*_KALBIM_* _Mamuhgee_ #Zafafabiyar 1 Bismillahir Rahmanirraheem Ina rokon ALLAH Subhanahu wata'ala yanda zan fara littafin nan lafiya cikin aminci da yardarsa ya bani ikon kammalawa cikin kwanciyar hankali da nishadi tareda dacewa lfy Ni da yan uwana gabaki dayanmu.AMIN. Dan Allah ku kasance masu uzuri idan an samu kuskure ko mantuwa da makamantansu,Thank you. ******** ZADEENs HEALTH CEN/SPEACIALIST, WEDNESDAY 1:40Am Tin kafin isowan motocinsu da suka tinakaro babbar gate din asibitin securities na asibitin suka taso kusan a tare suna wangale musu gate din cikin sauri sbd irin gudun da motocin Ahalin ZADEEN's din suka tinkaro dashi wanda duk wani ma'aikacinsu yasan idan ciwon motacin suka tinkaro asibitin to Hasken idaniyar ahalin ce ba lafiya wadda kullum take cikin ciwo. Sauran securities din da basu qaraso bude kofar gate din ba kaf dinsu fitowa sukai suka tsatsaya a gate suna bin motocin guda uku da kallan girmamawa duk da tsakar dare ne tareda fatan Allah ya bata lafiya. Motocin na gama shigewa aka rufe gate din tareda taresa sbd babu wanda yake shiga ta wannan gate din a qaidarsa sai masu asibitin wanda kusan koyaushe suna hanyar zuwanta. Kafin suyi parking likitoci uku da nurses biyu suka fito ta private kofar da zata kaika kai tsaye zuwa Vip room din dayake sama gaba daya. A tare duka kofofin motocin suka bude kusan a tare duka suke fitowa babu wanda baa cikin kayan baccinsa yake ba sai DZAD(Dad Zad) wanda shine asalin Zadeens din a yanzu da babu kakansu kuma shine mahaifin marar lafiyar tasu sanye yake da jallabiya da qatuwar rigar sanyi ash sai hula sbd idan ciwon 'yar dayake gani a matsayin tasa bugawar zuciyar ya tashi saukowa yakeyi gaba daya daga billionaire din da ganinsa ma yake wuya ya koma kaman asalin uban da bayada komai agajin gaske yake nema a gurin Allah. Gadon da aka tura ta dashi ne komai nata a rufe ko fuskanta baa gani sbd kwata kwata basa bari ana ganinta sosai sai iya likitocin dake kulawa da ita sa ciwonta ne kadai suka san kamanninta sbd tsaro da tsananin rashin wasa da duk abinda ya shafeta. Suna wucewa ciki sauran familys din suka musu baya babu wanda zuciyarsa bata harbawa da damuwa, A daidai irin wannan yanayin ne ko lokacin idan suna cikinsa babu abinda bazasu iya kawarwa ba dan biyan buqatansu dan kuwa mantawa suke da komai da kowa sbd JANNAH. Securities din ZADEEN's dinne da suka iso asibitin ba tareda kayan securities dinsu a jiki ba sbd basa son asan akwai wani me mahimmanci a asibitin suka zagaye private kofar har ciki batareda alamar da zata nuna securities ne su ba. A sama kuwa suna isa aka shige da ita inda iya doctors dinne zasu shiga familyn kuwa a nan wani wadataccen palon jira dayake a tsare suka zazzauna cikin yanayi mara dadi wasunsu kuma a tsaye suna kaida kawo cikin rashin sauti ko kadan sbd rashin dadin zuciya. Mimi data fisu karfin zuciya akan lamarin Jannah din koyaushe itace ta dago idanuwanta da sukai laushi ta kalli Dzad wanda shima juyowa yayi ya kalleta da idanuwansa da sukai jajir kafin ya sauke ajiyar zuciya ahankali yana hade hannuwansa biyu sbd sanyin dayake ratsasa ko zai rage masa wanda kai tsaye zuciyarsa yake jin kaman yana zuwa zai masa illa sbd a wannan lokacin komai zai iya zama ajalinsa dan komai nasa yana gab da mutuwa idan har wani abu ya samu Jannah. Hannu Mimi ta miqa duka biyu ta dora akan nasa hannuwan tana rufe masa su tareda bude baki cikin tsananin karfin hali da jarumtar da su suke rasawa tace, "Insha Allah wannan karan zaa dace da zuciyar da zatai mata, Zaa dace,Jan Zata rayu kaman kowacce 'ya insha Allah, Jan zata zama kaman kowanne dan adam,zatai karatu me zurfi ta zama abinda kakeson ta zama insha Allah.... Rawa muryanta tafara yi karfin zuciyarta na neman karyewa dan haka tai shiru tana damqe hannuwan Dad din da dan karfi tana qasa da idanuwanta dake neman cikowa da hawaye. Dzat din sake kame hannuwanta yayi da nasa yana kasa cewa komai dan irin hakan baya magana kowa ya sani. Anny matar yayan jannah din wadda ke tsaye gefen mijinta MAHIR ZADEEN riqe da hannunsa tana kokarin kwantar masa da hankali tareda basa kwarin gwiwa dik da itama a sanyayen take sbd duk lokacinda zaa ce jannah ba lafiya a cikin matsanancin tashin hankali take duk da tasan ta riga ta tsira ta fita daga layin wainda zaa iya rabasu da zuciyar dake bugawa a kirjinsu sbd dubawa ko zata daidaita da wadda zata zaunu a kirjin wadda suke son nemowa zuciya kota halin yaya. Baro gurin Mahir tayi ta dawo gefen Mimi tayi ta zauna ahankali tareda dafata ahankali tana furta mata kalaman kwantar da hankali da fatan ranar warakar jannah taxo. Mahir zaunawa yayi shima yana dora kafarsa daya akan daya sbd sanyi da shima yake ratsashi wanda yakejin kamar fatar jikinsa ce ta bude kai tsaye sanyin na shigar masa kashi yana daskarar da jininsa gashi kayan bacci ne a jikinsa riga da wando masu tsananin taushi sbd tsadarsu sai jacket daya doro akai. SALEEM ZADEEN wanda yake bin mahir kuwa kasa zama yayi sbd kansa dayake jin kaman yana motsi dan shi sam dan zafi ne baya da hakurin suspense irin wannan kansa yakejin kaman zai zare. Shima riga da wando ne a jikinsa na bacci sedai shi hoodie jacket ce a jikinsa sai kai da kawo yakeyi yana kasa dago jajayen idanuwansa da suka sauya. Kofar palon aka turo da sauri wadda ta saka dukkaninsu dagowa suna kallan Dr AMMAR ZADEEN wanda kai tsaye ya komar da kansa baya ne yayi karatun likitan Zuciya sbd Jannah kadai. Idanuwansa da sukafi na kowannensu sauyawa ya dago ya kalli kowannensu kafin ya kalli dzat ya basa kwarin gwiwa ya juya ya fice zuwa dakin da jannah din take da doctors sbd shi biyawa yayi inda aka sanar dashi ana tinanin an samu donor kafin ya wuto nan shiyasa suka rigasa isowa. Zaman kusan awa daya zuwa biyu sukai cikin tsananin daci da damuwar zuciya kafin Ammar ya fito ya shigo dakin yana sauke numfashi me tsananin zafi da huci ya qaraso ya zauna kujeran datake kallan su Dad din ya dago idanuwansa ya kalli dad. Ajiyar zuciya me sanyi dad din ya sauke a natse yanajin hankalinsa na dawowa jikinsa take yaji dacin zuciyarsa ya ragu sbd yasan Ammar ko zuciya dubu jannah ke buqata zai nemosu ayita gwadawa har a samu wadda zatai daidai a saka mata kota halin yaya ba damuwarsu bane. Mahir