[21/10/2021, 19:43] Ameera Adam🌚: 11.. Maganar Boka Marduska na sauka a kunnen Fulani Maryama ji tayi kamar saukar aradu muryarsa har wani amsa kuwwa take mata a kunne, nan take jikinta ya ɗauki tsuma bakinta har tuntuɓem harsge yake a hargitse ta ce. "Marduska ka taimaka mun ka tallafi rayuwata ka sanar dani ta yaya zan gane wace ce ita?" Boka Marduska wani kallo ya wurga mata yana ci gaba da hura wutar da ke cikin ƙoƙan ƙan ƙwarangwal yace. "Maryama me yasa taurin kai gare ki ne? Wannan maganar ba baƙuwar magana bace a gurinki ni kaina bazan iya ja da wannan yarinyar ba, hasali duk wani bincikena na gagara nemo ainihin kamannin yarinyar, abinda nake ta shakku a raina wai ma mutum ce ko itama ta fito cikin sigar aljanu? Waɗancen da suka shuɗe ɗaya ta fito cikin fararen aljanu ɗaya kuma ta fito daga baƙaƙaen aljanu. Abin da ban sani ba shin wannan ita daga wanne ɓangare take, taimako ɗaya zanyi miki Maryama idan har bincike ya bani dama..." Fulani Maryama har kusan faɗawa kanshi tayi jiki na rawa katse shi. "Marduska ka taimaka mun ko kamanninta ne ka gaya mini ta yadda zan fahimci wace ce daga ciki" Marduska ya tsuke fuska yace. "Maryama me yasa kin fiya rawar kai kamar wacce taci sadakar miji ne? Kinsan Allah da kin faɗa kan wannan wutar da kin gwammaci haɗuwarki da Rayzuta dukda kuwa karonku da ita ba alheri bane, kinsan wannan wutar ko yaya ta taɓa jikinki sannu a hankali nama jikinki zai fara zagwanyewa ga ɗoyin da zaki dinga yi kamar mushe" Fulani Maryama ta russuna ta ce. "Tuba nake sarkin bokayen duniya." Marduska ya cigaba da bincikensa a cikin wuta yana jefa waɗansu littafan tsafinsa, daga cikin wuta take wani fili ya bayyana, wata matashiyar budurwa ce a tsaye ta juya baya hannunta na saƙale da wani matashin saurayi." Yarfe gumin fuskarsa yayi sannan yace. "Maryama zo ki gani" Da sauri Fulani Maryama ta fara leƙawa fuska ɗauke da damuwa ta ce. "Marduska ban gane komai ba na hangi mace da namiji a tsaye, ka taimaka ka wayar mun da kai ka dubi girman tsafi ka siffanta mini ita" Marduska yace. "Yarinyar ƴar doguwa ce amma ba tsayi cen sosai ba tana da ɗan kauri kaɗan, kuma ba fara bace ba kuma baƙa wuluk bace. A taƙaice ruwan tarwaɗa ce sai dai a fuska kyakkyawa ce tana ɗauke da manyan idanu da dogon hanci yanayinta kamar na buzaye sai dai har yanzu ainihin siffarta yaƙi bayyana ta yadda zamu gane wace ce ita ya kamanninta yake, ni ina jin tsoron bincike akanta sabida rannan dana tura aljanu su ɗauko mun ruhin baiwarki Bintu ta kashe mun aljanun da suke mun wannan aikin, ina gudun karta fara waiwayo ni saboda tana ɗauke da ƙarfin iko akan mutane da aljanu." Fulani Maryama gabaɗaya ta haɗa gumi sai zare ido take kamar shege a rabon gado, hankali a tashe ta ce. "Marduska gabaɗaya kaina ya kulle ga wannan yarinyar ga warkewar Saif yanzu wane magani zaka bani wanda zai kuma nakasashi kuma idan na gano wace ce ita wane irin mataki zan iya ɗauka a kanta? Zan iya nasaka ta ko kuma na illa ta ta." Marduska wani kallo ya wurga mata sai kuma ya bushe da wata irin dariya har yana ƙyaƙyatawa. Sai da ya yi me isarsa sannan ya kalli Fulani Maryama da ta haɗe fuska kamar zata yi kuka, yanayinta ba ƙaramin ɗariya ya bashi ba nan take ya kuma bushewa da dariya ya ce. "Lallai Maryama yanzu na ƙara tabbatar da baki da hankali, yarinya da nace miki ta hallaka aljanu ita ce zaki iya karawa da ita? Shin idan hankalinki ya tashi tunaninki gushewa yake yi ne? Bazan ce miki komai ba ga fili ga me doki dan haka jiki magayi, wai bahaushe yace kowar tuba dan wuya ba daɗi. Idan kina ganin zaki iya da ita sai kin gwada, amma ki sani wannan abinda zakiyi kamar tarar aradu da ka ne. Shawara ɗaya zan baki ita ce, bayan kin gano ta kiyi yadda zakiyi Sarki Aminullah ya koreta daga cikin masarauta ta hanyar ƙulla mata sharri ko wani abun, wannan ita ce damar da zakiyi nasara akanta. A ɓangaren yaron kuma maganar gaskiya sai dai kiyi haƙuri dan babu wani abu zan iya aiwatarwa akanshi saboda ina gudun fushinta ya sauka akaina, ina me tabbatar miki wanann kogon da nake ciki tana iya rushe mu dasu gabaɗaya da ni da komai mu hallaka." Fulani Maryama gabaɗa zuciyarta ta gama dagulewa rasa abin yi tayi nan take ta rushe da wani irin matsanancin kuka. Sai fa tayi me isarta sannan ta fyace majina ta ce. "Mardusk me yasa al'amura suke ƙoƙarin juya mun baya ne, naji shawararka kuma zanyi amfani da ita kuma ina san ka ƙara mun ƙarfin iko agurin Takawa, ta yadda duk abinda na bashi umarni zai zartar ba tare da ya musa mini ba." Boka Marduska ɗan jim yayi sannan yace. "Wannan kam za'a iya aiwatarwa sai dai me zaki fansar mun saboda banasan na ƙara tura aljanu na nayi asararsu."Fulani Maryama ta ce. "Faɗi duk abinda kake so ya kai wannan babban boka mai cikakken iko" Boka Marduska yace. "Ga wani farin ƙyalle cen a cikin tsohon kabarin ce ki ɗauko shi ki dangwalar min jinin da kike yi na ɓarin cikin da kika yi." Fulani Maryama kanta tsaye ta wuce wajen da Boka Marduska ya nuna mata ta aiwatar da ya umarceta sannan ta dawo gurinsa, tana dawowa Boka Marduska yace. "Tashi karki zaune mini wuce ki tafi wannan buƙatar dai ta biya sai dai wata kuma." Yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Fulani Maryama miƙewa tayi ta fice daga cikin kogon dutsen. Lokacin da Fulani Zaliha ta ƙarasa gurin Saif da yake ta kwara amai riƙe shi tayi cikin tashin hankali tana kururuwar neman ceto, da sauri wasu bayi suka ƙaraso gurin suka taimaka mata suka rirriƙe shi da alama baya cikin hayyacinsa, jikinsa banda karkarwa babu abinda yake yi ga wani irin zafi da jikinsa ya ɗauka. Hatta da gumin da ke tsattsafowa ta jikinsa da wani irin zafi yake fitowa, Bayin da suka riƙe shi gazawa suka fara ƙoƙarin yi saboda zafin da yake azabtar da hannunwansu. Fulani Zaliha da gudu da nufi fadar Sarki Aminullah ta sanar dashi halin da Saif yake ciki, Salman na gefensa yana jin haka ya fara cika yana batsewa haɗe da wurga mata wani mugun kallo, cikin kallan tsana yace. "Wai kina nufin kwantaccen ne ya tashi?" Sarki Aminullah ya kalleshi yace. "Nima abin da nake mamaki kenan Saif yaron da ko rarrafe bayayi sai jan ciki wannan lamarin da mamaki" Fulani Maryama ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba ta ce. "Kai hawainiyarka ta kiyayi ramata a hir ɗinka banasan rashin kunya wallahi duk ranar da bakinka ya ƙara kuskuren laƙabawa ɗana mummunan suna irin wannan ranka zai yi mugun ɓaci" Salman dariya ya bushe da ita sannan yace. "Ƙarya nayi ba kwantaccen bane ko kina bakin ciki ne baya taka ƙasa har yanzu?" Fulani Zaliha a hassale ta kife Salam da mari ta ce. "Da alama tarbiyya tayi ƙaranci a gurinka..." a zafafe Sarki Aminullah ya katse ta. "Ke Zaliha baki da hankali ne? A gaba na kike niyyar nasaka ɗana saboda naki ɗan nakasasshe ne? Daga yau karki ƙara idan ba haka ba zan ɗauki mata ki akanki kuma matakin bazai miki daɗi ba." Idanun Fulani Maryama ne suka ciko da ƙwala ta ce. "Ranka ya daɗe ni kake cewa mahaukaciya akan wannan yaron shikenan ni ka wulaƙanta akanshi ko? Wallahi na gaji yau tsawon shekaru amma da ashirin ana abu ɗaya nida ɗana bamu da ƴanci sai wulaƙanci da cin zarafi, kullin ka tashi baka taɓa alaƙanta Saif da Ɗanka sai dai kace Ɗanki to babu komai tunda baka ƙaunarmu zamu fita daga rayuwarka, gani kake idan bama tare da kai bazamu iya rayuwa ba ko? Babu komai idan adalci kake mana zaka gani idanma ba adalci kake yi ba zaka ga..." bata ƙarasa maganar ba Sarki Aminullah ya zabga mata wani gigitaccen mari harsai da ta durƙushe a gurin, wani irin matsanancin kuka ta rushe da shi jiki ba ƙwari ta tashi ta fice daga gurin. Lokacin da ta koma Saif na kwance a gurin yana ta malala wani irin amai, sauran Bayin duk sunyi carko-carko a gurin Fulani Zaliha banda hawaye babu abinda take yi. Da sauri ta kira wasu Dogarai ta sa suka ɗauki Saif suka wuce da shi cen sashenta, wucewarsa da shi yayi dai-dai da dawowar Maryo saboda yadda taga yana aman ba ƙaramin tausayi ya bata ba, hanyar sashen Fulani Zaliha zata bi dan ganin halin da yake ciki, da sauri Abu da janyo ta tace. "Ke Maryo me kike shirin yi haka? Dan kinga yau da safe mun shiga sashen Fulani Zaliha shine yanzu zaki koma?" Bakisan yanzu da bambamci tsakanin ɗazu da yanzu ba? Ke fa yanzu Baiwar Fulani Maryama ce kinsan idan labari ya ishe mata ranki zai yi mummunan ɓaci? Wai ma wace ce ke a gidan nan da zaki dinga tura kanki cikin Mutane masu daraja, karki manta mu fa Bayi ne ƙasƙantattu marasa galihu ɗazu ina ce saƙo muka kai gurin Fulanin" Maryo da idanunta suka ciko da ƙwalla ta ce. "Abu ni kaina bansan me yake damuna ba sai nayi kamar na koma sashen mu sai kuma gangar jikina ta hanani aiwatar da haka, sai in dinga jina kamar yana da haki akaina idan ban taimakeshi ba kamar ban kyauta ba. Wani tsagi na zuciya ta na yawan raya shakku akan ni kuwa ANYA BAIWA CE? Sai in dinga wani irin tunani daban" Abu ta ce. "Wane irin taimako zaki yi masa baki ji labarin da aka bamu ba akace masu magunguna da yawa sun mutu akanshi, ki rufa mana asiri Maryo mu zauna lafiya a gidannan banda ma yaudarar kai har kin dinga tunanin ke ba baiwa bace idan ke ba baiwa bace mece ce?" Maryo ta ce. "Tambayar da har gobe bani da amsar ta hasalima bansan da me zan taimaka masa ba amma wallahi Abu tun ɗazu da nayi arba da wannan ɗan Sarkin naji zuciyata ta harba akansa lokaci ɗaya naji na kamu da ƙaunarsa." Abu ƙwalalo idanu tayi da sauri ta fisgi hannun Maryo ta ce. "Maza zo mu wuce tun ba'a yanke mana mummuna hukunci ba." Maryo ba dan ta so ba ta bi Abu suka wuce cen saahen su na Bayi kai tsaye suka wuce madafa domin sarrafa abincin da zasu ci. Bayan magari ba suna zaune a tsakar gida saboda zafi suna shan iska, daga cen nesa ta fara ganin giftawar mutane kamar wacce a ka tsikara haka ta tashi, suna ganin tasowarta suka juya suka fice daga gurin ita kuma ta rufa musu baya. Basu tsaya a ko'ina ba sai tsakankanin manyan bishiyoyin kukar nan guda biyu. Tana zuwa gurun ta hangi mace mai kama da ita sak tana rungume da wani namiji jikinsa duk jini da alama baya numfashi, matsawa ta fara yi a hankali tana ƙare mata kallo sai dai da alama kuka take rerawa cikin wata irin murya. Maryo matsawa tayi zata taɓa ta sai ji tayi ance. "Kije ki ceci rayuwarsa yana cikin wani hali wannan ne kawai taimakon da zaki iya yi masa." _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [23/10/2021, 19:44] Ameera Adam🌚: 12... Ɗaga kanta tayi tana waigen me maganar amma babu shi babu alamarsa dawo da kallonta tayi wajen me kama da ita, tsugunnawa tayi tana ƙare musu kallo, a hankali ta sa hannu zata taɓa ta saboda yadda taga tana gursheƙen kuka, ba ƙaramin tausayi ta bata ba. Tana kai hannu taji ta ce."Dan Allah ki ceci rayuwarsa iya abinda zan iya sanar da ke kenan bana fatan sake rasa shi" tana nan durƙushe ta hango wani ya tunkaro gurinta kafin ta ankara taji ya fara fisgarta da ƙarfin tsiya, Maryo so take ta ƙwace amma ta gagara saboda mutumin ya fita ƙarfi nesa ba kusa ba, yana cikin janta ta fara kururuwar neman taimako tana ihu haɗe da roƙo kamar wacce ta tuna abu haka ta fara karanto addu'in da duk suka zo bakinta, nan take taji ya saketa kuma ya ɓacewa ganinta. Waigawa tayi ta hango har zuwa lokacin wannan mace da namijin suna zaune da hawaye ɗauke a fuskarta, daga cen nesa taji ana ƙwala mata kira ba ƙaƙƙautawa jiki a sanyaye ta juya da niyyar ta ƙarasa gurin da take hango wannan mace da namijin da sauri taji Inna Habi ta ja hannunta tana cewa. "Ke Maryo kanki ɗaya kuwa me yake damunki zaki taho dokar daji a daren nan lafiyarki kuwa?" Maryo idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce. "Inna wallahi sai roƙona suke akan na taimaka musu ni bansan taimakon da zanyi musu ba, amma wallahi da alama suna buƙatar taimako na Inna" Inna Habi zaro idanu tayi tana kallan gurin da Maryo take kallo tana mata magana, amma ita bata ga komai ba. Inna Habi hannun Maryo ta ja ta ce. "Maryo anya kuwa makarai basu fara buɗe miki ido ba? yanzu cikin dokar dajin nan kizo kice wai wasu na yi miki magana, maza wuce mu tafi karki jaza mana masifa" Maryo juyawa tayi ta ga waccen me kama da ita tana hawaye ta miƙe tsaye ta riƙo namijin yana ɗingishi suka ɓace daga gurin. Maryo hannu ta fusge ta ce. "Shikenan Inno wallahi sun tafi kuma yana cikin wani hali nidai Inna gaskiya..." Da saurin Inna Habi ta fisgi hannunta suka fara tafiya har sai da suka baro gurin, suna shiga sashensu Abu ta ce. "Maryo ina kika je tun ɗazu Fulani Maryama ta aiko kiranki?" ɗigon jinin hancinta da ya fito ta goge kanta na ci gaba da sarawa, idanunta take suka rune jawur hannuwa biyu ta sa ta dafe kanta ta ce. "Abu kije a madadina wallahi bana jin daɗin jikina" Abu zaro ido tayi ta ce. "Fulani Maryama fa ita take kiranki gaskiya bazan iya zuwa ba, ki lallaɓa ko a hankali ne kije kuma kisan ƙaryar da zakiyi mata dan ta aiko kiranki yafi a irga." Inna Habi ta ce. "Gaskiya Maryo akwai abinda yake damunki anya bazamu fara nema miki maganin makarai ba, wannan jikin naki ba lau ba yanzu ki wuce kije kiran da Fulani Maryama take miki banasan abinda zaki yi wanda za'a hukunta ki da horo me tsanani." Maryo tafiya ta fara yi tana haɗa hanya hannunta ɗaya dafe har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama. Tana gabda shiga rumfar Fulani Maryama ta yanke jiki ta faɗi wanda yayi dai-dai da shigowar Jakadiya. Jakadiya na ganin haka ta rafka salati tana tafa hannuwa ta ce. "Yau me nake gani ni Kubura ke ƴar nan ya na ganki a sheme kamar gawar goɗiya jama'a ku kawo ɗauki" Fulani Maryama ce ta leƙo ta ce. "Jakadiya ihun me kike yi?" Jakadiya ta zaro ido ta ce. "Wannan mai kama da ƴar bararojin ce na samu ta faɗi a gurin" a yatsine Fulani Maryama ta kalleta ta ce. "Jakadiya maza ki fitar mun da ita idan kin kaita cen sashen su ki dawo ina san ganinki" Jakadiya ta kalli Maryo da take wani irin karkarwa ta ce. "To Allah gamu gareka Bawan sarki ya rasa doki, yanzu ki rasa inda zaki yi farfaɗiyar ta ki a babban sashe na Fulani Maryama, kekam ki haɗani da jaraba ɗaukar kamar ki ai sai na shirya. Ga dai yarinya a haka da ƙuruciya kamar na nauyi amma wallahi wannan sai ta kusa ɓalle mun baya, gwara na kira waɗancen ƴan iskan dogarawan su zo su tayani kwasar..." Fulani Maryama gajiya tayi da surutan Jakadiya ta ce. "Jakadiya bansan surutu a kwashe mini ita daga gurin nan?" Jakadiya juyawa tayi fara ƙwalawa Dogaran bakin ƙofa tana magana. "Kai Badaru kana ina kuzo" kafin su ƙaraso Maryo ta ɗan jin saukin yanayin da take ciki miƙewa tayi jiki ba ƙwari jiri na ɗaukanta, Jakadiya juyowa tayi ta taɓe baki ta ce. "Feleƙe ratayar jaka a duwawu dama farfaɗiyar ba ta gaske bace, to muje karki jazawa uwar ɗakina masifa ki mushe mata mu shiga uku." Jakadiya tasa Maryo tayi a gaba tana tafe tana zazzaga mata surutai suna gabda wuce tsoron tsakiya Maryo ta fara haɗa hanya, ji tayi ta yi karo da abu wanda yayi dai-dai da tafiyarta luuuuuuu. Kafin ta kai ƙasa ya taro ta dukda idanunsa a rufe suke jin alamun mutum yasa yayi saurin taro ta. Jakadiya ta kuma rafka salati tana cewa. "Shikenan wannan yarinyar zata ja mun taɓa gawa ina zaman zamana" Fulani Zaliha hannunta da yake sarƙe dana Saif ta ce. "Subhanallah Jakadiya lafiya?" Jakadiya ta ce. "Allah ya taimake ki wallahi yarinyar nan ce tana zuwa zata shiga sashen Fulani Maryama kawai ta zube ƙasa" Jakadiya ta ɗaga kai cen ta fara hange-hange sannan tayi ƙasa da murya ta ce. "Kinsan dai ba kowa yake da wadataccen Imani ba banda haka ya yarinya tana cikin wannan halin ace wai a fita da ita kamar wata kayan wanki" Fulani Zaliha ta ce. "Jakadiya ba wannan na tambayeki ba yanzu ina zaki kaita" Jakadiya ta taɓe baki saboda duk yadda zata kawowa Fualani Zaliha gulma ba ta bata goyon baya sannan ta ce. "A'a to Allah ya baki yawan rai ina kuwa zan kaita cen sashensu zan kaita" Kafin Fulani Zaliha tayi magana Saif ta taɓa mahaifiya ya fara mata nuni da hannu, Jakadiya sakin baki tayi tana kallansa sai kuma ta karya murya ta ce. "To banda abin ka Ƙanin Yarima ni yaushe na koyi maganar kurame wannan kam sai ranki shi daɗe...? Kallon da Fulani Zaliha ta wurgawa Jakadiya ne yasa ta ja bakinta tayi shiru. Fulani Zaliha ta ce. "To banda abin ka Saif idan kuma yarinyar bata amince ba, ko kuma ita Yaya idan bata lamunce ba fa naji ance yanzu Baiwarta ce, nifa banasan abin da za'a zo ana ƙananan maganganu" Jakadiya tayi karaf ta ce. "Sadaƙallahul azim Ranki shi daɗe haka za'ayi kawai tunda kowa ya sanki da tausayin talakawa." Fulani Zaliha ta kama hannun Saif ta ce. "Jakadiya ku taimaka masa mu wuce da ita." Fualani Zaliha dasu Jakadiya suka wuce ɓangarenta suna riƙe da Maryo da har lokacin bata cikin hayyacinta, suna zuwa aka shimfiɗar da ita akan tabarama Jakadiya na ganin haka ta zame jiki ta wuce ɓangaren Fulani Maryama. Jakadiya na zuwa sashen Fulani Maryama ta zayyane mata duk abinda yake faruwa Fulani Maryama taɓe baki tayi ta ce. "Cen sa ji da munafurcinsu daga yanzu ma na sallame ta dan naga alamar bazamu daidaita da ita ba." Fulani Maryama zayyawa Jakadiya duk abinda ya Boka ya gaya mata tayi ta ɗora da cewa. "Jakadiya me ya kamata mu gudanar wa kike zargi a cikin waɗannan bayin anyi sababbin bayi ne ko iya baƙin sarki ne kawai?" Jakadiya tayi jim sannan ta ce. "Allah ya taimake ki ai sallamar yarinyar nan bai kamaki ba kuma ni dama cen akwai wacce nak zargi dan dai kawai kar nayi miki katsalandan ne amma ai dama biri yayi kama da mutum, ya za'ayi ki ɗauki wuƙa ki taɓawa cikinko ranki shi daɗe." KU MUN AFUWA DA GAJEREN TYPING 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 PROMISE GOBE INSHA ALLAH 2 PAGES ZAKU SAMU. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI [26/10/2021, 15:45] Ameera Adam🌚: 13... Fulani Maryama a firgice ta ɗago da kanta tana kallan Jakadiya, da sauri ta sauko daga kan kujerar da take kai ta alfarma ta dafa cinyar Jakadiya ta ce. "Jakadiya me kike nufi kina nufin kinsanta amma kika bari nake zaune cikin dubu?" Jakadiya ganin yadda Fulani Maryama tayi a zuciyarta ta ce. "Yo dama ai komai nisan jifa ƙasa zai faɗo kuma duk nisan dare gari zai waye, Allah na tuba dama tunda naji labarin ɗan wajen Zaliha ya take ƙafarsa ai nasan tuni ginshiƙin dutse ta faso gi..." Jakadiya bata gama zancen zucin ba Fulani Maryama ta kwantar da murya ta ce. "Jakadiya ki mini rai ke nake sauraro" Jakadiya ƴar dariya tayi ta ce. "Fulani Maryama kenan Yaushe rabon duniya, da ayya-raye? Wai ni kike kwantarwa da murya haka lallai Duniya juyi-juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi." Fulani Maryama fusata ta farayi ta ce. "Jakadiya saboda na zauna ƙugu da ƙugu da ke ba yana nufin ki ci duniyarki da tsinke a kaina ba. Me ake ciki? Wacece yarinyar a cikin gidan nan?" Jakadiya ta ce. "Maganar gaskiya Fulani ina zargin yarinyar can da ta bar wannan sashen naki saboda alamu duk sun bayyana daga yanayinta" Fulani Maryama ta ce. "Da gaske kike faɗa?" Jakadiya ganin ta zurma Fulani Maryama ta shige yasa ta ɗaga kanta da sauri ta ce. "Ko ke baki dubi yanayinta ba? Haba ai duk me hankali ya dubi yarinyar nan yasan ba ita kaɗai bace. Kina ganin yarinya da ido a tsaitsaye kamar kamar Inuwar soja ai ko ba'a faɗa ba biri yayi kama da mutum" Fulani Maryama ta jinjina kai jiki a sanyaye tana nazari sannan ta ce. "Wacce hujja kike da ita da zai tabbatar mana da ita ɗince Jakadiya?" Jakadiya tayi yaƙe a fili saboda Allah ya sani ita kanta ta faɗa ne kawai bata da wata hujja hasalima ta faɗa ne dan ta ƙara ɗagawa Fulani Maryama hankali ta ce. "Eh man baki ga yarinyar sam bata da tsoro ba, ɗazu a gabanki fa makaran jikinta suka make ta gaskiya nidai ina da shakku akanta." Fulani Maryama ta ja guntun tsaki ta ce. "Wannan bai isa ya ban tabbacin ita bace ni nafi zargin a cikin sabbabin bayin da akayi ne makon da ya gabata, saboda sai bayan zuwansu haka ta faru da wancen tsinannan yaron." Jakadiya jim tayi tana nazari sannan ta ce. "Ehto mutum baya ƙin ta mutane yanzu ki barmun komai a hannuna zan yi ta shige da fice har na samo miki gaskiyar labari inyaso sai a tashi tsaye a san abinyi" Fulani Maryama har lokacin bata cikin nutsuwarta ta miƙe ta koma mazauninta na farko sannan ta gyaɗawa Jakadiya kai." Sallama Jakadiya tayi mata sannan ta tashi ta fice zuciyarta fes dan ko banza ta san Kwanciyar hankali yayi ƙaura agurun Fulani Maryama. Fulani Zaliha zaune take a gefen Maryo da har lokacin batasan waye a kanta ba, addu'a take ta tofawa Maryo har ta fara jin saukin jikinta. Miƙewa tayi zaune jiki ba ƙwari gabaɗaya ta haɗa uban gumi, a hankali take ƙarewa gurin kallo har ta sauke idanuwanta akan Fulani Zaliha da itama kallon nata take yi. Maryo sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce. "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Fulani Zaliha ta dafa kaɗarta bata amsa ba ta wurgo mata tambaya. "Ya kike jin jikin naki?" Maryo ta ce. "Da sauƙi" Fulani Zaliha ta ce. "Ki dinga yawaita addu'a kinji kuma karki dinga zama babu ɗankwali." Maryo ta gyaɗa kai sannan ta ce. "Insha Allah zan kiyaye ya shugabata" Miƙewa tsaye Maryo tayi Fulani Zaliha ta ce. "Ina zaki haka?" Maryo ta russuna ta ce. "Allah ya taimakeki Fulani Maryama ce ta aiko kira na" Fulani Zaliha ta ce. "Ki tsaya kiyi sallar magriba inyaso kya je kiran da take miki" Maryo bata musa ba ta miƙe ta ɗaura alwala tana mamakin mutumci da karamcin wannan matar saki, tana cikin wannan tunanin ta ga Fulani Zaliha ta miƙa mata wani abu kamar mayafi amma ba mayafi bane kuma yana da kauri sosai kamar bargo ta ce. "Ga wannan kiyi sallah da shi" Ta karɓa tana godiya cikin girmamawa sannan ta ta tayar da sallah. Bayan ta idar da sallah ta naɗe abin da tayi sallar da shi ta miƙawa Fulani Zaliha tana zabga godiya, Murmushi Fulani Zaliha tayi bata karɓa ba ta ce. "Ki tafi da shi ki dinga sallah" Maryo tsugunnawa tayi tana godiya da sauri Fulani Zaliha ta ɗagota ta ce. "Godiyar ta isa haka. Amma zan roƙe ki wata alfarma" a firgice Maryo ta zaro idanuwanta tana shirin magana Fulani Zaliha ta ci gaba da cewa. "Ba wata alfarma bace so nake duk lokacin da kika yi sallah kiyi wa ɗana addu'a kice Allah ya bashi lafiya ya dawo kamar yadda kowa yake" Idanun Fulani Zaliha ne suka kawo ƙwallah Maryo ta lura da haka nan take taji tausayinta ya kama ta, saboda babu wanda baisan labarin Saif ba a cikin gidan. Ko kai baƙo ne bazaka rufa kwana biyu a gidan ba sai an kwashe labarinsa a baka, dan haka ne ya faru da su a washegarin ranar da suka zo Jakadiya ta kwashe labarin Saif ta basu. Maryo ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Insha Allah nayi miki alƙwari kuma zai samu lafiya da yardar Allah. Amma Ranki shi daɗe ba naji ana ta ce wa ya warke ba" Fulani Zaliha tayi murmushi ta ce. "Alhamdullah a ranar da kika kawo mun saƙon gurin Delu Dillaliya bayan fitarku babu jimawa Allah ya bashi lafiya ƙafarsa ta samu lafiya garau yana takawa, saura idanunsa da bakinsa kawai ya rage kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi mini ba" Motsi suka ji daga bakin ƙofa suna kallan gurin suka ga Saif ne ya shigo da alama daga masallaci yake. Nan take wani abu ya tsargawa Maryo gabanta sai faɗuwa yake, kafe shi tayi da kallo yadda yake tafiya kai ka rantse yana gani da idanunsa, tunda ga idanunsa nan a buɗe tar sai dai ganin da baya yi. Wani irin so da ƙaunarsa ne suke fusgarta har ta shagala da kallansa ta manta a gaban wacce take. Muryar Fulani Zaliha ne ya katse ta ce mata. "Yauwa ni ya sunanki ne?" Maryo ta ƙara sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ta ce. "Sunana Maryo" Fulani Zaliha ta ce. "Masha Allah suna me daɗi to shikenan je ki kinji Allah ya ƙara miki lafiya" Maryo ta russuna tana godiya sai a lokacin Saif ya fahimci da wacce Mahaifiyarsa take magana. Alamu ya fara mata da hannu yana tambayarta yarinya da suka shigo da ita ce ta ji sauƙi har take magana?" Nan take mahaifiyarsa ta yi masa bayani yadda sukayi da Maryo. Duk wannan jawabin da Fulani Zaliha take wa Saifa Maryo ta tattara hankalinta gabaɗaya ta ɗora akan sa, har sai da Fulani Zaliha ta lura da irin kallon da Maryo take wa Saif, gyaran murya tayi a hankali sannan Maryo ta dawo cikin nutsuwarta ta gaida Saif cikin wata irin murya da batasan ma tana da ita ba sannan ta yi wa Fulani Zaliha sallama ta fice. Maryo kai tsaye bata wuce ko ina ba sai sashen Fulani Maryama lokacin da ta shiga duhun magriba yayi sosai, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga sashen. Fuska babu walwala Fulani Maryama ta kalle ta ba tare da ta amsa sallamar ba, Maryo na shirin magana ta dakatar da ita. "Ta shi ki fice mini daga sashena bana buƙatar ƙara ganin ki indai bani na aika kiranki ba" Jiki a sanyaye Maryo ta tashi har zata fita Fulani Maryama cikin tsawa ta ce. "A ina kika samu wannan abun na hannunki"rissiawa tayi ta ce. "Fulani Zaliha ce ta bani Allah ya taimake ki" A zabure Fulani Maryama ta ce. "Me ya kaiki sashenta kina matsayin baiwata?" Maryo ba ƙaramin tsorata tayi da yanayin da ta ga shugabarta ta shiga ba, jikinta har rawa yake bakinta na karkarwa ta ce. "Wallahi nima farkawa kawai nayi na ganni a gurinta shine da nayi sallah ta ce na tafi da shi" a hargitsi Fulani Maryama ta ce. "Kin haɗu da Saif?" Maryo ta ce. "Eh da zan fito ya shiga" Wani kukan kura Fulani Maryama tayi ta danƙo wuyan Maryon ta maƙure mata wuya ta ce. "Ƙanwar uwarki ce ko ta ubanki da zaki dinga shiga sashen nata?" Maryo sosai ta tsorata ga shaƙewar da Fulani Maryama tayi mata har idanunta sai da suka firfito nan ta ke ta fara tarin wahala, kanta ne ya sara idanunta suka fara canja launi jini ne ya fara ɗiga daga hancinta. Saboda masifar da ta rufe idanun Fulani Maryama bata lura da halin da Maryo take ciki ba sai bambamin faɗa take tana ranƙwashinta haɗe da dungure mata kai, kamar wacce aka haɗawa lantarkin wuta ta fara zuƙar jinin jikinta haka taji wani irin shocking a jikinta, cikin tsananin azabtuwa tayi wurgi da Maryo tana ja da baya haɗe da mayar da numfashi da ƙyar. Kafin Maryo takai ga faɗuwa ƙasa Salma da ya shigo ɗakin ya taro ta ta faɗa jikinsa, wani irin yar yaji tun daga tafin ƙafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Maryo lumshe ido take tana buɗewa saboda yanayin da take ciki, cikin zuciyarta ta fara karanta wasu ayoyin cikin kur'ani da ta sani. Ba ta jima a haka ba ta fara jin jikinta ya fara koma mata dai-dai, a hankali ta fara ƙoƙarin zame jikinta amma fir Salman yaƙi sakinta sai bin ta yake da wani irin mayataccen kallo mai wuyar fasaltuwa, muryar mahaifiyarsa ya riska tana cewa. "Salman wannan yarinyar ce wallahi babu ko tantama banayi ita ce" Salman da har lokacin riƙe yake da Maryo yace. "Wace ce itan me tayi miki?" Sai a lokacin Fulani Maryama ta fahimci ta so tayi suɓutar baki ta wayance da cewa. "Sheɗaniyar yarinya ce so ake a haɗa baki da ita a cutar damu alhalin tana matsayin baiwa ta." Salman bai bi ta kan maganar Mahaifiyarsa ba yasa hannunsa ya goge mata jinin da ke hancinta, fuskarta ya ƙarewa kallo yana jin wani abu na fusgarsa akanta, kayan jikinta na Bayi ya ƙarewa kallo a hankali ya furta. "Sam baki cancanci zama haka ba" ya faɗa cikin wata irin kasalalliyar murya. Fulani Maryama da bata fahimci inda zancen Salman ya dosa ba ta ce. "Banda abin ka mugu yana da kama ne har gane mutumin arziƙi ake a haka" Maryo kiciniyar ƙwace kanta ta farayi sai da ya ga dama dan kansa sannan ya sake ta yana binta da wani irin kallo haɗe da lashe baki. Yana sakinta ta fice da gudun gaske jikinta ta ko'ina rawa yake yi." Salman takawa yayi ya tsaya gaban Mahaifiyarsa da har lokacin tsoro ne ƙarara shimfiɗe akan fuskarta, ƙerere ya tsaya yace. "Ke ya akayi kika gane za'a haɗa baki da ita a cutar damu?" Fulani Maryama ta ce. "Wallahi Saif wannan yarinyar ba alheri bace a zamantakewarmu da ita." Guntun tsaki ya ja yace. "Wai ke tambayar da ake miki daban amsar da kike bawa mutane daban wai ma me kika yi mata naga jini a hancinta dan nasan halinki?" Idanu Fulani Maryama ta zaro tana maimata tambayar da Saif ya yi mata a fili sannan ta ce. "Saif yarinyar nan Baiwa ce fa akanta har kake tsareni da tambayoyi" Wani kallo ya watsa mata yana wani irin murmushi da bai san lokacin da ya sake shi ba sakamakon tuno fuskar Maryo da ya yi, ido ya zurawa Mahaifiyarsa yace. "Ke kike ɗaukanta a matsayin