Ajininsa yake 3-01 Posted by ANaM Dorayi on 06:55 PM, 19-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino face book, sakamakon haka muka yanke shawarar bude page a facebook din duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku, :-Whatssap. 08139787515 :-Blog Anamdorayi.mywapblog.com Saikuma ... :-Face book.. https://mbasic.facebook.com/ HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7% 2CPAGE_ID10%2C7370123473 Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin kanku.. Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin mu sanya littafi na gaba.. Naku har kullum ANaM Dorayi --------------------------------------------------------;------------------ Ya koma rigingine ya kwanta, ya rasa dalilin da yasa Nusaiba ta tinkare shi da wadannan maganganun banzan. So take ta hada shi da iyayensa ko me? Idan kuma ta gaji ne, ai bai yi mata tirke ba. Iyakar ta Alh. Basheer ya ce ya aje masa komai na sa, sai me? Daran nan Nusaiba bata yi barci ba, gaban Ubangiji ta gurfana kamar yadda ta saba kai kukanta. Allah ya za6a mata alkhairi. Haka kuma tayi kukan bakin ciki yau ita da mijin auranta take cacar baki. Lallai rayuwa shirin Allah ce, amma ko a mafarki bata ta6a tunanin hakan ba a rayuwar ta. A kodayaushe zuciyar ta na shirya mata kyakkyawar rayuwa da jin dadi tare da gamsashshiyar soyayya ga duk mijin da ta aura. A kunnan ta aka yi kiran sallar farko, ciwon kai ya ce ga shi nan irin wanda bata ta6a jin irin sa ba. Da kyar ta sallaci asuba. Ta jawo filo ta jefa bisa sallayar ta kwanta. Dora kan ta, ke da wuya ta ji fitar Naseer kamar da gudu. Ta tashi zaune tana sauraron buga kofar falon sasn su Abba. Ta mike ta fito kofar falonsu a gwame. Tayi waje can sasan su Umma. Naseer ta ji yana fadin,"Zarah ba lfy, yanzu Inna tayo waya inje maza-maza. Kafun su Abba su gama salati, ya fice. Ta koma daki da saurin ta, ta dauko hijab ta suro jakar hannu.don ta tabbata haka Naseer ya fita babu ko sisi ajikinsa. Ta fito, ta iske su Umma ma tsaye suke a waje, ya tafi ya bar su. Makullin motar ta na cikin jakar ta bude ta dauko,"Umma zo mu bi shi a wannan motar." Ta ce,"Ba ni so ki na yawon nan Nusaiba, cikin ki ya tsufa." Abba ya ce,"Gari bai k'arasa waye ba ma, kun tafi ku 2 mata a mota? Gara ku bari gari ya waye sosai." Ta ce,"Ba komai Abba, Allah zai tsare. Umma zo mu je yanzun garin zai waye." Umma ta shiga suka rankaya. Malam Balarabe na tayi masu addu'a. Hajaran majaran! Suka iske Naseer da Inna, domin ance jaririryar ta mutu a ciki, sbd haka Likitar za ta yi iya kokarinta su fito da ita, idan kuma abin ya faskara, aiki za su yi mata. Nusaiba ta nemi waje ta zauna jinin ta ya k'ara hawa, kan ta kamar ya tsage, sbd tsabar ciwo. Bayan kusan minti 40. Likitan ta fito ta ce, maza-maza su je su biya kudin aiki. Ta mika wa Naseer takarda, hannunsa na rawa ya rike ya duba. Dubu 35 zai biya. Umma ta ce,"Ka fito da kudi ko ko? Ya girgiza kai,"Sai na koma gida, kuma ina jin kudin da ke gidan dubu 10 ne kawai, banki kuma ba su fito ba, ya za'ayi kenan? Ya tambaya hankalin sa tashe. Kafin Umma ta ce wani abu Nusaiba ta miko rafar kudi, ga wasu yi maza kaje ka biya. Ya bi tada kallo kafin yasa hannu ya kar6i kudi ya kwasa da gudu ya nufi wajen biya. (Allah sarki baiwar Allah, Allah yahadamu da mata masu tausayinmu da kaunarmu) Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino face book, sakamakon haka muka yanke shawarar bude page a facebook din duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku, :-Whatssap. 08139787515 :-Blog Anamdorayi.mywapblog.com Saikuma ... :-Face book.. https://mbasic.facebook.com/ HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7% 2CPAGE_ID10%2C7370123473 Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin kanku.. Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin mu sanya littafi na gaba.. Naku har kullum ANaM Dorayi Nusaiba fa duk ta rude, ta k'ara rikicewa musamman yadda ta ga Nosis na shiga suna fita. Likitoci 2 ke kan ta, suna ta k'ara kokarin su, domin ba sa son ayi mata aikin. Allah da ikonsa kuwa Likitan da aka kira, yayi nasarar ciro matacciyar jaririyar, sai dai Zarah nan take numfashin ta ya dauke. Ba ta ba dalilinta, komai ya daina aiki a jikinta. Suka yi caa kanta, latsa nan, gwada can. Amma ba alamar motsi. Likita ya tura a dauko (Oxygen). Su Nusaiba na tsaye. Nos din ta fito da gudu, jim kadan ta dawo da shi da shige dakin. Zuciyar Nusaiba ta soma bugawa, ta nufin dakin tana fadin,"Shi kenan Antina! Su Umma suka rirriko ta, su ma kukan suke yi. Inna ta ce,"Zo ki zauna Nusaiba, kin ga ba ke kadai bace. Ki kwantar da hankalinki, ki yi mata addu'a. Tana shiru. Naseer na iso wajen, bai yarda da yanayin daya gansu ba. Ga Nusaiba na kuka tana ta fadin,"Shi kenan Antina." Ya ce,"Menene Umma? "Ba komai, ji ka ka gaya ma su ka biya kudin." Ya tsura wa Nusaiba ido, duk ta fita hayyacinta, ya ce,"Ki yi shiru mana." Ta ja hijabi ta rufe fuska, sannan ya wuce, ta biyo bayan sa. Yana isowa kofar. Likitin na fitowa. Ya mika masa takarda da siri,"Doctor an biya kudin,"Ya ce,"O.K, ka rike risit din za'a maida ma ku da kudin ku, an riga an ciro Bebin. Ita ma uwar sai dai ku yi hakuri.... Nusaiba ba ta gama jin bayayin ba, ta yanke jiki ta fadi, nan take ta hau fizga. Gaba daya suka yi caa kanta har da Likitan. Abin kamar bugun jinnu, duk gabobinta sun sandare, idanuwa sun kakkafe, baki kumfa. Likita ya ce, a kai ta ofishin sa. Naseer ya dauke cak! Ya kai ta ofishin, ya kwantar bisa dan gadon su. Su Umma ne biye da shi kamar za su yi hauka saboda tashin hankali. Shi kansa Naseer hawaye ne ke sauka bisa kuncinsa. Likita ya miko masa takarda,"Sa min hannu nan, dole a cire abinda ke cikin ta, don tsira da rayukansu." Bai jira Naseer ya gama sa hannun ba, ya fice da saurinsa. Jim kadan wasu Nosis suka shigo da gadon daukan maras lafiya, dukkan su da kayan dakin tiyata a jikin su. Irin kayan suka sanya wa Nusaiba, suka maida ta gadon da suka zo dashi, suka gara ta dakin tiyata. A tsakar wurin Naseer ya zube ya kame kan sa hannu 2, ya rasa duniyar da yake." Me zan gani yau? Inna-lillahi- wa"Inna-ilaihir-raji'un! Umma ce tayi karfin hali ta kar6i waya hannu Inna, ta kira Malam Balarabe,"Mallam ka yi maza ka zo, abubuwa sun rinca6e, daga Zarah har Nusaiba ba mu san halin da suke ciki ba. A zaton da mu ke yi ma dai Zarah babu ita. Nusaiba kuwa yanzu suka wuce tiyata da ita." Hankalin sa yayi mummunan tashi, salati yake yana k'arawa, har ya rufe gida, ya kama hanya. A mota ya kira Alh. Basheer ya labarta masa halin da suka wayi gari da shi. Subhanalillahi! Babu 6ata lkc suka baro Kaduna. Malam Balarabe na isa. Shi Malama Umar ya iso. Yadda suka same su zazzaune haka su ma suka nemi wuri suka zauna. Naseer na nan dunkule a kasa. Malam Umar bai ko shaida shi ba, sai da ya jima a wajen. Ya tashi ya matsa gun sa ya tsugunna ya dago kan sa,"Naseer! Tashi daga k'asan nan, zo nan ka zauna." Ya kamo shi ya taso da kyar, suka zauna bisa kujera, yana rungume da kafadar sa. M.Balarabe shi ma ya taso, ya tsugunna gabn su ya ce,"Sun bada gawar ne? Ya girgiza kai, hawaye suka kara kubce masa, ya ce,"Sun ce ba mutuwa tayi ba, doguwar suma ce, shine suka sa mata (Oxygen)Gaba dayan su suka sauke numfashi, suka yi hamdala ga Allah, tare da addu'ar Ubangiji ya ba su lafiya. Kamar wucewar minti goma da zuwan su Abba. Likita ya fito, duk suka mike suka nufi gun sa,"Yaya Likita? Yayi dan murmushi,"An yi nasara,"Bebi, na nan lafiya lau, shi da uwar sa. Za'a fito da su nan bada dadewa ba. Kowa sai hamdala. Umma da Inna suka rungume juna. Duk da haka hankalin Naseer bai kwanta ba, so yake ya gansu da idon sa, ya tabbatar da lafiya lau suke. An ba su izinin ganin Zarah na minti 5r. Haka suka yi tsaye gaban gadon suna mata kallon tausayi. Inna ta fara barin dakin ta dawo wajen ta zauna, tayi shiru hawaye na tsitaya, babu abinda za ta iya yi, komai Allah yayi, dai- dai ne. "Yan mintoci bayan fitowar su daga wajen Zarah, aka kawo ma su Bebin da aka ciro wa Nusaiba. Bebi ne katon gaske jajur da shi, sannan babu abinda ya bambata shi da Ameer. Illa girma daya fi shi. Kowa yasa masa albarka, suka mika wa Babansa. Ya zura masa ido kamar ya lashe shi so da kaunar Bebin suka kama zuciyar sa. Kwalla suka cika idanun sa,"Allah ka raya mi shi." Ya fadi a ransa.. A lokaci guda daran jiya ya fado masa, nan da nan ya mike ya ba Umma Bebi, ya fice da sauri ya sami wata kwana, ya hade kai da bango. Babu abinda ke yawo cikin ransa, sai maganganun daya cacca6awa Nusaiba, a idonsa yake ganin lokacin da ta miko masa rafar kudi, duk a tunanin take ganin halin da ta shiga. Wanda komai zai iya faruwa da ita. "Da mutuwa tayi da shi kenan, ta tafi ta bar ni da hakkinta a wuya na?" Ya fashe da kuka sosai, irin wanda bai ta6a yinsa a rayuwar sa ba. Ji yayi an kamo shi,"Malam Umar ne,"Haba Naseer, ka yi hkr mana, ka roki Allah ya ba su lafiya. Wannan koke-koken ai ba su da amfani. An san ka na cikin tashin hankali, amma jurewa za ka yi, ka zama namiji. Zo mu je, yanzu za mu tafi, don a samu a bizne jaririyar wajen Zarah. Yi hkr d'an gidan Inna." Ya goge masa fuska, ya riko hannun sa suka dawo. Yarinyar na lullube cikin zani, ya nuna wa Naseer ita, yayi jim, yana kallon ta, sannan ta dauke kai. Ya matsa kusa da Abba ya ce,"Ka zo da waya?" Ya ce,"Ga ta, ai na riga na gaya wa su Alhj, suna tafe." Ya ce,"To shi kenan, bari in kira Sageer." Ya kar6i waya, ya matsa gefe,ya kira duk wanda yake son kira, sannan ya maida wa Abba wayarsa, suka dauki shatan tasi ta maida su gida. Suna bada baya. Su Alh. Basheer na isowa. Abinka da asibitin Shika, sai suka rasa ina za su dosa, don haka ya kira wayar Naseer. Tana ta bugawa, amma da yake tana gida, babu mai dauka. Ya kira ta Abba, su kuma sun riga sun kusa gida, saboda haka Malam Umar yabasu lambar Inna, suka kira. Naseer ya fita ya nemo inda motar su tayi fakin. Yana isa wajen. Ummi ta fara kwalla. Yana neman tsugunnawa. Alhjn yayi sauri ya kamo shi,"Sannu Naseer ya fargaba? Ya ce,"Mun gode Allah." Ya ce,"Malam Balarabe ya ce ashe doguwar suma Zara tayi ko? Ya amsa da kai? Ya dan rungumo kafadar sa,"Ka yi hakuri kaji? Allah zai ba su lafiya." Ya gyada kai, ya dubi Ummi suka gaisa, sannan yayi masu jagora zuwa inda suke, suna tafe yana maida masu yadda abin ya faru. Bayan sun gaisa da su Umma. An jajanta wa juna, sai Alh.Basheer ya nemi ganin Likita. Abn ka ga mai kudi, nan da nan ya sami duk abubuwan daya bukata watau daki na musamman da likita shi ma na musamman. Kan ka ce kwabo, an hada Zarah da Nusaiba waje daya, an zuba masu komai na bukuta. Ummi na rike da Bebi, yana to son a zuba masa abinci a bakin sa. Da yake akwai kayayyakin Zarah, ruwan zafi kuma tana da zuma da dabino sbd tana yawan cin dabino, sai Inna ta kawo, duk Ummi ta ba shi, sannan ta dan kada zuma a ruwan dumi, ta cika masa ciki, nan da nan ya koma barci. Ganin hankali ya dan kwanta. Inna ta ce Naseer ya koma gida yayi wanka, daga nan ya kwaso wa Bevi kaya da ita Nusaiban. Yana fitowa su Sageer na shigowa shi da Fa'iza, dole ya sake komawa, suka gaida su Umma. Ya kawo masu Bebi suka gan shi. Wucewar 'yan mintoci 15 ya karbi mukullin motar Nusaiba, tunda ga Sageer zai tuka a maida ta gida. Sun yi fakin kofar gida, suka yi sallama suka tafi, ba tare da sun tsaya wani surutu ba, domin Naseer baya ma son yin magana. Yana shiga gida, ya tu6e kayan jikin sa, ya zaro sauran kudin da suka rage cikin rafar da Nusaiba ta ba shi. Ya zauna bakin gado ya zura masu ido, jim kadan ya sauke numfashi, ya aje su bisa filo. Ya wuce bayi ya sakarwa kan sa ruwa. Bayan yayi wanka, ya kimtsa ya kawo wayoyinsa da kudade ya zuba aljihu. Ya fito ya nufi dakin Nusaiba. Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Gaban hoton ta ya tsaya ya k'are mata kalo ba tare da ya san me zuciyar sa ke sakawa ba. Wadirof ya bude, ya d'ebo riga da Zani kala 5r. Yayi tsaye yana tunanin a ina zai ga kayan Bebi, tunda bai ta6a siyowa ya ce mata ga shi ba? Abinda ya yanke shawara shine ya shiga kanti, ya siyo. Wata zuciya kuma ta ce masa "Kai dai dudduba." Yana gama tunanin sa, ya nufi akwatuna ya fara budewa, abn ya ba shi mamaki, domin setin nan kaf kayan Bebi ne ciki a mak'are. Yayi shiru duk al'ajabi ya ishe shi, ya nemo jaka ya debi kaya iya dibar sa, kayan shafe-shafe, su pampas da setin bahon wanka, wanda komai na bukatar wankan Bebi. Akwai shi a ciki. Ya loda kaya a but, ya sallami Abba ya koma asibiti. Yana shigowa da kaya niki-niki, ya iske Zarah ta farfado, sai faman kuka take yi, sbd jin abin daya faru da Nusaiba. Su Umma na ta bata hkr. Ganin Naseer ya shigo, dukkan su suka fita waje.Ya matsa wajen ta ya zauna gefen gadon, da sauri ta fado masa ta sake 6arkewa da kuka. Idanuwan sa suka cike da kwalla, ya kasa cewa uffan tsawon lokaci. Sannan ya dagota, ya share mata hawaye ya ce,"Ya isa haka. Ya jikin? "Yayi sauki. Ashe abinda ya faru kenan? Ya ce,"To yaya za'ayi? Allah ya ba ku lafiya." Kwalla suka sake zubo mata ta ce,"Amin.", Na ga Bebin mu kamar Ameer ne aka dawo mana da shi." Yayi dan murmushi,"Shi ne ma, domin shi ma sunan za'a maida masa." Ta ce,"Yayi dai-dai." Suka k'ura wa Nusaiba ido, a lkc guda kuma suka kalli juna ya ce,"Allah yasaa ita ma ta farfado. Lafiya, kamar yadda ki ka tashi." Ta ce,"Amin yayana." Ta wuce da kanta kirjin sa, tayi ajiyar zuciya, ya sumbaci tsakar kanta, sannan ya gaya mata su Sageer sun zo shi da Fa'iza. Suna gaishe su." Ta dago a hankali ya taimaka mata ta kwanta tana fadin,"Muna amsawa." Ta bi shi d kallo, ta ci gaba da cewa,"Na san ba ka ci komai ba yayana, ka hada Tea mana ka sha." Ya kada kai,"Ban jin yunwa Zarah." Ta ce,"Ai kai ba za ka ji ya ba, amma tana nan tana cin ka." Yayi dan murmushi ya ja ha6arta, ya ce,"Hankalina bai gama kwanciya bane Zarah, sai na ga farfadowar yarinyar nan." Ta dan lumshe ido, ta bude wani dadi ta ji ya ratsa, ta miko yatsun ta, ya rike ta.. Ta ce,"Insha Allahu lafiya lau za ta farfado. Kar ka ka zauna da yunwa yayanmu, za ta iya yi ma illa." Ya sumbaci, yatsun ya ce,"Shi kenan, zan sha yanzu." Umma tayi sallama, ya mike da sauri yana amsawa, ita ma maganar abincin tayi masa, sannan ta bude jakar kayan daya kawo, ta debo wa Yaro kaya, ta dauke shi suka fice. Anan ya hada Tea ya dawo bisa kujera gaban Zarah yana sha, suna hirar Nusaiba. Bayan sallar la'asar. Alh. Basheer ya ce shi zai koma. Ummi ma ta ce me za ta tsaya yi, tunda ga su Umma ga Inna? Haka suka wuce, duk ba su ga farfadowar Nusaiba ba, idan Allah ya kai rai gobe, za su dawo. Bebi kuwa na lkie da Zarah. Naseer ya tasa su yana ta fama kallon abin sa, son sa na k'ara kwarara jikin jinin sa da bargonsa suna kashe jijiyo har bisa fatar sa. Karfe 9n dare ya baro Shika. Zarah tare da Bebi ta kwana, ko ya motsa, ita ake mika wa ruwan dimi ta ba shi, duk da jikin ta babu kwari sosai. Shi kuwa Naseer kasa runtsawa yayi, saboda tsabar tunanin abubuwan daya aikata wa Nusaiba, wadanda a yau yake ganin suna so su zame masa da na sani. Lokacin sallar asubahi ya yi, ya tashi ya je yayi alwala, ya bada farali. Da kansa ya shiga kicin, ya shirya duk abubuwan da yake son tafiya da su asibiti. Yayi wanka, ya kimtsa. Karfe 7 saura kwata, ya dauki hanyar Shika. Karfe 8:30 Nusaiba ta farfado da surutai tare da sambatun da babu wanda yake fahintar me take fadi.Likita ya ce ba damuwa, za ta wartsake nan bada dadewa ba. Suna fa jin dadi, musamman Naseer da zuciyar sa ke cike da zullumi. Ko su Alh.Basheer da suka zo, sun yi farin ciki kwarai, anan suka iske su Malam Balarabe da Malam Umar. Shi yake gaya masu cewa Bebi sunan marigayi watau Iliyas ya ci. Wasa-wasa Nusaiba ta kai har dare bata gane kowa, sai sambatu. Likita dai sai kara basu hakuri yake yi, yana jadadda ma su za ta warware. Amma haka suka kwana da ita, ba barci. Surutai babu ma'ana. Abinda yafi basu tsoro, shine yadda harshen ta ya karye, tana magana kamar wacce ta sami matsalar shanyewar gefen jiki. Da safe kowa ya zo da kuzarin sa, turus! Yake yi, saboda abin akwai ban tausayi, ballatanta da idanuwan ta suka bud'e waras! Tana kallon kowa, amma bata sanin ko waye. Murna fa ta koma wa kowa ciki, domin al'amarin Nusaiba k'ara gaba yake yi, abin tamkar tabin hankali. Kwana 3 kenan. Da sassafe ta tashi da wani kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi, babu abinda take kira, sai "Antina! Alhali ga Antin ta tana tallafe da ita. Ita ma kukan take yi, tana fadin,"Ga ni fa nan amarya, ba mutuwa na yi ba."Ta tsura mata ido zuru! Shi kan sa kallon mai ban tsoro ne, sbd idanuwan a juye suke, duk sun firfito waje. Zarah ta sake fadin,"Kin ganni? Ni ce amarya, ban mutu ba. Ki daina cewa za ki mike da gudu, kin ga (Operation) aka yi miki. Duba ki gani, kin ga Bebin mu? Ga Umma ga Inna. Yanzu yayan mu ma suna tafe. Ki na son ganin su ko? Ta girgiza kai, ta ce da karfi,"Antina ta mutu na ce! Wayyo Abba na, sun kashe Antina! Da gudu Zarah ta bar dakin, ta zube barandar waje, ta fasa kuka. Kwatsam! Sai ga su Ummi, tun daga nan suna jin ihun ta, tana kwala wa Abbanta kira. Ummi bata son lkcn da ta watsar da kayayyakin hannun ta ba, suka fada dakin. Su Umma na rirrike da ita. Alh.Basheer yayi azama ya rungumota,"Ga ni Nusaiba, ga ni, ki yi shiru." Amma kara fadi take,"Abba na ka zo sun kashe min Antina! Hankalin sa yayi mummunan tashi, ya dubi su Umma."Ina Doctor ne wai? Ta ce,"Sun zo har su 4. Nosis sun zuba magunguna cikin karin ruwar nan, sun mata allurai, har yanzu barci ya ki zuwa." Alh.Basheer yayi waje, ya nufi ofishin likitan daya dauka na musamman, cikin zafinsa ya shiga, a tsaye ya fara fadin. "Wai me ke faruwa ne Doctor? Ban gane condition din yarinya ta ba! Shi ma ya mike cikin sanyin murya ya ce,"Cool down Alhj, zauna." "No I can't sit Doctor! Kullum yarinya sai k'ara rikicewa take! Why? Wai ba anan ku ka yi mata tiyata ba ne? Ya ce,"Alhj babu wata maganar an ta6o mata wata jijiya. Infact, aikin ta bai shafi ko'ina a jikinta ba, sai inda Bebi yake. Ka zauna mu yi magana, Please! Da kyar ya zauna, shi ma Lkita ya zauna." Dama kai na ke jiran