ma ganin hakan ya sauke ajiyar zuciya a boye kafin ya juya ya kalli Anny da kusan itama take ta fahimci akwai wani abin kenan da ido yai mata maganar ta fita da Mimi. Ajiyar zuciya da numfashi itama ta sauke tareda dafa Mimin cikin kulawa da nuna tausayawa sosai da nutsuwa tace, "Mimi muje mu duba Jannah din doctors din sun fito" Dagowa Mimin tayi ta kalli Ammar wanda ya gyada mata kai alamar eh zasu iya zuwan, Mahir ta kalla shima ya sakar mata murmushin karfin halin alamar insha Allah jannah yanzu zata samu sauki. Miqewa tayi Anny tabi bayanta suka fice daga gurin Anny taja kofar ta rufe suka nufi dakin da jannah din take. Suna ficewa Ammar ya sauke numfashi tareda dagowa ya kalli dzad dake jiran bayaninsa ya bude baki yace "Ansamu donor wanda ta ko ina muke saka ran tayi.... Katsesa DadZad yayi da cewa "Mene ake jira to? Saleem da baida hakurin jiran komai batareda sanin abinda Ammar din zai fada ba ya matso gaban Ammar din kai tsaye yace "Indai ansamu zuciyar da zataiwa Jan ko duka tawa dukiyar dana mallaka akeso zan bayar a karbo heart din ko a inane take kawai ka tabbatarda ka amsota Jan ta sameta" Yana gama fadar haka ya juya ya nufi kofa ya fice zuwa dakinda jannah din take ya turo musu kofar da karfin daya saka dukkaninsu rintse idanuwansu banda Dad da bai motsaba har lokacin jiran sauran bayanin Ammar din yake wanda daman ba duka zance sukeyi da Saleem ba sbd zafinsa da rashin hakurinsa tareda rashin yadda da raayin kowa wani lokacin sai na kansa. Ammar takardin dake cikin aljihun jacket dinsa ya fitar ya ajiye akan table din gabansu ya mayar da bayansa jikin kujeran dayake ya jingina yafara cewa "Daya daga cikin asibitin da muka saka likitocinmu aka samo wadda zatai daidai insha Allah kuma kusan shekarunsu daya da Jannah din sedai matar Aure ce dan tanada tsohon ciki ma sedai batareda saninta ba likitocin sun duba zuciyar komai lafiya kalau." Ajiyar zuciya me tattareda samun kwanciyar hankali mahir da dad din suka sauke lokaci daya sbd abinda kawai suke son ji kenan indai komai lafiya kuma ana tinanin zatai to sauran bayanin ba damuwarsu bane sbd sai sun rabata da wannan zuciyar datake bugawa a kirjin ta sun sakawa tasu yar batareda saninta ba sbd itace kusan ta numbar da bazasu iya kirgawa ba sai an cire aga bata daceba. Dad din a natse yana komawa take Dzad dinsa ya gyara zamansa na asalin Me kudin dayake murza lokacinsa a yanzu ya kalli takardun batareda ya miqa hannunsa ya tabasu ba yace "Kawai ku saka lokacinda zaayi aikin shine abinda yakeda mahimmanci amma sauran aikin ba buqatan damuwa, Ku saka likitan datake gani acan asibitin gwamnatin ya turota nan asibitin batareda bata lokaci ba." Mahir daya miqa hannu ya dauko takardun ya bude ya zubawa sunan dayake kai idanuwansa tsawon seconds ya duba bayananta da bai fahimci komai a cikinsu ba sbd tin daga sunan da garin datake babu wanda ko a cikin wani yare ya taba ji sbd ba anan suka tashi ba bare susan sunayen garuruwa duka bare qauyuka dayake ganin kamar dabbobine kadai suke iya rayuwa a cikinsu. Jefa takardun yayi a kan table din kafin ya kalli dad din a natse yace "Inaga zaifi tinda an samu wanda zatai din and she's preg abari ayi amfani da tsufan cikin da haihuwansa" Kallansa Ammar yayi yana tinanin abinda yake fada wanda shi idan tasa zaa bi babu abinda zai tsaya jira bayan cirewa da sakawa Jan. Dad shiru yayi batareda ya kalli kowannensu ba sbd maganar mahir din dan mahir shine kusan kamar me hangen lamuransu a duk lokacinda zaayi huldan business da irin wannan mummunar ta bayan fagen shine yake aunawa da hangowa ya fada yanda zaayi kuma hakan akeyi a dace sbd yanada ilimin nutsuwar fahimtar komai da mutane, Hakama yanada wani irin ilimin dayafi duka familyn harshi dad din dan duk da dukkaninsu baa qasar suka taso ba sai yanzu ne da suka zabi dawowa gida sbd nemawa jannah kalbim. #MAMUH #ZAFAFABIYAR #MASTERPIECE #BESTSTORY #BESTLOVE #BESTROMANCE #BILLIONAIRES WAR #CRAZYLOVE #ZADEENS #LIMBAS ZAFAFA BIYAR KALBIM 500 mamuhgee A DUNIYATA 500 Huguma AJIYA A DUHU 500 Billyn Abdul KIRJIN ME HANKALI 500 Miss xoxo Pay at 0022419171 AccessBank Maryam sani gummi Shedan biya 09033181070 Or mtn vtu at 09032345899 _*KALBIM*_ _Mamuhgee_ #ZafafaBiyar 2 *ZUZEAMVENTURES* 08144015291 Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 3800 Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k 08144015291 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki *********** Shiru dukkaninsu sukai daga dzad din har Ammar suna sake shiga nazarin maganar mahir wanda yake sake kokarin nazarta yanda zasu samu damar samun komai batareda wani damuwa ba dan shi sam baya yadda da damuwa ko tangarda a aikinsa shiyasa yake tamkar maye gurin nutsuwa ya hango ya hanga kafin ya fada. Dzad duk abinda mahir ya fada yana kokarin bada damar abi hakan sbd yafi kaf yayansa nutsuwa da bin komai a tsare amma ayau yanajin kaman hakurinsa bazai barsa ya jira lokacin da mahir din yake fada ba sbd kada su rasa zuciyar wadda ake jiran kokuma idan gurin haihuwar ta rasu fa.? Sun raba mutane da dama zuciyoyinsu sbd jannah amma babu wanda aka dace wanda ma basu san adadinsu ba ta boyayyar hanya To ayanzu da suka samu bayan tsawon lokaci ana nema kuma a tsaya jiran wani haihuwar. Mahir daya fahimci tinanin da Dad din yake sake bude baki yayi yace "Jiran haihuwarta na nufin samun dama da dalilin rasuwarta ga mutane da yan uwanta shiyasa ana buqatan a jira lokacin haihuwan tayi sbd lokacin haihuwar ya matso sosai hakan ne zai saka komai ya tafi very neat tin daga cirewa da sakawan da rufe komai". Ammar da zuciyarsa ke bugawa da sauri yana jin kansa na juyawa idanuwansa na ja jin yakeyi kaman bazai iya jiran lokacinba dan kuwa shi jinma yake kaman ya fizgo zuciyar a daren nan yazo ya sakawa Jan, Shi a yanda yakejin yana zaucewa akan ciwon jannah duk mutanen dayake gani suna yawo zai iya ringa binsu yana fasa kirjinsu yana qwato zuciyoyinsu babu ruwansa da rayuwarsu indai jannah zata rayu. Mahir ganin alaman Dad ya aminta da hakan ya sakasa kallan Ammar shi da Dad a tare sbd sanin shine mai juyewan kai idan wannan lamarin ya taso kwata kwata bayaji baya gani kawai abu daya ya sani shine karban kalbim kota waye ba ruwansa. Dad ne ya bude baki a natse