Baiwa amma ni matsayin da na bata yafi wannan a gurina saboda ina jin wani abu da bantaɓa jinsa ba akan wata ƴa mace dukda kinsa dai ba yau na fara tarawa da mata ba, nayi mu'amala da mata kala-kala amma babu wacce na tsinci kaina a yanayin..." A zafafe Fulani Maryama ta kife Salman da wani gigitaccen mari cikin masifa ta ce. "Saif ni kake gayawa haka baka da mutumci ashe ban sani ba, ni kake gayawa kana tarawa da mata saboda ka riƙa..." Salman da sauri ya ture hannunta yana wani irin huci da muzurai yace. "Wallahi karki ƙara ɗora hannunki a kan fuskata idan ba haka ba zakiyi mamaki, kuma wannan yarinyar nan son ta nake kuma ba soyayyar da zan watse da ita ba son da zan aureta saboda ina san ta haifa mini ƴaƴa kyawawa masu kama da ita." yana gama faɗa ya fice ko waiwaye bai yi ba, Fulani Maryama zaro ido tayi tana bin bayansa da kallo sannan ta rushe da wani irin mahaukacin kuka. Maryo ilahirin jikinta rawa yake tana tafe ko kallan gabanta ba ta yi saboda tsoron abin da Fulani Maryama tayi mata, tana gabda shan kwanar katangar sashensu taci karo da wani matashin har kusan gware suka yi, da sauri Maryo ta ja da baya tana ƙwallah wata irin gigitaciyyar ƙara. Dariya ya bushe da ita sannan ya janyo hannunta yana cewa. "Ke meyasa kin fiya tsoro ne?" Sai a lokacin ta sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya tana kallan fuskarsa da matsanancin mamaki sakamakon hasken farin watan da ya gauraye filin gurin. Ganin irin kallon da take masa babu ko ƙiftawa yasa hannu a saitin fuskar ta, a hankali ta janye idanunta suna haɗa ido ya sakar mata wani tattausan murmushi, sunkuyar da kai tayi saboda wani kyau da kwarjini da ya ƙara mata sai kuma taji kunyarsa a hankali ta ce. "Dama kana magana ne?" Murmushi ya yi yace. "Gashi kuwa kinji" Bin gefensa tayi zata wuce ta ce. "Na maka murna" Janyota ya ƙara yi har sai da ta faɗa jikinsa yace. "Bani Hannunki" Da sauri ta tashi daga jikinshi ta ce. "Ni ka daina taɓa ni banaso haramun ne" Kafeta yayi da ido yace. "Ni ba haramun bane a gurinki dan Allah ki tuna Rayzuta ni Fauzaaan mijinki ne, kuma karki bari wani ya ƙara taɓaki bayan ni idan ba haka ba zai mutu naga wancen Ɗan Sarkin yana rawar kai akanki" Zaro idanu tayi tace. "Ɗan uwan naka zaka kashe? Dan Allah ka bari karka kashe shi" Murmushi ya yi yace. "Ni ba Ɗan uwana bane, to shikenan bazan kashe shi ba amma sai kin bani hannunki" Har lokacin a tsorace take saboda kalmar kisa da taji ya furta, jiki a sanyaye ta miƙa masa hannu. Wani irin zobe ya zura mata a hannu mai wani irin gwamammun rubutu da babu wanda zai gane me aka rubuta ajiki, ya zura mata a hannu nan take taji kanta ya sara daga cikin kunnenta taji wasu irin maganganu, lumshe ido tayi tana bin kalmomin da bakinta kamar ta taɓa saninsu a baya tana cikin haka daga cen taji muryar Abu da Dije suna ƙwala mata kira, da sauri ta buɗe idonta kallanta yayi yace. "Maza kije ga su Abu cen ƙarasowa." Jiki a sanyaye ta wuce inda take hango su Abu har ta ƙarasa gurinsu bata daina murza ɗan yatsan da zoben yake jiki ba. Dije ce ta fara magana ta ce. "Maryo tun ɗazu nake nemanki" Maryo ta ce. "Wallahi naje kiran shugabata ne" Dije wucewa tayi ta ce. "To nima bari na ƙarasa Fulani Bilkisu na kira na" Abu ce kawai ta iya amsa mata Maryo har lokacin tana cikin wani irin yanayi. Abu fisgar hannun Maryo tayi ta ja ta cen gefe tayi ƙasa da murya ta ce. "Ke Maryo ke da waye kike a tsaye a gurin cen?" Maryo ta ce. "Saif ne Ɗan wajen Fulani Zaliha" Zaro ido Abu tayi tana waige dan kar wani yaji abin a suke faɗa, Abu ta ce. "Ke Maryo kiji tsoron Allah mutumin da yake fama da jinya" Maryo ta ce. "Wallahi da gaske nake kuma har magana munyi da shi kin ga ma zobenyar da ya bani, wallahi kamar yasan yadda nake ƙaunarsa." Abu ta ƙara ƙwalalo ido waje tana duba zoben da yake ta walwali a hannun Maryo. _LITTAFIN ANYA BAIWA CE NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [26/10/2021, 19:44] Ameera Adam🌚: 14... Maryo Fisge hannunta tayi ta ce. "Ke Abu wannan kallon har ina" Abu ta riƙe haɓa ta ce. "Maryo har yanzu ina mamakin abin da kika faɗa mini ne. Yanzu Ɗan Sarkin gidan nan guda shi ne zai faɗa soyayya da ke, anya Maryo ba yaudararki zai yi ba?" Maryo ta ce. "Wallahi nidai ina ƙaunarsa Abu kuma shima haka sannan kinsan me yace mini? Cewa yayi fa..." Maryo ta tsuke bakinta ta ci gaba da cewa. "Ke mu bar zancen dai" Abu cikin yanayin tsoro ta ce. "Maryo! Maryo anya kuwa? Ni fa ina guje miki wani abu ance fa akwai wani Ɗan sarki yadda kikasan bunsuru haka yake, kibi sannu fa wallahi kar dukiya ta ruɗeki ya kaiki ya baro mu shiga uku, saboda banza bata kai zomo kasuwa ta yaya yana Ɗan sarki zai ce ke yake so duk sauran Bayin gidan nan babu wacce ta kwanta masa sai ke da ko wata biyar bakiyi da zuwa ba" Maryo ta ce. "Ke wallahi sam ban fahimci haka daga gareshi ba, nifa wallahi ji nake ma kamar tsohon tsimin soyayya ya tado mini" Abu ta ƙara ware idanu tana kallan Maryo da take ta zubo kalamai. Cikin mamaki ta ce. "Wai nikam Maryo yaushe idanunki suka buɗe haka bansani ba, nifa tun da muka shigo gidan nan naga duk kin wani sauya kamar bake ba" Maryo kafaɗar Abu ta dafa ta ce. "Ashe kin lura Abu wallahi ni kaina ji na nake wata iri musamman idan na tuna baiwa ce ni sai na dinga tunanin Anya baiwa ce? Ina jin girma da matsayi na ya wuce na kasance a matsayin Baiwa amma gabaɗaya na rasa amsar haka." Abu ta ce. "Maganar gaskiya Maryo muddin Inna ta san abin da yake faruwa hankalinta ba ƙaramin tashi zai yi ba, ni kaina yanzu haka a tsorace nake ina gudun abin da zai je yazo" Maryo ta ce. " Babu abin da zai faru sai alheri." Abu ta ce. "Allah yasa zan fi kowa murna" Maryo ta ce. "Wai ma kinsan wani abun farin ciki Abu" Abu ta girgiza kai" Maryo ta ce. "Wallah Saif ya warke garau ke baki ji muryarsa ba raƙwai kamar me, kai amma gaskiya anyi kyakkyawa ajin farko" Abu ta ce. "Ke dama fa a wata majiya me tushe naji ana raɗe-raɗin wai asiri fa aka yi masa, wasu kuma suka ce mayu ne suka lashe shi tun a ciki wasu kuma suka ce aljanu ne ke zance dai da yawa amma fa anfi ƙarfafa asirin ne akayi masa." Maryo ta ce. "Aikuwa aniyarsu ta bisu." daga haka suka ci gaba da tafiya har sun kusa ƙarasawa sashen Bayi Maryo ta ce. "Yauwa Abu dan Allah ko Inna zata ga zoben nan zan ce tsintarsa nayi saura ki tona ni dan nasan halinki." Abu ta ce. "Kika ci gaba da yi mini rashin kunya a matsayina na yayarki wallahi babu abin da zai hanani tonawa." Maryo ta marairaice murya ta ce. "Wallahi na daina Yaya Abu" Abu tayi dariya ta ce. "Dole gyaɗa tayi mai in taƙi ta sha matsa" lokaci ɗaya suka kwashe da dariya. Maryo da Abu ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba Abu ita ce Babba amma idan ka gansu zaka ɗauka Maryo ce babba, saboda Maryo tafi Abu tsayi sosai suna san junansu sai dai idan faɗansu na sakuwa da sakuwa ya motsa zaka ɗauka basu taɓa zaman mutumci ba, sai dai dukda haka basa taɓa bari wani ya ci mutumcin ɗaya daga cikinsu. Suna ƙarasawa gurin Inna Habi suka zauna Maryo ta bawa Inna Habi labarin kyautar da Fulani Zaliha tayi mata, sai da Inna Habi ta gama sauraronta sannan ta ce. "Maryo nikam ina jiye miki tsoro" Inna Habi sai da ta ɗaga kai ta lelleƙa ta ga kowa sabgarsa yake yi ta ci gaba da cewa. "Kinsan uwar gijiyarki alamu sun nuna ba mace ce me kirki ba, dan Allah kiyi taka tsantsan banasan kiyi abin da za'a azabtar mini da ke. Karki din ga shiga sashen Fulani Zaliha idan ba haka ba za'a kaɗa miki gangar munafurci, kuma bazaki ji daɗin zama da ita ba." Maryo sai a lokacin ta tuno da abin da Fulani Maryama tayi mata amma bata sanarwa da Inna Habi ba saboda karta ɗaga mata hankali sai kawai ta ce. "Inna ai tama sallame ni ta ce kar na ƙara zuwa sai ta neme ni" Inna Habi ta zaro ido waje kamar maye ya ga jariri ta ce. "Maryo ince ba wani abin kika yi mata ba ko?" Maryo dariya take sosai ganin yadda Inna Habi ta firgice lokaci ɗaya sai da tayi me isarta sannan ta ce. "Inna wai dan Allah me yasa zuwan mu gidan nan kika zama matsoraciya" Inna Habi tayi murmushi ta ce. "Yaro man kaza. Ai dole na zama matsoraciya nan fa gidan sarauta ne kuma a ƙarƙashin wasu muke bamu da kowa sai su, al'adar gidan sarauta daban da ta sauran gidaje kuma akan kunnenku ake bamu labarin irin azabarwar da ake ganawa mutumin da aikatawa Sarki, Ƴayan sarki ko Matan sarki mummunan abu. To kuwa kun ga ai kowa ya kwana lafiya shi ya so." Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai sannan Inna Habi ta ci gaba da yi musu nasiha akan zanantakewar rayuwar duniya. Daren ranar gabaɗaya Maryo haka tayi shi cikin farin ciki har sai Inna Habi ta lura da walwalarta ta tambayeta amma ta ce babu komai. Washegari da asubar fari Fulani Maryama ta aika kiran Jakadiya, Jakadiya ba ƙaramin haushin tashin da akayi mata taji ba tana tafe a zuciyarta tana mita. "Haka kawai mace da dameni ta addabeni ni kenan da zarya kamar nayiwa sarki ƙarya yasa a kamoni..." haka dai Jakadiya tayi ta mita har ta ƙarasa bayan ta gaida Fulani Maryama, ta ce. " Ranki shi daɗe lafiya kika aiko kira na da asubar fari?" Fulani Maryama da idanunta suka yi luhu-luhu saboda kuka da rashin bacci ta ce. "Jakadiya ko ban faɗa ba kinsan kwanciyar hankali yayi ƙaura akan fuskata da ilahirin jikina, Jakadiya harsashenki ya tabbata wallahi yarinyar nan ita ce dai da Boka ya gaya mini" Jakadiya na jin haka ta dafe ƙirji tana rafka salati Fulni Maryamm bata bi ta kanta ba ta ci gaba da cewa. "Wallahi jiya naga siddabaru a ɗakin nan kwana nayi banyi bacci ba, dubi hannuwa na" ta ƙarasa faɗa tana warawa Jakadiya Hannuwanta da duk suka kumbura sukayi taruwar jini. A tsorace Jakadiya ta ce. "Me nake gani haka ni jikar Sa'a meye haka a hannunki" Fulani Maryama ta ce. "Wallahi shaƙe yarinyar kawai nayi da hannuna shi ne yayi haka" Jakadiya ta ce. "To kuwa mun shiga uku wannan bala'in ai ba ke kaɗai zai shafa ba yanzu meye abin yi." Fulani Maryama ta ce. "Sannan wani babban tashin hankali cikin dare sai gani nayi yaron cen Saif ya ɓullo mini ta ƙarƙashin ƙasa yana yi mini kashedi kala-kala ke har zancen Salman ya yi mini wai yasan Salman ba Ɗan Takawa bane" Jakadiya najin haka ta zaro idanu haɗe da cewa. "Lallai kina cikin tashin hankali tashin alƙiyamarki yazo a gidan." _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [27/10/2021, 19:31] Ameera Adam🌚: 15... Fulani Maryama da duk tayi zuru-zuru ta ce. "Kina nufin ni kaɗai bala'inta sai faɗawa kenan? Ai uban kuturu ya yi kaɗan bare na makaho. Jakadiya kin manta duk inda zan sa ƙafata tare muke zuwa ko kinmanta ke kike rakani wasu guraeren da bansani ba, ke tsohuwar banza kalleni da kyau kin tuna ke kika fara yi mini rakiya gurin boka kinga kuwa duk abinda ya same ni dole ya shefeki" Jakadiya tayi murmushin takaici ta ce. "Maryama ni kike kira da tsohuwar banza? Lallai na yarda ɗan adam butulu ne. Da kike iƙirarin nina fara yi miki rakiya gurin boka kinmanta bala'in da kike ciki a lokacin? Sai yanzu da kwaɓarki tayi ruwa zaki mayar da ni ƴar iska ko. Kar nake kallanki Maryama kuma wallahi da sannu sai na farke miki laya tun da ke ba ƴar arziki bace."Fulani Maryama cikinta ne ya ƙara ɗurar ruwa ganin Jakadiya na shirin yi mata bore, tunowa tayi da batun Boka Ɗan Duna sai kuma ta sheƙe da wata iriyar dariya har tana riƙe ciki. Jakadiya zaro ido waje tayi saboda tafi kowa sanin wacece Fulani Maryama, tana shirin magana Fulani Maryama ta ce. "Kin makaro siyan kazar sayen baki ranar haihuwa, nasan kin fini sanin waye Boka Ɗan Duna tun da kece kika yi mini jagora gurinsa idan kinga dama zaki iya zuwa kice ya bincika miki naki matsayin agurin waccen yarinyar, saboda bazakiji mutuwar sarki a bakina ba dan waƙa a bakin me ita tafi daɗi, dama tuntuni na kwana da sanin duk daren daɗewa akwai ranar da zaki yi mini bore, dan haka idan kinje kinji daga bakinsa ganin damanki ne kizo mu haɗa kai mu yaƙeta ganin damanki ne ki ƙwaci kanki ke kaɗai." Jakadiya ba ƙaramin sanyi gwiwoyinta sukayi ba kallan Fulani Maryama tayi ta ce. "Maryama anya ba yaudara ta kike yi ba? Idan haka ne me yasa tun tuni baki sanar da ni ba?" Fulani Maryama ta tsuke fuska ta ce." Saboda na kwana da sanin wannan ranar zata zo nasan kina nan cike da jin haushina kuma nasan har gobe mutuwar jikarki na tsaye a ranki duk ta dalilina, ba tun yau na lura da irin kallon ƙiyayyar da kike yi mini ba dama kawai kike jira ki ɗau mummunan mataki a kaina, shiyasa na barwa zuciyata har sai ranar da kwaɓarmu zatayi ruwa." Jakadiya ta ce. "Amma tsakanina da ke Allah ya isa Maryama kin cuceni yanzu me Bokan yace miki a kaina?" Fulani Maryama ta ƙara sunkuyo da kanta ta ce. "Yace akwai wani al'amari da zai haɗa ku da ita zata tona miki asiri akan marigayi Mahaifin Sarki Aminullah, sannan zata tona miki asiri akan kisan da aka yiwa Mahaifiyar Sarki Aminullah" Jakadiya a firgice ta miƙe tsaye jikinta na rawa ta ce. "Maryama ya akayi kika san wannan bayan ko aurenki da Aminullah ba'ayi ba lokacin" Wani irin shu'umin murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Har yanzu baki gama sanin wacece ni ba Jakadiya shiyasa nace kibi sannu, kinsan har me ya gaya mini zata tona miki asiri akai? da sauri Jakadiya ta girgiza kai." Fulani Maryama ta ce. "Kawo kunnenki" Jakadiya har tuntuɓe take ta tsugunna saitin fuskar Fulani Maryama. Fulani Maryama raɗa ta yi wa Jakadiya a kunne a firgice Jakadiya ta ɗago tana bin Fulani Maryama da wani irin kallo, sai kuma ta rushe da kuka tana dafa ƙafar Fulani Maryama ta ce."Maryama kiyi mini rai ki bani mafita wallahi muddin abubuwan nan suka fito kashina ya bushe nasan alƙiyamata ta tsaya dan ba makawa kasheni za'ayi, dan Allah ki ceceni" Fulani Maryama ta ce. "Mu ceci juna dai Jakadiya, kyace na ceceki ni idan kura na maganin zawo ta yi wa kanta mana. Ai ya zama wajibi mu haɗa kai mu yaƙi yarinyar nan tun bata fara yaƙarmu ba" Jakadiya ta fara goge hawayenta ta ce. "Ta wace hanya kenen?" Fulani Maryama ta ce. "Na zauna nayi nazari asiri ko tsafi bazai kaimu ba, dole sai mun bi da dabara da makirci haɗe da zagon ƙasa. Dole mu shigo da Ɓoyayyiyar fuska cikin lamarin nan, idan ba haka ba muna ji muna gani wankin hula zai kaimu dare." Da mamaki Jakadiya ta ce."Waye kuma ɓoyayyar Fuska" Fulani Maryama ta ƙara yi mata raɗa a kunne wannan karan Jakadiya ta jima da baki a sake tana bin Fulani Maryama da kallon mamaki. Jiki a sanyaye ta ce. "Maryama kin wuce tunanin me tunani, amma ya akayi ya koma ɓoyayyar Fuska gaskiya lamarin Masarautar nan ya fara bani tsoro" Fulani Maryama ta ce. "Waɗanda kika sani kenan da zaki san sauran sai kin mutu a nan gurin saboda mamaki." Jakadiya da Fulani Maryama haka suka ci gaba da ƴan ƙulle-ƙullensu, sai da suka tattauna hanyoyin da zasu ɓullowa labarin sannan Jakadiya ta yi wa Fulani Maryama sallama ta koma sashen su jiki a sanyaye. TARIHIN MASARAUTAR KANO Masarautar Kano tana daga cikin manyan masarautu a kasar Hausa. Tarihi ya nuna cewar garin Kano ya kafu kimanin shekaru 400 kafin zuwan addinin musulunci. Ma'ana a yanzu garin ya kai shekara kusan 2000 da kafuwa. Masarautar ta taimaka wajen bunkasar garin Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya. Garin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin arewacin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar a tun kafin zuwan Larabawa da Turawa Kasar Hausa. Asalin Kalmar 'Kano' Mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka tashi daga garin Gaya domin neman kasa mai arzikin tama, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita. Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin mafarauci da ake cewa Kano, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na Kano. Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin tama, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta. Wajen ya kasance mai matukar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari. Daga cikin duwatsun da suka taras akwai dutsen Dala, Goron Dutse, Fanisau,Jigirya da Magwan. Akwai kuma koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Jakara, da kogin Kano. Hakan ya sa mutane da dama suka rinka yin kaura zuwa yankin domin zama. KAFUWAR GARIN KANO A lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama'a a karkashin mulkinsa. Jama'ar da suke zaune a kauyuka kamar Dala da Goron Dutse da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna karkashin shugabanci ne na mutanen da suke tare da su. Daga baya ne da garuruwan suka fara bunkasa, sannan dangantaka tsakaninsu ke kara inganta a lokacin ne aka samu shugaba guda daya da ya hada kan mutanen wato Barbushe. Masana tarihi na cewa Barbushe jika ne na kimanin 15 ga shahararren mafaraucin nan wanda aka bai wa birnin sunansa wato “Kano”. Barbushe shahararren mafarauci ne kuma shine mutum na farko da ya hada kauyukan a karkashin ikonsa a lokaci guda a bisa tsarin gudanarwan shugabanci da kuma addini. A lokacin sa ne addinin bautar Tsumburbura ya shahara. Barbushe shine babban bokan Tsumburbura. Bayan zamanin Barbushe da kimanin shekara 200 aka samu wasu mutane daga yankin Daura da suka ci Kano da yaki suka kafa sarauta a karkashin Bagauda a shekarar 999. Sarakunan Kano Da akwai gidaje da dama da suka yi mulkin Kano tun daga 999 zuwa yanzu. Masana tarihi sun ce, tun daga kan Sarki Bagauda dan Bayajidda har kan sarkin Kano na karshe kafin fulani wato Sarki Alwali dukkaninsu daga jini daya suke. Daga baya an ci gaba da samun sauye-sauye da kuma rungumar wasu sabbin abubuwa a tsarin shugabancin masarautar ta Kano. Wannan kenan! Maryo tun da gari ya waye ta kasa zaune ta kasa tsaye gabaɗaya zuciyarta so take tayi tozali da Saif ko taji daɗi, dabara ce ta faɗo mata dan haka ta saci jiki ta fice daga sashen su na bayi duk kuwa da kicimillin aikin da suke sha na shirin bikin al'ada, tana fita bata zame ko ina ba sai sashen matan sarki, tana gabda shiga ta hango shi zaune a wata ƴar inuwa, yana zaune ya jingina da bango idanunsa a rufe, ta jima a tsaye a gurin tana son tayi masa magana amma tana jin tsoro, kamar wanda aka tsikara haka ta ga ya buɗe idonsa karaf ƙwayar idonsu ta haɗu guri ɗaya, sunkuyar da kai tayi ta russuna tana murmushi ta ce. "Barka da hutawa Yaya Saif" ɗago ta idanunsa yayi a hankali ya gyaɗa mata kai. Maryo ta shafi kanta ta ce. "Dama nazo wuce ne nace bari nazo mu gaisa" Wannan karanma gyaɗa mata kai yayi kamar dai zata ƙara maganan sai kuma ta ce. "Na barka lafiya" haɗa hannu biyu yayi alamun godiya sannan Maryo ta wuce. Tana tafe tana waigensa har ta yi nisa da shi. Gabaɗaya sai taji babu daɗi saboda yadda ta ga Salf ya yi mata kamar ma bai santa ba, cen washen gari ta nufa bakin wata bishiyar tsamiya ta zauna isakar gurin me sanyi na ratsata nan da nan bacci yayi awon gaba da ita abinka da waɗanda bacci baya wadatarsu bacci take sosai harda minshari. A cikin baccinta ne tayi mafarki ta hange su kwance a cikin wata ƙorama mai matuƙar kyau da daɗi, yanayin gurin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba tana cikin ruwan suna wanka ita da Saif sai watsawa junansu ruwa suke, suna cikin nishaɗi sosai irin na masoyan da suka jima a fannin soyayya. Bayan sun fito daga wankan wani irin mayafi me walwali yasa ya rufe su sai da suka jima a haka sannan suka sanya waɗansu irin kaya masu tsananin kyau. Tsokanarta ya yi ya tafi da gudu sannan ta bishi suka fara wasan ƴar ɓuƴa idan ta kamoshi wannan karan wani karan shi zai kamo ta. Suna cikin haka bayan ya ɓuya ta fara nemansa ta rasa sai a cen nesa da ita ta hango wani namiji da bata ga fuskarsa ba ya saɓa shi a kafaɗa jini na zuba a jikinsa, wani irin kuka ta rushe da shi ta nufi gurin da gudun gaske kafin ta ƙarasa tuni sun ɓace daga gurin. Firgigit ta buɗe ido saboda yadda kanta ya sara mata nan take jini ya fara ɗiga daga hancinta, a fili ta furta. "Wai waye wannan da a duk lokacin nake cikin nishaɗi yake datse mini shi? Anya zancen Abu bazai zama gaskiya ba kuwa da tace ƙila asiri akayi masa." Miƙewa tayi tana lumshe ido saboda hasken ranar da ya haske idonta. Kamar daga sama aka jefoshi haka ta ganshi jikin bishiyar ɗorawa yana sakar mata lallausan murmushi, duk yadda taso ɗaure bakinta abin ya gagara har sai da ta mayar masa da martani. Takawa ta fara yi a hankali kanta na ci gaba da sara mata a hankali take sa wani ɗan ƙyalle tana goge jinin da yake ɗiga daga hancinta, tana gabda ƙarasawa gurinta ya ware mata hannuwa alamun ta shiga jikinsa da sauri ta tsaya a gurin tana sunkuyar da kai. Tana nan tsaye ta tsinkayi muryarsa yace. "Me ya kawo ki gurin nan ke kaɗai keda kike da tsoron amma kike zuwa gurin nan ke kaɗai" Maryo ta ɗago da ta kalleshi nan take gabanta yayi wata mummunan faɗuwa. Kayan da ta gani sanye a jikinsa cikin mafarkinta shi ta gani a jikinta, kamar ya shiga ranta ya katse tunaninta da cewar. "Kina mamakin kayan jikina ne?" da sauri ta gyaɗa masa kai murmushi yayi yace. "Ki wuce gida Inna na cen tana neman ki" bata musa masa ba ta wuce zuciyarta fal farinciki tana tafe tana waiwayensa har tayi nisa sosai. Shigowarta mararrabar da zata kaita sashen su ta hango Saif tafe da shi da wani Bafade har suna tafe wannan Bafaden na yi masa hira, abin da ya bata mamaki da ta ganshi da wani kaya daban ba wanda ta ganshi a jikin bishiyar ɗorawa ba, sai dai har lokacin da suka ƙaraso bai nuna ma yaga me yanayinta ba bare ya nuna ya santa. Bata wani damu ba sai tayi tsammanin dan yana tare da wani ne yasa ya yi mata haka, haka ta wuce cen sashensu gurin kiran da yace Inna Habi tana yi mata. Da daddare suna zaune suna hira su Maryo sai sauraron labarin da ake basu na bikin al'ada wanda sauran bayin suke basu labarin suke, Fulani Zaliha ce ta aiko a kira Maryo Inna Habi sam bata so haka ba saboda tana gudun ƙananun maganganun gidan. Maryo kai tsaye ta wuce sashen Fulani Zaliha da sallama ta shiga sashen, kan mazauninta na alfarta hangota zaune cikin shiga ta alfarma, bayin da suke kula da ita suna tayi mata hidima. Cikin girmamawa ta rissina ta gaida Fulani Zaliha, da fara'a ɗauke a fuskarta ta amsa mata sannan ta miƙa mata wasu kaya masu kyau ta ce. "Idan Allah ya kaimu gobe bikin al'ada so nake kiyi kwalliya da wannan kayan ina san ki fi kowacce Baiwa kyau." Maryo ba ƙaramin jindaɗi tayi ba haka ta dinga zabga mata godiya da Addu'a babu adadi, miƙewa Maryo tayi zata tafi har ta je bakin ƙofa Fulani Zaliha ta ce. "Ungo wannan ki miƙawa Saif Alkakin nan yana nan zaune yana bitar karatu" russunawa Maryo tayi ta karɓa da sallama ta ƙarasa gurin Saif ta miƙa masa, karɓa kawai ya yi ya ajiye sannan Maryo ta fice daga sashen. Tana fita mararrabar matan sarki sabuwar Baiwar Fulani Maryama ta ƙwala mata kira tana zuwa ta ce. "Ki shiga ciki dama yanzu shugabata ta aika a kira ki" Maryo kanta tsaye ta shiga ta russuna da ladabi ta gaishe da Fulani Maryama. Bayan ta amsa ta miƙa mata wata ƴar doguwar wuƙa a cikin gidanta ta ce. "Ungo wannan ki je turakar Mai Martaba duk wanda ya tambayeki ki ce masa ni ce na aiko ki, idan kinje ki zaro ta daga gidanta ki ɗora aka adakarsa, ɗazu da naje yana bani tarihin shekarunta na manta na taho da ita yace tana da muhimmanci a gurinsa shiyasa bazan bari ta kwana a gurina ba, idan kin kai ki dawo zan baki saƙo ki kaiwa uwar bayi." Maryo kanta tsaye ta karɓi aiken Fulani Maryama bata tsaya ko ina ba sai turakar Sarki Aminullah. Mamaki take sosai yadda ta ga gurin babu wani me gadi ko ɗaya kanta tsaye ta faɗa cikin turakar da yake da duhu haka ta fara laluben gurin da aka ce ta ajiye wuƙar. Wani uban itace aka buga mata a baya ana faɗin. "Ƙarya kike makira ƴar talakawa" da sauri suka zagayeta aka haske turakar da fitilu sannan aka ɗaureta cikin wata irin murtukekiyar sarƙa. YANZU BAKWA COMMENTS SOSAI BANSANI BA KO LABARIN NE BAYA MUKU DAƊI 😥😥😥😥 _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [28/10/2021, 19:07] Ameera Adam🌚: 16... Maryo cikin kiɗima da tashin hankali ta ce. "Dan Allah me nayi muku meye laifina?" Ɗaya daga cikin faɗawa ne ya kifeta da mari yace. "Tambayarmu ma kike yi me kikayi saboda tsabar rashin kunya?" Maryo shiru tayi tana jin jiri na ɗibanta da wani iri da kanta yake yi. A hankali Mai martaba ya ƙaraso gurin cikin ɓacin rai yace. "Ku wuce da ita gidan horo ɗaki na goma" tun bai rufe baki ba suka fisgi Maryo da ƙarfin tsiya suka fice da ita, Sarki Aminullah dafe kansa ya yi cikin damuwa ya furta. "Me na yi wa Zaliha take san hallakani me na aikata mata haka? Dama ƙiyayyar da take mini har ta kai haka? Ashe zata iya haɗa baki da wata a hallakani?" Ya jima a gurin yana zantuka kala-kala daga ƙarshe ya miƙe ya ɗauro alwala domin gabatar da sallar nafila. Maryo ban da kuka babu abin da take yi damuwarta ɗaya da har lokacin batasan laifin da tayi ba, tun da ga shi har Mai Martaba da kansa yace akai gidan horo ta tabbata wannan ba ƙaramin laifi bane. Gidan horo wani gida ne mai ɗauke da manyan ɗakuna guda goma kowanne ɗaki akwai irin masu laifin da ake kaiwa ciki, lokacin da suka ƙarasa gidan baƙiƙƙirin yake sai aci bal-bal da Dogarawan suke tafe da ita kamar masu bautar wuta, tunda suka shiga ta ga ana lelleƙowa ta jikin windon ɗakin da ya kasance guda ɗai-ɗai a kowanne ɗaki, dukda duhun da ke mamaye a gurin bai hanasu san ganin wacce aka shigo da ita a cikin tsohon daren nan ba. Suna zuwa ɗaki na goma aka buɗe aka hankaɗa Maryo a ciki nan take suka rufo ƙofa suka fice daga gidan gabaɗaya. Yadda suka wurgar da Maryo a haka ta durƙushe a gurin tana wani irin gursheƙen kuka tana ambatar sunan Inna da kuma Abu, tana cikin wannan yanayin taji an zabga mata mari daga cen gefenta na hagu, ɗagowa tayi a gigice dan ganin wanda ya mareta amma duhun ɗakin ya hanata fuskantar wanda ya mareta. Wani abu ne ya tsaye mata a rai sai kawai ta ƙara rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Cikin wata irin murya shugabar ɗakin ta ce. "Zaki rufe mana baki ko sai na saɓa miki a gurin nan? Akanki aka fara shigowa gidan horo zaki hana mutane bacci da tsohon daren nan da alama ke ƙaramar ƴar iska ce." Maryo bata bi ta kan me maganar ba ta ci gaba da rera kuka me ban tausayi. Batayi aune ba taji saukar duka ta ko'ina a jikinta, nan take kanta ya ci gaba da sara mata sai kuma jini ya ci gaba da zuba daga hancinta kamar wacce taji mugun rauni. Badariyya ita ce shugabar matan da suke cikin ɗakin kuma ita ta mari Maryo ta kuma jagoranci dukan da suke mata, daga jikin hannunta taji wani abu kamar jini, ta tsorata sosai sai dai babu damar ganin me yake faruwa saboda duhun da ke cikin ɗakin. Mutane huɗu ne suka rufawa Badariyya baya wajen dukan ta, dan haka Badariya jikinta ne yayi sanyi jin yarinyar da suke duka kamar bata motsi. A hankali suka ji iska ta fara kaɗawa a cikin gabaɗaya gidan, sannu a hankali winduna ko ƙofofi suka amshi tayin da iskar take yi musu suma suka fara kaɗawa, tun suna yi a hankali har suka fara kaɗawa da ƙarfin gaske wata irin guguwa ce take tashi daga ko'ina, ba ƙaramin tsorata mutanen da ke cikin gidan suka yi ba hatta Dogarawan da ke tsaron bakin ƙofofin kowa ta kansa ya yi, dan ba ƙaramin tsorata suka yi da ganin irin iskar da take kaɗawa ba. Sai da iskar ta ɗauki lokaci me tsawo sannan komai ya fara lafawa kamar babu wani abu da ya taɓa faruwa. Mutanen da suke cikin ɗakin su Maryo duk sunyi jigun-jigun kowa cikinsa ya ɗuru ruwa, duhun da ke cikin ɗakin shi ya hanasu ganin abin da yake faruwa. Da Asubar fari ƴan ɗakin su Maryo suka tashi da mummunan tashin hankali sakamakon ganin gawarwaki a tsakar ɗakinsu kwance cikin jini, kafin wayewar gari tuni labari ya isa gurin dogarawa daga nan kuma labari isa zuwa fada. A cikin daren bayan tafiyar da akayi da Maryo Mai Martaba ya jima a zaune sannan ya kira ɗaya daga cikin dogarawansa ya aika shi sashen Matansa akan ya kira masa Fulani Zaliha. Cikin girmamawa ya amsa tare da barin gurin. Lokacin da Dogari yaje bakin sashen Fulani Zaliha baiwarta ya kira ya yi wa bayani, fuskarta ɗauke da damuwa ta ce. "Naji abin da ka faɗa sai dai ina tsoron sanarwa da uwar gijiyata saboda halin da take ciki, tun ɗazu jikin Mabiyin yarima ya rikice banda amai babu abin da yake yi, yanzu haka tana cen tsaye akansa sai suma yake yi." Dogarin yayi jim sannan yace. "Haka zaki yi ƙoƙarin sanar da ita saboda Mai Martaba ba abin wasa bane." Laraba ta juya jiki a sanyaye ta shiga