shima an hanaka kaci?".murmushi kawai yayi tare da cewa"babu abunda zai hanani cin dad'an girkin Mamana nayi kewarsa sosai zanci komai kika bani Mommyna".ya k'arashe zancen yana rike hannayenta,murmushin itama tayi sannan suka fito zuwa dining ta fara loda masa abubuwan data dafa da hannunta domin shi,Dan duk yaranta Allah ya daura mata matukar son Lamin bata iya jure komai a kansa bare kuma har ace tayi fushi da shi....."I beg live me ka dawo zaka cika mun kunne".janye duvet din da Jabeer ya rufa Lamin yayi cikin tsokana yace"malam dallah tashi kazo ka mana kwance ga Miemie tana ta kiranka".mikewa sosai Jabeer yayi tare da dafe kansa yace"Ya Allah,,Lamin ko baka da d'aki a gidan nan ne?".Murmushi ya sakar masa tare da cewa"ina da,amma nazo maka labarin matanka ne".sound seriously Jabeer yace'tashi ka fita"."au labarin Miemie da husna ne baka so".pillows dake kusa dashi ya jefawa Lamin kafin ya kwanta tare da rufe idanuwansa yana jin kansa na barazanar tarwatsewa lallai dole kuwa yayi saukon komawa aiki bazai iya kwasar takaicin Lamin ba.Dariya sosai Lamin ya shek'e da kafin ya fita yana tsokanarshi...... Comment and share Ouhm Aryaan. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Page 8 Dedicated to Nasrullah. Da kallo kawai Ammi ta bita har tazo ta wuce zuwa bedroom dinta,tsaye tayi tana kallon Basma da Muhibba dake zaune a bed suna sakin shewa da alama labari sukeyi.shiga tayi tare da jan pillow ta kwanta tana kallon sama ba tare data kulata ba..."yauma an dab'a ko? Har abada ba zaku daina wannan rigiman ba Idan zaki sakawa zuciyarki salama k'arama ki saka mata,ki fita daga hanyar Yaaya Veer wallahi tun kafin wahala ta kaiki kushewa"Basma ta k'are maganan tana kallon Layan...sanyayyar ajiyar zuciya ta saki tana mayar da kallonta akan Muhibba data d'auka da cewa"nima dai kullun na fad'a mata amma yarda kika San kullun k'ara ingizata akeyi,ni nama rasa wannan tsana ta menene marar dalili Sam bansan asalinta ba bare mafari,to k'arama ki sawa ranki salama".wani murmushin takaici Layan ta saki tare da mikewa zaune tana k'are masu kallon da manya manyan idanuwanta duk su biyun cikin cushewar murya tace"lallai har yanzu Baku san menene so ba,kiyayya bata hana kaso Wanda kake so,haka Allah ya k'addaramun shi ya sanyamun soyayyar Yaya Veer a jinina da duk wani b'argo na jikina,duk ranar da kuka ga na daina san shi to kusanya a ranar duk wata jijiya ta jikina ta daina aiki,a ranar zuciyata ta dainawa gangar jikina aiki,kuma tabbas a ranar ranar raina yayi bankwana da gangar jikina,Dan haka Ku daina wahalar da bakinku Dan ko kasheni yaya Veer zaiyi wallahi bazan tab'a daina sonsa da son kasancewa tare da shi ba."tana kaiwa nan tasa hannu tare da share hawayen daya soma bin fuskarta ta mike da sauri ta wuce zuwa toilet tare da bude fanfo tana sakin wani kuka Wanda bata san dalilin zuwansa ba,itadai wani kewa da k'unci kawai takeji yana taso mata kawai tana jinta she's not complete, ba kuma tasan abunda zai iya cike mata wannan gurbin ba.....sanyayyar ajiyar zuciya Ammi ta sauke wacce ke tsaye kofar bedroom din na Layan tun shigowarta ta mara mata baya amma ta tsaya danjin abunda suke tattaunawa.hannu tasa ta shafi fuskarta tana zancen zuci lallai akwai sauran aiki a gabansu tun Layan tana 2years da ance waye takeso zatace Jabeer kowa yana dauka shirmenta ne da kuma irin yarda take son shige masa ashe abun babba ne har yanzu akwaishi har haka,lallai wankin hula yana Neman kaisu dare,duk muguntar da Veer yakewa Layan tun tana mitsitsiyarta hakan besa ta tab'a gudunsa ba har Allah yasa ta mallaki hankalin kanta......bedroom din ta tura tare da kare masa kallo kwance yake rubda ciki idanuwansa a lumshe kamar mai bacci sai dai tasan ba baccin yakeyi ba yana jinta,sanyayyan kamshi ne kawai ke tashi a d'akin ga ko ina Need kamar d'akin mace,sanye yake da white 3quater sai white singlet da alama hutawa yakeyi,k'arasa shiga d'akin tayi tare da saka hannu ta tab'a gadon bayansa.A hankali ya soma bud'e idonsa kafin ya idasa waresu gaba d'aya akan Ammi wacce tadan sunkuya a gabansa...d'an sakin fuskarsa yayi kamar yayi murmushi cikin Cool voice yace"Ammiiiina aida kin aika nazo".ya kare zancen yana gyara xama kusa da ita a gefan bed...tsura masa ido tayi kamar mai son karanto wani abu ,sunkuyar da kansa yayi sai kuma yace"ki gafarceni Ammi in ma wani wani laifi a sani na ko akasin haka,ina neman yafiyarki kuma insha Allah na za'a sake ba"...kama hannuwansa duk su biyun Ammi tayi tare da kallonsa cikin ido tace"ko kusa Jabeer ,babu abunda kamun komai na umarceka kana kokarin yimun biyayya akansa sai dai akan abu d'aya Wanda na kasa tankwara zuciyarka a kai kuma kasa kasa yimun biyayya akai why?"...kallonta kawai yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace"what's it is Ammi".Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace"Akan y'ata Layan Jabeer".Dandanan dan sakin fuskar da yayi ta gushe yarda kika san an aiko masa da sakon mutuwa lokaci d'aya hannuwansa ya zare daga rikon da Ammi ta masa tare da shafa fuskarsa amma bece komai ba."menene dalilinka na tsanar Layan? Meta aikata maka har haka Jabeer? Layan fa jininka ce yar wa'anda suka reneka suka daukeka tamkar Dan da suka haifa,Daddynta ya hanaka kukan rashin mahaifi Jabeer amma meyasa kiyayyarka ta bayyana akan y'arsu kwara daya tilo Wanda nasan sai dai suyi maka kawaici akai Veer"Ammi ta k'are maganar...Runtse idanuwansa yayi tare da cewa"Ammina Dan Darajar Allah ki daina ambatamun sunanta a nan,bana son ji,ni bana da wani dalili kawai I hate her with passion nothing more nothing less,kawai bana sonta a al-amurana ne"..."Amma kasan wannan ba d'abi'ar musulmi na kawarai bane? Kuma ba shine tarbiyar daka samu ba?"."yes I know" ya katse Ammi Wanda da alama zuciyarsa harta soma hawa Wanda daba Ammi bace a gabansa da yanzu wani zancen ake ba wannan ba"sannan yaci gaba da cewa"kiyi hakuri bazan iya son abunda na taso da kiyayyarsa bane tun asali ,bazan iya tursasa zuciyata ba".daga haka kuma yayi shiru,duk maganar da Ammi keyi beko d'ago kai ba bare tasa ran zai ansata,tasan kuma bazai kuma yin maganar ba,in dai akan wannan maganarne itace ma yake Dan tsayawa yana yiwa doguwar magana haka sai kuma Lamin,so da dama tana binsa ta zafi zafi ko ruwan sanyi ko wa'azi amma hakan bata tab'a sauya zani ba in dai akan lamarin Layan ne.shiru itama tayi ta kallesa tare da tashi kuma ta fita ta bar masa d'akin..kusan cin karo sukayi da Momy Badiyya dake rike da womer da alama kuma d'akin Dan lelen nata Lamin ta nufa,cikin ko in kula Ammi tace" barka da gida".A dakile kamar wacce akawa Dole Momy tace" sannu,nace kuma sintiri ya kamaki a part din nan ne ko kinyi ajiya ne?,a iya sanin kowa dai bakya zuwa nan,ko wancan d'an naki agola kafi Dan masu gida daya gagari kowa bakya zuwa wurinsa sai dai ya iskeki to kuma yau zuwan na menene?"....Murmushi kawai Ammi tayi dan ita bata shakkar kowa sai dai Momy tana cin albarkacin Dan uwanta nodding kai kawai tayi tace "kya iya shiga ki duba".sannan tabi ta gefanta ta wuce.Mommy tsaye tayi bata bita ba dan sarai tasan wacece Maryam bata daukar warkinta yanzu tayi mata kaca-kaca ta kama gabanta kuma Annie ta daure mata k'ugu kwafa tayi ta wuce ciki fuuuu tana kwala kiran sunan Lamin.jin shiru yasa ta wangale kofar bedroom dinsa amma wayam b'ab'atun da takeyi yasa Jafar ,Hydar duk fitowa daga d'akinsu Hydar yana cewa" Momy lafiya?"ko kallonsa batayi ba ta wangame d'akin Jabeer lallai ilaika kuma anan ta samu Lamin tsaye a kan Jabeer dake zaune ya dafe Kansa da hannuwansa,karasowa ciki tayi tare da cewa"me Maryam tazo yi wurin nan?"kallonta yayi sai kuma yace"Layan?" Wani banzan kallo ta watsa masa tace"zanci k'aniyarka a wajen nan Lamin mecece wata Layan,Maman wannan nake magana"ta k'are zancen tana nuna Jabeer da hannu.Girgiza kai kawai Lamin yayi tare da cewa"to ai ni banma san Ammi ta shigo nan ba"...hanya ta nuna masa,ganin baida niyar wucewa tace"dan kaza kazanka zo wuce,Wanda besan ciwan Kansa,Maryam da abunda ta haifa har abun sone ? Ta dalilinta har saki saida na samu a gidannan amma kullun kana gindinsu".....Annie dake tsaye bakin k'ofa tayi wata kwafa tare da cewa"tabdi jannan Ahmadu ya auro masifa a wannan Family"ta kare zancen tare da jinjina kai sannan ta ajiye basket din data ciko da kuloli sannan ta kalli Mommy tace"wallahi Badiyya idan baki canza hali ba zan nuna maki nima y'ar banza nake,kinsan zanyi maganinki me akayi akayi wata Badiyya da zaki zo ki b'ata mana Family kin cinye komai kin tada komar kin koma kamar tsohon buhun masara to wallahi ahir dinki da rabamun jikoki,maza zo kibar wurin nan kafin inyi da Wanda ya ajiyeki danni nafi karfinki kin sani"....Takaici yasa Momy barin dakin da sauri kamar zuciyarta zata buga dan takaici...... Comment and share Ouhm Aryaan RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Eu8jhXno1XdCkcuKbtprEg Page 9 Tsab tsab ta fito cikin shigar Doguwar riga na material mai budad'en wuya sosai rigan ya zauna a siririn jikinta ga fuskarta data kuma yin fayau sai daukar ido takeyi,mini hijab ta saka white tare da dauko lab coat dinta da school back ta dauko eye glasses dinta kenan ta juyo suka kusa cin karo da Muhibba,"Malama yada shigowa ba izini haka sora kad'an na zunduma da gudu ".tab'e baki Muhibba tayi tare da cewa" to inafa zan tsaya daukar izini aina dauka kina nan kina bitar karatun da babu ranar bada haddarsa bare kuma a samu riba,shiyasa nazo tashinki dan kada kiyi latti muma ki janyo mana,dan Basma tana da CA yau".kallonta kawai Layan tayi cikin cool voice tace" to naji".ta k'are zancen tare da daure fuska.murmushi Muhibba tayi tare da karbe school bag din nata tace"haba y'ar Abba ina mai bada hakuri,ke kanki kinsan takaicin sakamakon ki a lamarin nan ne yake kuma lassala ni nake neman maki mafita".wani murmushi mai wuyar fassara Layan tayi kafin ta zuba dara-daran kyawawan idanuwanta akan Muhibba kafin tace"in dai hubb'a sanki na neman rabani da Yayane kada Allah ya nuna mun ranar wannan taimakon naki,several time ,day and night zanci gaba da fad'a maku babu abunda zai iya rabani da soyayyar Yaya Veer sai dai mutuwa! Ranar da numfashina zai bar gangar jikina to ina mai tabbatar tafi, bankwana da jikin.,ina matukar sonsa idan ina tare dashi ko ina kusa da inda yake kawai nake samun natsuwa,kuma ina addu'ar Allah ya nuna mun ranar da Yaya Veer xai fahimci irin abunda yake damuna harya tallafe ni"...."you serious y'an mata? You mean kina jiran wannan ranar ne? To idan kin manta bara na tura maki Yaya Jabeer shine mutumin da besan menene shauki ko soyayya ba,shine mutumin da baisan ya akeji dan ganne da alak'a ta jini bama bare soyayya,dama kin tuba ko me zakiyu bazan gaji da fada maki gaskiya ba kuma dan ni na fiki jin zafin abunda ke faruwa da ke,kuma zanta rokon Allah ya yaye maki"Basma tare maganar wacce shigowarta kenan....tunda ta taho ya k'ureta da idanuwa hankalinsa gaba d'aya ya gama komawa kanta duk wata natsuwa ta gama kaura daga gangar jikinsa,takunta yake kallo yacce kasan d'awaisu na rangaji haka Layan ke doso su Wanda tun kafin ta ido turarenta ya sanar dasu zuwanta,a hankali cikin kasaita tana tafiya cikin nutsuwar nan nata wacce ba kowa ke fahimtar tana da wannan sirin ba...wani irin kyau haka yake ganin kullun tana k'arawa a idanuwansa,Momy Badiyya data dauki Irish zata saka a baki ta buga fork din da table tana dan gyaran murya,cikin sanyi Lamin ya dauke idanuwansa Wanda harsun soma canza launi ya lumshesu a hankali tare da shafa tulin sumar kansa cikin zuciyarsa yana fadin "*Allah Kaine Allah,Allah kaima jarabeni da soyayyar Layan a raina, Ya Allah Kaine buwayi gagara misali ina rokonka daka nuna ikonka ka mallakamun Layan a matsayin matata kuma mafakar sirina!*"...Fuskarta kawace ta murmushi ta k'araso kusa da Abba tare da dukawa tace"Abbana ina kwana". Hannunta ya kama ya d'agota tare da fadin" lafiya lau Mamana ,kin tashi lafiya".k'asa tayi da kanta tare da cewa "Alhmdllh"." Me kuma ya had'aki da Annie yar gidan Annie yau tun asuba take mitar kwana biyu yau baki shigo ba"..tura d'an karamin hakinta tayi Wanda yasha ado da white lipglose "Abba ai korata tayi " Dariya kawai Abba yayi be kuma cewa komai ya yaci gaba da cin abincinsa.kallonta ta matar wurin Momy da Aunty Amarya ta gaishe su Wanda Momy da kyar ta iya ansa gaisuwar shima ganin Abba yana wurin...bayan kujeran Lamin ta koma tare da daura hamnuwanta akan kafadunsa tana fadin"Good morning"...wani irin sanyi da natsuwa suka dirar masa lokaci d'aya cikin cool voice dinsa mai dadin sauraro yace"sai yanzu kika ganni?"shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka ta saka hannayenta duk biyun ta kama kunnuwanta alaman ban hakuri sannan ta kwashi jakanta ta baza da gudu.besan sanda murmushi ya subuce masa ba ,sai kuma ya kawar da kai.....Tsaye yayi yana karewa Annie kallo zaune a can edge na kujera hannunta da carbaha hawaye ne ke fita a idanuwanta sai kib-kibta ido takeyi taba kallon Jabeer daya ki cewa komai yana pressing phone as if babu shi a parlon.wani kwafan bosawa Annie ta kuma yi tana had'a ido kuma da Lamin sai ta fashe da kuka.da sauri Lamin ya karasa ciki yana tambayar lafiya,gefan zani Annie tasa ta goge hawayenta tace"dama ka rabani da Jabiru babu abunda na had'a dashi,dole ma yabar mun d'akina tunda babu abunda na had'a dashi,yanzu fisabilillahi ya kyauta mun?ina masa magana ya mayar da ni y'ar banza".zama kusa da Jabeer Lamin yayi tare da fadin"man meyake faruwa ne"har Lamin ya cire ran zai amsa shi sai kuma yaga ya mike yace"zanje nawa Hajja sallama anjima zan wuce"be kira cewarsu ba yayi waje abunsa...Annie kam idasa rushewa tayi da kuka cikin muryar kuka tace"Laminu tambayarsa fa nakeyi ina Laya,yau kwana biyu ko mai kama da ita ban gani ba,yanzu sabida Allah ina laifi a nan? ".Murmushi kawai Lamin yayi daya gano kan canzan yace" kiyi hakuri taje makaranta idan ta dawo nasan zata shigo".da sauri Annie ta katse shi tace"ta shigo ina? To wallahi wallahi lokacin zata san y'ar banza ce ni, dama tun wuri ka gaya mata kada ta shigo mun nan,babu abunda na had'a da ita,ni da mutuncina ita bata isa ta zubarmun ba,in ba haka ba insa Jabeeru ya karyamun k'afar yar banza"Dariya keson kwacewa Lamin amma sai ya daure ya daure fuska yace"to kunfi kusa dai,Kinga ni zamu fita karma ya tafi ya barni."....Har k'asa Lamin ya duka yana gaishe da Hajja Wanda bakinta yaki gajiya da fara'a sai washe hakora takeyi sosai taji dadin ganin Lamin din tana kuma fadin"ya ka baro su Hajiya Badiyyar ". K'asa yayi da kai tare da cewa" duk lafiya"."to alhmdllh mutanan turai sannunku da dawowa wannan karon kam ba sake guduwa da kai da abokin naka maza kusa azamar fito da mata kuyi aure lokaci baya jira".k'asa Lamin yayi yana shafa kansa fuskarsa da murmushi.Jabeer kam tab'e baki yayi yana ciro wayarsa a aljihu bebi takan uban kayan breakfast da aketa jerawa a gabansu ba.cikin sanyin murya kamar Wanda akayiwa dole yace"ina kwana Hajja".Dakuwa ta masa tare da cewa"sai yanzu milkin naka ya barka ka gaishe ni ,to gani daram akan kafafuna da izinin Allah,maza kuci abinci".Girgiza kai Jabeer yayi tare da cewa"I'm full"duk da ruwan Lipton kawai ne a cikinsa amma kab ranar ta juya masa sai danasanin shiga part din Annie yakeyi duk dan firan data masa,tuna hakan da yayi ya kuma ji wani kunci na mamayesa runtse ido yayi sannan yace"nazo maki sallama ne"."yaushe zaka wuce?"Sanin ba magana zeyiba yasa Lamin cewa "insha Allah da karfe 4:00". Jinjina kai Hajja tayi tare da cewa" Allah ya zama gatanka ya kareka aduk in da kake, ina rokon Allah ya jibanci lamuranka ya shige maka gaba,ya baka ikon rikon gaskiya da Amana".duk suka ansa da Ameen...haka ma sunje sunyiwa Ummi sallama duk da ba wani shiri takeyi da Jabeer ba a kwanan nan dan tana fushi dashi amma taji ba dadi da zai tafi.itama addu'a ta masa sannan suka dawo gida ya soma hada Kaya.. Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Page 10 Kallon kawai Ammi yayi fuskarsa a dan sake ba kamar ko yaushe da take a daure ba yace"yeah in 2weeks time insha Allah zanzo".jinjina kai tayi tare da cewa"to Allah ya bada sa'a ya kuma kaika lafiya stay safe."ta kare maganar tana shafa kansa fuskarta da murmushi dan sosai yayi mata kyau cikin kakin shi na soji tuni ya koma madakin maza zarataccen namijin da ko namiji ya kallesa sai ya kuma bare kuma mace,ita kanta wani lokacin tana jinjina baiwar kyau da kwarjini da Allah yayiwa Jabeer kuma ako da yaushe take binsa da addu'a".kamar kullun haka Umma ta hadashi da Rover's na dambun dama da dai sauransu Wanda tasan zai iya bukata duk da yawanci ko ya tafi Lagos din a nan gida Abuja yake weekend dinshi...sosai ya daure fuska ganin Annie ta kura mashi ido cikin husky voice dinsa babu alamun sakewa yace"menene kuma?" Sake baki Annie tayi ta kuma tafa hannayenta sai kuma tace"ni kakewa wannan tambayar kanka tsaye Jabiru ? To kul ko uwarka Maryam bata kai ba bare kuma kai karamin alhaki"..murmushi yake son yi ganin yarda ta hakikance amma ya basar dan so yake yau kafin ya tafi ya juye duk haushin data tara masa asubar fari sannan yabar mata gidan.kuma tamke fuska yayi ya kuma k'asa da murya yace"kiyi abunda ya kawo ki kona kama gabana ni bana son wannan tsaiwan taki marar dalili"...."ubanka Jabiru ubanka kaniyarka,ni ba yar banza bace irinka bare ka sakani a gaba ,daga maganar arziki sai ka sakani gaba,dama na fada maka in ka tashi zuwa toka nemi wurin saukarka badai gidan nan ba,ko ka fidda mata kayi aure".."au bayan ke kuma akwai wata matar da zan kuma aura ashe?"ya kare maganar yana kashe mata ido d'aya.kafin ta bada wata ansa kuma ya shige mota dan yasan yanzu sai ta tara masa mutane...da sababi tabi motar har Lamin ya fice da ita a gate din gidan......A gajiye suka dawo daga school dan sai yamma lis suka dawo banda Basmah data dawo tun 2.wanka kawai Layan tayi tare da saka saukaken Riga wacce xata sha iska kanta babu hula ta dawo parlon Umma ta zauna tana kokarin cin shawarman data shigo dashi."shi Abincin fa Layan?"Umma ta tambaya Dan b'ata fuska tayi kafin tace"Umma bana jin wani yunwa"."kin dai saka kwadayi a gaba dama ya za'ai kici abinci shiyasa kullun gani nan kamar dake ake miya a gidan nan firit"..sosai maganar Umma ta bawa Layan dariya sai tace"haba Umma yanzu ai irinmu ake yayi ina mutun zaita fama da jibgegiya kamar wata...."kallon da Umma ta bita dashi yasa tayi saurin wara idanuwanta masu matukar haske sai kuma ta fure bakinta data bari a bude danta tuna a in da take ashe ba Ammi bace Umma ce."karasa mana marar kunya"Umma ta fad'a tana jefa mata pillows din dake Jere a Sofa's na falon...Daddy da tun dazu yake jinsu yayi murmushi tare da karasowa parlon yace"a'a Mamana har yanzu yajin be karewa Annien ba? Kina nan kin saka wannan a gaba kuma kinsan yanzu ta korar mun ke".Dariya Layan tayi tare da daura kanta a kafadar Daddy tace"Daddy ai Umma tuni na saba da wannan nata,ita Sam komai zanyi zatace nayi shirme"."tashi ki saka hulanki ki fita " Umma ta fad'a in a serious voice.raurau da ido Layan tayi sai kuma ta zunburi baki tana kallon Daddy.murmushi ya mata tare da shafa lallausan gashin kanta yace"Good gals always obey"itama murmushin ta mayar masa ta saka silifas dinta ta kwashi hulan Umma data gani a wurin tayi waje da gudu....tsaye ta samu Ammi a gaban press dinta tanata jere mata kayanta a press da mai wanki ya kawo dazu bayan tafiyansu school."sannu da aiki Ammi,aida kin bari na dawo na kwashe kinje aiki nasan kin gaji".Juyowa Ammi tayi tana kuma daukar wasu set din tace"not at all yau banje office ba,kinsan yau Yayanki ya koma Lagos din shiyasa ina gida"..waro ido Layan tayi dandanan kuma jikinta yayi matukar sanyi ta ajiye sauran shawarmanta a bedside tare da folding hands dinta a kirji ta saki ajiyar zuciya cikin cool voice tace"kuma ban sani ba Ammi,ko wani banji yayi zancen ba"."kinsan halinsa ai,kuma ba yau aka fara haka ba".Ammi ta fada tana rufe press din...kallo d'aya tayiwa Layan taga yanayinta ya canza batace komai ba ta wuce ta fita tare da janyo kofan tana fadin"ki tashi ki dafawa Abba shayin kinsan yau yana gida and it almost magrib".kafin ta wuce sashin Annie,kusa da ita ta zauna tana gaisheta Annie ta kyab'e baki sannan cikin k'asa da murya tace"duk ke kika ja abunda yake faruwa in ba haka ba laya ta isa ma? Harni yarinyar nan zata watsar wallahi zan nuna mata ni yar banza ce kamar ita kuma tasan ni ke milki da iko da gidan badan bakin duniya bama ai sai in ce Habubakar ya zab'a ni ko ita Dan ita dama waccan farar kyanwar wacce ta gogawa jikata sirantaka tayi ta kanta inyi nawa dan babu abunda muka had'a".Murmushi kawai Annie tayi tare da cewa"ayi hakuri Annie tana nan shigowa insha Allah ta tsaya tafasawa Yaya ruwan shayi ne"..."meye wani Yaya ?waye wani haka?,kudai kuka sani ni dai Allah ya sani zaune nake da kowa da zuciya d'aya Wanda kuma ya cuci wani dan kanshi"..Layan kam kitchen ta wuce ta daura ruwan shayi a gas tana ta tsaye ta kurawa wuri d'aya ido tana jin zuciyarta babu dadi ga wani zafi da takeji from no where, haka kawai duk wani lamurra na rayuwarta taji sun tsaya mata cak.Lamin ne ya shigo kitchen din jin kauri kauri sama sama da sauri ya karasa a gas din ya kashe wurin shayin ya tafasa harya soma zuba akan gas din yana fidda k'auri k'auri sannan yayi tapping din Layan yana kallonta da alamar tambaya.Da sauri kawai tayi wurin gas din tana jiyar tab'awa ga wani tari daya tirnikota cikin sauri ya rike hannuwanta ya janyota yana fadin"u OK Layan?"kasa bashi ansa tayi ta soma tari sanadin kaurin da take shaka waje ya fito da ita ya taimaka mata zuwa dakinta inhaler dinta ya dauka ya bata yana kuma bubbuga bayanta a hankali har ta samu tarin yadan lafa mata sannan ya kyara mata pillow ta kwanta sai jin hawaye tayi suna bin gefan fuskarta,hannu tasa tana kokarin sharewa tare da fadin"su kuma wa'an nan daga ina haka?"...Murmushi kawai Lamin ya mata a hankali tace"Yaya!" Alamar tayi shiru yayi mata yace"just sleep"yana dan bubbugata a hankali kuma natsuwa ta fara zo mata sai kuma bacci mai dadi ya dauketa tana sauke numfashi a hankali...kura mata ido yayi yana kuma jin duk wani second zuwa minti soyayyarta kara lunkuwa takeyi a cikin zuciyarsa besan iya wanne lokaci tafiyar zata kaishi ba dan tabbas ya aminta ya kuma yarda soyayyar Layan ba karamin kamu tayi masa ba,in da ko a wasa ko a mafarki bayajin akwai hanyar da zai iya rabuwa da ita,sai dai yana fata da addu'ar Allah ya shiga lamuranshi ya zama gata da daidaituwar duk wani al-amurranshi dan wannan karon ya shirya komai yana nufin komai akan Layan besan kuma wani bigiri rayuwa da kaddara zata kaisu ba ,fatansa dai kawai hakan ya zama mai amfani a garesu kuma kada ya zama silar rabuwarsu,ya rayu da soyayyar ta tun tana cikin tsumman goyo,bata san wacece ita ba,ya ci kashinta fitsarinta duk wata dawainiya tata ya dauka duk dan cikar burinsa yana fatan hakan ya zama silar shiryuwan Familynsu gaba daya duk da yasan yaki ne ba karami ba ya tarowa kansa... Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 11 Leko d'akin Ammi tayi tana kallon Lamin da kuma Layan dake kwance tana bacci"a'a meyasa zaka barta tayi bacci Lamin? Kasan magriba ya k'arota ka tasheta"Ammi ta fad'a.rausayar da kansa yayi looking at Ammi trying so had calm him self down daga damuwar data gama cukuikuye mashi zuciya with cool voice yace"Ammina ciwanta ne ya tashi".kallonsa kawai Ammi tayi sai kawai tace"Allah ya sawake "ta juya ta fita danyin alwalan magriba.ganin lokacin sallah na neman k'ure masa yasa ya mike ya fita tare da ja mata d'akin.ido biyu suka yi da Momy dake baro part din Annie hannunta rike da Warmer's k'anana kallonsa kawai tayi batace komai ba ta wuce part dinsu tayi kamar ma bata gansa a compound din ba,Tsabar takaici ne ya hanata magana dama kuma badan taso ba tazo kawowa Annie tuwa taki karb'a ta gaggasa mata magana ne kawai ashe rabon ta kuma had'uwa da wani damuwan ne ya fiddota a lokacin.ko kallon Aunty Amarya dake dining tana shirya Abincin dare da maid dinsu d'aya dake taimaka mata ta wuce fuuu girgiza kai kawai Auntyn tayi taci gaba da abunda takeyi dan tasan yanzu tana yin magana buhun bala'in Momy a kanta zai k'are,Momy kam a table na parlonta ta dungure Warmer's din ta zauna a sofa tayi kan d'aya tana mayar da numfashi she's speechless and helpless bata san me zatayiwa Lamin ya rabu da wa'ancan mayun ba.Dan ita data had'a jini da Fatima k'ara Lamin ya k'are rayuwarsa beyi aure ba,ta shiryawa duk wani abu da Abba zai bijiro da shi ko da hakan yana nufin ita ta rasa nata auren ne dan duk duniya bata da makiya irin Fatima to ba zata tab'a lamintar jikin ya gaurayu da nata ba,hakanma Wanda ya had'u ya isamasa..Tsaye yake gaban mirror white towel ne dauke a k'ugunsa yayin da kansa ke tsiyayar da ruwa,fatar jikin nan fara tas sai daukar ido takeyi kamar jikin mace sanyayen kamshi ne ke tashi a cikin d'akin da yake nan gwanin kyau ,kuma kallon wayar gabansa yayi da take ringing kusan na biyar kenan,ganin sunan Lamin yasa ya dauki wayar tare da komawa gefan bed ya d'aga wayan yakai kunne .jin shiru yasa Lamin sakin murmushi dan yasan idan zasu kwana a haka bazaice komai ba katse shirun yayi da cewa"Broh"still be ansa ba sai hannu daya sanya yana kuma shafa tattausar sumar kansa wacce take nan bak'a sidik,"ka sauka lafiya? Or ready missing you broh gidan ya soma komawa ba dadi".Cije baki Jabeer yayi kamar ba zaice komai ba sai kuma yace"and so".sosai gaban Layan ya fad'i dajin tattausan muryarsa kuma runtse ido tayi daga kwancen da take tana kuma nuna alamun baccin takeyi still,Lamin dake gefansa yace"come on ka fad'a kayi kewata amma girman kai ya hanaka fad'a,ni nasan kawai rayuwa kakeyi idan ba ni a kusa da kai".Murmushi mai kyau Jabeer ya saki Wanda ba kasafai ya fiya yinsa ba,wani irin kyau yayi sosai kasancewar wannan ne karo na farko dana ga yayi murmushin yace"kana samun ciwan kan zanyi kewarka ?"...."wait wait na kiraka baka tambayi lafiyata bama bare ka ji ina nake?".Shiru Jabeer yayi sannan ya tambayi his where about.Dan shiru yayi tare kuma da jinjina kai sai kuma yace"ina wurin Ammi kasan Layan bataji dadi ba"...Dandanan Veer ya hadiye fuskarsa y'ar fara'ar data zo masa ma lokaci d'aya ta b'ace,a hankali ya hadiye wani yawu mai tsananin d'aci tare da runtse ido bece komai ba ya datse wayar tare da kwanciya kawai a bed yanajin gaba daya duniyar ta juya masa...Hawaye suka soma bin fuskar Layan saurin gogewa tayi dan tasan tabbas jin Lamin yana wurinta ya sanya Veer kashe wayarsa,sai dai ta wani b'angaren sosai taji dadin jin muryar Veer din koba komai taji saukin nauyin da zuciyarta tayi mata..cikin dibara ta saka hannu ta share hawayenta tare da mikewa tana kallon fuskar Lamin dake pressing phone ko damuwa ma beyi ba da kashe wayan da Veer yayi dan yasan may be ya gaji da magana ne,dan ko Ammi ba zata fad'a masa halin Lamin ba....kallonta ya koma yi kafin yace"Lil kin tashi?" Kai kawai ta iya jinjina masa sannan tace"zanyi sallah"..."should I help" Girgiza kai tayi ta bashi ansa da "Yaya zan iya"Da gudu khalifa ya shigo d'akin hannunsa da chocolate's da biscuit yana fad'in" Yaya Layan ,Yaya".tsaye tayi tana kallonsa kafin tace"Abbana what's up nasan baka zuwan banza".Dariyar jin dadi ya saki tare da cewa"Ya Faruk ya dawo"...murmushi ta saki tare da fadin"yes ina yin sallah zan zo kace masa ya ajiye mun alkawarina "Hannun Lamin yaja sukayi waje yana zuba masa surutu dan Khalifa badai surutu ba......Da kallo kawai Momy take bin Layan har tazo daidai kofar shiga part dinta daga can tace" don't you make that mistake ,idan naga wannan tsintsiyar k'afar naki a d'akina sai dai a daura aniyar sama maki wata,kin gama da wancan shine kika dawo wurin nan? Ke wacce irin mayya ce nikan? Wacce irin masifa ce wannan innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ni Badiyyah naga abunda ya she ni,tsakani na da Fatima sai dai Allah ya sakan wallahi "...k'asa daurewa Aunty tayi tace" Haba ,Haba Momyn yara wannan sam be kamata ba,gaba d'aya yaran nan duk naki ne dan Allah ki daina fadar duk wannan be dace dake ba".wani kallo kawai Momy tayi mata ta dauke kai dan yanzu bama ta ita takeyi ba tasan lokaci xaizo da zatayi maganinta...Layan kam dake tsaye kif-kifta ido kawai take jin an bude Door din yasa ta d'aga kai ta kalli Faruk dajin hayaniyar a parlo ta fito dashi,da sauri Layan ta dauke idonta to make sure kwallan dake taron mata a ido be zubo ba,kawai ta wuce tabar part din gaba daya,duk kiran da yake mata bata jiyo ba,yunkurawa yayi zai bita cikin serious voice Momy tace"zanga idan Fatima tayi mun cikinka ta Haifa mun kai,muddin kabi yarinyar nan sai dai ka sake uwar badai ni baja Kitchen ta koma bata kuma bi ta kan Aunty Amarya ba balle Faruk dake nan tsaye kamar wani statue...k'ara rike wayan sosai Ummi tayi a kunnanta kafin ta sauke ajiyar zuciya tace"to Ammi kina ganin hakan shine mafita?" In the other side ma Ammin ajiyar zuciya tayi tare da cewa"hakan dai nake tunani dan naga abun bana k'arewa bane kuma ni abun yana damuna kuma kinsan halin Annie dai ba jira zatayi ba idan taji abu makamancin wannan"."to shikenan babu damuwa mita addu'a har zuwa lokacin da kika fad'a din Allah ya sanya muji alkhairi ,danni abun gaba daya ya gama d'agamun hankali zuciya tana kasa dauka tunda nake ban tab'a ganin rayuwa irin hakan ba."Ummi ta kare maganar kafin sukayi sallama da Ammi...."ke kuwa lafiya kika shigo kinata wani hura wannan mabusar hancin naki? Ni bani son irin wannan halin da kike so ki tsirawa kanki in ma wani ya maki wani abu bance ki tsaya a gantale a wulakantaki a gidan nan ba,ni nan ni Maryam ni na haifi Sadeequ da cikina kin ga kuwa babu Wanda ya isa ya mayar dake y'ar banza yanzu sai in jawa mutun Allah ya isa kuma ta zauna tunda ba uban wani ya Haifa man y'ay'an ba"...kuma tura baki Layan tayi sai kuma tace"ni babu abunda aka mun."fiki fiki da ido Annie tayi sai kuma tayi kwafa kafin tace"sai kiji dashi in tayi tsami maji ".ta kare maganar tana tattare tafkeken abun sallahnta da carbaharta data gama ja,sai kuma ta juyo ta kalli Layan tace" ki duba can a kayana akwai kullun dambun kazar da Fatima ta kawo mun to na ibar maki dan nasan zai iya zama haramiyarki tunda abun naku kamar harda saka hannu nema kawai nakeyi naje sheka in samo magani uban kowa yayi ta kansa dan ba zan ragawa kowa ba bama-bamai kawai zasuita tashi a cikin gidan nan haske ya bayyanar mana wallahi"..... Share. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 12 Da sallama ya shiga bedroom din ya tsaya bakin k'ofa fuskarsa a sake yana kallon Momy dake mayar da kaya a press kallo d'aya ta masa ta dauke kanta bata dai ce komai ba.cike da murmushi Lamin yace"Momyna maganin kukana ,yau kuma ba zaki kula Dan gaban goshin naki ba? Momy nayi kewarki ,ina tashi yau kuma ake cemun kinje unguwa bamu samu damar haduwa ba sai yanzu".still batace komai ba,karasawa yayi cikin d'akin a hankali ya daura hannuwansa akan kafadarta tare da langabar da kai ya koma abun tausayi yace"Kiyi hakuri dan Allah Momyna! Fushinki a gare ni masifa ne ,yana kuma d'agamun hankali fiye da komai a duniyar nan,in ma wani abu nayi insha Allah bazan kuma aikatawa ba,ki sani sai dai idan na yishi bada sani na ba ,tuba nake farin cikin rayuwata".Ya kare maganar da kashe ido d'aya.kayan dake hannunta ta jefa masa gaba d'aya sannan ta koma gefan bed ta xauna tana kallon shi kafin tace"Lallai Lamin tambayama kake yi idan kayi wani laifi?,kuma tambaya kakeyi na fita bamu haduba? To ansa d'aya ce da wacce ka dauka ka bawa matsayina ce ai da kasan da fitarta ko ince har ka kaita ma,amma ni da ba a bakin komai nake ba ,baka ta tawa ai saidai daga baya kazo kana damuna da surutu marar amfani,aini tuni Lamin ina niyar sallamaka ga Maryam wallahi,tuni na kusa cire hannuna daga lamuranka"...dukawa yayi akan gwaiwowinsa ya kama hannuwanta yace"Momy dan Allah ki daina fadan haka,har abada bani da madadinki ba kuma zan tab'a samu ba,matsayinki gaba yake dana kowa a zuciyar Lamin,kawai dai naga Ammi batayin wani abu Wanda be dace ba kuma duk d'aya ta dauke mu da Dan data Haifa babu wani banbanci ko wani abun kyara data tab'a nuna mana Hasalima nakanfi Jabeer matsayi a...."