ƘARSHEN ZALUNCI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 BABI NA ƊAYA Wata mata ce mai shekaru talatin sanye da kayan fata riga da wando, ɗauke da juna biyu a jikinta ke ta faman tafiya babu sassauci, A wasu lokutan har tuntuɓe take yi ta faɗi ƙasa, amma sai ka ga ta miƙe tsaye da ƙyar ta ci gaba da tafiya a cikin kasaitaccen birnin ma'abocin dogayen gine-gine. Sa'adda ya zamana ta shafe rabin rabin sa'a tana wannan tafiya sai kishi ya addabeta sakamakon tsananin zafin rana. Duba ɗaya za ka yi mata ka fahimci cewa tana cikin matuƙar buƙata, domin ƙafarta ko takalmi babu. Lokacin da ya zaman ta shafe sa'a ɗaya cur tana wannan tafiya sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a dai-dai wannan lokaci ne wani saurayi ma'abocin kwarjini da haiba ya durfafo inda take, yayin da ya iso daf da ita sai ya durƙusa bisa gwiwoyinshi. domin ya ga mene ne ya same ta cikin alamun tashin hankali. Nan take ya lura cewa tsananin kishi ne ya addabe ta har ta yanke jiki ta faɗi, cikin matuƙar kaɗuwa ya ciro wata salka dake maƙale a kwiɓin cinyarshi ta dama ya buɗe murfin. sannan ya sanya hannunshi ɗaya ya tallafo wuyan matar ya kafa mata salkar ruwan a baki, take ta shiga kwankwaɗar ruwan har sai da ta sha ya ishe ta, tana kammalawa sai ta ja gwauron numfashi sannan ta yi ajiyar zuciya ta miƙe zaune tana mai ƙurawa saurayin idanu hawaye na zuba. Al'amarin da ya bawa saurayin mamaki kenan kuma ya ji ya kamu da matuƙar tausayin, ya dubata cikin damuwa ya ce “Ya ke wannan mata shin ina dalilin wannan zubar da hawaye naki? Koda jin wannan tambaya sai hawaye suka sake kwaranyowa daga idanuwanta kuma ta yi shiru ba tare da ta ce uffan ba. Daga bisa ne ta buɗi baki muryarta na rawa ta ce. "Ya kai wannan saurayi ma'abocin tausayi da jin ƙai ka yi sani cewa a halin yanzu ba zan iya baka amsar watdannan da ka yi mini ba. Kuma bani da abin da zan saka maka bisa wannan taimako da ka yi min sai dai kafin mu rabu ina neman wata alfarma guda daya a wajen ka.” Cike da mamaki saurayin ya ce, "Ke kuwa wace irin alfarma ki ke nema a gare ni?" matar ta yi murmushin karfin hali, sannan ta ce "Alfarmar ta farko da nake nema a wajenka ita ce, ina so ka taimake ni da abin hawa haɗe da guzuri, sannan ina so kar ka bayyana labari na ga wani domin matsawar wani ya sani tamkar ka rushe taimakon da kayi mini ne.” Da jin wannan batu daga bakin matar sai saurayin ya sake cika da tsananin mamaki, kuma hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa kogin tunani, abu na farko da ya faɗo mashi a rai shi ne; "Mene ne dalilin da ya sanya wannan mata tace na ɓoye labarin ta? idan na ba ta abin hawa da guzuri shin ina za ta je?" Amsar tambayoyin da saurayin ya kasa bawa kanshi kenan, kawai sai ya miƙe tsaye ya durfafi ƙofar wani gida ya shige ciki. Jim kaɗan sai gashi ya dawo gare ta janye da wani ingarman doki fari ɗauke da guzuri mai tarin yawa. Koda ya iso daf da ita sai ya taimaka mata ta tashi tsaye, sannan ya riƙe mata linzamin dokin ta kama ta haye. Sannan ta sakarwa dokin linzami ta ci gaba da tafiya tana mai waigen saurayin hawaye na kwaranya daga idanuwanta. Nan take ya ji ya ƙara kamuwa da tsananin tausayinta, bai san sa'adda kwalla ta cika mashi idanu ba, ya ji a zuciyarshi cewa tamkar zai rabu da ɗan uwanshi na jini. Har sai da ya zamana sun daina hangen junansu sannan saurayin ya juya ya fice daga unguwar zuciyarsa cike da tausayin halin da matar za ta kasance a ciki. Bayan kamar shudewar daƙiƙa hamsin da tafiyar ta sai aka jiyo ƙarar takun sawaye gami da haniniyar dawakai ta cika unguwar. Koda jama'a suka leƙo daga cikin gidajensu domin su ga mene ne yake faruwa sai suka ga a she waɗansu gabza-gabzan Samudawan dakaru ne su kimanin dubu biyu shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, hannayensu rike da zaratan makamai. Bawasu bane waɗannan dakaru ba face na Sarauniya Abidat da ke mulkin Birnin Sin. Duk wanda ya leƙo ya yi arba da su sai ka ga ya rufe tagarshi da kofar gidanshi, tamkar ya hango mutuwarshi. Ya yin da dakarun suka iso izuwa tsakiyar unguwar sai wani garjejen kato ma'abocin kwarjini da ya fi sauran kirar sadaukantaka, ya ja linzamin dokinshi ya tsaya cak! Sannan ya kama linzamin ya sakko. Kwai sai ya dakawa sauran dakarun tsawa, kafin ya gama rufe bakinshi duka sun shiga karya ƙofafin gidajen unguwar suna fito da mutanen, mata da maza yara da manya. Kafin cikar daƙiƙa arba'in an tara gaba ɗaya jama'ar unguwar a waje guda suka yi masu ƙawanya. Garjejen ƙaton ya tako tafka-tafkan ƙafafuwanshi har izuwa inda jama'ar suke ya yin da ya zamana tazarar tsakanin su bata wuce taku biyu ba sai ya ja ya tsaya ya zare wata sharɓeɓiyar takobia gadon bayanshi ya dubi gaba ɗaya jama'ar da jajayen idanuwanshi masu kama da garwashin wuta yana mai nuna su da tsinin takobin cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya ce, "Shin a cikin ku wane ne ya taimaki wata mata mai ɗauke da juna biyu? Ina so ku yi sani cewa rashin nuna wanda ya taimake ta dai-dai yake da rasa rayukanku baki ɗaya." Koda jin wannan batu daga bakin badakaren sai hankalin gaba daya jama'ar dake wajen ya dugunzuma ainun, kuma su ka kamu da tsananin tsoro da yawa daga cikin su ba su san sa'adda suka saki fitsari a wando ba saboda firgici, kuma aka rasa wanda zai ce ƙala. Da ƙyar aka samu wani dattijo mai ƙarfin hali ya buɗi baki ya ce "Ya shugabana mu a yau babu wani baƙo da muka sauka a wannan unguwa tamu.” Kafin dattijon ya ƙara she zancenshi shugaban dakarun ya sanya takobinshi ya datse wuyan dattijon, kanshi ya yi fitar burgu daga gangar jikin, jini ya yi tsartuwa gami da feshi take gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica! Kawai sai badakaren ya dinga sanyawa aka dinga kawo mashi jama'ar unguwar ɗaya bayan ɗaya yana yi masu yankan rago kai har ƙanan yara, mata da tsofaffi bai ƙyale ba. Haƙiƙa komai rashin imanin mutum da rashin tausayin shi idan ya ga yadda waɗannan dakaru ke yin wannan ta'addanci, dole ne ya zubar da hawaye saboda matuƙar tausayi. Koda kammala wannan kisan gilla ne sai ya sanya aka cinnawa unguwar wuta. Al'amarin wannan mata mai ɗauke da juna biyu kuwa, tun sa'adda ta rabu da wannan saurayi suna zubar da hawaye sai ta ci gaba da tafiya babu sassauci. Ta wanzu tana ratsa layuka da unguwanni har ta fice da birnin baki ɗaya ta nausa izuwa cikin daji. Tana cikin gudun ne ta iso wani waje mai tattare da kwazazzabi sai dokinta ya kama sassarfa a cikin wannan hali ne ta ji alamun na guda sun zo mata. Kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya cak ta kama ta sauko sannan ta durfafi kofar wani kogon dutse, kafin ta isa sai ta yanke jiki ta faɗi kasa, a cikin wannan hali naƙuda ta kamata ta haife abin da ke cikinta. Cikin matuƙar farin ciki maras misaltuwa ta ɗauki abin da ta haifa domin ta ga ko mene ne, ai kuwa sai ta ga wata santaleliyar jaririya ce ta gaban kwatance, duk da cewa tana cikin halin laulayi ba ta san sa'adda hawayen farin ciki suka zubo daga idanuwanta ba. A dai-dai wannan lokaci kukan jariri ya cika dajin baki ɗaya, cikin azama ta ɗauki wani siririn itacen mai kaifi ta yankewa jaririyar cibiya. Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Ba zato babu tsammani sai ta hango waɗansu zaratan dakaru haye bisa dawakai sun rugo izuwa inda take. Kafin ta yi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗana bakanshi ya harbe ta da kibiya a gadon bayanta, saboda tsananin zafi da zugin da ta ji ba ta san sa’adda ta kurma wawan ihu ba ta sulale ƙasa sumammiya jaririyar ta na ci gaba da tsala. kuka. Har badakaren ya sake zare wata kibiyar ya saka a cikin bakan ya ja ya taɓe da zummar ya sake harbawa matar. Kwatsam! Sai aka ga wata irin murgujejiyar zakanya ta yo fitar burgu daga cikin wannan kogon dutse ta dako suma ta bangaji kirjin badakaren da dukkan ƙarfin ta. Saboda ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokinshi suka yi sama kamar an janye su da ƙugiya, sannan daga bisa suka faɗo ƙasa tim ko shurawa ba su yi ba. Al'amarin da ya firgita sauran dakarun kenan kuma ya fusata ainun su suka zare makamansu a kara fara kallon-kallo tsakanin su da zakanyar. Shin abin tambaya a nan shi ne daga ina wannan mata ta fito kuma mene ne dalilin daya sanya waɗannan dakaru ke farautar rayuwar ta dalilin hakan kuwa shi ne. BABI NA BIYU Fiye da shekaru dubu uku da ɗoriya an yi wani ƙasaitaccen birni a yankin ƙasashen Larabawa da ake yiwa laƙabi da Nurul-Kusuf. Birnin Nurul-Kusuf ya bunƙasa a fannin noma, kiwo da ma'adan ƙarƙashin kasa. Sarkin dake riƙe da KAMBUN MULKIN birnin ya kasance dattijon mutum mai matsakaicin kaurin jiki kwarjini da haiba, yana da tausayin talakawanshi da son ganin ya kyautata masu. Ana kiranshi da suna Urwat ɗan Unaifa, yana matar aure guda ɗaya jal wata kyakkyawar gaske da ake kira da suna Suhaimat, sun kai shekara goma da yin aure amma ba su samu haihuwa ba. Al'amarin da yake matuƙar ci masu tuwo a ƙwarya, amma ba su taɓa yanke tsammanin cewa za su sami haihuwa ba. A iya wanzuwar birnin Nurul Kusuf ba su taɓa yaƙi ba kuma ba a taɓa kawo masu HARIN BAZATO ba. Bisa wannan dalili ne ya sanya biranen da ke maƙwabtaka da su ke tururuwar zuwa birnin domin yin aikin fatauci siye da siyarwa. hakan ne ya sanya a kowacce rana sai ƙarfin tattalin arzikn birnin ya ƙara haɓaka, har ya zamana sun zamto babbar cibiyar kasuwanci a nahiyar. Sai dai kash, wani abin takaici shi ne duk tarin arzikin da jama'ar birnin Nurul-Kusuf ke da shi ya tashi a banza, domin duk bayan wata guda suna bayar da haraji ga wata saruaniya da adadin shi ya kai dinare dubu ɗari shida. Wannan MULKIN ZALUNCI da Sarauniya Abidat ke yi masu yana matuƙar ci masu tuwo a ƙwarya domin a wasu lokutan da ƙyar suke samun ɗan abin da za su kai bakinsu. Wata rana da hantsi Sarki Urwat na zaune a bisa karagar mulki, sanye cikin ƙayatattun tufafi na alfarma, fadawanshi na kewaye da shi ana tafiyar a sha'anin mulki cikin walwala da jin daɗi. Kwatsam! Sai aka hango wani manzo ya durfafo fadar riƙe da wata doguwar wasika a hannunshi sanye da korayen tufafi irin na mutanen birnin Sin. Lokacin da rage saura kamar taku huɗu tsarkin shi da karagar mulki sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya miƙa wasikar wani bafade ya karɓa ya miƙawa magatakarda. Ba tare wani ɓata lokaci ba magatakarda ya warware wasiƙar sannan ya fara karanto abin da ke ƙunshe a ciki a fili kowa yana saurare. "Takarda daga Sarauniyar duniya uwar Hatsabibai Abidat bintu Hargal zuwa ga Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf ma'abocin biyayya a garemu. Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa ban rubuta maka wannan wasiƙa ba sai domin in ba ka wani umarni wanda amince da shi ne tsira a gare ka, saɓani shi kuwa na iya jefa al'ummarka cikin musiba. Na samu labarin cewa a koda yaushe tattalin arziƙin birninka yana daɗa bunƙasa, bisa wannan dalili ya sanya nake so ka nunka adadin harajin da kake kawo mani izuwa kaso uku, kuma kai da kanka na ke so ka zo ka kawo ba aike ba. Tabbas idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Daga Sarauniya mai cikakken iko, zuwa ga bawanmu Urwat Ibn Unaifa Sa'adda magatakarda ya zo nan a karatun wasiƙar sai hankalin gaba ɗaya jama'ar dake fadar ya dugunzuma ainun, kuma fadar ta yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Daga can sai Sarki Urwat ya yi ƙarfin hali, fuskarsa cike da alamun matuƙar damuwa ya yi umarni da a tafi da ɗan aiken Sarauniya Abidat izuwa masauki, sannan ya fuskanci jama'ar fadar ya yi gyaran murya ya ce, “Ya ku Jama’ar wannan fada tawa mai albarka ku yi sani tabbas a halin yanzu rayuwarmu na cikin tsaka mai wuya, bisa wannan wasika da sarauniya Abidat ta aiko mana, don haka na sallami kowa zamu tattauna tare da 'yan majalisa domin samun mafita. Kafin Sarki Urwat ya gama rufe bakinshi jama'a sun tashi daga wajen zamansu suna masu fice daga fadar cikin kaɗuwa da tashin hankali. Shiru ne wanzu a fadar bayan sauran jama'a sun fice sai daga bisa ne Sarki Urwat ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar yin gyaran murya sannan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya dubi 'yan majalisarshi ɗaya-bayan-ɗaya ya ce “Ya ku dattawan wannan birni namu mai albarka sanin kan ku ne cewa hanyar da muke biyan Sarauniya Abidat haraji muna fuskantar takura shin ta ya zamu iya riɓanya ukunshi? Sannan kun san cewa zamu iya yaƙar Sarauniya Abidat ba domin har abada linzami yafi ƙarfin bakin kaza ta ninka mu a yawan MAYAƘA. Koda jin wannan magana daga bakin Sarki Urwat sai hankalin 'yan majalisar ya dugunzuma ainu fiye da koyaushe, shiru ne ya sake wanzuwa. Waziri Samazan ya yi gyaran murya ya ce, "Ya 'yan uwana 'yan majalisa ku yi sani cewa, yanzu idan har muka bawa Sarauniya Abidat abin da ta bukata, tamkar mun rushe wannan birni namu ne da hannayenmu. Domin idan har muka bayar da kuɗaden tattalin arzikinmu zai durƙushe, baƙin fataken dake zuwa birnmu za su dai na zuwa, sannan a cikin muwane ne yake da tabbacin zamu iya mayar da abin da muka bayar kafin nan da cikar lokaci. Ina nufin a lokacin da zamu sake biyan wani harajin? Da jin wannan magana daga bakin waziri sai kowa ya ƙara shiga taitayinshi. Galadima Salmir ya fara magana a karo na farko da fara wannan tattaunawa ya ce, "Ya 'yan uwana 'yan majalisa hakika fa maganar Waziri abar dubawa ce, sai dai wani hanzari ba gudu ba, idan muka ce zamu yaƙi sarauniya Abidat rayuwar 'ya'yenmu da matayenmu tana cikin mawuyacin hali, sannan dole ne a samu hasarar dukiya da ba a san iyakarta ba, ina ganin kawai mu bi umarnin Abidat domin mu tserar da rayuwar jama'armu." Sa'adda 'yan majalisa suka ji wannan shawara daga bakin Galadima sai fiye da rabin su suka nuna goyon bayan su akan hakan. A inda aka tsaya akan cewa za a ɗebi dukiyar baitul-mali sannan kowanne magidanci zai bayar da dinare ɗaya. A ranar da mako biyu suka cika Sarki Urwat tare da wasu daga cikin 'yan majalisar da amintattun bayinshi suka shiga yin shiri domin tafiya birnin sin. Bayan Sarki ya kammala kintsawa ne sai ya nufi turakar uwargidanshi Suhaimat yana shiga ya tarar da ita zaune bisa kan ƙasaitacciyar kujera, kuyangi na kewaye da ita suna shayar da ita tacaccen ruwan inibi a kofin zinare, yayin da kuyangin suka yi arba da sarki sai suka fice daga turakar suna masu kwasar gaisuwa, ita kuwa suhaimat sai ta miƙe tsaye ta rugo izuwa inda maigidanta yake ta rungume shi. Daga bisa ne Sarki Urwat ya janye jikinshi daga nata fuskarshi cike da annuri ya dube ta ya ce. “Ya hasken ruhina ku yi sani cewa a yau ne zamu yi tafiya izuwa birnin sin domin aiwatar da umarnin sarauniya Abidat ta yi mana, ina fatan za ki yi mani fatan alheri har mu dawo lafiya.” Koda jin wannan batu sai fuskar Suhaimat ta canja daga Annashuwa izuwa tashin hankalin ta dubi maigidanta cikin alamun damuwa ta ce, "Ya Uban 'ya'yana ki yi sani cewa tabbas jikina ya bani wannan tafiya da za ka yi babu alheri a cikinta, shin me ya sanya za ka nisan ta da ni a lokacin da ya kamata a ce kana kusa da ni? Cikin alamun rashin fahimta Sarki Urwat ya dubi Suhaimat ya ce, "Ban fahimci abin da kike nufi ba ya farin cikina? Suhaimat ta yi tattausan murmushi ta ce, "ya farin cikin zuciyata a halin yanzu ina ɗauke da juna biyu har na watanni bakwai." Cikin matuƙar farin ciki da al'ajabi sarki ya ce, “Amma ta ya aka yi ki ka san hakan? Suhaimat ta ce "Na samu hakan ne daga baiwata kuma likitoci sun tabbatar mini da hakan." Koda jin hakan farin ciki ya turnuƙe Sarki Urwat har hawaye suka zubo daga idanuwanshi ya rungume Suhaimat suna masu fashewa da kukan farin ciki, sai da ƙyar da siɗin goshi sarki ya janye jikinshi daga na Suhaimat suka yi bankwana, suna masu karanto waƙoƙin baitoci. Dake nuna alamun tsantsar so da ƙauna. Inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje a lokacin da waɗannan masoya biyu ke zubar da hawayen begen rabuwa da juna dole ne ya kamu da tausayin su ainun, ya tabbatar da cewa babu abin da yafi rabuwa da masoyi ciwo. Kai tsaye Sarki Urwat ya fice daga gidan sarautar ya nufi inda ayarin su suke yana isa aka kawo mashi doki ya kama ya haye sannan ya sakar mashi linzami ya ɗauki sauran ayarin suka mara mashi baya, sai da jama'a suka yi masu rakiya har izuwa bakin gari sannan su Sarki Urwat suka ɗauki hanya aka fara tafiya aka nausa izuwa cikin daji. Da aka fara wannan tafiya sai Sarki Urwat ya yi umarni aka sanya raƙuman dake ɗauke da dukiya da guzuri a tsakiyar, jama'a suka suka yi mata ƙawanya. Sannan dakarun rakiya suka rabu gida biyu, kaso ɗaya kewaye jama'a kaso na biyu suka sake rabuwa gida huɗu, suka tsaya a gabas, yamma, kudu da arewa, domin tabbatar da tsaro. Daga birnin Nurul-Kusuf izuwa birnin Sin tafiyar kwana biyar ce ba tare da yada zango ba, amma da yake su Sarki Urwat suna so