sashen Fulani Zaliha a lokacin da ta shiga Saif na kwance ya samu jikin nasa ya lafa, Labara russunawa tayi cikin girmamawa ta ce. "Ranki shi daɗe Mai martaba ya aiko yana san ganin ki yanzu" da mamaki Fulani Zaliha ta kalli Laraba ta ce. "Ki je ki ce wa ɗan aiken ina zuwa." Laraba ta shi tayi ta wuce ta sanarwa da Dogarin sannan ta koma gurin zamanta ta zauna. Fulani Zaliha tayi mamaki sosai akan kiran da Sarki Aminullah ya yi mata saboda rabonda ya aika kiranta haka kawai har ta manta, alkyabbarta ta sa ta feshe jikinta da turare. Sai da ta ƙara leƙa Saif sannan ta kira su Laraba ta umarce su akan su zauna a bakin ƙofar saif su kula da shi, saboda ko da zai farka bata kusa. Tana fita kai tsaye ta wuce turakar Mai Martana, lokacin da ta ƙarasa ciki yana kwance ya lumshe idanunsa kamar me bacci. Bakinta ɗauke ta sallama ta shiga ciki tana shiga ta zame alkyabar jikinta, gefen kan shimfiɗarsa ta zauna ta ce. "Barka da hutawa Ranka shi daɗe uban mai marayu majidaɗin talakawa mai iyayenma suna Allah san barka, Ina zaune an aiko da..." bata ƙarasa magana ba Sarki Aminullah ya ɗauke fuskarta da wani irin azabtaccen mari, kafin ta dawo daga azabar raɗaɗin marin da ya yi mata ya ƙara ɗauke fuskarta da wani gigitaccen mari. Nan take ta kiɗime har wasu irin taurari take a idanuwanta saboda zafin marin da ya sakar mata, tana cikin wannan yanayin Sarki Aminullah ya damƙo wuyanta ya shaƙe idanuwanta suka firfito har tana kakarin tari saboda wahala, sai da ya ga ta galabaita sannan ya yi wurgi da ita cen jikin bango. A wahalce take sauke ajiyar zuciya saboda yadda ya shaƙe wuyanta ji tayi kamar zata mutu, ɗago da shayayyun idanuwanta tayi tana yi masa wani kallo murya na rawa ta ce."Ranka shi daɗe me nayi maka haka kake so ka kashe ni?" Wata razananniyar tsawa ya buga mata wacce tayi sanadiyyar gutsire ragowar maganar da take shirin faɗa, ba ƙaramin tsorata tayi da yanayin da ta ganshi tayi ba, jikinta har karkarwa yake. Tana nan a takure ta ji yace. "Ashe ke makira ce annaimiya bansani ba? Wannan lumbu-lumbunnda kike yu mini ashe mugun hali ne fal a ranki? Sai anyi magana ki fara Allah yace Annabi yace ashe sheɗan da zuri'arsa ne a ƙasan zuciyarki. Kin bani mamaki Zaliha duk cikin matana babu wacce nake ƙauna kamar ce babu macen da na nunawa so miraran kamar ke amma da abin da zaki yi mini sakayya kenan, bazan sauwaƙe miki ba haka zalika bazan sa a hukuntaki ba ta yadda wani zai yi tsammani har zancen ya fita, saboda idan na wulaƙanta ki kaina na wulaƙanta ko ba komai ke uwar Ɗana ce kuma idan za'a bada labari za'a ce tsohuwar matar Sarki Aminullah ce ko a ce Mahaifiya Saif Ɗan gidan Sarki Aminullah, zaki ci gaba da zama a ƙarƙashina kuma daga yanzu duk abin da ya same ni kece saboda akwai wani ɓoyayyun aminai na da suka san komai, ni da kike kainuwa ne dashen Allah kuma na zama ƙadarangaren bakin tulu a karni a kar tulu a barni na ɓata ruwa, kije da halinki Allah ya ƙara tsareni daga kaidinki." Fulani Zaliha ban da hawaye babu abin da take yi saboda irin maganganun da ya gasa mata har ta fi jin zafinsu akan zafin marin da ya yi mata. Murya a sanyaye ta kalleshi ta ce. "Ba tun yau na kwana da sanin ka jima da yakiceni daga zuciyarka ba, duk irin wulaƙancin da ƙasƙancin da aka nuna mini ban taɓa buɗe baki nayi magana ba, ni da Ɗana ka juya mana baya babu wanda nake gani a cikin gidan nan naji daɗi bayan Saif a koyaushe a kyara muke a gurinka, babu tausayi ko tausasawa a tsakaninmu saboda kawai na haifo maka yaro nasakasasshe, na janye yarona da ni kaina daga gareka wannan ma ban tsira ba har sai ka kirani ka tozartani ka ci mini mutumci, bansan laifin da kake tuhumata da shi ba da har kake alaƙantani da annamimiya." Kuka ne ya ci ƙarfinta sai da tayi me isarta sannan ta ci gaba da cewa. "A wannan ƙadamin da ake ciki tura ta kai bango ko da sakina ka saka aka wulaƙanta ni bazan yi kaico ba domin na lura ba mu ne a gabanka ba, abu ɗaya ne zai dameni wato Saif zanyi ta tunanin halin da makomarsa zata kasance tun da dama ni yake gani yaji daɗi a zuciyarsa. Bansan abin da nayi maka ba kuma bazan tilasta ka da ka gaya mini ba, nidai a kullin kuma a kodayaushe nasan Allah ba azzalumin bawansa bane sai bawan da ya zalinci kansa, tabbas Allah shi yake sanmu kuma shi ya kafamu a cikin gidan dan haka saniyar da bata da jela Allah shi yake kore mata ƙuda." Fulani zaliha daga haka ta miƙe tana hawaye sannan ta zira alkyabbarta ta fice daga turakar ko waiwayen Sarki Aminullah bata yi ba. Sarki Aminullah jim ya yi maganganun Fulani Zaliha na niyyar tasiri a zuciyarsa, a ɓangare guda kuma maganganun Fulani Maryama da kama yarinyar da akayi na ƙoƙarin danne zantukan da Fulani Zaliha tayi masa, kansa ba ƙaramin zafi ya ɗauka ba saboda abubuwa na neman rikita shi lokaci guda. A baya dai yasan ya yarda da Zaliha ɗari bisa ɗari amma me yasa zata aikata haka agareshi? Tashi ya yi ya fara kaiwa yana komawa dan ganin matakin da ya kamata ya ɗauka, wani tsagi na daga zuciyarsa yana san aminta da Fulani Zaliha ya yinda wani tsagin yake ƙaryata ta da kalamanta. Fulani Maryama na cikin rumfarta tana ta zarya kamar wacce ta yi wa sarki ƙarya, da wata mai sanye da kayan bayi ta shigo fuskarta a naɗe ta yadda babu wanda zai gane ta. Tana zuwa ta russuna cikin girmamawa ta ce. "Allah ya taimakeki aiki ya tafi yadda ake so si jiran sakamako. Babban albishir da zan sanar da ke uwar gijiyata tuni Takawa ya sa anwuce da ita gidan horo" Fulani Maryama tayi murimushi mai sauti ta ce. "Kije zan neme ki zuwa safiya akwai tukwicin da zanyi miki" Me ɓoyayyiyar fuskar ta ƙara russunawa tana godiya sannan ta fice daga rumfar. Fulanj Maryama farinciki ne ya kamata dan tasan ko ba komai haƙanta zai cimma ruwa, tasan ba makawa sai an turata gidan horo daga nan tana da tabbacin Mai Martaba sawa zai yi a kashe su gabaɗaya, idan kuma ya musu da adalci ya sa a ɗaure su ɗaurin rai da rai. Lokacin da Fulani Zaliha ta koma sashenta gari yayi shiru sai kukan tsuntsaye da ƙarananan dabbobi, tana zuwa ta sallami Bayinta suka wuce makwancinsu ita kuma ta wuce cikin ɗakinta, saboda ɓacin rai ko ɗakin Saif bata leƙa ba. Tana shiga ta faɗa kan gado ta fashe da wani irin matsanancin kuka, lokaci ɗaya taji zaman gidan gabaɗaya ya fice mata daga rai ji take a ranta ina ma ace Mai martaba ya saketa ko ta huta da baƙin cikin da take ƙunsa a cikin gidan. Sai da tayi me isarta sannan ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallar nafila tana kaiwa Allah kukanta akan ya magance mata matsololinta da abin da yake damunta. Ta idar da sallah tana tsaka da addu'a tashi motsin Saif ya fito daga ɗakinsa da sauri ta fita dan batasan inda zashi a tsohon daren nan ba tunda ba cikakkiyar lafiya gareshi ba. Tana fita ta riƙe shi tana yi masa sannu, ga mamakinta sai ji tayi yace. " Yauwa Ammi" a taorace ta ɗago ta kalleshi baki a buɗe ta ce. "Saif kaine kuwa?" tafiya ya yi luuu kamar zai faɗi da sauri ta riƙoshi ya dafa kansa yace. "Ammi kaina ciwo yake" Fulani Zaliha ido ta zura masa har lokacin kallonsa take da mamaki har ta kasa furta koda kalma ɗaya sai da ya kuma cewa. "Ammi kaina ciwo juwa nake ji" Riƙoshi tayi ta wuce da shi cikin ɗakinta tana binsa da kallo a gefe ɗaya kuma zuciyarta fal farinciki sai ta nemi damuwar da take ciki ta rasa gabaɗaya. Gabaɗaya mutanen da suke cikin gidan horo hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda tun da suke ciki basu taɓa ji ko ganin irin makamanciyar guguwar da akayi ba, uwa uba kuma gawarwakin su Badariya da aka wayi gari dasu duk anmurɗe musu wuya, wani babban tashin hankali jikinsu duk ya yi wani dabbare-dabbaren taruwar jini. A ɓangaren Maryo kuwa tana kwance cikin jini da alama ko numfashi bata yi, ga wani irin yalo da tayi shar kamar wacce jinin jikinta ya ƙare. Da sauri Dogarawa suka fara fitar da su ana kwantar da su akan tabarmin kaba, ana ƙoƙarin kaisu gurin da za'a yi musu sutura suka ji Maryo na sauke ajiyar zuciya, da saurinaka cireta daga cikinsu cikin gaggawa aka sanarwa Mai martaba halin da ake ciki. Nan take ya bada umarnin aka kaita asibitinsu kuma ayi musu sutura, bayan da aka wanke su aka Mai martaba da kansa ya sallaci gawarwakinsu sannan aka wuce da su gidansu na gaskiya. Sarki Aminullah da kanshi ya shiga cikin gidan horon dan ganin yadda al'amarin ya kasance, ƙofofi da windunan ɗakunan haka Dogarawa suka dinfa ɗebosu da hannunsu suna ajiyesu a gefe. Sarki Aminullah ba ƙaramin razana da ganin abin da ya faru ya yi ba, jiki a sanyaye ya wuce gida yana ta'ajibun lamarin saboda ko kaɗan babu wata guguwa da akayi a cikin gidan masarautar sai gashi gidan horo yayi fata-fata har da wasu guraren da suka rurrushe, bishiyoyi duk sun kaɗe wasu duk reshinansu sun faɗo. Kafin wani lokacin tuni labari ya baza ko'ina na cikin masarautar, daga labarin Maryo har zuwa labarin abinda ya farunda halim da take ciki, Inna Habi banda kuka babu abin da takeyi ita da Abu lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta lalace kamar wacce tayi jinya. Cikin kuka take faɗin, "Kaico yarinyar nan da wannan ƙaddarar tazo miki tabbas nasan Maryo bazata aikata abin da ake zarginta da shi ba sai dai, idan wani kaidin aka ƙulla mata, Allah ka na kallon baiwarka ƴar marainiyar Allah babu uwa babu uba ka dubi halin da take ciki ka kuɓuto da ita..." Abu ta yi ƙasa da murya ta katse Inna Habi da cewar. "Dan Allah Inna ki daina faɗin haka. Kina ganin yadda mutane suka kallo yanzu haka sai su fahimci cewar bake kika haifi Maryo ba kinga wani ma wata fassarar zai yi miki ta daban." TO FA MEYE HARSASHEN KU? KUYI HKR BAN TACE SHI BA👏🏻 _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [29/10/2021, 19:31] Ameera Adam🌚: 17... Inna Habi wata uwar harara ta watsawa Abu cikin hassala ta ce. "Su faɗa mana sai me indai za'a dawo mini da Maryo. Allah ya sani yarinyar nan jin ta nake har cikin raina kamar nina haifeta akanme bazanyi beken rashinta ba, yanzu fa shikenan ƙila kashe ta za'a" Inna Habi na zuwa nan a zancenta ta kuma rushewa sa wani irin kuka. Mutanen gurin sai bin ta suke da kallo ƴan ƙananan maganganu suna tashi, daga cen gefe Jakadiya na zaune tana jin abin da Inna Habi take faɗa, cikin zuciyarta ta ce. "Tsinanniyar yarinya ashe ma ɓalɓaltacciya ce duk ta susutamu ni da Maryama, ai koda kasheta za'a yi ankashe banza" Jakadiya wani nazari tayi da sauri ta miƙe ta ƙarasa gurun Inna Habi cikin yanayin damuwa ta dafa cinyar Inna Habi ta ce. "Kaico Habi dole kiyi kuka wallahi koni yarinyar nan da ba wani daɗewa nayi da ita ba duk ta shiga zuciyata, yanzu haka raina duk a dagule yake Allah dai ya ƙuɓuto da ita ya tashi kafaɗunta ya bata lafiya. Habi ba kuka zakiyi ba Addu'a zamuyi mata." da sauri Inna Habi ta ce. "Jakadiya Bangane Allah ya tashi kafaɗunta ba yarinyar da take tsare a gidan horo" Kafin Inna Habi ta gama magana Jakadiya ta kauda kai gefe a hankali ta ce. "La'ananniya daga cen ma Allah ya datse ranta ko ma huta, Astagafirulla wai ni ce harda yi mata addu'a" sai kuma ta ɗago ta cewa Inna Habi. "Habi ina take gidan horo yarinyar da aka kaita asibiti rai a hannun Allah ance jinin jikinta fa duk ya zuƙe, Allah na tuba wayasan zunubin da yake gidan horon ai shiyasa iftila'in ya tsaya iya kansu cen gayyar tsiya arna a idi." Inna Habi zaro ido tayi ta ce. "Maryo ɗin ce rai a hannun Allah? Yau na shiga uku ni Habi naga ta kaina shikenan sunyi mini sanadiyyarta Allah ya sa kar ciwon zuciyarta ya tashi na shiga uku na lalalce." Inna Habi ta ci gaba da sharɓar kuka cikin ƙunan rai da tashin hankali. Duk wanda yake gurin sai da yaji kukan Inna Habi har cikin zuciyarsa, ba ƙaramin tausayi ta basu ba wasu kuma daga ciki suna ganin kamar saka Maryo akayi saboda a ƴan shekarunta ba yadda za'ayi tayi wannan tunanin tunda ko da ta kashe Sarki Aminullah wace riba zata samu tun har lokacin labari bai je musu na cewar Fulani Zaliha ake zargi da haɗa baki da Maryo akan farmakin da Maryo ta kaiwa Sarki Aminullah. Fulani Maryama zaune take a turakar Mai martaba fuskarta ɗauke da damuwa ta ce. "Allah ya taimakeka naji ka aika kira na" Sarki Aminullah har lokacin fuskarsa ɗauke da damuwa yace. "Maryama na kiraki ne domin na tambayeki" Cikin Maryama ne ya ɗuru ruwa nan take gumi ya shiga tsatssafo mata tayi ƙarfin halin cewar. "Tambayar me ranka shi daɗe" Ajiyar zuciya Sarki Aminulla ya sauke ya ce. "Akan maganar da kika zo mini da ita" A firgice Maryama ta ɗago ta kalleshi ta ce. "Ina jinka Mai Martaba" Sarki Aminullah yace. "Ina san naji bayan ni wa kika sanarwa da maganar jiya" Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke ta ce. "Wa zan sanarwa Mai Martaba idan nayi haka ai kamar ban kyauta maka ba" Gyaɗa mata kai ya yi yace. "Ya yi kyau shiyasa nake ƙara ƙaunarki saboda kyawawan ɗabi'unki, zan gargaɗe kinda karki sake maganar nan ta fita banasan naji zancen a waje, yarinya dai mun turata gidan horo ita kuma Zaliha zamu ci gaba da zama da ida saboda rufin asirinmu, dan haka ki kiyaye" Fulani Maryama sam ba haka ta so ba ta so itama Fulani Zaliha an haɗa da ita amma ba yadda ta iya, ƙaƙalo murmushin ƙarya tayi ta ce. "Godiya nake ranka shi daɗe ai dole na ne tunda mutuncinka mutuncinmu ne gabaɗaya" yaji daɗi kalamanta nan take ya ci gaba da sa mata albarka sannan Fulani Maryama ta ci gaba da yi masa kalaman ƙarya, daga har ta lura da baccin da ya fara ɗaukan Mai Martaba, tashi tayi ta bashi guri sannan ya kishingiɗa nan da nan bacci yayi awon gaba da shi. A cen asibitin Murtala Maryo kwance take kamar gawa ta kuma yin wani yello shar su kansu likitocin sunyi mamaki dan basu taɓa cin karo da mara lafiya kamar ta ba, gwajin jini aka dnga yi dan a samu jinin da zai yi dai-dai da nata, Babban amintaccen Dogarin da Sarki Aminullah ya wakilta da shi ake ta shige da fice dan ganin an ceto rayuwar Maryo, haka ya dinga kiran ƴan uwansa fadawa ana gwada jininsu dan aga ko zai yi dai-dai da na Maryo amma gabaɗaya babu wanda yayi dai-dai. Ba ƙaramin damuwa likitocin suka shiga ba, haka daga gurin Babban Dogarin Sarki, yana tsaye a bakin ƙofa cikin damuwa wata almajira tazo bara wajensa tana neman taimako, cikin ƙosawa da zancenta yace. "Iya dan Allah ki saurara mini inji da abinda yake damuna, da yarinyar cen zanji ko da roƙon da kike mini" Tsohuwar cikin jimami ta tambayeshi a nan yake labarta mata abin da yake faruwa da Maryo, bayan ta tausaya mata ta ce. "Yaro me zai hana muje a ɗauki jini na?" da mamaki ya kalleta yace. "Iya majiya ƙarfima an gwada baiyi ba bare ke tsofai-tsofai, ganin ta dage yasa ya amince mata su kansu likitocin da farko ƙin amincewa sukayi dan gudun kar aje a ɓata biyu ɗaya bata gyaru ba. Sai daga baya suka amince ana ɗaukan jininta da aka gwada aka ga yayi dai-dai dana Maryo, yana ƙara mata jinin ta fara wani irin karkarwa da wani irin gumi da yake tsatssafo mata, bayan awa guda da ƙara mata jinin ta buɗe idanunta, da sauri Dogarin ya kira likitocin yana leƙawa dan ya kira tsohowar da ta taimakawa Maryo ya neme ta ya rasa, Likitocin na zuwa suka fara jero mata sannu, bata amsa musu ba tabi window da kallo a hankali ta furta. "Rujayma" sai kuma ta saki murmushi, tsohuwar da ta kira da Rujayma ta ce. "Na barki lafiya ya shugaba ta." _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [30/10/2021, 19:28] Ameera Adam🌚: 18... Maryo na ganin wucewar Tsohuwar ta saki wani malalacin murmushi sannan ta lumshe idonta, Likitan ne ya fara kiran sunanta amma ɗif kake ji ba magana da sauri ya fara bubbuga ƙafarta a hankali ta buɗe idonta ta kuma limshe su, da sauri ya kira sauran likitoci suka ci gaba da bata agajin gaggawa dan ganin sun ceto rayuwarta. Sunfi kusan awa guda akanta sannan suka samu ta sake farfaɗowa, tana farfaɗowa ta fara wata irin shaƙuwa babu jimawa tari ya sarƙe ta sannan ta fara wani irin aman jini, hankulan mutanen gurin gabaɗaya ya tashi ganin wannan aman jinin da take yi. Sai da suka yi mata allurai sannan suka samu aman jinin ya tsagaita. A hankali take sauke wahalallan numfashi fuskarta tayi fayau da alama tana jin jiki, bacci ne ya ɗauke ta sannan likitocin suka fice daga ɗakin suna sharce gumi, Dr Musa shine likita da ragamar kula da lafiyar Maryo yake hannunsa, yana zaune a office ya aika aka kira masa Babban Dogarin sarki da ke cikin asibitin, bayan ya shiga ya zauna yace. "Likita naji ka aika kirana Allah yasa dai lafiya?" Dr Musa ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye biron dake hannunsa yace. "Lafiya ba lau ba. Gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, rayuwarta na fuskantar barazanar mutuwa me kukayi mata haka da ya tayar mata da ciwon zuciyarta, kasan matakin da ciwonta ya kai kuwa? Gaskiya na tsorata sosai akan lamarinta kana ganin dai wahalar da aka sha kafin a samu me kalar jininta, abin da zan gaya muku akanta bai wuce kula da lafiyarta ba. Wai ma ya akayi kuka bari ciwon zuciya ya kama ƴar ƙanƙanuwar yarinya kamar wannan? Kuma me kuka aikata mata na ɓacin rai da ya tayar mata da ciwon nata?" Likitan ya faɗa yana tsattsare Dogarin da kallo. Dogarin ɗagowa ya yi yace. "Likita nifa waɗannan tambayoyin gabaɗaya bani da amsarta, ni da ka ganni aikin Allah ma nake yi saboda Baiwar Sarki ce bani da tabbacin lokacin da ta haɗu da wannan ciwon, nidai nasan a anwayi gari da samun gawarwaki har da ita a cikinsu sai ita kaɗai ce ta rayu ka ga kuwa bana ce ga silar ciwon nata ba" Likitan yace. "Ba dai sune gawarwakin da Mai martaba ya sallace su ba?" Dogarin yace. "Eh sune fa" Dafe kai Likitan ya yi yace. "Kaga inda aka samu matsala da angwada gawarwakin wata ƙila a samu silar mutuwar ta su, ita dai a namu binciken ciwon zuciyarta ne ya tashi sakamakon mumman fargaba da ɓacin ran da ta shiga, to kuwa ka ga baza'a ce duka ciwo ɗaya ne yayi silar ajalinsu ba." Dogarin tsai ya yi yana nazari yace. "Maganarka haka take Likita, sai dai a kiyaye gaba dan wannan dai ya faru Allah kuma ya bata lafiya." Likitan ya amsa da Ameen sannan ya ci gaba da bashi shawarwarin da ya kamata. Shi dai Dogarin binsa yake da "Eh a'a" dan yasan wannan dokokin babu inda zasu je tunda Yarinyar da ake zarginma kashe ta za'a yi wane ƙa'idoji za'a shimfiɗa akanta. Sai da ya gama sauraronsa sannan ya tashi ya fice daga Ofishin nasu. Fulani Zaliha na shiga ɗaki Saif ya zauna yana dafe kansa, har lokacin binsa take da kallan mamaki cikin zuciyarta take ayyana wai yau Saif ɗinta shi ne yake furta magana da bakinsa, ɗaga hannu tayi tana godiya ga Ubangijin sammai da ƙassai sai kuma ta fashe da kukan farin cikin, Saif dukda yana cikin wani irin yanayi sai da ya zubda ƙwallah ga mahaifiyarsa saboda yadda yaga tana cikin tsananin farinciki, cikin sanyin murya yace. "Ammi ki daina kuka godiya zakiyi wa Allah subhanahu wata'ala" Gyaɗa masa kai tayi ta ce. "Tabbas maganarka haka take Saif amma kukan da nake yi na farincik ne , Saif tun da na haifeka ban taɓa jin ka furta koda wata kalma bace kaga kuwa dole nayi kuka na godewa Ubangiji tabbas Mahaƙurci mawadaci ne" Fulani Zaliha sun jima suna hira ita Saife sai gabannin asuba Saif ya wuce ɗakinsa ya kwanta itama tayi kwanciyarta, a daren ranar sai ta nemi ɓacin ran da ta taho dashi daga gurin Mai Martana ta tasa amma taci alwashin kafin ya ƙara ganinta a turakarsa za'a jima kuma taci alwashin bakinta da nashi bazata taɓa gaya masa Saif ya warke ba sai dai yaji a gari. Salman tafe yake kai tsaye ya shiga sashen Mahaifiyarsa babu ko sallama, Fulani Maryama tana zaune tana hutawa ta ɗaga kai ta kalleshi. Zama ya yi kusa da ita yace. "Mama wai ina wannan Baiwar taki dana taɓa ganinta anan" Fulani Maryama sarai ta san wacce yake nufi ta yamutsa fuska ta ce. "Wace Baiwa fa kasan Bayin da yawa?" Guntum tsaki ya yi yace. "Wacce kika mareni akanta" Fulani Maryama ta yamutsa fuska tace. "oh! Wai Maryo?" Bai kalli gurin da take ba yace. "Eh ita fa" Fulani Maryama ta ce. "La'ananniya zaka ce, kai wannan yarinya anyi makira Allah dai ya tsine mata..." Wani hautsinannan kallo ya wurga mata ta ja bakinta tayi shiru bata ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa ba. A hargitse yace. "Me tayi kike mata wannan zagin?" Fulani Maryama ta ce. "Meye ma batayi ba? Yarinyar da aka kama da wuƙa a turakar Mahaifinka zata kashe shi" Murmushi ta ga ya fara yi a hankali zuwa wani lokaci ta ga ya ci gaba da ƙyaƙyata dariya sannan ya tsuke fuska yace. "Waye ya tura ta?" Fulani Maryama ta saci kallan bakin ƙofa murya ƙasa-ƙasa ta ce. "An ce Fulani Zaliha ce ta tura ta" Kallan Mahaifiyarsa ya yi yace. "Kai badai Uwar kwantacce ba matar da sam bata san ma kanta ba har ita zata iya sawa a kashe Takawa ki nemo wata dai ba ita ba. Kai ni banajin ma Yarinyar nan zata aikata abin da kika faɗa gaskiya" A hassale Fulani Maryama ta ce. "Wato ƙarya nake yi maka ko?" Salman yace. "Abu a duhu...Nifa gaskiya jikina bai yarda ba kuma zansa Mai Martaba ya fito da ita dan gaskiya santa nake yi bazan bari a kashe ta ba ina ji ina gani" Yana gama faɗa ya miƙe tsaye Fulani Maryama baki a sake ta kalleshi ta ce. " Da ta kashe Mahaifinka fa sakarai kawai?" Ya juyo yace. "Da batayi kuskure ba tunda ko yanzu zan iya riƙe ragamar masarautar Kano." Yana zuwa nan a maganarsa ya fice. A ɗan tsorace Fulani Marayama ta bi bayansa da kallo tana jujjuya maganganunsa a zuciyarsa. Miƙewa tsaye ta yi tana kaiwa da kawowa tace. "Tabbas dole na ɗauki mataki a kanka Salman." Mai martaba sarki Aminullah ne zaune a ɗaya daga cikin manyan tantuna (Rumfuna) da aka tanada saboda manyan baƙi, harabar filin da ke bayan gidan Sarki cike yake da mutane da baƙi daga sassa daga garuruwa waɗanda suke zuwa duk shekara dan taya Sarki Aminullah murnar wasan al'ada da suke yi duk shekara, ƴaƴan Sarakai da manyan daga jikin Gwamnati na halartar wannan taro saboda masarautar Kano babbar masarauta ce da ta kafa tarihi a ƙasar hausa. Mai Martaba Aminullah zaune yake da manyan Abokansa Sarkin Adamawa da Sarkin Nupe, lokaci-lokaci suke kallan wasan suna ɗan tattaunawa a junansu saboda ba ƙaramin ƙayatar da su yake ba. Maƙera ne suka fito suka fara gudanar da wasanninsu da wuta gwanin birgewa, sanye suke da wasu kayan saƙi da hulunan fatar ɓauna abun ya ƙayatar sai wanda ya gani. A bisa al'ada idan Maƙera sukayi wasansu na wuta zasu hura wuta a cikin wani ƙaton kasko su barta ta dinga ci, sai zaratan samari biyu daga ciki su fara ƙoƙarin kashewa abu biyu ne yake faruwa a duk shekara idan akazo bikin maƙera. Duk wanda ya yi nasarad kashe wutar nan ba tare da ta ƙona shi ba Sarki zai tambaye shi abin da yake so ko mai girman abin idan aka cire karagar mulkin da yake kai. Ɗaya daga ciki kuma nan take wutar zata ƙoneshi ƙurmus babu me cetonsa koda kuwa su Maƙeran da suka kunnata, saboda wutar siddabaru ce dama ba kowa ne yake iya shiga gasar ba sai wanda ya shirya. Sarkin Maƙera na gama wasa ya yi shela ga duk wanda ya shirya, a lokacin Sarki Aminullah ya tattara hankulansa kan zaratan Samarin da zai ga sun fito gasar, wani baƙon Bawa ne ya fito tare da Haro sarkin fasa dutse suka fito, Sarki Aminullah ido ya ƙurawa sabon Bawan da kallo nan take yaji gabansa ya faɗi. INA MUKU FATAN ALHERI MU HAƊE A COMMENTS🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [01/11/2021, 16:12] Ameera Adam🌚: *ANYA BAIWA CE?* PAGE 19 BONUS✋🏻😂🤚🏻 Kamar yadda Sarki Aminullah ya zubawa sabon Bawan nan ido haka shima ya zuba masa idanu yana yi yana zagaye kaskon wutar kamar yadda abokin takararsa yake yi, Zagaya wutar suka fara yi suna yi suna ɗiban yashin gurin suna murzawa a hannunsu da jikinsu, idanun jama'ar gurin gabaɗaya ya koma kansu dan ganin wanda zai fara tsokano wutar tunda ita kanta wutar ita kaɗai ma neman abokin lasarta take yi, Haro ne ya gyara tsayuwarsa ya damƙi ƙasa ya watsawa wutar aikuwa kamar wanda ya watsa mata Fetir haka ta kuma tashi sama tana cin bal bal bal kamar zata fara lasarsu tun basu basu taɓa ta ba. Daga Haro har Sabon Bawan ja sukayi da baya kowa na ayyana ta yadda zai fara ɓullowa lamarin wutar, saboda sihirinta ya wuce tunanin me tunani. Daga cen gefe Mai Martaba Aminullah ne ya yi murmushi yana kallan Aminansa biyu, Sarkin Adamawa Dr Musa Ɗan bahaushe ya kalli Amininsa yace. "Wa kake ganin zai iya cin wannan nasarar?" Sarki Aminullah ya yi murmushi yace. "Alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba. Dan nasan waye Haro ka ga kuwa ruwa ba sa'an kwando bane." Sarki Musa yace. "Amma ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare" Sarki Aminullah ya yi wani irin murmushi sannan yace. "Duk faɗin gurin nan kana gani babu wanda ya yarda ya shiga gasa da Haro, saboda wanda ya taka wuta, idan ya ga toka sai ya yi nesa da ita. Su kansu sun waye Haro wancen yaron ma da alama baƙo ne dan na lura da yanayinsa." Sarkin Nupe Sarki Abdullahi murmushi shima ya yi yace. "Yanzu fa duk harsashe ne kawai muke yi amma tuni Ubangiji ya zaɓi me yin nasara." Gabaɗaya suka amsa masa sannan suka mayar da kallansu wajen su Haro. Kallan kallo aka shiga yi da tsakanin Haro da Sabon Bawan sannan Haro ya yi kukan kura ta nufi wutar gadan-gadan, shima daga ɓangarensa Sabon Bawan cikin ƙwarin gwiwa ya nufi gurin nan take suka fara artabu da wannan wutar dake cikin kasko, duk lokacin da jikin Haro dana Sabon bawan ya haɗu sai kaji ya bada wani irin sauti kamar haɗuwar takubban da ake tsaka da azababben yaƙi. Sannu a hankali rigunan jikinsu suka fara ƙonewa suna bajewa cikin toka ya zamana daga su sai wandunan ƙarfe. Al'amarin da ya ƙara jan hankulan al'ummar da ke gurin, kowa ya yi shiru banda sautin kokawarsu babu abinda yake tashi agurin. Wasan ne ya fara ɗaukan zafi saboda yadda wandunan jikinsu tuni suka amsa tayin turirin zafin da wutar take yi musu, ganin wankin hula na hiyyar kaisu dare yasa Haro ya ƙara bada azama wajen ganin ya juya akalar wutar zuwa ga wannan Sabon Bawa, kamar wacce ya sanar da ita wutar haka ta juyar akalarta zuwa gareshi har ta fara ƙoƙarin kaishi ga halaka, ganin haka ba ƙaramin faranta ran mutanen da ke gurin ya yi ba saboda kowa fatansa bai wuce ace Haro ya yi nasara ba. Sabon Bawan na ganin haka ya miƙe a zabure yana motsa bakinsa nan take wutar ta juya ga Haro har ta kwantar shi ƙasa, miƙewa ya yi tsaye yana murmushin nasara sai dai babu walawala a fuskokin mutanen da ke gurin, ganin wutar ta tasamma halaka Haro yasa ya ƙarasa gurin ya kashe ta a lokacin tuni Haro ya fita hayyacinsa.Daga cen gefe Sarkin ƙira ne ya fito yana tafi haɗe da girgiza gwangwani mai ɗaure da wuri a hannunsa, yana zuwa ya kama hannun Sabon Bawan ya ɗaga sama tare da ɗaura masa wata ƙatuwar laya a damtsen hannunsa. Amma wani abin mamaki yana ɗaura layar sai ta suɓuce ta faɗo ƙasa ya gwada haka ya fi a irga, gabaɗaya mutanen gurin ido suka zubo musu suna kallon abin da yake faruwa. Da sauri wasu manyan Bayi suka ɗauke Haro da yake cikin wani irin yanayi. Sarkin Maƙera ya kalli Sabon bawa da mamaki shima shi yake kallo yana yi masa shu'umin murmushi. Sabon Bawan ƙasa ya yi da murya yace. "Ni da kake gani nafi ƙarfin siddabarunku ya kama ni" yana gama faɗa zubawa layar ido nan take ta hau ƙuncewa da kanta sai ga wasu irin ƙananun allurai da karyayyun reza haɗe da wani irin rubutu a ciki. Mutanen da ke zagaye basu san me yake faruwa ba a tsammaninsu Sarkin Ƙira wani abu na girmamawa yake masa dan haka aka ga sun haɗa kai guri ɗaya. Sabon bawan ya kalli Sarkin Ƙira yace. "Idan zaka gina ramin mugunta gina shi gajere dan bakasan wanda zai faɗa ciki ba, daga yanzu idan zaka shuka mugunta kasan wanda zaka aikatawa." Kunya ce ta kama Sarƙin ƙira yana shirin tsugunnawa ya roƙeshi ya ruƙo hannunsa ɗaya yace. "Idan kayi haka sauran jama'a zasu fahimci halin da ake ciki gwara ma mu bar lamarin a tsakaninmu, amma da sharaɗi guda ɗaya" bakin Sarkin ƙira har rawa yake yace. "Me nene sharaɗin a yanzu na aikata maka" Murmushi Sabon Bawan ya yi ya huro iska akan tafin hannunsa nan take sai ga Sarƙin ƙira tsaye tare da Haro yana yi masa bayani kafin shigar su Haro da Sabon Bawan filin gasa. Haro yace. "Sarkin ƙira kamar yadda aka saba duk shekara wannan shekararma haka zamu yi da kai ga layar nan a duk lokacin da muka shiga fafatawa idan kaga za'ayi nasara a kaina ka dinga murzata, idan kuma har anyi nasara akaina lokacin da zaka bawa abokin hammaya kambun girmamawa ka naɗa masa a hannunsa kafin a tashi daga taron wasan