yace "Ammar abari ayi hakan sbd tafiyar da komai batareda garaje ba ko dan ita jannah din hakama aikin nutsuwar da kwanciyar hankalin zaifi, Tinda aka riga aka sameta duk inda zata shiga bazata gujewa abinda yake jiranta ba sbd yanzu zuciyar Jannah ce kai tsaye take bugawa a kirjinta babu abinda zai hana jannah mallakar wannan zuciyar me bugawa." Numfashi me zafi da damuwa Ammar ya sake kafin yaji ya aminta da hakan dan haka zasu saka masu bibiyar yarinyar da bincike sosai akanta duk da babu ruwansu ba abinda ya shafesu da inda ta fito kokuma wace ita waye danginta. ******ASALIN LABARIN/SHEKARUN DA BAYA. PROF ZAHARADDEN ZAADEN shine asalin mahaifin Yayansu uku biyu maza sai mace daya wadda yayunta mazan ke tsananin kauna sbd mahaifiyarsu ta rasu a hannun matar mahaifinsu suka taso, Prof dan bokon gaske ne wanda ilimin bokon dana addinin suka shigesa sosai hakama yanada arziki sosai wanda ya dade sa barin qasar yana malaysia acan yake zaune da iyalinsa gabaki dayansu. BOUKHAR Zadeen shine babba sai MAHMOUD Zadeen tukuna qanwarsu ZAYNEB, Matar Mahaifin nasu bata taba haihuwa dashi ba dan haka su kadaine yayansa wanda suka girma kowannensu ya zama babban mutum, A malaysia suka taso acan sukai karatu sai daga baya dukkaninsu su ukun suka dawo Nigeria tareda mahaifin nasu wansa tsufa yazo masa sosai. Bayan tsawon shekaru Anyiwa Zeynab aure da wani prof itama a porthacort, BOUKHAR da MAHMOUD kuwa kowannensu na qasa daban gurin karatu, Mahmoud ya riga boukar aure kuma daga mahmoud din har zayneb babu wanda ya samu haihuwa a cikinsu har saida Boukhar yayi aure shine ya fara haihuwa a cikinsu. Familyn ZADEEN's din sunada wani irin tarin arzikin dayake da yawan gaske da basuma san ya zasuyi dashi ba, Bayan arzikin mahaifinsu prof me tarin yawa su kansu sun tara na kansu me yawan gaske dan kuwa ko Zaynab datake mace a cikinsu itama tanada nata arzikin sosai. Suna tsananin son junansu wanda hakan ya saka iyalansu ma kansu yake a matiqar hade duk da su ukun gaba daya basa qasa daya. Mahir shine babban dan Boukhar zadeen wanda ya haifesa a Greece, Bayan haihuwar Boukhar Prof ya rasu wanda hakan ya saka dukkaninsu tattarowa suka dawo Nigeria. Mahaifinsu nada kadarori sosai wanda bazasu iya gama hadasu lokaci daya ba dan haka mahmoud ne kadai ya koma boukar kuwa dole ya zauna Nigeria tareda iyalansa. Umma matar mahaifinsu wadda ta riqesu tamkar yayan data haifa ba cuta ba cutarwa hannun Boukhar ta dawo dan yayansu ma basusan cewan ba itace ta haifi iyayensu ba sbd kulawa da kaunar dake tsakaninsu ta uwa da yayanta. Mahir nada shekara biyar a duniya Zayneb ta samu ciki wanda yazo mata da matsala sosai sbd manyanci da dadewan datai bata haihun ba. Cikinta na sake gaba girman matsalarta na qaruwa wanda daga baya aka gano tanada heart diseases wanda basu taba sani ba. Hankalin familyn ya tashi sosai wanda ya sakasu dawowa da ita hannunsu aka fara neman mata lafiya. Lokacinda aka gama bincike sosai akan ciwon nata aka gano tana buqatan heart transplant maana dashen zuciya. Hankalinsu ya tashi sosai sbd ciwon nata bawai sbd zuciyar da zaa nema dinba sbd ganin sukeyi sunada dukiyar da zasu iya siyan mutum gaba dayansa su cire abinda sukeso a jikinsa. Cikinta na kaiwa wata tara suka tattara gaba daya familyn suka koma Greece sbd haihuwarta da basa fatan matsala komai kankantarta. Tin daga kan ummah da zayneb din da boukar da matarsa da mahir da mahmoud ma acan ya samesu da fmlynsa suka dawo zama. Cs akaiwa zayneb aka ciro mata Baby boy wanda Boukhar ne ya saka masa suna Ammar sbd har lokacin mijinta bai taho ba yana porthacort da matarsa daya dan haka suka suka tattara suka watsar. Tinda zayneb ta haifi Ammar bata sake lafiya ba sai ramewa takeyi tana wani irin hasken daya saka hankalin duk wanda yake familyn nasu tasu musamman yayun nata wainda suka ringa nema mata donors tako ina amma babu inda aka samu, Sassaucin da suke samu a zuciyoyinsu shine likitoci sun tabbatar musu da akwai sauran time sosai kafin zuciyar ta gaza gaba daya dan haka suka ringa zubarda dukiya qasa qasa suna neman donor. Ammar kuwa kusan Mimi ce mahaifiyar mahir matar Boukhar din ta renesa tin daga ranar da aka haifesa itace ta zama uwarsa dan ko nonon mahaifiyarsa baisha na wata biyar ba wata hudu aka ciresa daga nonon sbd bazata iyaba ta bushe sosai. Duk wannan ciwon da haihuwar mijin zayneb din baizo yaga matarsa da dansa ba sai so daya dan haka su kuma basajin zasu taba basa ita ta koma bare Ammar da sukejinsa fiyeda komai sbd tsananin kaunar da sukewa kanwarsu. Ammar tinda ya taso ya samu mahaifiyarsa a cikin mummunan hali harya fara girma a hakan yake ganinta wanda hakan ya taba zuciya da kusan lafiyarsa dan kuwa yanada qawa zucin mahaifiyarsa sosai musammam daya fahimci baida uba bayan Boukhar wanda Suke kira da Dad Zad sai Daddy mahmoud wanda takanas ya bude babbar asibiti sbd ciwon Zayneb kawai dan samun donors. Mommah zayneb tinda ta haihu ta cire rai daga rayuwa sbd yanda takejin ita kadaice ta sani a hakan tana dauriya ne sbd ragewa yan uwanta damuwa da 'danta wanda ya sakata aransa sosai fiyeda komai. Sbd ciwon zayneb Boukhar da Ammar da mahmoud saida suka koma abin tausayi duk girman arzikinsu, Ummah kuwa babu ranar da bata kuka idan ta kalli yanda zayneb ta koma, Mimi kuwa sosai itama ta tashi akan Ammar sbd saida ya zama traumatised kwata kwata baya gane karatun komai a school duk da mahir yana kokari sosai akan dan uwan nasa amma saida teachers suka gano suka bada shawarar Ammar din ya fara ganin likita. Ana cikin hakan ne Mimi ta samu ciki wanda itama ta fara shiga matsalar rashin lafiya me nauyi sbd ga cikin dayazo da ciwo ga lalurar Ammar ga kuma ta familyn da kowa yake cikin damuwa da qunci. a wannan lokacin ZAADENs suka shiga matsanancin halin damuwa da qunci, Gasu da abin duniya me tarin yawan da basa ma san menene rashi ba ko wata kalmar datai kama da hakan amma sam basa cikin farin ciki. A haka cikin Mimi ya isa haihuwa ta haifi Saleem wanda haihuwarsa ta fara dawo sa farin ciki rayuwarsu. Mahir da Ammar kusan tare suka taso kaman ba shekaru sosai tsakaninsu sbd kaunar datake tsakaninsu tafi karfi akan wadda ke tsakanin mahir din da saleem. Haihuwar saleem da shekaru biyar Allah yayiwa zayneb