ne su isa a cikin ƙanƙanin lokaci sai ya zamana ko yada zango ba a yi ba, kuma suna tafiya ne ba dare ba rana. A ranar kwana na biyu ne da La'asar sakaliya su Sarki Urwat suka iso ƙofar birnin sin, kai tsaye dakaru masu gadi suka wangame masu Ƙofar suka kunna kai zuwa ciki. Yayin da suka isa fada sai suka tarar fadar ta cika maƙil da jama'a duk inda mutum ya kai duban shi a wannan lokaci fadar ta cika maƙil da bil'adama rututu, tamkar dandazon kiyasai. Fadar ta kasance tanƙamemiya da aka ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun more rayuwa iri daban-daban, wani abin ma mutum bai taɓa gani ko jin sunan shi ba, girman fadar ya kai na wani ɗan ƙaramin gari, kai tsayawa misalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar ya huce tunanin mutum sai dai abin da idanuwa suka gani kawai. Bisa kan wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta jauhari aka yi matattakala biyar da dutsen zubardaju. BABI NA UKU Wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance. Tana da matsakaicin kaurin jiki ita ba doguwa ba ce ba gajera ba, fatar jikinta fara ce mai ratsin baƙi, tana dara-daran idanuwa farare ƙwal masu haske tamkar tacecciyar madarar shanu, ɗigon cikin su yakasance baƙi siɗik, tana da dogon hanci mai ɗaukar hankali, a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur. wuyanta dogo ne mai kyawu tamkar na barewa, ƙirjinta a cike yake kuma tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, saboda rigar dake sanye a jikinta har kana iya hangen sheƙin fatar su. Cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya yi tudu ainun ta yadda koda kofin lemu aka ɗora zai zauna daram akai. Tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi masu ɗaukar hankali, yatsun hannuwanta da ƙafafuwa zara-zara ne, gashin kanta baƙi ne mai ƙyalli ya zuwa izuwa gadon bayan ta har zuwa kan kwankwasonta. sanye take cikin koriyar alkyabba mai ratsin fatsi-fatsi. sanye a kanta akwai kambun Sarauta da aka yi shi da zunzurutun zinare yana sheƙi da ɗaukar idanu. Wohoho! Haƙiƙa komai nisan gari da wani a gaban shi. Kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Komai hassadar mutum idan ya yi arba da wannan budurwa dole ne ya tabbatarwa da kanshi cewa ta kai maƙura a kyan diri da sura. Babban abin da ya ƙara tona asirin kyawunta shine duk sa'adda ta yi murmushi sai kyawawan fararen haƙoranta sun bayyana, fuskarta na fitar da sheƙin kyawu tamkar hasken farin wata. Babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kamu da matukar kaunarta. Ba wata bace wannan budurwa ba face Sarauniya Abidat. Sarauniya Abidat Bintu Hatyal ta kasance gawurtacciyar Basadaukiya mai dakawa maza gumba a hannu, ta shahara ainun a sanin ilimin tsafi gami da tarin dukiya, daɗin daɗawa kuma ta tara zakwakuran MAYAƘA masu juriya a filin daga. Bisa wannan dalili ya sanya take kai farmaki izuwa ƙasashe da biranen da ke maƙwabtaka da ita domin ta faɗaɗa girman masarautarta. Tsananin zaluncin Sarauniya Abidat ya zarce tunanin mutum, domin babu wanda ta ragawa tsakanin talakawanta, attajirai har ma da fadawanta. Akwai wata rana da Sarauniya Abidat ke zagayawa cikin kasuwa domin ganin yadda al'amuran cinikayya ke gudana. Tafe take a bisa ingarman doki cikin ƙayatattun tufafi ta rufe fuskarta da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, waɗansu irin gabza-gabza samudawan dakaru ne ke take mata baya, hannayen su ɗauke da miyagun makamai sai muzurai suke yi tamkar za su ci babu, kallo ɗaya za ka yi masu ka fahimci cewa murmushi bai taɓa wanzuwa a kan fuskokinsu ba. Duk wajen da Sarauniya Abidat da dakarun suka durfafa a kasuwar sai dai ka ga yara da manya na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin ladabi, kuma suna darewa suna buɗa masu hanya tamkar sun hango mutuwarsu, ko ciniki ake yi da zarar su Abidat sun durfafo wajen sai ka ga masu siye da sayarwa sun zubar da kayayyakin dake hannayensu, sun faɗi ƙasa sun kwashi gaisuwa. Haka dai Sarauniya Abidat da tawagarta suka ci gaba da tafiya suna ratsa layuka da unguwannin kasuwa. Ana cikin wannan tafiya ne Sarauniya Abidat ta hango wani dattijo yana gyara waɗansu kayan marmari a cikin kwandon kaba, har ya zaman tazarar dake tsakaninsu bata huce taku shida ba amma dattijon bai daina aikin da yake ba ya zo ya kwashi gaisuwa. Koda ganin hakan sai Abidat ta fusata ainun zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta kone bisa ganin yadda dattijon ya nuna rashin ladabi a gareta. Cikin matukar fushi Abidat ta kama linzamin dokinta ta sauko ta yiwa dakarun ta inkiya da wutsiyar ido. Tamkar dakarun sun san abin da take nufi sai kawai suka je suka cakumo wannan dattijo suka gurfanar da shi a gaban ta Kawai sai Abidat ta zaro wata 'yar siririyar wuka a damtse ta yanke kunnen dattijon na dama, saboda tsananin raɗadi da zogin da dattijon ya ji bai san sa'adda ya kurma wawan ihu ba a lokacin da jini kezuba daga wajen, cikin alamun rashin imani Sarauniya Abidat ta sake yanke masa dayan kunnen na ɓarin hagu jini ya yi tsartuwa gami da feshi. Haka ta ci gaba da yankewa dattijon ƙananan gaɓoɓin da ke jikinshi. Haƙiƙa Sarauniya Abidat ta cika AZZALUMA ta gaban kwatance, domin komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda dattijon ke ihu da koke-koken neman agaji dole ne ya tausaya masa ainun. Da yawa daga ckin jama'ar da abin ke wakana a kan idanuwansu ba su san sa'adda ƙwalla ta cika muasu idanu ba suka fara zubar da hawayen tausayi. Koda Sarauniya Abidat ta ga cewar ta yanke duk wata gaɓa da ke jikin dattijon sai kawai ta takarkare ta bushe da dariyar mugunta. A dai-dai wannan lokaci ne numfashin dattijon ya sarƙe jikinshi ya sandare ya faɗi ƙasa, alamar dake nuna rai ya yi halinshi. Kawai sai aka jiyo ihu da kururuwa a tsakiyar jama'a, koda Sarauniya ta duba sai ta ga ashe matar wannan dattijon ce ta rugo izuwa wajen, tana mai rusa kuka, hannayenta riƙe da jariri ɗan shekaru biyu da haihuwa. Kafin matar dattijo Safwan ta iso wajen, Sarauniya Abidat ta zaro wani dogon mashi a jikin badakaren ta jefawa matar, mashin ya tafi cikin matsanancin gudu a cikin iska ya soke a ƙirji, ya fasa ta gadon bayanta jini ya kwaranya gami da tsartuwa, take ta sulale ƙasa tana shure-shuren mutuwa, kafin wani lokaci idanuwanta sun ƙafe, komai na jikinta ya daina motsi, alamar ta baƙunci barzahu, amma wani abu da ya ɗaurewa Sarauniya Abidat da sauran jama'a kai shi ne, duk da kasancewar matar dattijo Safwan ta sheƙa barzahu babu rai a tare da ita, amma hannunta riƙe yake da jaririnta gam! Kuma fuskarta cike da annuri. Cikin matuƙar mamaki Sarauniya Abidat ta nuna jaririn da ɗan yatsan ta na hagu, take jaririn ya baro hannun mahaifiyarshi ya sauka a hannayenta biyu yana mai tsala kuka, koda ta ƙura wa jaririn idanu sai ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, al'amarin da ya yi matukar ba ta mamaki, kenan ta ce a cikin ranta, "Me ya sanya da na haɗa idanu da wannan jariri zuciyata ta buga da ƙarfi alhalin hakan bai taɓa faruwa a gare ni ba?" Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenan kawai sai ta miƙawa wani badakare jaririn, sannan ta kama linzamin dokinta ta hau, ta zabure shi ta shige gaba dakarun ta suka mara mata baya, yayin da aka isa gidan Sarauta sai Saruaniya Abidat ta bayar da renon jaririn ga wata baiwarta mai suna Sunaifa, daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana face bincike bisa halarar tsafinta domin ta gano sirrin da ke tattare da jaririn dattijo Safwan. Sa'adda ya rage saura kamar taku huɗu tsakanin su Sarki Urwat da karagar mulki sai suka zube ƙasa bisa gwiwoyinsu suka kwashi gaisuwa ga Sarauniya Abidat, cikin matuƙar taƙama da BAKAR IZZA Abidat ta karɓi gaisuwar. Shiru ne ya mamaye fadar na ɗan wani lokaci sai daga bisani ne Sarki Urwat ya dago da kanshi sama ya buɗi baki cikin ladabi ya ce "Ya shugabata gani na amsa kiran ki kuma tare da abin da ki ka buƙata domin FANSAR RAYUKAN jama'ata." Koda jin wannan batu daga bakin Sarki Urwat sai Sarauniya Abidat ta miƙe tsaye tsam! Daga kan karagarta ta tako matattakalar fadar ta sauko ƙasa, sannan ta taka da kafafuwanta har izuwa inda Sarki Urwat da jama'arshi ke duƙe ta shiga kewaya su tana mai bushewa da dariyar mugunta a lokaci guda kuma sai ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da SAKON MUTUWA ta dubi sarki Urwat ta ce "ya kai Urwat ka bi dukkanin wani umarni da muka baka sai dai a halin yanzu ina so ka umarci mutanen ka su fice daga birnin Nurul-Kusuf su nemi wajen da za su zauna." Koda jin wannan batu daga bakin sarauniya Abidat sai idanun sarki Urwat suka zazzaro, cikin alamun matuƙar kaɗuwa da firgici ya dubi sarauniya Abidat cikin biyayya ya ce. "Haba ya sarauniyar duniya ta ya ya zan cewa al'ummata su fice daga birnin Nurul-Kusuf bayan cewa tun iyaye da kakanni suke zaune sannan fiye da rabin harajin da na kawo miki sune suka haɗa rabinshi ina neman alfarma a wajen ki da ki janye wannan ƙudiri na ki." Da jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta bushe da dariyar mugunta a karo na biyu daga bisani ta haɗe rai ta ce, "Tabbas duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, kuma rashin sani ya fi dare duhu" ya kai Urwat ka yi sani cewa, tun da nake a rayuwata kai ne mutum na farko da na taɓa faɗar magana ya ce ba haka ba, yanzu zan gindaya maka sharuɗɗa guda biyu dole ne ka zaɓi ɗaya daga ciki. Na farko shi ne ko dai kai da jama'arka ku fice daga birnin Nurul-Kusuf ko kuma ku bayar da ZARATAN MAYAKAN KU mutum hamsin." Sa'adda Sarki Urwat ya ji waɗannan sharudɗa daga bakin Abidat sai ya sake marairaicewa, yana mai yiwa yi mata magiya a kan ta janye waɗannan sharudɗa na ta. Al'amarin da ya jefa tausayi a zukatan jama'ar kenan kuma zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su kone, bisa ganin yadda Urwat ke ƙasƙantar da kanshi a gaban wacce bata huce 'yar cikin shi ba. Su kansu sauran jama'ar fadar sai da suka kamu da matukar tausayin shi. Ya yin da Abidat ta fahimci cewa Sarki Urwat ba shi da niyyar amincewa da ɗaya daga cikin sharuɗɗan da ta gindaya mashi sai kawai ta yi wuf ta zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanta ta datse masa wuya, take kanshi ya yi fitar burgu gangar jikin ya faɗi ƙasa rikica! JINI ya yi tsartuwa haɗe da feshi tamkar an buɗe kan famfo. Kafin ɗaya daga cikin jama'ar marigayi sarki Urwat ya yi wani yunƙuri sarauniya Abidat ta afka masu da azababben yaƙi cikin abin da bai gaza daƙiƙa talatin ba gaba ɗaya ta sare kawunansu ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa ɗayan su bai tsira da rayuwarshi ba, nan fa jini ya dinga malala tamkar an ɓalle ƙorama. Sannan aka ga Abidat ta runtse idanunwanta ta karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai aka ga wani baƙin hayaƙi ya ratso daga cikin karkashin ƙasa ya tashi izuwa saman fadar ya ɓace ɓat! Kawai sai ta sake bushewa da dariyar mugunta tamkar ba za ta daina ba. BABI NA HUƊU A can birnin Nurul-Kusuf kuwa, shugaba Hushaib na zaune a fada bisa karagar mulki a matsayin halifan Sarki Urwat ana gudanar da sha'anin mulki cikin walwala. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! tamkar hadari ya gangamo, nan take gari ya kaure da guje-guje haɗe da iface-ifacen jama'a. Har shugaba Hushaib ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu sai aka hango sarkin yaƙi ya shigo fadar hankalinshi a matuƙar tashe, tun kafin ya iso inda karagar mulki take shugaba Hushaib ya je ya tare shi ya dube shi cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Ya dirkar birnin Nurul-Kusuf shin mene ne ke faruwa?" Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi Ikram ya dube shi cikin tashin hankali ya ce, "ya shugabana ka yi sani cewa tabbas yau ce rana ta farko da zamu fita yaƙi iya tsawon kafuwar wannan birni namu domin kuwa waɗansu irin halittu ne suka sauka a wannan birni namu, ni kaina tunda nake ban taɓa ganin irinsu ba ko a labari. Koda jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi Ikram sai shugaba Hushab ya dube shi cikin kaɗuwa ya ce, "Haƙiƙa na ji a jikina cewa shugaba Urwat da tawagarshi na cikin halin tsaka mai wuya kuma waɗannan halittu da suka bayyana a garemu ba sa rasa nasaba da abin da ya faru da su a can birnin Sin ɗin saboda haka sai ka yi umarni a yi maza a je a buga kugen yaƙi domin a tari abokan gaba..." Kafin shugaba Hushaib ya gama rufe bakinshi sarkin yaƙi ya juya, ya fice daga fadar da sauri. *** A can fadar sarauniya Abidat kuwa sai da tayi dariya ta ishe ta sannan ta yi umarnin a kwashe gawarwakin sarki Urwat da jama'arshi kuma aka goge jinin da ya zuba a fadar, sannan ta koma kan karagarta ta mulki ta hakimce. Kawai sai ta zura hannunta a cikin aljihunta na hagu ta ɗauko madubin tsafinta wanda duka tsawonshi bai wuce girman faɗin tafin hannunta ba ta shafeshi da hannun hagu tana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai ga taswirar abin da ke gudana a birnin Nurul-Kusuf ya bayyana a kan madubin. Sa'adda sarauniya Abidat ta ga yadda waɗannan miyagun halittu da ta tura ke hallaka jama'ar marigayi Urwat ba ji ba gani tamkar suna kashe kiyasai, hatta dabbobin garin ba sa ƙyalewa ballanatana ƙananan yara. Koda ganin wannan al'amari sai farin ciki ya cika zuciyarta haka dai ta ci gaba da kallon yadda artabun ke gudana har kawo izuwa lokacin da halittun suka kammala kashe duk wata halitta da ke birnin kasancewar su ma su shugaba Hushaib ba karamar ɓarna suka yi masu ba. Jim kaɗan sai taswirar birnin ya ci gaba da canja launi har ya nuno taswirar wata mata tana gudu a bisa doki, a cikin daji waɗannan halittu na biye da ita a baya suna so su cimmata amma sun gaza. Ba wata ba ce wannan mata ba face Suhaimat matar marigayi sarki Urwat, Suhaimat na cikin gudun ne ta iso wani waje mai tattare da kwazazzabai al'amarin da ya sanya gudun dokinta, ya ragu kenan, kuma ya bawa ɗaya daga cikin halittun dama ya samu nasarar mako ta daga kan dokinta. Kash! Hakika rashin sani ya fi dare duhu, ashe inda dokin Suhaimat ya durfafa wani ƙaton rami ne wanda a ƙarƙashin shi akwai ruwa, koda wannan halitta ta make Suhaimat daga kan dokin sai ta ci gaba da mirginawa a ƙasa ya yin da ta isa daf da ramin ta ga inda za ta afka sai kawai ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu take numfashinta ya ɗauke. Sa'adda taswirar ta zo dai-dai nan akan madubin tsafin sarauniya Abidat sai ta bushe da dariyar farin ciki, ta mayar da madubin izuwa cikin aljihunta sannan ta sake miƙewa tsaye tsam! Daga kan karagar mulkin ta ta durfafi wata ƙofa da za ta sada ta da gidan sarautar dakaru na take mata baya. Nan take sauran jama'a suka miƙe daga wajen zamansu suka fice daga fadar suna masu faɗar albarkacin bakunansu bisa wannan tsantsar zalunci da Abidat ta yiwa Sarki Urwat da talakawansuhi, wasu har suna rokon abin bautarsu da ya a kawo KARSHEN ZALUNCIn Sarauniya Abidat. Lokacin da Suhaimat matar Margayi Sarki Urwat ta faɗa izuwa cikin wannan rami mai zurfi cikin halin suma sai igiyar ruwa ta ci gaba da tafiya da ita, sai da gari ya waye sannan igiyar ruwan ta kawo gaɓar tekun, kusa da wani daji ma'abocin tarin bishiyu da duwatsu da ƙoramu, kuma ya tara kayayyakin ni'ima, waɗansu irin kyawawan tsuntsaye na shawagi a sama suna fitar da sauti mai daɗin sauraro. Ya yin da hasken rana ya fito sosai sai Suhaimat ta farka daga dogon suman da ta yi tana mai jan dogon gwauron numfashi, kuma ta buɗe idanuwanta ta miƙe zaune koda ta ga a inda take hawayen baƙin ciki suka zubo daga idanuwanta. A sannan ne ta ji yunwa da kishirwa sun addabeta kuma raunikan da ke jikinta suna yi mata raɗaɗi da zugi, don haka sai ta miƙe tsaye da ƙyar ta shiga izuwa dajin domin ta samu abin da za ta yi kalaci. Daga wannan rana Suhaimat ta kasance a cikin dajin ba ta da abokan ɗebe mata kewa face tsuntsaye, a duk sa'adda ta tuna maigidanta marigayi Sarki Urwat da jama'ar birnin su sai ta fashe da kukan baƙin ciki. Amma da zarar ta tuna cewa tana ɗauke da juna biyu sai ta cika da matuƙar farin ciki domin ta san cewa za ta haifi abin da zai dawo mata da farin cikinta kuma ya kawo KARSHEN ZALUNCIn Sarauniya Abidat Sa'adda Suhaimat ta fahimci cewa juna biyunta ya cika wata tara. A koda yaushe naƙuda za ta iya kamata ta haife abin da ke cikinta, sai ta yanke shawarar ta ci gaba da tafiya domin ta samu wani birni a gaba da za ta haife abinda take ɗauke da shi. Sai da ta shafe tsawon kwanaki huɗu tana tafiya a ranar kwana na biyar ne lokacin da rana ta take ta yi tsananin zafi Suhaimat ta iso wani kasaitaccen birni tun da ta shiga birnin ta kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni a iya tsawon rayuwarta bata taɓa ganin birnin da ya ƙawatu kamarshi ba, tana mai tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin wannan wane birni ne na shigo? Kuma a wace nahiyar nake. Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, kawai ta ci gaba da tafiya a cikin birnin, tana cikin tafiya ne ta zo giftawa ta cikin kasuwa sai ta ji waɗansu dattawa guda biyu suna hira a tsakanin su a inda ɗayan ya dubi ɗan uwanshi ya ce, "Shin wai kuwa ka ji labarin abin da ya faru da Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf da jama'ashi na kisan wulakancin da Sarauniya Abidat ta yi masu." Ɗayan ya ce, "Kwarai kuwa na samu labari kuma na jinjina al'amarin matuƙa, fatana shi ne a samu wani GWARZON ƘARNI da zai kawo maka KARSHEN ZALUNCIN wannan sarauniya tamu." Sa'adda Suhaimat ta ji abin da dattawan ke tattaunawa a kai sai zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone ta ji ta tsani sarauniya Abidat fiye da komai a rayuwarta. Kuma a sannanne ta fahimci wannan birni da ta shigo shi ne birnin Sin tana tana cikin wannan hali wani tunani ya faɗo mata, tunanin kuwa shi ne ya zama wajibi ki fice daga wannan birnin matsawar kina bukatar ki haife abin da ke cikinki, domin da dazarar Abidat ta ganki ba za ta bar ki a raye ba. Koda Suhaimat ta zo nan a tunaninta sai kawai ta ci gaba da tafiya da sauri domin ta fice daga birnin baki ɗaya. Wannan shi ne dalilin da ya sanya dakaru Sarauniya Abidat ke farautar wannan mata wato Suhaimat matar marigayi Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf. SHIN SUHAIMAT DA JARIRIYARTA NA TSIRA DAGA SHARRIN DAKARUN SARAUNIYA ABIDAT! WACE IRIN ƊAUKAKA JARIRIYAR SUHAIMAT ZA TA SAMU A DUNIYA? SHIN INA LABARIN ƊAN DATTIJO SAFWAN WANDA SARAUNIYA ABIDAT TA BAYAR DA RENONSHI GA BAIWA SUNAILA? WANE IRIN AZABABBEN YAƘI ZA A YI TSAKANIN DAKARUN SARAUNIYA ABIDAT DA WANNAN ZAKANYA? Mu hadu a KARSHEN ZALUNCI 2 na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari. BABI NA BIYAR Sa'adda aka ci gaba da kallon-kallon tsakanin dakarun ke biye da Suhaimat matar marigayi sarki Urwat da wannan zakanya. Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa talatin a na wannan kallo-kallo daga can sai dakarun suka zare makamansu suka zaburi dawakan su izuwa inda zakanyar take suna aihu da kururuwa mai firgitarwa. Koda ganin hakan sai zakanyar ta sake dako wawan tsalle a karo na biyu ta dira a tsakiyar dakarun, tana gurnani mai ban tsoro. Nan take aka ruguntsume da azababben yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro gami da ban al'ajabi. Wohoho! Tabbas mai ƙarfi sai Allan ya isa ana fara wannan artabu ne wani abin al'ajabi ya fara gudana, domin halitta guda ɗaya jal ta addabi mutum dubu biyu ta zame masu alaƙaƙai sun rasa yadda za su yi da ita. A duk sa'adda dakarun suka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙita haɗe da zamewa ta zillewa saran kafin badakaren ya sake ɗaga takobinshi, zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya farantata ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye take ya sulale ƙasa daga kan dokinshi yana mai kurma wawan ihu a wasu lokutan idan ta bangaji badakare a kirjinta take badakare da dokinshi za su make 'yan uwansa dakaru fiye da goma sun zube a ƙasa matattu, kai wasu lokutan ma idan ta daki badakare a wuya sai ka ji ya karye ya yi ƙara ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi matacce ko shurawa bai yi ba. Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba, domin kafin cikar rabin sa'a zakanyar ta kashe fiye da rabin su. Babban abin da ya dugunzuma hankalin dakarun kuma ya fusata su shine. Gashi dai ƙiri-ƙiri suna saran zakanyar da makaman su amma sun kasa koda kwarzanar jikinta, nan fa dakarun suka fusata ainun suka zage damtse suna kaiwa zakanyar miyagun hare- hare. Nan fa karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki ɗaya. Ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin turmutsutsu, kofatunsu na kartar kasa. Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan wuya ta kai wuya sai ka ga ZARATAN MAYAƘA suna neman cika wandunansu da iska domin TSIRA DA RAYUKAnsu. Hakanne kuwa ya faru ga sauran 'yan tsirarun dakarun domin koda suka ga cewa a kowanne lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska da nufin tserewa. Amma sai zakanyar ta dinga ƙure masu gudu tana turmushe su suna faɗuwa ƙasa matattu, kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa. Koda samun wannan nasara sai zakanyar ta yi girgiza sannan durfafi inda Suhaimat ke kwance tare da jaririyar ta, koda ta ga halin da Suhaimat ke ciki sai ta ruga izuwa bakin wata ƙorama ta guntso ruwa a baki sannan ta dawo inda take ta fesa mata ruwan a kan fuskarta. Faruwar hakan ke da wuya sai Suhaimat ta ja dogon gwauron numfashi gami da ajiyar zuciya, idanuwanta suka buɗe tarwai, kuma ta miƙe zaune ya yin da ta yi arba da wannan zakanya sai ta razana ta ja da baya tana mai ɗaukar jaririyarta ta ƙanƙame ta a kirji. Koda ganin halin da Suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan kogon dutse da ke cikin dajin. Cikin matuƙar farin ciki Suhaimat ta miƙe tsaye ta matsa izuwa inda wannan ƙorama take ta yiwa jaririyarta wanka itama ta tsaftace ƙazantar dake jikinta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin wata bishiya, ta zauna ta shiga shayar da jaririyarta tare da shafa gashin kanta zuciyarta cike da matuƙar farin ciki. Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin wane ne ya kashe waɗancan dakaru, ko kuwa wannan zakanyar ce?. Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, a cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo izuwa gare ta, bakinta riƙe da waɗansu ƙunshin ciyayi ta ajiye a gaban ta a wannan karon bisa mamaki sai Suhaimat ta ji ko kaɗan ba ta tsora ta da ganin zakanyar ba. Ba tare da fargabar komai ba Suhaimat ta ɗauki ta shiga warware ƙunshin, ai kuwa sai ta ga ashe nau'ikan kayan marmari ne a ciki, dangin su ayaba da inibi kawai ta shiga ci har sai da ta ƙoshi sannan ta fasa kwakwa ta shanye ruwanta zakanyar na tsaye a gefen ta tamkar mai jiran umarni, a sannan ne ta lura cewa a jikin zakanyar akwai alamun jini take ta fahimci cewa ita ce ta hallaka waɗannan dakaru domin ta ceci rayuwarta da jaririyarta. BABI NA SHIDA Dukkanin abin da ya wakana tsakanin Suhaimat, zakanya da dakarun sarauniya Abidat. Abidat ta gani a cikin madubin tsafin ta tun daga farko har ƙarshe. Koda ganin wannan al'amari sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kurma wawan ihu. Ba komai ne ya sanya ta wannan baƙin ciki ba, sai domin ta tabbatar da cewa a halin yanzu Suhaimat da jaririyarta sun tsira daga sharrinta. Babban abin da ya dugunzuma hankalin ta kuma ya jefata cikin damuwa ainun shi ne wani al'amari da ta gani a cikin madubin tsafin ta. Ta gano cewar wannan jaririya da Suhaimat ta haifa ita ce za ta kawo KARSHEN ZALUNCIn ta daga doron ƙasa. Asalin dajin da Suhaimat ta haihu a ciki ya kasance mallakin wannan zakanya mai tattare da abubuwan al'ajabi ana kiranta da suna Juraima. Binciken bokaye da MATSAFAN DUNIYA ya tabbatar da cewa dajin Baitul-Shazwas na ɗauke da wata takobi ta musamman mallakin sarkin bokayen aljanu na duniya Sababul-Ukub, babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki takobin face ya zamewa duniya ANNOBA DARI. MANYAN SARAKAI haɗe da matsafa da JARUMAN DUNIYA sun rasa rayukansu bisa muradin mallakar takobin, domin zakanya Juraima ba ta barin duk wanda ya raɓi dajin a raye. Bisa dole bokayen suka janye ƙudurinsu na shiga dajin Baitul Shazwas domin mallakar takobin Saiful-Imfal. Abinda binciken ya ƙara tabbatar masu shi ne babu wani mahaluki da zai mallaki takobin Saiful Imfal da zakanya Juraima face wata jariya da za a haifa a dajin na Baitul Shazwas, sai dai ba a bayyana masu ga nahiyar da za a haifi jaririyar ba. kuma zakanya juraima na ɗauke rabin sirrikan tsafin sarkin bokaye a jikinta, takobin Saiful-imfal na ɗauke da sauran. Tsakanin Sarauniya Abidat da zakanya Juraima akwai gaba mai tsanani tun iyaye da kakanni, domin mahaifinta da kakanta sun rasa rayukansu ne ta hanyar mallakar takobin Saiful Imfal, kuma lokacin da mahaifinta yana raye ya gargaɗe ta a kan kar ta kuskura ta ce za ta shiga dajin Baitul-Shazwas domin ɗaukar fansa. Nan fa Sarauniya Abidat ta ƙara cika da matuƙar baƙin ciki tana mai tambayar kanta a cikin ranta tana cewa. "Hakika na tafka babban kuskure da har na bari Suhaimat ta shiga dajin Baitul-Shazwas yanzu gashi ta haife abin da ke cikinta yanzu shi kenan ba ni da ikon hallaka Suhaimat da jaririyarta har sai ranar da ta fito daga dajin Baitul Shazwas." Daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana bata aiki face gudanar da bincike a halarar tsafinta, domin ta gano lokacin da Suhaimat za ta fito daga dajin Baitul Shazwas. Bayan Suhaimat ta kammala kintsa cikinta da waɗannan kayan marmari sai Zakanya Juraima ta juya, ta nufi kofar wannan kogon dutse tana mai yiwa Suhaimat nuni da ta biyo bayanta. Ba tare da gardamar komai ba Suhaimat ta miƙe tsaye ta bi bayanta tana rungume da jaririyarta a kirji, da shigarsu cikin kogon dutsen sai ke da wuya sai Suhaimat ta ga kogon ya gauraye da wani irin haske na ban al'ajabi, sannan yana cike da dukkanin kayan more rayuwa da ɗan adam zai bukata, kai wani abin ma Suhaimat ba ta taɓa gani ko jin sunan shi ba. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaure mata kai kenan kuma ya ba ta mamaki ta kama kalle-kalle da dube-dube. Ba tare da ta jira wani umarni daga Zakanya Juraima ba sai kawai ta je ta kwantar da jaririyarta bisa wata shimfiɗa ta lulluɓe ta da mayafi sannan itama ta kwanta domin ta rintsa amma sai hakan ya gagara, ba komai ne ya haddasa hakan ba, sai domin raunukan da ke jikinta na yi mata zugi da raɗaɗi kuma inda wannan badakare ya harɓe ta da kibiya yana yi mata ciwo. Sai da zakanya Juraima ta kawo mata wani ganyen bishiya ta murza ta sanya a raunukan, sannan ta kwanta barci ya ɗauke ta. Wannan shi ne abin da ya faru da Suhaimat matar marigayi sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf a lokacin da ta tsira daga sharrin sarauniya Abidat ta birnin Sin. BABI NA BAKWAI Al'amarin baiwa Sunaila kuwa tun sa'adda sarauniya Abidat ta bata renon jaririn dattijon Safwan, sai ya zamana cewa dare da rana tana bawa jaririn kulawa, kuma suka shaƙu da juna ainun ya yi wayo sai Sunaila ta sanya masa suna Himlas, ma'ana ma'abocin hikima da abubuwan al'ajabi, domin tun yana da shekaru huɗu ta fahimci cewa yana tattare da kaifin basira da jarumtaka. Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai gashi Himlas ya girma ya zama cikakken saurayi. Nan fa ya zamana cewa ya zama zarra a tsakanin sauran 'yan uwanshi bayi, a wasu lokutan idan suna ba wa juna horon yaƙi suka yi masa rubdugu amma sai ka ga ya tarwatsa su ta karfin tsiya. Wata rana Himlas ya dawo daga farauta yana zaune tare da baiwa Sunaila a cikin ɗaki sai ya lura cewa tana cikin damuwa. Don haka sai ya dube ta ya ce "Ya Ummina shin mene ne dalilin wannan damuwa ta ki?" Koda jin wannan tambaya sai baiwa Sunaila ta yi murmushi a gare shi, mai tattare da takaici sannan ta sanya hannayen ta biyu ta dafa kafaɗunshi ta dube shi cikin alamun tsananin damuwa ta ce. "Ya ɗana abin alfaharina ki yi sani cewa ba komai ne ya sanya ni a cikin wannan damuwa ba sai domin na san cewa duk daren daɗewa ɓoyayyen sirrin da na daɗe ina ɓoye maka zai fito fili ƙarara." Koda jin wannan batu sai idanun Himlas suka zazzaro cikin tsoro ya kama sa cikin alamun rashin fahimta ya dubi Sunaila ya ce. "Ya Ummina ban fahimci abin da kike nufi ba, shin wane sirri ne ki ke son bayyana mani." Sunaila tayi ajiyar zuciya sannan ta kawo gwauron numfashi, ta ajiye kana ta yi gyaran murya ta ce, "ya ɗana ka yi sani cewa a yau ne zan bayyana maka sirrin da na daɗe ina ɓoye maka, ya farin ciki na ka yi sani cewa kamar yadda kake tsammani cewa ni ce mahaifiyarka to ba ni ce na haife ka ba." Nan take Sunaila ta kwahse labarin kaf abin da ya faru tsakanin dattijo Safwan da Sarauniya Abidat da irin mugun kisan gillar da ta yiwa mahaifinsa tun daga farko har ƙarshe ta zayyanewa bawa Himlas. Sa'adda baiwa Sunaila ta zo dai-dai nan a labarinta sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya shima Himlas bai san sa'adda ya fashe da kukan ba, yana mai rungume ta yana mai cewa "ba zan taɓa canja ki ba har abada ke ce Ummina." Inda ace mutum yana wannan waje lokacin da wannan al'amari ke faruwa dole ne ya kamu da tsananin tausayin Sunaila da bawa Himlas. Sai da suka ɗauki wani lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani Sunaila ta janye jikinta daga na Himlas ta dube shi a lokacin da hawaye ke ci gaba da kwaranya daga idanunta ta ce. "Ya ɗana ka yi sani cewa ba komai ne ya sanya na ɓoye maka wannan sirri ba sai domin ba na so ace na rasaka a rayuwata, a halin yanzu kai kaɗai ne ka rage mini ba ni da kowa." Da jin wannan batu sai hawaye suka sake zubowa daga idanun Himlas ya ji ya tsani Sarauniya Abidat fiye da komai rayuwar shi. Sunaila ta sanya hannunta ta share hawayen da ke fuskarta, sannan ta ci gaba da cewa, "Duk abinda za ka yi ina roƙon ka kada ka ce za ka ɗauki fansa a kan sarauniya Abidat a halin yanzu domin ba za ka taɓa samun nasara ba, jikina ya ba ni cewa akwai wani ma'abocin ɗaukaka da zai zo ya cire mu daga cikin wannan KANGIN BAUTA kuma ya taimake ka ka kawo KARSHEN ZALUNCI na sarauniya Abidat." Sa'adda Sunaifa ta sake zuwa dai-dai nan a zancen ta sai Himlas ya sanya hannunsa ya share mata hawayen da ke fuskarta yana mai cewa, "Ki daina kuka ya ummina duk abin da ki ka ce shi za a yi domin farin cikin ki shi ne nawa." Koda Himlas ya zo nan a zancen shi sai Sunaila ta sake fashewa da kukan farin ciki tana mai sake rungume shi tana cewa, "Ina alfahari da kai ya ɗana kai ne cikar burin rayuwata na tabbata cewa kai ne za ka kawo KARSHEN ZALUNCIn sarauniya Abidat daga doron kasa." Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin baiwa Sunaila da Bawa Himlas dan dattijo Safwan, wanda Sarauniya Abidat ta bayar da renonsa a hannun Baiwa Sunaila bayan ka yiwa mahaifinsa kisan gilla. BABI NA TAKWAS A can dajin Baitul-Shazwas kuwa, Suhaimat da jaririyarta na cikin ƙoshin lafiya walwala da jin daɗi. Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai kwanci tashi sai ga shi jaririyar Suhaimat ta cika shekara sha biyar da haihuwa, da ranar haihuwar ta zagayo ne aka raɗawa jaririya suna Sulairat bintu Urwat. Kyan ɗa ya gaji ubanshi, kamar yadda marigayi sarki Urwat ya kasance GWARZON MAYAƘI ma'abocin hikima, haka Sulairat ta kasance. Wasu lokutan idan Sulairat da zakanya Juraima na bawa junansu horon yaƙi sai ka ga Sulairat ɗin ta samu nasara akan Juraima. kasancewa Sulairat ba ta da abokan ɗebe kewa sai zakanya Juraima sai suka shaƙu ainun kwanciyar barci ce kaɗai ke raba su ko farauta Sulairat za ta je bisa gadon bayan Juraima take hawa su tafi tare. Idan a kazo batun kyawu kuwa Sulairat ta gaji mahaifiyarta Suhaimat har ta ɗarata ne sa ba kusa ba, kasancewar a koda yaushe ba su da wani abin kalaci da ya wuce naman tsuntsaye da nau'ikan kayan marmari sai ya zamana cewa fatar jikinta ta yi lub-lub ta yi kyau da sheki tamkar a tsaga ta jini ya fito. Wata rana da hantsi bayan Sulairat da mahaifiyar ta sun yi kalaci suna zaune a cikin wannan kogon dutse sai Sulairat ta dubi mahaifiyarta ta yi gyaran murya sannan ta ce. "Ya Ummina shin ina Abbana yake, ya tafi ya bar mu a cikin wannan daji, ko kuwa mu kaɗai ne bil'adama a wannan duniya?" Koda jin wannan tambayoyi sai Suhaimat ta yi murmushi mai taushi a gare ta, sannan ta dubeta ta ce, "Ke kuwa me ya sa ki ka yi mini waɗannan tambayoyi, bayan cewa kina tare da ni ina yi miki duk wani abu da ki ke buƙata na rayuwa." Sulairat ta ce "ya ummina ke kuwa mene ne ya sa duk sa'adda na yi maki waɗannan tambayoyi ba kya amsa su, tabbas akwai wani al'amari da kike ɓoye mini wanda ba kya so na sani." Koda ji wannan batu sai zuciyar Suhaimat ta buga da ƙarfi kuma hankalinta ya dugunzuma ainun ta ce a cikin ranta, tabbas rashin bayyana wa Sulairat gaskiyar lamari na iya sanyawa mutuncina ya ragu a idanunta, sannan kuma idan har na sanar da ita dole ne ta ce za ta je ta ɗauki fansa. Wani ɓangaren a zuciyarta kuma na cewa da ita ai babu wata mafita face ki sanar da Sulairat gaskiyar lamari, domin ai duk daren daɗewa dole ne ta sani. Koda Suhaimat ta zo daidai nan a tunaninta sai ta dubi Sulairat ta ce "Ya 'yata ki yi sani cewa a yau ne zan ba ki amsar tambayoyin da ki ka daɗe kina yi mani, na cewa ina abbanki yake." Nan take Suhaimat ta shiga bawa Sulairat labarin mahaifinta sarki Urwat da irin kisan gillar da Abidat ta yi mashi tare da jama'ar birnin su, har kawo izuwa lokacin da zakanya Juraima ta ceci rayuwar su daga sharrin dakarun Abidat daga farko har ƙarshe ta zayyanewa Sulairat. Sa'adda Suhaimat ta zo dai-dai nan a labarin ta sai ta fashe da kukan baƙin