zuwan ka mu yi magana. Nusaiba ta fada cikin matsananciyar damuwa, wacce har ta sanya ta fizge-fizge, alhalin tana da ciki. Babbar matsalar ce ga mai ciki idan ta sami kan ta a irin wannan yanayin, domin ya kan kai a rasa su duka. Shine za ka ga mutan kauye da suka jahilci abin sai su ce bugun jinin ne, maimakon a hanzarta kawo ta asibiti, don daukan matakin gaggawa, sai a shiga hayaki da shafe-shafen turaren aljanu. Daga karshe ka ga an rasa uwa da Da. Abinda na ke so ka gane anan, damuwa babu abinda bata haifarwa, amma ina son ku natsu, za mu bicike da kyau, mu gano aininhin abinda ke damunta. A halin yanzun muna Expecting comma ta shiga, abinda muke magana kenan da sauran Doctor." Alhj fa bai yarda."Wannan ba comma bace, ta6in hankali ne, sbd haka idan ku yi bincike a kwakwalwarta, ko nawa ne zan kashe! Ya ce,"Wannan duk ba matsala, yanzu zan rubutu gwaje-gwaje da hotunan da za'ayi. Idan an rubuta kudaden, sai aje a biya." Rubuta min, in je a biya kudin." Yana zaune Likita ya rubuta duk binciken da za'ayo. Tare suka fito, ya hada shida Yaron da zai raka shi ofisoshin da za su rubuta kudaden. Al'amarin Nusaiba kuwa ta rikita kowa, kuka kawai suke yi. Shi kan sa Bebin kukan yake tsalawa, yana jin yunwa, amma ta hana su yi 'yan dabara a lika shi, ya sha nono. Naseer ya doso wajen, tun daga Nesa ya tsinkari muryar ta. Da gudun sa ya karaso, yana tambayar Zarah! "Me ya faru?, Murya na rawa ta ce,"Nusaiba ta rikice Kai tsaye ya shiga dakin, ya zube jakar da ke hannunsa, ya nufi gunta yana fadin,"Ya haka Umma? Duk suka dare, suka ba shi wuri, tana kyallo ido ta gan shi, ta zaburo tana mika masa hannu, "Abba na! Abba na, ina ta nemanka za su kashe ni? Bai san lkcn daya rungumota ba,"Menene? Iye? Ba ki san akwai ciwo a jikin ki ba? Allah da ikon sa, shiru tayi, tana ajiyar zuciya,"Kai na ke ta kira Abba na, ka ki zuwa, kai ma ba ka so na ne? Idanuwansa suka cika da kwalla. Kowa yayi waje yana share hawaye. Ya jima kafin ya ce,"Ai gani na zo, me aka yi? Wa ya sanya min ke kuka? Ta zura masa ido ta ce,"Antina suka kashe min, shine suka zo ni ma suka danne ni, za su kashe." An ce miki Antinki bata mutu ba, tsaya ki gan ta. Zarah! Ya kira ta. Ta shigo, ya jawo hannayensu ya hada,"Kin gan ta? Antinki ce. Ta fizge hannunta, ta saka ihu,"Ba ita bace! Allah ba ita bace,"Antina ta mutu Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Ya rufe bakinta ya ce,"Shi kenan na ce, shi kenan ba ita bace." Zarah ta yi sauri ta fice. Sannan tayi shiru. Ya dube ta ya ce,"Abinda ki ke yi, ba shi da kyau, ki na jin Bebin mu na kuka, kin ki bashi nono, me ki ke nufi? Ta ce,"Abba na ina naga Bebi kuma? Ga shi can a waje, yana kuka."Ta ta6e baki ta ce,"Ban haihu ba, Antina ce ta mutu. Ya kamo ha6arta ya ce,"Dube ni, ki saurara da kyau, za ki ji kukan Bebi. A kawo shi ya sha? Tayi shiru, tana kallonsa. Ya sake kiran Zarah, ya ce ta kawo Bebi,. Ta zo da shi a shawul, ya kar6e shi, ta tsaya tana kallonta! Ya ce,"Yauwa, dube shi ki gani." Kyakkyawan kallo tai masa! Ya ce,"Yauwa, dube shi ki gani, kyakkyawa da shi." Ta leko ta dube shi,"Abba na wannan k'aton Yaron ai ya girme ni." Ya ce,"Ban son shirme, ba shi ki gani, idan bai sha ba, ki min duka." Ya dora mata shi bisa jikinta, ta 6allo wa Zarah harara, sannan ta dubi Naseer,"Abba na ka ce wa matar nan ta fita, ban son ganin ta. Munafuka kawai, duk sune suka kashe Antina." Hawaye suka kawo wa Zarah, ta juya ta fita. Ya ce,"To ta fita, ba shi ya sha. Ta ciro ta ba shi, ya kama sai tsotsa yake yi, bawan Allah ya sha kuka, shi yasa bai jima ba, barci ya kwashe shi. Naseeer yayi zuru, yana kallon su, tsabar tausayinta yake ji, kamar ya ce wayyo Allah. Ta ce,"Abba na ka daina kallo na mana." Ya ce, "Ah! Ai kowa dole in kalle ki, tunda ina son ki, kin zama abar kallona. Ko kuwa? Ta sadda kai, tana dan murmushi. Ya dan k'ara matso ta, ya ce,"Kin ga har yayi barci, to ke ma ya kamata ki kwanta ki yi barcin, ki huta ko?Ta yi hamma mai tsawo, yana rufe da bakinta, kafin ta ce, "Barci?" Kin ga ni ban son shirmen nan na ce. Kawo Bebin a kwantar da shi, ke ma ki kwanta ki gani." Ta ce,"Bar shi kawai, ya yi min dadin rikewa." Hirar su kawai suke yi, abin ya ba kowa mmk, har Alh.Basheer ya gama zirga-zirgar sa, ya dawo. Ummi ce ta mayar masa da yadda aka yi, ta yi shiru ta natsu. Ya shigo dakin a hankali Naseer ya mike yana masa sannu da zuwa, da ta fasa wata irin k'ara, gaba dayan su gigicewa suka yi. Naseer bai san lkcn daya koma gun ta ba,"Menene? Idanuwanta rufe tana fadin,"Ban son ganin sa! Ban son ganinsa!! Munafiki ne............. Ya rufe bakin ta, yayin da Alh.Basheer yayi waje da sauri. Naseer ya ce,"Ban son abinda ki ke yi Nusaiba, gaskiya ni ma zan tafi." Ta ce,"Na daina Abba." Ta ci gaba da surutu k'asa- k'asa,"Munafikin banza, munafikin wofi, ya wani shigo wa mutane ko kunya." Yayi shiru, ya kyaleta, kwalla suka zubo masa, ya share. Wannan al'amari da me yayi kama? Kuma fa duk shine sila ko? Ya tambayi kan sa. Wasu hawayen sharshar! Suka fito, ya sake gogewa. Alhj kuwa yana tare da su Ummi, shi ma sai da ya share kwalla, sannan ya mayar da yadda suka yi da Likita, kuma nan ba jimawa, za so zo su tafi da ita dakin hoto. Jama'a sun sha Zagi da tsinuwa lkcn da aka zo daukan ta, har da Naseer din da yake fada aji, ya zama munafiki, tunda yana gani zai kyale a tafi a kashe ta. Dole Likita yasa aka kawo masa wata allura, da kan sa ya zurkud'a mata. Take nan ta wuce luuuu....!!! Ba rai, ba dalilinsa. Sannan da masu daukan ta suka gara ta wajen hoto.Har aka dawo da ita, bata sani ba, nan suka bar ta tana ta barci. Hankalin kam ba a kwance yake ba. 'Yan dubiya na ta zuwa gaishe ta, amma tana barci, da yawa daga cikin su daga Kaduna suke zuwa. Haka Antin Jordan kodayaushe sai ta bugo ta tambayi jikinta. Bizar ta kawai take jira a gama, ta kamo hanya. Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Sakamakon duk gwaje-gwajen da aka yi mata suka fito. Likita ya kira Alhj ofishinsa, shi kuma ya kira Naseer, domin mijinta ne, hakkinsa ne ya san halin da matar sa ke ciki. Kowanne ya ja kujera ya zauna gaban Likita. Shi kuma ya firfito da sakamako, ya ci gaba da bayani."A gaba daya binciken da mu ka yi, babu wata matsala a tattare da ita. Kwakwalwarta lafiya lau, zuciya ma haka, k'oda lafiya lau, haka jirin ta lafiya yake. Saboda haka abin nan dana fara gaya maka Alhj, shi din dai za mu ci gaba da kula da ita akan shi." Alhj ya ce,"Yanzu ka na nufin tsabar damuwa ce ta jefa ta a wannan yanayin? Ya ce,"Kar ka yi mamaki, damuwa tana sanya hawan jini, kuma babu ga mai juna biyu. Saboda haka za mu ci gaba da bata taimakon daya dace, sannan daga wajen ku a matsayin ku na iyaye da mijin ta, rarrashi ne kawai. A ring'a lalla6ata, a kodayaushe, hanklinta ya zamana a kwance yake tare da samun isashshen barci. Insha Allah za ta warware, sai kun yi mamaki."Alhj ya munfusa, ya dubi Naseer,"Ka ji ko? Wannan aikin ka ne, ko dama kai kadai take son gani, mu duk mun zama munafukai. Don Allah ka yi hakuri da ita, sannan a rink'a had'a mata da addu'a. Idanuwansa cike da hawaye ya amsa,"Ya zama dole Abba, Allah ya taimake mu." Duk suka amsa da Amin." Tun lkcn aka bar wa Naseer ragamar komai ahanununsa, kowa ya koma gida, sai dai su zo akai-akai su duba ta, shi ma ta, taga, idan har idan ta 2, idan kuwa har ka ga wanin Naseer a kusa da ita, tabbaci hakika barci take yi. Zarah ma an sallame ta, ta koma gida, amma kodayaushe zuciyar na asibitin, shi yasa bata iya daurewa kullum ne sai ta zo, koda za ta wuni a waje tana lek'en taga tare da renon Ameer. Haka Likitocin ta ke iyakar kokarin su ba dare, ba rana akan ta. Magana ce ta kudi. Alh.Basheer kuwa ya saki komai ya dace ayi mata, komai tsadar magani. Shi kuwa d'an gogon, bai gajiya da yi mata hidima, shi ne cin ta, shine shan ta. Kullum yana like da ita, suna hiar shirme, domin kuwa shirme ce, yanzun nan za'ayi magana dai-dai, lkc guda sai ta ya6o shirmenta. Babu abinda ya dame ta.Idan dare yayi kuwa tana barci, zama yake bisa kujera ya zura mata ido, yana yi mata addu'o'i. Idan ya tuna da bayanin Likita kuwa, hawaye yake zubdawa sosai, domin ya tabbata shi ya tara maya damuwar sa ta jefa ta wannan mawuyacin halin.A haka so da k'aunar Nusaiba suka zauna kwarai da gaske cikin zuciyarsa, har yana mamakin kan sa." ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Kwanan ta 11 yau, ya gama kintsa Ameer, ya kwantar da shi cikin (Net) din sa. Ya dube ta, tana ta lissafin zucci, ya ce,"Za ki sha Tin ne kafin ki kwanta? Ta ce,"Had'o Abba." Ya had'o mata dai-dai wanda ta saba sha. Ya zo da shi bakin gadon, ya zauna. Ya debo a cokali ya ce,"Ungo, sha 'yar gidan Abbanta." Ta dube shi, tayi murmushi," Miss you."Dariya ta ba shi, ya ce"Za ki fara ko? Ai ni fushi na ke da ke."Me na yi Abba na? Ya mika mata, ta kur6e ya ce,"Batan kin kori kowa, mutane na son ganin ki, amma kin hana, me yasa? Hmm... Abba na kullum ina raba ka, amma ba ka ji. Me za'ayi da munafukai? Ya ce,"Na fa hana ki ce musu munafukai. Haka dazu ki ka cewa Umma, sa'ar ki ce? Ta dan 6ata rai, tayi shiru, ya miko mata Tea ta ki kar6a. Ya aje cokali ya dago ha6arta."Fushi ki ka yi? Da ni ki ke fushi, shi kenan bari in zo in tafi." Ta ce,"Yanzu saboda Allah Abba duk wanda ya nuna baya so na, ba munafiki bane? Yanzu dubi yadda ka ke k'aunar Naseer, amma k'iri-k'iri ya nuna min, baya so na, yayi ta wulakanta ni. Saboda Allah Abba me zan kira shi ba munafiki ba, tunda ya munafunce ka." Tunda ta soma mgn, gabn sa ya yanke ya fad'i, yayi sukuiti duk jikin sa ya mutu, ya rasa me zai ce? Ta zura masa ido, ta ci ga,"Abba ai dai ka san na maka biyayya da ka ce min shi ka za6a min, ban maka musu ba ko, Amma ka san Allah, shi baya so na, wannan cikin na jiki na ma, ya ce da shi zan koma gidanmu, baya so. Na ce ai ban je da d'a gidan sa ba, ko fan fadi gaskiya ba? Hankalin Naseer fa ya yi mummunan tashi, ya tabbata wata rana a surutanta za ta iya fadi a gaban kowa. Idanunwan suka kad'a, ya aje Tea bisa dirowa ya rufe.Ya kamo kafadunta 2, suka yi wa juna zuru kafin ya ce,"Wannan maganar bata dace ki na fadar ta ba 'yar gidan Abbanta. Naseer masoyin ki ne, ni ya gaya min yana son ki kwarai da gaske." Ta girgiza kai,"Na rantse da girman Allah, karya yake maka Abba. Naseer munafiki ne, ina gaya maka maganar nan, ka yarda da ni Abba." Ya sake ta ya kama kai. Ta bi shi da kallo ta ce,"Mamaki ma ka ke yi? Kai har yanzu ba ka san mutane ba, ka na dai kallo aka kashe Antina, me za'ayi? Yayi hucin zafi ya ce,"Duk na ji, amma kin san abinda na ke son ki da shi ? Ki kyale maganar nan, kar ki gaya wa kowa, ni zan yi maganin abin. Kin yarda? "ka dai gaya masa, idan na haihu zan aje Yaron, shi zai maida shi cikin lemon gwangw........................ Ya like bakinta,"Nusaiba na ce ki bar maganar nan, zan fa tafi abi na." Ta ce,"Yi hakuri." To kin yarda ba za ki gaya wa kowa ba? Na yarda, amma ka san Allah, ka yi hankali da wad'annan mahaukatan da suke zuwa 6arayi ne." Yayi shiru yana kallonta, duk ta dagula masa lissafi." Ba ni Tin mana." Ya dauko ya ci gaba da bata, sai zuba masa surutu take, shi kuwa bakin sa ya mutu har ta yi barci. Yayi tagumi bisa kujera, ya rasa abinda ke masa dadi.Ta dai ce ta yarda ne kawai, ba za ta sake fadi ba, amma abin maras hankali, ai ba'a sirri da shi. Dan saukin ta ma, bata kula kowa sai shi. Daran nan bai runtsa ba saboda tunani. Safiyar yau kuma daga ya ce, bude baki ayi burosh, shi ke nan ta fasa kuka. Yayi rarrashin dunuya, ta k'i yin shiru, ta k'i kuma mgn, a haka ta shafe sama da mintu 30 ita da kan ta ta yi shiru. Ta gyara kwanciya, ya sanya mata ido, tana ta ajiyar zuciya, har barci ya sace ta. A lokacin shi kuma ya fara na shi hawayen da kyar ya iya tsaida su, saboda tsabar tausayinta. Ko me yasa ta kuka? Oho! Ya tambayi kan sa, ya ba kan sa amsa. Idanuwan sa suka kara ja, kamar garwashin wuta, dama ga rashin barcin da bai yi ba jiya. Yana nan zaune zuru, ya ji motsin Ameer, shi ma ya farka. Ya tashi ya zuba masa ruwan dimi a fida ya zuba glucose ya karkada, sannan ya dauko shi suka fito waje, ya zauna a kujera yana ba shi har ya shanye. Idon sa 2, amma baya kuka, yana ta 'yan wasannin sa. Naseer na taya shi. Muryar Alhj kawai ya ji yana masa sallama, ya dago da sauri yana amsawa. Tare suke da Ummi da Antin Jordan. Ya mike yana masu sannu da zuwa. AntIn Jordan ta kar6i Bebi tana fadin,"Sannu Naseer, don kai ne abin gaisarwa. Yaro duk ya rame." Yana murmushi ya tsugunna, ya gaishe su.Alhj ya ce,"Mutuniyar barci ta ke yi ne? Ya ce,"Eh. Ummi ta ce,"Yauwa mun yi sa'a, shigo Fatima ki gan ta."Suka dungoma cikin dakin, shiru suka yi suna kallon ta kawai, don kar su yi surutu ta farka. Sun kusa minti 10 a tsaye, sannan suka fito dan koridon. Naseer ya baza darduma, suka zazzauna. Ya koma gefe ya zauna, suka ci gaba da tambayar sa yanayin jikin na ta? Ya ce,"Da sauki, an gode Allah, amma ko dazu ta sha kuka, kuma ta k'i magana, abinda ma ya sa ta barci ke nan." Antin Jordan ta goge kwalla, ta dubi Alhj,"Gaskiya yaya idan babu wani ci gaba a fita da ita waje kawai." Ya ce,"Wannan maganar na rai na, akwai iiya kwanakin da na dibarwa Likitocin nan din ne, idan sungaza, zan dauke ta." Ta ce,"Wannan tashin hankali da yawa yake." Ya ce,"Jarabci ne, mun gode Allah, muna rok'onsa sauki. Kai Naseer ka yi ta hakuri, ka ji? Ya ce,"Hak'uri na mu ne duka Abba." Haka suka kasance tare, jama'a na ta zuwa kamar kullum. Koda ta farka. Naseer ne kawai ya shiga, ya kai mata Bebi. Allah da ikon sa babu kuka, sai hira kamar ma ba ita ta sharari kukan dazu ba. Yayi mata burosh, ya bata Tea, ta sha. Abin yana ta 6a Antin Jordan mmk har ta tambaya,"Yanzu ina shiga, sai ta fara Ihu?, Ummi ta ce,"Ko za ki gwada ne? "Don daukan alhaki? Na gan ta ta taga, ya isa. Allah ya yaye mata." Ta ce,"Amin. Kwananta 7 ta koma Jordan. Ranar da ta tafi, ranar Kausar ta iso da mijinta. Bata 6ata lokaci ba, ta fadawa dakin, kanta ta yi ta rungume ta sa kuka. Wani ihun da Nusaiba ta yi, dole ta sake ta, tana kallo, jiki na rawa. Ta runtse ido, tana zagi tana fadin. "Ban son ganin su. Ban son ganin su! Naseer ya rirrike ta. Mijin Kausar ya fito da ita, me za ta yi ba kuka ba. Haka ta fada jikin Ummi, tayi ma isar ta. Naseer kuwa da kyar ya shawo kan Nusaiba tayi shiru, ta daina zage-zage. Ba karamin Huashi Kausar ta bata ba, sbd ta6a tan da tayi.Yini guda masifar da ta rink'a yi kenan,"Wata munafuka ta zo ta cakume ni za ta kashe ni! Sai bayan la'asar tayi barci. Kausar ta je gun ta, tayi mata addu'o'i. Hawaye na zuba. Da yamma lilis suka koma Kaduna. Haka Kausar ta tafi da bak'in ciki, a duk lkcn da ta tuna hawaye, ke zubar mata. (Allah sarki Nusaiba Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 3-02 Posted by ANaM Dorayi on 08:53 PM, 20-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
To shi kenan ya wuce." Ya kamo ha6ar ta, yi dariya,"Yi dariya 'yar gidan Abba!
Ta fado kirjinsa, tana murmushi.
Ya rungume ta, ya runtse ido, wasu kwalla suka yi masa caa, fadi yake a ransa, "Son ki ya kama ni Nusaiba, ki yafe min don Allah.". (Hhhhhhh, Anzo gurin, ammafaaaa...uhm! Maji ma gani)

Bai ko san ta kici-kicin tashi ba, sai da ya ji tana kira,"Abba!
Ka shake ni!
Ya hanzarta sakin ta, yana goge kwallah. Ta bi shi da kallo,"Wash!
Ka wani matse ni Abba, ai sai in mutu."Ya tashi ya bata wuri, ya shige bayi ba tare da ya ce komai ba.
Jim kadan ya fito, ya wanke fuskarsa, kwance ya same ta, ya matsa gabanta ya ce,"Hirar ta isa haka, ki yi barci ki huta." Ta amsa da ka, ya duk'o ya sumbace ta, ya ja mata mayafi. Ya ja kujera ya zauna, ya sauke numfashi,"Allah ka ga iya kokarin da na ke yi. Allah ka taimake ni yarinyar nan ta sami lafiya.
Ta ce,"Ka kwanta mana Abba." Ya ce,"Zan kwanta, ke dai yi barcin ki." Ta rufe ido.
Tare da gyara kwanciya.
Da asuba ya fito bayi da alwalar sa, ya shimfida sallaya, yayi sallah. Ya jima yana addu'o'i kafin ya jiyo motsin ta.
Ya waigo yana kallon ta, ta tashi zaune, tayi mika tana salati. Ta kalli can, ta kalli nan, bai ce da ita k'ala ba.
Ta k'ura wa Bebin da ke barci cikin (Net) ido.
Ta dago kai ta dube shi, suka yi ido 4.
Yayi murmushi, ya ce,"Kin ta shi?
Fashewa tayi da kuka, ya taso da sauri ya zauna gefen ta."
Nusaiba, ke Nusaiba, za ki fara koke-koken nan ko?
Tayi shiru tana tunaniin Antin ta.
Hawaye na ta ambaliya.
Ya rik'o ta, ta kwace jikin ta, kuka take tana k'arawa.
Ya ce a ran sa,"Na shiga 3, yau kuma da kukan ta tashi." Ya matso, ta matsa. Ya ce,"Ni Nusaiba, ni ki ke gudu? Bata kalle shi ba, balle ta ce wani abu. Ya sake matsowa, ta matsa. Ya ce,"Shi kenan, bari in yi tafiya ta, in tafi ko? Ta amsa eh, da kai. Ya ce,"Tabd'i! Da magana yau,"Cikin ransa.Ya rasa yadda zai yi, dole ya sa mata ido, tayi ta kuka. Can kuma ta tashi ta fito koridon ta zauna, bisa kujera. Shi ma ya biyo ta nan ya zauna, yana gadin ta.
Jim kada ya ji kukan Ameer.
Ya mike ya ce da ita,"Ga Ameer can ya tashi, in kawo shi ya sha? Ta kyale, bai ma ishe ta kallo ba, ya shige ciki ya dauko shi, ya tsugunna gabanta,"Yauwa, 'yar gidan Abbanta kenan, dubi Bebin mu kuka yake yana jin yunwa, dan ba shi ya sha." Ta dauke kai, tamkar bada ita yake magana ba.
Abu fa ya gagara, dole ya dauko wa Ameer fida ya tura masa, yayi ta tsotson ruwa da glucose.
Kullum karfe 7 nan take masu. Alh.Basheer suna nan zaune kuwa, sai ga su.
Naseer ne ya fara hango su, ya mike ya nufo su.
Su ma tsayawa suka yi cak, ganin Nusaiba a zaune wajen.
"Yaya dai? Alh.Basheer ya tambaye shi, yayin da Ummi ta kar6i Ameer a hannun sa.
Ya ce,"Ai yau ko Ameer ta k'i ba shi nono.
Kuka kawai take yi,"Ya ce,"Likita ya zo?
Ya ce,"Ka tsaya nan, kai kuma koma gun ta, bari in nemo Likitan." Ya koma wajen ta.
Alhj ya zaga ya wuce, ita kuwa Ummi ta lafe.
Jimawa kadan suka dawo da Likita. Abin ya ba Naseer mamaki daya ga Lkita ya zo, ya tsaya gabanta bata zage shi ba.
Ya ce,"Nusaiba, tashi mu shiga ciki, mu yi wata magana." Kai tsaye ta mike ta wuce. Naseer ya saki baki, shi ma ya taso ya biyo su. Ta zauna bakin gado, ya jawo kujera ya zauna ya ce,"Kukan me ki ke yi?