al'ada zai kwanta ciwo kamar yadda muka taɓa yi da Marigari Iliya Mudubi, dan wallahi da girmana ya faɗi gwara uban kowa ya rasa." Sarkin ƙira yace. "Maganar gaskiya Haro tsoro nake ji karfa asirinmu ya tonu dukda dai ba'a taɓa samun matsala ba, amma ina gudun ɓacin rana" Haro yace. "Haba kamar ba wayayye ba ina baka kana ƙin karɓa, kasan dai bana maka ƙaramin alheri duk shekara kawai ka share haka za'a yi" Sarƙin ƙira ya amsa tare da cewa. "Amma farashin wannan shekarar ya ƙaru sai ka ninnikamin kyauta ta" Haro yace. "Wannan mai sauƙi ne" Sarkin ƙira tun bai gama gani ba jikinsa ya hau tsuma a tsorace yace. "Tuba nake dan Allah ka rufa mini asiri" Sabon Bawan yace. "Idan ka bi abin da zan saka ka ba. Kaga dai ba a gaba kuka yi ba ko?" Da sauri Sarkin ƙira ya gyaɗa kai. Sabon Bawan yace. "To yadda na ganku ba tare da kun sani ba haka yanzu zan ganka a lokacin da na baka wannan aikin" yana gama faɗa ya huro iska daga bakinsa nan take sai ga wata farar leda me ɗaure da wani irin gwamamman rubutu a jikinta, cikin ta wani farin yashi nemai ƙamshi haɗe da sanyi, miƙawa Sarkin ƙira ya yi haɗe da cewa. "Wannan yashin nake son ka haƙa rami me zurfi a cikin gidan Sarki ka binneshi a haka, abin da nake so da kai kenan amma muddin ka saɓawa haka wallahi sai na kasheka da kisa me tsanani." Sarƙin ƙira na jin haka ya ɗago a firgice yana kallansa bayan ya karɓa yace. "Indai wannan ne ai ƙaramin aiki ne" Sabon Bawan yace."Ka adana shi sannan ka cigaba da shagali kamar komai bai faru ba." Sarkin ƙira karɓa ya yi ya sa a aljihu sannan ya ci gaba da wasa Sabon Bawa haɗe da rawa yana waƙa kamar yadda yake bisa ga al'ada ga duk wanda ya ci. Sarki Aminullah jin jikinsa yake wani irin sam bai so ace ba Haro ne yaci ba amma babu yadda ya iya, bayan fitar Sarkin ƙira da Sabon Bawa sai masinta suka fito suma suka shiga nuna tasu bajintar dan ganin sun faranta ran Mai Martaba. Kifaye masu rai suka fito da su suka zuba a ƙasa nan take Kifayen suka fara iyo a ƙasa kamar waɗanda suke cikin ruwan bayan kamar wasu mintuna sai suka ciro fatsarsu ta kamun kifi, saida suka ɗaga ta sama suna nunawa kowa babu komai a ciki sai suka sauke suka fara bazasu duk bazawa ɗaya idan mutum ɗaya daga cikin su ya yi sai ya ɗago fatsarsa cike da kifi fiye da goma a ciki kafin wani lokaci tuni sun cika fatsar su da kifaye manya da ƙanana. Sarkin masintan ya umarci a da ayi gaggawar haɗa wuta, ba'a ɗauki lokaci ba aka haɗa wuta tare da ɗora wani babban kasko aka shiga hidimar soya kifayen manyan daga ciki kuma aka dinga gasawa, wasan ba ƙaramin ƙayatarwa yake ba dan haka mutanen garin idan bikin ya ƙarato kowa da irin shirin da yake yi. Basu jima ba aka kamalla wasan masinta tare da gama suyar kifi suma suka tattara kayansu suka bar wajen, fitar su babu jimawa Wanzamai suma suka shigo suka fara nuna tasu bajimtar. Ɗan sarkin wanzamai me kimanin shekara goma ya fito rataye da jakar wanzamai, yana zuwa ya dire ta a tsakiyar wajen ya juya ya gaida Sarki cikin girmamawa, daga cen ɓangaren Bafaden Sarki Aminullah ya amsa da. "Sarki ya amsa an gaishe ka Ɗan sarkin wazamai" Yaron juyawa ya yi yace. "A cikin ku akwai wanda yake buƙatar aski daga nan gurin da yake?" Kallon kallo suka fea yiwa juma aka rasa wanda zai amsa har sai da ya kuma maimatawa a karo na biyu sannan wani Matashin saurayi ya ɗaga hannunsa tare da cewa. "Ga ni" Yana rufe baki Yaron ya kalli Jakarsa ya yiwa aska magana kaman wanda yake wa mutum magana, yana gama mata magana Jakar ta buɗe da kanta aska ta fita bata tsya ko'ina ba sai wajen saurayin da ya yi magana. Kafin wani lokaci tuni ta aske kan matashin, wannan abin da yaron ya yi ba ƙaramin ƙayatar da Sarki da Aminansa ya yi ba harma da mutanen wajen. Sarkin Aska da kansa ne ya fito ya juya ya fara kallan mutanen gurin ɗaya bayan ɗaya sannan ya bada umarnin a kawo masa babban mazubi, da sauri wani bafade ya ɗauko masa babban bokiti yana kawo masa ya zauna a gaban bokitin ya fara kwara aman jini a ciki ya jima yana abu ɗaya sannan ya cika bokitin fal da jini, gabaɗaya mutanen guri zaro ido sukayi suna kallan abinda yake faruwa, miƙewa ya yi yace a ɗauke bokitin aje a zubar dashi a wani gurin. Yana tashi ya ɗauki jakar wanzanci ya ɗagata sama sannan ya fara wulwulawa yana ajiyeta da ya buɗe sai ga Jaririya ya yafito da ita tana ta mutsuniya a cikin tsumma a wannan lokacin gurin hautsinewa ya yi da hayaniyar jama'a, a hankali Sarkin Wazaman ya taka ya miƙawa wani Dogarin Sarki yace a kaiwa Sarki Aminullah Jaririyar. Duk wannan shagali da yake faruwa Fulani Zaliha da Salf na gida a zaune dan yadda ta ɗau zafi taci alwashin komai na masarautar ta daina shiga, shima Saif saboda rashin jansa a jiki da Sarki Aminulllah yake yi yasa ko kaɗan bai ma yi gigin fita gurin wasan al'adar ba. Haka daga ɓangaren su Inna Habi gabaɗaya bayin gidan suka yi zuga suka tafi filin wasan al'ada, babu kowa daga ita sai Abu banda kuka babu abin da Inna Habi take yi musamman idan ta tuna halin da Maryo take ciki, dan ma Abu na ɗan kwantar mata da hankali tana ɗan rage damuwar. A lokacin da ake tsaka da shagalin wasa Sarkin ƙira ne ya saci jiki ya wuce cen gidan Sarki, yana shiga yaci sa'a babu mutane sosai yawanci sai masu tsaron ƙofofi. Ganin suna ɗan kallansa yasa ya wuce ya shiga dube-duben gurin da zai samu faragabar binnewa ba tare da wani ya gansa ba. Sai da ya yi tafiya me ɗan nisa sannan ya samu wani guri fara haƙa sai da ya yi haƙa me zurfi sannan ya binne yashin. Yana gama binnewa ya fito da sauri ko waiwaye baya yi, Sarkin ƙira na gabda ƙarasowa gurin da ake gudanar da wasan Al'ada yaji wuyansa ya yi ɗaure kamar wanda aka rataye, hannu biyu yasa yana riƙe wuyansa saboda azaba ya durƙushe a gurin kafin wani lokaci rai ya yi halinsa. Saif na zaune da mahaifiyarsa suna hira yaji kansa ya sara masa da sauri ya dafe kan nasa yana rumtse ido, rufe idonsa keda wuya ya hange shi a wani makeken fili da alama nemen wani abu yake daga cen nesa ya hango wata mace riƙe a hannun wani namiji yana gudu da ita tana fisgewa, yana shirin bin su yaji ƙasar gurin ta fara zabtarewa nan take ya faɗa ciki ƙasar ta rufe da shi, cikin wata irin murya yake faɗin, "Rayzutaaaa, Zulik karka tafi da ita" Fulani Zaliha a tsorace take bin Saif da kallo ganin irin surutan da yake yi yasa ta fara karanta masa addu'a tana tofa masa, buɗe idanunsa sukayi da suka rine jawur Fulani Zaliha har sai da ta tsorata da ganin idanunsa, kallanta ya farayi muryarsa a dace yace. "Ammi wani mafarki nayi yanzu" ƙara zaro ido tayi jin abin da ya faɗa ita dai tasan da faruwar yanayin da ya shiga ko minti biyi baiyi ba, ace mutum ba bacci yayi ba ya yi mafarki. Amma sai ta basar ta ce. "Meye a mafarkin?" lumshe ido ya yi ya buɗe yace. "Wani ne ya tafi da wata amma sai nake ganin kamar tana da muhimmanci a gurina." Maryo da ke kwance a asibiti firgigit ta miƙe zaune kamar wacce aka jonawa wutar lantarki haka jikinta ya ɗauki wani irin shock, da sauri ta fisge robar ƙarin ruwan da ke hannunta ta diro daga kan gado ta nufi hanyar bakin ƙofa a guje. Da sauri wannan Dogari ya bi bayanta tare da sauran Dogarawan da ke zaune a gurin, Maryo wani irin gudu take kamar wacce zata tashi sama, basu suka samu nasarar kamata ba sai da suka jima suna tseren gudu a tsakaninsu, suna riƙeta ta fara fisge-fisge tana cewa. "Ku barni na tafi zai cutar da shi dan Allah ku ƙyaleni, Furzaaan wayyooo zai cutar mini da shi" sai da sukayi da gaske sannan suka samu suka iya kama Maryo suka wuce da ita ɗakinta, wanda har lokacin bata daina ƙoƙarin ƙwacewa ba. Suna shiga suka rufe ƙofar da key suna mayar da numfashi, wani irin hawaye ne yake zuba daga idanun Maryo tsugunnawa tayi kan gwiwowinta ta haɗa hannuwanta biyu murya a raunace ta ce. "Dan Allah kar kuyi mini haka wannan ita ce dama kusan ta ƙarshe karku bari na ƙara rasashi wannan karan bazan jure rashinsa ba, kuyi haƙuri ku dubi halin da zuciyata take ciki idan ban isa gareshi ba komai zai iya faruwa, banasan na cutar da ku domin kunyi mini hallaci ku buɗe min na fita." Ganin basu da alamun buɗewa yasa Maryo ta durƙushe a gurin ta rusa wani irin kuka me tsuma zuciya, dukda Dogarawan nan basu san dalilin kukanta ba amma kukan nata ya taɓa zuciyoyinsu. Suna nan tsaye suka ji likitan ya ƙaraso suna buɗe ƙofar ta zabura zata fita lokacin tuni hancinta ya fara zubda jini, da sauri suka kamata suka mayar da ita kan gado cikin shammata likitan ya sakar mata alluran bacci, babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita suna ganin haka suka kwantar da ita amma wani abun mamakin har tayi bacci hawayen idanunta basu daina tsiyaya ba, haka jinin da ke fita ta hancinta shima yana ci gaba da fita lokaci-lokaci tana sauke ajiyar zuciya. Likitan ne ya kalle ya kallesu cikin damuwa yace. "Yarinyar nan har yanzu tana cikin zafin ciwo gashi har tana surutai so gaskiya sai an sa ido sosai a kanta, zan turo nurses su gyarata." Dogarawan cikin ƙosawa suka gyaɗa masa kai, dan su har sun fara gajiya da ciwonta cikin kwana ɗaya yarinya ta hanasu sukuni gashi suna burin ganin bikin al'ada amma bisa umarnin Sarki akanta yasa suka kwana suka wuni a asibiti. Wasu matasan ƴan mata da ke zagaye da gadon Maryo wanda likitan da Dogarawan basa ganinsu suka ja gefe cikin yanayin damuwa, idanunsu ɗauke da hawaye suka russuna gaban Gadon Maryo cikin haɗin baki suna faɗin. "Fartu kibarsi wargakina umkasu jilbas, wargisu fisadu kijalbi mirzatu Zulik gurwatu bisanit kaljuwas fargista kalminfat wargas girbat?" (Tuba muke ya shugaba amma bamu so kika ƙi bamu dama ba, yanzu haka zamu sa ido akan Zulik wannan karanma ya yi nasara akanmu?) miƙewa sukayi suna hawaye suka fara binta kusurwar bango suna wucewa. TO FA MEYE HARSASHENKU NE KUNA KAN BAKARKU NA MARYO BAIWA CE? KU DUBA DAI DA KYAU ANYA BAIWA CE? 🤣🤣🤣🤣 YANZU FA SAI KUCE INA NEXT PAGE 🙄 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [02/11/2021, 18:30] Ameera Adam🌚: 20... Fulani Zaliha a ɗan tsorace ta kalli Saif ta ce. "Wai duk a yaushe haka ta faru?" Saif cikin halin ko'inkula yace. "Ammi a mafarkin nan da nayi yanzu" Fulani Zaliha ta rasa abin cewa dan gabaɗaya bata fuskanci inda maganar Saif ta dosa ba, ya za'ace mutum daga dafe kai ko minti biyu baiyi ba amma har ya yi mafarki alhalin ba bacci yake ba, cikin zuciyarta take faɗin. "Allah ka dubeni ni da yaron nan bamu da gata bayan naka, Allah kasa ba wata matsalar bace take tunkaro yaron nan Allah ka jiɓanci lamarinmu" a fili ta kalli Saif ta ce. "Saif ka dage da Addu'a insha Allah babu abin da zai faru sai alheri." Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya amsa mata da baki yana dafe kai har lokacin kansa bai daina juya masa ba. Sarki Aminullah karɓar Jaririyar ya yi yana murmushj yana yabawa da wasannin da suke gudanarwa, ƙare mata kallo ya yi sannan ya karanta addu'a ya tofa mata tare da fatan Allah ya albarkaci rayuwarta, miƙawa Aminansa ya yi suma suka yi mata addu'a sannan aka miƙawa Dogarin ya ƙarasa ya miƙawa Sarkin Wanzamai ita, yana karɓarta ta buɗe cikin jakarsa ya zurata tare da riƙe hannun jakar ya kuma wulwulawa yana gamawa da ya ɗaga jakar ya zazzageta a idon mutane, ba ƙaramin mamakin wannan siddabarun nasa suka yi ba kuma abin ya ƙayatar matuƙa, Maƙera na fita sai maharba suka shigo suma suka gudanar da nasu wasannin gwanin birgewa kamar yadda yake bisa ga al'ada duk shekara, daga maharba sai Ƴan bori suma haka suka fito suka dinga wasanninsu da rawaye-rawayensu bayan fitar su babu jimawa mawaƙa da maroƙa suka shiga suka fara baje kolin tasu bajintar. Ana tsaka da shagali mutuwar Sarkin ƙira ta ƙarasa gurin wasan Al'ada ba ƙaramin kaɗuwa mutane sukayi ba saboda a yadda wasu suke faɗa ko awa guda basuyi ba da ganinsa a gefen fili ba amma ace ya mutu, wasu daga ciki muatane kuma musawa sukayi sai da aka hangi gawar Sarkin ƙira sannan suka yarda, ƴan uwansa Maƙera ba ƙaramin ƙaɗuwa sukayi da rasuwar shugabansu ba. A gurguje aka fara haramar tashi saboda mutuwar Sarkin ƙira ga kuma yamma ta fara yi, Gayyato Sabon Bawa aka ƙarayi domin a ji buƙatar da buƙata agurin Sarki Aminullah. Kamar wancen karon yana sanye da wandon ƙarfe haka ya shigo filin fuskarsa ɗauke da murmushi, yana shigowa cikin filin Salman da ke gefen Sarki Aminullah ya runtse idanu yana jin wani irin yaammm a jikinsa, kamar wancen karon nasa na farko da ya shiga filin gurin wannan karanma haka yaji, yana daga zaune yaji kamar ana fisgarsa duk yadda yaso ya dakatar da wannan yanayin ya faskara, daga cikin filin Dogarin ne ya fara tambayar Sabon bawan sunansa. Ɗagowa ya yi ya kalli sashen da Salman yake nan ya saki wani shu'umin murmushi sannan yace. "Suna nan Zulik" da sauri Dogarin ya kalleshi ganin yanayin kallon da Dogarin ya yi masa yasa ya fahimci suɓutar bakin da ya yi da sauri yace. "A garinmu sunan da ake kirana da shi kenan" Salman da ke gefe tun da ya kifa kansa a jikin kujera bai ƙara sanin abin da yake faruwa ba" Sabon Bawan ya saci kallan Sarki Aminullah ya ci gaba da cewa. "Amma sunana na ainihi Sulaiman" Dogari ya jinjina kai cin shela ya ce masa. "Sarki ya ji ka yanzu sai faɗi buƙatarka" Zulik ya sunkuyar da kai ya yi yace. "Akwai wata yarinya da naji ta aikata laifi ita nake san Mai Martaba ya fito da ita kuma ya wanketa daga laifin da ake zarginta da shi, saboda tayi ƙanƙanta da a yanke mata hukunci amma ayi mini afuwa idan maganata tayi tsauri" Gabaɗaya ido aka zubawa Zulik, gurin shiru ya ɗauka kowa ya kasa kunne yana jiran jin maganar da zata fito daga bakin Sarki Aminullah, shi kansa Sarki sai da maganar ta ratsa sassan jikinsa saboda bai taɓa tsammanin akwai wani Bawa da zai taɓa tunkararasa da wannan maganar ba, cikin zuciyarsa yake faɗin. "Amma wannan koma waye zan nemeshi a sirrance dan jin abin da yasa shi neman wannan buƙatar, bayan kowa yasan gabaɗaya Bayin da ke shiga suna shiga gasar ne dan neman suna, dukiya ko sarauta." sai da ya saita nutsuwarsa sannan ya buɗe baki a hankali dan na nesa da su bazai taɓa fahimtar abin da ya faɗa ba. Dogarin da ke cen gefensa ya miƙe ya fara zuba banbaɗanci. "Sikari bakai farin banza ba. Madafar bayi masu iyayenma kun gama musu komai, Allah ya taimakeka ya ƙara nisan kwana Hadari kake mai sauke dubun albarkai. Allah ya ja da zamaninka ɗan toron giwa sarkin Musulunci da Musulmai takawarka lafiya Madara mai farin gado..." Haka bafaden nan ya dinga bambaɗanci sannan daga ƙarshe yace. "Yaro ka kawo kuka gurin da za'a share maka hawayenka indai wannan ce damuwar duniya da lahira ta kau sai dai wata ba wannan Adalin Sarki Mai tausayin talakawansa ya amince da buƙatarka" Gabaɗaya gurin ya ɗau hanayaniya wasu daga ciki suna ganin sakarci da wawtarsa ace ka samu dama kamar wannan amma ace wai ka tsaya akan ceton wata Baiwa daban, wasu kuma na ganin taimako ya yi waɗanda suka yarda Maryo bazata iya aikata abin da ake zarginta ba, Har ila yau wasu daga cikin mutanen gani suke kamar da wata a ƙasa dan gani suke kamar bakinsu ɗaya tsakaninsa da Maryo. Zulik russunawa ya yi cikin girmamawa yace. "Godiya nake Allah ƙara girma da tsawoncin kwana" Bafaden da ya yi shela da farko yace. "Allah ya taimakeka yaro ya yi godiya ya daɗa ya yi godiya ga wannan karamcin da akayi masa." Sarki Aminullah da har lokacin idanunsa na kan Zulik ya gyaɗa kai. Bafaden yace. "Sarki ya amsa maka Yaro" Daga haka suka fice daga gurin. Bayan fitarsu babu daɗewa Salman ya buɗe idanunsa da suka rune jawur yana dafa kansa da yake sara masa, bin gurin da mutanen da ke zaune yake da kallo sannan ya fara jin waɗansu irin surutai a cikin kunnuwansa. Daga haka Sarki Aminullah ya yi jawabi ga jama'ar gari da faɗakarwa sannan wasu daga cikin Manyan baƙi suma suka yi nasu ƙarin hasken sannan aka tashi daga wasan gwanin birgewa, bayan tafiyar Mai martaba da manyan baƙinsa gida matasa suka fara wasan tseren doki a tsakaninsu. Inna Habi ita da Abu suna zaune sauran Bayi suka rinƙa shiga ɗaya bayan ɗaya, tun basu gama shiga ba akayi mata albishir da roƙon da Zulik ya yi, Inna Habi saboda murna har da kukanta, farin cikinta yaƙi musaltuwa, haka taci alwashin neman yaron da yayi wannan taimakon dan tayi masa godiya. Jakadiya baƙin ciki ƙunshe cikin zuciyarta ta wuce sashen Fulani Maryama, tana zuwa suka fara Jajantawa juna bisa amincewar da Sarki Aminullah ya yi. Da daddare Dogarawan da ke tsaye a kan Maryo suna nan zaune suka ji bugun ƙofa suna buɗewa suka ga Uwar Bayi ce da wata baiwa biye da ita. Hamdala suka yi a fili saboda sun san ko ba komai Uwar Bayi zata fanshe su wannan zaman jigum-jigum ɗin da suke yi. Uwar bayi kallansu ta yi bayan sun gaisa ta ce. "Takawa ya turo mu akan mu ci gaba da kula da ita har zuwa lokacin da za'a sallameta." Babban Dogarin yace. "Gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba bari mu zo mu wuce sai ku ɗora daga inda muka tsaya" Uwar Bayi mugun kallo ta watsawa Maryo da ke kwance tana sauke numfashi sama-sama, lokaci-lokaci take jan guntun tsaki tana hararata. Bayan tafiyar Dogarawan Sarki kamar daga sama aka jeho shi haka suka ga ya faɗo ɗakin ko wadatacciyar sallama babu a bakinsa, Uwar bayi a hassale ta kalleshi ta ce. "Kai yaro lafiyarka ka shigo mana saƙaƙa kamar wanda ya halarci taron kafirai?" Zulik bai bi ta kanta ba ya ƙarasa bakin gadon da Maryo take kwance ya tsugunna akan gwiwoyinsa fuskarsa saitin fuskarta ya fara shafawa. Uwar Bayi salati ta rafka tana tafa hannuwa tace. "Kai jama'a yau me nake gani a ido na garnaƙeƙen ƙato ya faɗo mana ɗaki zai aikata cin mutumci a kan yarinya" Wannan karanma bai tanka mata ba ya ci gaba da shafa fuskarta sannan ya kamo hannunta yana ƙoƙarin cire zobon hannunta, kamar wacce aka zubawa wuta haka ta buɗe idonta a gigice. Uwar Bayi miƙewa tsaye tayi tana cewa. "Wallahi ba zan zauna ana alfasha a idanuna ba Allah ya kamani ba gwara na kira hukumar asibiti su san halin da ake ciki ba, dan wannan sai ya ja mana girgizar ƙasa..." ɗagowa ya yi a fusace cikin wata irin murya yace. "Idan na kuma jin bakinki sai na murɗe wuyanki fuskarki ta koma baya" Uwar Bayi har lokacin bakinta bai mutu ba ta ce. "Kai Yaro dube ni nan tun kafin a haifi uwar me sabulu balbela take da farinta babu wani buɗe ido da zaka nuna mini, bar ganin kaci gasar maƙera..." kafin ta ƙarasa magana taga ya ɗora hannuwansa biyu akansa ya fara wana kansa kamar yadda ake wana tayar keke, daga Uwar Bayi har baiwar da suke tare cen ƙuyar ɗakin suka maƙale tare da ƙanƙame juna, Uwar Bayi harda sakin fitsari daga gurin da take. Cikin muryarsa mara daɗin saurare yace. "Wannan ƙaramin aikina ne na mayar da gabanki ya koma bayanki dan haka ki kiyaye..." Shima bai rufe bakinsa ba Maryo ta ɗauke shi da mari, kamar koyaushe duk lokacin da zata fuskanci wani yanayi yanzun ma hakance ta faru, jinin da ke ɗiga daga hancinta ya fara ɗiga a hankali. Sunkuyar da kansa ƙasa ya yi yana jiran yaji wani hukuncin nata da zai biyo baya amma sai ya ji shiru, idanunta ne suke ci gaba da rinewa ga wata irin ajiyar zuciya da take saukewa. Jin ta yi shiru ya sa ya ɗago yana kallonta hawaye ya gani kwance cikin idanuwanta yana shirin magana yaga tahowar hawayenta kafin ya ɗiga ya sa hannu, yana ɗiga ya kaishi bakinsa ya lashe. Runtse idanunta tayi ba tare da ta buɗe su ba ta ce. "Me ka yiwa Furzaaan" guntun tsaki ya ja yace. "Wato har yau bazaki daina zance wancen sakaran ba ko?" tun kafin ya ƙarasa maganarsa ta buɗe idanunta ta ɗorasu akanshi, da hannuwanta biyu ta shaƙo wuyansa tana jijjigashi ta ce. "Tambayarka nake me ka yiwa Furzaaan? Wallahi muddin wani abu ya faru da shi zaka yi mamakin hukuncin da ɗauka a kanka" Dariya ya farayi sama-sama sai kuma ya ci gaba da ƙyaƙyacewa da dariya sannan ya tsuke fuska yace. "Na ji na yarda duk abin da zakiyi ki aikata shi amma ki sani ke da Furzaaan har abada dan a yanzu kin yi gabas ya yi arewa, ammma idan kina ganin ƙarya ne bisimillah" Maryo runtse idonta tayi dan tabbas tasan Zulik ya faɗa ne amma Furzaaan bazai taɓa juya mata baya ba, kallansa tayi da idanunta da suka rine jawur ta ce. "Wani abun ka aikata masa?" Dariya ya yi ya kamo hannunta da sauri ta fusge tana tofa masa yawu a fuska, cikin rashin damuwa da abin da tayi masa yace. "Idan kina tantama ki cire zoben hannunki ki bani zan fayyace miki komai" Wani kallo ta wurga masa tace. "Kai ɗin? Kana tunanin akwai wata yarda da zan kuma baka kana tsammanin zan ƙara amincewa da ƙasƙantacce, makiri annamimi kuma azzalumi kamar kai? Sam har abada wannan kuskuren bazan ƙara aikatashi ba ka riƙe bayananka bana buƙata kuma ka fice mini dan bana ƙara muradin ganinka." tana zuwa nan a maganar ka ta rushe da wani irin matsanancin kuka, fuskar wani Dattijo ce take mata yawo a cikin ƙwayar idonta dan haka kukanta ya tsananta harda shassheka. Uwar bayi ita da Baiwa suka gefe banda Idanu babu abin da suka zura musu kamar waɗanda suke kallon wata dirama ko wasan kwaikwayo. Zulik runtse idanunsa ya yi yace. "Banasan kina damuwa akan waccen mara amfanin babu wani abu da zai amfane ki da shi bansan wacce tsiyar ce a jikinsa ba, amma tun da haka kike ganin ya fi miki shikenan idan mutuwa zakiyi saboda kuka wallahi mutuwa ita zata rabamu, keda Furzaaan sai kallo dan babu ke a shafin rayuwarsa." Maganganunsa jinsu taje kamar saukar aradau kukanta ne ya tsananta gwanin ban tausayi. Daga kusurwar bango ƴanmatan nan ne suka ƙara fitowa yanayinsu ɗauke da damuwa suna jifan Zulik da mugun kallo. Biyu daga cikinsu ne suka yo gaba ɗaya ta zagaya ta gefen hagunta ɗaya ta zagaya ta gefen damanta, dafata sukayi cikin lallashi suna lallashinta. "Shugaba kukanki yana nuna masa alamaun gazawarki wanda haka sam baya mana daɗi, dan Allah ki bamu dama ko da sau ɗaya ne mu wanke wannan hawayen naki da yake kwaranya." suka faɗa lokacin da suma hawaye ke fita a idonsu. Goge hawayenta Maryo tayi ta ce. "Baku san waye Zulik ba Fitya nina san wanene shi. Haka zalika wannan ba yaƙin ku bane dan babu tantama idan kuka saka kanku a ciki yana iya nakasta ku. Fitya idan na rasaku bayan Furzaaan da wa zanyi rayuwa?" Jinjina kai suka yi suna share mata hawaye sannan ta koma ta kwanta tana lumshe idonta. Duk wannan budurin da ake yi uwar bayi da Baiwa Salma suna tsaye suna kallon ikon Allah, tsoro da mamaki ne ya kamasu ganin yadda Maryo ke ta magangu ita kaɗai tana ambatar Fitya dan sun lura kamar da wata take magana ba Sabon bawa ba. Zulik taɓe baki ya yi ya kalli Maryo yace. "Rayzuta tun ina binki ta lallami kar mu kaiga yadda mukayi a wancen karan, abin da baki sani ba wallahi Furzaaan ba naki bane kuma akan idonki zai nemi matar aure ya aura gwarama ki samawa ranki salama." Yana gama faɗa ya juya ya fice ko waiwayenta baya yi. A firgice ta ɗago tana kallon bayansa gabaɗaya tsoro yake bata saboda tasan waye Zulik, tasan wannan iƙirarin da yake ba a banza ba" hawaye ne suka ci gaba da kwarara a idonta. Kamar wacce ta tuna wani abu ta juya ta kalli ɗaya daga cikin ƴanmatan tace. "Hikbiyat Maza kije gurin Abu ko Inna Habi inasan sanin abinda yake faruwa game da Furzaaan, ki hanzarta banasan a samu matsala." Uwar bayi kallan juna suka yi da suka ga Maryo na aike alhalin ita kaɗai ce kwance akan gadon, dan su tsoron ƙarasawa gurinta suke yadda suka ji tana surutai ba fasali. MU HAƊE A COMMENT💃🏻 BA NEXT PG WLH WUTAR TA LALACE _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [03/11/2021, 16:02] Ameera Adam🌚: 21... Maryo na ganin wucewar Hikbiyat ta kuma runtse idonta tana jin zuciyarta na wani irin suya. Daga gefenta ƴan matan ne suka russuna cikin girmamawa suka ce. Hutawarki lafiya Shugaba" bata buɗe idonta ba ta gyaɗa musu kai sannan suka bi ta gurin da suka fito suka wuce. Uwar Bayi suna nan daskare jikin bango sai zare ido suke kamar shege a rabon gado, ganin kamar Maryo ta fara bacci yasa suka saki juna suna tafiya saɗaf-saɗaf a hankali suka buɗe ƙofar suka fice harabar asibitin. Uwar bayi ido duk ya yi zuru-zuru ta kalli Baiwa Salma ta ce. "Ke Salame lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro fa anya ciwon nan nata babu bugun iska a ciki kuwa?" Baiwa Salma ta riƙe haɓa ta ce. "Nikam waccen mutumin da ya fita shi yafi ɗaga mini hankali, Uwar bayi dubi yadda yake wana kansa kamar kan babyn roba gaskiya nikam na gama tsorata da shi ai dole dama yaci gasar ƙira." Uwar Bayi ta ce. "Ke siddabaru ne fa kawai ina ce a gabanki sarkin wanzamai ya fiddo jaririya daga cikin jaka, kinga zancen da ake yi ya tabbata ko dama ni nasan ruwa baya tsami banza, ashe kuwa budurwarsa ce shiyasa ya shiga wannan gasar dan ya fitar da ita. Amma kuma fa kamar bulayi ne kawai yake yi dan na lura kamar bata san shi.?" Baiwa Salma ta ce. "Uwar bayi mu bar maganar danni na gama tsorata da lamarin mutumin nan kar muje ko yana laɓe yana jinmu." Uwar bayi shiru ta yi dan ita kanta har zuwa lokacin a tsorace take da lamarin Sabon bawan. Daga cen gidan Sarki abin ciccika kala-kala aka girgirka na al'ada gidan cike yake da mutane da sauran baƙin da ba a ranar zasu wuce ba. Inna Habi tun da aka sanar da ita hukuncin Sarki Aminullah taji ta garau sai ma ta saki jikinta ita da Abu aka ci gaba da shagalin bikin al'ada dasu a cikin gida. Gabannin magriba Inna Habi da kanta ta taka gurin Jakadiya bayan sun gaisa, Jakadiya take kallon Inna Habi a watse. Ita kuwa bata lura da irin kallon da take mata ba yasa Inna Habi ta ce. "Jakadiya dama zuwa nayi naji ko da wanda yasan ɓangaren da Maryo take kwance naji ana raɗe-raɗin wai Uwar bayi na gurinta, shi ne nazo dan naji ko wata tasan gurin da take" Jakadiya ɗage hanci gefe ɗaya ta yi sheƙeƙe ta kalli Inna Habi ta ce. "Habi Kya tambayi kaza hanyar rafi ki tambayi agwagwa kisha labari, ni zane na fiku da zan fiku sanin ɓangaren da Maryo take? Duk fa tare muke da ku a cikin gidan to hana rantsuwa dai na je filin wasan al'ada ke baki je ba banda nan ina na leƙa? Ki tambayi wasu ƴaƴan masanan ko sun sani amma ba ni ba jikar Hudu" Inna Habi bata ji daɗi ba sam a sanyaye ta miƙe tana kallan Jakadiya ta ce. "Allah ya baki haƙuri Jakadiya" Ai kuwa kamar ta watsawa Jakadiya ruwan zafi a zafafe ta ce. "Ki dai bawa kanku haƙuri Habi ku dai kuke cikin bala'i banda ma Allah ya fitar da ku amma bansan tsiyar da zaku samu ba idan Maryo ta kashe Takawa, kinsan dai har abada ba karagar Mulki ba ko sarautar Sarkin Dogarai bazaku samu ba." Inna Habi idanunta ne suka ci ko da ƙwalla zata fara tafiya wata matashiyar Baiwa ta ƙaraso gurin jikinta sanye da kayan bayi, kusan gware sukayi da Inna Habi da sauri matashiyar budurwa ta ce. "Wayyo sannu Inna ban sani bane." Inna Habi ta ce. "Ba komai yarinya" Jakadiya dake gefe ta ce. "Ina zaki lura yara sai tsinannaniyar rawar ya na balagaggen ƙadangare" daga Inna Habi har Baiwar babu wanda yabi ta kan Jakadiya. Inna Habi har tayi nisa Baiwar ta bi bayanta ta ce. "Inna naji kamar tambayar gurin da Maryo take kike yi ko?" Inna Habi ta ce. "Eh yarinya" Baiwar ta ce. "Ɗazu naje gurin idan kina so sai na raka ki" kafin Inna Habi ta bata amsa Abu ta ƙaraso gurin da mamaki take bin Baiwar da kallo dan sam bata santa a cikin gidan ba, Inna Habi ta ce. "Na gode kuwa yarinya amma kamar ban waye ki ba" Abu tayi karaf ta ce. "Gaskiya nima a cikin gidan nan bansan ta ba ko kuma baƙuwa ce?" Baiwar murmushi tayi ta ce. "Eh baƙuwa ce sunana Hikbiyat" Inna Habi da Abu suka kalli juna suna maimaita sunan cikin haɗin baki. Basarwa tayi ta ce. "Yanzu zan kai saƙon fulani Zaliha na dawo idan nazo sai mu tafi." Inna Habi ta amsa tana godiya sannan Hikbiyat ta wuce. Abu da mamaki ta ce. "Inna ina zaku je kuma?" Inna Habi ta ce. "Rakamu za ta yi Asibiti gurin Maryo" Abu washe baki tayi ta ce. "Kai amma naji daɗi wallahi, Allah sarki Maryo ko a wane hali take" nan take tausayin ƴar uwar tata ya kamata har idanunta suka ciko da ƙwalla. Hikbiyat na shiga sashen Fulani Zaliha ta faɗa ɗakin Saif a lokacin yana zaune yana shan fruit hankali kwance, har ta shiga ɗakin ta gama tsayuwarta bai san da wani mai numfashi a gurin ba, ta jima a tsaye a kansa sannan ta juyo ta fice. Bata jima ba ta ƙarasa cen sashen Bayi ta yi wa su Inna Habi magana. Irin kallon da yawancin mutanen gurin suke binta da shi yasa ta fara shan jinin jikinta, a gurguje ta nemi su Inna Habi da su fito ta yi musu rakiyar dan batasan ko kaɗan a samu matsala. Suna fitowa suka nufi asibitin da yake daga gidan