[14/11 à 12:10] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ 01 ‘ Lokacin da muna yara,da zarar an ce MAFIYA kawai abu guda kwanyata ke bani ƙungiyar shan jini ce mai sa a yi kuɗi.Amma yanzu da na girma,na kuma tsinci kaina a ciki sai na fahimci cewa MAFIYA na nufin cikar muradi. Sunana HAROON matashi ne ni ɗan kimanin shekara talatin da takwas a duniya,maraya na uba ,shalelen mahaifiyata.Na taso cikin matsin rayuwa ta talauci kafin kuma na tsinci kaina cikin daula...... ' “Haroon sakatariyarka ta ce yau ba za ka fita ba ko zan san dalili?” muryar Ammy ta katse mini ɗan taƙaitaccen tunanin zucina wanda kusan lokuta da dama nake zama haka kawai ina bai wa kaina labarin kaina. Na saki murmushi ina kallon sanyin idaniyata abar alfaharina,“ ban jin daɗi ne Ammy shi yasa,amma kar ki damu ciwon kai ne kawai” “Kamar ya kar na damu ? Ciwon kan ne kake faɗa ƙaramin abu? Jira ni ina zuwa” ta faɗa tare da yin gaba. Na bi ta da kallon ƙauna,Ammyna kenan uwa ta gari wacce a idonta sam ba na girma kullum tamkar ƙaramin yaro haka take ɗauka ta.Ina nan zaune ta dawo hannunta riƙe da wata tasa da kuma ƙaramin towel,na lumshe ido lokacin da ta soma tsoma towel ɗin a ruwa tana matse shi sai kuma ta dinga dadanna shi a kaina.Cikin ikon Allah na ji ciwon kan yayi sauƙi,“Ammy ya isa haka je ki huta mana ban san yaushe za ki daina ɗawainiya da ni ba,kamar wani ƙaramin yaro dai sai ririta ni kike” na faɗa ina mai riƙe hannunta mai ɗauke da towel ɗin. Ta dungure mini goshi cikin faɗanta da ta saba yi min ta ce “ sai ranar da ka kawo matar aurenka a gidan nan.Wai HAROON yaushe za ka yi aure ?” Da sauri na miƙe ina mai cewa “ aure! Aure dai kullum shine zancenki Ammy,duka nawa nake?” “Yanzu na haife ka” ta bani amsar da ta saka ni dariya,sai kuma na ce “ kar ki damu zan nemo miki suruka kafin ƙarshen shekarar nan in sha Allah!” na furta ina mamakin furucina na ƙarshe da na ambaci sunan maƙagina,wanda a ƙalla zan kai shekaru biyar da muka yi hannun riga ni da umarninsa.Yanzu haka ambaton sunansa sai da na ji maƙogorona yayi min wani zafi,halshena kuwa tamkar an saka reza ne an tsaga shi. “Allah ya nuna mini wannan babbar rana, Ubangiji yasa ina da rai albarkacin Manzon Rahama Ya Rabb ka dubi Harunana ka basa mata ƴar aljanna mai haska duk wani duhun gidansa” ita ce addu'ar Ammy gare ni,ban ko amsa ba na yi gaba abina. Ina fitowa harabar tsakar gida direbana yayi saurin tashi tare da nufar motar da a yau ita ce zan shiga.Da kansa ya buɗe mini gidan baya na zauna,sannan ya ja motar. Hanyar babban ofis ɗina ya ɗauka amma na yi saurin dakatar da shi.“ Ka ga kai ni wurin da zan ɗan shaƙi iska yau ban ra'ayin aiki ko kaɗan ” na faɗa don haka kawai nake jin yau raina a dagule babu daɗi ga wani irin bugawa da zuciyata take. Gudu yake da ni amma hankalina ba ya ga hanya na lula sosai cikin tunani,ƙiiiii ya ja wani uban burki sai a lokacin na dubi gabana.Wata kyakkyawar budurwa na hango tana tsallakar da yara ƴan makaranta,yayin da duk ababen hawa suka tsaya suna jiran sai yaran sun gama wucewa. “Yi haƙuri yalaɓai bari na canza hanya” cewar direba ,da sauri na ce “no ! Jira” ido kawai na tsura mata yadda take ta zulumniya cikin ƙaton hijabinta ,yayin da hannunta kuma wanda ya sha jan lalle ke faman kamo na yara. Ido na lumshe sa'ilin da ta game dukkan hannuwanta alamun godiya ,ban san mun bar wurin ba sai da na ji direba yana cewa “ba don Malam Zainab ba ce da ƙila mutanen nan ba su tsaya ba sai an samu waɗanda za su ce sai sun wuce” “Ka san ta ne dama?” na samu kaina da tambayarsa. Yayi ƴar dariya ya ce “to wane ne zai ce bai san Malama Zainab ba,yarinyar da duk shekara ita ce ke cin gasar musabaƙa ta duniya.Makarantar can ma gwamnati ne ya buɗa mata ita da sunanta,yalaɓai in ka ji yadda ɗalibanta ke yin larabci kai kace ƙyanƙyasar Saudiya ce uwa uba ita in tana yi.Zaƙin muryar.....” “Ya isa haka juya ka mayar da ni gida” na yi saurin katse shi saboda bugun zuciyata da na ji sai ƙara hauhawa yake.Muna isa gida ko wani burki mai kyau bai yi ba na yi saurin fita daga motar ba tare da na jira ya buɗe min ba. Ammy na falo ta ga na shigo a hargitse,ta yo kaina tana tambayar lafiya amma ban bata amsa ba na haye step ina taka shi bibiyu yayin da ita kuma ta mara min baya tana faman kiran sunana.Ina isa ɗaki kuma na rufe shi gam da key,ga ƙofar na jingina ina sauke numfashi kafin dakyar na ƙarasa na je na zauna kan kujera ina kallon kaina cikin baƙin madubin da shine silar canza rayuwata daga jiya zuwa yau.A zahiri ni mutum ne complet,amma a cikin madubi ba komai ne ba face ƙwarangwal ba tsoka saboda da kaina na sayar da ruhina ga MAFIYA......... [14/11 à 15:44] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA* 02 Karon farko kenan da na yi da na sanin shiga MAFIYA,a tsawon shekarun da na yi a ciki na yi su ne cikin farin ciki.Hawayen takaici nake yi yayin da ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi ke ƙyartata dariya,ita ƙwarangwal ɗin nan ba kowa ba ne face Ni,inuwata ce ko kuma na ce ruɓaɓen ruhina.Daga can bakin ƙofa ina jin Ammy na buga wa tare da kiran sunana amma na kasa tashi ,zuciyata ta yi rauni ba zan iya tsayuwa gabanta ba na shaida mata alƙawarin da na yi mata na samo matar aure ne ya cika sai dai kuma baƙin ruhina da farin ruhin kyakkyawar budurwar nan sam ba za su iya zama a inuwa ɗaya ba saboda rayuwar da ta rage min ƙalilan ce. Wayata ce ta ɗauki ruri,ina dubawa na ga sunan Oga.A dole na ɗaga,“ ka zo muna da meeting ɗin gaggawa” shine abin da ya faɗa kafin ya kashe. Jiki babu ƙwari na miƙe na shiga toilet na wanke fuskata na goge ta da towel sannan na fito.A bakin ƙofa na ga Ammy idonta sun yi jawur,na sakar mata murmushi na ce “ kar fa ki damu kan ki zan nemo wata tun da wannan ɗin ta fi ƙarfina” “Wa kenan?” “Budurwar da na gani yanzu da muka fita,kin ga Ammy kar ki damu zan cika miki alƙawarin da na ɗauka” ina gama faɗa na soma tafiya,ta biyo bayana har muka sauko ƙasa sannan ta ce “ ƴar wace ce ita da har ta fi ƙarfin ka?” “Ba kowa ba ce kawai malamar makaranta ce” na bata amsa,“ mi sunanta?” Na juyo muna facing juna sannan na bata amsa da “ zan fita yanzu in na dawo za mu yi maganar” “Allah tsare ka ya maido mini kai lafiya” Dakyar na amsa da “Amen ” .Ina fita na karɓi key ɗin mota,don in magana ta shafi Oga ban bari a yi draving ɗina.Tuƙi nake amma idona ita suke hasko min,dakyar na samu na kai kaina can inda muka saba meeting ɗin. Tuni mutane sun fara taruwa,na samu wuri na zauna muka ɗan soma cacabke wa da sauran members.Sai da kowa ya hallara sannan wurin yayi tsit,Oganmu sai a lokacin ya miƙe ya soma jawabi.“ Kamar yadda kuka sani wannan Association ɗin namu yana da tsari,ba a shiga kudin sirrin kowa hakan ne yasa wasu informations ɗin ba mu samunsu kai tsaye ta yadda za mu fahimci daga ina suka fito.Sai dai sosai dakarun bayar da kariya suke iya ƙoƙarinsu wurin ganin babu wata ƙungiya ko baƙin haure da za su kawo mana hari.To yau ma ɗin mun samu labarin cewa wani mummunan al'amari na tunkaro ƙungiyarmu ,kune ƴaƴanta kune kuka san yadda kuke gudanar da rayuwarku don haka ku nutsu ku yi nazari a cikinku babu wanda ya tsokano faɗa ko kuma yayi wani kuskure wanda bai dace da tsarin ƙungiya ba?” Oga na kawowa nan da zancensa sai duk ya soma bin mu da ido ɗaya bayan ɗaya. Ko kaɗan ban kawo a raina cewa malam Zainab da na soma jin ƙaunarta ita ce matsalar da Oga ke magana a kai ba wannan yasa sam ban ma nuna damuwa ba.Har aka gama meeting babu wanda ya ce ga wata matsala sai Oga ya sallami kowa.Har zan fita ya tsayar da ni,sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya ce “ HAROON ka shekara biyar a cikinmu” “Ai na sani Oga” na faɗa don ban ga amfanin sanar da ni ɗin ba. “Eh tuni ne na yi ma don kar ka shagala” ya faɗa yana ƙara yi min kallon nan da ke sa mutum ya tsargu,shiru kawai na yi masa.Can ya ce “ kana iya tafiya” na jinjina kai. Bayan na fito daga can direct wani gidan shaƙatawa na tsaya Park,wuri ne da iyaye suke kawo yaransu don shan iska da kuma buɗe ido.Karon farko da na ji sha'awar ajiye yara,yadda suke wasa gwanin ban sha'awa sai ya sake tuna min da Malama Zainab.Hoton fuskarta nake gani a kan fuskar duk iyayen da ke wurin,sai nake ganin tamkar ma a nan ita ce ke kula da su.Na ɓata lokaci sosai kafin na bar wurin,ina draving ina tunaninta har na isa gida.Cak na tsaya bakin ƙofa ganin Malama Zainab ɗin tare da Ammy a zaune.Na girgiza kai tare da dariyar kaina a zuci na ce ‘ HAROON ka haukace tun da har a cikin gidanku Malama Zainab kake gani ’ sai na yi gaba har na hau step ɗin farko sai na tsinkayo muryar Ammy na cewa “ HAROON zo ku gaisa da malamar da za ta dinga koyar da ni karatu” Da sauri na juyo sai muka haɗa ido da ita amma ta yi saurin kawar da kai,tamkar wani gumki haka na tsaya ina kallon ta .Sanye take cikin pink ɗin hijabi,tafin hannunwata a waje suke ta riƙe litattafai da su.Kamar wani sakarai haka jan lallen yatsunta ya ja ra'ayina har ban san lokacin da na taka can inda suke a zaune kan salon ba,“ mu ga littafin da za ku soma” na faɗa tare da kai hannuna zan karɓa amma wani azababen suraci da ban san na mene ne ba ya daki hannuna da bala'in sauri na yi baya har ina shirin faɗuwa. “Yi sannu mana,Malama miƙo min na basa” cewar Ammy ta karɓo littafan ta miƙo min sai dai sam na kasa amsa saboda wani irin haske da nake ganin yayi min katanga da littafafan.Na girgiza kai na ce “ a'a Ammy ba sai na gani ba” sai kuma na nufi step da mugun sauri na haye can sama,ina shiga ɗaki na ƙargame shi da key ina jin wani tsohon ilimina na baya na dawo min.A nan take a inda nake na fahimci wani abu,ina cikin fushin Allah mai tsanani ta yadda har har littafai masu kalmomin saninsa suka yi min tawaye suka haramta gare ni........ MRS SADAUKI ce 💫✍️ [15/11 à 15:32] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 03 Duk yadda na so nuna wa zuciyata ruwa ba a sa'an kwando ba ne amma sam sai ta yi min bore ta ƙi aminta akan muradinta.Soyayyar Malama Zainab ɗin dai ta zaɓa ,duk da tunanina ya ƙi bata haɗin kai wannan bai canza zane ba.Dakyar na cira ƙafafuna zuwa toilet,kayana na cire kafin na shiga ƙarƙashin shower na buɗe pampon duka.Ruwa suka soma jiƙa ni,sanyinsu na rantsa sumar kaina ina jin wata ƴar nutsuwa na sauko min.Rabon da na ji yanayin buƙatar mace har na manta,zan iya kai wata biyu haka ban yi lalata da ƴar kowa ba amma yau soyayyar Malama Zainab ta motso mini da tsimin. Pampon na kashe ba tare da na yi wankan sabulu ba,towel na ɗaura a ƙugu kafin na fito ina tsane gashina da ɗan ƙarami.Bayan na gama na saka ƙananun kaya na fashe jikina da turare kafin na sauko ƙasa ,sai na tarar tuni ta tafi sai Ammy kaɗai zaune a falo tana duba littafi. Na ƙaƙalo murmushin dole na ce “ Barka da yamma uwa ta gari” Ta ɗago ta ɗan dube ni na wani lokaci kafin ta ce,“ meke damunka HAROON ? Ina ce ganin Malama Zainab zai sa ka nutsu amma sai na ga saɓanin haka” Kusa da ita na zauna kafin na ce “ wai aka yi kika nemo ta? Ko dama kin san ta ne?” “To wane ne bai san Malama Zainab ba duk Yamai? Na san ta mana har gidan marayun da take kula da shi ina zuwa duk ƙarshen wata” Na ɗan saki murmushi,taimakon al'umma yana ɗaya daga cikin halin kirki na Ammy.Duk wata ƙungiya mai kula da marayu sun san ta sannan ba wata ɓoyayya ba ce a garin Yamai don kusan duk wani abu da ya shafi Islam sai an kawo mata takardar gayyata irin taron ci gaban addini da sauransu,amma ko kaɗan ban yi tunanin ta san Malama Zainab ɗin ba. “Bayan fitarka ne na tambayi direba sai yake sanar da ni,shine fa muka je har can inda take na nemi alfarmar ta dinga zuwa tana min karatu a gida ” Ammy ta faɗa murmushi kan fuskarta. Ita ɗin tana da son Addini sai dai ba tada yawan karatu,kuma samun ilimi na ɗaya daga cikin burinta sai dai ta karaya ne tana ganin ai shekarunta sun ja. “To Ammy sai ku yi ta karatun,yaushe da yaushe za ta zo?” “Duk bayan sallar magrib in sha Allah,zan dinga aika direba ya ɗauko ta in kuma ta gama sai ya mayar da ita” “Amma iyayenta sun bari?” “Eh sosai,ai a gabansu na nemi alfarmar shi fa mahaifinta gani yayi ma kamar zunubi ne ƙin yarda da abin da na roƙe su ɗin.Iyayenta ƴan mutumci ne kamar dai ita” ta ƙarashe zancen fuskarta na canzawa,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “ mene ne kuma Ammy? Don Allah kar ki tuna shi,kar fa ki manta kin yi mini alƙawarin haka” Kai ta jinjina mini kafin ta ce “ zan shiga ciki sallar magrib ta gabato zan yi wanka” sai kuma ta miƙe,na bi bayanta da kallo kawai.Ina nan zaune mai aiki ta kawo min abubuwan motsa baki,ko kallon ta ban yi ba na soma ci ina tunanin abar ƙauna.Na kurɓi lemun zoɓo kafin na miƙe na fita harabar gidan,mota na shiga na ƙara ficewa. Ban yi nisa ba kuwa aka soma kiran sallah,amma ban wani damu ba na ci gaba da tuƙina har na isa inda nake tunanin zan samu macen da za ta sama min nutsuwa. Daidai wurin bada hannu na tsaya,almajiran suka fara miƙo min robobinsu duk da kuwa gilashin motata a rufe yake ruf.Dayawansu ba za su wuce shekara ashirin zuwa da uku ba,ganin ban buɗe ba yasa duk suka tafi sai ɗaya ce ƴar jaraba ta tsaya .Sai a lokacin kuma na yi ƙasa da madubin motar,cikin daƙiƙa biyar na ƙare mata kallo fara ce ita amma dauɗa ta saka ya disashe sannan irin kamar Fulanin nan na daji. “Alhaji ka taimaka mini ina son kai Mamana asibiti ne” ta faɗa cikin marairaice murya. “Nawa ne farashinki? ” na samu kaina da furta wa,ido kawai ta zuba min da alamu ita sabuwar zuwa ce ba ta san tabi'ar nan ta ban manda na baka gishiri ba. “Za ki bi ni mu je in kina son na baki kuɗi” na faɗa a karo na biyu,sai na ga tsoro ya bayyana a fuskarta.A hankali na soma mayar da madubin motar amma ta yi saurin dakatar da ni ta hanyar saka hannunta daga sama ,sai na ƙara yin ƙasa da shi. “In mun je da gaske za ka bani kuɗin?” ta jefo mini tambayar cike da yarinta. Kai kawai na jinjina mata,sai na ga fuskarta ta faɗaɗa da murmushi.Gaban mota na buɗe mata kafin na yi mata key,tuni gari ya ɗauki duhu sai hasken fitilun kan hanya.Gudu nake sosai ta yadda ta soma yi min magana cikin tsoro “ don Allah Alhaji ka yi haƙuri kar ka sayar da ni ” Na ja tsuki ban tanka ta ba,sai dai na rage gudun motar sai ta saki ajiyar zuciya.Gidana na kai ta wanda babu kowa a cikinsa hatta mai gadi ban sa ba,a waje na yi parking duk muka fito.Na buɗe gidan na shiga sai na ga ita ta tsaya bakin ƙofa,“ki shigo” “A'a ba sai na shiga ba ka ɗauko kuɗin ka bani” tsabar takaici ban san lokacin da na wani jawo hannunta da ƙarfi ba na shigo da ita ciki tare da rufe gidan. “In kika ce ihu ko kuka za ki yi min zan sayar da ke ɗin tun da haka kike so” na faɗa tare da yin gaba,a dole ta take min baya har cikin falo.Na kunna wutar ko ina sannan na haɗe rai tare da nuna mata toilet na ce “ ki shiga ki yi wanka” jikinta na kyarma ta shiga ɗin,sama da minti goma amma ta ƙi fitowa sai na mara mata baya ina shiga na ja wani uban burki zuciyata ta soma bugawa fat! Fat! Fat! Sakamakon ganin Oga cikin shigar kayan yarinyar da na ɗauko a mota. Waige-waige na fara sai dai babu ita sai shi ɗin dai,kamar ƙyaftawar ido yarinyar ta dawo normal ta soma magana amma muryar oga ce ke fita. “ Tun da na soma meeting ɗin yau hankalina yake kanka,wato a fuskar kowa na lura da damuwa saɓanin kai.HAROON ka fara soyayya faɗa mini wace ce ita?” yana gama faɗa sai ya ɗauki siffarsa ta namijin kayan yarinyar nan suka zube a ƙasa sai nasa kayan jajaye masu kamar jini. Kasa furta komai na yi,don in na ce in yi magana ƙarya ce zan faɗa kuma tsaf zai gane.To mene ne ma abin yi wa mutumen da yake da ƙarfin power ɗaukar siffar mace? Shirun dai ne ya fi alkhairi a gare ni. Kafaɗata ya dafa sai na ji wani zuuut,sai muka ɓace daga cikin toilet zuwa daularsa wacce kusan a can muke taro masu muhimmancin sosai ko kuma in wani sabon members ya shigo.Ban fita daga wannan mamakin ba na ji na yi sama cikin iska kafin kuma in ji ni gammm,bayana ya bugu da bango yayin da hannuwana kuma aka banƙare su tare da ɗaure su da kacar tsafi. “Babu soyayya a tsarin ƙungiyarmu,amma kai ka karya doka! Zaɓi biyu zan baka ko dai ka sadaukar da budurwar da kake so,ko kuma na aika ka ɓoyayyar duniya yanzu nan tun kafin wa'adin shekarunka su cika” Ido na rumtse gam,a cikin zaɓin biyu babu mai sauƙi a gare ni.Shekara biyar ta rage mini a doron duniya kamar yadda muka yi yarjejeniya a ranar da zan sayar da ruhina,an bani shekaru goma na rayuwa a wannan duniya kafin na isa ɗayar,a cikin goman kuma na yi biyar saura biyar suka rage mini.‘Wane zaɓi zan ɗauka?’ na tambayi kaina a zuci....... [16/11 à 09:04] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 04 “Wato soyayyar da kake yi mata har ta kai ka kasa sadaukar da ita kai tsaye shi ne ka tsaya shawara? Hahaha! Ōgāfōr̃!” Oga yayi lafazin ƙarshe cikin Yaren matsafa a nan take kuma na ga tile ɗin ɗakin na darewa wata jar turɓaya na bayyana kuma sai girrrr kake shi tamkar ƙatuwar tirelar ɗan danƙarau mai yin gina. A inda nake can sama ɗaure a jikin bango nake kallon duk abin da ke faru,gidan ƙasa ne ya bayyana sai a lokacin kuma kacocin hannuna suka kwance kansu yayin da na soma yawo cikin iska ina kaɗawa kamar wata leda. Wasu ɗalasiman tsafi Oga ya soma kafin ya ce “ je ka ɓoyayyar duniya ka yi ziyara na tsawon kwana uku,in ka fito daga ciki sai ka bani zaɓin ka” rufe bakinsa ke da wuya na soma ji na ina yin ƙasa har na shiga dogon ramen mai ɗauke da wata daular . Ina shiga ciki komai ya soma komawa normal ya ɗinke,sai da na ja wani numfashi sa'ilin da na ji ƙafafuna sun dogane da ƙasa. Baƙar ƙofar na kalla ta gabana wacce nake da tabbacin ita ce za ta sada ni da ainahin abin da ake kira da ɓoyayyar duniyar.Na shagala sosai ina kallon ƙofar tare da tunanin da na san ba zai fishe ni dare ba,kawai sai na ji ƙiiiiii ƙofar ta buɗe da kanta. Ido na tsura ina jiran ganin wanda zai fito,amma sai na ji wata murya na cewa “ Barka da zuwa duniyar Ruhaniya ” ban amsa ba haka ban gusa daga inda nake ba . Sai na ji an kamo dukkan hannuwana biyu ana jana amma ban ganin masu jan nawa,a dole na soma taka ƙafata har muka bi ta ƙofar nan a take kuma ta rufe ji kake gammm.Duhu ne ya turniƙe wurin,sai a lokacin kuma na ga inuwar masu jaye da ni saboda wani jan haske da goshinsu ke fitar wa kamar wuta. Ci gaba suka yi da ja na izuwa ciki,matakala muka soma takawa muna daɗa yin can ƙasa.Har muka ainahin duniyar,nan ɗin ko ina da haske tamkar goshin azahar haka. Duk masu bi suna wuce wa na soma duba,dayansu siffar mutane ce da su yayin da sauran kuma suke ɗauke da sifofin dabbobi iri-iri. Irin inuwar nan gani ta waɗanda suka yi min iso,a zuci na ce ‘ ko su waye su?’ “Dōr̃ānī! Masu kula da shige da ficen duk al'ummar nahiyar nan.Ko da wasa wani ya tsaya hutawa dangane da aikin da yake yi za su hukunta shi ne” na ji muryar ɗazu ta faɗa wacce ta tarbo ni tun a bakin ƙofa. Saitin inda murya ta fito na duba,sai na ga yanzu ana ganinsa da kyau sai dai muninsa ma ba zai bari ka ci gaba da kallonsa ba. “Amma kuma ƴan Adam ne?” na tambaya. “Duk faɗin nan babu mai ruhin bil'adama sai kai ,duk waɗanda ka gani da irin siffarka to mutum ne da rigar aljan.Bima'ana gangar jikin ce ta mutum amma ruhin aljani ne a ciki” “To ya ake hakan tana faruwa?” na sake jefo masa tambayar. “Mutanen da suka sayar da ruhinsu ga MAFIYA ,bayan wa'adin shekarun da aka ɗibar musu ya cika za a aiko da su izuwa nan.Ruhikansu za su dinga yin bauta ,yayin da gangar jikinsu kuma aljanai za su ɗauke ta su dinga amfani da ita.” yana kawo wa nan sai yayi shiru yayin da ɗaya abokin aikin nasa ya ɗora da cewa “ dayawan jinnu na son ganin kansu a duniyar bil'adama sai dai babu damar yin haka don ba za su iya bayyana da siffarsu ba,wannan ya sa suka ƙulla yarjejeniya da manyan masu ƙungiyoyin asiri da su dinga sayar musa da gangar jiki” “To mi za su yi da ita?” na yi tambayar cikin zaƙuwa zuciyata na bugawa jin ni ma abin da ke shirin faruwa da ni kenan nan da wasu shekaru.Sai da suka ƙyalƙyace da dariya kafin su yi haɗin baki wurin cewa “ duk wanda ya sayi gangar jikinka in yana so zai iya shiga duniya yayi yawo,wasu ma har auren bil'adama suke yi ” Tsoro ne ya kama ni,sai nake ganin tamkar in na dawo da zama a duniyar nan aljanin da ya sayi gangar jikina zai iya zuwa ya cutar da Ammyna. “Amma wanda ya sayar da ruhinsa ga MAFIYA shin zai iya karɓe shi kuwa? Ina nufin akwai wata hanya da mutum zai bi ya rushe waccan yarjejeniyar ta farko sai a kafa masa ta biyu?” duk shiru suka yi suna kallona,na gyara tsayuwa tare da matsawa can gaba ta yadda za mu yi facing juna na ce “please ku sanar da ni” “Eh to ba za a rasa ba,sai dai sharuɗan suna da tsauri sosai” Duk da ban ji su ba haka na ji raina ya ɗan sanyaya har sai da na sauke ajiyar zuciya da kuma ɗan guntun murmushi ko ba komai zan samu damar da zan yi rayuwa da abar ƙaunata. Muna nan tsaye wata rundunar wasu inuwoyi ta zo wuce wa,inuwar siffar mutum ce da ita amma babu gangar jiki. “Ka ga wannan shine ruhi! ” ya faɗa. “Amma suna jin magana?” na tambaya,babu wanda ya bani amsa sai yin gaba suka yi har na soma take musu baya suka ce “ kar ka biyo mu,tuni mun gama aikinmu yi maka iso da kuma amsa tambayoyinka” “To amma ina zan je?” na yi tambayar cikin ɗaga murya,ko juyo wa ba su yi ba ballantana su bani amsa a haka suka ɓacewa ganina.Sai a yanzu ma ne na ji mugun tsoro ya shige ni fiye da na farko,haka na soma bulaye a ƙatuwar duniyar ina kallon abubuwan ban mamaki har na isa wani wuri inda ake yi wa wani aski.Duk suka ɗago suna dubana kafin su fara ƴar kallon-kallon,ɗaya daga cikinsu ya ce “ wane ne kai?” Ba tare da wani tunani ba na basa amsa da “ Ni bil'adama ne!” ko ida rufe baki ban yi ba suka yi min caaaa kowa na faɗar ra'ayinsa“ a'a ni zan ɗauka! ” “A'a wannan fa gangar jikin tawa ce! ” “ kai kana da wajen biyu fa ka bar min kawai” Ido kawai na rumtse ina rawar jiki,jin ana rigima akan gangar jikina wacce Allah ne ya halitta min ita amma saboda wata buƙatata na butulce wa rahamarsa na sayar.Ina cikin haka ne sai na soma jin canjin yanayi,ina ware idona sai na koma fanko wato ruhi babu gangar jiki.Da ido nake kallon yadda ake faɗan shiga gangar jikina wacce ta zama tamkar riga mai haɗe da wando............ Talla! Talla! Talla!!!! Set d'in gyaran gashinmu na dauke da * Shampoing don wanke gashi * Man ganshi da zai taimakawa gashin wajen k'ara tsayi * Man gashi wanda zai cire miki kwarkwashi/dandruff/Pellicules * Garin ambunu da zai hana karyewar gashi * Man karkar da zai taimakawa gashi wajen k'ara bak'i * Garim amrfit don sakawa a hamata ta kasance cikin kamshi * Man coco na asali don gyaran fata +22780416252 [17/11 à 15:36] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 05 Ni da gangar jikina amma banda iko da ita wannan lokaci,ban ma san taƙamaimai ya zan yi na mayar da ruhina a cikinta ba ko kuwa sun maido min ita.A yanzu da nake gantali cikin iskan ɓoyayyar duniya sai na fahimci a cikin MAFIYA ni ba kowa ne ba fa ce ɗan ƙaramin jinjiri ashe ban san komai a kanta ba. Dōr̃ānī kamar yadda aka sanar da ni sunansu tun shigowa ta nan,irinsu ne su biyu suka zo suka ƙwace gangar jikina daga hannun aljanan kafin su miƙo min . “Ka shiga gangar jikinka sannan ka koma duniyarku tun da wa'adin da aka ɗebar ma ya cika,ka yi kwana uku cicif ” Tsakanin furucinsa na cewa na yi kwana uku alhalin ni dai a lissafina ba zai wuce na yi minti talatin ba,da kuma tunanin yadda zan mayar da gangar jikin nawa a ciki sai na rasa wane zan yi. “Ka mayar mana za mu mayar da kai” ya ƙara faɗa . “Ban san ya zan yi na mayar da ruhina a ciki ba” na basa amsa. Suka kalli juna kafin kuma su haɗin baki wurin cewa “ kai ɗin ba ahalin MAFIYA ba ne?” Na jinjina kai na ce “sosai ni ɗin ɗana ga Mafiya amma ban san ya ake yin duk abubuwan nan ba” ban rufe bakina ba na ji sun soma karanta wasu ɗalasima wanda na yi imani na tsafi ne.Wani girrrr na soma ji,gangar jikina na haɗe wa da ruhina ban san ta yaya hakan ta faru ba amma tabbas yanzu na dawo HAROON ɗina. Na ja ajiyar zuciya lokacin da suka ja ni izuwa can wajen ƙofar fita,na kasa haƙuri na ce “ amma ɗazu kamar na ji ka ce wai har na yi kwana uku a nan,sai nake ganin kamar minti talatin ne ko zuwa da biyar haka” “Lokacin nan ba iri ɗaya ba ne da na duniyarku,duk minti goma ɗin ku matsayin kwana ɗaya yake a nan” ban kai ga ƙara yi masa wata tambayar ba suka cillo ni waje. Ta hanyar da na bi na shigo nan ta haka na koma,a gaban idona yanzu ma can saman ya tsage kamar wata leda marar nauyi haka na tashi cikin iska na fito har tsakar fadar Oga ,tile ɗin ya koma ya ɗinke kansa. Ɗaya bayan ɗaya nake kallon members ɗin ƙungiyar tamu,da dukkan alamu sun shirya wa fitowar tawa kamar yadda nake tsammanin Oga ya sanar da su komai. A cikin abin da bai fi minti biyu ba na ga wani sabon abu wanda can farko ban taɓa ganinsa ba,ba komai ne bai sai shatin Cross a goshin kowa na member ƙungiyar sannan a ƙasan Cross ɗin kowanne daga cikinsu yana da alamun lamba,wasu 9,wasu 18 da dai sauransu.Ban yi nauyin baki ba wurin cewa “ Oga lambobin mene ne nake gani a goshi mutane?” Bai bani amsa ba sai jin shuuu na yi,wani ɗan madaidaicin madubi ne ya zo yayi tsaye a gabana,ba wai wani ya riƙe shi ba a'a shi ke riƙe da kansa.A ta cikin madubin na hango hoton fuskata,wannan karon da tsokarta irin ta ƴan adam ba ƙwarangwal ce ba.Lamba ɗaya(01) na gani a tsakiyar goshina kuma ni ma ina da zanen Cross ɗin,ina gama gani madubin ya ɓace daga gabana. Sai a lokacin Oga ya soma magana,“ Barka da shigowa wani level daga cikin MAFIYA! A can farko ba kowa ne kai ba face costumer mu,amma a yanzu kana level 1 sannan kamar yadda ka nemi alfarmar janye yarjejeniyar mu ta farko domin kawo wata sabuwa,mun karɓi kokenka.Sai dai kamar tun can farko yanzu ma zan sake jaddada maka cewa kowanne tasiri yana da farashi,ina nufin yanzu shekaru biyar ɗin da suka rage maka a duniya za ka iya ƙara su domin yin doguwar rayuwa” yana kawo wa nan sai yayi shiru tare da nuna mini kujera na je na zauna kamar sauran. Zamana kan kujerar sai na ji tamkar ba normal kujera ba ce amma na dai yi shiru kawai ina jiran ƙarin bayani. “ HAROON ?” Oga ya kira sunana,na ɗaga kai na kalle shi sai kuma na je zan mayar da shi ƙasa amma ya hana ni ta hanyar ce mini “ tsakiyar ido za ka kalle ni sannan ka sanar da ni ka gani a ciki” Har sai da na ɗan ƙanƙance idona don ƙara samun tabbacin abin da nake gani shin gaskiya ne ko kuwa? “Mi kake gani?” ya jefo mini tambayar. “ Maƙabarta!” na basa amsa. “Ka san me ake yi a can?” “Eh na sani Oga!” “Yawwa madallah da kai HAROON tabbas alamu sun nuna kana yunwar ƙara tsawon rai” cewar Oga kafin ya nufi allon da yake yi mana rubutu ko nace darasi.Wani suna ne ya rubuta mai harafi bakwai wanda tuni na soma tambayar kaina ‘ mene ne kuma alaƙarmu da sunan?’ ashe kuwa amsar na kusa. “ HAROON ko tashi ka karanta mana abin da ke rubuce a nan” Oga ya umarce ni. Na tashi tsaye kamar yadda ya buƙata kafin na karanta “ likafani ” “Ƙwarai kuwa likafani ne kamar yadda ka karanta ɗin,ka yi daidai ina fatan kuma aikin da za ka yi da shi shi ma ɗin ya zama daidai” “Aiki kuma Oga?” na tambaya cike da tsoro,duk kowa ya kwashe da dariya sai da suka yi son ransu kafin Oga ya umarci kowa yayi shiru.Fuskarsa babu alamun wasa ya dube ni yana cewa “daga lokacin da wa'adin shekaru biyar ɗinka ya cika to za ka dinga farautar likafanin sabuwar gawa domin luluɓa shi a jikinka ka kwana da shi,ta wannan hanyar ce kawai za ka ci gaba da rayuwa a wannan duniyar akasin haka kuma za ka koma inda ka fito yanzu.Na sanar da kai ne tun yanzu don ka zamana cikin shiri,abu na biyu kuma da ƙungiya ke buƙata a wurinka shine tsofin takalmi na yara ƙanana.Kowa zai iya tafiya meeting ya ida” yana gama faɗa ya bi wata hanya ya shige yayin da kowa ya watse ya bar ni cikin zullumi. Dole dangin na ƙi ce ta saka ni fitowa ni ma,sai yanzu na tuna inda na bar motata wato can tsohon gidana.Taxi na shiga aka kai ni can amma abun mamaki babu motar a nan,a dole na ƙara shiga wata taxi ɗin na nufi gida. Tun a bakin ƙofa na ga kallon da direbana ke yi mini,kamar zai yi shiru sai kuma ya kasa ya ce “yalaɓai yanzu ko minti ɗaya ba a yi ba na ganka da baƙaƙen suite fa kuma ga shi har ka canza kaya” Na haɗe rai na ce “wato sa ido kake yi min?” “Yi haƙuri yalaɓai” ya faɗa yana rusunawa. Ina shiga cikin falo na ci karo da Ammy ita ma idon ta waro tana cewa “ HAROON canje-canjen kayan na mene ne? Ko don ka burge Malama Zainab ne? Hahaha! Wannan kayan fa kamar ma sun yi datti,waɗancan ɗin dai sun fi yi maka kyau” Murmushi kawai na sakar mata ina cewa “ina zuwa” sai kuma na haye can sama,ina buɗe ɗakina na hangi irina sak yana ƙoƙarin shiga madubina. “Dakata!” na faɗa da sauri,ya juyo muka haɗa ido amma bai saurare ni ba yayi wata suka cikin madubin tamkar wanda ya shiga ruwa haka ya nitse ciki tun ina ganin inuwarsa har madubin ya dawo normal........ Assalamu alaikum,mata da ƴan matan garin Agadas.CHAFA'ATU MAKE-UP fitacciyar kuma jajirtaciya mai koyar da kwalliya iri-iri.Ta yi tattaki tun daga Nigeria ta zo nan Nijar a garin Agadas domin horar da masu buƙatar koyon kwalliya,ɗaurin kallabi.Wannan horar wa da za a yi za ta kwashi kimanin sati biyu ,kuɗin koyo jika ashirin ne (20.000f).Ga masu buƙatar ƙarin bayanin za su iya kiranmu kai tsaye ta wannan lambar 88584336 ,ko kuma ku tuntuɓe mu lambarmu ta WhatsApp 09041604348 . [19/11 à 07:55] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 06 Gaban madubin na je na soma shafa shi tamkar wasu ruwan Teku haka na ji hannuna ya nitse a ciki.A kullum cikin ganin sabbin abubuwa nake tare da madubin da ni ne da kaina na saye shi,maimakon da na saka hannuna na ga ya nitse na fiddo shi a'a sai na gwada shigar da dukkan gangar jikina. Hazo-hazo na soma gani a cikin sabuwar duniyar da na tsunduma kaina,ban ganin komai sai wani abu da ke zuba kamar dusar ƙanƙara .Idona na soma ƙanƙancewa nan na hango gobena,ga ni tare da Malama Zainab har da yarinyarmu.Wani daɗi ya wanzu a zuciyata,ina son ƙara samun wani bayanin amma daga can waccan duniyar nake jin muryar Ammyna a kunnena raɗau.Da sauri na fito ina mamakin ‘ dama ana iya shiga cikin madubi ? ’ Sai kuma na watsar da tambayar na nufi ƙofa na buɗe murmushi kan fuskata. “ HAROON ka fito mana ko ka manta yau rana ce ta musamman a gare mu?” Ammy ta faɗa tana murmushi tare da gyara min zaman rigata ta sama. Sai yanzu na lura,kayan jikina sun sauya daga waɗanda na shigo da su zuwa irin mai kama da ni da ya ɓuya cikin madubi. ‘ Wane abu ne zai faru mai muhimmanci haka?’ na yi wa kaina tambayar a zuci,yayin da kuma na samu amsar tambayar kuma a cikin kwanyata “ yau za ka sanar da Malama Zainab kana son ta,shine alƙawarin da ka yi wa Ammy ” Shiru na yi ina tunanin ‘ ta ya aka yi nake jin muryar mutum na yi min magana cikin ƙwaƙwalwa? ’ Nan ɗin ma wata amsar aka bani “ saboda yanzu ka fita daga matsayin 0 ka koma level 01 ,kana da buƙatar ɗan kariya mai baka rahoto akan abubuwa da dama, waɗanda suka faru da kuma shawara wurin yanke hukunci” Ajiyar zuciya kawai na sauke ina kallon Ammy tsakiyar ido,“ ya dai? Kar ka ce min dai tsoro kake ji?” Ammy ta faɗa ,na girgiza kai na ce “ mu tafi ga ta can har ta iso” Da mamaki Ammy ta ce “ ta ya aka yi ka san ta iso?” sai ta ja kumatuna. Abin da na fahimta wannan ɗin sam ba furcin tunanina da niyyata ba ne, mataimakina ne ya furta ba ni ba.Amma sai na yi saurin cewa Ammy “ saboda ina mugun ƙaunarta shi yasa a duk in tana kusa da ni ina jin sautin zuciyata na canza wa” Ammy ta shiga yi min dariya kafin ta kama hannuna kamar wani ƙaramin yaro muka fito. Ina taka step ina kallon Malama Zainab wacce ke zaune tana duba wani littafi,yanayin nutsuwarta da cikar kamalarta sun fi komai burge ni a tattare da ita. Ammy ce ta yi sallama,da sauri ta ɗago tana amsawa tare da gaishe ta. “Lafiya lau Malama ya gida ina kuma iyayenki fatan duk kuna lafiya?” “Alhamdullah suna gaishe ki ma” ta faɗa cikin rawar murya tana sunne kai,cikin ƙwaƙwalwata na ji muryar nan na ce mini “ kar ka cika kallonta hakan fa zai sa ta fasa son ka” Ammy ta ɗan zungure ni,na dube ta sai ta yi min alamu kan na yi wa malamar magana.Na yi gyaran murya na ce “ uhum! Hajiya ko na ce Malama na gode sosai da kika karɓi wannan aiki na koyar da Mamana karatu muna godiya...” sai kuma na yi shiru, Ammy ta gusa ta bar falon tana harare na tare da yi min alama kan na zauna kan kujera .Abin da Ammy ba ta sani ba iya wannan tsayuwar ji na nake a takure,tamkar wanda ya shiga wurin da babu iskan shaƙa na san kuma hakan bai rasa nasaba da ƙarfin imaninta. Ɗan nesa da ita na yi,sai na ji abin yayi dama .Na sauke ajiyar zuciya kafin na ce “ Malama Zainaaab?” a hankali ta ɗago ta dube ni muka haɗa ido,sai na ji wani ƙuna tamkar ta watso min barkono wannan karon ni ne na sauke idona ina rayawa a zuci ‘ tabbas da matsala! Yarinyar da na kasa haɗa ido da ita ta yaya kenan za mu yi aure har mu haihu? Ko dai duk abubuwan da na gani cikin madubi ƙarya ne? ’ Ɗayar muryar mai min magana cikin kwanya ta ce “ sam wannan ba ƙarya ba ce,tabbas za ka aure ta sannan ku samu yara sai dai saurin yiyuwar haka na tattare da kai akwai abubuwan da ake buƙata ka yi kafin har ka cimma ƙudirinka in ka ji kana iya wa tun yau za ka soma” Tun da na soma jin maganar na yi shiru har aka ida kafin na sake tambayar muryar ‘ ta yaya kenan? ’ “Ta hanyar sato farin tauraro daga jikin wani bil'adama mai sakaci,tabbas da tauraronsa za ka yi amfani domin biyan buƙatarka” ina gama jin amsa na saki murmushi ,ina ɗago kai sai na kama Malama Zainab na satar kallona. Na sakar mata murmushi yayin da ta yi saurin miƙe wa tana cewa “ zan koma ina da ɗalibai da zan yi wa karatu” “Ok jira na kira Ammy ” na faɗa tare da zuwa ɗakin Ammy,tana gani na ta miƙe tana cewa “ komai ya tafi daidai? Ka furta mata ɗin kana son ta?” Na yi murmushi mai sauti na ce “ A'a Ammy amma mun samu kusanci sosai ina ga ita ma tana sona ” “Wato ba ka furta mata ba? Mtsww !” ta ja tsuki tana harare na tare da ficewa,duk sai na ji babu daɗi na take mata baya. Da murmushinta mai tsadar nan take sanar da Ammy uzurinta,“ HAROON ka sauke Malama a makaranta” “To Ammy ” na furta ba tare da na san yin haka babban kuskure ne a rayuwata ba.Har kusa motata Ammy ta yi mana rakiya,ita ce da kanta ta buɗe wa Malama Zainab gidan gaba.Dakyar na shiga na zauna na yi wa motar key,numfashina sai barazanar tsaya wa yake ba don komai ba sai don na yi kusa da farin ruhinta. Ina tuƙi ina haƙi kamar wanda yayi tseren doki,zuciyata ji nake tana matse wa tana takurewa wuri guda .Hancina kuwa tamkar wanda aka matse sam babu daɗi ,iya ta baki kawai nake samu ina sheɗawa.Tun ina daurewa har na kasa,ina ƙoƙarin tsayar da motar kuma wayar Malama Zainab ta hau ruri ƙira'ar Sheikh Aliyu Jabeer ce inda yake karanta suratul yaseen. “Yiiii!” na soma kyarma yayin da na kusa sakin sitiyarin motar ina,idona kuwa wani baƙin abu kawai nake gani da alamun lantarkin nasu ne yake dab da tsayawa.Hannunta na ji kan nawa on daidaita tsayuwar motar sai dai kafin wannan zuciyata ce ta tsaya cak da bugawa ........ Ga masu son fara yin payment ga detail nan ,500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 .Ki tura kawo sai ki turo min evidence sai na saka ki group. Talla! Talla! Talla!!! Set d'in gyaran gashinmu na dauke da * Shampoing don wanke gashi * Man ganshi da zai taimakawa gashin wajen k'ara tsayi * Man gashi wanda zai cire miki kwarkwashi/dandruff/Pellicules * Garin ambunu da zai hana karyewar gashi * Man karkar da zai taimakawa gashi wajen k'ara bak'i * Garim amrfit don sakawa a hamata ta kasance cikin kamshi * Man coco na asali don gyaran fata +22780416252 [21/11 à 15:01] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 07 Cikin ikon Allah Malama Zainab ta yi nasarar tsayar da motar wuri guda,sama-sama nake jin sautin muryarta tana kiran sunana haɗi da girgiza ni “ HAROON ! HAROON ! Please ka tashi ! Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! ” ta furta kafin ta fita ƙila don neman taimako. Fitarta yayi daidai da dawowar bugun zuciyata,na buɗe murfin motar na soma kelaya amai kamar raina zai fita.Ta zagayo tare da yin tsaye tana kallona,sai kuma ta je za ta tsallaka titi tana mai tsayar da mai sayar da ruwa .Manta wa na yi da halin da nake ciki na yi wani uban tsalle na jawo ta baya don kauce ta daga motar da saura ƙiris ta kaɗe ta. Tamkar yadda in boom ta fashe take ɗaga mutum sama ta cilla shi gefe haka ce ta faru da na jawo Malama Zainab,sai da muka yi sama ni da ita kafin mu faɗa can gefe kaina ya bugu da dutse yayin da ita kuma ta faɗo kan ƙirjina gaba ɗayanta.A wannan karon babu wani jinkiri ruhina yayi nisan zango daga wannan duniyar na fita daga hayyacina ban ƙara sanin abin da ya faru ba. A ruɗe Malama Zainab ta tashi daga jikin HAROON idonta na kawo ruwa,mutanen da ke bakin hanya ne suka matso.Ita ɗin ba wata ɓoyayya ba ce a garin Yamai wannan yasa cike da girmamawa suka fara tambayarta ba'asi. “Yayana ne ya faɗi ne kansa ya bugu” ta faɗa cikin kuka ganin kan HAROON sai jini yake zubarwa,wasu samari suka taimaka mata suka saka shi a gidan baya yayin da ita kuma ta hau mazaunin direba ta tuƙa shi zuwa wata asibiti ta kuɗi. Da isar su aka karɓe shi,duk da kuwa ba tada kuɗi a hannunta amma sai ta nuna musu katin ɗan ƙasarta cikin ikon Allah ma wasu sun santa.Abu na farko da aka soma yi wa HAROON shine tsayar da jinin kansa aka naɗe da bandeji,cikin ikon Allah kuma numfashin nasa ya dawo normal sai dai yana buƙatar hutu. Sai a lokacin kuma ta kira mahaifiyarsa ta shaida mata ,babu jimawa kuwa sai ga Ammy.Ita ma kukan ta soma sai ya zamana babu mai rarrashin wani,ita sai faman faɗin “ HAROON kar ka mutu ka bar ni,kai kaɗai ne farin cikina a duniyar nan” Ita kuma Malama Zainab cewa take “ duk laifina ne,da ace ban yarda ya sauke ni ba da ƙila hakan bai faru ba,saboda son kasancewa da shi yasa na aminta oh ni Zainabu na ga ikon Allah! ” sai kuma ta fashe da kuka. Bacci nake mai kamar mutuwa, sama-sama nake jin sautin kukansu a hankali na ware idona ba tare da na buɗe su tarau ba.Ta ƙasan gashin ido nake hango yadda masoyana biyun ke kuka,sai na shagala yadda manyan idon Malama ke tsiyayar da ruwa ,pink leɓenta kuma duk ya jiƙe da yawunta yana rawa.Yatsun nan nata masu ɗaukar hankalina sai shafar hawaye suke,na dafe gefen kaina da ke sara min kafin na kira sunan Ammy.Da sauri ta matso kusa da ni tana cewa “ ka tashi? Mi kake ji? Ina yake ma ciwo?” Murmushi na sakar mata tare da nuna mata saitin zuciyata da kuma yi mata alama da Malama Zainab,wacce ta yi tsaye tana kallona hawaye na bin kumatunta yayin da fuskarta ke ɗauke da ɗan murmushi. Ammy ta ce “ za ka same ta in sha Allah kar ka wani damu” sai kawai na lumshe ido ina tuna abin da ya faru da ni, a daidai lokacin da mugun iskan nan mai ƙarfi yayi cilli da ni kaina ya bugu da dutse ɗigon jinina na farko ya ɗiga ga ƙasa Oganmu na gani a can gefe a tsaye yana kallona,bai samu damar ƙaraso wa inda nake ba sai da Malama Zainab ta ɗan yi nesa da ni,abin da na fahimta shi kansa yana shakkarta.Hakan kuma sai yasa na ƙara jin mugun sonta da ƙaunarta sun ƙaru a Wani farin abu ya saka min a inda kaina ya fashe kafin ya ɓace wa ganina. Dakyar ta iya cewa “ ya jikin naka?” Ammy ta ce “ bari na kira likita” sai ta fice. Sai a lokacin na amsa mata “Da sauƙi! Na gode sosai” Ta ɗan dube ni cikin ido kafin ta ce “ babu komai!” sai kuma duk muka yi shiru ,ni na ƙure ta da ido yayin da ita kuma take satar kallona lokaci-lokaci .A haka Ammy ta shigo ita da wata nurse,awon tension ta yi min kafin ta ce “ ka gyara zan yi ma allura ga cinya” “Ga cinyaaa ?” Malama Zainab ta faɗa da sauri duk muka kalle dukkan mu ukun sai ta yi saurin wayancewa ta ce “ ina nufin wace irin allura ce za a yi ga cinya? A yi ga hannu ai zai fi” Nurse ɗin ta ce “ saboda cinya ta fi tsoka,in ga hannu ne za ta iya yi masa zafi” “Bai komai ai shi namiji ne,ki yi masa ga hannun kawai tun da dai ana yi” ta faɗa cike da kishin da ita kanta ba ta san ya fito ba,Ammy dai sai murmushi take. Hannun rigar na cire sannan nurse ɗin ta yi min allura ga damtse,ni aka caka da allurar amma Malama Zainab ce ta yi ƙara har da rumtse ido. Nurse ɗin ta yi dariya tana mai cewa “ ah Madam irin wannan tattali haka ? Ko duk don kar a yi miki kishiya ne?” “Wace irin kishiya kuma ? Ai ...ai ba mij...” sai kuma ta yi shiru ƙila yadda muka haɗa ido da ita ne yasa ta kasa idawa. “Zuwa an jima za a sallame ku in Dr ya hau aiki,sannan akwai gwaje-gwajen da aka yi ana jiran result” nurse ɗin ta faɗa kafin ta fice. “Ni ma zan tafi Mama,am...ina nufin Hajiya Allah ya bada lafiya” shine abin da ta faɗa kafin Mama ta yi mata rakiya. Suna fita Oga ya bayyana a cikin ɗakin fuskar nan tasa kicin-kicin,kamar zai fashewa da kuka ya ce “ ina mai yi maka gargaɗi akan ka bar sheɗaniyar yarinyar can.Sam tarayyarku babu alkhairi a tattare da ita,sannan ina so ka yi gaggawar barin asibitin nan kafin ta kwaso zugar ɗalibanta su zo duba ka” Sam ban yi mamakin ganin nasa ba,amma na fi mamakin yadda yake so na bar asibiti alhalin banda lafiya.“ Amma Oga me yasa zan tafi? ” “Za ka iya jurar addu'o'in da za su yi ita da zugar ɗalibanta? Kai ka rasa wacce za ka so sai babbar maƙiyiyarmu? Ko ba ka san manyan sheɗanu sun yi tirrr da halinta ba? In banda karatun littafinsu babu abin da ta iya,a haka ne kake tunanin haɗa wuta da ruwa wuri guda?” “Ina son ta!” na furta kai tsaye ba tare da shakka ba,“ dole ka rabu da ita” “Zan zauna da ita Oga,kai dai kawai ka zuba min ido” bai kai ga bani amsa ba Ammy ta shigo. “ Da wa kake magana HAROON ?” ta tambaye ni. “A'a ban yi magana ba Ammy ” “Yanzun nan kafin na shigo na ji kana magana fa” “To ƙila ko dai a ɗaya ɗakin ne” “Ok to .Ka ga Malama Zainab na son ka ko? In sha Allah zan je can gidansu ni da Kawunka ” sam ban ɗauki maganar da wani muhimmanci ba na miƙe na shiga toilet saboda yadda na ji marata ta ƙulle,kamar jira ake ina shiga toilet ɗin na ga an zagaye ni na zamana a tsakiyarsu.Duka mutanen na gane su ahalin ƙungiyarmu ne,ban san da wane Siddabaru suka yi amfani wurin ɓatar da ni ba sai kawai na tsinci kaina a wani gun daban. Cikin faɗa Oga ke faɗa “tun da ka ji za ka iya sai ka zo a ƙaddamar da kai ta yadda za ka samu power da yawa,sannan waccan abar ka sani lokaci guda ne kawai za ka iya kusantarta wato in tana period” Cike da mamaki nake kallonsa kafin na ce “wannan ai ƙazanta ce! Ta ya zan kusanci matata da jinin al'ada?” “Ba kada zaɓi” Oga ya faɗa yana matsowa kusa da ni hannunsa riƙe da wata ƴar tasa ,yatsana manuniyar ya kama ya sa reza ya tsaga shi nan jinina ya soma zuba cikin tasar nan har sai da ta cika duka.Ya ajiye tasar sannan ya saka wani abu ya rufe wurin da ya tsaga sai jinin ya tsaya. Daga nan wani ɗakin sirri dukkanmu muka shiga ,ni dai ban san da zamansa ba amma su sauran da alamu sun saba shigowa.Komai na cikin ɗakin baƙi ƙirin yake sannan an yi masa adon zanen Cross da jan penti,gaban wata aba mai kamar halittar duniyar sama Oga ya je ya tsaya jinina da ke cikin tasa ya dangwala a yatsa ya shafa daidai bakin halittar ,wani irin girrrr na ji a yatsan nawa kafin kuma a sannu wani abu ya game dukkan gangar jikina.A gabana dukkan members ɗin suka dinga dangwalar jinina da yatsa suna lasa da alamu ma kamar daɗinsa suke ji saboda yadda kowa ke ta ƙoƙarin ganin ya fi ɗan uwansa sha.Bayan nan sai Oga ya ja mu izuwa wani katafafen capet duk kowa ya zauna amma ni ya hana ni,na buɗe baki da niyyar tambayarsa don me banda ni,kawai na ga abokan ƙungiyarmu sun shiga yin aman kuɗi sabbi dal da su wani irin tsoro ya kama ni har ban san lokacin da na saki ihu ba. My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [23/11 à 07:44] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 08 Tun da uwar da ta haife ni ban taɓa ganin inda mutum ɗan Adam yayi aman kuɗi ba sai yanzu,tamkar wasu ruwa haka takardun kuɗin ke fito wa daga bakin kowanne members har sai da suka kusan cika ƙaton capet ɗin.Ni kuwa banda kyarma babu abin da jikina ke yi,a nan take a inda nake tsaye kuma na ƙaryata fassarar da na yi wa sunan MAFIYA daga “cikar muradi ” zuwa “tsafi da shan jini”. Ashe ban kai maƙura wurin mamakina ba sai da na ga kuɗin na ware kansu suna yin dunƙule-dunƙule na 100k ,kamar ƙyaftawar ido suka jeri rasss a hakan kuma kowace takardar kuɗi ta san wanda ya amayar da ita . “ HAROON wannan ɗin duk kuɗinka ne!” Oga ya faɗa yana murmushi haɗi da bubuga gefen kafaɗata. Na ce “ duk me zan yi da uban kuɗin nan?” Sai duk suka hau yi min dariya,can suka tsagaita Oga ya ce “ ka manta akwai aiki jajur a gabanka? Ko da kanka za ka dinga bin maƙabartu kana ciro likafanin?” “Wane irin likafani kuma?” na tambaya cikin tsoro. Oga ya haɗe rai ya ce “ wanda zai taimaka ma ka yi tsawon rai nan gaba,ko ka manta ne?” Murya na rawa na ce “ ban manta ba amma Oga ai sai nan da shekara biyar ko?” “Bayan wannan akwai wasu sharuɗan! Kowanne ƙarshen wata za ka samo mana jinin period na budurwa,kar ka tambaye ni ta yaya .Ka fara tunanin hanyar da za ka bi ka kawo na wannan watan don yau muna ashirin da uku ga wata” Wasu irin yawu na haɗiye masu mugun ɗaci,ido kawai na tsura musu da alamu ko a jikinsu sai harakar gabansu suke suna saka min uban tulin kuɗin a jakakuna. “Amma Oga ina zan ajiye kuɗin nan? ” “Bisa kaina” “Ka yi haƙuri in na je da su gida Ammy za ta zarge ni ” Ran Oga ya ƙara ɓace wa ya ce “ HAROON ka fita idona,kana yawan matsa min da zancen Ammynka in ba ka yi sa'a ba kai ne za ka yi silar mutuwarta ” Gabana ya bada rasss jin wata lukutar masifa,amma na kawar da tsoron gefe na ce “ wannan shine babban kuskuren da za ka yi kuwa a duniya shine taɓa Ammyna,duk duniyar nan banda tamkar ta.Kar ka manta silar ta ne a yau nake cikin wannan ƙazamar rayuwar,Ammyna ita ce komai nawa in babu ita ban ma ga tsiyar da zan yi a duniya ba” duk wurin tsit yayi suna kallona shaye da mamaki,na sani sarai yadda duk ake tsoron Oga ni ma ina tsoronsa amma ba zan juri a taɓa Ammyna ba ko kaɗan ai gwara ya yanki fatar jikina ya fi yi min sauƙi. Ban taɓa ganin Oga cikin fushi irin haka ba sai yanzu,tako ɗaya yayi ya isa inda nake idonsa sun kaɗa sun yi ja sosai. “Ōgāfōr̃!” furucinsa kusan tsinke igiyar da ke saita mini numfashi yayi,na riƙe hannunsa tare da roƙonsa “ please Oga kar ka hukunta ni ta hanyar kai ni ɓoyayyar duniya” sai dai da alamu roƙon nawa a banza ne wai an tsikari kakkausa.Tuni ƙasa ta soma darewa ginin cikin ƙasa ya bayyana,idona na zubar da hawaye na tashi cikin iska kafin na yi nitso cikin dogon ramen a haka ƙasa ta rufe da ni ruf sai gani tsaye a gaban baƙar ƙofar nan a karo na biyu. Yau ɗin ma Dōr̃anī ne suka buɗe min ƙofar tare da yi mini iso a ciki,sai dai fa wata jahar suka kai ni ba nan fara isa ba. “Wannan karon kuma wane laifin ka yi mai yawa har Oga ya ce a kai ka sashen bauta ?” ya tambaye ni. Ƙin basa amsa na yi sai ma tunanin yadda zan yi na fita na soma,“ fatan dai ba wani sirrin ƙungiyar ka fitar ba?” “Ban fa iya surutun nan yau ka bar ni da abin da ya sha min kai” na faɗa cikin masifa,daidai nan muka iso wata duniyar mai cike da abubuwan ban mamaki mutum da jikin maciji,ko kifi,ko doki,mage mai ƙafa ta fi ɗari,ko kuma mage da kan mutum.Maciji mai magana,kare da shan sigari. “Ina ne kuma nan? Me zan yi a nan?” na tambaya a firgice,banza suka yi da ni sai tafiya suke ina take musu baya har muka isa gun wasu tsofi. “Ina ka samo mana ɗan saurayi kuma?” ɗayar tsohuwar ta faɗa tana wani kashe mini ido,yayin da wasu biyun suka taso suka soma shafa ta da sauri na soma ture su ina son guduwa. Dōr̃anī ya ce “ ladabtar da shi za ku yi,shi ɗin yana da muhimmanci ga uwa MAFIYA don haka kar ku taɓa lafiyarsa” Yana gama faɗar haka duk suka ɓata rai waɗanda ma suka yi min ƙawanya sun gusa daga jikina,su ma Dōr̃ānī tafiyarsu suka yi. Wacce ta fi su tsufa duka ita ce ta miƙe tsaye ta ce “ ɗan samari biyo bayana ” Dole dangin naƙi haka na take mata baya zuwa wani sashe mai cike da yana don ta cikinta ma muke bi muna wucewa,mun ɗan yi tafiya sosai kafin ta ja ta tsaya. “Ruhinka nada ƙarfi sosai ta yadda har yanzu Octoba ya kasa karɓe shi duka duk da kuwa ka sayar da shi,uhum! Amma me yasa kake fusata shi haka? Ka san mene ne za a yi maka a nan ɗin?” tsohuwar ta tambaye ni. “Mene ne zan yi a nan ɗin?” na tambaye ta tare da share duk sauran zancen da ta yi. “Matso kusa ka gani” ta faɗa ,na ɗaga ƙafata na isa gare ta abun mamaki sai na hango duniyarmu ta Bil'adama.Wasu abubuwa ta dinga furta wa nan gidaje da ababen hawa suka dinga wuce wa kamar mai yin tariya har ta isa ga asibitin da aka shimfiɗe ni. Wani irina na gani zaune kan gado Ammy na ɓare ayaba tana basa yana sha,gefe guda kuma direbana ne ya ƙura masa ido yana kallo. “Ko ka san me yasa waccan mutumin yake kallon mai kama da kai?” tsohuwar ta tambaye ni. “Eh saboda ba haka nake zama ba,sannan in zan ci abu da hannun dama nake riƙe shi ba hagu ba.Ban cika son mutum ya ƙure ni da ido yana kallo ba” ina gama faɗa sai na ga mai kama da ni ɗin ya mayar da ayabar a hannun dama yana cewa “ Ammy har yanzu hannun ga nawa ciwo yake,kai kuma lafiya ka tsare ni kana kallo? Fita ka ban wuri” Direbana ya miƙe da sauri da ya kai bakin ƙofa sai da ya sake waiwaya wa,nan ɗin ma sai da ta tambaye ni “ me yasa ya waiwaya?” “Saboda yi wa mutum tsawa da hantara ba tabi'ata ba ce” na bata amsa kai tsaye. “To da zarar ka koma duniyarku ya zama dole ka kashe direban can” Sai da na dafe ƙirji na ce “ saboda me?” “Amsar na wurinsa” tana gama faɗa ta wani kamo hannuna muka yi suka tare da sauka can doron duniya mun iso bakin kwalta na ja na tsaya,ta wani ja hannuna tana mai cewa “ kai gara iya ruhinka ne kawai a nan gangar jikinka na can sama” Haka motoci ke ratsawa ta cikinmu ba tare da mun kauce musu ba,wani gidan cin abinci muka je.Da murna take cewa “ tsawon lokaci kenan da ban shigo duniya ba ,ina son abincin nan ya kamata in nemi gangar jiki na shiga ta yadda zan ji daɗin abinci” “Ta ya kenan?” ba ta bani amsa ba ta je jikin wata budurwa wacce ke tsaye jikin mota ita da saurayinta,a gaban idona tsohuwar ta shige jikin yarinyar.Ta ja hannun saurayin suka zauna ta yi odar kaji da lemun kwalba,“ yau sai na baka mamaki zan cinye dukkan kaji biyun nan” budurwa ta furta wanda a baɗini esprit ɗin tsohuwar nan ne.Aka kawo kaji biyu ta cinye su tasss ta sha lemun kwalba,tana gamawa ta fice daga jikin nata ta zo daidai inda nake tsaye tana dariya “ na tsani soyayya,yau na yi silar raba su” sai kuma ta ja ni muka tashi cikin iska muka koma can inda muka fito,gangar jikina na gani a tsaye tana zaman jirana sai dai ban san ya zan yi na koma ciki ba........ My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,DM +22795045822 .Saura page biyu na gama free page kafin nan zan yi discount ga mai so ya biya 400 sai ya tura min shaidar biya ta WhatsApp. Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [25/11 à 13:14] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 09 Wannan tsohuwar ce ta nuna min yadda matsafa ke yi wurin fitar da ruhinsu daga cikin gangar jiki da kuma yadda ake yi a koma. Cike da jin daɗi na isa inda gangar jikina take a tsaye kamar saƙaƙo,yadda ta koyar da ni ɗin da shi na yi amfani na koma ciki.Daga nan sabbin abubuwa ta soma koya min,irin yadda zaka juya tunanin mutum,kashe mutum ba tare da kaca masa wuƙa ko bindiga ba,yadda za ka cutar da wani normal mutum ba tare da shi kansa ya san an cuce shi ba. Daga wannan kuma sai ta soma yi min wani bayani da ya tafi da ruhina. “ HAROON ita duniyar MAFIYA da kake ganinta kowanne members yana samun power ne daga aikin da yake yi,wato iya yawan sacrifice iya adadin yadda ƙarfin ikonka zai ƙaru.Samun power ƙwaya ɗaya ya fi a baka miliyan ɗari,saboda su kuɗin za su ƙare ita kuwa power zaka iya sarrafa ta sosai ta yadda za ka samu dubban abubuwa marar ƙirguwa.Ka ga ko ita wannan wacce kake so ko? To tabbas kana iya yin galaba a kanta muddin dai ka samu power dayawa.Bari na nuna maka wani sirri na musamman da ba kowa ya san da shi ba” sai kuma ta miƙe ta ɗauko wani tandun kwalli ta miƙo min.Na karɓa ina dubanta,ta ce “ shafa shi da idonka sai ka sanar da ni me ka gani” Ban musa ba sai kawai na bi umarninta na shafa kwallin ga dukkan idanuwana,sanyi ne ya ratsa su kamar na ƙanƙara wannan ya sa na ɗan lumshe su.Ina buɗe su kuma na yi tozali da tsohuwar matar nan ta zama tamkar lagwami duk jikinta tattakaken ƙwarangwal ne babu kyawun gani. Ta ce “ wannan kwallin yana taimakawa wurin gane taƙamaimai asalin mutum da kuma niyyarsa a kanka,sannan zai ƙara ma ƙwarjina ta yadda babu wanda ya isa ya kalle ka cikin ido ciki kuwa har da Ammynka”sai ta yi shiru na wani lokaci kafin ta ɗora da “abubuwan da suka fi kawo maki a Mafiya sune mata da ƙananan yara,sai kuma mahaukata.Kowanna daga cikinsu da tasa rawar da yake takawa,in kana son a kowace irin jarabawa ko sabga taka ka yi nasara to da buƙatar ka yi sacrifice na ƙaramin yaro da bai balaga ba...” da sauri na katse ta da tambayar “ amma saboda me?” “Saboda ƙwaƙwalwa yaro a wanke take babu komai cikinta na tunanin wata matsala,sannan zuciyarsa ma haka fara ce fesss babu baƙin cikin kowa .Bakinsa kuwa gaskiya ce tsagwaron ta,irin haka ne zaka samu wasu mutanen da daɗin baki in sun yi magana sai ka ji tasu ta fi ta kowa” “Su kuma mata me yasa ake son sadaukar da su?” na tambaya. Ta yi wani murmushi kafin ta ce “ akwai wanda ya fi mace wuyar sha'ani a duniya? Ita fa kamar sawun keke take baka gane gabanta ballantana bayanta ,wannan ya saka Mafiya ke da buƙatar mata.A sassan jikin mace akwai waɗanda in aka yi tsafi da su aikin ya fi kyau ,daga ciki akwai al'aurarta da kuma mamanta,abu na ƙarshe kuma shine ana yi mata wankan ƙaddamawar sai namiji yayi amfani da ita irin haka ne ke janyo farin jini da dukiya mai tarin yawa” Na jinjina kai na ce “ su kuma mahaukata fa wane dalili ne?” Kai tsaye ta bani amsa da “ a gaskiya sabbin members na MAFIYA waɗanda suke son yin kuɗi sun fi amfani da mahaukata,dalili kuwa shine shi hauka launin cuta ce da ke zuwa daga ƙwaƙwalwa wasu ta jinnu ce wasu kuma haka aka haife su da ita,to ita kanta wannan launin cutar tana da matuƙar muhimmanci a mafiya tana sa member ya ji gamsuwa fiye da in da mutum mai hankali ne ka kusanta” Shiru na yi ina nazari,abin da na ƙara fahimta game da Mafiya wani rikitacen al'amari ne marar kyau.Duk abu na ƙwarai a wurin su ba mai kyau na ne sai gurɓatace,“ to amma yin mu'amala da mace yayin jinin al'ada fa me yake ƙarawa?” na jefo mata tambayar. “Yin haka tamkar rufe ƙofofin taurarin ita macen ne,sannan duk wasu lamurranta za su iya kwaɓe mata yayin da shi kuma namijin rayuwarsa ta ɓoyayyar duniyar za ta yalwanta ” Kasaƙe na yi ina zancen zuci ‘ kenan so ake duk na disashe taurarin Malama Zainab?’ “Bari ka ji HAROON ,babu abin da sheɗanu suka fi ƙauna irin warin jini musamman na al'ada yana da matuƙar muhimmanci a duniyarmu” “Wane irin sheɗanu kuma?” na tambaya kamar wani gara. Sai da ta sheƙe da dariya kafin ta jefo min tambayar ta saka zuciyata tsananta bugi,“ kai a tunaninka kai mutum ne? Bani amsa kai mutum ne?” shiru na yi na kasa cewa komai. Ta ci gaba da cewa “ ka sani tun ranar da ka kwashe kayanka a gaban Manzo ka fita daga sawun mutane,kai sheɗani ne HAROON !” ta faɗa cikin wani sauti wanda ya saka yanar da ke yaɓe ta ko ina ta soma kaɗawa kamar ana iska. “ Tashi ka bani wuri” ta faɗa cikin fushi,da sauri na ce “ na fita na je ina? Ki yi haƙuri amma ni ban ga abin ɓacin rai ba” ina gama rufe baki ta ja hannuna ta matso ni kusa a nan take madubina da ke can gida ya bayyana a nan. “Wannan ita ce siffar mutum? ?” ta tambaye ni tana nuna ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi ,na girgiza kai na ce “ a'a ba mutum ba ne fatalwa ce” Madubin ne ya ɓace ita kuwa sai ce min ta yi “ ai HAROON gwara fatalwa da kai,saboda kai sheɗani ne na musamman.Wai ma mene ne dalilin Oga na zaɓar ka alhalin ga dukkan alamu baka san muƙamin da ke jiran ka ba?” “Muƙami?” na maimaita. Dōr̃ānī ne ya shigo yana mai cewa “ lokacin komawar ka yayi” haka na bi bayansa muka fita. Sai da ya kai ni wani sashe aka yi min wanka da wasu korayen ruwa sannan na ci na sha kafin yayi min rakiya zuwa bakin ƙofa.Yau ɗin ma kamar kullum haka ƙasa ta dare na fito sai dai fa wani uban canji na ji,jin kaina nake yana hayaƙi yayin da kuma zuciyata nake jin tamkar an yi min musanyar ta,sauran tausayin da ya rage min ya kau a yadda nake ji ko wuyan jinjiri zan iya murɗe wa ya mutu.Ban gama mamakin kaina ba sai da na ga sauran members sun miƙe suna gaishe ni cike da girmamawa,yayin da shi kuma Oga yayi kicin-kicin da fuska haɗi da nuna min wata kujera da aka ƙawata ta da ado.A yau sai na yi wa Oga dubin uba mahaifi wanda kuma ban san dalilin yin haka ba,zuwa na yi na zauna nan ɗin ma wani sabon canji na ji amma dai na yi shiru ina ta nazarin komai daki-daki. “Daga rana irin ta yau na wakilta HAROON matsayin mataimakina wato shugabanku,in ba ni ga wuri shi zai ɗaukar matsayina sannan duk wani hukuncin ƙungiya da za a zarta ko ya shige muku duhu shine zai bada umarnin ƙarshe” Oga na gama faɗa suka shiga taɓa min kafin ya sallame su wurin ya zamana sai mu biyu kawai. “Wannan ɗin duk na mene ne Oga?” na samu dakyar na tambaya. Ya bani amsa da “ tun da aka kafa ƙungiyar nan kai ne na farko da ke iya maida min martani, wannan yasa na baka wannan muƙamin kana iya tafiya” ban sake ce masa komai ba na soma yin tsafin da zai kai ni inda mai kama da ni yake,aka yi katari kuwa yana cikin mota direba na tuƙa shi. Bayyana ta cikin motar yayi daidai da lokacin da direbana ke ƙara saita madubin gaba na mota,yayi ƙara tare da sakin sitiyarin motar sai a lokacin ɗayan ya ɓace saura ni.Na tashi da sauri na tsayar da motar tare da zama gefensa,direba ya dafe zuciya yana kallona kafin da sauri ya maido dubansa gare ni sai na fahimci tabbas ya ganmu mu biyun duka. Na saki murmushi na ce “ shi yasa bin didigi da ganin ƙwaf bai da kyau,duk yawan sa idon bai yi maka ba sai da ka nemo yadda za ka yi ka tantance shin mu biyu ne ko a'a .To ka tuƙa motar nan izuwa wani wurin cin abinci na ga alamun har da yunwa kake ji daga nan sai na aika ka barzahu” “Yalaɓai don Allah ka yi haƙuri!” ya furta tare da ƙoƙarin fita sai dai tuni na ƙargame dukkan ƙofofin yayin da kuma na saka motar ta soma tuƙa kanta da kanta ....... My is only 500 via2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 saura page ɗaya na gama free page in sha Allah. Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [27/11 à 09:31] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ Last free page 10 Ni kaina ban san taƙamaimai ina ne motar za ta je ba,gudu take tamkar aljani ne ke tuƙa ta.Cikin abin da bai wuce minti biyu ba har mun fita daga cikin garin Yamai mun shiga ƙasurgin daji sai a lokacin kuma motar ta tsaya cak tare da buɗe kanta.Na fito zuciyata na sake azalzala banda wani buri baya da na kashe direbana wanda har izuwa yanzu bakinsa bai gushe da bani haƙuri ba.Finciko shi na yi da sauri ya zube kan gwiwansa tare da kama ƙafafuna ya ce “yalaɓai ka yi mini rai ,na yi maka alƙwari zan kasance bafaɗenka mai yi maka hidima.Zan zama tamkar Kare da mai ikonsa,ka yarda da ni zan yi maka duk abin da kake so amma kar ka kashe ni ina da buruka masu tarin yawa da nake son cikawa kafin na bar duniyar nan!” Cikin ƙaraji na ce “ Illiya ka tabbata duk abin da nake so za ka yi shi?” “Eh yalaɓai koma mene ne zan yi” ya amsa mini cikin haƙiƙanin gaskiyarsa. “Za ka zama mataimakina kamar yadda ka ce akwai ayyuka masu tarin yawa da za ka yi min,in ka kuskure kuwa ka sani daidai yake da fitar numfashinka ” “Na gode sosai yalaɓai” ya furta tare da tashi har yanzu jikinsa bai bar rawa ba,haka muka shiga mota na lumshe idona ina jin wani matsayi ya hau kaina saboda na fara samo wa ƙungiyarmu member sannan duk wani wanda ya shigo ta sanadiyar ka to a ƙarƙashin kulawarka yake kamar yadda doka ta tsara. Ko da nake buɗe ido sai na tsinci kanmu a tsakiyar babban titin Yamai,na ɗan saki murmushi na ce “ Illiya na tambaye ka mana” “Eh yalaɓai ina ji tambaye ni” ya faɗa murya na rawa. “Matanka nawa?” “Matata guda yalaɓai da kuma yaronmu ɗaya” ya bani amsa a tsorace. “Zuwa gobe ka kawo min ita a babban ofishina ina son ganinta” na faɗa cike da gadara. “Yalaɓai ai ba ta yi makaranta ba” “Yaushe na ce ma zan ɗauke ta aiki ?” na yi masa tambayar a tsawace. Ya ce “ka yi haƙuri yalaɓai” Na juyar da kai ina kallon titi har muka isa gida,ina fita sai da na tsaya ina ƙarewa Illiya kallo gajere ne shi baƙi yana da ƴar ƙiba amma ba sosai ba,idonsa irin na munafukan mutanen nan ne masu son sanin sirrin wani. “Yalaɓai na faɗa ma zan yi duk abin da ka ce,ka yarda da ni ” ya faɗa cikin tsoro,na shafi sajena kafin na ce “in ma ba ka yi ba ai ka san meke jiran ka! Sannan duk faɗin duniyar nan ba za ka taɓa ɓoye min zan lalubo ka” ina gama faɗa na wuce ciki. Yau Ammy ba ta falo ban kuma nemi na san inda take ba kawai na shige ɗakina,wanka na soma yi kafin na fito ɗaure da towel.Kai tsaye kusan madubina na je na tsaya,ina son sanin abubuwa da dama game da MAFIYA wacce a yanzu garɗinta nake ji.Kamar wanda zai shiga ɗaki haka na yi na ratsa ta cikin madubin na shiga ciki,yau ɗin ma kamar waccan lokacin yanayin duniyar hazo-hazo ce sai dai hakan bai hana ni ganin abin cikinta ba.Wani aji na gani inda aka rubuta “TSAFI DA MATSAFI” babu wani tunani ai kuwa na je na tsaya sai na ga wata malama a tsaye tana koyawa wasu karatu,ba tare da neman izini ba na je na zauna ina kallon darasin . Tana gamawa kuma sai ga wani shi ma malamin ya bayyana kamar daga sama,kamar wani rediyo kuma ya soma yin magana. “Sannu Matsafana da kuma Mayuna!A yau za mu gano abokiyar sufi da muka fi so wato: cat da turanci,wacce a Hausa za mu kirata da mage ko kuma ƙuliya.Wannan halitta ko da yaushe tana da alaƙa da sihiri da mayu.Za ku ga a gidajen Mayu,matsafa ko malaman tsibo suna ƙawata shi da mage ko kuma ƙuliyoyi wanda normal mutum zai ɗauka iya soyayya ce kawai amma yanzu zan muku gwanjon sirrikan.Bari mu fara da labarin da zai burge ku!” sai ya tsaya da magana tare da soma yin rubuta a ƙaton allon da ke cikin ajin. # Cat da Bokaye: Tsohuwar ajiya a cikin kundin Labari na ƙarni biyu. Shine abin da ya rubuta kafin ya soma yi mana bayani dalla-dalla. “Tsawon ƙarnoni, ƙuliyoyi sun kasance abokan bokaye. Masarawa sun bauta musu a matsayin alloli. Indonesiya sun yi imanin cewa ƙuliyoyi na iya gani fiye da mayafi. A takaice, abokanmu na sirri sun fi dabbobi kawai. Abu na gaba shine : # Ikon Sufanci na Mage A naku hange me yasa mayu suke son kyanwa sosai? ” Mr Zulu na kawowa nan sai ya tsaya yana tambayar mu,wato ya bamu damar tsoma baki a ciki kamar yadda malaman makaranta ke yi. “ HAROON ko za ka faɗa mana dalili?” ya jefo min tambayar,duk sai hankalin kowa ya dawo kaina. Na ce “Domin suna da ƙarfin ikon sihiri” Yayi alama da babban yatsansa irin na jinjina kafin ya ce “ba shakka! HAROON yayi gaskiya a cikin halittun da duniyar Ruhaniya ta aminta da su mage nada kaso casa'in na ƙarfin tsafi yayin da sauran halittun kuma nada ƙarancin rinjayen.Daga cikin quality ɗin mage akwai: * Hankali, Cats suna jin kuzari da ruhohi mara kyau. Mafi dacewa don kiyaye gidanku.Ma'ana a duk lokacin da wani mummunan abu zai faru cikin gida mage tana sani kuma za ta iya kare mamallakinta daga wata cutar wa ita abin ya same ta. * Kariya :suna tunkuɗe mugayen ruhohi da munanan kuzari.Daga lokacin da mugu ya shigo gida zai ji ya kasa zama a ciki saboda wanzuwar ƙuliyar. * Warkarwa : Tsaftace su yana da tasirin warkewa, cikakke don rage damuwa.In mutum na cikin wata damuwa ta dalilin yadda yake mu'amulantar magensa zai iya samun sauƙi daga abin da ya shige masa. Sannan ku sani bayan wannan ɗin akwai wani ɓoyayyen sirri a tattare da kowacce mage.Abu na gaba da nake son ku sani shine TASIRIN LAUNI,kowacce mage da kuke gani da nata tasirin sannan ba haka kawai ake mallarkarsu ba sai an cika sharuɗa.Amma kafin nan bari na sanar da ku tasirin kowacce daga cikinsu. Kowane launin yana da ma'anarsa ta sihiri da tsafi. _Baƙar fata: Yana nuna kariya da sihiri. Saɓanin camfi suna kawo sa'a. _Fara: Yana wakiltar tsarki da waraka. _Grey: Yana jawo hikima da hankali. _Ja: Yana jan hankalin sa'a da kuzari. _Tiger: Yana wakiltar sassauci da daidaitawa, cikakke don lokutan canji. Zan tsaya a nan sai wani lokaci ” Mr Zulu ya faɗa tare da yin ɓaton dabo.Ina zaune dai cikin mamakin wannan lamari sai ga kuma wani tsoho shi ma ya shigo ajin tare da rakiyar dog.Na gyara zama don jin wane darasi ya zo mana da shi kawai na tsinkayo murya Ammy na faman kiran sunana,a dole na tashi na fito abun mamaki har yanzu jikina na ɗigar da ruwa kamar yanzu ne na fito daga toilet. Ƙofar na buɗe ina ƙirƙiro murmushi na ce “ Barka da maraice Ammy!” Ta dube ni da kyau kafin ta ce “ HAROON wai meke damunka ne? Ka dawo daga aiki amma ba za ka zo ka gaishe ni ba? ” “Yi haƙuri Ammy na gaji ne sosai,kaina kamar zai tsage haka nake ji shi yasa na soma yin wanka.Amma kina zuciyata ” na yi ƙaryar ciwon kai saboda shi ne abin da ke sa hankalin Ammy gusashe wa a duk lokacin da ta kama ni da wani laifi ni kuma ina gudun ta yi min faɗa . “Tun yaushe ka fara jin ciwon kan?” ta faɗa hankali tashe,na ce “ bai wuce minti goma” ba ta ce komai ba da sauri ta fita sai kuma ta dawo da ruwan ƙanƙara da towel,kamar ƙaramin yaro haka ta zaunar da ni ta soma yi min tausar kai har sai da na ce mata ya daina na bar ji.Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ta sauke wacce har sai da na ɗora ayar zargi da tambaya na ce “ Ammy me yasa hankalinki ke tashi in nace kaina na yi min ciwo?” Ɗan daburcewa ta yi kafin ta ce “ ka saka kaya ka sauko ƙasa na yi maka girki mai daɗi” tana gama faɗa ta fice,na bi ta da kallo ina cewa “ tabbas akwai wani ɓoyayyen sirri da Ammy take ɓoye min” haka na miƙe na kimtsa sannan na sauka zuwa ƙasa. Ammy ta zuba min abinci amma na kasa ci,ta zauna kusa da ni tare da soma bani a baki tana mai cewa “ zama da yunwa bai da kyau yana haifar da cutar olser,ka yi niyya ka yi aure HAROON ko hankalina zai kwanta na san matarka za ta kula da kai” ban ce mata komai ba sai murmushi. Da sauri na juya bayana jin kukan mage yau a gidanmu ,magen fara ce sol ko tabo ɗaya ba tada kuma dumul-dumul da ita kana gani ka san ba ta da yunwa. “Ammy ina kika samu mage?” na yi tambayar ina kallon magen sam na kasa ɗauke idona a kanta . “Ka jira yanzu mai ita ta shigo ” cewar Ammy tana dariya,babu jimawa kuwa sai ga wata kyakkyawar budurwa fara tas da ita har da wani ƙaton baƙi a goshinta na sallah .Sallama ɗauke da bakinta sannan kuma ta gaishe da Ammy,kafin ta soma kiran sunan magen “ Mira! Mira! Zo mana” kamar uwa da ƴa haka magen ta je da gudu wurinta,ita kuma ta duƙa ta ɗauke ta kafin ta zo ta miƙawa Ammy key ta ce “ ga shi in Mama ta zo ki bata ni zan koma makaranta” Ammy ta karɓa ita kuma ta fita,da sauri na yi jarumtar tattara nutsuwata na share zancen magen na ci abinci. Kiran sallar magrib aka soma,“ HAROON je ka yi alwala ka wuce masjid ni zan shiga daga ciki” cewar Ammy,a dole na amsa mata da “ toh” sai kuma na fita can harabar gidan. Da hannu na yi wa Illiya alama da ya zo,da sauri ya ajiye butar da yake alwala ya zo jikinsa na rawa .“ Ga ni yalaɓai” “Yarinyar nan da ta fita yanzu Mai mage wace ce ? Ka san ta ne?” na tambaye shi . Ya ce “ Eh yalaɓai Salima ce ƴar gidan Yakubu soja tana karatu a babbar jami'a ne” “Ina son ta ne,ka san yadda za ka yi ta yarda da hakan” na faɗa kai tsaye. “Amma yalaɓai Malama Zainab fa?” Har sai da ƙarar rawar zuciyata ta motsa jin an ambaci sunanta,na saki wani murmushi na farin ciki kafin na ce “ ita wannan ta musamman ce” sai kuma na bar shi nan na koma ciki. ILLIYA POV Bin bayan HAROON kawai yayi da kallo yana mamakin wane irin rikitacen mutum ne shi,a haka ya koma yayi alwala ya je masallaci.Har aka yi sallar isha'i yana ta tunanin hanyoyin da zai bi ɗin ya sanar da Salima,da kuma ya tuna zancen Yalaɓai na ya kai masa matarsa gobe sai hankalinsa ya ƙara tashi.Haka dai ya samu ya fito daga masjid ɗin ya je bakin hanya ya samu taxi ta kai shi can gidansa,yau ko motar bai tafi da ita gida ba kamar yadda ya saba. Yana shiga kuwa ɗansa Abdul ya rugo yana tara masa hannu,sam ya manta bai shigo da komai ba kamar yadda ya saba musu ba.”Yi haƙuri Abdul na manta ban sayo ba ka bari har zuwa gobe” yana gama faɗa yaron ya fashe da kuka,hakan ya jawo hankalin matarsa Mariya ta fito tana kallon mijinta ta fahimci ba ƙalau ba,gaisuwar da ta yi masa ma dakyar ya amsa. Ruwan wanka ta kai masa,haka ya je yayi ya fito ya zo ya shige can uwar ɗaka ya rabka uban tagumi. “Baban Abdul” ta faɗa cikin Hausarta da ba ta dafu ba. Ya zabura ya ɗago ya dube ta,sai kuma ya haɗe rai ya ce “ lafiya kike wani kirana haka?” “Kai dai zan tambaya lafiya duk ka bi ka sauya haka?” “Mariya haka ya dace a tarbi miji in yana cikin damuwa? Ko abinci fa ba ki bani ba” ya faɗa wannan karon ya sassauta murya.Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ ka yi haƙuri bari na kawo ma” sai ta fita ta je ta kawo masa.Ya ce “ ina Abdul?” “Ya gaji da kuka har yayi bacci ” ta basa amsa tare da zuba masa abinci a plate ya karɓa ya soma ci yana ƙare mata kallo,bafulatana ce ita kyakkyawa ba ta da ƙiba hakan yasa ƙirjinta har yanzu a cike suke kuma tsaye daram . “Lafiya kake ta ƙare min kallo kamar yau ka fara gani na?” “Kin san ke ɗin ce kullum kyau kike ƙarawa” ya faɗa tare da kashe mata ido ɗaya yana murmushi,ita ma dai ta ɗan saki ranta ta soma yi masa surutunta da wannan ta ɗan sassauta zuciyar Illiya har suka yi bacci,amma tsakar dare ya tashi a firgice saboda mummunan mafarkin da yayi.Sam kasa komawa yayi sai yayi zaune yana ta saƙa da warwara har garin Allah ya waye,suna tsaka da cin abinci kiran HAROON ya shigo wayarsa,gabansa ya faɗi rasss haka yayi ta kallon kiran har ya yanke wani ya sake shigowa amma shi ma ya ƙi ɗauka sai ana uku ne yayi ƙarfin halin tashi ya fita can tsakar gida sannan ya ɗaga idonsa na kawo ruwa ya ce “ yalaɓai ina zuwa yanzu nan zan kawo ta” yana gama faɗa kuma aka kashe kiran daga can ɓangaren.Illiya ya goge ƙwalla kafin ya dawo ɗaki,Mariya ta kafe shi da ido sai dai bai bata damar yin magana ba ya ce “ Ogana ne bai da lafiya yanzu nan aka kira ni,tashi ki saka hijabinki mu wuce” Ganin yadda mijin nata ya shiga tashin hankali yasa ta bi umaninsa kawai,Abdul ta kimtsa ta goya shi sannan suka fito bakin titi ya tsayar musu da taxi ya faɗa masa sunan babban kamfanin da za su je. HAROON Da abu uku na kwana daren jiya,na farko soyayya da ƙaunar Malama Zainab,na biyu kuma son mallakar magen Salima,na uku kuwa shine son ganin matar Illiya . Wannan yasa gari na wayewa na yi wanka na shirya,shayin Ammy kawai na sha kafin na fito sai kuma na tarar Illiya bai zo ba na yi tunanin don kar ya cika umarnina ne ya ƙi zuwa wannan yasa na soma jera masa kira domin yi masa gargaɗi sai kuma ga shi ya bani tabbacin zai kai ta. Ɗaki na koma na ɗauko key na mota,da kaina na yi draving na isa can kamfanina.Ko sauraren gaisuwar mutane ban tsaya ba na shige ciki,babu jimawa kuwa sai ga Illiya ya shigo shi da matarsa wacce idonta ƙurrr a kaina masu cike da mamaki da tambayoyi. Kujeru na nuna musu ,ta kwance goyonta kafin ta zauna shi kuwa Illiya ya ma kasa zama da alamu jira yake ya ji dalilin zuwan nasu. Rigar rashin mutumci na sake yaɓawa kaina kafin na ce “ Illiya karɓi yaron nan ku fita waje ina son yin magana da ita” jikinsa na rawa ya ɗauki yaron da tun da muka haɗa ido da shi ya soma kuka,Illiya ya je bakin ƙofa ya waiwayo yana kallona na banka masa harara da sauri ya fice ina mai ganin ƙwalla na zubo masa. Daga inda nake zaune na baiwa ƙofar umarnin rufewa,da sauri ita matar Illiyan ta juya tana kallon yadda key ke murɗa kansa handle kuma na motsi.Tana juyowa ta gan ni a zaune kan table gabanta har ƙafafuwanmu na gugar na juna,cikin ido na dube ta na ce “ ki cire hijabinki” Idonta ya kawo ruwa amma na san tabbas ba za ta iya musa min ba,haka ta cire shi nan na yi arba da siffarta mai ɗaukar hankali.Rabon da na yi mu'amala da mace har na manta, wannan yasa jikina ya ɗau rawa har ban san lokacin da na kai hannuna na zuge zip ɗin rigarta ba.Nan na yi arba da ainahin surarta,hawayenta da suke ɗiga sam ba su dame ni ba haka na yi mata sintiri ina shafar dukkan sassan jikinta.Daf da zan cimma burina na ƙarshe na ji sautin muryarta mai kamar tafasasshen ruwa,cak na tsaya ina sauraren amon muryarta wanda kuka ya gurɓata shi “ ka sani ni ma mace ce mai daraja kamar uwar da ta haife ka! Yadda baka son wani ya keta mutumcinta haka ni ma yarona da ke can waje yana kuka bai son a keta nawa” da sauri na yi baya ina dafe zuciyata ina kallonta ta soma mayar da kayan jikinta.Daidai nan na gama page na kyauta mai so sai ya biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Kawai ki tura in na zo zan saka ki group,wacce ta san ba biya za ta yi ba ta yi wa girman Allah kar ki yi min magana. Littafin MAFIYA labari ne ya cakuɗe da true life da kuma wanda na ƙirƙirar,sannan wannan duk shimfida ce ba mu ma shiga cikin zallar labarin ba. Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [28/11 à 08:15] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 11 Tun da nake babu wata ƴa mace da na taɓa rabawa da kayanta kuma ban kusance ta ba sai wannan.Har ta kai bakin ƙofa na dakatar da ita “ keee!” ta wani juyo a firgice jikinta na rawa,idona na kafe ta da su ina son sanin ko tana ɗauke da wani sirri ne na daban amma ban gansa ba.Na dafe goshina cike da takaici kafin na kwashi kayana na shige Toilet,gaban shower na je na tsaya na buɗe shi duka ruwan na soma sauka a kaina tsohuwar rayuwata ta baya ta fara zuwar min kamar wanda aka kunna wa video. Wannan labari yana ɗaya daga cikin mafi ruɗani da na samu. Yana da gami da madubi. Ba wai kawai kowane madubi ba, amma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da ake ganin suna ɗaukar wani abu fiye da kawai tunaninsu. A ƴan shekarun da suka gabata, na ci karo da wata kasuwar kayan gargajiya a wani gari da nake wucewa.Kasancewar ni ɗin direban babbar mota ne,ina son yawo a cikin waɗannan wuraren koyaushe suna samun abubuwa masu ban sha'awa tare da labari. Ina zagawa wani tsohon madubi ya kama idona tamkar mayen ƙarfe. Yana da ban sha'awa, tare da firam ɗin katako da aka sassaƙa, an ƙawata shi da ƙira. Wani katon madubi ne, kusan girmansa kamar ƙofa, ga fuska kamar ya ɗan dusashe da shekaru. Dillalin kayan tarihi ya gaya mani cewa wannan madubin ya fito ne daga wani tsohon gidan da aka yi watsi da shi kuma ya kasance a wurin shekaru da yawa, ba tare da wani ya so ya saya ba. Ya ce wasu mutane in sun ga wannan madubin suna cewa “yana tattare da damuwa” ba tare da sun iya bayyana dalilin da ya sa ba. Tabbas, a matsayina na mai son abubuwan bazata da na ban mamaki sai na yanke shawarar saya. Na kai shi gida da tunanin zai dace da duniyata. Tun daga ranar farko da na rataye shi, na ji wani abu mai ban mamaki. A duk lokacin da na wuce nakan ji kamar tunanina yana kallona ta wata hanya mai ban mamaki. Ba kamar wani tunani mai sauƙi ba, amma kamar wani sigar ni a cikin madubi yana kallona ta baya, ko da kuwa bayan na kawar da kaina. Da farko na ɗauke shi a matsayin gajiya ce da na yi, tunanina kawai hankalina ne ke wasa da ni. Amma da yawan kwanakin da suka wuce, wannan jin yana ƙara tsanantawa. Abin da ya fara damuna da gaske shine lokacin da na lura cewa tunanina yana motsawa. Wata rana da yamma, ina wucewa gaban madubin , sai na ga tunanina ya ɗan juya kaina kafin in yi haka. Tsawon daƙiƙa ne kawai, amma a fili yake. Har na yi gwaji, ta wurin tsayawa a gaban madubi ina motsi a hankali. A wani lokaci, tunanina ya lummm a gabana ya kasance da dabara irin ya ɗan jinkirta abin da na yi . Na fara firgita sosai, amma na gaya wa kaina tabbas tunanina ne. A daren nan na yi bacci a kan kujerar falo, kuma madubin yana can hangen nesa na. Da tsakar dare na tashi ba zato ba tsammani, sai na ji wani yana kallona lokacin da na buɗe idona, sai na ga inuwa a bayana a cikin madubi, kamar a mafarki amma gaske ne. Na juyo ba zato ba tsammani sai dai ba komai babu kowa a cikin ɗakin .Zuciyata ta fara bugawa ba zato ba tsammani na sake duba madubin, kuma wannan lokacin ya fi muni,inuwar ba ta da kyau, yana can a cikin tunanina can tsakiyar madubi amma ba a cikin ɗakin ba. Ita wannan inuwar irin siffata ce da ita amma jikinta duk ko ta ina jini ne ke fita,yadda na ƙure ta da ido ita ma haka take kallona babu motsi. A yadda ake son na fahimta wannan na cikin madubi ni ne da kaina kamar yadda kowanne mutum in ya tsaya a gaban madubi zai ga kansa,amma ni nawa ya sha banban da na sauran.In na yi motsi shi na cikin madubin bai motsa wa yana nan a daskare kamar saƙaƙo,in kuma ni na tsaya ɗam ba tare da na yi wata alamar motsi ba sai na ga shi ya motsa. A firgice na bar ɗakin a wannan ranar ban dawo ba sai da safe. Washegari, na yanke shawara mai tsauri. Na rufe madubin da farar ƙatuwar zanen gado. Tun daga wannan lokacin, ya kasance a can a ɓoye. Amma kuwa duk da na rufe shi har yanzu ina jin kasancewarsa. Wani lokaci ina tsammanin ina jin ƙararrakin hayaniya suna fitowa daga wajensa kamar surutu da sautin faɗuwar wani abu kamar tasa ko kuma an cilla dutse a rijiya. Kamar wanda aka yi wa dole haka kuma na ƙi fitar da madubin,na ci gaba da rayuwa da shi har wata baƙar rana ta zo wacce ba zan manta ba.Ina kwance ina baccin bayan la'asar aka kira ni a waya Ammyna ta zame jiki ta faɗi babu hannu babu ƙafa ga kuma zuciyarta ta kumbura.Ko wanke fuska ban yi ba na ɗauki makullin mota,a ƙa'ida sai jibi zan yi jigilar dabbobi kamar yadda tsarin yake in na zo asabar sai kuma ranar Laraba zan koma can gida Agadas.Kwana ɗaya da wuni na yi a hanya kafin na isa,direct kuma asibitin da aka sanar da ni take na nufa,a yadda na tarar an banzatar da Ammyna sai na ji takaici ya rufe ni don babu wata kulawa ta musamman tsabar wulaƙanci ma kan tabarma take ba a gado ba. Ba ta iya yin magana ,bakinta ya juye yawu na yi mata dalala,motsin kirki ma ta iyawa sai idonta da ta kafe ni da su masu cike da rauni da neman agaji a gare ni. A wancan lokacin da na tambayi nurse dalilin ƙin bai wa mahaifiyata taimako yadda ya kamata sai ce min ta yi “ sai kun biya kuɗi na gwaje-gwaje,na gado,da kuma alluran da za a dinga yi mata tausar ƙafarta da ta sandare ” ƴan kuɗaɗen da na samu waɗanda sun kasance na uban gidana ne da su na yi amfani na bayar aka ba Ammy gado ,sannan da taimakon da ba a rasa ba.Dandanan goshinta ya fara fitar da zufa sai bacci,ganin haka sai yasa na wuce can gidanmu domin yin wanka.Mahaifina na tarar wanda shine silar duk halin da Ammy ke ciki,kayan jikinsa na tarar yana haɗawa da alamu garin zai bari. Ina kawo daidai nan na kashe shower saboda a duk lokacin da nake tuna rayuwata babu gaɓar da na tsana irin ta Abbana.Cike da takaici na kimtsa na fito na zauna kan kujera,ina jin tabbas ya zama dole na mallaki matar Illia direbana. ILLIA POV Babu wani tashin hankali da ya taɓa shiga wanda ya wuce wannan,babban takaici ne yau ace ya miƙar matarsa ta aure ga wani namijin da yayi imanin cewa imani bai wanzu a ƙirjinsa ba ballantana ya sa ran ba zai keta haddinta ba. Kamar wani marayan uwa da uba haka ya takure jikin katanga ya rungume Abdul gam a ƙirjinsa wanda tuni ya gaji da kuka yayi bacci,ido kawai Illiya ya ƙura wa ofis ɗin HAROON tunani iri-iri na ta zuwar masa .Ya san halin Mariya da tsoro tun a tashin farko za ta sallama kanta ko da kuwa bai yi amfani da tsafinsa ba.Yana nan jibge kamar kayan wanki ya ga ta buɗo ƙofa ta fito,da sauri ya nufe ta yana cewa “ me yayi miki?” ba ta basa amsa ba ta karɓe ɗanta ta yi gaba.Ya take mata baya yana kiranta,duk mutane na kallonsu amma ta ƙi tsayawa haka suka dinga yin tafiyar ƙasa su biyu har suka isa gidansu duk da kuwa uban nisan da ke da kwai. “ Mariya mene ne haka? Ina tambayar ki amma kin yi shiru” Illiya ya faɗa bayan sun shiga ɗaki. Ta dube shi da idonta da suka yi jajur tsabar kuka ta ce “ abin da ka kai ni dominsa shi yayi! Wato Illiya ban taɓa sanin cewa baka ƙauna ta ba sai yau amma ka sani wallahi na gama aurenka!” sai kuma ta wuce can uwar ɗaka ta soma haɗa kayanta. Shi kuwa zaman ƴan bori yayi jin HAROON wai kusance ta,kukan baƙin ciki ya soma yi kamar ransa zai fita yana da kishi sosai amma yau yana ji yana gani an ɗauki abunsa mafi daraja an tozarta shi .Wata irin tsanar HAROON ce ya ji ta ɗarsu a ransa,ya ƙudiri aniyar zai yi masa aiki amma kuma tabbas shine ajalinsa...... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [30/11 à 07:46] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 12 Cike da takaicin Illiya da matarsa na dawo gida,ina shigowa da sanyi idaniyata na fara cin karo wato Malama Zainab.Cak na tsaya a bakin ƙofa jin zazzaƙar muryarta na fitar da sautin karatun Alqur'ani wanda ya zama barazana ga ruhina,ji nake tamkar an watsa mini ruwan zafi. Tamkar Ammy ta san halin da nake ciki ta dakatar da ita da karatun ,“ Malama gobe in sha Allah mu ci gaba ga HAROON nan ya dawo,ƙaraso ku gaisa ” Ammy ta faɗa tana murmushi,sai da na je na ɗauki gorar ruwa mai sanyi na sha sannan na ƙarasa wurin su. Ammy na fara gaishe wa kafin na zuba wa malamar ido,ta ɗago a hankali ta ce “ ya ƙarfin jikin?” “Ai na ji sauƙi” na bata amsa ina mai ci gaba da kallonta,da dukkan alamu kuma ta tsargu da hakan don sai wani takure jikinta take. “Ka zauna bari na kawo ma wani abu” Ammy ta faɗa tare da nufar kitchen,nesa da Malama na zauna ina son tantance ta amma sam babu wata ƙofar tauraronta da ke buɗe wacce za ta bani damar ganin sirrin ruhinta. Na ja ajiyar zuciya na ce “ ya aka yi yau kuka fara karatu da wuri haka?” Kamar mai tsoron magana ta ce “ ina da wani aiki mai muhimmancin ne bayan sallar magrib ɗin” “Mene ne shi?” Sai da ta ɗan ƙara sunne kai kafin ta ce “ dama... Dama wanda aka yi mana baiko ne ya d...” sauran maganar ƙarar fashewar gilas ta maƙale ta. Ammy ce ta yi ɓarin lemun zoɓo,hankali tashe kuma ta bi ta cikin kwalbar tana mai cewa “ an miki baiko?” “Eh tun shekaru uku da suka wuce ni da Sheikh Ali,ba ki dai ji ciwo ba ko Ammy?” ta ƙarashe da tambayar Ammy wacce ta zuba min ido,ƙila mamakin ganin ban wani razana sosai ba ko na tayar da hankali. “Allah sa alkhairi,je ki direba ya mayar da ke” Ammy ta faɗa tare da zubewa kan kujera yayin da ita kuma Malama Zainab ta fice.A hankali na tashi na tsuguna a gaban Ammy na kamo ƙafarta da ke zubar da jini.Kwalbar na cire sannan na ɗauko ɗan akwatin da ke da kayan magani na shafa mata tare da naɗe ƙafar da bandeji. “ Ka kuwa ji abin da Malama Zainab ta faɗa ?” “Eh Ammy na ji” “Shine kuma baka ce komai ba?” “Ammy a kullum fa ke ce da kanki kike min nasihar cewa duk wanda ya yarda da Allah to komai nasa zai zo da sauƙi,kin ga kar ki damu Malama ba ta da wani miji da ya wuce HAROON zan je har gidan nasu na fallasa mata sirrin zuciyata ” Ammy ta shafi sumar kaina tana wani ɗan murmushi kafin ta ce “ haka take yarona” na miƙe tare da sakar mata murmushi sai kuma na nufi step,a cikin kwanyata na soma jin ana yi min magana “ HAROON lokaci yayi da za ka fara amfani da powerka domin sato taurarin mutanen kirki,ta wannan hanyar ce zaka samu Malama Zainab ” Kamar wani zararre na tambayi kwanyar tawa “ ta ya kenan zan soma?” “Je ka fara yin wanka tukunna,sai ka je madubinka zai sanar da kai” Haka kuwa aka yi,bayan na yi wanka na je na shiga cikin madubina.Direct ajin nan da ake koyar da karatu na shiga,yau ma Mr Zulu ne ke darasi akan allo yayi zanen baƙar mage mai jajayen ido yana kuma yin bayani. “Baƙar mage , waɗanda galibi ana lulluɓe su cikin sirri da camfi, koyaushe halittu ne masu ban sha'awa, musamman a duniyar mayu da ayyukan sihiri. Baƙar mage a zahiri suna ɗaukar kuzari mai zurfi, kariya da sihiri. A cikin wasu al'adun arna da sihiri, ana ganin baƙar fatar mage a matsayin mai kula tsakanin talikai, mai tsaro na ruhaniya. Ya ƙunshi ma'auni tsakanin haske da inuwa, bayyane da ganuwa. Wataƙila wannan duality ne ya sa bokaye da matsafa suka zaɓi baƙar mage tamkar abokan hulɗa masu mahimmanci a cikin aikin sihiri. Suna kawo hikimar dare da ikon kewaya wuraren ruhi na ɓoye. A cikin gogewar kaina, baƙaƙen ƙuliyoyi sun kasance sau da yawa jagororina da masu kare ni a lokutan canji ko haɓakar ruhaniya. Suna tunatar da ni cewa inuwa ba abin tsoro ba ne, amma illa fahimta. Suna ɗauke da sihiri mai hankali amma mai ƙarfi a cikin su, ƙarfin canzawa wanda ke ingiza mu mu wuce fiye da kamanni don rungumar ɗaukacin halittarmu. Baƙar ƙuliya kuma alamun sa'a ne a wasu al'adu, suna kawo albarka da kariya ga waɗanda ke maraba da su cikin gidajensu. Kasancewarsu na iya zama abin tunatarwa akai-akai game da sihirin da ke kewaye da mu, yana ƙarfafa mu mu kasance a buɗe kuma mu yi maraba da mutane wanɗada ba mu sani ba da gaba gaɗi. Shin kun taɓa haɗuwa da su a cikin ayyukanku ko rayuwar ku ta yau da kullun? Menene ma'anar waɗannan sahabbai masu ban mamaki a gare ku? ” Hannu na ɗaga hakan yasa ya ce “ ina jin ka HAROON ” Na ce “ ta ya za a yi mutum ya mallaki ita baƙar magen? Sannan mutum ɗaya zai iya ɗaukar ƙuliyoyi biyu a lokaci guda don yin aiki da su ko kuwa sai ƙwaya ɗaya kawai aka yarje masa?” Mr Zulu ya bani amsa da “ a'a in kana so duk launinkan ƙuliyoyin da muka lissafa zaka iya aiki da su muddin dai zaka iya ciyar da su.Bari na faɗa muku wani sirrin iya ƙuliyoyinka iya ƙarfin tasirin alƙalumanka,mai son baƙar mage ina da su da yawa na sayarwa ga su nan na kawo” ya faɗa tare da buɗe wani tsohon akwatin ƙarfe .Cike yake da jariran baƙaƙen ƙuliyoyi duk idonsu kuma jajur suke ,nan fa duk kowa ya soma cewa yana so ganin kamar za su ƙare yasa da sauri ni ma na isa gaban akwatin don zaɓar tawa.Akwai ƙwaya ɗaya wacce ta banbanta da sauran ta fi su girma haka yanayin fuskarta ma kicin-kicin yake babu fara'a. “Wannan nake so” na furta tare da kai hannu na ciro ta,Mr Zulu yayi min kallo kafin ya ce “ HAROON ka tabbata ?” Ba tare da tambayar dalilin da yasa sai ni kaɗai ya yi wa tambayar ba na ce “ eh yalaɓai ita nake so ” ya saki ɗan murmushi kafin ya ce “ shi yasa Oganku ya ce kai ɗin na musamman ne taurarinka masu matuƙar ƙarfi ne” ni ma murmushin kawai na sakar masa,magen hannuna ta yi wani zillo ta ruga da sauri na take mata baya kawai sai na tsinci kanmu a wajen madubi a tsakiyar ɗakina. Da ido nake kallon magen wacce ta haye bed ɗina ta yi min ƙuri da ido,da sauri na nufe ta na ɗauko ta na rungume.Sai yanzu na lura ashe namiji ne muzuru,kansa na soma shafawa na ce “ daga yau sunanka Tony” daga bakin ƙofa aka soma buga wa tare da kiran sunana “ na'am Ammy gani nan zuwa” na furta tare da tashi na buɗe mata,da faɗa ta soma “ HAROON me yasa kake son zama da towel,to in ka shirya ka fito ina son ganin ka” har za ta tafi sai kuma ta yi saurin juyowa tana kallon gadona,sai na kai dubana na ce “ Tony ne fa” “Yaushe ka fara son ƙuliya ban sani ba?” “Na sosa ƴar ƙeya kafin na ce zan yi miki bayani daga baya” Ta fice,ni kuma na rufe ɗakin.A tsanake na shirya na ɗauki Tony muka sauka ƙasa sai wani kuka yake “minyau!” Ammy ta ce “ Laure zuba ma magen nan abinci ƙila yunwa take ji,kawai haka nan ka kama ka rufe ta a ɗaki” Tony ya wani zille ya bi Laure mai aiki can kitchen,wani tsohon plate ta samu ta zuba masa abinci tana masifa ƙasa-ƙasa “kawai don mugun hali ka rasa magen da za ka kawo cikin gida sai baƙa mtsww!” ta ja tsuki,ƙafa ta sa ta bugi Tony ya tsaya yana kallonta “ ni bari kallona shegiya da wasu ido nata kamar mayya” sai kuma ta fito. Na dube ta na ce “ kin zuba masa abincin?” yau ne karon farko da na taɓa yi mata magana saboda ni da ƴan aikin gidanmu gaisuwa ce ke haɗa mu ita ma sai na ga dama na amsa. “Eh ga ta can tana ci” ta bani amsa. Na ce “ namiji ne ba mace ba,sunansa Tony ” “Sai kace dai wani mutum yalaɓai ai duk ƙuliya da sunan mace ake kiranta” Laure ta faɗa cike da jin haushi tana mai ɗaukar kwanon abincinta ta kama hanyar fita tana gunguni ƙasa-ƙasa sarai kuma kwanyata ta sanar da ni abin da ta ce. “Tun da baƙin hali gare mu don muna da kuɗi da kuma jiji da kai ki je an sallame ki daga aikin” na faɗa cikin ɗaga murya,da wani mugun sauri ta juyo tana kallona kafin ta zo da gudu ta zube a gabana tana bani haƙuri,tsakiyar idonta kawai na kalla na fahimci Laure irin mutanen nan ne waɗanda akan kuɗi babu abin da ba za su iya yi ba,sannan tuni hassada da baƙin ciki sun gama gurɓata ruhinta.Jin daɗina guda da Ammy ta gusa ba ta falon,na saki makirin murmushi na ce “ zan maido ki aiki zan kuma ƙara miki da wani wanda ya fi wannan albashi na san za ki iya ” Ai kuwa ta washe baki tana cewa “ sosai yalaɓai in dai zaka bani kuɗi” Na ce “ yawwa yarinyar nan Salima ƴar gidan Yakubu soja kin san ta ne?” Ta ƙara washe baki ta ce “ Salima mai mage ko? Ai har gidansu Hajiya ke aikina” “Yawwa a kanta nake son baki aiki” “Koma mene ne zan yi Alhaji in dai zaka bani kuɗi” “Ok za ki iya tafiya,gobe zan faɗa miki bayanin aikin naki ” ta miƙe ta tafi da ƙarfin gwiwarta,sai lokacin kuma Tony ya fito daga kitchen yayi tsalle ya ɗare kan cinyata na soma shafa bayansa ina jin wani irin daɗi na mamaye ni. Ina nan zaune sai ga Illiya ya shigo fuskarsa kawai na kalla na fahimci damuwarsa,ya zo ya gaishe ni tare da zama kan capet idonsa suka fara tsiyaya. “Ai zata dawo ba za ta iya barin ka ba,sai dai ka sani ban janye ƙudirina ba ya zama dole na ɗanɗani zumarta” na furta ina cije leɓena na ƙasa. Da sauri Illiya ya ɗago yana cewa “ yalaɓai dama baka kusance ta ba?” Na kawar da kai gefe ina kallon cikin idon Tony da nake tsintar wasu abubuwa a ciki. “Yalaɓai wannan muzurun fa?” Illiya ya jefo min tambayar da tasa na maido dubana gare shi na ce “ faɗa min Illiya ta ya aka yi a kallo ɗaya har ka san muzuru ne? Kana da wankin ido ne ko yaya?” Ya ɗan washe baki ya ce “ yalaɓai lokacin baya fa na ɗan taɓa aikin tsibo sai kuma na bari saboda kusan haukata ni jinnu suka yi” “Ita ma matar taka da tsafi ka aure ta kenan?” “A'a wallahi auren soyayya ne ko rubutu ban taɓa bata ba” “Ya ake samun costumer Illiya ? Ina nufin malaman tsibo ta wace hanya ce za su bi domin ganin sun samu mutane da yawa?” “Ta hanyar shiga gidan rediyo da tv,ka yi musu alƙawarin aiki kyauta ne sai buƙata ta biya sannan mutum sai bayar da abin sadaka” Na saki murmushi na ce “ to ka shirya min zama da manyan ƴan jaridu da kuma wasu mutanen da za su bayar da shaidun ƙarya akan na yi musu aiki ya ci sun zo godiya” Ya saki baki yana kallona kafin ya ce “ yalaɓai kuma bayar da magani zaka koma?” Na haɗe rai na ce “ tashi ka bani wuri,ka yi abin da na ce su kuma mutanen da zaka samo ka sanar da su zan biya su ne” da saurinsa kuwa ya tashi,ni kuma na kai baki na sumbaci Tony don wannan dubarar daga gare shi ta fito. Bayan sallar la'asar kuwa sai ga mutane sun cika gidanmu,gefe guda ƴan jaridu biyu ne sai bayan na gama bayanan ƙarya kan cewa ina warkar da dukkan cututtukan duniya sannan mutane suka soma faɗin abubuwan alkhairin da na yi musu,na biya masu gidan rediyo da tv domin yi min talla da kuma lambar wayata da za a kira ni.Su kuma masu shaidun ƙarya Illiya na baiwa kuɗi ya raba musu,kuɗin da ace sun san sune ajalinsu to da tabbas ba za su karɓa ba amma ƴan magana na cewa kwaɗayi mabuɗin wahala...... NB:Ina ƙara yawan free page ne,niyyar kaina. My book is only 500 via2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [01/12 à 09:18] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 13 Washegari,afujajan Illiya ya shigo ofis ɗina ko neman izini bai yi ba. “Yalaɓai ya haka? Dukkan mutanen da suka bada shaidar ƙarya a kan kai malamin tsibo ne sai ɗauki ɗaiɗaya mutuwa take yi musu” Da wani mugun kallo na dube shi na ce “ au! So kake na bar su da ransu daga ƙarshe su tona min asiri? ” “Yalaɓai kisan kai fa ne jinin wajen mutum goma” ya faɗa hawaye na zubo masa akan kumatu waɗanda suka sa na ji zuciyata ta yi mugun sanyi don tsabar daɗi,don a yanzu in ga mutum cikin baƙin ciki shi fi faranta min rai. Ido na lumshe ina tuna yadda Tony yayi amfani da madubin tsafina ya dinga tsotse jinin duk mutanen da na bai wa kuɗi,sosai hakan ya ƙara mini ƙarfin power ta yadda a wannan karon har na yi nasarar toshe bakin Ammy ta yadda duk abin da zan yi ba za ta ga abunsa ba ko kuma ta yi min magana. “Yalaɓai ciki fa har da mace mai ciki ” Illiya ya faɗa cikin gwanjin kuka,na buɗe ido jin furucinsa .Na ce “ ya zancen Salima ka kuwa fara wani shiri a kai?” Ya saka idonsa cikin nawa yana zancen zucin da nake jinsa raɗau kwanyata na karanto min shi,‘ dama duk rashin imanina akwai wanda ya fi ni ? Anya akwai zuciya a ƙirjin yalaɓai? Wato duk wannan iftila'in da ya jefa mutane shi ko a kwalar rigarsa?...’ Tunanin nasa ne na katse ta hanyar cewa “ wani abun jin daɗi ma daga cikin wannan lamari shi ne kuɗin za su ci gaba da yawo a doron duniya,kuma iya masu son zuciya ne kawai za su je hannunsu haka kuma zan ci gaba da amfani da tataccen ƙarfin jikin mutane domin inganta gobena.Illiya ina so ka sa a ranka babu abin da ba zan iya yi ba yanzu,don haka kar ka kai ni bango yin haka ban kwana ne da rayuwarka.Je ka yi aikin da na saka,ka tabbatar Salima ta kasance cikin tsaronka sannan duk wani motsi nata ka sanar da ni” Ba tare da ya ce komai ba ya juya zai tafi,na tsayar da shi “ mene ne sunan matarka?” Ya juyo da sauri yana kallona tambayar ‘ me za ka yi da sunanta?’ shimfiɗe akan fuskarsa.Na ƙara haɗe rai ina juya idona zuwa na mage,murya na rawa ya ce “ Mariya ” na sakar masa murmushi,shi kuma ya fice. Kan kujera na zauna ina tunanin hanyar da zan ɓullowa mijin da Malama Zainab za ta aura,wanda alƙaluman tsafina sun tabbatar min da tabbas auren babu fashi .Na ja tsuki ina jin takaici,kukan Tony na ji ƙarƙashin kujerar da nake zaune.Na duƙa na ɗauko shi na ɗora shi kan table,jikinsa na fara shafawa tare da soma yi masa magana ina neman shawara “ Tony a daren jiya na yi bincike akan Malama Zainab kuma an nuna min sai ta auri mijin nan nata,ban so ya kusance ta ya zan yi?” “Turen aljani za ka yi wa mijin,tun da ita tana tsare iyakokin Ubangiji sosai babu ta hanyar da jinnu zai shiga jikinta.Amma kamar yadda ka yi bincike haka ni ma a jiya na yi bincike kan shi Sheikh ɗin,duk da yayi karatun addini amma fa bai amfani da shi in taƙaice ma dai fuska biyu ce da shi har da giya yake sha” Tony ya faɗa min da idonsa amma raɗam nake jin sautin murya na fita daki-daki.Tsabar murna ban san lokacin da na ɗauke shi na rungume tare da miƙe wa tsaye na soma yin rawa,“ ashe babban sirri ne da mage baƙa har haka? Hohoho! Wato shi yasa Tony ka kasance na musamman abin da ban saka ka ba yi kake yi domin sauƙaƙe min aiki” Tony ya ce “ yalaɓai ka manta a daren jiya ka yi min sacrifice? Ai muddin zaka bani jini abin da zan yi ma sai ka yi mamaki” sam ban damu da cewa illata rayuwar wasu babbar cutarwa ce ba na ce “ in dai jini ne Tony kar ka damu”. Ina nan zaune Illiya yayi min waya kan cewa Salima ta tashi daga makaranta,kuma shine ya kai ta gida da sunan ya rage mata hanya.Duk wayar da nake Tony ya buɗe kunnuwa yana saurare,bai ce komai ba ya fita da gudu.Na saki murmushi don na tabbata kuwa wani aikin ne zai yi min,wayata da key na ɗauka tare da ficewa . Ina draving ina tunanin surar Mariya matar Illiya ,na lashi leɓena na ƙasa ina mai cewa “ ko fyaɗe ne sai na yi miki muguwa!” a haka na ƙarasa gida.Ina shiga na ga Salima a zaune kan kujera tana taya Ammy saƙar kayan sanyi,na saki wani murmushin jin daɗi ganin Laure ta fito daga kitchen hannunta riƙe da kofin zoɓo ta kai wa Salima. “Ga wannan ki sha Madam yana ƙara gani musamman gare ku masu kallon zare” Laure ta faɗa amma kafin Salima ta kai ga amsa Ammy ta ce “ Laure miƙo min ganin zoɓon nan har maƙoshina ya bushe,je ki kawo wani” Da sauri na ƙarasa ina cewa “ haba dai Ammy ya za ki ce haka? Ita fa wannan baƙuwarmu ce ita ya kamata a fara karramawa,kuma kin ga ke kina da mura.Laure je ki kawo wa Ammy marar sanyi,ki dinga kula don Allah ko ta ce ki bata abu mai sanyi kar ki biye ta” Laure ta miƙa wa Salima kofin,za ta ajiye shi ita ma na tari numfashinta “ Hajiya ƙyanƙyamin mu kike shine ba za ki sha ba?” da sauri ta girgiza kai ta ce “ a'a wallahi bari na sha to” sai ta kai kofin bakinta har sai da ta sha rabi sannan ta ajiye sauran.Laure na fitowa na yi mata nuni da ido kan ta tafi da ragowar wanda Salima ta ajiye,ai kuwa tana miƙawa Ammy nata sai ta ce “ bari na ɗauke sauran kar ya zuba ga capet” “Laure wane irin abu ne wannan? Ta sha abu ta ajiye shine za ki tafi da shi? In kuma tana son ƙara sha?” Ammy ta faɗa cikin faɗa ,a doli Laure ta ajiye kofin tana kallona ta koma kitchen. Hira suke tsakanin Ammy da ita Salimar ni kuma ina gefe ina danna waya,hannun Ammy na gani ya ɗauki kofin zoɓon ban san lokacin da na ce “ Tonyyyy!” ban ida rufe baki ba ji kake Ammy na salati haɗi ƴar ƙara tuni Tony ya saka bindinsa ya buge kofin daga hannunta ya faɗi ƙasa ya zuba a ƙafarta. Laure ta fito tana tambayar lafiya,na soma shafa bayan Tony da tuni ya zo ya ɗare cinyata kafin na ce “ zo ki tsabtace wurin nan please ” Jikinta na rawa ta zo ta goge wurin da ya ɓace ita kuwa Ammy sai faɗa take,a ƙarshe dai na tashi na bar wurin na koma part ɗina.Ta cikin madubina na ga hanyar da Tony ya bi ya bai wa Laure maganin da ta zuba a zoɓon Salima,ya ajiye mata shi ne a kitchen da kuma ƴar guntuwar takardar da yayi bayani daki-daki. ★MALAMA ZAINAB Matashiyar budurwa ce ƴar kimanin shekara ashirin da bakwai a duniya,ta mallaki hankalin kanta.Duk wata cikar halitta da ƙima da ake nema wurin cikakkar mace mai ƙima duk ta mallake su.Mace ce ita wacce ta riƙi bautar Ubangiji matsayin abu na farko a rayuwarta,duk sauran abubuwa suna biyo wa baya ne.Tausayi,kyauta,jinƙai su ne suka luluɓe duniyarta suka ƙawata kyakkyawar fuskarta mai cike da hasken ni'imar imani.Tun da take ba ta taɓa soyayya ba,duk da kuwa maza dayawa sun nuna ra'ayin haka amma ita ba ta ji wanda take so ba.Sheikh Ali ya kasance cousin nata,tun da ta tasa ya ga tana da addini ya ɗauki son duniya ya ɗora mata tare kuma da zage dantse wurin nuna mata abin da zai kawo ci gaban karatunta.Wannan yasa ba tare da wani tunani ba ta amince za ta aure shi har aka yi musu baiko,bayan haka ne ya tafi Misira wurin karatu.Tun da ya tafi kuma ba wata gamsashiyar waya suke ba kasancewar shi da ita ɗin duk ba su da wani isasshen lokaci.Kwana biyu da dirar shi a ƙasar Nijar ya nemi a yi walimar aurensu,wacce kuma tuni aka soma shawarwari tsakanin ahalin biyu kafin shi ma angon ya nemi su keɓe domin tattaunawa. Ko da ta fito daga gidansu HAROON direct gida direba ya ajiye ta,zuciyarta cike da fargabar abin da take gudu take kuma zato kar ace gaskiya ne wato tana son HAROON . Ɗakinta ta shiga ta yi wanka ta canza kaya,bayan ta yi sallar magrib sai ta shafa mai.Tana nan zaune tana saƙa da warwara Innarta ta shigo tana cewa “ Zainabu ki fito ga Ali nan ya zo” Sai da gabanta ya faɗi,amma ta daure ta ce ” to Inna gani nan” sai kuma ta miƙe ta zaɓo wani farin hijabi ta saka tare da fesa turare marar ƙamshi. Sai da ta yi jarumta sosai sannan ta ƙaƙalo murmushi ta yaɓawa fuskarta mai cike da damuwa.Da sallama ta fita falon,yana ganin ta ya kafe ta ido ko ƙyaftawa bai yi.Ta zauna ƙasan capet ta ce “ ina wuni Imam?” “Alhamdullah malamata fatan kin wuni lafiya?” ya faɗa ba tare da ya janye idon nasa a kanta ba,cike da tsarguwa ta ce “ Imam babu fa kyau kallon mutum haka” Yayi murmushi mai sauti ya ce “ haka ne ! Amma kar ki manta saura ƙiris ki zama tawa na yaye duk wani hijabin kunya a tsakaninmu” Ba ta ce komai ta miƙe ta je ta kawo masa ruwa da abin da Innarta ta gyara mata domin tarben baƙon.Tana zuba masa ruwa ya kafe hannunta da ido,nan take jikinta ya soma yin rawa ta ɗaga kai ta banka masa wata muguwar harara. Ya ja ajiyar zuciya ya ce “ sai da na ji wani yarrr ” ruwan ta ajiye masa ya ɗauka ya sha,sannan ta zuba masa abinci har da su cewa ta zo su ci amma ta ƙi. Bayan ya gama ne ya ce “ Malama Zainab yau muna wace rana?” Ta basa amsa kai tsaye da “laraba” Ya ce “to rana irin ta yau kin shiga lalle da yardar Allah,sai a yi ɗaurin aure juma'a,taron biki kuma asabar” Shiru ba ta ce komai ba sai ma duniyar tunani da ta lula,ranar farko da suka soma ganin juna da HAROON ,yadda suka yi baya ta faɗa kan ƙirjinsa,yanayin yadda yake kallonta cikin tako da kuma salo,yadda yake mata murmushi... “ Zainab ?” Sheikh Ali ya katse mata tunanin,a ɗan firgice ta ce “ na'am HAROON !” “Haroon kuma?” ya tambaya da mamaki,sai ta diririce ta soma kame-kame,ita ɗin ba ma'abociyar yin ƙarya ba ce shi yasa ya gane. “Kar ki yi min ƙarya Zainab,wane ne HAROON ?” Ba tare da ta basa amsa ba ta tashi da sauri har da ɗan gudunta ta shige ɗakinta tare da faɗawa kan bed ta fashe da kuka....... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822. Ki zo ki yi payment domin a yi tafiyar nan da ke, wannan karon salon na daban ne salo ne da ban taɓa yin irinsa ba. BONUS! BONUS! BONUS!!! Ina makaranta kuma ma'abotan son littafan soyayya ko kuma na tsafi? To ku zo MRS SADAUKI ta yi muku gwanjon Books ɗinta akan farashi mai sauƙi,duk book ɗin 500 za ta bar muku shi ne a 300 kacal,wanda kuma yake 700 ko sama da haka za ku same shi a 500 kawai .Me kuke jira kawai ku tuntuɓe ta WhatsApp +22795045822. Domin ku kwashi garaɓasar. [02/12 à 15:50] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 14 Sai da Zainab ta ci kuka ta ƙoshi sannan ta shiga toilet.Tana shiga ƙarƙashin shower tunaninta ya soma nuna mata ga HAROON nan tsaye tare da ita suna wanka tare da wasanni irin na ma'aurata.Murmushi ne yayi nasara bayyana a kyakkyawar fuskarta wacce a ɗazu take shimfiɗe da baƙin ciki.Tamkar wata zautata haka take murmushi na wasar ruwa da niyyar nan HAROON ne take watsa ma su haɗi da yi masa shagwaɓa.Towel ta ɗaura ta fito ,sai ta tarar da Inna zaune bakin gado.Ta ƙara sakin ranta kafin ta ce “ Inna?” “Ungo wannan ki sha,su kuma waɗannan ki dinga zuba a abinci kina ci yaji ne” cewar Innar tana mai miƙa mata kofi.Karɓa ta yi ta zauna tare da yin Bismillah ta soma shan madarar har ta shanye,sai da Inna ta ƙarara jadadda mata kar ta saki ta yi wasa da su kafin ta fice.Ita kuwa tsaf ta shirya cikin riga da wando na bacci ,ta yi sallar isha'i sannan ta zauna ta soma duba takardun jarabawar da ta yi wa ɗalibanta.Sai dai sam hankalinta ya kasa kwanciya sai aukin tunanin HAROON ,wayarta ta ɗauka ta kira Ammy bayan sun gaisa sai ta yi shiru.Can dai ta ce “ ina HAROON ?” “Yana ɗakinsa,ko na baki shi?” “A'a turo min dai lambarsa” sai kuma ta yi saurin kashewa tana dafe saitin zuciya haɗi da waro ido.“ Zainab mi kika yi haka?” ta tambayi kanta,ƙarar shigowar saƙo ta ji da sauri ta duba sai ta ga lambar ce aka turo mata sai da ta yi ta kallon lambar kafin ta yi saving da “ NAWAN” sai ta ɗora love daga ƙarshe. Data ta kunna tana addu'ar Allah sa yana WhatsApp,tsawon lokaci kafin a nuno mata lambarsa mai ɗauke da hotonsa da Ammy su duka biyun suna murmushi.Da sauri ta ɗauki hoton sai ta yanke daidai nasa kawai ta tsura masa ido can kuma ta rungume wayar tana mai jan numfashi.Duba takardun da ba ta yi ba kenan ta je ta haye bed,MP3 ɗinta ta kunna ƙira'ar Sudais ta soma tashi tana biyar karatun tana kallon hoton HAROON a haka bacci ya ɗauke ta. Washegari sai da ta tsarkake jikinta kafin ta gabatar da sallah saboda mafarkin da ta yi.Bayan ta gama ta yi shara da gyaran ɗaki sannan ta ɗumama abincin kari,sai kuma ta je ta yi shirin makaranta.Cikin ƴar ƙaramar kula ta zuba abincinta kafin ta yi wa Inna sallama,sai da ta zo bakin titi sannan ta samu abin hawa .Tana isa makaranta ɗalinta suka fara gaishe ta ita kuma ta wuce cikin aji,sai a lokacin ta ci abincinta cike da tunanin mafarkinta na jiya.Sai da ta yi da gaske sannan ta hakice tunanin HAROON daga ranta ta gabatar da darasi wanda shine ya zama na ƙarshe.Tana komawa gida aka shafa mata lalle,don dole ta haƙura tuni kuma aka fara shirye-shiryen biki kamar yadda abin ya zo mata a bazata haka su ma dangin da abokai amma duk da haka sai da aka fitar da anko.Har aka kawo lefe aka yi ɗaurin aure ko sau ɗaya Sheikh Ali bai kira ta ba haka ita ma ta share shi ko saƙo ta kasa tura masa.Yanzu ma da ake ta hidimar biki babu abin da take sai tunanin da ya daɗe da aurenta,na masoyin da igiyar aure ta yi mata iyaka da shi .Da zarar ta tuna cewa yau ɗin nan wani zai karɓe budurcinta sai hawaye su yi ta mata zuba,mutane kuwa tunaninsu kukan rabuwa da Inna ne kasancewar ita ɗaya ce tal ta rage musu a duniya duk ƴan uwanta sun rasu tun suna jarirai. Har aka yi kiran sallah magrib Malama Zainab na kuka,da aka ce ta je ta yi wanka domin shirin kaita ɗakinta ji ta yi kamar ta fasa ihu ta yadda kowa zai fahimci tsananin damuwar da ta luluɓe sirrin zuciyarta. Da ta yi wankan sai da ta yi sallar isha'i sannan mai kwalliya ta soma yi mata simple make-up ba irin tarkacen nan ba.Doguwar rigar less fari sol ta saka sannan ta ɗora alkyaba sama a haka ma sai da aka ƙara ɗora mata darar amare.Sai da aka yi hotuna da bidiyo da abokan arziki kafin a ƙara yi mata wata nasihar,daga nan aka ja ta zuwa can waje inda motocin da ango ya turo suke jira.Banda kuka babu abin da Malama Zainab take yi amma hakan bai hana aka kai ta ɗakinta ba,har aka gama addu'a kuma ba ta buɗe fuskarta ba.Nan mutane duk suka watse yayi sauran ƙawarta guda tal Hafsat wacce sai yanzu ta samu damar yi wa Zainab ɗin nasiha “ kukan nan ya isa haka don Allah! Abin da muke ta jiran ranar nan amma ta zo sai kuka kike” Malama Zainab ta buɗe luluɓin ta ce “ Hafsat tsoro nake ji,wallahi zuciyata kamar za ta fashe don fargaba don Allah ki taimaka min ki bani shawarar da zan yi amfani da ita wacce za ta hana Sheikh ya kusance ni” Shiru ta yi kafin ta ce “ caɓɓɓ! Batu wuya,gurguwa da aure nesa! Amma kin san wannan ba mai yiyuwa ba ne,wallahi sai ya kusance ki sai in magani bacci za ki basa ya sha” da sauri Malama Zainab ta ce “ yawwa ko hakan yana yi,don Allah je ki karɓo min ” sai ta zuge zip ɗin jakarta ta bata kuɗin,sai da Hafsat ta yi ta juya kuɗin kafin ta fita ta je ta siyo mata sai a lokacin hankali Malama Zainab ya kwanta.Babu jimawa kuwa ango ya shigo tare da rakiyar abokansa,bayan sun gama tasu nasihar Hafsat ta bi su don su sauke ta gida. Ido Sheikh ya tsura wa Malama Zainab wacce tun da suka haɗa ido sau ɗaya ta sunne kai.Ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar ado da kyawu” Dakyar ta amsa masa da “ wa'aleykum Salam!” sai hawaye shaaa,ya kamo dukkan hannuwanta ya sauko da ita daga bed ɗin yana mai cewa “ mu je ki yi alwala” “Ka bari zan yi ni ɗaya” ta furta,sai ya bar ta ɗin ta shiga toilet ta ɗauro alwala bayan ta fito shi sai ya shiga.Da sauri jikinta na rawa ta ɗauko maganin baccin ta je buɗe ledojin da ya shigo da su ta zuba maganin cikin lemu sai dai aka yi rashin sa'a tuni Sheikh ya fito daga toilet ya ga kwalbar sirop ɗin kuma ya fahimci na mene ne.Yayi saurin komawa toilet ɗin ya bata lokacin da za ta yi rashin gaskiyarta ta gama. Yana fitowa a karo na biyu ya sakar mata murmushi kamar bai ga komai ba,ya ja su sallah bayan nan yayi musu addu'o'i ya miƙe ya ɗauko ledojin da sauri ta karɓe ta ce “ bari na zuba mana” bai ce komai ita ta ɗauko plate da kuma kofinan shan ruwa. Da ta zuba haka ta daure tana cin kazar shi kuwa tunani ne fal zuciyarsa ‘ mene ne ribar Zainab in ta bani maganin bacci? Wato ba ta son na kusance ta sai kace ba sadakina na biya na aure ta ba .Ko dai tsoro ne take ji? A'a ba shi ba ne inda shi ne da tabbas da magiya da kissa irin ta mata zata ɓulo min’ yayi tambayoyin duk a zuci amma ya kasa samo amsa,ya ƙure ta da ido lokacin da ta cika masa kofi da lemun ya karɓa a nan take kuma ya tuna da sunan HAROON wanda y'zuciyarsa ta yanke masa tabbas saurayinta ne. Kofin ya kai bakinta yana mai cewa “ namijin kirki shine wanda ke fara shayar da matarsa kafin shi ya sha” “A'a ka sha ni ma zan sha ai ga nawa nan sai na gama ci na sha” ta faɗa tana zarar ido, Sheikh ya saki murmushi ya ce “ in dai ba ki sha to ni ma ba zan sha ba sai da na sha ruwan pampo” Malama Zainab na jin haka ta yi saurin karɓa ta sha ,da tunanin can su yi ta baccin su biyu .Shi kuwa Sheikh haka ya tsura mata ido har sai da ta shanye tass,ta cika masa kofi ta ce “ saura kai” ya laƙace mata hanci ya ce “ ai ni bana shan kayan zaƙi saboda suna da illa, dama dai wayo na yi miki ” Tamkar wacce cutar sanƙarau ta kama haka ta sandare ta kasa motsi sai idonta da ke tsiyayar da hawaye tana da na sanin haƙa wa ramen muguntar da a ƙarshe ita ce ta faɗa .Ba a ɗauki lokaci ba ta ji fitilun idonta na disashewa,sai a lokacin ta miƙe da hanzari ta shiga toilet ta wanke fuskarta duk don kar bacci ya ɗauke ta sai dai ina tuni ta soma jin jikinta ma na saki.Da sauri ta fito kamar wata makauniya tana lalube, Sheikh ya je ya kamo ta tare da ɗora ta kan bed yana mai cewa “ shi yasa aka ce in za ka gina ramen mugunta ka gina shi gajere” sai kuma ya soma cire mata suturar jikinta.Sai da yayi mata zirr kafin ya cire nasa,jikinsa har rawa yake wurin ƙoƙarin haura gadon sai dai cak ya tsaya saboda yadda idonsa suka fara nuna masa ba daidai ba.Malama Zainab yake gani ta rikiɗe masa ta koma lakaɗeɗen maciji sai wani haske take fitarwa...... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [03/12 à 16:24] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 15 Jikin Sheikh Ali ne ya ɗau wata irin muguwar rawa ganin amaryarsa wacce aka kawo masa yau ta rikiɗe ta zama lakaɗeɗiyar macijiya sai wani kaɗan bindi take. Da gudu ya dawo falo ba tare da ya tsaya ɗaukar ko da wando ba ne,ɗakinsa da ya ware tun can a matsayin baraya ya shiga.Duk uban sanyin da ake zufa ce ke yi masa tsiyaya,tunani ya soma kamar wani zautace haɗi da suratai.“ Aljana ce aka kawo mini ko kuwa Jinnul ashiq ne da ita banda labari? Kaicona ni Ali ,ni kam banda rabo a duniya duk yadda nake mararin ganin wannan daren amma ya zo min ta wata mummunar siffa? Ai kuwa ba zan zauna da ke ba wallahi dole ki tafi gidanku” sam bai rumtsa ba haka yayi ta zagayen ɗakinsa yana tubka da warwara. ★HAROON Tun bayan da Salima ta sha lemun zoɓon nan sai ya zamana a kullum kafin na fita aiki sai ta shigo gidanmu.Haka za ta yi ta kallona amma ta kasa yin magana,gefe guda kuma Laure mai aiki na ci gaba da bata maganin da Tony ya ajiye a kitchen. Yau ma kamar kullum ina zaune ina duba takardun da nasa aka buga min irin wanda in kana son ganin likita patients ke cira,da sallama Salimar ta shigo.Ammy ba ta falo sai ni kaɗai,ido na zuba mata sai na ga ta soma kyarma yayin da bakinta ke ta rawa.Na fahimci kalmar so take son furta mini amma ƙarfin zuciyarta ya hana ta faɗa ,ni kuwa ta wannan hanyar ce kawai zan cimma ƙudirina a kanta. Idonta ne ya soma kawo ruwa,da sauri na kawar da kai gefe ina jin wani haushin ta .Sai ta fita a guje tana kuka,na ja tsuki tare da tashi na fito na shiga ɗakin da na ware domin duba maras lafiya da kuma masu son a yi musu aiki. Kamar yadda na tsara sai ranar asabar kawai zan dinga yin aiki,yayin da kuma Iliya direbana zai dinga karɓar kuɗin ganina sai ya bai wa mutum takardar shaida. Yau ce ranar farko da zan soma kamar yadda na sanar a sanarwar da nasa aka yi,amma mutane ne masu mugun yawa suka taru.