Ta ce,"Antina ta mutu ko?Ya ce,"An gaya miki bata mutu ba, Antin ki na gida." Ta runtse ido wasu hawayen suka tsunke mata, ta sa hannu ta share. Ya ce,"An ce kin ki ba Bebin ki nono, saboda me? Haka za muyi da ke saboda Allah? Ta dube shi da kyau ta ce,"Doctor ka yi min wani taimako don Allah, lambar Abba na zan ba, ka kira min shi." Idanuwan Naseer suka k'ara yo waje, ya koma da baya da baya ya fito waje. Shi kuwa Likita k'ara tsura mata ido, ya ce,"Abban ki? Ta ce, eh. Ya ce,"Ina zuwa." Ya leka yayi kiran Alhj da hannu. Ya taso daga inda yake zaune ya zo. Likita ya kamo hannun sa, ya shigo da shi a hankali. Kan ta na duke ya ce,"Wannan Abban naki ki ke nema? Tana yo ido hudu da shi, ta mike hawayenta suka yawaita, ta ce,"Abba! Wani tsananin farin ciki ya kama Alhj, dole kwalla suka cika idon sa, ya ce,"Bebin Abba! Ta rugo da gudu ta rungume shi. Tuni Ummi ta fado dakin ta hade su ta rungume, kuka suke saboda murna. Haka Naseer ke sharar kwalla. Amma ya rasa abinda zuciyar sa ke sakawa game da wannan al'amari. Tabbas Nusaiba ta warke, to me zai biyo baya? Da alamun zai shiga magana, yanayin da ta nuna. Yayi ta maza ya shigo. Alhj Basheer ya rungume shi, suna wa juna barka. Likita ya fita, ya bar su cikin farin ciki da murna maras misaltuwa.Bayan sun natsa. Ummi ta dubeta, duk ta rame ta ce,"Sannu Nusaiba, Ubangiji Allah ya k'ara karewa." Ta ce,"Amin. Ta miko mata Bebi ta ce,"Kin ga Bebin da aka ciro miki? Ta dan dube shi, tayi murmushi , ta dauke ido,"Na gan shi Ummi ta. Kwalla suka taru fal a idonta, ta kasa shanye su, sai da suka zubo. Abban ya rungomu kafadunta, ya ce,"Yi hakuri daina kuka, komai ya wuce Insha-Allah." Ya ce,"Allah ya yarda Abba. Bari in yi sallah." Ta mike ta wuce bayi ta jima bisa sallaya, tana yi wa Allah godiya daya dawo mata da rayuwarta dai-dai. Ta dawo gefen gado ta zauna kusa da Abban ta. Ya jawo ta jikin sa, ta dan numfasa ta ce,"Abba lokaci yayi da zan gaya maka wata magana, ina fatan za ka gafarce ni." Naseer na jin haka, ya mike ya bar dakin. Abba ya ce,"Babu komai Bebina, gaya min, me ke da mun ki? Ummi ta sa masu ido tana kallo. Ta k'ara gyara zama ta ce,"Na san za ka yi mamaki, idan na gaya maka cewa tun aure na da Naseer, babu kwanciyar hankali tsakani na da shi. Ai kuwa Alh ya sha mamaki, ba shi da kadai ba har Ummi da take zaune. Ya kara dubanta, baki sake, ya tambaya, "Saboda me? Ta ce,"Abinda na fahinta,"Abba, shine ya kar6i aure na ne kawai don ka cika masa ido, ba zai iya ce maka a'a ba. Amma a hakakin gaskiya Naseer baya so na, kuma ya nuna min kiyayya, ba don Antyna na tsaye ba, ina ganin wuyar da zan sha, ba 'yar k'arama bace.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Shi yasa na ke son ta, domin tayi min komai, kuma tayi iyakar kokarinta wajen jawo hankalinsa zuwa gare ni, sai dai haka bata samu ba, saboda babu sona a zuciyar sa." Ransa ya 6aci kwarai, ya ce,"Me yasa tuntuni ba ki gaya min ba? Ta ce,"Saboda kai ne Abba. Ba na son wani tashin hankali ya shiga tsakanin ku. Kuma ina ganin ai ya girmama ka ne, tunda ya kasa fitowa fili ya nuna maka baya so na. Shi yasa na yi ta kokarin zama da shi shekara daya da rabi, sai da Allah ya kawo rabon wannan Yaron, sannan ya shiga daki na. Daga baya na yi tunanin bai kamata mu zauna muna cutar da juna ba, shi yana jin haushi na, ni ma ina jin na shi. Sai na same shi a daran da wannan abin zai faru, na yi masa magana. Abba cewa yayi idan na k'ure shi, zai 6atacciya, dole in koma gidan mu, har d'an baya so, ya bar mana...................!!! Tana shiru. Ummi ta cafe,"Ina, inda kuma yayi karya kenan. Ai ba mu kai masa ke da Da ba." Alh.Basheer yayi shiru, zuciyar sa na tafasa, abin kamar a mafarki yake ganin sa, domin ko alama bai ta6a mafarkin Naseer zai ci amanar sa haka ba. Ya dubi Ummi ya ce,"Har hada mata kayan ta mu tafi." Ta mike tana fadin,"Ashe ga damuwar da ta kusan hallaka rayuwarki Nusaiba, kenan. Yayi wa kan sa. Kuma sai Allah yayi miki sakayya." Nusaiba ta kada kai,"Ba haka bane Ummi ta, ba laifin sa bane, kar ki manta soyayya, gamon jini ce, laifin sa 1, shine daya danki amanar da ba zai iya rikewa ba."Alhj ya ce,"Duk laifin iyayen sa............ Tayi saurin katse shi."A'a Abba, iyayen Naseer ba su da laifi kuma ina mai tabbatar maku yadda ya yaudare ku, haka ya yaudare su. Ba su san komai ba a game da zaman mu. Sun rike ni tamkar 'yar cikin su. Idan na ce ga abinda su kai min, na yi masu karya, sai Allah ya tambaye ni. Abba, rokon da zan maka daya ne, don Allah, don son Annabi kar ka k'ullaci kowa akan maganar nan, ni ce baya so, to ka dauki 'yar ka. Ai shikenan, an gama magana." Ya ce,"Haka ne Nusaiba, ki yi hkr, ni ma na gane kuskure na, ni na jawo miki duk abinda ya same ki." Ta ce,"Ban ta6a ba ka laifi ba Abba, ba kuma zan ta6a ba ka ba. Ai kai alheri ka k'ulla, sai dai ka san a wannan zamanin ba kowa yake son ayi masa za6in abinda ya kamace shi a ruywar sa ba. Ya fi son abinda ra'ayinsa ya ba shi. Ka ga kuskuren da aka samu. Ina alfari da kai Abba na, kuma ko a yanzu ka sake za6a min miji. Wallahi zan aure shi. Bai san lkcn da ya rungume ta, ya fara kwalla ba. Haka Ummi ke ta share hawaye, tana sawa Nusaiba albarka. Ta mike ta shiga hada kaya. Hayaniyar hama'a suka jiwo gaba daya jama'ar Naseer ne. Zarah ma kayan barci ne ajikin ta, ta dora zani ta sa hijabi. Suka doro cikin dakin. Zarah na fadin,"Amarya!Ta zaburo da gudu, "Antina! Suka rungume juna, sun sha kuka, sai da Umma ta raba su ita ma, ta rungume ta. Daga nan ta matsa ta gaida kowa. Su Malam Balarabe, Malam Umar. Ya gaisa da Sageer da amayar sa. Bayan an gama gaishe-gaishe. Malam Balarabe yasa aka yi addu'a, kowa ya shafa. Aanan suka lura babu Naseer tun shigowar su. Inna ta fara magana,"Jama'a wai ina dan Inna ne? Malam Umar ya ce,"Kai wai dama babu Naseer a wajen nan? Sageer ya amsa,"Ai kuwa baya wajen nan, tunda muka zo? Malam Balarabe ya ce,"Ah to ina ya je? Ya fadi, yana kallon Alh.Basheer. Ya ce,"Gaskiya ban san inda ya je ba. Kuma dama ina son ganin ka, idan ba za ka damu ba." Ya ce,"Bismillah Alhj, ba damuwa." Suka fito waje, yayin da Zarah da Nusaiba ke like da juna suna maida yadda abubuwa suka faru. Alh.Basheer ya kebe da M.Balarabe, ya kwashe bayanin da Nusaiba tayi masa kaf, ya gaya masa. Tun da ya soma magana, gaba daya jijiyoyin jikin Malam Balarane suka tsinke, jiri ya fara dibar sa. Allah yasa a zaune suke, da babu abinda zai hana shi faduwa. Tabbas ya san Naseer baya son auran nan, aka yi shi, amma ko alama bai ta6a sanin rashin mutunci da wulakancin da ya rinka aikatawa ba. Ya jima kafin ya ce,"Alhj wannan magana ta ban kunya, kuma Wallahi tallahi ban san komai a game da zancan ba. Nusaiba bata nuna mana ba, balle ta furta da bakin ta. Don girman Allah ka yi hakuri Alhj. Ya ce,"Ai magana ta k'are, tunda baya son ta, ni ina son abata kuma zan tafi da ita, ba tare da 6ata lkc ba. Amma D'a, ban sako mata shi cikin gara ba, sbd haka nan za ta aje shi ko ya kashe ko ya bar shi da rai, duk ya rage nasa. A karshe, ka gaya masa na gode. Allah ya saka da alkhairi. Kan M.Balarane yayi gingirinn! Kunya kamar ya nutse kasa. Idanuwan sa suka cika da kwalla, ya rasa me zai ce wa Alhj? Kawai sai ya juya ya dawo dakin, gaban kowa ya daga murya ya ce,"Nusaiba, don me za ki min haka???Akan me za ki zauna sama da shekaru 2 cikin wulakanci da bak'in ciki, amma muna tare, ki kasa gaya min? Ba ki min adalci ba Nusaiba, domin da kin gaya min da tuni na yanke hukunci, sai dai ya nemi wani uban, ba ni ba! Kowa yayi tsuru-tsuru. Nusaiba kuwa tuni ta fara kuka. Ya matsa gadabn Ummi ya tsugunna." Hajiya ki yi wa girman Allah, ki yi hakuri. D'a ne ka haife shi ba ka haifi halin sa ba. Ko alama ban san halin da suke ciki da matar sa ba. Ga mahaifiyar sa nan a zaune, ko ita da ke zama tare da su munafikin Yaron nan bai ta6a barin ta gane wani abu ba, balle ni da ban zama cikin gida. Maganar tafiya da Nusaiba kuwa kun yi dai-dai, domin ko ni ne hakan zan yi. Saboda haka kowa yayi shaida. Ni Balarabe na tsame hannu na akan komai daya shafi Naseer, duk abinda ya ga dama yayi rayuwa ce................ Ya fashe da kuka, jikin kowa yayi sanyi, matan da ke wajen ma tuni suka soma taya shi, musamman Umma da ta ji abin kamar saukar aradu. Sageer ma waje yayi kirjin sa na bugawa, ga ranar da yake jin tsoron zuwanta, kullum yana gaya wa Naseer. Amma kunnuwansa iskar duniya ta dode masa su. M.Umar da Alhj suka riko M.Balarabe,"Ka yi shiru haka,"Malam Balarabe, kar zuciya ya kwashe ka, ka yi masa baki." Ya dube su ya ce,"Ni Naseer yayi wa tijara haka, Babu komai, rayuwa ce!Ya dubi Umma ya ce gaba,"Ke dauko masa D'ansa mu tafi, ki kai masa kayansa, idan ya ga dama ya jefa shi bola! Malam Umar ya ce,"A' ba'a yi haka bane, duk ku zauna a sasanta magana. Ai in rai ya 6aci, hankali ke nemo shi. Alhj ka yi hakuri, mu zauna da Naseer mu ji ta bakin sa, don girman Allah kar ku yanke hukunci kai tsaye haka." Alhj ya kada kai,"Ban k'i taka ba. Amma Naseer ya riga ya k'are magana, sai dai hukuncin daya yanke ne ban yarda da shi ba, d'a kan ba na mu bane, na shi ne. Don haka anan za'a bar shi. Iya magana kenan." Malam Balarabe ya ce,"Magana tayi dai- dai Alhj, ku bar masa shi, ya san uwar da za ta shayar masa D'an shi. Ki dauko shi mu tafi, na gaya miki, idan kuma ki na nan, ni na wuce! Yayi waje. Malam Umar ya bi shi. Umma ta dubi Ummi, ta ce,"Don girman Allah Hajiya kar ku yi wa Yaron nan haka, shi bai san komai ba, ku tausaya masa." Tayi shiru, ta rasa me za ta ce? Yadda Alhj ya fusato, babu mai sa shi dukan D'an nan. Haka Zarah ta rike Nusaiba,"Amarya kar ki ta fi, don Allah ki taimake ni. Idan ki ka tafi da wa zan zauna? Suka k'ara fashewa da kuka. Ita dai Fa'iza ba baki, sai ido. Bata fahimce komai ba, take ta faman kuka. Alhj ya fice ya bar su nan, suna ta faman magiya. Jim kadan ya dawo tare da Likita. Shi dai ya ga ana ta koke- koke, a zaton sa duk na murna ne, yayi abbuwan da zai yi, ya gama ya ba su sallama tare da takardar magunguna da za ta ci gaba da sha na tsawon kwana 7.Alhj da kansa ya rink'a dibar kaya yana kaiwa cikin mota, har ya kwashe su duka. Ya kamo hannun Nusaiba, ya wuce da ita. Ummi ta biyo bayan su, suka bar Umma da jariri bisa gado, yana ta faman barci. Ta k'ara fasa kuka. Inna ta kamota tana rarrashi. Haka Zarah ke durk'ushe, hannu 2 bisa kai.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Daga inda Naseer ke 6oye, yana hango su Alhj suka zo suka wuce a moTa. Yasa hannu ya goge hawayen da ke kuncinsa. Jimawa kadan ya hangi su Umma. Inna na dauke da Ameer, suka shiga motar da ta kawo su. Direba ya ja suka bar asibitin. Wasu hawayen suka sake zubo masa, yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu. Ya nufi inda ya aje motar sa, ya shiga haka ya dawo gida, baya gani wuri sosai. Ya rasa inda zai je, sai yayi fakin kofar shago, ya shiga ya sallami su Abbas ya ce duk su tafi gida. Ya kulle kansa ciki, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Cikin gidansu kuwa kamar anyi mutuwa, shiru ba ka jin motsin kowa. Jim kadan Zarah ta fito da jakar kayan ta, ta lallabo zuwa sasan su Umma. Ta leko a hankali, ta ga babu kowa, ta cire takalmanta ta wuce sadaf-sadaf kamar 6arauniya. Tayi waje kan ta tsaye tayi gidan su. Inna ta zura mata ido, kafin ta ce,"Ke kuma fa? Ta shige uwar daki da gudu. Inna ta biyota,"Na ce ke kuma fa? Kin shige da gudu. Menene na ce? Ta ce,"Allah Inna ni ma ba zan zauna ba. Haba ai wulakancin yayi yawa, ko alama yayana baya jin magana. Ta balbaleta da fada,"Laifin waye? Ai duk ku na sane, aka rasa wacce za ta gaya wa manya, don ayi maganin abin, sai yanzu da zance ya lalace, za ki ce Naseer ne baya jin magana? Maza dauko jakar nan, ki koma inda ki ka fito, tun kafin Babanki ya k'araso gidan nan, ya sameki." Ta 6arke da kuka, tana fadin,"Ba inda za ni Inna, idan har na koma gidan nan, to yayana ya dawo da Nusaiba. Kuma ku matsa min ku gani. Wallahi tafiya ta zan yi." Inna tasa mata ido tallafe da baki. "Ki ka ce me? Lallai wuyanki ya isa yanka, to zan ji idan kke ki ka haife mu." Ta yi zamanta bakin gado, har Inna ta gama babatun ta, ta fice." Na rantse da Allah ba zan koma ba, ya je ya ci kan sa a gidan, tunda shi ba'a gaya masa ya ji." Koda Malam Umar ya dawo, babu yadda ya iya yi da ita, ya gama fadansa da barazanarsa ko gezau zuciyar Zarah bata yi ba, kuma ta rantse ta maya, muddin suka bari ta bar nan, ba za su sake ganin ta ba. Shi yasa da ta dauko jaka ta fito. Inna ta dauko muciya ta kora ta daki, ta ce,"Koma daki marasa kunya, idan Naseer din ya zo ya dauke ki! Ta maida jaka ta yi zamanta cikin dacin rai da takaici tare da tausayin Nusaiba da karamin goyonta.
Sageer ma da ke zaune a dakinsa, babu abinda ya fi damun sa irin dan karamin yaron da aka aje. Alhalin bai san komai ba. Fa'iza ta ce,"Yakamata ku taimaka wa yaron nan a maida shi wajen Maman shi,"Wallahi shi ne abin tausayi, ba ka ji yadda na ke ji ba, kamar inyi tsuntsu kai shi wajen ta." Ya ce,"Shirun nan da ki ka ga nayi. Ameer kawai na ke tunani." Yayi hucin zafi, ya dauko waya daga aljihu ya nemo lambar Naseer. Ta dan jima tana bugawa kafin ya dauka, ya ce,"Ka na ina ne? Murya dishe ya amsa,"Shago." "To ina zuwa." Ya kashe waya, ya dubi Fa'iza,"Wai yana shago, bari in je in same shi." Ta ce,"To ba za ka dan ci komai ba? Ya kada kai, bari dai in je in dawo. Ya fice, tana fadin a dawo lafiya. Ya kwankwasa kofar shagon, ya zo ya bude, suka koma ciki tare. Daga kallon Naseer kawai. Sageer ya gane yayi nadama, gaba daya ya jeme ya fita hayya cin sa. Ya dube shi a sanyaye ya ce,"Ka ga irin abubuwan da na ke gaya maka ko? Yanzu ina ribar wannan abu? Kullum ina gaya maka yi wa iyaye biyayya ibada ce, duk kuma mai yin sa ba zai ta6a ganin 6acin rai ba. Amma Naseer na ka ji, ni ban san abinda ke damun ka ba. Dan yaro jariri an ajiye maka shi, ina amfanin sa? Iyayen ka na ta kuka saboda kai, wacce irin masifa ce wannan? Ka farka daga bacci Naseer, kai ba yaro ba ne."Ya dube shi kwalla suka zubo ya ce,"Ban san abinda zan ce ba Sageer, domin ni kaina na san mai laifi ne, saboda haka duk hukuncin da aka yanke min, yayi dai-dai. Sai dai babu wanda ya san cewa na dade da yin nadama, sannan in na ce ba son Nusaiba yanzu, na yiwa raina karya. Shi ya sa na dage ba dare ba rana wajen kula da ita tare da rokon Allah ya bata lafiya, don in samu in nemi gafarar ta, na kuma nuna mata iya so da kaunar da na ke mata yanzu. Allah da ikonsa sai ta sami sauki, hankalinta ya dawo jikin ta, a lokacin da iyayen ta ke wajen, sannan bata 6ata lokaci ba, ta zayyane masu komai. Ka yarda da ni Sageer? Ka taimake ni, domin ni yanzu ban san yadda zan yi ba." Sageer yayi shiru, yana kada kai
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Tabbas ya yarda da maganganun Naseer, saboda yana daya cikin masu mmkin yadda Naseer ya rinka kula tare da ririta Nusaiba, sai dai a lokacin ya dauka saboda halin da ta shiga ne, kuma bata son kowa ya kusance ta, sai shi. Ya nisa kafin ya ce,"Yanzu tinkarar Abban, tashin hankali ne ba karami ba, kuma dole ne aje a same shi, tunda shine jigon komai. Abin yi shine, ka taso mu je wajen sa, ayi ta ta kare ko kashe mu zai yi." Ya kada kai,"Gaskiya Sageer ba zan iya ba.ka je kai kadai tukuna, ni na fi kowa sanin halin Abba." Ya ce,"Shi ke nan. Za ka jira ni a anan din ne? Je ka dawo ina jira. Ungo key din mota don ka yi sauri. Ya kar6a ya fito a sukwane, ya fada mota, yayi gidan su Naseer. Yayi sallama falon Abba, a lokacin Umma tana goya Ameer ta fito ta siyo masa madarar jarirai, bayan ta nemi Zarah ta rasa a cikin gidan, don bar mata ajiyar yaron kafin ta dawo. Shi yasa zuciyan Abba ke kara tafarfasa, ya sani babu makawa ita ma tafiyar ta ta yi. Da kyar ya amsa sallamar Sageer. Ya shigo a darare, ya nemi gefe ya makure, ya ce,"Sannu Abba." Ya ce,"Me aka yi Sageer? Ya ce,"Abba Naseer ne................Ya dakatar da shi da hannun sa kafin ya ce,"Tashi ka tafi! Sannan idan ka je, ka gaya masa ita ma wacce yake son ta tafi abinta, saboda haka ya zo ya kwashe kayan sa, ta bar min gidana in huta." Ya tashi ya durk'usa Abba................Ya runtse idanuwansa,"Sageer ina ganin mutuncinka, don Allah, don son Annabi ka tashi ka tafi. In dai akan maganar abokinka ne, na riga na datse magana, na yi rantsuwa Naseer ba zai sake sani kaffara ba. Saboda haka ka je ka gaya masa, shi 'yantacce ne, kar ya dami kan sa. Tashi, kanzil ban ka kara fadi ba, idan har ni ina isa in gaya maka. Idan kuma ban isa ba, to kacigaba da zama. Sageer ya shiga 3, Abba ya daddaure shi, ga magana bakin sa babu damar fadi, yana ji, yana gani, ya tashi ya fice. Yayi tsaye jikin mota ya rasa tudun dafawa. Ga wata sabuwa, kuma ita ma Zarah ta yi gaba. Duk da dai yana ganin na ta mai sauke ni, amma ba dadi ace ita ma tana gidan su.Ya fi minti 5r a tsaye, sannan ya bude mota zai shiga. Ya hango Umma tafe. Ya tar6e yana mata sannu da Zuwa. Ta amsa za ta wuce cikin gida, ya ce,"Umma ku taimaki ni Naseer na cikin wani hali, komai za iya faruwa da shi. Ta ce,"Shine me? Sai aka ce karshen Umma ya zo? Ya ce,"Ba haka ba ne Umma. Wallahi Naseer yayi nadama, tun ranar da ta sami kan ta cikin wannan yanayin, kuma ba shi da wani buri daya wuce idan ta ji sauki, ya bata hkr akan abinda yayi mata. Sai kuma aka sami akasi, komai ya yamutse. Ta yi dan murmushin takaici ta ce,"Yaro man kaza. To yanzu da ka zo nan ka na ta dogon bayani, akwai Nusaiba a nan ne? Tana fa Kaduna, a gaban Ka Babanta ya dauke ta. Ba sai ya je can ba, ya roke ta. Menene abin zafi? Ya durk'usa bisa guiwa, ya ce,"Ku yi wa girman Allah Umma ku yafe masa, ke ma kin san duk abinda ki ka fadi, ba zai yuwa ba. Sai da goyon bayan ku." Yana sa aya Abba na tsayawa kofar zauran, bai ce wa Umma komai ba, ta wuce cikin gida. Shi ma ya bi bayan ta. Sageer ya sauke numfashi, ya tashi ya fito ya tafi.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Yana shiga shagon zama kawai yayi, ganin haka Naseer din ma yayi shiru, ya san babu nasara. Sun dau minti goma a haka, kafin Sageer ya ce,"Wai Zara ma ta tafi gidan su."Ya dube shi da sauri." Me na yimata ita kuma? Kashe ni suke so su yi ko? Shi kenan." Ya goge kwalla. Wayar sa ta hau bugawa, da kyar ya dauka. Yakubu ne ke kiran sa. Ya rasa ta yadda zai yi ya dauka. Ya dubi Sageer, ya ce,"Zo mu je gidan Yakubu." Ya tashi suka tafi. Ya maida masa bayanin komai. Yakubu yayi masa fada kamar zai ari baki, shi kansa ba karamar kunya ya ji ba lokacin da Alhj ya kira wayarsa, yana gaya masa Naseer ya ci amanarsa. Duk da haka yayi masa alkawarin shiga maganar, sai inda karfin sa ya kare. Shi kuwa Naseer B ana maganar, yana kallon kowa a dage, zuciyar sa gwanin haske, har yana addu'ar kada Allah yasa su shirya. Amma bisa fuskar sa, ya fi kowa nuna damuwa kamar yayi kuka. Daga gidan Yakubu, wajen Zarah suka iso, misalin karfe 1 na rana. Sun shigo gidan. Inna na kwashe abinci cikin kula. Ta daga ido ta dube su, tana amsa sallamar su. Gaban ta ya yanke ya fadi, ganin yadda Naseer yayi wanu duhu lokaci guda. Ta ce,"Dan Inna! An gaishe ka da aiki. Ku shiga gani nan zuwa." Ya wuce simi-simi. Sageer ya bi bayan sa, suna zaune. Inna ta gama abinda take yi a kicin, ta bi su dakin. Zarah ta leko daga bayi ta ga Inna, ta shige sai ta sadado ta aje buta, ta suri hijabin Inna dake shanye bisa igiya ta yi waje ta bar unguwar. "Sannu dan Inna, ka sha aiki Wallahi, ya gajiya? , Ya sunkuyar da kai Sageer ya ce,"Inna kuskure ne, kin kuma san ajizanci irin na Dan-adam. Amma a yau ya gane, har ya tuba........ Ta katse shi, tuban mazuru? Sau nawa Naseer ke cewa ya tuba a gidan na ma kawai, wanda na sani? Ai ba zan iya fadi ba. Yanzu wa gari ya waya? Babu abinda ba mu gaya maka ba D'an Inna, tun kafin ayi auran nan. Bayan anyi kuma, ba mu fasa ba, sai dai in kafar ka bata shigo da kai gidan nan ba, amma ba ka ji. A fuska lafiya lau ka ke, halin ne kawai ka kasa gyara shi, su yi dai-dai da fuskar ka. Me yasa? A yanzu wa ka ke ganin zai iya tunkar Alhj? Babu abinda za mu iya gaya masa, ya yarda, saboda ka riga ka rushe ginin tun ranar zane. Naseer ya ce,"To Inna shi kenan, haka za'a sa ido, auran ya kare kenan? Ta ce, "Eh mana, ta riga ta gayawa Babanta ba ka son ta, wa ka ke zaton zai je ya ce, karya ne? Ya ce,"Gaskiya Inna ban yarda ba, na san ana zuwa biko Inna. Sai dai in ba za ki je min ba ne kawai
Ta yi dan murmushin dole ta ce,"Dan Inna manya, ga laifi, ga saurin tuba. To shi kenan, ka bari Baban na ku ya dawo, za mu san yadda za'a yi." Ya numfasa ya ce,"Wai ita ma Zarah don ta kara min hawan jini shine ta bar gida ko? Ina take, sai ta ci dan banzan duka yau, in ni sa'an ta ne, za ta gaya min." Dariya suke da Inna da Sageer, kafin Inna ta ce,"Yanzu ta shiga bayi, za ta yi alwala ta yi sallah." "Ina nan ina jiran ta ta fito,." Inna ta mike,"Bari in kawo maku abinci Sageer. To Inna. Sageer ya amsa. Ta fice,"Sageer ya ce, "Na ciro maka wayar Rediyon can ne?, Me zan yi da ita? Dukan mana harka mance? Tsaki yayi ya dauke kai. Inna ta shigo da abinci ta ce,"Ka fa ci. Sageer ka matsa ma sa ya ci. Ya ce,"Ai zai ci Inna." Ta yi waje ta koma daki. Shiru- shiru Zarah ta ki fitowa daga bayi. Inna ta fito da wannan mamakin, tana tambayar kanta,"Ita wannan zaman me take yi a bayi?" Tana sa aya, ta aje ido bisa buta a gefe. Ta leko dakin ta ce,"An gama dukan?" To ai ban ji kuka ba, bata daku ba kenan." Suna dariya ya ce,"Ai bata shigo ba Inna.." Ta gintse fara'a ya ce,"Ban gane ba? Ga shi ta aje butar a waje. Ta juya ta fito tana kwala mata kira, yayin da dukkansu suka aje cokula suka fito. Kamar wasa, babu Zarah acikin gidan. Mamaki ya ishi Inna. Ta kama baki, tana kallon igiya babu hijabin da ta shanya. Sageer ya ce,"Wai ita Zarah da gaske take yi? Inna tayi shiru abin ya girmi shekarun ta. Naseer ya numfasa ya ce,"Inna ki gaya mata, idan ta ji ina asibiti kar ta sake ta zo guna. Zo mu je Sageer. Ya yi waje. Sageer ya ce,"Inna ki ce Allah ya bata hakuri. Sai anjima." Da kyar ta iya amsawa,"Allah ya ba mu alkhairi." Shi ma ya wuce. Inna ta ja kujera ta zauna, yau na ga zamani ni A'isha. Kiri- kiri yarinya ta ban kunya? Suna tafe a mota Sageer, ya ce,"Yanzu ina muka nufa? Ya ce,"Gidan za ni, duk ayi ta ta kare, idan ma yankana ni za su yi, su yanka. Ba shi kenan ba? Idan kowa yayi min, ai bai kamata Zarah ta yi min ba. Duk saboda wa na shiga wannan halin? Ba saboda sonta ba ne? Duk ba ta ga hakan ba." Ya furta. Sageer yayi shiru domin ya lura abokin sa ya zare gaba daya, kar ya tofa wani abu, ya kara masa zafi. Ya ci uban birki a kofar gidan, ya fito yayi cikib gida, bai ko saurari Sageer ba. Sai dai yana shigowa ciki ya tsinkayi Ameer na ta tsala kuka. Nan da nan ya yi turus, guiwa sa ta kwa6e, a salu6e yai sallama falon. Umma na kokarin goya Ameer a lkcn Abba kuwa na zaune gefe iya wuya yake. Kuma yana ji da kowa, duk wanda ya kuskura yi masa wata magana akan Naseer. Yana shigowa. Abba ya mike ya debi takalman sa ya bar gidan. Naseer ya bi shi da kallo, ya kasa cewa da shi komai, har Umma ta gama goyon, ta sa hannu ta dauke gwangwanin (Prisso-cream) din da ta siyo ta dora bisa firij, ta dauki fidar ta yi waje. Ita ma ya bi ta da kallo, sannan ya bi bayanta. Tana famfo tana wanke fidar da soso da omo. Ya bi ta, ya tsaya a gefen ta ya sanyaya murya,"Umma!Ji ta yi tamkar ya watsa mata wuta. Ranta ya ci gaba da k'una kamar ta rufe shi da dukan fitar hankali. Ya durk'usa ya mika hannayen sa gaba gare ta. Idanuwansa dauke da kwalla. "Umma, ki yi wa girman Allah ki amsa min. Umma ki dube ni ki saurari rokona. Na yi laifi Umma, amma tuni na gane kuskure na, ku ba ni dama ta karshe Umma. Da yardar Allah ba zan sake saba maku ba, Umma ki taimake ni." Ta gama dauraye fida, ta yarfe ruwan, ta juya ta koma daki tana daddaure su yadda suke. Naseer ya nemi wuri nan ya zanau dirshan! Sageer ya matso zai masa magana, yayi sauri ya riga shi." Je ka gidan abin ka Sageer. Na gode." Ya yi dan jim, yana kallon sa,"Ka ta fi na ce, babu komai, sai mun hadu." Ya numfasa ya ce,"Shi kenan, Allah shi kyauta." Ya juya ya fice, ba tare da Naseer ya sake cewa wani abu ba. Nan yayi ta zama har ya tuno, bai yi sallah ba. Yayi alwala a nan famfon, ya wucce sasan su, yayi Sallah a falo ya ci gaba da zama nan bisa sallaya. Babu abinda zuciyarsa bata saka masa ba. Zarah kuwa bata dowa ba, sai bayan sallar la'asar, ba shakkar komai. Ta yi sallama ta shigi ta wuce Inna a tsakar gida ta shigo daki. Inna ta tafa hannu ta ce,"Da izinin wa ki ka bar gidan nan? Ina kuma ki ka je? Kai tsaye ta amsa,"Inna ai na gaya maku ba zan koma ba. Kin zaci wasa na ke yi ko? Ta ce,"To ba kuwa zama a gidan nan ba, bari baban na ki ya shigo. Na lura so ki ke ki kawowa mutane raini. Ta juya ya bar dakin. Zarah ta matsa inda kulolin abinci ke aje, ta buda ta zuba ta hau ci. Karfe 5 M.Umar ya shigo gida, Inna ta feshe shi. Ya jinjina kai ya ce,"Wai Zarah da na sani ki ke fadi? Ta ce,"Ka na wasi-wasi kenan? Shiga tana nan a daki." Tunda ya baro dakinsa yake balbala masifa har cikin dakin."Ki hada kayan ki, ki koma inda ki ka fito! Ta ki motsi, M.Umar har da barazara duka, amma ko alama Zarah bata motsa ba, sai sharar kwalla take yi. M.Umar ya cika da al'ajabi, yana haki, ya koma dakin sa. Inna ta yi zuru tana kallon sabon salo. Fadi take cikin ranta,"Zarah ta kangare." Haka kowa ya kwana a wannan dare. Babu barcin kirki.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ ------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Washe gari bayan sallar asuba. Nusaiba ke zaune bisa gado, tunani bisa tunani. Tun jiya take cikin wannan yanayin. Musamman da ga Abbanta ba shi cikin sukuni kuma tun isowarsu gida, babu inda ya sake fita. Tashin hankalinta ya k'ara tsananta, tun daga lkcn da ta ga nononta ya cika, har ya fara tsiyayewa a banza. Bakin takaicin dake cinta kenan, a halin yanzu bisa gado, ta rasa inda za ta tsoma ran ta, ta ji sanyi sbd tunanin dan kyakkyawan dan ta. Ta tabbata yana can yana kukan neman nono, ga shi nan yana zubewa a iska. Farkewa ta yi da kuka, sbd tausayin rayuwar da Naseer ya je fasu ita fa dan ta,. Ji ta yi an riko ta. Muryar Umminta ke fadin,"Nusaiba! Daina kuka, ki yi hkr. Ta fado jikin Ummi ta rungume ta. Ummi ta shafa kanta ta ce,"Ki yi shiru na ce. Allah ne ya kaddaro miki wannan al'amari. Yanzu dago fuskar ki ki ji. Ta dago, Ummi ta sa hannu ta share mata hawaye, kafin ta ce,"Abinda na ke so da ke Nusaiba, ki yi hakuri mu je a dauko yaron nan.Bawan Allah ne shi, bai da laifin komai. Sannan shayar da shi da za ki yi, shine yake sanya shakuwar uwa da danta, soyayya tare da jin kai.Ki sani Nusaiba Ubangiji ne kadai ya san dubun ladan da uwa take samu tun daga daukan ciki, haihuwa, raino tare da bada tarbiya, ga 'ya'yan da Allah ya bata,kar ki bari wannan gara6asar ta wuce ki Nusaiba. Ki dauko dan ki ya shaku da ke, ya san cewa ke ce mahaifiyar sa.