."ya isa dakata mun daga nan,in dai aka ce yaro to har abada yaro ne,duk wata soyayya da Maryam zata nuna maku ni nasan karya ce Maryam bata taba sona to haka zalika ba zata taba son abunda na Haifa ba,Wanda ya kika tun farko gaba ko yace yana sonka karya ne,but is a matter of time lokaci zai maka bayanin komai Lamin ,ka barni zan karasa aikina"...Murmushi kawai yayi ganin ta hassala kuma yasan ko zai kwana yana mata bayani ba zata taba fahimta ko yarda ba yasa kawai yayi shiru yace"ki bari zan karasa maki "be jira cewarta ba ya soma karasa kwashe kayan nata yana jera ko wanne in da ya dace....."ko kad'an na kasa gane wannan halin da kike neman daurawa kanki Layan,shin a ko yaushe kin fi son Ammin naki ta kasance cikin tunani,ni dai kinsan bazan dauki wannan sakarcin da kika Riga kika saba dashi ba,bafa zai yiwu kizo ki saka ni a gaba ba cas ba as kita mun kunburi ace yau kwana biyu kina ciwo kuma abinci ya gagareki ci ba,k'arama kin tattara kayanki ki koma wurin Annien ko Ammin taki nikan Fatima bada ni ba"... Rau rau da ido Layan tayi sai kuma tace" Umma yaushe Yaya zai dawo?".kallonta kawai Umman tayi ta kawar da kai sai kuma tace"I think you have his number? Meye amfaninta a wayanki ?"kallonta Layan tayi sai kuma ta kawar da kai kokari kawai takeyi ta hana hawayen da suka taran mata a ido zubowa,da sauri ta tashi tayi d'akinta na part din tana jin zuciyarta ta mata wani irin nauyi gani takeyi kamar duk wani kuncin duniya ita aka tattarawa a kai ganin bata da abunyi kawai yasa ta daura kanta akan pillow tana sauke numfashi hawayen nabin gefan fuskarta. Tuni ta Lula tunanin sai yaushe ne sai wace shekara ne Jabeer zai yi mata koda kallon mutunci ne,a duk duniya burinta d'aya a rayuwa ko da zai zama aiki na karshe a rayuwarta ya zama Jabeer ya kulata ko da bazai sota ba,ta yarda ita zata so shi ko da bata numfashi .saurin mikewa tayi zaune ta d'aga hannuwanta duk biyun ta kalli gabas cikin tsiyayar da hawaye tace"Allah kai ne ya Allah,kai ne buwayu gagara misali,Kaine mai bayarwa kuma mai hanawa idan ka bada ya badu,Kaine kuma Wanda kace mu rokeka da darajar annabinka, annabi muh'd SAW kayi alkawarin zaka ansa mana,ya Allah dan girma da iko da buwayarka gareka nake nema bani da wayau ko dubaran da zan taimaki kaina sai in kai ka taimake ni,ya Allah na miko kukana zuwa gareka albarkacin sunayenka tsarkaka kyawawa ya Allah na rokeka kafin nabar duniya kasa ina da rabon zama a karkashin inuwar auren Yaya Jabeer ko da bazai so ni kamar yarda nake sonsa ba ya Allah na rokeka kasa akwai ranar da ko gaisuwata zai ansa cikin saukin rai,ya Allah ka rage masa zafin tsanata da yake ji a ransa".ta k'are addu'ar tana silalewa akan bedsofa ta runtse idanuwanta tana ambaton sunayen Allah tare da dafe saitin zuciyarta dake barazanar tarwatsewa...in same time Jabeer ne zaune yana shan iska a madaidaicin parlonsa ,sanye yake da white 3quater sai short sleepless armless yana fitar da wani irin sihirtaccen kamshi gashin kan nan sai sheki yakeyi a always coppee cup ne a hannunsa sai tirir yakeyi ya mike long legs dinta a glass table da yake gabanta,idanuwansa a lumshe yayin da zara-zaran lashes dinsa suka sauka a fuskarsa gwanin kyau ,wayace kare kunnansa yana sauraran me ake fad'a masa,cikin husky voice yace"yanzu dan zubar da mutunci yarinyar sa'ar wannan yarance zakace ta kusa zautaka?".sanyayyar ajiyar zuciya Lamin ya sauke daga d'ayan bangaren yace"to gyambo uban son girma idan ban so y'ar 22 ba sa'an Annie kake so na nema?".sosai fuskar Jabeer ta sake kamar zaiyi murmushi sai kuma ya daure yace"ai itace daidai da kai mayen mata! Ni har abada bazan taba so ba,bani da lokacin b'atawa,kai da kaga zaka iya to bismillah".Dariya Lamin ya saki tare da cewa"na roki Allah yasa a maka auren dole dai in ga ta cika baki,kai kamar ba mutun ba,ace mutun bashi da feelings sai shegen taurin kai kamar na mutanan farko"."dafe kai Jabeer yayi alamun Lamin ya soma isarsa da surutu cikin law voice yace"to ko dai zaka gwada yimun ne ubana"."ai da nazo a iyayenka wallahi Jabeer da ka gane waye kai duk wannan fankan fankan din da bakayi ba,a kullun ma dukan da zaka rika kwasa kawai ya isheka,ina kuma fada maka I'm in love,yarinyar nan rayuwata ce kuma numfashina ce bana jin zai iya yin rayuwa mai tsayi idan har ban mallaketa ba to tabbas nima bazan wani amfana a duniyar ba zan mutu,ina so na zame mata garkuwa bango abun jigina na kuma jib'anci lamuranta sai dai bansan wani bigiren rayuwa zata kai ni ba,amma ina rokon Allah daya tabbatar da kasancewarmu a tare ko dan Ku rika gane kaina k'anena"..tsaki Jabeer yaja bece komai ba ya kashe wayarsa yana jin ansa kuwar maganganun Lamin a kunnuwansa kamar yanzu yake fad'a masa,tabbas a duk duniya bayan Ammi babu wata halitta da yake so take kuma fahimtarsa irin Lamin baya jin zai iya juran wani abu ya samu Lamin a duniyar nan,yana masa wani irin so marar algush so na tsakani da Allah Wanda yake jin har ransa xai iya badawa fansa a rayuwarsa idan yiwuwar hakan ta taso.Luckily ya saki murmushinsa mai tsananin kyau Wanda ba kasafai aka fiya ganin yayi shi ba sai dace tuna abunda Lamin yace na a masa auren dole.shi a rayuwa he's a man of principle yana da tsari da dokoki yana son ko aure xaiyi mace ta so shi dan Allah tayi masa tsananin so kamar yarda yake tanadawa duk wacce ta samu damar shiga gidansa a matsayin mata, shiyasa be taba soyayya ba bai kuma taba nuna zaiyi baa dan duk macen daya kallah sai yaga bazai taba samun abunda yake so ba shiyasa ma bai fara ba,a rayuwa ya tsani kalmar dole balle kuma hakan ta kasance a aure baya jin zai iya lamunta ko goyon baya ayiwa wani ma bare kuma shi...... Share fisabilillah. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 13 "Yau kuma a zama d'aki zaki k'are iyeee Laya? Ni gaba d'aya ma na kasa gane maki duk kwanakin nan,halan cuta na damunki bayan wacce kowa ya san kin goga daga dangin mahaifiyarki,dan mu kaf danginmu babu wani mai cutar azo a gani sai dai wacce Subhana yake daurawa bayi lokaci zuwa lokaci" Annie ta k'are magana tana kallon Layan dake kwance a bed.Tura baki gaba tayi sai kuma tace"wallahi ke Annien nan sam ba zaki barni in huta ba,na gudo wa fad'an Umma amma kema kin saka ni gaba,ni babu abunda yake damuna"."kedai kika sani,ki tashi ki shirya ki rakani gidan wancan narkekiyar matar kafin a kwana biyu kuma mujewa Hajja itama,danni ina so in fita hakkin zumunci bana so Allah ya kama ni,Allah yasan ina kokartawa iya iyawata komai dai ina yi daidai gwargwado dan baka biye ta halin mutun ba".Shiru Layan tayi sai kuma ta tuna idan ta fita duk tarin damuwarta ta rage mata ko da na kafin su dawo ne,dan yanzu yarda take jin gidan kamar kurkuku haka take daukarsa ya zamar mata kango indai har Jabeer baya cikinsa...Mikewa tayi sai tace"to ki jira ni na shirya zanje b'angaren Ammi"."wacece wace Ammi? Me hadinki da ita? Me kuma kika manta a can,ina in tsumakarai ne kina dasu a nan,to ni bana son terere yanzu sai kija ta bijiro da maganganun da ni ba iya dauka zanyi ba,sai in sa kai dama Laminu ne zai ajiye ni sai in wuce abina,komai ai yana son sirri".Layan bata kuma cewa komai ba ta shiga toilet din Annie dake bedroom din danyin wanka cikin minti 30 ta gama shiryawa cikin atamfarta brown mai ratsin fari da blue sosai tayi sanyayen kyau atamfar ta dace da chocolate skin dinta sai fitar da sanyayen kamshi take,as always agogo ta daura a left hand nata sannan ta dauki gogegen lite blue long hijab dinta data sha turare ta saka sosai ta kuma hadewa dan ita duk rawan kan Layan bata rabo da long hijab nasa school ne kawai shima dan akwai lab coat yasa take saka mini hijab amma sam ko gyale d'aya bata dashi duk kuwa irin yarda su Basma ke daukar wankansu ita bata damuwa ba Wanda ya tabayin complain akan shigarsa phone dinta ta dauka with white hand bag da with flat shoe saboda yana yin tsayinta ,tarkacenta ta saka sannan ta fito parlo ta samu Annie data gama gadewa cikin sabuwar Atamfarta ga babban mayafi an yafa sai Jikka irin tasu ta manya,sosai Annie ta washe baki tace"to ko kefa da kin tsaya nuku-nuku? Zamanin nan wa yake cutar kansa?komai ai a bude ne tunda ba zaman kowa kake ba,dama tun asuba na fadawa Ahmadu zan fita ".....lockily tunda suka fito idanuwansa na akan kofar part din Annie ,idanuwansa ne suka sauka akan kyakyawar fuskar Layan da tayi wani sanyayen kyau mai daukar hankali duk da a fuskar nata white lip gloss ne kawai sai kajol data saka a dara-daran idanuwanta Wanda suka kara girma da matukar haske ,sosai ya shagalta da kallonta yana sauke wani sanyayen ajiyar zuciya a Jere a Jere ,a ko wanne lokaci ji yakeyi Layan tayi daban ta kuma yiwa sauran mata xarrah,shine kadai daya mayar da hankali a kanta ya fahimci tarin qualities dake tattare da ita,sabanin yan gidan da suke mata kallon mai rawar kai da son hayaniya da guje-guje ga neman tsokana.tunaninsa ne ya katse lokacin da small cool voice dinta ta dokin dodon kunnansa tana kuma tafa zara-zaran dogayen siraren hannuwanta Wanda yatsun suka sha ado da Jan lalle a daidai fuskarsa,wani irin sanyi ya cakude da sanyayen kamshinta ya doke shi lokaci d'aya,lumshe idanuwansa yayi yanajin natsuwa sosai na ratsa duk wata gaba ta jikinsa,Murmushi kawai ya mata kafin yace" you look so Good".Murmushin itama tayi tare da cewa"thank you Yaya"Front seat ya bude mata ta shiga kafin ya budewa daketa kyab'e baki ita ala dole ya fara budewa Layan mota,shiga tayi sannan ya rufe ya zagaya driver seat ya tada motar da bismillah yabar gidan....kallon motar kawai Momy keyi har suka fice daga gate din gaba daya,ji tayi zuciyarta ta mata nauyi kamar an daura wani abu a kai,sakin curtain na kofar benan tayi dama Abba ne tazo ta kawowa Abinci yace ba dadewa zai shigo kuma a sama zai zauna dan yana so ya huta baya dan jin dadi.warmer din karshe ta ajiye ta fita zuwa parlonta tabajin zuciyarta kamar zata fasa kirjinta ta fito,A zaune ta samu Hajiya Sha'awa taci ubansun gayu da wani Danyan less wuya da hannuwa duk gold fuskarta dauke da murmushi take kallon Momy kafin tace "Barka dai Hajiya Badiyya,gani bakuwar da zuwa ba sanarwa na daizo goge laifina". Sake baki Momy tayi kafin tace" yaushe a gari Aminiya? Kin barni nan abubuwa duk sun dau zafi,yaushe ma kuka dawo k'asar?"ta kare zancen tana zama kusa da ita suna tafawa ta irin yaushe gamo.Hajiya Sha'awa aminiyar Momy ce tun ta yarinta ,ita tana auren Ministern ilimi ne to sun jima a England sai satin nan suka dawo Nigeria gaba daya saboda y'arsu kuma Autarsu ta karasa University a can yaransu biyu duk mata Jamila ita ce babba tayi aure sai Ihsan waccew ta d'an girmewa su Layan Auta...."wallahi 2days back muka dawo kinsan Y'ar taki ta karasa University din nata".Hajiya Sha'awa ta bata ansa,"kai alhmdllh kice sai munzo hada fati,Allah yawa abunda aka karanta albarka".Hajiya Sha'awa ta ansa da Ameen.kafin tace"naga kin shigo a birkice? Badai har yanzu kin kasa shawo matsalar gidan nan ne ba Badiyya!".Nauyayen ajiyar zuciya Momy ta sauke tare da cewa"bari kedai k'awa,wallahi nayi kewar tafiyarki,ni bama matsalar gidan nan bace gabana,wannan duk mai sauki ne akan mugun abunda ke shirin tinkaro ni ,nikan akan shi na yarda nayi yawo tsirara in dai zan hana faruwar wannan al-amarin"."to menene zai tinkaroki da har zata fiye maki matsalar gidan nan,gidan da aka cika da mata birjik".."bari Hajiya Yaron nan Lamin,Lamin na gama gano take takensa wancan yarinyar Mayyar mai zubin mutanan farko yake nema ya bayyana yana so kinsan idan hakan kuma ta faru kowa zai Goya baya,nikan kara na mutu dana hada jini da Fatima wallahi".wani kallo Hajiya Sha'awa tabi Momy dashi kafin tace"dankari,wannan shine an gudu ba'a tsira ba,lallai kuwa tashin hankali Wanda ba'a saka masa rana ,wannan kam abunda bazai taba yiwuwa bane,kara ki tashi tsaye in zaki tashi,amma ni a ganina ki turosa su daidaita da Ihsan kawai ita dama kinsan tana sansa ,dauketa a k'asar nan ne ya nisanta alakar dan ko yanzu sai da ta bani sakon gaisuwa zuwa ga barristern"Ajiyar zuciya Momy ta sauke tare da cewa"shikenan kuwa,kafin yayi wani yunkurin ni zan bijiro masa da bukatata wallahi badai ya kwaso man jinin matsiyata ba,kisa a ranki anyi har an gama Ihsan ta gama zama matar Lamin aini kara mun hakan,kai wallahi naji dadin dowarki dan kaina ya kulle duk wannan tunanin bai zomun rai ba,tashi mu shiga daga ciki ki samu kici ko wani abun,rudu yasa ko lemo bansan an kawo maki ba"."kinga ni wucewa xanyi dama nazo ne na goge laifina ki kuma san na dawo,to ashe zan iske wani abunne kuma,duk yarda ake ciki dai kya kira ni danni banma so kafin yasan da maganar ya fara ganina a gidan nan"..rakata Momy tayi har gate in da driver dinta ke xaune yana jiranta,sallama sukayi Kafin Momy ta dawo ciki zuciyarta cike fal da farin ciki,tana kuma tunanin ta ina zata fara. Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 14 Da Murna Ummi ta tari Annie cike da karramawa a babban parlon dake gidan ta sauketa, tana rungume Layan tare da cewa"your welcome Daughter ".Murmushi Layan tayi tace" I miss you Ummi"."ke tafi can idan kinyi kewata meya hanaki zuwa? In dai kince nan ne nasan Fatima ba zata hanaki zuwa ba uwa uba kam Ammin taki".kyab'e baki Annie tayi tare da cewa "to ko yanzu ma sai da na dinga hadata da Allah kamar ina neman wani abu wurinta sannan yarinyar nan ta fito sai kace wata sarauniya". Dariya taso kama Lamin sai kuma ya daure fuska yana gaishe da Ummi.cike da kulawa take ansa masa tana tambayarsa su Mummy da Aunty Amarya yace duk lafiya...rike haba Annie tayi tace" hmm barni barni Halin Badiyya ai sai ita ,yanzu ke kin manta komai har lafiyarta kike tambaya to amma badai Badiyya ta tako k'afarta tazo Ku sada zumuncin Allah ba".saurin kawar da zancen Ummi tayi wurin fad'in bari a samo maku breakfast, kafin a daurawa Annie lunch yau dole ayi gargajiya ai".washe baki Annie tayi tace"wallahi shiyasa sam ban kullace ki ba,nasanki akwai karrama bako da son zumuncin Allah,munci mun koshi Inaga Laya ce kawai ta tashi daga baccin sakalcin da suka saba".Ummi bata bi takan Annie ba taje ita da maid dinta suka kwaso kulolin da suka k'arsa break kamar ta sani akayi yau da yawa.tana jera kulolin ta soma kwalawa Jalila kira ,Gurasa ne da farfesun kan rago sai ruwan shayi da yaji kayan kamshi sai farfesun catfish. Jalila ne ta fito with much of surprise ta tsaya tare da zaro ido sai kuma ta saki dariya ta karaso parlon da sauri ta zauna kusa da Annie tana fadin"lale lale da Hajiya Annie ,kai yau rana ce mai kyau sannu da zuwa sannu da zuwa yau dole na daura tukunyar dambu ".kyab'e baki Annie tayi tare da cewa" ke wuce can kinsan zakiji dadin ganina amma kika gagara takawa in da nake? To ni dan uwarku nazo badan Ku ba,Dan in an biye ta taku a hanya ma sai in juya kai dama mena had'a daku wacece wata Lila ana zaune k'alau to ina kuma Ma'un take ne?".sosai Jalila da Layan suka kwashe da dariya kafin Jalila tace"Ma'u na wanka nasan yanzu kin ganta da wannan suna nata na yan gayu da kika saka mata".sai kuma ta matso tare da kama Hannun Layan tace"your welcome sis".harara Layan ta watsa mata tace"sai yanzu kika ganni? Dadin abunm a Annie ai ba'a mata gwaninta beside ga Yaya Lamin fa".zaro ido Jalila tayi fuskarta na nuna tsantsar farin ciki tace"wallahi Allah Yaya ban lura da kai ba sam",sannu da zuwa ,Good morning".Murmushi kawai yayi tare da cewa"ya kk ya school".Alhmdllh ta bashi ansa dukkansu suka mayar da kallonsu kan Asma'u dake fito sai wani sinsinne kai take tana murmushi daga dan nesa da Annie ta zauna kafin tace"barka da zuwa Annie ,ina kwana"ta fada tana kallon kasa sai kuma ta fara wasa da zoben dake hannunta."meye kuma haka Ma'u? Sai wani sinsinne kai kikeyi kamar wacce akace taje gaishe da sirikai? "Dariya kawai Jalila da Layan sukayi sai kuma Jalila tace" hmm kya kara gani Annie kuma aike Kaka ce".kallonsu kawai Ummi keyi da alamar tambaya ganin kuma Asma'un taki cewa komai sai saukar da kai takeyi kasa,tab'e baki tayi bata dai ce komai ba,cikin sanyi ta kuma gaishe da Lamin shi kanshi yayi mamaki ganin sanyin da Asma'un tayi kuma har lokacin bata karaso in da yake ba,Asma'un daya sani da shegen surutu da rawar kai abun ba'a cewa komai.."wait wait what's going on here ? Ina lil Husnata dana sani ko dai an canza mun ita ne?"Ganin abun nasu bana k'arewa bane Ummi tace"Annie muje Ku gaisa da Janar din naji shigiwarshi yanzu daga ki shiga ki huta dan yaran nan ba barinki ki huta zssuyi ba"kyab'e baki Annie tayi tana masu wani kallo kafin ta tashi ta kwashi k'atuwar jakarta tabi bayan Ummi zuwa d'ayan part din...Sai lokacin Layan ta samu damar kara gyara zama tace"wallahi Yaya ka kara gani ,duk tsabar kinbibi ne wai ita an fad'a komar soyayya ina kaga zama kana matsayin Babban Yayan ango "sai kuma ta kwashe da dariya.Mikewa kawai Asma'un tayi da gudu tabar parlon.Jalila ta dauki zancen da cewa" she's your feature in law Yaya Faruk ke crushing ".shi kanshi Dariya ta basa yarda ta k'are maganar sai bai kuma cewa komai ba ,kallon tsadaden agogon hannunsa yayi tare da cewa" I think I will take my leave now,anjima after magrib zan dawo da daukeku"da to ta ansa kafin suka raka shi ya tafi,ta parlon suka biyi Jalila tace"baki ma ci komai ba duk zamanki a nan,bari na iba maki sai mu wuce d'aki".catfish din ta iba mata kad'an sai ruwan shayin dan tasan bacin sauran zatayi ba,kai tsaye bedroom dinsu suka wuce.small stool ta janyo ta daura komai da suka had'o spoon ta sanya taci kifin so d'a sai kuma ta koma tana juya spoon idan ba zata manta ba wannan cimar yana d'aya daga cikin best Abincin da Yaya Jabeer yafi so a duniya ,Ammi takanyi shi sosai saboda shi musamman idan zai dawo gari tun bata so harta koya ci ."kun gama mun tereren a cikin mutane ko?"Asma'u ta tambaya."Allah babu kowa Yaya kadai muka fadawa,amma kinsan Ummi zata sakamu a gaba ne kam".Ganin Layan bata ma san me sukeyi ba ta lula duniyar tunani yasa Jalila girgizata "as always and for ever thinker lady,ke ba zaki bar zuciyarki da Ruhinki su huta ba,anya Layan kinwa rayuwarki adalci kuwa? Cikin few minutes har kin tafi duniyar tunani ? To zaki kashe kanki ne saboda soyayya? Bayan kinsan Wanda kikeyi dan shi bema san kina yi ba". Jalila ta fad'a tana rike kugu da fuskar tausayi irin abun ya dameta.Sanyayyar ajiyar zuciya Layan ta sauke kafin tace" ko kusa Jalila batun bema san inayi ba bata taso ba,ko ba komai duk yarda yake kuntata mun hakan namun dadi dan yasan ina tare dashi ko yaushe,kinyi kuskuren fahimta,ita soyayya ana so ne ko mutun na sane ko baya sane,ana so ne ko mutun na Raye ko yana a mace ,zuciya ake so ake da muradin mallaka ba sura ba ko wani kyalekyalen duniya,k'ask'antar da kai kuma duk a cikin bautawa soyayya ne,nasan one day one time Yaya Veer zaiji kiran da zuciyata take masa ko da hakan shi zai zama aikina na karshe a duniya to zanyi farin ciki da burin cikar burina,kuma Allah maji rokon bawansa ne,so ki daina ganin wai ina wahala wani lokacin zaki fahimci manufata".sake baki kawai Jalila tayi tana binta da fuskar tausayi sai kuma ta tab'e baki tace"wallahi nikan zan maki addu'a Allah ya yaye maki ne kawai,ina dalili ni har Yaya Jabeer din nan ma ya soma fita a kaina acwe mutun sai shegen taurin kai kamar mutanan farko,ina ma ina ma ina zuciyarki ta maki adalcin kai ki in da aka san daraja da kimarki aka san mutuncinki ake kuma sonki,ji kalli idanuwan Yaya Lamin babu komai a ciki sai zallar soyayyarki da begenki sai dai kash ke da yakeyi danke ma baki san yana yi ba".saurin ture plate din gabanta tayi da sauri tana dafe zuciya sai kuma ta saki dariya tace"kinyi kuskuren fahimta Jalila,kin kuma karanto ba daidai ba,babu wani abu makamancin wannan a zuciyar Yaya Lamin son da yake mun yarda yake son Muhibba da Basma haka nima yake sona Yayana abun alfaharina hakan bazai taba faruwa da mu ba".kallon tausayi kawai Jalila tayi kafin tace"time will tell,ni kinga mubar wannan maganar mu koma wani gobe kinsan muna da CA".manya manyan text books suka ware tare da fara karatu. Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 15 After Magrib Lamin ya dawo daukar su Annie sai dai fir taki komawa cikin had'e fuska tace"dama ni da kayana kala biyu na taho,ina so insha iska shi Ahmadun bai fad'a maka ba? A'a ni kam bana son takura gidan nan ai da can duk d'aya ne".k'asa da kai Lamin yayi yana murmushi dan yasan za'a rina,Annie bata taba zuwa gidan Ummi ta tafi a ranar ba bare kuma ta samu General yana nan.Murmushi General yayi tare da cewa"hakane Annie sai in da kike so zaki zauna dan haka kiyi kwanakin ki ni da kaina ma zan kira Alhaji Ahmad din"..."to tashi ban wuri kaji Wanda suka san zumuncin Allah,kwana biyu zanyi na dawo,itama Layan din kuma ba in da zataje".Tura baki Layan tayi sai kuma tace"Yaya zanje nikan".kallonta kawai Annie tayi sai kuma ta kyab'e baki bata dai ce komai ba ta gyara kafarta d'aya akan d'aya tana girgizawa .Sallama sukayi Ummi ta bawa Layan perform guda ukku a jaka tace ta gaishe da yan gidan....tunda motarsu ta tsaya a compound take k'are mata kallo as if her life depend on it,since fitar Lamin da bayan magrib ta kasa zaune ta kasa tsaye daga benen still take kuma kallonsu yarda hasken wurin ajiye motocin ke haskosu abu ta hadiye da kyar sannan ta koma saman ta zauna shima dan bata so Abba ya fito ya sameta a wurin..kama hannuwan Layan yayi duk biyun yana kallonta,sunkuyar da kanta tayi sai kuma ta d'ago da sauri tace"Yaya wani abun yana damunka ne?"sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke sai kuma yace"nothing kawai ina ga gajiyane"."to Yaya kaje ka huta ka daina bawa kanka wahala haka da yawa,bana jin dadi naga kana damuwa ".murmushi kawai yai mata ya bude motar ya fito itama ta fito.part din Umma suka soma shiga ya gaishe tana zaune da littafin hisnul muslin a hannunta fuska a sake ta ansa kafin yace" Daddy fa"."tunda ya fita sallahn isha bai shigo ba ina ga ko ya tsaya wani abunne"Umma ta bashi ansa kafin ta mayar da kallonta kan Layan tace"kije kiyi sallah ki fito ga abinci a can,dan yanzu zan zubawa Lamin bamai biye maki".Murmushi yayi tare da cewa"ko Umma kamar kinsan na shigo da yunwa kilama duka zan cinye".dariya duka suka saka kafin Umma tace"kasan kuma favorite dinka ne"Dan waro ido yayi be jira komai ba ya karasa dining din.Layan kuma ta wuce bedroom dinta bayan kaman 10mint ta fita tayi joining dinsu a table,ba laifi ta dan sake taci Abincin musamman da Daddy da Lamin suke firar Jabeer a nan ne kuma take jin cikin weekend zai shigo gidan duka kwannan shi 8 kenan da tafiya,wani irin farin ciki taji ya lullubeta sai dai ganin Umma a wurin yasa bata ce komai ba hardai ta samu ta wuce b'angaren Ammi.tana shiga main parlo din ta samu wayarta tana ta faman ringing karasawa tayi tare da daukar wayar sunan data gani akan wayar yasa ta kura mata ido,kasa rike hannunta tayi akan daga wayar sai da ta dauka takai a kunne tana sauraro daga can b'angaren cikin cool voice sanyayya yace"Ammina".wani irin ajiyar zuciya ta kub'uce mata bata san tayi kewarsa ba sai da daddar muryarsa ta daki dodon kunnanta cikin sarkewar murya tace"Yaya".Jabeer dake zaune yayi saurin mikewa sai dai ya kasa furta komai daga karshe kawai ya kashe wayar yana jin zuciyarsa ta hawa na daga masa kira da wancan Monster din tayi sosai yaji d'acin hakan komawa yayi ya zauna tare da lumshe ido yana ambaton sunan Allah...sororo Layan tayi wayar da kallo bawai tayi mamaki bane dan tasan zaiyi fiye da haka ba,tasan ko a mafarki yaji muryarta zaiyi kokarin tashi a barcin ne babu shiri,sai dai har gobe ta kasa gane musabbabin wannan kiyayyar da yayan nata yake mata hannu tayi saurin sawa ta tare hawayen dake kokarin zubowa akan kumatunta ,dukawa tayi zata ajiye wayar taga Ammi na kallonta cikin son kawar da yanayinta tace"Ammi Yaya ya kira baki kusa".Ammi kam bata ce komai ba ta karbi wayar sai kuma tace"ya kuka baro Ummin naku?""Alhmdllh tace ma duk a gaishe Ku,Annie kuma dai ana can wai zata kwana biyu tunda Abban Husna yana nan",Murmushi kawai Ammi tayi dan tasan dama za'ayi hakan sai kuma tace"kije kici abinci kiyi shirin bacci"."naci abinci wurin Umma zan daiyi wanka ne"Layan ta bata ansa tana yin kasa da kanta.k'afadarta Ammi ta dafa tana kallonta kafin tace"mun fara boye damuwarmu ga juna ne Daughter? Those days ina lura akwai abunda yake damunki amma kina boyewa".Murmushi kawai layan tayi tare da rungumar Ammi tace"kawai dai Ammi ina jin zuciyata tayi mun nauyi,amma bayan nan babu komai ,dan Allah kimun Addu'a".rabata da jikinta Ammi tayi tace"kije ki kwanta,sai da safe".bata jira cewarta ta wuce zuwa bedroom dinta tana dialing number din Jabeer...kwance yake akan makeken bed dinsa idanuwansa a lumshe as always tunani yake yi ji yakeyi kamar ya fasa zuwa gidan sanadin muryarta da yaji dan harga Allah ya manta da ita a duniyar shi amma yanzu kwatsam dan raini ta d'aga masa waya dan raini kuma take kiransa Yaya gaba daya ta bata masa mood.a hankali ya bude lumsasun idanuwansa kamar mai jin bacci ganin Ammi ke kiran yasa ya d'aga wayar yakai kunne bedai ce komai ba.Zama Ammi tayi a gefan bed tace"dama nasan ai ba magana zakayi ba,Jabeer na fada maka ka fita hanyar yarinyata,ka daina sakamun yarinya kuka wallahi zanyi maganinka akan Layan cikin gidan nan ,menene na duk wannan fisabilillah me innocent yarinyar nan ta tab'a yi maka,to bana so kar na kuma ji karna kuma gani dan hakurina ya fara k'arewa".sanyayyar ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa"keda waye haka Ammi? Wani abun ya faru ne?".wani takaici ya kama Ammi tace"a'a da kaina nake tunda ni da wani nake waya bada kai ba".Dan sake fuskarsa yayi alamun murmushi sai kuma yace"kiyi hakuri"daga haka yayi shiru tasan ko kwana xasuyi a haka ba wani abun zai kuma cewa ba,sai da safe tace masa ta kashe wayarta tana tunanin yarda zata bullowa wannan al-amarin....Daga toilet Abba ya fito da alamu alwala ya gama yana mayar da links din hannunsa yace "a'a Momyn yara me yake faruwa naga kuma kin daddaure fuska ?". murmushin yake Mommy ta kirkiro tare da cewa" ina fa babu komai kawai na fada tunanin duniya ne da kuma sakon da Lamin ya bani na fada maka sai yanzu ma nake tunawa".Murmushi Abba yayi ya zauna tare da jan plate din da Mommy ta zuba masa Abincin yayi bismillah ya soma ci sannan yace"ina jinki ,Allah yasa alkhairi ne".murmushi sosai ya bayyana fuskar Mommy ta kuma washe baki"tace alkhairi ne mana tunda mun kusa daukar sirika,yace mun a sanar maka ya tsayar da Ihsan y'ar wajen Hajiya Sha'awa a wacce xai aura tunda ta karasa karatunta".sosai fuskar Abba ta kawata da yalwataccen murmushi yace"kai alhmdllh ashe ina da Rabon fara aurar da yarana,Ihsan dai yar wajen Alhaji Sada dana sani,to Allah ya amince bari Dan uwansa yazo shima sai ya gabatar da tasa sai ayi gaba daya dana Jabeer din,in zai yiwuma Faruk da Jafar duk zaman me zasuyi a gidan".dandanan fara'ar fuskar Mommy ta bace jin ya ambaci Jabeer da kyar ta iya saita kanta tace"to Allah ya kaimu"."ki turo man da Lamin din".Abba ya fada. Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 16 A can edge na bedroom ya hango Mommy zaune da alama zaman jiransa kawai takweyi,karasawa yayi ya zauna kusa da ita kafin yace"Mommy kin kira".kallonsa tayi na tsawon mintuna kafin ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya tana kuma jin tayi na'am da shirinta dan tasan yarda Ihsan kesan Lamin tun kafin subar k'asar tasan ba za'a kuma samu matsala ba,fuska a daura tace"so nake ka fada mani matsayina a wurinka Lamin".Dago idanuwansa yayi yana kallon Momy yace"ban gane wannan tambayar ba Mommyna".."eh ai kaji abunda na fada abunda kuma kaji shi nake nufi kuma nake son ji".shiru yayi sai kuma yace"kece Mamana wacce ta haifeni ta kuma so ni tun ina ciki ta Raine ni har izuwa girmana ,bani da wani tamkarki duk duniyar nan".Jinjina kai Mommy tayi kafin tace"in dai har ka yarda da wannan matsayin da nake da shi a wurinka kuma ni na tsugunna na haifeka ina so ka ansawa Abbanka a matsayin kai ka fitar da Ihsan a matsayin matar Aure,kuma kaje Ku ganta dan mun gama magana da Hajiya Sha'awa na zaba maka matar aure".Tunda Mommy ta anbaci Aure sam Kansa ya daure yayi masa wani mumunan sarawa wani tsoro da fargaba a take zuka lullubesa gaba daya ya dabaurce ya kasa fahimtar manufarta,irin kallon da yake binta dashi yasa ta gane ya daina fahimtar komai ne hakan yasa ta kuma jaddada masa maganarta da zallar bada umarni.Gyad'a Kansa kawai ya soma yi kafin cikin cool voice mai nuna alamar karaya yace"Mommy Ihsan dai dana sani?"."to ina da wata bayan ita ne?".Nan ma girgiza kai kawai yayi sai yace"Mommy ki rufa mun asiri dan Allah,wallahi ni da Ihsan sam bamu dace ba,Ihsan bata da natsuwar da zamu iya zama a mazaunin maaurata,ki ceci rayuwata Mommy wallahi ina da wadda nake so"."bana kuma son jin komai daga bakinka,wacce irin dauka to kakeyiwa Ihsan din? To Ihsan ita na zaba kuma haka na bada umarni,batun kana da wacce kake so wannan ka ajiyesa gefe dan nasan wacce kakewa hari sauran cuta to Lamin ko ina cikin kabarina ban lamunce maka ka auri Layan ba bana bukatar hada jini da Fatima in dai ni na haifeka"..Runtse idanuwansa yayi yana jin yarda zuciyarsa ke bugawa ga wani zazzabin dake rufesa lokaci daya,cikin deep voice yace"kiyi hakuri wannan be kai ki bata ranki ba,insha Allah zanyi duk yarda kika ce,zanje na gantan harda Abban ma"Hydar da yake tsaye a bakin k'ofa zuciyarsa na tafasa ya turo dakin ya shigo dawowarsa kenan daga Gombe fuskarsa a matukar daure yace"yanzu Mommy dan Allah ba zaki tausayawa Yaya Lamin ba,ki kallesa lokaci daya yarda ya juye,meye da Lay uncut arts zaki ce ba za'a aureta ba? mommy dan Allah ki tausaya masa rayuwar aure fa ba kwana daya ba biyu bace rayuwace ta har abada so please let him be".sakin baki Mommy tayi tana kallon Hydar ta sani duk cikin yaranta babu mai zafin ranshi duk da yana mata biyayya amma baya iya hadiye magana idan tazo bakinsa tsab a gaban kowa zai fada mata wani irin murdadden hali ne dashi baya shakka baya tsoro,dakuwa ta watsa masa tace "kaniyarka ubana bari na zauna kamun bayani sai ayi abunda kake so,wallahi wallahi Hydar idan baka fita a hanyata ba a gidan nan ni da Kaine ne,wato labe ka soma mun ko? Daga gidan ubanwa ma kake ka dawo ba sanarwa?". Kallon Momy kawai yake bece komai ba ya juya yabar dakin,kwafa kawai Mommy tayi tana jin zuciyarta na zafi." Kiyi hakuri Mommy insha Allah za'ayi yarda kika ce"ta tsinkayi muryar Lamin".Murmushi ta saki dan tasan tsananin biyayyarsa gareta tace"Allah ya maka albarka tashi kaje Abban naka na jira"...koda ya fita ji yakeyi har baya gani sosai kasa wucewa yayi dakin Abban da kyar ya gaishe da Aunty Amarya dake parlon ya wuce part dinsu ya shige d'aki ya kwanta yana sauke numfashi a jere-jere....hannu Ammi ta sanya ta karbi karamin picture din dake hannun Layan ta tsurawa ido tana zancen zuci Wanda hakan yasa har bataji shigowar Ammi dakin ba,saurin yin kasa tayi da kanta tana wasa da zara-zaran dogayen yatsun hannunta,zama kusa da ita Ammin tayi tana k'arewa hoton Jabeer kallo Wanda ta karba a hannun Layan,Murmushi tayi sai kuma tace"gashi kuma Yayan naki yayi kyau a hoton".fuskar Layan sosai ta fad'ad'a da murmushi ta rike hannun Ammi sosai cikin nata tace"to Ammi aishi dama Yaya Veer mai kyau ne,duk gidan nan babu mai kyan sa"...Murmushin Ammi ta sakar mata tare da cewa"kuma Layan saboda kyau kenan kike son sa".kallon Ammi tayi duk da tasan aduk duniya yarda Ammi tasan komai nata ko Basma da Muhibba basu sani ba,yes Ammi ta raineta amma ta zame mata uwa,kawa kuma abokiyar shawara tana taka muhimman bangarori da yawa a rayuwarta sam mantawa ma takeyi da Ammi ce mahaifiyar Yaya Jabeer .girgiza kanta tayi duk da kunyar data rufeta cikin sanyin nan nata Wanda ba kowa ya Santa dashi ba tace"ko kusa Ammi,ai kyau yana gushewa ko ba mutuwa ai akwai tsufa,kawai so ne na tsakani da Allah marar algush".Jinjina kai Ammi tayi kafin tace"kuma duk da zuciya,izza da d'agawa da nuna mulki irin na Jabeer amma kikaji kina sonsa kina son kasancewa dashi?".wannan karon kallon Ammi tayi daga zuciyarta take jin tsananin gamsuwa dan haka tace"wannan ai ba wani hali bane marar kyau Ammina,sanin kanki ne babu wacce ba zata so ta mallaki Yaya Jabeer ba saboda duk wani qualities da ake buk'ata he has it,wannan ai halittar Allah ne kuma Wanda ya hada duk wasu nagartattun halaye mezai hana a same shi mishkili irin haka duba da irin rayuwar daya taso,kawai Yayana he's a man of principle kawai"..Rike hannuwanta Ammi tayi duk biyun tana kallonta kafin tace"ni na haifi Jabeer my Dear,amma bana jin soyayyar Jabeer a zuciyata kamar yarda nake jin soyayyarki a raina Layan,aure rayuwane na har abada ba jeka ka dawo ba,sanin kanki ne akwai wata kaddara da Allah ya kaddara a tsakaninku da Jabeer Wanda babu Wanda yasan mafarinta bare kuma ranar karewarta kullun namu shine kawai addu'a,amma nayi maki fatan kiyi auren kina so ana sanki ,in da zakiyi mutunci ki kuma shinfida zuri'arki cikin aminci Layan,sai dai zuciyarki bata bi dake ta wannan bigirin ba,sai tabi dake tsani mai tsananin wahalar wucewa ,in da zakbi shawara da kin hakura da Jabeer ,rabuwa da Jabeer is not the end of your life my Dear kawai zaki sake sabuwan rayuwane kiyi addu'a Allah zai kawo maki da wani Wanda yafi Jabeer din,amma auren Jabeer bana jin hanyace mai billewa a gare ki Daughter "...hawayene Ammi ta gani suna riga rigan safkowa daga idanuwan Layan cikin dishewar murya da rudewa da rashin sanin abunyi tace" Ammi bazan iya ba,banzan iya ba,nasha gwada hakan a rayuwata amma bana tashi da komai sai damuwa da tsananin tashin hankali,even kasancewa dashi will be the last thing da zanyi a rayuwata Ammi zanso hakan ,muddin na rabu dashi wallahi Ammi mutuwa zanyi".ta karashe zancen tana fadawa jikin Ammi ta saki kuka daga zuciyarta...Bubbuga Bayanta Ammi taci gaba dayi tana tunanin tabbas tana da ikon saka Jabeer Auren Layan sai dai bata san wanne irin zama Layan zata yi ba,dan ba zata bisu gidan auren ta zauna dasu ba,tasan waye Jabeer ta kuma san wacece Layan tasan tunda yace baya yi ko ya ansa hakan bazai taba sa yaso Layan din ba,Jabeer wani irin murdaden mutun ne Wanda keda wata bakar zuciya, izza da mulki duk a cikin jininsa suke duk da bai kasance dan sarauta ba amma rayuwarsa da tsari,ga taurin kai kamar mutanan farko,bata fatan Layan tayi rayuwar kunci a gidan Aurenta sai dai kuma tayi nisa bata jin kira kuma bata iya jin zata iya tursasata tayi mata dole akan rabuwa da Jabeer din... Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 17 Cikin isa izza da tsantsar kamewa yake barin parking lot din in da yanzu Driver ya dauko shi daga Airport, sam ya kasa samun wayar Buddyn nashi bare kuma yaje ya d'aukosa kai tsaye d'akin Ammi yayiwa tsinke sai dai turus ya tsaya daga k'ofa ya kasa karasowa yana wani sauke ajiyar zuciya...plate din hannunta ya subuce indomie din dake ciki ta zube a wajen jikinta har rawa yake ta kuma rasa what next da zata iya yi,wani irin takaici ya kumesa yana kuma kara ganin rawar kai da rashin hankalinta dan shi a rayuwa bai taba daukar Monster a matsayin mai hankali ba,k'asa kawai ta tafi akan k'afafunta tana niyar saka hannu a Abincin daya zube muryar Ammi ta karade parlon da fadin"ke kam lafiyarki? Da zafin zaki saka hannu? Bana son sakarci kin bar wajen nan ko kuwa"Ammi ta kare maganar tana bin shigar jikinta da kallo,3quater siket ne mai robar Wanda ya fitar da dan sirirn kugunta kamar an zana ash colour sai armless fara k'al kanta babu ko hula,sai a lokacin kuma Ammi ta mayar da kallonta kan Jabeer dake tsaye jikin k'ofa ,sai yanzu ta gano bakin zaren tabbas shi Layan ta gani har tayi mata b'ari a nan sharewa tayi tare da cewa"oya work out idan ba zaka shigo ba".ji yakeyi kamar ya juya sai dai yasan Ammi won't take it easily yasan sarai zata masa tas ne ta masa koran gaske, karasowa kawai yayi ciki yana mata sannu da gida,zama tayi a chair din dake facing dinsa ta ansa kafin tace"Layan ,Layan".lumshe idanuwansa yayi yana jin yarda zuciyarsa ke halbawa da karfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito a iya jin ambatar sunanta ma kadai,bai gama recovering ba muryar Ammi ta karasa hargitsayi ya soma regretting zuwa garinma gaba daya"zaman me kikeyi a d'aki ? Ki kawowa Yayanki abun sha ".samun Kansa yayi da marairaice fuska ya tsurawa Ammi ido as if his life come to an end yana son yin magana amma he's speechless at all....Layan kam jiki na rawa ta karasa kitchen ta hado masa ruwa da drink din da tasan don shi Ammi ke ajiyewa ta daura duka a tray with glass cups ta taho making sure babu wani abu daya b'aci ko ya nuna rikicewarta.A cup ta zuba komai with cool voice tace"Yaya gashi". Ji yayi kamar an zuba masa wuta a kunnuwansa musamman data kasance a kusa dashi,sai dai ya kasa yin komai ganin yarda Ammi ta tsare shi da ido yasa ya sauke ajiyar zuciya yana kuma yin k'asa da kansa kamar bazaiyi magana ba yace"zan dauka"... murmushi Layan tayi ko ba komai yau kam zata bugi kirji tace yayi mata maganar arziki ko domin darajar Ammin data ci dama ta sani ko a lahira wani yana cin albarkacin wani...Mikewa tayi a sanyaye tabar wajen......da idanuwa kawai ya tsarr Ihsan dake fitowa cikin tankamemen parlon nasu Wanda ya gama tsaruwa da haduwa dan kyau ya kuma ji kayan more rayuwa.sanye take da atamfa dinkin gown tayi matukar d'ameta kamar a jikinta aka zana rigan,ga fuska taci uban make-up sosai tayi kyau amma sam hakan ya kasa burge Lamin dake kallonta kamar wata halitta ta daban,dauke kansa yayi ya mayar akan waya yana pressing kamar besan tana tahowa ba.da Dan sarsarfa ta karaso wurinsa fuskarta cike da farin ciki Ihsan bata da tsawo sosai sai dai tana da cika tana da kyau daidai misali bata da haske can sai dai man da take Shafawa ya hadu da Hutu ya karasa mayar da ita fara tas ,kusa dashi tazo ta zauna fuskarta kamar gonar auduga cikin dauki tace"baby sannu da zuwa,ya hanya? Ai na dauka ba zaka zo ba harna gaji da jira".Kokarin danne zuciyarsa yayi kafin ya kalleta yace"mezai hanani zuwa ,yasu Momy?".d'age kafad'a tayi Wanda yanayin dinkin ya bayyanar dasu a waje tace"sun fita"sai kuma ta mayar da kallonta a gabansa cike da zafin nan nata da yauk'i ta soma kwala kiran"suwaiba,suwaiba,uban meye kikeyi a ciki? In ajiye Mijina a nan amma baki kawo masa komai ba".Cikin sauri Suwaiba ta fito jikinta har rawa-rawa yakeyi tace"Aunty dan Allah kiyi hakuri ina had'a kayan ne ba'a shigo da drinks da wuri ba".tsuka kawai taja ta karbi tray din ta kori suwaiba tana kuma kara ruwan masifarta,Lamin kam bece komai ba sai binta kawai yake yi da ido.duk irin yarda suke gaisawa yasanta tun yarinta amma yau sai yaga ta canza masa ta zama wata ta daban duk ta koma masa wata bakuwa .....Murmushi kawai yayi ya karbi cup din drink da Aunty Amarya ta bashi yana kuma kallon Daddy kafin yace"kai maa sha Allah,Allah ya tabbatar mana da alkhairi".."badai bakuyi magana da shi Dan biyun naka ba?"Abba ya tambaya.drink din Kamun ya shafa kansa fuskarsa a sake yace"a'a na sani Abba,ban dauka azarbabi yasa harya fada maka bane".jinjina kai Abba yayi kafin yace"to kai fa Captain? Kasan dai bazan aurar da Lamin kai na zuba maka ido ba,kamar yarda kukeyin komai a tare to haka ma aurenku bana fatan na raba ba Jabeer".k'asa da kai Jabeer yayi baidai ce komai ba ,to mema zai ce bayan yasan ansan shine shi bashi da matar aure babu kuma wacce ya tsayar."aishi aure lokaci ne Alhaji,kowa daka gani Allah ya tsara masa nasa lokacin,ta yiwu ta nan Allah ya banbanta,kamar yarda ya banbanta nisan sama da k'asa sai a fara yin Wanda ya samu kawai ,tun da ba'a zauna zaman jira ba"Momy Badiyya ke fada tana zama kusa da Abba.abincinsa yaci gaba da ci kafin yace"insha Allah babu abunda zai raba,tare duk zan rika aurar da yarana da yardar Allah".sosai Aunty Amarya ta fad'a da fara'arta race"Allah ya amince ai ba dadi rabawan kam".Lamin da yayi sallama ya katse masu firan gaishe dasu yayi kafin ya zauna suna musabaha da Jabeer kafin cikin sanyi yace"Abba ka kira,jiya banji dadi bane shiyasa ban shigo ba"..sannu da jiki suka masa kafin Abba yace"naji sakonka wurin Mommynku to shine nake so na kuma jin tabbacin zance daga wurinka..."haba Alhaji to zan kirkira abunda bashi bane na fad'a? Yaron nan shi da kansa yaga Ihsan kuma kowa ya sansu tare tun ba yau ba,abune na tun kuruciya"Momy ta fad'a...tsura mata idanuwa Abba in a serious note yace"kinga Badiyya idan ba zaki mun shiru ba ga hanya ki fita,idan kin fada magana bazanyi aikina matsayina na uba ba?".kasa da kai Momy tayi sai kuma tace"ayi hakuri banyi tunanin haka zaka dauki zancen ba"...kuma kallon Lamin Abba yayi.Lamin kam Sau daya ya kalli Momy ya dauke kansa da Sauri sai kuma yayi kasa da kai ,all his attention is with him trying to figure what's going on da Lamin din dan tunda aka fara maganar ya gama fahimtar komai kawai out come na Lamin din yake son ji kafin ya gama tattara komai....sanyayyar ajiyar zuciya Lamin ya sauke sannan yace"eh Abba,ni nace mommy ta fara fada maka ,ni na zabi Ihsan din".A boye mommy ta sauke ajiyar zuciya duk da tasan Lamin din bazai taba bada ita ba,amma taba tsoron Abban ya gano wani abun..."to Alhmdllh insha Allah za'ayi komai kamar yarda ya dace dan bana so a ja lokaci,kaima Jabeer kaje ka huta zuwa gobe zamuyi magana da kai insha Allah".godiya sukawa Abban sannan suka fita.at all Lamin is looking so disturb kallo daya zaka masa ka fahimci haka,jan kunnansa Jabeer yayi da karfi har ya dan saki kara kafin yace"you okey? Waya fada maka ana wasa da aure ? Shifa har abada ne,tunda ka ansa kasan kuma magana bata canzuwa so guy chill".kyab'e fuska Lamin yayi kafin yace"Mommy love's the girl so I think I will do this for her,ba wata damuwa".... *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 18 Without any concerns dan yasan dama hakan zata faru,murmushin daya dade beyi bane ya sub'uce masa yana kallon Annie data takarkare tana mashi bayanin yarda akai tabar gida tazo gidan Ummi"to ni yar banza ce Jabeeru ? Ai kana barin gidan nan naji ya koma mani imty wallahi sam zaman ba wani armashi kawai na hada kayana na taho nan,ahto naga ai duk an zama d'aya zumunci dai Wanda yayi dan kansa, nasan ina komawa zaka samu maryam din can tana wani bubud'a hanci to ni bata daman ba,babu kuma Wanda ya iya ya sanya ni in yanke zumunci,jiya nan har Ali ta turo mun nayi masa fata-fata nayi masa korar kare,amma yau kafarka kafata"...."to ni ba gidan zanje ba".ya fad'a slowly ".." To meye wani ba gida zaka ba?,Allah na tuba kai kana da wurin zuwa ne?".Ummi ce ta katse masu firan tana fadin"yaushe a gari"...gaisheta ya farayi kafin ya fada mata lokacin daya dawo ,jinjina kai tayi tare da cewa"yau kuma Annie sai gida zaki bar mana kewa kuma".washe baki Annie tayi kafin tace"ai ba jimawa na dawo insha Allah,balle kinji auren yaron can aketa kokarin shiryawa kara naje kafin waccan narkekiyar matar tayi Kane Kane akan komai ta nemi maida kowa bare,ni kuma a lokacin zan nuna mata ba a banza muke ba wallahi,dan in zuciya ta ibeni tsab zansa Ahmadu gaba yayi mani maganinta".murmushi kawai Ummi tayi tana jinjina lamurran Annie jiya ba yarda Aliyu beyi da ita ba harda albishir din auren amma tayi fatali kuji yanzu kuma hankalinta gaba daya ya karkata can gidan Hajjan ma ta fasa zuwa...ba wani dadewa Jabeer ya ibi Annie suka wuce gida,kafin ta dawo Ammi taje ta gyara mata part dinta duk da ba wani barinshi akeyi ba gyara ba amma tasan Annie tana zuwa zatace dan anga bata nan aka wulakanta mata gida an barshi duk datti....d'aya kan d'aya Annie ta zauna tana k'arewa ko ina kallo ta tsuke fuska dan sam bata bukatar wata doguwar magana bare a kawo mata ba'asi .har k'asa Ammi ta dauka ta gaisheta tare da mata sannu da dawowa.ba wani sakin fuska Annie ta ansa tana wani kawar da kai kafin tace"to Allah yayi albarka tashi kije,ina so zan gana da jikokina".Murmushi Ammi tayi dan tsab ta gama gano in da Annie ta dosa maganar zaman gidan Ummi fatyma ke bata so a mata dan haka batace komai ba ta mike ta fice.sai lokacin Annie ta saki fuska ta kuma yi k'asa k'asa da murya tace"kaga yanzu ai nayi maganinta da yanzu tana nan yana kare mun tanadi kamar wata uwata,to haka duk zan fatattaki Ahmadu da Sadeequ in nuna masu ni na haifesu basu suka haife ni ba,nima su gane matsayina".kallonta kawai Jabeer keyi bece komai ba yadai lumshe ido kawai..da sallama Layan ta shigo d'akin ganin Jabeer a zaune yasa ta kuma kame kanta cikin sanyi tace"ina wuni Yaya" jin zuciyarsa ta halba da karfi ya kuma ji abunda ya tsana ya tabbatar masa ta shigo wurin bai gama tunani ba muryarta wacce take masa ansa kuwwa yake jin kamar ana masa idin tashin hankali a kai ,kuma runtse idonsa yayi bece komai ba yasa tayi saurin karasawa ciki.a hankali kuma asanyaye ya bude idanuwansa yana niyar mikewa idanuwansa suka sarke cikin nata da azama ya kawar da kansa sai kuma ya zazzare lion eyes dinsa a matukar fusace yace"you you,ko ke mayya ce to naman Jabeer yafi karfinki,har abada na haramta a gareki.Witch tsakiya... ...tuni jikinta ya soma rawa tayi kasa da kanta dan dama tsautsayine ya saka su had'a ido ,itakam har abada ba tajin zata iya jurar had'a ido da Yayan nata sai dai kamar wata statue wacce aka dasa a wurin ta kasa motsawa bare tabar wurin...cikin saurin Lamin ya rike hannunsa da yake kokarin kai mata wani wawan Marin da take da yakinin jinta zai iya daukewa na wani lokacin,idanuwansa da suke a lumshe hawaye na tsiyaya ta soma budewa a hankali tarwai ta budesu a fuskar Lamin dake binta cike da matukar tausayi Wanda duk abunda ya soma faruwa yana bakin kofar a tsaye har a yau a wannan lokacin ya kasa gazagata irin doguwa kuma nisan kiyayyar da Jabeer yakewa Layan abun tun yana bashi mamaki harya daina cikin sanyin murya yace"still Jabeer? Har yau kuma abun bazai taba canzawa ba? Har yau kana nan a in da na barka ? Ya kake so muyi da rayuwa Jabeer"...fizge hannunsa da Lamin ya rike yayi cikin tsantsar fushinsa da yake kasa sarrafa kansa aduk lokacin da yayi tozali da Layan ya soma magana da kakkausar murya yace"wallahi billah idan har bata daina zuwa in da nake ba ina dab da ilatata ,illah mai yawa kuwa wacce kowa bazai so hakan ba,I just hate her with passion, har abada kuma har gaban abada zamu ci gaba da kasancewa a in da ka sanmu Lamin, she just stay away from me"...ko kad'an doguwar maganar da Jabeer yayi akan Layan bata bawa Lamin mamaki ba,sam yasan in dai har kaji doguwar maganarsa da hayaniyarsa to tabbas akan Layan ne,dafe kansa yayi ya kasa gane madosar wannan kiyayyar,wacce bata da asali bare kuma tushe,a yanayij yarda gidansu yake masu halayya da ra'ayika mabanbanta ya kamata a tsari kuma ace Layan da Jabeer sunfi kowa shiri amma sam lamarin ba haka yake ba,,,duk yarda Layan keson kasancewa da Jabeer amma shi kamar wuta yake yana kuma kallon Layan kamar karmami jiranta yake kawai ya ganta ya cinyeta without any though. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya mayar da kallonsa in da Jabeer yake amma sai yaga wayau yayi halin NASA yabar wajen,wani irin tausayin Layan ya kamasa "ya Allah na rokeka ka kawo wani abun da zai sassauta wannan wutar kiyayyar ta Dan uwana ,Ya Allah na rokeka ka bude masa idanuwansa yaga haske idan zaiyi tsana yayita dominka idan zaiyi so yayi shi kuma dominka"... Cikin sanyin murya Layan tace" ameeen Yaya"hannu ta saka ta sahare hawayen fuskarta tana murmushi tace"Yaya ka manta kawai.ba yau aka fara ba bana tunanin kuma za'a kare yau,amma insha Allah komai zai wuce kamar ba'ayi ba,to karka damu kanka akan wannan as always,naji anata maganar aurenka ina dab da yin fuahi Yaya sai kuma nayi maka uziri ,nice ya kamata ace na fara sanin Auntyn nan tawa amma shine ko sanar da ni baka yi ba sai dai naji Daddy suna maganar kai kudi da Umma"...kallonta kawai yakeyi yama rasa me zaice ko mai zai fada can dai yace"I'm sorry lil komai ya faru ne da sauri,but surely I will take you to her".murmushinta mai karawa chocolate colourn fuskarta kyau ta saki ta soma zuba masa surutu da sam baya fahimtar komai bare kuma yasan in da ta dosa kallonta kawai yake yi,shi dai yasan koma menene kawai yana jin dadin kasancewa da ita a hakan..wani kayataccen murmushi ya subuce masa yana kallon dan karamin bakinta data tura a gaba alamun tayi fushi wai ita kadai ke labari sannan yahau aikin rarrashi.sai lokacin Annie ta shigo dakin daga kitchen hannunta rike da plate data saka Dan wake shigarta ajiye plate din tayi tana k'arewa Lamin kallo kafin tace"kai kuma fa daga ina? Sai kace Wanda aka jefo,daga jin dawowa harka lallabo ni wannan kwakwa haka har ina?".Dariya kawai Lamin ya saki tare da cewa"ki daice mun kawai rowarki ta motsa kuma ba abunda zai hanani cin Dan waken nan ni da kanwata"ya kare zancen tare da janyo hannun Layan suka saka Annie a tsakiya.... Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* Telegram at https://t.me/jorderhmajidadi 19 Daidai kofan shiga room dinsa yaga Ammi tana niyar juyowa kallonsa kawai tayi ta kawar da kai sai kuma tace"ina kaje".cikin k'asa da murya kamar ko yaushe yace"no where".jinjina kai tayi tana karantar yanayinsa tsab sai kuma ta share tace"meet me at my room immediately "bata jira cewarsa ba ta fito kawai da kallo yabi bayanta sannan ya tura d'akinsa ya shiga dan canzawa...wani irin murmushi ne ya subucewa Momy Badiyya ta fito rike da hand bag da alamar fita zata yi tace" a'a maryam kwana biyu bamu hadu ba,ince dai kinji niyya da kuma abun alkhairin dake tunkaro d'ana ko ince ya dangwalo arziki ya samo yar gidan tarbiyya,aure insha Allah nan da wata d'aya za'a daura"..Murmushin itama Ammi tayi cikin ko in kula dan tsab ta gama fahimtar in da Momyn ta dosa tace"Allah yasa alkhairi ai munyi magana da Lamin din,Allah ya kaimu lokacin lafiya"bata kuma jira cewarta ba ta wuce abunta dan a yanzu abubuwan dake kanta sun fi mata sa'insa ko ta zauna Momyn ta bata mata rai duk lokuta da dama tana shakkar hakan dan tasan maryam din ba kanwar lasa bace,kallon Basma tayi dake gaisheta da mata sannu ta ansa tana kallonta ,sunkuyar da kai Basma tayi tace"Ammi Abba yace wai kizo".jinjina kai kawai tayi ta kuma jan mayafin abayarta kafin ta wuce wuce part din Abban,kamar ko yaushe da barkwanci suka gaisa da Aunty Amarya kafin ta mata jagora zuwa parlon Abban ta fita ,ganin suka Yayun nata yasa ta tabbatar maganar mai mahimmanci ce ta zauna a daya daga cikin sofas na parlon sannan ta soma gaishe su...gyara eyeglasses Abba yayi kafin yace"Maman Layan mun kira ki ne akan maganar Jabeer,a cikin satin nan nake so a tsayar da ranar auren Lamin to sanin kanki ne bazanwa Lamin aure ba nabar Jabeer, munyi magana da shi duk da ba wani mahimmanci yaba maganar ba amma sam banga alamun ma yana da wacce zai iya gabatarwa ba,wannan dalilin ne yasa na kiraki ki zauna dashi kiji ko yana da wani ra'ayi ko wacce zai gabatar idan kuma babu mu Sai mu zab'a masa nasan insha Allah kuma bazaiyi dana sani ba"....Murmushi Daddy Sadeeq yayi kafin yace"gaskiya lallab'a mun my son za'ayi dan bashi ma da wacce yake so a yanzu kam,bana tunanin a zaba masa kuma mafita ce in an zaba din ma ina rokar mana alfarma a bamu lokaci muji mun aminta da ita"..."kace kuwa Yaya Sadeeq babu ranar da Jabeer zaiyi aure kenan,kafi kowa sanin halinsa da kafiyarsa hasalima mata basa gabansa ,ni a gani na batun ma a tsaya tambayar ra'ayinsa bata taso ba ,Ku ke da iko da Jabeer nasan ba zaku samu matsala da dangin mahaifansa ba tunda abun alkhairi kuke da niyar kullawa,duk abunda kuka yanzu hakan za'ayi bamu da wani ja a cikinsa fatanmu kawai Allah ya tabbatar mana da alkhairi ".jinjina kai Abba yayi ya kuma cewa" duk da haka Mamana jin ra'ayin nasa nada mahimmanci,kiyi magana da shi sai ki sanar da ni yarda kukayi insha Allah koma menene zan nemi General kuma akan maganar".Da haka suka rabu Momy ta taho tunaninta na kuma rabuwa gida biyu,a yanzu ne take da damar aikata abunda ke ranta sai dai can kasan ranta tana jin rashin kwarin gwaiwa da kuma fargaba amma tana ganin kamar hakan shine mafita da kuma kwanciyar hankali da zasu samu baki d'aya.a parlonta ta same shi a zahiri ya kurawa TV manya manyan idanuwansa masu matukar haske da kyau sai dai sam hankalinsa gaba daya baya kan TVn dan bama zai iya fad'ar me ake cewa ko akeyi a ciki ba,shidai kawai kallah yakeyi yayin da zuciyarsa tayi nisan kiwan lulawa duniyar tunanin takaicin da kuma yarda zaiyi da rayuwar yarinyar can da duk yarda yake sai ta bata masa rai ko san ganinta baya yi,har Ammi ta zauna kusa da shi sannan ya juyo yake kuma gane wani ya iso in da yake be furta komai ba ya kuma jingina da kujerar yana lumshe ido.tasan idan za'a kwana a haka bazai taba cewa komai ba zallar b'acin rai da damuwa karara kawai take iya fahimta a kyakyawar fuskar shi.bata damu ba sam Dan tasan bakin halin nasa ne ya motsa tace"Abbanku ne ya aiko ni wurinka, yana so yaji shin ka tsayar da wacce kake so ,ko kuma kana da ita wacce kakejin hankalinku ya hadu da ita?".sai a lokacin ya ware manyan idanuwansa yana kallon Ammi sai kuma yace"ban gane ba Ammi".."ya za'ai ka gane dama ? ,kasan na zama k'awar wasanka ai".wani kyakyawan k'yataccen murmushi ya sub'uce masa Wanda ba kowa ke samun damar ganinsa yana murmusawan ba sai Ammi kawai da Hajja na ukkunsu kuwa LAMIN,ita kanta sai da tayi kasa da kanta tana tasbihi ga Allah daya cika halitta ya kuma wanzar da kyau a jikin Danta Jabeer ."babu ,ni meye hadina da Mata kuma Ammi?"Yayi maganar cike da shagwab'a .kallonsa take yana kuma tuna mata da abubuwa da dama sai fuskarsa duk yarda ake cewa tana tsananin kama da shi a yau sai ya juye mata sak mahaifinshi dama ba'a maganar murya da yawancin halayayyansa...Daure fuska ta kuma yi tace"to count your self among wa'anda zasu fara kulla alaka da matan "...Shidai kawai kallon Ammin yake yi as if his life defend on ita ko yana shirin gano wani abun a jikinta sai kuma yayi murmushi yace" ni dai ki fada masa bana son auren kuma".ko kallonsa bata yi ba ta tashi ta wuce d'aki abunta tana kuma tinano irin durgar da za'asha da wancan murd'ad'en halin nasa to amma kuma duk da hakan bashi zai sa a kyale shi ba .aure kam ya zama dole ko yana so ko baya so...Sosai Ummi tayi dariya ta kara gyara wayan dake hannunta tace"kai lamarin Jabeer sai shi Allah,yanzu dan Allah in banda shirme meye na wani a fadawa Abban baka son auren?"...other side Ammi tace"to ai Dan naki ne sai kin tashi tsaye kam sam baya jin ya girma sai shiririta cike da kai"..."kuma ai ba kyaleshi za'ayi ba,ni sai yanzu ma nake jin son auren daga baya ya gode mana duk zaiyi ya gama,ni yanzu babban tashin hankalina akan Asma'u ne,bansan ya akai hakan ta faru ba,ko kusa bana jin zan iya sarakuta da Badiyya bare harna wanke y'ata na kaita gidan nan a matsayin sirikarta ,I just can't think zan iya gaskiya"...ajiyar zuciya ammi ta sauke sai kuma tace"addu'a dai shine mafita, tunda yara suna son junansu bamu da sauran abunyi,kuma duk abundata in Allah yace za'ayi ai dolenta tayi hakuri,beside bana jin ma in maganar taje wurin Yaya zaki iya yin wani abu a kai"..."ko wajen General taje kuwa,ni gaba daya bana cikin natsuwa Allah Aunty Maryam ,Asma'u nason ta janyo mani abunda bazan iya jurewa ba"..."just pray Fatima,Allah ya zab'a abunda yafi alkhairi "...da Ameen ta ansa kafin ta ajiye wayar tana zancen zucin idan hakan ta kasance a ina zata saka kanta,dan ko kusa ba zata iya daukar lamurran Momy Badiyya ba dole ta taka mata burki....." Shi Jabeer din ya fada haka?"Abba ya tambaya.Dariya sosai Aunty Amarya tayi kafin tace"kasan dai wanene Jabeer to na jadadda zance kam be ta so ba,yanzu ina ga sai abi wata hanyar"...jinjina kai Abba yayi yace"to Allah ya zab'a abunda yafi alkhairi zan ganshi da kaina,in banda sakarci waye yake kin aure a wannan shekarun nasa.beside zan ma ga General kawai amma zamansa hakan bazai yiwu ba,bana so kuma wani ya sake tada masa maganar a cikin gidan nan Ku barsa kawai nasan abunda zanyi insha Allah"gaba dayansu da addu'a sukabi lamarin musassan Daddy dan shi in a nashi ne beki an gyale Jabeer ba har zuwa ranar da zai shirya da kanshi.... Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* *SHIN KINA D PALMPAY ACCOUNT? KO KINA NAN ZAUNE GIDA ANAYI BABU KE? GASKIYA A GAISHE KI,SANNU D ZAMA ANA SHANAWA BABU KE ,PALMPAY ALKHAIRI NE,HAJIYATA KINA ZAUNE A GIDA ZAKI IYA SAMUN 3K ,5K,10K,22K ME KIKA MANTA BABU AIKI KOMAI? KAI SHIFA DUK IN DA KIKA TABA KUDI NE,ACCOUNT KAWAI ZAKI BUDE DASU. BABU SISINKI BARE KISHA WAHALA,ME KIKA MANTA KULLUN KIN SAMU KIDINKI A ACCOUNT. TO MAZA GARZAYO DAN SAMUN NAKI RABON.GA MAI SO ZAI IYA TUNTUBAR* 07033636337 Page 20 Kallon Hajjan kawai yake yi sai kuma yace"kika ce zakije can?".cike da dattoko da tsantsar mutunka irin wacce ta kama ta tun yarinta ta murmusa kafin tace"to Jabiru wani abunne dan nace zanje gidanku? Wannan ai daddan abunwe tsakanina da Annie Wanda ka riga ka dade da sani,tsufane kawai da ciwan k'afa ke hanani dan zagayawa,amma insha Allah kam wannan karon babu fashi"....jinjina kai yayi sai kuma ya kama Hannun masoyiyar kakar tasa Wanda yakeji tana d'aya daga cikin matan daya keb'ance a zuciyarsa yake masu madaukakiyar soyayya yace"to ki zauna sai na kawo maki Annie,itama naji tana cewa zata zo,kinga baki da lafiya Hajja".ya karashe zancen cikin cool voice dinsa wacce ta riga ta gama kama masa jiki..Girgiza kai tayi tace"wannan ladan zumuncin sai na sameta,zanje na zagaya kowa,wama ya sani ko shine na k......"kafin ta karasa yayi saurin tsureta da idanuwansa da suka soma sauya launi lokaci d'aya fuskarsa tana nuna madaukakin tashin hankalinsa ya soma Girgiza kai muryarsa a dishe yace"Hajja dan Allah kada ki soma,ni bana son irin maganganun nan,nasan mutuwa dole ce,amma bana kwatanta tafiyarki a yanzu ban shirya dauka ba,dan Allah ki daina".wani murmushin ne ya kwace mata a kan kyakyawar farar fuskarta Wanda daka kalla zakasan a zamaninsu anyi gwagwarmaya a kyau,ta shafa kansa tace"Ayya Jabiru mutuwa ta Allah ce ko yanzu ya kira mu dole mu ansa kira,fatan kawai Allah ya mana arzikin kyakyawan karshe ya mana maganin abunda yake damunmu"ta kare zancen tana tattare littafanta na addini da take karantawa tare da carbahan hannunta ta saka a jakarta irin tasu ta tsaffi tace"to tashi muje ka kaini,dan yau a can zan wuni".karbar mata jikkar yayi kafin suka fito a hankali yake bin bayanta har wurin mota ya bude mata back seat ta shiga ya gyara mata Hijab dinta ya rufe kofar sannan ya zagaya Driver seat ya shiga ya rufe ya tada motar suka wuce gida......A parking lot ya ajiye motar kafin ya fito Layan dake tsaye a wurin tana bawa gateman kulan Abincin da Umma ta bata yana mata godiya ta juyo da sauri ganin Hajja a motar Jabeer din ,kwata kwata ta manta da duk wani abu da zai iya yi mata ta rugo da gudunta zuwa wurin motar,Daga glass na motar yake hangota ,English wear ne jikinta siket red irin mai budadden nan sai ya baje sosai ko kafarta baka iya gani,sai white T-shirt itama mai fadi red veil mai dan girma ta yafa a sakalkeken dogon gashinta data tunkushe wuri daya wani tsabar takaici da kunci ya tokare masa zuciya ganinta da yayi.saurin dauke idonsa yayi yana hadiyar yawu da kyar na takaici.kafin yayi wani yunkuri tuni ta iso taja murfin motar ta budewa Hajja wani irin farin ciki yana cikata kallo daya zaka mata ka gane irin farin cikin ganin Hajjan da tayi,cikin sanyin muryan nan nata take fadin"oyoyo Hajjana sannu da zuwa ,barka da zuwa ,lallai tsohuwar nan da kokari kike harkin rigamu zuwa gobe muke cewa muzo tare da Annie"jin muryarta yake har cikin kokon kwanyar kansa saurin lumshe idanuwansa yayi ya daura kansa a sitiyari sai kuma kamar Wanda aka mintsina ya mike ya balle murfin motar da sauri ya fito,sai dai yayi tsaye yana kallonta harta fito da Hajjan tana rike da hannuwanta cikin nata tana kuma gyara mata takalmanta dan suyi mata saukin sakawa tana a duken tace"Yaya Jabeer ka dauka mata Jakkan a mota sai in karasa da ita wurin Annien ".bata damu ba sam ko tuna yanayin da zai iya kasancewa ba ta soma jan hannun Hajjan suna yin gaba,lallausan gashin kansa ya shafa Wanda ya ragewa yawa kasancewar ya koma aiki yayi ,jakkan ya dauko ya rufe motar ya biyosu baya,very carefully take tafiya da Hajjan da tsantsan gudun kada tayi wani abu ba daidai ba,musamman ma yarda take tsananin son Hajjan da kuma jin tausayinta jinta takeyi kamar Anninta suna zuwa daidai k'ofa cikin kausashiyar murya yace" ya isa haka,barta zan shiga da ita".kallonsa tayi da manya manyan idanuwanta tace"Yaya zan iya,ai ina shigowa da ita idan baka nan"..."kaji mun ja'irin yaro Maryam din meta kasa mun? Tsakanina da yarinyar nan ai sai dai saka albarka Fatima da Sadiqu sunyi farar haihuwa,Allah ya jibanci lamurata ya bata miji na gari".saurin yin kasa da kai Layan tayi dan maganganun Hajja sai suka mata nauyi a kai taji kadaukakiyar kunya ta rufeta tace"Hajja muje"har kan sofa na Annie ta ajiyeta d'akin Fes da sai tashin kamshi yakeyi kamar ba'a shiganshi sai gyara kullun .daidai k'afar Hajjan ta zauna tana dan mamatsa mata kafan da mata sannu tace"bari a kirawo Annien nasan tana kitchen ".kafin ta kik'e ta nufi kitchen din tana kwalawa Annie kira .Hajja ta dubi Jabeer tace" Allah da Sadeeq xai iya daya bani yarinyar nan mun zauna,Allah ya sani ina matukar sonta da jin dadin zama da ita fiye da ko wacce yarinya".kallon Hajja kawai yayi ya kawar da kai bece komai ba,danshi nan zuciya ta gama kaishi karshe gaba daya duk tayi kane-kane da Hajja ta hana ya mata komai,bayan aikinsa ne in dai yana tare da ita baya bari wani ya mata wani abu ko da su Ummi ne ke zaune kuwa..."lafiyarki kuwa? Kamar wata tsohuwar makauniya zaki isheni da kira ko me zan maki ma oho"Annie ta fada tana karasa juye miyan zogalen da tayi a kula...Dariya Layan ta saki tace"ni bazan biye maki bama,Hajja ce tazo".saurin ajiye ludayin hannunta tayi tace"kai dan Ma'aiki? Hajjan dai dana sani? Hajja tawa? Dan duk garin nan bani da kamarta wani ma sai ya fiye maka dan uwanka na jini wallahi"..."ita dai da kanta tana parlo tana jiranki"Layan ta fada tana dauko tray ta nufi fridge zata dauko ruwa da lemun tattatun itatuwa da Annie keyi ta ajiye dan bata shan na kwali ko roba sam"....Baki a washe Annie ta karaso tana lale lale da ganin Hajjan tana nuna jin dadin ganinta da tayi ta zauna tana fadin"godiya ta tabbata ga Allah kafa tayi kyau alhmdllh,kinga Wanda bega damar kaini ba,tun jiya nake rokonsa kamar wani abun arziki zai bani amma yamun kunnan uwar shegu,dama Laminu ko Faruqu nake jira gobe su kawo ni kuma sai gaki".Jabeer be kula Annie ba ya fita yabar mata dakin gaba daya dan yasan yau tsab sai tayi masa terere na duk wani abu da Wanda ya sani da Wanda bai sani ba......"nima sai yanzu da yaje na taso shi gaba in ba haka ba ya fita ba kuma ganinsa zanyi ba,sai yace wai bazan fita ba"...rike baki Annie tayi tace"to Hajja wake biyewa Jabiru ? Waya gaya maki yana zumunci shi? Ai lamurran Jabiru sai dai addu'a kawai kam ya sab'a da Sadiqu mariganyi Allah ya jikansa ,muda muke so ya zama makwafinsa amma kin ganshi nan kullun fuska a hade ba annashuwa zuciya cike da bakin hali,ya zamarwa yarinyar nan kamar Dodo duk kokarin da uwayenta sukeyi a kanshi amma sam baya duba wannan,na kusa fara sawa a fara masa rokon Allah ko Allah zaisa a dace da wannan hali nasa mu samu sauki".Annie ta kare maganar tana kallon Kayan dake bawa Hajja Lemu a glass cup,ta karba ta saka mata albarka.... Share *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* *SHIN KINA D PALMPAY ACCOUNT? KO KINA NAN ZAUNE GIDA ANAYI BABU KE? GASKIYA A GAISHE KI,SANNU D ZAMA ANA SHANAWA BABU KE ,PALMPAY ALKHAIRI NE,HAJIYATA KINA ZAUNE A GIDA ZAKI IYA SAMUN 3K ,5K,10K,22K ME KIKA MANTA BABU AIKI KOMAI? KAI SHIFA DUK IN DA KIKA TABA KUDI NE,ACCOUNT KAWAI ZAKI BUDE DASU. BABU SISINKI BARE KISHA WAHALA,ME KIKA MANTA KULLUN KIN SAMU KIDINKI A ACCOUNT. TO MAZA GARZAYO DAN SAMUN NAKI RABON.GA MAI SO ZAI IYA TUNTUBAR* 07033636337 21 Jinjina kai Annie keyi cike da alhini sai kuma ta tab'a hannuwa tare da cewa"gaskiya kinzo da babban al-akari duk da abun duka na gida ne kowa naka ne,kuma kowa zaiso jin hakan wannan gyaruwar al-amarin amma ,kuma ai an zama daya komai kika yanke bazance a'a ba in dai ni yar halasce wacce bata manta alkhairi to amma kamar yarda kika ce bari yanzu in da Laminu yamun kiran Ahmadun dan shi Sadiqu ba'a ma ta tashi shima cewa zaiyi a tuntubi amadun".waya Annie ta lalubo tace "bari a sanar da muta gidan zuwanki in kuma kira shin dan ba'a barki da girmanki kina jiran shi ba". Murmushi Hajja tayi cike da jin dadin duk da tayi tsammanin kin amincewar Annie duba da yarda al-amuran ke kasancewa amma kuma sai taga sam ba hakan bane ita a nata b'angaren bata wani ba....Bakinta dauke da sallama ta shiga parlon duk suna zaune Hydar ne yace" a'a Hajiyar masu gida da kanta,tuba muke yau ke da kanki kika fito"Aunty Amarya na dariya ta karaso gaban Annie tana gaisheta with Respect tana sunkuyar da kai tace"Annie akwai wani abunda kike buk'ata ne?"ansa gaisuwar tayi sai kuma tace"dukanku Baku san Hajiya Aisha tazo bane da babu Wanda yaje ya gaisheta?".sunkuyar da kai Aunty Amarya ta kuma yi tace"a hafarcemu Annie dama ina so na karasa girki ne sannan kun gama gaisawa sai mu shigo,amma tun dazu Jabeer ya sanar mana da shigowarta,to ina so a taho mata da abincin ne"....kyab'e baki Annie tayi tace"itafa Badiyar?".kallon sashen Momy Badiyyan Aunty Amarya tayi sai kuma tace"tana ciki".wuceta Annie tayi ta mikawa Faruq wayarta tace"latso man ubanka".Dariya Faruk din ya kunshe cikin son tunzura Annie yace "uwayen nawa ai da yawa to wanne daga ciki?". Sake baki Annie tayi sai kuma tace" to da wancan narkekiyar matar kake,nace ka kira man Amadu kana mun marshin kunya".kafin yayi magana ya tsinkayo hararar da Momy Badiyya ke xabga masa ba arziki yaja bakinsa yayi shiru ya soma laluben wayar Abba yana dauka ya mika mata,ansa sallamarsa tayi kafin tace"karfe nawa zaka dawo?".cike da girmamawa yace"da yamma ne Annie"...."to yau dai ba batun yamma in ka dan samu sarari karka taushe hannu ina nemanka,maganar bata waya bace gaskiya"....Annie ta fada...Dan Jim Abba yayi sai kuma yace "wani abun ya faru ne Hajiya?"