rasuwa bayan ta gama qarewa ta koma kamar qaramar yarinya hakama anyi mata dashen zuciyar wanda ta samu chronic rejection maana transplant failure. Rasuwar Zayneb ta girgiza duniyar ZADEEN's gaba daya ta yanda tin daga lokacin suka sauya kaman basu din ba. Ammar ya shiga sabuwar trauma wadda ta sakasu barin qasar gabaki dayanta sbd a sauya environment a bisa shawaran doctors dake dubasa. Daddy mahmoud ma barin qasar yayi kwata kwata ya koma Nigeria. Dad Zad kuwa UK ya koma da iyalinsa da ummah suka bude sabuwar rayuwa acan doctors kuma na duba lafiyar Ammar wanda kansa kamar ya tabu amma ahankali ahankali ya samu sauki harya koma karatunsa tareda yan uwansa. Hankalinsu ya kwanta rayuwarsu ta koma ta asalin jin dadi da kwanciyar hankali arzikinsu kuwa sai abinda yaketa qara yin gaba duk da ciwon rashin Zayneb yana zuciyar dadzad kwata kwata ya kasa dena jin radadin rasata hakama Ammar ya kasa cire ciwon da rashin mahaifiyarsa yabar masa duk da ya danne ya koma kaman kowanne dan adam karatu yakeyi sosai. Mahir,Ammar da saleem ZADEENs sun taso cikin wani irin gata da hutu tareda rayuwar rashin kwaba da rashin sanin mahimmanci komai da kowa bayan abinda sukeso. #MAMUH #ZADEENS #LIMBAS #BESTLOVE #BESTSTORY ##CRAZYLOVE ZAFAFA BIYAR KALBIM 500 mamuhgee A DUNIYATA 500 Huguma AJIYA A DUHU 500 Billyn Abdul KIRJIN ME HANKALI 500 Miss xoxo Pay at 0022419171 AccessBank Maryam sani gummi Shedan biya 09033181070 Or mtn vtu at 09032345899 *_KALBIM_* _Mamuhgee_ #ZafafaBiyar 3 *ZUZEAMVENTURES* 08144015291 Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 3800 Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki *********** Mahir Zadeen shine kokarin naci akan komai saiya gano komai akan duk abinda yaga zai shiga rayuwarsa ko ta familynsa, Baya maamala da mutune ko abu ko wane iri ne kuwa batareda ya samu sanin mai zurfi akansa ba, Bayan familyn baya son kowa dan hakan ne ma baya shiga mutane sosai ko hulda dasu hakama bai yadda kowa ya kusanci fmlynsa ba sbd bai yadda da kowa ba akansu, Hakama tin kafin shekarunsa sukai ya fara shiga huldodin familynsa sbd bi da kauce duk wani abu da zai cutatar dasu ko dukiyarsu. Allah ya basa wani irin sharp kai da qwaqwalwa kamar maye dan hakan ne yasa dole da wuri su Dad suka bari ya shiga huldan duka zadeens babu wanda bai sani ba. Hakama tin daga Dzad da daddy mahmoud babu wanda yake boye masa komai sbd ganin wani sharp kaine dashi. Ammar ma yanada ilimin sosai sedai trauma dinsa tana damar masa da lissafi so da dama dan haka shi ya kasance kamar mara hankali akan abinda yakeso, Akan familynsa zai iya komai me kyau da mara kyau bai damu ba, Kaf familyn ZADEEN's babu wanda yake kallan gaskia ko adalci akan yan uwansu, Sunada wani irin son kai da basa duba komai da kowa sai kansu, Babu ruwansu da ko rai zaa rasa indai akan buqatarsu ne ko abinda suke so kuma hakan tamkar a jininsu yake dan kuwa babu wanda bazai iya komaiba a cikinsu akan abinda suke so ko buqata, Inda tsananin son zuciyarsu da son kansu yayi mugun munana shine ko dayansu yake buqatan abu to zasu hadu su samar masa da abin nan koda kuwa hakan na nufin wasu zasu shiga mummunar matsala koda kuwa ta rasa rai ce su ba damuwarsu bane. ZADEEN's sunada power me karfin gaske,sunada kudi,sunada kwarjini sunada isa,sunada duk abinda dibbin mutane da yawa ke tsananin nema da so na rayuwa basu samu ba, Duk wannan lokacin da aka dauka bayan qara habbaka da samun power babu abinda sukeyi dan hakan ne ma ya saka koda basa zama a qasarsu sunyi suna da ficen da aka sansu dan kuwa ko a Nigeria din sunada power din da ko wasu masu mulkin basuda ita. Sukan taho Nigeria din sosai dukkaninsu sedai basa wani jimawa sosai suke komawa dan hakan kan yayan yake sake budewa da gogewa a harkansu sosai. Wani cikin Mimi ta samu wanda ya saka ya saka Ammar ajiye komai ya koma kulawa da ita sbd dukkanin qawa zucin dayake dashi da mommah akan mimin ya dawo Hakama wani irin tsananin so da kaunar cikin Allah ya jarabcesa dashi wanda ya ringa rokom Allah yasa mace zaa haifa a saka mata sunan mahaifiyarsa. Yanda Ammar ya kwallafa rai akan son cikin da fatar a haifi mace ya saka kusan kowa familyn tsananin son hakanta shigesa sai gasu dukansu kaf sun qwallafa ran Wata zayneb zaa haifa. Kusan komai ajiyewa sukai suka maida kaf nutsuwarsu akan cikin dan haka Mimi ta dage da adduar Allah ya bata mace sbd samunta shine hasken dazai qara cike rayuwar zadeens da suka kasa manta radadin rashin zayneb. Yanda kaf familyn suka duqufa da rokon samun Zayneb suka manta da komai zaka roqa ka roqi me albarka ko kuma zabin mafin alkhairi, Ita haihuwa sam ba sai wanda kakesoba Duk wanda Allah ya baka ka roki me albarka kawai kokuma lafiyayye. Tin daga kan ummah datake tsohuwarsu har kan duk wanda yake familyn Allah suka ringa roqo akan zayneb sukeso kota yayane Allah ya basu wata zayneb din da suka rasa. Hankalin Mimi fara tashi yayi ganin yanda duka hankalinsu ya gushe ko yayane so suke Allah ya karbi Addua da fatansu. Damuwa da tsoro ya saka naquda zuwar mata batareda cikin ya isa haihuwa ba dan haka suka dunguma asibiti. Ko asibitin da aka kaita babu me zuwanta sai wanda yakeda matsayi da kudin da kusan koina ka san dashi dan haka tin tana ciki aka fara yada ZADEEN's na shirin welcoming sabuwar princess din familyn. Tsaron asibitin kadai zakasan masu abin duniya ne a asibitin dan haka Kusan su kadai ne a asibitin ranar. Naquda sosai Mimi tayi kafin Allah ya bata ikon haihuwar abinda suka roka 'Ya mace Kyakkyawa da ita fara tas kuma kusan kammanin mommah zayneb din ta dauko dan kusan familyn kamanninsu daya shiyasa suke da wani irin kyau da kwarjini dukkaninsu tin daga kan su dzad din. Tin a asibitin Dad ya saka mata sunan ZAYNEB BOUKHAR ZADEEN bayan ya dauketa da hannuwansa yanajin soyayyarta da kaunarta fiyeda duka sauran yayan daya haifa sbd tsananin kaunarsa ga zayneb da suka rasa. Mahir ma jin yayi tafi masa duk abinda suka mallaka dan haka ya rungumeta sosai yana addua. Saleem kuwa take yaji zai iya komai akanta. Ammar ne na karshe a daukanta sbd idanuwansa da suka ciko da hawaye zuciyarsa na harbawa da wani irin tsananin kaunarta dan fuskan mommansa kawai yake gani akan nata ga kuma sunan da Dad ya ambaceta dashi na