ABU NAKA… 3 HAFSAT C. SODANGI Haqqin Mallaka (m) Naquin mallakar littafin na Hafsat C. Sudan ne (Mrs. Yunus Abdullahi Davai) Shekarar Bugu: 2006 An sake Bugawa A: 2015 Alura An xan yi gyara a cikinshi kaxan saboda wasu dalilai, sai dai yana nan a kan tsarinshi na farko. Na gode. 11/8/2006 TA`ZIYYA Ubangiji ya ji qan HAJIYA AISHATU BALARABE (JAZAN). Marubuciyar litattafan ABOKIN HIRA da rahamarsa. Ubangiji ya kyautata makwancinta, in tamu ta zo kuma yasa mu cika da imani. Amin. ABU NAKA…-3 A garin Misau gidan Gwaggo Habiba ranar Laraba da hantsi, Abu tana zaune kan kujera ‘yar tsugune a tsakar gida, ya yin da Gwaggo Habiba take zaune gabanta kan tabarma tana kuma goga mata goronta bayan ta gama gyara mata farcenta da ta yanke mata. “Ni kuwa Inna sai nake ganin kamar bakya jin daxi saboda rashin walwalarki ta yi yawa, tun bayan kai Saddiqa gidan mijinta da kika yi har yanzu baki dawo cikin sukuninki ba. Sannan a zaman yanke miki farcen nan da na yi sai na fahimci jikinki yana vari tamkar wani abu ya tsorataki”. Abu ta kalli ‘yan yatsun nata da aka ce suna vari kafin ta yi maza ta xauke qafarta daga kusa da ita, ranta a vace ta soma magana cikin faxa. “Kin ga fa shi yasa jiya da shekaran jiya duk ban zo gidan nan ba, saboda yawan tasani a gaba da kike yi kina tuhumata zuwan Malam kan wai ya ganni ko bani da lafiya ne jiya, shi yasa yau ya zo kuma tun ban gama hutuwa ba za ki fara. To jikina ba zai yi vari ba ni ba tsohuwa ba ce?” Gwaggo Habiba ta yi murmushi ta ce, “Haba Inna yaushe kika yi tsufan da jiki zai rinqa rawa haka?” Ta xan kawar da fuskarta gefe ta ci gaba da yin bayani a nutse. “Ni dai a zuciyata na san akwai xayan biyu in ma dai kina voye min halin da kika baro Saddiqa da mijinta a ciki, ko kuma ke xin baki da lafiya baki yarda kin gaya min ba, amma ki yi haquri”. Abu ta zovara baki ta ce, “A’a, mene ne na vacin rai kuma daga magana, ko don an mai dani kububuwa don faxa?” Suka ci gaba da wata hirar. Zuwa can Gwaggo Habiba ta ce, “Ni dai Inna yawan mafarkin Saddiqa da nake yi yana damuna”. Gaban Abu ya yanke ya faxi, mafarkinta na daren jiya ya faxo mata. A firgice qwarai ta tambaye ta kema kina mafarkin ne? Gwaggo Habiba ta xaga ido ta kalli Abu cikin nazari da lura, a hankali ta buxa baki ta ce mata, “Dama kina mafarkinta ne Inna baki tava gaya min ba? Kema ashe hankalinki bai kwanta da yanayin da kika barotan a ciki ba”. Ta soma kuka, kuka kuma mai tsanani. Abu ta yi hanzarin abka mata da faxa don ta kawo qarshen kukan nata. “Sai na daina zuwa gidanku tunda haka kuke ke da mijinki, kun tasa Mus’abu a gaba bakwa mishi fatan alheri kullum burinku…..” Ba ta kai ga qarshe ba ta tsaya saboda jin maganar da Gwaggo Habiba ke faxa. “Zan tafi can garin in gano halin da Saddiqa ke ciki, zan je in gani da kaina in bai yi min ba zan xauko ta. Saddiqa marainiya ce ba ta da kowa sai ni, nice uwarta nice kuma ubanta. Yaya Gixe ne ya cuce mu ni da ita, shine ya xauke ta ya baiwa mutumin da ya fi mu sanin ba zai riqeta ba, baqin ciki kawai zai cusa mata. To ba zan barshi ba, dama tunda na ga ina munanan mafarkai a kan ta na san…….” Abu ta katse ta da cewa, “Babu wani mafarki kina dai son zuwa wurin xanki ne kawai, in kuma kika fito ma kika ce za ki je ganin Mus’abu wa zai hana ki”. Gwaggo Habiba ta zuba mata ido cikin kaxuwa wasu sababbin hawaye suka zubo mata masu zafi saboda takaicin kalaman na Abu, sai dai babu yanda za ta yi. Cikin nutsuwa ta ce, “Haba Inna, ni kuwa me zai sa ki gaya min haka? Kin sani sarai in ban da Saddiqa tana wurin nan babu abin da zai sa qafata ta taka gidan nan”. Abu ta ce, “Oh’oh! Ni za ki kawowa wayo, in so kike a dubo miki Saddiqa ba wurinshi za ki ba, ba kya tunanin in je in gano miki in zo miki da wani sabon labarin”. Ta miqe tana jan zanin ruhuwarta tana tafiya, fita gidan take nufin yi tana kuma qarasa zancenta, “Ba fa hanaki zuwa gidan nashi nake nufin yi ba, ai ba a raba xa da uwa”. Takaici ya kama Gwaggo Habiba, can cikin maqogwaronta har wani xaci take ji saboda vacin rai, sai dai babu halin ta tanka. “In kin je ki gai da Mus’abun”. Ta faxi daidai tana fita. Da daddare Gwaggo Habiba tana tare da mijinta Malam Abdallahi a gefen tabarmar da yake zaune yana cin abincin shi, yana kuma sauraron bayanin da take mishi na yanda suka yi da Abu. Sai da ya ji ta yi shiru sai ya yi murmushi ya ce, “To ai sai ki haqura ki tura ta xin tunda ta ga za ta iya wannan wahalalliyar tafiyar”. Gwaggo Habiba ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce, “To amma Malam wane bayani Inna za ta zo da shi in dai a kan wannan yaron ne? Ka santa sarai halinshi na zahiri ma in za a faxa ranta vaci yake yi, ko yanzu ma kuma na fi zaton akwai abin da take tsoron kar a je a gani wanda yasa take faxanz uwan da na ce zan yi balle a ce ita ta zo ta faxa da kanta”. Ya ce, “Eh, duk da hakan cikin biyu ne za ki zavi xaya, ko ita xin ta tafi ne ko kuma a haqura gaba xaya tunda ga irin kalaman da take furtawa”. Gwaggo ta ce, “Ni kam gara in dangana in yi ta yi mata addu’a Ubangiji ya kuvutar min da ita daga dukkan sharri”. Ya ce, “Eh, hakan ma yana da kyau”. AJAKUTA Mus’ab yana tsaye a falon cikin tashin hankali da fargabar rashin ganin Saddiqa a cikin gidan. “Ke Zainab”. Ya sake qwala mata kira da sake fitowa da gudu hawaye suna zuba a idonta “Kin leqa nan maqwabta zuwa wajen su Abida ba ta nan?” Ba ta iya amsawa ba saboda yanayin da ta ga Mus’ab a ciki, in ban da rawa babu abin da jikinta ke yi, ga shi kuma kusan awa xaya da rabi ne tunda suka nemi Saddiqa a gidan basu ganta ba cikin gida da cikin Ajakuta babu ita babu dalilinta. “Kika ce kinga tana waya?” Ta gyaxa kai nuna alamar eh, haka ne. “Me kika ji tana faxa?” Ya sake wata tambayar. “Ban ji tana magana ba sauraro kawai na ji tana yi”. Gabanshi ya sake faxuwa da ya gane wayarshi da Sarah ta saurara. Anya Saddiqa tana garin nan ma kuwa? Kai tsaye tambayar ta fito mishi daga cikin zuciyarshi. Kar dai gudu ta yi za ta koma Misau? Bai jira jin amsar da zuciyar tashi za ta ba shi ba ya yi waje da gudu ya nufi cikin motarshi, sai da ya tabbatar ya xaure kanshi tamau da belt xin dake jikin motar sannan ya shiga tayar da ita, cikin zuciyarshi kuwa addu’o’I yake ta karantowa iri-iri na neman tsari da taimako wurin Ubangiji. Mus’ab yana tafiya cikin matsanancin gudun da ba zai kwatantu ba, duk da kashedin da zuciyarshi ke yi mishi saboda yanda iska ke kaxa motar duk da mota ce mai nauyi. Wayarshi ta yi qara a karo na uku, ya yi kamar ya sake yin buris da ita sai kuma ya yi tunanin to ko dai wani cikin masu taya shi neman ta ya ganta? Ya yi maza ya miqa hannu ya xauki wayar ya karata jikin kunnenshi. “Hello!” “Mutanen nan fa sun qi yarda su karvi cikiyar da muka kai musu, wai sai bayan awa ashirin da huxu da vacewar ta tukunna”. Muryar Sani ce ta yi mishi wannan bayanin. Bai tanka ba ya mai da wayar mazauninta ya ci gaba da tuqinshi, cikin zuciyarshi kuwa mamakin hukumar ‘yan sanda yake yi wai basa karvar labarin vacewar mutumin da ya shekara goma sha takwas sai bayan awa ashirin da huxu da vacewar tashi. Ko mene ne dalilinsu na yin hakan? Oho! Ya kwatanta yawan awa ashirin da huxu abin da za su iya yiwa Saddiqa sun isheta ta je har Misau ta zauna ta huta, ta ma kwana tana baiwa Gwaggonta labarin Mus’ab da abubuwan da ta gani a tare da shi. In har Saddiqa ta samu nasarar isa gaban Gwaggo anya auren shi da ita zai xore? Tambayar da ta zo cikin ranshi kenan. Tafiya mai tsanani ta awowi uku da mintoci arba’in kafin ya iso wata mararraba ta motocin da suka fito daga kudu suka nufi arewa, a nan ya yi parking cikin surquqin bishiyoyin da suka lulluve wurin, ya fito daga cikin motarshi riqe da kwalin sigarinshi a hannu da fankon ashana, cikin zuciyarshi yana tunanin a irin tafiyar da ya yi in dai Saddiqa motar haya za ta shiga kuma direban mai hankali ne, to ya wuto shi a baya, yana lissafi tare da raba awowi da mintocin tsakanin abin da ta yi kafin isarta tasha da shigar ta mota, da sallamar direba, har kawo isowarsu wannan mararrabar da ya ja ya tsaya. To in kuma vuya ta yi a cikin garin fa? Wata zuciyar ta aiko mishi da wata tambayar. Wurin wa? Ya sake tambayar kanshi. Nan da nan ya kori wannan tunanin. A sanin da ya yiwa Saddiqa gida kawai za ta dosa ba za ta tsaya neman mavoya cikin mutanen da ba ta sani ba. Da wannan tunanin ya isa wurin ‘yan sandan dake lura da wajen waxanda suka tsare hanya suna ta faman karvar naira ashirin wurin qananan motoci, hamsin ko xari wurin manya, gwargwadon dai irin lodin da ka zo da shi. Barka da aiki Yallavai”. Mus’ab ne yake isar da gaisuwarshi wajen xan sandan dake zaune kan wata mota a gindin wata bishiya mai yawan ganye da inuwa, wanda shi ke shugabantar wannan Road Block xin. “Yauwa barka dai”. Ya amsawa Mus’ab gaisuwar tashi bayan ya gamsu da kallon da ya yi mishi. “In ce ko lafiya?” Ya tambaye shi. Mus’ab ya sanya hannu cikin aljihunshi ya zaro hoton Saddiqa da ya saka a ciki daidai yana cewa, “Lafiyar ba ta da yawa yallavai”. Ya miqa mishi hoton yana cewa, “Matata ce ta baro gida ina kyautata zaton za ta biyo ta hanyar nan in har ba ta riga ta wuce ba, taimako nake so ka yi min na in tsaya tare daku”. Ya yi mishi bayanin abin da yake so suyi mishi. Xan sandan ya zubawa hoton ido ba tare da ya ce komai ba, tamkar dai wani nazari yake yi. Bai barshi ya kai qarshen tunanin nashi ba ya zaro bandir xin xari biyar-biyar ya jefa kan kujerar motar yana cewa, “Wannan a baiwa yara su sha kunun zaqi”. “Ai ba sai ka yi wannan wahalar ba don za ayi maka xan wannan taimakon, su mata waxansu irin mutane ne, al’amarinsu har mamaki yake bani, ga shi dai duk wahalar da muke yi a rayuwarmu mafi yawancinta a kansu muke yi, amma basa gani balle su yaba mana, sun fi so kowane lokaci su rinqa tayar mana da hankali. Ni wani lokacin idan abin takaicinsu ya ishe ni sai in ji tamkar a raba mana wurin zama a ce ga garin mata ga na maza, su yi harkarsu muma muyi namu kowa ya yi harkar gabanshi ba ruwan wani da wani ko kuwa?” Mus’ab ya yi murmushi daidai lokacin da ya gama fitar da hayaqin sigarinshi daga bakinshi, ya ce, “To amma yallavai da anyi hakan anya duniyar za ta yi mana daxi kuwa? Ai ina ganin da bamu yi jarumtakar da muke yin ba ma”. Yallavai ya yi tsaki mai qarfi ya ce, “Ai kuma tsiyar kenan”. Ya diro daga kan motar ya nufi cikin motarshi kamar zai ajiye sandar hannunshi, nan kuwa yana nufin sanin abin da Mus’ab ya ajiye mishi ne. yasa hannu ya xauka ya adanasu kafin ya fito, ya kalli Mus’ab cikin yanayin murmushi ya ce, “Amma wannan kunun zaqin ba zai yi musu yawa ba kuwa?’ “A’a, haba Yallavai wannan wuni da kuke yi a rana”. “To an gode, bari in haura can wajan nasu don in ga irin aikin da suke yi”. “To Yallavai”. Mus’ab ya yi godiya, ya koma inda ya voye motarshi a surquqi ya zauna yana hangen abin da su Yallavai suke yi a inda yake voye. “Park well!” Tun Yallavai bai qarasa isa ba ya shiga ba da umarni, nan da nan motoci suka yi ta yin parking a gefen hanya. Qananan ‘yan sanda suka shiga sosai leqa motoci, har duba but saboda umarnin Yallavai. Shi kuma hankalinshi yana wajen fasinjojin motocin ko zai dace da ganin yarinyar da hotonta ke sunne cikin aljihun wandonshi. Ta kowanne vangare motoci sunyi dogon layi, ga matsanancin bincike cikin zafin rana Yallavai sai xigar gumi yake yi amma babu alamar zai gaji. Mus’ab yana zaune cikin motarshi cikin fargaba da zaquwa daxewar lokaci ne ya dame shi, anya basu riga sun wuce ba ma kuwa? Ya tambayi kanshi. Yawan harbawar da zuciyarshi ke yi ya hana shi ci gaba da zaman cikin motar, ya fito ya nufi bakin hanyar shima. “Yallavai na ce anya basu riga sun wuce ba kuwa?” Ya yi tambayar a yanayi na damuwa. Ya zubawa agogonshi ido tare da nazarin daxewar da suka yi a wurin suna cajin motocin. Ya xago ya kalli Mus’ab ya ce, “Ina ganin har yanzu ba zamu fidda rai ba, ai ka san ba daga gida kai tsaye za ta kamo hanya ba, sai ta je tasha tukunna. Don haka ka qara haquri a wurinka don ba zamu so tsayuwarka a cikin mu ba”. Mus’ab ya sake kunna sigarinshi ya sanya a baki, kafin ya sake gangarawa wurin zaman shi. A daidai wannan lokacin wata mota ta iso wajen peogout qirar station wagoan, ta bi bayan sauran motocin dake tsaitsaye. Yallavai ya nufe ta da sauri zuciyarshi tana dakan uku-uku, anya ba ita ba ce wancan? Zuciyarshi ke tambayar shi. Cikin hikima ya qara kallon hoton don ya qara tabbatarwa. Ita ce. Zuciyar tashi ta qara tabbatarwa. Yasa hannu ya buxe qofar motar. “Fito nan”. Ya nuna ta da sandar dake hannunshi. Mutumin dake jikin qofar motar wanda sai ya fita kafin ta samu damar fitowa, wanda tun shigar shi motar hankalinshi yake kanta, iyaka dai bai ga fuskar yi mata magana ba, don haka ya mai da nutsuwarshi kan mujallarshi yana sauraron zuwan lokacin da zai dace da yi mata maganar. Ya xago kanshi ya kalle shi ya ce, “Ta fito ta yi maka me?” Gaba xaya jama’ar motar suka zubowa Yallavai ido. “Common fito nan”. Ya ba da umarni mai zafi don tuna musu ko shi waye? Mutumin dake varin nashi ya fito ya tsaya gabanshi suna kallon juna. “Wai kai waye da kake ja da hukuma? Ka kuwa san matsayin wannan abin da kake yi?” “Ban sani ba Yallavai sai ka gaya min”. Ya yi mishi bayani a yanayi na gatse. Yallavai ya rabu da shi ya mai da hankali wajen baiwa Saddiqa umarnin fitowa”. Mai mujallar ya kalle shi ya ce, “Haka kawai za ta fito ba tare da ka yi mana bayanin dalilin fitowar tata ba? Me yasa baka ce kowa ya fito ba sai ita wannan yarinyar?” “Ita wannan da kake gani ta gudo ne daga gidan mijintaa, shi yasa zan fito da ita don in mayarwa mijinta da ita”. Jin wannan bayani na Yallavai yasa wurin ya kaure gaba xaya fasinjojin cikin motar, waxanda mafi yawancinsu maza ne suka firfito suka kewaye Yallavai, daga masu gyaran zanzaro sai masu naxe hannun riga tare da faxin, “Wannan ai shine zance, ka tsare mu cikin jeji ka fitar da tsaleliyar budurwa a cikinmu ka ce wai za ka mayarwa mijinta da ita. To a wane matsayi, waliyi ko wakili?” Hargowa ta jawo hankalin sauran jama’a suma suka firfito, masu isowa ma kowa ya zo sai ya yi parking ya fito don ganin abin da ke faruwa, duk wanda ya iso sai ya buqaci sanin me ke faruwa? Tun ana bayani na gaskiya har aka koma qara gishiri a kai. Mus’ab ya iso wurin don ya kasa fahimtar abin da ke faruwa, cincirindon jama’a yasa ko motar ba a gani daga nesa, da qyar ya kutsa kai ya smau ya isa wurin da abin ke faruwa. Yallavai wanda tuni ya gundura da lamarin ya shiga fargaba saboda cincirindon mutanen dake kewaye da shi waxanda suka zamo mishi barazana, don ya san kes suke jira su afka mishi, don sun riga sun tunzura. Yana ganin isowar Mus’ab ya yi maza ya ce, “Yauwa ga ma mijinta nan ya zo da kanshi”. Gaba xaya wuri ya kaure da hayaniya, “Haxin baki ne da shi suka haxa baki”. Wasu har suna cewa, “Za ma ku sani, mu nan da kuke gani ba za a kawo mana wannan iya shegen ba”. Yallavai ya yi maza ya ciro hoton dake aljihunshi zai nuna musu don ya samu ya wanke kanshi daga zargin da jama’a ke mishi. Wani mara kunya a ciki ya yi maza ya fige hoton ya raba shi biyu ya jefa shi a baki ya tauna ya haxiye yana cewa, “Hoto kuma har wata shaida ce”. Mus’ab ya yi shiru yana kallo cikin nazarin al’amarin, kafin ya zaro karan sigarinshi ya sanya a baki ya kunna yana zuqa a hankali yana kallon Saddiqa dake amsa tambayoyin mai mujallar. “Kin san wannan da ya ce wai shi mijinki ne?” Ta girgiza kai nuna alamar ba ta san shi ba, ta kuma qara da cewa, “A’a”. “Za ki iya tunawa kin tava ganin shi ko da sau xaya ne a rayuwarki?” Ta tave baki ta ce, “A’a”. Mus’ab ya gama sauraron ta zuciyarshi cike da mamaki, bai ce mata komai ba sigarinshi kawai yake sha cikin nutsuwa. Ya miqa hannu ya jawo Saddiqa daga cikin motar ba tare da wani ya lura da lokacin da ya yi hakan ba, sai kawai ganinta aka yi a tsaye yana riqe da ita ya mayar da qofar motar ya rufe. “Ba fa za ka je ko ina da yarinyar nan ba”. In ji mai mujallah. “Kai waye da za ka hanani yin hakan?” Mus’ab ya buqaci sani. Yasa hannu a cikin aljihun gaban rigarshi ya zaro kati (conplimentry card) xinshi ya miqawa Mus’ab ya karva ya gani. Lauya ne mai zaman kanshi, ya saki katin ya faxi a qasa sannan ya yi mishi lalataccen kallo tare da tambayarshi “To sai me?” Kallon da tambayar suka tunzura shi ya ce, “Sai ka san ba za ka ko ina da ita ba tunda ko matarka ce sai ina tana son zama da kai, don haka ni zan tafi da ita in kaita gaban iyayenta, in kana sonta sai ka bita can ka same ta ku sasanta, amma baka tsare mu a jeji ka cireta a cikin mota ba bayan mun san mugaye sun yi yawa”. “Kana da wata shaida ne Yallavai da za ta nuna ita xin iyalinka ce?” Wani daga cikin fasinjojin ne ya yi tambayar. Mus’ab ya kalle shi a nutse cikin kwanciyar hankali ya ce mishi, “Babu”. “To tunda shi da kanshi ya ce babu shiga mota mu tafi kin ji, ya tsai damu yana vata mana lokaci”. Mai mujallah ne yake wannan bayanin. “Wasu mutanen basu da hankali, mace ba ta son su sai suje su baiwa iyayenta kuxi su aura musu ita a kan dole”. Saddiqa ta yunqura za ta shiga motar Mus’ab yasa hannu ya kama hannunta ya riqe. “Da kin sallame su sun tafi kar ki yi ta vata musu lokaci”. Ya zuba mata ido yana kallon cikin idonta. Ita kuma ta fara kuka tana faxin “Ka sake ni, ka sakar min hannuna ban sanka ba”. Ta shiga kici-kici da qoqarin qwatar kanta daga gare shi. “Malam in ma matarka ce ba ta sonka”. Mai mujallah yasa baki, ya kuma yi nufin taimakon Saddiqa ta qwaci kanta wurin Mus’ab. Mus’ab ya yi maza ya saki hannun Saddiqa dake hannunshi, cikin zafin nama ya taqarqare ya danqarawa mutumin naushi mai qarfi a muqamuqi, abin da ya yi sanadin faxawarshi kan mutanen dake tsaitsaye bayanshi suka tare shi daga kaiwa qasa. Ya taso fuskarshi cike da mamaki. “Ni ka buga? Za ka yi dana sani, za ka gane ku…..” Kafin ya qarasa faxin abin da yake so ya faxan Mus’ab ya yunqura ya sake kirva mishi wani wawan naushi. Wuri ya kaure da hargowa, jama’a suka kasu kashi biyu dake qoqarin shiga tsakanin daben dake shirin aukuwa tsakanin Mus’ab da mai mujallah saboda tasowar da ya yi zai rama dukan da ya yi mishin. Haquri suke bayarwa a sasanta al’amarin cikin ruwan sanyi ba tare da anyi tashin hankali ba. Mus’ab yana riqe da karan sigarinshi da yake qoqarin kunnawa yana kuma sauraron maganganun da kowa yake yi, ya yin da hankalinshi da nutsuwarshi suke kan duk wani yunquri na Saddiqa. Wani dattijo ya iso wurin yana faxin, “Haba Yallavai ya ya kuna wuri kai da yaranka amma kuma rikici yake nema ya tashi a gabanku kana kallo?” Yallavai ya yi mishi bayani kan yanda Mus’ab ya zo wurin ya nemi taimakon shi da duk abin da ya faru, don haka shi a ganin shi yanzu tunda abin ya zama haka, to sai a xunguma ayi can gaba inda za a samu hukumar ‘yan