Ta yadda zai ji kan ki, a cikin zuciyar sa, idan Allah ya raya shi. Na yiwa Abban ki magana, na rarrashe shi, na kuma yi nasara, ya amince, yanzu yardar ki na zo nema, domin ya ce shi ba zai matsa miki ba, duk abinda ki ka za6a shi za'ayi.
Shi kuma Naseer din muna nan muna jiran sa, ya kawo miki takardar ki.
Yanzu me ki ka ce?
Ta goge kwallan da suka dararo mata, ta ce,"Ki je ki dauko shi Ummi, babu komai."
Ta tallafo fuskarta ta ce,"Yayi kyau. Allah yayi miki albarka.
Amma ki tashi ki shirya Direba zai kai mu, don ki kintso kayan ku a natsa.
Tashi ki daina kuka, ba na son ki na damuwa, kin kuma san Abbanki hankalin sa ba zai kwanta ba.
Ta goge hawayenta sarai,. Umma ta kama ta ta riko, ta raka ta hanyar bayi, sannan ta fice ita ma, don shiryawa.
Abban ke kwance a falon sama bisa kujera, shi kadai yake kallon silin yana lissafon halayyar Dan- adam mai abin mamaki.
Nusaiba ta shigo cikin shirin tafiya.
Kamar mai ciwo yake kwance, bai motsa ba har ta zo gun sa, yana kallon ta.
Ta tsugunna ta kwanto kanta jikinsa, ta yi shiru.
Ya daka kanta ya ce,"Bebina, ki je ki dauko dan ki, ki shayar da shi.
Allah zai ba ki lada, kin ji?Ta amsa da kai. Ya ce,"Mike ku tafi, na ga Ummin ki ta gama shiryawa.
Allah ya kiyaye hanya." Ta ce,"Amin Abba na." Ta mike ta wuce ya bi ta da kalllo, ta kai kofa, ta waigo suka hada ido, yayi dan murmushi yana mata (bye-bye) da hannu.
Ita ma ta yi masa, sannan ta sauka, lkcn karfe 7:30am. Ummi ta matsa mata ta dan ci kayan karin safe.
Karfe 8 Direba ya dauko su, suka damk'i hanya.
Karfe 8 din dai-dai. Naseer ya shigo falon, Umma, don gaishe su ko ba za su amsa masa ba.
Umman kadai ke falon,
tana ta faman gyangyadi.
Da alama Ameer ya sami barci, domin cikin dare yana ta jin kukan sa.
Bata kalle shi ba, ya durk'usa gaban ta, ya ce,"Umma ina kwana?
Kamar za ta kyale shi, sai wata zuciya ta ce, amsa.
Bata kalle shi ba ta ce, lafiya.
Farin ciki ya lullube shi, ya ce,"Na gode Umma.."
Ta kyale shi.
Yayi dan jim yana kallonta, kafin ya ce,"Umma ina Abba?
A fusace ta dube shi, ta yi masa tsawa,"Ga shi nan a baya na a goye!
Tabatacce maras kunya.
Ka sake zuwa ka tambaye ni, ina Abba ya ke, sai na ci mutuncin ka!
Yasa hannu ya dafa guiwoyinta ya ce,"Yi hakuRi Ummana, ba zan sake ba.Dama Zarah ce ta ce ba za ta dawo ba, sai Nusaiba ta dawo, shine nace ko za ki sa baki ta yi hkr ta dawo kafin a shawo kan Alhj?
Kai tsaye ta dube shi, tsakar ido ta ce,"Ban zuwa." Kar mu yi haka dake Ummana. Wallahi na yi nadamar abinda ya faru, ku sa ke ba ni dama ku gani zan rike Nusaiba iya rayuwata.
Ta dube shi a dage ta ce,"Bakin alkami ya riga ya bushe maka Naseer, domin jiya da daddare su M.Umar da M.Lawar sun zo. Amma Abbanka ka ya rantse, ya masu, babu ruwan sa a cikin maganar ka.
Haka ni ma bai lamunce min ba.
Saboda haka ka makara, dabara kuma ta rage wa mai shiga rijiya. Ina fatan ka gamsu. Yayi zuru kafin, ya numfasa ya dube ta ido sun kawo kwalla.
"Shi kenan Umma, na gode. Abinda na ke son ki rokin min Abba, shine, don Allah yayi hkr, idan na gaishe shi ya rinka amsawa. Ni zan fita, ga wannan koda Ameer yana bukatar wani abu." Ya ciro dubu 2, ya aje bisa hannun kujera ya tashi ya fice.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~­ ~~~~~~~~~~------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Karfe 9 ta gota kadan Jeep din su Hajiya Zulai ta yi fakin kofar gidan su Naseer. Suka fito Ummi na rike da hannun Nusaiba. Ummi ta yi sallama tsakar gida. Umma ta amsa daga falo, a lkcn kuwa ta kammala shirya Ameer tsaf!Yana ta tashin kamshin hoda. Bata dauki murya sosai ba, don haka ta ce,"Maraba, ku shigo mana." Ummi ta yaye labule. Umma ta mike baki har kunne,"Hajiya!
Ah!
Nusaiba!
Sannun ku da zuwa."
Suka zauna a kujera Umma ta mikawa Ummi Ameer, ta karbe shi. Sai ta wuce firj za ta dauko kayan sha.
"Dama kin bar shi, kin san safiya ce." Duk da haka ta kawo da Jus din kananan kwali da kufuna 2.
Bayan sun gaisa, Umma ta tambayi Alhj? Sai Ummi ta ci gaba da cewa,"Ba wani abu ya kawo mu ba.
Ameer mu ka zo tafiya da shi, ya zauna wajen uwar sa ta shayar da shi. Ko dama 6acin rai ne yasa aka aje shi."
Kwalla suka cika idanuwan Umma ta ce,"Gaskiya ne kuwa, na ji dadi, domin a gaba daya wannan al'amari Ameer shine abin tausayi.
Shi kuma wancan sakaran, ai kyale shi ya gasu, duk da cewar ya ce yayi nadama." Ummi ta yi dan murmushi ta ce,"Ai ba'a soyayya dole, mu ma mun san haka shi yasa Alhj ya ce a gaya masa, tana jiran takardarta, ko zuwa jibi. Insha- Allah za mu turo mota akwashe kayan ta a dauki motar ta."
Umma ta goge kwalla ta ce,"Ba laifi, ki yi hkr Nusaiba kin ji? Allah ya amfana miki dan ki. Ta dan sadda kai ta ce,"Ba komai Umma.
Idan kuma na yi miki wani laifi, ki yafe min." Ta girgiza kai,"Baba abinda ki ka yi min Nusaiba, Allah yayi miki albarka."
Ta ce,"Amin." Ummi ta ce,"To bari mu je, za ta debi wasu kayan kafin a zo kwashewa." Umma ta ce,"To bari in kawo maku wani makullin, ya fita da na hannun sa."Nusaiba ta ce,"Ina Antina Umma?
Ta ce,"Ita ma ta tafi."
Suka dubi juna, kafin Ummi ta tambaya,"Saboda me?------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 3-03 Posted by ANaM Dorayi on 11:46 PM, 21-Nov-15 _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
Fa ce,"Ita ma ba za ta zauna ba.
Sai Nusaiba ta dawo.
Kin ga ya 6ata 2 kenan, sai wani gyaran Allah.
Nusaiba ta dafa kirji ido waje, sun kawo kwalla, ta dubi Ummi ta ce,"Me yasa Antina za ta yi haka? Ai ni ba zan ta6a dawowa ba, yakamata yayi ta gane wamman.
Ummi mu je in debi kayan, mu wuce wajen ta."
Suka mike, Umma ta kawo makulli. Nusaiba ta debi kayayyakin da take son diba. Abubuwan dake firj din ta duk ta kwaso ta kaiwa Umma. Bayan Direba ya zuba kaya a mota, suka sallami Umma suka rabu suna daga wa juna hannu.
Babu Abinda zata yi, Nusaiba ta hana ta tafiya, babi abinda za ta iya yi.
Duk iya kaunar da take wa Nusaiba data zauna dakinta, dole ta kyale.------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Babban abin godiya ma shine, da suka tausayawa baWan Allah suka zo da kan su suka dauke shi.
Shi yasa take ta yi wa Allah godiya, ba 6ata lkc ta kira wayar Abba a kasuwa, ta shaida masa. Ba karamin farin ciki yayi ba, domin rabon sa da fara'a tin asubahin jiya. Sai kuwa yau da aka ce su Hjy sun zo da kan su sun dauki Ameer.
Cikin gidan su Zarah su kai sallama yanzu. Inna ta amsa. Ta leko daga dakin Malam Umar. Ah! Nusaiba! Maraba. Fit Zarah ta fito daga dakin Inna, baki har kunne,"Amarya! Antina." Zarah ta matso suka rungume juna." Kin dawo ko amarya?
Ta daga ta dube ta,"Haba Antina, zo mu je daga cikin in gan ki."Ta kama hannunta suka shige daki. Inna ta ce,"Ke Hajiya shigo nan, kafin su gama ganawar. Ina fatan dai na dawo mata da amaryarta ne, mu huta." Bata ce komai ba, suka shige, tana 'yar dariya.
Nusaiba ta dubi Zarah,"Me yasa haka Antina? Bai kamata ki yi wa yayanki haka ba." Ta ce,"Ni kuwa a waje na hakan ya kamata, domin ciwon 'Ya mace, duk na 'Ya mace ne. Na kuma shaku dake amarya tafiyar ki za ki ta jefa ni cikin wani yanayi na dacin rai."
Ta dafa kafadar ta, ta ce,"Kin fadi gaskiya,"Antina, kuma na san ki ni nuna min iyakar kaunar da ba duka mace za ta nuna wa abokiyat zamanta wannan kaunar ba.
Allah ne ya kaddaro zan sami Ameer, amma ke ce sila Antina.
Ban mancewa har ta kai ki ga rasa na ki cikin. Ina so ki sani Naseer, yana da halayya masu kyau, yana da kula tare da tsare hakki, ni ce kawai da bai so yake nuna min banbanci.Bai damu da ni ba, balle ya kula da hakkoki na. Kar ki damu Antina, ba laifin yayanki ba ne. Allah ne bai sa masa soyayyata ba, saboda haka na ke rokon ki idan ya zo daukan ki, ki yarda ki bi shi, domin ke ce rayuwar sa.
Ke yake so, da ya ke yake ra'ayin zaman aure. Abin alfaharin ki ne a wannan zamanin da ki ka sami miji kamar Naseer, mai tsayuwa akan alkawarin soyayya. A karshe ina son ki sani, har karshen rayuwata ba zan ta6a mancewa da ke ba Antina. Hasalima dole wata rana Ameer wajen ki zai dawo, kin ga har yanzu mu na tare ke nan. Kin hakura ko?
Abinda ya fi ba Zarah mmk, shine ashe Nusaiba na sane da abinda ya faru kafin Naseer ya shiga dakin ta. Gaskiya Nusaiba mai hakuri ce, irin wanda sai an sha bincike kafin a sami irin sa. Ta zura mata ido cike da kwallan tausayi. Allah na ganin bata son rabuwa da amaryar ta.
Nusaiba ta kamo hannun ta, ta dora bisa kan ta,"Ki yi min Alkawarin Antina, a yau za ki koma dakin ki, ba gobe ba, kin ji? Ta goce da kuka, suka rungume juna, haka wahayen ya kubce wa Nusaiba,"Za ki koma ko? Ta dago ta goge kwalla ta ce,"Zan koma Amarya, amma kema ina rokon ki idan a an dai-daita da su Abba, don Allah kar ki kafe ki ce ba za ki dawo ba.Ta yi dan murmushi, ta ce,"Shi ke nan, bari mu zo mu tafi, sai mun yi waya, shi kenan na ji, alkawarin za ki min kamar yadda na yi miki." Ta yi dan jim, kafin ta ce,"Ai ba laifi na bane Antina, ke ma ba za ki yarda in zauna inda ba'a so na ba."
Ta kada kai.------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Da ke nan amarya, amma yanzu ina mai tabbatar miki yayanmu yayi nadama, ko bai gaya min da bakin sa ba, ni na yi imanin yana son ki, ba ki ga yadda ya fita hayayyacin sa ba, lkcn da lalura ta kama ki kuma ya kula da ke yadda yakamata.
Ta ce,"Anitina ki na so ki gyara yayanki ne kawai, amma ni na san tausayine irin na musulunci. Kin san musulmi mai imani ya kan tausayawa dan- uwansa a lkcn daya shiga wani hali.
A bar maganar nan Antina, ki yi min addu'ar Allah ya zaba min abinda ya fi zama alkhairi."
Ta numfasa, hannun ta bisa kafadar ta,"Zan miki amarya. Allah yasa alkhairin a gidan yayanmu yake."
Ta mike tana dan murmushi, ta fito ba tare da ta ce komai ba, sbd bata son maimaita zancan. Dakin da su Ummi suke, suka yi sallama. Inna na rike da Ameer.
Zarah ta nufi gun sa, ta dauka, Ummi ta ce,"Zo nan. Ta wuce wajen ta da Bebi a hannun ta, ta tsugunna gefenta, ta dafa kafadar ta, ta ce," Zarah ba'a wasa da aure, hkr za ki yi ki koma dakin ki kinji?Kan ta sunkuye tana dan ta6a kuncin Ameer, ta amsa da kai, sannan ta ce,"Wallahi Ummi Naseer ya gane kuskuren sa, tun jiya yake kuka, yana bin mutane ya samu aje masa biko. Abban sa ne ke fushi da shi, ya ki bada hadin kai.
Don Allah Ummi, ku yafe masa ku bar amarya ta dawo."
Ta ce,"Babu abinda Innar ki bata fada ba yanzu, amma Naseer ya riga ya rushe katangarsa.
Alhj na da saukin kai, sai dai idan ka ta6i shi, nan ne za ka gane ma yana da zafi.
Saboda haka ku taya mu addu'a. Allah yayi masa zabi." Zarah ta yi shiru idunwanta suka kawo kwalla. Ummi ta mike, ta ce,"Allah yasa mu gana." Duk suka tashi suna fadin Amin.
Har mota suka rako su, sannan Zarah ta mikawa Ummi yaron. Ta dubi Nusaiba, kowacce hawaye ya zo mata, suka rungume juna. Da sauri Nusaiba ta shige mota, haka ita ma Zarah ta ruga cikin gida, bata son ganin tafiyar Nusaiba.
Hawayen ta suka yawaita, tana sharewa, wasu na sauka. Direba ya damki hanya. Nusaiba ta yi shiru cikin mota, ta sak'a wannan, ta kwance wancan a game da maganganun Zarah. Tabbas su Abba sun gaya mata Naseer yayi dawainiya da ita sosai a cikin kwanakin nan 50 da ta samu kanta a wani yanayi.Sai dai babu wanda zai tantace me Naseer ke nufi cikin ransa? Ko ita ma Zarah hasashe ta yi, domin da bakinta ta ce bai fito fili ya gaya mata ba.
A cikin tunanin ne ta ji Ummi na fadin,"Ke ba shi nono ya sha, ya farka."------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Ta dube su firgigi. Ummi na masa mika tana cewa ka sha barci ko? Nusaiba ta mika ruwa aka ba shi, sannan ta karbe shi, ta mika masa nono ya kama yana sha.
Nan da nan so da kaunar sa suka kara shiga zuciyar ta har bata san lkcn da fa kura masa ido ba.
Karo na farko da ta tantance kamanin danta.
Tamkar Ameer na farko. Haka kuma hoton Naseer take gani zahiri bisa cinyoyinta. Tsigar jikinta ta tashi yar!
Saboda kyan surar yaron nan, musamman daya buda ido tar!
Yana dube-duben sa.
Ya sha sosai. Ta juya shi daya gefen, nan ma ya sha mai isar sa. Bai koma barci ba. Ummi ta karbe shi, ta ci gaba da renon mai gida.
Jimawa kadan Kausar ta kira wayar Ummi, ta mika wa Nusaiba ta ce,"Ungo Kausar ce." Ta kar6a da saurinta, ta danna O.K."
"Hello."
Ta ce,"Hello Nusaiba ya karfin jiki? Alhamdulillahi."
Ta ce,"Ya maganar Bebi ne? kin san Allah jiya ban yi barci ba." Ta ce,"Bisa hanyar komawa gida muke yanzu, mun je an dauko shi.Ta nisa ta ce,"Better. Ai ni ba zan iya ba, ka aje a jariri, ai ka cuce shi.
Shi me ya sani? Ta yi dan murmushi,"Kausar kenan."
Ta ce,"Tare ku ke da Ummi ko? Bari in yi shiru, idan kin kebe, kya kira ni. Ku sauka lafiya." Ta ce amin. Ta kashe waya.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~­ ~~~~~~~~~~------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Sun iso gida 2 rana. Alhj na falon kasa. Suna isowa Ameer yasa a kafada ya haye sama, yana fadin "Ku hayo sama in gan ku."
Suka haye suka bar Direba na shigo da kaya. Mariya na taya shi. Bayan sun natsa a zaune.
Alhj ya dube su ya ce,"Bayan tafiyar ku. Yakubu ya zo min da maganar Naseeer, haka shima M.Balarabe ya kira ni a waya, kodayake yana min godiya ne akan dauko Ameer da aka yi, har ya ce zai zo musamman yayi min godiya.
Nace ya bar shi kawai, ta wayar ma ya wadatar, na kuma ji dadi. To koma dai menene, ban son mutane su dame ni akan maganar nan.
Lokacin da zan ba Naseer 'ya ta ban yi shawara da kowa ba.
Shi yasa ban son kowa ya sanya min baki, duk hukuncin da na yanke. Na riga na yanke shi. Saboda haka na kira wayar Fatima, na gaya mata za kikoma Jordan, ni zan kar6ar miki takardarki ki a wajen Naseer.
Ina fatan hakan yayi dai-dai.
Idan kuma akwai gyara ina jin ku?
Ummi ta ce,"Zabin Nusaiba ne, me ki ka gani? Ta ce,"Hakan ya ma fi Abba na.
Hankalina zai fi kwanciya."
Ya ce,"To shi kenan.
Insha Allahu nan da kwana 3 za ki bar kasar nan.
Allah ya kawo miki mai son ki, ki aura."
Ummi ta ce,"Amin."Sun jima suna hira nan, kafin Nusaiba ta dawo dakinta, duk bata da kuzari a jikinta, ita kanta bata san dalilin ba. Ta dan kwanta don ta huta. Sai ga Ummi da Ameer ya sake tashi barci.
Ta kar6e shi. Ummi ta fice.
Bayan ya gama sha tashinfidar da shi, ita ma ta kwanta tana fuskartar shi. Rike yatsun sa ta yi tana dan kada su, tana murmushin jin dadi. Sai da ta ci abincin rana, sannan ta kira Kausar suka kebe. Ita ma Kausar din ta goyi bayan Alhj akan komawar Nusaiba Jordan, domin a ganin ta zatafi samun nutsuwa.------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Al'amarin Naseer kuwa, bayan ya baro wajen Yakubu, don jin yadda suka yi da Alhj, ransa 6ace ya isa gidan su Zarah.
An riga anyi sallar la'asar. Yana shiga Inna ta yi masa albishir da cewa su Nusaiba sun zo, sun dauki Ameer. Take nan yayi wa Ubangiji sujada, yayi godiya gare shi, sbd tsabar tausayin da Ameer ke ba shi.
Nan da nan wani yanki na 6acin ran sa ya goge. Sai da ya natsa. Inna ta sake fadin,"Sannan su zo nan sun rarrashi Zarah, ta ce za ta koma, nan ma kai take jira, dama kuma ko ba ka zo ba, ni zan maida ta anjima." Ya numfasa, kaunar Nusaiba ta k'ara shigarsa.
Yarinya mai hankali, haka kawai ya tsaneta. Ko me yasa? Ya karkada kai ya ce,"Inna na gode. Ina Zaran take? Ta zo mu tafi." Ta ce,"Tana nan a ciki tana jin ka." Ya mike daga inda yake zaune, ya shiga dakin. Tana zaune bisa kujera, jakarta na aje gefe.
Ya tsaya kan ta ya ce,"Sai na miki dukan musulunci tukuna, bari ki gani." Ya nad'e gefen rigar sa, ya tsula mata." Ni ki ke ba wuya ko? Ta 6alla masa harara. Ya mammare kuncinta. Idanuwanta suka kawo kwalla, sbd Nusaiba da ta fado mata rai.
Ya tsugunna ya kama kunnuwan sa 2, ,"Na tuba." Ya zura mata ido, tana share kwalla," In dai amarya ce, ki kwantar da hankalin ki. Insha Allah za ta dawo. Taso mu tafi." Bata tanka masa ba, ta mike tana ci gaba da share fuska, ya dauki jakar tayo waje, ya biyo ta.
Inna tana zaune, suka sallame ta, ta k'ara jajja masu kunni, suka tafi.
Ko cikn mota ta k'i magana, ya dubeta, yayi d'an murmushi,"Zarah manya,
yanzu ke ma ko tausayina ba kya ji, ina ku ke so in sa raina?
Ta yamutsa fuska, a karo na farko, ta ce da shi.
Oho?
Ai dama wanda bai ji bari bari ba, zai ji hoho!
In banda son kai ma, wa ka ke zaton zai tausaya maka?Ya ce,"Ke mana sanyin raina. Ina ganin ai saboda ke hakan ta kasance, sbd sonki kadai na aje wa zuciya ta. Bai kamata ki juya min baya ba, idan duka duniya sun dora min laifi.
Kalaman sa suka sa jikinta yayi sanyi, ta yi dan shiru kafin ta ce,"Na san haka yayana, amma lokacin da kowa ke gaya maka gaskiya, bai dace ka ki daukar maganar na gaba da kai ba.
Yanzu ina amfanin abinda ya faru? Ya kamo hannunta ya ce,"Wallahi babu, ban ta6a gane ni ba ni da wayau ba, sai wannan karon Zarah. Abin kamar almara na ke ganin sa."
Ta ce,"To yanzu menene abin yi? Ya ce,"Gaskiya ban sani ba, domin Yakubu ya je, amma Alhj ya ce mai kama da ni ma bai son gani, balle ya ji wata magana akan bikon Nusaiba.
A karshe ya ce masa ya riga ya soke ni a rayuwar sa.
Kin ji bayanin Alhj, sbd haka ni ban da wata dabara."
Ta yi tagumi, kafin ta ce,"Tabd'i!
Kai yanzu in tambaye ka tsakanin da Allah, ka na son amarya ta dawo? Ya dube ta ya ce,"D'ari bisa d'ari na zuciyata ke kaunar Nusaiba ta dawo, sbd ta yi min abinda ba zan ta6a mancewa da ita ba a rayuwa."
Ta ce,"To ka gwada wannan dabarar ka gani. Ka ajiye wani tura mutante wajen sa, ka tafi da kan ka, ka ce masa, sai ka ga abinda ya ture wa buzu nadi.!Duk wata bak'ar magana da wulak'anci, ka jure shi, da kansa zai hakura, yana ji, yana gani zai sakar maka 'yar."
Yayi d'an murmushi,"Zarah ke nan, bai saurari manya ba ma, sai ni uban laifi? To zan gwada. Amma ni kunya ma na ke ji mu hada ido da shi." Lallai ba sokake ta dawo ba, kunya ai murje ta ake yi." An gama Zarah,"Allah yasa amarya ta dawo, ko don in huta da ciwon kai."
Ta 6allo masa harara, ya dube ta yayi murmushi,"Ai kin ga na dan sami sauki, ko hararar na rinka sha ta isheni jin dadi." Ta d'an buge shi a kafada,"Allah za ka sani yayana."
Ya take birki a kofar gida, ta dauko jaka a kujerar baya, ta fito ta riga shiga gida. A falon Umma ya isketa.
Umma na mata fada. Ya zauna gefe ya ce,"Umma sun zo sun kar6i Ameer ko?
Cikin rashin kulawa ta ce,"Sun zo."
Ya ce,"An gode ma su."
Ta yi biris da shi ta ci gaba da mgnr ta da Zarah. Jimawa kadan ta koma sasan su, ta yi share- share da goge-goge.
Har dakin Nusaiba ta gyara shi, ta goge zuciyarta na saka mata lallai amarya za ta dawo da zarar Naseer ya je da kan shi.
Kwana 3 kenan Naseer ya kasa zuwa Kaduna, sbd kunya da jin nauyin Alhj. Yau kan Zarah har kuka tayi masa, tana hada shi da Allah da Manzon sa.------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Yayi shiri tsaf!
Ya biya ya dauki Sageer suka danki hanya. Gida suka fara zuwa. Mai gadi ya ce ma su babu kowa cikin gidan, duk sun yi tafiya.Daga can ofis suka nufa, sakataransa ya gaya masa Alhj ya tafi Abuja.
Kai abinda babu sa'a. Haka suka dawo jiki babu kwari tare da mamakin ina za su je kuma gaba dayan su har da Nusaiba?
Koda suka dawo irin tambayar da Zarah ta rink'a yi kenan.
Har ta k"arawa Naseer haushi ya ce,"Wai ina zan sani ne Zarah da ki ka dame ni da tambayar nan?
Haba!
Yayi tsaki, ya tashi ya bar mata gidan, don sai su yi fada.------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Karfe 10 na safiya su Alh. Basheer na filin jirgin. An gama bincike, an tantance Nusaiba da Ameer tare da kayayyakin ta. Suka yi sallma da su Ummi, ta wuce tana hawaye sabeda Ameer bisa kafadarta, hannunta daya yana kan Beby. Sai dai jirgin da za su shiga, sai sun dan jira shi, ya gama hutawa.
Kamar yadda aka bada sanarwa.
Duk fasinjojin da ake tantance su, na zaune falon, kafin a ba su umurnin shiga jirgi. Nusaiba ta zo ta zauna kusa da wata mata.
Ita ma rungume take da Bebi cikin shawul, ga wata yarinya a tsaye gaban ta, za ta kai shekaru 4.
Tana zama, ba ta yi aune ba, ta ga yarinyar nan a gabanta, tana ta6a Ameer,"Bebi! Mamanta ta juyo tana murmushi ta ce,"Husna ba kya ji ko? Ba na ce ki tsaya waje daya ba? Ta ce," Umma kin ga Bebi mai kyau? Zo ki gan shi."
Suka fara dariya.
Nusaiba ta ce,"In ba ki shi ne ku hada da na ku? Ta ce,"Eh.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Ya sunan shi? Ta ce,"Ameer, ke ya sunan ku? Ta ce,"Adnan.
Mamanta ta ce,"Oh ni, kin ji dadin halinki Husna."
Ko a jikin ta, sai k'ara kwanciya take jikin Nusaiba, tana wasa da kuncin Ameer.------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Tun daga nan hira ta goce tsakanin Maman Husna da Nusaiba.
Kamar minti 15, aka sanarwa fasinjoji. Su wuce su shiga jirgi.