..." Babu komai sai alkhairi kaidai kawai kazo"..da to ya ansa sannan ya kashe wayar...k'asa Momy Badiyya ta duka tana gaishe da Annie tsuke fuska tayi kadaran kadahan ta ansa gaisuwar kafin tace"so nake naji Badiyya meya hanaki shigowa gaishe da Hajja?",..wani abu Momyn ta hadiye da kyar kafin tace"ban samu labarin zuwanta bane da wuri sai yanzu Ahmad karami ke fadamun.".."duka dai ya rage naku,mai son zaman lafiya dai yazo ya gaishe da matar nan salin alin cikin mutunci kamar in da suke mutuntamu danni bazan kwashi rashin zaman lafiya da zumunci mai kyau ba tun da duk an zama daya"..."kiyi hakuri Annie zamu shigo yanzu"...bata kuma bi ta Kansu ba tayi waje abunta tana gyara rikon wayarta...A parlon ta samu Umma da warmer's guda biyu ta kawowa Hajjan suna gaisawa dan harta zuba mata farfesun catfish a bowl da karamin spoon ta bata ,ita kuma tana zaune wurin kafarta...."sannu da kokari yar albarka,Wato dai kinsa ta riga fara cin abincin sashenki".Murmushi kawai Umma tayi tana gaishe da Annie tace"ai nasan Hajja da son kifi ne kamar Jabeer shine Layan na fadamun na daura mata kuma tadanji dadin bakinta"..."sosai kuwa yar albarka Allah ya wadata naku yaran ya masu albarka ya basu ikon yi maku,kamar yarda kuke dawainiya da mu,na gode sosai Allah ya jibanci lamuranki".da Ameen duk suka ansa sannan suka ansa sallamar Momy Badiyya dake shigowa fuska a dan daure,nesa da Umma ta zauna kafin tace"Hajja barka da zuwa,mun sameku lafiya,ya karfin jiki kuma?"."lafiya alhmdllh,ya naku gidan da iyalin"...alhmdllh kawai Momyn ta fada sai kuma ta mike tace"to a gaida gida Hajiya zan fita ne nace bari nazo mu gaisa"...godiya sosai Hajja ta mata sannan ta fita,ba Jimawa ma Aunty Amarya ta turo da Warmer's na abincin Hajjan sannan itama tazo daga baya suka gaisa...slowly yake tafiyan kamar baya son taka k'asa ya tura main Door ta babban parlon ya shiga bakinsa dauke da sallama.in ba ka saurara ba ba zakaji me ya fada bama.looking everywhere amma parlon so silent babu abunda ke magana sai babban plasma TV dake ajiye a tvstand sai karan AC kuma zama yayi a daya daga Sofa's na parlon yana shafa cikinsa sai kuma a hankali yace"Ummana we're are you".to two minutes ya tashi heading to the dining table area kawai tsaye ya wuce kitchen zai dauka ruwa marar sanyi.A nutse kuma hankali kwance duk wannan shirmen babu shi take soya favorite Noodles dinta cikin kwan data hada a gas Allah Allah takeyi ta karasa ta wuce wurin Hajja dan har ranta da zuciyarta take jin soyayyar matar,kashe gas din tayi ta dauko plate da fork ta soma juyewa..at all bataji shigiwarsa bama,duk da yaji zafin ganinta shima amma ko kallon in da take bai kuskura ya sakeyi ba dan sai da ya shigo gaba daya sannan ya lura tana kitchen din.ruwan ya dauka ya juyo zai fita Yaga ta kuresa da dara-daran fararen manyan idanuwanta masu daukar ido da hankali,bece komai ba duk yarda zuciyarsa ke azalzalarsa akan ya mammareta ya wuce amma the other side yana tuna gargadin Ammi bayan ya ajiye ta office data ce masa yarta na gida idan ta dawo ya tab'a lafiyarta kuma zaiga the other side of her..."yaya aida sai kace na kawo maka ruwan,Umma na wurin Annie bari na kawo maka abincin tayi saving naka a warmer,ta karashe maganar tana ajiye fork din hannunta.wani abu mai daci daya tsaya masa a makoshi ya hadiye da kyar,yana jin bak'ar kiyayyar da wutar zuciyarsa ke rura masa from no where, can cikin makoshi yace"wallahi monster if u there make that mistake na zuwa dining can you will regret in all your life time,idiot mayya ".bottle watan daya dauka kawai ya juya ya jefa mata shi a k'afa ya fice da sauri dan zuciyarsa fada masa kawai takeyi ya karkaryata ko yaji saukin kiyayyar da yake mata a zuciya.sosai yake regretting na shigowa part dinma gaba daya,baisan dalili ba bai kuma daga ina ba amma tabbas yasan dai ya tsani yarinyar fiye da duk wani abu da yake ki a doron duniya,idan ya ganta ji yakeyi kamar his life come to and end.gaba daya ji yayi gidan ma ya masa zafi baiji sassauci ba sai da yabar gidan kafin ya samu peace of mind....karamar kara Layan ta saki ta durkusa tana shafa kafarta in da ya jefeta saboda zafin daya ratsata sai kuma kawai ta saki murmushi ta mike ta dauki noodles dinta da drink ta wuce dining din tana tura baki dan tasan ko da wasa ba kuma zai kara zaman part din ba tunda yasan tana ciki.... Share fisabilillah *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 22 Babu dadewa Abba ya shigo gidan,part din Annie ya nufa direct be tsaya kiran kowa ko jin me yake faruwa ba a gidan,tunda ya kira Aunty Amarya kuma ta fada masa Hajja ne kawai taso amma gidan lafiya qlau.to ya yarda kuma ya amince akan Jabeer ne ko kuma makamancin hakan shiyasa bai bata lokaci ba cikin ladabi da mutuntawa ya zauna a kasa ya gaishe da Hajja tare da Annie da suke zaune a wurin.kafin ace komai Annie ta dubi Muhibba da Basma tace"to Ku tashi zamuyi magana.kafin kuma na fara jin ana tanbele da gararamba da abunda aka saurara a duniya, bare wancan da jira takeyi"Ganin Abba a wurin babu Wanda yace komai a cikinsu kai tsaye suka bar wurin....nisawa Hajja tayi kafin tace"Alfarma nazo nema,nasan bani da iko ko damar tursasawa amma nazo ne da kokon barata da kuma tunanin hakan shine mafita wacce ko bayan ranmu zamu kwanta cikin salama da kwanciyar hankali,ina fatan zan samu wannan abun da nazo nema,sanin kanka ne Ahmad Jabeer da Maryam basa shiri kuma ni da kai da duk Wanda ke rayuwa dasu bashi da kwakwaran hujja ko makamar dazai fada wacce ta zama sanadiyyar faruwar kiyayyar nan,duk da hali irin na Jabeer yaci ace sunfi kowa shakuwa da Maryam amma hakan bata faru ba,ko Baku fada ba Ku iyayene kuma ba zaku taba jin dadin irin yarda suke rayuwa ba,wannan ne Dalilina na son nemawa Jabeer auren Maryam idan har hakan bazai zama da cutarwa a gareku ba,insha Allah kuma wata rana zakuyi alfahari da hada wannan auren".jinjina kai Abba yayi without second though yace"Hajja kinfi karfin komai a gidan nan,muma kasanki muke zaki iya yanke hukunci a kanmu kuma ta zauna ,da mu da abunda muka mallaka duka zaku iya yin hukunci dashi Hajja,duk abunda kuka yanke mu masu biyayya ne"...sosai Hajja taji dadin maganganun Abban cikin dauki da tsananin jin dadi tace"Allah yayi maku albarka baki daya,Allah ya cika maku burikanku na alkhairi baki d'aya"Annie na washe baki kamar sabuwar Amarya tace"Ameen ameen ya rabb,to amma kuna gani wannan yaro yasan maganar xai yarda kuwa?".sanyayyar ajiyar zuciya Hajja ta sauke tace"bana so cikin yaran nan ko daya su san da batun Hajiya Maryama a bari har sai an daura auren sannan a masu duk bayanin daya dace,a lokacin su san muke iko dasu,dan kinsan idan anbi ta nasu ba zamu taba samun abunda muke so ba"..."Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ya tabbatar mana da dukkan haske da gyaruwar ko wacce b'araka insha Allah da anjima san hada iyayen nasu na masu bayani yarda duk kika fada Hajja".cike da farin ciki da jin dadi Abba yabar parlon Annie dan sosai har ransa ya gamsu da shawarar Hajja Wanda be taba kawowa ransa tunanin hakan ba......."sannu Mrs Jabeer karewar soyayya,iska dai tana wahal da me kayan kara banga alamar nasara ba bare kuma za'a tsira,dan Allah ki sawa ranki salama dan Allah"Muhibba ta fada tana gyara zamanta akan makeken gadon Layan din dake part din Ammi.kyab'e baki Layan tana hararar Muhibba tace "idan har ba zaki yi mun fatan alkhairi ba,to kara kiyi shiru dan banga alamar nisan tafiyar da nayi hargaginki ko surutunki zasu dawo dani baya ba,komai lokaci ne kuma zaki fada da bakinki,Yaya Jabeer mallakina ne kuma zai soni is just a matter of time just wait and see"..... Dariya sosai Basma tayi tace" to Allah ya tabbatar da alkhairi sarkin soyayya ni dai na kagara a daura auren nan in dai rabonki ne ko ma huta da daure fuska a gidan nan" .......sanye take da material dinkin bubu mai dan fadi ta kashe dauri a gaban goshi,sosai fuskarta tasha make-up sai fitar da sihirtaccen kamshi takeyi ga chewing gum tana taunawa k'as k'as daga ita sai kawarta Humaira wacce kusan shigarsu iri daya ne itama siririyarce kamarIhsan.Humaira itace kawa daya tal ga Ihsan ,parking motar tayi a cikin babban parking lot na gidan kafin ta kwashi hand bag dinta da wani siririn mayafi data sako a motar dan gaishe da sirikan nata.kayan jikinta ta kuma kallah ta saki siririn tsaki tace"Wallahi sam gaba daya rigar nan ta takura mun dan dai ance harda kakarsa zan gaida da me zai sakani wannan shigar kamar a wani kauye".Dariya Humaira tayi tace"to tunda kina son Lamin kam ai biyayya ta zama dole,tun da kakar ai itace komai a gidan...."bari duk zanyi maganinsu da wannan Dan uwan nasa da bashi da magana sai tashi,ni gani ma nakeyi an danka komai a hannunsa ne an barmun Lamin din a baya,bayan shi bama gidan ubansa bane,wallahi duk zan zama daidai dasu".wani irin takaici ne ya kuma kamata kafin ta karasa fadan abunda zata fada ta turawa Lamin da Layan idanuwa Wanda suke fitowa daga part din Umma.murmushi sosai kwance a fuskar Lamin yana kuma dungure kan Layan dake sanye da long blue black hijab har kasa da littafai a hannunta da alama masallaci zata shiga ta bada karatu...bata kuma wani tunani ba ta balle murfin motar ta fito tana kuma daure fuska da kare masu kallo....kai tsaye wurin motar shima ya nufa Layan din na binsa a baya tana korafi akan bai fada mata zuwan Ihsan din ba,da fara'a fuskarta ta karaso ta kama Hannun Ihsan tace"sannu Aunty you're highly welcome, duk da Yayan nawa bai sanar mana da zuwan ki ba,ko kuma mu ya kawo mu".Kadaran kadahan Ihsan ta kirkiro murmushi bata dai ce komai ba sai ta kuma juya kallonta ga Lamin tace"Honey kace mun baka gida kuma,kasan naso kazo ka taho da ni "...." Yanzu ma shigo nima na dauka ma har kinzo kin tafi ai,anyway ki karasa ciki wurin su Momyn".Layan dai bata yarda ta bita part din su Momy ba "au ba zaka rakani ba Baby" ta kare maganar a shagwabe.kallonta yayi sai kuma ya dauke kai tare da cewa"zanje na duba Annie ne,zan shigo"be jira cewarta ba ya kama Hannun layan sukayi part din Annie,da kallo kawai take binsu tana kisisima abubuwa da dama a kanta....kusan cin karo sukayi da Jabeer dake shirin fitowa fuskarsa a hade kamar ko yaushe, kallon Hannun Lamin yayi dake rike dana Layan sai dai bece komai ba ya rabasu xai wuce,janyo shi Lamin yayi yace"c'mon,ni zaka fara ignoring Mr man?"....Dan waro manyan idanuwamsa yayi sai kuma yace"ni ban ganka ba".murmushi Lamin yayi tare da cewa "oh I see,ina Hajjan ko harta koma nabi da rabon addu'a a yau?"...." Abba ya saka Hydar ya mayar da ita".be kuma tsayawa ba yaja hannunsa ya wuce da sauri,yana jin wani takaici na taso masa na kallon da wancan Monster din take binsa dashi dan idan ya tsaya xai iya illatata da shegen dukan da kowa xaiyi nadama...itakam Layan da manya manyan idanuwanta Wanda suke nan farare tas ta tsura masa su ko kiftawa batayi harya wucewa ganinta,Hannun Lamin yayi tapping a face dinta yace"Yaya dai? Wannan kallon fa Lil sis?".Murmushin ta saki tace"babu kai Yaya,naso na gaishesa ne amma nasan as always ba ansawa xaiyi ba"...."you not worry about him,I assure you one day one time Jabeer xai maki dariya zai soki xai kuma kiraki lil sis insha Allah,ki tsaya ki gani".....wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta from no where tunda take babu Wanda ya taba bata kwarin gwaiwa akan Jabeer ji tayi aduk duniya tana kuma kara jin girma da son Yayanta Lamin shine daya dake fahimtarta a ko wanne hali ,duk taje ta dawo kuma xaiyi backing dinta,cikin sanyin murya tace"thank u so much Yaya".Murmushi ya mata yaja hannunta suka wuce wurin Annien kawai. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 23 Gyaran murya Abba yayi yace"kamar yadda na taraku ba wani abu bane illah ina son sanar da Ku insha Allah in 2weeks time za'a daura auren Jabeer tare dana Dan uwansa Lamin Wanda duka kunsan da shi"....."y'allabai wanne Jabeer din dai? A tunanina Lamin kawai za'a aurar a gidan nan,Jabeer bai gabatar da wacce yake so ba,to kuma kace zaka hada"Momy Badiyya ta fada.kallonta Abba yayi sai kuma yayi murmushi yace"ni na zab'a masa,ba yanke shawarar aurar da Mamana ga Jabeer".....Aunty Amarya tace"Layan dai Yallabai?".jinjina mata kai yayi yace"ita ma fada kuma na zaba masa,ina fatan kuma hakan bazai janyo komai ba sai gyaruwar duk wani abu da muke tunaninsa ba dai dai ba".......Duk maganganun da akeyi Annie tana kallonsu ne kawai bata ce komai ba,Umma ma da Ammi ba Wanda ya tanka Momy Badiyya ta saki wani Murmushi can tace"lallai wannan gaggarumin abu ne,ina Jabeer ina Layan? Layan ina taga lafiyan zama da Jabeer ,sanin kanka ne kuma ba jituwa tsakaninsu ,kara dai a duba maganar nan,Jabeer ba abunda zaiyi sai illata yarinyar can,ita kuma gata duk cuta sauran ciwo,a barta tayi karatunta shima kuma naga bai sanya niyar aure ba,bare kuma ace za'a masa dole".Sosai Ammi ta shaka haushi duk ya cikata bawai kuma dan Momy ta saka Jabeer ba kawai irin yarda ta muzanta Layan ne bai mata ba,kasa daurewa tayi tace"Halan ita mai cuta ba'a aurenta? Beside ma ki fada mun wanne irin cutar ne kuma kika Santa da shi? Insha Allah kuma haka za'ayi auren su zauna da juna cikin kwanciyar hankali dan banga alamun in da wata damuwar zata bullo ba"....."to ke bakiga dama Dan naki kamar kin gaji dashi bane? Aini Murna ma ya kamata na maki da yanzu Cikin nawa yaran za'a jajibawa dan naga kamar neman kai ake da ita"Momy ta fad'a.....wani kallo Annie tabi Momy Badiyya da shi sai kuma tayi dariya irin ta basawa tace"hmmmm wallahi wallahi Badiyya ke ko ba y'ar arziki bace,ban taba ganin marar mutuncin tukekiyar mata irinki ba,ace bakinki baya haila baki da katsari ko kadan? To ke duk yarda Ahmadun ya dauko ki a gantale bamuji kyama ko nuna bakin ciki ba muka rikeki muka maida ke mutun har kin zama haka ki had'a komai ba gida?to ki sani har gobe zaman Sadeequ kikeyi a gidan nan da darajar y'ay'anki idan kin manta ni bari in tuna maki,Jinin Sadeequ kam yafi gaban ki wallakanta shi,in banda Jabeer din akayi niyar aura mata bana so Hajja ta dauke ni mutuniyar banza da tuni yau a Pamilyn nan an shaida auran Lamin da Layan,to mu ba mutanan banza bane,ahir dinki nasan duk me kike kullawa idan kuma kin musa kici gaba kiga idan Lamin ya auri wannan higaggiyar aljanar yarinyar da kuka lika masa"....Tunda Annie ta fara tijararta Momy tayi kasa da kanta shab ta manta Annie ba wurin tsabar kishin ance za'a hada auren tare dana Lamin ne yasa ta tanka amma batayi tunanin wannan tereren daga Annie ba....maganar Annie ta dawo da ita hayyacinta tana fadin"Aure insha Allah babu fashi za'a daura,kuma kada naji ko na gani na wani ya fadawa yaran nan,muna da hikimarku na boye ,duk kuwa Wanda naji maganan ta bangarensa to ni da kaina zanyi hukunci kuma Wanda ba zaiwa kowa dadi ba,musassan ke Badiyya da bakinki ya iya yin abunda ba'a umurce shi ba,to tun wuri ki kiyaye ni".ta kare maganar tana nuna Mommy.k'asa tayi da kanta tace"insha Allahu Annie za'a kiyaye"a haka taron ya tashi kowa da abunda ke ransa.Umma kam kanzil bata ce ba har akayi aka gama kamar bata a parlon,da aka sallami kowa kuma tabi hayan Ammi suka wuce....."ina gaya maki rashin mutuncin da take mun a gidan nan kenan,bana da ikon fadan ra'ayina ko wani abu sai ta fara mun terere kamar wata karamar yarinyar"Momy ta fada tana sauraran wayarta.Dariya Hajiya Sha'awa tayi tace"ni ai bani ganin laifin kowa a gidan nan Badiyya sai ke, kuma tsakani da Allah ya kamata ki mike tsaye,bazai yiwu na bada y'ata a gidan da sirikarta ta kasa mallakar kowa ba,kin san dai wacece Ihsan bata son ganin wani a samanta,ni ai k'arama da aka sanya auren nan,tunda tun dawowarta na lura yarinyar nan bata sonta kinsan dai mutuniyar"....nisawa Momy tayi tace"kinsan nima duk wani abu daya shafi Fatima ba san shi nake yi ba,amma na godewa Allah tunda ba yarana aka likawa ba,dan shine abunda na zan taba yarda ba kam duk me zai faru"...."ki daina wannan maganar Hajiya Badiyya,ki cire kudi ki cire tsoro ki biyawa kanki bukata,wallahi wallahi kinji na fada maki idan kikaje wurin nan ba Ahmad ba har Ita Annien take ko wa sai yarda kikayi da ita ni ba gani da nawa mutumin ba tuni nayi maganin komai,ni bazan iya jurar duk wannan CeCe kucen da kike iya dauka ba"Hajiya Sha'awa ta fada.nisawa Momy tayi tace"to nifa ba tsoro nake ba,kawai dai kinsan yanayin komai kakeyi kana tuna mutuwa da tsoron Allah dai,amma komai zai zama tarihi duk zanyi maganinsu daya bayan daya".A haka dai suka kare wayar kowa da abunda yake sakawa....tab'e baki Ihsan tayi wacce ke sauraren conservation din Mom dinta da Momy tace"hala wannan Dan jin kan sojan za'awa aure?"..."eh shine za'a aurawa yarinyar da kika zo kina complain a kai.na rasa irin son da sukewa wannan yaron"....tuno kyakyawar fuskar da Jabeer Ihsan tayi yasa kyakyawan murmushi subucewa a fuskarta tace"mom amma fa ya hadu,I loved him so badly, kawai ya daina kulani a Paris shiyasanya na hakura na koma akan Lamin amma Jabeer is my first love mom"...kyab'e baki Mom tayi tace"yau naga shirme wannan kyau ba hali ina amfaninsa,ai kara maki Lamin din,amma wannan Dan iskan yaron da ko gaisuwa bayajin zai iyawa mutun sai uwarsa da fatyn to ina amfaninsa,ni bama zan iya hada zuri'a da maryam ba sam bata mun ba"...Dafa Mom Ihsan tayi tace"kedai mom kawai dai na kama girmana na hakura da Jabeer ne,amma har gobe ina jin san sa a raina ,beside ma wannan y'ar kauyen yarinyar bata dace da Jabeer ba sam,ba girmansa bane sun gama zubar dashi ace duk class irin na Jabeer ya kare a wannan bak'ar yarinyar no beyi ba"Ihsan ta kare fada tana hade fuska kamar wacce akawa wani abun kuma...kallon tsab Mom ta mata sai kuma tace"to babu dai ruwanki,na kuma rabasa da ke kinsan kuma akai maganar Dan uwansa a kanki karna kara jin kin ambace sa,babu abunda Jabeer yafi Lamin sai bakin hali,kinji ma na fada"..tana kaiwa nan ta fice tabar mata d'akin ma gaba daya....Murmushi kawai Ihsan tayi tare da kwanciya ta rungume pillow tana tunano kyakyawar fuskar Jabeer kamar ta sace shi ta gudu. .....Daudauke duk wani clothes da Layan ta zubar a k'asa Ammi keyi fuskarta a daure tana jiran fitowar Layan daga bathroom gaba daya ta mayar da room din out of order kamar wata baby.tana ta tsaye Layan ta fito daure da Babban pink towel dinta daya sauka har gwaiwanta kanta sanye da hulan wanka,kallon d'akin tayi sai kuma ta ware manya-manyan idanuwanta tayi murmushi tace"Ammi I'm sorry dama yanzu zan tattara"....wani kallo Ammi ta mata taci gaba da abunda takeyi sai bayan ta gyara komai tace"kici gaba da acting like a baby gal kinji,zanyi maganinki ne"bata jira cewarta ba ta bar mata d'akin...Murmushi Layan tayi kafin ta wuce ta shirya ,tana duba kaya a so be careful gudun kada ta kuma batan d'akin Ammi tayi maganinta... *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 24 Rigace mai irin mai fadin nan ta material ash colour sai ta daura black veil a sakalken gashinta silent performs kamshinsu d suka gama bin jikinta ke tashi ,parlon ta fito tana tura dan karamin bakinta ta tsaya a bayan Ammi dake zaune a sofa da littatafai a gabanta tana dubawa,eyeglasses dinta ta cire ta dago tace"to tsayuwar me kike mun a kai kuma?"kuma tura baki tayi bata ce komai ba...shigowar Jabeer da Lamin yasa ta saki fuskarta ta kuma kura masu kyawawan fararen idanuwanta tana murmushi ,Lamin ne ya kalleta sai kuma shima ya saki murmushin yace"y'ar Ammi lafiya dai ko?"..Ammi ce tace"barni da yarinyar nan Lamin,nema takeyi yau nayi maganinta,tamun tsaye a kai kamar wata sabuwar kamu".Dariya sosai Lamin yayi yace"haba Ammi kema kin fada ne,wake shiga tsakaninku da Auta? Mudai namu kallo ne"ya fada yana tabo Jabeer daya zauna kasa kusa da Ammi yana latsa waya ko sanin abunda sukeyi ma beyi ba.kallon Lamin yayi sai kuma ya mayar da kallon ga Ammi yace"Good morning".."ka tashi lafiya ya hutun"Ammi ta bashi amsa, da Alhmdllh ya ansa ya kuma dukar da kansa yaci gaba da latsa wayan shi..."kije ki kawo masu breakfast"Ammi ta fada...Da sauri Jabeer ya dago yana kallon Ammi amma bece komai ba ya kuma dukar da kansa yana daure fuska ga wani abu daya masa tsaye a zuciya.kunshe Dariya Lamin yayi yana dukar da kai dan yasan irin yunwar da Jabeer ya shigo da ita,bedaice komai ba ya juya yana kallon Layan dake shirya table bayan ta karasa cikin sanyin murya tace"Ammi me za'ayi saving".kallonsu tayi ta mike tana tattare books dinta wuri daya ba tare data kallesu ba tace"to the dinning area"bata jira cewarsu ba ta mike ta wuce dining din,Lamin ya fara mikewa ganin Jabeer beda jiya yasa ya soma jansa da karfi,wani harara ya jefa masa yace"Malan meye haka kuma".."c'mon bansan fulako ka tashi muje ka kwashi girkin Lil sis ,ko ka kwantar da wannan mahaukaciyar yunwar da kake yawo da ita,ance mutun yayi aure amma ya gagara to a kare acin na kanne"...kyab'e baki Jabeer yayi amma bece komai ba ya dago kai ganin Ammi na kallonsu yasa ya mike suka karasa dining din ,yaja kujera ya zauna..Layan kam ta fara saving Ammi kafin ta karasa kan Lamin ,saurin mikewa Jabeer yayi ya dauki Cup da sosage din shi da tea spoon ya karasa a sink ya fara wanke su ya dawo ya zauna zaiyi making coffee, sake komawa yayi ya kuma wanke cup din sannan ya zuba coffee powder kallonsa Ammi tayi tace"har raina Jabeer ina tausayin matar da zata aureka,su cups din me sukayi? Wannan hali dai ba zaka barsa ba".shidai bece komai ba ya soma juya coffee shi Wanda bema tunanin zai iya saka shi a ciki saboda tsayuwarta a wurin...cikin sanyin murya a hankali tana tsoran kada yace ta masa ihu tace"Yaya me za'a zuba maka?".ko kallonta beyi ba bare tasa ran zai amsa tana ta tsaye a kusa dashi rike da plate.....kurba ruwan tea Ammi tayi tace"ina ga da kurma ake magana a wurin nan ko Jabeer"...marairaice fuska yayi ya bude baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru,can dai yace"Ammi I'm not hungry "...Bata kulasa ba taci gaba da cin Abincin tace"Layan ajiye plate din ki zauna kiyi karinki shiya sani". Daure fuska tayi sosai ta dube shi in a serious note tace"kada na kara ganinka kazo nan cin abinci in ba haka ba zaka ga me zanyi".. Da kallo yabi Ammin data tashi tabar dining din.phone's dinsa ya dauka yabar dining din shima ....Hannu Lamin yasa ya dago fuskar Layan data dukar da kanta bata san dalilin da yasa hawaye ya soma bin fuskarta ba yana tsere a fuskarta,B'ata fuska yayi yace" lil kuka? Yau kika san Jabeer din ko meye?",Girgiza kanta kawai tayi tasa hannu ta share fuskarta ta ajiye spoon din hannunta tace"a'a Yaya kawai na koshi ne".Shima ajiye spoon din yayi yace"OK fine you can go"...kamar zata mike sai kuma ta kallesa tace"to ba zaka ci Abincin ba Yaya"...."na koshi"ya bata ansa ya soma tattara wayoyinsa cikin sanyin murya tace"to kayi hakuri ka zauna sai muci".Girgiza kai yayi yace"no na koshi ina sauri akwai wani case da nakeyi ne".raurau tayi da ido ta turo baki.Murmushi yayi ya zauna yace"let eat"suna cin abincin yana kwantar mata da hankali duk da ba wani ci takeyi ba dan gaba daya kuma yanzu damuwa ta gama kanainaye zuciyarta batajin dadin ganin Yaya Jabeer a haka,gaba daya sai ta rasa sukuni taji kamar taita yin kuka ga zuciyarta ta dinga mata zafi kenan,a kullun kuma kamar kara mata tsananin son shi akeyi ta rasa ta ina zata fara ma...kamar saukar aradu haka taji tambayar Lamin a kwalwar kanta duk da ba yau ta soma jin irin tambayoyin ba amma bata taba tsammanin ya gama fuskantarta ba cikin rawar murya tace"a'a Yaya"...Da manya manyan idanuwansa ya kalleta da kyau yace"karya kikeyi Maryama,idanuwanki basa iya boye gaskiyar abunda ke zuciyarki,kowa ya kalleki zai iya fuskanta kina son Jabeer just accept the fact"...wani hawayen ne ya kuma zubo mata amma bata ce komai ba...kafin yaci gaba da cewa"kiyi addu'a in alkhairi ne Allah ya shige maki gaba ya mallaka maki shi,,,nima fa na taba yin irin haka,ko ince ina ciki ma".saurin Dago kanta tayi tace"you mean"..."ina son wata sosai kamar raina,har gobe ina jin idan na rasa ta ko wani abu na cutarwa ya sameta zan iya rasa raina a kanta ,bana jin kuma zan iya daina sonta har karshen rayuwata lil"...waro ido tayi da alamun tashin hankali tace"to yaya ka aureta mana,tana ina kuma".murmushi yayi mai ciwo yace"is too late lil,ita ai bata sona akwai Wanda take so,kuma nima kinga aure zanyi"...tura Dan karamin bakinta tayi tace"ai ana auren mata fiye da biyu,kuma banga Wanda zaice baya Sonka ba".Dariya yayi yaja kumatunta yace"to ni dai kinji kiyi addu'a kawai ni zan fita" harya fara tafiya tace"to Yaya baka fada mun wacece ba"...waro ido yayi yace"ba amfanin sanin haka gaskiyar dai itace ina sonta kuma zanci gaba da sonta har karshen rayuwa Lil".be jira cewarta ba ya fita daga dining din....da kallo tabi bayansa harya fita a parlon.ji kawai tayi tausayinsa ya kamata gaba daya abincin ya kuma fice mata a kai ta tashi ta tattare wurin ta wuce dakinta dan bata son ma fita yau din nan bata son yin magana ...Dafe kirji Annie tayi tare da furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"tayi tsaye a kofar bedroom room din tana mayar da numfashi sai kuma ta karasa kwashe labulen ta shiga taba kabbara tace"wallahi wallahi maryam ta haifo mana jaraba a gidan nan,anya Jabiru kana tsoron Allah kuwa,har yanzu ba zaka daina sata ba?"sai kuma ta fashe da kuka tana bin kwanon furarta da tasha fresh nono ta dame abunta da daddare ga kular farfesun yan cikinta Jabeer yaci yayi nak kadan ya rage furan yana ta shan farfesun abunsa..."ka sani ba yafe maka zanyi ba,hakkina kadai sai ya hanaka kwanciyar kabari,yau sai ka bar gidan nan ,ka koma can wurin dangin ubanka,yanzu in yi magana ace nayi maka sharri,amma kuma mugun halinka yafi karfinka Jabiru"tana kuka tana goge fuskarta da habar zani....Jabeer kam bece komai ba ya ajiye sauran farfesun ya goge bakinsa da tissue ya mike ya kwashi phones dinsa yace"tunda a kanki nake zaune ai sai ki Kore ni ko",...Duka Annie ta kai masa a baya tace"da uwarka Maryam kake badai ni ba,mutumin banza labcecen kawai ai kara ma a maka auren kabar gidan,ko sadaka sai an bayar da kai".Dafe bayansa yayi in da ta masa dukan yayi murmushi yace"to kin daki kazarki Allah"...gwalo ido tayi tace "a'a ai bansan zaka siyomun kazar ba,to yi hakuri, karasa cinyewa maza ,zauna bari ma na kawo maka Fankasu dana toya dazu da miyar kai"... Bata jira cewarsa ba tayi waje...murmushi mai kyau ya subucewa Jabeer Wanda ba kasafai ake ganin Yana yi ba,tuni yaji duk wani damuwarsa ta yaye yana matukar jin yarda yake son Annie a ransa ga kwadayi ga rigima *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 25 Gaba daya b'angarorin biyu shirin biki sukeyi,kyab'e baki Layan keyi kamar wacce zata fasa kuka tace"Dan Allah Aunty Amarya nikan na koshi da abunnan,babu dadi banma san menene ba"Harara Aunty Amarya ta watsa mata tace"ina guba nake baki,kin dauka kin shanye ko sai nayi maganinki a nan".Murmushi Layan ta saki tare da saka dogayen zara-zaran yatsun hannunta da suka sha ado da jan lalle duk yatsa ta rufe bakinta tace"Allah ya baki hakuri Auntyn mu,nikan wasa nake"..."ke kinma samu tana baki,nikan nama kasa gane kan gidan nan kwana biyu gaba daya,ina dalili mu ba'a tamu ko ina ke ko ina ke"Basma ta fada tana kyab'e baki Muhibba kam jinjina kai tayi tace"to ina dalili ki kwallafawa ranki shan abu ba dadi Basma?"..pillow Aunty Amarya ta dauka ta jefa masu tare da cewa"find your way guys"sun san Aunty Amarya ba wasa har Riga rigan fitan sukeyi suna kunshe dariyar da sukewa Layan daketa mammate ido.....kayane baje kama daga less,atamfa jadda all women's wear daya kama a saka a boxes na lefe jibge a tsakiyar parlon Mommy tana hakimce a babbar tausashiyar sofa dinta waya a hannunta tana lissafa kayan ita da kanwarta Hajiya Sadiya da tazo daga Kaduna dan hada lefen,yanzu duka duka auren be wuce 2weeks ba shissa komai take yinsa akan lokaci,so takeyi ayi auren da ba'a taba yinsa ba,wani Less Hajiya sadiya ta daga tace"nikan in an biye ta nawa boxes din sunyi yawa kayanma gasu a jibge sai kace za'a kaiwa yar Governor, a'a gaskiya sai kace a bola Lamin din yake ebo kudin Yaya? Ke ba zaki tsawata masa ba". Lamin dake zaune gefe murmushi kawai yayi dan duk abun nan da akeyi shidai Mummy sai dai tace ya tura kudi kawai,amma be taba kin turawan ba,shine ta hada da nata ta jibga uban kayan nan,shi kallon abun kawai ma yakeyi duk kamar a mafarki...tsuke fuska Mummy tayi tace"ni dai gaskiya Halima mitarki ta ishe ni haka,kedai kiyi abunda ke gabanki ko in nemi kawayena su shirya mun,sai kace kin mance wacece Hajiya Sha'awa? Ko ita Ihsan din ke baki sani ba,su dai ba kananun mutane bane bare a masu karanta meye marabar Ihsan da yar Governor? Wallahi biki zamuyi na kece raini,duk hadawan da za'ayi so nake a banbance a karara babu yaron da zaiyi auren gata sama da Lamin"...ita dai Aunty Sadiya bata kuma cewa komai ba dan ita tun farko Hajiya Sha'awa ba mutuniyarta bace bare kuma wata Ihsan dan dai tasan Yayar tata ba mai fada mata taji ne tun bayan rasuwan iyayensu,ita wani abunma har mamaki yake bata,meye wani Ihsan Allah na tuba...wayarsa ce keta ringing ba kakkautawa tun dazu yake silenting wayan dan shi a tunanin shi wani abun Annie ta cewa Ummi yayi,ganin ba sarki sai Allah yasa ya daga wayar ya kara a kunne bakinsa dauke da sallama yace"Ummi"...."Halan Jabeer ka makance baka ganin missed call's ne?,bana son sakarcin nan naka,tun dazu nake kiranka amma baka dauka ba kuma baka biyo ba"...kasa yayi da murya sai kuma yace"kiyi hakuri ina office ne,wani abun ya faru ?"...."yaushe zaka shigo bikin Lamin din"Ummi ta tambaya ,shiru yayi sai kuma yace nan da one week insha Allah Ummi"...shiru Ummi tayi sai kuma tace idan ka tashi tahowa ka dauki hutun saki ko ukku ne a gaba akwai tafiyan da nike so muyi".Waro manya manyan idanuwansa yayi dake cike da gajiya yace"Ummi ina da aiki after bikin da da 2days fa"..."to kawai kace mun ba zakaje ba yafi mun sauki,aikin har yafi zumuncin Allah Jabeer wannan ya zama dole ne"...shiru yayi sai kuma yace"to sai na shigo insha Allah,ina aiki sai anjima "be jira cewarta ba ya kashe wayar yana tunanin ina kuma zasu ko mai zasuje yi,haka nan dai ya ajiye tunanin gefe yaci gaba da aikinsa kawai .....Agogon parlon nashi ya kallah yana zaune a reading table sai kuma as if his life defend on the phone haka ya kura mata ido yana kallon sunan Ammi a jiki,haka nan kawai yake jin wannan kiran da suke masa is like he's smelling something amma bamai fada masa komai,tattausan gashin kansa da yasha aski ya shafa wayar na dab da katsewa ya daga,daga can b'angaren Ammi tace" where have you been Son?"."Good evening Ammi"..."evening baka ce komai ba Jabeer is everything right ?"Ajiyar zuciya ya sauke yace "komai lafiya lau Ammi yana yin aiki ne ". Ai kunyi waya da Umminka ko?" Kamar tana kallonsa ya jinjina kai yace"eh Ammi"tace "to dan Allah karka bata lokaci ko wani abu da beyi daidaiba "... Cikin cool voice yace" to wai ina zamuje beside ina da aiki lokacin Ammi,ni bansan ya zanyi ta fahimta ba"..."kilan dai siyar da kai Fatimar zatayi ko Jabeer,kasan bana son halin nan naka na kafiya just obey shikenan ka dauko hutu as she say na fada maka bana son other reasons kuma ko wani maybe a lamarina Bawan Allah,tun da ai kasan ba'a taba maka haka ba,in kuma baka yarda ba do what suit you dama ko yaushe ai gaban kanka kakeyi "..." Kiyi hakuri Ammi,,sai na shigo insha Allah".sallama sukayi Ammi ta kashe waya ta dubi Ummi tace"idan ba haka aka masa wuta wuta ba kinsan ba zuwan zaiyi ba,wallahi Jabeer is the real copy of his late Father komai ba abunda ya baro"Dariya Ummi tayi tace"to saukin ma ai yana sauraranki ko wannan zuciyar ta gado ta taso,shissa kika ga ni ban masa da sauki duk da nasan wannan ba zai hanasa iyar shegensa ba,shiyasa tsab na shiryawa duk wata tabararshi bayan auren nan,dan naga almun sai munyi da gaske wallahi".Murmushi Ammi tayi tace"to kun daifi kusa,yanzu me da me kike ganin za'a kara a boxes din? Yanzu na maki transfer a karasa,kinsan idan na koma office ba time balle duk kusan weeks din nan ina da Wanda nakewa CS to bana samun isashen lokaci".kallon Ammi Ummi tayi tace"haba sai kace dai Jabeer din tsintarsa nayi Ammi? Kin mata ubansa ne kadai Allah ya bani ? Daga ni har Janar ubansa ne silarmu zuwa wannan matsayin,shine kuma a hidimarsa har sai kudinki sun shiga? Can dai kya masa wani abun amma boxes 16 duka an gama saka komai shoe ne kawai muke bukatar ki bamu size,even Gold's dinta duka an saka a boxes din kowa zaisan Jabeer yayi auren gata ranar daurin auren zamu kawo,kamar yarda kika bukata fatanmu dai Allah yawa abun albarka ya bida mana wannan Captain din".Dariya Ammi tayi ta tashi ta dauki handbag dinta da veil har gate Ummi ta rakata sannan sukayi sallama ta shiga mota zuwa gida......"ah kul na haneki da gulma,kidai kisa ido kawai ki kallo,koni nan da kika gani zuwa ido nakeyi dan wannan biki jinsa akeyi kamar yafi na kowa to a ranar daurin auren nima zan baza nawa tanadin sai na bawa ko wanne shege mamaki a gidan nan,kowa zaiga irin nawa ikon Wanda basu taba tunani ba,,wallahi zasu ga karshen iya shege,ranar Badiyya zata raina kanta".Dariya Layan ta tuntsure da ita tace"to gaskiya babu ruwa ,karma kice da ni kike maganar Momy a gidan nan,ni dai ba ruwana wallahi"kyab'e baki Annie tayi tace"menene kuma wata narkekiya Badiyya? Me akai akai Badiyarma gaba daya wacce muka yanta muka dauketa duk Doyi duk wari a gantaki? Sadeequ dai ubanki shine silar zaman Badiyya a gidan nan harta kankame mun 'Da danma Allah yasa nima ba a banza nake ba tsaye nake kamar hakori kullun cikin nema nake da yanzu wani bayani akeyi ba wannan ba,nidai dama da farko korarta nayi nace tsabta ma cikon addini ce ta rufa mana asiri ta tafi kafin ta goga mana wata cutar,amma Sadeequ ya tsaya kai da fata harna hakura ta auri Ahmadu sannannefa ta fara wanka da Dan gyarawa ga kan nan kamar hammatan Dan iska ke lamarin dai babu dadin tunawa,amma yanzu take ganin harta isa ,ita watace to wallahi wallahi kinji na rantse a ranar zata san nima ba a banza nake b,yar banzar kaina ce duk kyaleta nakeyi".. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 26 Layan kasa rike dariyarta take duk da tana jin hakan sam bai kamata ba ko dan darajar su Muhibba amma sam ita Momy bata a lamarinta, hakanan Allah bai had'a jinisu ba,daurewa tayi tace"Annie ta wajena yanzu dai ya isa haka ni dai ba ruwana kinsanta yanzu tana ji kowa sai yaji a gidan nan,bari ma ni kitchen zanje Ammi ta sani girki tana dawowa banyi ba kuma nasan sauran"....mitsi-mitsi da ido Annie tayi tace Laya "nifa ba kanwar uwarki bace bare ta ubanki,da nayi magana jira kike akan Badiyya ki taka mun burki,kul na haneki da shiga lamurana idan ba haka ba wallahi wallahi kinji dai na rantse zaki kwashi kashinki a hannu,in dai Badiyya ce kici gaba da wani kakkareta ina nan zata kullo maki wata tsiyar tunda baki san ciwan kanki ba,tashi ban wuri tun kan nayi kukan kura a kanki". Wani Dariyan Layan ta matse ta fice da gudu tasan ta yita a gaban Annie zata sha terere ne....kallonta kawai Lamin yakeyi Dariyan sosai ya mata kyau ga dimples dinta da suka lotsa sosai gaba daya gani yake ta wani canza mai har wani kyalli kyalli takeyi ga fatarta tayi fayau kamar ba Layan ba,kullun ji yakeyi a ransa kamar ana kara mashi sonta,he wish Momy bata saka baki a aurensa ba,da yanzu Layan za'a aura masa ba Ihsan ba,amma duk da haka bai cire rai ba jira kawai yake bayan biki ya lallabi Momy ya auri Layan dan baya jin xai ita ci gaba da rayuwa da wannan soyayyar tata mai matukar wahalar da zuciya,he can't take it any longer zuciyarsa zata iya fashewa a ko da yaushe haka yake ji,runtse idanuwansa yayi yana jin sanyi a zuciyarsa na ganinta da yayi,itama da gudunta ta karaso in da yake tana cewa"Yaya",.idanuwansa da suka soma canza launi ya bude ya zuba mata su amma bece komai ba,cikin dauki tace"yau Annie tace zatayi maganina zan kwashi kashina a hannu".yadda take describing yarda Annie ta mata shi kadai ya bashi dariya badan yaso ba ya dara yace" da kika mata mene?,na dai san u and Annie 24/7 alkawarinku na nan"...."hmm not any longer kwannan nan naga hari take kokarin kaimun".murmushi yayi sai kuma yace"zaki raka ni unguwa Lil".waro ido tayi tace"sure Yaya,bari na daurawa Ammi girki sai muje".jinjina kai yayi yace"muje na tayaki" daga haka ya kama hannunta zuwa kitchen din,all the work sunyi shi a tare ne suna yi suna labari ,daga karshe ya jingina da cabinet yana kallon yarda take aiki dan girki is her favorite, ta iya sosai ,bata wasa da girki,shiyasa kowa a gidan rububin tayi girki ko kad'an ne,sai dai favorite Yayan nata ko kad'an baya iya kallon abunda ta dafa ma bare kuma har yaci kullun gani yake jagulgulo takeyi.ajiyar zuciya Lamin ya sauke yace"lil idan akai aure zaki koma gidana,I don't want miss this delicious girkin naki gaskiya".washe hakoranta tayi tana dariya tace"ah Ammi ba zata bari ba,u know idan na dawo school ni nake mana girki,da kula da gidan".Sallamar Ammi a kitchen din ya tsayar da surutun Layan da sauri ta ajiye spoon din hannunta da take juya orange juice ta ruga ta rungume Ammi cikin cool voice tace"you're welcome Ammina".kafin ta karb'a handbag dinta da laptop dake rike a hannunta,Murmushi Ammin tayi ta shafa kanta tace"ya aikin" ta ansa da alhmdllh kafin tayi hanyar waje zuwa bedroom din Ammi.sai a lokacin Ammi ta gaisa da Lamin sannan suka fito tare ya zauna jiran Layan...kallonta sama har k'asa Ammi tayi tace"zuwa ina kuma ?".."nima dai yace zan rakasa kawai ne Ammi,dan Allah kada kice bazanje ba".Layan ta kare maganar da alamun ban tausayi...kallon Agogo Ammi tayi kafin tace"kada kuyi magriba a waje".daga haka ta wuce tana rage kayan jikinta zata shiga ban d'aki,da long ash hijab Layan ta fito a har k'asa kamar yarda ta saba shigarta..."Yaya bari na karashe juye farfesun Ammi a collar"bata jira cewarsa ba ta shige kitchen din ta dauki coller making very careful ta samu ta juye farfesun cat fish din daketa tashin kamshi sunsha hadi,ta rufe colarn ta goge da tissue ta dauko ta ajiye a dining sannan ta fito suka fita....as always kamar yarda ta saba gaba daya tafiyan bata bar bakinta yayi shiru ba labari kawai take bashi cike da kuruciya shikam dariya da murmushi kawai yake yi sai ansa mata da yakeyi in ya kama,gaba daya farin ciki ya gama cikasa,tun tafiyar Jabeer bega tayi farin ciki irin na yau ba,gaba daya sai yaji yau din ta zamar masa special day ,A daidai wani tankamemen gate yayi parking ,gate man ya leko ya tabbatar da waye sannan ya bude masu suka shi,da kallo Layan tabi babban compound din da kallo ba laifi gidan yana da girma sosai amma bekai nasu ba sai dai gidan ya tsaru kallonsa tayi kafin tace"gidan waye muka zo Yaya".yana pressing phone dinsa yace "zata zo yanzu ki ganta". A kunne ya kara wayar.Ihsan dake zaune tsakiyar babban bed din dakinta tana ta daddaga wasu English wears da suka siyo da Husna ta juyo da kanta taga Wanda ke kiranta,dandanan fara'a ya cika fuskarta ba wani bata lokaci ta dauki wayan tace" Baby ka iso?".lumshe ido Lamin yayi yace"ina jiranki a waje".be jira amsarta ba ya kashe wayar .ba dadewa sai ga Ihsan ta fito daga entrance na gidan sanye da tsadaddun English wears dinta Riga da wando sai hula a kanta,sosai kayan suka mata kyau ta taho tana chewing gum a bakinta,kai tsaye driver seat ta nufa ta kwankwa glass din,zuge glass din lamin yayi dan danan uban kamshinta ya cika wurin sai dai tana sauke idanuwanta akan Layan ta wani daure fuska kamar taga mutuwarta,ta koma gefe taja ta tsaya tana wani cika da batsewa,kallon Layan Yayi yace"ki sauka ki gaisheta".kafin tayi magana kuma ya bude motar ya sauka.vividly take tuna irin rashin mutuncin da tayi mata ranar da taje gida gaishe dasu Annie,run daga ranar kuma taji gaba daya Ihsan din ta fita daga ranta,bata son musu da Yayan nata yasa ta bude motar ta fito fuskarta adan sake ta zagayo in da suke,ko kad'an baya tsaya duba yanayin Ihsan ba tace"good Evening ".wani wawan kallo Ihsan ta bita dashi sai kuma tace" yauwa sannu" daga haka ta kuma take fuskarta,Layan kam mota ta koma dan bama zata iya jurewa kallon da Ihsan ke binta dashi ba,Wanda ta kasa gane manufarta.kallonta Lamin yayi kamar mai irgan abu yace"me yasa zaki ansa mata a haka Ihsan,baki san sisterna bace?"..."kar kace zaka mun masifa a kanta Lamin,kasan nasan wacece ai,bata yimun ba,ba kuma zaka tursasani nayi alaka da ita bane tunda ba Momy ta haifeta ba,ina dalili duk in da zaka je tana biye da kai,kai kuma kaita rawar kai kana wulakanta ni a kanta to wallahi bazan dauka ba tun wuri kara asan abunyi"ta kare maganar tana tauna gum din bakinta yana kara...cike da mamaki Lamin yake kallonta sai dai bece komai ba ya juya ya barta nan a tsaye ya shige motarsa ya tada yabar gidan.ko kadan be canza fuskarsa ba hasalima a yanzu shi yake jan Layan da labari har ya tsaya yayi mata siyayyan da ya saba mata duk date kafin suka wuce gida....Ihsan kam fuuuu ta wuce cikin gida kamar zata tashi sama tana jin zuciyarta na tafarfasa kamar zata fasa kirjinta ta fito dan takaicin irin walakantata da Lamin yayi. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 27 Yacce kasan wata zautacciya haka Ihsan ta shigo cikin d'akinta ta ibe hulan data rufe tulin sumar gashin data kara aka mata kalaba ta watsar gashin ya zubo a bayanta duk ACn dake aiki a dakin amma wani irin zufa ke tsatsafo mata ga wani irin nauyi daya danne mata zuciya, kallonta Husna tayi sai kuma tace"waike lafiya? Lamin din bezo bane?"hannu ta daura a kai sai lokacin ta samu hawaye suka zubo mata tace"na shiga ukku Husna,wallahi in dai ina ganin Lamin da yarinyar can zuciyata bugawa zatayi,wallahi sonta yakeyi babu komai a kwayar idonsa sai tsantsar soyayyarta,I can't any more zan iya haukacewa wallahi,na hakura da Jabeer amma bazan kuma rasa masoyi na biyu ba wallahi"...Dariya Husna ta saki tace"yanzu akan wata kike wannan tashin hankalin Ihsan?wallahi na raina wayonki da ajinki,me akayi akayi wata mace ,ni idan ni keson namiji ko uwarsa wallahi sai dai hange bare wata kanwarsa "wani kukan Ihsan ta kuma saki tana fadin"na lura baki da hankali Husna baki san mena gani bane,Lamin kuma ba irin duk mazan da kike tunani bane" Mom da Aunty Jamila dake tsaye a Kansu basu sani ba,Mom ta kyab'e baki ta karasa shigowa cikin dakin,da Gudu Ihsan ta karasa ta rungume Mom tana gunjin kuka tana fadin"wallahi Mom ni baxan iya zama da kishiya ba,mom zuciyata zafi takemun na tsani ganin yarinyar nan amma kullun tana tare da shi,yanzu haka fa da ita yazo mun ya barni tsaye a walakance Mom"Dagota Mom tayi daga jikinta cikin zafin nan nata tace "ke ni bansan sakarci da rashin wayau karma ki karasa Hassalani,ki kwantar da hankalinki yadda nake gidan Ubanki ni kadai ga Yayarki har mijinta ya rasu bata da kishiya to ba za'a fara a kanki ba Ihsan,ki nutsu kisan abunda kikeyi bana son kukan nan naki,yanzun nan zan kira uwarsa wallahi duk Wanda yaci tuwo da ni miya miya yasha"tana kaiwa nan ta zame jikinta ta fice a dakin.Aunty Jamila ce ta kamata ta zaunar da ita sai tabara takeyi da koke koke......parking yayi a in da ake parking luck ya sakawa motar Layan ta juyo da manya manyan idanuwanta tana dubansa cikin cool voice tace" Yaya".bece komai ba ya kama duka hannuwanta guda biyu cikin nasa cikin sanyin murya yace"Layan please I'm sorry for what happened earlier".tab'e baki Layan tayi sai kuma tace"I didn't complain Yaya,wani abun ya faru ne?".Dungure mata kai yayi sai ta saki dariya kuma,shagala yayi da kallonta har dariyar ta lafa mata sannan yace"u look beautiful, I mean, kimun alkawari Layan".ido ta waro tace"alkawari kuma Yaya?"gyada mata kai yayi yace"just at any cost kiyi backing dina Layan,just believe me goyon bayanki da yardarki shine abunda kawai nake bukata lil."jinjina kai tayi sai kuma tace"Yaya aikai bakayin abunda ba daidai ba,I trust you,insha Allah in Allah ya bani iko".back seat ta yunkura ta kwashi ledojinta ya bude mata lock din ta fita ,yakai musan 5 minutes zaune a motar ya jinginar da kanshi ya lumshe ido sai kuma ya bude ya fito.....Momy kam ta Gaza zaune ta gaza tsaye wani irin tashin hankali ke dawainiya da ita,tunda ya shigo da mota a gidan take jiran fitowarsa duk da tasan abunda Hajiya Sha'awa ta fada mata wai Lamin nasan Layan tasan bamai yiwuwa bane har bayan ranta,ranta tafarfasa kawai yakeyi da kyar ta iya controlling kanta ta hana kanta fita waje tayi maganin Layan din ,tana ganin Lamin ya nufo part din su ta koma ta zauna a gefe bed tana cika tana batsewa.so silent ya iska parlon Momyn kai tsaye bedroom dinta ya bude yanayin daya ganta zaune yasa ya karasa ciki da sauri ko noticing Hydar dake shigowa parlon na beyi ba,kai tsaye gabanta ya karasa yace"Momy lafiya? Wani abun ya faru ne?".kwafa tayi tace"uban meyema be faru ba,wallahi wallahi Lamin na kusa maka baki ka lalace kowa ya huta,Lamin ni zaka walankata ka zubarmun a daraja a idon duniya? Ace ban isa da kai ba? Akan waccan y'ar iskan Layan? Yau sai dai ka zaba ko ni ko Fatima zanga idan ita ta haifarmun kai"...innalillahi wa inna ilaihir raju'un kawai Lamin ke maimaitawa be taba jin maganganun da suka masa nauyi ba a kai irin yau cikin shakewar murya yace"kiyi hakuri,kiyi hakuri Momy bani da kamarki duk duniya ,Momy na maki biyayya ne zan auri Ihsan badan type dina bace,Momy ina san Layan Momy ina Santa hakan kuma bawai yana nufin bijirewa umarninki bane,ki yafe mun bayan auren Ihsan zan auri Layan,Momy rayuwata zata rushe idan na rabu da it.....".."kayi mun shiru marar zuciya da Sanin ciwan kai, babu Wanda ya isa Lamin ko bayan raina ka auri jinin Fatima sai tsinuwata ta bika ,har abada bani ba jinin Fatima ".turo kofar dakin Hydar yayi idanuwansa jajir yace" you can't say this Momy ,kin yarda ki tarwatsa rayuwar danki akan wani dalili da kiyayya marar amfani,Momy you can't do this to him wallahi in dai harke kika haifesa ,aduk cikinmu wa yake maki abunda yake maki Yaya Lamin ne cancanci haka gareki ba".Abba ne ya katsesa da fadin"tayi masa haka mana saboda cikar burinta da muradinta mana Aliyu".gaban Momy sai da ya fadi sosai amma ta dake tana girgiza kafa jin muryar Abba kamar daga sama,kallonsa ya mayar kanta yace"yace sai dai kiga lalacewa a wani wurin Badiyya amma ba akan son dina ba,ni na sani wannan auren ke kika kullasa amma ina so ni sani idan yanzu Lamin ya canza ra'ayi babu Wanda ya isa ya aura masa yarinyar da baya so..let me make this clear to you bancin na yanke hukunci akan Layan da a yau zan daura aurenta da Lamin kina tsine masa kuma kema a bakin naki auren,kullun girma kikeyi amma kina cin kasa sai yaushe zaki san ciwan kanki ,to ina tabbatar maki albarkacin yaranki kike ci da yanzu nayi maganinki"kuka Momy ta fashe dashi tana cewa"dama ni kullun cikin laifi nike ,ka tsaya kana walakanta ni gaban yarana".da sauri Lamin ya karasa gabanta yana fadin"kiyi hakuri Momy insha Allah hakan ba zata sake faruwa,kiyi hakuri"..."ki kallah da idonki amma wannan yaron shi zuciyarki keson lalatawa kinji kunya Badiyya"yana kaiwa nan ya fice,Hydar ya bisa a baya......"kwanciyar me kike mun a nan Laya? Sharafa nakeyi ,yau naga lukutar masifa ni Maryama".tura baki Layan tayi tace"ke Annien nan sai mutun na tunaninsa kizo ki tsorata shi,shara da tsakar daren nan,nifa nan cite ciye zanyi abuna ".kwalo ido Annie tayi sai kuma ta fizgi ledan dake gefan Layan ta duba kwalo ido tayi ganin gasheshen kaza dasu chocolate kala kala sai ice-cream,kanne ido tayi tace"gidan ubanwa kika samu? Badai fita kikayi ba Laya,yau na shiga ukku na taba ganin biki saura kwanaki ana gantali a titi?". Murtuke Fuska Layan tayi tace"to ai Yayan ne ya siyo mun,gidan amaryarsa ya kaini,ni za'a daurawa aure da zaki ce kada na fita ikon Allah". Tuna katobarar da take son yi tayi sai kawai ta saki murmushi ta bude ledan ta yagi gasashiyar kazar ta saka a baki tace"yaro man kaza yaro yaro ne" sai kuma ta zauna a kujera tana b'are kazar tare da cewa"tashi ki dauki kasanki kada ma kice da cuta a lamurrana,ni kam nafi son komai gaskiya da daskiya". *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 28 Yau ya kama bikin sora kwana biyar cif,A hankali ya fito daga cikin motar da Hydar ya daukosa daga Airport, sanye yake cikin complete uniform dinsa kaki ,sosai kakin ya masa kyau ga wani irin haske da fuskarsa ke kuma sakarwa sai dai ya dan fada kad'an kasancewar ayyukan da suka saka shi gaba,k'atuwar Jakkan goyonshi Hydar ya dauko yana kuma masa sannu da zuwa ga kuma Faruk da Jafar da suka karaso suma, jinjina kai kawai yake yi ta haka ya amsa gaisuwarsu ya taka zara-zaran k'afufuwansa yana tafiyar nan tasa ta zaratan mazaje ,part din Annie ya kallah sai dai sam baya son fara shiga wurinta dan gajiyar daya ibo hutawa kawai yake son yi,kai tsaye part din Umma ya wuce,da sallama a bakinsa ya tura main entrance na part din ya shiga in ba kana kusa dashi sosai ba ba yarda za'ayi kaji,babu kowa a parlon sai k'afar Ac da wa'azi dake tashi a sunna TV Wanda plasma TVn data kusa mamaye bangon d'akin take fitar da sauti babu abunda parlon yake fitarwa sai kamshi mai tsananin dadi Wanda lokaci daya ya saka shi lumshe manya manyan idanuwansa da suka dan rage girma .da gudu ta karasa zuba turaren wutan a borner data jona tana yaryarfe hannu tare da kiran sunan Umma tana turo baki cikin cool voice dinta da baya fita sosai kasancewar muran da take fama da ita kwana biyu,Baya baya ta soma yi with out her notice tayi ta zame a tayil tayi baya zata fad'i sosai ta runtse idanuwanta har hawaye ya kawo a idon tana tunanin ta ina zata fara jin radadin azaban zafin in da zata bugu.sai jinta tayi ta fad'a jikin mutun a duk tunaninta Yaya Lamin ne sai dai jin kamshin dadden turarensa Wanda bata iya mantawa ya kaiwa hancinta ziyara cikin hikima ta kuma saka hannuwanta ta mak'alk'ale shi,a Daidai nan kuma Umma ta fito daga kitchen rike da plates da spoons zata ajiye a dining saurin dauke idonta tayi ta koma kitchen da sauri bata ma son su ganta.Zaro ido Jabeer yayi yasa hannu ya kwace gaban rigarsa data rike,tuni zuciyarsa ta fara azalzalarsa ji yakeyi kamar an jona masa shocking iya karfinsa ya goce daga jikinta ya saketa akan tile ,wani siririyan kara ta saki lokacin data saka hannunta ta fad'a a kanshi tare da fadin"Yaya hannuna ya kare,wayyo Allah Ammi wayyo Allah Anniena".ta kare zancen idanuwansa suna ciccikowa da hawaye suna safka a fuskarta.ko kallonta beyi ba ya wuce cikin parlon yana jin zaman parlon ma gaba daya yana neman gaggararsa dan tsab zai karyatan da gaske sai ta samu kiranshi da wani Yaya can data kwallafawa bakinta,tsaki ya saki ya karasa kitchen in da yake jin motsi fuskarsa a dan yake yace"Umma"juyowa Umma tayi cikin da farin cikin ganin yaron nata tace"oyoyo my son sannu da zuwa".murmushi ya dan saki ya karaso tare da kama Hannun Umman ya durkusa yace"Ummana ina wuni,na same ki lafiya?".gashin kansa ta tsafa da yake nan a gyare tas sai tashin kamshi take tace"alhmdllh sannu da zuwa".gyad'a mata kai kawai yayi,sanin halinsa yasa bata ja da tsayi ba tace"muje kaje kayi wanka sai ka fito kaci abinci".bin bayanta yayi zuwa parlon basu samu kowa ba hakan yasa ya fice daga wurin....hawaye take matsa kallonta Ammi tayi tace"bana son sakarci ki tsaya naga hannun ko kinji ciwo a wani waje,a ina kika fad'in?".k'ibk'ibta ido tayi kafin tace "a d'akin Umma ne ina saka turaren wuta"... " sai kuma aka ce ba zaki natsu kiyi abu a hankali ba ko Daughter yanzu kiji kukan da kike yi kin bige hannu".Sallamar Jabeer yasa Ammi yin shiru tana binsa da kallo sai kuma ta girgiza kai tana had'e fuska tace"kai kuma daga ina? Daga zuwanka harka illata mun y'a Jabeer? ".cikin sauri Layan ta daga ido tare da cewa" Ammi bafa shi bane,faduwa nay.....".kin rufamun baki ko sai hakoranki sun zubo a nan wajen ,tunda ke baki san ciwan kanki ba,to duk a tare zan hadaku nayi maganinku".Da kallo kawai Jabeer yabi Ammi sai kuma yace"itace tace naji mata ciwo Ammi"...."Jabeer wallahi idan baka fita idona ba zanyi maganinka a gidan nan waye besan muguntarka ba? To wallahi kayi na farko kayi na karshe in ba haka ba zaka hadu da b'acin raina bana wasa ba,na gaji da wannan halin naka marar tushe".Sunbure baki Layan tayi kamar ta fasa ihu haka takeji Ammi ta kalleta fuska a daure tace"nawa Babanki magana ranki ya baci ko Maryam? To tashi fita mun a d'aki dukanku bana bukatarku a nan,ranar da kika fara amincewa da zalincin Jabeer a kanki kyace na fada maki"..turo bakinta tayi gaba ta tashi ta wuce d'akinta dake part din.."Ammi tasan ko zasu kwana a nan bazai fada abunda ya hadasu ba,kasa yayi da murya yace "Good afternoon".. Shiru tayi sai kuma tace" Afternoon,look Jabeer this should be my last warning going to you ,daga yau har a daura auren gidan nan bana son wani abu ya hadaka da Layan,billah duk idan ka kuma dukanta ko wani abu haka kasan ni kayiwa,kuma zanyi Fushin da ban tabayi da kai ba,you can leave "..kasa yayi da kansa sai dai bece komai ba ya tashi a fita a part din yana jin dama bezo yau din ba,daga zuwanshi akan yarinyar can an fara damun rayuwarsa...kallonsa sama har kasa Momy tayi kafin ta fara tafa hannuwa tace" Jabeer yanzu harka shigo gidan nan amma sai ka gaba zagaye ko ina mu bamu samu darajar da zaka iya shiga ka gaishe mu ba? Waye babba a gidan nan? Kazo kayi zaune labcece gidan mutane amma gaishe mu ya gagareka?"Shidai bedai ce komai ba kamar bazai kulata ba sai yace"ina wuni"kallon sama da k'asa ta masa a tsawace tace"ban wuni ba,ban wuni ba nace Jabeer,dama ai ba tarbiya ta ishi maryam din ba bare kuma kai ta dauraka a in da ya dace".Runtse idanuwansa yayi da sauri da suka soma canza launi ,sunan Lamin kawai yake masa yawo a kai yasa kawai ya gitta Mommy ya wuce bece komai ba,wannan aibata masa mahaifiya da takeyi duk yana daya daga cikin abubuwan dake hanasa zuwa gidan gaba daya baya tunanin bayan auren Lamin zai kuma dawowa gidan da wuri,waya ta ishesa ya gaishe da kowa in ba haka ba zai iya canza zuciyarsa ya aikata abunda kowa zai iya dana sani.tsaki yaja tare da buka kofar dakinsu daya shiga yasan zai samu dakinsa yarda yake so matsawar Umma na rayuwa a cikin gidan,bata barin d'akinsa ko Abincinsa a hannun wani,yana shiga ya murzawa kofar nashi key,wani Dadden kamshi ya ziyarci hancinsa ya lumshe idanuwansa ya bude ko boot dinsa bai cire ba ya fada akan lausasan bed dinsa da yasha sabon bedsheet kamar wani d'akin mace ya lumshe ido yana jin zuciyarsa na sauka a hankali a hankali *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 29 *Masoya ina bada hakuri ,to gashi dai Jorderh ta dawo akan makamar aiki insha Allah cikin kwanakin kad'an zamu karasa ayi hakuri da uzururikan da suka sha gabana,na gode maku da jimurin bibiyata,masu waya masu text duka ina godiya can't luv u less Allah yabar tare,yau dai inji ruwan comments ta ko ina su tashi kaina,nasan kuma page din zai kayatar daku kamar yarda aka saba.* Hangangan haka Annie ta wake kofar dakin Jabeer tana wani kyab'e baki kamar taga kashi a d'akin kafin ta saka kai tana rabka sallama.Jabeer dake kwance har lokacin be tashi ba tun shigowarsa gidan ya ware manya manyan idanuwansa da sauri kasancewar ciwan kan dake damunsa,akan Annie ya sauke idanuwansa sai dai ya kasa cewa komai sai binta da kallo yake,Annie tace"to tashi Allah ya kamaka yanzu Jabeeru ni,ni nan ni Maryama dana haifi uwarka naci fitsarinka naci shegen kashinka mai doyi ni ka gagara shiga ka fad'awa dawowanka gidan nan? Akwai ubanda ya rainan mun kai ko ya haifa mun maryama din,kul na haneka to ko marigayi Allah jikansa Sadeequ ko kara na ajiye baya tsallakawa ba ruwana bare kuma na masa sharri,amma yau d'aya samb'al ka labce a d'aki,to ko dai bak'in halinka yasa an koroka daga aikin sojan ne mu shiga ukku?"...A hankali Jabeer ya mike zaune cikin sanyin murya yace"kinzo kin cika mun kunne ina bacci,lafiya?"...wani gwalo ido Annie tayi kafin tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,harda rashin kunya ka koyo a wannan karon to nace uwarka ke cika kunne badai ni ba,wallahi Jabeeru kasan nasan kan tsiya daidai da kowa nake".Murmushi kawai yayi ya mike ya sofa rage uniform din jikinsa,kyabe baki Annie tayi ta fice tana sababi,duk yarda Lamin zuciyarsa ke a cunkushe days din nan da kunci amma dariya yakeyi harda kwanciya da rike ciki kan tsiyar da Annie tawa Jabeer,tsaye Jabeer yayi kamar wani statue sai kuma yace "kilan baka da lafiya ko?". Wani dariyan ne ya kuma tunkuro Lamin yace" wallahi kai zan cewa marar lafiya,anya Jabeer basai na dubaka ba,ba maka duban k'wak'wab at 32 ace ko budurwa baka taba yi ba? Baka ma maganar aure,dole na duba ko mata maza ne".wani wawan suka Jabeer ya kawowa Lamin da sauri ya goce yace"tabdi waye xai tsaya ka masa wannan dukan naku na mararsa imani? The great barrister zakawa wannan cin fuskar? Kuma ai gaskiya na fada zanwa Annie bayani dallah dallah a bin cika mana kai,kasan ko gidan redio albarka"yana kaiwa nan ganin Jabeer yayo kansa yasa yayi waje da gudu yana kuma sakin dariyar daya Dade beyita ba,wayarsa ce ta fara ringing ya Ciro daga aljihu ya duba ganin sunan Ihsan yasa ya dauka,yana daga wayan tace"Lamin gaskiya na gaji da wannan walakancin da kake mun,tun karfe nawa mukace zamu fita amma har yanzu ban ganka ba,ko su kawayen nawa basu da darajar da zan gayyacesu ne? Kuma kasan ina neman bazaiyiwu kace wai aurenmu ba za'ayi shagalin komai ba sai kace zan auri liman? As big as I I'm sam ka canza tunani,saboda kaga na nace sai kai amma bai cancanta na rika samun out comes daga wurinka irin haka ba haba Lamin".sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, shikam har ya gaji da complain na Ihsan sam komai nata a baki yake kamar tana jira"look Ihsan,ni bana bukatan yin komai a aurena,idan zakiyi ban hanaki ba amma count me out dan bazanje ba,ki fada ko nawa kike so zan tura maki ki shirya,maganan fita kuma ina da wani uzirin ne Driver xai zo ya same ki kuje"be jira cewarta bama ya kashe wayan shi dan yasan karshen zancen wani ihun ne zata kuma tarara masa a kunne.......kansa a sunkuye bedaice komai ba Ummi tace"yau naga lalata Jabeer in tambayeka kuma kamun shiru?".kallon Ummi kuma yayi can dai harta fidda ran zai amsa yace"nifa bata mun komai ba,Allah ne kawai be hada jininmu ba".."amma ai ya hadu dana iyayenta ko?,ko kunya bakaji ko yaushe kana manne dasu,sun tsaya maka kai da fata ,baka taba kukan maraici ba,amma y'arsu ta gagareka kulawa,dazun nan Amminka ke fadamun abunda kawai yarinya a hannu kuma a cikin parlon uwarta,anya Jabeer rayuwa zata tafi a haka kuwa? Anya kawa kanka adalci kuwa? ,Jabeer ina guje maka ranar dana sani ranar da zakayi kuka babu mai taimakawa,ranar da zaka so wata ta soka ta taimaka maka kamar Layan din amma babu ,kayiwa kanka adalci ka sassauta zuciyarka ka daina kuntatawa yarinyar nan,so ba karya bene,in kana tunanin Allah ya daura maka kiyayyarta kuma kana jin ba zaka iya dainawa ba,to itama ka tausayeta Allah ne ya jarabceta da sonka kuma har abada tana backing dinka tana bukatar damar rike hannayenka kuyi tafiya da zama na har abada,kuma zaka ce na fada maka wannan even when k'asa ta rufe idona Jabeer "Da sauri ya dago kansa ya dubi Ummi sai dai bece komai ba,maganganun ma ji yayi sun ishesa baya son ji ya juya yace" zanje na gaishe da Hajja"..."Allah ya tsare idan kaje ka gaishe ta,kuma baka mun maganar hutun naka ba" .phones dinsa yake kwasa yace"na dauka kamar yarda kika ce amma sati biyu dai na samu saboda wani aiki da yake tunkaromu"..."Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ka gaishe da Hajjan"...sallama sukayi kafin ya fita ya wuce gidan Hajja a mota yana tunanin what's so special about Monster da kowa ke nanan da ita,shidai yasan banda hauka rawar kai da rashin natsuwa da mugunta bata da wasu nagartattun halaye bayan wannan,to shi ina ruwansa da ita ko harkarta baya ma shiga,ko abu ya mata to ita ta kawo kanta,saboda kyamar zama da ita da yakeyi ma yasa sam baya son zuwa gidan ,sirirn tsaki yaja a fili yace"ya bakin fuskarta ya bakin halinta,stupid gal"A haka ya shiga gidan Hajjan tuni ya manta duk wani damuwa da bacin rai daya kwaso,lallai zaici gaba da addu'a Allah ya dube shi ya karawa Hajja lafiya da tsawon kwana dan Hajja wani bangone garesa abun jingina....."Ban gane kace harda su Maryam za'aje kai lefe ba Yallabai?saboda ni bani ga kowa? Duk yan uwana da kawayen nawa sai suyi zuru,ina da wa'anda zasu kai basai sun bisu ba gaskiya"Mummy Badiyya ta kare zancen da alamun b'acin rai a tattare da ita...kallonta kawai Abba yayi da kausashiyar murya yace"Badiyya let me send this warning to you,daga yau na kara yanke magana kika ja da ni zakiyi mamaki na,kinsan kuma bana magana biyu,ki kuma gwadani kiga idan ban juya wannan auren da kikewa ba,lefe Maryam da Amarya da Sadiya su shirya su kai ya isa bana son gayya".yana zuwa nan ya sauki eye glasses dinsa ya saka ya soma karatun jaridar shi.har wani shidewa Mummy takeyi dan takaici tace"zasuje da kawayena su biyu,ba zasuji dadi ba dan harna sanar dasu tun farko,ni bansan meyasa komai zan fada zakace neyi ba,alhali da ba haka kake mun ba".Abba dai bece komai ba can dai yace'ina so in huta ki rufemun kofar".be jira cewarta ba ya kwashi tarkacen shi yayi bedroom da takaicin Mommy Badiyya cike a rai yana tunanin ko yaushe zata girma har tayi hankali *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 30 Murmushi kawai Daddy yayi yace"to why not ka barta ta saka wa'anda take so su kai lefan Yaya? Kasan maryam ma ba son shiga sabgoginta take ba tun ba yau ba,ba wani abun zaka duba ba kuma illa dan ayi hidimar nan lafiya a kare lafiya tashin hankalin ba dadi"."bawai naki bane Sadeeq abubuwan Badiyya sun fara mun yawa ne a gidan nan,kullun idan ana biyeta har yaushe zata san ta girma?,beside ma auren nan gaba daya itafa ta takurawa yaron nan sai anyi shi ina ake haka fisabilillahi"...jinjina kai Daddy ya kuma yi yana kallon Yayan nashi yace "da dai anyi hakan Allah ya rufa asiri insha Allah komai zai wuce ". Da ameen kawai Abba ya ansa bai kuma cewa komai ba kuwa ya tashi yabar parlon dan yana da in da zaije Daddyn ya tsayar dashi akan maganar kuma yasan kararsa Momy Badiyyan zata kai ba ko kunya kuma a wurin kaninsa,shikan yaga ranar da Badiyya zatayi hankali tana girma tana cin kasa.....d'ad'aga kayan lefan akeyi kwanin burgewa kowa na jinjina kai ganin yarda set na boxs din suka hadu kowa ya yabawa Lamin kam kowa yasan Ihsan ta samu miji na kece raini,duk wani magana da akeyi tana gefe a chair tana kuma kallon kawayenta dake kallon kayan suma suna yabawa sai wani bubud'a hanci takeyi tana jin kanta a sama ita babu ya ita,kallon Husna tayi tace" sai yau na kara tabbatarwa Baby na sona,ya fitar da ni kunya na dauka yarda baya son kashe kudi to bazaiyi abun kirki ba duk da wayayye ne".murmushi Husna tayi tace"kema da gangan tunda kinsan ai sirikarki da son iyayayi da nuna tafi kowa ai ba zata bari ayi abunda ba dai dai ba,Dan wallahi karfinki a gidan nan kab itace wannan mijin naki da shegen taurin kai kamar mutanan farko".tsuke fuska Ihsan tayi rai b'ace tace"dan na baki fuska kuka bashi ke nuna ki walakanta mun miji ba,gaskiya kisan abun rika fada in ba haka ba ki rika jina dib ba wani out come wallahi,haba kamar jira kikeyi".Husna dai batace komai ba ta juya taci gaba da kallon box's din da ake harhadawa tunda an gama daga duk wani abu dake ciki sai kace za'a bude wani shago......Shafa kansa tayi cike da kewa da tsananin soyayya tace"rayuwa sai hakuri Jabeer,ina so duk halin da ka tsinci kanka karka manta da Allah duk wani rintsi shi ya kaddara maka kuma zai baka mafita ka zama mai hakuri a ko da yaushe,kada kuma ka zama mai garaje ko saurin yanke hukunci a al-amuran rayuwarka,duka duniyan nawa take? In yau mune gobe bamu bane,ina fada maka wannan ne wata kila dan yau nake da dama wata ranar bazan samu lokaci kamar haka ba,ka zama mai gaskiya da rungumar duk abunda kaddara zata baka kai dai kayi kokari ka furta alhmdllh a ko wanne hali Yarona"..Manya manyan idanuwansa ya daga yana kallon Hajja sai kuma ya rike hannuwanta sosai cikin nashi kamar wani karamin yaro yace"Haba Hajjana dan Allah ki daina sai nake ganin kamar bankwana kike mun,idan babu ke ina zai zama mafakata kenan? Bana tunanin zuciyata zata iya daukar rashinki Hajja"...Murmushi mai matukar kyau Hajja ta saki tace"Ayya Jabeer in yanzu mutuwa tazo garemu ai batayi sauri ba ,idan kuma ta tsaya batayi jinkiri ba,idan mutuwa tazo dole mu ansa kiran mahaliccinmu ,fatanmu dai Allah ya mana arzikin kyakyawan karshe ,mutuwa dole ce"Bai kuma cewa komai ba ya soma sauke ajiyar zuciya kawai amma gaba daya ya rasa sukunin zuciya sai wurin karfe tara na dare da Daddy ya kirasa sannan yayi sallama da gidan Hajjan ya tafi.ko da ya shiga parlon Umma anan ya samu Lamin shima zama yayi tare da cewa"Ina wuni Daddy "cike da soyayya da kulawa Daddy yace" lafiya qlau my son,ya aikin yaka baro Hajjan?"da alhmdllh ya ansa yana yin kasa da kansa.bags manya guda biyu Daddy ya dauko daga gefansa ya tura masu tare da cewa"ka kayanyakin da zakuyi amfani dasu a fitar biki nan,sai Ku duba abun da babu sai kuyi magana ko kuma za'a karo"Murmushi Lamin yayi tare da cewa"mun gode kwarai Allah ya saka da alkhairi Daddy ai nasan komai ma akwai a ciki".Dan shafa kai Jabeer yayi fuskarsa a sake yace"Allah ya kara budi Daddy,amma ni da ba ango ba".Dariya