mommansa. Ahankali ya rungumeta a kirjinsa hawayen dake idanuwansa na gangarowa ya bude baki Ahankali yace "JANNAH" Tausayinsa me tsananin gaske ne ya rufe Mimi ta miqa masa hannu tana kokarin boye nata hawayen sbd rasuwar momman data dawo musu sabuwa. A sanyaye ya qaraso gurinta ta nuna masa gefenta ya zauna ahankali yana kama hannunta daya datake miqa masa ta dan kwanta gefen jikinsa tana cewa "Ka samu jannah" Murmushi yayi yana zubawa fuskan babyn idanuwansa tana baccinta hankali kwance kamar ba rai a jikinta. Saida Mimin ta kwana asibiti kafin aka sallamesu suka koma gida cikeda farin cikin da suka manta rabonsu da irinsa. Haihuwar Jannah zadeens itace babban Farin cikin daya cike gaba daya rayuwar ahalin gabaki dayanta dama duk wanda yake muaamala da huldan business dasu, Duk wanda yake aiki a karkashinsu ma yayi farin cikin samun jannah sbd tayasu farin ciki dan haka tin tana jaririyarta duniya tasan da irin tsananin son da Ake mata, Duniya ta sheda jannah zadeen itace hasken idaniya da rayuwar ZADEEN's. Rayuwarsu ta dawo kamar sabuwar duniya da suke barewa a leda yanzu, A baya komai ma wasa ne a yanzu ne ZADEEN's ke sake zamowa ZADEEN's da kowa yake shakka gashi daddy mahmoud ma ya dawo da familynsa sun hade sun sake bunqasar datake bawa mutane tsoronsu amma har lokacin matarsa shi bata haihuba amma bai wani damuba sbd yayan 'dan uwansa da Ammar dan zayneb sun ishesa. *******A DAYA BANGERN KUWA CAN BAYA. Kauyen Bondi Ruwa akeyi sosai tsakiyar dare guraren karfe daya da rabi gari yayi tsit babu kowa babu komai bayan ruwan da suke sauka sosai da karfi. Qaramin gidan ne sosai wanda rabinsa yake a zube katangar ruwa ya zubar tintini. Dayan bangaren da bai fadi ba daki daya ne sai qaramin ban daki wanda shima rabinsa ya zube buhu ne a rufe da rabin, A cikin dakin macen datake kwance tana hada wani irin zufa me tsananin gaske duk da sanyin ruwan da akeyi yana zubowa cikin dakin daga sama sbd gefe daya langa langar dakin ya bude. Dan ta dake gefenta idanuwansa sunyi jajir sbd tsananin dacin ganin mahaifiyar tasa a hakan. Tsohon cikin dayake jikinta ya kalla idanuwansa suka sake kadawa sbd damuwa da dacin a halinda mahaifiyarsa zata haifo masa kaninsa ko kanwarsa. Hannuwansa ya miqa ahankali ya janyo zanin da bayada sanyi ya rufawa Umman tasa ya bude bakinsa da muryansa me sanyi yace "Umma sannu" Kasa magana tayi sbd wani tsananin azababben ciwon marar daya taso mata tanaji jini na balle mata amma ta danne cikin tsananin azabar da bata taba jinta ba sbd batason daga hankalin 'danta dayake shi kadai hasken rayuwarta da batada kowa sai shi hakama batason ya gani ya duk da tasan duk ayita a qare shine zai tayata haihuwar kila tinda batada me taimakonta a rayuwar nan yanxu bayan shi data haifa. Daqyar ta iya bude idanuwanta da sukai tsananin nauyi ta kalli farar fuskansa ta asalin fulani da dasashiyar murya tace "ABDULAZIZ" kasa dagowa yayi ya kalleta sbd hawayen da suka ciko idanuwansa yanajin duk duniya babu abinda ya tsana kamar dangin mahaifinsa da suka kasa taimakon mahifiyarsa bayan rasuwar mahaifinsu. Numfashi take kokarin saukewa cikin azaba sbd sanin taurin zuciya irin ta ABDULAZIZ har abada bazai taba so da kaunar ko mutum daya a cikin dangin mahaifinsa ba dan duk da abinda ya tsana da gaske yake tsanarsa. Jini ne ruwan dayake zubo musu ya gangaro daga karkashin Umman. Jajayen idanuwansa ya dago cikin duhun daren zaiyi magana sai kawai umman ta masa wata irin riqo me qarfin gaske tana rintse idanuwanta cikin azabar gaske tayi wani irin nishi take ta haifo abinda yake cikinta. Hawayen azabar ne suka gangaro musu shida umman a tare sbd irin riqon datai masa amma jin kukan jaririyar ya sakasa bude idanuwansa duk da baya ganin komai sosai ya sunkuyar da kai yana Godewa Allah cikin hawaye duk da ba wasu shekaru ne dashi ba sosai iyakacinsa shekaru goma sha hudu. Batason abinda zai saka Abdul din yasan meyake wakana dan haka ta dade da tanadar rezanta dan haka da kanta ta yanke cibiyar ta dauki yar hannunta na rawa da hannu ta shafa gabanta taji mace ce dan haka yaye zanin daya rufa mata ta saka yar a ciki ta miqa masa tana numfashi daqyar sbd jinin dayake neman bugar da ita. Hannuwansa rawa sukeyi sosai ya karbeta tana bude idanuwansa sosai a cikin duhun dan yaga halinda umman take ciki amma baya ganin komai. Shiru dakin ya sake dauka yana rungume da yar yana jin wani irin tsananin so da kaunarta da yakejin ko rayuwarsa zai iya badawa dan bata kariya itada ummansa. Kanwarsa ce uwa daya ta haifesa hakama daga tsotsan uba daya suka fito kuma batada kowa bayan shi da umman, Hakama ummansa batada kowa sai shi, Shine zai zama gatanta itada umma koda kuwa zai rasa ransa to tabbasa zaiyi gwagwarmaya dan inganta rayuwar su biyun nan. Guraren asuba ruwan saman ya dauke dan haka ya ciro yarinyar daga jikinsa ya kwantar gefen umman ya fita cikin duhun ya nufi can karshen kauyen gurin macen da ita kadaice aminyar mahaifiyarsa duk kauyen kuma ita kadai take taimaka musu. #MAMUH #AZIZ AY LIMBA #BESTLOVE #BESTSTORY #HEARTTRANSPLANT #JANNAH ZADEENS #UMMITA LIMBA ZAFAFA BIYAR KALBIM 500 mamuhgee A DUNIYATA 500 Huguma AJIYA A DUHU 500 Billyn Abdul KIRJIN ME HANKALI 500 Miss xoxo Pay at 0022419171 AccessBank Maryam sani gummi Shedan biya 09033181070 Or mtn vtu at 09032345899 *_KALBIM_* _Mamuhgee_ #ZafafaBiyar 4 *ZUZEAMVENTURES* 08144015291 Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 3800 Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki ************* Duk duhu da tsit din daren baitaba jin tsoronsu ba dan a haka ya taso komai dare haka yake ratsasa gurin nemowa ummansa Abincin da zata sakawa cikinta sbd ita da babyn datake cikinta su rayu. Tafiya yayi mai nisa kafin ya isa gidan da zashi din, Kofar gidan ya tsaya idanuwansa da sukai jajir ya dago ya kalli kofar gidan yana jin zuciyarsa na quna sbd baida ikon buga kofar bisa ga dokar mai gidan, Ya saba komai dare haka yake zuwa ya buga kofar gidan idan mahaifiyarsa bata lafiya sbd Mama Sakina taje ta taimaka mata, Mama sakina kuwa komai dare yaxo ya buqaceta bata taba fashin xuwa komai fadan da mijinta zaiyi kuwa, Duk masifarsa da tsanar da yayiwa Abdul din da mahaifiyarsa sbd sun hanasa kwanciyar hankali da masifar rayuwarsu amma