Tare suka sa6a yara suka wuce, ita fa Husna bata yarda ba, son Ameer take yi, don haka Nusaiba ta kamawa jaka tana bin ta da gudu.(First class) dukkan su za su zauna, sbd haka ga kujerar Nusaiba, ga ta su. Adnan da Manan sa. Su dai ba su yi sukuni ba. Sai da barci ya kwashe Husna. Sun sauka lafiya, ga 'yan tarbar 'yan uwan su nan fululu kowa na jira. Nusaiba ta dudduba, bata hango Antinan ba, haka Maman Husna ke fadin,"Husna kin ga Abbanki bai zo ba ko?
Tana rufe baki ta yana kira,"Husna! Ta kwace hannun ta, ta bi 6angaran da ta hango shi." Abba!
Karo na farko da Nusaiba ta dubi Abban Husna, sam bata gaskanta idanuwan ta ba. Ta kara duban sa da kyau, babu ko shakkar Ibrahim ne.
Jikin ta duk yayi la'asar saboda al'ajabin sake haduwar ta da Ibrahim, wanda tuni ta mance da shi a duniya. Suna tafe Maman Husna na fadin,"Sai yaushe ke nan?
Ta ce,"Ai ina hada layi na, za ki ji kira na. Ai ba zan yi wasa da lambar da ki ka ba ni ba, dole ne in kira Husna."
Suka yi dariya. Nusaiba yanke tabi wani 6angare,"Bari in jira su Antina a nan. Ta ce,"Ah! Ba za ki sallama da Husnar ta ki ba." Ta ce kyale ta, ta ga Abban ta, ta mance da ni." To shi kenan, sai na ji ki." Ta wuce inda su Husna ke tsaye da Abban ta, duk da cukuikuye shi, ta hana shi sukuni.
Babban yaron dake tare da shi, ya rugo ya rungume Maman su, shi ma zai kai shekara 6 ko 5 da rabi. Nusaiba na tsaye duk ta kosa Antinta su zo.......Ta bar wajen. Don bata son Ibrahim ya gan ta, kawai ji tayi Husna na rikota tana fadin,"Zo ka gan shi Abba, Bebi mai kyau."
Gabanta ya fadi, ta waigo cikin tsarguwa, suna hada ido da Abban Husna ya ji kamar zai fadi, sbd faduwar gaba. Bai san lkcn da yayi zuru, ya zuba mata ido ba.
Ta shiga dan yake, tana wa Husna magana,"Ke wai ba mun yi sallama tun a jirgi ba?
Tsayuwayar Maman Husna wajen yasa Ibrahim ya dawo duniyar daya tafi, yayin da Husna ke fadin,"Abba na zai ga Bebi mai kyau.
Ka gan shi? Suka fara dariya, ya kar6e shi ya dan daga sama ya ce,"Good day handsome Bebi!
Yayin da Nusaiba ta juya tana tambyara sunan yayan Husna, ya ce,"Imran." Ta ce,"Uhnmm..............Sunanka da dadi." Husna ta ce,"Ni ma sunana da dadi. Ta kama habarta ta ce,"Sosai ma, ke mai babban suna ma ba'a fadi, shi yaya ake kiran ki Husna."
Dadi ya kamata har da yi wa Imran gwalo.
Ibrahin ya numfasa, ya dubi matar sa ya ce,"Gaskiya wannan haduwa tana da ban mmk. Ai dole ayi dalla-dalla. Wannan ita ce,"Nusaiban da na ta6a ba ki labari. Nusaiba ga Madan din na Sakina." Mamaki ya kama Maman Husna, take nan kishi ya kulle ta. Ta dan daure fuskata ta ce,"Ka ce min wacce ta kusan zarar min da kai.
Nusaiba ma ta gyara fuska, ta ce,"Ki bar maganar nan Maman Husna ta riga ta wuce." Ya ce,"Sai zumunci ko? Yana da kyau, ina fatan kin bata adires, kafin ta koma, za ta kawo mana Ziyara."Sakina ta gyada kai tana yamutse fuska,."Na dai bata lambar waya."
"Mts, ina ganin ya kamata mu wuce Abban Husna, na fara gajiya wallahi."
Ya ce ,"Tunda ba'a zo daukan ki ba, why not ba za ki bi mu, mu sauke ki gida ba? Sakina ta kauda kai yayin da Nusaiba ke 'yar dariya, tana fadin,"Ku bar shi Allah na gode. Ai na san za su zo."
Ta mika hannu ta kar6i Ameer a hannun sa.
Ya maida hannaye aljihu, ya numfasa, amma bai iya cewa komai ba.
Ta shashshafa kan su Husna ta ce,"Sai anjima ko Husna!? "Bye-bye Bebi, sai ka zo gidan mu." Suka yi sallama da Sakina, ba wata walwala a fuskarta, ganin haka Ibrahim yayi gaba rike da hannayen yaran sa.
Sakinta ta bi bayan su cike da kishin babu gaira babu dalili.
Nusaiba na nan tsaye, duk takaicin al'amarin ya dameta ta, kamar minti 5 da wucewar su.
Antinta ta iso,"Allah sarki Nusaiba, sorry,"Wallahi sharrin mota ne, cak ta tsaya mana a titi da kyar Direba ya gyara."
Yaranta mata duga guda 4, suka yayyame ta, kowa son ya dauki Bebi yake yi.
Babu 6ata lkc. Direba ya kwashe kaya suka rankya.
Tunda daga mota, har gida Antin Jordan ke balbala tsiya akan abinda ya faru.
Dakin ta daban, aka ware mata ita da Bebin ta, bayan an gama duk kayaniyar ganin juna har da maigidan ya tofa na sa albarkacin bakin sa.
Sai dai nasihohi yayi mata akan ta aje hankalinta waje daya, kar ta sa wa ranta damuwa.Daki ta koma ta yi wanka, ta yi alwala ta yi sallolinta. Gefen gado ta zauna tana tanunanin yanayin da suka hadu da Sakina, fara'a kamar gonar auduga, amma tashi guda ta sauya fuska, saboda mijinta ya nuna ya santa.
Ta yi dan murmushi, ta ce,"Allah sarki Antina, alkhairin Allah ya kai miki."
Ta sa hannu ta jawo jakar Bebi, ta daukko lambar da Sakinta ta bata a rubuce, ta sa hannu ta yayyaga, tana fadi a ranta,"Sa ran ki a inuwa Maman Husna, kullum ni da mijinki haduwar [Aiport] ce, rabuwar (Airport)." Ta matse a hannun ta, ta wuce bayi ta watsa (Dosbin).
-----------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Washe gari da wuri Naseer ya nufi Kaduna. Shi kadai kuma ya tafi, wannan karon zuciyar sa ta bushe, matar sa kawai yake son ta dawo.
Shi yasa ya kwashe duk wani tunanin dake ran sa a game dake ran sa a game da tinkarar Alhj.
Yayi fakin, ya fito kai tsaye falon yayi sallama.
Mariya dake goge-goge, ta amsa sannan, ta durk'usa ta gaishe shi ya ce,"Hau sama ki kira min Ummi." Ta ce,"Tana ma kicin, bari na kira ta."
Ya zauna Mariya ta wuce. Jin kadan ta dawo ta ce,"Ga ta nan zuwa." Ya share minti 5 nan, kafin Ummi ta iso falon.
Ya mike kai sunkuye ya ce,"Sannu Ummi." Bata tanka masa ba, ta wuce ta haye sama. Yayi tsaye nan kirjin sa na harbawa.Bai sake ganin kowa ba, wucewar minti 30 har ya gaji da tsayuwa ya koma ya zauna.
Can Alh.Basheer ya tinkaro falon.
Ummi na rike da jakar sa suna maganganun su.
Naseer ya kuma mikewa yayi tsaye irin na marasa gaskiya. Ko inda yake Alhj bai kalla ba, jakarsa ya karba. Ummi ta ce," A dawo lafiya." Ya ce,"Amin." Ya fice.
Ummi na ta wuce kicin, ta ci gaba da hidimomin ta.
Naseer yayi kamar ya nutse a kasa, jiki babu kwari ya biyo bayan Alhj, amma kafin ya karaso.
Alhj ya shiga mota. Deriba ya tayar. Haka ya tsaya kamar dolo, yana kallo aka bude get.
Motar ta fice. Ya wuce ya shiga ta sa, ya bi bayan sa.
Ofis ya ga sun nufa, shi ma ya bi su. Yana zuwa zai wuce sakatare, ya ce,"Alhj ya ce ka dan jira shi a nan tukuna."
Ya ce,"To." Ya zauna.
Shi kansa sakataran dauke da mamaki yake, domin bai ta6a yi wa Naseer iso ba wajen Alhj.
Yana nan zaune Alhjn ya kira waya, ya bada izinin Naseer ya shigo.
Ya mike ya tura kofa, ya sjiga Alhjn na ta aikin sa bisa (Laptop), bai ko kalle shi ba. Ya duka ya gaishe shi, ya amsa a dakile.
Yayi shiru, haka shima Alhjn bai dube shi ba.
A haka ya daure ya fara magana,"Abba, na san babu abinda zan gaya maka wanda zai faranta maka rai, amma duk da haka ina mai gurfanar da kai na gare ka a matsayin mai laifi.Ka yanke min duk hukuncin da ya dace dani, wanda zai sanyaya maka rai, har ka huce ka ban Nusaiba, in koma da ita.
Da sunan Allah na ke wannan rokon Abba, ka taimake ni don son Manzon mu.
Yayi shiru. Shi kuwa Alhj sai a aikinsa yake yi.
Kamar ba zai tanka ba, wucewar mintoci, kafin ya ce,"Ka na iya tafiya, zan neme ka."
Ya durk'usa guiwa 2 ya ce,"To shi kenan, na gode Abba.
Kuma ina k'ara neman afuwa akan kuskuran da na yi.
Ka gafarce ni Abba."
Ya ce,"Ka je zan neme ka na ce."
Ya mike yana fadin,"Na gode, a tashi lafiya."
Bai amsa masa ba ya fice.
Alhaji ya sauke numfashi, ya dafe goshinsa, bai san dalilin da yasa son Naseer yayi masa yawa a zuciya ba, duk lokacin da ya gan shi kaunar sa karuwa take.
Dole ce tasa ya yanke hukuncin nan, saboda ya kar6o wa Nusaiba 'yancinta.
Ofishin su Yakubu Naseer ya nufa, can bargar dawakai, amma wurin na kulle babu kowa, sai mai ba dawaki abinci.
Bai tsaya 6ata lkc ba, ya damko hanyar dawowa gida, yana tafe wasi-wasi ne fal cikin ransa, wata zuciyar na saka masa zai yi wuya Nusiba ta dawo, wata kuma na tabbatar masa za ta dawo ne, tunda ya ce zai neme ka.,
Ai kai d'an gaban goshin sa ne. Daya iso shago, ya tsaya wajen Sageer.
Bai dawo gida ba, sai karfe 1,abu na farko sada fara gani, shine babu motar Nusaiba dake lullu6e a wajen.
Gabnsa ya fadi, ya fito da sauri ya fada cikin gida.
Zarah na zaune a barndar sasan su, tana ta faman goge kwalla."Menene wai?
Ban ga motar Nusaiba ba a waje!
Murya na rawa ta ce,"An kwashe kayanta, ka ga shi kenan ta faru, ta k'are, tuntuni na ke gaya maka, ka je ka k'i................
Ya katse ta da masifa,"Don Allah isa haka, kar ki kara 6ata min rai!
Ko yanzu daga ina na ke? Ya ce zai neme ni? Ai shi kenan tunda baya son ta dawo!
Ya nemi waje nan ya zauna dabas, ya cire hula zufa ta keto masa.
Zara bata iya kara komai ba, ta ma tashi ta bar wajen.
Umma na jin sa, kanzil ba ta ce da shi ba.
Bayan sallar la'asar, yana kwance dakin sa ya rasa abinda ke masa dadi, kamar an kwaso son Nusaiba an kara cusa masa cikin zuciya, sannan a 'yan kwananin nan da bai ga Ameer ba, duk kewarsa ta ishe shi.Gaba daya abubuwan sun dagule masa, domin ya sani ba za su ta6a daidaitawa da Abbansa ba, muddin Nusaiba bata dawo cikin gidan nan. Ya runtse ido, ya dafe kai kamar ya kwarma ihu. Zumbur ya mike ya kwashi makullai, ya fice ko Zarah bata sani ba, ya fada mota. Ya sake yi wa Kaduna tsinke. Yana zuwa. Sakatare ya ce Alhj ya tashi.
Yana kokarin fitowa daga get. Motar Yakubu na shigowa. Suka tsaya kowa ya fito gaba dayan su, babu mai walwala a fuska. Yakubu ya fara magana,"Ko ka ji abinda ya faru?" Ya ce,"Na me ? Ya ce,"Na rufe (Dabai Riders) mana.
Alhj ya rufe kulob, yadda yake gaya min ma ya sa dawakan a kasuwa har an samu masu siya." Salati Naseer ya fara yi, kafin ya ce,"Saboda me? Ya numfasa ya ce,"Wallahi ban sani ba, amma tun faruwar wannan al'amarin na ku hankalin Alhj a tashe yake. Iyaka kokari na, akan ya sauya shawara, amma ya ce ra'ayin sa ne.."
Naseer ya k'ara tarus! Idanuwan sa suka kawo kwalla, ya ce,"Yakubu ban san yadda zan yi ba, dazun nan na zo na yi magiya gun sa, ya ce in je zai neme ni, wai ina zuwa gida. Na tarar an kwashe kayan Nusaiba kaf. Lambarta ba'a samu.
Kuma ni na san rufe kulob din nan, duk baya rasa nasaba da matsalar nan, wata kila yana ganin ta dalililin Polo ya hadu da ni.Ban san abin yi ba Yakubu? Ya ce,"Gaskiya ne. Magana kan ta gama lalacewa. Ka san komai Alhj zai iya yi saboda Nusaiba, kar ka manta ita ce 'yar sa kawai. Sannan duk abinda ya faru, kai ka jawa kanka, domin ba karamar asara ka yi ba. Sai ka yi addu'a Allah ya sa hakan shine alkhairi. Gida ka nufa?
Ya kada kai,"Ina nan sai na ga abinda ya turewa buzu nad'i. Yakubu ya ce,"To sai ka dawo,"Goodluck." Na gode." Naseer ya fice, shi kuma ya karaso wajen sakatare, ya aje abubuwan daya zo da su.
Gidan Naseer ya nufa. Alhj na tare da baki. Yayi sallama ta gaishe su. Alhj ya bi shi da kallo. Ya ce "Dama na zo ganin ka ne, bari in jira ka." Ganin mutane a wajen yasa ya amsa." To ina zuwa."Naseer ya fita, motar sa ya zauna yayi ta ji Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajinisa Yake3-04 Posted by ANaM Dorayi on 05:24 AM, 23-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
Zan yafe maka komai, ya wuce har abada, amma sai ka kawo min takardar Nusaiba."Kansa cikin giuwa, ya girgiza kai, ya ce,"Ba zan iya ba Abba, ka yi hkr." Ya ce,"Wannan ba hukunci na ba ne.Nusaiba ce ta buk'ata ta kuma bar min sallahu jiya kafin su wuce Jordan.." Ji yayi numfashinsa ya shake gaba daya, yana neman faduwa.
Ya kasa motsi, balle ya ce wani abu. Ya ci gaba da cewa,"Na ba ka nan da jibi ka zomin da takardar, daga nan zan maka bayanan wasu abubuwa da suka kamata ka sani.
Ka na iya tafiya dare yana k'ar yi." Ya dago idanuwa jajur! Ya ce,"Ummi ku taimake ni, ku ba ni lambar ta mu yi magana, na san zata saurare ni. Amma a raba auran a haka, abin babu dadi.."Abba ya ba shi amsa,"Ban son dogon nace Naseer, raina k'ara 6aci yake yi. Kwanciyar hankalin na da kai shine ka kawo min takardar Nusaiba. Yadda ba ka so, haka ita ma bata so, shi kenan magana ta k'are babu lallai babu tilas."
Ya sunkuyar da kai, yayi shiru. Ummi ta ce,"Yakamata ka tafi, dare ya fara yi Naseer, muna sauraronka."Yayi wawan ajiyar zuciya, ya mike da kyar ya ce da su,"Sai da safe,gaba daya suka amsa,"Allah ya kai mu, a gaida mutan gidan."Bai k'ara komai ba, ya sakko a hankali ya tafi.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Karfe 11 dare, ya shigo gida,. Zarah na zaune a falo ta ci uban tagumi, ya turo kofar ya shigo." Ta mike tsaye da sauri ta tarbe shi."
Yayana!
Kai kuwa ina ka shiga yau?
Bai tanka ba, ya wuce kujera ya zauna, ta bi shi hannun kujerar ita ma ta zauna. Ganin yayi zuru- zuru, yasa tausayinsa ya rufe ta.
Ta nunfasa ta ce,"Ina ka je yayana? Ya ce,"Kaduna na koma." Ya aka yi to? Ya mayar mata da abubuwan da Alhj ya ce,yayi shiru ta rasa ta cewa. Ya kwanto da kan sa bisa cinyoyinta, shi ma ya yi shirun Ta dafa kan sa ta ce,"Kai yanzu me ka shawarta."Ya ce,"Na hukara Zarah. Allah na gani na yi ikayar kokarina. Abinda ya fi damuna maganganun da Alhj yayi. Ba k'aramin dafa min jiki suka yi ba, sbd a zahiri Alhj masoyina ne.Sai kin ga yadda ya cika hotuna na a falonsa, kya rantse da Allah ni ne dan masu gidan.
Ni dai na yi abin kunya, ban san ta yadda zan yi in wanke kai na ba."
Ta ce,"Gaskiya ne, amma duk da haka ka tuntubi su Umma ka ji ko za ta ce wani abu." Ya mike ya wuce bayi, yayi wanka ya ji sanyi a jikin sa, sannan ya kwanta.
Zarah na k'ara kwantar masa da hankali.
Da safe ya shiga wajen su Umma ya gaishe su.
Abba bai amsa ba, ya tashi ya koma cikin daki.
Daga can yana jin duk bayayin da yake wa Umma.
Yana gamawa ta ce.
"To ne menene nawa a ciki? Duk abinda ka ga ya dace, ka yi, tunda wannan 'ya ba ta mu bace, k'arewa ma ka ce bata k'asar.
Ka ga da gaske Abbanta ya ke yi." Yayi dan jim kafin ya mike, ya bar falon.
Umma ta bi shi da kallo, tausayin sa ya dan kama ta, ta kada kai ta ce,"Kai ka jawo wa kan ka."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Sati 1 Naseer yayi yana sintiri Kaduna, wai ko ya sanmi sauyin baki daga Alh.Basheer, amma sam babu.
Yau daya je ma. Alhj cewa yayi yau ce rana ta karshe daya ba shi, idan bai kawo takardar ba, to kar ya sake zuwa gun sa, kuma duk abinda ya biyo baya, kar ya ce yayi masa wulakanci.
Babu yadda zai yi, a daren ya rubuta takarda, saki 1 ya sa a ambulan ya rufe.
Washe gari ya isa gida, ya sami Alhj yana shirin fita.Bayan sun gaisa Alhj, na kallo irin ramar da Naseer din yayi. Ummi ta zo suka gaisa. Yasa hannun aljihu ya ciro ambulan, ya tsugunna ya mika wa Alhj. Ya kar6a, ya buda, ya karanta, bai ko karasa ba, ya rufe saboda irin lausasan kalaman da ke cikin takardar.
Ya dube shi ya ce,"Magana ta kare Naseer, kuma duniya da lahira na yafe maka abinda ka yi min. Son ka a cikin jini na yake, na rantse da Allah ba zan iya cire shi ba, saboda haka ka saki jikin ka, kai da na ne.
Magana ta 2, ita ce,"Gida da motocin da na ba ka, mallakin ka ne, ba na bukatar su. Abinda na ke son ka da shi ne, ka dauki Zarah ku koma can da zama.
Wannan umurni ne a matsayin na Babanka."Gaba daya tsigar jikinsa suka tashi yar! Idanuwansa suka kawo kwalla.
Ya zamo daga kujera ya ce,"Na gode Abba. Allah ya saka da alkhairi."
Ya ce,"Koma ka zauna. Yanzu yaushe za ka kammala karatun ka? Ya sunkuyar da kai, kunya ta rufe shi, ya rasa me zai ce? Da kyar ya daure ya ce,"Ai dama ban fara ba."
Da mamakinsa ya maimaita ,"Ba ka fara ba? To da ka ce min ka na zuwa?
Ya sunkuyar da kai, kamar ya ratsa kujera ya shige. Alhj yayi dan murmushi ya ce,"Allah da iko yake, yanzu yaushe za ka fara? Kidimewa tasa ya ce,"Gobe." Ummi ta ce,"Gobo kuwa? Ba dai gobe- gobe ba, ai kuma sai an sake nema ko? Ko kuwa ka na da "(Admission) ne a hannun ka?
Ya girgiza kai,"A'a.Duk sun lura a daburce yake, saboda haka Alhj ya ce,"Shi ke nan, ka je ka yi duk abinda ya kamata, idan ka sami ( Admission) din ka kawo min." Ya ce,"To na gode Abba."
Ya kosa ya tashi saboda tsarguwa, zufa ce kawai ke kwararo masa cikin riga.
Yana samu aka sallame shi, jikin sa na rawa yayi godiya, ya fice.
Alhj ya dubi Ummi ya ce,"Kawai Allah ne ya dora min son yaron nan, ba don haka ba, inda na ke ma idan aka ce ya zo da kudi ba zai zo ba."
Ta ce,"Ya za'ayi, ga kuma zuri'a a tsakani, dole a rage wani abin." Ya numfasa yana kada ambulan, sannan ya mika mata,"Karanta ki ji bayanan dake ciki." Ta kar6a ta karanta, ta yi dan murmushi ta ce,"Allah sarki da alama ya saduda Alhj."
Ya ce,"Kyale ni da shi dai."
Ta ce,"Na kyale."
Kowa ya ji abinda Alhj yayi, sai ya sanya masa albarka.
A hakikanin gaskiya Alh.Basheer mutum ne wanda ba'a samun su a wannan zamanin, sai an shekara ana bincike cikin mutanen kirkin da ake wa zaton suna da halin mutan da can. Karshen soyayya Alh.Basheer ya nuna wa, Naseer shi yasa Naseer din ke k'ara nadama kan nadama, so da kaunar Nusaiba ke k'ara dabaibaye zuciyarsa.
Kewar ta ke jefa shi.
Nisan tunanin ta musamman lukutan daya samu a asibiti yana jinyarta.Ya kan rink'a ganin kamar wata sabuwar rayuwar soyayya ce suka yi a tsakanin su, wacce yake mafarkin ci gaba da irin ta.
Malam Balarabe kuwa kalaman godiya sun kare a bakin sa.
Washe gari daya tafi Kaduna, ba tare da sanin kowa ba, don nuna girmamawa ga Alh. Basheer. Tabbas ya nuna halin girman, dole a jinjina masa. Haka shi ma Alhjn ya roke shi akan ya daina fushi da Naseer, tunda ya tuba, to ya kamata ya karbi tuban sa, sbd fushin sa tamkar dafi ne a gare shi.
Malam Balarabe ya amince, yayi farin ciki ya kuma zubda kwallan bakin cikin rabuwar auran Naseer da Nusaiba.
Ba 6angaran su Malam Balarabe kadai bakin cikin rabuwan auran ya dama ba, ita kan ta uwar gayyar, yau ta tsinci kanta cikin wani yanayin da bata gane masa ba, a tun lokacin da sako ya zo mata ta waya daga Nijeriya cewar ta fara iddar ta.
Zaune take dirshan bisa gado, ta takure kanta, tunanin yayi mata yawa.
Tana tambayar kan ta, ita kuma haka Allah ya kaddaro mata? Mutuwar aure ita ce matsala ta farko da ke ci mata tuwo a kwarya, a rayuwarta.
Ta tsani, ace anyi aure ya mutu, sai ga shi yau ya tabbata akan ta.
"Kaddara!
Ta fada a ranta hawaye, suka kubce.
Ta dawo tana zargin kan ta,"Watakila Naseer ya so ya gaya mata wata magana lkcn da ta wayi gari ta gan shi tare da ita asibitin, amma ta ki ba shi dama.
Yi hakuri ki ba Bebinmu nono. Haba 'yar gidan Abba."
Tabbas rarrashin ta yake yi, amma ta dauke kai, ta nuna bata san abinda take yi ba.
Alhalin ta warke, hankalin ta ya dawo jikinta.
Da kenan amarya, amma, a yanzu ina mai tabbatar miki yayanmu yayi nadama, ko bai gaya min da bakin sa ba, ni na yi imanin yana son ki.
Ba ki ga yadda ya fita hayyacin sa ba.
Lokacin da lalura ta kama ki, kuma ya kula dake yadda ya kamata!
Ta toshe kunnuwanta ta daga kai.
Idanuwanta tamau a rintse, hawaye suka ci gaba da sauka.
Istaharar ta ta tabbata gaskiya.
Bata sami isashen barci ba, sbd a yanzu take tunanin ya kamata ace ta ba Naseer dama shi da ita sun yi magana.
Yanayin daya suka kwana ita da Naseer, domin a ranar suka koma Hanwa. Yayi sintiri a sashin ta iya yadda ya ishe shi, wanda a da bai ta6a shiga cikinsa ba. Tun Zarah na taya shi sintirin, har ta hakura ta sakar masa. Daga ranar ya daukar wa kan sa alkawarin zama lafiya da kowa, zuwa k'arshen rayuwarsa.
Idan ba shi gida, yana shagon dinki ne, daya samu Abba ya fara amsa gaisuwar sa, kuma bin sa yake sau da kafa.
Komai bai zartarwa sai abinda ya ce. Haka yake bin Alhj, bai ketare umurinin sa. A haka aka share watanin 2. Mamakin sa 1 shine. Alhj ya ki dawo da wasan Polo, shi kuma yana jin nauyin yi masa magana.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
A 'yan tsakanin ne. Fa'iza ta haihu da namiji k'aton gaske mai kama da Babansa. Ranar suna, ya rada masa Mohammad. Zarah gidan sunan ta wuni duk da ta wayi gari baya jin dadi.
Tun daga ranar jikinta ya k'i yi mata dadi,
tsoro ya fara kamata, sbd fargaba daukan ciki.
Lalurar ta ta fara bata tsoro.
Lalai kuwa, abinda take wa tsoron ne ya samu.
Shi kan sa Naseer tausayi take ba shi, shi yasa wannan karon murnar sa raggiya ce.
Zarah na tsakiyar laulayi, aka biya kudin jarrabawar (External)
Naseer ya biya duka WAEC da NECO.
Daga nan Sageer ya shawarce shi daya fada makarantun bada (Lesson), don ya k'ara wanke masa kwakwalwa.
Babu musu, ya nema ya shiga guda 2, yana zuwa.
Ranar da za'a kai Zarah daurin mahaifa, ranar ce suke da jarabawar farko. Hankalin Naseer ba'a kwance yake ba, babu yadda zai yi.
Haka nan ya hakura suka tafi tare da su.
Umma da Inna Sageer ya kai su a Jeep din sa.
Shi ya tafi jarabawar sa da Civic.A saukake yayi jarabawar sa, duk da ba shi cikin nutsuwa, babu tambayar da ta gagare shi amsawa.
Yana tashi ya wuce asibiti abin sa, ya duba Zaraha, sannan ya dawo shago yayi ayyukansa. Can yake zama su ci su yi hira, zuwa karfe 9 ya dawo gida.