Ɗaya bayan ɗaya suke shigowa ,in na karɓi receip/reçu ɗin hannun mutum ni ne zan sanar da shi sunansa da kuma matsalar da ta kawo shi .Dukkan bayanin kuma Tony ne ke sanar da ni komai,yanzu ma layi ya kawo kan wata budurwa da ta shigo.Ta miƙa mini takardar hannunta na karɓa ina dubawa “ sunanki Shukuriya,kina son a yi miki aiki kan Salele don ya saki matarsa ke ya aure ki saboda ba ki son kishiya sannan shi ma ya faɗa miki bai da tsarin yin mata biyu saboda bai da cikakken lokaci a matsayinsa na soja” na faɗa ina mai kallon ta,a zahiri fuskarta ce nake kallo amma a baɗini ruhinta ne abin dubana.Sam ba ta da mutumci ga kuma muguwar zuciya,uwa uba rashin imaninta yayi ƙasa sosai.Bayan na gama ganin qualitynta sai na saki murmushi,yayin da kuma muryar Tony ke ce min “ HAROON wannan ɗin ma ka riƙe ta gam da alamu za ta kawo ma ci gaba a tafiyarka ” “Eh haka ne malam,shine abin da nake so amma nawa zan bada?” ta tambaye ni tana wani sunne kai.Zama na gyara ina jawo tasar da na zuba ruwan tsafina na soma shafa su,sai na ce “ kina da hoton shi saurayin naki?” “Sai dai a waya kawai” ta bani amsa,na ce “ nemo ki miƙo min” da sauri kuwa ta miƙo min wayar don hotonsa ne kan screen.Saitin tasar ruwan na kara hoton tamkar mai yin scanning nan take zanen hoton ya zauna raɗam kan ruwan,cikin abin da bai kai minti biyar ba na gama kwashe duk wasu bayanansa. Na ɗago na dube ta na ɗan wani lokaci kafin na ce ,“me yasa kika yarda da shi har kika basa kanki? Cewa yayi zai aure ki ko? Yana son ki? To duk ƙarya ce kawai yana wasa da hankalinki ne,jikinki kawai yake so.Amma zan yi miki aikin da sai ya aure ki,fatan za ki bi duk sharuɗan da zan gindiya miki?” “Eh malam in dai zai aure ni koma mene ne zan yi” “Ina so ki kawo min maniyinsa” na faɗa . Ta waro ido tare da cewa “ ta yaya malam?” “Abu mai sauƙi,in za ku yi mu'amala ki saka condom ta mata ko kuma shi ki basa ya saka kin gane dai ko?” “To malam zan yi,sai me kuma?” “Shi kaɗai nake buƙata za ki iya tafiya,in kin samo shi ko yau ne ki dawo” na faɗa ta yi godiya tare da fita,wasu suka ci gaba da shigowa a cikinsu babu wanda na yi wa aiki sai dai cutarsu da na yi ina kwashe taurarunsu ina adanawa kaina domin ƙarin power a haka har dare yayi. Ina shigo wa falo Ammy ta soma yi min sannu tare da addu'ar ci gaba akan aikin alherin da na soma yau.Ko abinci ban ci ba na shiga ɗakina,madubina na ga yau yayi kicin-kicin da fuska alamun akwai matsalar da ke tunkara ta. Tony na duba na ce “ mene ne wannan?” sai kuma na yi tsaye gaban madubin. “Ana shirin kai abar ƙaunarka ne gidan Ali” Tony ya bani amsa,wani ɓacin rai ne na ji ya sauko min na ce “ fatan ka yi duk abin da ya dace?” “ Kar ka damu na aika masa da aljani mai juye hasken ido” Na saki murmushi,kafin na shiga na yi wanka.Kamar wata tv haka na zauna ina kallon idon Tony waɗanda suke fitar da wani jan haske ta cikinsu ne nake ganin duk abin da ke wakana.Tun daga ƴan kan amarya har lokacin da Malama Zainab ta zuba maganin bacci da yadda shi Sheikh ya fita a guje babu kaya jikinsa,raina fari ƙal tsabar murna haka na jawo Tony na rungume tare da ja mana blanket. Tunanin Malama Zainab ne ya addabi ruhina,yayin da muguwar sha'awarta ta yi min kamun kazar kuku.A haka dai na samu bacci ya ɗauke ni sai dai bai yi nisa ba na ji ana kiran sunana. “ HAROON ? HAROON ?” a hankali na soma buɗe idona da suka yi min nauyi,ban gani sosai amma ita muryar tabbas na san mai ita sai dai na manta a ina. “ HAROON za su kashe ni,ka cece ni HAROON ban bar gida ba don cutar da ku sai don na zaɓa wa kaina rayuwa mai inganci ” muryar ta sake faɗa ,a wannan karon zumbur na miƙe ina kallon madubina wanda hoton Abbana ya fito raɗau kuma yana motsi idonsa suna zubar da hawayen jini.Ko kaɗan ganinsa a cikin wannan hali bai sa na ji tausayinsa ba sai ma tuna min da yayi da tsohuwar rayuwata ta baya a ranar nan wacce na tarar da shi yana haɗa kaya ban manta ba abu na farko da na ce masa shi ne “ Abba ina kuma zaka je da kaya?” Ya juyo a zabure kafin kuma ya haɗe rai ya ce ,“ zan tafi na yi nesa da ku,zan auri yarinya sabon jini wacce zata kula da ni.Wacce ta san darajata da ƙimata,wacce duk abin da na nemo na bata ba ta raina wa sai ma dai ta ƙara da nata kuɗin.Na gaji da zama Ammynka,mugun halinta sai ƙara yin gaba yake,ta hana ni na ƙara aure na ƙi hannuwa shine ta tsiro da faɗuwar ƙarya wai jininta ya hau.To can ku ƙarasa rayuwarku ni ma zan yi tawa ” Cike da takaici na ce “ duk ƙoƙarin da take yi na yin ƴar ƙaramar sana'a domin ciyar da kai ba ka gani ba? Abba a wannan yanayin ne za ka ƙara aure? Ka manta nan gidan haya ne muke? In ka aure ta ina zaka kai ta?” “Ita ai ba matsiyaciya ba ce irin uwarka,ita shahararriyar ƴar kasuwa ce mai ji da kanta .Ga tsafta ga gayu,ga cima mai kyau ka ga sai an jima ni zan tafi” “Abba ka sani muddin ka bar gidan nan ka fita daga sawun masu rai a wurina” na faɗa sanin yana mugun sona.Amma ga mamakina sai na ji ya ce “ wannan ta fi nono fari a wurina” yana gama faɗa ya fice ya bar ni ina zubar da hawayen takaici. Yanzu ma gumin hawayen ne ya dawo da ni daga duniyar tunanina,na dubi Abba da ke haɗe hannuwa yana roƙona yafiya.Ban ce komai ba haka kuma ban motsa ba,Tony da ke kan jikina yayi tsalle ya kai wa Abbana farmaki a gaban idona ya kafa haƙoransa ga wuyan Abba . Na zabura na sauka daga bed ɗin,sai dai ko kafin na isa ga madubin duk hotunan suka ɓace ya dawo normal.Duk yadda na yi ƙoƙarin shiga ciki kuma abu ya cuttura,daga can bakin ƙofa na ji ana buga min ɗaki .Ba tare da na tambayi wane ne ba na je na buɗe,Ammy ce tsaye duk jikinta rawa yake da alamu a tsorace take. “Ammy lafiya kika fito da tsakar daren nan?” na tambaye ta. “ Tsoro nake ji HAROON ,yau ashirin da biyu ga wata Yulin ” “Eh mene ne ?” “Zagayowar sallar Lugnasad ” ta faɗa tana kuka,“ Ammy ni ban fahimci komai ba” “Ai dai kanka bai ciwo ko?” ta faɗa tana tallabo fuskata,na ce “eh bai yi” sai ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta juya ta fita tsaye na yi cike da mamaki,tabbas na ƙara yarda Ammy na ɓoye min wani sirri. Ɗakin na rufe tare da jingina jikin ƙofa,ina shirin rufe ido na ga saukar Oga tsudum.Da sauri na isa gare shi ina cewa “Oga kai ne a daren nan?” Fuska ya ƙara haɗewa kafin ya ce “ HAROON na taɓa wasa da kai?” “A'a Oga” “Amma mene dalilinka na ɓoye min gaskiyar kai wane ne?” “Ban gane ba Oga me kake faɗa haka?” “Dubi madubinka” ya faɗa tare da yi min nuni da shi,na kai idona nan na yi arba da wata siffa marar kyawun gani kai tsaye za a kira shi da aljani ko kuma dodo.Tsaye yake cikin iska yayin da wata mata ke yi masa kirari wutar na ɓulɓulowa ta ƙasa . “Wace ce ita?” na tambaya. “Amsar da nake son ji kenan daga bakinka,ita ɗin ahalinka ce maganar da nake yi ma yanzu rigima ce muke don ta ce kai ɗin nasu ne ” Oga ya faɗa . Na girgiza kai na ce “ban taɓa shiga ƙungiyar asiri ba” “Abbanka fa?” Oga ya jefo min tambaya,na ce “ba na tunanin yana ciki,domin kuwa da ace haka ne da talauci bai yi wa duniyarmu ƙawanya ba ,har ta kai ga Abba ya guje mu ya koma wurin wata mata wacce ba Ammy ba” “Yanzu na fahimta, wannan ɗin matar mahaifinka ce! Ita ɗin baya ga tsafi da take kuma ƴa ce ga ƙungiyar asiri,mahaifinka ya bayar da jininka matsayin sacrifice .Ya zama dole ka nemo mafita tun cikin daren nan,sannan ka tambayi ita Ammynka ta baka labarin ainahin abin da take ɓoye ” yana gama faɗa ya fice.Na dafe goshi ina shirin shiga toilet sai madubina ya soma fitar da wani haske,da mugun sauri na dafe gaban goshina saboda wani abu da na ji ya caki wurin kamar mashi sai kuma na zaro ido ganin kamar giftawar Malama Zainab,can kuma mijinta ya bayyana hannunsa riƙe da lakaɗeɗen belt.Da mugun sauri na isa bakin madubin,na kai yatsana manuniya na dakatar da mijin nata ta hanyar furta kalaman tsafi sai ya zube nan a yashe kan tile. ★MALAMA ZAINAB Tamkar gawa haka ta yi ta sharar bacci,ba ita ta farka ba sai ukun dare.Kanta ta soma jin yana ciwo,ta tashi dakyar ta zauna.Duk abubuwan da suka faru ne suka soma dawo mata daki-daki,sai ta duba jikinta sam babu alamar an yi amfani da ita amma kuma ga jikinta babu sutura.Toilet ta shiga ta yi wanka tare da ɗauro alwala,ta saka jallabiya tana shirin ƙabarta sallah ta ji ihun Sheikh Ali,da sauri ta fito ta soma tafiya har ta isa cikin ɗakin nasa sai ta tarar ashe mafarki ne yake. “Subahanallah Sheikh lafiya kake?” ta faɗa tare da ɗan bubuga gefen gadon,daidai nan ya tashi suna haɗa ido da ita ya tashi tsaye tare da kwaɗa mata mari ko kafin ta tambayi dalili ya rufe ta da uban duka.Dole dangin naƙi ce ta sa ta fito a guje,shi ma Sheikh ya ɗauki belt ɗin da ya gani kan gado ya biyo ta a tsiyace sai dai aka yi rashin sa'a kafin ya isa gare ta ya ji wani abu mai kamar tartsatsin wuta ya naushe shi .Yayi ƙara tare da faɗuwa timmm a ƙasa,hakan ya jawo hankalin Malama Zainab ta juyo sai kuma ta ga abin da ke faruwa ta dawo da sauri tare da zubewa tana kiran sunansa “Sheikh? Sheikh Ali ?” sai dai shiru bai ko motsa ba saboda babu numfashi a tattare da shi,ta ɗora hannu saman kai tana mai cewa “innallilahi wa'inna ileyhi raji'un!” daga wannan page ɗin ba zan sake fitar da wata ba,duk mai son ci gaba za ta biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ta turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 Mu haɗe a PAID group 🤗 NB: daga lokacin da ya zama Complete 1k ne farashinsa. [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: 😪😪😪😪 *ZAWARCI*😓 😪😪😪😪 LoVe aNd HoRrOr StOrY *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman. _____________________ 21/10/24 1-2 #Damagaram Ƙarfe uku na dare agogon ɗakin ya nuna,a sa'ilin da mutane ke kwance suna hutawa a daidai wannan lokacin ne Hajara ta hana idonta bacci saboda yawunta da suke tsinkewa tsabar yadda suke kwaɗayin ɗanɗanon jini. Idonta ta fara rikiɗarwa tun farko kafin ta tura ƙofar ɗakin wacce ta yi sa'a ba a kulle ba,ɗakin cike yake da duhu amma bai hana idon Hajara hango Safeenat ba wacce ke kwance ta tallabe ƙaton cikinta tana sharara bacci. Yawun Hajara suka ɗiga ga ƙasa lokacin da ta yi tozali da ɗan jinjirin da ke kwance a marar uwarsa,ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare ta kawai sai ga wani haske da ba ta san daga ina ya fito ba ya luluɓe Safeenat.Da wani mugun sauri ta yi baya tana zarar idonta da suke jawur kamar wuta kafin kuma ta fice daga ɗakin gaba ɗaya,ba wai don ta haƙura ba sai don ƙara yin wani sabon shirin. “Hajara lafiya kika zo kika tsaya tsakiyar falo?” muryar mijinta Dayyabu ta daki kunnenta,da mugun sauri ta lumshe idonta gudun kar asirinta ya tonu,ba tare da ta amsa masa tambayar ba ta yi gaba ta koma ɗakinta ta ja ƙofa ta rufe.Sai a lokacin ta ja wani numfashi haɗi da buɗe idon, ƙarƙashin gadonta ta je jawo wata tukunyar laka.Banda baƙin hayaƙi babu komai a ciki,wani yare ta yi sai ga shi ta rikiɗe ta koma tsakaka haka ta fito ta fara bin bango ba ta zame ko ina ba sai ɗakin Safeenat a karo na biyu.Har yanzu hasken bai ida gushe wa ba,wannan dalili yasa ta sauka kan dressing mirror ta fiddo harshenta tare da fara zuba yawunta cikin man shafawa da Safeenat ta bar shi a buɗe . Bayan ta gama ne ta ƙara bin bango ta fito mijinta ta gani ya buɗe ƙofar ɗakinta ya shiga ya kuma fito da alamu rashin ganin ta ne yasa haka. Da sauri ta koma ta je ta ɗauki siffarta ta bil'adama,gefen gado ta zauna tana jin har yanzu kwaɗayinta bai kau ba.Haka wannan dare ya kasance daren rashin sa'a gare ta,sam ba ta yi wani baccin kirki ba. Washegari Tun safe Safeenat ta yi wanka ta shafa mai da turare sannan ta shirya cikin doguwar riga kasancewar cikinta ya tsufa ba ta da wata sutura mai yi mata in ba doguwar rigar ba. Cikin sanyin jikin da ya zama tabi'arta ta fito,a falo ta tarar da ahalin gidan kan table suna cin abinci. “Daddy ina kwana?” ta gaishe da mahaifinta,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa “ lafiya lau Feenat ya ƙarfin jikinki?” “Alhamdullah!” ta amsa tare da maida dubanta gefen Hajara ta ce “ina kwana Gwaggo?” Hajara ta haɗe rai ta ce “ da ban kwana ba za ki gan ni ? Tsabar munafurci ba ki tashi fito wa ba sai da baiwarki ta gama girki kin fito ki kwashi banza to ban girka da ke ba” Feenat ta sunne kai tana jin wani irin zafi na tasowa daga ƙasan zuciyarta,babban takaicinta kuma da ta ji Daddy yayi shiru bai ce komai ba.Yaran Hajara Munir da Munira suka shiga yi mata dariya,ba ta kula su ba ta wuce kitchen ɗin ta nema wa kanta abin da za ta ci.Ƙasan tile ta zauna dirshen ta soma tunanin bayan ta gama cin abincin,hawaye suka zubo mata ba ta shirya ba da sauri kuma ta dafe ƙaton cikinta da ke faman juyawa tana jin muguwar ƙaunarsa don a yanzu shine kawai zai rage mata raɗaɗin rashin masoyinta Bashir. “A yi dai mu gani in tusa ta hura wuta! Yo wannan kukan shi zai maido miki mijin? Ai dama duk abin da aka yi shi da cin amana ba zai je ko ina ba.Yanzu da kika yi sanadin hana Bashir auren Murjanatu ina ce ya mutu ya bar ki,kuma ita Murjanatun na can Saudi Arabia cikin gata tana auren farin ciki” Goggo Hajara ta faɗa lokacin da ta tarar da Feenat a kitchen tana kuka.Ta yi kutufo da ƙafafunta ta ce “ ja ki ban wuri na wuce ko kuma na sabanta ki muguwa mai halin uwarta” da mugun sauri ta janye ƙafafunta wani sabon kukan na ƙwace mata. Cikin masifar nan Goggo Hajara ta ci gaba da balbale ta da masifa,“ ki tashi ki fitar min daga kitchen zan ɗora girki ,ki koma can ɗaki ki ci gaba da munafurcinki” Daga bakin ƙofa Daddy ya ce “Hajara ki zo ina son ganin ki ɗakina” Idonta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yadda take hararen Feenat,haka ta wuce ta je ɗakin Daddy a tsaye ta tarar da shi ya ba ƙofa baya. “Daddyn yara ga ni ” ta faɗa cike da ladabi. “ Haja ki kiyaye ni,bari gani na ƙyale ki ɗazu kin ci mutumcin ƴata,na yi shiru ne kawai don in nunawa Feenat ba ta kyauta da ta bar ki ke ɗaya ki ka yi aikin gida ba .Amma ba zan lamunci ki tozarta min ƴa ba,nan gidana ne don haka tana da ƴanci sake wa yadda take so.Mine ne na yi mata gori? Maimakon ki rarrashe ta akan halin da take ciki shi ne za ki tsiro mata da wata sabuwar masifar? Ta rasa mijinta wannan kaɗai abun tausayi ne,sannan ga tsohon ciki.Na san tun bayan da Feenat ta auri Bashir ki ka tsane ta,kin manta cewa matar mutum kabarinsa tun can farko Allah bai nufa Murjanatun ce zai aura ba” Cike da munafurci Goggo Hajara ta soma kuka har da jan majina kamar wata yarinya,da mugun sauri Daddy ya juyo tare da jawo ta jikinsa yana cewa “mine ne kuma na kuka? Ke fa uwa ce bai kamata sai an faɗa miki abin da ya dace ba,ɗa na kowa ne ba ka san mai taimakon ka ba” “Amma Daddyn yara ka fi kowa sanin yadda na riƙe Safeenat da zuciya ɗaya amma rana tsaka ta ruguza alaƙar nan don kawai ta ga banda burin da ya wuce Murjanatu ta yi aure” “To ai yanzu komai ya wuce,ba ga shi ta yi auren ba? Jiya ma mijinta ya min magana kan yana so ta dawo gida ta haihu ” Jin ƴarta za ta dawo sai ta manta da zancen kuka ta washe baki ta ce “au ! Madallah! Yaushe za ta zo?” Daddy ya murmusa ya ce “a'a ƴarki ta ce kar a sanar da ke za ta yi miki bazata kawai ki zamana cikin shiri” da wannan Daddy ya fice ya bar gidan zuwan can Company wurin aikinsa. Goggo Hajara kuwa kitchen ta koma sai ta tarar da Feenat ta ɗora girkin rana sai gumi take saboda zafin wutar gas,ta taɓe baki kafin ta fito. Ita kuwa Feenat baiwar Allah sam ba ta ƙaunar tashin hankali wannan ya saka ta ɗora girkin duk don a zauna lafiya.Kafin ta gama jikinta ya soma ƙaiƙayi, soshe-soshe ta fara yi ganin abun na ta yin gaba yasa ta kashe gas ɗin ta fito.Ɗakinta ta je,direct toilet ta shiga ta soma yin wanka sai dai ba ta canza zane ba sai ma wani ja da fatarta ta yi.Dakyar ta daure ta je ta ida girkin ta zuba a kuloli ta jera kan table,da ta koma ɗaki sai ta ɗauki hoton hannunta inda alamun jan ya fi yawa ta tura wa ƙawarta Sakeenatu tana tambayarta ko mene ne wannan kasancewarta likita .Babu jimawa ta kira ta bayan sun gaisa ne take cewa “ sai dai ki zo asibiti a duba ki ta waya ba a ganewa,kuma ni ba aikina ba sai dai na haɗa ki da likitan fata” Feenat ta ja ajiyar zuciya ta ce “ KEENAT kin san Daddy ba zai bari na fita ba,kuma dama bai dace mace mai takaba ta fita ba” Cike da tausaya wa KEENAT ta ce “ na sani amma ai lafiya ta fi komai ,ƙila kuma kin ci wani abu ne da ya haifar miki da hakan” “Ban ci komai ba fa,ya aikin ana ta fama ko?” “Wallahi kuwa,in sha Allah in na sauka zan biyo nan gida na duba ki” sosai suka yi hira kafin su yi sallama. Daga inda take zaune ta fara kallon hotunan Bashir inda yake sanye da Kakin soja,nan ta lalace wurin kallonsu har sai da Munira ta shigo kiranta .Ta miƙe dakyar ta fita,a falo ta tarar da Goggo Hajara tun da ta fito ta lura idonta na kan cikinta.Ta sunne kai tana mai karanta ‘ Hasbunallahu wani'imal wakil ’ a can ƙasan zuciyarta,cikin nata ne ya soma yin motsi kamar zai fito mata ta cibiya.Tsabar yadda take jin ciwon juyinsa yasa ta kai hannu ta dafe ƙasan mararta tana mai fitar da nishin wahala,ido rufe ta ci gaba da sauraren azabar da ke ratsa duk sassan jikinta. Goggo Hajara ta yi wani makirin murmushi tana mai cewa “ Safeenat lafiya kuwa?” Sai a lokacin ta ware idonta da suka yi wani mugun ja,bakinta sam ba zai buɗu ba ballantana ta iya yin magana.Bayanta da ƙugunta suka ƙage lokaci guda wanda ya haifar mata duƙawa ba ta shirya ba,tuni idonta sun fara ganin dishi-dishi duk da wannan ne cikin farko tuni ta fahimci haihuwar ce ta zo bilhaƙi. Goggo Hajara ta ce “ Haihuwa ce kam,Munira fita waje bari na ɗauko leda ” “Mama in kira mai taxi ku wuce asibiti ko?” Munira ta faɗa tana kallon Safeenat wacce tuni ta fara wani gurnani mai haɗe da nishi. “Uwar mai taxi za ki kira ,fice na ce” Goggo Hajara ta faɗa tana mai shiga ɗakin Safeenat ta ɗauko robar da aka tanadi duk wasu kayan haihuwa. Da kanta ta shimfiɗa leda ta ɗora wasu zannuwa akai kafin ta ce “ Safeenat ki cire rigar nan mai haihuwa ina ruwanta da wata sutura” tsabar azabar da take ji yasa ba ta yi yunƙurin hana Goggo cire mata kayan ba. Yawun Goggo Hajara har wani dalala suke suna tsinkewa lokacin da ta ga kan ɗa ya sawo kai.Jikinta har rawa yake wurin taimakawa yaron ya fito ,babu wani jinkiri ko ɓata lokaci ta fara juya ido tare da soma kai wa kurwar jinjirin hari sai dai ba ta ida cin galaba ba nishin Safeenat haɗi da kukan wata babyn ya dawo da ita hayyacinta. Ƙirjin Goggo Hajara ne ya kusan ɓallewa zuciyarta ta faɗo tsabar firgici,jaririyar da faɗo cibinta a yanke yake sannan kuma babu marakiya saɓanin shi namijin da har yanzu take masa reto. Sai a lokacin ne ma ta samu zarrar yanke mahaifar,ba tare da kuma ta san dalilin kawar mata da mugun nufinta ba ta soma kimtsa Safeenat wacce babu laifi ta dawo hayyacinta. Goggo Hajara ta wanke kayan da kuma gyara ɗakin ta saka turaren wuta,ita ce kuma ta zaɓo wa Safeenat riga da zane.Har da haɗo mata tea mai zafi ta sha,gefe ta koma bayan ta gama komai tana tunanin zuci ‘ mi ya shiga kaina ni Hajara? Kamar ni kamar ba ni ce ba’ kukan jariran ne ya katse mata tunani ,ta ce “ ki ɗora su ga abincinsu” sai kuma miƙe ta soma nuna mata yadda za ta yi.Namijin kawai ya sha ita kuwa macen baya ga kuka babu abin da take,Goggo Hajara na ɗaukar ta sai kuma ta yi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba.Muƙut ta haɗiye wasu yawu hango wani baƙin kallo daga cikin ƙwayar jaririyar da ko minti talatin ba a yi ba da haihuwarta...... [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman. _____________________ 21/09/24 1-2 #Damagaram Ƙarfe uku na dare agogon ɗakin ya nuna,a sa'ilin da mutane ke kwance suna hutawa a daidai wannan lokacin ne Hajara ta hana idonta bacci saboda yawunta da suke tsinkewa tsabar yadda suke kwaɗayin ɗanɗanon jini. Idonta ta fara rikiɗarwa tun farko kafin ta tura ƙofar ɗakin wacce ta yi sa'a ba a kulle ba,ɗakin cike yake da duhu amma bai hana idon Hajara hango Safeenat ba wacce ke kwance ta tallabe ƙaton cikinta tana sharara bacci. Yawun Hajara suka ɗiga ga ƙasa lokacin da ta yi tozali da ɗan jinjirin da ke kwance a marar uwarsa,ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare ta kawai sai ga wani haske da ba ta san daga ina ya fito ba ya luluɓe Safeenat.Da wani mugun sauri ta yi baya tana zarar idonta da suke jawur kamar wuta kafin kuma ta fice daga ɗakin gaba ɗaya,ba wai don ta haƙura ba sai don ƙara yin wani sabon shirin. “Hajara lafiya kika zo kika tsaya tsakiyar falo?” muryar mijinta Dayyabu ta daki kunnenta,da mugun sauri ta lumshe idonta gudun kar asirinta ya tonu,ba tare da ta amsa masa tambayar ba ta yi gaba ta koma ɗakinta ta ja ƙofa ta rufe.Sai a lokacin ta ja wani numfashi haɗi da buɗe idon, ƙarƙashin gadonta ta je jawo wata tukunyar laka.Banda baƙin hayaƙi babu komai a ciki,wani yare ta yi sai ga shi ta rikiɗe ta koma tsakaka haka ta fito ta fara bin bango ba ta zame ko ina ba sai ɗakin Safeenat a karo na biyu.Har yanzu hasken bai ida gushe wa ba,wannan dalili yasa ta sauka kan dressing mirror ta fiddo harshenta tare da fara zuba yawunta cikin man shafawa da Safeenat ta bar shi a buɗe . Bayan ta gama ne ta ƙara bin bango ta fito mijinta ta gani ya buɗe ƙofar ɗakinta ya shiga ya kuma fito da alamu rashin ganin ta ne yasa haka. Da sauri ta koma ta je ta ɗauki siffarta ta bil'adama,gefen gado ta zauna tana jin har yanzu kwaɗayinta bai kau ba.Haka wannan dare ya kasance daren rashin sa'a gare ta,sam ba ta yi wani baccin kirki ba. Washegari Tun safe Safeenat ta yi wanka ta shafa mai da turare sannan ta shirya cikin doguwar riga kasancewar cikinta ya tsufa ba ta da wata sutura mai yi mata in ba doguwar rigar ba. Cikin sanyin jikin da ya zama tabi'arta ta fito,a falo ta tarar da ahalin gidan kan table suna cin abinci. “Daddy ina kwana?” ta gaishe da mahaifinta,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa “ lafiya lau Feenat ya ƙarfin jikinki?” “Alhamdullah!” ta amsa tare da maida dubanta gefen Hajara ta ce “ina kwana Gwaggo?” Hajara ta haɗe rai ta ce “ da ban kwana ba za ki gan ni ? Tsabar munafurci ba ki tashi fito wa ba sai da baiwarki ta gama girki kin fito ki kwashi banza to ban girka da ke ba” Feenat ta sunne kai tana jin wani irin zafi na tasowa daga ƙasan zuciyarta,babban takaicinta kuma da ta ji Daddy yayi shiru bai ce komai ba.Yaran Hajara Munir da Munira suka shiga yi mata dariya,ba ta kula su ba ta wuce kitchen ɗin ta nema wa kanta abin da za ta ci.Ƙasan tile ta zauna dirshen ta soma tunanin bayan ta gama cin abincin,hawaye suka zubo mata ba ta shirya ba da sauri kuma ta dafe ƙaton cikinta da ke faman juyawa tana jin muguwar ƙaunarsa don a yanzu shine kawai zai rage mata raɗaɗin rashin masoyinta Bashir. “A yi dai mu gani in tusa ta hura wuta! Yo wannan kukan shi zai maido miki mijin? Ai dama duk abin da aka yi shi da cin amana ba zai je ko ina ba.Yanzu da kika yi sanadin hana Bashir auren Murjanatu ina ce ya mutu ya bar ki,kuma ita Murjanatun na can Saudi Arabia cikin gata tana auren farin ciki” Goggo Hajara ta faɗa lokacin da ta tarar da Feenat a kitchen tana kuka.Ta yi kutufo da ƙafafunta ta ce “ ja ki ban wuri na wuce ko kuma na sabanta ki muguwa mai halin uwarta” da mugun sauri ta janye ƙafafunta wani sabon kukan na ƙwace mata. Cikin masifar nan Goggo Hajara ta ci gaba da balbale ta da masifa,“ ki tashi ki fitar min daga kitchen zan ɗora girki ,ki koma can ɗaki ki ci gaba da munafurcinki” Daga bakin ƙofa Daddy ya ce “Hajara ki zo ina son ganin ki ɗakina” Idonta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yadda take hararen Feenat,haka ta wuce ta je ɗakin Daddy a tsaye ta tarar da shi ya ba ƙofa baya. “Daddyn yara ga ni ” ta faɗa cike da ladabi. “ Haja ki kiyaye ni,bari gani na ƙyale ki ɗazu kin ci mutumcin ƴata,na yi shiru ne kawai don in nunawa Feenat ba ta kyauta da ta bar ki ke ɗaya ki ka yi aikin gida ba .Amma ba zan lamunci ki tozarta min ƴa ba,nan gidana ne don haka tana da ƴanci sake wa yadda take so.Mine ne na yi mata gori? Maimakon ki rarrashe ta akan halin da take ciki shi ne za ki tsiro mata da wata sabuwar masifar? Ta rasa mijinta wannan kaɗai abun tausayi ne,sannan ga tsohon ciki.Na san tun bayan da Feenat ta auri Bashir ki ka tsane ta,kin manta cewa matar mutum kabarinsa tun can farko Allah bai nufa Murjanatun ce zai aura ba” Cike da munafurci Goggo Hajara ta soma kuka har da jan majina kamar wata yarinya,da mugun sauri Daddy ya juyo tare da jawo ta jikinsa yana cewa “mine ne kuma na kuka? Ke fa uwa ce bai kamata sai an faɗa miki abin da ya dace ba,ɗa na kowa ne ba ka san mai taimakon ka ba” “Amma Daddyn yara ka fi kowa sanin yadda na riƙe Safeenat da zuciya ɗaya amma rana tsaka ta ruguza alaƙar nan don kawai ta ga banda burin da ya wuce Murjanatu ta yi aure” “To ai yanzu komai ya wuce,ba ga shi ta yi auren ba? Jiya ma mijinta ya min magana kan yana so ta dawo gida ta haihu ” Jin ƴarta za ta dawo sai ta manta da zancen kuka ta washe baki ta ce “au ! Madallah! Yaushe za ta zo?” Daddy ya murmusa ya ce “a'a ƴarki ta ce kar a sanar da ke za ta yi miki bazata kawai ki zamana cikin shiri” da wannan Daddy ya fice ya bar gidan zuwan can Company wurin aikinsa. Goggo Hajara kuwa kitchen ta koma sai ta tarar da Feenat ta ɗora girkin rana sai gumi take saboda zafin wutar gas,ta taɓe baki kafin ta fito. Ita kuwa Feenat baiwar Allah sam ba ta ƙaunar tashin hankali wannan ya saka ta ɗora girkin duk don a zauna lafiya.Kafin ta gama jikinta ya soma ƙaiƙayi, soshe-soshe ta fara yi ganin abun na ta yin gaba yasa ta kashe gas ɗin ta fito.Ɗakinta ta je,direct toilet ta shiga ta soma yin wanka sai dai ba ta canza zane ba sai ma wani ja da fatarta ta yi.Dakyar ta daure ta je ta ida girkin ta zuba a kuloli ta jera kan table,da ta koma ɗaki sai ta ɗauki hoton hannunta inda alamun jan ya fi yawa ta tura wa ƙawarta Sakeenatu tana tambayarta ko mene ne wannan kasancewarta likita .Babu jimawa ta kira ta bayan sun gaisa ne take cewa “ sai dai ki zo asibiti a duba ki ta waya ba a ganewa,kuma ni ba aikina ba sai dai na haɗa ki da likitan fata” Feenat ta ja ajiyar zuciya ta ce “ KEENAT kin san Daddy ba zai bari na fita ba,kuma dama bai dace mace mai takaba ta fita ba” Cike da tausaya wa KEENAT ta ce “ na sani amma ai lafiya ta fi komai ,ƙila kuma kin ci wani abu ne da ya haifar miki da hakan” “Ban ci komai ba fa,ya aikin ana ta fama ko?” “Wallahi kuwa,in sha Allah in na sauka zan biyo nan gida na duba ki” sosai suka yi hira kafin su yi sallama. Daga inda take zaune ta fara kallon hotunan Bashir inda yake sanye da Kakin soja,nan ta lalace wurin kallonsu har sai da Munira ta shigo kiranta .Ta miƙe dakyar ta fita,a falo ta tarar da Goggo Hajara tun da ta fito ta lura idonta na kan cikinta.Ta sunne kai tana mai karanta ‘ Hasbunallahu wani'imal wakil ’ a can ƙasan zuciyarta,cikin nata ne ya soma yin motsi kamar zai fito mata ta cibiya.Tsabar yadda take jin ciwon juyinsa yasa ta kai hannu ta dafe ƙasan mararta tana mai fitar da nishin wahala,ido rufe ta ci gaba da sauraren azabar da ke ratsa duk sassan jikinta. Goggo Hajara ta yi wani makirin murmushi tana mai cewa “ Safeenat lafiya kuwa?” Sai a lokacin ta ware idonta da suka yi wani mugun ja,bakinta sam ba zai buɗu ba ballantana ta iya yin magana.Bayanta da ƙugunta suka ƙage lokaci guda wanda ya haifar mata duƙawa ba ta shirya ba,tuni idonta sun fara ganin dishi-dishi duk da wannan ne cikin farko tuni ta fahimci haihuwar ce ta zo bilhaƙi. Goggo Hajara ta ce “ Haihuwa ce kam,Munira fita waje bari na ɗauko leda ” “Mama in kira mai taxi ku wuce asibiti ko?” Munira ta faɗa tana kallon Safeenat wacce tuni ta fara wani gurnani mai haɗe da nishi. “Uwar mai taxi za ki kira ,fice na ce” Goggo Hajara ta faɗa tana mai shiga ɗakin Safeenat ta ɗauko robar da aka tanadi duk wasu kayan haihuwa. Da kanta ta shimfiɗa leda ta ɗora wasu zannuwa akai kafin ta ce “ Safeenat ki cire rigar nan mai haihuwa ina ruwanta da wata sutura” tsabar azabar da take ji yasa ba ta yi yunƙurin hana Goggo cire mata kayan ba. Yawun Goggo Hajara har wani dalala suke suna tsinkewa lokacin da ta ga kan ɗa ya sawo kai.Jikinta har rawa yake wurin taimakawa yaron ya fito ,babu wani jinkiri ko ɓata lokaci ta fara juya ido tare da soma kai wa kurwar jinjirin hari sai dai ba ta ida cin galaba ba nishin Safeenat haɗi da kukan wata babyn ya dawo da ita hayyacinta. Ƙirjin Goggo Hajara ne ya kusan ɓallewa zuciyarta ta faɗo tsabar firgici,jaririyar da faɗo cibinta a yanke yake sannan kuma babu marakiya saɓanin shi namijin da har yanzu take masa reto. Sai a lokacin ne ma ta samu zarrar yanke mahaifar,ba tare da kuma ta san dalilin kawar mata da mugun nufinta ba ta soma kimtsa Safeenat wacce babu laifi ta dawo hayyacinta. Goggo Hajara ta wanke kayan da kuma gyara ɗakin ta saka turaren wuta,ita ce kuma ta zaɓo wa Safeenat riga da zane.Har da haɗo mata tea mai zafi ta sha,gefe ta koma bayan ta gama komai tana tunanin zuci ‘ mi ya shiga kaina ni Hajara? Kamar ni kamar ba ni ce ba’ kukan jariran ne ya katse mata tunani ,ta ce “ ki ɗora su ga abincinsu” sai kuma miƙe ta soma nuna mata yadda za ta yi.Namijin kawai ya sha ita kuwa macen baya ga kuka babu abin da take,Goggo Hajara na ɗaukar ta sai kuma ta yi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba.Muƙut ta haɗiye wasu yawu hango wani baƙin kallo daga cikin ƙwayar jaririyar da ko minti talatin ba a yi ba da haihuwarta...... [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 22/09/24 3 Sannu a hankali Gwaggo Hajara ta soma jin wani sanyi na ratsa ɓargo da tsokarta,kamar wacce aka yi wa doli kuma ta ƙi kawar da dubanta daga cikin idon Babyn.Idonta suka soma kafewa saboda wata irin shaƙa da ta ji an yi wa wuyanta,babu shiri ta buɗe bakinta na maita kurwar jaririn da ta soma cin galaba kansa ta fara fitowa daga can cikin hanjinta tana fitowa ta bakinta .Wani koren hayaƙi ne ya soma shiga cikin jaririn wanda daga bakin Gwaggo Hajarar yake fitowa,wata irin atishewa ya soma yi kafin ya tsala kuka. Da mugun sauri ta yi baya ta zauna kan kujera,idonta na kan babyn wacce tuni ta soma bacci. “Gwaggo ya ƙi yin shiru ko cikinsa ke ciwo?” Safeenat ta faɗa kamar za ta