hakan bai taba saka sakina janyewa daga garesu ba sbd kauna ce sosai a tsakaninta da Fatimar da bazata iya barinta a mummunan halinda take ciki ba itada Abdul. Ba so daya ba mijinta ya saba yiwa Abdul din dukan tsiya sosai akan zuwar masa gida tsakiyar dare. Zafafan hawaye ne suka cika idanuwansa yana kallan kofar gidan kaman zuciyarsa zata fashe da ciwo da radadin bazai iya kiran Mama sakinar ba dan yana taba kofar gidan baba ilan dukan da bazai iya bawa ummansa kulawa ba a yanzu datake tsananin buqatansa zai masa shikuma bazai iya barin komai ya samesaba a yanzu dayake son kulawa da umman da 'yar data haifo musu. Gefen kofar gidan ya koma kadan ahankali ya durqusa yana sunkuyar da kansa qasa dan jiran ayi kiran asubar da yasan lokaci yayi insha Allah. Wani irin sanyi ake kadawa sosai Sauran ruwan da aka dan dauke suna yayyafowa akansa ahankali suna ratsasa amma bai ko matsaba bare alamar tashi bakin kofar gidan. Jiran kusan awa daya da mintina yayi kafin masallaci daya kwal dayake kauyen suka rangada kiran sallan daya sakasa miqewa da dauri kafafunsa da sukai wani irin riqewa suka kasa daukansa ya zube a gurin cikin ruwa da lakar datake lalace sosai da kofar gidan. Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa data fara bushewa tin yana karamin nasa ta masa wani irin nauyi yana jin kirjinsa na masa ciwo. Hawaye masu dumi ne suka gangaro masa ya dafa yana kokarin miqewa aka bude kofar gidan. Baba ila ne da babban dansa dayake uztaz wanda shi yake sako uban nasa gaba zuwa masallaci lokutan asuba a gida yake sallan baya zuwa masallaci da asuba. Bude kananun idanuwansa masu kama da kamar an kashe kwarkwata ya waresu akan Abdul din duk da akwai duhu sosai har lokacin amma baya buqatan wahalarda kansa gurin sanin waye dan kai tsaye yasan baida tsohon dan iskan dazai zuwar masa gida bayan Abdul din wanda yake fatar Allah ya nuna masa sunbi duniya sunbar kauyen ko gidansa zai huta da maitar Abdul din. Cikin zafin rai ya harbi Abdul din da kafarsa yana cewa "Uban waye a kafar gidana cikin duhun nan?? Cikinsa daya harba ya dafe da hannunsa daya yana dagowa cikin tsananin azaba ya dafa hannunsa daya ya miqe yana kokarin bude baki zaiyi magana Baba ilan ya rigasa da cewa "Nace uban waye ne a gurin? Gali dayake gefen baban fitilar hannunsa ya kunna yana haske Abdul din da ita cikeda mamakin ganinsa duk da yasan yana zuwan amma a cikin ruwa da sanyin nan me yakeyi a kofar gidan wanda da alama ya dan jima. Wasu hawayen ne suka sake gangarowa daga jajayen idanuwansa kafin ya bude bakinsa muryansa a sanqare da sanyi duk da yasan suna sane da waye din amma bude baki yayi yace "Nine Abdul" Katsesa Gali yayi da cewa "Lafiya kuwa cikin sanyin? Bude baki yayi zaiyi magana amma Galin ya wuce cikim sauri yayi masallaci sbd jin angama kiran. Baba ila ne ya kallesa cikeda baqin ciki da tsana me tsananin gaske yace "Allah ya tsinewa sanayyar datake tsakanin Sakina da Uwarka dan kuwa babu abinda kuke qararta dashi sai baqin talauci da baqaqen masifun da kuke yawo dashi, Ace har tsakar dare bata huta da masifunku ba, Yanzu ubanme zatai muku da asubar farin?? Wani abu me daci da nauyi Abdul ya hadiye kafin ya bude baki yace "Haihuwa ummana tayi" Cikin sabon baqin cikin daya tirniqe baba ilan ya tsaki tsokin daya saka Abdul din rintse idanuwansa yace "An haifowa sakina wata sabuwar Masifar kenan,to wlh tallahi baa gidana ba, Na gaji bazan iya ba,duk yanda nake shan rantsuwa da masifa sakina ta ture bata ji bata gani saita ringa daukan abincin danake wahala ina nemowa na gidana ta baku to daga yau ankai karshe sbd bazai yiyu ni ban tara nawa yaran dazan ringa ciyarwa ba haka kawai na koma ciyar da 'yayan wani katan" Juyawa yayi ya koma ciki yana fasa zuwa masallacin bakinsa na cikowa da kumfan masifa sbd yasan yana tafiya wlh sai an dauki abincin gidansa ko wani abin antafi dashi sbd sakina dai sedai ya barwa fatima da 'danta dan bazata iya rabuwa dasu ba. Abdul cikin tsananin sanyi da azabar data gama shigarsa ya bi bayan baban da sauri dan kada ya hanasa ma shiga. Kai tsaye dakin sakina ya nufa ya kiran sunanta cikin tsananin baqin ciki da masifa taresa bacin rai yana cewa maza ta fito. Daman ba wani nauyin bacci ne da ita ba dan haka cikin bacci taji yana kiran sunanta da karfi ta bude idanuwanta tana kokarin tashi zaune ya shigo dakin sbd daman baa dakinta ya kwana ba ranar a dakin uwargidansa ya kwana. Yana shigowa dakin ta lalubo fitilarta ta kunna haske ya wadata dakin, Akan Abdul dayake tsaye a kofa bai qarasa shigowaba idanuwanta suka sauka. Faduwa gabanta yayi da sauri ta janyo dankwali tana daurawa akanta ta miqe daga katifar datake kai tana ambatar sunansa baba ila ya katseta da cewa "Ayau idan har kika fita gidan nan kika bi yaron nan gurin uwarsa wlh tallahi a bakin aurenki hakama abinci na ko wani abin dayake nawa a gidan nan kika basu shima a bakin aurenki, Bazan iya ba na gaji da renan 'da da uwar da banda hadi komai dasu bare yanxu wata wahalar da aka sake haifowa...... Da sauri sakina ta dago idanuwanta da ciko da hawayen tashin hankali da firgicin maganarsa ta farko ta kalli Abdul jin maganar haihuwar. Shima dago jajayen idanuwansa yayi ya kalleta cikeda girgiza da tsoron abinda Baba ilan ya fada. Gangarowa hawayensa masu tsananin zafi sukai ya dan ja baya ahankali batareda ya iya cigaba da tsayawa ba sbd bai san me zai fadawa mama sakinan ba kuma. Bude baki tayi ahankali tace "ABDULAZIZ" Cak ya tsaya batareda ya dagoba. Kofar inda kayanta suke tai batareda ta cewa baba ilan komaiba, Zannuwan kayanta na sakawa masu tsafta ta dauko tareda guda biyu da rigarta ta sanyi daya da ita kadai takeda ita ta dauko wanda itace da kanta ta siya abinta da yan kudinta. Inda take ajiye kudi ta duba tana saka hannu cikin kofin silver me murfi taji babu komai a ciki. Juyawa tayi ta duba gurin ajiyarta daya taga dari bakwai ne kadai da ita dan haka ta dauko dari biyar ta juyo ta nufi kofar ta fito. Kayan ta miqa masa cikeda kunyarsa duk da yana qaramin yaro ta bude baki asanyaye tace "Ka siya mata koko me zafi sauran canjin ka siya itace ka dafa mata ruwan zafi tayi wanka itace da abinda aka haifa" Hawayensa ne suka gangaro ahankali suka sauka akan dari biyar din data dora masa a tafin