ciki tana mai rungume 'yarta su duka biyun suna zubar da hawaye tamkar ba za su daina ba. Sai daga bisani ne Suhaimat ta janye jikinta daga na Sulairat har ta buɗe baki da nufin ta ce wani abu sai suka ji alamun motsi a bayansu, koda suka waiga sai suka ga ashe zakanya Juraima ce a tsaye idanunta sharkaf da hawaye. Al'amarin da ya yi matuƙar bawa Sulairat da mahaifiyar ta mamaki kenan, abinda ba su sani ba shi ne dukkanin hirar da ta gudana tsakaninsu zakanya Juraima ta ji, saboda haka tsananin tausayinsu ne itama ya sanya ta zubar da wannan hawaye. Suhaimat ta ci gaba da cewa, "Ba komai ne ya sanya na ɓoye miki wannan sirri ba, sai domin sanin cewa za ki iya yunƙurin ɗaukar fansa a kan sarauniya Abidat a halin yanzu. "Ina so ki kwantar da hankalinki ki sani cewa lokaci zai zo da za ki shiga har cikin birnin Sin ki ɗauki fansa a kan Sarauniya Abidat ki kawo KARSHEN ZALUNCIn da take shimfiɗawa al'umma." Da jin wannan ƙarin wajabi sai Sulairat ta ji ta daɗa ƙaunar mahaifiyarta fiye da ko yaushe. Sannan ta sake duban mahaifiyarta ta ce "Ya Ummina idan ba za ki damu ba ina neman wata alfarma a wajenki." Cike da matuƙar mamaki Suhaimat ta dube ta ta ce "faɗi alfarmar da kike nema a waje na ni kuwa zan yi miki ita." Sulairat ta numfasa sannan ta gyaɗa kai ta ce, "alfarmar da nake nema a wajen ki ita ce ki amince na shiga birnin Sin domin kawai na ga yadda sauran bil'adama irinmu ke rayuwa." Koda jin wannan alfarma sai Suhaimat ta dubi 'yarta cikin alamun tsananin damuwa ta ce, "Haba ya 'yata yanzu ta ya zan bar ki ki ziyarci birnin Sin bayan cewa a koda yaushe Sarauniya Abidat na farautar rayuwarki." Ya yin da Sulairat ta zo nan a zancen ta, sai ta hango zakanya Juraima na yiwa Sulairat nuni da ta zo inda take. Ba tare da gardamar komai ba Sulairat ta miƙe tsaye ta taka da kafafuwanta har zuwa inda zakanya Juraima ke tsaye, da zuwanta sai Juraima ta yi mata nuni da ta tona wani waje a kogon da ke saitin kafarta. Cikin hanzari Sulairat ta tsugunna ƙasa ta sanya hannayenta biyu tana ƙwakule kasar wajen ta yi rami da girmanshi bai huce kamu ɗaya ba, sai ta ji ta taɓo wani abu tamkar ƙarfe ya yin da ta ciro shi, sai ta ga ashe wata sarƙa ce fara sol da aka yi ta da ƙarfe jauhari, sai sheƙi take yi tana ɗaukar idanu. Kawai sai zakanya Juraima ta yi mata nuni da ta sanya sarƙar a wuyanta. Sannan Juraima ta yi wa Suhaimat ishara da ta ƙyale Sulairat ta ziyarci birnin Sin tana yi mata nuni da cewa wannan sarƙa da Sulairat ta sanya a wuyanta za ta bata kariya har ta je ta dawo lafiya. Koda fahimtar hakan sai Suhaimat ta dubi 'yarta ta ce "Na amince ki ziyarci birnin Sin kuma ina yi maki fatan samun nasara." Da jin hakan sai murna ta kama Sulairat ta yi godiya ga mahaifiyrta sai ta juya ta fice daga kogon dutsen, sai da zakanya Juraima ta yi mata rakiya har izuwa gaɓar dajin Baitul-Shazwas sannan ta dawo bayan ta dora ta a kan hanya. Kai tsaye Sulairat ta tasamma hanyar da za ta sadata da birnin Sin tun a kan hanya ta fara cika da matuƙar mamaki har ta isa birnin Sin domin sau tari za ta haɗu da miyagun namun daji amma sai ta ga sun ratse sun ba ta hanya, tamkar ba su ganta ba, ƙiri-ƙiri gashi masu gadin ƙofa na ganinta amma haka ta kunna kai zuwa ciki ba tare da sun yi yunƙurin afka mata da yaƙi ba, da shigarta zuwa birnin sai ta kama kalle- kalle da dube-dube tamkar dan ƙauye ya shigo birni. Abin da Sulairat ba ta sani ba shi ne matsawar tana sanye da wannan sarka da zakanya Juraima ta ba ta, babu wani mai cutarwa da ya isa ya ganta, ya kusanci inda take ballantana har ya cutar da ita. Haka dai Sulairat ta wanzu tana tafiya a cikin birnin Sin ta wanzu tana ratsa layuka da unguwanni, ba tare da ta haɗu da wani abu mai cutarwa ba. Tana cikin tafiya a kasuwa ne sai kawai ta hango jama'a suna guje-guje da iface- iface, maza da mata yara da manya. Nan fa aka dinga barin kayan abinci, masu ƙarfi suka dinga bangaje masu rauni suna zubewa a kasa ana tattaka su. Al'amarin da ya yi matuƙar bawa Sulairat mamaki kenan, kawai sai ta koma gefe guda ta ja ta tsaya, tana mai zuba idanu, domin ta ga abinda ya sanya jama'a suke GUDUN CETON RAYUKA. Tana nan tsaye kwatsam sai ta hango dakaru masu tarin yawa shirye cikin matsananciyar shigar yaki sun shigo kasuwar su bisa tsakiyar dakarun wani ƙasaitaccen keken doki ne da aka yi mata ado kayan kyale-kyale na sarauta. Bisa cikin keken dokin wata budurwa ce a kishingiɗe sanye da tufafi na alfarma. Budurwar ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance, ma'abociyar dara-daran idanuwa farare kal a cikin su akwai ɗigon baƙi, hancinta siriri ne gwanin ban sha'awa, tana da madaidaicin baki wanda leɓɓanshi suka kasance jajur, ƙirjinta a cike kuma ya tsaya kyam! Tamkar nunanniyar gwanda fatarsu tana sheƙi da ɗaukar hankalin duk mai kallo. Sun cika tsaleliyar rigar jikinta tamkar za su fito waje, Gashin kanta baƙi sidik mai ƙyalli da sheƙi ya zuba har izuwa kan kafaɗunta. Haƙiƙa duk inda kyawu yake wannan budurwa ta kai maƙura domin duk irin tsantsar kyawu na Sulairat da ta yi arba da wannan kyakkyawar halitta sai da ta raina kanta ta tabbatar da cewa gaba da gabanta aljani ya taka wuta." Ba wata ba ce wannan kyakkyawar budurwa da ke kishingiɗe a cikin keken dokin ba face Sarauniya Abidat. Sulairat ta ƙurawa budurwar idanu ta sa kare mata kallo, a sannan ne ta fahimci cewa wannan budurwa ba wata ba ce face Sarauniya Abidat wacce take neman ta ruwa a jallo. Nan fa zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone kuma ta ji ƙiyayyar Abidat ta daɗu ainun a zuciyarta. Ya yin da ya zamana cewa sarauniya Abidat da dakarunta sun matso daf da inda Sulairat take tsaye, sai Sulairat ta hango wani zabgegen kyakkyawan saurayi jikinshi ko riga babu face bante da ya rufe cibiyarshi zuwa cinyarshi, gashin kanshi ya zubo izuwa kan fuskarshi, hannayenshi da kafafuwanshi sanye suke cikin da sasari na baƙin ƙarfe yana jan keken dokin da Sarauniya Abidat ke ciki a maimakon ace dawakai ne ke janye da keken. Nan fa Sulairat taji ta kamu da matuƙar tausayin saurayin, kuma ta tabbatarwa da kanta cewa, tabbas duk inda mutum ke tsammanin zaluncin Sarauniya Abidat ya wuce nan. Ana cikin wannan hali ne wannan kyakkyawan sarauyi da ke janye da keken dokin ya dago da kanshi sama, ya kalli inda Sulairat ke tsaye sadda suka yi arba da fuskokin juna sai nan take a karo na farko a rayuwarsu suka ji sun kamu da matuƙar ƙaunar junansu, Sulairat ba ta san sa'adda ta sakarwa sarauyin wani tattausan murmushi ba mai tattare da tsantsar so da ƙauna. Bisa mamaki sai Sulairat ta ga saurayin ya mayar mata da martanin murmushin, kuma ya tsaya cak daga jan keken dokin yana ci gaba da sakar mata lallausan murmushi. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Abidat kai kenan, kuma ya fusata ainun ta dakawa badakaren dake kula da keken dokin tsawa. Abin da ya ɗaure mata kai kuma ya bata mamakin shi ne ita dai ta duba ba ta ga komai ba amma mene ne ya sanya bawa Himlas kw kallon wajen yana murmushi, abin da ya fusatat a kuwa shi ne ta ya Himlas zai daina tuka keken dokin. Kafin sarauniya Abidat ta gama rufe bakinta badakaren dake kula da keken dokin ya daga bulalarshi sama ya zabgawa bawa Himlas, take inda ya dake shin ya dare jini ya yi tsartuwa ya zuba a ƙasa, amma har sai da badakaren nan ya yi mashi bulalar fiye da talatin amma Himlas bai daina kallon wajen da Sulairat take ba yana yi mata murmushin. A ɓangaren Himlas kuwa, babban abin da ya ɗaure mashi kai kuma ya ba shi mamaki shi ne gashi dai kuru-kuru dakarun sarauniya Abidat na kallon na Sulairat amma ba su yi yunƙurin cutar da ita ba. Koda Sulairat ta fahimci cewa matsawar wannan saurayi bai daina kallonta ba to wannan badakare ba zai daina dukanshi da bulala ba. Sai kawai ta juya ta nufi hanyar da za ta fitar da ita daga birnin tana mai waigen saurayin suna jifan junansu da ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar soyayya. Sai da Sulairat ta ɓace ɓat! Sannan bawa Himlas ya yunƙura cikin juriya da jarumtaka ya ci gaba da jan keken dokin, a lokacin da raunukan da badakaren ya yi mashi suka shiga yi mashi zugi da raɗaɗi, ga zafin rana na ƙona tafin kafarshi. Komai rashin imanin mutum babu yadda za a yi ya ga bawa Himlas a cikin wannan hali face ya kamu da matukar tausayinsa. BABI NA TARA A can dajin Baitul-Shazwas al'amarin Sulairat kuwa tun sa'adda ta fice daga birnin Sin zuciyarta cike da matuƙar ƙaunar bawa Himlas, sai ta ci gaba da saƙe-saƙe a zuciyarta har ta isa dajin Baitul Shazwas, da zuwanta sai suhaimata da zakanya Juraima suka tare ta cikin tsananin farin ciki suna yi mata sannu da dawowa. Da yake a wannan lokaci duhun magariba ya kawo kai Suhaimat ta shiga haɗa masu abin kalaci, bayan da ta kammala ne sai ta zauna tare da 'yarta Sulairat domin su fara cin abincin. Suna fara cin abincin ne Suhaimata ta lura cewa Sulairat na cikin damuwa, domin har sai ta yi loma biyar ba ta yi guda ɗaya ba, don haka sai kawai ta dube ta ta ce "Ya 'yata abar alfaharina shin ina dalilin wannan damuwa ta ki?" Koda jin wannan tambaya sai Sulairat ta yi murmushi ga mahaifiyarta sannan ta ce "Babu wani abu da yake damuna ya immi kawai sai ina tuna irin zaluncin Sarauniya Abidat ne." Suhaimat ta yi murmushi da yake nuna fahimtar wani abu game da furucin 'yarta ta dube ta a karo na biyu ta ce. "Ya 'yata bai kamata ace kin ɓoye mani gaskiyar abin da yake damunki ba, domin kar ki manta cewa baki da kowa a duniya face ni kaɗai, bisa ga yadda fuskarki ta nuna alamu ba komai ne ya haddasa miki damuwa ba face tarkon soyayya ko ba haka ba ne?." Koda jin wannan batun sai kunya ta kama Sulairat ta sunkuiyar da kanta ƙasa tana mai cewa, "ki gafarce ni ya ummina, haƙiƙa na yi kuskure da na ɓoye maki gaskiyar abin da yake damuna." Suhaimat ta dafa kafaɗun 'yarta Sulairat da hannayenta biyu ta ce, "Ya 'yata ki yi sani cewa ba wai zan hana ki ki yi soyayya ba ne, sai dai ina gargaɗin ki da ki kiyayi so, domin babu komai a cikinsa face tsantsar wahala da takaici." Cikin alamun matuƙar mamaki Sulairat ta dubi mahafiyarta ta ce, "Ya Ummina shin ta ya ya so zai zama tsantsar wahala da takaici, bayan cewa rayuwar ɗan adam tana tabbata ne idan akwai so." Suhaimat ta yi lallausan murmushi mai taushi a gareta ta ce, "Kwarai kuwa maganarki gaskiya ce amma da a ce kin karanta hikayar manyan sarakunan duniya uku dake cikin KUNDIN HIKAYA haƙiƙa da kin gasgata abin da na faɗa miki." Da jin hakan sai mamaki ya kama Sulairat ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tana cewa, "Shin me ya faru da manyan sarakai uku me so ya zamo masu a rayuwa?" Amsar tambayoyin da Sulairat ta kasa bawa kanta kenan kawai sai ta ɗauraye hannunta da ruwa a cikin wani ɗan ƙaramin akushi, sannan ta je inda shimfiɗarta take ta kwanta, domin ta huce gajiyar da ke tattare a jikinta, amma sai ta kasa rintsawa, ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsananin bege da tunanin bawa Himlas, domin duk abin da ta kalla a kogon dutsen sai ta ga fuskar bawa Himlas take gani yana yi mata murmushi mai taushi, haƙiƙa Sulairat ta yi zurfi a kaunar bawa Himlas wacce ba za ta taɓa jin kira ba, haka ta kasance a cikin wannan hali har barci ya yi awon gaba da ita. Wannan shi ne abin da ya faru da Sulairat bayan ta dawo daga ziyara izuwa birnin Sin. BABI NA GOMA A can brinin Sin kuwa, washegari tunda duku-dukun safiya fadar Sarauniya Abidat ta cika ta batse da jama'a maza da mata yara da manya, duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu masaka tsinke tamkar dandazon kiyasai. Abin tambaya anan shi ne ko me ya sanya jama'ar barin gidajensu suka halarci wannan fada tunda duku-dukun safiya haka?. Ba komai ne ya sanya hakan ba sai domin a yau ne sarauniya Abidat za ta yankewa baiwa Sunaifa da bawa Himlas hukuncin kisa ta hanyar sare masu wuya. Bisa wani BOYAYYEN AL'AMARI da ta gano a cikin halarar tsafinta a daren jiya, abinda ta gano din kuwa shi ne. Ba wani abu bane ya sanya bawa Himlas yake wannan murmushi a jiya a lokacin da suke tafiya a cikin kasuwa ba har ya dai na jan keken dokin da take kai ba face arba da ya yi da Sulairat, har suka kamu da soyayyar junansu. Abin da zai ƙara tabbatar maka da hakan shi ne idan ka yi duba izuwa ga waɗansu manyan diraku da ke tsakiyar fadar, za ka yi arba da bawa Himlas da baiwa Sunaila ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa. Fiye da tsawon rabin sa'a jama'a na cece-kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi bisa jinkirin fitowar Sarauniya Abidat. Ana cikin wannan hali ne sai aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura daga cikin gidan sarauta alamar ga Sarauniya Abidat nan tana gab da bayyana. Jim kaɗan sai ga Sarauniya Abidat tare da muƙarrabanta sun kunno kai izuwa cikin fadar waɗansu gabza-gabzan samudawa dakaru ma'abota baƙaƙen tufafi na take masu baya, a wannan lokaci sarauniya Abidat tana sanye da shuɗiyar alkyabba mai ratsin ruwan zinare da ta kama jikinta, surorinta suka bayyana ainun kanta sanye da kambu na sarauta fuskarta a murtuke babu annuri. Kai tsaye ta huce izuwa inda karagar mulkinta take ta taka matattakalar fadar ta juya tana mai fuskantar jama'a, nan take fadar ta yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Sarauniya Abidat ta sake murtuke fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA ta buɗi baki cikin kakkausar murya sannan ta ce, "Ya ku jama'ar wannan fada tawa mai albarka ku yi sani cewa, ba komai ne ya sanya na taraku anan ba sai domin ku ganewa idanuwanku irin hukuncin da zan yankewa bawa Himlas da baiwa Sunaila bisa mummunan laifin da Himlas ya aikata mani na kin bayyana min abokiyar gaba ta Sulairat 'yar marigayi sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf a lokacin da yake jan keken doki na a cikin kasuwa." Sa'adda sarauniya Abidat ta zo dai-dai nan a jawabinta sai fadar ta kaure da cece-kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi. Zukatansu cike da matuƙar takaici gami da baƙin ciki bisa hukuncin da Abidat za ta zartarwar bawa Hilmas da Sunaifa. Ya yin da Sarauniya Abidat ta ga fadar ta kaure da hayaniya sai kawai ta daga hannunta sama, jama'a suka yi shiru, sannan ta ci gaba da cewa. "Sanin kanku ne cewa a iya tsawon rayuwata ba a taɓa aikata mani laifi mafi muni da ya huce wanda Himlas ya aikata min ba, saboda haka a yanzu zan zartar masu da hukuncin kisa ta hanyar sare masu wuya." Koda gama faɗin hakan sai sarauniya Abidat ta koma kan karagarta ta hakimce, kawai sai wani basamuden ƙato ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi mai tsawo da kaifin tsiya, ya durfafi inda Himlas da Sunaifa ke ɗaure, yana huci tamkar zai ci babu ya yin da ya isa daf da inda suke sai kawai ya daga takobin domin ya datse wuyan bawa Himlas, a dai-dai lokacin da baiwa Sunila tare da wasu daga cikin jama'ar fadar suka fara zubar da hawaye saboda tausayi. SHIN WANNAN BASAMUDEN ƘATON YANA SARE WUYAN BAWA HIMLAS DA BAIWA SUNAILA? SHIN YAUSHE NE SULAIRAT ZA TA ƊAUKO TAKOBIN SAIFUL-IMFAL DAKE CIKIN DAJIN BAITUL SHAZWAS? YAUSHE NE ZA TA SHIGO HAR CIKIN BIRNIN SIN DOMIN TA ƊAUKI FANSA AKAN SARAUNIYA ABIDAT? A WANE HALI ZA TA KASANCE NA KAMUWA DA MATUKAR SOYAYYAR BAWA HIMLAS? Mu haɗu a ƘARSHEN ZAMUNCI littafi na uku domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari. Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi ƘARSHEN ZALUNCI Littafi na uku Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 BABI NA SHA ƊAYA Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu masifaffun kibbau sun soke badakaren a idanuwanshi ya kurma wawan ihu ya zube ƙasa yana shure-shure take jikinshi ya sandare ya sheƙa barzahu. Cikin hanzari mutane suka waiga bayansu domin su ga wane ne ya harbo kibbau ɗin. Ai kuwa koda suka yi tozali da ko mene ne sai suka yi turus! Bakomai suka gani ya ba su mamaki ba face wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa. Budurwar takasance mai matsakaicin kaurin jiki ba doguwa ba ce ba gajera ba. Tana da dara-daran idanuwa farare ƙal! Masu haske tamkar tacecciyar madarar shanu, hancinta dogo mai lankwasa a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur, wuyanta dogo mai kyawu tamkar na barewa, ƙirjinta a cike yake kuma a tsaye ƙyam basu ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda saboda kyawun su, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya yi tudu ainun ta yadda koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi masu ɗaukar hankali, babban abin da ya ƙara tona asirin kyawunta shine dogon gashin kanta baƙi siɗik mai ƙyalli ya zuba har izuwa kan kwankwasonta. Wohoho! Haƙiƙa wannan budurwa ta cika maƙura a kyawu, domin babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi arba da ita face ya kamu da matuƙar ƙaunar ta. Tana sanye cikin ƙayatattun tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama, a gadon bayan ta tana rataye da wani kwari, hannunta riƙe da baka, kuma tana zaune ne akan wata ƙatuwar zakanya. Wata ba ce wannan kyakkyawar budurwa ba face jaruma Sulairat yar Marigayi sarki urwat tare da zakanya Juraima. Sa'adda sarauniya Abidat tayi arba da ita sai ta miƙe tsaye zumbur daga kan karagarta fuskantarta a murtuke babu annuri tamkar an aiko mata da WASIƘAR MUTUWA, Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su, cikin tsantsar ƙiyayyar juna, inda a ɓangaren guda kuma Sulairat ke satar kallon masoyinta bawa HIMLAS. Tsawon daƙiƙa hamsin ana cikin wannan hali. Daga can Abidat ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, a lokaci guda kuma ta turɓune fuska tamkar ta buɗi baki cikin kakkausar murya ta ce "lale marhaban da zuwan manyan abokanan gabata, haƙiƙa wannan rana ce mai ɗumbin tarihi a gare ni, domin gashi dukkanin abokan hamayya sun taru a waje guda. Na rantse da ƙabarin kakana sarki Zaujatul-ashiƙ ba zan ƙyale ɗayan su a raye ba". Koda gama faɗin hakan ta zare wata sharɓeɓiyar takobin a gadon bayanta ta dako tsalle a sama tamkar an harbo ta daga cikin baka, ta durfafi inda Sulairat take. Suna saman suka kaiwa juna sara a kafaɗa. Cikin matuƙar zafin nama suka sanya takubbansu suka kare harin tartsatsi wuta ya tashi gami da ƙara, sannan suka sauka ƙasa bisa diga-digansu take suka ruguntsume da azababban yaƙi, ita kuwa zakanya Juraima sai ta afkawa dakarun fadar da ciwo da yakushi. Jaruman biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Wohoho! Haƙiƙa idan gwani da gwani suka haɗu a filin fama dole artabu ya zamto abin sha'awa da tashin hankali. Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce ranar bikin BABBAR GIWA babu wanda ke fitowa ya taka rawa face JARUMAN DUNIYA. Komai hassadar mutum idan yaga yadda jaruman ke yin artabun cikin gwaninta dole ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA. A ɓangaren zakanya Juraima kuwa duk inda ta sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa matattu waɗansu magashiyan. Nan fa fadar ta kaure da guje-guje da ifice-ificen jama'a kowa ya shiga gudun ceton rai. Sannu-sannu sai ga shi GWARAZAN MAYAKAN sun shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna bawa hammata iska, suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance tamkar ifritai. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaure wa jama'a kai kenan kuma ya ba su mamaki suka ce a cikin ransu "haƙiƙa yau sarauniya Abidat ta ɗebo ruwan dafa kanta, kuma ta ɗebo ruwan dafa kanta, domin a iya tarihi ba su taɓa ganin jarumin da ya yi GABA DA GABA da sarauniya Abidat na tsawon wannan lokaci ba ba tare da ta kawar da shi ba, wannan fa shi ake cewa ɗan hakin da ka raina shi ke tsoka ne maka idanu. A ɓangare guda kuma a ran su suna cewa yau abidat ta sayi ajalinta da kuɗin ta. Kuma mucijin da ta kashe bata sare kanshi ba. Ma'ana ta kashe Sarki urwat ga 'yarshi ta zame mata ciwon idanu. Duk sa'adda ɗayansu ya kaiwa abokin gwaminshi hari idan ya zille sai kaga duk abin da takobin ta sauka a kai sai ya yi bindiga ya tarwatse koda kuwa gini ne, nan fa manyan giwayen suka hargitsa fadar baki ɗaya, kuma suka tashi duk halittar dake ciki, a ɓangaren zakanya Juraima kuwa ta zame wa dakarun sarauniya Abidat ANNOBA ƊARI kuma ƙadangaren bakin tulu sun rasa yadda za su yi da ita, duk inda ta sanya gaba sai dai kaga zaratan mazaje na zubewa ƙasa matattu, waɗansu cikin mawuyacin hali. Nan fa fadar ta kaure da ihun mazaje gami da ƙarar karafniyar ƙarafa. Ana cikin wannan hali ne jaruma Sulairat ta fahimci cewa idan aka ci gaba da wannan artabu a haka gine-ginen dake rushewa za su iya raunata bawa HIMLAS da baiwa SUNAILA. Koda gama tunanin hakan sai ta dako tsalle daga inda take ta dira a daf da inda bawa HIMLAS da baiwa SUNAILA suke cikin zafin nama ta sanya takobi ta sare sasarin dake jikinsu, sannan ta sake dako tsalle ta dira akan zakanya Juraima, kawai sai juraima ta dako sufa izuwa inda su Himlas suke suka haye gadon bayanta sannan ta durfafi ƙofar fita daga fadar. Amma sai sarauniya Abidat ta dako tsalle sama ta sha gaban su ta kaiwa SUNAILA sari da takobin ta, cikin zafin nama ta sanya takobi ta kare saran sannan ya mayar da martani, duk da ƙoƙarin da abidat ta yi na kare harin sai da takobin sunaila ta tsarga kumatunta kaɗan jini ya yi tsartuwa. Kafin Abidat tayi wani yunƙuri, Cikin wani irin baƙin zafin nama Juraima ta daka wawan tsalle ta tsallake Abidat da dakarunta dira a ƙofar fadar ta falfalwa da azababban gudu cikin matuƙar takaici da baƙin ciki dakarun sarauniya suka rufa masu baya, amma kaico! Koda suka fita sai suka tarar wayam babu kowa, cikin matuƙar takaici suka suka ja suka tsaya, abin da ba su sani na shine jaruma sunaila ta sanya wannan sarƙar sihiri, bisa wannan dalilin ya sanya idanuwansu basu iya ganin su. Koda labarin ɓacewar su bawa HIMLAS ya zo wa sarauniya Abidat sai kawai ta ɗauko madubin tsafinta a cikin aljihunta ta shafe shi da hannunta na hagu tana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, domin ta gudanar da bincike akan su, amma sai madubin ya yi bindiga ya tarwatse. Cikin matuƙar takaici ta ƙarƙare kurma wawan ihu da karaɗe fadar baki ɗaya kuma ya amsa kuwwa izuwa gidan sarauta. Tsawon daƙiƙa talatin tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta tsuke bakinta sannan ta durfafi ƙofar da zata fitar da ita daga fada ta kai ta izuwa gidan sarauta, fuskarta a murtuke babu annuri tamkar an watsa mata garwashin wuta a kai, cikin hanzari dakaru suka rufa mata baya. BABI NA SHA BIYU Al'amarin su jaruma Sulairat kuwa sa'adda ta ceci rayuwar su bawa HIMLAS suka cigaba da gudu a bisa kan zakanya Juraima sai suka shafe tsawon sa'a ɗaya suna tafiya, sannan suka iso dajin Baitul-Shazwas, tun daga nesa Suhaimat ta hango su koda ta ga su uku a maimakon 'yarta kaɗai sai ta cika da matuƙar mamaki, sannu a hankali suka iso gare ta bakin Kogon dutsensu. Bawa Himlas ne ya fara sakkowa daga kan zakanya Juraima sannan Sunaila, Sulairat ce a ƙarshe. Cikin matuƙar farin ciki Suhaimat ta tare su tana mai yi masu lale marhaban, fuskarta cike da annuri tamkar ta haɗu da 'yan uwanta na jini. Kai tsaye ta jagorance su har izuwa cikin kogon dutse ta zaunar da su, sannan ta kawo masu abin kalaci da ruwan sha. Da yake Sunaila da hilwas suna cikin matuƙar galabaita da yunwa nan fa suka shiga cin abincin hannu baka hannu kwarya, ita kuwa Sulairat sai ta dinga satar kallon Hilwas a fakaice. Bayan sun kammala ne sun samu nutsuwa nan take Sulairat ta kwashe labarin abin da ya faru da ita a daren jiya ta yi mafarki bawa Himlas da Sunaila na cikin mawuyacin hali bisa wannan dalili ya sanya ta ziyarci birnin sin domin ceton rayuwar su. Kuma ta bata Labarin irin gwagwarmayar da ta sha kafin ta ceto rayuwar su bawa Himlas tun daga farko har ƙarshe. Sa'adda Suhaimat taji wannan batu daga bakin 'yarta Sulairat sai ta cika da matuƙar tausayin su Sunaila, kuma hankalinta ya dugunzuma ainun. Abu na farko da ya dugunzuma hankalinta shine haƙiƙa ceto rayuwar su bawa Himlas tamkar siyan ajalinsu ne da kuɗin su domin zai kasance dare da rana sarauniya Abidat na farautar rayuwar su. Sannan a halin yanzu shin Sulairat ta samu gagarumin ƙarfin da za ta iya GABA DA GABA da sarauniya Abidat har ta FANSAR RAYUKAN jama'ar birninsu da mahaifinta. Kawai ta ɗago da kanta ta dubi Sunaila da Hilwas ta ce "haƙiƙa labarin ku akwai taɓa zuciya, kuma ni da 'yata Sulairat zamu zauna tare daku cikin amana, har kawo lokacin da zamu ɗauki fansa akan AZZALUMA sarauniya Abidat. Amma wani hanzari ba gudu ba, dole ne a kodayaushe mu kasance cikin shiri domin a kowane lokaci Abidat da dakarunta za su iya kawo mana FARMAKIN BAZATO" Koda jin wannan batu daga Suhaimat sai Hilwas da Sunaila suka cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Hilwas ya buɗi baki ya yi gyaran murya sannan ya fara magana a karo na farko ya ce "haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki yadda kuka ƙarɓe mu kuma kuma bamu mafaka tare da ceton rayuwar mu, bamu da wani abu da zamu iya biyan ku. Ina mai yi maku alkawari ni da ummina cewa ba za mu ci amanar ku ba. Sannan game da batun sarin bazato da Abidat zata iya kawo mana ina da wasu shawarwari da idan muka bi su za su cimma nasara. Da farko a yau zamu kafa dukkan tarkuna a sama bishiyu da duk wata hanya ta shigowa wannan daji, Sannan zamu kasu gida huɗu kusa da juna ta yadda zamu dinga samun bayanan juna, Sannan dole ne mu yi amfani da makamai biyu Kwari da baka da wani daban domin kai hari ta nesa kafin yin karon batta da abokan gaba." Sa'adda bawa HIMLAS yazo dai-dai nan a zancen shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, domin ya kawo shawara mai kyau. BABI NA SHA BIYU A gabar tekun Baharul-Aswad dake yamma maso kudancin duniya an yi wata babbar ƙasa da ake kira da suna Madinatul-haiwan. Kasar Madinatul-haiwan ta bunƙasa a noma kiwo da ƙarfin tattalin arziki, daɗin daɗawa kuma sun tara zaratan mayaƙa masu juriya a filin daga. Sarkin dake mulkin birnin yakasance GWARZON MAYAƘI mai tarwatsa dandazon mayaƙa a filin fama, mashahurin attajiri ne kuma gawurtaccen matsafi na kiran shi da Nadiyar ibn shaiban. Sarki Nadiyar ya shara a kaf nahiyar a jerin sarakunan dake makwabtaka da shi bisa ƙasaitar sa ne ya sanya sarakunan dake shakkar shi, domin ya zame masu ciwon idanu" kuma ƙadangaren bakin tulu". Sarki Nadiyar yana da matan aure guda bakwai. Gaba ɗaya matan sun kasance 'ya'yan 'ysn majalisar sarki bakwai, baki ɗaya 'yan majalissar sun kasance wakilan ƙabilu bakwai mafiya yawa a ƙasar. Domin haka kowacce ƙabilar tana matuƙar kwaɗayin ace jinin ƙabilarsu ta samu juna biyu ga sarki Nadiyar, sai dai duk cikin su babu wacce ta taɓa samun rabo, sarki ya gudanar da bincike sai shirun masaƙi domin ya gano mene ne ya sanya ya kasa samun magani amma sai halarar tsafin shi ta bayyana mashi cewa ba zai taɓa samun haihuwa ba face ya mallaki abubuwa guda biyu masu matuƙar wahalar gaske waɗanda neman su dai-dai yake da neman jaki mai ƙaho. Abu na farko shine wata takobi mai abubuwan al'ajabi, mallakin sarkin bokaye. Na biyu shine wata zakanya mai abubuwan al'ajabi dake ake kira da suna Juraima. Waccan takobi zai yi amfani da ita wajen kashe wata mucijiya dake zaune a kogon Garul-musib, wacce da ake yiwa laƙabi da kuburul-shamshan wato uwar mucijan duniya, bayan ya kashe mucijiyar zai samu damar shiga wata ƙorama har ya ɗebo ruwanta ya kawo ɗaya daga cikin matanshi ta sha ruwan sannan zai samu magaji. Binciken bokaye da masu hasashe ya tabbatar da cewa a halin yanzu a duk jinsin miyagun halittu babu mai ƙarfin damtse da sihirin tsafi tamkar mucijiya kuburul-shamshan. Waccan zakanya kuwa zai yi amfani da ita a matsayin abin hawa, lokacin ita kaɗai dabbar da za ta iya jure wahalhalu har ya cimma nasarar isa kogon Garul-musib. Sa'adda sarki Nadiyar yaga wannan al'amari sai hankalinshi ya dugunzuma ainun kuma ya cika da matuƙar farin ciki. Abin da ya sanya shi farin ciki shine ya gano hanyar da zai samu haihuwa. Abin da ya dugunzuma hankalinshi kuwa shine halarar tsafin shi ta kasa bayyana mashi cewa a ina ne zai mallaki takobin haɗe da zakanya. Wata rana sarki Nadiyar na zaune a turakarshi bisa kujera, sanye da riga 'yar shara da gejeran wando irin na hamshaƙan sarakai, ya ɓaje alƙalumman sihirin shi yana gudanar da bincike domin ganin irin wainar da ake toyawa a duniya, yana cikin wannan hali ne kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki. Bakomai ne ya sanya sarki Nadiyar wannan dariyar farin ciki ba sai domin wani al'amari da ya gani a cikin halarar tsafin shi, wannan abu ba komai ba ne face a halin yanzu yana da halin da iya mallakar takobi tare da zakanya Juraima, kasancewar jaruma Sulairat dake da mallakin su ta bayyana kuma tana shirin kwabza yaƙi da wata ƙasaitacciyar sarauniya dake mulkin birnin sin. Sai dai wani tunani da ya faɗo mashi shine ta ta ya ya zai mallaki abubuwan biyu, shin zai haɗa kai ne da sarauniya Abidat ko kuwa shi kaɗai zai farki dajin Baitul-Shazwas. Haka dai ya cigaba da binciken a inda ya gano cewa akwai ɓoyayyen jarumi da zai kawo mashi cikas wajen cika wannan buri na shi, sai halarar tsafi bata bayyana mashi a ina jarumin yake ba. Tun daga wannan rana sarki Nadiyar ya fara shirye-shiryen tafiya izuwa dajin Baitul-Shazwas domin farautar zakanya Juraima da takobin sarkin bokaye. Ranar da tafiya dajin Baitul-Shazwas tazo tun da duku-dukun safiya sarki Nadiyar ya kammala shiri tsaf kuma yayi bankwana da dukkan iyalinshi gami da al'ummarshi ya kama abin hawa tare tawagar rakiya dakaru dubu biyar suka ɗauki hanyar da zata kai su izuwa birnin Sin. Wannan shi ne abin da ya wakana ga sarki Nadiyar na kasar Madinatul-haiwan. BABI NA SHA UKU Al'amarin sarauniya Abidat kuwa lokacin da ta Kaɗaita a cikin turakarta cikin matuƙar takaicin yadda abokan gabarta suka suɓuce mata, sai ta wanzu tana kai komo a cikin turakar ta kasa zaune ta kasa tsaye tana juya al'amarin a cikin ran ta. Tana cikin wannan hali ta iso madubi yake koda ta kalli fuskarta taga yankan da SULAIRAT ta yi mata bata san sa'adda ta dunƙule hannunta ɗaya ba ta naushi madubin ya tarwatse sannan ta taƙarƙare ta kurama wawan ihu, tsawon daƙiƙa goma tana cikin wannan hali sannan daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA. Kwatsam! Sai taji an tura ƙofar shigowa turakar, wani garjejen ƙato mai ƙirar samudawan farko ne sanye cikin sulken yaƙi ya bayyana gare ta. Sannu a hankali yana takawa da ƙafafuwanshi har yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku uku sannan ya zube ƙasa bisa gwiwoyinshi ya kwashi gaisuwa kanshi a sunkuiye. A sannan sarauniya Abidat ta juya cikin ƙasaita da baƙar izza ta dube shi da kyawawan idanuwanta masu haske da kwarjini, sannan ta buɗi baki cikin murya mai tattare da fushi ta ce " ya kai dirkar birnin Sin kayi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka nan ba sai domin kafi kowa sanin abin da ya faru da ni a fada na suɓucewar abokan gabata. Ba'a taɓa keta mutumcina da ƙasƙanta darajata tamkar yau ba. Saboda haka ina so ka shirya tawagar mayaƙa da baka taɓa tsara tamkar ta ba, gami da abin guzuri da masu hidima domin ba zan dawo gida ba face na kawar da abokan gabata kuma na mallaki takobin Saiful-imfal, ina so asubar fari ta yi mana a gaɓar shiga dajin Baitul-Shazwas." Koda jin wannan batu daga bakin Abidat sai sarkin yaƙi ya buɗe bakin ladabi ya ce "an gama ya sarauniyar kyawawa hadari malafar duniya. Kece guguwar ajali mai share TAWAGAR MAYAƘA, GAWURTACCIYA kike uwar hatsabiban duniya. KAIFIN TAKOBI kike mai raba tsakanin masoya, ANNOBA ƊARI kike duk wanda ya tono ki zai baƙunci barzahu. Kasaitaccen daji kike babu mai yi miki ƙyaure sai mahaukacin kafinta. MURUCIN KAN DUTSE kike baki fito ba sai da kika shirya. DAMISA ƘI SABO kike ki fyaɗe na gida ki fyaɗe na daji". Lokacin da sarkin yaƙi ya zo nan a kirarin da yake yiwa sarauniya Abidat nan take taji wata irin BAƘAR IZZA da ƙasaita ta cika kwanyarta. Ta dube shi ta ce "ya kai Hunaifu maza ɗago da kan ka ka dube ni haƙiƙa ka cancanta ka kalli sura a matsayin tukwicin wannan kirari naka". Koda jin wannan batu sai sarkin yaƙi Hunaifu ya buɗi baki cikin ladabi ya ce ya shugabata ba zan iya duban kyakkyawar surarki a matsayina na bawanki ba. Sai dai ina tsoron saɓa umarninki." Koda ya zo nan a zancen shi sai ya ɗaga kan shi ya ƙurawa Abidat idanu yana kallon surarta ko ƙiftawa ba ya yi tamkar wanda ruhinshi ya fita daga gangar jikinshi. A wannan lokaci sarauniya Abidat tana sanye ne da wata ƙasaitacciyar alkyabba mai shara-shara gaba ɗaya surar jikinta ta bayyana, tun daga wuyanta har ƙirjinta a bayyane suke, har kana iya ganin tsinin kan ƙirjin tamkar idan aka tsoka ne su da yatsa koda harshe zasu fito waje, cinyoyinta har zuwa kwankwason ta sai sheƙi suke suna ɗaukar hankali. Tun da sarkin yaƙi yazo duniya bai taɓa ganin wata 'ya mace mai kyawun sura tamkar sarauniya Abidat ba. Koda Abidat ta fahimci cewa idan har ba ta suturta jikinta ba sarkin yaƙi ba zai dawo da hankalin shi sai kawai ta juya mashi baya, a sannanne ya dawo hayyacin shi yana mai sauke numfashi. Cikin matuƙar shauƙi sarkin yaƙi ya buɗi baki muryar shi na rawa ya ce cikin ladabi "ya shugabata na rantse da wannan kyawun sura da zati naki farautar su jaruma Sulairat zai zamo tamkar kawar da yunwar cikina." Da jin wannan batu sai Abidat ta yi murmushi da ya ƙarawa tona asirin kyawunta har fararen haƙoranta suka bayyana cikin zazzaƙar murya mai ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji ta ce "je ka abin ka ya kai garkuwar birnin Sin." Koda jin hakan sai sarkin yaƙi ya juya ya fice daga turakar. *** Bokanya Zulaima ta ƙurawa tukunyar tsafin