sanda a awurin. Mus’ab ya ce, “Shi daga inda yake tsaye ba zai qara taku xaya zuwa gaba ba tunda ya riga ya ga abin da ya fito nema, sai dai ko a xunguma a koma gari na baya tunda shima ya wuto ofishin ‘yan sandan a can”. “Dubi nan yaro”. In ji dattijon. Mus’ab ya mai da kallon shi gare shi da girmamawa. “Gaya min gaskiya ka ga tsayawa nan ta yi yawa, inda muka dosa nan ba nan kusa bane arewa fa zamu. Me ke tsakaninka da wannan yarinyar?” Mus’ab ya kalle shi cikin girmamawa ya ce, “Baba qanwata ce, kakanninmu xaya, mahaifinta wan mahaifiyata ne a wurinshi na girma, shine kuma ya bani ita matata ce”. “Kai ku tafi ku barshi da matarshi kowa ya shiga mota ya nufi inda za shi”. In ji dattijon. Mutanen da tsayuwar ta riga ta gundiresu suka nufi motocinsu suna tsaki tare da faxin “MATA! Hum sai a barsu kawai”. Mai mujallah kuwa tsayawa ya yi ya ce, “To ai ita yarinyar ba ta gaskata maganar ba balle mu yarda da gaskiyarshi”. Dattijo ya kalli Saddiqa ya ce, “Yarinya ba ki yi kama da mutuniyar banza ba, abin da ya faxa gaskiya ne ko akwai gyara a ciki?” Ta ce, “Gaskiya ne”. Ya kalli mai mujallah ya ce, “To kai ka ji”. Nan da nan jama’a suka watse aka bar Saddiqa da Mus’ab suna tsaye cirko-cirko, hatta Yallavai ya koma wurin sauran ‘yan sanda sun koma kan aikinsu. Mus’ab ya kalli Saddiqa cikin murmushi ya ce, “To ya ya kenan? Waxanda kika sani sun tafi sun barki da wanda baki sani ba, ya ya kenan? Za mu tafi gida ne ko kuwa?” Ta yi kamar ba ta ji ba, ta soma kuka. Ya kamo hannunta ya jata zuwa inda motarshi take, ya buxe ya sanya ta a cikin wurin mai zaman banza ya rufe, sannan ya juya ya koma nashi wurin ya shiga ya zauna. Sai da ya kunna sigarinshi ya sanya a baki kafin ya juya kan motar ta nufi inda ya fito, bayan ya yi sallama da su yallavai. Sun fara tafiya ko wani nisa basu yi ba Saddiqa ta soma kwara amai, nan take ya tuna kalaman Innarshi. “Saddiqa da kake gani warin sigari ma sa ta amai yake yi balle a ce ta ji warin barasa a jikin mijinta”. Ya yi maza ya wurgar da sigarin tare da sauke gilasan motar saboda samun tsarkakakkiyar iska. “Ki yi haquri Aisha na mance bakya son hayaqin sigari”. Ba ta yi magana ba in ban da kukan da take yi, duk da tsayuwar da ya yi don ta gyara jikinta ta kuma xan huta. Mus’ab ya biyo Saddiqa xakinta da shigarsu gidan. “Ina kika samu kuxin motar da kika biyasu?” Ta yi shiru ta qi yin magana. “Ni dai na san tun zuwanki wurina ban tava baki kwabo ba, da abokaina suka zo ganinki suka baki kuxi ma na karve, saboda dama ni zuciyata ba ta kwanta dake ba, na daxe ina ganin kamar za ki iya aikata abin da kika aikatan, shine kika gudu ashe ba kuskure na yi ba. Wato ke kina nufin za ki iya yin dalilin da mahaifiyata za ta qara yin fushi dani? Kina nufin bayan duk abin da kika sani na tsakanina da ita za ki iya yin dalilin da zai fi haka rashin daxi? In bakya sona ai ba zan tilasta ki zama dani ba, ni wani irin mutum ne da yake girmama abin da yake son shi. Ko da kika ga na bi hanyoyin da na bi wajen karvar auren ki na lura da quruciyar dake gareki ne, sai kuma na ga ni za a gwada min qarfi, amma in bakya sona ai zan iya yin haquri ba zan so kaina a kanki, zan mutunta al’amarinki in bi son zuciyarki tare da adalci a kai. Amma ai babu wulaqanci ko tozartarwa a tsakanina dake, ki tashi daga nan ki je ki shiga cikin qartin maza ki nufi Misau ki je ki cewa iyayenmu me?” Cikin matsanancin vacin rai yake jero kalaman nashi, don haka bai ko saurari kukan da take yi ba. “Waye ya baki kuxin mota?” Ta yi shiru. “Ko shi wannan mutumin ne ya biya miki?” Ta yi maza ta ce, “Eh”. Ya zuba mata ido shi ba abin ya xauke ta da mari ba. Ya yi qarfin halin sake tambayar ta. “A ina kika san shi?” Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, “Tare da shi muka zo daga Misau”. “Ke da shi da Abu?” Ta ce, “Eh”. “Zancen banza kenan”. Ya miqa hannu ya kamata, ya ce, “Ai duk inda mavoyar kuxin naki suke sai na gansu yau, tunda na ganeki”. Ya soma cire kayan jikinta yana watsarwa, ita kuma tana kici-kicin hana shi da qoqarin rufe abin da take ganin shi ta fi qin ya gani. Ba tare da ya saurari kukan ta ba. Lilita ya tarar xaure kan siket xin ta, ya zubawa likitar ido cikin sanyin jiki. Wannan ai lilitar Inna ce dake zuba cinikin kayan miyanta a ciki. Wato Inna ce ta baki kuxin da za ki gudu daga nan ki koma gida ke kaxai? Wai me na yi? Gaskiya ba zan bar maganar nan ba. Ya miqa hannu ya ciro lilitar don ya cire kuxin dake ciki, har da qullin magani a xaure. “TAFXIJAM! Har da magani ta baki ki rinqa saka min?” Ya zuba mata ido yana kallon ta. “To bari Kawu Gixe zan kai wa in yi mishi bayanin komai don ya ga irin abin da aka shirya min”. Jin ya ce, “Zai kai wa Kawu Gixe maganar yasa Saddiqa buxe baki ta ce mishi, “Ba Gwaggona ta bani magani ba Abu ce ta bani”. Ya ce, “A’a, babu ruwan Abu, ita za ta yarda a qwareni ne? Kuma in ma ita ta bakin na yarda ni gara min magani da a baki kuxin motar da za ki gudu ki bar gidana ba tare da izini ba, ko wannan xan fitan da kika yi kin san iyakacin mutanen da kika tayarwa da hankali? Ba gara a tara miki magunguna ba, za ki ba masu mota magani ne su xauke ki a motar haya?” “Is any one at home?” Wannan kalmar da Mus’ab ya jiwo ita ta katse shi, a lokaci guda kuma ta jefa shi cikin fargaba da faxuwar gaba mai tsanani saboda fahimtar muryar da ta yi maganar. Jennifer ce, to me ya kawo ta? Ya fito falon da nufin fita waje inda take, sai kawai ya ganta cikin falon zaune kan kujera riqe da karan sigarinta a hannu tana zuqa, ga kuma kwalbar giyarta a gabanta. Mamaki ya kama shi, ya ce, “Ya ya haka Jennifer? Ya ya za ki shigowa matata wuri ba tare da kin jira ta baki izinin yin hakan ba?” Ta kalle shi a lalace kafin ta tambaye shi cewa, “Ina ne wurin nata?” “Kar mu yi haka dake Jennifer, kashe sigarin muje can wurina sai in ji abin da ya kawo ki, mai nan xin ba ta son warin sigari”. Ta yi dariya ta ce, “Ba zama da kai ta zo yi ba kenan, any way wannan ku ya shafa, ina fata ba kirana ka yi don ka gaya min abin da matarka take so da wanda ba ta so ba?” “Ni na kiraki?” Ya yi tambayar a yanayin dake bayyanar da rashin jin daxin shi, don bai son fitina da ita a lokacin. “In baka kirani ba me zai kawo ni?” Ta ja tsaki tare da tofar da yawu tuf! Nuna alamar tir bai isa ba. Hakan da ta yi ya qara fusata shi. Ya ce, “To na ji na kira ki kin zo, na ji kuma bana son ganinki don haka tashi ki fita”. Ta ce, “Ai kuma baka isa ba tunda ka kirani sai na huta, sai na shanye barasata”. Ya yi maza ya ce, “Ba a nan ba”. Ba ta saurare shi ba ta jawo ledar da kwalbar ke ciki za ta buxe. “Ba a nan ba Jennifer, kar ki neme ni da magana”. Ya yi maza ya nufo ta don ganin ba ta fasa ba, nufin shi ya hana ta yin abin da za ta yin ta hanyar fitar da ita daga falon, ta yi zumbur ta miqe, yana isowa gareta ta yi maza ta wanke mishi fuska da wani irin lafiyayyen mari mai qarfi tau! Ya ja ya tsaya ya zuba mata ido yana kallon ta zuciyarshi cike da mamaki. “Marina kika yi Jennifer?” Ta ce, “An mara, kai da kake marin mutane fa?” Ya ce, “Ai kuwa kin sayawa kanki wahala, don kuwa zan tabbatar da wannan hannun naki ya daxe baki more shi ba”. Yana rufe baki ya cafke hannun da ta yi marin da shi, yana cafkewa ta soma kururuwa saboda wahala. “Ka yi haquri Mus’ab”. Ya ce, “Haba, ai gara kar ki ba da haquri Jennifer, ai kin daxe kina burin marina na kuma daxe ina yi miki kashedin hakan, don haka tunda baki ji ba nima bari in yi abin da na yi alqawari”. “Na tuba Mus’ab”. “A’a, ai gara kar ki tuba, in kika yi haka ai baki zama cikakkiyar ‘yar iska ba”. Saddiqa ta gaji da leqen abin da ke faruwa ta koma gadonta ta hau ta zauna cikin rawar jiki da tsananin tsorata da abin da ke shirin faruwa da hannun Jennifer. Ban da duk wani mugun halinshi da Gwaggo ta sani bai da tausayi ko na anini. Ta faxi hakan cikin zuciyarta. A waje Mus’ab ya tari mai tasi ya jefa Jennifer a ciki ya miqawa mai tasin jakarta a hannunshi, ya ce, “Ku tafi ta gaya maka inda za ka kaita, in kun je ka xebi ladan aikin ka a ciki”. Ya juya ya koma cikin gidanshi inda ya bar Saddiqa. “Kukan me kike yi Aisha?” Ya miqa hannu zai tava ta, ta yi maza ta maqure a jikin bango. “Kar ka tava ni”. Ta yi mishi kashedi. “Bana son ganinka kusa dani tsoro kake bani, duk abin da Gwaggo ta gaya min game da kai haka abin yake, sa’a ma ka ci ba ta san rashin tausayinka ba da ta qara tsanarka. Na sha jin tana cewa, halinka guda xaya da ta sani shine kai xin mai tausayi ne, ba ta sani ba shima tausayin ka daina shi. Abin da ya fi komai bani mamaki cikin lamarin shine, wai Gwaggo ce ta haifeka”. Mus’ab ya miqe tsaye ya nufi toilet xin dake xakin ya barta tana kuka. Ruwan wanka ya haxa mata ya fito ya kalle ta a nutse qwarai ya ce mata. “Shiga ki yi wanka tunda kin ce bakya so in rinqa tava ki zan kiyaye al’amarinki qwarai matuqa kika kiyaye nawa, ni wani irin mutum ne da na fi so inda hali in baiwa kowa haqqinshi, ina girmama mace, in kuma ji tausayinta har in yi mata adalci. Amma kuma bana iya yiwa wacce ba ta san darajarta kanta ba, ko kuma wacce ta nemi shige iyaka”. Ya juya zai fita tare da faxin, “Amma kin san in har na je na dawo baki yi ba zan yi miki”. Ta yunqura ta tashi ta shiga toilet xin da nufin yin wankan, shi kuma ya fita waje ya kira qarti da za su tsabtace falon Saddiqa daga qazantar da ya samu na fitsarin da Jennifer ta yi ta sakewa a dalilin wahala da kuma barasar da ta zube. Saddiqa tana zaune kan kujerar gaban madubi tamkar mai shirin yin kwalliya, sai dai zuciyarta kawai take sauraro. Ko me yasa Kawu Gixe xaukan aurenta ya baiwa Yaya Mus’ab? Anya kuwa Kawu Gixe yana sonta ma kuwa? Ta zurfafa cikin tunani. Wani abin da Kawu Gixe ya tava yi mata da zai sa ta yarda eh, lallai yana yi mata so irin wanda uba ke yiwa ‘yar da ya haifa. Shigowar da Mus’ab ya yi ya katse ta. Ya zauna a gefen gadon cikin wata lallausan jallabiya, ga qamshinshi mai daxi yana tashi, da alama shima wankan ya yi. Tiren abinci da ‘ya’yan itace ya ajiye a gabanta. “Fara da wannan kafin ki ci kazar”. Yana maganar ba tare da ya kalle ta ba, bai kuma fasa yanka mata kazar ba duk da zafinta, haka nan yanayin fuskarshi bai sauya ba da alamar har lokacin ranshi a vace yake. “Kar ki sake yunqurin gudu ki ce za ki tafi gida ke kaxai, ni kaina zan iya mayar dake gida gaban Gwaggonki tunda har yanzu kuna ganin bani aurenki da Kawu Gixe ya yi kuskure ne. To na ji na yarda, tunda ita Gwaggon nine wanda ba ta so, to na ji na yarda, tunda abin haka ne na ji na yarda zan kai ki gaban Gwaggon in baku zavi…..” Kan ya qarasa ta katse shi ta hanyar hankaxa tiren abincin ya kife a qasa, ta yi maza ta miqe tsaye cikin kuka. Shima ya miqe yana kallon ta tare da mamakin abin da ya yi wanda ya jawo hakan. “Bana so, ina jin kunyarka ina kuma girmamaka, ka barni in ci gaba da hakan. Muna magana da kai kana sa sunan Gwaggo a ciki, ita ce za ka kai ni gabanta ka bamu zavin auren ka? Ka bani ni da kai mana, ko kuma don ka ga an baka ni ba da yardar ta ba sai kuma ya zama…..” Ta qara tsananta kukan da take yi. “Ki yi haquri Aisha, ki yi haquri na yi kuskure da na ambaci sunanta, to amma me yasa da za a kawo ki ba za ta yi miki irin nasihar da take yiwa sauran ba? Sai ta ce in kinga ba daidai ba ki gudu, ba za ta qarfafeki a kan ki tsaya ki taimakeni in gyara halina da take ganin a kanshi ne take qina ba?” Saddiqa ta galla mishi harara karo na farko da hakan ya tava faruwa a tsakaninsu. “Nice ma zan taimakeka ka gyara halayenka? Lallai kam”. Ya xan yi murmushi kaxan karo na farko shima tun bayan da ya neme ta ya rasa a gidan. “To shi kenan na ji in ba za ki taimake ni gyara halina ba, ai kuma bai kamata ki yi dalilin da mu’amala tsakanina da Gwaggon taki zai qara lalacewa ba ko? Kin tava tunanin inda kin yi nasarar isa gabanta ke kaxai da sunan gudu abin da zai biyo bayan hakan tsakanina da ita? Ke bakya sha’awar kyakkyawar mu’amala ta shiga tsakanina da ita? Ai har da kwaxayin hakan ya qara sani dagewa a kan auren ki Aisha, don na san tana sonki za ta yi mu’amala mai qarfi da gidana, ko ba don ni ba saboda ke. Kina tsammanin ina jin daxin abin da ke tsakanina da ita ne? Ita ta haife ni fa, nine namiji guda xaya da take da shi, don me ba za ki gyara tsakanina da ita ba sai ki nemi ya qara lalacewa?” Jikin Saddiqa ya xan yi sanyi, lura da hakan ya sa shi qara yi mata magana. “Kawu Gixe da ya bani ke ba kuskure ya yi ba Aisha, ya san ina sonki ne, ya san ba zan iya zaluntarki ba, ya san zan yi miki adalci, ya san babu wani wanda ya fini cancantar aurenki ko da kuwa a ya ya halayen nawa suke, domin nine nake zaune ni da Innata mu biyu sai aka same ki kika shigo cikinmu. Muna ta murna muna ta ina muka saka dake, muna ta sonki muna renonki cikin kulawa da tausayawa, duk da yawan kukan ki da yawan rikicinki, raina kan vaci in na ga yanda Inna ke wuni hidima da xawainiya, da daddare kuma ki hanata barci da yawan kukan ki, ta yi ta fama dake, ta yi jijjiga tana girgiza ki har sai asuba ta yi kafin ki yi barci, lokacin nan kuma ba lokacin barci bane a wurinta, za ta kwantar dake ne kawai ta miqe ta shiga wasu sabgogin. Ran nan raina ya vaci haushinki ya yi matuqar kamani na fito na zo na sameta na ce Mama bani fitinanniyar yarinyar nan ki gani ki samu ki kwanta kema ki huta kamar kowa, zan je da ita xakina in rarrasheta, in kuma kin fi so a goyata, to goya min ita a bayana ki xaure min ita ta yanda zanin ba zai kwance ba. Sai na ga ta yi murmushi ta ce min, kar ka ji haushinta komai ta yi kar ta vata maka rai yarinya ce ba ta da baki, bamu sani ba ko wani abu ke damun ta. Kalamanta kan sanyani jin tausayinki, in zauna in yi ta taya ta rarrashinki ina tausayi, ina ganin ba laifinki bane damuwa ce tasa kika hana min Innata bacci. Gari in ya waye in yi maza in yi mata ayykan da zan iya taimakonta dasu, wanki, wanke-wanke, shara, xiban ruwa duk babu abin da bana yi kafin in tafi makaranta, don ta xan samu lokacin kwantawa ta huta da rana, dana……” Qwan! Qwan! Qwan! Xim! Xim! Xim! Xum! Xum! Xum!!! Bugun qofa ake yi babu qaqqautawa. Mus’ab da Saddiqa suka zubawa juna ido saboda jin yanda ake bugun qofar. Gaba xaya suka kalli agogon dake xakin, tara saura kwata ne na dare. “Iko sai Ubangiji, ko waye kuma yanzu?” Mus’ab ya kalle ta jikinshi a sanyaye. “Ki yi haquri Aisha bana nufin vata miki rai, ban kuma karvi aurenki don in saki ki yi baqin ciki ba”. Ya miqe ya nufi inda ake bugun qofar, a zuciyarshi yana tunanin to ko dai Jennifer ce ta turo mishi ‘yan iska don su xaukar mata fansa kan abin da ya yi mata? Ubangiji dai yasa ba wata fitinar ce ta sake biyo shi har gida ba. Mus’ab ya isa qofar ya xan saurara kaxan don tantance muryar dake magana. “Anya Baba basu tashi daga gidan nan ba kuwa?” “Kai tafi can kai ma sakarai dukan qofar ne baka iya ba, kana yi kamar kana tsoro” “Zan ji tsoro kai Baba in na tarwatsa gilasan gidan nan ya ya zan yi? Masu tsada ne fa”. Ta ce, “A hau! Babu abin da za ayi maka ai jikokina ne a gidan suna nan a ciki babu wani tashin da suka yi, sun hangame bakuna ne kawai sun kwanta suna bacci, ana bacci kamar na mutuwa to ba a tunanin komai balle a rage dare a xan yi nafilfili”. “Abu ce”. Zuciyar Mus’ab ta gaya mishi. “Me ya sake dawo da Abu yanzu?” Ya tambayi kanshi cikin tsananin faxuwar gaba. “Yanzu haka Inna ce ta turo ta”. Ya juya ya koma wurin Saddiqa ba tare da ya buxe qofar ba, duk da su ma basu daina dukan da suke yi mata ba. “Aisha, Abu ce ta zo”. “Abu?” Ta yi tambayar a yanayi na tsananin mamaki tare da dirowa daga gadonta. Mus’ab ya juya don komawa ya buxe musu qofar ta yi maza ta ce mishi, “Ka shigar da ita wurinka kar ka kawo ta nan”. Ya ce mata, “To”. Mus’ab ya isa jikin qofar yasa hannu yana buxewa tare da tambayar, “Waxanne baqi ne haka basa sallama sai dukan qofa?” “Kai tafi can ka bani wuri, a ga qato kamar ka a ce wai shi ake bugawa qofa haka saboda yana bacci bai farka ba, ai kuwa dai ya ji kunya”. Ya yi murmushi ya ce, “Abu kenan, to ba a gidana nake ba?” Ya shigar dasu qayataccen falonshi daga ita har direban. “Sannunku da zuwa”. Ya sake yi musu gaisuwar bayan sun samu wuri sun zauna, shima ya koma wata kujerar ya zauna. Saddiqa ta shigo falon cikin kwalliyar burgewa, ga shi ta yane jikinta da gyale sai qamshi take yi. “Wa ya vata miki rai a hanya Abu na ji kamar kina faxa?” Abu ta harareta ta ce, “Yanzu idonku biyu ake ta buga qofar nan baku fito kun buxe ba?” Ta yi murmushi ta ce, “Hirar amarci fa muke yi”. Ta ajiye tiren da ta shigo da shi a gaban Abu ta koma ta sake shiryowa direban nashi ta ajiye mishi, bayan ta gaishe shi ta koma kusa da Mus’ab ta zauna a gefen kujerarshi. Mus’ab ya sallami direban da ya kawo Abu tare da alheri mai yawa, ya dawo ya sake zama kusa da Abun yana taya ta matsa qafafuwanta da take yi. “Ai kin wahala da yawa ne Abu, kwanan nan kika tafi kin sake dawowa, wannan tafiyar ai ta yiwa jikinki tsanani. In ce ko dai lafiya?” Abu ta ce, “Ina fa lafiya, fitinanniyar uwarku mana ta yi sanadin tasowata wai ita za ta zo ta ga halin da na baro mata ‘yarta a ciki saboda hankalinta bai kwanta. Ko da yake dai nima nawa hankalin ba kwanciyar ya yi ba, saboda yanayin da na barku a ciki”. Ta basu labarin al’amuran duka. Saddiqa ta miqe ta nufi kicin tana cewa, “A’a, Abu ni bana son haka, in za ku yi maganarku ku yi amma ban da Gwaggona a ciki, Gwaggo ce za ta turoki ki zo ki ganan mata halin da nake ciki hankalinta bai kwanta ba, wa take yiwa haka a cikin surukanta? In kin ji marmarin ganina kin zo kawai ki ce kin ji marmarin ganina, amma ba ki ce Gwaggona ta turo ki ba”. “Ka ji ta ko? Ka ji min ja’irar yarinya ko? Wani marmarin ganinki za a yi? Na sani da uwar taku ta ce za ta zo in barta ta zo da kanta tunda baki ga abin arzikin da na yi ba”. “Qyale ta Abu mu yi zancenmu”. “Kun zauna lafiya ne?” Ta yi tambayar cikin raxa wai kar Saddiqa ta ji. Ya xan kalle ta a yanayi na murmushi ya ce, “Me kika gani yasa kika tambaya?” Kan ta sake gaya mishi abin da ta ganin Saddiqa ta fito riqe da kwanon farfesu ta ajiye mata, ta koma kusa da Mus’ab ta zauna. “To kin ce Gwaggo ce ta turoki ki yi bincike in muna zaune lafiya mene ne? Ina ce dama don kin san zamu zauna lafiyan ne yasa kika gudu kika barni?” Mus’ab ya ce, “Rabu da ita Abu ba ta so ne in gaya miki gaskiya, sai dai abin da nake so ki sani shine, ko na zauna lafiya da Aisha ko wane irin hali nake ciki ba zan sake daxewa ban zo Misau ba, ba zan barki ki ji marmarin ganina baki ganni ba Abu, saboda na san kina sona”. Ta ji daxin maganar tashi, nan take ta yi ta sa mishi albarka. Sun yi hira gaba xayansu har suka kai lokacin da Aisha ta ce mata dare ya yi Abu muje in rakaki ki yi wanka ki sha magani ki kwanta don ki huta gajiyarki”. Ta ce mata, “To”. Mus’ab yana zaune a falon cikin tunani za ta dawo ne ko za ta zauna a can, sai gata ta shigo. Kwanukan dake wurin ta kwashe za ta fita dasu. “Ke nake jira fa Aisha”. Ba ta yi magana ba ta tafi ta dawo. “To zo daga nan mana ya ya za ki zauna kuma a can?” Ta ce, “A’a, nan xin ma ya yi”. Ya qara gane don Abu ta yi abubuwan da ta yin duka. “Ina ce nan za ki zo mu kwana?” Cikin nutsuwa ta kalle shi ta ce, “Saboda me?” “Saboda shine abin da ya dace ki yi, kema kin sani ko ba a gaya miki ba abubuwan da kike yi min sun yi yawa, bai dace a ce kina yiwa mijinki haka ba”. Ba ta kalle shi ba ta ce, “Ba ka ce za ka kaini gaban Gwaggona ka bamu zavi ba?” Ya yi murmushi ya ce, “Wannan maganar ba ta wuce ba”. Ya taso daga inda yake zaune ya zo wurinta yasa hannu ya sureta, ya ce, “Tunda kin riga kin kawo kanki falon bari kawai in qarasa dake cikin xakin kawai”. Ya zaunar da ita a kan gadon ya koma gefe ya zauna. “Ina ce wannan maganar mun gama ta, kuma in bakya so in rinqa sa sunanta a cikin maganarmu ke me yasa kike yi min abin da kika ga dama? Yanzu kina nufin inda kin san zan kai qararki wurinta ta yi hukunci a tsakaninmu za ki rinqa yin irin waxannan abubuwan? Yanzu su Bilki za su yi haka?” Shi da kanshi ya baiwa kanshi amsar “Ba za suyi ba, saboda sun san mazansu suna da….” Bai qarasa ba ya yi murmushi saboda kallon da Saddiqan ta yi mishi, ya canza maganar tasu da tambayar ta. “Me kike ganin za ki yiwa Abu na karyawa da safe?” Ta ce, “Da zai yiwu waina da miya ko funkaso”. Ya yi maza ya ce, “To muje kicin xin mana in taya ki ki duba abubuwan”. Qarfe xaya ta yi lokacin da suka gama haxa qullin masar da na funkason, sannan ya tasota a gaba suka dawo xakin shi, ta shiga banxakinshi ta xauro alwalarta ta fito, ta zo ta zauna a bakin gadon ta yi addu’o’in da za ta yi tun daga suratul Mulk, Qulhuwa, Falaqi, Nasi, Ayatulkursiyu da sauran addu’o’inta, ta shafe jikinta sannan ta wuce can qarshen gadon ta kwanta. “Amma a irin shirin kwanciyar da kika yi ta hanyar neman lada da albarkar daren ya dace ki yiwa mijinki irin wannan juya bayan? Sannan ko abin arzikin da na yi miki ma yau baki gani ba”. A hankali ta tambaye shi “Me ka yi min?” “Ai ba ki ma lura kin gane ba? To babu laifi, yanzu yau rabon da in sha sigari tun yaushe?” Ba ta kalle shi ba ta ce, “Saboda Abu dai?” “Abu ai ta saba ganina ina shan sigari Aisha, in don ita ne zan sha iyaka ta roqa min shiriya”. Ba ta kalle shi ba ta ce, “To na gode”. Ya ja jikinshi ya isa gareta ya ce, “Tukwici za ki bani ba godiya ba”. Yasa hannu ya juyo da ita gareshi ya yi maza ya qanqameta jikinshi, tsawon lokaci yana sumbatarta tare da lugwigwita duk wata gava ta jikinta, da qyar ta samu ya sake ta. Ta miqe a hankali ta tashi, ya miqa hannu ya kamota ya ce, “Ina za ki?” Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Xakina”. “Zo ki yi kwanciyarki ba zan sake tava ki ba”. Ya juya bayanshi ya barta ita ma ta gyara kwanciyarta. Kusan minti goma sha biyar da kwanciyar tasu ya kira sunanta a hankali, ga zaton shi zai ji tana bacci sai ya ji ta amsa, zuciyarshi ta yi mishi daxi jin ita ma ba ta yi bacci ba. “So nake na sha sigari”. Da sauri ta miqe ta zauna a firgice qwarai ta tambaye shi. “Sigari fa ka ce?” “Eh, na kasa bacci ne, bana zaton zan iya bacci in ba shi na sha ba”. “To bari in je xakina kawai”. “Kina nufin saboda zan sha sigari sai ki nunawa Abu abin da muke ciki ba za ki rufa min asiri a gabanta ba, in ta san mun zauna lafiya ai daxi za ta ji, kin sani sarai saboda ke ta dawo garin nan”. “Saboda ni?” Ya ce, “Eh mana, saboda ke”. Ya faxi hakan daidai lokacin da ya miqa hannu ya xauko ta daga inda take ya kifata a kan qirjinshi, ya kuma zagayeta da hannayenshi duka biyu ta yanda ba za ta zame ta sauka ba. “Haka Inna take yi miki sanda kike damunta da rikicinki Aisha”. Tsawon lokaci yana yi mata kalamai masu daxi kafin ya soma tsotson bakinta cikin nutsuwa, babu alamar za ta bijire mishi kan abin da yake yin. Suna cikin wannan halin suka jiwo kiran sallar asuba daga masallacinsu, don haka suka tashi suka yi shirin yin sallah. Suna idarwa Mus’ab ya shiga xakinshi ya kwanta don ya samu ya xan yi bacci kafin ya fita ofis. Ita kam Saddiqa kicin ta nufa ta kama aikinta, kafin qarfe takwas tuni har ta gama aikinta ta shirya komai ta yi wanka ta yi kwalliyar ta, ta nufi wurin Mus’ab cikin qamshinta mai daxi don tashin sa daga baccin da yake yi. Saddiqa da Abu suna falonta suna hira bayan sun gama karyawa, Mus’ab ya shigo yana qamshi, ofis zai fita, bai zauna ba ya ce, “Abu bari in je ofis in dawo sai mu gaisa sosai na riga na makara”. Ta ce, “To, a dawo lafiya, Ubangiji ya kiyaye”. Ya ce, “Amin”. Saddiqa ta vata rai ta ce, “Ba ka karya ba za ka fita?” “Na makara ne fa”. Ta xaure fuska sosai ta ce, “Ko kuma kana da wani wurin karyawar ba?” Ya yi murmushi. Abu kuwa ta galla mata harara tare da jan tsaki. A hankali ya ce, “Ban kunun gyaxar kofi xaya”. Ta zuba ta miqa mishi ya karva ya shanye, ya yi musu sallama ya tafi. Mus’ab ya isa ofis ko zama bai yi ba qawayen Jennifer suka tare shi da labarin rashin lafiyar ta da kwanciyar ta a asibiti, sai dai wai ta qi faxin wanda ya yi mata abin. Ya nuna musu jimaminshi kan abin da ya faru, ya kuma ce musu zai dubo ta da zarar ya rage ayukan dake gabanshi. Suna barin ofis xin ya koma kan ayukanshi, har zuwa lokacin da Sarah ta iso. Tana zaune a gabanshi ta fiddo kwalin sigarinta daga jakarta ta kunna ta miqa mishi, ya ce, “A’a, Sarah sha kawai”. Ta zuba mishi ido fuskarta a yatsine. “Ba ka da lafiya ne?” Ya ce, “A’a, lafiyata qalau ina dai son rage yawan abin da nake sha ne, matata ba ta son warin taba, kinga yau ma tun a wurin wanka da na sha biyu sai xazu da na sake sha, ina ganin kuma ba zan sake sha ba sai na kusa tashi daga ofis kafin in je gida”. Ta kalle shi ta tave baki ta ce, “Yana da kyau”. Tasa hannu cikin jakarta ta zaro wani kati ta miqa mishi ya karva ya duba cikin nazari, kafin ya xago kanshi ya kalle tana murmushi. “Barthday xin Diana ne ai ka santa, ban yi inviting xin kowa ba in ban da kai, ina fata ba za ka yi min irin na jiya ba na yi ta zaman jiranka baka zo ba”. A hankali ya ajiye katin hefen tebur xin dake gabanshi ya haxa hannayenshi wuri xaya ya zuba mata ido cikin nutsuwa, ya ce mata, “Ki yi haquri Sarah, gaskiya idan na sake yi miki alqawari ban cika ba ranki zai fi haka vaci, kin san matata yarinya ce qarama ba zai yiwu in rinqa raba dare a waje ba ina barinta ita a gida”. Ta zuba mishi ido tana kallonshi tare da qoqarin voye vacin ranta. “Amma kai ne ka ce min don ka yi aure ba wai yana nufin mun rabu bane”. Ya ce, “Eh, amma ba ina nufin zan ci gaba da irin waxannan abubuwan bane, amma ai ba zamu daina gaisawa ba”. Ta miqe tsaye ta suri jakarta ta ce, “To sai anjima mijin jinjira”. Ta fita ta barshi yana kallon qofar da ta buga mishi, tsawon lokaci yana kallon qofar kafin ya miqa hannu ya xauki kan wayar dake gabanshi. Gidanshi ya kira, ya jiwo muryar Saddiqa tana amsa sallamar da ya yi. A hankali ya kira sunanta. “Aisha baki ga kamar in dawo gida in same ki yanzu zai fiye mana komai daidaituwa ba?” Ta gane abin da yake nufi, cikin nutsuwa ta ce mishi, “Eh, to amma sai ka yi min rantsuwar tun zuwan ka ofis yau baka tava wata mace da hannunka ba?” Ya mai da kan wayar ya ajiye a mazauninta, cikin ranshi yana tunanin irin karvar da ya yiwa Sarah lokacin da ta zo. Wayar ta yi qara yasa hannu ya xauka cikin mamakin yanda nan da nan daga ajiyewarshi ta bugo. “Ya ya dai Aisha, in zo xin ne?” “Ai baka amsa min ba, abin da kake son ci za ka gaya min in shirya maka”. “Komai kika yi zan ci amma gani nan ma zuwa gidan mu yi maganar gani ga ki. Kin canza shimfixar xakin nan?” Ta yi kamar ba za ta amsa ba, a hankali ta ce mishi, “Eh”. “To ki yi min kwalliya irin wacce za ta sani in xan ji sanyi”. Ta ce, “To sai ka zo”. Mus’ab yana zaune a gida da daddare suna hira bayan sun gama cin abincin da Saddiqa ta yi musu shi da Abu, ya yin da ita kuma take ta kaiwa da kawowa tsakanin wurinta da kicin, bayan ta sha kwalliya sai sheqi take yi. “Ni me Saddiqa ke yi ne ta dame mu da zarya?” Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Abu kenan, gidanta ne fa ki ce kar ta yi zarya?” Sai da ta gama kawo musu tsiren da ta yi musu na naman rago suka xan yi hira, sai ta miqe ta ce, “Ni zani in kwanta Abu sai da safe”. Abu ta bita da kallo ta ce, “Ki ce kawai kin gaji da zaman mijinki a nan kina so ku tafi, to ku je sai da safe, tashi ka bita”. “A’a, Abu ba abin da take nufi ba kenan, baki ga sammakon da ta yi ta toya miki waina da funkaso ba kina ta santinshi”. Ta gyaxa kai ta ce, “Na gani, gobe ma kuma shi nake so in sake ci”. Ya ce, “A to, in ba ta kwanta da wuri ba ai sai ta kasa tashi”. Ta ce, “Haka ne, to ku je sai da safe”. Kayan baccin da ta samu a kan gadon ta xauka ta sanya saboda tana so ta xan yi mishi abin da zai ji daxi ko da babu yawa. Ba ta daxe da kwanciyar ba ya shigo, wutar xakin ya kunna hasken ya bayyana, ta yi maza ta ja abin rufa ta rufe jikinta, zuciyarshi ta yi mishi daxi saboda ganin ta bi umarnin da ya yi mata. Ya canza wutar zuwa mara haske kafin ya isa gadon. Ta yi maza ta kawar da fuskarta gefe saboda ganin yanayin da ya zo gadon a ciki. Ya miqa hannu a hankali ya juyo da ita gareshi. “Daina juyawa mijinki baya Aisha babu kyau, dakata ki gani, tsaya ki ji abin da zan gaya miki”. Hankalinta a tashe saboda gane abin da yake son yi da ta yi. “Ni mu bari sai Abu ta tafi”. Ta faxi hakan cikin murya mai rawa. “Ai babu ruwanmu da Abu, Aisha muna wurinmu ne tana nata, ba ta zo gidanmu don ta takura mana ba, ta zo ne don ta tabbatar da zaman lafiyarmu, in ta kama zamu iya zama da ita gida xaya muna sha’aninmu tana nata. Saurareni kawai ki ji”. Ta kama kuka tana faxin, “Ba ta so”. Sai dai hakan bai sa ya saurara ko ya haqura da abin da yake nufin ba. Kar dai na wahalar da ita? Ya faxi saboda ganin yanda jikinta ke vari. “Aisha”. Ba ta yi magana ba, ba ta kuma bar kukan da take yi ba. Miqewa ya yi ya shiga banxaki ya zuba ruwan zafi ya zo ya xauke ta ya je ya tsoma a ciki, ya yi mata abin da yake ganin ya dace ya yi mata, sannan ya yi mata wankan sabulu, ya kuma ba ta umarnin ta yi wankan ibada, ya fito ya canza musu shimfixar gadon. A hankali ta hau kai ta kwanta saboda tsabtace shi da ya yi, a haka suka kwana da Saddiqa, in ban da ajiyar zuciya babu abin da take yi. Ba ta samu rintsawa ba sai bayan da suka yi sallar asuba. Ganin haka yasa shi gyara mata rufa ya fito ya shiga kicin xinta wai zai toyawa Abu wainar da ta ce yau ma in so samu ne ita za ta ci. Ba a je ko ina da fara tuyan nashi ba ya kama tari babu qaqqautawa, ita ma Abu ta fito daga wurinta tana faxin “Kai wannan tuya yau dai kam ya yi gardama, ya ya aka yi? Ta jiya ai qamshinta kake ji gwanin daxi ba irin wannan qaurin ba”. Suna haxa ido da Mus’ab ta ja ta tsaya ta yi turus. “Au! Haba, yau kai ne mai tuyan ina matar gidan?” Ya kalle ta ya ce, “Na karveta ne ta xan huta, ko za ki taimakeni ne kema ki karveni?” Ta ce, “A’a, a na me tunda ka karve ta ai ka iya ne, gara kawai ka qarasa”. Ta juya tana cewa, “In ban da saunanci mene ne haka? Mace tana can a kwance shememe miji yana kicin yana fama da aikin abinci, sai ya gama ya tasota ta zo ta ci ko?” Mus’ab ya ce, “A’a, Abu yau dai don Aisha nake yiwa shi yasa kika kira abin saunanci, amma ni kam tun yaushe nake karvarki girgi kina zaune in yi tankaxe, in yi talge, in kaxa miya a gidanki, ai na yi shi ya fi sau nawa?” Ta ce, “To ai shi kenan ka tsayar da wannan qaurin da yake yi don hayaqinshi yana sirqeni ya sani tari”. Shi da kanshi ya san qaurin ba mai daxi bane irin na jiya, ga shi kuma duk sun qone, mafi yawancinsu ma sun gutsittsire basu da wani sha’awa, ya kuma san Abu da halinta babu yanda za a yi ta ci abincin da bai mata kyau a ido ba, ko xanxano a baki, don haka ne ya yiwa kanshi qiyamun lailai ya tattara ya ajiye tuyar ya shiga shirya musu wani abin karyawar na daban. Nan da nan ya gama. Yana tsabtace wurin sai ga Abun ta sake dawowa. “Ni in ce ko dai ba kukan yarinyar nan na ji jiya da daddare ba?” Bai kalleta ba ya tambaye ta, “Wacce yarinyar?” Ta ce, “Saddiqa”. Idonshi yana kan aikinshi ya ce mata, “Ita ce Abu”. Ta xan yi shiru kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta sake tambayar shi, “In ce ko dai lafiya?” Ya ce, “Lafiya qalau, mafarki ta yi wai damatsirin gidanki sun cijeta”. Shaqiyancin da ta ji ya shigar cikin maganar ya sata wucewa ta tafi ta ba shi wuri tare da faxin “To madallah”. Ya gama shiryawa Abu abin karyawar da ya shirya matan a gabanta, ta zuba mishi ido tana kallo, ya xaga ya kalle ta saboda shirun da ya ji ta yi. Kallon da take yiwa abin karyawar yasa shi murmushi. “To baki yi min addu’a irin wacce na ji kina yiwa Saddiqa ba jiya da ta kawo miki abin karyawa ba”. Fuskarta a xaure ta ce mishi, “Addu’ar me zan yi maka bayan ka hana yarinya ta zo ta yi min abin da zan iya ci, wannan duk ai ba abincina bane”. “Ba hanata na yi ba Abu”. “To me ka yi?” Ya xan yi shiru kafin ya ce, “Jiya ne ranar aikinta yau kuma nawa”. Ta yi tsaki ta ce, “Ai sai ka yi ta yi, jeka ni ka xumami miyar wainar da na ga yarinyar nan tana shiryawa da daddare ka xebo ka haxo min da wainar da ka toya in tsinci wacce zan iya tsomawa cikin miyar in ci ko don sha’awarta”. Ya ce, “To Abu yanzu kuwa”. Yana gama kawo mata abin da take so ya yi maza ya nufi wurinshi, bai saurari maganar da take yi na “To ya ya za ku watse ku barni ni kaxai in karya?” Yana tura qofar xakin ya ga ta buxe ido, a hankali ya matsa kusa da ita. “Sannu Aisha, bari in kira Dr. Usman ya zo ya xan taimaka miki don tun xazu na ji jikinki da xumi”. Ta xan kalle shi na xan wani lokaci ta kawar da kai, ya yin da zuciyarta ke raya mata Yaya Mus’ab wane iri ne? Abin kunya ba ya ba shi kunya. Ya kira likita ya ce mishi me? Sanin da ta yi matuqar tana wurin zai kira likitan ya sata miqewa cikin qarfin hali ta nufi wurinta, in ban da haka da ita kam yau ba ta yarda ta haxa ido da kowa ba. Tana tafiya yana binta a baya. “Aisha! Aisha tsaya mana ki saurare ni”. Ba ta kula shi ba balle ta saurari wata magana. Abu ta na zaune a falo tana jan carbinta bayan ta idar da sallar walaha, ta kammala addu’o’inta. Saddiqa ta wuceta ta shiga xakinta ta hau gado ta kwanta. Da sauri Abu ta bi bayan ta. “Lafiya dai ko Saddiqa? Ko baki ji daxi bane?” Ta yi tambayar daidai ta xora hannu a kanta. Ba ta yi magana ba ta soma kuka. “A’a, mene ne na kuka kuma Saddiqa? In ba a da lafiya saia yi kuka?” Tana maganar tana nazarinta. Nan da nan ta gano kan al’amarin. “Uh-uhum! Mus’ab ne ya vata miki rai?” Ta yi tambayar tare da zama a bakin gadon. Saddiqa tana jin ta ambaci sunanshi ta kawar da kanta daga kallonta ta juya kallon bango tare da tsananta kukan da take yi. “Yi haquri, yi haquri, yi haquri shatuwallena, yi haquri ‘yar Gwaggonta ba qwararki ya yi ba, bai kuma zalunce ki ba girma ne ya ja miki, in aka girma ai haquri ake yi, sai kuma a nutsu. Shi kam ma ai ya yi haquri dake, yau kwananku nawa yana zuba miki ido, Mus’abu ai mai haquri ne. yi haquri kin ji. Ubangiji ya yi miki albarka, ya zaunar miki da aurenki lafiya, ya baki zuriya xayyiba su faranta miki rai kema kamaar yanda kika farantawa iyayenki. Bari ki gani in tashi yanzu zan yi miki maganin ciwon da jikinki ke yi”. Ta tashi tana shirin abin da za ta yi Mus’ab ya shigo. “Abu likita ya zo duba Aisha”. Abu ta galla mishi harara. “Kai kar ka damu mutane ka ji, duk wahalar da ka gana mata ba ta isheka ba sai ka kira wani likita ya sossoke mata jiki da allura, to babu inda za ta”. Ta ja tsaki tana harkar gabanta tana mita. “Shi yasa ko qwari baku da shi, to duk kashi a soke”. Mus’ab ya yi kamar bai ji kunyar kalaman nata ba, don shi kam yana son sirrin mu’amala tsakaninshi da iyalinshi. Cikin qarfin hali ya ce, “Abu da kun bari an duba ta jikin nata babu lafiya”. “Ai ba rashin lafiya take yi ba wahalar da ka ba ta ne ya xumama mata jikin, saboda baka da haquri. Ai ni bana son rashin haquri, in aka yi haquri aka bi a hankali ma mene ne wata rana ba sai labari ba?” Kalaman Abu suka gunduri Mus’ab, ya juya ya fita ya je ya sallami likitan dan ya san Abu ba za ta bar Saddiqa ta fito ba. Ya yi kamar ya bi bayan likitan shima ya yi tafiyarshi don kalaman nata suna sa shi jin kunyarta da yawa. To amma in ya yi haka ita Saddiqa fa? Ya shiga wurinshi ya gama abin da zai yi ya fito cikin shiri da qamshi, ya sake komawa wurin nasu har lokacin Saddiqa tana kwance, bacci take ko ido biyu bai sani ba. Ya kalli Abu cikin yanayin murmushi ya ce, “Amma Abu…..” Bai qarasa ba ya yi shiru, ta gane inda ya dosa. Ta xan taya shi murmushin haxi da cewa, “Babu komai jeka abinka ka dawo za ka zo ka samu matarka ta yi tsaf na kintsa maka ita, ruwan zafi ai shine maganinshi sadidan, sai ko gasasshen nama, farfesu da kuma yaji-yaji, wannan kuwa duk akwai a gidan zan kula maka da ita”. Ya ce, “To Abu”. Ya juya zai tafi ta yi maza ta sake kiranshi. “To zo mana”. Ya dawo yana sauraron ta. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Zanin gadon naku za ka xauko min in tafiwa uwarku da shi don ya zama mata albishir”. Mus’ab ya tsuke fuska ya ce, “A’a, Abu ni bana son irin wannan abin da kuke yi tonon asiri ne kawai”. Nan da nan ta taso cikin fushi, “Za ka bani zanin gadon ne ko sai ka yi dalilin vacin raina a gidanka?” Ya yi maza ya ce, “A’a, Abu wane ni in vata miki rai”. Ta ce, “To maza xauko ka kawo min”. Ya ce, “To”. Ya je ya kawo mata ya juya ya fita ya barta rungume da zanin gadon tana ta faman sanya musu albarka. Ofis rannan a nishaxi mai yawa Mus’ab yake, ba yau ya fara sanin mace ba a rayuwarshi, amma bai tava samun kansa cikin nishaxin da ya samu kanshi ba jiya. Kai girma da darajar aure yawa ne da shi, in ban da shaixan ma to me za a yi da matan banza ne? Ya tuna tsawon lokacin da Kawu Gixe ya yi yana fama da shi ya yi aure yana qi, wanda inda tun a wancan lokacin ma ya furta cewar Aishan yake so ya san ba zai hana shi ita ba duk da qanqantar tata. Sannu a hankali Mus’ab ya yi ajiyar zuciya tare da lumshewar ido, cikin zuciyarshi ya yi tunanin al’amura masu yawa, kafin daga bisani ya saki wani lallausan murmushi, a hankali kuma sai ya furta sunan nata a bakinshi Aisha kenan. Kafin ya isa gidan da yamma aiken shi biyu, abubuwan amfanin gida yake ta aikewa, cikin zuciyarshi yana tunanin yana zuwa zai tura gidan Idris a kawo mishi Zainab don ta taimakawa gidan nashi. Abin mamaki yana zuwa sai ya tarar da komai a kintse a kammale a kan tsari, Saddiqa tana zaune a falonta tana cin tuwo miyar kuka da Abu ta yi da naman rago, ga yajin daddawa. Ya kalli Saddiqa ya kawar da kanshi, har lokacin idanuwanta basu wattsake daga kukan da ta yi ba, iyaka dai ta yi wanka ta kuma yi kwalliya ‘yar kaxan. Sannu da Abu tana fara’arta ta amsa, sannu da qoqari Mus’abu ka dawo ba? Ya ce mata, “Eh”. “To sannu da zuwa, Ubangiji ya yi muku albarka ya rufa muku asiri, ya kuma sa ku gama da duniya lafiya”. Ya ce mata, “Amin Abu”. Ya juya zai tafi wurinshi. Ta ce mishi, “Ga abincinka nan a kicin sai ka shiga ka xauka”. Bai kalle ta ba ya ce, “Aisha ba ta ji sauqi bane Abu? Ki bata ta kawo min mana”. Ba ta tanka mishi ba don haka ya biya ya xauka ya tafi da shi wurin nashi. Kwana biyu a jere Abu tana cikin hidimar tarirayar Saddiqa, kulawa da shagwava, har dai Mus’ab ya gundura da abin saboda ko kusa da ita ba ta barinshi yaje. Ya shiga kicin inda ya hangeta tana gashin nama, ya same ta cikin nutsuwa ya ce mata, “To wai ni Abu ni kuma ni shi kenan ne?” “Shi kenan kamar ya ya?” Ta yi tambayar tana kallon shi. Ya xan yi murmushi tare da miqa hannu wajen tayata aikin da ya tarar tana yi. “To ba kema na ji kiuna ce mata ba cutarta na yi ba, kuma ban zalunce ta ba?” Ta ce, “Eh”. Ya ce, “To tunda haka ne ba sai ki lallavata ki xan rinqa turo min ita ba, kina gani fa har yanzu ko magana na yi mata ba ta amsawa”. Abu ta yi dariya ta ce, “Naqi in lallava maka itan, ai sai daxin ya yi maka yawa, randa na tafi na barku ku biyu a gidanku ka san yanda ka yi ka lallava abinka”. Satin Abu guda a gidan ta sanar da Mus’ab shirinta na komawa Misau a kwanaki biyu masu zuwa a gaba. “Da sauri haka Abu?” Ta yi murmushi ta ce, “Ai na zauna muku Mus’ab ina laifi, in ban da gidanku kai da matarka ina za ni in yi wannan zaman?” Cikin nutsuwa da girmamawa ya ce mata, “Ai mun gode miki Abu, Ubangiji ya qarawa rayuwarki albarka”. Daga gefenta Saddiqa ta yi magana a yanayi na sanyin jiki. “Zan biki gida Abu”. Abu ta waiwaya ta kalle ta, tuni har hawaye sun fara zuba a idanuwanta. “A’a, Saddiqa dena wannan kukan ki share hawayenki ki ji abin da zan gaya miki, ki bini gida Misau kina so mujewa iyayenku da abin da zai baqanta musu rai ne? Ai ni jakadiya ce ta alheri a garesu, zan je musu ne da labari mai daxi mai faranta musu rai. Na zo na same ku lafiya, na kuma barku lafiya har ga albishir mai daxi zan je musu da shi”. Ta ci gaba da maganarta da cewa, “Aure ai girma ne, girma kuma haquri ne, don haka ki yi haquri ki zauna tare da mijinki, ki yi mishi biyayya, yi na yi bari na bari, ba ki ga irin kai kawon da yake yi a kanki ba? Yana sonki, to in kin tafi ki barshi da wa Saddiqa? Kar ki yi haka”. Mus’ab ya tashi ya tafi ya basu wuri. Tana ganin fitar Mus’ab ta qara mai da hankalinta wurin Saddiqa. “Sa hannu biyu ki rungumi al’amarin mijinki, kar ki yarda ki yi wasa da aurenki, kullum ki je ki gaishe shi, kullum ki karkaxe mishi shimfixarshi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi. Ki sa ido sosai a kan shi, kar ki yarda hannunshi ya tava wata mace in ba ke ba ce, kar ki yarda ya mai dake qaramar mace, kina gida a zaune shi yana can wurin matan banza a waje. In tafi dake gida to ki barwa wa shi? Ki barwa matan bariki ko? Ke bakya kishi ne?” Ta tsareta da ido. “Ni kuwa ai kishi ne dani, ban tava barwa wata mace mijina ba shi yasa ma bayan rasuwarshi ban yarda na sake yin wani auren ba, sai na yi zamana kawai saboda na fi so ko a lahira a ce shine mijina na aljanna cikin yardar Ubangiji”. Yanda Abu ta yiwa Saddiqa nasiha da kalamai masu daxi, haka ta zaunar da Mus’ab ta yi mishi irin wanda za ta yi mishi, sai dai shi kam ba irin rarrashin da ta yiwa Saddiqa ta yi mishi ba. “Kar ka zalunceta ka yi haquri da ita, ka yi mata adalci, ka sani ba ta da kowa a garin nan in ba kai ba”. Ya ce, “To Abu, na gode Ubangiji ya saka miki alherinki a gareni”. Ta yi murmushi ta ce, “Amin Mus’abu ya saka mana tare”. Duk kalaman da Abu ta yiwa Saddiqa na rarrashi da kwantar da hankali, da yanda zuciyar Saddiqan ya karvi maganganun da ta yi mata bai hana zuciyarta ta karaya ba har ta yi ta zubar da hawaye tana kuka tare da faxin, “Zan bi ki Abu”. A lokacin da ta ga ana ta fitar da tsarabar da Mus’ab ya yi mata ana jibgawa cikin motar da za ta mai da ita gida Misau. GARIN MISAU A RANAR ALHAMIS DA YAMMA Gwaggo Habiba tana cikin kicin xinta tana qoqarin dama kunun tsamiyar da za suyi buxa bakin azumin nafilan da suke ita da mijinta. Tsayuwar motar da ta ji ‘jiiyim’ kusa da qofar shigowa zauren gidan yasa ta fitowa da sauri ta zo ta tsaya a tsakar gidan tana kallon hanyar shigowa gidan, cikin zuciyarta tana faxin wannan motar dai da qyar in ba Inna ta kawo ba. “Assalamu alaikum”. Muryar Abu cikin fara’a da murmushi ta shigo gidan tamkar ba ta wahala a tafiyar tata ba. “Lah! Ashe kuwa ke ce Inna, Inna sannu da zuwa, dama tunda na ji tsayuwaar motar dama na ce wataqila kece a ciki, sannu da zuwa, Inna kun shawo hanya”. Suka nufi xakinta tana shimfixa mata tabarma tana faxin “Tun shekaran jiya muke sa rai dake a gidan nan”. Abu ta yi murmushi irin wanda ta daxe ba ta yi ba. “Gidan Mus’abu fa na je a yau xin ma da ya ya na baro shi? Duka yaron nan ki gani in ya gama shigo da kayan tsarabar nan ki samu abin da kika ba shi ya ci, duk da dai ba yunwa muke ji ba”. Gwaggo Habiba ta yi murmushin jin daxin yanayin da ta ga mahaifiyarta a ciki, ta nufi wajen direban tana faxin “Wannan doguwar tafiyar da kuka yiwo Inna ki ce bakwa tare da yunwa”. “A’a, baya fa ba ta kaxan, kar dai a ce xan fitar nan da na yi ne Inna ta dawo a bayana?” Abu ta yi maza ta ce mishi, “Ai kuwa dai nice malama, hala tarin tsarabar da ka gani a tsakar gidanka ne yasa ka gane hakan?” Ya ce mata, “Eh”. Ta yi murmushi ta ce, “Aikin Mus’abu kenan”. Da daddare bayan sallar isha’i Gwaggo Habiba da Abu suna falonta, sun gaisa sun ci abinci suna hira. Ta qosa qwarai Abun ta ba ta labarin yanda ta baro Saddiqa, ita kuma sai ja mata rai take yi. Malam Abdullahi ya shigo falon ya same su a dalilin ya dawo daga sallar isha’i. “Gwaggo sai yau?” Ta yi dariya ta ce, “To yau xin ma da ya ya? Ai dagewa kawai na yi na ce in dai ba tayaku zaman auren naku zan yi ba, ai gara ku barni nima in koma wurin iyalina”. Malam Abdullahi ya yi dariya, ita kam Gwaggo Habiba sai murmushi take yi, ya yin da kanta ke sunkuye. “To ya ya kika baro su Gwaggo?” Ta yi maza ta ce, “Sai alheri, ga tsaraba can ya ce a kawo a rabawa ‘yan’uwa da maqwabta, in kuma gaya maka cewar kai da Kawunshi ku yi shirin tafiya aikin Hajji, ni kuma ni da uwarsu zamu je Umara na ce mishi a’a, ni kam Hajji zan ce don ban sauke farali ba, ga kuma girma ya riga ya kama ni, gara in je tun ban kai ga ba zan iya ba. Ya ce, to sai yanda muka shawarta”. Cikin farin ciki Malam Abdullahi ya ce, “Eh to, Gwaggo ai sai ku je Hajjin ke da Yaya Gixe mu sai mu tafi Umarar da Habiba”. Abu ta ce, “A’a, ni da kai dai mu yi Hajji, ita da xan’uwanta suyi Umarar, ai tafiyar da kai za ta fi min dai-dai”. Malam Abdullahi ya ce, “To, Ubangiji ya yi musu albarka”. Abu ta yi ta faxin “Amin-amin”. Har ya tashi ya fita saboda sallamar da aka yi da shi. Gwaggo Habiba dake zaune shiru a gefe ta xago ta sake tambayar ta, “To ya ya kuwa Saddiqa Inna?” Abu ta kalle ta cikin murmushi ta ce, “Duk wannan labari da nake bayarwa bai isheki ba sai kin ji na Saddiqa ita kaxai? To lafiyarta qalau na barota tana ta hidimar aurenta, ta ce a gaisheki, ga kuma saqo ta ce in kawo miki”. Cikin sauri Gwaggo Habiba tasa hannu ta karva tana warwarewa ta ga abin da ke jikin zanin gadon ta yi maza ta rufe tana salati, cikin sanyin jiki ta kalli Abu. “Irin wannan cin zarafin ya yi mata Inna? Wannan ai rashin tausayi ne”. Abu ta galla mata harara. “Ke kam ai ba za ki yaba mishi ba, ina can ne fa abin ya faru amma baki kalli haqurin da ya yi da ita ba, kin kuma san a kan ‘yarki ne maza suka fara yin haka. Ya dai ce in gaishe ki in kuma roqa mishi ke ki yafe mishi abubuwan da ya yi miki”. Ta miqe tana tafiya tana yafa zanin rufar ta. “Ni gidana za ni in kwana, in yara sun shigo ki xora musu kayana su biyoni da shi”. Gwaggo Habiba ta bi bayanta tana faxin, “Ki huta gajiya Inna, sai na zo miki ban gajiya”. AJAKUTA Mus’ab yana zaune a qofar gidanshi cikin shirin yin alwalar sallar magariba, ya kalli agogon hannunshi bayan ya kalli yanayin sama, zuciyarshi ta raya mishi da sauran lokaci. Nan take ta sake raya mishi yanzu kam cikin yardar Ubangiji in har komai ya tafi daidai kamar yanda ake fata, to Abu ta isa gida tana can tana bai wa su Inna labarin Aisha ta kai budurcinta, ya san babu wani labari da zai fi wannan daxin bayarwa a wurin Abu. Ya xan yi shiru kaxan cikin wani tunanin, zuciyar tashi ce dai take sake tuna mishi da irin wunin da ya yi tare da Saddiqa bayan tafiyar Abu a ranar cikin kuka da takura mai yawa, wanda ya yi dalilin da ko aiki bai samu damar zuwa ba. Son shi ne ba ta yi yasa take waxannan abubuwan ko kuwa? Ya yi maza ya kawar da wannan tunanin saboda dalilai guda biyu. Na farko mu’amalarshi da ita a farko, yanda ta bijirewa auren Sadisu ta nemi a barta kawai ta yi mata yanda ita da kanta ta gayawa Gwaggonta ita xin shi take so, da yanda ita da kanta ba tare da ya nemi ta yi mishi hakan ba ta voyewa Abu halin da suke ciki a lokacin da ta zo gidan. Waxannan dalilai guda biyu sune suka qarfafa zuciyarshi ya xan ji sanyi, ya kuma qarfafa zuciyar tashi a kan himmatuwa wajen ganin ya shawo kan lamarin nashi. Hadari ya taso tare da iska mai tsanani, wanda ya yi dalilin da liman ya bayar da umarnin haxa jam’in magariba da isha’i a masallacin. Ya shigo gida daidai ruwan saman yana saukowa, zuciyarshi ta yi mishi daxi saboda sanin da ya yi Saddiqa matsoraciya ce. Wurinta ya fara isa bayan ya gama rurrufe qofofin gidan. “Kin yi sallah kuwa?” Ta amsa mishi da eh. Ya wuce ta yana tunanin irin takurar da ya ga ta yi, ina ma dai NEPA su xauke wutar lantarkin. Yana yin wannan tunanin ya miqa hannu kan mitar gidan ya kashe wutar, duu ya bayyana a ko’ina. Ya wuce ya nufi wurinshi. Bai daxe da shiga wurin nashi ba ya ji motsin Saddiqa a cikin falon nashi. “Waye aa nan?” Ya yi tambayar don ya gane maganar ne ba ta son yi. A hankali ta ce mishi, “Nice”. “Kina son wani abu ne?” Ta xan yi shiru kafin ta daure ta ce mishi, “Wuta aka xauke ni kuma bana son duhu “. Cikin nutsuwa ya ce mata, “Eh, Aisha duhu ai ba shi da daxi”. “Ko za ka sa a kunna Jean?” Ya ce, “To, sai dai ruwan ya yi yawa bai kamata in fitar da shi a cikin ruwan ba, saboda kuna Jean ai kinga babba ne mu xan bari mu gani ko ruwan zai yi sauqi”. Ta yi shiru. “Ko kina tsoro ne?” Ta ce mishi, “Eh”. Ya yi kamar ya ce ta shigo wurinshi sai ya fasa, ya fito ya zo inda take ya kama hannunta ya ce, “Muje in rakaki wurinki”. Da hikima da lallami ta yarda suka hau gadonta tare suka kwanta, shima kuma ya yi haquri ya kawar da kai daga gareta, don ya fi son shiryawarsu maimakon kara tsoratata. Sai da aka kira sallar asuba ya miqe zai yi alwala ya mai da wutar gidan. Har wajen qarfe taran safiya ba ta sake ganin ya shigo wurinta ba, ba ta ga yana shirin tafiya aiki ba. Kalmomin Abu suka faxo mata, kullum ki gaishe shi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi, kullum ki gyara mishi shimfixa. Don haka ta miqe ta nufi wurin nashi da nufin zuwa ta gaishe shi. A hankali ta tura qofar xakinshi tare da yin sallama, saboda ganin ba ta ganshi a falon ba. Ya amsa yana daga kwance a gadonshi, ta kai gwiwowinta qasa a yanayin girmamawa ta ce mishi, “Ina kwana Yaya?” Ya amsa “Lafiya lau Aisha, ya ya gidan ya kwana?” Ta ce mishi, “Lafiya, me kake so ayi maka na abin karyawa?” A hankali ya ce mata, “Huta kawai Aisha”. Ta xan kalle shi ta ce, “Ba ka da lafiya ne?” Ya zuba mata ido yana kallon ta tare da tambayar ta, “Me kika gani?” Cikin nutsuwa ta ce, “Na ganka a kwance bayan yau xin akwai aiki, kuma na ce me kake so in yi maka ka ce in huta”. Bai kawar da kanshi daga gare ta ba ya ce mata, “Bana cikin yanayin da zan ji daxin zuwa aikin yau, saboda na xan takura, in kuma abin da nake so za ki yi min ki zo kusa dani mana ki rage min damuwa ta”. Ta xan yi shiru kanta a sunkuye, a hankali sai ya ce mata, “Sai na ji kamar Abu ta yi ta yi miki magana a kan kar ki yi wasa da auren ki, na xauka ni da ke zamu yiwa nasihohin da ta yi mana biyayya Aisha”. Ba ta kalle shi ba balle ta yi mishi wata magana, sai dai hawayenta da suka soma zuba. Ya shure abin rufar nashi ya zo ya kama hannunta ya shigar da ita xakin. “Zo muje ki gaya min abin da ke saki yawan kuka. Nisa da gida da kika yi? Kina son ganin Gwaggonki ko?” Ta yi maza ta gyaxa kai nuna alamar, “Eh”. Yasa hannu ya share mata hawayen. “Ai na sani, na san kina ganin Gwaggonki nima kuma ba zan hanaki ko in qi kai ki wurinta ki ganta ba, illa iyaka dai kawai zan bari sai kin kwantar da hankalinki mun zauna lafiya tukunna, ko yau xin nan kika yarda muka fara zama lafiya, to ni kuma a shirye nake mu daidaita lokacin da zan kai ki ga Gwaggon naki”. Da irin waxannan kalaman na dabara ne da yawan nuna na fiki daxewa a duniya Mus’ab ya samu ya shawo kanta cikin ruwan sanyi, ta yarda ta miqa mishi al’amarinta ya samu ya yi yanda yake so da ita, ta kuma jurewa hakan. Wunin ran nan ko qofar gidanshi bai buxe ba sai da ya yi nufin tafiya sallar juma’a, ana idarwa kuma ya dawo gida. Haka washe gari asabar da kuma lahadi yana gida yana hutawarshi. “To Yaya yaushe zamu je wajen Gwaggo?” Sai ya yi maza ya soma lissafi. “To bari ko kwana talatin da tafiya Abu ta yi don kar a ganmu yanzu ayi zaton ko babu lafiya”. Ta ce mishi, “To”. Kwanaki talatin xin suna cika ya xauke ta ya nufi qasar Italy in da ya je ya yi hutun aikinshi na kusan watanni biyu, tafiyarshi ta farko tun bayan dawowarshi daga can inda yaje ya sadu da aminai, abokai da kuma tsofaffin malamanshi da aminanshi. A lokacin da suka dawo gida kuwa tunanin Saddiqa da tattalinta bai wuce na me za ta yi ko ya ya za ta yi ta kyautatawa mijinta ba. Watanni biyar sun cika bayan kawo Saddiqa da Abu ta yi har lokacin bai ce ga ranar zuwa gida ba, tamkar ya mance alqawarin da ya yiwa Abu na ba zai bari ta rinqa jin marmarinshi ba ta ganshi ba. Ita ma Saddiqa mafi yawancin lokaci ta kan tuna Gwaggon nata ne, ta ce kai Yaya yaushe ne za ka samu lokacin da zamu je gida ne? Ina fa marmarin ganin Gwaggona”. Ya yi tsaki ya ce, “Ai ayyuka ne bari dai mu gani daga nan zuwa qarshen watan nan. In ta ce to. To sai kuma wani jiqon in ta sake tunawa. Daga shi har ita sun zama tamkar basu ba, ko Liman da Mus’ab xin ya tasata a gaba ya kaita gaishe shi mamakin ganinta ya yi, ya cewa, Mus’ab xin yi qoqari ka kai wa iyayenku ita su ganta don su sanya maka albarka. Ya ce, “To malam”. Suna zaune a falonshi suna hira, sun gama karyawa Mus’ab ya kalle ta ya ce, “Ki gama aikinki da wuri ki shirya in anyi sallar magariba zamu je mu ga Dr. Usman”. To kawai ta ce saboda ya yi maganar ya fi a qirga, yau xin dai ya zartar da hukuncin tafiyar ne kawai. Da daddare Mus’ab da Saddiqa suna zaune gaban likita, Mus’ab ya gama yi mishi bayanin abin da ke tafe dasu. Gwaje-gwaje sosai ya yi musu, ya kuma umarcesu dasu kawo mishi wasu abubuwa na jikinsu. Bayan sunyi hakan ne ya xibar musu kwanaki uku ya ce su dawo don su ji sakamakon gwajin nasu. Sun dawo suna zaune gaban likitan wanda yake kallon takardun dake gabanshi cikin nazari kafin ya xan xago ya kalli Saddiqa ya ce mata, “Ko za ki xan jiramu a waje?” Mus’ab ya harzuqa da jin maganar tashi ya ce, “Matata ce fa, me za ka gaya min da ba za a faxa a gabanta ba?” Saddiqa ta miqe tsaye ta ce, “Babu komai Yay bari in je in jiraka a mota, in ka gama kawai sai ka sameni a can mu tafi”. Ya bita da kallo har sai da ta fita ta ja musu qofar kafin ya dawo da kallon shi wurin likita. “Me kake so ka gaya min likita wanda yasa ka korar min mata?” Likita ya ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, “Ba korarta na yi ba, bana yi maka sha’awar tashin hankali ne da ita, na san a yanda ka renita ta zama haka ba za ka so komai tsakaninka da ita ba illa zaman lafiya da kwanciyar hankali”. Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, cikin sanyin jiki ya tambaye shi “Me ya faru likita?” Ya tsare shi da ido yana kallon shi tare da sauraron abin da zai gaya mishi. “Barasa da sigari sun riga sun yiwa kayan cikinka lahani, haka nan ka daxe kana xauke da ciwon sanyi da ake samu wurin matan da basu tsaya wuri xaya ba, saboda baka kula ka xauki matakin da ya dace a kanta ba har ta yi maka illa, ka kuma san ita wannan cutar tana cikin cututtukan dake hana maza haihuwa, don tana toshe jijiyar dake fitar da qwai zuwa mahaifar mace. To ga kuma wancan matsalar da na ce maka barasa da sigari sunyi maka, ban da wannan ita ma matarka mun same ta da ciwon, sai dai bai riga ya yi mata qarfi sosai ba, na kuma san zai yiwu a wurin ka ta samu”. Mus’ab ya ji tamkar a sama yake saboda tashin hankali, gaba xaya kunnuwanshi suka daina jin komai in ban da kalaman da likita ya furta mishi sune kawai suke ta nanata kansu. “Ka yi haquri Mus’ab kar ka xauki abin da tsanani sosai, akwai magungunan da zamu baka in ba suyi ba mu canza wasu, kai dai kar ka bari matarka ta san abin da kake ciki ba wani tabbas ne dasu ba. Kar ka kalli wannan xawainiyar da ka yi a kanta ka mai da ita matar zamani ta bijire maka ba komai bane, musamman ma da yake abin ya shafi haihuwa. Don haka in ta matsa tana so ta san abin da ake ciki ni zan iya ba da result xin da zai nuna matsalar a wurinta yake, don dai ka samu zaman lafiya a gidanka. A nan asibiti kuma ba za ta samu mai gaya mata komai ba”. Mus’ab ya miqe tsaye tare da faxin “Na gode likita”. Ya fita ba tare da ya saurari rakiyar da likitan yake yi mishi ba. Saddiqa tana zaune a qasa gaban Mus’ab, kuka take yi. Ya buxe ido a hankali cikin nutsuwa ya ce mata, “Yanzu nan baki yarda da abin da na gaya miki ba cewar ni lafiyata qalau bani da wata damuwa ba”. “Ya ya zan yi in yarda bayan ba haka na saba ganinka ba, ni idan na yi maka laifi ne baka son gaya min to ka yafe min”. Ya miqe zaune a kan kujerar ya ce,”Haba Aisha, ni kuwa a rayuwata me za ki yi min ya vata min rai?” “To mene ne? Tun daga ranar da muka je asibiti gaba xaya ka canza ka sauya, ka zama wani irin, in bani na yi maka laifi ba waye?” “To bari mu yi sallah kin ji ana kira, jeki ki yi alwala ki yi taki sallar kafin in dawo daga masallaci”. Bai jira amsarta ba ya miqe ya fita, bai dawo gidan ba ko da aka yi sallar ya yi zamanshi a waje yana hira tare da jama’ar unguwa. Saddiqa tana kwance a xakinta saboda ta dena zuwa xakin Mus’ab, shi da kanshi ne kuma ya nuna mata bai son zuwan nata, don haka ta yi qoqari ta kame kanta. Me ya samu Yaya Mus’ab? Ta yiwa kanta tambayar. Tsawon lokaci tana tunani wani abu ne ya same shi bai son gaya mata, ko kuwa dai haka kawai yake fito mata da waxannan halayen da ba ta tava sanin yana dasu ba. Ta yankewa kanta shawarar zuwa ta same shi ko barci yake