Zaman sa shi kadai yana kara taso masa da kewar Nusaiba, a lkc irin wannan can baya, duk da ta san baya maraba da ita cikin dakin sa, ta kan shigo har ta tambaye shi ko yana da bukatar wani abu.
Shi yasa ya dauki filo ya nufi sashin ta cikin dakin barcinta, ya jefa pilo bisa kafet ya kwanta.
Nan ya kasance wajen barcinsa, kodayaushe, yana laluben inda zai ji motsinta.
Watannin 3 sakamakon jarabawarsa ta fito.
Allah da ikon sa gaba daya sakamakon Naseer masu kyau ne.
Yayi matukar sa'a.
Allah ya kubutar da shi daga sharrin hukumar jarabawa da yanzu abin yake neman zama kasuwanci.
Ko ma ince ya zama din."
Magidanci na fama da kansa, duk da haka ya dage da karma-karma ya biya zunzurutin kudi, sai jarabawa ta fito, ace yaro bai ci ba, alhali da kokarin sa da komai.
Sannan ya dage wajen neman taimakon makarantun (Lesson), tunda daman makarantun gwamnati sai a hankali.
Ba duka (Syllabus) ake (Covering) , ba, balle yaro ya san makamar jarabawarsa.
Allah ya sawwake.
Ilimi ya zama wahala ga 'ya'yanmu talakawa.Shi kam Naseer yayi sa'a kamar yadda Allah ya halicce shi, shi mai sa'a ne a rayuwarsa.
Da rawar jikinsa ya kai wa Alh. Basheer takardun ya gani.
Yayi murna kwarai, daga nan ya shiga neman makaranta, don samun (Admission).
Sageer na taimaka masa.
Ba jimawa ba, ya sami Poly ta hannun Sageer din, Babu kudin kirki a hannunsa a wannan 'yan tsakanin, sbd zaman Zarah a asibiti.
Ya zauna yana tunanin yadda za'ayi.
Ba tare daya takurawa kowa ba.
Abin mamaki yana zuwa Kaduna, ya nuna wa Alhj,("Admission) din, kamar yadda ya umurce shi, cewar da ya samu ya kawo masa ya gani.
Take nan ya ware dubu 50 ya ba shi, ya ce ya je yayi hidimar makaranta.
Allah mai iko.
Tun daga ofid har ya dawo gida, godiya yake wa Alhj cikin ransa.
Ya kawo wa Abbansa, suka sa albarka shi da Umma, balle Zarah da take jin tausayin sa, sbd hidimar da yake sha a asibiti, ga kuma makaranta ta kunno kai.
Lallai Alhj ba karamin taimako yayi ma su ba.
Ciki lafiya, ba ka lafiya, ya kama karatun sa a (Poly Computer Science) yake karantawa, kamar almara yake ganin abin.
Lokacin kuwa cikin Zarah ya shiga wata 7.
Zullumi ya ishi kowa, musamman ita mai dauke da cikin.
Kusan kullun da ciwon mara take kwana.
Bata dai yin magana ne kawai.
Saboda ciwon ba wai ya tsananta ba ne.
Sati 2 da fara karatunsa, abinda ake gudun ya faru.
Ta haifi da namiji.
Aka sanya shi a kwalba kwana 7. Ya ce ga garin ku nan kuma shi ya ci sunan Alhaji, watau Mohammad Basheeeeeeeeeeeeerrr­ rrrr!!!!!.......
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Labarin haihuwar Zarah har Jordan, amma da aka ce ya koma. Jikin Nusaiba yayi sanyi, ta dubi Ameer yana ta rarrafen sa, yayi k'atob gasket, dauki da nishi jajur, ga suma baka wulik! Kamar kan Babansa.
Tausayin Antinta ya kama ta, ta yi tagumi ta ce a ranta,"Allah sarki Antina." Ta numfasa, Ameer ya rarrafo gun ta, ya dafa ta ya mike, ta sa hannun ta dauke shi ta rungume.
Tabbas ta sani dole Naseer ya sa Ameer a ransa.
Ta k'ara matse shi jikin ta, tunanin ta wai ace Naseer ya tada k'ayar baya, dan sa yake so a ba shi. Abinda ba zai samu ba kenan, yadda ta shaku da Ameer.
Ai mai raba ta da shi, sai wanda ya bata shi. Ta yi dai yi masu addu'ar Allah ya ba su mai albarka."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
BAYAN SHEKARA DAYA
Shekara guda da rushe(DABAI RIBERS),sauran kolub-kolub din wasannin polo sai kawo wa Naseer takardun gayyata suke, suna neman ya koma kungiyoyinsu.
Gayyata har da Ghana, Kamaru, Benin Republic, da sauran kasashen makwafta, wadanda suka san Naseer, suka kuma san irin rawar daya taka a wasan tsern Polo.
Amma sam ya ki amsa kiransu, duk da ya san dumbin alkhairin da zai samu a can. Sam-sam zuciyarsa ta fita daga wasan Polo tunda Alh. Basheer ya bar harkar.Hakan ya gaya wa Yakubu ranar da ya same shi da wata takarda da ta zo ta hannun sa daga Sakkwato. Magana ta kawo magana, suna hira tsakanin Yakubun da Alhj.
Shi kuma yake ba shi labari.
Saboda haka Alh.Basheer ya kira Naseer yayi masa magana. Baya ketare umurinin Alhjn, amma wannan karon Naseer kad'a kai yai ya ce,"Abba karatuna ya fi min wannan wasan, kuma ban jin zan iya wasa da wani (Polo club) a halin yanzu.
Alhj ya bi shi da kallo, tsaf ya kasa ganeme yake nufi.
Yayi dan murmushi ya ce,"Shi kenan tunda ka kawo zancen karatu. Allah ya bada sa'a."Ya ce"Amin. Alh.Basheer ya dade yana nazarin maganganun Naseer kuma yana tausaya masa, domin ya saba da Polo.
Yana sha'awarsa, bugu da k'ari wasan Polo A JININSA YAKE.Abinda kuwa daka saba da shi zai yi wuya ya fice maka a rai, sai dole. Alhjn bai yanke hukunci ba, tukuna, amma yana nan yana nazari a kai.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Al'amarin Nusaiba kuwa a birnin Jordan, ba yabo, ba fallasa a yanayin jikinta. Ta kasa samun natsuwa a ranta, saboda yawan zancen aure da Antin Jordan ke yi mata, tunda Ameer yayi wayau sosai, yana gudun sa ko'ina gwanin sha'awa.
Kullum amsar ta ita ce bata da wani bazawari tsayayye ko a Nijeriya, balle kuma a nan Jordan da babu wanda ta sani kasancewar ba fita take yi ba.Idan ba (Shopping) ba tare da yaran gidan da Direba. Ta damu kwarai domin ba ta san dalilin da yasa Antin ta damu da yin sabon aurenna taba. Shekara 1 kacal da mutuwar auranta.
A yammacin yau (Shopping) din za su da yaran gidan.
Kowace ta shirya cikin dogayen kaya kala daban- daban.
Direba ya aje su katuwar (Super market) din da suke saba zuwa.
Suka shige kowa, yayi na sa wuri, yana neman abinda yake so.
Nusaiba na jaye da Ameer cikin kwandon Shopping din ta saka shi, don kar ya rink'a bata wahala, yana gudu, tana kamo shi.
Bata ko lura da mutumin dake tsaye 6angarn kayan abincin yara ba, sai da ta ji yana fad'in,"Ameer!
Haka ka yi girma?
Ta waigo da sauri ta dube shi.
Ibrahim ne ke wasa da habar Ameer.
Bai kalle ta ba, ya ci gaba da cewa,"Ka ba Husna kewa, kullum maganar ka take."
Ameer washe baki yake yana dariya.
Ita kuwa Nusaiba jikinta rawa ya dauka, ta tsura masa ido.
A hankali ya dago, ya dube ta yayi dan murmushi ya ce,"Hajiya Nusaiba."
Ta yi yake, tana fadin a ranta, "Ibrahim ko maye ne?Kafin ta ce ,"Ya ku ke? Ina su Husna da Mamanta? Ya ce,"Lafiya lau suke.
Amma ba ki da kirki? Ta gyara fuska,"Da aka yi me?
Shekara 1 ki na garin nan, ki kasa kawo mana ziyara, ba ki yi alkawari ba.
Sakin ta ce min ta ba ki (Phone Number), amma ba ki kira ba." Lambar ce ta 6ace. Ka gaida min Husna."
Ta fadi tana tura keken (Shopping) tana ci gaba da kiran yara,"Sumayya ina ku ke? Ku zo mu tafi!
Ya dan sauke numfashi, ya biyo ta a hankali.
Suka hadu da yaran a wata kwana,"Anti ba mu gama ba,"Inji babbar cikin su Sumayyah.
Dai-dai Ibrahim na tsayuwa wajen.
Ta ce,"Gaskiya ba zan jira ku ba, gobe Direba ya sake kawo ku." Yayi fit yasa masu baki,"Haba Anti, bai kamata ba, ki kyale su su gama."
Duk suka bi shi da kallo.
Ya juya kan sa,"Ga Sumayyah ko? Ke fa? Ya nuna mai bi mata, ta ce,"Khadija."
Ke fa? Ta ce,"Mahadiyya." Ya duka ya kamo 'yar kamar ,"Ke fa? Ta ce,"Zainab." Ya runtse ido ya ce"Wash! Uwa da magani. Sannu Husna.
Mahadiyya ta cafe,"Ba husna sunanta ba ZEE AFLAN! Ta kai mata duka, suka kwashe mata da dariya. Takaici ya ishi Nusaiba, ta tura keke ta yi gaba.Ta bar shi yana rabon fada, wa ya radawa uwa ta ZEE AFLAM? Lalai ba zai sha (Ice-cream) ba yau."Mahadiyya ta ce,"Ba ni bace. Anti Sumayyah ce."
Ya kada kai,"Ba ki kyauta ba.
To ku tsaya in tambaye ku, yaushe Anti Nusaiba ta zo nan? Sumayya ta ce,"Ta dade, tun Ameer na jariri." Baban Ameer yana nan garin ne? Ta ce,"A'a yana Nijeriya." Wai ko ba za ku zo mu tafi ba ne?
Yau na ga yara.
Nusaiba ta leko tana kiran su.
Sumayya ta wuce da saurarinta. Khadija ta biyo bayanta. Ya kamo hannayen su. Zainab tana tambayar sa,"Kai ya sunan ka? Ya dube ta ya ce,"Suna na mai son Anti."
Suka kwashe da dariya,"Wannan suna, ban ta6a jin irin sa ba."
Inji Mahadiyya,"Ya ce,"Ga shi yau kin ji. Ko a gida aka tambaye ki, ki ce mai son Anti, sunana."
Ta ce,"To."
Ya debo kwalayen cakulet 2 da biskit 2, ya mika ma su. Suka yi godiya.
Wajen biyan kudi, suka same su, duk cin maganin Nusaiba sai da Ibrahim ya biya kudin.
Suka shiga mota, yana tsaye yana tunanin ta yaya zai binciko gaskiyar lamarin? Sun bada baya kadan, ya manta bai ma tambayi inda gidan su yake ba.
Ya zabura da sauri, ya fada motar shi, ya bi bayan su.
A haka a hankali yake bin su.
Nusaiba na jin Mahadiyya na tambayar su,"Kun san sunan mutumin nan? "Wai mai son Anti."
Gabanta ya fadi, ta zaro ido.
Sumayya ta ce,"Ah lallai ma wannan.
Antin Nusaiba, wai kin san shi ne? Ta ce,"Ina fa na shan shi, ku da ganin mutum kun tsaya ku na surutu da shi." Ta ce,"Anti ba ki san shi ba, shine ya san sunan ki da na Ameer? Ta ce,"To saura in ji maganar a bakin Anti, sai na murje bakin yarinya." Sumayayya ta kwa6e fuska, ta dubi 'yan uwanta, suka kama dariya,
suna toshe baki.A haka suka iso gida, yana biye da su. Yana kallo suka shiga get, yana kallo duk suka wuce cikin gida.
Farin cikin ya kama shi, domin ya san mai gidan.
Injiniya Ahmad Kaita.
Abokin ogan sa ne a ofis, kuma yana aiki da (Internet Global Services Jordan) ne."
Suna da manya rassa a Potugal, Iraq, Swedan,. Hedikwatarsu na birnin New-York. Hamdala yayi, sannan yayi ribas ya koma, farin cikin zuciyar sa ya dawo sabo ful!
Washe gari karfe 9, yana (Internet Globar Services). Ofishin Injinya Ahamd Kaita.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------ a
Bai sha wahalar ganin sa ba, saboda dama sun saba gaisawa idan ya zo wajen ogan sa.
Bayan sun gaisa, yayi masa bayanin abinda ke tafe da shi. Nan take dadi ya kama Injiniya, domin ya san Ibrahim mutumin kirki ne, ogansa ma na yabon sa.
Nan take yayi maraba da shi, ya kuma ba shi kati, ya ce idan ya zo ya kira wannan lambar.
Yayi godiya, ya fito.
Ofishinsu ya wuce yana mai murna da farin ciki, babu abinda yake hangowa, sai an daura auran sa da Nusaiba.
Wai! Yaya zai ji ranat? Yayi sauri ya dafe kirji, dadi zai kashe shi.
Injiniya na koma wa gidan kan sa ya kira Nusaiba, ya gaya mata anjima za ta yi bako, kuma yana rokon ta, don Allah ta ba shi hadin kai, domin mutumin kirki ne.
Ta amsa da to.
Ta koma dakin ta, ta yi iya tunanin ta, amma ta kasa gano mai neman dama mata lissafi. Su Sumayya da sun rantse sun maya ba su gayaea Ibrahim gidan su ba, balle ya san mai gidan.
To ko hadin Injiniya ne? Ta tambayi kan ta. Ta runtse ido takaicin duniya ya isheta.Dan ta karami, an dame ta da maganar aure.
Ita kuma ba shine a gaban ta ba, tana son isashen lokaci, don kula da dan ta.
Ta sallaci isha'i. Bayan cin abinci.
Wankan ma ta ki yi, balle ta gyara jikinta.
Yadda take tun safe, haka take zaune tana tana jiran ta ga dan rigimar dake neman auranta.
Bata gama tunanin ta ba.
Zainab ta zo da gudu ta gaya mata sako, inji Abbanta.
Ta kura wa Ameer ido dake barci, sannan ta wuce ta fito.
Zuwa karamin falo, inda aka ce bakon yake.
Kai,"Inna-lillahi"Wa-Inna-ilahir-raji'un!
Haka ta fada lkcn da ta yi ido 4 da Ibrahim.
Ya ce,"Dole ki yi salati, kin ga mayaeb zai cinye ki."
Ta ce,"Saboda Allah menene na bn diddigi? Ya girgiza kai,"Ba ki ma sani ba?
Lallai yau ne na gane cewa da hadin bakin ki Abba ya hana ni auran ki."
Ta dan yamutsa fuska,"Allah ne,Abba bai isa ya hana ka ba."
Kin di ni baki Nusaiba, kuma hakan yana k'ara min son ki.
Wannan karon da alamun nasara, ki dubi tsawon tazarar dake tsakanin Najeriya da Jordan, amma Allah ya ce je ki Nusaiba mijin ki na can." Ta yi dan murmushi, ta rasa me za ta ce da shi."
Ba karamin dadi murmushi ta yasa shi ba.
Ya dan langwabar da kai, ya sake fadin,"Kamar an fama min gyambo Nusaiba, tun ranar da na sake ganin ki tare da Sakina, kodayaushe sai mun yi hirar Ameer ni da Husna, shi yasa har yanzu bata mance da shi ba.
Da gangan ki ka batar da lambar da Sakina ta ba ki, saboda ba kya son in san komai game da ke?
Ta ce,"Tabbas haka ne, na kuma kar6i lambar ta ne kafin in san ko ita wace ce, da na zo na sani, sai na kiyayi kai na, saboda tunanin me zai je ya dawo?
Ya jinjina kai,"Kin yi gaskiya, amma da yake Ibrahim mai sa'a ne sai ga shi abinda ya je, ya dawo din.
Ko ba haka ba? Saura a ban dama, ayi ta ta kare"
Ta ce,"Yaro na karami ne, ban ko yaye shi ba, da dai............
Ya katse ta,"Ki na nufin Ameer? Je ki ji yadda yayi suna a gida na, balle kuma ki kawo min shi, gaba daya zai zama da na.Ta ce,"Ban tsara masa hakan ba."
Ko?
Ta ce,"Tabbas."
Yayi dan shiru, kafin ya ce,"Ba kya so na dai ke nan."
Ta ce,"Ban fad'a ba."
Ya ce,"Idan ba haka ba,"Ameer ne kawai zai hana ki k'i aure na? Ta nisa kafin ta ce,"Har da matarka, domin na lura Sakina na son ka da yawa, bai kamata in shiga tsakanin ku ba.
Mun yi hira sosai da ita a jirgi, amma ka na zuwa, ka nuna mata ka sanni, shi ke nan ta sauya min fuska.
Ka ji dalilin yaga lambar da ta bani, don ba na son tashin hankali."
Hankalinsa ya tashi kwarai, ya ce,"Ba ki fahimce ta ba ne Nusaiba.......
Ta ce,"Haka ne Wallahi, ai ka ga lokacin ba ta ma san halin da na ke ciki ba.
Ta ganni da Bebi, ba ita ba, kai kan ka ka yi zaton ina gidan mijina.
Quite O.K a lokacin ba mu rabu ba, sai daga baya.
To ina ga ace ga shi za ka aure ni?
"Babu abinda zai faru. Haka Sakina take, bata iya rufe kishin ta, amma bata da fada, idan ku ka fahime juna za ki gane tana da hakuri."
Ta ce,"Na ji."
In turo kenan?
"Ai na gaya maka ba yanzu na shirya yin aure ba."
Ya runtse ido, dafe da goshi ya ce,"Nusaiba ba kya so na.
Please!
Ki je ki yi shawara, abinda ki ke fadi ba hujja bace."
Ya bata tausayi kwarai, amma gaskiya ba za ta iya aure yanzu ba, shi yasa haka suka tashi hirar babu fahimtar juna, kowannan su ya koma cike da tunani.Musamman Ibrahim da yake ganin Nusaiba na son ta yi wasa da rayuwarsa, bayan ya lashi takobin wannan karon, sai ya ga abinda zai ture wa buzu nadi."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Abubuwa da dama suke damun Nusaiba, ta kan ji kamar ta tsero ta bar k'asar, domin Injiniya da Antina sun tasa ta gaba, akan zancan Ibrahim, kamar yadda shi kan sa ya addabe ta da zuwa.
A hak'ik'anin gaskiya tana tunanin Istaharar ta, kuma tana aji a jikin ta akwai maganar da Naseer yake son gaya mata, dama ce kai bata ba shi ba.
A wannan gwagwarmayar suka shafe shekarar har ta yaye Ameer, yana neman wata 6 da yaye.
Ibrahim bai hakura ba, ita kuma bata sakar masa ba.
Anti kam har ta yi fushi ta daina yi mata magana, kamar yadda Injiniya ya sa ido, abinda ya sa a ransa shine wata kila Ibrahim din ne bata so.
Shi kuwa Ibrahim har su Husna ya kwaso ya kawo mata tabbacin cewa Sakina ta sani kenan.
Wannan bai dami Nusaiba ba, domin bata san irin bala in da ya sha a gida ba, akan hakan.
Ta fara riga ta ga duniya, babu wata yaudar da Da namiji zai nuna mata.
Idan gaskiya ne, ya ce zai kai ta gun Sakinar mana?
Bai ta6a gigi ba, sai dai ya kwaso mata su Husna.
Kwatsam! Sai ga Alh. Basheer a Jordan, ba zato ba tsammani. Kai murna a wajen Nusaiba, kamar ta zuba ruka k'asa ta sha.Tana kewar sa sosai, tunda ya zo take like da shi.
Shi kuwa Ameer ke zuciyar sa, ji yake kamar in zai koma ya wuce da shi, ya zauna gidan sa.
Yaron yayi saurin girma kamar ba dan shekara 2 da watanni ba.
Suna zaune dare ya fara yi ga Injiniya ga Antinta.
"Alhaji ya tambaya,"Wai 'yar gidan ta ku bata fidda wani ba? Jin haka yasa Nusaiba ta tashi ta bar falon.
Injiniya ya ce,"Ai mu Nusaiba ba mu san inda ta dosa ba."
Kamar yaya?
Ya ce,"Wani yaro ke son ta kamar zai yi hauka,
amma ba ka ga yadda take wahalar da shi ba.
Ni Wallahi tausayi yake ba ni.
Yana da mata da 'ya'ya'yen sa 3.
Ibrahim sunansa, yana aiki da (Nijeriyan Embasy) , yaro mai hankali, amma ta ki ba shi goyon baya."
Ya ce,"Ibrahim?
Ni kuwa kamar na san sunan nan?
Anya kuwa ba yaron nan ba ne daya so auran ta da?
Fatima ta ce,"Oho,"Nusaiba wani bayani za ta zauna ta yi.
Yarinya da ka fara magana, sai kuka.
Ni dai yara suke gaya min wai a (Super market) suka hadu, amma sun ga kamar dama can ya san ta.
Ya ce,"Lalai Ibrahim din da na ke magana ne.
Kuma da akwai alamun tana son sa, ni ne na cusa mata Zancen Naseer.
To me yasa yanzu ba za ta aure shi ba?