yi kuka tana ririga yaron,ran Gwaggo Hajara ne yayi mugun ɓaci sai yanzu tunaninta ya dawo a tunzure ta ce “ uban mi zan yi masa to? Lokacin da na yi haihuwata uban wa ya kama min wurin rainon ? Ki riƙe abin ki” ta faɗa tare da ajiye mata babyn kusa da ita,jikin Safeenat sai yayi sanyi dakyar ta samu yayi shiru bacci ya ɗauke shi.Ta shimfiɗe shi kusa da Baby girl ɗin kafin ta je ɗakinta don ɗauko wayarta,tana dawowa sai ta hangi maciji kan jaririyar duk ya naɗe jikinta da shi ba ta san lokacin da ta saki wata ƙara ba wacce ta yi daidai da ɓacewar macijin.Safeenat ta zo da mugun sauri ta ɗauki yaranta ta mayar da su ɗakinta,sai da aka ɗauki lokaci kafin nutsuwarta ta dawo ta soma kiran mutane tana shaida musu zancen haihuwar.Hatta Daddy sai da ta kira shi ta sanar da shi,babu jimawa kuwa sai ga ƙanwarsa Habiba ta zo gidan sosai Safeenat ta ji daɗin ganinta musamman da ta ga har da ƙullin kayanta ta zo da alamu za ta jima. Ruwan zafi ta je ta ɗora cikin ƙatuwar tukunya kafin ta dawo,“ Safeenat ya zama doli ki kula da yaran nan musamman namijin don na ga shi ne mai rauni” Habiba ta faɗa tana shafar twins ɗin. “In sha Allah Gwaggo Habibah zan yi,da alamu ma ya fi kuka dakyar na samu yayi baccin nan” cewar Feenat. “Hum! Baccin wahala ne,ah to ai doli ma yayi Allah dai ya kyauta” “Amen!" Feenat ɗin ta amsa ba tare da ta san dalilin Gwaggo Habibah na faɗar haka ba.Bayan ruwan sun tafasa ta juye su ta yi wa yaran wankan,namijin ana saka shi a ruwa ya farka tare da canyara kuka amma ita hajiya babba har aka gama wankan tana bacci tamkar wacce ba ta rai.Gwaggo Habibah kuwa sai murmushi take tana jin wani farin ciki ƙasan ranta,dama ita Allah bai taɓa bata haihuwa ba . Safeenat ma sai da ta yi wanka da ruwan zafin ta gasa kanta da kyau ta fito ɗaure da towel,sai kuma yanzu ne Gwaggo Habibah ta lura da yadda fatar Safeenat ta yi ja.Da wani mugun sauri ta tashi ta cabke hannunta da ke ƙoƙarin ɗaukar kwalbar mai,“ jira na duba na gani” ta faɗa tana mai duba man ba tare da ta ce komai ba sai kuma ta fita direct ɗakin Gwaggo Hajara ta wuce ko sallama ba ta yi mata ba kuwa ta yi tsaye kai gare ta tana mai cewa “ an gaishe da uwar mugaye ta duniya,wato baƙar zuciyarki na nan daram babu canji .To asirinki ya tonu na ga bala'in da kika zuba cikin man shafawar Safeenatu,sai dai ki sani sai dai ki ci kanki amma Twins sun fi ƙarfinki ” Da wani mugun sauri Gwaggo Hajara ta tashi zaune,dama tun bayan da ta shigo ɗaki take jin duk jikinta babu daɗi dalilin kwancin da ta yi kenan sai kuma yanzu da ƙanwar mijinta ke feso mata kalaman rashin mutumci.Wani makirin murmushi ta yi kafin ta ce “ da alamu dai kin manta wace ce ni ko Habibah? Amma za ki gani” “Babu abin da zan gani sai alkhairi...” “Eh lalle wuyanki ya isa yanka” Gwaggo ta faɗa tana juya ido,Habibah ta tuntsire da dariya ta ce “au kin zata guntun tsafinki zai iya yin tasiri a kaina? To ki canza shawara tun wuri bai ƙure miki ba don yanzu daidai nake da ke” Ganin alamun tabbas ba Habibar da ce ke tsaye a gabanta ba yasa Gwaggo Hajara haƙura da surkullen,idonta masu cike da mugunta ta tsura mata ta ce “ mi ya kawo ki ɗakina?” “Ina so ki fita sabgar Safeenat da ƴaƴanta,in kuma ba haka ba....” sai kuma ta yi shiru tana cije baki haɗi da jinjina kai. “Ki tona min asiri? A tunaninki akwai wanda zai yarda? Hahaha! Yaro man kaza,Habibah kar ki manta hatta gyatumarki a tafin hannuna take....” ta yi saurin katse ta da “sai dai shi wanda kike tutiyar da shi mugun tsafinki bai yi tasiri kansa ba ,na san kin san haka” Ran Gwaggo Hajara ne ya ƙara yin baƙi,duk duniyar nan Habibah ce kawai ta zame mata ciwon ido duk yadda take son gudanar da lammuranta to muddin tana ga wuri sai ta roga su. Ƙarar buga ƙofa ce ta maido ta daga guntun tunanin da take,ta bi bayan Habibar da mugun kallo tana jin baƙin cikin da ba ta da MAITAR IDO (MRS SADAUKI,duk mai son complete book ɗin nan zai iya tuntuɓa ta kai tsaye ta lambar da na rubuta a can sama) da tabbas ta jefa wa Habibah ƙwayar cutar da za ta zama ajalinta. SAKEENATU Tana tashi daga aiki ta fito don samun adaidaitar da za ta kai ta can gidansu Safeenat kwatsam sai ga kiran wayar mijinta Abbas . “Mamuh ta ce yau ba ki bar mata abin da za ta ci ba ina son sanin dalili?” shi ne abin da ya fara cewa ko sallama babu,ran Sakeenatu ya ɓace amma ta haɗiye shi ta ce “ na samu ƴar aiki fa kuma kafin na fito na shaida mata kan ta girka mata abin da za ta ci” “Ƴar aiki za ta kula da uwata? Keenat mi ya shiga kan ki ne? Yanzu dai na baki minti goma ki tabbatar kin yi mata girkin abin da take so” yana gama faɗa ya yanke kiran. Tamkar za ta fashe haka take ji,mai ɗan sawu ma dakyar ta faɗa masa inda zai kaita.Tana shiga gidan ta tarar da Mamuh zaune kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani yamutsa fuska,gaban Sakeenatu ya faɗi kamar kullum muddin dai za su haɗa inuwa ɗaya da surukarta ta. “Barka da yamma Mamuh” ta faɗa murya na rawa,Mamuhn ta ce “ in kin gama yawon tanbaɗar sai ki shiga kitchen ki girka min wake da shinkafa” Idonta tab ƙwalla ta shiga kitchen ɗin ta ɗora tukunya ko kayan ba ta cire ba haka ta tsaya sai da ta tabbatar ta gama sannan ta zuba a plate ta kai wa Mamuh. Da zafi da komai ta saka hannunta tana ci mai na bin hannunta sai wani lumshe ido take alamun yana yi mata daɗi, Sakeenatu wacce ta tsaya don ganin ko yau ma Mamuh za ta yi irin yanayin nan sai kuwa ta ga ta yi.Idon Mamuh sai wani haske-haske suke fitar wa kamar kullum muddin dai wake da shinkafa ta girka mata. A tsorace ta nufi ɗakinta ,kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet.Shower ta sakar wa kanta,kamar abun almara haka ta soma jin yanayin jikinta na canzawa tana jin feeling wanda kuma abu ne mai wuyar faruwa da ita muddin dai ba Abbas ke a wurin ba. Abu kamar wasa amma sai yin gaba-gaba yake,kafin Sakeenatu ta farga tuni ta hankalinta ya soma gushewa ta dumulmiya duniyar son kasancewa da mijinta.Tamkar a mafarki ta soma jin kamar ana wasa da sassan jikinta,sai dai idonta sun yi nauyin da ba za ta iya buɗe su ba ballantana har ta ga shin zahiri ne ko kuwa? Sama da minti goma tana cikin wannan yanayi kafin ta dawo hayyacinta,a doli ta tsarkake jikinta ta fito tana mamakin al'amarin.Bayan ta shirya tsab cikin riga da zane sai ta fito falo,Mamuh ta gani sai sharar bacci take kamar matatta .Dining ta je ta zauna ta buɗe kulolin da ƴar aikinta ta yi girki,shinkafa ce da miyar kaji haka ta zuba ta soma ci tana mamakin yadda aka yi Mamuh ta zaɓi cin wake da shinkafa akan lafiyayen abincin nan .Bayan ta gama ta ɗauki waya ta kira Safeenat ta shaida mata za ta zo yanzu ,sai kuma ta koma ɗaki ta saka hijabinta ta ɗauko jaka ta fito.Tana fita ba ta wani wuya ba ta samu ɗan sawu ya kaita,da sallama ta shiga gidan har ta wuce can ɗakin da Safeenatu take wanda ya cika da mutane kusan dangin Bashir ne. A mutumce take gaishe da kowa amma yanayin jikinta na bata ana kallonta,tana juyawa suka haɗa ido da Habibah wacce ta kasa ɗauke idonta kan Sakeenatu har sai da ta ji ta tsargu.Ta zauna kusan Safeenat tana mai cewa “waccan wace ce sai kallona take?” “Ƙanwar Daddy ce fa ba ki gane ta ba?” Feenat ta faɗa tana mai miƙa mata boy bayan ta shafi kansa sai kuma ta ajiye shi aka miƙa mata girl ɗin.Wani irin shock ne ya ratsa Sakeenatu har sai da ta zabura,yayin da gabanta yayi mummunar faɗuwa ganin Babyn ta buɗe idonta tana kallon ta alhalin lokacin da aka miƙo mata ita tana bacci.Sakeenatu ba ta ida shiga tashin hankali ba sai da ta ga tamkar Babyn na yi mata murmushi...... [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 23/09/24 4-5 Wani irin abu ne marar misaltawa ke ratsa Sakeenatu tun daga kan babban yatsan ƙafarta har zuwa kwanyarta da ta soma toshe wa .Lamarin da take ji a al'aurarta kuwa kusan girme wa hankalinta ya yi,tamkar wacce ake fitar wa da wani dafi haka take jin ana yi mata motsi gami kuma da samun sassauci a doli ta lumshe ido ba ta shirya ba.Ita kuwa Gwaggo Habibah da ke can gefe sai murmushi take tare da yin zancen zuci don duk tana ankare da abin da ke faruwa.‘ Tabbas a duk inda ke da mugunta da cutar wa Allah sai ya kawo mai ceto mai magani,na zo kenan a gidan nan mutuwa kawai za ta fitar da ni zan saka ido sosai akan jaririyar nan zan raine ta da hannuna ta yadda zan taimaka mata wurin fahimtar baiwar da Allah ya yi mata da yadda za ta sarrafa ta’ sai kuma ta miƙe tana yin wani murmushin nasara.Babyn ta ɗauke daga cinyar Sakeenatu wacce gumi ya jiƙa ta har goshinta na ɗiga,babu kuma wanda hankalinsa ke wurin hatta ita Safeenat sai hira take da dangin mijinta waɗanda suke cewa shi namijin a saka masa suna Bashir a yi madadi. Sakeenatu ta ware idonta jikinta na ɗan rawa kamar wacce ta farka daga mummunan mafarki.Idonsu ya sarƙe cikin na juna,Gwaggo Habibah ta ce “ sannu! Bari na nemo miki ruwa masu sanyi” sai kuma ta shimfiɗe babyn wacce tuni ta koma baccinta. Kitchen ta nufa don samo ruwa masu sanyi,sai suka yi kiciɓis da Gwaggo Hajara ƴar kallon-kallon suka yi kowacce na hararen ƴar uwarta. “In tusa za ta iya hura wuta a yi mu gani mana,sai shegen kinibibi da nuna isa kan an san ɓoyayyar duniya nan kuma ba asss ” Gwaggo Hajara ta faɗa don kuwa a goshin Habibah ta fahimci sun karya wata muguntar tsafi. Ita kuwa Habibar murmushi ta yi don ta fahimci mi take nufi wato in ta isa ta yi wa kanta maganin damuwarta.“ Nan gishirinki zai ƙare a dafuwar ƙaho,yadda bacci ya bar ido haka za ki gaji ki bar Habibah saboda kabewar kan kabari nake baƙin cikin masu taushe” “Aikin banza sai aukin cika baki ,a hakan kuma na yi sanadin hana ki baccin kullum cikin kukan kin ƙi haihu ba” “Haihuwa ai ta Allah ce,kuma alhamdullah yanzu na samu irina wacce tsoron samun ta yasa kika jefo min mugun nufinki ” Habibah ta faɗa tana wani murmushi,Gwaggo Hajara ta kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ ko ba ki gane abin da nake nufi ba? To Safeenatu ta haifi wata Habibar sak irina ce ko na ce ma ta fi ni don ita murucin kan dutse ce ba ta fito ba sai da ta shirya” muƙut! Gwaggo Hajara ta haɗiye wasu yawun tsoro don kuwa ta fi kowa sanin babyn Safeenatu ba normal jaririya ce ba tun da ta ga zahiri. Ta ja wani irin numfashi jin saukar ruwan sanyi kan fuskarta,dakyar ta ware ido tana kallon Habibah wacce tuni ta juya ta yi tafiyarta tamkar ba ita ce ta gama zuba mata ruwan a fuska ba.Cike da baƙin ciki ta koma ɗakinta,a yadda take jin jininta ya hau in ba jini ta sha ba ƙila zuciyarta sai ta buga.Tukunyar tsafinta ta ɗauko ta yi ƴan surkullenta kafin ta ɗauki mayafi ta fita waje,yara ta gani suna wasa daga inda take a tsaye ta soma kiran kurwar wani yaro cike da ƙwarewa wurin maita tsafi.Yaron ya dafe gefen wuyansa inda ya ji kamar an tsikare shi da allura amma bai bar wasar ba haka yake ci gaba da gudun yana son kamo wani,idonsa ne suka soma rufe wa kafin bugun zuciyarsa ya tsaya cak kawai sai ya faɗi ga ƙasa.Ita kuwa Gwaggo Hajara da wani mugun sauri ta rufe ƙofa,tuni yara sun fara ihu suna faman kiran sunansa. Ɗakinta ta koma ta ci gaba da tsotse jinin yaron ko jira ba ta yi ba,don ta san sarai in ta jinkirta ajiye kurwarsa Habibah za ta iya fahimtar haka.Tsawon lokaci ta ɗauka cikin siffar mugunta kafin ta dawo normal,zuciyarta ta ji fayau babu ƙunci.Tana nan zaune sai ga Munira wacce rabon ta da gidan tun lokacin da aka ce ta fita.Kusa da mahaifiyarta ta zauna ta soma bata labarin yadda yaron maƙwabciyarsu ya faɗi suna tsaka da wasa,“ je ki nemo min Munir ya dawo gida ” shi ne kawai abin da ta ce tana jin wani daɗi a ranta ba don komai ba sai don ta yi mugunta. Habibah na shiga ta miƙa wa Sakeenatu gorar ruwa mai sanyi haka ta shanye su tasss tana sauke ajiyar zuciya.“Ki dinga kula da kan ki mana,ko barin kai a buɗe ai yana sa maƙiya su yi galaba kanka” “To in sha Allah ” Sakeenatu ta faɗa tana mai ɗan satar kallon jaririyar ƙawarta,ido ɗaya babyn ta buɗe ita ma tana kallonta babu shiri Sakeenatu ta miƙe tsaye tana cewa “ Feenat zan tafi sai kuma gobe in sha Allah zan zo da safe tun da babu aiki” “Na gode sosai Keenat wai ina Ma'idah?” “Tana wurin Mama tun wancan satin na kai ta kin san Komandan ta zo” Safeenat ta waro ido ta ce “ ki ce dai a takure kuke yanzu,kai tsohuwar nan an yi ƴar masifa mine ne na zuwa hutu ke ba ƴar makaranta ba” Sakeenatu ta tuntsire da dariya ta ce “ kar a yi babu ita mana,duk gani take wasu kuɗi ne da shi ba ta san rabin hidimar gidan ni ke yi ba a haka kuma za ta dinga tsiro da abubuwa tana saka sharaɗin abin da take so” Safeenatu ta ce “ ah lalle ta ci sunan Komandan ɗin” nan dai suka yi sallama Sakeenatu ta fito.Kafin ta isa gida sai da ta saya wa Mamuh kifi don ta san tana son shi,da sallama ta shiga amma ta ƙi amsa mata sai ma tambaya da ta jefo mata “ daga gidan uban wa kike? Wato kin matsu na koma ƙauye shi ne kika je gidan malamai da bokaye a yi min asiri na tafi ban shirya ba” Jikin Sakeenatu banda rawa babu abin da yake yi,kanta ƙasa ta soma rantse-rantse tare da sanar da ita inda ta je. “Ita ƙawar taki ce ta baki magani kika yi wanka da shi ta yadda zan ji tsoron ki? Sakeena lalacewar taki har takai ki dinga faɗawa ƙawarki ƙarya da gaskiya akan ta baki magani? In maganin za ki nema mi yasa ba ki ce a baki na haihuwa ba sai na korar maƙiyiyarki” “Wallahi Mamuh babu wani magani da aka bani,na faɗa miki barka kawai na je” Keenat ta faɗa cikin muryar kuka. Mamuh ta tsure ta da ido,sam babu tabon duk muguntar da ta ajiye a jikin Sakeenatun komai ya rushe ta koma normal.Sannan a baccinta aka nuna mata ta yi wanka da ruwan magani duk mugun nufinta ya fita daga jikinta,jin shiru yasa Sakeenatu ta ɗago ido da zumar kallon Mamuh mugun ganin da ta yi ne yasa zuciyarta kusan faso allon ƙirjinta ta faɗo. Idon Mamuh sak irin na maciji yanayin fuskarta ma ya canza duk ta yi baƙi,“ in kin gama gulmar sai ki wuce ki ɗora min wake da shinkafa” Mamuh ta faɗa tare da yin gaba,Sakeenatu ta ce “ akwai sauran na ɗazu bari na zubo miki ” Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ban so wani nake so ki dafa min” Jakarta ta ajiye ta shiga kitchen ta ɗora girkin,wannan karon ko waken ba ta wanke ba kamar yadda tsarin dafa shi ya zo mata daga Mamuh ɗin ,dama ita shinkafar ba irin wacce ake wankewa ce ba.Cikin plate ta zuba bayan ta tsalala mai dayawa,sai ta fito ta nufi ɗakin Mamuh da sallama ta shiga duk da ta san ba za ta amsa ba. Cike da ladabi ta duƙa har ƙasa ta miƙawa Mamuh plate ɗin wake da shinkafar amma ta ƙi karɓa sai ido da tsura mata.Tuni gaban Sakeenatu ya fara dukan uku-uku,“ ba zan ci ba!” “Amma ke kika ce na girka miki ” ta faɗa murya na rawa. “Tun zuwana gidan nan na faɗa miki sai an dirje wake an waken shi da hannu sannan ake girka min mi yasa yanzu ba ki yi ba?” “ Na zata kina jin yunwa ne sosai shi yasa na yi haka don na yi sauri” “To sai ki je ki sake dafa wani” Mamuh ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye,cikin dakiyar zuciya Sakeenatu ta ajiye plate ɗin ta ce “ ki yi haƙuri Mamuh akwai aikin da nake son yi yanzu,ki ci wannan ɗin gobe in Allah ya kai mu sai na yi miki irin wanda kike so ɗin” Sam ko kaɗan Mamuh ba ta yi mamakin furucinta ba ,don dama da tsafi ne ta ci galaba har Sakeenatun ke mugun tsoronta yanzu kuma komai ya karye.Ita kuma tana gama faɗar haka ta fice,da ta fito har sai da ta ja ajiyar zuciya tana mamakin yadda yau ta cire tsoron Mamuh. Tana shiga wanka sai ta ga period ɗinta ya zo,wanda kuma ba komai ya haifar da haka ba sai gwagwarmayar fitar da sihirin jikinta.Cikin ƙananan kaya ta shirya sannan ta haye bed tare da kiran Abbas,cike da nishaɗi suka yi hirar soyayya nan ne kuma ya shaida mata gobe zai zo sannan a karɓo Ma'idah don ita yake son fara cin karo.Har ƙasan ranta ta ji daɗin furucinsa , wannan yasa suna gamawa ta kira can gidansu ta ce a kawo mata Ma'idar. Washegari Kuwa tun safe Sakeenatu ta soma gyaran gida ita da ƴar aikinta wacce ba za ta wuce shekara ashirin ba mai suna Fa'iza.Mamuh dai na ta kallonsu ba ta ce komai ba don fushi take da Sakeenatu,da kanta ta yi girki Fa'iza na kama mata. “Shi kuma waken nawa sai yaushe za a girka?” Mamuh ta leƙo kitchen ɗin tana mai faɗar haka. Sakeenatu ta ce “ yanzu zan yi” ba ta ƙara cewa komai ba ta tafi. “Fa'iza wanke min waken nan da kyau sai ki girka wa Komandan ban son ta kawo min cikas ina cikin farin ciki” Ƴar dariya Fa'iza ta yi kafin ta soma wanke waken kamar mai wankin kaya,ita ce ta girka shi kuma.Sakeenatu ta zuba a plate da kanta ta kai wa Mamuh jikinta har rawa yake ta soma ci tana lumshe idonta waɗanda tuni suka soma yin hasken nan.Ita dai Sakeenatu Allah na gani tsoron yanayin nan take ,da sauri ta wuce ɗakinta ta yi wanka ta shirya cikin wani rantsatsen less tana tsaka da fesa turare Ma'idah ta shigo da gudunta ta na kiran Ammyna.Ita ma sosai ta yi kewar yarinyar sai ta rungume abarta tana cewa “ ke da wa ne?” “Anty” ta bata amsa. A ɗan firgice Nafisa ta shigo tana cewa “ anty Sakeena wace ce waccan a kitchen? Zo ki ga abin da take” “Ƴar aikina ce lafiya?” “Zo dai ki gani” cewar Nafisar tana mai yin gaba Sakeenatu na take mata baya har suka shiga kitchen ɗin. Fa'iza suka tarar duk ta cire suturar jikinta tana fitar da wani nishi idonta a rufe suna tsiyayar da hawaye....... [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 24/09/24 6-7 Tamkar wacce ke wata mu'amala da namiji haka Fa'iza ke yi ,hankalin Sakeenatu in yayi dubu to ya watse.Ta kalli ƙanwarta ta ce “ Nafisa ko iskokai ne? Dubi abin da take yi” Nafisa ta ce “ anty Sakeena tun da nake ban taɓa ganin mai kalar iskokan nan ba,hatta masu aljanin soyayya ai sai in suna bacci ne suke zuwar musu dubi ita wannan fa tamkar idonta biyu fa” “Yanzu dai don Allah ki taimaka mata tun da ke Malama ce kin ga Ma'idah har ta soma kuka” cewar Sakeenatu tana mai jan ƴarta zuwa waje.Nafisa ta cika kofi da ruwa ta tofa ayatul ƙursiyu da amanar rasulu sannan ta shiga watsa ma Fa'iza ruwan,a sannu a hankali ta soma barin abin da take daga ƙarshe ta buɗe idonta waɗanda suka kaɗa suka yi ja.Nafisa ta shiga yi mata sannu kafin ta taimaka mata ta mayar da kayan jikinta,“ dama kina da aljanu?” Sakeenatu ta tambaya wacce ta dawo. Fa'iza ta girgiza kai,“ to tashi ki yi wanka sai ki zo ki zuba abinci ki ci” Da “ toh” ta amsa kafin ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida kamar yadda Sakeenatu ta shaida mata da ita za ta dinga amfani. Wanka ta soma sai da ta saɓa jikinta har sau biyu sannan ta fito,wasu kayan Sakeenatu ta bata ta saka abincin ma da ta zuba gidansu ta wuce da shi. Su kuwa a falo suka zauna suna hira Nafisa na bai wa Ma'idah abinci a baki,Abbas yayi sallama da gudu ta nufe shi tana “ Daddyyy” ya caɓe ta tare da cira ta sama yana yi mata wasa haɗi da kai mata sumba. Cike da farin ciki ya ƙarasa ya zauna,Nafisa ta gaishe shi yayin da suke aikawa juna wani kallon so shi da Sakeenatu mai cike da kewa. “ Mu je ka fara yin wanka ko?” “A bani abinci tukuna don Allah ” ya faɗa yana wani murmushi,Ma'idah ta ce “ Daddy ni ma ina ci” sai aka zuba musu ya dinga bata a baki ita kuma sai surutu take yi masa.Suna tsaka da nishaɗinsu sai ga Mamuh ta fito,fuskar nan kicin-kicin,“ ita kuma wannan farar tinkiyar?” ta yi tambayar tana zunɗen Ma'idah wacce ta tsorata da ganin Mamuhn. “Ina wuni Mamuh? Fatan na same ku lafiya?” Abbas ya faɗa cike da ladabi. “Ka bani amsa ta” “Ma'idah ce fa ƴar wurin Keenat” ya bata amsa a sanyayye. “Shegiya za ka ce wacce ba a san taƙamaimai wane ne ubanta ba,kai da ka iya kwashe-kwashe ka rasa wacce za ka auro sai wadda ta gama yawon duniya ta tsiyayar da duk ƙwayaƙwayin haihuwarta a titi.To ban yarda ban lamunce wannan tinkiyar ta zauna a gidan nan ba” Mamuh ke faɗa cikin masifa ita kuwa Ma'idah tuni ta soma kuka musamman irin abin ban tsoron da take hangowa a fuskar Mamuh. Abbas ya sunne kai ya ce “ a dai yi haƙuri Mamuh dukkan bawa bai wuce jarabawa,Ma'idah ita yarinya ce ba ta san komai ba” “Wallahi sai ta bar gidan nan” Mamuh ta faɗa cikin ƙaraji, Sakeenatu kuwa banda kuka babu abin da take yi . Hannun Ma'idah ta kama da niyyar jawo ta,ita kuwa baiwar Allah cike da tsoro ta ɗauki cokali mai yatsu ta caka ma Mamuh ita a ido da zumar ceton kanta ga dodo. Wani uban ihu Mamuh ta yi tana cewa “wayyo idona! Ƴar daba ta kashe ni” jikin Abbas na rawa ya je ya kamo Mamuh wacce tuni idon ya soma fitar da jini,hankali tashe ya soma goge jinin wani na zubowa a doli ya kama ta zuwa asibiti. Bayan tafiyarsu ne Nafisa ta soma tofa ma Ma'idah addu'o'i saboda yadda take wani irin kuka tana firgita,cikin kuka Sakeenatu ta ce “ Nafisa ki ɗauke ta ku wuce gida don Allah” “Ke kuma a nan za ki zauna? ” “To ina zan je Nafisa? Haƙuri zan yi dama aure ya gaji haka sanin kan ki ne a can gidan ba wani jituwa muke ba ni da Mama ta ɗauki ƙiyayyar ɗan farin ta ɗora min” “To amma dai ki kula da kan ki,in kin ga abin ya yi yawa kawai ki tawo gida” Kuɗi ta basu sannan suka bar gidan,ita kuma ta ɗauki waya ta kira Abbas don jin asibitin da suke shi da Mamuh yana shaida mata ita ma ta fita ta je.Tuni Mamuhn ma ta yi bacci an naɗe idon nata da bandeji ga kuma ƙarin ruwa an saka mata. Jikinta a sanyayye ta ce “ ka yi haƙuri” Abbas ya kamo hannunta ya ce “ dama haka Allah ya tsara,ina Ma'idah?” “Nafisa ta koma da ita can gida” “Don me? Zan rarrashi Mamuh na san za ta amince ta zauna da mu” Ta sakar masa murmushi ta ce “ na gode sosai da kawaicinka gare ni” wani kallo yake aika mata yana mirza tafin hannunta,da ido ɗayan mai lafiya Mamuh ke kallonsu tana jin wani irin haushi da takaici. “Mine ne haka? A asibiti fa muke ka bari har mu koma gida” Sakeenatu ta faɗa tana janye jikinta daga nasa ganin abin zai wuce gona da iri. “Mu je gidan to tun da kin ga Mamuh ta samu bacci ,sai mu dawo daga baya” Abbas ya faɗa yana langwaɓar da kai saboda ba ƙaramar kewar ta yayi ba. “To ai na farka” cewar Mamuh tana mai tashi zaune haɗi da hararen Sakeenatu,da ɗan sauri ya miƙe yana tabayarta jiki.“ Ka kira likita ya cire min ƙarin ruwan nan sai mu wuce gidan tun da uwarka ba za ta barin ka cikin salama ba” cewar Mamuh a zafafe,Abbas ya fita don kiran likita. “Duk tsiyarki dai ba za ki iya canza ma tuwo suna ba,Abbasi ɗana ne ba naki ba don haka ni ke da iko da shi ba ke ba.Kuma wannan shegiyar taki sai ta san ni ta caka da cokali sai na shayar da ke mamaki” Da wani mugun sauri Sakeenatu ta je gaban Mamuh ta tsuguna ta ce “ don girman Allah Mamuh ki yi haƙuri , Ma'idah yarinya ce ba ta da wayo ko me za ki yi to ki yi min amma kar ki taɓa ƴata” ta ƙarashe maganar hawaye na zubo mata saboda zuwa yanzu ta yarda Mamuh muguwa ce. Kafin ta kai ga bata amsa Abbas ya shigo shi da likita,ya ce “ sai kin yi kwana uku sannan za mu sallamar ki” “To ka sanar da uwarmu wacce ta matsa mu je gida” Mamuh ta faɗa a zuciye tana hararen Sakeenatu. Likitan yayi murmushi ya ce “ yanzu yadda za a yi sai ka nemo wacce za ta zauna da Mama,amma gaskiya ba za mu sallame ta ba yau” sai yayi wa Mamuh allurar bacci,duk yadda masifa ke cin ta haka ta haƙura saboda ƙarfin allurar. Shi kuwa Abbas Gwaggonsa ya kira wacce ke nan Damagaram ita ke bi ma Mamuh,babu jimawa kuwa ta zo .Ya ja matarsa zuwa gida,cike da zallar soyayya suka gamsar da junansu. SAFEENATU Tun bayan da kowa ya watse aka bar su ita da Gwaggo Habibah sai ta nutsu sosai kafin ta ce “ Gwoggo ni kam ɗazu wani abin ban mamaki ya faru,maciji na gani ya naɗe Baby girl ɗin nan ina yin ihu ya ɓace kamar aljani ” Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ kar ki wani ji tsoro,sannan ina so ki kwantar da hankalinki duk wani abu da za ki gani ki yi shiru da bakinki.Duk kusan ƴan biyu suna da wannan baiwar,to ke macen ce ke da shi don haka ki shirya ganin abubuwa iri-iri wasu na tsoro wasu kuma na almara” Safeenat ta ja wani numfashi kafin ta ce “ to Allah cire min tsoron” ba ta ida rufe bakinta ba hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya turnuƙe shi kai ka ce dare ya tsala.Duk tsit suka yi babu wanda ya ce wani abu,sai kukan jaririyar da ya soma tashi sannu a hankali tsawon minti biyu kafin ta yi shiru.Hasken ɗakin na dawowa Safeenatu da Gwoggo Habibah suka yi ƴar rige-rigen ɗaukar babyn duk suka yi tsaye suna kallon yadda goshinta ke fitar da wani haske yana ƙyalli a gaban idonsu ya ɗauke sai ga shatun haƙoran maciji ya bayyana raɗau .Safeenat ta kai hannu ta shafi wurin sai kuma ya ɓace,ta ja ajiyar zuciya tana mai ɗaukar jaririyar ta soma shayar da ita. Daddy ya yi sallama ya shigo,duk suka gaishe shi kafin a basa babys ɗin ya gani.Sosai yayi musu addu'a sannan ya fita,haka suka ci gaba da yin hirarsu har dare ya tsala.Duk sun yi shirin bacci za su kwanta amma ita Baby kamar ɗiyar aljanu ta ƙi baccin sai ma wani kuka-kuka da take yi. “Safeenat ki bata abincinta mana” Gwaggo Habibah ta faɗa tana shirin tashi ta kunna wuta. “Ina ta ƙoƙarin bata ta ƙi karɓa” cewar Safeenar. Kusa da ita ta zauna tana shirin ɗaukar babyn sai ta lura da yadda hannunta na hagu ke fitar da wani zane mai hasken wuta kamar ta murhu.Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Gwaggo Habibah ba tare da ta shirya ba cike da murna ta jawo hannun jaririyar ta riƙe sannu a hankali har zanen ya fito raɗam letter M ta fito sai a lokacin kuma jaririyar ta yi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa. A ɗan ruɗe Safeenatu ta ce “Gwaggo mine ne kuma wannan?” Sam Gwoggo Habibah ba ta bata amsa ba sai safar hannu da ta je ta binciko cikin kayansu ta saka wa hannun mai zane.“Daga yau kar ki ƙara barin hannunta a buɗe ki dinga saka mata safar hannu ” “Gwaggo ina tambayar ki mine ne ba ki bani amsa ba” “Alama ce ta prophétie/prophecy,da yawan ƴan baiwa tana soma aiki ne in sun kai shekara sha takwas amma ke yarinyarki tun farkon dirowar ta duniya tata baiwar ta fara aiki.Ta ceci ɗan uwan tawaicinta sannan kuma ta ceci ƙawarki Sakeenatu ” Ba don ta fahimci zancen da kyau ba ta ce” mi ya samu Keenat ɗin?” “An yi mata ajiya cikin ruhinta ta yadda esprit zai samu damar yin yanda ya so da gangar jikinta har ya cutar da ita” “Ya aka yi kika sani to?” “Safeenatu yi bacci in lokacin fahimtarki yayi babu buƙatar ki yi tambaya” Da wannan duk suka yi bacci, Safeenatu na tsaka da yin mafarki akan goben ƴarta Gwaggo Habibah ta tashe ta daga bacci.