Sarki zuwa asibitin Murtala babu nisa da ƙafa suka tafi suna tafe suna hira, Hikbiyat haka ta saki jiki da su kamar wacce ta shekara ɗari da su, a cikin hirar ne ta fara bugar cikinsu akan lamarin Saif basu wani bata amsa yadda take buƙata ba saboda basa shiga ɓangaren Matan Sarki idan ba da wani ginshiƙin abu ba.Suna Ƙarasawa asibitin tuni anyi sallar magriba a gefen ƙofar shiga ɗakin suka samu su Uwar Bayi suna sallah, Hikbiyat ce ta fara ƙoƙarin shiga ɗakin wani securitie ya taso yana mata magana domin a wannan lokacin ba lokacin ziyartar marasa lafiya bane. Kwantar da murya ta yi cikin roƙo ta ce. "Dan Allah ka taimaka wannan mahaifiyarta ce tun da aka kawota asibiti bata samu ganinta ba" Tamke fuska ya yi yace. "Ke banasan sakarci ai kun san doka ce ko Malama ku zo ku wuce." Hikbiyat fakar idonsu Inna Habi tayi ta hura masa iska a fuska, Kamar wanda aka matsawa remove haka ya juya ko kalma ɗaya bai ƙara furtawa ba.Ta juya ta kalli su Inna Habi ta ce. "Inna kuzo mu shiga." A dai-dai lokacin su Uwar bayi suka idar da sallar, da fara'arta ta fara yiwa su Inna Habi sannu da zuwa saboda dama tun tuni suke fargabar shiga gurin Maryo dan basu san abin da zasu gano ba." Gabaɗaya suka ɗunguma suka shiga Hikbiyat na gaba suna biye da ita a baya. Uwar bayi da mamaki ta kallo Hikbiyat ta ce. "Yarimya ke kuma wacece dan ban wayeki ba" Hikibiyat bata waiwaya ba tace. "Dama ba lallai ki waye ni ba dan ba zamanki nake yi ba." A hassale Uwar Bayi ta ce. "Ke yarinya karki nuna mini tsageranci dan wallahi tsaf nayi jika da ke" babu wanda ya tankawa Uwar Bayi ita dai Inna Habi babban burinta ta shiga ta gano halin da Maryo take ciki. Shigar su ɗakin daga cen nesa da su kan sauran gadajen, waɗansu marasa lafiya ne guda huɗu, sai da Inna Habi ta yi musu ya jiki sannan suka wuce gadon Maryo. Tana kwance idanunta a lumshe kamar me bacci, kana kallanta zaka fahimci zallar ramar da tayi ta rame sosai ta yi wani haske daga wuyanta sai ƙasusuwa.Suna zuwa da sauri Abu da Inna Habi suna rungume ta Inna Habi harda ƙwallarta, a hankali ta buɗe idanunta ta sauke su akan Hikbiyat da ke tsaye tana kallonsu cikin tausaya saboda irin soyayyar da suke nunawa Shugabarsu. Inna Habi ce ta ɗago ta kalli fuskar Maryo zata yi magana Maryo ta rigata. "Inna yaushe kuka zo?" Abu ta turo baki cikin zolaya ta ce. "Au Inna kiɗai kika gani baki ganni ba ko? Lallai Maryo ba amana a tsakaninmu bari na tafi kya nemi wata ƴar uwar ba ni ba" Maryo ɗaga kai tayi ta kallo Abu cikin so da ƙauna ta ce. "Ni na isa wallahi sharrinki ne kawai Abu amma kinsan ko cikin dabbobi Zaki shine sarki dan haka Inna cen kan gaba kafin ke" Uwar bayi ido ta zura mata tana mamakin yadda ta ga Maryo ta ware tana maganar masu hankali, Inna Habi ta ce. "Maryo ya jikin naki" Maryo ta ce. "Da sauƙi Inna amma kaina na yawan ciwo kuma wallahi ina yawan jin tsoro" Inna Habi ta ce. "Ki daina jin tsoro kinji ƴata insha Allah babu abin da zai faru sai alheri." Maryo idonta ne ya ciko da ƙwallah ta ce. "Inna kuma kun yarda zan iya cutar da Sarki, wallahi ni bansan komai ba aike na fa kawai Fulani Maryama tayi ta yaya zan iya cutar da Mahaifina" Inna Habi ta ce. "Dai-dai da ƙwayar zarrah ban taba gasgata maganar ba saboda nasan irin tarbiyyar da na baku tun kuna ƙanana, Allah ya dubi lamarinmu ya ga baki da haƙƙi a ciki tun da Allah ya kuɓuto da ke. Wani bawa ne yayi gasar ƙira a ƙarƙashin buƙatarsa shine yace a fito da ke." Maryo ta runtse ido ta ce. "Inna ko da bai fito da ni ba nasan zan fito kuma dan Allah karku kasankance da shi." Inna Habi bata bi ta kan zancen Maryo ba dan ta mata uzurin wasu maganganun nata ko harda zafin ciwo. Abu da ke gefe ta ce. "Amma Maryo gaskiya idan aka sallamo ki sai kin yi taka tsantsan saboda mugu baida kama." Maryo ta ce."Haka ne Abu amma bansan ribar da zasu samu a kaina ba, bayan ni ɗinma jinin masarautar ce" Inna Habi ganin ba su kaɗai ne a gurin ba yasa ta ce. "Ba komai Maryo Allah dai ya kyauta ya kuma kiyaye gaba." Maryo ɗagowa tayi ta kalli Hikbiyat ta ce. "Ya ake ciki ne" Hikbiyat russunawa tayi ta ce. "Shugaba babu wani abu me muni da ya faru yana cikin ƙoshin lafiya" Maryo wani malalacin murmushi ta saki ta ya bawa su Inna mamaki, da mamaki Inna Habi ta ce. "Maryo dama kinsan yarinyar nan ne?" Maryo ta ce. "Na santa Inna Baiwata ce" Cikin haɗin baki gabaɗaya mutanen gurin suka furta. "Baiwarki" Cikin rashin damuwa da yanayin da suke ciki ta ce. "Eh" Uwar bayi kuwa ta ce da wa Allah ya haɗa ta inba da Maryo ba. "Yau naga faɗin rai irin na talaka kina baiwa har ki dinga ƙafafar kina da baiwa, kai Allah wadaran naka ya lalace ashe shiyasa kike yunƙurin hallaka Takawa..." Wani mugun kallo Maryo ta wurgawa Uwar bayi tun bata ƙarasa maganarta ba taja bakinta ta tsuke. Inna Habi ta dafa kafaɗar Maryo ta ce. "Maryo dan Allah ki dinga kiyayewa, mu zamu wuce kar dare ya yi mana Allah ya baki lafiya." Maryo ta ruƙo hannun Inna Habi ta ce. "Inna wallahi na gaji da zaman gurin nan" Abu ta ce. "Insha Allah kwana kusa za'a sallame ki kinji." Idanunta ne suka ciko da kwalla Inna Habi na ganin haka ta kauda kanta gefe ta miƙe ta yi mata sallama Abu ma sallama ta yi mata har zata tafi Maryo ta ruƙo hannunta ta ce. "Maryo har yau bai zo ya duba ni ba alhalin yasan harda nauyinsa nake tafe, da shi nake kwana nake tashi bansan a wane hali yake ba." Abu sunkuyowa tayi dan kar sauran mutanen su fahimci inda zancen su ya dosa ta ce. "Wa kenan wai kina nufin Saif?" da sauri Maryo ta ce. "Eh shi bai zo gurina ba Abu, dan Allah idan kun koma kije ki sanar da shi halin da nake ciki wataƙila bai sani ba" Wani kallo Abu take mata na lallai baki da hankali sannan ta ce. "Maryo kanki ɗaya kuwa? Kinsan dai kowa yasan zarginki ake akan ƙoƙari kisan Mai Marataba, wai kin manta Saif ɗan Sarki Aminulla ne? Me yasa kike so ki yaudari kanki da soyayyar wanda ba lallai ma yasan kina yi ba?" Maryo idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce. "Ki daina faɗin haka Abu wallahi masoyina ne ki duba zoben da ya bani fa, wani abu da baki sani ba ina ɗauke da junan biyun shi ta yaya zaki ce baisan da ni ba?" Zaro idanu Abu tayi har tana ƙwarewa da wani irin wahallalen yawun da ta haɗiya, Dai-dai lokacin Inna Habi ta ƙaraso jikinta har tsuma yake saboda jin abin da Maryo ta faɗa. Uwar bayi da suka kai baki ƙofa a hassale ta ce. "Habi nifa banasan a dinga kwan gaba kwan baya ko inbarki ke zaki ƙarasa jinyar ta" Inna Habi bata saurari Uwar Bayi ba tayi ƙasa da murya ta ce. "Maryo me bakinki yake faɗa?" A firgice Maryo ta ɗago ta fara kame-kame dan bata yi tsammanin bayan Abu ba wani zai ji wannan maganar ba. Sunkuyar da kai ƙasa Maryo tayi ta ce. "Ki gafarce ni Inna amma munyi alƙwarin aure da shi..." kafin ta rufe baki tuni Inna Habi ta ɗauke ta da wani gigitaccen mari. Da sauri Hikbiyat ta taso cikin tsawa Maryo ta dakatar da ita. Hawaye bibbiyu ne ke sauka akan fuskar Maryo haka daga ɓangaren Inna Habi da Abu. Abu cikin kuka ta ce."Maryo me yasa? Me yasa zaki yarda da zaƙin bakin namiji me yasa kike ƙoƙarin kai kanki inda Allah bai kaiki ba ina ke ina Ɗan sarki? Kar dai ace abin duniya ya fara rufe miki ido?" Maryo banda hawaye babu abin da take yi Inna cikin fushi ta juya ta fice zuciyarta na ƙuna. Tana fita harabar asibitin ta ga Uwar Bayi a tsaye da wani mai fararen kaya da alama likita ne, Uwar bayi na hango Inna Habi ta ce. "Zo zo zo Habi dama likita ne yace zai mini bayanin abubuwan da ƴarki zata dinga ci, tun da yace dole cimarta ta yanzu ta sauya wataƙila zaki iya jurar siya tunda naji yace harda ganyaryaki da sauransu." Gaban Inna Habi ne ya faɗi ta ƙarasa gurin Likitan kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki. WOLLAH SARKI AMINULLAH SAI YA KARƁIN JIKA ƊA A GURIN BAIWARSA TABBAS AKWAI ƘURA 🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️ _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [04/11/2021, 18:37] Ameera Adam🌚: 22... Likitan ya juya akalar tsayuwarsa zuwa fuskantar Inna Habi yace. "Sannu Inna" Inna Habi ta saki yaƙe wanda yafi kuka ciwo ta ce. "Yauwa Likita ya masu jiki?" Likitan yace. "Da sauƙi! Dama wani ɗan bayani ne zan ƙara muku dangane da abubuwan da ya kamata yarinyarku ta dinga ci saboda yanayin jikinta" Inna gyaɗa masa kai tayi ya ci gaba da cewa. "Tana buƙatar abinci masu gina jiki da ƙarin jini saboda yanayinta ya matuƙar bamu tsoro danma Allah yasa anshawo kan matsalar da tuni wani zancen ake ba wannan ba" Likitan ya jima ya yiwa Inna Habi bayani daga ƙarshe ya yi musu sallama sannan ya wuce ofis ɗinsa. Jiki babu ƙwari Inna Habi ta yiwa Uwar Bayi sallama sannan suka wuce gida ita da Abu zuciyarta cike da saƙe-saƙe iri-iri. Washegari gidan Sarki ya roraye yawancin baƙinsa kowa ya koma garinsa. Sarki Aminullah yana cikin Fada a zaune Fadawansa na gefe waɗanda suka haɗa da Ciroma, Galadima da su Wambai harda su Waziri. Cikin girmamawa Ciroma yace. "Allah ya taimake ka mun aika akira yaron yana tafe." Sarki Aminullah ya amsa cikin izza irin ta jiƙaƙƙun jinin sarauta." Ana cikin haka Zulik ya shigo fadar jikinsa sanye da kayan Bayi, daga cen gefe ya zauna ya gaishe da Mai Martaba cikin ladabi. Sarki Aminullah yace. "Yaro wasu ƴan tambayoyi zamu yi maka muna fatan zaka bamu haɗin kai." Zulik ya amsa yana me russunar da kai ƙasa. Sarki Aminullah yace. "Burin duk wani jarumi na gidan nan yaci wannan gasa saboda ya samu sukunin dukiya daga garemu, amma wani abun mamaki sai gashi kai ka samu damar amma ka ɓige da nemawa waccen yarinyar mafita ko meye dalilinka? A binciken da akayi mana an tabbatar mana da babu wanda take tsayawa da shi da sunan saurayi bare mu ce ko kai saurayinta ne, hasali ma an sanar da mu cewar a ranar da ka fito wannan gasar a ranar ne aka fara ganinka a cikin gidan nan, meye gaskiyar lamari shin meye alaƙar dake tsakaninku?" Zulik yace. "Allah ya taimake ka duk abin da ka faɗa haka ne, amma ni na taimake ta ne ba dan komai ba sai saboda Allah tunda na sami labarinta nake ji a jikina yarinyar bazata iya aikata abin da ake zarginta ba, sai dai idan maƙarƙashiya aka ƙulla mata, Allah ya baka yawan rai ka duba lamarin sosai kai ne Ubanta Mahaifi kada yankewa ƴarka hukunci daga baya abin ya dame ka" Duka mutanen Fadar ido suka zuba masa suka kallo hatta Mai martaba ido ya ƙura masa sosai yana auna maganar da ya faɗa yana ɗora ta a mizani, numfasawa Sarki Aminullah ya yi bai wani ɗauki maganar Zulik da wata manufa ba saboda yawanci haka bayin suke faɗa masa shine Uba kuma Mahaifinsu mai share musu kuka, jinjina kai ya yi yace. "Haka ne! Magana ai ta ƙare sai fai zamu sa masu leƙen asiri au lalubo mana gaskiyar lamarin. Daga haka aka sallami Zulik ya fice. Bayan fitarsa Sarki Aminullah da fadawansa suka ci gaba da tattaunawa. Wata fuska na gani ɗaya daga cikin Fuskokin da akayo zaman fadar da su cikin dare ya nufi soron tsakiya fuskarsa ya yane ta da wani baƙin ƙyalle, yana tsaye a soron sai kaiwa da kawowa yake dan gudun karna samu matsala shirin su ya lalace. Kamar munafuka haka take tafe tana sanɗa ta ƙaraso gurin tana ganin sa ta ce. "Zakaran dawaki kukanka ba alheri ba." murmushi ya yi kamar bai ji zafin kalmarta ba yace. "Fulani Maryama kenan Baƙon munafuki bana mutum ɗaya bane, haka nan ƙadangaruwa bata ramin banza sai dai idan ƙwai zata zuba." Fulani Maryama ta taɓe baki ta ce. "Ɓoyayyar fuska kenan kasan fa Kuwwa da kuwwa bata korar Buzu kuma ko a cikin tumaki rago ke zuwa fada." Mutumin da ta kira da ɓoyayyar fuska yace. "Wanda za'a kashe dan an rataye shi ai ba komai bane, a juri dai zuwa rafi wata rana tulin zai fashe." Fulani Maryama ta gyara tsayiwarta ta ce. "A dana wannan kalaman naka wata ƙila zasu amfani a gaba amma me ake ciki yanzu?" Ɓoyayyar fuskar ya kwashe duk abin da ya faru a fada ya gaya mata, baƙin ciki haɗe da tashin hankali ne ya turniƙeta a fili ta furta. "Lallai kuwa tsugunne bata ƙare ba dan dole kuwa mu ɗauki mataki akan wannan yaron saboda yarinyar nan karta fallasamu." Ɓoyayyar Fuska yace. "Maryama ki bi komai fa a sannu dan ba kowanne nama ne yake ciwu ba wani idan ka ci shi kwanan keso zaka yi." Harara ta watsa masa tace. "Duk wanda yace garinsu da nisa ba'a kama shi ya zuɓuce ba, idan bazaka iya wannan yaƙin ba ka sakar mini linzamim dokin bazai gagareni sarrafawa ba, kasan bahaushe yace me tsoron a mutu shi yake maho ni da ka ganni ba gudu ba ja da baya har sai na cimma buri na a gidan nan." Dukda suna cikin duhu hakan bai hanashi watsa mata muguwar harara ba, cikin zuciyarsa yana ayyana ta hanyar da zai ɓullowa lamarim Fulani Maryama ta ruwan sanyi yadda bazata fahimci indai ya sa gaba ba. Gyaran murya yayi a hankali yace. "Ragamar damisa a jaki da nisa, randar cikin ɗaka Allah ke baki ruwa. Fulani Maryama sarauniyar mata nina isa nace tazugen Sarki ya kunce ai duk inda kika saka ƙafarki kina ɗaukewa zan ɗora tawa. Me za'a fasa mutuwa ko hisabi?" Fulani Maryama tayi murmushi sannan suka ci gaba da ƙulle-ƙullensu daga ƙarshe kowa ya kama gabansa. Washegari da sassafe Salman ya shigo sashen Mahaifiyarsa kamar wanda aka jefo shi daga sama ko sallama babu, hatta Bayin da suke cikin sashen ba ƙaramin razana suka yi da ganin yanayin da Salman ya shigo ba, da ƙarfin gaske ya bankaɗa labulen ɗakin nata ya shiga a lokacin tana kwance a kan gado ko sallar asuba batayi ba. Yana shiga ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan gado sannan ya sa hannu ya fara tashinta da ƙarfi, kamar saukar aradu haka ta tashi firgigit tana dube-dube. Wata uwar tsawa ya buga mata yace. "Mama wallahi ki kiyayeni babu ruwanki na gaya miki babu ruwanki, ki cire kanki daga cikin sabgar yarinyar nan idan ba haka ba wallahi zaki tsinci talatarki a labara, ina raba ki da kiwon kyalla kina akuya ta haihu muddin kika bari kika kaini bango wallahi zakiyi mamaki na gaya miki babu ruwanki da yarinyar nan amma kinƙi ji ko to shikenan jiki magayi maji ma gani an binne tsohuwa da rai, wallahi wani abu nake dubawa ina duba hallaci banasan na yi miki butulci, kinyi mini hallacin da ko Mahaifiyar da ta haifeni bata yi mini ba shiyasa nake ɗaga miki ƙafa amma bakya gani, ina ƙara jaddada miki da ko fita harkarta saboda mallakina ce idan kuma ba haka ba wallahi zaki sha mamaki. Akan Maryo babu wanda bazan iya ganin bayansa ba dan haka gwara ki shafawa ranki salama ki ga aurena da ita kamar yadda kika ɗauko da farko bansan ma akan wane dalili ne zaki juya mini baya ba alhalin kinsan nafi kusanci da ke, Mahaifiyata babu yaffa bata yi dani ba akan na rabu da ke amma na fifita ki akanta, sai da kika san sirrina zaki juya mini baya? Sam bazan ɗauki wannan ba dole cikin biyu a yi ɗaya zaɓi ya rage naki amma wallahi kika nemi ki kawo mini cikas akanta sai inda ƙarfina ya ƙare." Yana zuwa nan a zancensa ya fice daga ɗakin yana wani irin huci kamar kumurcin macijin da yake gabda kai mummunan sara. Tsoro, mamaki, fargaba haɗe da tashin hankali ne suka yi caraf suka samu gurbin zama a cikim zuciyarta haɗe da sassan jikinta, da ya sanyaye kamar wacce aka zarewa laka. Tun da ta ƙurawa bayansa ido bata ɗauke su daga kallon ƙofar ba, bawaye take yi bibbiyu wani irin tsoron Salman na ɗarsuwa a cikin zucuyarta, gabaɗaya kanta kullewa ya yi ta rasa gane inda maganganun Salman suka dosa, a hankali ta furta. "Yau me yake faruwa da Salman ne ko sauran matan Sarki ne suka fara sa masa hannu, me yake faɗa haka ne akaina ina mahaifiyarsa amma yana ce mini wata ce mahaifiyarsa anya so suke su rabani da shi ba sannan su haukatar mini da shi, duk rashin kunya da rashin mutumcin Salman har ya kai yazo ya tashe ni har gadon baccina ya yi mini wannan tijarar? To wai ma ya akayi yasan da na tattauna maganganu akan yarinyar cen? Na shiga uku wai me yake shirin faruwa da ni ne?" Fulani Maryama kamar taɓaɓɓiya haka ta dinga surutai babu kai ba fasali tana daga zaune daga ƙarshe ta yanke shawarar ziyartar Boka Marduska ko zai bata mafita. Baccin da ya gagari idanunta kenan jiki a mace ta miƙe ta fita ta ɗauro alwala sai a lokacin ta gabatar da sallar asuba. Bayan kwana biyu Jikin Maryo ya yi kyau sosai dan tana cin abinci kuma har ta warware tana takawa da ƙafafauwanta, Inna Habi duk yadda take fushi da Maryo hakan bau hanata siya mata abubuwan da Likita ya zayyana mata ba, idan wanda zata siya ta girka ne tana siya ta dafa ta bawa Abu ta je ta kai mata. Duk yadda ta ƙaugauta ta ƙara ganin jikin Maryo danne zuciyarta tayi dan ta nuna mata kuskurenta, cikin kwana biyu Inna Habi ta rame ta lalace kamar ita ce mara lafiya, ƴar sana'ar kwalliyar dokin da take yi tana siyarwa gabaɗaya ta watsar da ita saboda rashin kwanciyar hankali. Babu wanda ya tambayeta dalilin yawan damuwarta da ramar da tayi saboda kowa gani yake rashin lafiyar Maryo ne ya jefata cikin wannan halin. Kwanan Inna Habi uku da zuwa aka sallamo Maryo daga asibiti, Uwar bayi ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farin ciki, tun daga farkon shigowarsu gidan Maryo ta fara wurga Idanu tana kalle-kalle kamar wacce abin ta ya ɓata take nema ruwa a jallo. Da yake tare suke da Abu ta lura da yanayinta nan take tausayi da mamakin ƴar uwarta ya kamata dan duk wanda ya fahimci Maryo ya san ta zurfafa cikin zazzafar soyayya, ta wani gefe kuma za'a iya kiranta da makauniyar soyayya. Har suka ƙarasa hanyar sashen Bayi Maryo bata daina waige-waigen da take yi ba, suna shiga ciki aka fara turuwar shiga gurin su Inna Habi. Masu zuwa dubiya dan Allah da masu zuwa ganin ƙwaƙwaf sai turuwar shiga suke yi, Bayan an lafa da zuwar musu Maryo cikin jin kunyar Inna Habi ta ce. "Dan Allah kiyi haƙuri Inna" Fuska a tamke Inna Habi ta ce. "Haƙuri da me?" Maryo ta sunkuyar da kai ta ce. "Akan abin da ya faru" Inna Habi ta watsa mata mugun kallo tana jin ɗaci a zuciyarta ta ce. "Maryo bani zaki bawa haƙuri ba kanki zaki bawa Allah ya gani duk wanda ya zageni akanki ban yafe ba, na baku tarbiyya dai-dai gwargwado meye bana muku? Me yasa zaki kai kanki ga ɗan sarki alhalin kina ƙasƙantacciya mara galihu, kina tunanin idan kika ce kina da cikin Ɗan Sarkin nan zasu yarda, wai bakya banbace matsayinki da nashi ne shi fa Ɗan Sarki ne ke kuma Baiwa ce." Maryo ta sunkuyar da kai cikin ladabi ta ce. "Inna ni ba Baiwa ba ce shi ma yasan da haka, kuma munyi alƙawarin aure da shi nasan zai yi murna da abun cikina. Babu wanda zai ƙi amincewa da abin da yake cikina tunda Sarki Mahaifina ne Inna kina ganin akwai me ja..." Cikin takaici Inna rufe Maryo da duka saboda wani ƙululun baƙin ciki da ya tokare mata zuciya, cikin kukan baƙin ciki Inna Habi ta ce. "Maryo yaushe kika fara hauka ban sani ba? Anya kuwa kina cikin nutsuwarki kinsan me kike faɗa kuwa a wane dangin kika haɗa jini da Takawa, tunda haka kike gani yafi ga fili ga me doki zamu ga wanda zai yi nasara tsakanin ke da shi" Inna Habi ta ci gaba da magana cikin kuka me ban tausayi. "Maryo na ci buri akanku amma lokaci ɗaya kin wargaza min shi yanzu da wanne ido zan kalli mutanen gidan nan? Tun baki fita daga masifar da kike ciki ba kin janyo min wata, a da ina shedar ku amma a yanzu Allah ɗaya zaku gaya mini ke da ƴar uwarki na aminta, kin dasa mini zargi a kanki dangane da laifin da ake zarginki da shi, Allah ka na ganin halin da nake ciki ka kawo min mafita." Gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi Abu ma banda hawaye babu abin da take yi, Maryo ta raɓe gefe guda itama sai hawaye take gogewa. Sarki Aminullah murmushi ɗauke a fuskarsa yace. "Gaskiya Yarima naji daɗin wannan maganar da ka zo mini da ita, dama ina gabda im zaɓa maka mata a cikin ƴaƴan abokai na sai gashi Allah ya tarfawa garinka Nono." murmushi Salman ya yi ganin Mahaifinsa ya yi na'am da maganarsa farad ɗaya. Sarki Aminullah yace. "A cikin gidan nan take" Da Mamaki Takawa yace. "A gidan nan kuma? Ƴar wajen Ciro ma Hajara?" Salman ya girgiza kai yace. "Maryo ce a cikin Bayin gidan nan take..." Bai ƙarasa faɗa ba daga bakin ƙofa suka ji ance. "Ƙarya kake ka sauya zancen ka domin ni ba Baiwa bace." Sarki Aminullah ido ya zura mata yana kallon kayan jikinta sannan ya fara maimaita kalmomin da ta faɗa a hankali." Maryo bata saurare su ba ta tako a hankali ta zauna a ƙasa gefen sa na dama ya yinda Salman yake gefensa na hagu. Cikin izza ta ci gaba da magana, "Baba ka ja masa kunne ko da wasa kada ya kuskura ya ƙara ambatona da Baiwa, haba Baba kamar ka manta wanene shi kamar ka manta ta'addancinsa har ka amince masa ya shigo fadarka. Wallahi har abada bazan aureshi ba." Salman sunne kai ƙasa ya yi yace. "Idan wancen karon nayi kuskure wannan karon dan Allah ku bani dama, dan Allah Mai martaba karka hana ni ita idan ka hanani komai zai iya faruwa" Sarki Aminullah shiru ya yi yana bin su da kallo dan gabaɗaya kansa ya kulle, ya rasa wacce irin magana suke yi ita kanta Maryo fa ta tako ta shigo gurinsa ya rasa wanda ya bata damar shiga alhalin tana matsayin baiwa. Maryo a hassale ta ce. "Tashi ka fice mana idan ba haka ba ranka zai yi mummunan ɓaci. Mai martaba kana jin abin da fa yake faɗa wai komai zai iya faruwa, kaga kuwa bazai taɓa saduda ba ni babu wanda nake so nake ƙauna sai Saif." Kamar daga sama suka ga shigowarsa da mamaki Sarki Aminullah ya kalli Saif dan ya manta rabonda ya sa shi a idonsa, Maryo na ganin Saif ya shigo ta miƙe da sauri ta ƙarasa gurinsa tana kama hannunsa ta ce. "Dan Allah Saif ka gayawa Mai martaba halin da muke ciki, ka gaya masa ni kai nake so ba Salman ba ka tuna masa da alƙawarin da ya ɗauka akanmu, ka gaya masa da bakinka Salman mayaudari ne bazai taɓa sake halinsa ba..." Tun bata ƙarasa magana ba Saif ya kifeta da wani irin gigitaccen mari ya nuna ta da ɗan yatsa yace. "Ki kama kanki banasan shirme da rashin hankali" Yana gama faɗa ya wuce gaban Sarki Aminullah. Daga Sarki Aminullah har Salman kallon mamaki suka bishi da shi jin wai yau da bakinsa ya furta magana, a gefe ɗaya kuma Salman yaji zuciyarsa fes har da sakin wani malalacin murmushi, ya saci kallon Maryo da ta sandare a tsaye yana kashe mata ido ɗaya. Maryo daskarewa tayi a tsaye riƙe da kumatu ga wani irin hawaye na bin fuskarta, ganin kukan zai ci ƙarfinta yasa ta juya ta fice da sauri. Tana zuwa bakin ƙofa suka yi gware da mutumin har ledar hannunsa na faɗuwa, da sauri ta tsugunna ta ɗauka ta miƙa masa muryarta na rawa ta ce. "Kayi haƙuri." ta raɓa ta gefensa ta fice. Bin ta ya yi da kallo har ta ƙurewa ganinsa gabansa na ci gaba da faɗuwa a hankali ya furta. "Me ya take yi a nan? Dama duk tsawon shekarun da ta ɗauka bata tare da ni tana gidan nan ina ta kai mini ƴan tagwayena, me yasa tayi kamar bata sanni ba? Why Shukura laifin me nayi miki kika nesanta da ni..." Bafaden da ke tare da shi ne yace. "Yallaɓa mu ƙarasa gurin Mai martaba" Sarki Aminullah tun daga nesa da ya hango shi ya ya faɗaɗa fara'arsa yana cewa. "Marhabun lale da babban baƙo amma gaskiya ka Shamma ce ni Son" KUYI HAƘURI DA TYPING ERRORS BANYI EDITING BA. TO FA KU KAFTA🤣🤣🤣🤣🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️ ANA WATA GA WATA AMUN AFUWA GOBE BA LALLAI NA SAMU DAMAR TYPING BA WALLAHI SABODA WANI UZURI AMMA IDAN NA SAMU SUKUNI KO BA YAWA ZAKU JINI👏🏻 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_ [08/11/2021, 17:22] Ameera Adam🌚: 23... Baƙon da Sarki Aminullah ya kira da Son ya nemi kan wata lallausar dadduma ya zauna, har lokacin waigen bakin ƙofa yake da alama hankalinsa ya karkata acen. Saif da bai wani waye shi ba yace. "Barka da zuwa ya hanya?" Sai a lokacin ya juyo da kallansa ya amsa da, "Alhamdullah" sannan ya mayar da kallonsa ga Sarki Aminullah yace. "Abba barka da hutawa da fatan mun same ku lafiya?" Sarki Aminullah yace, "Lafiya ƙalau Son ya hanya?" yana shirin bashi amsa Salman yace. "Ɗan uwa ya hanya?" Baƙon yace. "Lafiya ƙalau yasu mama" Salman ya amsa da, "Lafiya ƙalau" Baƙon yanasan ya tambayi yarinyar da ta fita yana shakkun kar aga zaƙewarsa. Ƙarfin hali ya yi yace. "Salman lafiya naga kamar baiwa ce wacce ta fita, ta fita da kuka?" kafin Salman ya yi magana Sarki Aminullah yace. "Maleek rabu da sakarcin yaran nan shirmensu ne kawai suke yi" Maleek ba haka yaso ba yaso ace ko yaya ne ya ɗan ji wani abu game da yarinyar dan tabbas babu ko tantama wannan Shukura ce. Saif ne ya miƙe zai fita Maleek yace. "Ranka shi daɗe wannan kamar Saif amma..." tun bai ƙarasa faɗa ba Salman yace. "Eh kwantacce ba ka ga dai Allah ya yi har ya miƙe ga baki ya samu" Da tsananin mamaki Maleek yace. "Da gaske ya samu lafiya gabaɗaya?" Sarki Aminullah da har lokacin shi kansa cike yake da al'ajabi ya gyaɗa kai yana murmushi, mamaki yake sosai yadda kayi Saif ya warke daga ƙasan zuciyarsa yaji wani irin farinciki da ya rasa dalilinsa. Saif murmushi ya mayarwa da Maleek sannan ya wuce saboda ba wani sanin ƴan uwan Mahaifinsa ya yi va saboda kodayaushe yana gida gurin mahaifiyarsa, dama Salma ne ɗan zaman fada shiyasa duk wasu ƴan uwa da baƙin Sarki babu wanda bai sani ba. Musamman da ya kasance kowa yasan shine Yarima magajin masarauta hakan yasa duk inda Sarki Aminullah zai sa ƙafa tare suke zuwa. Abu ɗaya mutanen garin suka riƙe wato albasa batayi halin ruwa saboda ta kowacce siga Salman ya sha bam-bam da mahaifinsa, mahaifinsa mutum ne me adalci da sanyi hali, kyautatawa tausayi tare da taimakon talakawa, ya yinda Ɗansa Salman yake da halaye akasin haka. Maryo wani irin kuka take mai taɓa zuciyar mai sauraro, duk inda ta gifta kallanta ake yi saboda hawayen da ke zuba bibbiyu a idanuwanta. Bata tsaya ko ina ba sai cen cikin daji-daji hanyar da tayi shiru sabida rashin mutane da ke bin hanyar duk kuwa da kasancewar a cikin gidan Sarkin ne, cem bakin bishiyar tsamiyar da ta saba zama tace ta zauna ta haɗa kai da gwiwa tana ci gaba da rusgar kukanta saboda yadda zuciyarta ke yi mata ƙuna. Sai da tayi mai isarta sannan ta goge hawaye ta ɗago a hankali tana furta. "Me yasa zaka yi mini haka? Me yasa zaka guje ni a lokacin da na fi kowa buƙatarka?" Hannunta ta ɗago tana kallan zoben dake jikin ɗan yatsanta ta ce. "Ashe zaka iya manta alƙawarin da muka ƙulla da kai me yasa haka idan wasa kake mini ka farka dan Allah" tana rufe baki kamar wacce aka ce ta juya daga cen tsallaken bishiyar ta hango wasu mace da namiji suna wasanninsu sai dai sun jiya mata baya yadda bata iya ganin fuskoki su, sautin muryoyinsu ta fara ji tare da wata irin sarewa mai tashi a tsakiyar ka, a hankali ta miƙe zata ƙarasa gurinsu sai dai tana miƙewa ta hange su suma sun tashi sunyi gaba suna suna ci gaba da wasanninsu. Maryo batayi ƙasa a gwiwa ba ta cigaba da binsu suna gaba tana binsu a baya har sai da suka yi tafiya mai tsawo, sannan ta hango hangesu sun nufi wani kogi itama batayi ƙasa a gwiwa ba ta nufi hanyar kogin. Kamar daga sama taji kiran da wasu Fadawa suke mata hannuwansu ɗauke da wasu manyan itatuwa wanda da alama bishiya suka saro a gurun. Ƙiƙam ta tsaya tana kallonsu ɗaya daga ciki yace. "Ke Maryo kanki ɗaya kuwa me ya kawo ki cikin wannan dajin da rana tsaka" Maryo dai har lokacin bata tanka musu ba. Ɗaya daga ciki ne ya ƙarasa gurin ya fisgota da ƙarfin tsiya ganin taba gabda da nufa bakin wani rami da babu komai a gurin sai tarin bolar da ake zubawa a gurin. Murya a raunace ta ce. "Ganin nayi suna tafiya shiyasa na bi bayansu wallahi kamar nasansu ji nake kamar nice tare da Furzaan kuma sai suka faɗa cikin kogin cen" Ɗayan Bawan ne ya yi mata kallon baki da hankali yace. "Ramin bolar ne ya miki kama da kogi kina cikin hankalinki kuwa?" Ɗayan da ya ƙarewa Maryo kallo yace. "Kai Bulama riƙo hannunta mu ƙarasa ciki kawai" ba musu suka wuce Maryo na biye da su har lokacin bata daina waige ba har suka ƙarasa cikin jama'a. Sai da suka shiga cikin mutane ya saki hannunta sannan suka wuce gidan bayi suka tura Maryo sannan suka wuce kai itacen da suka ɗauko.Maryo ɗakinsu ta shiga kamar koyausne zaune ta ga Inna Habi ta zuba tagumi ga hawaye na bin fuskarta ɗaya bayan ɗaya, Inna Habi gabaɗaya ta rame ko abincin kirki bata ci. Abu na ganin Maryo ta janyota da sauri ta ce. "Abu ina kika shiga muna ta nemanki tun ɗazu" Kamar an buɗe famfo haka Maryo ta faɗa jikin Abu ta fashe da wani irin kuka, Inna Habi da sauri ta ɗago ta kalleta sannan ta kauda kanta gefe ɗaya tana rumtse idonta. Wasu bayi da ke cen gefe ne suka juyo suna kallon Maryo, dukda basusan abin da yake damun Maryo ba