dake gabanta idanu ko ƙiftawa bata yi, kwatsam sai taswirar wata runduna guda biyu mabanbanta ta bayyana, runduna ta farko bisa jagorancin wata kyakkyawar budurwa ce ma'abociyar sarauta, runduna ta biyu kuwa bisa jagorancin wani namijin sadauki ne ma'abocin tarin shekaru. Baki ɗaya tawagar biyu suna tafiya ne cikin hanzari a cikin ƙasaitattun dazuka. Koda taswirar tazo nan sai bokanya Zulaima ta nuna tukunyar da hannu taswirar ta ɓace ɓat! Sannan ta dawo da duban ta izuwa ga ifritu Shammar da ƙwala-ƙwalan idanuwanta da suka ƙarawa fuskarta muni cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ta ce "ya kai sarkin matasan ifritai na duniya kayi sani cewa haƙiƙa abun nan da masu iya magana ke faɗa ya faru gare mu wato, "kowa ya daɗe zai ga daɗau, kuma a bari ya huce shine kawo rabon wani" Amma dai ai masu iya maganar sun ce sa'a tafi sammako. Kuma duk mai nema yana tare da samu. Takobin Saiful-imfal da na shafe tsawon shekaru ɗari huɗu ina jiran bayyanar ta yanzu lokaci ya yi. A halin yanzu takobin tana tare da wata jaruma yar baiwa mai suna Sulairat, raba Sulairat da takobin abu ne mai matuƙar wahalar gaske domin wata zakanya dake gadin takobin ba za ta taɓa bari wani mahaluki ya kasance ta ba. Babban abin damuwar shine babu wani mahaluki da zai iya sarrafa takobin Saiful-imfal face ya mallaki wata sarƙar sihiri dake rataye a wuyan jaruma Sulairat. Bincike ya tabbatar min da cewa manyan sarakunan duniya biyu sun fito domin farautar zakanya Juraima da takobin Saiful-imfal. Wannan ita ce damar mu ta ƙarshe da zamu ɗauke takobin ta kowacce fuska. Haƙiƙa burina ya kusa cika na mulkar duniya baki ɗaya domin cigaba da shimfiɗa baƙin mulkina. A halin ruhikan sarakunan duniya guda dubu shida dake aijye a cikin akwatin siddibaru sun kammala tsumuwa da sihirin tsafina, a ranar da zan mallaki takobin Saiful-imfal dukkan ruhukan za su shiga jikina, wannan shine zai bani damar shafe miliyoyin shekaru a duniya, domin sai na rayu adadin shekarun da kowanne ruhi zai yi a duniya. Ya kai sarkin matasan ifritan duniya kayi sani cewa sai na sanya duniya a cikin musiba da annobar da bata taɓa gani ba. Zan shafe duk wani addini dake doron ƙasa. Lokacin da bokanya Zulaima yazo dai-dai nan a zancenta sai sarkin matasan ifritai ya dube ta cikin ladabi ya ce "tsafi ya taimake ki ya uwar bokayen duniya uwa ma bada mama, yanzu batare da ɓata lokaci ba gaba ɗaya rundunar afritai za su bayyana a gare mu wacce ba ki taɓa ganin tamkar ta ba. Da yardar tsafi abin dogaro sai kin cimma nasara." Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Shammar sai bokanya Zulaima ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, al'amarin da ya sanya baki ɗaya kogon dutsen ya kama girgiza tamkar zai tsaye. Take ifritu Shammar ya ɓace ɓat! Daga kogon tamkar bai taɓa bayyana ba. Ita dai bokanya Zulaima ta kasance gawurtacciyar matsafi da tayi shura a cikin bokaye har masu bincike da hasashe na duniya ke yi mata laƙabi da uwar matsafa, Babban burin Zulaima shine ta mulki duniya baki ɗaya, bisa binciken da ta yi ne ta gano cewa dole sai ta mallaki ruhikan sarakunan duniya guda dubu shida ta tsafe su sun shiga jikinta, bisa wannan dalili ya sanya ta dinga farautar sarakunan tana hallaka su ta ƙarfin sihiri. Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin uwar bokayen duniya bokanya Zulaima tare da sarkin matasan ifritai na duniya. BABI NA SHA HUƊU A can dajin Baitul-Shazwas kuwa kamar yadda bawa Himlas ya tsara haka al'amarin ya kasance wato a daren wannan rana suka kammala sanya dukkan tarkuna a dajin cikin kyakkyawa shiri, ta yadda komai kallon ƙurillar mutum ba zai iya gane an sanya abubuwa masu cutarwa a dajin ba. Kashe gari tun da duku-dukun safiya aka hango ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari zai gangamo a kece da ruwa. Koda ganin hakan sai kowa ya miƙe ya kimtsa jikin shi, Sulairat shigar kayan fata tayi tun daga ƙasa har sama a gadon bayanta tana rataye da wata rantsattsiyar kwari da baka, a gwiɓin cinyarta kuwa tana ɗauke da takobin Saiful-imfal wacce a daren jiya zakanya Juraima ta yi mata jagora izuwa inda takobin take ta ɗauko, a wuyanta kuwa tana rataye da sarƙar tsafinta kuma ta raba gashin kanta gida biyu ya zuba akan kafaɗunta. Shigar ta yi matuƙar yi mata kyawu da kwarjini, bawa Himlas da Sunaila tare da Suhaimat shigar tufafi iri ɗaya suka yi sak gaba ɗaya sun rufe fuskokinsu da baƙin yanki idanuwansu kaɗai ake gani. Cikin hanzari kowanne ya tsaya a matsayar shi kamar yadda aka tsara. Sulairat ta tsaya a ɓangaren gabas tana zaune bisa kan zakanya Juraima, Suhaimat a yamma, Himlas kudu sai Sunaila a yamma. Tsawon daƙiƙa ɗari aka shafe a cikin wannan hali sai daga bisani ne duhun dake sararin samaniya ya ye sai aka jiyo ƙarar takun sawaye haɗe da haniniyar dawakai ta cika dajin baki ɗaya. A can bakin gaɓar shigowa dajin Baitul-Shazwas kuwa sarauniya Abidat tare da tawagar ta na ƙara kusantar dajin, lokacin da ya rage saura taku arba'in tsakanin su da dajin sai Abidat ta ɗaga hannunta sama aka tsaya can! A wannan lokaci Abidat tana sanye cikin baƙin sulken yaƙi tun daga ƙasa har sama kanta sanye da hular ƙarfe a gadon bayanta tana rataye da wata rantsattsiyar takobi a cikin kubenta, sanye a jikinta akwai makaman yaƙi fiye da guda ashirin, kaico! Haƙiƙa babu wani gwarzo da zai yi arba da Abidat a cikin wannan hali face ya razana domin shigar da tayi, shiga ce ta tawagar mutuwa. A gefen hannunta na dama sarkin yaƙi ne cikin shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. Abidat ta ƙarewa dajin kallo tana nazarin shi zuwa can sai ta dubi sarkin yaƙi ta ce "ya dirkar birnin Sin kana ganin cewa su Sulairat ba su san da zuwan mu ba, ko kuwa wani tanadi suka yi mana domin su yi mana mamayar bazato? Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi ya dube ta cikin ladabi ya ce "ya shugabata haƙiƙa abokan gabarmu sun shirya wani tuggu domin su mamaye mu, na tabbata cewa suna cikin wannan daji domin babu wani waje da zamu ɓuya da huce nan, sannan koda a ce ba su san da zuwan mu ba ai bayyanar mu ta zo masu domin hakan dole mu fara kai farmaki na somin taɓi." Koda jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta ce "zancen ka dutse ya kai dirkar birnin Sin dole ayi hakan, sannan kasancewar ba ni da ikon shiga dajin Baitul-Shazwas dole ne mu tura dakarun mu su kai hari da yadda dole su Sulairat za su fito mu yi GABA DA GABA da su." Ya yin da sarauniya tazo nan a zancen ta sai sarkin yaƙi Hunaifu ya risina kawai sai ya yiwa waɗansu dakaru mutum dubu inkiya ta wutsiyar idanu, tamkar dakarun sun fahimci abin da yake nufi sai kawai suka sanya hannayensu suka ciro kibbau daga cikin kwarinsu suka tsoma su a cikin wani kuttu mai ɗauke da guba, kana suka sanya a cikin bakansu suka ja suka ɗame sannan suka harba. A lokaci guda kibban suka tafi cikin matsanancin gudu suka durfafi dajin, duk inda suka sauka sai wuta ta kama koda korran tsirrai ne sai wutar ya ƙonamu. Nan fa hayaƙi ya turnuƙe dajin wuta ta kama ci ganga-ganga. Tsawon daƙiƙa ɗari ana cikin wannan hali al'amarin da ya fusata sarkin yaƙi Hunaifu kenan ya fara wasi-wasi ya fara tunanin shin ko su Sulairat sun yi nisa a cikin dajin. Kawai sai ya dakawa dakaru dubu uku tsawa da ke nuna ba su umarni suka afka cikin dajin. Cikin hanzari dakarun suka zaburi dawakansu suka durfafi dajin. Kaico! Haƙiƙa rashin sani ya fi dare duhu kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka inda ace waɗannan dakaru sun san abin da zai faru da ba su gangancin kutsa kai ba. Lokacin da suka isa ciki nan take suka fara faɗawa tarkuna suna hallaka tare da dawakansu. Nan fa ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin baki ɗaya Sa'adda sarauniya Abidat taga yadda dakarunta ke yin mutuwar wulaƙanci sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kunna kai izuwa cikin dajin amma da ta nuna babu halin hakan sai ta haƙura, Kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin fiye da mutum dubu na dakarun sun baƙunci barzahu, cikin hanzari sarkin yaƙi Hunaifu ya yi umarni a ja da baya, kamar taku goma sannan aka tsaya cak aka yi cirko-cirko. Sai da ƙura ta lafa sannan aka jiyo ihu da gurnanin zakanya Juraima daga can sai ga su sun ratso ta duhuwar bishiyun sun bayyana a fili. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu cikin matuƙar ƙiyayyar juna da mugun tanadi. Daga can dukkan ɓangarorin biyu suka yunƙura izuwa kan juna gami da falfalwa da azababban gudu, suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA, lokacin da ya rage saura kamar taku shida tsakani sai sarauniya abidat ta dako wawan tsalle daga kan dokinta tun a sama ta zare takobinta ta kaiwa Sunaila wawan sara. Cikin baƙin zafin nama irin na GAWURTACCIYA ta zare takobin Saiful-imfal ta kare harin, koda takubban suka haɗu da juna nan take aka kwantsama wata tsawa gami da walƙiya marar daɗin sauraro wacce ta sanya bishiyu karairayewa suna haɗu izuwa kan mayaƙa da dama suka faɗi ƙasa matattu. Sannan Abidat ta sauka ƙasa cikin gwaninta bisa diga-diganta. A dai-dai lokacin ne bawa Himlas ya tari sarkin yaƙi Hunaifu, baiwa Sunaila da Suhaimat kuwa suka kutsa izuwa cikin abokan gaba. A lokaci guda duka ɓangarorin suka haɗu da juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini muni daban tsoro, Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai ziyarci filin yaƙi ba to bai ga maƙurar tashin hankali ba. Domin yaƙi shine ke sanyawa a rasa rai, dukiya, da mutunci baki ɗaya. Wohoho! Idan gwani ya haɗu da gani a filin fama dole yaƙi ya zamo gwanin sha'awa da tashin hankali. A ɓangaren manyan giwaye biyu Sarauniya Abidat da jaruma Sulairat kuwa gaba ɗaya sun ɗauki hankalin duk wata halitta dake filin yaƙin, domin kuwa suna artabun ne cikin gwaninta da ƙwarewa tamkar na'ura ce ke sarrafa su, jikkunansu ba su kasance na jini da tsoka ba, ita kuwa zakanya Juraima aiki biyu yake tana kaiwa sarauniya abidat hari tare da farmakar dakaru tana yi masu ɓarna. A ɓangaren Bawa Himlas da sarkin yaƙi Hunaifu kuwa sun wanzu suna kaiwa juna hare-haren cikin JURIYA DA BAJINTA irin ta 'yan MAZAN JIYA, duk sa'adda takubbansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara marar daɗin saurare. Suhaimat da Sunaila kuwa duk inda suka sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa magashiyan waɗansu matattu. Wohoho! Haƙiƙa komai hassadar mutum idan ya ga yadda Waɗannan zaratan mataye ke ragargazar 'yan maza suna maishe su mataye, dole ne ya jinjina masu ya tabbatar cewa tabbas sun cika mataye masu kamar maza kuma zaratan mayaƙa. Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da rabi ana wannan ɗauki ba daɗi. Nan fa ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo, ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu da kururuwar mazaje haɗe da haniniyar dawakai suka cika dodon kunne. Haƙiƙa a wannan rana dakarun sarauniya Abidat suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin tamkar ta ba. Ana cikin wannan karon batta ne sarauniya Abidat ta kaiwa Sulairat wani wawan sara da takobinta a kafaɗa da nufin tsinke mata wuya. Cikin wani irin baƙin zafin nama Sulairat ta wurƙila da zillewa harin gami da mayar da martani, koda Abidat ta sanya takobin da nufin karewa take ta karya gida biyu ta faɗi ƙas. Kafin ta yi wani yunƙuri Sulairat ta dunƙule hannunta ɗaya ta kirɓa mata wawan naushi a fuska, saboda ƙarfin naushin sai da Abidat ta yi sama ta sauka daga kan dokin ta tayi katantanwa sau biyu sannan ta faɗi ƙasa amma sai ta miƙe tsaye zumbur! Tana mai gyara tsayuwarta, koda ta sanya hannunta ta shafa kumatunta nan take taga jini a inda Sulairat ta naushe ta ɗin. Koda ganin hakan sai sarauniya Abidat ta cika matuƙar baƙin ciki, kawai sai ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu ta zare sabbin makamai biyu a jikinta ta sake afkawa Sulairat a karo na biyu, suka ruguntsume da sabon artabu. Abu kamar wasa sai gashi dukkanin makaman yaƙin Abidat sun karairaye sun faɗi ƙasa. Abin da bata sani ba shine har abada babu wani makami da zai iya yin tasiri akan takobin Saiful-imfal, bisa wannan dalili ya sanya makamanta suka lalace. Nan fa taurarin biyu suka ja da baya suna haki da zufa, suna hararar juna tamkar waɗansu zakaru saboda yadda suka bawa hammata iska. Ita zakanya Juraima sai ta dinga buga ƙafarta ɗaya a ƙasa tana gurnani domin shirin kar-ta-kwana. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! Tamkar dare biyu ne ya haɗu waje guda, sannu a hankali sai aka hango waɗansu irin halittu marasa adadi na ketowa daga cikin gajimare suna sauka a bisa turba, duk sa'adda ɗayansu ya saukan sai ƙasa ta amsa, ya yin da halittun suka kammala sauka sai suka yiwa dajin ƙawanya. Nan fa dawakai suka firgice suka kama haniniyar suna zubar da mahayansu suna nausa cikin daji bisa arba da suka yi da halittun. Su dai halittun suna matuƙar muni, kwarjini daban tsoro. Baki ɗayan su suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini, hannayensu ɗauke da miyagun makamai. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Sulairat Abidat da tawagar halittun. Daga can nesa kaɗan sai aka jiyo ƙarar takun sawayen dawakai haɗe da haniniyar su, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, sannu a hankali sai aka hango tawagar mayaƙa guda biyu mabanbanta sun durfafi sansanin. Lokacin da yazamana tazarar dake tsakani bata huce kamu ashirin ba, sai dukkanin su suka yi turjiya suka tsaya cak! Sa'adda zakanya Juraima taga abin da ke faru na bayyanar waɗannan baƙin rundunoni uku sai kawai ta yi wani gurnani. Ashe Sulairat ta fahimci abin da take nufi don haka sai kawai ta murza wannan sarƙar tsafi dake wuyanta. Nan take su duka jama'arsu suka ɓace ɓat! Daga filin artabun tamkar ba su taɓa wanzuwa ba. Cikin matuƙar takaici da baƙin ciki sarauniya Abidat ta taƙarƙare ta kurma wawan ihu a karo na biyu tamkar baza ta daina ba. BABI NA SHA BIYAR Kaico! Haƙiƙa a wannan rana sarauniya Abidat tayi matuƙar baƙin ciki da bata taɓa yin tamkar shi ba, kuma ta kunyata a idanun talakawanta. Tsawon daƙiƙa goma tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta tsuke bakinta kuma ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA. Ta dubi sarkin yaƙi a lokacin da ya so daf! Da ita ta dube shi ta ce "ya kai dirkar birnin Sin yanzu gashi a karo na biyu na sake yin rashin nasara, sai dai hakan ba zai sanya gwiwata tayi sanyi ba, zamu yada sansani a nan har izuwa lokacin da za mu sake yin nazari game da kai farmaki ga abokan gaba." Koda jin wannan batu daga bakin Abidat sai sarkin yaƙi Hunaifu ya risina ya ce "zancen ki dutse ya sarauniya mai duniya, amma wani hanzari ba gudu ba, shin Waɗannan tawagar sarakai da halittu mene ne manufar su na zuwa nan. Shin sun zo ne domin farautar zakanya Juraima da Sulairat ko kuwa domin mallakar takobin Saiful-imfal? Sa'adda Abidat ta ji wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai tayi shiru tana mai zurfafa cikin kogin tunani daga bisani ya dube shi ta ce "haƙiƙa maganarka akwai ƙanshin gaskiya a ciki, ai gamu ga su za muga abin da zai turewa buzu naɗi. Domin kuwa ba zamu lamunci kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi ba. Yanzu sai kayi umarni ayi maza a kafa tantuna, tun da rana ta fara zafi ainun, akwai buƙatar mayaƙanmu su samu ƙwarin jikin da za su cigaba da kai farmaki." Da jin wannan furuci sai sarkin yaƙi ya ce"an gama ranki shi daɗe. Cikin hanzari ya juya da baya tare da umartar dakaru su fara aikin kafa tantunan, kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin sun kammala dukkan jama'a sun shiga ciki. Al'amarin waɗannan halittu da suka sauka a wajen kuwa, ya yin da suka ga cewa su jaruma Sulairat sun ɓacewa su sarauniya Abidat kuma su Abidat sun kafa sansani, sai suma suka janye izuwa gefe guda nesa kaɗan da inda suke suka yada na su sansanin a bisa kan waɗansu dawatsu. Haka al'amarin ya kasance ga sauran tawagar sarakunan biyu inda kowannen su yaja gefe guda nesa da ɗan uwanshi ya yada sansani. Ba wasu ba ne waɗannan tawaga biyu face, ayarin sarki Nadiyar na kasar Madinatul-haiwan, da ya fito farautar zakanya Juraima da takobin Saiful-imfal, domin cika burin shi na samo maganin da zai bawa ɗaya daga cikin matanshi ta samu haihuwa. Tawaga ta biyu kuwa tana bisa jagorancin sarki Damzaru ibn Gauras na birnin Salsalul-mahabba dake yamma maso arewacin duniya a gaɓar tekun nil. Shi dai sarki Damzaru ya kasance matashin saurayi kyakkyawa, da masu hasashe suka tabbatar cewa a duka nahiyar babu namiji kyakkyawa tamkar shi, GWARZON ƘARNI mai tarwatsa dandazon mayaƙa a filin daga, ya shahara ainun a fagen ilimin tsafi gami da tarin dukiya dangin lu'ulu'u da dinare. A rayuwar sarki Nadiyar bai taɓa soyayya ballantana aure, 'ya'yan manyan sarakai da attajiran