Daddy yayi ya tari maganarsa yace "Babban Abokin ango ma ai angone,ina so ne in ganku komai iri daya kun fito gonin Sha'awa yan samarina,su Hydar ma dai su ukku ga nasu can"... Sosai sukaji dadi sukayiwa Daddy godiya sannan suka dauka zuwa part dinsu a parlo suka baje kayan tsadaddun shadda,da voyels na maza ne iri da kala har kala goma ga hula da agoguna da turaruka hatta da boxers da singlet sai da Daddy ya zuba masu a ciki,dinkin ya dinku dan kab family din su a RASHEED MAKERA FASHION DESIGN suke dinki ma'ishi Wanda sai wane da wane ke samun dinki a can ko wanne b'angaren na dinkin maza da mata babu wanda basayi kai harma da kayan mazan suna siyarwa ka zaba a dinka maka daidai da ra'ayinka kuma a tura maka ako ina a fadin Nigeria gamai bukata ga number su 07047230000.....A gajiye lis su Layan suka shigo gidan musamman ita da ko kad'an bata jurar wahala danma Ammi na tare dasu da wallahi tuni gudo wa zatayi lalle ne aka cancad'a mata ja da baki ga kitso yan yarfa mata duk da ita ba gwanar yin kitson bace sam,Muhibba kam da Basma dasu Asma'u sai washe baki sukeyi dan dama sun saba kwalliyarsu irin haka,itakam tafi kowa jigata saboda rashin sabo.kai tsaye toilet ta wuce bayan ta rage kayan jikinta ta zubar a tsakar dakin nata,wanka tayi da ruwa mai zafi sosai sai kallon kanta takeyi a madubi sai kace wata sabuwar Amarya ga fatarta sai wani glowing na musamman takeyi yarda ta samu gyara da kulawa sai fitar da wani sihirtaccen kamshi takeyi mai masifar dadi da jan hankali sosai taji dadin jikinta ta fito ta saka wani sakalken dogon rigan material mai kallon purple hula ash ta saka sosai ta haska kamar ba ita ba,kamar ka saceta ka gudu,sai lokacin ta kwashe kayan data zubar tana gudun Ammi ta shigo ta samu kayan a haka,kai tsaye dining ta wuce sakwara ne akayi da miyar egusi,kad'an ta iba a plate ta zauna ta soma ci a hankali dan wani irin masifan yunwan da take cinta abun ba'a cewa komai,ga gidan duk ya cike da baki dan yau sora kwana biyu ne biki,kara b'angaren Ammin shine ma ba mutane sosai, da sallama ya shigo parlon amma in ba kana kusa da shi ba sam ba zaka ji meya fada ba ,da sauri ta ajiye spoon din hannunta taso tana ansa sallaman tare dayi masa sannu da zuwa.idanuwansa ya runtse da karfi yana kokarin calming kansa down dan yana son ya cika umarnin da Ammi ta basa,amma ya rasa dalili yarinyar yarda kasan Mayya haka take sata barinsa ko kadan.cikin cool voice tace"Yaya ina wuni sannu da shigowa.kana son wani abunne?"layan ta fada tana tsuresa da idanuwanta masu matukar haske da suka kara fayau saboda gajiyan data kwaso...yarda Kasan da dutse take magana bece komai ba sai kallon Ammi yakeyi dake fitowa daga bedroom dinta da alama itama wankan tayi dan rage gajiya,kai tsaye dining din ta karasa ta zauna kafin tace"sai kace wani kurma? Ina kanajin kanwarka na gaisheka".bece komai ba ya karasa Dining din zuciyarsa na bugawa ya duka har kasa yace"ina wuni Ammi,dazu na shigo bakya nan,na kira wayanki kuma ba'a dauka ba".ansa gaisuwan tayi kafin tace"wayan na mota,na kai Layan lalle ne da gyaran kai,kasan in ba zuwa nayi ba nayi tsaye a kanta ba tsayawa zatayi ba shiyasa daga office na wuce can kawai".wani malolan bakin ciki ya tsaya masa a zuciya yanzu wannan y'ar iskan yarinyar ce katuwa da ita ace sai an kaita lalle da wannan bakin Hannun nata dan shi bega amfanin lallen bama kanma da askesa akayi kowa ya huta amma shine sai an wani rakata kwafa kawai yayi yace"to sai anjima"...Allah ya kaimu kawai Ammi ta fada ta soma cin abincinta ko kuma kallonsa batayi ba,sai bayan ya fita ta kalli Layan tace"kada kizo kici Abincin ki tsaya kina kallonsa kina b'atawa kanki lokaci yanzu inyi maganinki a gidan nan".A sanyayen ta karaso dining din gaba daya ma Abincin ya fice mata a kai kasa ci tayi daga karshe ganin Ammi tabar dining din itama ta fice kawai ko zatayi sanyi a zuciyarta.... *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 31 "Look Ihsan duk wani abu da kike tunanin zaki iya bazai dameni ba,haka tsarina yake bana komai bana party ina na baki duk wani abu da kike bukata? Damuwarki ne kiyi ko kada kiyi is none of my business abu d'aya na sani Billah babu Inda zanje" be jira cewarta ba ya kashe wayansa yana sakin siririn tsaki,Tab'e baki Jabeer dake kwance a bed yayi cikin cool voice yace"ina dalili harka da mata? Kana zaman zamanka yarinya ta nemi juyaka,wannan ne abu na karshe da bazan iya jurar dauka ba".Tsaki Lamin ya kuma saki tare da cewa"mata sha'aninsu ai sai su,at all ni bana son hayaniyar nan amma ta matsa sai naje wani program, ta barni ma inji da tarbar bak'i na goben nan,lokaci ya kure kuma"....wani wawan Kuka Ihsan ta saki kamar wacce aka aikowa cewa uwarta ta mutu hada daura hannu bisa kai tana gunjin kuka da duk wani effort nata har wani shidewa takeyi,cikin sauri Husna da Yayarta Jamila suka turo dakin suka shigo dukkansu a rude suna tambayarta ko lafiya,hannu ta saka ta zare daurin head din da aka mata tana kokarin zare gown din kalar ash colour da aka gama mata shirin tafiya party din.saurin rike rigar Aunty Jamila tayi ta zazzaro ido tace"ke bansan isakanci meye haka kikeyi? Kinsan nawa aka kashe a wannan shirin da aka maki?.komai ace ba zaki bishi a hankali ba Ihsan Kuma rushewa tayi da kuka tana cewa"Aunty wai bazaije ba,wannan wanne irin abun magana yake son janyo mun ga kawayena I can't take it any longer wallahi Aunty"wani siririn tsaki Jamila ta saki wani haushi na kuma kumeta tace"to kimin shiru wallahi,danni ke kike bani ma haushin ba kowa ba,dama tun a waje zaki rinka lalata mana aiki to ba haka akeyi ba,kici gaba da shiri I assure you Lamin zaizo party din nan bana son sakarci"bata jira cewarta ba ta juya ta fice daga dakin abunta.sulalewa a gefan makeken sofa bed daya kawata dakin nata tayi hawaye na kuma wanke fuskarta da tasha make-up.....k'asa yayi da kansa ya kasa cewa komai,a tsawace Momy ta kuma kallon Jabeer tace"to in ma kai ke hure masa kunne da rashin tarbiyarka to ka fita a hanyata,danni wannan shiru shirun naka da rashin kunya wai baka son aure to ba yarda zanyi ba wallahi"ta kuma juya kallonta kan Lamin tace"idan na isa baso kakeyi ka walakantani ba to maza ka tashi ka shirya kaje auren nan ,tunda ba auren dole bane,gacan su Muhibba sun shirya"bata jira ansarta ba ta fice tare da buga masu kofan..Murmushi mai kyau Jabeer ya saki lokacin da suka hada ido da Lamin da gaba daya mood dinsa ya canza na maganan da Momy tawa Jabeer din,at all baya jin dadin yarda suke mu'amala a gidan.mikewa Jabeer din yayi yazo yana Dan bubuga shoulder din Lamin yace"guy wallahi ka tashi mu shirya kafin Mommy tayi band'ashenmu a gidan nan,especially ma ni"ya kare maganar yana dariya tare da zare T-shirt din dake jikinsa Wanda be dade da sakawa ba,take fara tas singlet dinsa ta bayya ya soma kokarin shiga wanka..mikewa Lamin yayi shima dariya na kubce masa dan yasan dalilinsa ne Jabeer yace zaije wurin,kuma kullun bai taba nuna abunda mommy take masa ta dameshi ba.kai tsaye dakinsa ya wuce dan ya shirya.....tura baki kawai Layan keyi dake tsaye fuskarta tayi wani irin fayau sai sheki takeyi jikinta kuma na fitar da wani irin sihirtaccen kamshi mai tsayawa a zuciya.kamar zata saki kuka take bin Basma da Muhibba da kallo ko wacce taci ado a cikin Sabon dinkin da Ammi tayi masu sosai dinkin atamfar ya zauna a jikinsu."kinga wallahi mu dai zamuyi tafiyarmu karshenta sai dai ki biyo motar su Yaya Lamin da Yaya Jabeer,dan su Yaya Jafar dukkansu basa gidan nan"Basma ta fada da alamun kosawa.Muhibba ta cabke da fadin "kara dai dan su Aminata da Jalila su Asma'u tun tuni sun tafi" wasu ne daga cikin cousins sister's dinsu da suka zo bikin....tab'e baki Layan tayi kamar zata saki kuka cikin deep and her sweet cool voice tace"dan Allah yanzu fa nake shigowa a gidan nan,ga gajiya da bacci na kwaso sai kace wata wacce za'awa aure ba Hutu"..."to Yaya Lamin kam zaice maki ya gode da safe kam insha Allah,dan haka mu kinga tafiyarmu"kafin ta ankare sun bar parlon Umman,Wanda gudowa tayi dan ta samu ta dan rage gajiyan data kwaso ta rasa duk gyaran menene haka Ammi keta faman yi mata ina dalili ko hutawa da zuwa IT dinta kwana biyu an hanata"...daga sama har kasa Umma ta kalleta kafin tace"inaga ke kin cire kanki daga jerin yaran gidan nan ko ?bana son tashin hankali da neman magana Layan,ki wuce ki shirya kibar gidan nan yanzu"...ji tayi inama kasa ta bude ta shige ciki ta boye saboda gajiyan data kwaso kuma tasan tunda Umma ta saka baki tayi kad'an ta gujewa zuwan nan"kasa karasa shigowa tayi ganin Ammi na shigo parlon da sallama ga kaya a hannunta a Leda sai wata y'ar budurwa tana biye da ita,gaisawa sukayi da Umma kafin tace"Layan maza kije ki kuma watsa ruwa ga mai kwalliya nan zata dan gyara maki fuska kiyi sauri Yayanku na jiranki zaku wuce,kowa ya tafi bana so kuma a fassara rashin zuwanki ta wani fuska"kamar wata doluwa haka duk ta bisu da kallo to amma bata da wani zabin daya wuce bin umarnin Ammin Wanda haka Umma ta kuma jaddada mata shi murmushi ta mayarwa mai kwalliyan daketa mata tun dazu kafin su wuce ciki,cikin kasa da minti arba'in Layan ta fito d'as cikin hadaddiyar lite blue wedding gown dinta wacce ta fitar da shape ko ina kamar an zanata a ciki Dan kugun nan yayi carab.kasan rigan kuma a bude,white head aka daura mata daga hannuwanta har wuyanta duka gwalagwalai ne da Ammin ta kawo aka saka mata,plate shoe white shima ta saka ga fuskarta da yasha lite make-up ba hayaniya ko kadan ya kuma fiddo da tsananin kyawunta,masha Allah shine abunda Ammi da Aunty Amarya ke fada lokacin da suka fito parlo gaba daya ko ina ya dauka wani kamshi da Layan din ke fitarwa ta haska parlon gaba daya ta fito a amaryarta sak.hannuwanta Ammi ta kama sosai cikin nata ta fito da ita compound din gidan tana gwada number Jabeer,A sanyaye ya d'aga wayan Wanda tun dazu yake zaune a parking lot yana jiran kiran Ammi,tun dazu ta tsayar da shi hakan yasa Lamin shima ya zauna a motan suna jiran Ammin.A kasalance yace"ina parking lot Ammi".bata kuma cewa komai ba taja Hannun Layan ta karasa wurin.kamar wani statue haka ya kafe Ammi da ido kamar yaga sabbin halitta ganin ta riko mace zuwa wurinsu,bai wani kalleta ba bare kuma ya gane wacece.sakin baki ya kuma yi lokacin da take mika masa Hannun Layan tana fadin"ga y'ata nan amana Veer aje lafiya a dawo lafiya a kulamun da ita kamar ina wurin,idan kaci amana kuma Amanar Allah zata cika Jabeer,hannunka hannuna zaka dawo mun da y'ata idan an tashi.tunda suka taho Lamin ya kafeta da ido yana jin zuciyarsa na tsananin bugawa ya soma karanta innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ya soma karanto sunayen Allah ,a hankali yaji zuciyarsa na sauka yana kuma dawowa natsuwarsa dake neman kaura dashi ganin wani irin kyau na musamman da Layan din ta masa....Layan kam manya manyan idanuwanta Wanda suka sha ado da kwalli ta d'aga tana k'arewa Jabeer kallo Wanda tuni kamshinsa ya cakude da nata ya bada wani kamshi na daban.sanye yake da wata bugaghiyar shadda sky blue sosai ta haska farar fatar jikinsa,Riga ne da wando,rigan iya gwaiwa da gajeran hannu sai wani azababben aikin hannu data sha daga Rasheed Makera fashion Design Wanda suka san aikinsu.hula ta zauna d'as a kansa kamar danshi aka yota a Hannun hagunsa agogon Rolex ne daure wacce ta lashe kudade da yawa sai kyalli takeyi,kafarsa na sanye a half cover na maza masu azabar kyau.kamar Ammi ta daura masa mutuwarsa haka yaji lokacin data saka masa Hannun Layan a nasa kafin ta wuce tana masu Allah ya tsare,yana ganin ta wuce yayi saurin sakin hannunta a gaggauce yace"ki wuce muje ko kuwa na tafi na barki a nan sokuwa kawai". *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 32 Cikin mutuwar jiki tana kuma kallon fuskar veer din ta shiga motar ko lura da irin kallon da Lamin ke mata ma batayi ba,tafiya ya zama so silent kowa da abunda ke damunsa musamman Veer da yake Jin duk motar ta matse masa gaba daya duniyar tana jujuya masa as if Layan akansa take zaune haka yake Jin takaicin kasacewa da ita inuwa d'aya a haka har suka karasa wurin program din.lallai Ihsan yar gata komai a wurin yaji kai kanka idan kasan matsayinka be kai ba bama zaka fara dosar wurin ba,wani irin decorating wurin sukayi kamar ba za'a bar wurin ba,Amarya na mota har lokacin bata fita ba tana jiran karasowar Lamin.kamar an sauke mata wani lodin kayan data dauko haka taji tare da sauke sanyayyar ajiyar zuciya lokacin da Lamin yake fitowa daga gaban motar Veer yayi mata matukar kyau sai dai fuskarsa a daure Babu fara'a ba kuma zaka iya gano wai wani abu na damunka ba.tuni wurin ya dauka da hayaniya aka saki kida na tarbar Amarya da angonta...cikin kufuluwa Jabeer ya juyo bayan motarsa in da Layan take zaune yace"hala Jira kike nazo na dauke ki?let me tell you idan ma kin fita in kin so kibar wurin get out"ya fada a tsawace Wanda yasa Layan zabura da sauri har tana niyar kifowa daga motan ta sauke kasa da sauri tana rarraba manya manyan fararen idanuwanta Wanda kwalliya ta Kara fito dasu ras.wurin ba kowa hakan ke Kara tabbatar mata da kowa ya shiga dakin Taron kenan.wurin da suke babu wadatuwar haske sosai saboda parking lot ne,hakan yasa ta danji tsoro cikin sauri ta koma side din da Jabeer yake tana matse rigarta da kyau kamar zata saki kuka tuni ta saki wannan shagwab'ab'iyar fuskar tata wacce bata rabo da koke koke da shagwaba sak ta koma Layan din Ammi .kafin kace me hawaye ya taru a fuskarta,duk da a cikin duhu suke hakan bai hanata ganin irin azabben kallon tsanar da Jabeer yake jefa mata ba,cikin rawar murya tace"Yaya tsoro nake ji"kuma kallonta yayi ko kad'an beji mamaki ba Dan yasan wannan kad'an daga iskancinta ne da kuma rainin wayanta to shikam bazai dauki wannan ba,sa'arta d'aya da Ammi tace amana amma billah da sai ya kulleta a wurin yaga ko mutuwa zatayi.beko kulata ba ya rufe motarshi ya soma takawa cikin sassarfa irin takun irgarman namijin da yake jinsa ya isa ya kuma kai tsaiko ga wani irin fitinan kanshi dake baibaye wurin gaba daga.hannu tasa ta d'an tattare gown din jikinta ta bisa a baya harda d'an gudunta saboda tazarar da ake samu a tsakaninsu kuma sam ba zata iya wannan saurin da yakeyi ba...gaba d'aya holl din ya natsu har an fara gabatar da program mc nata bayani.kamar fitowar farin wata daga sararin samani haka suka dauki idanuwan dubban mutanan dake wurin .tuni kallo ya koma garesu wani sanyayyen kyau kamar dansu aka tanadi Taron haka sukayi Yana gaba tana biye dashi a baya daga gefansa kad'an hakan sai ya bada wani abun dabban.ganin idanuwa da yawa ya kuma linka tsoron Layan Sam bata Saba zuwa party ba bare kuma har ta fita babu hijabi a jikinta,ji tayi kamar gaba daya mutanan duniyar sun taru a kanta ne ,tuni siririn hawaye sun soma silalowa akan kyakyawar bak'ar fuskarta wacce tasha sanyayyen ado ,tuni ta manta da Wanda take tare a hankali ta kuma matsawa jikinsa ta zuwa dogon hannunta daya k'awatu da Jan lalle da bak'i ta zurashi cikin na Jabeer ta kuma matse hannuwan nasa sosai cikin nata,har jikinta na neman fara rawa rawa.rintse idanuwa yayi da matukar karfi lokacin da hannuntaa ya sauka a cikin tattausan nashin hannu.lokaci daya ya ware idanuwa shi tas suka daukar masa hoton fuskarta tana mashi wani irin kallo,kallon Idi cikin Ido,yasan Layan farin sani tun tana zanin goyonta bashi da shamaki a halayyarta tar tar suke a kansa a kuma hardace kamar yarda ya hardace ayyukansa na yau da kullun .tunda suke a duniya bata taba masa irin wannan kallon ba Mai wuyar fassaruwa kallo ne da take masa na rashin madafa,rashin garkuwa,kallo ne dake masa tuni da cewa itadin amanarsa ce wacce Ammanshi ce ta bashi amanar lokaci daya fuskarta ta juye masa zuwa ta Amminsa sak da sak,ga kallon dake nuna masa a yanzu ta mance da kowa a wurin bata kuma ganin kowa sai shi,shine garkuwanta kuma abun dogaronta a wurin.tuni Layan ta kuma takurewa ta matsar da jikinta zuwa nasa jikin Dan samun kariya daga masifaffan kallon da mazan wurin suke mata rakiya da shi.sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tuni bugun zuciyarsa ya sauya ya kuma Kara dadda sauti,bece komai ba sai hannunta da yaja da d'an sassarfa ya soma nufar wurin zama in da bayawaitar idanuwan jama'a.ido suka hada da Lamin ya sakar masa wani sanyayyar murmushi duk da Yana Jin wani nauyin abu da yazo ya tare masa makoshi ya kuma danne masa zuciya.sai dai abun ya masa dadi yarda Jabeer bai hantari Layan ba ya kuma zama bango abun jingina a rayuwarta,shi kansa yasan hudubar Ammi ya tuna amma daba haka ba,da yanzu an kwasheta a tsakiyar holl din yayi rugu-rugu da ita,haka yake fata da buri kuma kamar a ko yaushe da Jabeer kan iya tsayawa a rayuwar Muhibba da Basma dasu Asma'u yaran Ummi haka yake fata yaga Jabeer yayi tsaye akan duk wani lamurran rayuwa na Layan Yana fatan ko bayan ranshi Allah ya ansa addu'ar nan...suna isa bayan ya tillar da hannunta har tayi taga yaga zata Fadi sai kuma ta tare kujeran dake gefan tayi mata garkuwa .cikin silent voice din san nan da murya Mai kama da gargadi yace"to uban meye ya kawo ki wurin Nan ba? Kinsan ba zakiyi iya zama ba kika soma ? Na fada maki kuma karki kuma kuskuren yin garkuwa da ni ,ba zaki taba samun wannan karar daga gare ni".kalaman Jabeer da masifarsa babu bako a cikinsu a wurinta amma sai take Jin hakan bai mata ba,na yau Sam bata ji dadinsa ba,kafin ya sake wata magana kuma ta saki Siririn kuka.a harzuke yace"ko kimun shiru ko na ballaki na zubar da abanza a wurin nan idiot kawai".jikinta har rawa yake ta samu wurin ta zauna,sosai tayi nadamar zuwa wurin Nan Dan danan kafin a kasarasa taron wani irin zazzafan zazzabi ya rufeta har hakoranta haduwa sukeyi...lokaci lokaci yake kallonta kafin a tashi wurin kawai ya fizge hannunta suka fice ta baya.har kofar part din Annie ya rakata bece komai ba ya wuce part dinsu Dan Sam ji yakeyi kansa ya masa wani irin zafi ga zazzabi dake neman rufesa.......Tun safe gidan ya soma daukar harami ko ince unguwar gaba daya .Ammi ce data ci ado cikin wani danyan leshi sai rawa yake,ta dauko atamfar super Holland data gama haduwa ta dinku take tsaye akan Layan dake dukunkune cikin duvet,time ta kuma kallah d'aya saura ta Gani,hannu tasa ta janye duvet din tare da cewa"yi hakuri Layan tashi ki Saka kayan Nan sai ki kuma Shan magani feature Dr a kwance,ae naji zazzabin ma ya sauka".mikewa tayi sannan ta karbi kayan daga hannun Ammi ta mike ta zare towel din dake jikinta ta soma shirya tun daga tasasun undies din da Ammin ta bata,sosai tayi matukar kyau cikin atamfan duk Wanda ya kulleta so daya zai so ya kuma a wannan lokacin.duk da babu makeup a jikinta wani sanyayyen kyau tayi...ras angwayen suka fito cikin shigar shadda white colour with brown sosai sukayi kyau komai nasu irin daya kai kace twins ne.jiki a sanyaye Jabeer ya Kalli Lamin kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,kawai tun jiya gaba daya yake Jin like is not him.hulan shi kawai ya dauka ya wuce mota,saboda sun kusa makara ko Yan gidan basu gaisar ba suka wuce babban masallacin gidan in da a nan za'a daura aure... *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 33 Kamar ko yaushe kuma kamar kullun masallacin a cike yake sai dai wannan karon yasha banban dan duk wasu danginsu na nesa dana kusa suna wurin ga manya manyan k'asa y'an kasuwa da dai sauransu taro ne daya tara manyan mutanan da basu tab'a zato ba.kallon kowa Jabeer yake yi musamman General wato mijin Ummi shima da mutanan sa ga kuma manyansa na wurin aiki da abokanan aikinsa,wara idanuwa yayi sosai ganin Ahmad,Ahmad babban abokinsa ne kut da kut wani lokacin ko bacci baya rabasu course ne ya fita dashi ko jiya sunyi waya amma sam bai sanar masa yana dawowa ba,sallah aka fara gabatarwa kasancewar kowa yasan da daurin auren yasa mutane zama.anan akayi shela aka soma daura aure..kamar statue haka Jabeer ya tsaya Yana sauraren sunan da ake fada ,tunani yayi ko mai shelar beji daidai ba,sai kuma ya Kara Jin sunayen har cikin tsakiyar kansa.An daura auren JABEER ABUBAKAR SADEEQ da amaryarsa MARYAM ABUBAKAR SADEEQ (LAYAN) sai LAMIN AHMAD tare da amaryarsa IHSAN MUH'D akan sadaki naira dubu dari bibiyu lakadan ba ajalan ba,shi da Lamin bansan waye yafi shiga rudu ba a wannan lakacin,tsoron Lamin dama Jabeer ne mijin da Abba ya zab'awa Layan ya akai sukayi wannan aikin bayan sun san tashin hankalin dake baibaye da hakan Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai ya samu bakinsa da maimaitawa Yana d'aga hannu da k'yar Yana ansa gaisuwar masu yi masa Allah yasa alkhairi Yana yaken dole...Jabeer Kam wani butum butumi ya zama ko kad'an ya kasa motsawa daga in da yake,shi kansa bazai iya fada maka a wacce duniyar yake ba,Abba ne ya karaso ya Saka duka hannuwansa duk biyun ya dafa kafadunsa da suka gama jikewa da zufa jagab ya d'agasa Yana sakin murmushi tare da fadin "yau burina ya cika Jabeer,Allah yasa alkhairi ya Baku zaman lafiya karka damu kanka zan maka bayanin komai kuma insha Allah watan wata rana Jabeer zakayi alfahari da wannan auren za kuma ka gode mun ko bayan ba raina "kallon bakin Abba kawai yakeyi amma sam kunnuwansa duk irin hasashen da yake yowa da kuma karfin ji da Allah ya masa ya kasa jiyo ko fahimtar abunda Abban ke fada kallonsa kawai yake yi Yana Jin wani irin mumunan tashin hankalin dake rubtowa a bisa kansa yarda kasan am dauko duka duniya an daura masa a kai haka yake Jin kwatankwacin nauyin da kansa da kuma idanuwansa dake neman rufesa sukai masa,a hankali ya tattare busashen yawun da yayi saura a bakinsa ya had'a tare da lasan tattausan lab'ab'ansa da suka yakune suka bushe a cikin sakanni sannan ya lumshe Dara daran idanuwansa Wanda suka sauya launi zuwa launin ja suka kuma Kara girma alamar mamallakinsu yayi nisa da duk wata natsuwa daga gangar jikinsa da ruhinsa,Abba ya damka hannunsa ana Lamin sannan ya wuce cikin jama'arsa .shidai Jabeer tun daga wannan lokacin bai furta ko kallama d'aya ba,haka zalika baya fahimtar komai ake cewa,Jin kansa na neman tarwatsewa yasa ya silale yayi cikin gida zuciyarsa na lugude da fama da madaukakin tashin hankalin da bai taba shiga ba tsawon rayuwarsa....sakin k'walbar turaren hannunta tayi take ta fad'i k'asa ta tarwatse ta fashe turaren ciki kuma ya malale,da kallo kawai take bin su Muhibba da ko wanne a cikinsu yayi cirko cirko,cikin dakusashen murya tace"kunji Mai kunne na ya jiyo man kuwa Basma?"Layan ta kare tambayar tana tsaresu da manya manyan fararen idanuwanta Wanda kwallin Kajol ya Kara kawatasu da addo na daukar hankali .jinjina kai dukkansu y'an matan dake d'akin suka yi kafin Asma'u tace"an daura aurenki ne da Yaya Jabeer yau burinki ya cika ".wara idanuwa tayi kamar Mai son Karin bayani sai kuma wasu sanyayyen hawaye suka soma gangarowa akan kyakyawar fuskarta,dandanan taji wani sanyi na ratsata,irin sanyin data dade tana farauta da nema,kamar an zare k'aya a abu haka taji wani malolon kullutu daya dade dayi mata wurin zama a zuciya Yana dargajewa tuni ta nemesa ta rasa,ba shiri ta tafi sujudur shukur ,sijjadan godiya ga Allah buwayi gagara misali Mai cire rayayye a matacce matacce a rayayye,a sujadan kuka ya kwace mata,cike da kallon tausayu duk suke binta kafin Aminata da Muhibba suka dagota suka zaunar da ita a gefen bed.....Annie Kam Kabbara kawai take saki ta rasa in da zata Saka ranta,ta rasa meke gareta yau ta bayar raji Dadi,kukan farin ciki ta saki tare da cewa"ko yau Allah ya karbi raina ni maryama burina ya cika,Allah kai ka kaddara auren Nan,Banga ubanda ya isa ya hanasa wanzuwa ba,da Yan naki da Yan naso duka dai Allah yafi karfinku sai kowa ya rungumi kaddara yau dai Mai ciwon cuta da bak'ar kala ta samu mijin kera sa'a Ina Badiyya tayi kukan Jin kunya? Taki Allah ya so yau ga ranar mayar da murtani"duk hali irin na Annie kyauta ta dinga yi abunta har zannuwan sakawanta sai da ta bayar ta kuma bude kofar d'akinta baja-baja bata tsegumi wa kowa....."Ashe auren kuma biyu aka daura bana Lamin kad'ai bane"Hajiya Nana ta tambaya.tabe baki Momy Badiyya tayi wacce ta gama haduwa cikin tsadaden leshinta tace"auren cushe ba,to ko angon da amaryar yanzu suka San da daurin auren kamar yarda kuma kuka samu labari,ni dai can dasu gada tunda sauran cuta bata mak'alewa y'ay'ana ba"rike baki Hajiya Nana tayi sai kuma tace"to godai a zamanin mu ba'ayu haka ba,har Yan atamfofin nan da kayan shafa ake kawowa na fitar biki".Dariya Momy Badiyya ta saki tace"to namu auren dai daga maggi sai kuka,aini zanga yarda wannan drama zata kaya a gidan nan wallahi ".ko karasa rufe baki batayi ba khalifa ya shigo da gudu Yana fadin "Aunty Amarya,Aunty Amarya kuzo Kuga kayan Yaya Layan akwatina kawai ake safkewa daga manyan motoci wai kayan lefenta ne na aurenta da Yaya Jabeer"sak Mommy ta juya tana bin bayan khalifa da kallo sai ya zama kamar magana yake jefa mata ji tayi kamar wani Mayen karfe na janta har tana tuntube tayi waje cikin gate din gidan.mota hud'u ce,Ummi ce ta fito da few of her friends Wanda daka gansu kasan sunci sunsha sun kuma tada kai da nera dan tayi kuka a jikinsu boxes ne jere a tsakiyar tankamemen gate din gidan har 24 set biyu sai manya manyan bags guda biyu daka kallesu kasan tsadaddune ,mutane keta dauka ana shiga dasu part din Annie Dan anan ta tubure a kawo mata kada a kai wani wuri ayi sata,a Nan kuma tasa a tsakar gida a bude lokaci daya kowa ya Gani Dan tace rufesu zatayi a daki ba dalili a samu masu Yan hali a kwashewa Laya kaya.kowa sai dai yace Masha Allah a kayan ko Gold's kala hud'u ne a ciki Dandanan Annie ta bawa Ammi su ta adana kowa sai da ya jinjina irin kokarin su Ummi Babu Wanda ya taba tunanin Rabin haka Layan zata samu daga garesu a yanayin yarda auren yazo kai ko falle ba Wanda yayi tunanin za'a kawo mata.da k'yar Mommy Badiyya ta taka tabar in da take lab'e Dan kin fitowa tayi tasan tsab Annie zata fara yab'a mata magana da kuma habaicin data Saba,in kuma ta gaji kai tsaye ta kama sunanta. *Inga ruwan comments sai muci gaba da tafiya yarda aka Saba,idan naji shiru kuma zakuji shiru ,ahtou Dan ba zaku barni a gantale ba* *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 34 "Kiyi sauri ki shirya ki fito Abban suna parlo suna jiranki"Ammi ta fad'a tana mikawa Layan babban milk mayafinta wacce lokaci d'aya jikinta yai sanyi ganin da gaske yau kuma barin gidan zata yi,bata tab'a tunanin zataji wani abu ba idan ta kasance a matar Yaya Jabeer dai gashi daga jiya da aka daura auren zuwa yau kwata kwata ta kasa sukuni ta rasa inama zata Saka ranta.Mayafin ta karba kamar wacce bata da lakka sannan ta zira flat shoe dinta shima milk colour tabi bayan Ammi wacce tuni tama bar part din.Annie ce ta turo kofar da karfi tace"Laya zaman me kikeyi?kinsan mijin nan naki burkeken mota yama fishi tabbas amma kike nan kin shanyamu parlon Amadu kamar wasu gantalallu".kasa Layan kawai tayi da kai bata ce komai ba tabi bayan Annie wacce keta zuba kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tsananin farin ciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan aljanna....da sallama ta shiga parlon ganin Hajiya Badiyya a zaune yasa ta daure fuska ta dawo da baya ta rike hannun Layan a cikin hannunta taja ta suka shiga ta samu kujera ta hakimce.a kasa kusa da ita Layan din ta samu wuri ta zauna tanayin kasa da kanta wani hawaye na taruwa a idanuwanta.....Abba ne yayi gyaran murya ya Kalli Direction din da Jabeer ke zaune tamkar an ajiye gawa a wurin ,tunda Lamin ya janyo shi suka shigo da k'yar ya iya gaishe su ya zauna ya dukar da kanshi baya um baya um'um."Jabeer yau Allah ya nufa ka zama magidanci ,Layan dai kanwarka ce ka riketa amana ka kula da ita ,kai kafi kowa sanin condition dinta,kayi hakuri nasan mun maka laifi amma hakan shine kawai mafita da kuma cikar burin ko wannan mu,nasan bazan samu matsala da kai ba Jabeer ka kula bani da abunda zance maka bayan wannan,insha Allah Mamana nasan ba zaka samu matsala da ita ba ta kowacce fuska,Allah yayi maka albarka"jinjina kai kawai Jabeer yayi kansa a kasa cikin cool voice and deep yace"Abba Babu laifi tsakanin iyaye da yaronsu,duk yarda kukayi da rayuwata bazan biyaku ba Abba"Wani murmushi Momy Badiyya tayi kafin carab tace"to Jabeer adai rika kulawa,kasan yaran yanzu ba wani abun kirki suka iya tsinanawa ba an kula da yaro ya ya kare bare kuma wannan da uwarka ta Riga ta gama sakalkaltata,Allah dai ya rufa asiri amma kam akwai aiki gabanka"wani wawan kallo Ummi da tun safe tazo gidan ta soma jefar Momy Badiyya dashi kafin tayi magana kuma Annie tayi mitsi mitsi da Ido cikin daga murya tace"yau naga abunda ya ishe ni,Amadu ka kwaso wa kanka bak'ar tsiya,wacece wata Badiyya Allah ma tuba bare kawai .ki fita idona,bakinki ya fita akan jikokina idan ba haka ba kuwa ran uban kowa zai b'aci a gidan nan,wallahi wallahi zakiga tsiya zakiga rashin arziki,duk tsiyar da kike shukawa yau zanyi maganinta a gidan nan."kasa da kai kawai Lamin yayi bayan ya gama kallon Annie sai dai bece komai ba amma komai Momy zatayi uwa uwace dai baiji kuma dadi ba Sam..Abba ne ya Kalli Daddy yace"y'allabai ko kana da abun fad'a ne,ga yaran naka?".Murmushi kawai Daddy yayi yace"ai ka gama fadan komai Yaya Allah yayi masu albarka baki daya ya basu zaman lafiya,shima Lamin din ya kamata yau yaje gida shikenan anyi an wuce wurin,Allah kuma ya cida Yan baya"kowa ya ansa da Ameen......wani irin kuka Layan ta saki lokacin da Abba ke kokarin sakata motar da sauri ta rungume Abba iya karfinta tace"Abba Dan Allah ni dai zan koma wurin Ammina,ni dai na fasa tafiya Dan Allah"wani irin kuka takeyi Mai ban tausayi,barin da taga Basma da Muhibba na tayata kukan Aunty sai lallashinsu take yi....tab'e baki Annie tayi kafin tace"nifa bana son sanabe da shiririta Ahmadu kasa yarinya tabi mijinta su wuce ka tsaya wani lallab'ata salan Yan hassada su fito,dama haka jiya ta tara narka narkan mata kamar aladu,kai Badiyya wallahi akwai shahararriyar tab'ab'iya"ta kare zancen tana dariya.tura baki gaba Muhibba tayi bata dai ce komai ba..Layan dake kusa da Lamin ta kamo hannunsa tana cewa"ni dai Yaya a barni nan".murmushi yayi ya leko ta gefan Abba yace"be the best wife you can be lil,kiyi biyya, wishing you a peaceful marriage life Dear"a hankali ya zare hannunsa be kula kowa ba yabar wajen cikin sauri.Abba Kam mota kawai ya Saka Layan ya rufe,ya dafa kafadar Jabeer yace"kuje kawai nazo gidan".jinjina kai Jabeer yayi Wanda ya zama kamar wani kurma ya masu sallama ya zagaya ya shiga motan be kula Annie daketa washe baki ba yaja motar yabar gidan..."to Ahmadu yaushe zanje? Kasan Laya sai da rarrashi kafin ta Saba gashi ba cikekken lafiya gareta ba".sunkuyar da kai Abba yayi yace"idan ta kwana biyu sai kuje dasu Basma Annie"rike haba Annie tayi sai kuma tace"shikenan daga Laya ta tafi zaka fara hadani da wannan gandama gandam yayan naka da basu da niyar aure? A'a ni maryama a barshi kawai Aliyu ya kaini,yo Ina ni Ina wannan yaran"bata ce komai ba tayi gaba abunta tana surutu kasa kasa.Ummi da Ammi da Aunty bangaren Umma suka nufa zaune suka sameta a parlon tana kallon Sunna TV da sallama suka shiga,da fara'a sosai Umma ta tarbesu Ummi tace"ba zama nazo yi ba,na biyo ne inji meya hanaki fita rakiyar y'ar tawa?".murmushi sosai Umma ta saki sai kuma tace"to Ina ruwan uwar miji da rakiyar mata? Ni ta 'Dana nake yi Kam"...Dariya dukkansu sukayi,mikewa Umma tayi ta cika masu gabansu da kayan drinks da abinci sumata fira abunsu......Tunda suka shiga motan wani takaicin da kunci from no where Jabeer ya soma ji Yana tokare masa zuciya har d'aci d'aci yakeji a makoshi.a matukar tsawace yace"Billah idan baki rufemun wannan Dan iskan bakin naki ba zakiga karshen iskanci da munafurci a motar nan.shashasha"rasa abun fad'a yayi ya Saka dayan hannunsa yana cakuda sumar kansa ya danna motar da gudu...tsoro sosai ya shiga Layan lokaci daya,irin tsoron da bata taba ji na Jabeer ba tuni ta takure wuri daya tana rarraba Ido cikin mayafi......tunda suka shigo unguwar tasan unguwar na masu da shi ne,a jikin gate din wani madaidaicin gida ya tsaya Yana horn,gateman yazo ya bude Yana gaishesa suka shiga gate din zai iya daukar mota biyu zuwa ukku .parking yayi be kulata ba ya bude motar ya fice abunsa da sauri itama ta bude tabi bayansa, entrance din gidan yaje ya Saka key ya bude ya suka shiga,maa Sha Allah gidan well furnished three bedroom with two parlo sai kitchen da dining.sosai gidan yayi matukar kyau yadau hankalin Layan tsarin gidan kawai ta kallah tasan aikin Ammi ne,a nan first parlo ta rakube bakin kofa wani tsawa da Jabeer ya mata bata San ta mike ba da sauri hawaye na rige rigen saukowa a idonta murya na rawa tace"Ai bansan Ina ne d'akina ba...kallon tsana ya watsa mata yace"see duk in kika kuskura