“Ruwan wankan ki na can toilet ta tsakar gida,ki je yi wankan sabulu kafin na zo na gasa miki jikinki da towel” Ta yi miƙa ta tashi a gajiye saboda kwana dare ta yi tana shayarwa,sai da ta ɗauki wani zane da hijabi sannan ta fita ta bar Gwaggo Habibah za ta yi wa Twins wanka. Sakeenatu na fitowa suka yi kiciɓis da Gwoggo Hajara ta gaishe ta sannan ta wuce toilet.Ita kuwa tsabar mugunta yasa ta koma ɗakinta ta yo shirin mugunta yau ma siffar tsakaka ta ɗauka ta yi tsinke can toilet inda Safeenatu ke wanka tun tuni.Da ga can saman katanga Gwaggo Hajara ke ƙarewa surar Safeenat kallo,cikin salon mugunta ta mayar da harshenta dogo sannan ta zuro shi tun daga can sama har ƙasa yana taɓa tile. Safeenatu ta yi wani ihu wanda bai sauka ko ina ba sai cikin kunnen ƴarta jaririya,kwacaaaa Gwaggo Hajara ta faɗo cikin ƙatuwar robar tafasasshin ruwan zafi....... Ga masu son fara yin payment su yi min magana ta lambata na basu detail na sabon account number da za a tura kuɗin ba waccan na Ecobank ba.DM +22795045822 [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 25/09/24 8 Da wani mugun sauri Safeenatu ta yi tsalle ta koma jikin ƙofa tana kyarma ,idonta ƙur cikin robar wacce tsakakar ke ta ƙoƙarin fitowa daga ruwan .Ganin ta soma yin girma sosai yasa Safeenatu ta buɗe sakatar toilet ɗin zane a hannu ta fito Allah yayi sa'a babu kowa a tsakar gidan,dakyar ta yi ɗaurin ƙirji kafin ta nufi can ciki da gudu. “Ke lafiyar ki?” Gwaggo Habibah ta yi tambayar . Feenat ta dafe gefen zuciyarta da yake mugun bugawa ta ce “ tsaka...ka ce ta faɗa cikin ruwan da nake wanka” “Shi ne kike wannan haƙin? Kai Allah ya shirya min ke ban san lokacin da za ki girma ba” “Gwaggo ba normal tsakaka da kika sani ba ce, wannan ƙatuwa ce inda kin ga yadda halshenta ke da tsayi ya fi pampo fa” Shiru Gwaggo Habibah ta yi tana kallon Baby girl don kuwa a gaban idonta da tana yi mata wanka wani mugun haske ya fita goshinta tamkar an jefa kibiya. “Allah ni dai ba zan sake shiga toilet ɗin waje ba ƙila ma aljani ne” muryar Safeenatu ta katse mata ɗan guntun tunaninta. “Bari na je na gani ” cewar Gwoggo Habibah kafin ta miƙe ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida,tun kafin ta ƙarasa ciki take jin nishin wahala . Ido huɗu suka yi da Gwaggo Hajara wacce zuwa yanzu tuni ta galabaita ta yi wani tsamo-tsamo cikin ruwan zafin ta kasa fita . Gwaggo Habibah ta yi wani murmushi tana kallon yadda ruwan suka yi baƙi tsabar yadda muguntar da ta shiryo ma Safeenatu ba ƙarama ba ce. “Ƙarshen alawa ƙasa! Yanzu wa gari ya waya? Shi dama ramen mugunta an ce ka gina gajere in kuma ka gina dogo kai za ka faɗa .Ai wallahi ba zan taimaka miki ba sai dai ki dawwama a ruwan zafin nan,in kuma kin ga na taɓa robar nan to wallahi cikin masai ne zan zubar da ku ke da ruwan” Gwaggo Habibah ta faɗa tana wani murmushin jin daɗi. Kamar daga sama tsakaka ta soma magana wacce ta kasance Gwaggo Hajara ,“ ki taimaka min Habibah na yi miki alƙawarin daga yau na zubar da makaman yaƙi” “Kar ma ki zubar ki yi ta riƙon su har sai Mahadi ya bayyana,ba dai maita ita ce jarinki ba? Ki ci gaba da yi wata rana mutuwarki za ki ci” tana gama faɗar haka ta fito daga toilet ɗin,sai kuma ta tuna duk wanda ya mutu a ruwa yayi shahada da sauri ta koma ba tare da ta ce komai ba ta ɗauko robar ta fito da ita tsakar gida tare da juye ruwan ga ƙasa. Tamkar acid haka turɓayar ta soma yin bori tana fitar da kumfa tsabar bala'in da ke tattare da ruwan,a kunyace Gwoggo Hajara tsakaka ta soma jan ciki ta nufi hanyar ɗaki. Ita kuwa Gwaggo Habibah ji ta yi kamar ta sa ƙafa ta laɓe shegiya kowa ya huta.Tana komawa ciki ta cewa Safeenatu “Ki shiga toilet to kafin na juye ruwan yi miki wankan” sai kuma ta fita ta ciko ƙaton bokiti da ruwan zafi,da ɗan ƙaramin towel ta soma yi wa Safeenatu wankan jego ita kuma tana ihu kamar wata ƙaramar yarinya. Macijin jiya ne ya sake bayyana a jikin macen yana wani naɗe jikinta,ita kuma ta buɗe ido taram tana kallonsa kamar mai wayo.Tsawon lokaci ya ɗauka tare da ita yana yi mata wasa kafin ɓace jin motsin su Safeenatu za su fito.Gefen gado ta zauna ta soma shayar da yaran kafin ta kimtsa cikin riga da zane,sai da Gwaggo Habibah ta gama wanka ita ma ta fito ta shirya sannan ta je ta kawo masu abinci suka ci daga nan suka wuce asibiti bayan sun karɓi kuɗi wurin Daddy.Lafiyarta da ta babys aka duba kafin su dawo gida,tuni kuma ƴan Barka suka fara zuwa in waɗannan sun fita wasu sai su shigo. SAKEENATU Tana rungume jikin Abbas ta ce “ Yau tana ɗaya daga cikin ranakun ovulation ɗina,yau na gama period ” cikin tsokana ya ce “ period ɗin ɗaya rana ” ta ja hancinsa ta ce “ eh na dai ji,inda ina jimawa kafin ta ɗauke ai da yanzu ba ka kasance da ni ba don jiya ne na gan ta” Ya gyara mata kwanciya kan ƙirjin nasa yana mai cewa “ Keent don Allah ki dinga bin Mamuh a hankali kin san ta tsufa,ban so kina yin abin da zai ɓata ranta ki guji ɓata mata don farincikina.Ina yi miki wani mugun so ne wanda na san ke ko rabin shi ba ki yi min” “To in sha Allah na yi ma alƙawari zan kiyaye,ai Ma'idar ma an tafi da ita” “A'a za ta dawo,sanin kan ki ne yadda nake mugun sonta ba zan iya yin nesa da ita ba” Wani daɗi ne ya luluɓe zuciyar Sakeenatu,ita ce shaida kan son da yake yi wa ƴarta duk da ta fito ba ta hanyar aure ba.Za ta iya cewa halarcin bai nuna mata ƙyama ba ne ya ɗunguza ta ga aurensa,soyayyarsa ma ba ta jima da samun gurbi a zuciyarta ba. “Ina son ki Keenat!” furucinsa ya katse mata tunani,ta yi murmushi mai ɗan sauti ta ce “ na gode” “Ke ba za ki faɗa kina sona ba? Keenat sai yaushe zan ji furicin so daga bakinki?” Ta laƙace masa hanci ta ce “ sai ranar da na haifo ma kyakkyawan Prince mai kama da kai” sai kuma ta miƙe ta je ta shiga toilet,shower ta sakarwa kanta tana tunanin saurayinta mahaifin Ma'idah.Ruwan hawayenta haɗi da na pampo suka haɗu wuri ɗaya suna zuba.Daga bayanta ta ji an rungume ta,da sauri ta juyo suna fuskantar juna kallo guda yayi mata ya hango damuwa a shimfiɗe a ƙwayar idonta.Zuciyarsa kuma ta basa ta yi kuka,bai tsaya tambayar ta ba ya ɗora bakinsa kan nata a wannan rana a kuma daidai lokacin nan Abbas ya shayar da ita zumar ƙauna mai haɗe da yayafin kalaman soyayya masu nuni da sadaukarwa.Ba tare da ta shirya ba ta ce “ I love You Abbas!” numfashinsa ne ya kusan tsaya wa tsabar murna da farin ciki,kamar wani ƙaramin yaro ya soma yi mata kuka saboda kawai ta ce tana sonsa. Shi yayi musu wanka ya shirya su,a ranar a gida ya ja su sallah har ta isha'i .Bayan sun salamce sun yi dogayen addu'o'i ya dube ta da kyau ya ce “ Keenat fatan bayan tafiyata duk salloli kin yi su kan lokaci kuma kin tsare su?” Da sauri ta sunne kai ba tare da ta basa amsa ba,yatsun ƙafarta ya soma ja mata tare da soma yi mata nasihar da ya saba game da mai wasa da sallah a ƙarshe yake cewa “ in kuma na ga kin ƙi yi zan kawo miki ƙanwa ustaziya” a shagwaɓe ta faɗa jikinsa ta ce “ to ai ina yi ko” “Kina yi ko za ki dinga yi?” “Duka biyun! Ba za ka koma asibiti ba?” “Tare za mu koma tashi ki shirya” da “ to” ta amsa kafin ta canza kaya suka fito,sai da ya tsaya ya saya musu fruits sannan suka isa asibitin.Da sallama suka shiga ɗakin Gwaggo Rahamu ce ta amsa yayin da Mamuh ta juya musu baya tana jin wani irin baƙin ciki ya turnuƙe ta saboda a yadda ta gansu cikin farin ciki suna nishaɗi ta san sun keɓe da junansu.Abbas ya ƙarasa yana mai cewa “ Mamuh ya jikin naki?” “Ka damu da ni ne ka sa ƙafa ka yi tafiyar ka? Wato Abbasi matarka ta fi ni ko?” ta faɗa cike da masifa tana juyowa. “Ki yi haƙuri Mamuh Allah dai ya baki lafiya ” ya faɗa kansa ƙasa. Tsabar fitina ta Mamuh sai cewa ta yi “ ina wakena?” Abbas ya ɗago da sauri yana kallon ta yana mai cewa “ wane irin wake kuma Mamuh yanzu da daren nan? Ga ayaba nan da lemu da apple na sayo ” “Na yi da kai na ce ka sayo? Ita waccar abar ai ta san wake nake ci mi yasa ba ta dafo ba?” “Yi haƙuri Mamuh gobe sai a daf....” bai rufe baki ba Mamuh ta saka kuka yana cewa “ shinenan tun da mata ta fi uwa” Da mugun sauri Sakeenatu ta ce “ bari na koma gida sai na dafo mata” Abbas ya ce “ to ki yi sauri” ta yi tunanin shi zai kai ta amma sai kuɗin ɗan sawu ya bata,tana zaune tana hawaye har suka iso gida ta biya shi kuɗin kafin ta wuce ciki. A gaggauce ta soma aikin tana mita “ an yi tsohuwa kamar mayya kullum wake yanzu nan in ban wanke shi ba sai ta sani mtsww ” ta ja tsuki tana dirje waken amma jin ita ma an ja mata tsuki yasa ta zabura tana dube-dube sai dai babu kowa.Watsar da tunanin ta yi ta ci gaba da aikinta wani tsukin ta kuma ji sannan ana magana ƙus-ƙus,gabanta ya faɗi jin tamkar ana tafiya cikin falo.Tana shirin fitowa aka ɗauke wuta,lalubo ta soma yi cikin duhu ko Allah yasa ta ɗauko wayarta ta kuwa yi sa'a ta samu jakarta hannunta har rawa yake ta zuge zip ta ciro wayar sai ta ga saura ƙiris batirin ya mutu alhalin a cike ta bar ta.Tana ƙoƙarin ganin ta kunna fitilar ta ji tamkar saukar huci kusa da ita,ta wani juyo da sauri ta inda take jin abin tare da haska hasken screen babu kowa sai ƙafafuwan ƙofato da ta yi arba da su babu kuma gangar jiki....... My book is only 500 via 6042551755 Hassana ibrahim Keystone bank,DM +22795045822 [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 26/09/24 9 Babu shiri Sakeenatu ta saki wayar ta arta a guje,sai dai ta nemi ƙofar fita ta rasa saboda mugun duhun da ya mamaye gidan baki ɗaya.Cikin ƙanƙanan lokaci duk ta firgice,dakyar ta iya samu ta fito tsakar gida da lalabe zuciyarta sai ƙara tsananta gudu Waige-waige ta fara sai ta ga ashe kaf unguwar ne babu wuta,ba ta gama daidaita numfashinta ba wata baƙar mage baƙa ƙirin ta soma yin kuka miyau!miyau! Kukanta duk ya cika gidan. Ta ɗaga kai dakyar ta dubi inda sautin kukan ke fitowa,ido huɗu suka yi da magen wacce hasken idonta yake kamar na lantarki sai canza kaza suke.A hankali ta sauko daga katangar ta soma nufo inda Sakeenatu ke tsaye da gajiyayun ƙafafunta,Allah ya gani ba ta wani ba wai karatun addini muhimmanci ba dukkan lokacinta da hazaƙarta ta zuba su ne a harakar boko wannan ya sa ba ta iya wasu addu'o'i ba .A halin yanzu da take tsaye ta yarda kuma ta aminta rayuwarta na cikin haɗari,tabbas ta san wannan magen ba normal ba ce muguwa ce cutar da ita za ta yi. Ta na dab da ta kawo kusa da ita ta samu bakinta na furta “ la haula wala ƙuwata illa billah!!!” ƙiiii magen ta wani ci burki tana mai canza salon kuka zuwa na jarirai amma sam Sakeenatu ba ta yi gigin yin shiru da bakinta ba sai ma ƙaimi da ta fara wurin maimaita addu'ar.A gaban idonta magen ta soma mayar da idonta kamar na mutane kafin ta ruga a guje ta yi tsalle ɗaya ta haye katanga,daidai nan kuma aka maido wuta yaran unguwa suka hau ihun murna.Sakeenatu ta ja ajiyar zuciya tana mai yin hamdala ga Ubangiji,bakinta bai gushe ba yana ta furta lahaula wala ƙuwata illa billah a haka ta koma can ciki.Gas ɗin ta kashe saboda muguwar gajiya da ta saukar mata wacce ba ta san dalili ba,wayarta ta ɗauka Allah yayi sa'a babu abin da ya same ta abun mamaki kuma yanzu cajin wayar a cike yake saɓnin ɗazu da aka nuna mata ta kusa mutuwa. Lambar Nafisa ta kira,tana ɗauka babu wani tsaya wa gaisuwa ta ce “ Nafi ki turo min karatun nan da kike saurare don Allah duk dare” “Anty Sakeena lafiyar ki kuwa?” “Ki turo min karatun dai don Allah ina son saurare ” “Ok to bari na hauda data yanzu zan turo miki” “Yawwa ina jira” ta faɗa tare da kashe kiran,ita ma datar ta kunna babu jimawa kuwa karatun ya shigo suratul Baƙara ce ta turo mata sai Yasin .Tamkar abun tsiya network ɗin ya ɗauke ɗif ko ɗaya babu wanda ya buɗe,juyin duniya ta yi amma sun ƙi buɗewa har wayar ta kashe ta kunna amma network ɗin ya ƙi yi.Cike da damuwa ta sake kiran wayar ƙanwarta,tana ɗauka sai ta rasa abin da za ta ce mata kawai ta fashe da kuka.Daga can ɓangaren Nafisa ta ce “ subahanallah! Anty Sakeena don Allah mike faruwa? Mike damun ki?” Cikin muryar kuka take cewa “ Nafisa tsoro nake ji! A tsorace nake ji nake kamar ba ni ɗaya ba ce cikin gidan nan tamkar ina ....inaaa” ta kasa ida maganar saboda motsin da ta gani ana yi can cikin labule wanda ta tabbata kuma ba ɓera ne ba saboda girman halittar.Ihu ta fasa ganin ƙatuwar gafiya ta faɗo timmm da ƙasa,yayin da kuma wata ta biyu ita ma ta sake fitowa a guje ya kama waccan wacce ta faɗo a gaban idonta suka soma faɗa suna cizon junansu.Babu shiri Sakeenatu ta haye ɗaram kan bed ta na kuka,Nafisa na jin haka ta ziri hijabi ta fito ko Mamarsu ba ta sanar ma ba ta fito ta samu ɗan sahu.Allah yayi sa'a ba wani nisa ne sosai a tsakaninsu ba,da gudu ta shigo gidan tana ambaton sunan Allah daidai nan gafiyoyin suka yi ɓatan dabo hatta. Nafisa ta je ta rungume ƴar uwarta wacce da ace tana da cutar asuma da tuni numfashinta ya fita,“ yi shiru don Allah ya isa yi min bayanin mike faruwa? Ina shi Abbas ɗin?” “Yana asibiti wurin Mamuh,na dawo na dafa mata wake da shinkafa ne shi ne ake ta firgita ni” nan ta kwashe duk abin da ya faru ta shaida wa ƙanwarta. Nafisa ta ja dogon numfashi bayan ta saurare ta,sannan ta ce “ wannan duk sharrin miyagu ne shi yasa a kullum ake son bawa ya keɓe wani lokaci don nemawa kansa kariyar ruhi da gangar jiki ba wai gyaran duniyarka ba kawai.Ni wallahi na fara zargin Mamuh ɗin nan,kina dai ganin yadda Ma'idah ta caka mata cokali da dukkan alamu ta hango abin da idanunmu basu gani.In ba masifa ba cikin daren nan za ki dafa mata wake kamar mayya,ke ƙila ma ita ce.Tashi mu je ki yi alwala ai zama bai gan ki ba tun da kin ji kin gani aure a inda ba a ƙaunar ki” Da taimakon Nafisa ta yo alwala dama ita Nafisar kusan kowanne lokaci tana da alwala mace ce mai riƙo da addini ba ta da sake,hasali ma malamar makaranta ce a wata islamiyya. Karatun Alkur'ani ta soma koya wa Sakeenatu kamar wata ƴar yarinya haka take biyawa inda ta yi kuskure kuma ta gyara mata. “ Ki kasance kullum cikin tsarki bima'ana alwala saboda tana da muhimmanci sosai wurin bada kariya,ko sheɗanu suna shakkar mutum mai zama da alwala a koyaushe,ke ko period kike to ki yi abarki sannan ki riƙe azkhar na safe da maraice” “Amma ai kin san ban iya su ba ko?” “Ki koya mana anty Sakeena ,shi ilimi ai bai da ƙa'ida shekaru ko tsoho ɗan shekara ɗari zai iya shiga makaranta ballantana ke da ko talatin ba ki kai ba” “ Ni rubutun larabcin ne ke bani wuya ” “Zan nemo miki littafi mai fassarar Hausa ,sai na dinga koya miki yanzu bari na tura miki app ɗin Alkur'ani sai ki dinga saurare ” Ta karɓi wayarta ta tura mata tare da saita mata komai ta kunna sautin ya soma tashi,ta ce “ to ni zan tafi gida ko Mama ban sanar ma ba” “ Don Allah Nafisa kar ki tafi ki bar ni ki jira har Abbas ya dawo,bari na kira Mamar na shaida mata” haka suka yi kuwa,tun suna jiran Abbas har ƙarfe sha biyun dare bai zo ba a tare suka fito suka rufe gida da ko ina sannan suka je suka kwanta. A can asibiti kuwa bayan fitar Sakeenatu,Gwaggo Rahamu ta yi wani kishingiɗa ga kujera kamar mai bacci nan kuwa ruhinta ne ta soma fitar wa daga gangar jikinta.Sawun Sakeenatu ta bi,hasali ma ta rige ta zuwa gidan duk abin da take yi akan idonta hanyar farko da ta soma bi shi ne tafiya ta shiga tunanin mai kula da nepa na unguwar ya ɗauke wuta ba tare da shi kansa ya san dalili ba a cikin wannan duhun ne ta yi ta yi wa Sakeenatu mugunta.Da ta koro ta da addu'a shine ta biya wurin wasu miyagun ƙawayenta ta basu address suka je a siffar gafiya,su ma ba su bar gidan ba sai zuwan Nafisa. Abbas na daga can gefe Mamuh na yi masa hira tana murmushi saboda duk abin da ke faruwa ita tana gani saɓanin shi Abbas ɗin.Bayyanar esprits biyun yasa yanayin shaƙar iskan ɗakin ta sauya saboda tsabar muguntar su, wannan karon hatta Abbas sai da ya ji wani iri.Har yanzu Gwoggo Rahamu ba ta farka daga baccin ƙaryar da take ba,cikin hirarsu ta ƴan duniyar ɓoye suke bata labarin yadda suka firgita Sakeenatu tana ta yin kuka. “Na gode sosai ƙawayena,kar ku manta in kun gama yawon Maitar dare ku biyo ta nan mu sake komawa mu uku mu haɗa ƙarfi mu shayar da ita mamaki” baƙin ruhin Gwaggo Rahamu ya faɗa ,suka yi dariyar mugunta tare da ɗaukar mata alƙawari kafin su bar wurin.Cikin ƙwarewa ta dawo da ruhinta a gangar jikinta,ta dubi Abbas tana mai cewa “ bacci ya ɗauke ni duk yau ban rintsa ba,ina sauran waken ni ma na ci yunwa nake ji” Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun ɓaci,“ uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani ƙato ya taushe kar ki yi gardama” Mamuh ta faɗa ,yayin da Gwaggo ta karɓe “ i sosai ita ma wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya ɗirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai Abbasi wai ya ƙaƙaba maka aurenta?” Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da zuciyar namiji sai ya ji zargi ya ɗarsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaɓa ma Sakeenatu sosai kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu shaidar ƙwarai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita . Ƙarfe biyu da rabi na dare ƙawayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ƙofar falon sai dai da zarar sun yi niyyar ɗora ƙafarsu a tile ɗin bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke ɗora su.Gwaggo Rahamu ta ƙanƙance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta ɗora wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ƙara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido My book is only 500 via 6042551755 Hassana ibrahim Keystone bank DM +22795045822 [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 28/09/24 10 A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa ɗakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta ƙurma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa ɗakinta ta ɗauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta ɗauko ta shafe jikinta da shi tana matsar ƙwalla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ƙasan zuciyarta. A fili ta furta “ sai na wulaƙanta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki ba zan ɗora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin ruguje plan ɗina” shiru ta yi jin an turo ƙofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluɓe jikinta. “Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ƙullun wainar da ya ji yis?” Daddy ya faɗa yana ƙare mata kallo.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya ƙara turnuƙe Hajara ta ce “ uwar waina ce....” ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani baƙin tauraro tsakiyar goshinsa wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi. Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa,“ wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta koma da baƙin cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki ɗora girki tsabar lalaci muna da mai jego a gida amma kin zo kin shige ɗaki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman kowacce za ta yi aikin ƙwarai” yana gama faɗa ya nufi ƙofa,sai kuma ya juyo ya ce “ Murjanatu na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta” kawai ya fice. Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer ɗin tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi. Duk abin da yake faɗa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki murmushin nasara tana mai cewa ‘ mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar zuciyarki’ “Habibah karɓi wannan ko kuna da buƙatar wani abu sai a ɗauka ciki” Daddy ya faɗa yana mai katse mata tunanin zuci.Ta karɓa tana mai cewa “ Yaya Ɗayyabu na ce bayan biki sai Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?” “Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?” “Eh to ni ma da haka na ce ɗin amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na zo idonta kamar za su faɗo tsabar yadda take jifana da mugun kallo” Ran daɗi ya ɓace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ƙara yin baƙi ba tare da ya ce komai ba ya ƙara komawa ɗakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna. Daddy na shiga ɗaki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaɓe bakin.Da wannan baƙin cikin ya fita ya bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta ɗora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo .A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi mata irin wannan ladabin tun ranar da Ɗayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa “ to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji” Hajiya ta faɗa tana murmushi a doli ita ma ta yi murmushin yaƙen a can ƙasar zuciyarta tana cewa ‘ an haifo mana masifa dai aljanar jaririya muguwa wacce ta yi gadon jaraba ’ “Zan shiga daga ciki” hajiyar ta faɗa tare da nufar ɗakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana kallon jariran Gwaggo Habibah ta ɗauki namijin ta bai wa Hajiya ta karɓa tana mai kai masa sumba haɗi da yi masa addu'a sannan ta miƙa shi.Ana ɗora mata macen jikin Hajiya ya ɗau kyarma kamar mazari,murya na ɗan rawa ta ce “ wane suna za a saka musu?” “Basheer da Baseerat ” Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu kuma ya fara barazanar tarwatsewa. Hajiya ta ce “ karɓar ta” tana mai miƙo Baseerat don ruhinta ya soma yin rauni, Habibah ta ce “ Hajiya don Allah ki riƙe t...” ba ta kai ƙarshe ba Hajiya ta miƙe ta je ta shimfiɗe Baseerat a shimfiɗa,sai aka yi rashin sa'a safar da aka saka ma hannunta na hagu ta fita wani mugun haske ya fito ya shiga ƙirjin Hajiya saura ƙiris ta faɗi saboda yadda fitilun idonta suka rufe jiri kuma ya ɗebe ta. Safeenatu dai na daga gefe tana kallon abubuwan ban al'ajabi , Gwaggo Habibah ce ta kamo Hajiya ta taimaka mata ta zauna.Kamar mai cutar huka haka numfashinta ke fita,ruwan sanyi ta nema da sauri aka bata ta shanye ƙatuwar gora. “Habibah bani pilow bacci nake ji” cewar Hajiya ,da sauri ta ɗauko ta miƙa mata ita kuma ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta . Safeenatu ta ce “ Gwaggo Habibah ni fa na fara jin tsoron lamarin Baseerat kina dai ganin abin da ya faru, wannan ai ba zan fita da ita unguwa ba gudun ta jawo min masifa ace mayya ce ma” Da mugun sauri Habibah ta katse ta “ kar na sake jin kin faɗi haka,saboda ƴarki ba mayya ce ba ƴar baiwa ce” “To amma ai wasu ba za su ganin haka ba ko? Tun yanzu tana jaririya tana haka ina ga ta girma?” Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ Safeenatu bari dai na soma ɗan guntsira miki labaran duniyar ɓoye, kowane mutum da kike gani a duniyar nan yana da matriculation na sama.Ko kuma lambar sirri ta samaniya,da wannan ne in aka sayar da ruhin mutum daga lokacin matriculation ɗinsa ta saminiya sai ta canza.Duk wani ɗan Adam kasance yana da taurari iri-iri waɗanda suke taimakawa wurin gudanar da al'ammuran duniyarsa.Ya zama doli kowa ya kare taurarinsa ya basu tsaro,muddin ka yi sakaci da su kuma to wannan mutumin zai iya zama cikkaken maƙasudi wurin tallafawa masu sayar da taurari su ƙwace masa su.” Safeenatu ta katse ta da cewa “ ta ya za a ƙwacewa mutum taurarinsa alhalin mallakinsa ne?” Gwaggo Habibah ta bata amsa da “ ba ki taɓa jin labarin wata ma'aikaciyar saloon ba mai gyaran gashi? Ki nemi littafin Mrs Sadauki na MAITAR IDO a nan duk za ki samu cikakken labarin.Ki sani cewa matsafa don su kama ruhinka ma abu ne mai sauƙi,abin da suke buƙata shi ne kawai keɓaɓen abu na gaskiya ta atomatik da ke fitowa daga mutumin da ake son cutarwar,kamar gashinsa,sunansa,date ɗin ranar haihuwarsa,zufar jikinsa wato tufafin da ya saka ba a wanke ba,ko kuma jinin jikinsa.Daga lokacin da matsafi ya riƙe ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya buɗe katinka na samaniya kuma ya karɓe ƙarfin ikonka wato power daga nan sai yayi abin da yake so” A sanyayye Safeenatu ta ce “ duk Baseerat za ta iya yin wannan? Gaskiya ni dai ban so in kin san hanyar da za a toshe wannan baiwar tata ni dai ki taimaka min don ina ji a jikina muddin aka bar ta da ita a gaba za ta zame mana masifa” Gwaggo Habibah ta yi mata wani irin kallo irin na ba ki da hankali kafin ta je ta ɗauki safar hannun ta saka ma jaririyar wacce ta buɗe ido sai kalle-kalle take kamar mai wayo,kafin kuma ta kafe idonta ga madubi Gwaggo Habibah ta yi kasaƙe tana kallon Baseerat a sannu a hankali ta ga idon yarinyar na sauya kala har suka zama farare tasss babu ɗigon baƙi,wani abu kuma ya soma fita daga bakinta yana bin direction ɗin madubi.Habibah ta ja wani dogon numfashi don kuwa ta fahimci Baseerat za ta yi tafiya ne ko kuma yawon buɗa ido wanda dayawan mutane na yinsa ba tare da sun san mine ne ba.Sai ka ji tamkar jikinka ya zama gawa kana son tashi daga bacci amma ka kasa tamkar an danne ka da dutse,har kwatanta buɗe ido ake amma baka iyawa saboda ruhinka da yayi balaguro ya bar gangar jikinka a kwance. #SAKEENATU Gefen da Nafisa ke ta sharar bacci ta duba kafin ta ɗaga kanta sama tana kallon yadda rufin ɗakinta ke wani lomaƙawa tsabar yadda ake tafiya a guje.Kukan jaki da na kare ga kuma na mage duk a lokaci guda,gefe guda kuma wata siririyar murya take ji tana kiran sunanta.Idonta ya ciko da hawaye,fitsari take ji amma tsoro ya hana ta tashi.Nafisa ta soma tayar wa,ita kuwa dakyar ta buɗe ido ta ce “ mine ne ?” “Fitsari nake ji” ta bata amsa kamar wata ƙaramar yarinya,cikin magagin bacci Nafisa ta ce “ ki je ki yi mana” sai ta koma baccinta.A hankali Sakeenatu ta zuro ƙafafunta ƙasa a tsorace ta shiga toilet ko Bismillah ba ta yi ba ballantana karanto addu'a,a tsorace ta je ta haye WC ɗin ta soma fitsari sai kuma jikin ya soma kyarma ganin ruwa na ta ɓulɓulowa ta ƙasan tile suna cika toilet ɗin ko kafin ta ƙyafta ido sun kawo mata a wuya ta yunƙura za ta tashi amma sai ta ji tamkar an saka super glue an manna ta a jikin WC ɗin ta ƙurma wani uban ihu wanda dama su mugayen shine suke jira ai kuwa suka tsaga rufin ɗakin ji kake ƙiiiiii kamar suna yaga zane.Idon Sakeenatu duk a waje take kallon yadda bindi mage,na kare da kuma idon wata baƙar mujiya a daidai wurin da suka tsaka.Cike da mugunta suka diro toilet ɗin wanda yayi daidai da tsinkewar numfashin Sakeenatu..... My book is only 500 via 6042551755 Hassana Ibrahim Keystone bank DM +22795045822 💛💛💛GHT B-CLEAR,FEMALE CARE AND GANODERMA💛💛💛 💛💛*BACK TO VIRGIN KIT* *(SABON BUDURCI)* 💛💛Assalam alaikum Mata albishirin ku🧏‍♀️🧏‍♀️ga abin da kuka Dade Kuna mafarkin samu ya samu💃🥰 💛💛Abin nema ya samu ,Kowacce mace aduniya tana mafarkin sake kasancewa virgin 💛💛Ina manyan Mata da suka hayayyafa😁 💛💛ina zawarawa masu shirin aure😍 💛💛Ina budurwa da iftila'i ya fadawa a yayin tsallaka rame 😢 💛💛Ina Mai jego da keso ta dinke ta game tsaf ciki da waje❤️ 💛💛Duk ku marmatso kusa ga GHT back to virgin set na kawo muku ,magunguna ne namu na gargajiya bana bature ba 💛💛Kuma Sha akeyi ,insha Allahu muddin kikayi amfani da wannan Kayan Zaki dawo da martabar ki ta farko 💛💛Sai kin gwada za ki tabbatar da hakan. Sisters no 08142506271 mmn Khadeejah sai najiku [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 29/09/24 11 💛💛💛GHT B-CLEAR,FEMALE CARE AND GANODERMA💛💛💛 💛💛*BACK TO VIRGIN KIT* *(SABON BUDURCI)* 💛💛Assalam alaikum Mata albishirin ku🧏‍♀️🧏‍♀️ga abin da kuka Dade Kuna mafarkin samu ya samu💃🥰 💛💛Abin nema ya samu ,Kowacce mace aduniya tana mafarkin sake kasancewa virgin 💛💛Ina manyan Mata da suka hayayyafa😁 💛💛ina zawarawa masu shirin aure😍 💛💛Ina budurwa da iftila'i ya fadawa a yayin tsallaka rame 😢 💛💛Ina Mai jego da keso ta dinke ta game tsaf ciki da waje❤️💛💛Duk ku marmatso kusa ga GHT back to virgin set na kawo muku ,magunguna ne namu na gargajiya bana bature ba💛💛Kuma Sha akeyi ,insha Allahu muddin kikayi amfani da wannan Kayan Zaki dawo da martabar ki ta farko 💛💛Sai kin gwada za ki tabbatar da hakan. Sisters no 08142506271 mmn Khadeejah sai najiku Duk da Sakeenatu ta suma hakan bai sa mugayen nan sun ƙyale ta ba,haka suka ajiye mata cutar a jikinta kafin su bar ta nan yashe a toilet.Cike da murna suka koma asibiti suka dinga bai wa Mamuh labarin abin da ya faru,cike da mugunta ta ce “ gobe da safe da hannunta za ta dafo wake ta kawo min ,daga nan kuma zan datse alaƙar farin cikinsu ita da Abbas zan maye mata gurbinsa ” duk suka sa dariya suna ƙara tsara mata wani salon muguntar. Washegari Kiran sallar asuba ya tashe da Nafisa,ta sauka daga bed ta shiga toilet nan ta ci karo da Sakeenatu a yashe babu numfashi.Hankalinta a tashe ta cika bokiti da ruwa ta zuba mata,ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta soma kuka cikin firgici.Nafisa ta kamo ta tare da fiddo ta haɗi da tambayar ta,duk a tsorace take wannan yasa ta kasa yi wa ƙanwarta bayani.Ganin haka yasa ita kuma ta je ta yo alwala ta yi sallah,bayan haka ne ta matsa wa Sakeenatu ta je ita ma ta yi sallar.Ko wanka ba su yi ba ta ce “ Nafisa tashi mu je gida wallahi tsoro nake ji” haka suka runguɗa suka je can gidan Mama wacce ke ta ƙoƙarin hura wuta domin ta ɗora ɗumame,tana ganinsu ta san ba ƙalau ba.Kamar wata ƴar yarinya haka ta je ta rungume mahaifiyarta tana wani sabon kukan,“ Subahanallahi! Nafisa mike faruwa?” “Wallahi Mama ban sani ba ni ma na yi ta tambayar ta amma ta ƙi faɗa min,alamu dai sun nuna tsorata ta ake yi a can gidan nata” Nafisa ta bata amsa. Mama ta ce “ to Allah ya sawwaƙa,ku wuce ciki bari na kira malam na shaida masa ” Can cikin mitsitsin ɗakinsu suka shiga,Ma'idah na kwance sai bacci take ba ta farka ba.Sakeenatu ta ɗauki abarta ta rungume ƙam kamar an ce za a raba su,mugun mafarkin da ta yi kan Ma'idar ya dawo mata a kai.Ta lumshe ido ruwan hawaye na kwaranya a kumatunta,ta yi tunanin kakarta ta yanke saƙa,ba ta taɓa tunanin za ta sake yin ƙunci a rayuwa bayan wanda ta yi a baya ba tun lokacin da Abbas ya shigo rayuwarta komai ya dawo mata normal ashe da sauran kallo a sama.Tsohuwar shuɗaɗiyar rayuwarta ce kwanyarta ta soma yi mata tariya,cikakken sunanta shi ne Sakeenatu Abubakar,ƴar gwagwarmayar rayuwa mai zuciya cike da burin zama wata aba a duniya.Karatun boko shi ne abokin da ta riƙa sannan kuma tubali don gina rayuwa mai inganci,sai dai ƴan magana na cewa rashin sanin ya fi dare duhu.Sakeenatu ba ta taɓa sanin cewa ba sanadin boko ne za ta zubar da mutuncinta ba,zuwanta jami'a shi ya ƙara buɗe mata ido sosai ta waye ta zama ƴar gayu,ƙwazonta a wurin karatu shi yasa ta ciri tuta a wurin malaman makaranta kusan duk maganarta suke suna yabon baiwar da Allah yayi mata banda malam Agali wanda tun ranar da ya ɗora idonsa kanta yake jin mugun sha'awarta saboda ta haɗu ta kowanne fanni.A wata rana Laraba ce wacce ta kasance ranar farko da ya fara ɗana mata tarko da kuɗi,“ki hau taxi” ya faɗa cikin taushin murya a gaban ɗalibai ba tare da ya ɓoye ba kuma ya sakar mata murmushin nan nasa wanda yake haukata ƴan matan makaranta da na wajensu .Ba za ta cewa tana sonsa ba,amma ita ma tana cikin waɗanda yake burge su saboda yadda yake da kyau kamar Balarabe ga baƙar sumar kansa ko wata macen ya fi sannan ɗan gayu ne kullum cikin shiri mai kyau yake.