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

---------------------------------------------------------------------------------------------- Zaharaddeen shomar Whatsapp 08168575100 Ajinisa Yake3-05 Posted by ANaM Dorayi on 11:43 AM, 25-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Ta ce,"Ba zai wuce wannan yaron da ta kwallafawa rai ba. Ta shaku da Ameer ko alama bata son a raba su. Ameer kuwa dole ya koma gidan ubansa, sanin kan ta ne ba zai kyale mata shi ba. Alh. Basheer yayi shiru, Injiniya ke fadin,"Nusaiba manya, abubuwanta dariya suke ban, na ga yadda za'ayi wannan al'amari." Alh. Ya ce,"Ku kyale ta, zan yi maganin abin."Suka saki wannan shafin, suka kama wani, dare yayi Alhj ya tafi masaukin sa. Yana tunani tare ba tare da yayi wa Nusaiba maganar Ibrham ba. Koda dama bisa hanya yake, harkokinsa ne, suka kawo shi, hanya ta ratso da shi nan. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Yana zaune cikin ofis a gida Nijeriya, misalin 11 rana. Naseer yayi sallama ya shigo. Ya amsa,"Lafiya lau. Ya jikin na Zarah? Ya ce,"An gode Allah. Wannan karon dai Likita ya ce dole ta huta daga wannan, saboda mahaifar ta ta yi rauni da yawa. Ya dan kada kai,"Ayya, gaskiya ya kamata ta huta, saboda lafiyar ta, ayi hakuri da abinda Allah ya kaddaro." Ya ce,"Haka ne. Dama tun jiya na zo in nuna maka Result. Ya fito na kammala Diploma." Ya washe baki,"Ah! Lallai abin ba wuya a wurin Allah." Yasa hannu ya kar6i takardu, ya duba,"Kai! First class! Gaskiya takardun sun yi kyau. Yana 'yar dariya ya shafi keya, ya ce,"Sun ba ni (Adimission ABU), Direct. Next month za'a fara Rigistireshon. Alhj ya miko masa hannu,"Congrat! Kai na ji dadi., Allah ya bada sa'a." Amin." Ya fadi bakin sa ya ki rufuwa, ganin yadda Alhj ke murna. Ya mike yana fadin,"Zan koma Abba, na gaishe ka." Ya ce,"To na gode. Zan tura ma da sako(Acconut) din ka, ba yawa, sai ayi Rijistireshon ko? Ya tsugunna yayi godiya.Alhjn ya jawo dirowa, ya dauko farar ambulan ya mika masa,"Wannan ma sakon ka ne." Cikin mamaki yasa hannu ya kar6a ya kara godiya ya fice. Yana shiga mota da rawar jiki, ya buda ambulan, don ganin me ke cikin su? Wasu zaradan hotunan Ameer, ya rinka zarowa daya bayan daya guda 24 kala-kala. Wasu tun yana dan wata 4 a zaune, wasu yana rarrafe, da yawa a tsaye yake. Ya zura wa hotuna ido, kamar ya sume, saboda doki da farin ciki. Ya sumbata, ya rungume ya ma rasa inda zai aje su. Take nan ya kira wayar Zarah,"Kin ga yadda Ameer dina yayi girma? Ta ce,"A ina ka gan shi? Hotunansa Abba ya zo min da shu, sai kin ga yaron Zarah, kamar dan larabawa." Ta ce,"Ka na ta sa min rai, yayana ka kawo min in gani mana." Ya ce,"Ki jira, yanzu zan baro Kaduna." Ta ce,"Allah ya tsare." Ya ce,"Amin. Ya kashe waya. Ya bi hoton hannun sa da kallo, can ya sauke numfashi, ya sake sumbatar sa, sannan yayi wa mota key, ya ya wuce. Yana isa Zariya. Su Umma ya fara kai wa hotuna suka gani. Umma ta dauki daya. Ya kai wa Inna ita ma ta za6i na ta. Daga nan ya cilla Shika ya kai wa Zarah. Wai ta ga hotuna kamar ta dauko Ameer yayi motsi a gaban su. Nan ya bar mata 2. Fitowar sa asibiti a hanya ya shiga shagon sai da (Gift) da (Frem) na sa Hotuna ya siyo kanana guda 24. Gaba daya hotunan sai da ya sa su cikin frem har da na wajen su Umma da Inna. Sageer an ba shi. Yakubu ma, ya samu har da dakin Hajiyar sa.Naseer B ma ya ce yana so a ba shi. Naseer kamar zai hauka ce, saboda son Ameer. Bayan kwana 2 daya koma Kaduna. Haka ya ga hoton bisa tebur din Alhj gaba dayan firem din mai kyan gaske. Ba k'aramin dadi ya ji ba. Shi yasa ya k'ara kaimi wajen addu'ar sa. Allah ya dai-daita auran sa da Nusaibansa. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sati 3 tsakani, cikin Zarah ya k'i zama, wannan karon ko wata 7 bai kai ba, watan sa 6. Dole aka bi shawarar Likitan nan take aka juya mata mahaifa, don ta huta da wahala, domin ba k'aramar wuya take ci ba kafin ta haihu, ban da jinin da take zubdawa. Yaya za ta yi? Haka Allah ya kaddaro. Ubangiji yasa kaffara ce. Bayan ta gagije, lafiya ta zauna mata sai Naseer ya neman mata F.C.E. Ta samu a saukake, shi ya gama mata komai ta fara karatu. English/Islamic. Asabar da lahadi ya fita da ita koyon mota, tun tana tsoro har ta kware. Cikin sati na 3, ita ke kai kan ta makaranta. Shi ke nan ya sakar mata (Honda Civic) din sa. Shi yana amfani da Jeep kawai. Kasancewar Sageer zai tafi sabis din sa bana, sai shagon dinkin sa yayi rauni. Ba sosai yake zama ba, su Abbas ne kula masa da shi. Idan ya taso makaranta yake zama ko ranakun da babu karatu. Kusan ace hankalin Naseer kwance yake, amma Allah kadai yasan abinda ke damunsa a dangane da son dawowa da Nusaiba gidan sa.Ba shi da bakin magana ne kawai, ko kuma mu ce babu wanda zai kai wa kukan sa balle a share masa hawaye. Shi yasa wani lokacin za ka gan shi a rame, wani lokacin kuma babu laifi. Bayan wata 2 da dawowar Alh. Basheer Jordan yana ta binciken halin da Nusaiba suke ciki da Ibrahim. Babu wani sauyi, kodayaushe nuna masa take ba za ta aure shi ba, shine dai ya k'i hak'ura. Jin haka yasa Alh.Basheer ya ce maza-maza ta dawo gida Nijeriya ta yi aure anan. Ta shiga shirin kaya, cikin bak'in ciki da 6acin rai har ta rink'a jin kamar ta cewa Ibrahim ya fito, don ta san tabbas Ibrahim na tsananin sonta. Amma da ta tuna abinda Sakina ta yi mata a filin jirgi, sai ta yi turus! A tunanin ta da kyar Sakina za ta bar ta sakewa gidan Ibrahim. Saboda haka ta watsar da maganar Ibrahim, ta ci gaba da shirinta ko gaya masa bata yi ba. Ana gobe za ta dawo. Alh. Basheer ya kira Naseer ya same shi a ofis. Yana zaune, yayi shiru yana jiran ya ji dalilin kiransa. Alhj ya dan gyara fuska ya ce,"Gobe Nusaiba za ta dawo maka da Ameer, saboda ta sami miji za ta yi aure. Shine nace zan gaya maka, idan sun iso, ka zo ka kar6i abin ka, ka sa shi makaranta, tunda da bakin sa. K'iris ya rage ba'a zare ran Naseer ba, daga inda yake zaune, domin ilahirin kwakwalwarsa sa ta daina aiki.Yayi zugudun, kai sunkuye, bai motsa ba, balle ya ce wani abu. Alh. Basheer ya zura masa ido, jim kafin ya sake fadin. "Ka na iya tafiya, dama shi kenan sak'on, da zarar sun iso, zan kira ka a waya." Ya dago ya dube shi, ido cike da kwalla, sun kada jajur, bakin sa dauke da magana, sai dai ya kasa furtawa, sai ya ce to kawai. Da kyar ya mike ya nufi kofa. Alhj ya bi shi da kallo. Goge hawaye yake da bayan hannu. Yasa kofa zai buda. Alhajin ya kira shi. Ya waigo a gigice, yana amsawa. Yayi jim kafin ya ce,"Don Allah ka gaida min Malama Balarabe da kyau." Ya hadiye miyau, ya ce,"Zai ji Insha-Allahu." Ya buda, kofa ya fice. Ya shigo gida karfe 7 na magariba. Kwanciya yayi a dakin sa ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Zarah ta yi tambayar duniya, ya kyale ta. Ta yi mita har ta gaji, bata samu wata amsa ba, duk ranta yayi mata k'unci. Cikin dare ta farka, ba shi cikin dakin." Ta fito ta biyo shi, yana falo zaune cikin duhu, sai da ta kunna fitila sannan ta gan shi. Ta matsa gaban sa ta ce,"Ikon Allah, watau yayana she akwai wani lokaci da zai zo, wanda ba dole ba ne in san me ke damunka? Gaskiya ne.............. Ya katse ta,"Zarah ba wata magana bace. Ameer ne za'a dawo min da shi. Nusaiba za ta yi aure." Ta numfasa ta koma dirshan ta zauna kafin ta ce,"Amma yaya ka na da abin mamaki. Nusaiba za ta yi aure, ba dole ta dawo maka da danka ba? Menene abin damuwa a nan? Yayi mata wani mugun kallon da bai ta6a yi mata irin sa ba, ya ce "Babu! Rok'ona gun ki shi ne ki koma ki sha barcin ki. Please and Please!Ta bi shi da kallo, bata ma san me ke bata mamaki ba. Ta buda baki za ta yi magana, ya kwarara mata tsawa,"Ki tashi na ce ko? Ban son jin komai nace! Idanuwanta suka cika da hawaye, ta tashi da gudu ta nufi. Sashin ta kuka kala-kala ta rink'a yi, kamar yadda tunanin ta yake kala-kala. Lallai son Nusaiba ya zauna masa, ko kuwa don yana ganin ita bata aje masa da ba ne, shi yasa ya fara yi mata kwakwazo? To ai daga Allah ne, kuma bata bakin cikin soyayyar sa da Nusaiba. Me yasa zai juya mata baya yau? Kafin safiya, idanuwanta sun kunbura. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Naseer na kallon ta, tana shirin tafiya makaranta. Ransa ya k'ara 6aci. Tana ta wanke- wanke a kicin ya biyo ta, bayan ta ya rungume, ya sumbace ta, ya rada mata,"I'm sorry. Jini na ne ya hau, kar ki yi fushi da ni sweet Zarah." Ta runtse ido, hawaye suka zubo, ya juyo ta ya share su." Ya isa haka, ai ya wuce ko? La66anta na rawa ta ce,"Yayana ba na bakin ciki. Ko ka fara son Nusaiba, kuma ina maku murna idan da za'a ce gidan nan za ta dawo. Amma menene na yi min ihu saboda na fadi gaskiya? Saboda ban aje maka da ba ko? Nan da nan idanuwan sa suka kada,"Kin san abinda ki ke fadi kuwa Zarah? Kin maida ni jahili kenan, ban san Allah ba? Ya juya mata baya, ban ta6a zaton wannan maganar ba daga gare ki Zarah."Take nan ta amsa laifinta, sai dai ka fin ta mik'a hannu, ta kamo na sa, yayi waje ya bar kicin din. Tana kokarin biyo shi, ta ji tashin motar sa. Tana fitowa wajen Mai gadi na rufe get, ya riga ya fice. Ta koma falo ta zauna, tana mai nadamar furucin ta. Daga ita har Naseer babu wanda ya fahimci karatun ranar. Shi kam Naseer caji 2 ke kan sa, shi yasa ya kashe wayayinsa, baya son magana da kowa. Bai dawo gida ba sai bayan issha, yana shigowa falo, ya ji ta a jikinsa, kiris ya rage ta kada shi. Mafarin daya rike ta sosai kenan. Ta ce,"Yayana na tuba. Allah na tuba ba zan sake ba." Yayi ajiyar zuciya mai karfi, ya kamo hannunta, suka zauna. Ya dube ta ya ce,"Magana makamanciyar wannan kar ki sake min ita, idan ki na son farin ciki na a duniya." Ta kama kunuwanta 2, ta ce,"Ba zan sake ba yayana." Ya jawo kafadar ta, ta kwanto masa,"Ya wuce, shi kenan." Ta ce,"To yaya su Nusaiba, sun iso? Ya ce,"Ni wayoyina ma kulle suke tun safe, ba na son ya kira ni, so ban san halin da suke ciki ba." Ta ce,"Hakuri za ka yi yayana, su gani suke har yanzu ba ka son ta ne." Yayi shiru ya rasa me zai ce? Ta dan dube shi. "Zo mu ci abinci ko? Ya ja hancin ta, ya ce,"Sure." Suka tashi suka nufi tebur don cin abinci."A dai- dai wannan lokaci Alh.Basheer da Nusaiba tare da Ameer suka shigo gida. Alhj ya dauko su daga filin jirgi. Ummi ta tar6e su, murna kamar su lashe juna. Duk da Ameer bai santa ba, ya saki jikinsa da ita sosai. Da yake shi ba mai bakunta ba ne. Bayan sun ci abinci, an yi masa wanka yai barci, ita ma ta kintsa, ta tafi kiran Abbanta, yana falonsa kwance labarai yake kallo. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Tana shigowa ya tashi zaune yana fadin,"Zo nan 'yar albarka." Tana murmushi ta zo gun sa ta zauna. Ya ce,"Yauwa. Magana za mu yi. Kin tuna alkawarin da ki kai min a asibiti? Ta dube shi,"Wane alkawari Abba? Ya ce,"Lokacin da rigamar auran ki da Naseer ta taso. Ina ganin laifina ne, amma ki ka ce a'a, kuma ko nan gaba na sake za6a miki wani mijin, za ki aure shi. Kin tuna? Ta kada kai, ta ce,"Na tuna Abba." To za ki iya ciki min shi? Ta dan yi shiru, kafin ta ce,"Zan cika Abba na, umurnin ka kawai na ke jira." Ya rungumo kafadar ta ya ce,"Allah yayi miki albarka. Kafin nan na riga na gaya wa Naseer za ki dawo masa da Ameer. So kafin ya zo, ki tsaya ki duba wannan takardar, wasika ce daga mijin da na sami miki." Ina fatan za ki aje hankalin ki waje daya." Ya sa hannu kasan filon kujera ya dauko amblun, ya mika mata ta amsa jiki ba kwari. Tashi ki je ki karanta, ki yi nazari akai, kafin Allah ya kai mu gobe inji ta bakin ki." Ta mike ta wuce babu wani ishashen kuzari a jikinta. Ameer ta tsurawa ido, ta fashe da kuka. Shi ke nan za'a raba ta da shi. Rayuwa kenan, abinda ya kamata ita da Babansa su ba shi tarbiyar da ta tace Hakan ba zai samu ba ko? Ta tambayi kanta, gocewa ta sake yi da kuka. Can wata zuciya ta ce,"Ba ga Antin ki ba? Ai za ta iya rike miki shi tsakani da Allah. Ta goge hawaye, ta ce,"Haka ne. Na san Antina za ta iya." Ta ci gaba da share hawayen, tana ajiyar zuciya. Ta dauko ambulan din dake gefe ta jujjuya ta, sannan ta farke ta, ta warware ta fara karantawa, "Gaisuwa irin ta addinin Islama. Kafin na ce dake komai, ina mai neman gafarar tarin laifin da na yi miki. Da ace ki na cikin hankalin ki a lokacin da na ke tare da ke a asibiti. Da kin tabbatar da cewa na tuba, na kuma fad'a cikin kaunar ki, son ki ya kama ni, a lokacin da zaman mu tare ya zo k'arshe. SAKI DAYA na yi miki ya ke ma'abociyar hakuri. Amma ki sani, a duk bagun numfashin da zuciya ta za ta yi a duniya, tare da bikon soyayyarki. Da ace zan sake samun wata dama ta auran ki, na yi rantsuwa da wanda ya halicce ni, zan nuna miki za6i na gari Abba yayi miki. A karshe ina addu'ar Allah ya raya mana Ameer, rayuwa mai kyau cikin addinin musulunci. Mai son kiNaseer Iliyas Balarabe! Bata gaskanta idon ta ba, balle ta yarda da abinda ta gani a rubuce. Ta sake maimaitawa. Ta tsaya kasake tana sauke Numfashi. Me ke cikin ranta wanda bata tantance shi ba? Kamar farin ciki ne ya kamata, to me yasa hawaye ke neman kubcewa? ----------------------------------------------------------------------------------------------- Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Gaba daya ta kidime. Ta sake duba takardar bisa sunan mai ita Naseer Iliyas Balarabe! Ta cicci6o Ameer ta rungume shi tana fadin,"Tare za mu koma gidan Babanka! Allah na yafe masa! Da kyar ta sami barcin kirki. Da safe ta tafi gaida Alhjn, tun daga fuskarta ya shaida tana cikin walwala, ba kamar dawowar ta jiya ba. Bayan sun gaisa, ya ce,"Kin ga sak'on? Ta amsa da kai, tana d'an murmushi. Ya dan dago habarta, ya ce,"To yaya? Ya fito bazawarin? Ta fado jikin sa ta kudundune fuska,"Kai Abba! Ya fasje da dariya,"Shi ke nan, na bari, to tashi ki ji." Ta mike ya ce,"Na san anjima zai zo, sai da ba shi da labarin komai, illa Ameer da zai dauka. Za'a ci kwalliya ko? Ta tashi da gudu, ta bar dakin. Ya kama dariya yana kwanciya bisa kujera,"Bebin Abba kenan 'yar albarka.," Karfe 9 da rabi Naseer ya iso gidan su, don gaida iyayen sa kamar yadda ya saba duk ranar asabar da lahadi. Yana shigowa. Malam Balarabe ya hau fada,"Kai menene dalilin kulle wayoyin ka. Alh.Basheer na ta neman ka tun jiya, bai same ka ba? Ya ce,"Uhm.............Ba su da caji ne. Ya ce,"Amma kai k'aryar ka ko hanyar masallaci bata sani ba Idan babu Nepa, ba akwai jenareto ba? Yayi shiru." Watau abin zai dawo ko? Da sauri ya ce,"A'a Abba! Ya ce,"To mike maza! Yana neman ka." Ya mike yana fadin,"Sai na dawo. "Umma ce kadai ta amsa mashi. Ya wuce babu kuzari. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sha daya yana ofis din Alhj ko zama bai yi ba, yace ya ke can gida ya dauke shi, an riga an gama kimtsa kayansa. Tafe yake kawai, amma ko alama baya son ganin Nusaiba, kar kwadayin dawo da ita ya taso masa. A haka ya iso. Yayi ta maza yayi sallama falon. Ummi ke zaune a falon ta yi masa sannu da zuwa, ya tsugunna ya gaishe ta. Ta kira Mariya, ta ce ta kira Nusaiba, ita kuma ta haye sama abin ta. Yayi zuru a zaune kirjinsa na duka. Mariya ta kawo masa tiran kayan motsa baki. Bai ta6a komai ba, wani lafiyayyen kamshi ya doki hancinsa. Ya ware ido saitin kofa. Zuwa can Nusaiba ta ratso rike da hannun. Ameer. Ya zura masa ido, ashe ma kadan ya gani, kyan Ameer a hoto. Jikin sa ya dauki rawa. Nusaiba ta daki zuciyar sa sosai. Bai daina kallon su ba har suka iso tsakar falon, tayi masa sannu da zuwa. Baki sake ya amsa. Ta zauna ta dubi Ameer ta ce,"Ga Abba." Ya kura mata ido ya ce,"Abba? Ta yi dan murmushi,"Babanka ne, je ka." Ta tura shi ya nufo Naseer. Mikewa yayi ya tarbe shi, ya rungume, "Oyoyo Abba na! Ya jima da shi a kirjin sa, kafin suka zauna, ya dora shi bisa cinyoyinsa, suka bi juna da kallo. Ya ce,"Ka sanni? Ya girgiza kai. Ya ce,"Baba ne. Ka ce Baba inji? Ya ce,"Baba." Ya sumbace shi a dukkan kuncin sa. Sannan ya dubi Nusaiba, suka hada ido, yayi dan murmushi, ya ce,"Kun dawo lafiya? Ta ce,"Lafiya lau, ya su Antina da su Umma? Ya ce,"Lafiyar su lau, sun ce a gaishe ki." Ta ce,"Ina amsawa." Suka yi shiru na dan lokaci, kafin suka sake kallon juna. Kowa yayi murmushi, ya dauke ido. Naseer ya kama yatsun Ameer ya hau kadawa, ya rasa abinda zai ce. Ameer ne ya katse shirun,"Baba, wai tare za mu tafi? Ya tallafo kuncin sa ya ce,"A'a za ka zauna tare da Mama tukuna ko? Ka na so? Ya kada kai,"Ni zan bi ka." Ya kwanto jikin sa ya lafe. Ya k'ara rungume shi, ya dubi Nuasaiba, murmushi kawai take yi kafin ta ce,"Yaro ya san gaskiya." Ya ce,"Wace gaskiya? Ai kyan sa ya zauna tare da ke in rink'a zuwa ina ganin sa." Ta ce,"A gidan wani? Ya 6ata fuska ya ce,"Anan gidan na ke nufi, idan son samu ne, mu kasance yana ganin mu tare kowane lokaci, shi zai taimaka ya san mu ne iyayen sa. Ta dan kada kai,"To ai kuma ba zama na zo yi ba gidan. Matsalar kenan." Ya sauke numfashi yayi shiru, ba don shi da abin fadi ba. Ta ci gaba da cewa,"Yanzu za ku tafi a fito da kayayyakin?? Ya dan kalle ta, kin kosa ne mu tafi? Ban ce ba, ayi hakuri." Haka hirar ta ci gaba su kamo nan, su kamo can, alamun babu natsuwa a tattare da Naseer. Sun sami awa 2 tare. Ya kwaso kayan Ameer ya taho da shi, hankalin sa tashe. A Zariya kowa na murnar ganin Ameer, shi ta shi ragaggiya ce, sbd zullumin sun kusa rabuwa da Nusaiba kwata-kwata sai wata k'addara za ta hado su Shi yasa kodayaushe yana Kaduna tare da Ameer wai yana kawo mata shi ne ta gan shi. Dariya take yi, ta ce ta gode." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sati 2 suka wuce Naseer na lilo tsakanin Kaduna da Zariya. A yau da la'asar ya isa bayan barin sa makaranta ya sa Ameer a mota suka zo. Suna tare da Nusaiba a waje suna shan iska. Alh.Basheer ya dawo, Naseer ya nufe shi suka gaisa daga nan Alhjn ya ce,"Yauwa tunda ga ka, shi kenan sai ka kai wa Malam Balarabe katin daurin auran Kanwar ta ka, wani satin." Naseer ya dask'are nan, har Alhj ya dauko jakar sa a mota ya buda, ya debo katuna." Ungo guda 10 ka ba shi. Haka kuma ga na ka nan, in za ka ba Friend din ka ne, in ba ka Twenty? Kamar ya ce,"A'a." Sai wata zuciya ta hana shi, ya ce,"Toh Alhj." Ya mika masa guda 30. Yasa hannu ya kar6a. Bayan sun yi sallama da Alhj, ya wuce ciki gida, ran sa 6ace, ya koma gun Nusaiba,"Me za ki 6oye min? Ashe Next week ne auran ki shine ko ki gaya min? Ni na isa in hana ne? Baki sake ta ce,"Shirin gaya maka na ke yi, sai Abba ya dawo ka tashi. Ayi hakuri. Ya suri Ameer,"Mu mun tafi. Allah ya bada zaman lafiya." Ya wuce ya bar ta zaune tana masa dariya. Yana zuwa, ya watsa katuna bayan mota, suka tafi. Iya wuya yake yau. Duk wanda ya ta6a shi, zai ji masifa, gida ya wuce da katunan bai kai wa Abba na shi ba. Yana zaune. Zarah da Ameer kadai ke hidimarsu cikin gidan Baya ko fahimce shi ba, suna kici ita da dan lelwn ta, suna girki. Yayi nisa a tunanin sa, kamar ya hadiye zuciya, don haushi. Me zai ci da katuna, banda ya banka wa 'yan iska wuta? Ya zabura a fusace ya fado kicin, babu magana ya hau bincike, ya 6aro mata da kayan cikin dirowar sama. Tayi tsaue tana fadi,"Yayana me ka ke nema? Ashana." Ta ga ya dauka, yai waje. Ta jefar da ludayi, ta biyo shi,"Yayana me za ka yi da ashana? Ya buda mota ya kwaso katuna, ya aje k'asa. Kafin ya kyasta ashanar ta kwashe su. Ya kama da karfin yana fadi,"Ki saki na ce ko? Ta dade bata yi auran ba, idan har sai mun je masu daurin aure! Ya fizzge iya rabon sa, ya watsar kasa, ya kyasta ashana. Ya cinna, yayin da Zarah ta buda ambulan, don ganin takardun da yake rawar jikin konawa? Kati ta gani ta zaro shi ta karanta. Dada masa duka ta yi a tsakar baya, yana duke yana cinna wuta, ta fadi da karfi,"Kai yaya na da kai ne! Duba ka gani,"Naseer Iliyas Balarabe aka sa! Ya mike ya fige katin a hannun ta, ya karanta. Gaba daya jikinsa yayi la'asar, ya zura mata ido, sannan ya dafe goshi, duk kunya ta kama shi. Ta ce,"Komai ba ka bincike, sai ka yanke hukunci." Ya rungumo ta, hayaki yayi sama, ta ce,"Ga dai sauran nan na cin wuta." Ya sake ta ya hau tsalle yana kashewa, tana masa dariya, duk da haka wasu sun k'one, wasu kuma sun yi dameji. Ya kwaso yana nuna mata,"Ni yanzu yaya zan yi? Katunan nan har da Abba? Ta yamutsa fuska, ta dubi Ameer dake tsaye gefenta, ta ce,"Mu ina ruwanmu ko sweetyna? Ya amsa da kai, yana dariya. Ta mik'a masa hannu,"Come on give me five! Ya bata hannu, suka kashe. Ta sure shi, ta ce,"Zo mu tafi abin mu, kar abincin mu ya kone. Baban ka ya zare! Ya kawo mata wawura, ta kwasa da gudu. T-shirt da wandon dake jikin ta ya bata damar gudu sosai. Ameer dariya yake yana murna. Kicin ya iske su suna ta yi masa dariya."Don Allah ki aje girkin nan, ki zo ki raka ni." Ta kama k'ugu, ta tambayi Ameer,,"Mu muka ce ya konawa Abba kati? Ya girgiza kai,"A'a, ta dube shi ta nuna shi da ludayi,"Ka ji ko? Saboda haka ba ruwan mu." Ya matso ya manne da jikinta,"Don Allah ki daina wasa, ki zo mu tafi."Ta k'are masa kallo kafin ta ce,"Jira ni ina zuwa." Ya sumbace ta, saboda Ameer yayi waje. Ta sauke numfashi, ta ce,"Allah na gode maka amarya za ta dawo." Ta sauke girki ta kashe (Cooker), ko dama sitiyu ce, ta rage mata. Daki ta je ta dora (After dress) akan kayan jikin ta, ta yafo mayanin ta fito, ta kulle gida. Ta same su a mota. Suka tafi Ameer na bisa cinyoyin ta. Shi kuwa waya ya dauko ya kira Sageer a Bauchi."Banza, ka na can za'a sha shagali! Shagalin me? Amaryar Zarah za ta dawo." Ah haba don Allah? Komai yayi dai-dai kenan." Ya ce,"Walllahi ni ban ma san Abban na ta ya hakura ba, kati kawai ya ba ni dazu." Cikin murna ya ce,"Congrats. Insha Allahu zan zo a daura da ni, wannan dole ne. Yaushe ne? Next week,"Ai kuwa zan zo da yardar Allah." Suka yi sallama ya aje waya. Ya dubi Zarah,"Ya ce, yana gaishe ki." Ina ansawa. Amma ba ka gaya masa ka zare ba, har ka kona katunan." Ya dunkule hannu ya dora bisa kuncinta. Allah zan kwashe miki hakora, ki kiyaye ni! ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya kuwa kama, ya danna masa cizo, ya janye da sauri yana dariya. Su ma suna yi masa. Ya shafa kan Ameer ya ce,"Ta koya ma mugunta ko? Ya lafe a kirjin ta, suka kwakume juna. Naseer ya sha mamaki da suka kai wa su Abba ragowar katin da suka rage masu kyau guda 15. Malam Balarabe ya ce idan ya na son k'ari ya zo ya ba shi. Kunshi 1 ya fito da su, wani samfu daban kuma bugun Malam Balarabe. Abin ya daure wa Nasrr kai, ya ce,"Ni fa ban gane ba? Umma ta ce,"Ai ba za ka gane ba, domin Abbanka da Alhj sun barka cikin duhu. Amma tun ranar da ka zo da Ameer gidan nan. Alhjn ya gaya wa Malam cewaR Nusaiba za ta dawo." Ya shagwa6e fuska,"Saboda Allah ya za'a min haka? Da na mutu fa kafin lokacin saboda damuwa? Zarah ta ce,"Sai a rufe ka mu ci sadaka. Ya harare ta. Umma na fadin, gaya masa dai Zarah. Take nan ta ba su labarin abinda yayi dazu. Me za su yi ba dariya ba. Koda ya je Kaduna dariya suka rinka yi masa, musamman Nusaiba. Shirye- shirye ya kankama. Da yawa mutane ba sun san Nusaiba bata gidan Naseer ba, sai da suka sake ganin kati, musamman jama'ar Alhj. Ranar juma'a da daddare Sageer ya iso, don haka da shi aka daura aure. Washe gari karfe 1 da rabi na rana. Antin Jordan ta dubi Naseer ta ce,"Lalai kai mai sa'a ne, ka yi wa Allah godiya, domin yayi maka baiwa." Ya sunkuyar da kai,"Na gode Anti." Ya wuce ta bi shi da kallo. Ibrahim ya fado mata, tausayin sa ya kamata. Ranar daya zo Injinya na masa bayanin hukuncin da Alhj ya yanke har ya bar wajen, fadi yake,"Ai dama na san Abba baya so na. Wannan karon ma har da Nusaiba, tunda ta iya barin k'asar nan, ba tare da sani na ba." Ta girgiza kai, ta ce a ranta,"Matar mutum kabarin sa." A ranar Nusaiba ta tare su Kausar suka rako ta. Suna shigowa Zarah ta kar6e ta, suka rungume juna, ta kamo ta zuwa sashinta. Kausar na ta fama da tsohin cikin ta, ta ya6e bakin gado. Naseer ya shigo, bayan sun gama cin abincin, suna shirin komawa. Ya ce,"To ga motar can sun shawo man sun dawo." Kausar ta ce,"Na ga ka na rawar jiki ne Jah-Jah, sai wani korarmu ka ke, ni fa ina nan an sai jibi zan koma." Ya ce,"Ga Jah-Jah nan a gaban ki, kin yi wani turus, in za ki kai jibin? Aka kwashe da dariya. Ta ce,"Anan gidan kuwa." Ya ce,"Ina, taso maza in lalla6a ki in sa a mota, kar ki caza min aiki. Ina angwancina, ace in taso asibiti zan kai ki." Ta ce,"Gaskiya ne, ba laifin ka ba ne, tana ji ta yi shiru, shi yasa ka ke kara fadi. Ta na shiru. Antin Jordan ta shigo. "Kausar cicci6o mana, sai da nace ki yi zaman ki gida, ki ka ki." Simi-simi Naseer ya fice. Kausar ta ce,"Ya ka tsere? Dawo mana mu ci gaba. Ka na Angwanci ko? Ya waigo a bakin kofa, ya amsa da kai, ya wuce yana dariya. Duk an watse. Kowa ya koma muhalinsa. Ba ango kadai ba, hatta Ameer yana murnar ganin Maman sa a cikin gidan, yayi ta tsalle-tsallensa ya bi can, ya bi nan. Amma yana cin abinci. Zarah ta yi masa wanka, gadon ta ya haye yayi barcin, bai nemi Maman sa ba. Tana zaune misalin 9, nazarin litattafanta take yi. Naseer ya shigo. Ta dube shi tana. Murmushi,"Ango kenan. Kamshin nan yayi Wallahi." Ya tsugunna ya dada mata duka a baya,"Ba kya ji ko? Ta ce,"Na kai ka rashin ji? Ya ciji kunnanta, ta shafi wajen, ta ce,"Amarya na jiran ka, tashi mu je in raka ka." Ta aje littafi ta kamo hannun sa, ya mike ya rungumo kafadar ta, suka fito zuwa sashin amrya. Ta turo kafar tare da sallama ta shiga. Amarya ta sha ado, sai wanda ya gani. Zarah ta ce,"Kai amarya, ai sai yayan mu ya mance sunansa." Ta sunkuyar da kai,"Antina kin dame ni tun dazu." Ta ce,"To babu ruwana, ga shi nan na kawo shi amana, gobe in an ga ya susuce, ke ce." Ta kama baki tana 'yar dariya. Ya kamo kunnanta,"Shi yasa nace ba kya jin, zo ki wuce." Yana rike da kunnan ya kai ta kofa, suna dariya. Ta tsaya ta ce,"Amarya ya kore ni, sai da safe kenan."Ita dai ta kasa magana, sai dariya. Zarah ta ja kofa." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya tsaya ya k'are mata kallo, sannan ya sauke numfashi. Ya tako a hankali ya tsugunna gabanta, suka dubi juna, ta dan kauda kai, tana murmushi. A natse ya kwantar da kan sa bisa kafafuwanta, ya nisa yayi dan shiru. Haka ita ma take kallon sa idanuwanta suka kawo kwalla. Bata san lkcn da ta dora kan ta bisa bayan sa ba. Sun jima shiru haka kafin ya ce,"Na gode Allah, na sake gode masa daya nuna min wannan rana. Haka kuma na gode wa Abba daya sake mallaka min ke. Na yi kuskure gare ki Nusaiba wanda baya misaltuwa, ba na kuma son tuna su. Ki yafe min Nusaiba. Ta ce,"Tuntuni na yafe maka yayanmu. Ya wuce." Ya dago ya ce,"Na gode." Kin san wani abu? Ta kada kai. Ya lalibo aljihunsa ya dauko kudi, ya kamo hannun ta ya dora mata, ta ce "Na menene? Kudin ki ne, canjin ki dubu 15 da ki ka ba ni a asibiti. Ta saki baki tana kallon sa,"Kai yayanmu, shekara 2 da rabi? Ya sake kwantar da kan sa, ya ce,"Ba zan ta6a mancewa da su ba Nusaiba, domin daga ranar da ki ka miko min su. Allah ya manna min son ki a raina. A lkcn ba wai ba ni da su ba ne, amma ba su da amfani, tunda ban san yadda zan yi in ciro su ba. Alhalin ina matukar bukatar su. Da gaggawa. Kin min abinda ba zan ta6a mancewa da ke ba rayuwa, kin taimake ni a lkcn da na wulak'anta ki na.......... Ta rufe bakin sa."Na ce ya wuce yayan mu, ka daina tunawa." Ya dube ta ido cike da kwalla,"Kar ki yi kokwanto Nusaba, Ina son ki! Ina son ki!! Ina son ki Nusaiba!!! Ta ce ,"Na sani." To kice kina so na in ji, ko sau 1 ne." Ta yi dan murmushi ta ce, "Ina son ka yayan mu. Ga kuma kudin ka har canji na bar ma ka." Yahayo shimfidar sosai, ya ce,"Kin saye baki na ke nan? Ta yi 'yar dariya,"Na siya." To me ki ke sha'awar sha? Ta ce,"Uhm.......Cock, irin mai dan inabin nan. Ka gane ai? Ya tsura mata ido, tana masa dariya. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Zaman lafiya mai ban sha'awa ga kowa ya dore a gidan Naseer. Hankalinsa kwance, ba shi da matsala. Ya k'are Digirinsa. Shine gwarzon shekara, wanda ya fito da ajin farko a fanni da yake karanta, sannan ajin farko cikin jerin wadanda suka zo na farko a sauran kwasa- kwasai a wannan shekara. Don haka yana daya daga cikin masu rubuta jarabawar tantance masu tafiya Turai don karo ilimi tare da tallafin gwamnati. Kowa yayi masa murna. Shi kan sa ganin abin yake kamar a mafarki. Allah yayi gaskiya ya ce tashi in taimake ka. Tabbas hake ne, Naseer ya ga Zahiri. A Kaduna suka rubuta jarabawa 'yan makwanni tsakani sakamo ya fito. Naseer ya haye ya ci Nasarar tafita Ingila. Shirye-shirye ya kankama a lokacin cikin Nusaiba ya fara tsufa, domin kuwa ya shiga wata na 7. Ranar da zai tafi daren kasa barci yayi, saboda tunanin shekara 1 ba zai ga iyalansa ba, wad'anda ya riga ya aje su cikin ransa, baya son kasancewa da kowa sai su. A duk inda yake. Allah.Allah yake ya yi yadawo gida, saboda tsabar son da yake musu. Amma babu yadda zai yi, yana son ci gaba kuma a yanzu ya tauna dadin karatu ya dandana ya gane fa'idar sa. Kan dole ya dake zuciyar sa. Washe gari karfe 8 na dare jirgi ya cilla da su birnin Sarauniya. Sun kama karatu gadan-gadan, amma kodayaushe cikin waya suke da iyalansa. A haka watan haihuwar Nusaiba ya tsaya. Umma ta sa ido sosai a kan ta, babu ranar da bata zuwa Hanwa. Allah da ikonsa da safe ta fara nakuda, ga shi Zarah na da jarabawa kuma ta karshe ce, don kammala NCE din ta. Duk da haka ta hada kayan haihuwa ta wuce da Nusaiba asibiti. Sai da ta tabbtar an shiga da ita dakin haihuwa kafin ta kira Umma ta gaya mata asibitin da suke. Nan take Umma ta watsar da abinda take, ta biyo hanya. Tana isowa 8 dai-dai, sannan Zarah ta bar mata Ameer, ta wuce jarabawa, ta iske an shiga, sai da ta sha surutu, ta samu aka ba ta fefar. Da namiji Nusaiba ta sake Haifa, lafiya lau daga ita har Bebin. Umma da Ameer na murna. Nan da nan ta kira wayar Ummi, ta shaida mata ta sake sabon ango.... ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajinisa Yake3-06 Posted by ANaM Dorayi on 12:04 PM, 25-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Suka yi farin ciki. Ta lallatsa ta nemo lambar Naseer. Suna gaisuwa, kudinta suka kare. Tir! Haushi ya kama ta, sai ga shi ya kira,"Menene Umma? Ta ce,"Ka yi Da. Nusaiba ta haihu yanzu." Farin ciki kamar yayi tsuntsu ya baro Ingila." Ina take Umma? Ta ce,"Ai tana ciki ba su riga sun fito da su ba, amma sun ce lafiya kalau suke ita da Bebin." Alhamdu-lillah! Allah ya amfana mana." Ta ce,"Amin. Haka ya kasance cikin doki, kamar yadda Zarah ke makaranta cikin zakuwa da son ta koma wajen Nusaiba. Kafin yamma gidan su ya cika da baki 'yan barka, angon karni kuwa ya ki barin mai jego sakat da waya, shi so yake ji kukan Bebi, "Bebi kuma ya ki yin kukan. Barcin sa kawai yake kwasa. Ranar suna, yaro ya ci sunan Alhj. Haka kuwa suke kiran sa(Alhaji) Ya ci gaba da girma tamkar Ameer, shi yasa idan Naseer ya rufe ido, baya ganin kowa illah 'ya'yan sa, tamakar 'yan 2. Watanni 3 bayan haihuwar ta. Alh.Basheer zai tafi harkokinsa Turai, ya wuce wa Naseer da hotunan dan sa, ya gan shi. Hankalinsa ya kwanta. Ya cire na Ameer daga firem ya zira wanda suke su 2. An ci gaba, renan Naseer Jah-Jah. Shi kansa yana mamakin kansa. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Kwanci tashi, shekara ta zagayo. Naseer ya dawo cikin iyalansa, kamar yadda yake so. Bayan ya huta sati 1. Alhj ya kira shi suka tafi bargar dawakansa. Abin ya ba shi mamaki, irin dawakan da ya gani suna harbin iska. Sake da baki ya dubi Alhj yace "Abba za'a fara wasa ne? Ya dafa shi ya ce,"Haka na ke zato, idan na sami amincewar Jah-Jah." Bakin sa har kunne ya ce,"Abba in dora sirdi in hau? Yayi murmushi ,"Why not." Ya kira mai kula da wajen, ya ce,"Je kawo sirdi." Nan da nan ya dora Naseer ya haye jikin sa na rawa ya zagaye bargar dawakan. Kamar kar ya sauka, dokin yayi masa dadi." Abba yaushe za'a fara? Ya ce,"Yau da yamma za'a fara a tisaye, sannan akwai club guda 3 da na ba takardar gayyata wasan sada zumunci. DABAI ta dawo sabuwa." Ya ce,"Insha- Allah kuma gagara gasar masu gasa." Ya kamo shi suka nufo mota yana fadin,"Akwai wani kokari da na ke maka, amma ba zan gaya maka ko menene ba, sai Allah ya tabbatar da abin, za ka ji. Ka ci gaba da addu'a. Allah za6a mafi alkhairi." Ya dan rankwafa ya ce,"To Abba, na gode. Allah ya saka da alkhairi." Wasa ya kankama. (DABAI RIDERS) ta dawo duniyar tseran Polo. Tutar Naseer Jah-Jah ta yi sama ta neman ta wuce yadda take da can baya. Watannin 9 yana ketawa cikin kungiyoyin Polo, yana ba su mamaki. Kwatsam! Abinda Alhj ke masa kokari ya samu. Ba wani abuba ne, illa samun shiga shaharrariyar kungiyar wasan Polo ta kasar Potugal. Naseer fa kamar yayi hauka, don murna. Haka Malam Balarabe, bai san abinda zai ce da Alh.Basheer ba. Kamar yadda aka bukace shi, daya iso 15 ga wata, haka yayi sallama da kowa suka tafi tare da Alhjn. Sun gwada shi, sun ga iya kwarewar sa a zahiri ko dama Alhj ya sha kai masu SD filet din wasaninsa na gida da waje. Kwarai sun gamsu da wasan Naseer, kuma da alamun za'a samu da shi. Can Alhj ya baro shi yana fafatawa cikin turawa. A lokacin ne ya k'ara tabbatar cewa komai in ka na da ilimi ya fi tafiya dai-dai, musamman a wannan zamani. An bashi gida da motar hawa. Naseer ya kasance ba shi da wata matsala sai ta kewar iyalan sa. Ita ma sun kusa magance ta. Cikin watanni 2 takardun zamansa dindin a Potugal suka kamala, ya sami izinin shigowa da iyalansa. Babu son kai. Zarah ce ta fara zuwa a matsayin ta, ta babba. Ameer yayi kukan son biyo ta, amma ina makaranta, ta hana. Wai! Wa ya gane min Zarah a Potugal? Ta shakata kwarai tsawon wata 1, ta koma Nusaiba ta damk'o hanya. Haka suka kasance suna yi wata guda-guda babu matsala balle tashin hankali. Kowacce ta zo Naseer yana jin dadin kasancewar tare da ita, bisa adalci da tsoron Allah. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Shekara 5 Naseer yayi karfi sosai a k'asar Potugal a fagen tseren Polo. Yayi farin jini kwarai da gaske, kowa na son shi. Sau da yawa wasu kungiyoyin na kawo masa cafka ta hanyar ninka masa abinda yake samu, amma ya kauda kai, saboda Alh.Basheer. Domin a halin yanzu arziki sai dai ya ba wani, bai ma san iya wadanda suke cin gajiyar sa ba a gida Najeriya. Duk shekara idan ya je hutu. Bayan dawowa ba tare daya buda wata cibiyar siye da siyarwa ya zuba matasa sun samun abinci ba. Hatta Naseer B dan hassada, ya saduda ya nemi gafara, ya dawo yana cin arzikin da Allah yayi wa Naseer. Yayi farin jini ba na wasa ba a Potugal, domin har tallace-tallace yake wa manyan kamafoni ta hanyar sana'arsa. Ba kananan dololi yake kamawa ba, kowacce talla yayi. A 'yan shekarun nan biyar. Nusaiba ta hada 'ya'yanta 4 a gidan Naseer, 2 maza, 2 mata. Hakika hankalin Naseer a kwance yake, kuma Alhj ya lura karfi sosai a club din sa, tseren dawaki sai dai ya ba 'yan baya tirenin. Saboda haka yayi iya yin sa wajen Injiniya Ahmad Kaita ta hannun sa ya samar masa a aikin yi ta 6angaran karatun da yayi, don kar ya tafi a banza. Allah mai ko! Takarda kawai aka ba Naseer ya je inta-biyu ofishin(Internet Globl Services) reshen Potugal, take nan suka yarda da takardunsa. Ya sami shiga aiki. Duk da haka bai bar Polo ba, amma ya zama na manya, wanda ake son tafiya da shi, musamman a gagarumin wasan duniya. A farkon wannan watan Zarah ce ke da zuwa Potugal, a filin jirgi ya je ya dauko ta. Suka shiga harkokin su kamar yadda suka saba. Zarah na nason ziyartar Singafo da Malesiya, don haka washe gari suka wuce suka kwana 4. Kwana bibbiyu a kowace k'asa. Sun ci gaba da hutawa a Potugal. Sati 2 dai-dai da zuwanta, ciwon ciki mai tsananin gaske ya murda. Zarah kamar ba za ta yi rai ba. Naseer ya gaggauta kai ta asibiti. Babu 6ata lokaci ta ga Likita ya bata kwararrran bincike. Allah da iko tare da yin yadda yaso. Wai Zarah ciki gare ta na sati 2 a wajen mahifa. Naseer yayi wa Likitan ta bayanin matsalarta. Nan da nan aka buda bakin mahaifa aka maida cikin mazaunin sa. Ta sami kulawa sosai a asibitin har ta wartsake. Yayin da Naseer tuni yayi waya gida, ya shaida masu halin da ake ciki. Kowa ya sha mamaki. Shi yasa tana murmurewa ta fara amsa wayayinsa masu gaishe ta, musamman Nusaiba da ta kan bugu sau 3 zuwa 4 a rana. Mafarin zamanta a Potugal kenan tana samun taimakon daya kamata. Anyi wa yara hutu. Nusaiba ta aje su wajen Umma, ta zo duba Antinta, sati 2 ta koma gida. Sannu a hankali cikinta ya wuce wata 7, ya shiga na 8 kuma Bebi lafiya lau, kowa na ta murna, musamman Naseer da yake tausaya wa Zarah. Rashin da, ga ta ita ma ita kadai wajen iyayen ta. Satin da za ta shiga wata na 9, jini ya goce kamar famfo. Da kyar suka tsaida jinin suka shiga binciken mai ya kawo hakan. Ai da gudu Likita yasa aka gara ta tiyata, bai yi bayanin komai ba, sai da ya ciro k'aton Bebin namji, sannan yayi mata duk abinda ya ga ya dace, don tsira da lafiyar ta. Daga Bisani ya kira Naseer ofishinsa yake gaya masa matsalar da Zarah ta samu. Mahaifarta ta fashe gaba daya, wanda dole ya kasance ya fitar da ita baki daya, hakan shine wajibi a gare ta, don zaman lafiyar ta. Kuka ne kadai Naseer bai yi ba, amma ilahirin hankalinsa ya tashi. Gani yake yi kamar ma cire mahaifar, zai iya jawo mata wata matsalar, sai da likita yayi masa bayani sosai, sannan ya gamsu. Yayi addu'ar Allah ya k'ara mata lafiya, ya kuma bar mata abinda aka samu, ita ma ta rink'a ganin abin ta. Ko gida Najeriya hankalin su ba kwance yake ba, duk Nusaiba ta k'osa a kammala mata biza ta tafi. Bayan kwana 3 kuwa ta isa Potugal. Antin tana a kwamce, duk ta rame ta dushe, bata san lkcn da ta fara zubda hawaye ba. Ga Bebi kato, gwanin sha'awa kuma duk 'ya'yan Naseer da shi suke kama, har matan. Nan ta zauna tare da Bebi (Aliyu), zuwa lkcn da Zarah ta yi sarai, tsawon kwana 12 a asibiti, kafin Likita ya bata sallama suka dawo gida. Sai da Zarah ta yi 40, ita da Aliyunta, sai k'ara murjewa suke, ita dai Zarah ta ki sakin jinkinta dashi, gani take kamar shi ma mutuwar zai yi. Sun dawo gida Najeriya yana da kwana 45, gaba dayan su da Naseer. Gagarumar walima ya shirya, bata wasa ba, 'yan uwa da abokan arziki suka taru, aka taya juna murnar samun Aliyu tare da fatan Allah ya raya shi cikin danginsa, rayuwar Islama. Sati 1 Naseer yayi ya dawo Potugal. Tun Zaran na fidda rai da Aliyu, tana ganin yau zai mutu ko gobe har ta zo ta saki jikinta, zuciyar ta ta zauna waje daya ta daina ba Aliyu mutuwa. Watansa 9 kenan yayi girman mamaki, da kan shi yake mikewa tsaye, yana nema cira k'afa yayi tafiya. Yana kuwa shan ja wajen 'yan uwan sa suna son yayi tafiya dole. Rayuwar su mai dadi suke sha, tare da abokan huldar shi, domin a halin yanzu Sageer yana lakcarin a nan (State Poly) da yaransa 3. Kausar na da 2. Zumunxin su kodayaushe k'ara k'arfi yake tare da k'aruwar arziki. Ko Zarah ta gyara gidan su dai-dai gwargwado tare da taimakon Naseer. A cikin su da iyayen su babu wanda bai keta hazo ba, ya sauke faralinsa. Komai maka Allah shekaruna mikawa hada da tarindaukaka. Naseer ke zaune shi kadai bisa kujeran alfarma a farfajiyar bayan gidansa. Yayi shiru ya zunduma taunan baya, har ya zo kan rayuwar da yake cikin ta a halin yanzu. Ya dubi tafkeken gidan sa a birnin Potugal, mallakar sa wanda ya zuba makudan daloli ya siya. Babu abinda ke ransa, sai dumbin godiya ga Ubangiji da yayi masa baiwar da ba kowa ke samun irin ta ba. Sannan ya mallaka masa ingantattun mata na nunuwa a fadin duniya.Zarah idan ya tuna irin baiwar da Allah yayi mata na kaifin hankali da sanin yakamata, ya tuna ita ta fara gaya masa rayuwa shirin Allah ce, bai kamata Dan-adam yana alkawari a hurumin da ba nasa ba, sai ya ji son ta ya shafe ko'ina a jikin sa, yana neman zautar da shi. Nusaiba matar da yake wa yak'inin sa'a ce a gare shi, Allah ne yayi masa arziki daga gare ta, 'ya'ya da dukiya tare da fice a duniya. In dai ana maganar wasan Polo, duk masoya wasan sun san da Naseer Jah-Jah. Shi yasa idan ya dube ta, haka kawai ya kan ji hawaye sun cika idanuwansa, sbd tsabar tausayin kan sa, da ace ya rasa ta akan wautar banza. Son ta ruwa ne, ya aje wa ransa, don ko ya fadi, shi kansa yana ganin karya yake yi. Yayi mika, take nan kewar su ta kama shi, domin babu ko dayan su a tare da shi. Zarah na jarabawar karshe ta kamala B-ed din ta. Nusaiba kuwa ta na watan haihuwa ta 6. Ita kadayaushe ta fi son haihuwa a gida. Gaba daya hankalin sa ya koma gun sun, daren nan ya kasa barci. Kamar wasa zuciyar sa ta rasa sukuni, ba shiri ya nemi hutun shekara. Bai hada sati ba, ya baro Potugal, sai ganin sa suka yi kwatsam! ----------------------------------------------------------------------------------------------- Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ 'Ya'yan sa suka baibaye shi, tun isowar sa har la'asar yana tare da su. Direba yayi kiran su lkcn Islamiyya, kowanne ya fito cikin shiri, ya shiga mota. Direba ya wuce da su. Zarah ta idar da Sallah, ta fito babban falo ta iske Nusaiba zaune tana kallo. Kusa da ita ta zauna tana fadin,"Ki na nan ki na kallon fadace-fadacen nan da ya ki ci ya kicinyewa." Ta ce,"Ke dai bari, ai ni wannan fadan na k'asashen larabawan nan tsoro yake ba ni." Zarah ta ce, ke me kika fahimta daga gare shi? Ta ce,"Karshen duniya mana. Dama ance idan zamani ya zo karshe, alamun har da 6arkewar rikicin k'asashen gabas ta tsakiya. Yanzu dubi k'asashe nawa ke rigima, ana kashe su, kamar ana kashe kiyashi, tsakanin mu a musulmi kenan." Zarah ta tallafe kunci ta ce,"Wannan rayuwa tana firgita ni, me mu2m ya kamata yayi, banda ya kadaita Allah, yayi masa ibada, sannan idan ya ci, ya bada sadaka, don neman karshe mai kyau? Ta ce,"Wallahi kuwa Antina, musamman na mu mata da aka ce mun fi yawa a gidan wuta. Biyayyar aure ce matsalar mu komai muka yi gidan miji lada ne. Amma sai ki ga abin ya gagara. Kar ma ace miki akwai abokiyar zama, abin ya fi kazanta. Sai ki ga mace ta mance cewar akwai hikimomi da yawa cikin auren mace fiya da daya shi yasa Ubangiji ya halasta shi. Haka kawai ta dauki bakin kishi ta dorawa kanta, daga nan ne za ta fadawa hallaka. Allah ya kiyashe mu. Zarah ta kamo hannun ta, suka runtse,"Kin yi gaskiya amarya, shi yasa na ke wa Allah godiya da yasa ke ce abokiyar zama na." Ta yi murmushi,"Ni din Antina? Na fi kowa farin cikin samunki. Allah ya k'ara hada kan mu, ta yadda yayanmu zai ci gaba da samun kwanciyar hankali. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Tafi suka ji ana yi ta bayan su. Duk suka waigo,yayan na su ne a tsaye yana jin su. Ya zagayo suna dariya ya tsaya gaban su, ya ce,"To a matsa min in zauna." Suka ware ya zauna tsakiyar su." Allah ya kamaku, ashe zama ku ke kuna gumalta ko? Zarah ta kama baki, "Lah! Allah mai halitta, jaba ta dubi bakin mijinta. Gulmar me kuma a mu ka yi ta ka? Ya kamo kunneta. Nusaiba na kwasar dariya, ya ce,"Ita jabar 6ata dubin ta ba ne? Ta ce,"Oho." Ya k'ara murdawa, ta yi k'ara. Nusaiba ta kamo na shi ta ce,"Allah sakar min Antina, ko ni ma in cire na ka. "Ya saki ya dube ta,"I see, kun hada kai ko? O.k, yayi kyau, ke ba zan ta6a ba, kin zama yangwam! Amma ke, za mu hadu." Duk suka yi dariya. Ya rungumo kafadansu ya sake fadin,"Allah ya yi maku albarka, kun zama abin alfahari na, kun zama jigon rayuwa ta. Na kuma gane rayuwa shirin Ubangiji ce, mutane da yawa suna samun dama, amma sai su ki amafi da da damar har ta wuce su, daga baya su zo suna cizon yatsa. Allah ya ba mu ikon amafin da damar mu." Suka nisa suka amsa da Amin. Kowacce ta dora kanta bisa kafadar gefen sa. Suka yi shiru na 'yan dakikai. Cikin shirun ne suka ji kamar suatin T.V, a wani sashi na gidan. Naseer ya ce ,"Wai ba duka yaran nan sun taifi makaranta ba?. Eh mana." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya mike yana fadin,"Ga sautin (Game) can ina j? Duk suka mike suka bi shi sashin yara. Ameer ne ya kuke yana buga Game na tseren Polo, sautin T.V ya rage can k'asa, yi yake kamar zai tashi sama, sbd kwaikwayon yadda dawakan ke gudu. Naseer ya lalla6o ya cafke kunnansa, a tsorace ya waigo manyan idanuwan nan na sa. Suka kara yo waje tamkar Naseer a zamanin da yake shagalinsa a filin sukuwa. Bai tanka masa ba, yai ta jan kunnan sa har falo, sai su Zarah ke ta faman salati suna fadin,"Amma dai Ameer Allah ya shirye ka! Ya tsaya ya k'are masa kallo, kafin ya ce,"Kai ne babba, amma babban kwabo? Kullum da kai ake complain! To zan kwashe Game din tunda shi ke hana ka zuwa makaranta! Yayi sukuiti yana kumbura. Nusaiba ta zungure shi, "Maras kunya, sai anyi magana, ya rink'a cika yana hura hanci, wa ka fi zuciya? Come on wuce ka dau ko jaka Lado ya kai ka! Zarah ta kamo shi,"Wuce mu je, ka dauko jakar, kai ba ka ganin kannin ka sun tafi? Ta raka shi ya dauko jaka. Nusaiba na ta fada, ta fita ta kira Lado Direba, yasa shi a mota zai wuce da shi." Nusaiba ta zauna kusa da Naseer ta ce,"Ameer sai addu, ace yaro baya maida hankali a karatu. Sai game din tsiya? Shi yasa ban so ka kawo masu wannan sabin Game din ba." Ya ce,"Zai bari ne." Zarah ta dawo ta zauna inda ta tashi,"Ameer kenan an dai tafi ana ta kunci,"Nusaiba ta ce,"Ai kin ji Babansa ya ce zai bari ne, amma complain din Ameer yayi yawa, ko makarantar kuka suke da rashin maida hankalinsa, ga masifa, ni na rasa irin sa." Ya ce,"Ni kuwa in na kalle shi, dariya yake ba ni." Kin ji ko Antina? Ta ce,"Ya dai kamata ka sa baki, ka yi masa fada sosai, kafin ka bar garin nan, kila ya fi jin na ka. Ameer yan aikin gidan nan bai kyale ba, haka 'yan kanninsa. Aliyu kadai bakin sa ke ceton sa da yake duk gautan ja ne. Baba na da Alhaji kuwa, sai dai su yi kuka su share hawaye, balle kuma 'yan matan." Ya kama kai, ya ce,"Wayyo Abba na, duk wannan laifin shi kadai? Wai ba yarinta bace? Nusaiba ta ce,Yarinta? Me yasa............ Ya katseta,"Ya isa! A yimin shut up nace! Rashin jin nan fa kowa yayi shi, ke kin yi, ke ma kin yi. Ni ma na yi." Nusaiba ta ce,"Oho, ashe abin gado ne, ta 6angaranka, amma mu ba muyi rashin jin kin zuwa makaranta ba." Yayi 'yar dariya ya ce,"Yan rainin wayau, kun cika ni da , kamar ban san sirrin kowacce ba." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Zarah ta gyara zama ta ce,"Ai sai ka fadi"Yalla6ai, mu na ji." Ya dube ta, ya ce,"Ke fa kullum ki na like bayan taga, ki na zuba ihu, hawaye sharaf-sharaf, majina har baki. Da an tambaye ki menene? Sai ki ce kudin (Break) dina ne suka 6ace." Ya fadi yana kwaikwayon muryart har da shashshekar kuka. Ya juya kan Nusaiba,"Ke kuma ai Abba ya gaya min da zarar Direba ya fito da mota, zai kai ki makaranta, sai ki ce kashi ki ke ji." Ni din? Zarah ta ce,"Ke ma ki ka tsaya tambayar sa. Ta figo filon kujera. Nusaiba ma ta dauko na ta, suka rufe shi da duka. Me zai yi ba dariya ba, yana fadin,"Mugaye, k'arya na yi.........? Na kwashe 'yan biro na da takarduna na bar gidan, don ba zan iya ceton Naseer ba. Tsokanar fada A JININ SA YAKE!!! , saboda haka ALHAMDU-LILLAH, na gaji da shari"a. Idan kuma akwai ma iyawa, to Bismillah! Jah-Jah na can yana dakuwa a hannun zaratan matan sa.." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ afuwan bakujini da wuriba sakamakon wayata tadan samu matsala, daga bayakuma nadanyi rashim lafiya, your prayer is needed pls Zaharaddeen Shomar Whatspp 08168575100