naga wannan shegen kafan naki Mai kama da tsintsiya a sama wallahi sai na karyaki.up stairs nawa ne,ki kare ratuwarki a kasa".be Jira cewarta ba yayi sama abunsa one bedroom ne a sama da tailet sai babban parlo a can.komai dama choice dinsa ne aka zuba a sama yayi wani irin kyau so maa Sha Allah..... *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 35 Da asuba a sanyaye yake fitowa daga Saman kamar baya son taka k'asa kamar zai wuce sai kuma ya Kalli corridor in da jerin well furnished two bedroom ji yakeyi kamar ya wuce ga kansa dake masa wani irin ciwon Dan kwana biyu kenan ko bacci baya yi,karasawa yayi babban ciki ya bude a Yana leka kansa a ciki,Jin motsin ruwa a bathroom yasa ya gane harta tashi kenan,siririn tsuka yaja sannan ya rufe mata kofan ya wuce masallaci.....Layan Kam tunda ta karasa sallan asuba take nan zaune akan sallayan tana lazimi ga wani irin juyawa da cikinta yakeyi gaba daya yunwan ta gama galabaitar da ita har bata gani da kyau.a daddafe ta samu tayo wanka tazo ta bude press kallon kayan kawai takeyi dan babu abunda babu a ciki Wanda zata bukata inner wears ta xaro ta Saka ta samu wata saukaken dogon riga ta Saka marar nauyin lite blue turare ta samu ta fesa ta dauki hula tana tura dogon gashinta a ciki Wanda tunda Ammi ta kaita saloon bata kuma yarda ta taba gashin ba,gefen 🛏️ ta dawo ta zauna tana wani kyabe baki kamar zata saki kuka,.mikewa kuma tayi ta zura slippers dinta tayo hanyar waje.kad'an ta bude kofar ta leka babu kowa sai karar Ac a parlon ,a hankali ta janyo kofan to make sure batayi wani sound ba tasan yanzu Yaya zaice tayi hauka wani irin zazzaro manya manyan idanuwanta tayi waje a matukar tsorace ganin Jabeer kwance sanye da jallabiya fara k'yal sai tashin kamshin turarensa perlon yake yi gaba d'aya...cikin cool voice yace"kici kanki ,idan baki daina kallonta haka ba sai na kwakwale wannan idon".da sauri ta marairaice tayi k'asa da kanta kamar zata fasa kuka cikin wahalliyar muryarta da yunwa ta gama cinyewa tace"Yaya wallahi yunwa nake ji".ta karasa zancen siraran hawaye na zubowa a fuskarta.bude idonsa daya dan canza launi yayi da sauri ya ware su kanta sai kuma ya mike zaune gaba daya Yana jifanta da wani mugun kallon with much expression a fuskarsa calmly yace"to yi maza zoki cinye ni kinji".duk da kallonta b'ata masa Rai yakeyi Amma haka ya tsureta da Ido cikin takaici yace"let me make it clear to u,idan kika kuma Saka ni a sabganki gidan nan,dama ki fara neman gidan ubanda zaki buya billah zan kaklaryaki in zubar,in kuma ni na zama kitchen sai in Gani".turo Dan karamin bakinta tayi sai kuma ta rushe da kuka gaba d'aya kamar wacce aka aikowa da Ammi ta mutu,yunkurawan da Jabeer yayi yasa tayi Shirin kwasawa a guje sai kuma Jiri ya ebeta ta zube anan wajen.tsaki ya saki beko kalleta ba ya haura sama Yana Jin idan ya tsaya wurin zai iya illatata da shegen dukan da ba'a taba mata ba,lallai shi zata rikawa iskancin da takeyi a gida?in ko haka ne da matsala zama inuwa d'aya garesu ya haramta dan bazai dauka ba....da k'yar Layan ta ta dafa daya daga sofa ta parlon tayi wurin dining anan ta bude kofan kitchen, kitchen din babba ne sosai babu abunda babu a ciki sai karamin kofa a wurin tana lekawa taga store an jibge uwayen buhuhunan abinci da kwalaye babu abunda babu a store din.cikin sauri ta kunna gas ta daura karamin tukunya ta Saka ruwa kad'an kafin ruwan yayi ta ebi kayan shayi a cup,kamar Mai yunwa ta juye ruwan shayin ta kada ta koma dining ta shanye tas ta zauna tana sauke numfashi,ta soma tunanin tunda aka fara Shirin bikin nan bata wani ci abun kirki ba shiyasa yunwa ta kusa haalakata sai da taji ta dawo daidai sannan ta kuma komawa kitchen din.Irish ta dauka a bowl ta zauna ta fere ta kuma kunna gas ta zuba man gada a fan yayi zafi ta zuba kafin ya soyu ta hada egg tana karasawa shima ta soya egg din ta kuma hada ruwan shayi ta fitar da wormer 's din a dining.ta zauna ta cika plate ta hada ruwan Lipton ta soma ci a hankali tana tunanin ya rayuwa kuma zata sake juya mata ga kuma tunanin gida daya addabeta......fuska daure Jabeer ya dawo parlon ya zauna Yana pressing phone can dai yace"if you're done,Ina jiranki,mikewa kawai tayi ta iso gabansa sai tace"Yaya in ibar maka Irish din?"kallonta kawai yayi sai kuma yace zaki duk'a ko sai na shureki kin duka a dole?"b'ata fuska tayi ga kuma tsoronsa from no where dake kuma dirar mata,sai dai babu abunda ya ragu a soyayyar da takeji ta masa.ta duka akan kneels dinta tayi k'asa da kai.cikin dakakkiyar murya Jabeer yace"Allah yasa kina ji sosai,Dan wannan katton kunnuwan naki kada ace sun tashi a banza, firstly kisan ba hutu kika zo yi a gidan nan ba,idan kika karya dokata daya you will see the other side of me,which bana so mukau haka da ke,dama gidan nan kinsan kiyi harkarki ne,idan kin tashi jagolgolon girkin ki dama zakiyi iya ke kad'ai ne,bana son k'azanta da lalacin banza,ba wani Kato ko katuwar Yan aikin da zan bukata a gidan nan u will take all the duties since from gate to nan ciki in baki da nose max ki nemo tun wuri"saurin zare Ido Layan tayi tace"Yaya ai bana shara dust yayi yawa Asthma Dina zai tashi in ta wahala".wani banzan kallo ya mata a tsawace yace"kinsan kina da Asthma din kika aure ni,yar yarinya dake har kinsan aure?let me not repeat my self if not you will make your life a living hell a gidan nan Layan"ya kare zancen cikin cool voice.wani iri taji daya kira sunanta sai taji kamar duk duniya yafi kowa iya Kiran sunanta sosai hakan ya dauki a hankalinta tuno makarantarta kuma tace"Yaya school fa".bece komai ba sai kuma yace"idan kina cika duties dinki to zaki koma school,shima akan sharuddan da zan gindaya maki idan lokaci yayi,aikinki zai fara daga gobe.bana son tuna maki kuma"...jinjina kai takeyi sai a hankali tace"bani da nose max din Yaya"..ledan kusa da shi ya tura mata bece komai ba ya mike ya fita daga gidan dan dama ya shirya fita zaiyi.A hankali ta mike ta nufi dining ta dauki fork amma gaba daya taji abincin ya fice mata a kai rufewa tayi,ta mike da ledanta a hannu ta wuce bedroom dinta tana ji gaba daya duniyar ta mata ba dadi a stool na morrow ta zauna sai kuma ta turo bakinta sai hawaye sharrr sharr,tasa hannu ta goge tana kallon ledan data shigo da shi a hankali tace"ni da bama da lafiya ta yaya zanyi duk wannan aikin? "Tama kanta tambayar da bata da ansa a nan ta zauna tasha kukanta har ta gangaro k'asa a rug's na wurin bacci ya dauketa da tunanuka iri iri.....ba ita ta Farka ba sai gab la'asar da sauri ta Kalli agogo ta zaro manyan idanuwanta tana tura baki,ta wuce toilet wanka ta sake yi ta dauro alwala ta fito ta shirya sannan tayi sallah ta kuma fita dining kallon Irish din dake ajiye tayi ita bata San ya zatayi da shi ba kuma dole a haka ta zauna tana cinsa tana tura baki da k'yar ta cinye ta tattare kayan ta wuce kitchen ta wanke ta ajiye komai in da yake sannan ta fito parlon ta zauna a sofa tana karewa ko Ina kallo ga kadaici da kewa ya dameta ko waya babu a hannunta... *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 36 Kallonta kawai yake yi kamar Mai son gano abu ko kad'an beyi mamaki ba,girgiza kansa yayi ya karasa cikin bedroom din nata ya soma kiranta"ihsan,ihsan" Jin shiru yasa ya bubbuga pillown da take kwance da dan karfi sannan ta bude Ido tana kare masa kallo be bata change ba yace"Amma Ina ga tun asuba nace ki tashi kiyi sallah Kalli lokacin almost 8 na safe amma bakiyi sallah ba,haka kikeyi a gidanku?"wani irin turo baki ihsan tayi cike da masifa tace"Dan girman Allah Lamin let me be,ban taba ganin ango kamarka ba,Ina dalili ka tafi ka barni sai da na gaji na kai maka kaina sannan kuma bayan na kwaso gajiya kazo ka wani dameni ko karfe nawa ne ai dai dole nayi sallahn na gaji da irin walakantani da kake yi this is real you Lamin".wani murmushin takaici ya saki kafin yace"to komai zakiyi zan iya dauka Ihsan amma banda rashin sallah tunda gidan ba gidan kafirai bane,dama tun wuri ki ajiye wannan d'abi'ar ko kuma zakiga yarda zanyi maganinki a gidan nan."be Jira cewarta ba ya nufi kofa ya fita yana tunanin ta wacce hanya zai zauna da Ihsan.siririn tsaki ta saki kafin ta mike ta shiga bathroom ta hada ruwan zafi tayi wanka tare da alwala tana fitowa tahau shirinta ta tsuke cikin Riga da skirt na material Wanda suka kamata sosai ta murza dauri ga fuska tasha make-up tako Ina,sai a sannan ta kuma tunawa da sallah ta zura hijab tayi sallahn ta mike ta fita Dan yau kamar an kwashe mata Yan cikinta haka takeji don yunwa,kai tsaye stairs ta nufa tana kallon Lamin dake zaune ya lumshe idanuwa kamar Mai bacci Yana kallon sama tab'e baki tayi ta karaso ta zauna kusa dashi cikin cool voice tace"hey,Good morning ".bude lumsassun idanuwansa yayi Yana kare mata kallo bece komai ba ya Dan gyada kai kawai sannan tace"to nifa yunwa nake ji".wani kallo ya mata yace"to wa kike Jira ya shiga kitchen din"waro idanuwa tayi tace"ai Amarya bata girki beside bayan tafasa ruwan zafi ma billah ko indomie ban iya girkawa ba,bana son stressing kaina"da mugun mamaki Lamin ke binta da kallo sai dai bece komai ba ya mike ya nufi kitchen ruwa a flaks ya Iban mata a cup sannan ya soya mata egg ya dauko da break ya daura a tray ya kawo mata tana nan parlo tana danna waya.wani kallo ya mata kafin yace"dama kisan yarda zaki nema abunda zaki ci ,bazanyi nema a waje nazo kuma na kare a kitchen ba".wayoyinsa dake a kujeran ya kwasa yayi sama ko ansa thank you din da take fada masa beiyi ba ya haye stairs abunshi........tun Kiran sallahn farkon na asuba ta Farka wanka tayi tare da dauro alwala ta dawo ta shimfida sallaya tayi raka'atanil fajir tana ta zaune har aka kira asubahi sannan tayi sallah ,ta Saka Riga marar nauyi ta feshe jikinta ta turaruka masu Dadi ta soma gyaran dakinta sannan ta wanke toilet ta Saka turaren wuta ta fito waje tana kokarin Saka hulan kanta suka kusa cin karo da Jabeer Yana dawowa daga masallaci,ko kallonta beyi ba ya rab'a ta gefenta zai wuce cike da sanyin nan nata ta bude baki zatayi magana saurin d'agaata hannu yayi tare da cewa"karki cika mun kunne da wannan rashin natsuwar taki tunda asuba"be bata listening ear ba kuma yayi wuce warsa ciki.jiki a sanyaye ta karasa fitowa parlon.nose max dinta ta dauko ta Saka da bucket da mop ga tsintsiya da faka tana tunanin ta Ina zata fara kuma".tana ta tsaye tana kyab kyabta manyan manyan idanuwanta,kamar zatayi kuka haka ta taka tana kuma tina gargadin da yake mata a jiya,amma haka nan ta daure ta hau stairs din daidai kofar dakin da take kyautata zaton nan ne d'akinsa ta soma kwankwasawa a hankali gaba daya tsoro ya gama cikata kamar k'afarta ba zata dauketa ba,har sai da ta cire ran zai bude kofan tana niyar juyawa taji alamun tafiyarsa wani irin daskarewa a wurin tayi dana sanin zuwa wurin lokaci d'aya ya dirarta kamar zata saki fitsari,suna yin ido biyu ta lumshe idanuwanta da sauri ta soma ja da baya.shikam mamaki ne ya kashe sa gaba d'aya watau yarinyar nan dan tana Jin an daura masu aure har ta kuma rainasa kenen? Be isa ya Saka doka ta bi ba kenan Aiko zata gane kuranta,wani kwafa ya saki ganin tana yin baya yace"billahil Azeem idan kika gudu sai na karkaryaki a gidan nan ,uban me ya kawo ki nan?"...saurin zaro idanuwanta tayi ganin irin seriousness dake fuskarsa,da k'yar ta hadiye yawun daya taru a bakinta na tsoro tasa dogayen hannuwanta ta rike k'asa doguwar rigarta kwarai kamar zata b'alla ta kasa cewa komai sai girgiza kai da takeyi kawai....wani zuciyan ne ya kuma kume Jabeer yayo kanta bejira komai ba ya kwasa mata wani lafiyayyen mari cikin takaici yace"wato rainin har yakai haka tsakani na da ke,ni da gidana ban isa na Saka doka ba ki bi,ubanme kika ajiye a nan jarababbiya kawai, monster to sai dai kici kanki a gidan nan"...wasu hawaye ne masu zafi suka soma zaryar sauka a kuncinta wasu na bin wasu ga hannunta dafe da kuncinta Wanda sahun yatsunsa suka fito radau radau a jiki,kasa cewa komai tayi ganin Yana neman yowa kanta yasa tayi baya da gudu tare da sakin Kara tayi k'asa a garin tsallake stairs ta fad'i a wurin ta soma gangarowa harta karaso kasa gaba d'aya wani irin wahalalliyar Kara da bata fita sosai ta saki tare da cewa"wayyo Annie na wayyo Ammina mutuwa zanyi,bayana ya kare,Yaya,Yaya"....Jabeer dake tsaye ya kura mata Ido harya mance Rabon da yayi mata irin wannan kallon siririn tsaki ya saki wani takaici na kumeshi ganin da gaske ta kasa tashi yasa ya karaso wurin tare da cewa"gobe ma idan halinki ne gulma kya Kara hawa "hannu daya yasa ya d'agota ta saki Kara tare da mak'alk'aleshi ta fashe da kuka tana fadin"Yaya k'afarta ta karye wallahi bazan iya takawa ba wayyo Allahna "ta kuma sakin wani kukan,hannu yasa ya bige mata baki cike da takaici yace"kimun shiru ko inyi maganinki a wurin nan,sakaryar yarinya kawai".duk yarda yaso ya banbareta daga jikinsa kasawa yayi Dan riko tayi masa bana wasa ba,tsuka yaja sannan ya dauketa kamar yar baby ya wuce dakinta da ita,a gefan bed ya dungurar da ita Yana jefa mata harara ita kuwa bata San Yana yi ba sai aikin kuka da take yi,fitowa yayi daga dakin ,d'akinsa ya koma ya dauko man zafi ya dawo ya duka daidai k'afarta,kokarin janye kafar takeyi yaja tsuka fuska daure yace"idan na tafi ke kike da asara ba ruwana"be Jira cewarta ba ya fizgo kafar da karfi Murda kafar yayi ya gyara targaden data samu ya shafa mata man zafin ya mike ya fita,ransa fal takaici .hawaye mararsa dalili suka soma zarya akan fuskar Layan daga haka har bacci ya kwasheta.Jabeer Kam Yana fitowa ya dauki su tsintsiyan yayi shara yayi mopping har plates da ya Gani a ajiye duk ya wanke ya gyara ko Ina Dan shi ya tsani k'azanta be kuma iya zama in da take.sama ya koma ya sake yin wanka ya kwanta baccin gajiya. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 37 A hankali ta soma bude rinanun idanuwanta Wanda suka kumbura saboda uban kukan da taci soma zagaye dakin tayi kamar Mai bitar abunda ya sameta dafe kanta tayi tare da fadin"ash wayyo Annie na,so take ta tashi amma abun ya faskara kamar ance ta juya sukayi Ido biyu da Jabeer Wanda ke tsaye jikin kofar,siririn tsaki ya saki tare da karasowa ciki dawowarsa daga masallaci kenan,kamar Mai counting steps haka ya karaso ko kallonta baiyi ba ya janyo hannunta ya taimaka mata daidai kofar toilet din ya tsaya ya bude mata kofar a hankali tace"na gode"d'age kafadunsa yayi alamar ko in kula ya dawo gefen bed side drawer ya zauna Yana pressing phone dinsa tare da taune jajayen lips dinsa Wanda hakan ya dade da zama d'abi'arsa Yana ta zaune harta fito ba laifi tana takawa a hankali alwala tayo ,abun sallah ya shinfid'a mata ya ajiye mata hijab yayi gaba abunsa.wani sanyayyen murmushi ne ya kubce mata sosai taji dadin kulawar daya bata,ko ba komai ya nuna ita wani naauyi ce a wuyansa kuma da alama Yana kokarin ganin ya fita hakkinta,ba dan badan ba da tace ita ciwan ma alkhairi ya zamar mata,sai dai bata fatan haka,kamar kullun kamar ko yaushe yau ma addu'a ta samu kanta dayi masa sosai har fiyema data kullun,tana ta zaune kan sallayan ya shigo hannunsa dauke da takeaway da ruwa ya ajiye mata kusa da ita cikin kausasshiyar murya yace"ke kina jina"juyowa tayi in da taci karo da fuskarsa kamar jadarin gabas dake dab da tsinkewa da ruwa kasa tayi da kanta bata ce komai ba dai.cikin deep voice yace"zan fita,salan garin wannan rawar kan naki ki kuma turgude kafar,na maki alkawarin ba abunda zan iya maki,tunda rashin natsuwa ke damunki"be Jira cewarta ba ya fice abunsa duk da bataji dadin maganganunsa ba amma dai haka nan ta daure ta lallaba ta shiga bayi wanka tayi ta dawo ta Saka kaya marassa nauyi sannan ta zauna tana cin abincin daya ajiye mata cike da walwala da Jin Dadi,haka nan take Jin zata iya zuwa ko wanne stage danta kasance da Jabeer din Babu abunda ke dawainiya da ita sai tsananin soyayyarsa dake sake bijiro mata ta ko wacce fuska.....zaune yake yaki furta komai Yana kallon TVn dake Aiki a dakin ,da sauri Annie ta ajiye bowl din soyayyen naman dake hannunta sai tirin kamshi yake taja da baya sannan tace"la'ilaha'illah,kai Bukar ya tafi yabar jaraba a Doron kasa,yanzu Jabeeru da na Fadi na zubar da hakwara sai dai ka cuceni ka cuci y'ay'ana ka barsu da zaryar neman magani,to saboda Allah ba,kazo labcece ka girkemun a daki ,kayi auren ma ba'a huta ba".idanuwansa yakai sosai akan naman sannan cikin sanyin murya yace"zuwa fa nayi na gaishe ki duk kwarki ta dameni"sosai Annie ta washe baki ta zauna tana gyara daurin dankwali tace"Allah sarki mutumin kirki,ni wallahi dama nasan sai kasha wuya na zama babu ni Jabeer,shikam wancan Mai kama da uwarsa ta aura masa zabaya uwar jaraba kaga ko kafarsa bamu sake Gani a gidan nan ba wallahi Jabir,to dama wake gare ni banda kai din,nace zanje gidanka amma Bukar ya hana wai ba yanzu ba,to ni dai bazanyi musu dashi ba Dan nasan Maryam ce ta tirashi sai wani bubudawa takeyi ita ta aurar da kai da waccan figaggiyar ban dai ce masu komai ba".ta gefan idanuwa Jabeer ke karewa Annie kallo murmushi kawai yayi yace"gobe ki shirya zanzo ja dauke ki da kaina,yanzu zan tafi".washe baki Annie keyi sai ta mike bari na baka dambun da nawa Laya ka kai mata ko taji dadin bakinta wannan aure ai mutu ka raba Rukayya na can hassada zata kashe ta dazu na leka na mata tas nace wallahi idanuwanta su fita akan jikata ko kuma hukace zata rabamu".Shiru Annie tayi tana karewa parlon kallo ba Jabeer ba dalilinsa ba kuma bowl din namanta data ajiye ,wani salati ta saki ta jikinta har rawa yakeyi ta yo waje tana cewa"ku tare mun shi,Jabeeru ya zama jaraba,dama kada a Kara shigowa gidan nan a mana katangar karfe innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "sai ta fashe da kuka kawai tayi part din Annie tana matsar kwallah a daidai kofa ta hangi Jabeer yana rufe motarsa yaja da gudu yayi baya gateman ya bude masa ya fice yabar gidan.wani dukan kofan Annie keyi tana kwalawa Ammi kira,da sauri Ammi ta ajiye Documents din da take sakawa a laptop dinta ta cire eyeglasses dinta ta taho da sauri ta bude kofar tana fadin "lafiya Annie".wani kallo Annie ta watsa mata sai kuma tace zuwa nayi ki fada mun ko Bukar uban Jabiru nawa yabar mun gado da zai mutu ko kuma idan kin Saka sisi kin siyomun naman da Kika taras Amadu ya siyomun Ina soyawa"ta kare maganar fuska a daure.girgiza kai Ammi tayi tace "kiyi hakuri Annieeya faru"...Annie ta rufe Ido tare da cewa"wallahi wallahi tsakani zaki mun da Jabeer kuma dama duk gidan ubanda ya kaimun nama na yau ba sai gobe ba a dawo mun da nama na,ko in tashi hankalin kowa a gidan nan".dafe kai Ammi tayi tana son bawa Annie hakuri amma tayi ficewarsa,karasawa tayi a table din da take aiki ta dauki wayarta ta soma Kiran number Jabeer,Yana Driving yaga Kiran Ammi dama yasan za'ayi haka,murmushi kawai ya saki ya kashe wayar gaba daya ya ajiye yaci gaba da driving dinsa Yana cin naman Annie daya dauko.kai tsaye gidan Ummi ya wuce da sallama ya shiga parlon ya zauna ,Ummi Kam fitowarta daga kitchen kenan Asma'u a bayanta suka jera wormer 's din hannuns sannan ta karaso parlon tana cewa"Asma'u ki sakawa Layan abinci idan yayanku zai tafi ya wuce mata dashi shi dai nasan idan ba niyya yayi ba he's always owk daukar magana kawai ya Saka a gaba".kallon Ummi kawai yayi yace"Ina wuni"tace"lafiya qlau ya iyali?"sai tambayar tayi masa wani iri ya kasa cewa komai,kallonsa kawai Ummi tayi sai kuma tace"iKon Allah,Jabeer ko har yanzu baka da iyalin ne?".shiru bece mata komai ba.kasa da murya Ummi tayi tare da cewa"Jabeer kana da ilimi daidai gwargwado you have to know what you're doing,koma me zai faru yanzu Layan nauyinka ce idan ka cutar da ita Allah Yana kallonka idan ka gyara duka kanka kaiwa,ka dauki kaddara,ko ba komai Allah ya rubuta sai ta kasance a mazaunin matarka,so kaji tsoron Allah".shi dai bece komai ba Yana shafa kansa can kuma yace"zan wuce dama nace bari nazo na gaishe ki ne"karar wayarta yasa ta juya tana daukar wayàn dake kusa da ita,tana dauka Ammi bata tsaya sun gama gaisawa ba tace"Ina Jabeer,dama ki fada masa duk in da yake ya dawo wa uwata da abunda ya dauka mata,I don't wante disrespectful da yake nuna mata,wallahi zanyi maganinsa saboda raini ni ko ganinsa ma banyi a gidan ba Ashe ya shigo"..."ayi hakuri insha Allah zak kira shi".sannan ta ajiye wayàn fuska a daure tace"me kaje ka daukanwa Anni?har yau dai ba zaka girma ba ko Jabeer".daure fuska yayi yace"ta ganni a Ina? Ko gidan banma ke ba".kallon ka raina mana hankali Ummi ta bisa da shi sai kuma ya saki murmushi kad'an yace"nama nefa kuma harna cinye".kuma daure fuska Ummi tayi tace"can kai ka sani,duk in da zaka nemo kaje ka biyata abunta yaro baka da aiki sai cin nama" kulan da Ummi ta basa a dole ya karba ya wuce gida baida niyar komawa wurin Annien ma gaba daya. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 38 BAYAN WATA BIYAR Kallonta kawai yake ji wani abu na tsarga masa rai kanta a duke cikin sanyin murya tace"Allah Ammi babu ruwansa,nice dai nace bana so naci gaba,Kara na ajiye shekarar in yaso next year sai in ci gaba"wani kallo Ammi ta jefa mata fuska daure tace"Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau,me ke damunki Layan? To bari in fada maki ba'awa namiji haka in ma wani dadin baki ya maki kika yarda to kanki kika cuta kije ki canza shawara Dan bazan taba amincewa ki ajiye karatunki a daidai wannan lokacin ba"sannan ta mayar da kallonta kan Jabeer kallon tsab da tuhuma take binsa.ya wani zaro Ido alaman babu ruwansa sai kuma yayi kasa da kansa .ya Lula duniyar tunanin daya Sanya Layan cewa zata ajiye karatunta,shirye ta fito tsab cikin dogon riga baki ta yane kanta da mayafin ,lab coat ce a hannunta da katuwar school bag dinta sai laptop Wanda zuwan su Basma suka kawo mata jiya,sai fitar da wani sanyayyen kamshi takeyi,safkowa yakeyi daga stairs din da dan sauri da alamu fita yake son yi da kallo ya bita kafin yace"Ina zakije?"Dan waro manyan idanuwanta tayi tana karewa shigarta kallo sai kawai tace"Yaya makaranta mana mun kusa fara C.A kuma Allah ka duba aikin gidan tun asuba na Saka nose max Dina nayi ko Ina da kyau".kallon baki da hankali yayi mata tare da cewa"to sai ki zaba makaranta ko zaman gidan Jabeer danni bani ra'ayin wacce aka tursasani ta ansa sunan mata a gareni ta rika yawo a titi tana tallar jiki da gogayya da kartai wai sunan makaranta impossible".wasu irin hawaye ne masu zafi suka soma biyo kyakyawar bak'ar fuskarta ta lumshe Ido cikin kuka tace"Yaya Dan Allah,Ina son karatuna"...beko kulata ba tasan kuma idan zata kare rayuwarta a haka bazai taba cewa komin ba.jakarta ta dauka tayi ciki tana rushewa da wani matsanancin kuka Mai karya zuciya a nan tsakiyar dakin ta baje tana kuka tana kuma tunanin tsawon wata BIYAR da tayi a gidan kwata kwata babu abunda ya canza na zamantakewa a tsakaninsu kamar yarda yace yar aiki ce ita to har yanzu wannan sunan take ansawa ita ke gyaran ko Ina da duk wani aiki Wanda a yanzu har Mai gadi basu dashi duk tsawon dare ita zaiwa horn ta taso ta bude masa babu kalar aikin wahalan da bata yi ga wankin kayansa da guga data gama kwarewa girkinta ne kawai baya ci,sai kuma idan tayi laifi bazai taba Jira ba zata samu hukuncin kyakyawan Mari wani lokacin ma har fiye da haka,a yanzu nema taga ya daina dukanta sai dai tsabar tsawa da masifa ,wani murmushin takaici ta saki tare da cewa"har abada wahala ba zata taba sanyawa na gujeka ba Yaya Jabeer,har sai ranar da kai ka koreni da kanka ko wahalar ta zama silar rayuwata Amma soyayyarka Allah ne ya Sanya mun kuma zan jure duk wani yanayi domin na kasance tare da kai,na zaba zama da kai Yaya Jabeer n hakura da makaranta"...kallon Ammi yayi tare da dawowa duniyar tunanin daya Lula tace"Jabeer me yake damun Layan naga tayi wannan ramar haka?,bayan kullun kai da ita kalmarku daya everything is owk"...kasa yayi da kansa yace"Babu komai Ammi"tasan kome zatayi bazai Kara daga hakan ba cikin kakkausar murya tace"idan ma kana mata wani abunne kayi gaggawar sauyawa Dan wallahi idan na gane you will see the other side of me,Jabeer zakaga bacin ran da har abada baka taba sanin Ina dashi ba,so respect your wife kasan me kake yi"...bece komai ya tashi ya fita dan besan kuma mezai fadawa Ammi ba,shidai yasan babu wani abu da zai canza Layan daga kallon da yake mata,to bayan nan kuka besan me suke so yayi ba,a bangaren Annie yaci burki Yana Jin muryar Layan daketa tsandara kukan iskancin nata yanda yake fada shiru yayi Yana jin abunda Annie ke fada,cike da karadi take fadin"yau naga tashin hankali,Allah ya tsinewa bokon ,mecece wata bokon ?kardai maryam bakin ciki takewa Bukar ya samu ya aurar da ke,to duk Wanda ya sawa jikata Ido nidai bazance komai ba gashi ga Allah nan.yanzu kuma zanje naji me take nufi.tura baki gaba Layan tayi tace"ni dai na cewa nayi kije ba,kawai cewa nayi idan tazo kice nazan koma makarantar ba".Shikowar Jabeer ya katse mata sauran maganar,Layan Kam jikinta har rawa yake ta mike da fice da sauri daga parlon Annie,gwalo Ido Annie tayi tace"mezan Gani haka? Wanne mugun abun Kawa jikata ?shiyasa naga ta rame kamar kudin guziri"bece komai ba ya nemi wuri ya zauna Yana ci gaba da latsa wayàn shi.......part din su Muhibba ta nufa tun a parlo ta iske Ihsan zaune ta cab'a ado kamar wacce zata kar kasa,ga Momy Badiyya a gefanta sai washe baki takeyi ta cika mata gabanta da kuloli,Lamin Kam dake gefe kansa a kasa Yana aikin danna wa,kallon tsana Ihsan kewa Layan har bata son ganin yarinyar Sam,tun daga ranar farkon data ganta da Lamin ta kuma fahimci duk burinsa da farin cikinsa ya ta'allak'a ne akan yarinyar,Kara sautin karar gum din da take ci tayi,Layan Kam a hankali ta karaso cikin parlon cikin sanyi murya tace"Ina wuni Momy".gaba d'aya mommy ta juyo sai kuma ta tafa hannuwa tare da cewa"dama kin Saba gaishe ni ne da zaki zo kimun tsaye akai sai kace Mai cutar k'anzamau haka kika koma,a'ah to Allah ya rufa asiri"...cikin yatsine fuska ihsan tace"to Hajiya Ina tarbiya bare kuma a gaishe ki da ladabi,daga sama ma ba'a samota ba bare ayi kankanba".still Lamin yayi Yana karewa ihsan kallo sai kuma cikin kakkausar murya yace"mind you Ihsan kisan me kike fada,na dade da gargadinki akan duk wani abu daya shafi gidan nan,idan kuma kinki ji ba kyaki Gani ba"sakin baki mommy tayi sai kuma tace"tunda ga Rukayya an taba ko sallammme?"."to kya Kara fada mommy,Ina dalili nima yanzu ai na dade da zama ahalin gidan nan,abunda ya shafeka ai ya shafeni Lamin,Amma sai kaita yin wani abu kamar bakasan nice wacce igiyoyin aurenka ke akai ba".cewar Ihsan.layan Kam ko tsayawa ta karasa Jin zancensu bata yi ba ta wuce part din Aunty Amarya dan bata ma da lokacin Ihsan.....plate din gabansa ya ture alamun ya koshi kenan fuskarsa a sake yace to "Umma na koshi"jinjina kai tayi sannan tace to"madallah,ita Layan din bata maka girki a gidan ne".murmushi ya sakarwa Umman yace"tana yi Umma,kin dai san bana son wuce tayin abincinki ne,ita na rako ma wurin Ammi".kallonsa Umma tayi sai kuma tace "ince dai lafiya? Danni ko ganinta ma banyi ba".shiru yayi sai kuma yace"Ina fa zata shigo Umma,anata fama da ita wai sai ta ajiye school".sakin baki Umma tayi sai kuma tace"to Allah ya rufa asiri ya zaba abunda ke alkhairi,komai dai tayi ai kanta tawa, feature dinta zata duba tunda ba wani zata amfana ba,amma idan ta zaba hakan sai kowa ya Saka mata Ido tayi gaban kanta"jinjina kai yayi yace"to magana ta kare ai tunda har taje ta fadawa Annie".tab'e baki Umma tayi tace"taji dashi"ta tashi ta soma tattare kayan da Jabeer din yaci abinci dan ita har gobe bata masa kallon siriki tana nan tana masa kallon Jabeer dinta data raina tun baisan wanene shi ba. RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 39 Cikin cool voice tayi sallama kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta tako tattausan carpet din dake malale a faffad'an parlo din nasu,bata ma San Daddynta ya dawo ba sai da ta d'aga kai taga ya tsura mata Ido,cikin sassarfa ta karaso in da yake a hankali ta silale ta zauna fuskarta kunshe da murmushi,sai dai Sam ba murmushin bai kayatar dashi ba,a kasan murmushin nata yake hango wata damuwa a kwance.gyara zaman shi yayi Yana ajiye jaridan hannunsa ya dawo da dukkan hankalinsa zuwa gareta yace"are you owk".samun kanta tayi da saurin d'aga kai bata yarda sun hada Ido ba tana boye hawayen dake kokarin zubowa a fuskarta,kallonta yake yi irin ramar da yaga tayi ,a hankali kuma yace"meke damunki Mamana?kina cin abinci kuwa?".Nan ma kai ta d'aga masa sannan a hankali tace"Daddyna lafiyana qlau,kwana biyu dai banji Dadi bane,amma Yaya ya duba ni".sosai yaji dadin abunda ta fad'a sai yace"kije kici abinci ki huta,idan zaku wuce Ummanki zata baki Sako,Naji kuma abinda Annie tace Allah yasa hakan shine Mafi alkhairi,be the best wife you can ne Daughter Allah ya maki albarka"...kanta a kasa take ansawa da Ameen tana kuma Jin tsananin son Daddyn nata Wanda bata da kamar shi duk duniya,cikin sanyi ta wuce dining a nan ta samu Umma itama dai kallon ta bita da shi ganin irin uban ramar da tayi sai dai bata ce komai tace"kije ki cire abayan,sai kizo ki dauki abincin,sakon Abbanki kuma na Saka maki a jakkanki da Jabeer ya kawo tun dazu"jinjina kai kawai tayi ta juya ,Umma tabi bayanta da kallo tausayin only child din ta na kamata da alama akwai damuwa a tattare da ita sai dai tasan idan zasu shekara tambaya ba zata taba fada ba,fatanta dai kawai Allah ya shiga lamurranta...lokacin data dawo dining din still tayi ganin Jabeer zaune a wurin Yana saving abinci Yana wa Umma magana,ganinta ya Sanya ya kashe mata idanuwa daya tare da cewa"karaso mana,tsaiwar na menene kuma?"ya kare maganar Yana langwabar da kai,Umma bata tanka ba dan tasan da Layan yake taci gaba da dauraye plate dake gabanta,runtse idanuwa da karfi Layan tayi tana Jin wani abu na taso mata,Inama inama,inama ace tsawon rayuwarsu Jabeer zai kasance a haka ba pretending a gaban iyayenta ba,da yasan yarda Allah ya jarabceta da tsananin soyayyarsa da duk bai aikata mata hakan ba,sai dai ba zata gushe ba tana rokon Allah ya karkato mata da hankalinsa,a hankali ta soma taka k'afarta izuwa dining din taja kujera ta zauna,cikin tattausan lafazi yace"ga abinci nan na zuba maki,kiyi ki cinye sai mu wuce gida is almost magrib".kai kawai ta gyada masa sai hawaye suka balle mata Wanda bata San daga Ina ba,wani irin daure fuska yayi ta kasan table din ya Sanya kafarsa dake cikin shoe ya take nata Yana jefa mata alamar gargadi da kwayar idanuwansa,idanuwa ta runtse tare da yarfa hannuwa tana Jin tsananin zafin takawan ta ratsata sai dai ba yarda ta iya,hannu bibbibiyu ta Saka tana dauke hawayen dake zubo mata cikin sanyin murya wacce ta dishe tace"kayi hakuri bansan sun zubo bane"sai a lokacin dayaga ta share hawayenta sannan ya daga mata k'afar......sai bayan sallahn magriba suka wuce gida sosai taji dadin kyautar da Daddyn ya bata kudi ne masu kauri duk da babu abunda zatayi dasu amma taji dadi.sai abunda Aunty Amarya ta bata magunguna ne na gyaran jiki murmushi tayi tana tuna me zatayi da wannan a gidan Jabeer zata iya cewa abinci ne kawai bata rasa ba a gidan Jabeer da duk wani abubuwan bukatar rayuwarta sai dai bayan nan bata da wani saurin Karin bayanin fada,abun yayi mata dadi lokacin da ya canza akalar motar tasa zuwa gidan Hajja,sosai hakan ya mata dadi har yaso bayyana a fuskarta,Hajja badai kirki ba mata Mai karamci da sanin ya kamata kowa nata,sosai take Jin dadin zama da matar dan dolema ka karu ka kuma kwashi darussan rayuwa.tun a mota ya mata kashedin salan taje ta rika masa sakarci da rashin wayanta data saba.kas tai da kanta karon farko maganar na mata ciwo a ranta,sai dai bata ce komai ba ta bude motar tabi bayansa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki....Hajjan na kishingide Jamila Mai aikinta tana shafa mata man zafi a kafa kasancewar ciwon kafan da take dashi ya soma tashi kwana biyun nan,da madaukakin farin ciki take masu lale tare da cewa "ai na dauka maryama kin manta da ni,kullun sai dai Yayanki yace kina gaishe ni amma na kasa ganin kafafuwanki a gidan nan"Murmushi Layan ta saki wani sanyi na ratsata ta karasa ta karbi man zafin daga hannun Jamila da suke gaisawa ta duka tana fadin"Ashe zan iya mantawa da kaina Hajja,kwana biyu ban samu sararari bane shiyasa amma kullun kina makale a raina"sannan ta soma shafa mata man zafin a hankali yarda zata ji dadi,kafin tace"Ina wuni Hajjiya,mun sake ku lafiya,ya jiki jikin?"jinjina kai Hajja tayi kaunar yarinyar na sake ratsata tace"alhmdllh Maryama, alhmdllh,jiki Kam yanzu sai mu Saka tsare da ke nan zaki gane irin kafin dana samu"duka suka Saka Dariya banda shi ogan daya hakimce Yana latsa waya kamar Wanda akawa dole zuwa gidan.kallonta Hajja ta kuma yi sannan tace"maryama