amma da jin irin kukan da take yi ka san daga cikin zuciyarta kukan yake fitowa. Abu bubbuga bayanta ta fara yi cikin tausayin ƴar uwarta ta ta ce. "Me yake faruwa Maryo?" Maryo hawayen ne ya kuma zubo mata da sauri ta kama hannun Abu ta kai saitin ƙirjinta. Abu zaro ido tayi jin yadda zuciyar Maryo ke bugawa da ƙarfi cikin sauri. Kafin Abu tayi magana ta ce."Duk bugun numfashi yana sauka da dakom soyayyarsa Abu mutuwa zanyi ba zan iya rayuwa babu shi ba, shi ya koya mini zallar soyayyarsa yanzu kuma ya juya mini baya. Ina ji a jikina kamar ba shi bane kamar ba zuciyarsa bace idan har zuciyarsa ce a jikinsa babu yadda za'ayi baiji abin da nake ji a zuciyata ba, Abu ki taimaka min bansan sanda na fara sonsa ba ban san yaushe na dulmiya cikin tekun ƙaunarsa ba, abu ɗaya na sani wallahi ina sansa ina ƙaunarsa amma ya juya mini baya Abu kin ga" Maryo ta janyo hannun Abu ta ɗora akan ɗan yatsan da zoben hannunta yake kai ta ci gaba da cewa."Har nuna miki na yi a ranar da muka haɗu da ke da hannunsa ya bani, tun kafin wannan ranar kowa yasanni da shi amma me yasa lokaci ɗaya yi mini haka. Abin da ban taɓa tsammani bane amma yau ya mareni a gaban mahaifina Abu ki duba irun hallacin da mahaifina ya yi masa, bansan laifin da nayi masa amma duk laifin da nayi ban cancanci irin wannan hukuncin..." bata ƙarasa magana ba Abu ta sa hannu ta toshe mata baki saboda yadda mutane suka fara taruwa a bakin ƙofar suna leƙensu, rumgume ta Abu tayi a saitin kunnenta ta ce mata. "Kiyi shiru Maryo mutane suna kallonmu kinasan a dinga yi da mu a cikin gidan nan kenan?" Sororo Maryo ta yi tana kallon Abu cikin sanyin murya ta ce. "Shikenan Abu na bar maganarsa kenan?" Abu da gyaɗa mata kai. Abu ta fara girgiza kai ta ce. "Bakiji yadda zuciyata take yi mini ba Abu, ba zan iya ba..." bata ƙarasa magana ba wani irin tari ya sarƙe ta nan take ta fara wani irin kakari sai ga wani irin aman jini na fita daga bakinta nan take numfashinta ya fara ɗaukewa ta yanke jiki ta faɗi a gurin. Lokacin da aka kaishi masauki kwanciya ya yi akan katifa ringingine idanunsa sun ciko da ƙwallah yana tuna soyayyarsa da Shukra. Zaune take a wani ɗan madaidaicin ɗaki ta ga ya shigo hannunsa ɗauke da wata babbar leda, turo baki gaba tayi ta ce. "Ya Maleek wallahi tun ɗazu nake jiranka har na fara jin tsoro" hancinta ya lakace yana kwaikwaiyar muryarta yace. "Tsoron me bayan kinsan ba daɗewa zan yi ba" Juya masa baya tayi alamun tayi fushi tana ajiye ɗinkin hular da take yi, ta bayanta ya rumgumota ta faɗo jikinsa yace. "Tuba nake amma kinsan dai nima ba da san raina na daɗe ba" Kafin ta yi magana ya fara buɗe ledar da ya shigo da ita sannan ya ɗauko Ƴar tsala ya sa mata a bakin yace. "Na cika alƙawari dai tunda ga ƴar tsalanki" ci ta fara yi harda lumshe ido tana haɗiyewa kamar wacce ta haɗiyi maɗaci ta fara kakarin amai, da sauri ya janyo mata rigarsa dake rataye yasa a gabanta nan ta hau amai har sai da ta amayar da duk abin da ta ci" cikin tausayawa ya fara mata sannu ta langaɓar da kai ta ce. "Ya Maleek anya ba mutuwa zan yi ba?" ta faɗa hawaye na zuba daga idonta. Ya sa hannu ya goge mata yace. "Shukura ki daina faɗin haka, laulayi ne kawai. Kina tunanin idan kika mutu zan iya rayuwa ne" Murmushi tayi ta ce. "Ba sai ka kula da abin da zan haifa ba" Tashi ya yi zaune yana goge hawayen da ke zuba a idonsa, a hankali ya furta. "Shukra me yasa me yasa zaki yi mini haka" kamar wanda aka mintsina haka ya zabura ya miƙe zaune ya ciro wayarsa lambar Mahaifinsa ya kira har sai da ta tsinke ba'a ɗauka ba, kira ya ƙarayi sannan ya ji murya mahaifin nasa a tsakiyar kansa sakamakon dogon tunanin da ya shiga. "Maleek ya akayi?" Maleek ya shafa kai yace. "Ranka ya daɗe barka da hutawa" Mahaifin nasa ya amsa sannan yace. "Allah ya taimakeka naga Shukra a gidan Kawu" da mamaki Mahaifin nasa yace. "Wace shukuran?" Maleek yace. "Shukra dai tawa" ajiyar zuciya Mahaifinsa ya yi sannan yace. "Maleek Allah har yanzu baza ka sawa zuciyarka salama ba, ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo" Maleek kamar zai yi kuka yace. "Wallahi da gaske nake yi na ganta da idona" Muryarsa ce ta fara rawa ya ci gaba da cewa. "Amma ko kaɗan bata nuna ma ta sanni ba Mai martaba" Mahaifin nasa yace. "Maleek ba tun yau ba fa na ce maka ka dage da addu'a domin na lura mutuwar yarinyar nan yana san taɓa maka ƙwaƙwalwa, Shukra yau shekararsu nawa da mutuwa ina jin ta kusa biyu idan ba mantawa nayi ba, saboda irin haka nace maka dama ka fitar da wata matar ka yi aure amma fir kaƙi" Maleek ya taƙarƙare ya fara zabga rantsuwa. "Na rantse da girman Allah ita na gani Ranka shi daɗe, kasan bazan maka wasa ba a cikin fadar Kawu fa na ganta ta fita tana hawaye da alama ma kamar shari'a yake musu, ni dama na daɗe da ji a jikina Shukra tana nan da ranta bata mutu ba tunda har gobe ba'a tsinci gawarsu ba." Mahaifinsa yace. "Dama ya za'ayi aga gawarsu bayan wuta ta cinye su ƙurmus, wallahi Maleek ina tsoron kar yarinyar nan ta fara yi maka fatalwa" Maleek yace. "A fadar Kawu fa na ganta ka yarda dani wallahi ka turo wani daga nan yazo ya ganta idan ƙarya nake." Ganin ya dage yasa Mahaifinsa yace. "To shikenan zan yi nazari akai" suna yin sallama ya kira Mahaifiyarsa ya sanar da ita halin da ake ciki itama ba ƙaramin kaɗuwa tayi da jin zancensa ba, bayan ta gama sauraronsa ta ce. "Maleek ka tabbatar da abin da ka faɗa gaskiya ne kuwa kar na kira Yaya naji akasin haka" cike da ƙarfin gwiwa yace. "Wallahi da gaske nake Umma" har lokacin mamaki take ta ce. "To amma wannan lamari akwai ɗaure kai to Ina Hassan da Hussanin ko baka gansu ba? Kuma ita me tace maka?" Maleek yace. "Bangansu ba Umma, kuma ba wata doguwar magana mukayi da ita ba, bige ni tayi gar ta miƙo mini kayan tana bani haƙuri" Umma tayi jim ta ce. "Anya Maleek wannan lamarin naka akwai ƙamshin gaskiya, ace Shukra ta ganka amma ta kasa nuna farincikinta a fili? Amma babu damuwa zan kira Yaya zan ji daga bakinsa." Maleek ya sauke a jiyar zuciya yace. "To Umma" daga haka suka yi sallama da ita, tashi ya yi ya dinga kaiwa da kawowa lokaci-lokaci yana naushin iska. Gabaɗaya kansa ya kulle banda faɗuwar gaba babu abin da yake ji. Saif na shiga sashen Mahaifiyarsa ya kusa karo da Baiwa Bintu dukda alokacin ba ƙwarin jikinta taji ba haka ta rissuna cikin girmamawa ta ce. "Tuna nake ranka ya daɗe" Gyaɗa mata kai ya yi yana binta da kallon tausayi har ya shiga ɗakin yana jin matsanancin tausayinta, zama ya yi ya gaishe da Mahaifiyarsa sannan yace. "Ammi wannan ba baiwar nan bace ni bansan sunanta ba" Fulani Zaliha ta ce. "Bintu ba ita ce wallahi baka jinyar da yarinyar nan ta sha ba kamar bazatayi rai ba, bayan na asibitin da akayi na hausa ma fa haka ake ta fama kasan jikar uwar bayi ce baka ga tashi faɗin da ta dinga yi ba, ciwo kamar mayu kamar kuma iska gashi nan dai" Saif yace. "Amma me ya kawo ta nan ba Baiwar Umman Salman bace.?" Fulani Zaliha ta gutsiri tufa ta ci gaba da cewa. "Eh a baya baiwarta ce amma gaskiya har yanzu bata koma mata ba tunda jikin nata har yanzu da saura, yanzu ma langa ta kawo mun wacce Uwar bayi ta tafi da tuwo rannan" Shiru Saif ya yi yana ƙara jin tausayin Bintu a ransa lokaci ɗaya yaji ta kwanta masa a zuciya a hankali ya furta. "Allah ya bata lafiya" Fulani Zaliha ta amsa da Ameen sannan ta ce. "Dama tun ɗazu na ji ka shiru ance min anga fitarka Saif banasan ka dinga nisa da gida fa" Saif yace. "Ammi dama naje gaida me martaba ne" ɗan tsuke fuska ta yi sannan ta ce. "Hakan ya yi kyau amma ka dinga lura" Saif yace. "In sha Allah! Ammi naga wani baƙo yazo amma naga yana yanayin kama da ni naji Mai martaba yana kiransa da Maleek" Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce. "Ɗan uwanka ne ai" sai kuma yanayin fuskarta ta sauya cikin damuwa ta ci gaba da cewa. "Dan dai baka sansu ba, amma ɗan wajen Addanku ne Adda Zainabu me tsokanarka idan tazo" Murmushi ya yi yace. "Kai amma me yasa bansan shi ba" Fulani Zaliha ta ce. "Ai kasan shi sojan ruwa ne basu cika zama ba idan yazo kuma a ya daɗe ya kwana ɗaya" Saif ya jinjina kai yace. "Ai ta daɗe ma bata zo ba" ta ce. "Ai kuwa dai" daga haka suka ci gaba da hira Saif yana san sanar da ita yadda sukayi da Maryo a fadar Sarki Aminullah amma yana kokwanto, daga ƙasan zuciyarsa kuma yana jin kamar bai kyauta ba amma lokaci ɗaya sai yaji haushinta ya kamashi dan a duniya yanzu babu wacce yake jin haushi kamarta. Tsaye suke a bakin tsibirin Fulani Maryama ta kalli Jakadiya ta ce. "Jakadiya wannan karan bafa zuwa na bane ni kaɗai, zuwan mu ne domin nemarwa kanmu mafita" Jakadiya sai raba idanu take ta ce. "Eh haka ne amma wallahi nikam lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro" Fulani Maryama ta yi mata wani kallo tana shirin magana akayi musu iso zuwa cikin kogon dutsen Boka Marduska. Kamar ko yaushe yanzu haka ma yana zaune a gaban wuta daga shi sai wata rigar fata me baza da wandon fata. Kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai ya ci gaba da sha'anin gabansu kamar ma bai gansu ba, kallan juna sukayi tsakanin Fulani Maryama da Jakadiya saboda tun da suke zuwa Marduska bai taɓa yu musu irin haka ba. Fulani Maryama ce tayi ƙarfin halin fara magana. "Barka da aiki sarkin bokayen duniya Marduska me dogom zamani" Marduska ya kalleta bai tanka mata ba ya ci gaba da watsa wasu ƙasusuwa a cikin wutar sannan ya ɗago yace. "Maryama meke tafe da ke?" a nan ta fahimci Marduska fushi yake da ita saboda kana zuwa gurinsa kafin ma ka buɗe baki zai sanar da kai abin da yake tafe da kai. Ta russunar da kai ta ce. "Muna neman yafiya da alama munyi gagarumin laifi" Marduska yace. "Nasan akan Ɗanki Salman kika zo da Rayzuta" Jakadiya tare da Fulani Maryama kamar ƙadangaru suka gyaɗa kai lokaci ɗaya. Bushewa ya yi da wata mahaukaciyar dariya sannan ya kallesu yace. "Wuya ko da magani ba daɗi. Maryama dubi yadda kuka yi zumu-zumu kamar an jiƙa kasa a ruwa. To maganar gaskiya Maryama gidan ku na cikin wani irin yanayi ni da kike gani na wannan ƙurar tafi ƙarfi na dan bazan iya dakatar da ita ba. Shuɗaɗɗun ruhika haɗe da rayayyun ruhika ne suka gogawa a tsakani kinga kuwa ni meye nawa a ciki, maganar da Saif ya gaya miki tabbas haka ne domin Ɗanki sam baida imani irin zuciyar ubansa gareshi, wallahi kika nemi ki bashi matsala yana iya aikaki ƙiyama sannan matsawar kika bari aka ɗaura masa aure da Rayzuta to na tabbata mai ƙwatar kansa a gidan nan sai mai yawancin kwana. Ke in taƙaice miki labari wallahi gidan zasu tada gabaɗaya dan ko Sarki Aminullah banajin zai tsira da numfashi, domin tsoguwar gaba ce kuma kema kina da hannu a cikin wannan shuɗaɗɗiyar gabar." Fulani Maryama ta zaro idanu tana dafe ƙirji ta ce. "Marduska me ye nawa a ciki?" Murmushi ya yi bai tanka mata ba yace. "Kafin zuwan wannan ranar nima bansan da haka ba har sai da Zulik ya bayyana, duba nan" ya ƙarasa faɗa yana nuna mata wata ƙwarya kusan lokaci ɗaya suka leƙa ita da Jakadiya, Fulani Maryama ce zaune a gaban wata sarauniya tana motsa baki da alama magana take yi mata, kafin ta gama fahimta suka ga ya ɗauke. A razane Fulani Maryama ta ce. "Marduska yaushe haka ta faru? A iya sanina bantaɓa zama baiwar wata ka duba fa ka gani kowa yasan ni ƴar Sarki ce gaba da baya kuma Sarki nake aure" Marduska yace. "Wannan amsar tambayar taki tana gurin Zulik wato Salma ki bishi a sannu shi zai warware miki komai ko shi ko Rayzuta, amma karkiyi fatan Rayzuta ta waiwayoki domin sam bazai yi miki kyau ba." ya nuna Jakadiya yace. "Ke kuma ina jiye miki ranar da Saif ɗan wajen Zaliha zai juyo gareki tabbas a lokacin me ƙwatarki sai Allah, dan sai ya ƙasƙantar da ke a cikin gidan sannan kuma ya yi miki kisan wulaƙanci domin Furzaan cike yake da baƙin cikinki" Jakadiya ta ce, "Waye kuma Furzaan ni ƴasu" Marduska yace. "Ɗan wajen Zaliha ne sannan ita kanta Rayzuta bata kyaleki ba ko dan abin da kika yiwa Sarki Aminullah domin Mahaifinta ne" A zabure Fulani Maryama ta miƙe tsaye ta ce. "Me kake faɗa? Yarinyar ce ƴar gidan Takawa?" Daga cen Masaraurar Adamawa wata mata na gani Aƙalla zata yi shekara Arba'in da biyar, safa da marwa take ta yi a cikin ɗakinta cikin tashin hankali. Wayarta ta ɗauka ta doka kira babu jimawa aka ɗauka ko amsa sallamar ba'ayi ba ta ce. "Ka san wanne mummunan labari na samu yanzu? Wai Maleek ya je Masarautar Kano gidan Wan Mahaifiyarsa ya kira Mai martaba wai ya ga Shukra a cen" daga cen ɓangaren yace. "Fulani me kike faɗa ne wai? Yarinyar da muka bankawa wuta ita ce ta aka gani a masarautar Kano?" Matar da ya kira da Fulani ta ce. "Wallahi da gaske nake fa yanzu haka Sarki ya tashi Mutum biyu daga nan sun tafi cen yanzu ina muka kama idan yarinyar nan ta bayyana? Kasan asirinmu ya gama tonuwa dai.Ni kam har bansan ya zanyi ba wallahi" Mutumin yace. "Lallai tsugunne bata ƙare mana ba, Amma kuwa dole musan abin yi matsawar Shukra ta dawo gidan nan hatta zaman duniyar ma sai ya gagaremu." INA MUKU FATAN ALHERI🥰 BA WANI PAGE DAN WALLAHI WUTARMU TA LALACE TUN KWANAKI KUYI HAKURI DA ERRORS KU HAƊE A COMMENTS🤾🏻‍♀️🤣 _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [09/11/2021, 18:13] Ameera Adam🌚: 24... Marduska ya kalli Fulani Maryama da yadda take ta tada jijiyoyin wuya, wani tsohon ƙoƙon kan ƙwarangwal ya ɗauko ya kantami wani kore-koren ruwa ya sha sannan yace. "Maryama meye naki na ta da jijiyoyin wuya bayan duk ƙafafar da kike yi Salman fa ba ɗan masarauta bane" Fulani Maryama ta kalli Jakadiya da tayi ƙuri tana raba ido kamar shege a rabon gado, wani yawu ta haɗiya me ɗaci ta ce. "Marduska duk ba wannan ba. So nake na ji ta ya akayi yarinyar ta haɗa jini da Takawa? Ni ce uwar gidan Sarki Aminullah kuma duk a kan idanuwa aka haife ƴaƴan sa guda ashirin da bakwai biyu sun rasu, ko a mafarki ban taɓa jin ance wata daga cikin ƴaƴansa ta ɓace ba, kuma Sarki Aminullah ƙwarƙwararsa ɗaya ƴaƴanta biyu duka mata ta ina suka haɗa dangantaka?" Marduska ya kafeta da ido yana kallo sannan yace. "A inda ba ƙasa anan ake gardamar kokawa. Duba mini nan" ya janyo wani ɗan ƙoƙo da bai fi tafin hannuwan kakkauran mutum ba ya nuna mata, daga cikin ruwan ƙoƙon Maryo ce ta bayyanawa cikin shiga ta alfarma daga cen kan karagar mulkin rangaɗaɗau fuskar Sarki Aminullah ta bayyana ɗauke da murmushi, Maryo ce ke motsa baki bayan wani lokaci ta miƙe ta rungume shi sannan ya sumbaceta a goshi ta fice daga fadar, fitarta babu wuya sai ga mace mai siffar Fulani Maryama ta ƙaraso ta durƙusa gaban Sarki Aminullah tana gaishe shi cikin girmamawa. Boka Marduska yasa hannu ya shafe saman ƙoƙon su Jakadiya suka daina kallon, kamar haɗin baki suka sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya. Jakadiya ta ce. "Marduska ni bansan ta ina zan fara ba saboda al'amuran duk masu sarƙaƙiya ne? Ka fayyace mana abin da yake ɓoye" Marduska yace. "Bani da hurumin fayyace muku abubuwan da ba hurumina bane, ina ta ƙoƙarin inbaku haske dai ta yadda zaku fahimci al'amuran. Amma muddin nayi katsalandan ina iya fuskanta barazana daga waɗannan ɓangarorin guda uku. Karku manta da gaya muku shuɗaɗɗu da rayayyun ruhina ne suke gwabzawa kuma dukkanninsu zaƙaƙurai ne kowanne ka nemi ka yiwa shisshigi to tabbas zaka iya zama shuɗaɗɗe." Lokacin da Marduska ya dire da zancensa ya kallesu a zatonsa zasu kuma jefa masa tambaya amma sai yaji shiru da alama sun miƙa masa lamuransu. Ya gyara zama ya ci gaba da cewa. "Zan iya baku satar amsa akan abubuwan da ya kamata ku kiyaye wataƙila zai taimaka muku wajen binnuwar wasu sirrika na ku. Ku kiyaye zaƙewa cikin lamarinsu gabaɗaya su ukun nan, Rayzuta, Furzaan da Zulik duk kuwa abin da zaku ga sun aikata a tsakaninsu. Duk irin gumurzun da zasu tafka kar wanda ya shiga tsakaninsu domin a lokacin idanuwansu a rufe yake, sai a asiri karku kuskura kuce sihiri zai yi tasiri a jikinsu ina me jaddada muku sai dai ku haɗa da kissa. Abu na ƙarshe da zan gaya muku ba mai daɗi bane wataƙila ya faru wataƙila ku riski akasin haka, akwai gagarumin tashin hankalin da yake tunkarar masarautar ku ni dama nasan tunda Kalimsiyat ta wanzu a doron ƙasa dole a zubda jini. Dan haka lokaci na zuwa da masarautarku take cikin barazanar zubar jini sai wanda Allah ya tsare. Amma fa ban tabbatar ba bincike ne ya nuna mini ina ƙara ankarar da ku ne saboda ni nan babu uwar da zan iya yi muku indai ba so nake tsibiri na ya kama da wuta ba." Wata gwauruwar ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke Jakadiya ta furta. "Tirƙashi" Fulani Maryama ta ce. "Marduska yanzu babu wani abin da zaka iya aiwatar mana?" a hassale Marduska yace. "Babu tun da nima ta kaina nake, bana taɓo tsuliyar dodo ba haka kawai tunda kinji dai ance kowa ya kwana lafiya shi ya so. Amma akwai mutane huɗu a cikin gidanku masu daraja waɗanda ko kaɗan baza'a taɓa cutar da su ba. Sai kuma wasu tsirarin bayin Allah da naga suna da riƙo da addini suma dai bance akwai wani abu mummuma da zai faru da su ba. Sannan meye tuƙwicin ziyarar mu tunda Rayzuta ta hana mu ɗaukan rayuwakan masarautarku" Jiki babu ƙwari Fulani Maryama ta ce. "Duk abin da ka faɗa" Marduska yace. "Yanzu ki ciro mini gashin sassan jikinku zanyi wani aiki da shi daga haka kun biya ni sai kuma wani jiƙon" Jakadiya ta hau raba idanu tana wuri-wuri Fulani Maryama ta ce. "Da me zamu yankar maka?" Marduska ya yi wani nazari yace. "Karku damu zan tura Murduss zai ɗebar mini da kansa" cikin halin ko'inkula suka yiwa Marduska sallama suka koma Masarautar Kano jiki a sanyaye saboda rashin nasara. Sarki Aminullah kallanta yake yana jin yadda zuciyarsa ke yi masa wani iri musamman da ya ga yadda duk ta bi ta rame kamar wacce ta yi jinya, lokaci ɗaya kuma yaji yana jin kewar matarsa saboda ko babu komai yasan ita ɗin ta dabance a cikin mata. Ganin irin kallon da yake mata yasa ta ƙara tsuke fuska tana ƙara gyara zaman alkyabbarta tare da sunkuyar da kai ƙasa. Sarki Aminullah ya kalleta yace. "Zaliha yaushe Saif ya samu lafiya ban sani ba?" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya turniƙe zuciyarta, ta ɗago tana kallonsa kamar bazata yi magana ba a daƙile ta ce. "Rannan" sai da ya ja shiru na ƴan sakanni sannan yace. "Me yasa baki sanar da ni ba?" Wannan karan bata ɗago ta kalleshi ba ta ce. "Saboda na ga kamar bai shafe ka ba" wani irin kallo ya wurga mata a ɗan fusace yace. "Saboda ba nine mahaifinsa ba ko" Ita ɗin ma a fusace ta kalleshi ta sauke a jiyar zuciya sannan ta ce. "Idan ma kaine wani abu kake masa da zai tabbatar da cewar kai mahaifinsa ne" Sarki Aminullah ya tamke fuska cikin tsawa ya ci gaba da magana. "Karki manta a gaban wanda kike magana idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci, banasan rashin kunya Saif dai Ɗana ne ko kina so ko bakya so dan haka na fiki iko da shi ace Ɗan cikina yana fama da wannan lalurar har ya warke baki sanar da ni ba, wallahi da ace ƙaramin yaro ne babu abin da zai hana na ƙarɓe shi na bawa sauran matana riƙonsa. Sakarcin banza sakarcin wofi ko dan kinga nasa a kira ki ne har zaki nemi ki yi mini wulaƙanci?" Tun da ya fara zazzaga Faɗa idanunwanta suka fara zubda ƙwallah, tuna irin baƙar hawalar da ta sha akan Saif tayi da irin wulaƙancin da yake musu ita da shi har sauran matansa suka ara suka yafa, tun yana tsumma har ya yi wayo take wahala, tunowa tayi akwai ranar da Saif ya je fada gurinsa amma yasa aka dawo da shi gurinta wai zai yi baƙi kar su ganshi yaji kunya. Tana jin ya dire zancensa a zafafe ita ma ta ɗora da nata faɗan dan kamar wacce ta manta a gaban Sarki take, Sarkinma Sarkin Kano Sarkin da duk inda yaje aka ambaci masarautar da ya fito sai an bashi girma kuma an jinjina masa. "Ni kaina da nasan maganar da zata kawo ni kenan da ban tako na zo turakarka ba, Wai me ka ɗauke ni ne ko dan kana matsayin Sarki? Kana tunanin a duniya bayan Ubangiji akwai wanda ya isa ya karɓe Saif daga hannuna? Wallahi idan zanyi yawo tsirara babu wani wanda ya isa ya rabani da Ɗana. Wato saboda yanzu ya warke ya koma cikakken mutum kamar kowa, babu nakasa a jikinsa shiyasa har zaka nuna shi wani mai muhimmanci ne a gurinka. Saif Ɗana ne nina ci wahalarsa ban ƙyamaci abuna ba, safe, rana, dare, sanyi zafi da damuwa ban taɓa jin kunyar wani ya ganni da shi ba saboda ni uwa ce a kowane yanayi Ɗana yake bazan guje shi ba, Dan Allah idan zakayi iko kayi da Ɗan lelenka wanda kasan ciwonsa baka jin kunyar nuna shi a idon duniya ba Saif da ya zame maka Alaƙaƙai ba. Na roƙe ka da girman Allah ka ƙyale mini Ɗana tun da na samu Allah ya bashi lafiya, karka jawo shi a jiki a nemi a salwantar mini da shi tunda ni shi kaɗai na mallaka."Tana kaiwa nan ta miƙe fuska ba walwala ta gyara alkyabbarta sannan ta juya ta ce. "Ranka ya daɗe na barka lafiya" ta yi ficewarta ba tare da ta ji daga bakinsa ba. Sarki Aminullah ko kaɗan bai ji haushin maganganunta na ƙarshe ba domin ga duk wanda yake cikin gidan yasa Salman shine ɗan gaban goshinsa, sai dai wannan karan tsakaninsa da Allah yaji yana marmarin jan Ɗansa a jikinsa ba wai dan ya samu lafiya ba. A gefe ɗaya tunanin su Maryo ne ya faɗo masa maganganun da suka dinga furtawa ne suka shiga kai komo a ƙwaƙwalwarsa, a hankali ya furta. "Wacece ita yarinyar nan? Meye ma asalinta ya akayi tazo gidan nan a matsayin baiwa." Shiru ya yi yana nazarin yadda yadda take furta kalamanta da yadda ta tako cikin fadarsa ba tare da tsoro ko shakka ba, a ɓangare ɗaya ya lura da rashin kwarjinin da ya yi mata uwa uba ga kalaman da take furtawa Salman kai tsaye. Salman da kowa a cikin gidan yake tsoron yi masa laifi ko da a cikin kuskure ne amma ace har Baiwa ta tsaya tana gasa mata maganganu haka. A fili ya furta. "Saif! To meye alaƙarta da Saif? Shi da ba wata isasshiyar lafiya ba" Lumshe idanunsa ya yi kamar wanda aka tsirawa allura a zabure haka ya buɗe su yana cewa. "Ita ce yarinyar da aka kama a turaka ta da wuƙa yanzu kuma ta dawo kan Ƴaƴana, ANYA BAIWA CE? Anya ba wani ne ya turo ta domin tayi masa aiki a kaina da iyalaina ba kuwa? Tabbas dole ayi mini binciken sirri domin na gano inda ta dosa." Yana rufe baki Wayarsa ta fara ringing yana dubawa ya ga sunan Sarki Abdallah Abdulmanaf, daidaita nutsuwarsa ya yi sannan ya ɗauka da sallama. Bayan sun gaisa Mahaifin Maleek yace. "Sirikina Ɗanka ya zo mini da wata magana" da yake sukanyi wasa a tsakaninsu kowannensu yana kiran kowa da Sirikina. Sarki Aminullah yace. "Sirikina wacce magana kenan" Babu ɓata lokaci Mahaifin Maleek ya zayyane masa duk abin da Maleek ya kira ya sanar da shi ya ɗora da cewa. "Ka san yaran zamani da ƙwallafa rai akan abin da suke so, yaron nan babu yadda bamu yi da shi akan ya yi haƙuri ya fauwalawa Allah lamuransa akan mutuwar matarsa amma ina abun ya faskara, yanzu dai na taso mutum biyu daga nan akan su zo su zama sheda akan ita ce ko ba ita ɗin bace." Sarki Aminullah ya fahimci wacce Maleek yake nufi jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ba, mamaki haɗe da jimami ya kamashi. Sai da ya tattaro jarumta yace. "Shikenan Siriki Allah yasa muji alheri" daga cen ɓangaren ya amsa da Ameen sannan suka yi sallama. Sarki Aminullah ya jima a zaune yana nazari sannan ya tashi ya ɗauro alwala ya fara gabatar da sallar Nafila. Inna Habi ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, da sauri ta nufi kan Maryo tasa aka ɗebo mata ruwa ta fara yayyafa mata, sun jima a tsaye a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya. Carko-carko mutanen gurin suka yi ana kallon abin da yake faruwa, ganin haka yasa Abu ta ce. "Dan Allah ku bamu guri ko ta sha iska" ba dan sun so ba suka marmatsa daga gurin ƙananan maganganu na tashi daga tsakar gidan. Inna Habi ce ta zurfafa cikin tunani ganin Maryo ta fara wahallalen bacci cikin zuciyarta take cewa. "Ya Allah ka kawo mini ɗauke a cikin baƙon yanayin da muke ciki, nikam dawowar mu cikin gidan nan sam bai amfanar da ni komai ba. Haƙiƙa akwai ɓoyayyen lamari saboda Maryo sam bata da waɗannan ɗabi'un, amma me yasa zata sauya haka me yasa zata yarda da hurewar kunnen ɗa namiji har ya kai ga cutar da rayuwarta. Allah kana gani nayi bakin ƙoƙarina akan tarbiyyar yaran nan, ya Allah ka kawo mana salama a cikin halin da muke ciki." hawaye ne ke gangarowa daga Idanun Inna Habi, Abu na ganin haka ta matsa kusa da ita ta ce. "Inna dan Allah ki daina kuka. Addu'a ita ce mafita." Inna Habi kamar jira take ta ci gaba da zubda ƙwalla cikin kuka ta ce. "Abu kina ganin halin da Maryo take ciki, yaushe rabon da ciwon ta na zuciya ya tashi? A ƙalla amfi shekara kusan biyar bai tashi ba, ki ga yadda yarinya ta lalace duk ta fita hayyacinta akan Ɗa namiji, Abu ki dubi fa Maryo ko abinci bata ci yarinya ta zama kamar taɓaɓɓiya sai dai tayi ta magana ita kaɗai tana kuka, da rana kuka da daddare kuka koyaushe kuka alhalin wanda take yi dominsa ma baisan tana yi ba. Yanzu ya kike so muyi idan abun ɓoye ya fito fili? Ina zan sa kaina da kunya Abu? Kinsan dai yadda gidan nan yake" Abu itama hawaye take ta ce. "In sha Allah, Allah zai kawo mana mafita amma har yanzu gani nake kamar mafarki ne Inna ace wai Maryo na da ciki." A daidai lokacin Maryo ta buɗe idonta tana yamutsa fuska saboda yadda cikinta yake hautsina mata da tsananin yunwa, a hankali ta ce. "Abu zan sha ruwa" da sauri Abu ta miƙa mata wani saurin ruwa kamar mayuwanciya haka take ɗaɗɗakar ruwa har sai da ta shaye duka, tana gama sha da sauri ta fice daga ɗakin tana yunƙurin amai. Daga Inna Habi har Abu bin Maryo suka yi da kallo da take ta kwara amai kamar zata amayo hanjin cikinta. Abu ta miƙe ta kai mata ruwa a buta sai da ta kuskure baki sannan ta taso suka shiga ɗaki, a wahalce ta zauna tana mayar da ajiyar zuciya. Inna habi kallan Maryo ta yi ta ce. "Me kike sha'awar ci" A kunyace Maryo ta saci kallan Inna Habi a hankali ta ce. "Kunun tsamiya kawai nake so" Inna Habi bata bata amsa ba ta miƙe ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wace madafa domin nemowa Maryo kunu dan basa rasa kunun tsamiya da kunun kanwa a madafar. Washegari tun asuba Jakadiya ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da kawowa take, Umma uwar soro ce ta leƙa ɗakin Jakadiya ta ce. "Jakadiya lafiya ke kaɗai sai ɓuruntu kike ko bakya jindaɗi ne?" Jakadiya ta kwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta ce. "Cikina ne yake ɗan hautsina mini" Umma Uwar soro ta ce. "To sannu ko wani abun kika ci, kizo randar magani ki ɗiba kisha ko ya ɗaure miki ciki" Jakadiya daga ɗakinta ta amsa. "To bari sai zuwa wayewar gari" Jakadiya cen ƙuryar ɗaki ta shige ta tura kanta tana tura bakinta cikin zanin rufarta ta fashe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan ta kai hannunta ta ƙara shafa ƙwaryar molon da ta wayi gari da shi a kanta, kuka ta ƙara rushewa da shi ta zura hannunta cikin hammatarta nan ma taji siɗib kamar wacce aka sa wa aska aka aske. Duk wanda ya ga Jakadiya zai fahimci irin tashin hankalin da take ciki duk tayi zuru-zuru, tana ganin gari ya waye ko ta kan kayan kari bata bi ba kai tsaye ta wuce sashen Fulani Maryama. Bayin Fulani Maryama sunyi mamakin ganin Jakadiya dan haka sai da suka shiga suka sanar da ita sannan aka yiwa Jakadiya iso. Jakadiya na shiga ta tsugunna gaban Fulani Maryama ta rushe da wani irin kuka, wanda dama jiran wannan sukunin take dan ta samu tayi kukanta san ranta, sai da tayi me isarta ta ce. "Maryama yau na wayi da tashin hankali abin da bokan ya yi mini ya shammace ni, dubi kaina yadda na wayi gari da shi da ƙwaryar molo" sai kuma ta fara tattare hannun riga tace. "Dan Allah leƙa hammata ta ki gani" kukan kura Fulani Maryama tayi cikin kuka ta ce. "Jakadiya kanki ko kaina yanzu me zan cewa Takawa? Dubi fa yadda kika san silba haka kaina ya koma ɗazu da na kalli mudubi har ɗauke kaina nayi, a haka Takawa zai dinga kallo na?" Jakadiya ta saki hanci da baki tana kallon rankwalelen kan Fulani Maryama ta ce. "Maryama dama haka kike da rafkeken kai kamar na jinjirin Jaki, wallahi idan Takawa ya ganki a haka idan bai nemi tsari da ke ba shegiya nake." Sarki Aminullah zaune a cikin fada cikin ƙasaitacciyar shigarsa ta alfarma irin ta ƙasaitattun sarakuna, Maleek ne a gefensa na dama sai Salman dake gefensa na hagu, wani bafade ne ya shigo ya russuna yace. "Allah ya taimakeka suna tafe ita da Mahaifiyarta da ƴar uwarta." Jinjina kai Sarki Aminullah ya yi sannan