Ƴan matan ajin suka hau yin shewa suna taɓi tare da cewa yau dai an samu wacce ta sace zuciyar Dr Agali,da ido ta bisa kawai lokacin da yake fita daga ajin yayin da ɗalibai duk suka dawo kusa da ita kowacce na tofa albarkacin bakinta.Sakeenatu ta ji wani irin girman kai ya zo mata tare da alfaharin ita ce ta ciri tuta,cours ɗin da aka yi musu na gaba sam ba ta fahimci komai ba saboda tunanin malam Dr Agali.Ba ta buɗe ƴar enveloppe ɗin kuɗin ba sai da ta je gida, kuɗi ne ƴan jika-jika sabbi da su har guda goma.Ta kai su kusan hancinta ta shaƙi ƙamshin turarensa,tuni jikinta ya mutu murus ta na shirin saka kuɗin a jaka ne ta lura ɗaya daga cikin takardun kuɗin an rubuta lamba a jiki.Kamar wacce ake tsikara ta ɗauki wayarta ta loda lambar sannan cike da waswasi ta tura masa saƙo babu jimawa ya kira ta,kamar wani mutumin ƙwarai har da yi mata sallama ta amsa tare da ce masa “ fatan ka je gida lafiya?” Cikin muryar nan tasa ta buzaye waɗanda ba su ida iya Hausa ba ya amsa mata da “ a'a ina wata asibiti an kira ni in tiyata” Ta saki murmushi mai sauti ta ce “ ina son ganin ranar da za a ce Sakeenatu na yin tiyata” “Lokacin zai zo ke dai ki ci gaba da dagewa wurin yin karatu,na ji malamai sai yabon ki suke ashe ba a cours ɗina ne ba kawai kika ƙware” nan ma murmushi mai sautin ta yi kafin ta ce “ burina shine zama babbar likita wacce duk duniya za ta yi alfahari da ita,ana dinga nuno ni a TV” “Kina iya barin Nijar Keenat?” Dr Agali ya tambaye ta,kai tsaye ta basa amsa da “ eh sosai sai in gwamnati bai ɗauki nauyin karatun nawa ba” “To ki fara shiri in sha Allah ni nan zan sa burinki ya cika” “Keee Sakeenatu keee!” Mama ta faɗa tana mai kamata dundu wanda shi ya katse mata tunanin shuɗaɗiyar rayuwarta,da sauri ta dawo hayyacinta tana mai kallon Mama wacce ta janye Ma'idah da sauri tana mai ci gaba da cewa “ kawai ki kama yarinya ki riƙe gam tana kuka da ranta amma kin ƙi sakin ta” Sam ita ba ta san riƙon da ta yi wa Ma'idar ya cutar da ita ba,cike da takaici da zugin da zuciyarta take yi ta tashi ta fita ta cika bokiti da ruwan ta shiga banɗaki.Wanka take son yi amma tunanin Dr Agali sai ƙara kawowa kwanyarta farmaki yake,abin da ya faɗo mata a rai a yanzu kuma shi ne ranar da ya kira ta ya shaida mata Visa ɗinta ta fito ta zo ta karɓa bai jin daɗin jikinsa.Ba tare da wani tunani ba ta je gidan nasa kamar yadda yayi mata kwatance,duk a tunaninta yana da mata amma sai da suka shiga ciki ne ta ga shi ya bata ruwa sannan ya kawo mata lemu wanda ya zubar da shi a jikinta da gayya har tufafinta suka ɓace.Ta wani rumtse ido don takaicin ganin video yadda Dr Agali ya ɓalle maɓallan rigarta ya cire ta ya bar ta daga ita sai bra ya je wanke mata ita duk ta yi tunanin ƙauna ce ta kawo haka sai bayan ya dawo ne ya soma yi mata wasu zafafan romance.“ Ni fa dama ba zan yi miki komai ba, wannan ɗin ma ban san ya aka yi ya faru ba ki yi haƙuri ba zan sake ba sai bayan aure” Dr Agali ya faɗa lokacin da ta sakar masa kuka. “Anty Sakeena don Allah ki aje tunanin nan gefe ki yi wanka ki fito ga malam nan ya zo” Nafisa ta faɗa daga bakin ƙofa.Sai a lokacin Sakeenatu ta fara wankan ,bayan ta fito ta je ta gaishe da malam wanda ya kasance ƙanen Mama ne.Cikin garwashin wuta ya zuba ƴaƴan habbatu sauda hayaƙi ya turniƙe ɗakin,idon Sakeenatu duk suka fito waje ta soma tari kamar ranta zai fita shi kuwa karatu ya soma nan lamarin ya ƙara yin gaba don tuni ta soma yin kuka .Tsawon lokaci kafin ya bar ta haka nan,magani ya bada wanda za ta dinga shafawa da hayaƙe jikinta da kuma gidan.Bayan tafiyarsa ne ta samu ta ci abinci,wunin ranar dai Mama haka ta ƙare shi wurin yi mata nasiha dab da magrib Nafisa ta yi mata rakiya zuwa gidanta.A tare suka yi gyaran gidan da girki kafin ta yi wanka ta shafa man da malam ya bata ta kuma yi turare. A can asibiti kuwa tun safe da Abbas ya bar su bai koma ba,kuɗi kawai ya bar musu hakan bai yi wa Mamuh daɗi ba.Ana yin sallar magrib ba tare da likita ya sallame ta ba Gwaggo Rahamu ta haɗa tarkacensu suka fito a ɓoye.A bakin hanya suka samu adaidaita wacce za ta kawo su gida ,suna tafe suna hira “ ai tun da kika ga bai dawo ba to tabbas babu makawa da ya koma gida karuwanci ta yi masa kin san halin namiji kan mace sakarai yake zama” Gwaggo Rahamu ta faɗa . Mamuh ta tsuke bakin nan nata ta kasa cewa komai saboda baƙin cikin da ke addabar baƙin ruhinta,gani take yi ma tamkar adaidaitar ba ta gudu. Suna isa gida tun a bakin ƙofa suka canza kalar idonsu daga na mutum zuwa na mugunta,sai aka yi rashin sa'a Nafisa na tsakiyar falo tana hayaƙa hantiti da tazargade .A tare suka shigo,a tare kuma suka saki ihun azaba suna masu faɗuwa ƙasa suna yin wani irin huci a gaban idon Nafisa suka rikiɗe suka zama jibga-jibgan macizai kowa yace shi ba ma matsoraci ne ba to bai ga abin tsoron ba .Da wani mugun sauri Nafisa ta mangal ɗin hannunta mai cike da garwashi,da azama ta nufi hanyar ɗakin Sakeenatu sai dai kafin ta isa Gwaggo Rahamu ta yi wani uban tsalle ta naɗe handle ɗin ƙofar da bindinta tana mai buɗe ƙaton bakin,Nafisa na shirin komawa baya ta ji ana bin ƙafafunta wanda kuma tunaninta da ruhinta tuni sun shaida macijiya Mamuh ce...... My book is only 500 via 6042551755 Hassana ibrahim Keystone bank DM +22795045822 ASSALAMU ALAIKUM Mata masu abun dadi *Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa 🗣️🗣️🗣️😁🎁💃🏽💃🏽 Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 5500 na 1. Kaza rabi 2. Ciccibi 3. Gumba 2 4. Gari 1 5. Tsimi 2 sunada kyauta abubuwa kamar haka 1.Matsin ba a Fira da wando sa mai gida kukan dadi 1k 2. Matsin maganin infection 300 3. Dripping pills 1pcs 300 4. Matsin dare daya wanka goma 400 Total total gift 2k 😁 Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 5500 dinki ki mallaki kayan da ko 10k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah *08144015291* Maman yasmeen takuce 😍 Wa.me/+2348144015291 For more information say hi 👋 Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku💃💃💃 muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu *DAHUWAR KAZA* Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya* Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta 🎁 mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya* *INA MASU JEGO DA AMARE* Karku bari wannan dama ta wuceku *08144015291* Zuzeam empire ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1000 kacal 👌🏽 Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd Maganin karin kiba Maganin nono da hips Rage tunbi da kiba Infection set Sabon budurci set Niima set Basir set Matsi mallaka Amarya set Uwar gıda set Mai jego set Dadai sauransu [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 30/09/24 12 ASSALAMU ALAIKUM Mata masu abun dadi *Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa 🗣️🗣️🗣️😁🎁💃🏽💃🏽 Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 5500 na 1. Kaza rabi 2. Ciccibi 3. Gumba 2 4. Gari 1 5. Tsimi 2 sunada kyauta abubuwa kamar haka 1.Matsin ba a Fira da wando sa mai gida kukan dadi 1k 2. Matsin maganin infection 300 3. Dripping pills 1pcs 300 4. Matsin dare daya wanka goma 400 Total total gift 2k 😁 Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 5500 dinki ki mallaki kayan da ko 10k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah *08144015291* Maman yasmeen takuce 😍 Wa.me/+2348144015291 For more information say hi 👋 Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku💃💃💃 muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu *DAHUWAR KAZA* Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya* Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta 🎁 mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya* *INA MASU JEGO DA AMARE* Karku bari wannan dama ta wuceku *08144015291* Zuzeam empire ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1000 kacal 👌🏽 Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd Maganin karin kiba Maganin nono da hips Rage tunbi da kiba Infection set Sabon budurci set Niima set Basir set Matsi mallaka Amarya set Uwar gıda set Mai jego set Dadai sauransu Ido ta lumshe jikinta na ci gaba da kyarma,tuni Mamuh macijiya kuma ta ɓullo kanta tsakanin ƙirjin Nafisa ta fiddo halshe ta lashi fuskarta,yawunta masu mugun ɗohi suka daki hancin Nafisa.Ba tare da ta buɗe ido ba ta buɗe bakinta murya na rawa can ƙasan maƙoshi kamar mai yin raɗa ta soma karanto wasu ayoyin Alkur'ani da ke cikin suratul Yusuf daga aya ta 79 har zuwa 82 .Jikin Mamuh macijiya ne ya soma yin sanyi tsabar yadda ayayoyin ke dagargaza ruhinta musamman da ya zamana Nafisa ta soma ɗan ɗaga murya.Sululuuuu Mamuh macijiya ta faɗo daga jikin Nafisa ,a mugun tsiyace Gwaggo Rahamu ta bi ta ƙarƙashin ƙofa ta shiga ɗakin Mamuh don kuwa ƴan magana na cewa in ka ga gemun ɗan uwanka ya kama da wuta to kai ka shafa wa naka ruwa. Nafisa na jin saukar macijin ta buɗe idonta a hankali tare da sauke su ƙasa inda Mamuh ke kwance har yanzu cikin siffar maciji sai wani irin numfashi take fatar cikinta na lotsawa kana gani ka san ta wahala. Nafisa ba bakinta bai gushe da ci gaba da yin duk addu'ar da ta zo bakinta ba,a yadda take tsayen suka ƙure juna ita da Mamuh wacce duk wanda ya san ta to tabbas in ya ga macijin zai shaida wannan idon na Mamuh ne.Nafisa ta saki wani murmushin nasara lokacin da ta ga hawaye sun fara fita daga idon macijiyar,ta sani sarai har da kunya da gajiya suka hana Mamuh ƙoƙarin guduwa don babu abin da Mayu suka fi tsana kamar asirinsu ya tonu wannan yasa Nafisa ta nufi ɗakin Sakeenatu.Tana shiga daidai ita kuma ta fito daga Toilet ta yi wanka ƙugunta ɗaure da towel,“wani wankan kika sake yi?” Nafisar ta tambaye ta ba tare da ta nuna mata alamar wata damuwar ba. “Eh wallahi,maganin nan da na yi hayaƙi da shi sam babu daɗi shi yasa na yi wanka” Sakeenatu ta bata amsa tana mai kallon Nafisa,“Me? Wannan kallon fa?” “Fuskarki ce nake ganin kamar tana min wani iri” “Wani iri kamar ya fa?” Nafisar ta tambaya tana mai shafar fuskarta a daidai wurin da Mamuh ta lasa. “Babu komai! Bari na shirya na san yanzu Abbas zai shigo” “Ni zan yi sallah” cewar Nafisa tare da shiga Toilet,har ta gama alwala tana tunanin abin da ya faru da ta zo ta yi sallah sosai ta yi addu'ar neman tsari. Sakeenatu ma ta yi sallah tare da fara bitar karatun jiya da aka koya mata,in ta yi kuskure sai Nafisa ta gyara mata suna nan zaune har aka kira isha'i suka miƙe suka gabatar sai bayan sun ida ne suka fita falo. Nafisa ta dubi daidai wurin da ta bar Mamuh a ɗazu,tuni capet ɗin yayi alamun datti. “Anty Sakeena ni kam ina mai aikinki?” “Wa Fa'iza ? Wallahi kin ga shaf na manta da zancen ta.Ga shi kuma ba waya ce da ita ba ballantana na kira ta amma gobe in ba ta zo ba zan je gidan nasu na gani tun da babu nisa nan baya ne gidan Fulanin nan” “Oh! Can take ashe,tun da babu nisa bari na je na dubo” Kafin Sakeenatu ta bata amsa Abbas yayi sallama tare da shigowa,duk fushinsa ne ya ɓata nan take ganin uban adon da matarsa ta yi. “Ina wuni Ya Abbas ?” Nafisa ta gaishe shi tana mai yin murmushi don tana mugun sha'awar soyayyar antynta da mijinta,ba ƙaramin so yake yi mata. “ Lafiya lau Nafi ya gida?” ya amsa. “Alhamdullah” ta faɗa tana mai fita,ita kuwa Sakeenatu kamar wata yarinya haka ta wani rugo da gudu ta faɗa a jikinsa tana kuka.Abbas ya lumshe ido ya na mai cewa “ mene ne kuma na yin kuka uhum?” ba ta basa amsa ba ta dai lafe a jikinsa,tsawon lokaci suna a haka kafin ta hauƙura ta ja shi zuwa cikin bedrom ɗinsu.Da taimakonta yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya sannan suka fito suka ci abinci,cikin hira ne take faɗa masa ba ta da lafiya har sai da ta je gida. Ya ja dogon numfashi kafin ya ce “ni kina Keenat ban san abin da ke damuna ba yau gani nan dai” “Allah kawo mana sauƙi” “Amen!” FA'IZA Tun da lamarin nan ya faru da ita duk jikinta ya zama wani iri,tun da take ba taɓa jin makamancin abin da ta ji ba a ranar nan.Tana da saurayi don har manya sun shiga zancen amma duk tsawon lokacin da suka ɗauka ita tun can ba ta taɓa jin sha'awarsa ba don a tunaninta ma ba ta da lafiya ne tun da ta ji ana faɗar akwai matan da basu jin feeling.Sai ga shi babban al'amari ya faru da ita mai kamar mafarki kamar zahiri an yi wasa da sassan jikinta,a ranar da ta isa gida kasa cin abinci ta yi.A washegari kuma ta tashi da zazzaɓi dalilin da yasa ba ta je aiki ba,yanzu ma tana kwance kan tabarma ta shafe jikinta da wani maganin zazzaɓi sai ga sallamar Nafisa.Duk da gidansu bai da ƙwan lantarki zamani amma suna kunna uban sanjo wannan yasa ta gane Nafisa duk da ƙarancin haskensa.Ta tashi da sauri tana mai cewa “sannu da zuwa” Ita kuwa Nafisa gaisa wa take da Mamar Fa'iza wacce ba ma sosai take jin Hausa ba,ta zauna kan tabarmar tana mai cewa “fatan dai lafiya? Anty na ta jira shiru ba ki zo aiki ba” “Zazzaɓi ne ya rufe ni amma da sauƙi gobe zan je in sha Allah ” Fa'iza ta bata amsa. “Allah ƙara lafiya,ni zan koma” cewar Nafisa tare da miƙewa,har ƙofa Fa'iza ta rako ta sai a lokacin kuma ta yi mata tambayar “ni kam Fa'iza abin da ya faru da ke gidan anty Sakeenatu dama kina yin haka?” “A'a wallahi ban taɓa yi ba” “To ki dage da addu'a kin ji ko,saboda yanzu duniyar sai a hankali” “To na gode” da wannan suka rabu maimakon Nafisa ta koma gidan Sakeenatu sai ta yi tsinke gidansu tun da dai ga mijinta nan ya zo. #GIDANSU SAFEENATU Wuni guda currr jaririya Baseerat ta ɗauka tana bacci wanda gangar jikinta ta koma kamar gawa ko motsi ba ta yi. Idon Safeenatu taf da hawaye ta ce “ Gwaggo Habibah jaririyar nan fa ba ta motsi,ina ga ta mutu ne” “Da ranta Safeena,don Allah ki fitar lamarin yarinyar nan tun da dai ba ki da ƙarfin zuciya.Tun farko na faɗa miki Baseerat ba normal ba ce,kenan sai ki shirya ganin abubuwan ban mamaki.Wannan kwancin da kika gani ruhinta yayi tafiyar dogon zango ne amma da ranta,ƙila sai goshin magarib su maido ta” Hawayen da take ƙoƙarin mayar wa ne suka yi nasarar sauko wa akan kumatunta,ta girgiza kafin ta ce “ ni kam ba zan iya rainon ta ba,don muddin na ce zan zauna da ita zuciyata na iya bugawa.Su wane ne za su maido ta? Yarinya kamar ɗiyar jinnu ace tun safe tana bacci ko nono ba ta sha ba alhalin ɗan uwanta ya sha fiye da goma.Haba kuma ace ba zan yi magana ba?” Safeenatu ta faɗa zuciyarta na yi mata ciwo kafin ta miƙe ta fita, frigine ta buɗe ta ɗauko ruwa masu mugun sanyi ta juyo a roba sannan ta koma ɗakinta.Babu wani tunani ta ɗauki Baseerat ta tsoma cikin ruwan ƙanƙarar nan ,ko daƙiƙa biyu ba yi ba ta buɗe idonta farare tasss babu ɗigo baƙi kafin su rine su koma ja kamar nunnanen tumatur.Safeenatu ta yi baya da sauri cike da tsoro,tana jin wani azababen sanyi na game duk illahirin jikinta tamkar wacce aka jefa a frigini.Haƙoranta ne suka fara dantsewa suna fitar da wani ƙasƙas,sai a wannan lokacin Gwaggo Habibah ta miƙe ta cire Babyn tare da lumshe ido tana mai bata haƙuri “ku yi haƙuri uwa-uwza ce ta yi kuskure ba za ta sake ba” tana maganar ne tana jimƙe da hannun hagun Baseerat wanda ke fitar da haske,Gwaggo Habibah ba ta buɗe idonta ba sai da ta ji Sakeenatu na sauke numfashin wahala ta yi mata wani kallo ta ce “yanzu kin fahimci abin da nake son yi miki nuni?” kai ta gyaɗa,Baseerat ta soma yin kuka. “Zo ki bata ta sha” Safeenatu ta maƙe kafaɗata ta ce “wallahi tsoronta nake” “Sun tafi yanzu ita kaɗai ce ,zo ki bata yunwa take ji” tana ji tana gani haka ta shayar da jaririyar. Ana kiran sallar magrib Murjanatu ta dira a gidan da ɗirkeken cikinta,cike da murna suka rungume juna ita da Gwaggo Hajara.“Na yi kewarki sosai Mama ” cewar Murjanatu tana matsar ƙwalla,shiru Gwaggo Hajara ta yi jin ƙaton cikin ƴarta na tokare ta yayin da kuma yawunta suka soma tsinkewa tsabar maita...... My book is only 500 via 6042551755 Hassana ibrahim Keystone bank DM +22795045822 💛💛💛GHT B-CLEAR,FEMALE CARE AND GANODERMA💛💛💛 💛💛*BACK TO VIRGIN KIT* *(SABON BUDURCI)* 💛💛Assalam alaikum Mata albishirin ku🧏‍♀️🧏‍♀️ga abin da kuka Dade Kuna mafarkin samu ya samu💃🥰 💛💛Abin nema ya samu ,Kowacce mace aduniya tana mafarkin sake kasancewa virgin 💛💛Ina manyan Mata da suka hayayyafa😁 💛💛ina zawarawa masu shirin aure😍 💛💛Ina budurwa da iftila'i ya fadawa a yayin tsallaka rame 😢 💛💛Ina Mai jego da keso ta dinke ta game tsaf ciki da waje❤️ 💛💛Duk ku marmatso kusa ga GHT back to virgin set na kawo muku ,magunguna ne namu na gargajiya bana bature ba 💛💛Kuma Sha akeyi ,insha Allahu muddin kikayi amfani da wannan Kayan Zaki dawo da martabar ki ta farko 💛💛Sai kin gwada za ki tabbatar da hakan. Sisters no 08142506271 mmn Khadeejah sai najiku [03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI* LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. *Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman _____________________ 01/10/24 *Last free page 13-14* Wani irin mugun ƙishi ne ya wanzu a maƙoshin Gwaggo Hajara saboda Maitar shan jini ta motsa.Dakyar ta iya sakin Murjanatu ta koma gefe tana kallon ta,sai kuma ta kasa haƙuri sai da ta shafi ƙaton cikin da mugun sauri Murjanatu ta kai hannunta ita ma kan cikin saboda mugun juyawa da yayi. “Washhh! ” ta furta a wahalce kafin kuma ta dafe ƙugu jin kamar ta soma naƙuda ne,“ sannu Murjanatu ki zauna mana” Gwaggo Hajara ta faɗa tana haɗiyar yawu don tsaf take kallon jaririn wanda sai juyi yake a ciki. Kan gwiwanta ta zube tana mai ci gaba da yin gumurzu,tuni ita Hajara ta san da yau in ba wani iko na Allah ba sai ƴarta ta haihu.Da sauri ta shiga cikin ɗaki ta fito kafin ta ce “tashi mu je asibiti” a wahalce ta ɗago ta dubi mahaifiyarta ta ce “ wallahi Mama ban iya tashi” “To haka za ki zauna? Sai nake ganin kamar haihuwar ce” Ba ta rufe bakinta ba Murjanatu ta fasa wani uban ihu wanda ya jawo hankalin Gwaggo Habibah da saurinta kuwa ta fito tana tambayar lafiya sai kuma ta yi tozali da Murjanatu a cikin mawuyacin hali.Da taimakonta suka samu suka Murjanatu ta miƙe tsaye,Munir ne ya je ya nemo musu mai ɗan sahu.Kayan robar Safeenatu aka yi aro aka kai ta asibiti,sai uban ihu take tana kururuwa tana faɗin za ta mutu. Daga nan waje kuma inda mutane ke zauna wa,ran Gwoggo Habibah ya ɓace sosai tun tana ɓoyen abin har ta kasa ta ce “ yanzu ke hatta ƴarki ba ki bari ba? Wannan mugun hali naki bai yi ba.Wato babu babban makunyaci a duniya irin maye,tun da har jininsa bai bari ba” Gwaggo Hajara ta ƙanƙance idonta da suka kaɗa suka yi ja kafin ta ce “ ina ruwanki da ni ? Ke kika haifa min Murjanatun? Ƙanwar uwa ko ta uba?” Gwaggo Habibah ta miƙe ta ce “ kina fa da gaskiya,amma ki yi haƙuri farar zuciyata ta taimakon jama'a tasa na zo na tsoma hannnuna inda ba a gayyace ni ba.Tabbas Murjanatu ƴarki ce in kina so ki haɗa har da ita duk ki cinye” tana gama faɗa ta yi tafiyarta ta bar Hajara a zaune babu jimawa kuwa Murjanatu ta haifo ɗanta namiji. Ɗakin hutu aka kai ta,murya na ɗan rawa Gwaggo Hajara ta ce “ yo ina jaririn?” “Nurse na duba shi ne don tabbatar da lafiyarsa” ta bata amsa. Tsawon lokaci kafin a kawo shi jikinta har rawa yake ta karɓe shi,nurse ta ce “ a basa abincinsa ya sha da alamu yunwa yake ji” “Toh! Toh” cewar Hajara tana wani kafe yaron da idon mugunta,ya soma kuka Murjanatu ta tashi zaune babu kunya ta ce “ Mama kawo shi” ba don ta so ba ta miƙa mata shi ta koma gefe cike da ƙwarewa ta damƙe kurwar yaron .Da ta fita wankin kayan da suka ɓace ta samu wuri ta haƙa rame ta binne ,duk da zuciyarta babu daɗi amma ji take ya zama doli ta cinye jikanta na farko ko yawunta sun koma. Daren nan dai ba su yi bacci ba jariri nata yin kuka hatta likitocin sai da suka shigo suka duba shi,sai asubahi ya rumtsa wuraren ƙarfe tara na safe aka basu takardar sallama bayan sun biya.Hajara ce ta je ta taro ɗan sahu,bayan ta saka kayansu Murjanatu ta shiga sannan ita ma ta shige tana kallon wurin da ta binne kurwar jariri can ƙasan zuciyarta ta furta ‘ zuwa dare zan zo na tone’ haka suka isa gida. Ta kuwa ci sa'a Daddy bai fita ba,Murjanatu ta gaishe shi ya amsa tare da yi mata barka kafin ya maida dubansa ga Hajara wacce sai raba ido take kana gani ka san ba ta da gaskiya. “ Hakan da kika yi daidai ne? Don dai ba ni ne na haifi Murjanatu ba shine kika koro Habibah daga asibiti? ” “Ka yi haƙuri ba koro ta na yi ba,na dai ce ta dawo gida tun da ba za a barin mai jego ita ɗaya ba a gida” “Mi yasa ba ki kira ni kin shaida min zancen haihuwar ba? Ban cancanta ba ne ko me?” “Ka yi haƙuri Daddyn yara,yanzu dai ka kira shi mijin nata ka shaida masa zancen haihuwar ” Bai amsa mata ba ya fice,sai a lokacin Habibah ta fito idonta kan jaririn wanda ke baccin wahala.Cike da tausayinsa ta ƙarasa ta ce “ barka Murjanatu Allah raya shi kan sunnah” “Amen na gode” ta amsa tare da miƙa mata jaririn,Habibah ta karɓe shi tana mai zaunawa kan kujera ta shafi sumar gashinsa tana kallonsa da kyau ta tabbata kurwarsa na gidan yari ba a cinye ba sai dai ba ta san a ina aka binne ta ba.Haka ta gaji da binciken ta miƙa shi ga uwarsa ta miƙe suna ƴar kallon-kallon ita da Hajara wacce idon nan nata suke wiƙi-wiƙi na maras gaskiya. A sanyayye Habibah ta koma ɗakin Safeenatu,“ ya dai Gwaggo Habibah lafiya na gan ki duk kin yi wani iri?” Feenat ta tambaya. “ Babu komai Safeena,bacci Baseerat take?” “Eh ba ta jima da rufe idon ba” “Mu gan ta” Habibah ta faɗa tare da yin zama, Safeenatu ta ɗora mata jaririyar kan cinya.Hannunta mai safa ta kamo ta cire sannan ta soma shafa shi ,zuciya cike da rauni ta soma yin magana “ ki tausaya ki ceto jaririn da bai san komai ba,ki sani shi ma tamkar Basheer yake mai rauni ne.In kuma har yanzu kuna cikin fushi ne shi yasa kuka hana ta ɗauki mataki ku yi haƙuri,amma dai a duba lamarin” tana gama faɗa Baseerat ta buɗe idonta taram cikin na Habibah,ita kuwa ta shiga kallon abubuwan da suka faru bayan ta bar asibitin a cikin ƙwayar idon jaririyar ta ga komai har inda Hajara ta binne kurwar.Tana gama gani Baseerat ta maida idonta ta rufe, Safeenatu dai na gefe a yanzu ma kallonsu take ba tare da ta ce komai ba. Habibah ta ja ajiyar zuciya ta sakar mata murmushi ita kuwa kai ta ɗauke,tana mai jawo wayarta ta kunna data so take ta yi bincike don gano shin abubuwan da suke faruwa zai iya kasancewa ko kuwa ƴarta ce kawai ke da shi. Tunanin ta watsar ta shiga WhatsApp ta fara duba saƙonnin mutane masu yi mata barka kafin kwatsam ta ganta cikin wani group.A hankali ta soma biyayar abubuwan da ke faruwa sai ta ga amsoshin tambayoyinta kan wani posting. ```“M” CIKIN TAFIN HANNU,MAUME HAND/PAUME DE MAIN Chiromancy wata daɗaɗiyar hanya ce ta hango makomar mutum da kuma fassarar halayyar mutum daga dalilin layukan hannu. Wani lokaci waɗannan layuka na iya samar da lambobi da haruffa. Ɗaya daga cikin waɗannan wasiƙun na iya zama wasiƙar M, ma'anar wacce mystics da dama suka yi nazari a kanta. Kamar yadda mutane da yawa suka yi imani, layukan da ke kan tafin hannunmu suna bayyana halinmu da ƙaddararmu. La lettre M est attribuée à des personnes vraiment spéciales(The letter M is assigned to truly special people). An ba su kyakkyawar fahimta kuma suna wakiltar abokan haɗin gwiwa akan dukkan wasu kasuwanci. Idan mutanen da kake so suna da wasiƙa ta musamman M a cikin tafin hannu ya kamata ka sani cewa ba za ka iya raina masa hankali ba kuma ta wata hanyar ba za ka iya yin ƙarya ko yaudarar wannan mutumin ba. Kasancewar shi mai dubara da hankali da tsantsar lura sosai, mutamin da ke da harafin M a tafin hannu cikin sauƙi zai fahimci cewa ana yi masa ƙarya ne ko yaudara. ``Matan da suke da harafin M a tafin hannunsu suna da zurfin tunani fiye da maza, har ma da waɗanda suke da wannan wasiƙar. Ana yi musu baiwa da ikon sarrafawa da shawo kan duk wani cikas a rayuwa, kuma sun san yadda ake amfani da albarkatu da damar da ake da su. Harafin "M" a kan tafin hannu ma na iya nufin: • Ƙwarewar shugabanci • Iko wato power/pouvoir``` Zuciyar Safeenatu banda bugawa babu abin da take yi har sai da ta ajiye wayar ta je ta ɗauki ruwa masu sanyi ta sha .Ta dawo ta zauna don ƙara duba saƙon sai dai hatta shi kansa group ɗin ya ɓata a wayarta babu shi sam .Kamar mahaukaciya haka ta miƙe ta je ta yi wani gurwanau a gaban net ɗin da aka saka Baseerat,ta zuge zip ɗin ta kalli ƙofar toilet inda motsin ruwa ke ta zuba da alamu Habibah wanka ta shiga ba tare da ita ta san yaushe ta shiga ba . Murya a ɗan kasalance ta ce “ Baseerat ni ce mahaifiyarki,ni na haife ki.Duk wani wanda bai son ganin kin cutu to tabbas sai dai ya biyo bayana,don haka kar ki ga kamar ban son ki a'a wallahi zuciyata raunk ne da ita.Magana nake son yi miki game da abin da na gani cikin wayata,shin kina da masaniya? In dai tabbas ke ƴar baiwa ce kamar yadda saƙon nan ya bayyana to ki buɗe idonki ki kalle ni” ko rufe baki ba ta yi ba kuwa Baseerat ta buɗe idon sai da Safeenatu ta dafe ƙirji saboda tsoro. “Mine ne wai?” daga bayanta Habibah ta tambaya ,zip ɗin net ɗin ta mayar tana mai cewa “ babu komai Gwaggo Habibah,na yarda na aminta da lamarin nan gaske ne ana samun ƴan baiwa to Allah bata ikon yin amfani da ita ta hanyar ƙwarai” ruwan sama ne suka fara sauka a daidai lokacin da Safeenatu ta rufe bakinta. Gwaggo Habibah ta yi wani ɗan ihun murna tare da rungume Safeenatu ta ce “ kin ga ko? Ƴarki ta musamman ce ancestor/ ancêtre suna tare da ita” A wannan daren cike da zullumi da tunani Safeenatu ta yi shi,da ta samu bacci ya ɗauke ta mafarkai ta yi barkatai akan goben Baseerat. Washegari tun da safe kukan jaririn Murjanatu ya cika gidan kamar wanda ake cirewa rai. “Jaririn can ba dai kuka ba” Safeenatu ta faɗa . Habibah ta ja baki ta yi shiru tana tuna jiya irin gumurzun da suka yi ita da Hajara akan kurwar yaron.Dakyar ta yi nasara ta tone ta tare da saka Hajara don doli ta mayar masa abarsa wacce tuni ita kanta kurwar ta yi rauni,kukan da yake yi kuma saboda ciwon jiki ne. ★A kwana a tashi babu wuya wurin Allah yau ne sunan Twins ɗin Safeenatu waɗanda dangin Bashir suka yi bajinta sosai wurin yankan manyan raguna uku biyu na BASHEER ɗaya kuma na BASEERAT .A wannan rana ta farin ciki Safeenatu ta rakuɓe wuri guda tana ta yin kuka,ga shi dai ta sha ƙunshi da kitso ga kuma gizner ta gani ta faɗa amma rashin masoyinta ya dawo mata daram musamman yadda ake ta faɗar an yi masa madadi da kuma addu'o'in da mutane ke yi. Da wannan damar Gwaggo Hajara ta shirya mugunta wacce take kambacin fansar da ta yi niyyar ɗauka akan Habibah da hana ta rawar gaban hantsi.Sai da ta bari duk hankalin mutane ya ɗauku,sannan jarirai duk an fitar da su can tsakar gida saboda zafin da ɗakin ya ɗauka sannan ta nufi ɗakin Safeenatu.Duk da akwai mutane hakan bai hana ta gwada sa'arta ba,“ ungo Safeena Gwaggonki Habibah ta ce ki ci abincin nan kafin ta zo ta yi miki ta ƙarfi tun da dai ke ba ki jin magana kina jego amma kin ƙi cin abinci ” Hajara ta faɗa tare da miƙa mata plate mai cike da nama ya sha jar miya,ta karɓa tana turo baki tare da soma ci don ita duk a tunaninta gaske dai Habibar ta bata.Cike da murna Hajara ta bar ɗakin ta je ta kasa kunne tana jiran sakamako. Da rana mutanen arziki sun cika gida, Safeenatu ta shiga Toilet ta yi wanka da canza kaya daga shadda zuwa less.Kamar wacce aka yi wa wankin ido haka take ganin ƴan biki tsirara tamkar babu kaya jikinsu,zuciyarta ta yi wani mugun bugawa ganin ta soma ganin hanjin cikin mutane yayin da kuma take jin wani abu a bakinta da ba ta san mine ne ba.A daidai nan free page ya ida,duk mai son ci gaba za ta biya kuɗi domin shiga PAID GROUP. *FREE PAGE/ PAGE NA KYAUTA YA IDA* Detail 500 via 6042551755 Hassana ibrahim Keystone bank DM +22795045822 In kin san ba ki shirya saya ba kar ki min magana,ga detail nan kawai ki tura kuɗin ki turo min evidence ta WhatsApp. *NB:* daga lokacin da ya kammala ya zama complete zai koma 1000. 01 octoba 2024 #CHAMSIYA LAOUALI RABO MRS SADAUKI 💫