ajiye man nan haka kije kitchen ki haduwa Yayanku tuwo Yana nan dazun nan na tuka shi".da to ta ansa ta mike ta fice.a matukar mamakance Hajja ta kurawa Jabeer Ido cike da taraddadi tace"Muhammad Jabeer lafiya kuwa? Meya samu yar mutane haka? Wacce iriyar rama tayi haka?kardai kace mun har yau ka kasa rike amanar da kowa ke danka maka,kardai kace mun ka zama daya daga cikin masu cuzgunawa matansu idan dai ko haka ne Allah Yana kallonka ba kuma zai taba yafe maka ba Jabeer".warwas yaji shi duk wani abu daya ebo ya nema ya rasa rarraba idanuwa ya soma yi sai dai kanshi tsaye yace"ko kusa Hajja ban rageta da ci ko Sha ba ko sutuura,sai dai har yanzu na dauketa a matsayin matata na kasa isa wannan bigirin na kasa aminata da wannan Hajja,ni saboda Allah a raba ni da wannan dawainiyar haka"...dakuwa Hajja ta masa tace"karbi nan ungu naka nace,maras kunyar banza,har yau kai baka San gatan da Maryam ta maka ba? To Ina so ka sani har bayan raina Babu Wanda zai raba wannan auren JABEER in ma zaka dawo a hankalinka to Kara ka dawo,ka koyi zama da ita,kai kardai ka zama cikin butulun mutane Wanda basa mayar da alkhairi da alkhairi ko bayan ranmu na dauka jinin Sadiqqu da Fadima sunfi gaban hakan Jabeeru a wurinka,to ka tattara kafufunka kabar mun nan kada na sake ganinka har sai ka shirya tsakaninka da matarka ,idan kuma ka cutar da ita ka sani Allah subuhanahu wata'ala Yana kallonka kuma shi yasan irin hukuncin da zai maka"shigowar Layan yasha Hajja yin shiru ta kuma saki murmushi tace"Mika masa yaci ku tashi ku wuce,ki rike mijinki da kyau Maryam Allah yayi maku jagora ya jibanci lamurranki Allah ya maku albarka baki daya"da Ameen ta ansa ta Mika masa abincin a gabansa,duk yarda yake son abincin kasa ci yayi wasa yayi dashi kawai ya tashi yace su wuce gida. RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 40 Tun a mota tunani kawai yake yi maganar Ammi da Hajja sai yawo suke masa a kwakwalwar kansa Sam ya rasa me zai aikata,har gobe kuma bai iya Jin zai karbi Layan matsayin matar aurensa in dai wannan dalilin daya hanasa sonta na ci gaba da wanzuwa a doron kasa,satar kallonta yayi yaga yarda ta lafe jikin kujeran motar tamkar wata marar Rai,kamar wacce take jiran kiris ta ruga a guje,ya sani tabbas shine silar gigita duniyarta zuwa wannan matakin bai San kuma zuwa wanne lokaci zata bar bigiren daya daurata ba,matukar tsoronsa take yi duk lokacin da ta kasance a tare da shi dalilin irin marin daya dakko Yana mata,Amma Sam tun tuni yayiwa kansa fada na daina dukanta duk yarda take matukar son shi amma ya zama abun gudu gareta,wani yawu Mai masifar d'aci ya hadiye Yana dubanta yarda ta kuma takurewa tana kallon hanya yarda kasan yau ne ta fara ganin titin,har suka karaso gida wannan tunanin bai bar zuciyarsa ba,motar Ahmad daya Gani a gidan ita ta tabbatar masa yana gidan kenan,Dan tun wancan satin da Yana wurin aiki yaso yazo ya shaida masa baya nan ya bari sai zuwa wani satin hakan tasa ya masa zuwan bazata bai ko sanar dashi zasu zo gidan ba....Yana tsayawa da motar cikin sanyin nan nata Wanda Jabeer bai taba gani ba ta bude motar ta sauke dogayen fararen kafufuwanta Wanda yanzu yanayin rayuwar da take ciki ya Kara Saka su wata sabuwar ramar motar ta rufe tabi bayansa kamar wacce bata son taka k'asa,Yana zuwa ya bude gidan suka shiga,tsaye yayi cak na wasu seconni b'acin Rai na kokarin mamaye sauran salamar daya soma samu da tarin matsalolin rayuwarsa Husna ce,Asma'u ce Gani yake kamar gizo yake yi ta kwabe mayafinta tana dining tana jera abinci yarda kasan gidanta ko gidan wani shakikinta,tana ganinsa ta wani kashe Ido tare da yauki na daukar hankali ta fara takowa cikin shigarta ta Riga da Wanda Wanda suka matukar d'ameta sai fitar da masifaffan kamshi take yi kanta Babu ko hula sai mayafin data ajiye ,k'afarta takalmi ne masu matukar tsini tana taku daidai,ta karaso cikin ainihin tsakiyar parlon.da karfi Layan ta runtse Ido tana ambatar innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,a'uzubikalmatillahi tammat min sharri ma kala'qa tana kokarin danne wani azabar wutar kishi dake kokarin taso mata,wani dunkulen abu takeji yazo ya tare mata makoshi gaba d'aya...saurin bude idanuwanta da har sun soma sauya kala tayi tana kure Husna da manya manyan idanuwanta tana kare mata kallo da son ganin in da abun zai tsaya.dab da Jabeer ta tsaya fuskarta kunshe da murmushi tace"barka da dawowa my man,tun dazu muke tsumayenku amma shiru,sai dai kasan bazan taba gajiya da jiranka ba,da kuma Ina so in ga kanwata"wani b'acin rai ke kai kawo a kwalwarsa kokarin cooling temfer dinsa yake yi da duk addu'ar da tazo bakinsa idan ba haka ba kusa yasan tsab zai iya illata yarinyar mutane Wanda kowa ba zaiso yaga abunda zaije ya dawo ba.fuska a daure cikin kausasshiyar murya yace"keda waye?" Farr ta kuma yi da idonta da suke can ciki ita a dole ta dauki hankalinsa tace "tare da oga Ahmad muke ya shiga kitchen ne dauko ruwa"kafin ta karasa rufe bakinta Ahmad ya fito da wani Dan iskan Aski a kansa Yana tsotsar baki tare da fiddo harshe Yana fadin"how fa,Ashe baka gida ni kuma ban nema wayanka ba Dan so nake na baka surprise ".jinjina kai Jabeer yayi duk da yasan ada sam Ahmad ba haka yake ba amma a yanzu ya rasa meya shiga kansa har yayi sanadiyar sauyawar dabi'unsa gaba daya kikarin hadiye b'acin ransa yake tare da cewa"waya ce ka kawota gidana?".tage kafadunsa yayi alamar ko in kula yace"ita ta nuna tana so,ni kuma kasan bana son kwakwa,Husna kuma d'abi'arta ce ka sani to bana son damuwa shiyasa na kawota".lumshe idanuwansa yayi da matukar sauri ya budesu Yana karewa Ahmad kallo Wanda yake fadin"wow wow maa Sha Allah,kai man wacce kyakyawar beb ce a bayanka haka? Ko dai kaima ka soma d'anawa ne? Abeg ko saura ne ka barmun wallahi na kwadaitu kuma kasan sai na Dana ba komai zan Jira ragowarka"jikinsa wani irin tsuma ya soma yi har wani rawa rawa jikinsa keyi tsananin b'acin Rai na kuma hassalosa a matukar tsawace yake fadin"you idiot keep quiet,wane irin dabbanci ne wannan ka kwaso"ya kare maganar tare da cin k'walbar Ahmad da duka hannuwansa bibiyu Wanda besan lokacin da yakai gabansa ba.Layan dake tsaye tuni tsaiwar Jabeer tasa hantar cikinta kad'awa jikinta ya soma rawa da karfi ta kama hijab din dake jikinta ta rike da matukar karfi tana kokarin fasa maganganun Ahmad amma Sam ta kasa,Abu daya ke mata yawo a kwalwa kardai ace Yaya Jabeer mata yace bi? Kardai ace Yaya Jabeer mazinaci ne tayi saurin katse tunaninta da korar shaidan tana fadin "a'uzibillahi mishshaidanir raj'im"...bata San a fili tayi maganar ba sai da Jabeer ya tsura mata idanuwansa da suka soma canza launi a matukar tsawace yace"ubanme kika tsaya dauka a Nan? Wallahi idan na iskeki nan sai na karya wannan Yan iskan tsintsiyan kafafun naki da basu da amfani".da gudu ta kwasa tayi cikin dakinta tare da dannawa kofan key tana saune wani wahalallan ajiyar zuciya kafin daga bisani wani irin kuka Wanda bata San daga Ina ko meye dalilinsa ba ya kwace mata ta silale anan bakin kofar tana rairawa....Hannu Ahmad yasa ya kwace kwalwarsa yace"meye haka wai,daga magana sai ka hauni da zazzare Ido".hannu Jabeer ya kada a gaban fuskar Ahmad cikin zallar b'acin rai yace"ka sani wannan din da kakewa wani kallo matata ce,ta Sunna sadaki aka biya aka aura mun ita to ka dauke idanuwanka a kanta tun kan ayi mumunan Gani"...sakin baki Ahmad yayi sai kuma yace"to Ina ce baka son auren? Har yau kuma ka kasa karbarta a matsayin mata,to meye amfanin ajiyeta ka sawwake mata kabawa Mai rabo dama mana Aboki".Girgiza kai kawai Jabeer yakeyi baya so ayi b'atacciya ko wani abun Allah Wadai yasa ya kaiwa wani jadden table na glass dake daidai hanyar shigowa dining area duka da hannu tuni ya tarwatse flower vase dake gefe ya dauka ya kuma jifa dashi ita ta tarwatse hannuwansa ya Saka cikin gyararriyar sumarsa a matukar hassale yace"wallahi wallahil Azeem Ahmad zan iya illataka cikin gidan nan,ko na maka abunda har abada ba zaka mance wanene Jabeer ba,kazo ka kwashi wannan tsiyar kayan tarkacen naka kubar gidan nan tun Ina ganin sauran kima da darajarka a idona ,ko da bana son Layan ta haramta ga kowanne da namiji matsawar ni Jabeer Ina numfashi,kuma ita din dolena ce,dawainiyata ce kanwata ce matata ce jini na ce,hijabin aurena Yana lullube a kanta giyoyina ukku sun dade da zama garkuwa a rayuwarta ka fita tun kafin na canza zuciyata ayi b'atacciya nayi maka alkawarin ka Kara minti ukku a gidan nan,sai dai a fitar da kai amma badai ka sake amfanuwar kafafuwanka ba".jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa"relax Aboki,yau har anyi macen da zata shiga tsakaninmu? Mecece mace har da zata Saka ka wulakanta ni haka,babu komai amma duka zakayi nadamar abubuwan daka fada lokacin da basu da amfani"Yana zuwa Nan ya Kalli Husna tare da cewa"beb let's go "be Jira cewarta ba yayi gaba abunsa.da gudu gudu ta kwashi kayanta ta mara masa baya Dan dama tun kallon Jabeer na farko komai a karfin hali take yinsa....Jabeer Kam kujera ya dafe dake dining din da k'yar ya zauna kansa na wata irin sarawa lokaci daya da k'yar ya dauki cup daya Gani Ahmad din na zuba lemo Mai sanyi a ciki ya soma kwankwada,sai da ya shanye tas sannan yayi wurgi da cup din ya dafe kansa da hannuwansa duk biyun Yana sauke ajiyar zuciya.. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 41 Cikin shiga ta alfarma Hajiya sha'awan ke safkowa daga matakalar benan har ta karaso cikin babban parlon nata cike da farin ciki tace"a'a Hajja Badiyya Ashe kece,shine zasu barki a nan ba'a karasa da ke bedroom ,kinsan duk sabbin masu aiki ne a gidan".itama Momyn murmushi tayi tare da cewa"naga bansan yarinyar data sauke ni a nan din ba ai"Sam Hajiya sha'awa sai ta fasa zama tace"muje daga ciki,Dan naga alamar bakinki da motsi Hajiyata"Saman suka koma cikin makeken bedroom din Hajiya Sha'awa sai ka kallah tsayawa fadan irin kyansa da abunda aka jere a ciki bata lokaci ne dukiya dai tayi kuka harta gaji a gefan wasu matsiyatan sofas dake cikin dakin suka zauna kafin kace me an cika gaban Momy da kayan motsa baki,ruwa Mai sanyi kawai tasha sannan ta sauke ajiyar zuciya.cikin tattara hankali Hajiya Sha'awa wato mahaifiyar Ihsan tace"yau kuma meke damunki? Ina ga kin gama cikar burinki tunda dai wannan yarinya bata auri lamin ba".wani kallo Momy tawa kawar tata kafin tace"nikan Ina zan cika buri bayan Maryam da abunda ta Haifa suna shakar munfashi cikin walwala da Jin Dadi? Nifa wallahi bana Jin ma Aunty Amarya kishiyata akan yarda nake Jin kishin Maryam da Fatima sune duk ummul aba'isin duk shiga wani kunci nawa,kin ha kuwa bazan taba bari masu hankalin ya kwanta ba,so nake wannan auren da suke tutiya suke ganin sun kulla ya zamar masu ciwan Ido,ya zamar masu bala'in da zai kawo karshen su,Kinga sai suje su karata da iskancinsu dama wannan yaron Mai zubin maguzawa ba son auren yake ba har yanzu,duk da naga yarinyar ta fige ba kwanciyar hankali a tattare da ita hakan bai ishe ni ba wallahi Sha'awa".murmushi sosai Hajiya Sha'awa ta saki Mai ma'anoni da yawa tare da cewa"duk farrakun da kika masu bai isa ba kenan? Ni har yau na kasa ganin yarinyar nan dan na dade da ganin ma tawa Autata Ihsan tsaye a Ido,kuma itama nasan tabbas da nata Shirin ba zata zauna ba,to ko wajen mutumin nan zamu koma?".girgiza kai Momy tayi tare da cewa "wannan aikin kai da kai ne bana bukatar malami a ciki sukam sun gama nasu,Amma tabbas bazan taba zuba idanuwa ba har sai duniya ta gama yiwa wad'an nan maciya amanar juyin waina ta gama masu daurin huhun goro,zan San abun yi".jinjina kai Hajiya Sha'awa tayi taci gaba da cewa"tabbas na sanki ba zaki zama sakarya a lamurranki ba amma Ina mai kara jaddada maki ki Nemo kudi kizo ki rufe bakin waccan tsohuwar da gidanku kuma gaskiya aiki mijin nan naki na bukatar service Bangea alamar abubuwan na tafiya kamar a waccan shekarun ba".tsuka Momy Badiyya taje tace"to Ina zasu tafi daidai wannan tsohuwa da kike Gani tsaye take akan y'ay'anta da kuma wannan shaidanun jikokin nata,bata Jin kowa a Rai kamar yarda take jinsu,Kara ma Hydar shima na hannun damanta ne tunda bakin hali Babu irin uban Wanda bai iya ba,Allah da ba'a gida na haifesa ba tsab zan ce canza mun shi akayi,Ina nan Ina zuba Ido da Jin ta Ina zai ballo tashi Sabon rikicin Dan na fara Jin yarinyar Ummi Fatima kanwar uban Jabeer Asma'u take ko ubanwa wai ita yake nema,zanga ta in da zai kunce mun zani a kasuwa shima".Rike haba Hajiya Sha'awa tayi tare da girgiza kai cike da takaici tace"to gaskiya lamari ya karasa lalacewa wai yaushe Rukayya har kikai sanyin da lamurra suka gama kwabe maki haka? Gaskiya da sakal,in m kudin me baki dasu ni zan bada wannan cin fuska har Ina".....Tagumin dake fuskarta ta cire tare da kuma Saka hannu ta yaye uban blanket din da Lamin ya rufe jikinsa har kai,Babu abunda yake yi sai rawar sanyi,yau kwana hud'u kenan Yana kwance a haka kuma ya hana a sanarwa kowa kuma yaki zuwa asibitin, kallo d'aya zaka wa Ihsan kasan tsananin damuwa da tashin hankalin ciwan mijin nata sun gama fita da ita a hayyacinta,ko Mai baya iya ci komai yaci sai ya amarya hawayen dake idanuwanta ta share tare da cewa "wallahi ni dai na gaji Baby,bazan zauna ciwo ya Kashe mun kai ba,kaki zuwa asibiti yanzu nan kuwa zan kira Mommy ko kuma ka tashi mu tafi can gidan kawai asan nayi,Dan ba zamu Kara kwana a haka ba .sake lumshe idanuwa Lamin yayi Yana Jin karadin Ihsan din har cikin tsakiyar kansa sai dai bai ce komai ba,uban dukan gidan da akeyi yasa Ihsan zabura da sauri tace fadin"waye kuma wannan,daga Ina?"Jin ba za'a daina dukan ba yasa ta Kalli agogo ko 8 na safe bai karasa ba cike da masifa da b'acin Rai kuma ta fice fuuuu zuwa kasan taga uban waye ke mata wannan dukan....Annie dake waje ta kuma takarkarewa zata gabzawa kofar duka aka bude da karfi a irin fusacen nan,gwalo idanuwa Annie tayi tana karewa Ihsan kallo daga ita sai wata yar fingilar sleeping dress wacce ko gwaiwa bata sauka ba,sai kuma ta washe baki tace"Kisha iskanki hankali kwance ai ana zuba zafi,nima da shimi nake wuni Ina Shan iska".Basma dake bayan Annie rike da katuwar kula ta boye dariyar da takeyi.Annie bata ko kulata ba ta rab'a ta gefan Ihsan ta shige cikin parlon tare da cewa"wannan yaro Lamin na biyo,tunda nake bai taba mun haka ba gaskiya,Danshi duk yafi yayan Ahmadu hankali da biyayya Amma na jishi shiru kamar an Aiki bawa garinsu yasa na biyo sahu naji ko kece kika hanasa fita ko kuma wani abun aka masa a gidan uban nasa,Dan Sam ba zan ragawa ko ubanwa keda hannu na hana jikana zuwa gida ba,Sam ba haka Lamin yake ba"ta kare zancen tana zama a daya daga cikin parlon.duk da Ihsan taji haushin zuwan sassafen da Annien tayi masu sai dai ta wani bangaren taji Dadi Dan tasan zata taimaka a ciwan Lamin,wannan ciwo da ita ta kasa gane kansa, murmushin yake Ihsan din ta saki tace"bari na canza yanzu zan dawo Hajiya"sai lokacin Annie taga Basma tsaye a gefen kujera,tsuke fuska Annie tayi tace"kufa yayan Amadu matsalarku kenan Sam Baku San Ina ke maku ciwo ba,ki zo gidan Lamin Amma ki rabe kamar wata bakuwa ubanwa ya isa ya hanaki yin yadda kikaga dama gidan Yayanku? To ni gulma ke bani so,in kuma haka wannan kodaddiyar uwar taki ta turoki kimun to maza yanzu sai in Maida mata ke,danni wallahi Laya ta fiye mun kowa a gidan nan,mu kashe mu rufe Babu Wanda yasan me muke ciki,kai Amadu dai ya haifawa kansa".tsuke fuska Basma tayi ta dawo kusa da Annie ta zauna.Ihsan Kam sama ta wuce ta shiga dakinta a gurguje ta watsa ruwa ta canza kayan jikinta zuwa atamfa dogon riga ba laifi wannan ta Dan saki bata kamata ba,kallabin ta daura ta fito zuwa dakin da tabar Lamin,Yana nan a yarda ta barsa karasawa tayi kusa da shi hannu ta daura a goshin shi still taji akwai zafi sai kuma tace masa"Grandma tazo,zaka iya saukowa ?"sai a lokacin ya bude idanuwansa Wanda suka gama sauya launi gaba daya suka kankance ya zuba su akan Ihsan sannan ya fara kokarin mikewa,jallabiya ya Saka ba tare da yace komai ba ya nufi kofa Yana dan Jin Jiri....wani irin kwalalo idanuwan Annie tayi a matukar tsorace da kuma firgice ta furta"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Laminu Kaine?"wani iri fari da yayi ga tsananin rama sai kace Wanda ake Iba ,shidai bai ce komai ba ya karaso cikin parlon ya zauna Yana kallon Annien dake ta faman tafa hannu cike da al'ajabi *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* 42 Cikin sanyin da mutuwar jiki ta mike daga jikin kofar kai tsaye bathroom ta wuce ta yi wanka tare da dauro alwala tayi sallan isha'i dake kanta ta dade zaune a sallayan kafin a hankali ta mike danji takeyi gaba daya kirjinta na cunkushewa kamar numfashinta na son daukewa lotion dinta ta shafa da turare sannan ta samu rigan bacci marar nauyi silik white colour p kawai ta Saka ta zura rigar a daddafe ta isa a bed din ta kwanta tana sauke numfashi tare da lumshe dara-daran idanuwanta Wanda suke hasko mata abunda ke faruwa a dazu ga tunanuka iri iri dake neman wargaza mata kwakwalwa ta shafe tsawon lokaci a haka tana tubka da warwara da tunanin wani b'igiri kuma wannan rayuwar zata kaita ? Menene kuma ke rubuce a shafin kaddarar nata? Abu daya dai ta sani duk tsawon zama da tsawon lokaci ba zata iya daina soyayyar Jabeer ba,wata Kila sai ranar da ruhi zaiyi ban kwana da gangar jikinsa,lokacin da ko wacce gaba a jikinta zata daina aiki ,tabbas idan soyayyar Jabeer zata iya kasancewa cikin zanen kaddarori to tabbas zata ce ta hadu da tata kaddarar mai matukar wahalar cinyewa sai dai tana fatan kada ta gaza ko samun rauni a wannan tafiyar.Hannu tasa tare da shafo hawayen dake gangarowa a gefan idanuwanta sai kuma ta tashi zaune da sauri Jin an turo kofar dakinta,wani irin luguden duka zuciyarta keyi kamar zata fasa kirjinta ta fito dan tsananin tsabar tsoro da k'yar ta hadiye yawu tana niyar kwara ihu ya kunna wutan d'akin tuni haske ya gauraye ko Ina ,ganin Jabeer dake da kofa ya lumshe idanuwansa ya Sanya tsoronta dan raguwa kafin cikin mutuwar jiki tace"Yaya kana son wani abu ne?"ganin beda niyar ansata yasa itama yin shiru tana karewa yanayinsa kallo,sai dai bata ce komai ta dukar da kanta kasa.Cikin tangadi da tunzurawan zuciya ya karasa gefen bed din ya zauna Yana dan cicije lip's tunda yake yasan Yana kasancewa a yanayi irin haka lokuta daban daban to amma na wannan lokacin karara yaga kasawarshi ga wani irin juyi da yake ji kamar Wanda ya dirka kayan maye,a hankali ya dafe kansa ya kwanta a gadon Yana kokarin hana kansa abunda ke Shirin faruwa,wani irin tsikararsw da mararsa tayi yasa ya birkito da Layan gaba daya ta rikoto akan jikinsa ya kuma kankameta kamar Wanda za'a kwacewa,wani irin yamutsata yakeyi kamar zata guje masa,da aika mata da salo kala -kala masu wuyar fassaruwa da b'acewa a zuci,zaro manyan manyan idanuwanta tayi Wanda harsun tara ruwan hawaye Jin irin sumbar da yake aika mata dasu ta ko wanne gaba na jikinta tana kuma sauke numfashin wahala dan rikon dayayi mata yafi karfin kwarin k'ashinta,bata gama tsurewa ba sai da ya lalubi bakinta dib kakejin ta sai faman raba Ido,daga nan kuma wasan ya canza daga ita har shi basu Kara sanin in da kansu yake ba......Can wurin 3 na dare ya soma bude idanuwansa da dafe kai Wanda yake Jin ya masa nauyi amma kuma yau din sai ya kasance Yana jinsa Saka yau ,a hankali komai daya faru ya soma dawo masa a kwakwalwa kamar bitar karatun safe da matukar karfi ya mike Yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,hasbunallahu wani'imal wakeel,ya kare tare da waro idanuwansa a deep light din bedside lamp dake kunne sosai kansa ya daure da ganin in da yake da kuma irin katobarar daya aikata,kallon cute long chocolate baby face dinta yake yi ko Ina duk jirwayen hawayen daya gama bushewa gata can a gefen cikin yanayi na Suma.A nitse ya mike ya shiga toilet ya gyara jikinsa yayi wanka da kyau ya gargasa jikinsa danji yake yi wani zazzafan zazzabi na bin ko wacce gaba ta jikinsa dan harya fara rawar sanyi da k'yar ya kuma hada wani ruwan masu dumi yazo ya dauketa kamar ya dauki yar baby saboda rashin nauyi kai tsaye cikin ruwan ya tsundumata,wani wahalallan Kara ta saki da muryarta data gama disashewa dan tsabar kuma,zafin da taji shi ya farfado da ita daga suman data yi,kankame Jabeer din tayi tana sakin kuka dason mikewa cikin dakiya ya kuma dannata a ruwan fuska a daure da Jin duk ya gama muzanta yace"keep quiet,Allah yasa naga kin tashi a ruwan nan,kiga yarda zan b'allaki har a rasa me Dori"..Layan Kam bata ma fahimtar abunda yake yi kukanta kawai takeyi sai kuma tsananin tsoron Jabeer din daya gama lullubeta Dan tiryan tiryan wahalar data kwasa a hannunsa ke dawo mata gaba daya ta idasa firgicewa.ko kallonta beyi ba so ukku Yana canza mata ruwa sannan ya taimaka mata ta fito,wani doguwan rigan ya bata ta canza ya bata dugs sannan ya zaunar da ita a soma ya gyara gadon tas ya canza bedsheet sannan ta kwanta ya lullubeta yaje ya kwanke zanin Dan duk zazzabin da yakeji bazai iya barin zanin a haka ba,a daddafe ya karasa ya wuce d'akinsa ya kwanta sai dai ya nemi bacci ya rasa Yana ta kwance har akai Kiran asuba bai iya fita masallaci ba a nan yayi sallan sai kuma wani nauyayyen bacci ya daukesa............girgiza kafa kawai Annie keyi sai kuma cikin masifa tace"yau naga bala'i wacece wata BADIYYA da zata tsaida mutane har yau bata dawo daga gantalinta ba,jikan nawa zaku bari a walakance haka cikin cuta? Ni Sam ban ganewa wannan abun ba,Kara azo asan nayi tunda akai auren nan jikana ya birkice azo ayi zaman metin idan auren ne baya so wallahi wallahi ko sakan bazai Kara da wannan auren da aka rasa gabansa da bayansa ba wallahi".kallon kasan Ido kawai Ihsan kebin Annie da shi sai dai ganin Abba dasu Aunty Amarya yasa bata ce komai ba.numfashi Umma taja tace"kiyi hakuri Annie wannan ruwan daya kare tunda Ammi tace idan ya kare za'a Kaisa asibiti a masa kwaje kwaje "..."Dan Allah Fatima yanzu abunda akawa yaron nan daidai ne? Ke zaki dauka idan Laya akawa?,wacece wata Ammi ni dai kawai idan wani abu ya samu jikana Mai tsananin biyayya bai taba fada na fada ba to wallahi ba yafewa zanyi ba shara'ace har gaban Allah dama waccan kodaddiyar matar tashi ta soma hada kayanta dan bam na fashewa ita da BADIYYAa sai dai su nemi wani gidajen auren"...Momy BADIYYA Kam ko bin takan kalaman Annie ma batayi ta fado parlon a rude cikin matukar tashin hankali tana kallon Lamin yarda ya koma ,lokaci daya duk ya gama fita a hayyacinsa,kuka ta sakin tare da fadin"wannan wanne irin ciwo ne ni Badiyya,Allah ka tashi kafadun yarona,aniyar kowa ta bisa,tunda aka ga yayi aure na nunawa tsara shikenan ya tsole idon kowa,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"ta kuma fashewa da kuka tayi zaune tare da kama hannun Lamin Wanda ba'a sakawa drip ba.Girgiza kai Abba yayi cike da takaici sai dai bece komai ba,Dan yasan muddin ya bude bakinsa ba abu mai dadi zai fito ba Sam ya rasa meke shiga kan Badiyya at times ma baya gane in da ta dosa wani abu ya hadiye Mai d'aci yana mikewa yabar wajen,ganin yabar wajen Momy tace"to zaman me kuma marar lafiya irin wannan yake yi a gida? Gaskiya mu wuce da shi asibiti yaga kwararrun likitoci".tab'e baki Aunty Amarya tayi tace"sai ruwa ya kare dan Ammi ta gama dubasa komai da za'a masa kuma an gama tsarawa a asibitinta".wani irin kankance Ido Momy tayi tace"to badai jinin Badiyya ba wallahi,idan Jabeer ne wancan tabbataccen marar kunyar ta zauna tana kallonsa a wannan halin? To ni zan kai Dana asibiti dan Sam ni banma yarda da karatunta ba,haka kawai yarona yaje ya salwanta".sai lokacin Annie ta dauke kallonta daga Momy Badiyyan sannan tace"to ko Ahmadu ubansa bai isa ba bare ke kayan karere,anan Lamin zai zauna kuma anjima a kaimun shi asibitin Maryam nayi jiyyar kayana ubanda bai zuwa can shi ta dama".Daga haka ba Wanda ya kuma cewa komai,Dan Sam Momy mutuwar zaune tayi tasan tanayin ba daidai ba yanzu Annien zata fatattaketa ta hanata ganin Lamin din ma gaba daya,ita kuma ba zata iya dauka ba,the only favorite child dinta da take matukar so Yana cikin wannan halin ace bata tare da shi sai tarkacen kishiya da Sako Ina bazai yiwu ba. *RUHIN JIKI* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________* *JORDERH MAJIDADI* End of part 1 Tunda ya kwanta bacci bashi ya Farka ba sai wurin 12pm cikin sanyin jiki da karyewar zuciya ya tashi zuciyarsa da zantuttuka iri iri,Sam ya rasa in da ya dosa sai tuna irin bannar daya tabka wa karamar yarinyar yake yi,Sam baya son ko hada idanuwa da ita,abu daya ya sani Yana Jin wani nauyi a kasan zuciyarsa sai dai ya kasa fassara hakan da komai.cikin sanyi jiki Dana kafafu ya mike kai tsaye ya nufi kasan benen dan zuwa dubata,dakin ya shiga a hankali kwance take tayi rub da ciki da alama tayi kuka ne harta gaji baccin ya dauketa a haka ,shi kansa yayi mamakin irin zafin zazzabin dake jikinta har duvet din data rufa,tashi ta yayi tare da bata tea din daya hada cikin sanyin murya tace"zanyi fitsari"bece komai ba,be kuma kalleta ba yadai jinjina mata kai.tana safko da kafufuwanta ta saki wani wahalallan kuka tana kaiwa ta duke a wurin ,tana sauraron irin zafin azabar dake ratsata kamar ana yayyanka kasanta haka takeji,sauke ajiyar zuciya yayi Dan yasan shi kansa beje mata ta sauki ba ya mike ya dauketa cak zuwa toilet kafin ya dawo bakin kofa zaman jiranta,sai da ta karasa sanna ya dauketa zuwan gefan bed din ya zaunar da ita,kad'an tasha tea din sai drugs dinta da yake bata.cikin sanyin murya yace"ki hada kayanki a jakka Ina zuwa yanzu".be Jira cewarta ba ya koma d'akinsa kaya ya had'a a karamin jakka da duk wasu takardunsa da yasan zai bukata ko a Ina sannan ya shiga yayi wanka a gurguje cikin minti 20 ya shirya cikin kananun kaya da sukayi masifar karbarsa sosai ya fafeshe jikinsa da dad'an turarensa masu matukar kamshi da Jan hankali.jakkar ya sak'alo a kagadarsa ya safko tare da shiga dakin layan.sai dai me Taurus ya tsaya Yana karewa dakin kallo Babu kowa sai cup din daya bari a hannunta,karasa yayi cikin zuwa toilet nan ma babu komai a ciki,jakar kafadarsa ya sauke a tsakiyar dakin ,cikin natsuwarnan tasa ya fito ya dudduba ko Ina a parlo har kitchen Amma Babu Layan Babu alamarta ,kai tsaye gate ya nufo ya zagaya har backyard amma babu kowa,gateman daya kawo 2days baya ya karasa ya sama.da sauri Yana gaishesa cike da girmama,kasancewar tsohon ya Dan manyanata yasa Jabeer gaishesa kafin yace"Baba ko akwai Wanda ya fita daga gidan nan?"Jin jina kai Baba yayi cikin tabbatarwa yace"Babu Wanda ya fita Ranka ya dade,kuma tunda safiya tayi nake bakin gate din nan,amma ba Wanda ya shigo ko ya fita"sai lokacin ya soma Jin hankalinsa na tashi gaba daya yama rasa abun cewa cikin rashin kwarin jiki ya koma ciki wurin daukar jakkarsa yaga farin takarda anyi rubutu layi biyu an ajiye a gefan gado,cikin sauri ya karasa Yana saukewa rubutun manyan idanuwansa da suka soma canza launi ya kallah *kada kuce zaku matsanta da nemanta,Dan har abada tayi maku nisan da ba zaku taba ganota ba,tana tare da ni* kamar idanuwansa zasu fado haka yake kallon rubutun ko kuma zaiga layan din a ciki tuni kansa ya matukar sarawa zuciyarsa ta tsinke amma d'aya ke masa yawo a kansa shin waye ya dauki Layan?ba ansa yasa ya Saka papern a aljihu ya dauki key din motarsa ya wuce gida.kamar Wanda beson taka k'asa haka ya shiga part din Umman ya zube a kujera tun gate Yana Jin karadin Annie amma ya boye ta bayan motoci ya shigo nan ya zauna tare da dafe kansa dake barazanar tarwatsewa,yafi minti 30 sannan Umma ta fito daga bedroom dinta turus tayi ta tsaya rike da baki tace"son yaushe ka shigo? Aida kaimun magana kasan in Daddynka baya nan na shiga cikin nan nakan dade ban fito ba"Ganin har lokacin bai juyo ba kamar yarda ya Saba da yarda yake zama kamar an dasasa a wurin yasa ta karaso da sauri tana tambayarsa ko lafiya.shiru baice komai ba sai dai kansa dake kasa har lokacin ya kasa kallon Umma bare ya samu kwarin gwaiwar yi mata magana,cikin sanyin murya ta soma da fadin"kayi hakuri kaji son,komai yake faruwa ka kaddara Yana rubuce ne cikin kuncin kaddararka,wannan nuna b'acin ran da fushi babu abunda zai kawo sai wani damuwan kuma na daban".sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke ,ya rasa ta Ina zai fara shi dai Sam bai iya karya ba,kuma baya kwana kwana a magana cike da rashin kwarin gwaiwa ya mikawa Umma takardar dake hannunsa content din ciki ta karanta ta kuma maimaitawa sai kuma tace"wacece kuma son?"kasa magana yayi tare da yin kasa da kansa sai kuma a hankali yace"LAYAN ".jinjina kai Umma tayi tare da waro idanuwanta Wanda zamu iya cewa a wurinta Layan ta gado girman idanuwa sai kuma a hankali ta fara furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Allahumma ajirni fi musi bati wa'akilibni Khairan minha"sai kuma ta mike tsaye tana kuma kallon papern dake hannunta cikin sanyin murya da sarewa Jabeer ya fara fadin"kiyi hakuri Ummina,kiyi hakuri Ummina na kasa rike amanarki gare ni".komawa tayi ta zauna kusa dashi ta shafa kansa tare da cewa"har Abada zuciyar Ummanka ba zata tana zarginka da kasa rike amanarta ba ,sai dai nasan akwai wani al-amari Mai girma dake niyar tunkaro mu,fatana kawai ka jure ka kuma ci gaba da kasancewa Jabeer dinka gudun magauta suyi nasara da rauninka,duk da nasan baka son Layan amma nasan ba zaka taba bada kofar cutarwarta ba Son".waya ta d'aga tayi Kiran Aunty Amarya da sanar mata abunda ke faruwa,cikin kankanin lokaci maganar ta karade gidan gaba daya har su Ummi sunji Dan a rikice ta biyo hanya iKon Allah ne kawai ya kawota gidan.......tsit parlon yake baka Jin motsin komai sai karar kukan Annie sai kuma ta saki salati da fadin"na ga rayuwa ni Maryama,naga tashin hankali ni maryama meya faru da jikata,innalillahi wa 'inna ilaihir raju'un Jabeeru duk in da ka kai Mani jikata ka fito da ita in ba haka ba hukuma ce zata rabamu"sai kuma ta fashe da kuka.cike da karfin hali Daddy yace"Annie Dan Allah kiyi hakuri kibar kuka insha Allah Babu abunda zai samu Layan,addu'arki kawai take bukata,Babu kuma abunda ya alakanta b'acewar Layan da Jabeer ,kinsan bazai taba salwantar da matarsa kuma kanwarsa ".wani irin zabura Annie tayi ta mike tace"kai dai Bukar bakaji Dadi ba,wallahi baka ji Dadi ba,Allah ya wadaran naka ya lalace Sam dama kai baka da zuciyar Imani da tausayi,bana son wata magana Abu daya nake bukata shine naya Laya cikin gidan nan,kuma daga nan wannan kaddarar auren ya kare"....Jinjina kai Ammi tayi tare da share hawayen da suka zubo mata itama ta mike tare da cewa"nima Ina bayan Annie,duk in da Jabeer ka kaimun yarinya ka maidota kafin dare idan ba haka ba kuma duk abunda kake bukata zaka samu,zaka samu b'acin ran da baka taba tunani ba wallahi"cak Annie ta tsaya da kukan da takeyi sai kuma tace"ke Maryam ya haka? Karki Saka mun jika a haki,kowa dai yaci kansa Allah na tare da jikana,Ina zaikai wannan yarinyar da kowa zai Saka mun shi gaba"kai tsaye Annie ta kama hannun Jabeer ta mike ta wuce da shi tana banbami da fada.Girgiza kai Abba yayi tare da anbaton"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,I don't know what to do "...share hawaye Umma tayi cike da karfin hali tace"idan duk kuka zargi Jabeer to kuma tantama da irin tarbiyar Dana basa kenan,Jabeer bazai taba cutar da Layan ba ni nayi Imani da hakan,sai dai a bincika wani wurin,tabbas akwai abunda ba daidai ba,Amma Dan Allah kada ku zargi yarona akan abunda bashi ya aikata ba"tana kaiwa nan ta mike tabar masu parlon...ajiyar zuciya Ummi ta sauke tare da cewa"ya kamata dai mu Sako hukuma a ciki,danni kaina ban yarda Jabeer zaiyiwa Layan wani abunba kuma....bayan wani lokaci....gaba daya duk in da ake Saka rai na ganin Layan babu ita babu alamarta,gaba daya rayuwa ta gama canzawa a gidan ta maye gurbin da tashin hankali da dunbin damuwa da kowa ya kasance a ciki sabanin Momy Badiyya da kowa ya kasa gane in da ta dosa Dan ko a kwalarta a cewarta ma a daina damunsu yarinya ta tafi yawon ta zubar dinta amma azo a wani damu mutane,ko kuma a bincike mijin nata Shi yasan in da ya kaita Dan wannan uwar dukiya da yake da ita ma ai abun a bincika ce,sai da Annie ta mata wankin babban bargo sannan aka Dan samu saukin habaice habaicen da takeyi....... *To jama'a ku biyo ni danjin ya zata kasance,shin menene makomar Jabeer? Ina Layan?shin Lamin zai tsallake daga ciwan daya damesa? Shin menene fassarar maganganun Momy Badiyya? Shin ya rayuwar Ammi zata kasance Babu yarta a kusa da ita,kudai ku biyo ni domin Jin ya zata kasance,insha Allah bada jimawa ba zamu saki sauran kuma a complete dinsa idan yayi ready zan sanar maku sai dai part 2 din na kudi ne akan naira 300 kacal ki biya Kisha karatu lafiya cike da kwanciyar hankali.07033636337 ku biyo ni danjin ya zata kasance.*