hannunsa. Kasa magana yayi kai ya gyada mata ahankali yana damqe kayan hannuwansa na qara daukan sanyi. Baba ila daya kasa motsawa sbd baqin ciki da mamaki kallanta yayi ita kuma taqi kallansa Baqin ciki sake rufesa yayi kamar zai fashe sbd baqin ciki yace "Sbd ki nunamun ban isaba shine a gaban nawa ko matsawa daga inda nai maganar banba zaki dauki abubuwa ki basu?? To meye amfani na a rayuwarki sakina tinda kinada Fatima da 'danta ai saiki fice ki bisu kije na bar musu ke wlh" Abdul kafafuwansa da sanyi yayiwa mugun shiga ya ja ahankali yabar gurin yana qanwame kayan data basa da kudin. Yana ficewa gidan Mama sakina ta dago ta kalli baba ila har zatai magana sai ya katseta cikin tsananin zafi da cewa "Wlh tallahi na barwa fatima ke kawai ki tattara ki bar mun gidana ki bita can saiki kwasheta kiyi kauyenku da ita da 'yayanta" Kofa ya nufa yana ball da butarta dake hanyarsa ta wucewa yana jin zuciyarsa na wata irin tafasa da bacin rai me tsanani. Numfashi me sanyi da mutuwar jiki ta sake tana danne zuciyarta akan furucinsa wanda shedan ke ingizata data bar masa gidan nasa ta tafin sbd su fatima sunfi buqatarta amma kuma girman auren nata take kalla ta danne zafi da bacin da ranta yayi dan yanzu ne zata biye masa suyita masifa a cikin gidan har wayewar gari da wuni zasu iya wuni suna masifa. Butarta dayayi wurgi da ita ta nufa ta dauka tana qarasa zubar da ruwan ciki da suka rage ta nufi gurin diban wasu ruwan tana duba butar idan bai fasa mata ita ba. Tana diban ruwan bandaki ta fara shiga tana fitowa tai alwala ta shige dakinta. #MAMUH #ZADEENS #LIMBAS ZAFAFA BIYAR KALBIM 500 mamuhgee A DUNIYATA 500 Huguma AJIYA A DUHU 500 Billyn Abdul KIRJIN ME HANKALI 500 Miss xoxo Pay at 0022419171 AccessBank Maryam sani gummi Shedan biya 09033181070 Or mtn vtu at 09032345899 *_KALBIM_* _Mamuhgee_ #ZafafaBiyar 5 *ZUZEAMVENTURES* 08144015291 Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 3800 Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki ************ Abdul kuwa yana fita gidan tafiya me dan tsayi yayi kafin ya durkushe a gurin yana fasa wani irin kuka me tsananin gaske sanyin gaske na ratsatsa. Saida aka fito masallaci kafin ya daure ya qarasa gida, Koda ya isa zanin dayake rufe da umman me sanyi kawai ya yaye mata ya rufa mata daya daga cikin wanda mama sakina ta basa, Leqa babyn datake kwance gefen umman yayi yaga bacci takeyi lafiya kalau dan haka ya fice. Alwala yayi ya dawo daga kofar dakin ya samu inda yayi sallah. Yana idarwa ya dawo cikin dakin ya taba ummansa yaga tana numfashi. Ajiyar zuciya me tsananin sanyi ya sauke kafin ya fita sbd gari ya waye sosai. Gurin me siyarda koko ya tafi Sai alokacin ma take hada wutar hada kokon dan haka yabar kudinsa ya koma ya nufi daji ya samo abinda zai hura wutan ruwan zafin da mama sakina tace. Duka sun jiqe abubuwan daya tsinto amma hakanan yaje ya siyo ashana ya karbo kokon daga nan ya kawo mata. Daqyar ya iya taimakawa umman ta tashi zaune ya dora mata robar kokon wadda ta bude bakinta daqyar kokon na shiga wanda zafinsa ya sakata jin hanjinta da suka nade suka dunqule fara warwarewa harma cikin na dan mata ciwo. Tana gama shanye kokon amai ya taso mata gabaki daya ta amayar dashi. Wutar ya hau hurawa wadda ta cinye gaba daya ashanar daya siyo sai daya koma ya qaro wata itama saida ta kusa qarew kafin wutar ta kama jikinsa na rawa ya dora ruwan. Hura wutar ya zauna yanayi sosai batareda ya hutaba har saida ruwan sikai zafi sosai. Umman daqyar ta iya tasowa ta nufi bandaki yakai mata ruwan shima ya fito ya dauko babyn ya fito daga daki sai a lokacin ya zuba mata idanuwansa yafara yi mata wani irin kallan tsafta me hade da wata irin kauna me tsananin gasken da batada sirki. Wanka sosai umman tayi ta gyaro kanta ta fito har lokacin bata iya ko tsayuwar kirki. Uwar haihuwar data bari a dakin ta shiga ta dauko ta goma gefen gidansu daya zube ta binneta daqyar jikin yana kakkarwa sosai sbd jirin gaske ma take gani. Yana ganin hakan ya shiga dakin da sauri ya dan gyarosa ya share ya goge duk sanyin dakin tas ya sake shimfida mata wani zanin akan qaramar katifarsu umman ta kwanta. Fita yayi ya sake siyo mata koko da saura Canjin daya rage ya kawo mata sedai koda ya dawo gabaki daya ta fice hayyacinta bama zata iya ko motsawa ba bare sanin meyake fada. Ajiye robar hannunsa yayi yana kokarin dagota amma gaba daya jikinta ya sake. Ambatar sunanta yafara yana shafa fuskanta zuwa wuyanta kuka na zuwar masa sosai. Kuka me qarfin gaske babyn datake gefensu ta fasa wanda ya sakasa saurin juyowa yana rasa ya zaiyi. Kuka sosai baby tafara wanda ya sakasa sakin umman ya zauna tsakiyarsu yana sunkuyar da kai shima ya fara kuka yana wani sheshekan da har jikinsa rawa yakeyi. Ya jima a hakan batareda yasan me zaiyiba har babyn ta gaji tayi shiru ta koma bacci. Ummansa kuwa wata firgita ta fara tana jijjiga. Qanqameta yayi yana ambatar sunanta amma batasan ma yanayi ba. Kusan awa daya a hakan kafin jikinta ya sake sakewa tayi baccin wahala. Shima a gurin cikin jikinta baccin walaha da yunwa ya daukesa. Sai azahar ya farka ya fita gidan ya nufi gurin aikin lakar dayake zuwa yana dan tayasu suna basa nera dari. Acan yayi sallah yayita musu aiki har wanda yafi karfin shekarunsa. Daga can wani kokon ya sake siyowa ya kawo yasha shida umman wadda sedai ya bata daga kwancen dan bata iya tashi hakama gabaki daya ta koma kamar ba umman tasa ba sbd wasu abubuwa takeyi da fizge fizge da zabura. Yamma nayi yasan baba ila baya gida dan haka ya dauke babyn ya rufeta da zani kusan uku ya nufi gidan mama sakina da ita sbd tanada kuka. Harya isa gidan babu wanda ya taresa ya tambayesa sbd gudunsu ma akeyi a kauyen sbd camfa ummansa da akai da baqar mace. Mama sakin wuni tayi cikin damuwa da tinaninsu dan haka tana zaune tana hada saka da warwara tagansa ya shigo da zani kallo daya tai masa ta gane jaririyarce ya dauko. Cikeda mamaki da tsoro ta kallesa tana miqewa ta karbi 'yar tana cewa "Abdul meyasa ka fito da ita?? Yaya ummanku? Ya jikinta? Kasancewarsa mara hayaniya da rashin sabo da magana sosai sbd baida abokan wasa ko wasu yan uwan daya taso cikin gata yasa ita kadaice ma wacce yake magana da ita sosaima Ya dan dago kansa batareda ya kalleta ba