duniya sun rasa rayukansu bisa kamuwa da ciwon soyayyar shi. Bakomai ne ya sanya sarki Damzaru bai taɓa ƙarɓar soyayyar wata 'ya mace ba ko batun aure ba sai domin wata lalura dake damun shi. A jikinshi yana ɗauke da halittar mace da namiji, tun ranar da aka haife shi bokaye suka tabbatar da cewa idan har likitoci suka yi masa aiki domin cire al'auran mace a tare da shi to fa za a rashi baki ɗaya. Kuma bokayen ba su gano inda wane magani zai magance lalurar ta shi ba. Tun daga wannan lokaci dare da rana sarki Damzaru bashi da aiki face gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi domin ya gano maganin lalurar shi amma bai taɓa samun wani bayani ba. Al'amarin da yake matuƙar jefa shi a cikin damuwa kenan har takai yana zubar da hawayen baƙin ciki. Wata rana yana zaune a turakarshi bisa kan ƙasaitacciyar tujera yana gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi kwatsam! Sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki tamkar na zai daina, Al'amarin da yayi matuƙar bawa kuyangi da dakarun tsaro mamaki kenan domin yau tsawon shekaru goma rabon da aji sarki Damzaru ya yi wanan dariya. Abin da basu sani ba shine bakomai ne ya sanya sarki Damzaru wannan dariyar farin ciki ba sai domin ya gano maganin da zai sha ya warware mashi lalurar shi. Bakomai ne maganin ba face wata saiwar itaciya da ake kira da Shajarul-shifa'a dake ajiye a dajin fatalwa. Zai jiƙa saiwar Shajarul-shifa'a sannan ya sha ruwanta, da zarar aiwatar da hakan halittar 'ya mace dake tare dashi zata fita ya dawo cikekken namiji, Asalin Shajarul-shifa'a ta tsiro ne daga cikin tukunyar tsafin wani shu'umin boka da ya rayu a dajin fatalwa, saboda bishiyar na ɗauke da waɗansu muhimman ɗalasiman tsafi da a halin yanzu babu wani matsafi da yake da irin su a duniya. Sannan muhimmin abin da sarki Damzaru ya gano shine burin shi ba zai taɓa cika ba na samun saiwar Shajarul-shifa'a face ya mallaki takobin Saiful-imfal wacce da ita ne kaɗai zai iya yaƙar halittun dake rayuwa a jikin bishiyar. Su dai halittun sun kasance masu kama da tsuntsun batoyi, suna ɗauke da fuka-fukai irin jemage, bakunansu suna kaifi fiye da na takobi, duk abin da suka yanka da shi koda ƙarfe ne sai sun raba shi gida biyu, tsananin zafin naman su ya huce tunanin bil'adama. Sai da sarki Damzaru ya shafe tsawon daƙiƙa goma yana wannan dariyar farin ciki, sannan ya tsagaita, nan take ya fito daga turakarshi ya dinga ɗibar dinare yana rabawa talakawa, al'amarin da yayi matuƙar ɗaure jama'a kai kenan suka ce a cikin ransu shin ko mene ne ya sanya sarki Damzaru sannan farin ciki haka? Ko kuma ya samu abokiyar rayuwarshi ne. Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu. Kashe gari tunda asubar fari sarki ya kammala shirin fita farautar takobin Saiful-imfal, bayan aiwatar da hakan sai ya yi bankwana da talakawan shi suna masu yi masa fatan samun nasara kasantuwarshi adali mai tausayin jama'arshi. Wannan shine dalilin da ya sanya sarki Damzaru ya fito farautar takobin Saiful-imfal. *** Budurwa ce kyakkyawa ta gaban kwatance sanye da fararen tufafi masu yalwa tun daga ƙasa har sama. ta rufe fuskarta da baƙin rawani idanuwanta kaɗai ake gani a gadon bayanta tana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta tana zaune bisa farar taguwa. Tafiya take cikin hanzari a cikin wani ƙasaitaccen daji mai ɗauke da sahara. Sai da shafe tsawon zango biyu tana tafiya babu sassauci, tana cikin wannan hali ne kwatsam sai ta hango ƙura ta turnuƙe a can nesa kaɗan da inda take, koda ganin hakan sai taja linzamin taguwarta ta tsaya cak! Sannu a hankali ƙurar tana Kusanto inda take har yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce kamu goma ba. Lokacin da ƙurar ta lafa sai ga waɗansu irin karen daji uku masu matukar girma da kwarjini, sai gurnani suke sun durfafo inda take wani yawu mai yauƙi yana dalala daga bakunansu. Su dai waɗannan karnuka sun kasance na sahara masu cinyin naman bil'adama, yau tsawon kwanaki huɗu ba su komai ba, domin haka suna cikin tsananin buƙata, bisa ɗabi'ar kurayen suna jiyo ƙamshin bil'adama a tsawon nisan rabin zango. Lokacin da kyakkyawar budurwar ta hango karnukan sun durfafo inda take cikin mugun nufizsai kawai ta dako wawan tsalle daga kan taguwarta ta dira bisa diga-diganta gami da zare takobinta suka shiga yin kallon-kallo. Daga can kawai ta ruga izuwa gare su domin tarar juna tana mai furta waɗansu kalamai da ita kaɗai ta san me take nufi. Sa'adda suka haɗu da juna sai suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. Abin tambaya anan shine daga ina wannan kyakkyawar budurwa take kuma ina ta dosa? Amsar hakan kuwa shine :- Sarki Shaibat ibnu Abbas yakasance dattijo ma'abocin haiba da SADAUKANTAKA da tarin duniya, mutum ne shi mai son addini da kyautata al'ummarshi, baya nuna bambanci a wajen hukunci tsakanin talaka da attajiri, bisa hakan ya sanya al'ummarshi ke matuƙar tausayin shi, hakan ya samo asali ne kasancewar shi ma'abocin addinin Musulunci. Yana da matan aure ɗaya da ta haifa mashi 'ya'ya biyu. Gimbiya Husnat da Hasinat, an haife su tagwaye masu matuƙar kama da juna tamkar an tsaga kara, sun tashi cikin gata da kulawar mahaifin su. Wata rana kwatsam! Sai aka wayi gari matar sarki Shaibat tare gimbiya Hasinat sun ɓace an neme su an rasa, nan fa hankalin sarki da jama'a ya dugunzuma ainun aka shiga bincike saƙo da lungu amma tsawon kwanaki biyu babu labarin su, wani abu da ya ɗaurewa al'umma kai shine babu wani sahihin labari da aka samu na dakarun sumame. Lokacin da sarki Shaibat ya tsananta da bincike sai ya fahimci cewa tabbas anyi aiki da sihiri a sace gimbiya da mahaifiyarta. kuma babban abokin gabar shi ne ya aikata haka sarki Marwatu, kuma ya yi hakanne domin shirya mashi baƙin tuggu na shafe birnin sa da addinin musulunci a doron ƙasa. Asali tsarkin sarki Marwatu da Shaibat sun kasance ba a ga maciji da juna, kuma gaba ce data samo asali tun iyaye da kakanni. Amma rana tsaka sarki Marwatu ya yi mubaya'a aka yi sulhu, aka cigaba da hulɗar kasuwanci da auratayya tsakani, yazamana cewa wasu daga cikin al'ummar sarki Marwatu na barin bautar gumaka su karɓar addinin musulunci, batare da sun fuskanci wata tsangwama ko hukunci ba. Lokacin da alaƙa ta yi ƙarfi sosai sai sarki Marwatu ya aikewa da sarki Shaibat cewa babbar 'yarshi gimbiya maulut ta kamu da matuƙar ƙaunarshi kuma ta na so ta aure shi. Lokacin da wannan labari ya riske shi sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana nazari akan wannan al'amari inda daga ƙarshe ya yanke shawarar amince domin wata ƙila idan ya aure ta hakan zai janyo hankalinta da na mahaifinta zuwa addinin musulunci. Bisa wannan dalili ya sanya sarki Marwatu ya auri gimbiya maulut har ta haifa masa 'yan biyu mata gimbiya Husnat da Hasinat. Abin da sarki Shaibat bai sani ba shine a daren ranar da matarshi ta haihu sarki Marwatu ya bayyana a turakarta cikin alƙalumman sihiri ya shayar da jaririyar Hasinat tsufin tsafi, bayan ya ɓace ɓat daga turakar ne da daƙiƙa goma aka haifo Husnat. Bisa wannan dalili ne ya sanya gimbiya Husnat ta taso da son ibada da addini saɓanin 'yar uwarta Hasinat. Sirrin da aka ɓoyewa sarki Shaibat shine an aura mashi gimbiya maulut domin ayi amfani da ita wajen cin amanar shi da ganin bayanshi. A halin yanzu 'yarshi gimbiya Hasinat babu wanda ta tsana a duniya fiye da shi. Wani abin takaici da sarki Shaibat ya samu labari shine, a halin yanzu sarki Murwatu ya tura gimbiya Hasinat izuwa dajin Baitul-Shazwas domin ta mallako takobin Saiful-imfal wacce da zarar ta mallaki takobin zata shigo har birnin Niyaƙul-kabir ta hallaka shi. Daga wannan lokaci za ta cigaba da azabtar da dukkan Musulmi a faɗin duniya. Lokacin da sarki Shaibat ya samu wannan bayani sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya kasa zaune ya kasa tsaye, bisa wannan dalili ya sanya ya yi ganawar sirri da manyan hakimanshi, inda daga ƙarshe suka yanke shawarar a tura 'yar uwarta Husnat domin ta hana ta cimma burinta na mallakar takobin Saiful-imfal domin ta hallaka mahaifinsu. Wannan shi ne dalilin da ya sanya wannan kyakkyawar budurwa ta fito farautar 'yar uwarta Hasinat, kuma take so ta isa dajin Baitul-Shazwas. BABI NA SHA SHIDA Lokacin da waɗannan masifaffun karnuka da gimbiya Husnat suka ruguntsume da azababban yaƙi a tsakiyar sahara. Sai suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Karnukan suka wanzu suna kai Husnat yakushi ya cizo cikin wani baƙin zafin nama da ya huce tunanin bil'adama, ita kuwa ta wanzu tana kare hare-haren gami da zillewa cikin gwaninta da ƙwarewar yaƙi. Wohoho! Haƙiƙa duk wanda ya iya ya huta, komai hassadar mutum idan yaga yadda Husnat ke kaucewa hare-haren karnukan tare da mayar da martani cikin baƙin zafin nama JURIYA DA BAJINTA sai mutum ya yi tsammanin ko wata na'ura ce ke sarrafa ta. Sai da suka shafe tsawon rabin sa'a suna kaiwa juna hare-hare cikin baƙin zafin nama, babu alamun nasara ga kowanne ɓangare. Al'amarin da ya fusata dukkan ɓangarorin biyu kenan kuma ya fusata su ainun. Abin da ya fusata karnukan shine a iya tsawon wanzuwar su a dajin basu taɓa haɗuwa da halitta mai matuƙar zafin nama da nacin tsakiya tamkar Husnat ba. Ita kuwa abin da ya fusata ta shine lokacin da gudanar da ibadar Ubangiji ya yi gashi ta kasa nasarar koda ƙwarzanar jikin ɗaya daga cikin karnukan, tana cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗo mata, tunanin kuwa shine haƙiƙa bakomai ne ya sanya ta gaza samun nasara akan abokan gwanin ta ba sai saboda da ta shagala da neman taimakon Ubangijin musulunci. Koda ta zo nan a tunaninta sai kawai ta buɗe baki ta kwala kabbara da ƙarfi tare da ɗaga takobinta ta kai sara, bisa sa'a sai KAIFIN TAKOBINTA ya ratsa wuyan ɗaya daga cikin karnukan, kanshi ya yi fitar burgu jini ya yi tsartuwa gami da feshin, gangar jikin ta faɗi ƙasa rikici! Kafin sauran karnukan su yi wani yunƙuri Husnat ta sanya takobinta ta datse masu wuya ta zubar da gawarwakinsu kwance cikin jini. Koda samun wannan gagarumar nasara sai Husnat ta yi godiya ga Ubangiji bisa baiwar da ya yi mata, cikin hanzari ta durfafi inda taguwarta take ta ciro salkar ruwa ta wanke jinin da ya ɓata tufafinta ta haɗe da takobinta. Sannan bugi ƙasa tayi taimama kasancewar bata da tabbacin ruwan da take ɗauke da shi zai ishe ta har ta fice daga cikin wannan sahara, bayan ta kammala sai ta shiga gabatar da sallah ba tare da fuskantar alƙilaba, kasancewar a sahara ba a iya gane ina ne gabas da yamma a lokacin da rana ta take, kuma addinin musulunci ya amince mutum ya yi sallah a duk halin da ya tsinci kanshi a ciki. Bayan ta kammala gabatar da bautar Ubangiji ne sai kawai ta miƙe tsaye ta kama linzamin taguwarta ta haye sannan ta cigaba da tafiya tana sassarfa, domin ta na so ta fice daga cikin saharar kar dare ya riske ta a ciki. Haka dai ta cigaba da wannan tafiya, kwanaki na bin kwanaki mako na bin mako, har ya zamana Husnat ta shafe tsawon mako uku tana tafiya. Cikin taimakon Ubangiji da addu'o'in da take karantawa ta ba haɗu da wasu miyagun halittu masu cutarwa ba ko 'yanfashi da makami. Wannan shi ne abin da ya wakana ga gimbiya Husnat ma'abociyar addinin musulunci da ta fito farautar 'yar uwarta Hasinat domin hanata mallakar takobin Saiful-imfal da za ta yi don hallaka mahaifinsu sarki Shaibat tare da azabtar da al'ummar Musulmi. BABI NA SHA BAKWAI Lokacin da sarakuna gami da matsafa haɗe da manyan bokayen duniya su huɗu suka yada sansani a agaɓar shiga dajin Baitul-Shazwas domin dakon su jaruma Sulairat ma'abociyar zakanya. Sai suka shafe tsawon sa'a bakwai ba tare da sun ji wani motsi ko labari akan su Sulairat ba har duhun magariba ya kawo kai, lokacin da dare ya tsala sai sarauniya Abidat ta karanta ɗalasiman tsafi ta rikiɗa izuwa wata kyakkyawar tsuntsuwa ta fice daga tantinta kai tsaye ta durfafi sansanin su sarki Nadiyar tana tafiya cikin hanzari. Lokacin da iso inda wani faffaɗan dutse yake kwatsam sai ta hango waɗansu tsuntsayen masu kama da ita sak tamkar an tsaga kara sun sauka a bisa kan dutsen, koda ganin hakan sai ta saki fuka-fukanta tayi ƙasa luuuh! Ta sauka a bisa dutsen, aka shiga yin kallon-kallo tsakanin ta da sauran tsuntsayen. Daga can sai tsuntsayen suka rikiɗa izuwa, sarauniya abidat, bokanya zulaima, Damzaru da sarki Nadiyar. Nan take gwarazan duniyar huɗu suka shiga kallon juna cikin mugun tanadi, tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sarauniya abidat ta katse shirun da ya wanzu tsakanin su ta hanyar buɗe baki ta ce "ya ku manyan sarakuna da kasuwar buƙata ta kawo ku nan ku yi sani cewa, baki ɗayanmu nan manufa ɗaya ta tara mu shi ne mallakar zakanya juraima da takobin Saiful-imfal, dole ne mu yi abin nan da masu iya magana ke cewa "a rashin uwa akan akan yi uwar ɗauki, wajibi ne mu ajiye kasuwar buƙata mu fuskanci abun hari, ma'ana mu tabbatar mun mallaki zakanya juraima da takobi, kuma mu hallaka waɗanda zasu hana mu cimma burin mu jaruma Sulairat da tawagarta". Koda jin wannan jawabi daga bakin sarauniya abidat sai sarakunan suka yi shiru suna dogon nazari, daga can bokanya Zulaima ta bushe da yar ƙaramar dariya mai kama da kukan jaki sannan daga bisani ta turmuke fuska, cikin kakkausar murya kai kama da haushin kare ta bude baki ta ce "haƙiƙa wannan shawara ce mai kyau, amma wani hanzari ba gudu ba, shin yanzu idan mun kawar da su Sulairat mun mallaki zakanya da takobin Saiful-imfal shin a cikin mu wane ne zai iya haƙura ya ƙyalewa ɗan uwanshi ya mallaki Saiful-imfal? To amma dai masu iya magana na cewa sai an gwada akan san na kwarai, ga fili ga mai doki" Sa'adda bokanya Zulaima tazo dai-dai nan azancen ta sai kawai tayi murmushi mai tattare da mugun tanadi da baƙin tuggu. Shi kuwa sarki Nadiyar abin da ya faɗo mashi a rai shine taya ya zai samu nasarar mallakar zakanya juraima da takobin cikin sirri ba tare da kowa ya farga ba. Wani ɓangaren a zuciyarshi ya ce da shi ya zama wajibi ka canja tunanin ka a game da wannan yarjejeniya, tunda sanin kanka ne cewa gaba ɗayanku yaudara ce a tattare da kowanensu, burin kowanne ya ci amanar ɗan uwanshi, saboda haka shawara a gare ka ita ce a lokacin da sauran abokan gabar suka yunƙura wajen hallaka su Sulairat kai kuma kayi ƙoƙari wajen ceton rayuwarsu tare da basu goyon baya. Hakan zai sanya su aminta da kai har su baka goyon baya su taimaka maka wajen cimma buƙatar ka ta samun ruwan ƙaramar shajarul-shifa domin samun haihuwa. Sa'adda sarki Nadiyar yazo dai-dai nan a tunanin shi sai ya yi murmushin farin ciki. Daga wannan furuci ne sarakunan suka sake rikiɗa izuwa tsuntsayen suka kaɗa fuka-fukansu, kowannensu ya nufi sansanin shi. A can dajin baitul-shazwas kuwa, al'amarin su sulairat tun sa'adda suka kammala fafatawa artabu da su sarauniya Abidat, sai suka kasance cikin shirin ko ta kwana, lokacin da dare ya tsala sai suka hallara a cikin kogon dutse. Bawa Hilwas ya katse shirun da ya wanzu a tsakanin su ta hanyar buɗar baki ya yi gyaran murya, ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya ce "ya 'yan uwa abokan share hawaye ku yi sani cewa haƙiƙa abun da ya faru a yau a filin yaƙi ya tabbatar mana da cewa sai mun sake tanadi, domin masu iya magana na cewa na zaune bai ga gari ba, kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Idan a yau mun yi artabu da sarauniya Abidat kaɗai to ku sani cewa a gobe zamu yi fito-na-fito ne da tawagar sarakuna biyar. Kar mu manta cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, kuma alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba. Dole a yauzu mu canja tunanin mu da nazari akan tunkarar gumurzun gobe". Sa'adda bawa Hilwas ya zo nan a zancen shi sai kowa ya shiga damuwa ainun aka yi shiru tsawon daƙiƙa talatin babu wanda ya ce ƙala. Sai daga bisani ne Sulairat ta yi gyaran murya ta ce "haƙiƙa zancen ka dutse ya kai Hilwas, wani abu da baka sani ba shine dukkan sabbin tawagar sarakunan da suka bayyana ba komai ne ya kawo su ba face, buƙatar mallakar takobin saiful-imfal da zakanya, Sai dai abin da suka manta shine masu iya magana na cewa "kifi na ganin ka mai jar koma" babu wani a cikin su da isa ya sarrafa takobin saiful-imfal koda ya mallake ta face yana tare da sarƙar tsafi, domin matuƙar ya ce zai sarrafa ta take takobin za ta hallaka shi. Bisa dogon nazari da nayi akwai yiwuwar a gobe sarakunan za su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin su kawar damu, daga baya a tsakanin su sai su san abin yi" Lokacin da Sulairat tazo nan a azancen ta sai kowa ya jinjina kai yana mai yuya al'amarin a ran shi. Suhaimt tayi gyaran murya a karo na farko ta ce "tabbas dukkan maganganun ku suna kan tsari, kuma a halin yanzu hankalin duniya yana kan takobin saiful-imfal da zakanya juraima, duk da cewa matuƙar yawan abokan gaba bamu da tabbacin zamu samu nasara akan su, amma kar mu manta cewa yaƙi ɗan zanba ne, Dole a gobe mu yi amfani da tuggun yaƙi ba iya na takobi ba, Shawarar da zan bamu ita ce me zai hana a gobe mu tura iya zakanya juraima da takobi a gaɓar shiga daji, mu sai mu ɓuya a cikin duhuwa mu hangi yadda yaƙi zai ɓarke tsakanin sarakunan, zasu yi ta kashe junan su inda daga ƙarshe dole wani ya yi nasara a cikin su ya mallaki takobi da zakanya. Shi kuma koda ya mallaka sun tashi a banza domin dole ne takobin ta dawo hannun Sulairat. Wannan wata mafita a gare mu bayan baƙin artabu, kun san masu iya magana na cewa "gida biyu maganin gobara". Sa'adda Suhaimat mahaifiyar Sulairat tazo nan a zancen ta sai kowa ya cika da farin ciki bisa jin wannan kyakkyawar shawara, daga wannan kowa ya koma can gefe inda shimfiɗar shi ta ke ya kwanta domin huce gajiyar dake tattare da shi. Amma koda su Sulairat ta zo hucewa ta gaban Himlas sai da ta jefe shi da wani ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar so da ƙauna, shima ya mayar mata da martanin murmushin. Wannan shi ne abin da ya wakana a dajin baitul-shazwas. BABI NA SHA TAKWAS Kashe gari tun da duku-dukun safiya, su bokanya Zulaima da sauran tawagar sarakunan suka yi sahu-sahu a gaɓar shiga dajin baitul-shazwas, domin tsumayen fitowar tawagar su jaruma Sulairat, Sai dai wani abu da ya ɗaurewa tawagar kai shine babu su ga sarki nadiyar da dakarunshi. Shin ina sarki nadiyar da ya shiga? Shin ya koma izuwa birnin shi ne ko kuwa ya canja wani tunanin domin cin amanar su. Amsar da tawagar da suka kasa bawa kan su kenan. Duk da cewa a daren jiya sun samu ƙari a cikin tawagarsu wato gimbiya Hasinat 'yar uwa ga gimbiya Husnat ma'abociyar addinin musulunci. Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali ba tare da anji motsin komai ba, Daga can sai aka ji ganyayyakin bishiyun dajin suna motsawa alamun dake nuni da cewa wani abu mai rai yana shirin bayyana a wajen. Zuwa can sai aka hango Jaruma Sulairat, bawa Himlas, Suhaimat, baiwa Sunaila tare da wasu baƙin jarumai biyu da suka rufe fuskokinsu da baƙin yanki, idanuwansu kaɗai ake gani. Baki ɗayansu suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro kana gani kasan fitowar yau cike take da mugun tanadi, kuma fitowa ce ta ko a mutu ko ayi rai. Ba wasu ba ne baƙin jaruman da suka bayyana ba face. Jaruma Husnat yar uwa ga gimbiya Hasinat tare da sarki nadiyar, nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin duka ɓangarorin ashe abin da su su sarauniya Abidat ba su sani ba shine a daren jiya Jaruma Husnat ta samu shiga dajin baitul-shazwas kuma ta bayyanawa su Sulairat abin da ke tafe da ita. Kuma a halin yanzu baki ɗayansu sun ƙarɓi addinin Musulunci. Wannan dalili ya sanya aka ajiye zakanya juraima da takobi a cikin daji kasancewar abubuwa ne na shiri. Daga can sai ɓangarorin suka tunkari juna, yayin da ya rage saura taku goma tsakani sai kowannen su yaja ya tsaya, aka sake sabon kallon-kallo na tsawon daƙiƙa arba'in, daga can sai Husnat ta dubi 'yar uwarta Hasinat tayi gyaran murya ta ce "yake yar uwata kuma gudan jinina kiyi sani cewa ban zo nan domin na yaƙe ki ba sai domin na yi miki nasiha ki tuba zuwa ga Ubangiji ki dawo zuwa addinin Musulunci". Koda jin wannan batu daga bakin Husnat sai 'yar uwarta Hasinat ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, daga can ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa ta ce "wannan nasihar ta ki abbanmu ya yi dubunta amma bai sanya koda kwarzane na imani ya ɗarsu a raina ba. Ina mai tabbatar miki da cewa sai na cimma burina na mallakar takobin saiful-imfal domin ɗaukar fansa akan abbanmu saboda haka ki shirya ga maza nan bisa kan ki". Koda gama faɗin hakan sai ta miƙa hannunta a gadon bayanta ta zare wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta, sannan ta ruga da gudu izuwa kan 'yar uwarta tana ihu da kururuwa mai firgitarwa. Koda ganin hakan sai Husnat ta zare takobin dake damtsenta ta tare ta gami da ƙwala kabbara da ƙarfi. Sa'adda tawagar sarakunan duniya suka ga abin da ya ke faruwa sai suka yi ɗauki kan su Sulairat. Sarauniya Abidat ta tari Sulairat, bawa Himlas ya tari sarki Damzaru, Baiwa Sunaila ta tari bokanya Zulaima, Suhaimat, sarki Nadiyar da dakarunshi suka tari tawagar sarkin matasan ifritai na duniya, da dakarun sarki Damzaru. Lokacin da ɓangarorin biyu suka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro da ban al'ajabi gami da tashin hankali. Wohoho! Haƙiƙa yaƙi KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka sha gwagwarmaya a GUMURZUN SHEKARA DUBU. Haƙiƙa ranar bikin farar kaza balbela ba abar gayya ba ce, idan manyan giwaye suka fito fagen artabu dole ne yaƙi ya zamto tashin hankali kuma ban tsoro. Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo, za'a kece da matsanancin ruwan sama. Husnat da Hasinat suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi. Wani abu da zai ɗaurewa mutum kai kuma ya bashi mamaki shine yadda salo da dubarun yaƙin 'yan uwan yakasance iri ɗaya sak. Amma a ɓangaren manyan giwaye kuwa wato Jaruma Sulairat 'yar baiwa da sarauniya Abidat, tuni labari ya sha banbam, domin gaba ɗaya sun zamto taurari ababan haskakawa a filin yaƙin, domin komai hassadar mutum idan ya ga yadda suke artabun dole ne ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika mata masu kamar maza, masu ƙarfi na Allah ya isa. A ɓangaren Bawa Himlas da sarki Damzaru an yi kunnen doki babu rinjaye ga kowanne abokin gwami. Ma'ana anyi kare jini biri jini, Sai dai ana samun asarar rayuka tsakanin dakarun sarki Nadiyar da tawagar muridai haɗi da na sarki Damzaru, Yazamana cewa duk inda mutum ya kai dubanshi sai dai ya ga Suhaimat da Sunaila na bazar da dakaru a ƙasa tamkar suna sassabe a gonar auduga. Nan fa waje ya cika da mutuwar mazaje, ƙarar karafniyar makaman yaƙi haɗe da hargowa da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne, duwatsu suna dinga karo da juna suna yin bindiga suna tarwatsewa, dawakai suka dinga dudufniya suna haniniya kofatunsu na kartar ƙasa suna tayar da ƙura, wasu na zubar da mahayansu suna nausawa cikin daji saboda matuƙar firgici. Wohoho! Haƙiƙa duk wanda ya iya ya huta, komai hassadar mutum idan yaga yadda Zaratan matan biyu ke ragargazar yaran ifritu da sauran abokan gaba dole ya jinjina masu ya tabbatar cewa sun cika GWARAZAN JIYA masu ƙarfi na Allah ya isa. Nanfa sarkin matasan ifritai ya ɗinauce bisa ganin yadda Suhaimat da Sunaila suka zame masu gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu. Kaico! Haƙiƙa yaƙi shine mabuɗin dukkan wata musiba a doron ƙasa, domin yaƙi shine ke haddasa asarar rayuka, dukiya, fari da JUYIN SARAUTA. Haƙiƙa wanda bai san shi shine yake fatan zuwan shi shine yake fatan zuwan shi. Abin da sarakunan kafuran ba su sani ba shine bakomai ne ya sanya su Sulairat ke samun galaba akansu ba sai domin addu'o'i da suke karantawa. A wannan rana sai da aka shafe tsawon sa'a biyu da daƙiƙa arba'in ana wannan ɗauki ba daɗi. Haƙiƙa Ubangiji ya nuna ikon shi a wannan rana domin ya kunyata maƙiya Addinin Allah, Baiwa Sunaila ta samu nasarar hallaka bokanya Zulaima ta hanyar karya mata wuya ta jefar da gawarta a ƙas. Shi kuwa sarki Damzaru ya miƙa wuya ga bawa Himlas bisa ganin cewa zai iya rasa rayuwar shi, zai tashi a tutar babu. Kamar yadda ya wakana tsakanin Damzaru da bawa Himlas haka al'amarin ya kasance tsakanin sarauniya Abidat da Jaruma Sulairat domin sai da Sulairat ta samu nasarar kai ta ƙasa sau babu adadi amma bata hallaka ta ba. Lokacin da Abidat ta fahimci cewa kowanne lokaci zata iya rasa rayuwarta, nan take ta miƙa wuya. Domin dai ina amfanin baɗi ba rai, A ɓangaren gimbiya Hasinat da 'yar uwarta Hasinat kuwa sun yiwa juna ƙananun raunika, kuma Hasinat ta miƙa wuya tayi nadamar abin da tayi. Sai dai sarkin yaƙinta ya rasa rayuwarshi. Wohoho! Haƙiƙa a wannan rana Ubangiji ya nuna ikon shi akan bayinshi ya kunya kafurai maƙiya addinin shi. Cikin matuƙar farin ciki Jaruma Husnat ta karanta kalmar shahada baki ɗayansu suka amsa, faruwar hakan ke da wuya nan take sarki Damzaru yaji yanayin jikinshi ya canja, koda ya duba sai ya ga cewa halittar mata maza dake tare da shi ta bar shi, yanzu yana ɗauke da cikakkiyar halitta ta kowanne ɗa namiji lafiyayye. Nan fa ya cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa, ya ji ya ƙara imani da Ubangijin gaskiya. Kafin ya bar filin yaƙin sai da Jaruma Husnat ta fito da takobin saiful-imfal ta lalata shirin dake jikinta ta hanyar karanta ayatul-kursiyyu ta tofa, ita kuwa zakanya juraima koda aka tofa mata ayatul-kursiyyun nan take wani baƙin aljani ya fito daga jikinta ya kama da wuta ta ƙone ƙurmus, ashe duk abin da take gudanarwa wannan aljani ke sarrafa ta hanyar amfani da sarƙar tsafi. Haƙiƙa a wannan rana babu wanda ya kai Sulairat da mahaifiyarta matuƙar farin ciki bisa ganin cewa suna kawo ƘARSHEN ZALUNCI a doron ƙasa baki ɗaya. Da yake akwai sauran sa'o'i kafin faɗuwar rana sai aka ɗunguma izuwa birnin Sin, aka kafa tutar musulunci dukkan al'umma suka yi mubaya'a bisa jin abin da ya faru da sarauniya Abidat. Sai da Jaruma Husnat ta shafe tsawon mako guda tana koyar da dukkan al'umma yadda ake gudanar da ibadar Ubangiji, sai da aka aika da wasikar gayyata izuwa ga sarki Shaibat domin ya zamto waliyyi a ɗaurin auren 'ya'yanshi, ya yi matuƙar farin ciki bisa jin labarin nasarar da Husnat tayi. Sai da ya iso tare da tawagarshi sannan aka shiga shagalin bikin sarauniya Abidat, Jaruma Sulairat ma'abociyar zakanya, Jaruma Husnat da bawa Himlas. Sarki Damzaru da Gimbiya Hasinat. A wannan rana anyi shagalin da ba'a taɓa yin tamkar shi ba iya tsawon wanzuwar birnin Sin. Ango Hilmas ya tare da amaren shi Abidat, Sulairat da jaruma Husnat, Kuma ya zamo sabon sarkin birnin Sin mai cikekken iko, sarauniya Abidat ta zamto shugabar sarauniyoyin birnin Sin. Farin ciki maral-musaltuwa ya mamaye zuciyar Suhaimat matar marigayi sarki Urwat da baiwa Sunaila mahaifiyar sarki Hilmas. Al'amarin sarki nadiyar kuwa lokacin da ya koma izuwa ƙasar shi nan take ya tarar da dukkan matayenshi sun samu juna biyu, ashe duk sihirin tsafin da aka yi masa ne ya kwantar da juna biyun. Yanzu kuma tun da ya karɓi addinin musulunci, sihirin dake tare da shi da matayenshi ya lalace. Nan fa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa kuma ya sanya aka rushe dukkan ɗakunan bauta aka jaddada addinin Musulunci. Faruwar hakan ya sanya dukkan al'ummar ƙasar shi suka kasance cikin aminci da soyayyar juna. Daga wannan rana farin ciki ya mamaye dukkanin sassan duniya, aka kawo ƘARSHEN ZALUNCI, uwar azzalumai sarauniya Abidat ta dawo sarauniyar adalci saboda hasken musulunci. Alhamdlillah. Anan na kawo ƙarshen wannan littafi mai taken ƘARSHEN ZALUNCI daga littafi na 1&2 zuwa na 3 ina fatan Ubangiji ya yi min afuwa bisa kusakuren da nayi. Abun da nayi na alheri kuma Allah ya bamu ladan baki ɗaya. Godiya ga dukkan masoya littattafai na a ko ina suke maza da mata. Sai mun haɗu a sabon littafi na ɗaya tamkar da dubu. KUNDIN AL'AJABI Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 ƊANƊANO Daga Littafin KUNDIN AL'AJABI Ƙasaitaccen keken doki ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan ado na sarauta. Kuma dokin dake janye da keken yakasance ingarmar doki fari sol!. Dokin na janye da keken ne cikin matsanancin gudu na keta sa'a a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin kwarjini daban tsoro, haɗe da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi, duwatsu da ƙoramu. Abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne, Duk da irin ƙawatuwa da kayan alatun da keken dokin ke tare da shi amma babu bil'adama a kanshi face wata akwatu ta baƙin karfe guda daya jal ajiye a cikin shi. Sai da ingarmar dokin ya shafe tsawon sa'a ɗaya yana falfala azababban gudu a dajin ya wanzu yana ratsa ƙoramu, duwatsu, sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, gami da ƙwazazzabai babu alamun gajiya a tattare dashi, Babu abin da zai burge mutum face yadda dokin yake gudu cikin gwanin ta da ƙwarewa, Duk da irin duhun daren da ya mamaye dajin tamkar akwai wani bil'adama dake sarrafa shi, Sa'adda yazamana dokin ya shafe tsawon zango biyu yana tafiya sai karfin gudun sa yafara raguwa. Ana Cikin wannan hali ne bisa kuskure wasu saiwar bishiya ya harɗe ƙafafuwan dokin na gaba, Take ya hantsila yayi adungure wannan akwatu dake cikin keken ta faɗi can gefe guda. Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu ashe inda dokin ya faɗi gangare ne wanda a ƙarshen shi wani rami ne mai zurfin gaske, Ai kuwa sai keken dokin ya dunga gangarawa har ya faɗa izuwa ƙarshen ramin. A dai-dai wannan lokaci ne wani mafaraucin ya rugo izuwa wajen sakamakon haniniya gami da kukan dokin ya cika cika dajin baki ɗaya, Ko da isowar shi sai ya kai duban shi inda ramin da keken dokin ya faɗa, Nan take takaici ya turnuƙe shi bisa ganin cewa bai samu nasarar ceto rayuwar keken dokin da mutanen dake kanshi ba. Yana cikin wannan hali ne idanuwanshi suka kai kan wannan akwatin baƙin karfe da ta faɗo daga cikin keken dokin, Cikin matukar farin ciki ya taka da ƙafafuwanshu zuwa wajen da akwatun take ya tsugunna ƙasa ya sanya hannunshu ya buɗe murfin akwatun sa'dda ya yi arba da abin da ke cikin ta sai ya miƙe tsaye zumbur cikin matukar kaɗuwa. Bakomai ne ya firgita shi ba face arba da yayi da wata tsaleliyar jariiriya, Wacce tunda yazo duniya bai taɓa gani ko jin labarin mai tsananin kyawun ta ba. Ita dai jaririyar an lullluɓeta da mayafi na alhariri a gefen ta kuma an ajiye wani kambu na damtse da aka yi shi zallar zinariya da jauhari, Mafaraucin ya ƙurawa jaririyar idanu wacce take kwance ta na sharar barcin bata san abin da ke gudana ba, Abin tambaya anan shi ne daga ina wannan jaririya ta fito? Kuma mene ne dalilin da ya sanya aka sakata a cikin wannan akwatu? Amsar tambayoyin da mafaraucin ya kasa bawa kansa kenan. An ya kuwa badan a tseratar da rayuwar wannan jaririya ba ne yasa aka sakata a cikin akwatin? Koda ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya durƙusa ƙasa a karo na biyu ya sanya hannuwanshi ya rufe murfin akwatun sannan ya cicciɓeta ya ɗora akan kafaɗarshi ya juya ya cigaba da tafiya yana mai kunna kai izuwa cikin dajin, Jim kaɗan da tafiyar shi sai ga waɗansu ZARATAN DAKARU sun iso wajen, Dakarun suna ɗauke da miyagun makamai dangin gatari, Sungumi, Takobi, Al'amudi da takobi, adadin su ya kai dubu da ɗoriya wasu akan dawakai wasu a ƙafa, Sai muzurai suke yi suna dube-dube a dajin tamkar zasu ci babu. Ko da bayyanar su sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna nazarin takun sawayen keken dokin, Kaico Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arna da mayaƙan dole ne ya firgice. A lokaci guda su ka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak, suka shiga haska takun sawayen keken dokin da fitilar ice tsawon waɗansu daƙiƙu. Daga bisani shugaban dakarun ya dawo zuwa inda dokinshi ke tsaye ya dubi sauran dakarun cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce " Ya ku 'yan uwana dakaru kuyi sani cewa binciken da na gudanar a yanzu ya tabbatar msni da cewa keken dokin da ke ɗauke da jaririyar Hunaisat ya faɗa izuwa cikin wannan rami dake gaban mu, Kenan kanan ya nuna cewa jaririyar bata raye a halin yanzu. Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban sai wani saurayi daga cikin dakarun yayi gyaran murya ya dube shi cikin ladabi ya ce " Ya shugabana shin wata shaida ka ke da ita da ya tabbatar da cewa keken dokin da ya faɗa wannan rami shine ke ɗauke da jaririyar Hunaisat? Kasan fa masu iya magana na cewa "kaɗa Mage ba yankawa ba ne". Ko da jin wannan tambaya daga bakin saurayin sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya shafi gemunshi mai tsawon kamu huɗu tamkar an tufka igiyar ya ce " Ya kai Hamsil ka yi sani cewa ai "Komai gudun kare baya ƙure daji" ina da tabbacin cewa jaririyar Hunaisat bazata taɓa kuɓuta daga tarko na ba, kada ka manta cewa fiye da shekaru sha uku nine ke kula da dawakan da ke ɓangaren gimbiya Hunaisat. Koda jin wannan batu daga bakin shugaban sai dakarun suka ƙaure da shewa da ihun murna , muryoyin su su ka amsa kuwwa izuwa cikin dajin su na masu ɗaga makamansu izuwa sama. Tsawon daƙika goma su na cikin wannan hali sai daga bisani ne suka kaɗa linzamin dawakansu suka koma izuwa cikin dajin. Abin tambaya a nan shi ne mene ne ne dalilin da sanya waɗannan dabaru ke farautar jaririyar? Daga ina keken dokin ya ɗauko jaririyar kuma wane ne ya sanya ta a cikin wannan akwati?. Dalilin faruwar hakan kuwa shine. Domin yin rigester na group ɗin littafin za'a biya ₦500 ta hanyar bank 8137237071 Usman Umar Mansur Opay Daga mai ɗeɓe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071