yi ta tashe shi in yaso su yita ta qare, ta gaji da kauce-kaucen da yake yi mata. Ta jawo zaninta ta xaura kan rigar baccin dake jikinta ta nufi xakin nashi, tun daga falonshi ta soma shaqo warin sigari, gabanta ya faxi, kar dai Yaya Mus’ab ke shan sigari a wannan tsohon daren? Ta kutsa ta shiga cikin xakin nashi ba tare da ta yi mishi sallama ba, yana zaune a bakin gadonshi da karan sigarinshi a hannu, gefe guda kuma kwalbar barasarshi ce ‘whisky’. Saddiqa ta zube gabanshi cikin kuka mai tsanani, nan take ya sureta da sauri ya yi waje da ita ya nufi falonta ya shimfixeta a kan doguwar kujerarta. “Ba na ce ki dena zuwa wurina ba ki gaya min ba?” Ta ba tanka mishi ba kukanta kawai take yi, ba ta dena ba har ya bar wurin ta ya koma nashi, saboda zai yi shirin sallar asuba. Kafin ya dawo har ta gama yin shirinta, yana shigowa ya kalle ta cikin nutsuwa ya tambaye ta, “Wannan jakar fa?” Ba ta kalle shi ba ta ce mishi “Gida zan tafi”. “Gida ina?” Ya yi tambayar cikin wani irin yanayi. Ta ce, “Misau”. “Na yi miki wani abu ne?” Ta ce, “A’a”. “Ban miki komai ba amma kike so ki tafi ki barni, don kin ganni a cikin damuwa kina so ki qara min ita?” Ba ta kalle shi ba ta ce, “Ai ban santa ba balle ka ce ita ce za ta koreni”. “Ko baki santa ba ai kin san ina da ita”. Ta yi maza ta ce, “Kai kaxai ta shafa bana kuma so in jita”. Ta miqa hannu ta soma jan jakarta za ta fita ya yi maza ya kamo ta ya riqe. “Kar ki tafi ki barni Aisha, in kin barni da wa kike so in zauna?” Ta ce, “Da halayenka”. Ya qi sakinta. “Me na yi miki Aisha kike nema ki qara min damuwa bayan wacce nake ciki, ban son ganinki cikin tashin hankali ne yasa ban gaya miki ita ba, Aisha ba wai ina voye miki ita bane, ki yi haquri ban gaya miki ita bane saboda ni na jawo komai sai nake ganin ya kamata ne ni kaxai in yi ta damuwar ba in watsa ta zama damuwar kowa da kowa ba. Duk da hakan kuma ban samu kwanciyar hankali ba saboda na riga na cuci kaina na kuma cuce ki ta hanyar sanya miki cutar da baki san hawa ba baki san sauka ba, ko Innata bana jin za ta yafe min abin da na yi mata, tunda dai ke ce ‘yarta guda xaya da ta bari a duniya”. “Kai Yaya Mus’ab wacce irin magana kake yi haka?” “Na cuci rayuwata Aisha, na cuci rayuwata, na cuci rayuwata”. Saddiqa ta soma kuka sosai saboda kalaman nashi. A hankali cikin nutsuwa ta gama sauraron bayanin da yake yi mata. “Shine dalilin da yasa ka koma shaye-shayenka ka sha barasa ka sha sigari? Wato duuk ma abin da zai faru ya faru? Wacce irin rayuwa ce wannan? Yanzu ko abinci me daxi ne aka ce ya cutar da lafiyarka ba za ka fita hanyarshi ba balle savo? Ka yi savo an jarrabeka sai kuma ka ce to tuban da ka yi ma ka fasa? Wataqila har neman matan ma ka koma”. Ya yi maza ya ce, “A’a, Aisha ai ba zan yi miki qarya ba, ban tava kowa ba, ai kema na haqura dake balle wasu can qazamai. Ki ji tausayina kar ki tafi ki barni ki yi min alqawari kuma za ki taimakeni ki rufa min asiri a kan abin da nake ciki, ki yafe min ciwon da na sanya miki”. Ba ta kalle shi ba ta ce mishi, “Ni ba kai ka sanya min ciwo ba rayuwata ta san qaddara tana kuma shirye da karvar ta a kowanne lokaci, kuma cikin godiyar Ubangiji”. Tausayin Mus’ab ya kama ta, ta saki jaka ta shiga kicin don shirya mishi abin karyawa. Sai lokacin ne ta lura da irin ramar da ya yi, lokacin ne kuma ta tuna rabon da ta ganshi ya zauna yana karyawa ko yiwa kanshi wani abin da ya dace. “Kin barni ina ci ni kaxai ko baki huce bane?” A hankali ta ce mishi, “Ni bana fushi da kai, ina dai Azumi ne kawai, anjima dai ina so mu koma wurin likitan”. Da sauri ya kalle ta ya ce, “Me zai mana Aisha? Ya ce ba zan haihuwa ba”. Ta ce, “To sai kuma a zauna da cuta? Haihuwa ma ai ba shine mai ba da ita ba, ba kuma a wurinshi muke neman ta ba. Ciwon da ya ce muna da shi shine zamu koma wurin shi ya bamu magani”. Ya ce mata, “To Aisha”. Mus’ab da Saddiqa suna zaune gaban likita. “Ta san komai likita na riga na yi mata bayani na gaskiya, yanzu abin yi kawai za ka gaya mana”. Likita ya gyara zama ya ce, “To magani ne za a baku kai da ita ka san na gaya maka cewar ita cutar cuta ce mai wuyar war…….” Saddiqa ta katse shi da cewa, “Likita bamu magani kar ka yi bayani, ai ka riga ka yi mishi ya ji ya kuma yarda”. Ya kalle ta ya ce, “Haka ne, to babu damuwa”. Ya miqe yaje ya haxo magungunan ya kawo ya shiga yi musu bayani. “Wannan za ta rinqa sha ne da safe da daddare na tsawon watanni huxu, kar ta yi fashi. Wannan kuma na cusawa ne za ta rinqa sanya shi a gabanta sati-sati har na tsawon sati shida. In ta gama sai ta dawo mu sake yin wani gwajin don mu san halin da take ciki”. Ya ce, “To”. Ya kwashe su ya miqawa Saddiqa ta zuba a jakarta. Ya sake juyawa wurin likita yana jin bayaninshi. “Za ka sha magani da safe da daddare tsawon shekara guda kafin mu sake yi maka gwaji don mu ga yanda qarfin ciwon yake”. Ya ce, “To”. “Ga wannan na wata guda ne, a haka za ka rinqa karvarshi wata-wata don ba zai yiwu cewa ka je ka ajiye a gida ba”. Ya sake cewa, “To”. Ya sake kwashe su ya sake miqa mata, ita ma ta sake xiba ta sake zubawa a jakarta, suka dawo gida. Saddiqa tana kwance jikin Mus’ab cikin yanayin kwalliyar da ya fi son ganinta a ciki, ga qamshinta a tare da ita. “Ban qi kowane lokaci ina jikinki ba Aisha, amma in na tuna wai ta hakan ne na sanya miki ciwo sai in ji na haqura”. Ba ta kalle shi ba ta ce mishi, “Wannan kuma ruwanka, kai ka zavarwa kanka hakan ba ni ba, balle ko ka ce na takura maka. Kuma ma ni daga yanzu kar ka sake yi min wannan maganar tunda muna shan magani maganar ta qare a wurina na barwa Ubangijina”. Ya ce, “Haka ne Aisha”. Shekara guda da auren Saddiqa da Mus’ab, tana kwance a xakinta bayan ta karanta katin murnar cikarta shekara guda da zuwanta Ajakuta, wanda Mus’ab xin ya aiko mata da shi, zuciyarta ta shiga tunanin Gwaggonta da daxewar da ta yi ba ta je gabanta ba. Anya na yiwa Gwaggo adalci kuwa? Tana cikin tunanin Mus’ab ya shigo xakin cikin yanayin da ta san akwai abin da ya yi dalilin dawowar nashi, cikin murmushi yake rage kayan jikinshi yana cewa, “Dawowa na yi ki bani goron cika shekara guda da zama ango”. Ta kawar da fuska ta ce, “In don wannan ne ai babu wani goron da za ka samu, sai dai ko hukunci. Tunda shekara guda kenan rabon da in ga Gwaggona, tunda na zo kuma baka tava kai mata ni ba ko sau xaya don ta ganni”. Ya iso gareta yana faxin, “Bari dai yau kam ina ganin ya kamata in tsaya muyi maganar zuwa wurin Gwgagon nan”. Tsawon lokaci yana jikinta yana yin yanda yaso, har sai da ya kai ga samun yanda yake so ya huta ya koma cikin nutsuwarshi, zai soma yi mata wata hirar sai ta ce mishi, “To, Yaya ai ka ce yau kam za ka zauna mu yi maganar zuwa wurin Gwaggon”. Yana jin haka ya yi maza ya rage fara’ar dake tare da shi. “Kin fa matsa min a kan maganar nan, babu halin ki ganni ina hutawa sai kin kawo min maganar zuwa Misau, da wani wanda bai san zaman aure bane? Ina ce kwanan nan Bilkisu da Hamida suka tafi?” Ba ta kalle shi ba ta ce, “To ai shi kenan zan daina damunka, amma dai in ka dawo gida baka sameni ba kar ka ce ranka zai vaci, don na gaji ina so in je in ga uwata, zuwansu Anti ai ba zuwanta bane”. Jin haka da ta ce yasa ya shigar da maganar wasa. “Kina so in xaure muku hanya kenan direban ya rasa inda zai bi”. Ya sake jawota ya maqale yana faxin, “To ke aikin aure da haqquwan cikinshi wasa ne da za ki ce don kin shekara baki je gida ba sai ki tafi ba da izinin mijinki ba, bari daga nan zuwa gobe zan ga abin da zan iya yi a kai”. Ta ce mishi, “To”. Washe gari suna karyawa Saddiqa ta ce, “Yauwa, Yaya Mus’ab ka ce zamu yi maganar tafiya Misau yau”. Ya ce, “Kai ni Mus’ab”. Ya sauke cokalin dake hannunshi ya ajiye ya kalli Saddiqa ya ce, “Na ga dai alamar in ban yi maganar tafiya Misau xin nan ba za ayi min tawayen da zai hanani shan ruwan da zai tsriga min a gidan nan. Faxi yaushe kike so mu tafi”. Ta yi murmushi ta ce, “Ko gobe”. Ya xan motsa kafaxarshi ya ce, “In kinga za ki tafi ba tare da kin tsaya yi musu tsaraba ba sai mu tafi tunda Juma’a ne mu dawo lahadi, amma ni ina ganin me zai hana ki qara yin haquri kaxan tunda zan fara hutuna na qarshen shekara a qarshen wannan watan, in ma bamu yi hutun duka a can ba sai muyi ko da wata guda ne”. Ta ce, “To, Ubangiji yasa mu gani”. Ya ce mata, “Amin”. Tun daga ranar Saddiqa ta kasance cikin shirin tafiya, kullum da irin lissafin da za ta baiwa Mus’ab, Yaya yi haquri na sake tunawa da gida, kaza da kza ta sake ba da wani sabon lissafin, ko na mance da saka gidan su wance su wance ba a lissafin. Ana gobe za su tafi Mus’ab ya dawo gida bai samu Saddiqa ba, al’amarin ya yi matuqar ba shi mamaki, don kuwa hakan bai tava faruwa ba. Ya fito waje ya tsaya don ganin ta inda za ta vullo. Kusan minti talatin da tsayuwa kafin ya hango shigowar motar da ta fita a ciki. Tana shigowa ya juya ya shiga cikin falonshi ya ja ya tsaya yana jiran isowarta. Fusrkarshi a xaure ya tambaye ta, “Ina kika je?” Ta tsaya tana kallonshi cikin murmushi. “Haba Yaya, babu ko sannu da zuwa?” “An qi ayi miki sannu da zuwa, na aike ki ne? Ko kuwa don kina gadarar za ki yi tafiya sai ya zama kowane lokaci za ki rinqa zarar mota kina fita? Kuma ta kai ma har ba za ki gaya min ba ma sai kawai in zo in tarar bakya nan? Ki bari raina ya vaci da tafiyar ki gani in ban hanata ba gaba xaya in ce na fasa in ga qaryar zumuxi”. Idanuwanta suka cicciko karo na farko da ta ga irin wannan vacin ran a tare da Mus’ab, ta sunkuyar da kanta qasa cikin rawar murya ta ce mishi, “Ka yi haquri magungunan da kake sha na je sayowa don na duba na ga ba za su kai mu dawo ba, sai na ji tsoron kar su qare a inda bamu san inda zamu same su ba, na kuma ta yi maka waya in gaya maka baka xauka ba”. Ta kasa danne kukan nata, don haka ta yi maza ta wuce ciki ta barshi nan wurin a tsaye yana kallon wayar tashi. Miss call har shida, duka kuma nata ne. Ya bi bayanta zuwa wurin nata. “To mene ne kuma na kukan? Da kika yi bayanin na yi wata magana ne? Amma ai kema kin san ba qaramin tashin hankali zan shiga ba idan na zo gida ban same ki ba ban kuma san da fitar naki ba, ai sai in yi zaton gudu kika yi kika barni”. Ba ta kalle shi ba ta xan yi murmushi don ta san zolayarta yake yi. “Zo nan ‘yar shatuwallena”. Ya qanqameta a jikinshi. “In mun je Misau a gidanmu zamu sauka daga can ne za ki rinqa zuwa duk inda za ki kina dawowa gida kina kwana”. Ta ce, “To”. Tare suka tafi gidan Idris suka yi mishi sallama, daga nan suka wuce gidan Liman, shima sallamar suka je mishi. GARIN MISAU RANAR TALATA DA YAMMA Direban dake janye da motar su Mus’ab ta yi parkin a qofar gidansu da misalin qarfe huxu da rabi na yamma, Mus’ab yana karanto addu’o’in godiya ga Ubangiji bisa kariyar da ya yi musu suka iso lafiya. Bai san sanda Saddiqa ta fice daga cikin motar ba, ya shiga gida yana riqe da jakarta da takalminta da ta fita ta bari a motar tana rungume da Gwaggo Habiba tana kuka. Fitowar Malam Abdullahi daga xakinshi cikin hamdala ya dawo dasu cikin nutsuwarsu. “Sannunku da zuwa, sannunku da zuwa”. Abin da yake ta faxi kenan. Mus’ab ya ja ya tsaya daga bakin zauren. “Shigo mana Mus’abu ka tsaya daga can kamar wani baqo?” Ya bi bayanshi zuwa cikin xakinshi kamar yadda Saddiqa ma ta bi bayan Gwaggonta suka qule cikin nasu xakin. Mus’ab da babanshi suna gaisawa ita ma Saddiqa ta yi sallama ta shigo, cikin ladabi ta tsuguna tana gaishe shi. “Iko sai Ubangiji, jiya Habiba take maganarku ashe kuna tafe. To kun zo lafiya ko?” Ta ce, “Lafiya qalau”. “Ya ya abokan zama?’ Ta amsa cikin girmamawa, “Duka sun ce a gaishe ku”. Ya ce, “Madallah, Ubangiji ya yi muku albarka”. Ta tashi ta fita ta barsu ta sake shigowa, ta ajiyewa Mus’ab kwanon furar da Gwaggo Habiba ta dama mishi da kanta, wanda ba a tava yin hakan ba sai dai tasa ayi mishi. Saddiqa tana zaune a kicin tana ta taya Gwaggonta aikin abincin da take yi suna kuma hirarsu, duk lokacin da ta kalle ta sai ta ga ita take kallo. Ta yi murmushi ta ce, “Gwaggo kina kallona kina mamakin rashin zuwana gabanki shekara guda ko?” Gwaggo Habiba ta ce, “A’a, Saddiqa ba shi bane, aure ai ya wuce haka, ya kan kuma sa ayi abin da ya fi haka. Canzawarki ce take bani mamaki, ban tava zaton za ki zama haka ba, gaba xaya kin sauya min, sai nake tunanin ashe dai yayanku zai riqe aure”. Saddiqa ta yi ‘yar dariya ta ce, “Uhm! Gwaggo kenan, wai ku me kuka mai da Yaya ne?” Gwaggo ta tayata yin murmushin ta ce, “Ke dai kawai an godewa Ubangiji ga shi shima……” Ta fasa faxin abin da za ta faxa xin saboda b ta saba zancenshi da kowa ba. Saddiqa ta gane abin da take nufim, ta miqa hannu cikin ladabi ta karvi ludayin miyar dake hannunta don ta yi mata abin da take son yi, daidai lokacin kuma tana yi mata bayanin Yaya Mus’ab ai masu ganinshi kullum ma suna mamakin yanda ya zama, to balle wanda ya shekara bai ganshi ba, to ya dena komai Gwaggo, baya shan taba balle barasa, duk wani abin da kika sani ya bari. Cikin jin daxi ta ce mata, “Iko sai Ubangiji, ashe a kan bari?” Ta ce, “Eh, to shi dai ya daina, na kuma yarda ya daina don baya faxin abin da ba gaskiya bane”. Wani daxin ya sake kama Gwaggo saboda irin shaidar da matarshi ke bayarwa a kanshi. Ta ce, “Eh, haka dama waxanda suka sanshi nake jin suna faxa, to Ubangiji ya qara shirya mana”. “Aisha!” Ta fito ta zo ta same shi. Ya ce, “Gayawa Inna ta yi haquri Baba ya ce muje masallaci magariba ta gabato, sai mun dawo zan zo mu gaisa”. Ta ce, “To, sai kun dawo”. Ta koma tana gayawa Gwaggon nata, su kuma suka fita. Malam Abdullahi yana gaba yana ba shi wani labari, shi kuma yana biye a yanayi na girmamawa da amsawa cikin ladabi. Da daddare xakin Gwaggo Habiba ya cika da jama’a ‘yan sannu da zuwa, qannen Mus’ab mata duk sun zo, ga maqwabta da suka shirshigo ana hira, Abu tana basu labarin irin borin da Saddiqa ta yi ranar da za ta barosu, tana yi kuma tana kuka tare da faxin ni zan biki, ni zan biki ki kaini gun Gwaggona, ana ta dariya. Ta kalli Saddiqa dake kwance kan qafar Gwaggon nata ta harareta tare da faxin, “Ashe-ashe duk gulma ne da iya shege, jira take yi in tafi in basu wuri ta sa hannu biyu ta rungume al’amarin mijinta, tunda ga shi ba ta zo gaban Gwaggon nata ba sai yau shekara guda har da kwana goma sha takwas”. Gwaggo Habiba ta yi maza ta ce, “Yanzu kwanakin dawowarki daga can kenan Inna? Ta yi maza ta ce, “Eh mana, to ko dawowarmu daga aikin Hajji yau wata nawa ne?” Ta hau lissafi. Gwaggo ta girgiza kai ta ce, “Kai kwanaki suna gudu, Ubangiji dai ya azurtamu cikawa da imani”. Gaba xaya aka amsa “Amin-amin”. Abu ta sake juyawa kan Saddiqa, hannu tasa ta kai wa kuturinta duka ta ce, “Ke, tashi mki zauna kema kamar kowa, kin zo gabanta za ki yi ta tumurmusar ta, in kin koma wurin miji ki mance da ita. Waxannan mazaunan da kika ajiye in baki zauna a kansu ba mene ne amfaninsu?” Saddiqa ta soma shure-shure da kuka sai dai hawayen sun qi zubowa. Gwaggo ta ce, “Ba fa laifinta bane Inna, kuma da kanku kun yi ta faxa bai zauna ba, ga kuma qarin girma da ya samu, to ai ita ma ba ta zauna ba tunda tare da ita yake yin tafiyar”. Mus’ab ya tsaya daga tsakar gida ya kira Hamida, ta yi maza ta tashi ta fita, ba ta daxe ba ta dawo ta ce, “Anti wai ki je yana kiranki”. Saddiqa ta xaure fuska ta ce, “Gaskiya ni bana son Antin da kuke ci min, a kirani da sunana kawai”. Ta miqa hannu ta buxe jakarta tana xiban magunguna. Abu tana faxin, “Ai tunda kika auri tsoho mai tsofaffin qannen da suka haifeki, to dolenki kema ki karvi tsufan”. Saddiqa ta yi dariya daidai ta xauki kofi da robar ruwan swan tana faxin, “Uhm! Abu kenan, yanzu nan Yaya Mus’ab xin ne tsoho?” Ta fita ta barsu suna dariyarta. Minti kusan biyar da fitar Saddiqa sai gata ta dwo tana kuka, gaba xaya aka yi tsit! Ana kallon ta. “Mene ne kuma na wannan kukan da kike yi?” Tana sharve ta baiwa Abu amsa da cewa, “Wai dole sai na fita mun tafi can gidan mun kwana”. Da sauri Abu ta ce, “Ke wuce ki shiga xakin uwarki ki hau gadonta ki yi kwanciyar ki ko ‘yar hira ku yi ku xebewa juna kewa kin ji?” Saddiqa ta yi hanzarin bin umarnin nata ta wuce cikin xakin ta hau gadon ta kwanta, ta barta tana faxanta. “Haba, ni bana son fitina, fitanannen mutum kawai mara haquri, shekara guda baka kawo yarinya gaban uwarta ba kuma kun zo ba za ka barta ta sake ba?” Da haka hirar ta watse kowa ya nufi gidanshi. Washe gari da sassafe Saddiqa ta fito daga wanka kenan tana zaune kusa da Gwaggonta tana shafa, sai ga Abu ta shigo tare da sallamarta. Ta kalli Abu ta ce, “Gaskiya ko tare dake muka kwana iyakar sammakon da za ki yi kenan ki shigo mana xakinmu”. Ta zauna kusa da Saddiqan suka gaisa tana kallonta. “Ni kina da ciki ne?” Ta ce, “Nima ban sani ba”. Ta yi tsaki ta ce, “Kar ki sani”. Ta juya wurin Gwaggo Habiba, “Ba ta ce miki komai bane?” Cikin nutsuwa ta ce, “A’a, ba ta da komai Inna, ta dai ce wai tana da matsalar al’ada. Na ce daga baya kenan hakan ya sameta ko? Tunda ita ai ba mai irin wannan lalurar ba ce”. Abu ta ce, “To ba sai a karvo mata magani ba?” Saddiqa ta fito cikin kwalliya sosai sai sheqi take yi, ta yi kyau har ba a magana. Abu sai binta da kallo take yi. Ta kalli Abun ta yi murmushi ta ce, “Kar ki karvo min magani don ba zan sha ba, Yayana yana kaini asibiti”. Ta wuce ta fita saboda jin isowar Mus’ab, daga fitar nata ta dawo ta zauna. Mus’ab ya shigo ya nemi wuri ya zauna kan tabarma, ya yi kwalliyar manyan kaya babbar riga da ‘yar ciki da wando na farin yadin voil, ga hularshi ta zauna d ata yi matuqar sakuwa. Tuni qamshinshi ya gauraye ko’ina. Ya shiga yiwa Innarshi bayanai tana sauraro har tana faxin haka ne, abin da baya faruwa a tsakaninshi da ita. Hatta Abu dake tayata sauraron daxi ne ya kamata. Saddiqa ta tsuguna a gefen Mus’ab riqe da kofin ruwa da kuma magani a hannunta, tana jin ya yi shiru ta yi maza ta ce mishi, “Ga shi ka sha’. Yasa hannu ya karva ya sha saboda ba zai yi musu da ita a gaban Innarshi ba. Abu ta ce, “A’a, ni wane irin magani ne wannan kike xura mishi? Ba ki gaishe shi ba ba ki ba shi abin da zai ci ba kin kawo qwayoyi kin ba shi. Haka jiya yana kiranki kika kama xiban qwayoyi. Baka da lafiya ne Mus’abu?’ Kafin ya amsa Saddiqa ta ce mata, “Sai ana ciwo ake shan magani? Kema ba na ga safe da yamma kike sha ba?” Bai biyewa Saddiqa ya mayar da maganar wasa ba sai ya ce mata, “Bani da lafiya Abu”. Abu ta kalle shi ta ce, “Wane irin ciwo ne wannan da bai hanaka qiba ba, bai kuma hana fatarka gogewa ta yi kyau ba? Ko kuwa dai irin shagwavarku ta ‘ya’yan yau ku yi ta xirkawa kanku qwayoyi haka siddan?” Ya ce, “A’a, ciwo nake yi sosai”. Abu ta riqe baki cikin mamaki ta ce, “To hala ciwon ne ya mai da kai haka?” Ya yi murmushi ya ce, “Ba shi bane, ina zaune lafiya ne a gidana na yi sa’a Aisha ta karvi lalurata ba ta tayar da hankalinta ba balle nawa ya tashi, ban da haka kuma na daina shan abubuwan da da nke sha, shi yasa kika ga na canza da yawa. Amma ina buqatar ku qara yi min addu’a”. “To a qara yi maka addu’a baka faxi damuwar da ta same kan ba don mu san irin wacce zamu qara akan wacce dama muke yi”. Bai vata lokaci ba ya yi mata cikakken bayani. “Ba za ka haihu ba Mus’abu?” Abu ta yi tambayar. Nan take kuma ta soma kuka, wani irin kuka mai tsanani tamkar wacce aka yiwa wani abu mai tsanani. Kanshi a sunkuye qafafuwanshi a harxe yanda dama yake zaune tun farko bai motsa ba. A haka yake jin kukan da Abu ke yi, yake kuma sauraron kalaman da Innarshi ke furtawa. “Abin da na gudarwa Saddiqa kenan, ga shi kuma shine ya sameta”. “A’a Gwaggo, A’a, Gwaggo kar ki shiga wannan maganar don ni na warke”. Abu ta daka mata tsawa ta ce, “Ke tafi can shashasha, wani warkewa za ki yi shi bai warke ba, ina ce shi yake sa miki? To ta ina za ki samu lafiya?” “Gaskiya ni bana so, Abu bana so, ke ba za ki sasanta magana ta zama mai sauqi ba za ki qara lalatata?” “Ke matsa can wawuya, wannan maganar taku ai dama a lalace take, a ina kika tava ganin zama ya yi dai-dai tsakanin mai lafiya da mara lafiya? Sokuwa kawai, wai ke ga mai son miji ko? Zai kuwa kai ki ya baro, rashin haihuwa wasa ne? An ce miki in kece ba za ki haihun ba zai yarda ne wata zai je ya kawo in ba ki yi haquri ba ki kasa zama, shi kam ai shi ya jawa kanshi, tun yaushe ne ake baqin cikin wannan shaye-shaye da Mus’abu ke yi? Tun bai isa komai ba”. Ta bar maganar ta kama kuka sosai. Cikin nutsuwa Gwaggo ta ce, “In kun gama hutun sai ka tafi ka barta a gida”. Saddiqa ta yi maza ta ce, “A’a, Gwaggo zan bishi ba yaji na yi ba, ba kuma qarar mijina na kawo muku ba, baqonta muka zo yanda muka zo tare kuma haka zamu tafi tare, ina sonshi”. Ta soma kuka. Mus’ab ya buxe baki an hankali ya ce mata, “Inna ni zan fita”. Ta ce mishi, “To”. Abu ta miqe ta bi bayanshi suka tafi suka bar Saddiqa tana ta faman kuka. A hankali cikin yanayin rarrashi ta ce mata, “Da kin yarda kin zauna a gida har kafin a ga yanda lamarin zai kasance”. Ta ce, “A’a, zan bishi, zan je in zauna da shi, bai yi min komai ba, ban ga kuma abin da sauran surukaye suke wa matansu ba wanda shi bai yi min ba. Da nice nake cikin yanayin da na ga Kubrah jiya da kin ce an qwace mishi ni, in muka tafi kuma ni ba zan ma sake…..” Gwaggo Habiba ta katseta ta hanyar tambayarta, “Kina cikin hankalinki kuwa Saddiqa ko wani abu ne ya same ki?” “Ki yi haquri Gwaggo ba abin da ya same ni, bana jin daxi ne kawai na yanda ake tafiyar da al’amarin Yaya Mus’ab a gidan nan, sai yaushe za a fara tausayin shi? Duk wani wanda zai yi baqin cikin al’amarin ai tayashi yake yi ba finshi ya yi ba”. Ta soma ba ta labarin halin da Mus’ab ya shigo lokacin da likita ya ba shi labarin abin da yake ciki, da yanda aka yi ta shawo kanshi har ya samu nutsuwar da yake tare da ita. Har ta gama Gwaggo ba ta sake ce mata komai ba, iyaka dai zuciyarta ta kai matuqar da ba za a iya kwatantawa ba. “To sai kuma mu zo gabanku Gwaggo shi da kanshi ne ya faxi al’amarinshi sai a turashi a gaba da maganganu masu zafi, Abu tana yi ku kuna yi? Kenan babu mai tausayinshi?” Gwaggo ta fita ta bar mata xakin ta nufi kicin ta kama aikin abincinta, ita ma Saddiqa ta yi shiri ta fita ta bar gidan. Mus’ab yana zaune kan tabarma xakin Abu yana cin gasasshiyar masara suna hirarsu lokacin da Saddiqa ta yi sallama ta shiga gidan. Abu ta yi mata sannu da zuwa kamar ba yanzun nan suka rabu ba. “Me za ki ci a kawo miki?” Ta ce, “Masara”. Ta ce, “Ai kuwa iyakarta kenan, sai dai mijinki ya sn miki. Kai ka san mata masarar ka raba biyu ka ba ta rabi”. Mus’ab ya kalli Abu ya ce, “To ke ki yi shiru mana ki barta ta yi maganar da bakinta”. Saddiqa ta yi shiru ba ta yi magana ba. Abu ta lura basa magana da juna da ita kaxai suke yi. Ta yi dariya ta ce, “Au ni fushi da juna kuke yi ne?” Mus’ab ya ce, “Take yi dai, ni ina fushi ne?” Saddiqa ta yi maza ta ce, “Waye ma ya fika? Ba ga shi don ka yi fushi wai kana so nima ka bani haushi ba ka je ka aske qasumbarka? To na rantse kanka za ka qarawa haushi, don ba zan sake yin magana da kai ba sai randa ta koma daidai yanda take kafin ka asketa”. Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “Ai kuwa dai taka ta sameka, kai kuwa me yasa ka yi wannan aski tunda ka san ba a so?” Ya yi tsaki ya ce, “Abin haushi ne da ita Abu, daga zuwanmu garin nan har ta fara sava alqawuran da ta yi min”. Ya kwashe bayani tas ya yi mata. Abu ta ce, “Eh to, ba ta kyauta ba, amma kai ma fitana ne da kai, don haka an yi dai-dai dukanku kun yiwa juna shi kenan magana ta qare sai ku sasanta a shirya kawai a kori gaba”. Ya kalli Saddiqa ya ce, “To kin ji Aisha, Abu ta ce mu shirya”. Ta yi kamar ba ta ji shi ba. Kwanansu uku da zuwa Misau kullum a gidan Gwaggo Habiba Saddiqa take kwana, tun da ta je gidan Abun ma sau xaya ba ta sake fita ba, kowane lokaci tana manne da Gwaggonta, in tana kicin suna tare, in ma xakin ne haka, ko sallah za suyi ga sallayarta ga tata. Zuciyar Gwaggo ta yi matuqar jin daxi ganin yanda Saddiqa take matuqar son mijinta, take xai-xai da shi a duk lokacin da ya shigo gidan. Sai dai abin da ya dameta guda xaya ne, maganar da Mus’ab da bakinshi ya gaya musu cewar likita ya tabbatar mishi da cewar da wuya qwarai ya haihu. To haka za su zauna shi da Saddiqa ba za su haihu ba? Tana yiwa kanta tambayar take yin maza ta kawar da ita ta hanyar mayar da al’amuran gaba xaya ga Ubangiji, don tsananin abin ya wuce duk wani kwatance. Ranar asabar da yamma bayan sallar la’asar Mus’ab ya shigo falon Innarshi suna tare ita da Saddiqa, cikin nutsuwa ya ce mata, “Inna sanda zamu zo garin nan Aisha ta yi min alqawarin da da muka zo ta qi cikawa”. Cikin kulawa Gwaggo Habiba ta tambaye shi, “Wanne irin alqawari ne wannan?” A hankali ya ce mata, “Na gaya mata in mun zo zamu sauka a can gidana ne, daga can ne za ta rinqa zuwa duk inda za ta, amma in dare ya yi za ta koma can ta kwana ta ce to”. Saddiqa ta yi maza ta ce, “Ba haka bane”. Gwaggo Habiba ta yi maza ta kalle ta, “Za ki qaryata mijinki ne a gabana?” Ta yi maza ta yi shiru saboda ganin yanda Gwaggon ta xaure mata fuska. “Bana son iya shege”. Ta juya wurin Mus’ab ta ce, “In ka tashi tafiya ka kirata ku tafi, in kuma yanzu kake son tafiyar ma sai ku je”. Hankalinshi a kwance ya ce, “Na fi so mu tafi yanzu saboda su Bilkisu sun yi min waya wai mazansu za su zo gaisheni na ce to a sameni a gidana”. Da sauri Gwaggo Habiba ta ce mishi, “Qwarai kuwa su sameka a gidanka, ke Saddiqa xebo mishi girkin da nake yi ki riqe mishi”. Ta yi maza ta ce, “To Gwaggo”. Ta je ta dawo tana cewa, “To amma Gwaggo ai mun ce zamu Bauchi gobe da sassafe”. Gwaggo Habiba ta ce, “Eh, in hali ya yi na ki fito da sassafen sai ki fito, in kuma bai yi ba sai ki haqura sanda mijinki ya samu zarafi sai yasa a kaimu”. Ta ce, “To”. A mota suna tafiya Saddiqa tana gaya mishi kar ka ga ka haxani da Gwaggona ta tilastani binka ka yi zaton ko in munje wani abin arziki zamu qulla ba kulaka zan yi ba”. Ya ce, “Babu komai Aisha in dai zan samu in tava jikinki ai magana ta qare”. Washe gari da safe Saddiqa da kanta ta yiwa Gwaggonta waya, “Gwaggo ku yi haquri ba zan samu fitowa daga gidan ba yau su Anti Hamida za su zo wuni. Na ce ko ita ma Kubrah za a yiwa mijinta magana don ta zo tunda ‘yan’uwa za su haxu”. Gwaggo Habiba ta ce, “To, sai a gwada”. Baqunta mai daxi su Saddiqa suka yi da kuma tafiye-tafiye masu yawa, har wurin su Ishak da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki. Sati huxu suka yi kafin suka yi shiri suka koma gida da xinbin tsarabar da suka yi ta rarrabawa maqwabta da abokan mu’amala na cikin gari. Bayan dawowar su Saddiqa gida sun ci gaba da zamansu lafiya a sannu da fahimtar juna dake tsakaninsu. Mus’ab ya fita hanyar duk wata masha’a, ya mai da hankali kan istigfari, neman gafarar abin da aka aikata a baya da qoqarin gyara na gaba. A yanzu matsalarshi babba ita ce rashin lafiyarshi, zuciyarshi ta qi yarda ta ji daxin zaman da zai yi da Saddiqa, ita ba haihuwa shi babu, bayan kuma lalurar tashi ce shi ya jawowa kanshi ita. In shi Gwaggo Habiba ta samu yaxuwar zuriyarta ta wurin wasu ‘ya’yan, to ita Innarshi fa, Saddiqa kaxai ta bari a duniya. Wannan shine abin da ya fi komai damun shi. Auren nasu ya cika shekaru biyu, yau ma suna gaban likita, zuwa yanzu kuwa an yiwa Mus’ab canjin magani har sau biyu saboda wasu lalurorin nashi da aka sake ganowa. Sauraron shigowar likitan suke yi don jin sakamakon sabbin gwaje-gwajen da aka yi musu. Ta xaga ido ta kalle shi cikin sanyin jiki, a hankali ta buxe baki ta ce mishi, “Gabana sai faxuwa yake yi”. Ya yi murmushi ya ce, “A kan me Aisha?” Kafin ta ba shi amsa Dr. Usman ya turo qofa ya zo ya zauna a kan kujerar shi, gaba xaya suka mai da hankali wajen sauraron abin da zai gaya musu. “Ina ganin mun xan samu ci gaba tunda ita Hajiya ba a sameta da wata matsala ba, don haka za ta rinqa shan magani ne kawai na hana haihuwa da qwayoyin cuta. To kaima kuma mun gano inda asalin matsalarka take, kamar yanda na riga na tava gaya maka ne, ita wannan cutar ta kan yi riqar da take daskarewa har ta toshewa qwai hanyar shiga mahaifar mace, to abin da ya faru da kai kenan, shi yasa magungunan da muke ta amfani dasu basu wani yi aiki na a zo a gani ba”. “To yanzu babu wani abin yi kenan?” Ya yiwa likita tambayar. Ya yin da Saddiqa ta yi kasake tana sauraro. “Eh, akwai abin yi, shine tiyata a buxe wurin a kankare ita jijiyar a cire ciwon daga cikinta, sai kuma ka ci gaba da shan magani zuwa wani lokaci da zamu ga abin da zai faru”. Saddiqa ta yi shiru in ban da tunanin inda jijiyar take babu abin da take yi. Sun dawo gida Saddiqa tana zaune tana kuka. “Ni ban yarda da aiki ba, kaima ka san yinshi hatsari ne, shi yasa ma ka qi tambayar likitan hatsarin shi. Ai ba murxarka ciwon yake yi ba balle ko ka ce yana damun ka”. Mus’ab ya kalle ta ya xan yi murmushin qarfin hali. “Hatsari Aisha? Har ya wuce na ina zaune ana cewa in abin ya gagara sai a san yanda za ayi? Me ake nufi? Haka zan zauna duk sanda na je gida sai anyi min kalamai na barazana?” Ta xan yi shiru kafin ta ce mishi, “Ba dai Gwaggo ce ta yi maka maganar ba Abu ce, ita kuma baka iya nuna mata ka ji haushi balle ta sani, ko ranar da aka yi hakan kuma a kaina fushinka ya qare, ka ce wai na ji daxin abin da ta faxa xin bayan ni ban tava tayar da maganar likita ba a gabansu kai ne”. Ya yi shiru fuskarshi a xaure alamar ranshi ya sosu, ita ma ta ja bakinta ta yi shiru, dama ta ga abin zai yi nisa ta miqe ta nufi wurinta ta ci gaba da harkokinta. In har Mus’ab yana da wata matsala a yanzu da ta addabe shi, ta takurawa zuciyarshi, to ba ta wuce matsalar rashin haihuwarshi ba, duk da bai tava ganin wata damuwa a wurin matarshi ba, to amma kuma ya yarda da maganar da Abu ke yawan gaya mishi cewar quruciya da kunya ke hanata nunawa, nan gaba in abin ya yi nisa ba za ta jure ba. “Hajiya lafiyarta yanzu qalau, mahaifarta kuma a shirye take in aka sa mata qwai za ta xauka”. Wannan shine kalamin da likita ya yi musu a zuwa asibitin da suka yi na qarshe. Ya waiwaya ya kalli Saddiqa dake ta faman sharar bacci a bayanshi, bacci ne mai nauyi da alama kuma bacci ne na gajiya. Ya kawar da kanshi daga gareta, cikin wani tunanin wanda daga baya ya ga ba zai fissheshi ba. Ya miqe ya shiga banxaki ya yi wanka tare da alwala ya fito ya fara gabatar da nafilfili. Washe gari da safe suna tare wurin karyawa, suna kuma hirarsu cikin nutsuwa. Ya sake shigo mata da maganar da ta riga ta ce mishi ba ta son ji. “Aisha bai fa kamata a ce muna cikin matsala sai mu kawar da ita mu yiwa kanmu qaryar bamu da ita ba. Kin yarda da maganar aikin nan da kike yi sai in ga kamar nine baki damu dani ba”. Ta yi maza ta xago ido ta kalle shi. Ya ce, “Eh mana, yanzu ke ba za ki fata da sha’awar ki ganki xauke da cikina a jikinki ba?” Da sauri ta ce, “Ina yi mana Yaya”. Ya ce, “To in kina yo don me ba za ki qarfafa min zuciyata ba sai ki rinqa nuna ke baki da matsala, amma kuma kullum kina aiken a kawo miki jariri ki rena? Kullum fa sai kin tura an kawo miki xan da Zainab ta haifa”. “Ba ina qin aikin bane hatsarinshi ya yi yawa, sai na ce to mu tuntuvi iyayenmu don mu ji abin da za su ce kai kuma ka qi”. A hankali ya ce mata, “Ina tsoro ne kar su ce basu yarda ba, in suka yi haka kinga ba zan tafi babu izininsu ba, in kuma aka yi sa’a suka amince nan kuma hankulansu za su tashi suyi ta fargaba suna zullumin yaushe za a yi, in anyi kuma me zai faru? Shi yasa na fi so sai anyi sai mu gaya musu tunda lokacin babu sauran zullumi ko fargaba”. Da irin waxannan kalaman Mus’ab ya rinjayi Saddiqa ta amince da maganar aikin nashi. Nan da nan ya tasata a gaba suka koma gaban likita don ya sanya ranar da za a yi aikin, inda ya xibar musu kwanaki ashirin da xaya a dalilin akwai magungunan da ake buqatar Mus’ab xin ya yi amfani dasu kafin lokacin. Duk da Saddiqa a kan ta amince ake yin shirin jikinta a sanyaye yake qwarai. “Zo ki ji, kawo kunnenki nan ki ji abin da zan gaya miki”. Ya soma yi mata maganar a kunnen nata cikin yanayin raxa. Ta xago ido cikin murmushi tana kallon shi saboda maganganunshi. Bai rama mata murmushin ba, maimakon haka magana ya soma yi mata cikin nutsuwa yana mai kallon idanuwanta. “Sanda Innata take raye haka take yi min in na yi mata wani xan abin da ya faranta mata rai, sai ta jawoni kusa da ita ta raxa min wani abu mai daxi a kunnena. Zan tafi tiyatar nan Aisha zuciyata cike da fata da buri na ayi nasara in samu ki haifar min ko da ‘ya mace guda xaya ne da zan yi mata takwara da ita”. Saddiqa ta qara matsawa kusa da shi a hankali ta cusa hannayenta cikin rigarshi tare da kwantar da kanta a qirjinshi, a hankali cikin kalamanta mai sanyi ta ce mishi, “In ka haifi mace guda to Gwaggona fa Yaya?” Kwanaki ashirin sun cika saura guda xaya tal! Saddiqa tana xakinta a kwance Mus’ab ya shiga ya sameta, ta yi maza ta share hawayenta tare da sakin fuskarta don kar ya gane abin da take ciki. Shima ya yi kamar bai gani ba. Matsawa kusa da ita ya yi ya kwanta, ya miqa hannu ya jawota jikinshi yana sansanar qamshinta. Ta yi qoqari ta xan ture shi ya xan matsa kaxan. “Mene ne haka?” Ba ta kula tambayar tashi ba ta yi maza ta miqe ta zauna. “Da ka tsaya mun yi magana tukunna”. Ya ce, “Ba zan yi ba sai na yi abin da ya kawoni tukunna”. Bai yarda ya bari ta sake ce mishi komai ba ya shiga sarrafata, sai da suka samu nutsuwa sai ta ce mishi, “Ni Yaya baka da damuwa ne, gobe ne fa aikin nan? Bai kalle ta ba ya ce, “Bani da ita, takin ma bana son ki gaya min addu’a kawai na ce ki rinqa yi”. “To ai ni munanan mafarke-mafarken da nake yi ne suke bani tsoro, in zan gaya maka abin da na gani kuma ka ce wai baka son ji”. “To a ina kika ji an ce a ba da labarin mummunan mafarki? Ina ce addu’a aka ce a rinqa yi mishi?” Bai tsaya ba ya tsallaketa ya shiga banxaki ya yi wanka ya fito tare da alwala, ya shiga gabatar da nafila. Ita ma ta bi bayanshi, basu daina ba har sai da aka kira sallar asuba. Yana dawowa daga sallar asuba ta je kusa da shi don ta gaishe shi, ya jawota ya rungume a jikinshi yana shafata. “Santsin jikinki kaxai ya isheni ni’ima Aisha”. Ta yi maza ta zame daga jikin nashi ta ce, “A’a, Yaya kana faxa ne kawai don in ji daxi, amma in da haka ne ai da ka haqura da wannan tiyatar da za ka tafi yau, tunda na gaya maka ni kam Yaya Mus’ab ina sonka rashin haihuwa kuma ba zai rage komai ba a tsakaninmu da kai”. “Na sani Aisha”. Ya faxa cikin jin daxin kalaman nata. “Na sani Aisha, na san za ki iya zama dani da lalurata. To amma mene ne tukuicin son da muke yiwa juna? Ina son ganinki da ciki”. Ya faxi hakan cikin raxa har ya sata jin kunya. “An jarrabi zuciyata da son in ganki a hakan, in san nine, mutanen duniya ma su tayani shaida hakan a ce matar Mus’ab juna biyu ne da ita”. Ta yi murmushi, yana ganin murmushin nata ya yi maza ya miqe ba tare da ya ba ta damar da za ta sake narke mishi ba. “Bari in yi wanka Aisha in shirya kafin su Idris su iso”. Kafin ya fito daga wankan sai ga Idris da matarshi Abida sun shigo, ‘yan mintoci kaxan kuma sai ga Sani shima ya iso tare da amaryarshi. Saddiqa tana tsaye a xakinta jikinta sai rawa yake yi, Mus’ab ya shigo sanye da jallabiya mai ruwan shuxi, silifas xin wanka ne a qafarshi, qamshinshi na kullum yana tare da shi. Ya kama hannayenta duka biyu ya riqe a cikin nashi, ya sunkuyo da idanuwanshi cikin nata da tuni suka fara zubar da hawaye. “Ai nima zan bika, zan je ayi komai a kan idona ina gani”. A hankali ya ce mata, “A’a, Aisha yi haquri ki yi zaman ki a gida, ga ‘yan’uwanki mata nan sun zo za su tayaki zaman gidan zai fi miki sauqi da nutsuwa”. Za ta yi magana ya yi maza ya ce mata, “Shhhhhh!” Kan ta yi wani abu ya yi hanzarin sanya bakinshi a nata, kusan minti guda kafin ya saketa. “Kar ki yi min musu, addu’a kawai za ki yi min”. “To Yaya”. Cikin rawar murya ta faxi hakan. Bai jira ya ji sauran maganar ba ya yi maza ya fita daga xakin, ya samu su Idris da Sani a waje da suka zo don suyi mishi rakiya. Saddiqa ta nemi wuri ta zauna a qasa tana ta faman kuka Abida tana rarrashinta. “Ki yi haquri Aisha, ki yi ta addu’a kawai Ubangiji dai yasa ayi a sa’a”. Ta xago ta kalleta cikin hawaye ta ce, “Iyayenmu fa basu san da aikin ba, na yi na yi mu gaya musu ya qi, wai yana tsoron kar su hanashi gara in an yi kawai su ji”. Abida ta jinjina lamarin, nan take kuma sai ta ba ta shawara. “To yanzu tunda ya riga ya tafi ai sai ki gaya musu su sani, don kuwa ai yana buqatar addu’arsu”. Ta yi maza ta miqe ta xauko wayarta, lambobin Gwaggonta ta danna, tana jin muryarta ta soma kuka. “A’a, me ya sameki Saddiqa ba dai wani abin ne ya faru tsakaninki da mijin naki ba ko?” Saddiqa ta ce, “Eh, Gwaggo”. Gwaggo ta yi maza ta ce, “Yau to ai yanzu muka gama magana da shi ya kirani muka gaisa, mun kuma xan jima muna magana ban ji alamar damuwa a tare da shi ba”. Cikin nutsuwa Saddiqa ta tambayeta ya gaya miki daga ina ya kira ki Gwaggo? Da sauri ta ce mata, “A’a, bai gaya min ba, wani abu ya faru ne?” Ta yi tambayar a yanayi na nuna damuwa. “A’a, Gwaggo babu abin da ya faru, amma shi yana asibiti wai za a yi mishi tiyata”. Da sauri ta tambaya, “Tiyata? Ba shi da lafiya ne?” Tana share majina tana maganar, “Lafiyarshi qalau a kan dai maganar nan ne, na yi na yi ya qi ya bari, na kuma ce ya gaya muku wai ba zai faxar muku da gaba ba, bayan haka kuma yana tsoron kar ku hana”. Shiru Gwaggo ta yi na wani lokaci alamar jikinta ya yi sanyi, a hankali cikin nutsuwa Saddiqa ta jita tana cewa, “To Ubangiji yasa ayi mishi aikin a sa’a”. Ta ce, “Amin”. Tana ajiye wayar kiran Mus’ab ya shigo. “Albishirinki Aisha”. Ta yi maza ta ce mishi, “Goro”. Yana murna ya ce mata, “Yau hira sosai muka yi ni da Inna da na kira ta”. Ta ce, “Kai Yaya Mus’ab, wannan ne abin albishir xin, ni ina ce ma za ka ce min an fasa yin tiyatar ne”. A hankali ya ce, “A’a, Aisha ai likitocin da za suyi aikin ma sun riga sun iso tun xazu, Dr. Usman ya gaya min cewar shi da wasu likitoci uku ne za suyi aikin. Kin san wani abu?” Ta yi maza ta ce mishi, “A’a, sai ka faxa”. Ya ce, “To zan shiga tiyatar ne hankalina a kwance bana tsoro ba kuma na fargaba, na kuma yarda cewar duk wani abin da ya faru ko zai faru, to daga Ubangiji ne, na roqe shi ya yafe min zunuban da na yi ta aikatawa waxanda suka zama sanadin da na cutar da lafiyata. Ke kuma na gode miki Aisha, na zauna dake zama mai daxi, kowane lokaci a cikin tattalina da kyautata min kike, kin yi komai don ki faranta min. Mafi alherin al’amarinki kuma shine, kin zama sanadi na daidaituwar tsakanina da mahaifiyata, in ban fito daga wannan tiya…..” Ta yi maza ta saki wayar a qasa saboda firgitar da ta yi tare da faxin “Na shiga uku!” Nan take kuma ta soma kuka. Da qyar ta iya yin shiru saboda rarrashi da kalaman qarfafa gwiwa da su Abida suka yi ta yi mata. “Gaskiya ba zan iya zaman nan ba gara min kawai muje asibitin”. Abida ta ba ta haquri. Jimawa can ta sake cewa, “Nifa gara min kawai in tafi don ban ga amfanin zaman da nake yi a nan ba”. Tasa hannu ta kira layin Mus’ab don ta gaya mishi ya barta kawai ta zo asibitin don ta ganshi. Sani ne ya amsa. “Hello! Aisha akwai wani abu ne?’ A hankali ta tambaye shi “Yaya fa?” Ya ce, “Ai tun qarfe takwas da rabi suka shiga dashi, dama shine mutum na biyu a tiyatar da za suyi yau”. Cikin Saddiqa ya ba da sautin qulululuuu! A lokacin da idanuwanta suka kai kan agogon dake wurin, qarfe goma sha xaya har da kwata, kusan awowi uku kenan da shigarwar da aka yi mishi. Ko a wane hali yake ciki yanzu? Oho! Ta yi maza ta ajiye wayar ta nufi banxaki saboda kaxawar da cikinta ya yi. Wunin ranar zirga-zirgar da ta yi ta yi kenan. Wajen azahar ta isa asibitin bayan ta riga ta yi sallarta a gida. A hankali ta tura qofa ta shiga xakin da aka nuna mata cewear shine nashin inda aka bashi, jallabiyar da ya baro gida da ita ne a ajiye a kan gadon. Ta miqa hannu ta xauka ta ninke ta sanya cikin jakar dake hannunta, ta ajiye jakar a kan gadon ta nufi inda ta hango Sani da Idris a tsaye. Tana isa wurin ta gane a kusa da xakin tiyata suke tsaye. Su dukansu biyun babu wani annuri a tare dasu, gaba xayansu idanuwansu sunyi zuru-zuru, bakunansu sun bushe. “Sannu Aisha”. Idris ne ya yi mata gaisuwar a yanayi na qarfin hali. Ta yi nufin wucewa zuwa inda ta hango qofar da aka rubuta Theater room a jiki, da sauri suka ce mata, “Ai ba a zuwa nan, iyakar wurin tsayuwar kenan inda muke xin nan, ki dawo kawai ki yi haquri ko kuma ki koma can xakin ki samu su Abida in an fito da shi ai nan xin ne dai za a kawo shi”. Ba ta yi magana ba kuka kawai take ta yi. Dr. Usman ya zo wucewa tana kallon shi yana magana da su Idris ba ta iya qarawa ta ji abin da suke faxa ba, tana dai kallon fuskokinsu zuciyarta kuma tana raya mata, ta gaji da kallon nasu ta yi qoqarin matsawa kusa dasu don ta ji me yake gaya musu haka wanda bayanin ya qi qarewa. “Yanzu dai sai mu qara haquri mu haxa da addu’a”. Qarshen maganar likita da ta ji kenan. “Me ya faru? Me ake ciki na ji yana cewa ayi haquri?” Ta yi musu tambayar a firgice saboda ba ta same shi ba ya riga ya wuce. Tun kafin su san me za su ce mata ta fara kuka. Da sauri Idris ya soma yi mata bayanin “Ba fa wani abu bane mai tsanani al’amari ne da yake faruwa da mutane da yawa, kin san kowa da yanda qarfin jininshi yake, an gama aikin sai dai bai dawo sosai ba ta yanda za su iya fito da shi”. Yana nan kenan tsakanin akwai da babu. Zuciyarta ta raya mata. Nan take jiri ya xebeta ta tafi za ta faxi, da sauri wata mace dake wucewa ta bayanta tasa hannu ta tare ta, su Abida suka yi maza suka kama ta aka kaita xakin aka kwantar da ita. “Ki fa kwantar da hankalinki kar kuma shi a fito da shi ke kuma kin samu matsala”. Kukanta kawai take yi ba ta ko kallon su balle ta amsa. Awa xaya baya aka fito da Mus’ab. “Gareka nake ya Ubangiji, gareka nake neman taimako”. Abin da yake ta nanatawa kenan. Gaba xaya ana tsaitsaye a kanshi cikin sauraro. An fito daga sallar magariba kenan sai ga Kawu Gixe da Abu sun iso asibitin, nan da nan Saddiqa ta xan samu nutsuwa a tare da ita. “Iko sai mai shi, haka al’amarin yake? To Ubangiji ya ta da kafaxarshi”. Gaba xaya aka amsa “Amin”. Kalaman Abu ne wannan bayan ta amsa sannu da zuwa da gaisuwar da aka yi ta yi mata. “To a nuna min inda zan yi sallah”. Saddiqa ta wuce za ta nuna mata, ta tarar tuni har Kawu Gixe ya idar. Ta tsuguna a gefe tana gaishe shi. “Ya ya aka yi aka yi irin wannan aiki haka baku sanar da gida ba?” Ba ta iya ce mishi komai ba in ban da kukan da take yi, saboda ta riga ta gama tsorata da yanayin da aka fito da shi a ciki. Har suka bar asibitin ran nan bai wani dawo cikin hayyacinshi ba, ita kam ta so a ce an barta ta kwana a wurinshi Abu ce ta ce gara su tafi wai in sun zauna me za suyi mishi bayan ga likitoci suna ta kaiwa da kawowa, ga kuma Kawu Gixe da Sani suma a nan za su kwana? Sun dawo gida Saddiqa sai bin Abu da kallo take yi, zuciyarta tana raya mata duk halin da Mus’ab ke ciki hankalinta a kwance yake, da kanta ta xebo abinci ta zauna ta ci ta xora da ‘ya’yan itace, ta yi wanka ta hau gado ta yi kwanciyar ta tana tambayar Saddiqa,. To don kin qi ci kin qi sha sai me? Ina ce duk iya shegenku ne ya jawo hakan? Da kin hanashi ai da bai yi ba. Saddiqa ta zuba mata ido tana kallon ta cikin matsanancin takaici, ta ma rasa me za ta ce mata. Dare ya yi nisa sanda ta farka ta duba agogon wayarta uku da rabi ne na dare, ta shafa inda Abu ke kwance ba ta nan, ta tashi ta tura qofar banxaki a hankali don ta gani, nan ma ba ta nan. Ta fito falo ba ta ganta ba. Har ta zuwa za ta koma xaki sai ta tura qofar xaya xakin, Abu tana ciki a zaune kan sallaryarta hannayenta duka biyu a xage zuwa sama, kuka take yi hawaye sai gudu suke yi a fuskarta. “Ya Ubangiji, wannan yaro Mus’abu….” Abin da kawai Saddiqa ta iya ji kenan. A hankali ta mai da qofar ta rufe ta nufi xaki ta je ta kama tata harkar. Suna idar da sallar asuba suka isa asibitin, har lokacin Mus’ab yana kwance a rigingine kamar yanda suka barshi, bambancin kawai shine a yanzu yana furta kalmomi da wanda ke kusa da shi yake iya ji. “Cikina, cikina, a san min ruwa in sha”. Saddiqa ta kalli mahaifinta ta ce, “Baba wai zai sha ruwa”. Kawu Gixe bai kulata ba sai Sani ne ya yi mata bayani, “Sun ce kar a ba shi komai”. Tausayin halin da yake ciki yasa Saddiqa ta soma zubar da hawaye. Da sauri Kawu Gixen ya ce mata, “Ke, kar fa ki kawo mana iya shege a nan? Kuka? Ba ki san za a yi hakan bane da kika ingizashi yaje ya yi? Wannan fitina da me ta yi kama? Dole ne sai kowa ya haihu? Waxanda basu haihu ba basa rayuwa ne? Yanzu babu bayin Allah mutanen kirki da su basu haihun ba?” Abu ta tave baki ta ce, “Uhm! Nima dai abin da na ce mata kenan”. Sani ya yi maza ya ce, “A’a, Kawu Aisha kuwa babu yanda ba ta yi da shi ba shi ya qi”. Da sauri Kawu Gixe ya ce, “To me yasa ba ta faxa ba ta ja bakinta ta yi shiru?” Cikin nutsuwa Sani ya ce, “Kawu ina ganin tuna an riga anyi sai ayi addu’a kawai ayi dace, ita Aisha kam Kawu kowa ya ganta ai ya san ta shiga wani al’amari, tunda ai ko shekaran jiya gidansu ba haka na ganta ba, daga jiya zuwa yau ne fa ta yi wannan zabgewar”. Kwanan Mus’ab uku kafin ya dawo cikin hayyacinshi sosai ya san abin da yake ciki da waxanda suke tare da shi. Kowa sai murna yake, yana fara samun sauqi Abu ta yi xib! Ba ta ko kallon inda yake kwance, ko ya yi qarfin hali ya yi mata magana ba ta wani kulawa balle ta amsa. Saddiqa ta kalle shi ta ce, “To kai ka yi haquri mana ka yi shiru dole ne sai ka kula Abu?” Abu ta galla musu harara dukansu biyun, ta ce, “To ni don ba a kulani ba sai me? Ni ai bake ba ce ya dena kulani mana. Fitinannun mutane masu neman fitinar tsiya, ana zaune lafiya ku tada mutane a tsaye”. A hankali ya buxa baki ya ce, “Ki yi haquri Abu, Aisha ba ta da wani laifi nine na hanata gaya muku, in ta bi umarnina kuma ai ba laifi ta yi ba”. “To amma kai me yasa za ka yiwa kanka irin wannan abin, kai baka san haquri ba?” Ya xan yi murmushi ya ce, “Zuciyata ce Abu ta qi ta yi min daxi, babu abin da take so irin ta ga Aisha da ciki, ko ganin mace mai juna biyu na yi sai in ji inda a jikin Aisha yake da ya ya zan ganta ta yi?” Ta kawar da kai tare da tsaki ta wuce ta yi tafiyarta ta barsu su biyu. Ya miqa hannu ya yafito Saddiqa ta matso kusa da shi, a hankali ya buxa baki ya ce mata. “Ki yi haquri Aisha, mun sha wuya amma kwanan nan in muna raye da yardar Ubangiji buqatarmu za ta biya, zan ganki kema kina tura cikinki kamar yanda nake ganinshi wurin matan mutane”. Saddiqa ta yi murmushi ta ce, “Amma dai kuwa kafin ayi hakan Yaya ai kuwa dai kam an sha wuya”. Ya ce, “Eh, amma ai babu komai Aisha, in dai har buqata ta biya to ai kuma duk wata wahala tarihi ce”. Ta ce, “Haka ne Yaya”. An sallamo Mus’ab ya dawo gida a dal8ilin sauqin da ya smau. Kawu Gixe da Abu kuma sun koma gida Misau. SHEKARU BIYAR BAYAN YIWA MUS’AB TIYATA Saddiqa da mijinta suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali da nunawa juna qauna mai yawa, sai dai har yanzu matsalar gidan ba ta kau ba, buqata kuma ba ta biya ba, haihuwa da ake neman ba ta samu ba. Bayan tiyatar farko da aka yi mishi, Mus’ab ya sake komawa wata tiyatar nan ma ya tsira da qyar, ita ma dai anyita ne a dalilin jijiya ta toshe, wato dai lalurar farkon ce ta sake dawowa. Har yanzu kuwa babu wata alama da ta nuna an samu nasara, domin cikin shekaru bakwai xin aurensu ba a tava ko da vari ne a gidan nashi ba, sai dai al’ada ta xuake, in anyi bincike a ce wani ciwo ne yake neman tava mahaifa. Suna cikin rumfa a harabar gidan bayan Mus’ab xin ya dawo daga gudun motsa jiki suna tattaunawa. Ya miqa hannu ya xauki inibin da ya tarar tana ci a tiren silba yana taunawa a hankali. Saddiqa ta zuba mishi ido cikin nutsuwa saboda ta gane akwai abin da yake son gaya mata. “Na ga kamar magana za ka yi?” Ya xan yi murmushin qarfin hali tare da faxin, “Hankalinki nake so ki bani”. Ta yi maza ta ce, “Dama a wurinka yake”. Ya ce, “To, kin gane ko?” Ta ce, “Uhm! Ina jinka”. Ya yi ajiyar zuciya mai qarfi ya ce, “Yanzu ke Aisha kina ganin zamanmu haka a gidan babu qaruwa ya yi dai-dai?” Ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce, “Babu haihuwa mana, ke kin ce ba ki yarda a ce za a sake yi min wani aikin ba, a gabanki ne kuma likita ya tabbatar mana da cewar ciwon nan ya sake dawowa, amma in anyi saurin cire shi ba zai zamo mai tsanani sosai ba. To ina ce gara kawai in je ayi aikin tun bai qara yin qarfi ba?” Ta zuba mishi ido tana kallon shi a wani yanayi na rashin sanin abin yi, da qyar ta iya buxa baki ta ce mishi, “Ashe maganar sake yin aikin nan bai qare ba?” Ya gyara zama cikin sakin fuska ya ce, “Ba wai bai qare bane, so nake mu fahimci juna ni dake Aisha, nima ba son aikin nan nake yi ba, to amma ya ya zan yi?” Ta zuba mishi ido kamar ta yi magana, sai kuma ta fasa. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ina zuwa”. Da sauri ta miqe ta shiga gida tamkar mai xauko wani abu ta dawo. Ya zauna nan wajen minti sha biyar bai ga ta dawo ba, ya miqe ya bi ta cikin gida su qarasa maganar. Yana shiga falonta ya tarar da ‘yar guntuwar takarda ajiye a kan kujera. Ga abin da ya gani a rubuce. YAYA MUS’AB Na dai lura babu abin da kake so irin ka ganni cikin tashin hankali da damuwa, ka ganni cikin matsanancin hali. To na gaji ba kuma zan sake yarda ka sake jefani cikin wata fitinar ba, don haka na tafi, daga yau na bar maka gidanka, zan koma gaban masu tausayina”. Sai wata rana. Mai qaunarka Aisha. Mus’ab ya zubawa wasiqar ido cikin kixima, ya rasa me ya faru? Me ya yi da zafi haka har da za a xauki irin wannan matakin? Tsawon lokaci yana tunani ya kasa ganowa. To ko dai ta gaji da zama dani ne babu haihuwa? Tunda ta san matsalar tawa ce. Ya xauko wayarshi ya danna lambobinta, ta xauka ya jita tana kuka, jikinshi ya yi sanyi maimakon vacin rai zalla. “Aisha me ya faru? Ki dawo mu yi magana”. “Ka qyale ni kawai, ka barni kawai in huta na gaji, na gaji da ganin fitina gara in yi nesa da ita”. “Kina ina ne yanzu?” Ta ce, “Ina kan hanyar tafiya gida, zn tafi Misau zan koma gaban iyayenmu”. Ba ta jira wata magana daga gareshi ba ta yi maza ta kashe wayar tata. Ya zubawa wayar ido yana kallonta tare da nanata faxin Misau. Cikin kixima. Saddiqa tana zaune gaban Gwaggonta cikin gajiya da vacin rai, tunda ta isa take zaune gabanta tana kuka, hankalin Gwaggo ya kai matuqa wajen tashi saboda kukan da take yi da kuma halin da ta ga Saddiqan a ciki. Abu ta iso saboda aiken da Gwaggo Habiban ta yi mata, ganin Saddiqa ya sata mummunar faxuwar gaba, ta nemi wuri ta zauna cikin sanyin jiki tana tambayar ta. “Lafiya? Me ya faru? Me ya kawo ki gida ke kaxai? In ma rikici kuka yi ai bai kamata ki biyo doguwar hanyar nan ke kaxai ba, in kika yi haquri zai wuce kina xakinki. In abin ya yi tsanani da za ta faxa ma sai a tashi babba ya je” “Inna ai tunda aka kai mishi ita ba ta tava shiga wannan yanayin ba, in dai kuma ba matsalarsu bane”. Gwaggo Habiba tana faxin hakan ta kama kuka, duk da a gaban Abu take ta kasa haquri yau kam ta voye damuwarta kan lalurar rashin haihuwar Mus’ab, xa guda xaya namiji da take da shi. A baya ba ta tava tsammanin hankalinta zai koma gare shi har damuwarshi ta zama tata ba irin yanda ta zama a yanzu, ta rasa dalili, xinbin jikokin dake gareta sun kasa sanyaya zuciyarta ta yi sanyi kan rasa xa a gidanshi da aka yi. “Me ya faru Saddiqa? Yi magana mana, ki gayawa uwarki damuwarki kinga kin sata tana kuka. Yi mata bayani dan ta samu sauqin damuwarta”. Cikin zuciyarta ita ma ta yi tunanin yarinyar nan wataqila ta gaji ne da lalurar Mus’abu tunda ta riga ta san matsalar tashi ne. tausayin Mus’ab ya yi matuqar kama ta. Cikin kukan ta ce, “Na gaji, fitinarshi ta isheni, don haka na bar mishi gidanshi yaje ya yi ta yin abin da ya ga dama”. Ta miqe taje ta hau gadon Gwaggonta ta yi kwanciyarta saboda kasancewar hutun sallah take yi. Gari ya waye sanda ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan xumin da Gwaggonta ta kai mata, ta fito ta zauna tana shafa. Gwaggo ta kalleta cikin nutsuwa da kulawa ta ce mata, “Kin rame Saddiqa, tunda kika je gidan mijinki ban tava ganin ki na kasa jin daxin ganin naki ba irin wannan karon, ku rinqa yiwa rayuwa haquri, duk abin da kuka gani zai wuce wata rana har ayi ta bayar da labari”. Ta ce mata, “To Gwaggo”. Ta miqe ta xauko doguwar riga ta sanya ta rufe kanta da gyale, ba ta tsaya yin kwalliya ba tasa kai za ta fita. “To ina za ki ba ki karya ba?” Ta ce, “Da na je na gai da Baba ya ce in na kintsa in je yana son magana dani, kuma na ga shigar Abu ma wurin shi kar in tsare su”. Ta ce mata, “To”. An haxu a xakin Malam Abdullahi shi da Abu da Saddiqa, ta sake gai da shi cikin ladabi da nuna girmamawa. A hankali cikin nutsuwa ya tambaye ta. “Me ya faru kika baro mijinki kika dawo gida ke kaxai Saddiqa?” Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Baba na gaji da zama da shi ne kawai”. Gaban Malam Abdullahi ya yanke ya faxi, cikin zuciyarshi ya tabbatarwa kanshi rashin haihuwar Mus’ab ne ya isheta, tausayin Mus’ab xin ya kama shi. Sai dai kuma nan take sai ya ji zuciyarshi tana raya mishi zai tsaya ya ga an yiwa Saddiqa adalci tunda dai ai ta yi haquri, bana shekaru bakwai ne da auren nasu, amma ba ta tava buxa baki ta yi wata magana ba. “Assalamu alaikum”. Suka jiyo muryar Kawu Gixe yana sallama daga bakin zaure. Da sauri Gwaggo Habiba ta fito daga wurinta don taran xan’uwan nata, sai dai ganin Mus’ab biye da shi ya sata kaucewa ta koma zuciyarta ta yi mata qunci ganin yanda Mus’ab shima ya rame har ma gara ta Saddiqan da tashi. “Kin tarasu ne a nan kina yi musu qarya suna sauraron ki? Za ki fita ki ba mutane wuri ne ko kuwa?” Da sauri Malam Abdullahi ya ce mishi, “A’a, ba fa irin wannan hukuncin a a zartar a tsakaninsu ba, don tunda ta kawo maganar gabanmu, to gaskiya da gaskiya ne kawai zai yi maganin al’amarin”. Abu ta yi maza ta ce, “Gaskiya kenan, ke Saddiqa dawo ki zauna ki faxi abin da ya dameki babu zare ido cikin lamarin balle a je ana tsorata wani”. Ta koma ta sake zama can gefe a rakuve. Malam Abdullahi ya zuba ido yana kallon ta. “Kin ce kin gaji da zama da shi me kike so ayi miki?” Cikin nutsuwa ta ce, “So nake a rabamu”. Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, kanshi a sunkuye ya yi maza ya qara sunkuyarwa. “A raba ku a kashe auren kike so?” Ya yi mata tambayar idonshi yana kallon ta. Ta ce, “A’a, Baba zama da shi wuri xaya ne kawai ba zan iya ba”. Gaba xayaa kowa a xakin ya samu sauqi, tun ma ba Mus’ab da Abu ba. “A barni in zauna a gida shi kuma yaje can ya yi zaman shi”. “Ya yi miki wani mummunan abin kenan?” Abu ce ta yi tambayar hankalinta a kwance saboda ta gane rikici tsakaninsu ne ya dawo da Saddiqa gida ba rabuwar aure take so ba. Ta ce, “Bai min komai ba na gaji da zama da shi ne kawai, saboda na gaji da halinshi na son kai, bai san kowa ba sai kanshi, abin da ya ga dama yake yi, in ya tashi yi kuma baya tausayin kowa, ba……..” Kawu Gixe ya ce, “A’a, ya fa isa haka, ya isa, don sun xaure miki gindin ki yi magana ba yana nufin za ki zaunar damu ki zage shi a gabanmu bane, ki faxi abin da ya kawo ki in ji tun ranki bai vaci ba”. Kanta a sunkuye ta ce, “Aikinshi zai sake”. Kawu Gixe ya qara tunzura, ya ce, “To in zai sake aikinshi ina ruwanki, da can ke kika samar mishi wannan xin da yake yi?” Abu ta kalleta a hankali ta tambaye ta cewa, “Wani garin zai koma bakya so?” Ta gane dai ba a gane maganar ba, don haka ta gyara da cewa, “Ba aiki ba, tiyata”. Gaba xaya aka xauki salati. “Tiyata?” Abu ta yi tambayar da qarfi. Ta kama baki ta riqe tana kallonshi cikin mamaki. Saddiqa ta ci gaba da bayani kanta a sunkuye. “Aikinshi na farko tilastani ya yi na yarda ya kuma hanani faxa muku, da aka ce ciwo ya dawo ya ce zai koma na ce a’a, a haqura har muka yi rikici da shi, na ce to kar ya sake yi min maganar. Ban ankara ba sai kawai na jishi a asibiti wai ana aikin, yanzu kuma sun sake cewa wai ya fara dawowa ya zo yana gaya min zai sake komawa, duk da na ce a’a, na san ba zai fasa ba. Shi yasa na yi hanzarin dawowa gabanku don ban san ranar da zai tafi ba”. “Kina da gaskiya, Mus’abu ya ci a guje shi”. Tana maganar tana kuka. “Wata tiyatar za ka sake komawa bayan duk hatsarin da aka tsallake? Ana yiwa Ubangiji qarfi ne?” Kawu Gixe ne ya jero mishi tambayoyin yana mai tsare shi da idanuwa. Kan Mus’ab a sunkuye ya shiga bayani cikin ladabi don ya samu goyon baya. Abu ta katse shi ta hanyar faxin. “Kai tafi can, Saddiqa ba za ta sake binka ba ka je can ayi ta yi maka tiyata ana maimaitawa kai kaxai, za ta zauna kusa da iyayenku ta samu nutsuwa, ta gaji da ganin fitina, ta gaji da fitinarka. Kai fitinannen mutum ne, a ce mutum bai san haquri ba”. Ta soma kuka, kuka kuwa mai tsanani da ya yi dalilin da ta fita ta bar gidan ta tafi nata. Tsawon lokaci xakin shiru babu wanda ya sake cewa wani abu. Kawu Gixe ya kawar da shirun ta hanyar yin magana a hankali, kuma cikin nutsuwa. “Ina fata wannan maganar da ta yi na kana shirin komawa wani tiyatar ya zama qarya ta yi maka ba gaskiya ta faxa ba”. Shiru ya yi bai iya cewa komai ba, duk da ya san Kawu Gixen shi yake sauraro. Gajiya da shirun Kawun ya yi ya ci gaba da maganar da ya katse. “Kar in sake jin ka tayar da maganar tiyata a gidanka balle har aje ga sake yanka maka wani wuri a jikinka, ya isa haka. Abu guda xaya da zai hanani haramta maka komawa asibiti shine, neman magani halal ne, amma ban yarda ya kai ga yanka jiki ba. Muma a nan zamu yi iya namu in mun ji mai magani na halal zamu karvar muku, muna yi muku addu’a zamu qara, in mun sadu da mutanen da alherinsu ya bayyana zamu roqesu su taimaka mana da addu’a. Mai bayarwar Ubangiji ne, shi kuma in ya yi nufin samun, to kun ne kawai fayakunu. Shi kenan sai ka ga an samu. Ku dai ku dimanci istigifari, ku kuma haxa da haquri. Ke Saddiqa ki je wurin uwarki ki yi mata sallama ku je wajen Inna ku yi mata sallama ku ba ta haquri, don ta tafi hankalinta a tashe”. Ta ce mishi, “To Baba”. Ta tashi ta fita ta barshi yana ci gaba da yiwa Mus’ab nasiha kan muhimmancin haquri da miqa wuya ga Ubangiji. Ya ce, “To Kawu”. Mus’ab ya shigo falon Gwaggonshi cikin ladabi, ya koma kan shimfixa can gefe ya zauna cikin nutsuwa, qafafuwanshi a harxe ya shiga ba ta haquri. “Ku yi haquri Inna ba zan sake ba, dama ni wai burina in dai ga Aisha ta haifar muku xa ne ko da guda xaya ne da zai rinqa zuwa yana yi muku zarya a tsakar xakin nan ne kuna ganin shi, to ga shi ta zo ta haxani daku har Kawu Gixe da su Abu duk sun mara mata baya a kan wai basu yarda in sake zuwa tiyatar ba. Shi kenan ni kuma ba zan haifar muku kowa ba kenan?” Ya sunkuyar da kanshi qasa, hawayen da suka taru a gefen idonshi suka xiga. Gwaggo Habiba ta yi kamar ba ta gani ba saboda kawar da kanta da ta yi, cikin nutsuwa sai ta ce mishi, “Tashin hankalin dake cikin tiyatar ya yi yawa, ka bar gidanka ya zauna lafiya tunda ita matarka ba tayar maka da hankali take yi ba, kai ma sai ka yi haquri. Ai ana addu’a ba kuma za a daina ba, al’amarin kuma duk na Ubangiji ne”. Ya ce, “To Inna”. Cikin zuciyarshi daxi ya kama shi, godiya yake ta yiwa Ubangiji da ya nuna mishi daidaituwar al’amuranshi da iyayenshi, musamman ma mahaifiyarshi. “Ke Saddiqa tashi mana baki ji mijinki ya shigo bane?” Ta ce, “Qyale shi kawai Gwaggo, ya riga ya vata min rai ba wani binshi zan yi ba”. Ta ce, “A’a, a’a, bana son rashin haquri, ina ce an riga anyi mishi faxa ya kuma ce ba zai sake ba?” Mus’ab ya xan gyara a hankali ya ce, “Nima fa tana vata min rai Inna ina dai yin shiru ne kawai, saboda ni xin babba ne kar a ce bani da haquri”. “Me take maka?” Gwaggo Habiba ta buqaci sani. “Tana takura min ne Inna”. Saddiqa ta yi maza ta tashi ta zauna tana kallon shi, ya qi kallon ta balle ya ga kallon da take yi mishin. A hankali cikin nutsuwa ya ci gaba da yiwa Innarshi bayani. “Magana da baki ne kawai ba ta yi Inna, amma kullum aiyukanta na nuna matsuwarta ne kan son haihuwa, kullum a cikin sayayyar kayan jarirai take, babu halin mu fita mu dawo ba ta sani na sayi kayan jarirai ba wai sun ba ta sha’awa. Sannan ina yi mana qoqarin jariran mu samu ko da guda xaya ne ta zo ta kawo qarata an hanani. To ku gaya mata Inna ta fita hanyata da irin wannan sayayyar, kar kuma in sake dawowa gida in samu tana karkaxe kayan, in na yi magana ta ce wai qura suka yi”. Daga shi har Saddiqan tausayinsu ne ya qara mamaye zuciyar Gwaggo Habiba, sai dai ba ta bari sun gane ba. Ta ce, “Ke Saddiqa in kun je gida ki yi kyauta da kayan jariran nan da kika tara mishi a gida, ina dalilin su? Kayan sha’awa yana qarewa ne? In haihuwar ta zo kece mai sayen riga? To bana so”. A hankali ta ce mata, “To Gwaggo”. Ta sake kallon Mus’ab ta ce, “Ku dage a kan yin addu’a, in ka ga har ka samu dagewa kan roqon Ubangiji kan wata buqata taka, to qila ya yi nufin biya maka buqata ne, don haka kar ku gaji da addu’a, in za ku kwanta kuma ku rinqa karanta (Suratul Maryam) bayan addu’o’inku na kwanciya sau uku in har da rabon to zamu sadu da biyan buqata”. Ya ce mata, “To Inna”. Suka yi mata sallama suka nufi gidan Abu, daga can suka nufi gidansu inda za su kwana washe gari suyi sammakon tafiya Ajakuta. SHEKARU GOMA DA AUREN SU MUS’AB Mus’ab yana zaune a falonshi yana rubuce-rubuce, ya isa ya yi qiba ya yi jajur saboda wadataccen kwanciyar hankalin da ya samu shi da matarshi, a yanzu sun daina zancen haihuwa da damuwa kan al’amarinta, iyaka dai kullum a cikin addu’a suke, suna kuma ta shan magani na asibitin da na Hausa, saboda kullum iyayensu a cikin aiken magungunan suke. Tun ma ba Gwaggo Habiba ba, in da duk aka ce mata ga mai magani za ta je ta karvo ta kuma aike musu. Saddiqa ta shigo falon cikin kwalliya da qamshi mai daxi, kana ganinta za ka tabbatar eh, ta dace da zama matar Mus’ab. Can gefe ta je ta zauna tana cin kilishinta, a hankali ya xago ido, ya ce, “Haba Aisha wannan wane irin rowa n? Kin yi min rowar qamshimki to kilishin ma ba za ki yi min ta yi ba?” Ta yi murmushi ta ce, “Kilishi kai ka ce bai maka daxi ba”. Ya ce, “To na ji ke fa?” Ta taso daga inda take ta zo gare shi, ya ware hannayenshi duka biyu ta shiga cikinsu ya mayar ya rufe, tsawon lokaci suna wasanninsu kafin ya gaji ya miqe tsaye xauke da ita a hannunshi ya nufi xakin kwanciyarshi, tare da faxin muje daga ciki zan fi ganin fasalin kwalliyar taki. Gabanta ya faxi, sai dai kuma ta yi maza ta shanye. Yana daga kwance yana kallon ta bayan ya kammala abin da zai yi. “Kina da matsala amma kin qi ki yarda a tsakanin duk lokacin da na kusanceki sai na gane dauriya kawai kike yi kina haquri dani, amma na tambaye ki kin ce ba haka bane”. Ta yi murmushi ta ce, “Me ka gani?” Ya harare ta bai tanka ba. Ta sake wani murmushin ta ce, “Ni bani da matsala”. “To ai shi kenan tunda abin da kika ga ya fi miki kenan. To maganar tafiyar fa?” Cikin nutsuwa ta ce mishi, “A’a, Yaya ba bana son binka bane, amma ina so Gwaggona ta zo ta yi min baqunta, shekaru goma ne fa tunda ta aurar dani amma ba ta tava sanin xakina ba, in ma kunya ne ya hanata zuwa xakina, to yanzu kam ai na girma na isa a zo min baqunta”. Ya jawota jikinshi ya qanqame, ya ce, “To in surukinta take kunya fa?” Ta ce, “Eh, ai shi yasa nake so in yi amfani da lokacin tafiyar taka sai ta zo mu sake a gidan, tunda ta san baka nan”. “In dai tafi kenan in barki”. Ta ce, “Eh, ina maka fatan alheri”. Kwana biyu bayan nan Gwaggo Habiba ta iso gidan don yiwa Saddiqa baqunta kamar yanda ta nema a dalilin tafiyar Mus’ab xin zuwa qasar Bulgeria kan wani aiki da aka tura shi, inda zai je ya yi watanni uku. Saddiqa sai kaiwa da kawowa take yi tana tarairayar Gwaggonta wacce ta mayar tamkar wata jaririya saboda tattali da kulawa, ta sake kewayeta da nau’o’in abin sha bayan ta kwashe na cin. Ta dawo ta zauna kusa da ita suna hira. “Iko sai Ubangiji, gaba xaya mijinki ya canza Saddiqa, xan kwana biyun da na yi tare daku a gidan nan kafin ya tafi sai na ga gaba xaya ya zama kamar ba shi ba, na ce hala shi yasa kema kika sauya. Rabon da ki yi kyau irin wannan tun farkon zuwanku gida”. Saddiqa ta yi murmushin jin daxin yabon da aka yiwa mijinta, ta ce, “Don ma bani da lafiya Gwaggo”. Da sauri Gwaggo ta tambaye ta cewa, “Baki da lafiya me ya same ki?” Ta xan yi shiru ta rasa ta inda za ta soma maganar. Gwaggo ta kalleta ta ce, “Ni kuwa ai ba wacce za ki voyewa al’amarinki bane in dai ba kina nema ki canza bane”. Da sauri ta ce, “A’a, Gwaggo ba haka bane, wani abu ne ya same ni babu halin Yaya ya tavani sai cikina ya qulle ya yi ta faman ciwo, in yi ta murqususu ina wahala, sai da qyar zan samu ya sakeni bayan na yi gumi na yi kashirvan. Ko jiya da daddare Gwaggo ba rashin kunya zan yi miki ba, na yi haquri da shi ne kawai don na san wayewar garin yau xin nan tafiya zai yi”. Jikin Gwaggo a sanyaye ta ce mata, “To amma ba ki gaya mishi ba?” A hankali cikin nutsuwa ta ce mata, “Shima ya gane don ya gane ina fargabar ya tavani, na dai qi yarda ne kawai sanda ya yi min maganar”. “To me yasa kika qi yarda Saddiqa? Matsala irin wannan ai ba za ki yi shiru ba”. Cikin nutsuwa ta ce mata, “Gani na yi mun samu nutsuwa bai cika ma yin maganar asibiti ba in ba dubiya muka je ba, maganin da kuke aiko mishi kawai yake sha. In na ce mishi bani da lafiya sai kuma ya ta da hankali ya ce shine yasa min ciwon. Sannan kinga wani qullutun dake nan gefen marata Gwaggo ba ki ji ciwon da yake yi min ba, duk abin da nake yi qarfin hali ne kawai, in na nuna mishi wannan ai ban san tashin hankalin da zai yi ba”. Gwaggo tasa hannu tana tava gefen marar tata, abin da ta jin ya yi mummunar faxar mata da gaba. “Gareka muke bauta ya Ubangiji, gareka kuma muke neman taimako”. Kalmomin da take ta furtawa kenan. Cikin nutsuwa ta kalli Saddiqa ta ce, “Wannan ai ba abin voyewa bane, kar ki sake yin haka, yanda duk kika kai da gudun tashin hankalinshi ai dole ya san damuwarki, in kika voye mishi wa za ki gayawa? Shirya mu tafi asibiti yanzu”. “To ko zamu bari sai gobe Gwaggo tunda yamma ta yi?” Gwaggon ta kalleta, ta ce, “Ke shirya mu tafi za ki yi ta zama da ciwo ne? In ta kama mu kwana a can ba sai mu kwana ba”. Dr. Usman ya gama duba Saddiqa, ya kalleta cikin nutsuwa ya ce mata, “Sauka ki zauna a can”. Ya nufi wajen zamanshi ya zauna Gwaggo tana binshi da kallo. “Ciki ne!” “Na’am”. Kamar cikin firgita Gwaggon ta faxi hakan. Hankalinshi a kwance ya sake faxin, “Ciki ne ya fita ne daga cikin mahaifa yana so ya kawo matsala, in ba wanke shi aka yi ya fita gaba xaya ba za ta samu lafiya ba”. Gwaggo ta soma kuka, “Wankewa ya fita likita bayan duk wannan wahala da aka yi?” Ya ce, “Eh, to ina ganin kamar ya fi sauqi tunda an samu lafiya ai za a sake samun wani, in kuma kin fi so a gyara mishi zama sai a gyara. Sai dai za ta yi ta wahala don za ta yi ta zama cikin dokoki”. Ta ce, “Eh, gara a gyara”. Gwaggo tana zaune kan kujera tana jiran a fito da Saddiqa daga xakin da ake yi mata gyaran cikinta, cikin zuciyarta kuwa kiran sunayen Ubangiji take yi tana qara yi mishi tasbihi. Sun dawo gida Saddiqa tana kwance saboda umarnin likita na kar ta yi wani aiki ko kuma motsi mai qarfi na tsawon sati biyu. Gwaggo ce take kai wa da kawowa a cikin gidan, sai ji da Saddiqan take yi kamar ta lasheta don farin ciki. Kusan kullum raba dare take yi tana roqon Ubangiji ya tabbatar da wannan ciki ya zaunar da shi lafiya, ya tsare mai xauke da shi daga duk wata wahala. In kuma lokacin haihuwar ta zo yasa a samu haihuwar cikin sauqi, abin da za a haifan kuma yasa ya zama mai albarka. Sati uku Gwaggo Habiba ta yi maimakon biyu da ta zo da niyyar yi, tana komawa gida kuma Abu ta taho da niyyar zama, ba za ta koma ba har sai Saddiqan ta haihu ta yi mata jego. Ran nan da asuba misalin qarfe huxu da rabi na asuba Mus’ab ya bugo mata waya. “Wash! Yaya daga bacci fa ka tasheni”. “Ai gara in tasheki Aisha don ki qara sanin nima ba wani baccin nake yi ba, ba ki san irin haushin da nake ji ba da na yarda na baroki a gida, na riga na saba a tattaleni sai in rinqa jin na takura da yawa, ga shi kwanakin sun qi gudu balle in samu in yi in dawo in same ki”. Ta yi murmushi ta ce, “Ka yi a hankali Yaya kar ka damu kanka da son sai ka yi sauri, magana guda xaya dai da zan yi maka ita ce, ka taho da goron albishir mai girma, don za ka dawo ka samu abin da zai faranta maka rai irin farin cikin da baka tava yi ba a rayuwa”. Ya yi dariya ya ce, “Kin mai da maganar wasa Aisha tunda kika faxi hakan, ni yanzu da wani farin ciki da zan yi wanda ya kai na ranar da Kawu Gixe ya bani ke balle har ya fishi?” Ta ce, “To ai shi kenn Yaya mu bar maganar kawai sai ka dawo”. Ya ce, “To shi kenan sai na dawon”. Cikin Saddiqa ya shiga wata na shida lokacin da aka soma shirye-shiryen dawowar Mus’ab. Ran nan tun safe ya iso gidan a dalilin saukar asuba da ya yi, ga mamakinshi bai ga Saddiqa wajen taren shi a airport ba, sun iso gida bai ganta a qofar gidan ba. Ya shiga falo yana zaton ganinta, Abu ya gani. Cikin mamaki ya buxe baki ya ce, “Hajiya Abu nake gani a gidan ko mafarki ne?” Tana murmushi ta ce, “Ba mafarki kake yi ba nice”. “Kar dai ki ce min kema zumuxin dawowar nawa ne ya saki yin wannan doguwar tafiyar don ki tareni”. Ta sake wani murmushin ta ce, “Zumuxin yi maka albishir da taryen abin alherin da ya samemu ne ya kawoni Mus’abu, ni kam ai ba jiya ko yau na iso gidanka ba, watana biyu kenan. Matar gidan ce kawai ba ta yarda a gaya maka ba”. Kan Mus’ab ya xauke jin kalaman Abu, amma don ya sauwaqewa kanshi komai sai ya tambaye ta. “Ina Aishan take Abu?’ Ta nuna mishi xakinta, ta ce, “Ni na hanata tashi tarenka na ce ta jiraka nan inda take za ka zo ka sameta saboda ta bi dokar da likita ya sanya mata”. Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, kar dai lalurar da ya bar Aisha tana vovvoye mishi ce ta yi riqan da har likita yake doka a kai? Da sauri ya faxa xakin nata, qamshi da ni’imar dake ciki bai hanashi kaxuwa da ganin da ya yi mata a kwance ba. “Me ya same ki Aisha?” Ya yi tambayar a sanyaye. Ta saki lallausan murmushi tana daga kwancen ta ce, “Qaraso mana Yaya, so nake in jika a jikina”. Tana faxin hakan ta ware hannayenta nuna alamar shi take sauraro. Ya yi maza ya qarasa gareta, nan take suka soma tumurmusar juna, sai dai basu je ko’ina ba ya ja ya tsaya yana kallon ta cikin kixima. “Mene ne wannan Aisha?” Ya yi tambayar yana mai kallonta. Ta saki lallausan murmushi a hankali cikin yanayi na raxa ta ce mishi, “Ciki ne, cikin da kake ta fatan ganinshi a gidanka ne yau kake ganinshi, shine albishir xin da dama nake gaya maka na tanadar maka”. Yasa hannu biyu ya qanqameta a jikinshi tamkar dai ba a cikin hayyacinshi yake qanqamar ba saboda tsananinta. “Haqiqa kin yi min albishir Aisha da abin da tuni na haqura da ganinshi a gidana, don haka nima zan yi miki tukwuici da abin da ba ki tava tsammanin samun shi ba”. SHEKARU GOMA BAYAN NAN Mus’ab mai shekaru hamsin da huxu a duniya, yana zaune a hamshaqin gidanshi dake unguwar G.R.A kan titin T/Valewa a cikin garin Bauchi. Mus’ab ya ajiye aikinshi ya dawo gida shekaru biyu da suka wuce, ya kuma zavi zama kusa da Kawu Gixe, don haka ya gina wani tafkeken gidan a Bauchi. Ya yi hakan ne kuma don cika burin da yake da shi na ganin ya sadaukar da abin da ya saura na rayuwar wajen ganin ya bayar da ingantacciyar tarbiya ga yaran da ya haifa, a ganin Mus’ab tarbiya wata aba ce dake buqatar lokaci, haquri, juriya, tausayi, kulawa da kuma soyayya. Haka nan aiki ne da ya hau kan iyaye duka biyu, wato uwa da uba. Yana zaune cikin hamshaqin falonshi da duk wani abin da ke ciki daga qasar Italy ya shigo da shi, tare da ‘ya’yanshi guda uku, Maryam, Abdullahi da Muhammadu Gixaxo takwaran Kawu Gixe. Gaba xaya litattafansu suke nuna mishi lokacin da Saddiqa ta shigo cikin falon sanye da doguwar riga xinkin senegal a jikinta, ta yi kyau sai sheqi take yi, ta nemi wuri ta zauna sannan ta kalli yaran ta ce musu. “Maza ku tashi ku tafi ga Malamin ku ya zo”. ‘Yan samarin biyu suka yi waje da gudu suna rige-rige, ya yin da ‘yar budurwar ta qara lanqwashewa jikin mahaifinta tana tambayarshi. “Baba ina ce nice mamanka?” Ya yi maza ya amsa mata tare da zuba idanuwanshi a gareta, “Ke ce mamana Mama”. Saddiqa ta sake kallon yarinyar wacce ta yi kamar ba ta jita ba, ta ce mata, “Kema tashi ki bisu”. Ta miqe tsaye ba don tana so ba sai don bin umarni, ta kama hanyar fita daga falon. Mus’ab ya bita da kallo har sai da ta vace mishi daga gani. Maryam ita ce yarinyar da Mus’ab ya xauki son duniya ya xora mata saboda dalilai masu yawa, farko samunta da ya yi bayan ya xebe tsammani, na biyu takwarar Innarshi ce matar Kawu Gixe wacce take mahaifiyar Saddiqa. Na uku tsananin kamanninta da mahaifiyarshi Gwaggo Habiba, ko cikin ‘ya’yan da Gwaggon ta haifa ba a samu mai kama da ita haka ba. Sai na huxu basirarta, yarinya ce mai kaifin basira, duk shagwavarta da sakarcinta sau xaya tak malami yake faxar abu ta kama. Ya dawo da kallon shi ga Saddiqa cikin nutsuwa ya ce mata, “Kin korar mun uwata ba ki kyauta ba bayan ina jin xuminta”. Ta matso kusa da shi cikin shagwava ta langave a jikinshi ta ce, “Tausa nake so Yaya jikina ciwo yake yi min, Yaya ga shi kuma kasala ta dame ni”. Hanni biyu ya saka ya rungumo ta a qirjinshi, ya sake miqa hannunshi na dama ya tallabo qasan mararta cikin tausayawa da kulawa yake ce mata, “Haquri kawai za ki yi Aisha, ina ganin matsalolin nan naki suna samuwa ne a dalilin za ki sake samo min wata Innar tawa”. Saddiqa ta yi murmushi cikin shagwava ta ce, “Haba Yaya, ka rinqa samun Innar kenan? Ai gara nima ka yi min kara ka sanya min sunan Gwaggona”. Ya kalle ta cikin nutsuwar dake qara bayyanar da gaskiyar abin da yake faxi, ya ce mata, “Aisha ke a gareni tamkar wata tauraruwa ce da kusurwowi biyar ke gareta, kusurwar farko tana bayyana matsayinta, kusurwa ta biyu tana bayyana tausayinta, kusurwa ta uku tana bayyana gargaxinta, kusurwa ta huxu ita ke bayyana soyayyarta. Sai ta cikon biyar xin ita ce mai bayyanar da abotarta. Aisha gabana kan faxi in ji tamkar zan razana in na tuna a baya kin tava qina, sai in ce to da za ki sake yin hakan a yanzu a wane hali zan samu kaina?” Saddiqa ta yi murmushin farin ciki saboda gamsuwar da ta yi da matsayinta wurin mijinta. Ta ce, “Ai a wannan lokacin ina cikin wauta ne Yaya, ban san mene ne so ba, ban fahimci yanda soyayya take ba, ban gane soyayya ta asali ba. Zamana da kai ne ya fahaimtar dani na gane soyayya ta asali, babu ganin girman laifi a cikinta sai yanda za a yi a yafe, babu maganar sauraro a cikinta sai fahimta, babu rabuwa sai yanda za a yi a zauna tare har abada. Ni taka ce Yaya Mus’ab, Innarka ce ta haifar maka ni, dama don kai ta haife ni kar gabanka ya sake faxuwa a kaina, na kuma gode maka da ka yarda ka zaveni na zama nice tauraruwar zuciyarka”. Sai anjima. Mu sadu a wani littafin cikin yardar Ubangiji. Taku. Hafsat Chindo Sodangi. Alura: Sabon littafin MATA DA KICIN XINSU littafi na biyu yana nan fitowa ba da daxewa ba, a neme shi don samun qaruwa har da abincin masu lalurori.