yace "Tanata kuka ne tin dasafe, Umma kuma batada lafiya tanata firgita" Kasa cewa sakina tayi ta nufi daki takai yar da sauri tana fitowa ruwan zafi tafara dorawa kafin ta dauko abincinta na rana da bata samu ci ba sbd damuwa ta miqa masa tace "Maza zauna ka cinye yanzu" Zaunawa yayi yaci abincin ita kuma tana sauke ruwan dauko babyn tayi tahau yi mata wanka sbd batason baba ila ya dawo ya taddasu hakama batason yayi dare a hanya da 'yar. Wanka sosai me kyau tayi mata duk da bata taba haihuwaba batasan yaya akeyiba amma dayake anata haihuwa a gidan tana gani kuka tana dan saka hannu sai ta iya. Tana gama mata wanka kayan data siya guda daya na jiran haihuwar matar Gali 'dan mijinta ta dauko ta sakawa yar ta dauko madarar shanun datake da ita me kyau ta bata kuma cikin ikon Allah yarinyar tasha take ta koma bacci abinta. Sake nade masa ita tayi sosai ta basa tace maza ya koma. Karbanta yayi ya juya ya fice daga gidan. Koda ya isa gida ummansu ta tashi tana zaune ta zubawa kofa idanuwanta da sukai fari fes hakama bakinta ya bushe sosai. Cikeda mamaki da dan farin cikin ganin ta tashi ya qaraso yana cewa "Umma kin samu lafiya? Juyo idanuwanta da suke kamar a buge tayi ta zuba masa batareda tace komaiba sbd kamar ba yayanta bane take gani. Sake tambayarta yayi yaga ko kyaftawa idanuwanta basayi kallansu takeyi numfashinta baya fitama daidai. Babyn ya bude daga zaninta ya dora mata a hannunta yana cewa "Mama sakina tai mata wanka ta saka mata kaya" Babyn ta saukar da idanuwanta ta zubawa ido tsawon mintina kafin ta dago ta zubawa Abdul din idanuwan shima Shima ita yake kallan cikin tsoron irin kallan datake musun. Sakin babyn tayi da sauri ya tare tareda daukanta ya ajiye gefensu yana cewa "Umma kin gaji ne? Har lokacin batace komaiba bata kuma dena kallansaba kaman wanda bata saniba ko bata taba ganiva. Zamewa tayi ta koma ta kwanta tareda zubawa babyn gabanta ido. Har dare yai suka kwanta batareda sun samu abinda zasu ci ba umman batai magana ba har lokacin hakama bata dena kallansu ba. Cikin tsakar dare cikin bacci yaji motsin umman ya bude idanuwansa sai yaga ta tashi zata fita ko dan kwali babu a kanta hakama bata ko iya tsayuwa da kyau. Kasa daukanta kafafunta sukai ta zube qasa kanta na buguwa da bangon kofar fita dakin take goshinta ya fashe da jini. Tashi yayi da sauri yana riqota cikin tsoro da tashin hankali yana cewa "Umma ina zaki? Zaki bandaki ne? Kallansa ta juyo tanayi kafin ta dago hannunta dayake wani irin rawa ta nuna masa kofa batareda tace komaiba. Kofar ya kalla kafin ya kalleta sai ya rasa me zai fada ya kamo hannunta kawai ya dawo da ita kuma ta biyosa kamar yarinya qarama. Kwantawa suka koma sukai take kuma saita koma baccinta. Gari na wayewa yaje yayo aikinsa ya dawo mata da koko ya sake dafa mata ruwa ya sake ficewa. Sai yamma ya dawo musu da tuwon dawa da miyar kuka dan kadan wanda aikin wahala yayi ya samosa. Kasa cin abincin umman tayi duk yanda yayi sa ita dan haka kaman yanda yake bata koko haka ya zauna ya bata abincin a baki da kansa. Babyn kuwa sake kaita yayi gurin mama sakina ta bata irin madaran jiya tasha ya dawo da ita gida. Yana dawowa a hanya ya hadu da ummansa tana tafiya tana jiri ba dankwali akanta, Da sauri ya kama hannunta suka juya gida yana mamakin abinda ya samu umman ga jikinta duk jini. Suna komawa gida ya zaunar sa ita yana mata magana amma kwata kwata batacewa komai kallansa kawai takeyi. Hawaye ya fara batareda yasan me zaiyiba. Da daddaren ranar ma so biyu tana kokarin fita yana dawowa da ita tim anan ya fahimci ummansa ta kamu da wani sabon rashin lafiyar. Kuka ya ringa yi har safe kuma da safen ma daqyar ya iya fita yabarta. Koda ya dawo bata fita ba amma tana zaune babyn nata kuka sosai kamar bataji sai kallanta takeyi idanuwanta sunyi jajir kamar zasu fashe. Daukan babyn yayi ya zauna gaban umman ya fada jikinta yana fasa kuka shima yana ambatar sunanta. Kukansa ne ya saka wani irin hawaye masu tsananin zafi da ciwon da bata saniba tsinke mata tana qanqamesa tana jin tsananin sonsa shi kadai dan shi kadai take jin sonsa amma babyn kwata kwata kamar bata santaba dan kanta dake kokarin juyewa koma ya juyen. Sun jima a hakan suna kuka duka su ukun harda babyn da suka matse a tsakiyarsu. Sun jima a hakan kafin umman tayi bacci da babyn shi kuma ya fita sallan magrib yana dawowa a gida yayi ishai sukai baccinsu. ***kwanaki suka fara tafiyar musu ahankali ahankali ya fahimta da kyau kamar ummansa ta haukace sedai hauka bame tashin hankali ba wanda asalin yunwa da infection ne daya mummunan shigarta a gurin haihuwar me mugun karfi daya juyar mata da kai kwata kwata ta manta wai haihuwa tayi. Mama sakina na cikin tsananin damuwa da tashin hankalin da suke ciki sbd yunwa da ciwo me karfin gaske na kokarin shigar babyn wadda tafara qanqamcewa ga Abdul din da shima wahala take neman kashesa da qananun shekaru. Abdul kuwa da ummansa sun koma masu baran karfi da yaji sbd duk zai tafi gurin aikin wahalar dayake yi binsa takeyi bata zama fitowa takeyi dan haka tare suke zuwa ya zaunar da ita guri daya wasu su bata sadaka sbd tinanin almajirace wasu kuma gudunta ma sukeyi. A cikin wannan halin sukai sati kusan uku sedai zuwa lokacin duk jamaar kauyen sun fahimci fatiman ta samu tabin kwakwalwa dan haka sadakar ma aka dena bata. ****FATIMA UMMITA shine sunan da Abdul ya sakawa qanwarsa dayake jinta kamar ransa dan kuwa shine me goyata da kansa duk yawon da zaiyi da ummansu yarinyar tana bayansa harya saba yanzu kauyukan gabansu suke zuwa tallan yalo dayake sara yana siyarwa. UMMITA daga baya umman na bata nono dan haka tafara lafiya ta koma cikakkiyar lafiyayyar baby sedai har lokacin sitirar sakawanta daya ce tak wadda mama sakina ta saka mata, Wanka kuwa sai suyi sati baayi mata ba sai daga baya yake kaita mama sakinata tayi mata harda hudan kunne tai mata ta saka ma yan kunne harda wasu kayan ta sake siya mata guda daya dan itama batada wani karfi. ##MAMUH #LIMBAS #ZAADENS #BESTSTORY #UMMITA LIMBA #JANNAH ZADEEN #DONOR ZAFAFA BIYAR KALBIM 500 mamuhgee A DUNIYATA 500 Huguma AJIYA A DUHU 500 Billyn Abdul KIRJIN ME HANKALI 500 Miss xoxo Pay at 0022419171 AccessBank Maryam sani gummi Shedan biya 09033181070 Or mtn vtu at 09032345899