Bafaden ya fita, daga cen gefe baƙin Sarki Abdallah ne sai Waziri da Galadima daga cen bakin ƙofa Ɗan more ne sai dogarawan ƙofa. Inna Habi ce a gaba Maryo da Abu suna rufa mata baya har suka ƙarasa cikin fadar, cikin girmamawa suka russuna suka gaida Mai martaba. Maleek da tun shigowarsa ya kafe Maryo da kallo ba ƙiftawa, Inna Habi kana kallan ta zaka fahimci tana cikin tashin hankali ta russuna ta ce. "Allah ya taimakeka ance kuna buƙatarmu a fada" Sarki Aminullah ya gyaɗa kai a hankali ya fara motsa baki yace. "Hakane! Munaso mu ji sunayenku" Inna Habi ce ta fara gabatar da kanta sai Abu daga ƙarshe Maryo ta gabatar da kanta tana watsawa Salman harara." Sarki Aminullah yace. "Maryo kinsan wannan" Maryo kallan Maleek da aka nuna mata tayi tun daga ƙasa har sama sannan ta ce. "Bansan shi ba Allah ya taimakeka" Sarki Aminullah ya kalli Maleek da ya dafe kai da hannu biyu jin kalaman Maryo yace. "Kaji abin da ta ce, dama na gaya maka ba lallai ita bace saboda wannan Baiwa ce" Maryo kallan Sarki Aminullah tayi cikin rashin jin daɗin kalamansa ta ce. "Allah ya taimake ka ni ba Baiwa bace..." tun bata rufe baki ba wani Bafade ya zabga mata doruna yana cewa. "Ƙarya kike ƴar talakawa..." bai rufe baki ba yaji andamƙi wuyansa nan take ya fara wani irin kakari.... JAMA'A WAI BA ME TAMBAYAR ASALIN TARIHIN SARKI AMINULLAH DA IYALANSA NE🤣 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [10/11/2021, 18:26] Ameera Adam🌚: 25... Fulani Maryama ta murtike fuska ta ce. "Jakadiya ki iya bakinki bar ganin na sake miki fuska ki nemi ganin makwancina." Jakadiya har wannan lokacin bakin buɗe tana ƙarewa hallitar kai da fuskar Fulani Maryama, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Yooo ƙarya nayi wallahi Maryama tun wuri ki nemar mana mafita idan ba haka ba wallahi sai kin fi Bora ƙanƙanshi agun Takawa, to wai ma me zaki ce masa idan ya ga kan a haka ko bari zakiyi sai ya kai hannu yaji mulmulallan kai?" Fulani Maryama shiru tayi tana nazarin maganganun Jakadiya dan a duniya babu abin da tafi tsana ace Takawa zai juya mata baya, murya a raunace ta ce. "Jakadiya wallahi bansan ya zanyi ba. Gaskiya Marduska ya cuceni ya taƙauceni" Jakadiya ta keɓr baki ta ce. "Ya cuce ki ko ya cucemu?" Fulani Maryama ta ce. "Jakadiya ba gwara ke ba. Yanzu saboda Allah duk ranar da Takawa ya ganni a haka wacce irin kunya zanji? Danma babu wani kataɓus da yake aikatawa yanzu amma duk da haka ai da kunya." Jakadiya ta ce. "Mu koma gurin Marduska ba sai asan abin yi ba" Fulani Maryama na shirin magana daga tsakar gida taji ana yi wa Farida barka da zuwa, da sauri ta janyo Ɗan kwalinta ta ɗaura ta cewa Jakadiya. "Maza ɗaure kanki naji muryar Farida zata shigo" Jakadiya ɗaure kai tayi ta miƙe ta ce. "To na barki lafiya" A dai-dai wannan lokacin Farida tayi sallama cikin murna ta ƙarasa ta rungume mahaifiyarta, barka da zuwa Jakadiya ta yi mata sannan tayi musu sallama ta fice. Fulani Maryama ta dubi Farida ta ce. "Wai dama da wuri haka zaku sauka na ɗauka sai zuwa azahar?" Farida ta miƙawa Fulani Maryama Jaririnta da bai fi watannin shida ba sannan ta ce. "Mama wallahi saukar wuri muka yi ina ta kewarku ina Salman?" Fulani Maryama jin ta ambaci Salman sai da gabanta ya faɗi tayi ta maza ta ce. "Ina jin yana cen sashensa. Ya Auwal ɗin?" Farida ta ce. "Lafiya ƙalau ya wuce gaishe da Mai martaba. Mama ya jikin Saif kuwa?" Fulani Maryama ta ce. "Da yake ƙanin Ubana ne ko? Sai inyi ta bibiyar lafiyarsa" Farida sauya fuska tayi dan jininta ba ƙaramin haɗuwa ya yi dana Saif ba, duk lokacin da zata zo gida hutu a sace take zuwa gurinsa su gaisa. Farida ta kuma cewa. "To ya su Ummansu Hidaya da Ummansu Yusra?" A daƙile Fulani Maryama ta ce. "Lafiya kalau. Zaki dameni da tambaye-tambayen jaraba ko gama gaisawa bamuyi ba" Farida tayi murmushi sannan ta sakowa musu wata hirar, suna nan zaune aka dinga shigo da akwatinta da kuma tsarabar da ta kawo musu. Cikin tashin hankali Sarki Aminullah ya furta. "Subhanallah Yakubu." Da sauri wasu dogarawa suka ƙarasa gurinsa suna riƙe shi lokacin har ya fara fita daga hayyacinsa. Daga tsakiyar kanta taji yace. "Ba shi da laifi, a bakin aikinsa yake tun da kike zo a ƙarƙashin masarautarsu dole kibi umarninsu idan ya mutu ranki zai ɓaci" A hargitse Maryo ta furta. "Furzaan" Abu na ganin haka danne cinyar Maryo tana mata alamar da ta nutsu tasan a gaban wanda take, Miƙewa Maryo tayi ta fara kalle-kalle ta ce. "Kana ina ne Furzaan?" bin ta suka yi da kallo kowa na yi mata kallon ta fara samun taɓuw, ido ta zurawa Dogarin da ke cikin wani hali nan take ya fara jin komai yana lafa masa a hankali ya fara buɗe idonsa yana kallansu ɗaya bayan ɗaya a wahalce, Ajiyar zuciya Sarki Aminullah ya sauke ganin Dogarin ya fara dawowa dai-dai. Ɗan more ne ya taimaka musu aka ɗauke shi aka fice daga fadar. Har lokacin Maryo na tsaye tana waige-waige ragowar dogarawan tsoron taɓa ta suka ji musamman da suka ga abin da ya faru da Ɗan uwansu. Inna Habi ce ta kalli Maryo cikin tsawa ta ce. "Maryo nemi guri ɗaya ki zaune ko ranki ya ɓaci." Ba musu Maryo ta zauna kafin ta kai ga zama hawayen da take maƙalewa ya fara sharara a fuskarta, Sarki Aminullan ya yi mata kallan tsaf yana nazarinta sannan yace. "Me yake damunki?" Kamar jira take ta rushe da kuka, sai da tayi me isarta babu wanda ya tanka ta sannan ta ce. "Allah ya taimake ka Saif ne" Takawa ya gyaɗa mata kai alamar neman ƙarin bayani ta ci gaba da cewa. "Yanzun nan ya yi mini magana amma kuma ya guje ni" Galadima cikin tsawa yace. "Ke yarinya ki samu nutsuwa a gaban Mai martaba kike" Maryo ta watsa masa wani kallo da idanunta da suka rune jawur, tayi ƙwafa ta ɗauke kanta. Sarki Aminullah wani tunani ya yi sannan ya yi murmushi yace. "Yanzu ki bamu nutsuwarki daga baya sai muyi maganar Saif ɗin" Maryo goge hawayenta ta farayi ta tattara hankalinta waje ɗaya ta ce. "Ina jinka Ranka shi daɗe" Sarki Aminullah ya kalli Maleek yace. "Ki dubi girman Allah kiji tsoron Allah, ki sani zaki muti ki tarar da Ubangiji ki gaya mana gaskiyar abin da kike sani game da Maleek" Maryo kallon Maleek tayi da Mamaki saboda ita dai ta san tun da take ma bata taɓa ganinsa ba sai a cikin Fada. Gyara zama tayi ta ce. "Allah ya taimake wallahi bansan shi ba hasalima ni bantaɓa ganinsa ba sai yau ko Inna" Inna Habi ta gyaɗa kai cikin gamsuwa da maganar Maryo, Maleek ya yi farat ya ce. "Shukra dan Allah karkiyi mini haka kinsan ko me ya faru ba laifina bane, ki tuna irin ƙaunar da na nuna miki da bakiki kike cewa duk rintsi duk wahaka bazaki gujeni ba amma me yasa kika mini..." Sarki Aminullah ya katse Maleek da cewar. "Maleek ɗan saurara mun" Shiru Maleek ya yi Takawa ya kalli Inna Habi yace. "Menene gaskiyar labarin yarinyar nan kinga wannan Ɗan ƙanwata ne yanzo yana iƙirarin Ƴarki Matarsa ce, ki gaya mini gaskiya tsakaninki da Allah" Inna Habi ta share gumin goshinta ta ce. "Allah ya taimakeka wallahi-wallahi Maryo dai ko auren fari bata taɓa yi na hasalima ko samari basa kulawa tunkafin mu shigo gidannan" Maleek ya karɓe zancen da. "Gaskiya akwai tuntuɓen harshe a maganarta, ku duba nan ku gani" ya faɗa yana lalubo salularsa mai kusan ƙirar rakani kashi wani hoto ya nuna musu da bai fito sosai ba, sai dai ga duk wanda ya san Maryo yana ganinta zai tabbatar da ita ce a jikin hotonsa duk kuwa da rashin kyawun camerar.Shiru fadar ta ɗauka kowa da abin da yake saƙawa a zuciyar shi. Baƙin da suka taho daga Masarautar Sarki Abdallah suma suna gani Maryo suka tabbatarwa da Sarki Aminullah cewar ita ce Shukran da Maleek yake faɗa. Itama kuma Inna Habi ta tsaya kai da fata akan cewar Maryo ba Matar Maleek bace, dan ta ce ko kur'ani zata iya dafata akan haka ita kanta Maryo taci alwashin haka saboda ko a mafarki bata taɓa sanin ko da mai yanayin Maleek ba bare kuma a zahiri.Tun da aka fara maganar Salman ban da muzurai da harare-harare babu abin da yake yi, gani Sarki Aminullah ya fi karkata ga ɓangaren Maleek yasa Salman miƙewa tsaye cikin ƙaraji yace. "Ya isa haka! Kai Maleek wai me kake faɗa ne? Babu wata alaƙa da ke tsakaninka da ita, Ita ɗin tawa ce nine kaɗai zan mallaketa dan haka ka iya takunka tun kafin na ɗauki mataki a kanka" Maleek ya kalli Salman cikin nutsuwa yace. "Yaro man kaza. Matar tawa zaka dinga iƙirari da wacce zaka aura? Duk masarautarmu babu wanda bai san Shukra matata ce idan ma wani abun ka yi mata wanda yasa ta mance ni da ikon Allah sai komai ya warware, nina dogara da ikonsa kuma da sannu zai bayyana gaskiya." Wani kallo Salman ya watsa masa sannan ya saki wani malalacin murmushi ya fice daga fadar. Inna Habi da duk sauran mutanen gurin mamakin kalaman Salman suke idan aka cire Sarki Aminullah da Maryo da suka taɓa jin hakan daga bakinsa. Ganin haka yasa Sarki Aminullah ya umarci su Inna Habi da su koma sashensu bayan wani lokaci zai kuma nemansu idan buƙatar hakan ya taso, godiya suka yi masa sannan suka bar cikin fadar. Bayan fitar su idanun Maleek ya ciko da ƙwallah lokaci ɗaya ya fara zubda hawaye sanna ya kalli Takawa yace. "Allah ya taimakela dan Allah kayi wani abu kar na rasa Shukra dan Allah" Ba ƙaramin tausayi ya bawa Sarki Aminullah ba dafa kafaɗarsa yace. "Karka damu Son zan kira Sirikina muyi magana duk abin da ake ciki zaka ji, kai dai ka ci gaba da Addu'a Allah ya kawo mana mafita." Maleek ya gyaɗa kai sannan ya miƙe ta fice jiki babu ƙwari. Inna Habi suna tafe magana na cinta har ta kasa daurewa ta cewa Maryo. "Maryo wato shima wannan Ɗan sarkin sonki yake ko? Saboda ga ki sakarai ki bada kanki kare da doko kowa naki ne yanzu meye fa'idar haka? Muna neman mafita ga wata matsalar ta ƙara ɓullowa yanzu mecece mafita?" Maryo tayi shiru kamar bazatayi magana ba zuwan bayan ƴan sakanni ta ce. "Inna wallahi babu wata alaƙa a tsakaninmu da wancen mahaukacin, shi kuma wancen mutumin kece sheda ko a mafarki bantaɓa ganinsa ba" Inna Habi ta sauke ajiyar zuciya ta faɗa wani tunanin. Har sun kusa ƙarasaw ɓangaren bayi ta hango Saif a zaune a kan dadduma da sauri ta canja hanya ta nufi gurinsa, da sallama ta ƙarasa sannan ta tsugunna har ƙasa ta ce. "Ina wuni Yaya Saif" Bai ɗago ya kalleta ba yace. "Lafiya" a gefen ta zauna ta ce. "Ɗazu a fadar Takawa naji kana mini magan. Dan Allah me yasa kake guje mini ko tambayar abin da yake cikina bakayi, yanzu haka kake san na haihu baka kula da lamuranmu?" har lokacin bai tanka mata ba Maryo ta fara hawaye tana jin ƙaunarsa na ƙara nuƙurƙusar zuciyarta, ta kamo hannunsa tana ƙoƙarin kaiwa saitin ƙirjinta ta ce. "Ka tausaya mini kaji yadda zuciyata take harbawa saboda kai, ni ce wacce a kodayaushe bama rabuwa dare, rana, safiya, zafi, sanyi da damina..." Da sauri ya fisge hannunsa ya kifeta da mari. Yana ɗago kai yaga wasu bayi har sun fara taruwa suna kallonsu, ganin ya kallesu yasa suka yi maza suka bar gurin. Maryo kafeshi tayi da ido sai kuma hawaye ya fara zuba zuciyarta na bugawa akai-akai. Tamke fuska ya yi tamau ya nuna ta da ɗan yatsa yace. "Wannan ya zama shi ne kashi na ƙarshe da zan gargaɗe ki da karki ƙara shiga sabga ta idan ba haka ba zan ɗauki mummunan mataki akanki, ke wacce irin mayya ce ne? Ban da mace Karya wace mace ce take bim namiji yake yakice ta. Uban waye ya yi miki cikin da zaki haifa? Wallahi idan na kuma jin waɗannan kalmomin naki sai na sa ankaiki gidan turu" yana gama faɗa miƙe ya wuce har yana hankaɗeta ta faɗi a gefe. Kuka ta rushe da shi mai tsuma zuciya nan take kanta ya sara ta fara wani irin tari tana tofar da jini, tana waigawa ta hango Inna Habi a tsaye tana kallonta ga hawaye na zuba daga idanunta. Abu ce ta ƙaraso gurun ta kama hannunta ta miƙe suka nufi gurin Inna Hani, suna zuwa gurin Inna Habi saboda baƙin ciki ta ɗauke da mari sannan ta rushe da kuka cikin takaici ta rufeta da duka tana cewa. "Maryo yanzu a gabana namiji yake dukanki saboda kin bada kanki a banza anya kin yiwa kanki adalci kuwa Maryo abin da zakiyi mini kenan" nan da nan gurin ya fara taruwa da mutane. Abu ce ta janye Maryo da har lokacin aman jini take yi, Inna Habi ta wuce su tana share hawaye sannan suma suka bi bayanta. Kafin wani lokaci tuni maganar marin da Saif ya yi wa Maryo ya zaga cikin gidan masarautar, dan har da masu yaddawa su Inna Habi da baƙar magana babu abin da take ce musu saboda tasan duk me ma aka gaya mata Maryo ce ta janyo musu. Bayan kwana biyu gabaɗaya Maryo ta ƙara fita daga hayyacinta, ta rame ta lalace ko ruwan kirki bata iya sha, hatta makaranatar bokon data allon da suke zuwa gabaɗaya ta watsar bata da aiki sai kuka, idan abin duniya ya isheta sai dai ta wuce cikin daji ta nufi bakin bishiyar tsamiya ko kuka ta zauna, anan ne take samun nutsuwa wani lokacin har bacci take samu tayi. Sati Biyu da zaman fadar su Maryo Sarki Aminullah ya tara su a lokacin wannan zaman harda Sarki Aminullah da da Mahaifiyar Maleek Hajiya Fahima, tun zamansu a fadar Sarki Abdallah da Hajiya Fahima suke bin Maryo da kallo, waɗansu hotuna Maleek ya ciro ya miƙawa Sarki Aminullah yace. "Waɗannan sheduna ne na farko" Sarki Aminullah ƙuri ya yi yana kallon hoton tabbas babu ko tantama wanna Maryo ce, miƙawa wani Dogari ya yi yace a miƙawa Inna Habi. Karɓa tayi tana kallo gabanta ya faɗi gani mace sak Maryo a kusa da Maleek sauran hotunan kuma tare da Sarki Abdallah ne da wasu mutane. Ta tsinkayi muryar Sarki Aminullah yace. "Me zaki ce game da wannan" kafin Inna Habi tayi magana Hajiya Fahima ta ce. "Nima ina da laifi a cikin wannan maganar saboda da ban musguna mata ba da bazata taɓa gujewa Maleek ba, ki sani nima nayi haka ne saboda wasu maganganu da aka gaya mini akanki" Sarki Aminullah ya dakatar da Hajiya Fahima ya kalli Inna Habi. Inna Habi ta ce. "A gafarce ni Allah ya taimakeka a baya na faɗi haka ne saboda banasan rabuwa da ita amma tabbas Maryo matar Maleek ce, hakan ne yasa na sauya mata suna zuwa Maryo a madadin Shukra" Ba Maryo ba hatta Abu a zabure suka kalli Inna Habi da ta sunkuyar da kai tana hawaye. Sarki Aminullah ya kalli Maryo yace. "Kinji me ta ce haka ne?" Maryo ta kalli Inna Habi nan take hawaye ya gangaro mata ta kalli Sarki Aminullah ta ce. "Eh haka ne amma ina nemar mata afuwa" Inna Habi ta ɗago da sauri ta kalli Maryo, Maryo ma ita take kallo tana hawaye. Sarki Aminullah yace. "Alhamdullah yanzu kin amince zaki bi mijinki" Abu tayi karaf ta ce. "Allah ya taimake ka yanzu bata da sha'awar zama da shi" Maryo ta sunkiyar da kai ta ce. "Eh ranka ya daɗe" Maleek ya ɗaga hannunsa yana godiya ga Ubangiji, Hajiya Fahima ta rungumo Maryo ta ce. "Matso ƴata Allah ya yi miki albarka" Sarki Abdallah yace. "Sirikina godiya muke Allah ya bar zumunci." Sarki Aminullah yace. "Akaita sashen Fulani Maryama a kintsata cikin shiga ta alfarma a yau za'a bashi matarsa ya wuce da ita" A firgice Inna Habi ta ɗago ta ce. "Ranka shi ɗaɗe amma..." Da sauri Maryo ta ce. "Amma barni yanzu ina san ƙeɓancewa da Inna" babu wanda ya hanata dan haka suka wuce cen sashen su na baya. Suna zuwa Inna Habi ta fisge hannunta daga cikin na Maryo ta ce. "Barni fada zan koma" Maryo ta ruƙo ta cikin kuka ta ce. "Me zaki ce?" Inna Habi ta ce. "Zan ce musu ƙarya nake bake bace" Maryo ta ce. "Inna gwara ki bari na tafi dan ko kin koma bazan fasa tafiya ba, dama tuni nayi niyyar nisa da gidan nan saboda soyayyarsa kasheni zata yi koda ban bi su ba zaku wayi gari da gawa ta ko kuma na gudu." Inna Habi ta fashe da kuka ta ce. "Amma me yasa baki ce musu ƙarya nake ba?" Maryo ta ce. "Ba zan iya ba Inna bazan taɓa kunya ta ki ba" Inna Habi ta ce. "Amma Maryo ya za'ayi ki zauna da mutum alhalin ba'a ɗaura muku aure da shi ba" Maryo ta ce. "Idam naje dole za'a ɗaura ku dai kuyi mini fatan alheri" suka rungumeta gabaɗaya suna kuka. Daga bakin ƙofa suka ji ana magana da Maryo da sauri ta yakice ta nufesu kai tsaye suka wuce sashen Fulani Maryama. _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [11/11/2021, 18:02] Ameera Adam🌚: 26... Inna Habi na ganin haka ta durƙushe a gurin tana rushewa da wani irin matsanancin kuka, Abu ma kifa kanta tayi jikin Inna Habi tana rusgar kuka kamar wacce aka yi wa bushara da mutuwa, Carko-carko mutane suka yi a bakin ƙofar daga cen ƙasa ƙananan maganganu suna tashi sama-sama, Umma uwar soro ce ta shiga ɗakin da sauri zaninta har yana neman faɗuwa, tana shiga ta dafa Inna Habi ta ce. "Habi labarin da nake ji ya riskeni shin da gaske ne wai Maryo tsohuwar matar Maleek ce Ɗan wajen Fulani Fahima?" Inna Habi bata bi ta kanta ba ta ci gaba da raira kuka, ganin ta wannan sigar bazai fisshe da uwar soro ba yasa ta fara lallashinta cikin nuna alamun tausayawa tana cewa. "Kiyo haƙuri Habi ummm ko ba daɗe ko ba jima kinsan wannan ranar tana tafe bare kuma dama kin saba da ita tun da abaya ma haka ta faru, oh ashe dai Maryo ba Baiwa ba ce da ƙimarta Habi nikam garin yaya haka ta kasance ne?" Inna Habi ta ɗago da kai ta ce. "Me yasa baki tambayi waɗanda suka kai miki labarin ba?" Umma uwar soro ta kyaɓe baki tana wurga mata harara ta ce. "Samun sarararin kuturu gaɗa a cikin rama, saboda kun taka wani matsayo har kika fara yiwa mutane wulaƙanci, aikin ɓur inji tusa." Tana gama faɗa ta fice fuuuu daga ɗakin dan haka ta so ba taso ace taji komai daga bakin Inna Habi yadda zata ji daɗin idar da labarin. Maryo suna tafe banda hawaye babu abin da take yi har sun kai gabda shiga ɓangaren Fulani Maryama ta ce wa Bayin da suke biye da ita. "Ku dakata a nan zan je wani uzuri yanzu." Kamar su tanka mata sai dai babu wannan damar, cikin girmamawa suka ce. "Hutawarki lafiya" Kamar wacce ake janta haka ta dinga bin hanyar daji tana tafe har sai da ta dangana da bakin murgujejiyar bishiyar kukar da ta saba zama, tun kafin ta ƙarasa ta farajin sautin shassheƙar kuka waigawa tayi taga babu kowa a gurin daga cen hanyar rafin ta hango shi tsaye da hawaye ɗauke akan fuskarsa yana miƙa mata hannu alamun ta taho gareshi, dukda kukan da takeyi hakan bai hanata sakar masa murmushi ba dan haka ta fara ɗaga ƙafarta da niyyar ƙarasawa gurinsa, daga bayanta taga wasu mutane suna janta da ƙarfi dan karta ƙarasa gurinsa, fisgewa ta fara ƙoƙarin yi amma babu hali saboda sun fi ta yawa cikin kuka ta juya ta ce. "Bulbiyat meyasa zaki ci amanar Mahaifina me yasa kika ha'ince mu ku barni naje gareshi kafin su tafi da ni" Wacce ta kira da Bulbiyat ta bushe da dariya ta ce. "Dama cen bana tare da Mahaifinki a fuska ne kawai na nuna masa goyon baya amma ni ta hannun daman Zulik ce ko Mahaifiyarsa bata kaini kusanci da shi ba" Duk yadda taso ƙwacewa daga gurinsu ta kasa har ta hango shi ya nutse a cikin rafin da karfi ta fisge ta rushe da wani irin kuka, tana tsaka da rusa kuka daga cen bayanta ta ji ance. "Ke lafiyarki me ya kawo ki nan?" Tana waigawa ta ga Saif a tsaye ya harɗe hannuwansa, sanya yake cikin kaya na alfarma irin na ƴaƴam sarakuna ba ƙaramin kyau da kwarjini ya yi mata ba sai dai fuskarsa a murtuke take babu alamun fara'a ko kaɗan. Goge hawayenta ta fara yi sannan ta fara takawa a hankali tana murza ɗan yatsan hannunta, sai da ta matsa gabda shi ta miƙa masa hannunta tana zubda ƙwallah murya na rawa ta ce. "Dan Allah koda bazaka tuna ni wacece a gurinka ba ina san ka kama hannuna ka sumbace shi ko da sau ɗaya ne a wannan karan ko zan ji daɗi. Wannan zoben da ka bani ne dan Allah kayi mini kallan rahama ko naji daɗi acikin zuciyata ta yadda zan ginga tuna irin kallon da kayi mini." shiru ya yi yana kallanta cikin zuciyarsa yana cewa. "Wannan wacce irin mayyar yarinya ce haka?" Kuka take sosai ta tsugunna a dai-dai ƙafafuwansa ta haɗa hannuwanta guri ɗaya alamun roƙo ta ce. "Nasan kana jin abin da nake ji a cikin zuciya inda haka ba bazaka taɓa zuwa gurin nan ba, dan Allah karka juya mini baya indai zaka amshi soyayyata a shirye nake na bijirewa umarnin Mahaifina da Mahaifin Maleek saboda ni ba matarsa bace." kukanta ne ya tsananta tana yi ƙirjinta na wani irin suya sannan ta ci gaba da cewa. "Wallahi ni ba ta shi bace kaine nawa kaine wanda na aminta da shi kaine wanda mukayi alƙwari tare duk wuya duk rintsi bazamu gujewa juna ba amma me yasa zaka yi mini haka, nice wacce ka sadaukar da komai naka akaina nice wacce aka azabtar da kai akaina nice wacce take ɗauke da cikinka Ɗanka ko Ƴarka, dan Allah ceci rayuwa wallahi bazan iya jure rashinka ba" wannan karanma kukanta ne ya tsananta nan take ta ƙware tare da fara wani irin tari tana fesar da jini daga bakinta, zaro ido ya yi yana mamakin kalaman da take faɗa ko kaɗan bai ji tausayinta ko ɗar a zuciya ba har sai da ya ga ta fara aman jini, sai da ta tsagaita sannan ya ciro wani ƙaton ƙyalle ya miƙa mata. Sororo ta tsaya tana kallansa da mamaki murna ce ta kamata a tunaninta ya fahimci abubuwan da take gaya masa da sauri ta karɓa ta fara goge bakinta, sai da ta gama sannan matsa gabda da shi tana wara hannuwa alamar zata rungumoshi. Da sauri ya ja baya bata damu ba ta ƙara matsowa ta fara jikinsa tana sauke wata irin ajiyar zuciya tana runtse idonta ta fara hango rayuwar da suke gudanarwa, da sauri ya yakice ta yana kifeta da wani irin mari kafin ta dawo hayyacinta ya ƙara ɗauketa da mari, ba marin ne ya ɗaga mata hankali ba illa rabata da jikinsa da ya yi shine babban abin da ya sa ta cikin damuwa. Hancinta ne ya fara ɗigar da jini hawaye na zuba daga idonta, da sauri ta riƙe hannunsa tana ja suka nufi hanyar rafin da take hangowa sai da suka je bakin rafin ta nuna masa tana cewa. "Kalli nan shin baka ga abin da nake gani ba? Shi ka manta ƙoramar da muke gudanar da soyayyarmu, ka manta a nan gurin na sanar da kai abin da yake cikin cikina, ka manta irin albishir ɗin da kayi mini nida abinda zan haifa." hawaye ne ya ci gaba da tsiyaya daga idanunta ta ce. "Karka manta nan gurin anan ne aka tarwatsa farincikinmu dam Allah karka bari wannan karan suyi galaba akanmu" Kallan ramin gurin da yake cike da tarin bola ya yi sannan ya kalli Maryo yace. "Waɗannan abubuwan da kika faɗa a cikin nan abun ya faru?" da sauri ta gyaɗa kanta. Jinjina kai ya yi ya ja dogon tsaki sannan yace. "To banyi mamaki ba wataƙila aljanune kikayi rayuwa da su a cikin wanan ƙatuwar bolar amma ba ni ba" yana gama faɗa ya fisgi hannunta suka koma cen inda suka fara tsayawa da farko sannan ya wurgar da ita da ƙarfi har kanta ya bugu da jikin bishiya ya fashe ya kalleta a fusace yace. "Wannan ya zama karo na ƙarshe da zan gargaɗeki wallahi-wallahi kika ƙara yi mini makamancin irin wannan saina karkaryaki na watsar, banz karya banda mace mara aji kina da aure me zaki yi da wani namijin Allah ya tsareni daga kaidinki." Yana gama faɗa ya juya ya nufi hanyar cikin gari dan dama ganyen magarya yaje cira ya haɗu da ita, fasa cirar ganyen ya yi koma gida rai a ɓace. Maryo kuka ta rushe da shi a gurin kamar ranta zai fita fuskarta tayi jawur ta kumbura kamar wacce ta kwana ta wuni tana kuka, ƙyallen da ya bata ta rungume tana jin wani irin sanyi a zuciyarta. Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta miƙe ta nufi cikin gari tana haɗa hanya. Maryo duk daɗewar da tayi tana zuwa gurin da ta bar bayin da suka zo tafiya da ita a inda ta barsu a nan ta samesu, gaba ta wuce suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Maryama. Lokacin da Maryo ta shiga kallo ɗaya ta yi wa Fulani Maryama ta ɗauke kanta gefe, Jakadiya da wasu bayi ne suka ɗauki Maryo aka shiga wani ɗaki da ita dan shirya ta. Fulani Maryama da har lokacin cikin jimamin sabon labarin da ya zo mata take yi ta kalli Fulani Fahima ta ce. "Nifa har yanzu mamaki nake ace wai Shukra ita take rayuwa a gidan nan batare da wani ya sani ba sai yanzu" Fulani Fahima ta ce. "Yaya Maryama kenan kinmanta yadda auren Maleek ya kasance kina ganin yarinya ƙwaƙwaran zaman wata biyar ba muyi da ita ba fa. Kinsan fa ko lokacin da ya zo mana da ita cikin jikinta ma ya girma, kinga kuwa ta ya za'ai wani ya santa a nan mu kanmu a waccen masarautar ba kowa ya santa ba" Fulani Maryama tayi zuru kamar me nazari a gefe guda kuma farinciki ne mamaye a zuciyarta tun da tasan ko ba komai zasu rabu da alaƙaƙai, babban farincikin ta da Salman bazai samu Maryo a matsayin matar aure ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "To Allah ya bada zaman lafiya gaskiya yarinyar akwai hankali" cikin jindaɗin addu'arta Fulani Fahima ta ce. "Ameen bari na zagaya gurin su Yaya Bilkisu na dawo" Maryo ce aka fito da ita cikin shiga ta alfarma sanye take da alkyabba silva da ratsin ja, ba ƙaramin kyau tayi ba sai zuba ƙamshi take kamar wacce aka ciro daga cikin kwalbar turare, gashin kanta aka wanke aka gyara kamar bashi ba. Fulani Maryama ba ƙaramin razana tayi da ganin irin kyawun da tayi tai ba, suna haɗa ido gabanta ya faɗi. Jakadiya sai sunne kai ƙasa take lokaci-lokaci taje tamke kanta dan kar ɗankwalinta ya zame ta sha kunya. Kai tsaye fadar Sarki Aminullah aka wuce da ita sai dai har lokacin fuskarta sata koma dai-dai ba saboda irin kukan da ta sha, babu yadda basuyi da ita ba akan ta bada ƙyallen hannunta amma fir taƙi babu yadda suka iya haka suka haƙura suka ƙyaleta da shi. Suna shiga aka zaunar da ita a gaban Sarki Aminullah da Sarki Abdallah, zamanta babu daɗewa su Inna Habi suka shigo bayan zaman su Fulani Fahima ta shigi fuskarta ɗauke da murmushi. Sarki Aminullah ne ya fara magana. "Assalamu alaikum. Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin talikai, mun godewa Allah da wannan al'amari ya faru har gashi Maleek da iyayensa zasu koma da matarsa wato Shukra. Amma ke Habi muna so muji alaƙarki da Shkra tunda Maleek ya shaida mana cewar akan idonsa aka kashe mahaifiyar Shukra wannan dalilin ne yasa har ya ceci Shukra daga ƙarshe kuma har Allah ta ƙaddara ta zama matarsa?" Cikin Inna Habi ne ya kaɗa saboda ko kaɗan bata taɓa zatan zata iya fallasa wannan sirrin a gaban Maryo ba amma babu yadda ta iya idan tace ita ta haifeta zasu ce ina shedarta ita kuwa bata da wata shaida. Gyara zama tayi tace. "Allah ya taimakeka a hanya muka haɗu da ita ganin haka yasa na riƙe ta itama ta zama kamar ƴata saboda gujewa faɗawa cikin ruɗin zamani" Sarki Abdallah yace. "Ina ƴan biyun da ta tafi da su?" Inna Habi shiru tayi dan batasan me zata ce ba." Maryo tayi karaf ta ce. "Duka Allah ya yi musu rasuwa" lokaci ɗaya suka nuna jimami sannan aka yi musu nasiha sosai daga ƙarshe Sarki Aminullah yace an ɗaga likafar su Inna Habi sun tashi daga matsayin Bayin zuwa ƴaƴan cikin gida. A dai wannan lokacin ne ya zartar da cewar zaman Inna Habi zai koma Sashen Fulani Maryama yayinda Abu zata koma sashem Fulami Zaliha da zama. Daga ƙarshe akayi addu'o sannan suka rufe taron Sarki Aminullah da iyalansa suka fita da jiyyar tafiya Masarautar su. Maryo jikin Inna Habi ta faɗa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya haka itama Abu, da ƙyar aka cire Maryo daga jikinsu suka wuce da ita bakin mota. A dai-dai nan gurin Salman ya ƙarasa gurun fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙawa Maleek hannu yace. "Shar kake yau sabon Ango ina ta ya ka murnar samun Shukra Allah sanya alheri" Maleek ya yi mamakin yadda Salma ya sake masa fuska saboda yaga rabuwar baram-baram suka yi, shima mayar masa da martanin murmushi ya yi sannan yace. "Ameen ya rabbi Ɗan uwa, kaima ya kamata kayi gaggawar fito da mace ko mu kaɗa maka gangar gwauro" Salman ya saci kallan Maryo cikin zuciyarsa yace mata. "Amaryar Maleek ki shirya takaba, babban albishiri tuni Furzaan antura masa matar da zai aure dole dai ni ɗin nine mijinki" Maryo ta watsa masa harara ta mayar masa martani da. "Maleek bazai mutu ba sai dai kai ka muti saboda zuciyarsa me kyau ce, Kaidinka zai koma kanka domin Furzaan ni kaɗai ce ta shi bazai taɓa auren wata ba, kuma zai yi biyayya ga Maleek domin ko kaɗan banjin haushin abin da ya yi ba wataƙila yana da gaskiya bansani ba ko na taɓa rayuwa da shi a baya." Maleek ne ya ce. "Salman kayi shiru hirar ce baka so?" Fulani Maryama tayi karaf ta ce. "Maleek kaga kaja matarka ku tafi karka biyewa wannan sakaran" Maryo yana buɗewa ƙofa tana ɗaga kai ta hango Saif dake hango su yana zaune a cikin rumfa nan take ta fara zubda hawaye, jiki babu ƙwari ta shiga motar su Inna Habi na ɗaga mata hannu suna kuka, Sarki Abdallah ne ya yiwa Sarki Aminullah sallama sannan motocinsu suka tashi suka nufi garin Adamawa. Magariba liƙis suka sauka a Masarautarsu kafin zuwansu anshirya musu tarba da kayan ciye-ciye kala-kala, Maryo wucewa da ita akayi sashen Fulani Fahima ruwan wanka aka shirya mata sannan ta shiga tayi wanka ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallolin da ake bin ta, bayan ta idar aka shirya mata kayan ciye-ciye a gabanta amma gabaɗaya a ciki lemon inibi kawai ta iya ɗauka ta sha daga haka ta ce musu ta ƙoshi, basu takura mata ba suka ƙyaleta. Kan shimfiɗa ta alfarma aka kai Maryo gurin baccinta Maryo tun da ta kwanta ta kasa runtsawa banda hawaye babu abin da take yi har gari ya waye. Washegari Tun da gari ya waye Fulani Fahima ta fara haɗawa Maryo kayan gyara na mata kala-kala, saboda ta ce bazat tare ba har sai bayan sati guda da zuwansu. Maryo babu yadda ta iya haka take turawa tana ci wani taci ya zauna wani kuma ta amayar da shi. A ranar da ta cika kwana bakwai da gidan da daddare aka shiryata cikin rantsattsatsun kaya masu kyau sai zuba ƙamshi take, har sashen da aka ware gurin zamansu da Maleek aka kaita tana shiga ta samu bakin gado ta zauna gabanta na dukan uku-uku. Cikin shauƙin ƙauna da kewar matarsa ya tako ya ƙarasa gurinta yana zame mata alƙyabbar dake jikinta, sanye take da wata doguwar rigar mai adon duwatsu an naɗe mata gashin kanta ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Kiss ya manna mata a goshi sannan ya ce. "Shukra nayi kewarki na tsawon shekaru dan Allah nan gaba karki ƙara hukuntani da irin wannan hukuncin domin ba zan iya ɗauka ba" Maryo shiru tayi har lokacin gabanya faɗuwa yake, miƙewa ya yi yace. "Tashi ki ɗauro alwala mu gabatar da Nafila domin wannan ranar jin ta nake kamar sabon ango ya zama wajibi mu godewa Ubangiji." Kama hannunta ya yi ya nufi banɗaki da ita sai da ya tura mata ƙofar ya ce ta shiga. Tana shiga ta fara alwala ta ga hannunta ya yi wani irin bau dai-dai gurin da ya riƙe mata hannu nan take ta ga jini na tsatstsafowa daga gannun, ruwa ta sa ta wanke sannan ta fara gabatar da alwala. Bayan ta fito sallah suka gabatar ya jima yana addu'a sannan ya fara ciyar da Maryo naman ƴan shiloli, sau biyu kawai ta karɓa ta ce ta ƙoshi dan har lokacin hannunta raɗaɗi yake mata. Bayan sun kammala koma Maleek ya riƙe hannunta suka koma saman gado cikin kewarta ya miƙa hannu ya fara shafa mata fuska cikin so da ƙyauna. Lokaci ɗaya ya ga ta yi wata girgiza harsai da gadon da suke kai ya motsa. Ɗaya bayan ɗaya ya dinga ganin me siffar Maryo na tashi daga jikin tana dira a kusurwar bango harsa da guda biyu suka fita daga jikinta, Maryo ce ta miƙe ta dira ƙasa itama ta koma kusurwar bango ta tsaya, ɗayan kusurwa da ta rage babu kowa ya ga alamar inuwar namiji a atsaye. Ta farkon ce ta fara cewa. "Muhainish ba matarka bace" sai ta biyun ta ce. "Kalimsiyat ba matarka bace" sai ta ukunsu ta ce. "Rayzuta ba matarka bace, sauran duk suna da mazajensu dan haka nima ga mijina nan" ta faɗa tana nuna inuwar dake jikin ɗayar kusurwar bangon. KARFA KU SHIGA RUƊU IDAN KUN TUNA BAYANIN BOKA TUN A SHAFI NA UKU DAMA YACE SHUƊAƊƊUN RUHIKAN ƳAƳAN SARAKUNAN ALJANU NE ZASU TASHI KARSHE SU YADA ZANGO AKAN TA UKUNSU, DAN NAGA KAMAR WASU SUN RIKITA DA LABARIN HARDA MASU CEWAR KO WANI LAIFI SUKA AIKATA😂😂 SAM BA HAKA BANE KU DAI MUJE ZUWA MU HAƊE A COMMENTS🤾🏻‍♀️ _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [13/11/2021, 19:30] Ameera Adam🌚: 27... Maleek ja ya yi da baya cikin tashin hankali, binsu yake da kallo ɗaya bayan ɗaya jikinsa ban da karkarwa ba abin da yake yi. Inuwar da ke kusurwar bangon ce ta fara takawa a hankali zuwa gurin Maryo dake kusurwar kudu, dafa shi tayi ta ce. "Ashe kana tare da ni kake ƙoƙarin juya mini baya?" Maleek zaune yake yana kallon ikon Allah. A hankali ya fara karanta ayoyin tsari yana tofa musu nan take fara bajewa ta jikin bango suna ɓacewa, Inuwar da ke jikin bangon ce ta bi ta jikin bango ta ɓace itama Maryo ta yanke jiki ta faɗi a gurin. Ajiyar zuciya Maleek ya sauke yana runtse idanuwansa, a hankali ya miƙe ya ƙarasa bakin gurin da Maryo take kwance ya sa hannu ya ɗaukota ya ɗora ta akan gado sannan ya koma banɗaki ya ɗauro alwala ya fara gabatar da sallar nafila. Maryo ba ita ta farka ba sai cen tsakiyar dare jikinta banda raɗaɗi babu abin da yake yi, daga ɓangaren Maleek shima hannuwansa ɗaɗi suke yi masa Kamar yadda jini yake kwanciya a jikin Maryo haka shima hannuwansa suka yi jawur da taruwar jini, ita kuwa Maryo jikinta har tsatssafar da jini yake yi a hankali take kai hannu tana sosa jikinta ganin haka yasa hankalin Maleek ya tashi, ƙarasawa ya yi gurinta yana mata sannu idanunta cike da hawaye ta ɗago ta kalleshi ta ce. "Jikina zafi yake yi mini dan Allah ka daina taɓa ni" Ba ƙaramin tausayi ta bashi ba saboda yadda take maganar zaka fahimci daga cikin zuciyarta maganar take fitowa. Yana san ya janyota jikinsa ya rarrasheta amma yana tsoron taɓa ta saboda yadda shi kansa jikinsa yake masa raɗaɗi bare kuma ita da har jini yake fita daga jikinta. Fuskarsa ɗauke da damuwa yace. "Shukra!" Ya faɗa yana kafeta da dara-daran idanuwansa, ɗauke idanuwanta tayi saboda ba ƙaramin kwarjini ya yi mata ba, hasali wannan shi ne karo na farko da ta kaɗaice da wani Ɗa namiji a rayuwarra, sunkuyar da kai ƙasa tayi tana tuna soyayyarta da masoyinta nan take ta ci gaba da zubda hawaye. Hannu ya miƙa zai rungumota sai kuma ya fasa ya ci gaba da magana yana kallonta. "Shukra yaushe kika gamu da wannan lalurar, tun da nake da ke ban taɓa ganin haka daga gareki ba. Dubi hannuwana" ya faɗa yana nuna mata hannuwansa da suka yi ruɗu-ruɗu musamman da yake farin mutum hannuwan sukayi jawur kamar ka taɓa jini ya zuba" Maryo shiru tayi tana jinsa daj ita kanta bata taɓa fuskantar haka ba ko dan ita tunda take idan aka cire Saif babu Namijin da ya taɓa riƙe ta har ya kai ga ya rungumeta. Ɗagowa tayi tana kallonsa har lokacin hawaye be kwance a fuskarta, karantar yanayinta ya yi cikin wata irin murya yace. "Shukra me yasa bakiyi farincikin dawowa gareni ba? Tun da muka haɗu a koyaushe babu abin da nake gani a fuskarki sai hawayen baƙin ciki, Me nayi miki ne? Ko bakyasan ci gaba da zama dani?" da sauri ta ɗago da kanta tana kallansa kamar zata amsa masa sai kuma ta girgiza kanta tana ci gaba da hawaye. Shiru ya yi yana nazari sannan yace. "Shikenan ki kwanta ki huta" kwanciya tayi ta rumtse idonta tana jin zuciyarta na yi mata suya, lokaci ɗaya tunanin Saif ya faɗo mata haka ta ci gaba da hawaye. Ƙyallen da ya bata ta ciro tana rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya akai-akai. Idanu ya zura mata yana kallo shi kaɗai yake jin zuciyarsa babu daɗi, cikin zuciyarsa yake jin kamar bai mata adalci ba gani yake kamar yaso kansa da yawa, kamata ya yi ya keɓence shi da ita ya ji tw bakinta tun kafin ya taho da ita tunda zaman aure ba na mutum ɗaya bane. Miƙewa ya yi jiki ba ƙwari ya zagaya ta ɗayan ɓarin ya kwanta yana lumshe idanu. Inna Habi ta jima a gurin ban da Kuka babu abin da take yi da ƙyar Abu ta ja hannunta suka wuce cen sashensu, bayan tafiyarsu babu daɗewa Fulani Maryama ta aika wata Baiwarta kiran Inna Habi, Inna Habi bata ɓata lokaci ba ta ƙarasa cen sashem Fulani Maryama. Cikin girmamawa ta russuna gaban Fulani Maryama ta ce. "Allah ya taimakeki ya kara miki lafiya ance kina nemana" Fulani Maryama da farincikinta yaƙi ɓoyuwa saboda tafiyar Maryo ta ce. "Tsohuwa sannunki, ni ya sunanki ne?" Inna Habi ta ƙara russunar da kai ta ce. "Allah ya taimakeki Suna na Habiba" Fulani Maryama ta ce. "Habiba kece Takawa yace zaki dawo sashena da zama ko?" Inna Habi da gyaɗa kai ta ce. "Nice ranki shi daɗe" Fulani Maryama ta taɓe baki tana ƙarewa Inna Habi kallo dake rakuɓe a ƙasa cikin tsummokaran kayanta ta ce. "Me ya sa tuntuni baki ɗebo tsummokaranki kin dawo nan ba? Salan Takawa yace bana farinciki da dawowarki? Anya ma kuwa zamu wanye lafiya kuwa? Ace tun daga yanzu kin fara ƙoƙarin haɗa mini tuggu" Ita dai Inna Habi shiru tayi gabanta na faɗuwa dan Allah ya sani ba ƙaramin tsoron Fulani Maryama take ba, tun kafin ta haɗawa Maryo wannan tuggun dama cen jininsu bai haɗu ba, murya na rawa ta ce. "Tuba nake Allah ya taimakeki" Fulani Maryama bata amsa ba ta ce. "Ga ɗakince na daga jikin soro sai ki gyarashi za'a kawo miki wasu kayan sawar dan bazan iya zama da ke da waɗannan tsofaffin kayan uniform ɗin naki ba." Inna Habi cikin rawar jiki ta ce. "Godiya nake Ranki shi daɗe, Allah ya taimakeki ya ƙara nisan kwana Zuma kike me farar saƙa ba'a miki lasa ɗaya, Zinariya kike a cikin Mata tauraruwa mai walƙiyar alkairi, babu wata Fulani a gabanki ke ɗin ce dai me dogom zamani. Allah ya raya Yarima mai jiran gado Sarkin gobe da yardar Allah." murmushi Fulani Maryama tayi dan a duniya babu abin da Fulani Maryama ta fi so iri ka wasa ta, duk irin ɓacin ran da take ciki nan take zaka ganta cikin walwala bare a wannan lokacin da ji take kamar wacce aka yiwa albishir ɗin shiga aljanna. Gyara zama tayi tana buɗawa tana daidaita zaman alkyabbarta cikin isa da ƙasaita ta ce. "Habiba anjima ki zo ki karɓi kyautar alkaki da maɗi" russunawa Inna Habi tayi ta ce. "Ina godiya ranki shi daɗe Allah ya ƙara girma" tana gama faɗa ta miƙe ta fice daga gidan tana mamakin hali irin na Fulani Maryama, cikin zuciyarta take ayyana tabbas dole ta san irin zaman da zatayi da Fulani Maryama, dan ta lura mace ce mafaɗaciya uwa uba kuma makirci da iya kissa da kisisina. Tana fita kai tsaye sashen su na bayi ta wuce, babu ɓata lokaci ita da Abu suka haɗa kayansu suka fara yi wa sauran Bayin da ke sashe sallama. Masu taya su murna suna yi masu kuma jin haushin haka sama-sama suka amsa sallamar ta su, dan a ganinsu ya za'a ce su Inna Habi da suke ƴan baya-baya ace har sune suka samun wannan matsayin na ɗaga likafarsu har aka ƴanta su. Abu da Inna Habi lokacin da suka zo mararrabar sashen matan Sarkin Aminullah da ƙwallarsu suka rabu. Inna Habi ce ta rungumo Abu ta ce. "Abu na cucemu na tarwatsa mu lokaci ɗaya dan Allah yanzu meye fa'idar haka, banyi haka saboda wata manufa ba ko dan ba ni na haifi Maryo ba. Na yi haka ne kawai dan ganin na nema mata mafita daga tsananin soyayyar da ta faɗa ta gaibu mara amfani, yanzu babban tashin hankalina idan suka fahimci yarinyar nan na da ciki bamusan me zasu ce musu ba, ko a mafarki kina ganin mun isa mu ce musu cikin Ɗan Sarki Aminullah ne" lokacin da Inna Habi ta zo dai-dai nan a zancen ta faɗa tana ƙasa da murya. Abu ta goge hawaye ta ce. "Inna kin yi kuskure ko kaɗan banso kika amsa cewar Maryo matarsa ce ba." Yanzu fa ba'a ɗaura musu aure da Maryo ba yanzu wanne irin zama yasu yi da ita. Inna kin fi kowa sanin wacece Maryo da kanfiya akan abu idan ta kafe babu me canja mata ra'ayi, kinsan tun da ta kallafawa zuciyarta soyayyar Saif wallahi babu mai canja mata da wani" Inna Habi sai lokaci ta farga dan tasan halin Maryo sarai. A tsorace ta ce. "Wallahi Abu na sani nasan Maryo tana cen" sai kuma ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa. "Ina tsoron kar ciwonta ya tashi wallahi nasan wacece Maryo" Ganin Inna Habi na niyyar rikicewa yasa Abu ta ce. "Inna ki kwantar da hankalinki kinsan fa tun da Maryo ta ce taji ta gani zata bisu babu abin da zai faru da bazata zauna da su ba kinsan idan duniya ce zata haɗu a kanta babu wanda ya isa yasa ta bisu, idan ma kuma ta bisu kinsan ko baɗaɗe ko bajima sai ta dawo. Karki ɗaga hankali nasan tana cikin ƙoshin lafiya, kedai ki bita da addu'a da fatan alheri." Inna Habi ajiyar zuciya ta sauke da jin maganganun Abu, babu ko tantama maganar Abu na hanya babu wanda ya isa ya tilasta Maryo akan abin da bata yi niyya ba, da wannan tunanin Inna Habi ta ɗan samu ƙwarin gwiwa sai dai har lokacin cike take da zullimin halin da Maryo take ciki. Inna Habi da sauri ta yiwa Abu sallama akan sai sun dinga haɗuwa, dan tana tsoron karta ɓata lokaci ta ƙara laifi agun uwar ɗakinta tun da ta samu ta goge wancen da tayi na baya. Abu da sallama ɗauke a bakinta ta shiga sashen Fulani Zaliha, Bayinta ne suka amsa sannan suka yi mata jagora zuwa rumfar Fulani Zaliha. Abu na shiga ta russuna ƙasa cikin girmamawa ta ce. "Barka da hutawa Ranki shi daɗe" Fulani Zaliha da murmushi ta amsa ta ce. "Barka dai" Abu ta ce. "Dama ni ce..." Katse ta Fulani Zaliha ta yi da. "Ke ce sabuwar ƴar da nayi ko" Abu ta gyaɗa kai tana murmushi ta ce. "Ni ce Ranki shi daɗe" Fulani Zaliha ta ce. "Ya sunanki" Abu ta ce. "Suna na Abu" Fulani Zaliha ta ce. "Wane irin Abu ƴata daga yau na soke sunan nan kin koma Zainab" Abu cikin jindaɗin tarbar da ta samu ta ce. "Godiya nake ranki shi daɗe Allah ya ƙara girma da jinkiri me amfani Ubangiji ya ƙara lafiya ya raya Yarima Saif." Ba ƙaramin daɗi Fulani Zaliha ta ji ba ta ce. "Ameen, daga yau ki ɗauki Saif kamar yayanki ki dinga kiranshi da Yaya Saif" Abu ta ce. "Insha Allah ranki shi daɗe" Fulani Zaliha kallan Baiwa Salima tayi ta ce. "Ku kaita ɗakinta da aka gyara mata a haɗa mata ruwan wanka ta gyara jikinta." Abu godiya ta ƙara yi sannan ta miƙe suka wuce sabon ɗakinta. Da daddare Sarki Aminullah na turakarsa a kwance, shi kaɗai ne ranar da yake sanarwa da Jakadiya baya buƙatar kowacce mace daga cikin matansa ta ziyarce shi, ban da juyi babu abin da yake yi tunanin abubuwan da suka faru a ranar yake yi. Tabbas akwai abubuwa masu rikitarwa fuskar Maryo ce take ta yi masa gizo a ido, ya rasa wane dalili ne yasa ya kasa cireta daga zuciyarsa kukan da take yi ba ƙaramin taɓa masa zuciya yake ba, runtse idonsa ya yi bacci ya fara fisgarsa kamar almara haka yake jiyo sautin kukanta, firgigit ya yi ya buɗr idonsa yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Gyara kwanciya ya yi babu jimawa bacci ya yi awon gaba da shi. Mafarki yake wani matashin saurayi ya tunkaroshi gadan-gadan da makami zai kashe shi, yana dubawa da kyau sai ya lura da Ɗansa Salman ne nan take suka fara kokawa ba ƙaƙƙautawa. Daga cikin mafarkin ya hango fuskarta tafe akan doki har ta ƙaraso gurinsu tana zuwa ta shiga tsakiyarsu ta kalli Sarki Aminullah ta ce. "Ya kai Mahaifina wannan faɗan sam ba naka bane ka barni da shi wannan ba Ɗanka bane maƙiyinka ne" tana gama faɗa ta juya gurin Salma suka ci gaba da fafatawa da faɗa, Sarki Aminullah tsaye ya yi yana kallan ikon Allah cikin rashin nasara Salman ya sareta a hannu ta durƙushe a gurin, ganin haka yasa ya koma gurin Sarki Aminu da niyyar halaka shi nan take suka fara faɗa amma har wannan lokacin Salam bai yi nasara akan Sarki Aminullah ba. Firgigit ya fara bakinsa ɗauke da salati buɗe idon da zai yi ya ga Salman tsaye a gabansa. Nan take gabansa ya yi mummunan faɗuwa saboda abin da ya faru a cikin mafarkinsa. Washegari bayan Maryo tayi sallar asuba ne ta samu ta ɗan koma bacci saboda rashin baccin da bata samu tayi ba, sai kusan goma ta tashi a lokacin taruwar jinin hannunta ya fara bajewa Bayin da suke sashenta ne suka haɗa mata ruwan wanka, bayan ta fito tana gaban madubi ya shigo ɗakin da sauri Maryo ta janyo mayafi tana rufe jikinta, girgiza kai ya yi yana mamakin yaushe ta fara kunyarsa haka matar da har ya haihu da, ficewa ya yi daga sashen gabaɗaya. Yana fita bai tsaya ko'ina ba sai sashem Mai martaba dan dole ya sanarwa masa halin da ake ciki, ko dan saboda a tashi tsaye da neman magani. Maryo na gaban mudubu taji kanta ya sara mata ta jikin window ɗakinta ta fara jin iska na kaɗawa, a gaggauce ta sa kaya ta ɗauko abayar da aka ajiye mata ta saka bakin window taje ta tsaye tana ƙarewa gurin kallo lokaci ɗaya ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ƙyallen nan ta janyi tana goge hawayenta sai da ta gama gogewa sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin. Bayinta ne suka fara bin ta a baya nan take ta dakatar da su sannan ta ci gaba da tafiya, duk inda tafi Bayi ne ke russuna mata wasu kuma suna bin ta da kallo tana wucewa kaji ƙananan maganganu suna tashi. Tana wucewa bata tsaya ko ina ba sai bayan ɗakin me babban ɗaki, durƙusawa tayi a gurin ta fara haƙa gurun da wani ɗan ƙarfe daga cen nesa bayi da sauran dogarawa ne suke leƙenta, sai da ɗanyi haƙa me zurfi sannan ta ciro wata sarƙa da tai datti cikin jar ƙasa, da sauri ta sa kayan jikinta ta fara gogewa tana ɗago katon kwaɗon sarkar wani babban tambarin masarauta ne a jiki, ƙare masa kallo tayi ta rushe da matsanancin kuka, sai da tayi me isarta sannan ta miƙe zata koma sashenta daga bayan Jakadiya Muna ta ce. "Shukra lafiya kuwa me kike haƙawa haka" Maryo kusan mutuwar tsaye tayi ta juya a hankali dan jin muryar me yi mata magana, da gudu ta tafi ta faɗa jikinta tana cewa. "Didi dama kina nan" Jakadiya kallan gefe da gefe tayi dan ganin wacce ta kira da Didi amma bata ga kowa ba, sororo tayi tana bin Maryo da kallo, ita kuwa bata damu da irin kallon da Jakadiya take mata ba ta ce. "Didi kinga sarƙarki Dan Allah karki bari su ƙara kwace miki wallahi wannan karan bazamu juri haka ba" Jakadiya zaro idanu tayi tana ƙarewa sarƙar kallo dan har ga Allah ita kallan sarƙar ma tsoro yake bata. Maryo bata bi ta kanta ba ta zura mata ita aka sannan ta ɗora da cewa. "Wallahi duk wanda ya yunƙurar rabaki da sarƙar nan sai na kashe shi kowanene shi." Nan take cikin Jakadiya ya kaɗa tsoro ya kamata, suna nan tsaye Maleek ya ƙarasowa Maleek yace. "Jakadiya ashe kuna tare da Shukra na neme ta ban..." wata uwar tsawa Maryo ta buga masa ta ce. "Mahaifiyata ba Jakadiya bace. Ka kiyaye harshenka idan ba haka ba zan datse maka shi" Jakadiya ban da gumi babu abin da take Maryo ta ce. "Ko ba yanzu ba ki sanar da ni ga duk wanda ya nemi ci miki zarafi domin wannan karan kinfi ƙarfin ƙasƙanci" Maryo na gama faɗa ta wuce gaba daga Jakadiya Muna har Maleek ido suka zura mata, da sauri ya bi bayanta yana cewa. "Mu je Mai martaba ne yake nemanki" Maryo ta juyo fuska a ɗaure ta ce. "Ko bai neme ni ba dama zanje domin ina ji a ajikina yana tare da Jullifat kuma idona idonsa wallahi sai dai gawarsa. Maryo haka ta ci gaba da tafiya kamar wacce zata tashi sama kai tsaye fadar Sarki Abdallah ta nufa tana zuwa ko sallama babu tayi musu ƙerere a tsaye, Waziri dake gefe yace. "Ke gidanku baki ga gaban wanda kike bane?" A hassale ta kalleshi ta ce. "Dama nasan banza bata kai zomo kasuwa, naji a jikina kana nan kuma wallahi yadda ka wulaƙanta Mahaifiyata sai ka wuƙanta." Galadima da shigowarsa kenan yace. "Subhanallah ke me nake ji haka?" Maryo juyowa tayi idanunta suka kawo ƙwallah tana haɗa hannuwa biyu alamun roƙo ta ce. "Ya kai Mahaifina banasan ka hana ni abin da nayi niyya haƙurinka ne ya basu damar aiwatar da duk abin da suka yi akanmu, dan Allah karka ce mini a'a" Tana gama faɗa ta damƙi wuyan Waziri ta ɗaga shi sama nan take ya fara kakari, sa gudu dogarawa bakwai suka yo kanta da niyyar ƙwatar Waziri, da hannu ɗaya ta hankaɗe su lokaci ɗaya suka yi baya suka faɗi ko motsi basa yi. NASAN KUNGA KURA KURAI AMUN AFUWA PLS TO FA KU MU KAFTA🤾🏻‍♀️ _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [14/11/2021, 13:18] Ameera Adam🌚: 28... Hankalin Sarki Abdallah ba ƙaramin tashi ya yi ba hatta sauran fadawan da suke cikin fada tsoro ne ya kama su, Maleek zaro idanu ya yi dan ko kaɗan bai taɓa tsammanin lamarin nata ya kai ga haka ba, Waziri tun yana cikin hayyacinsa har ya fara fita ban da kakari babu abin da yake yi, Galadima da sauri ya ƙarasa gurin yana cewa. "Ke wai me kike yi haka ne ya kike shirin aikata kisa kai ne?" Sassauta riƙon da ta yi wa Waziri ta yi ta ce. "Dan Allah ka ja bakinka kayi shiru karka hana ni abin da nayi niyya" tana gama faɗa ta kuma cakumar wuyan Waziri Maleek ne ya ƙarasa gurinta yana ƙoƙarin kwace shi daga hannunta, kallonsa tayi da runannun idanuwanta ta ce. "Ka matsa daga nan banasan laifinsa ya shafeka" Galadima na ganin haka da sauri ya matsa suka ci gaba da kiciniyar ƙwace Waziri amma kamar ƙara turata suke, Galadima lura ya yi indai ƙarfi zasu sa bazai fisshesu ba, janye hannu Maleek ya yi ya kalleta ya ce. "Ƴata na haɗaki da girman Allah ki sake shi ki dubi girma da daraja ta" Maryo kamar wacce aka zarewa laka a jiki haka ta jiyo jiki babu ƙwari ta ce. "Na san dama bazaka taɓa bari ba, amma me yasa duk irin cutarwar da suka yi mana bazaka bari na aiwatar da muradin ruhina ba" Galadima da har lokacin bai fahimci inda zancen Maryo yake tafiya ba yace. "Eh naji nidai na ce ki sake shi." Maryo sakinsa ta yi ta zauna daɓar hawaye na bin idanunta, zamanta babu jimawa kanta ya ci gaba da sarawa jini ne ya fara ɗiga daga hancinta, hankali a tashe Maleek ya ƙarasa gurinta yana mata sannu, Galadima da sauran Dogaran gurin kan Waziri suka ƙarasa suna yi masa firfita da sannu. Sarki Abdallah shiru ya yi yana nazari ganin abun yake kamar al'amara saboda ko wata guda bai yi da yin makamancin mafarkin abin da ya faru ba, tsoronsa ɗaya kada mafarkin da yayi munana na bayan kwanakin su biyo baya, numfasawa ya ƙarayi yana kallan Maryo da take zaune tana share jinin hancinta da ƙyalle. Maleek lallaɓa Maryo ya yi da ƙyar ya samu ta tashi suka fice daga cikin Fadar tana tafe tana watsawa Waziri mugun kallo, a hanyar su ta kawawa sashensu ta ƙofar baya ya bi da ita saboda idanun mutane, suna wucewa ta sashen matan Sarki Maryo ta tirje a gurin. Maleek ya waigo yace. "Muje mana Shukra" Maryo ta kalli sashen matan Sarki Abdallah ta nuna da ɗan yatsanta ta ce. "Nan zan shiga" Maleek yace. "Zaki je gaishe da Umma ne?" Maryo ta girgiza kai ta ce. "A'a wani abun ɓoye nake san tonowa" da mamaki yace. "Abun ɓoye kuma" bata kalleshi ba ta karkata akalarta zuwa sashen sannan ta ce. "Eh wanda ake cutar da bayin Allah, alƙawari na ɗaukarwa kaina wannann karan duk wani azzulumi da ke cikin daularmu dole ya gane kurensa." Har tayi gaba Maleek ya dafe kansa dan gabaɗaya ya rasa gane kanta, a sanin da ya yiwa Shukra mace ce da bata da hatsaniya bare tashin hankali, hasalima duk abin da zakayi mata na musgunawa sai dai ta zauna tayi ta kuka amma yau sai gashi ita ce take bankaɗo da tashe-tashen hankula, yana nan yana tunani bai yi aune ba sai jin ƙarar buɗe ƙofarta ya yi da sauri ya bita yana ƙoƙarin riƙe hannunta. Hakimtacciyar matar sanye take da kayan alfarma, dukda kasancewarta mace ce mai cike da izza, ƙarfin hali, dakiya, jarumta, alfahari da nuna isa uwa uba kissa da kisisina. Amma hakan bai hana tashin hankalin da take ciki ya bayyana ƙarara akan fuskarta ba, Baiwar nisawa tayi ta ƙara rissinawa hankali a tashe ta ce. "Wallahi na matuƙar kaɗuwa da yadda aka ce ta yiwa Waziri nikam anya ba wani asirin ta dawo da shi ba? Ina laɓe fa na hangota ta haƙo abu a wani rabi muna haɗa ido ta watsomini idanunta wallahi bakiji yadda gabana ya faɗi ba..." Maganarta ce ta maƙale lokacin da suka ji shigar Maryo ɗakin ta bankaɗa labule, daga gurin da take ta tsaya tana ƙare musu kallo. Baiwar ce ta miƙe sum sum sum tana cewa. "Na barki lafiya ranki shi daɗe." Maryo wata uwar tsawa ta daka mata ta ce. "Wallahi idan kika fita ba tare da izinina ba kin dinga tafiya kenan har abada." A dai-dai lokacin Maleek ya shigo yana cewa. "Shukra wai me kike yi ne haka? Ki zo mu tafi mana" Fulani ba ƙaramin faɗuwar gaba ta shiga ba amma sai ta dake ta ce. "Ke Shukra lafiya zaki shigo mini ɗaki babu ko sallama..." tun bata rufe baki ba Maryo ta ɗaga mata hannu tana dakatar da ita cikin tsawa ta ce. "Baki cancanci sallama ba tunda bakisan muhimmancinta ba, ki saurara mini ki kuma bani haɗin kan abin da na zo aiwatarwa, idan kika bani haɗin kai zanyi ingama kuma inyanke hukuncin da naga dama amma..." Maleek da sauri ya hankaɗa ta gefe yace. "Wai baki da hankali ne Umma Babba kike gayawa haka?" Fuska babu alamun tsoro Maryo ta kalleshi ta ce. "Akan wannan abar kake ɗaga mini murya? Ka iya bakinka ina raga maka ne saboda abu ɗaya wallahi kaci albarkacinta amma ba dan haka ba da tuni labarin wani ake ba kai ba." Juyawa tayi ta kalli Fulani ta ce. "Maza ki tono mini abin da kika binne yanzun nan?" Fulani rushewa tayi da kuka tana cewa. "Maleek dama kawo matarka kayi dan ta ci mini mutumci ni zata laƙawa sharri ina zaune ƙalau." Maryo a hassale ta juyo ta ɗauke Fulani da wani irin gigutaccen mari, ba Baiwarta ba hatta Maleek sai da ya zaro ido cikin tashin hankali yana ganin haka yasa hannu itama ya ɗauketa da wani irin gigitaccen mari yana huci yace. "Wannan ya zame miki na farko kuma na ƙarshe, wannan da kike gani kamar Mahaifiyar da ta haifeni haka nake kallanta, wallahi idan kika kuma aikata abin da kika yi yanzu zan baki mamaki, karki rainawa mutane hankali mana." Fulani daɗi taji har cikin ranta sai ma ƙara keɓe baki tayi tana kuka, Maryo murmushi ta fara yi lokaci ɗaya sukaji tana dariya harda ƙyaƙyatawa. Kallan Maleek tayi tana nuna shi da yatsa fuska a turɓune ta ce. "Wannan shine marin da zaka yi mini na farko na ƙarshe dan wallahi sai na hukunta ka." ta juya ta kalli Fulani Babba ta ce. "Daga yanzu zaki san na shigo cikin gidan nan gado sai ɗan gado gararanba sai ɗan taka haye, sai kin tabbatar da cewa ni ɗinnan dawowata daularmu bazai taɓa yi miki daɗi ba" tana gama faɗa ta ƙarasa dai-dai tsakiyar ɗakin Fulani tana tsayawa a gurin ta tsugunna ta fara bubbuga gurin nan take ƙasar gurin ta fara rozayewa tana fashewa, da ƙarfi ta fara ƙwaƙule gurin tana zura hannunta tana ɗaukowa sai ga wani ƙaton abu a naɗe a cikin fatar bunsuru, zazzagesu ta fara yi sai ga kayan Sarki Abdallah harda rawaninsa na faɗowa, daga gefe ɗaya wata hallita suka gani ita ba mutum ba ita ba dabba ba, Fulani cikinta ne ya kaɗa hankalinta ya tashi saboda ganin an tono abin da tafi shekara sama ashirin da biyar zuwa talatin da binne shi. HAPPY WEEKEND🥰 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [16/11/2021, 13:32] Ameera Adam🌚: 29... Tattaro Jarumta Sarki Aminullah ya yi sannan ya kalli Salman yace. "Lafiya Salman me kake yi anan da daren nan?" Salman da idanunsa suka yi jawur ya furzar da iska mai zafi yana jefawa Sarki Aminullah mugun kallo a daƙile yace. "Ba komai" yanayinsa ba ƙaramin tsorashi ya yi ba, haɗiye yawu ya yi cikin ɗari-ɗari sannan yace. "To shikenan ka wuce sai da safe" Salman tsaye ya yi kamar bai ji me Takawa yace ba, har ya ɗan fara takawa ya juyo yace. "Ranka shi daɗe me yasa ka bada yarinyar cen suka tafi da ita alhalin ba ka tabbatar da cewar matarsa ce ko ba matarsa bace?" Sarki Aminullah ba ƙaramin faɗuwar gaba ya shiga ba, tashi ya yi zaune yace. "Saboda ita kanta yarinyar ta furta da bakinta kuma ga shaida nan mun gani" Salman ya wurga masa idanunsa da sukayi jawur kamar gauta, Sarki Aminullah kasa ci gaba ya yi da kallan ƙwayar idon Salman, Salman yaja gajeren tsaki sannan yace. "Wallahi ba matarsa bace dani tafi dacewa dan haka duk abin da zai faru sai ya faru" yana gama faɗa ya fice daga cikin turakar. Abu ba ƙaramin jindaɗi yadda ake tarairayarta a sashen Fulani Zaliha taji ba, tun tana ɗari-ɗari har ta sake ta fara harkokinta a cikin gidan, bata aikin fari bare na baƙi sai dai taci ta sha ta kwanta. Sallah da abubuwan da suka zame mata dole su kaɗai take yi, kasancewar Fulani Zaliha na matuƙar san ƴa mace kuma bata da ita yasa ta ɗauki so da kulawa ta ɗora akan Abu wacce a yanzu suke kiranta da Zainab. Saif shi yake koya mata karatu addini dukda a lokacin ba'a wani waye da makarantar boko ba, hakan yasa basu wani damu da ita ba. Tayi matuƙar mamakin yadda Saif ya iya karatun alƙur'ani tiryen-tiryen tun da kowa yasan irin rashin lafiyar da Saif ya yi, sosai take gane karatunsa saboda mutum ne me sauƙin kai. Sai da suka fara wannan mu'amalar da shi ta fahimci yadda yake da saukin kai kamar ba Ɗan sarki ba, gashi akwai barkwanci da iya magana. Abu ɗaya ta lura da shi daga cikin ɗabi'unsa ba yasan raini ko kaɗan sai dai shi mutum ne ba me ruƙo ba kuma da kayi abu zai nuna maka kuskurenka. A gefe ɗaya kuma idan ta kalleshi sai ta ga kamar ba shi ba musamman idan ta tuna yadda yake yiwa ƴar uwarta sai ta ji babu daɗi, sai ta yi kamar zata yi masa maganarta sai kuma tsoro da fargaba su ɗarsu a zuciyarta. Maryo kallan Fulani Babba tayi ta saki wani malalacin murmushi ta ce. "Wannan abun ba ke kika binne shi ba shekara talatin da suka wuce?" Fulani Babba ta zauna daɓar kamar wacce aka zarewa laka sai kuma ta fashe da kuka ta ce. "Kai jama'a wai saboda a wulaƙantani a tozartani shine za'a ƙirƙiro waɗannan abubuwan ina ji ina gani ace daga ɗakina suke, akan idanun kowa kika aiwatar da siddabarun ki amma dan ni kaɗai kika tsana kice wai nina binnesu." Baiwar Fulani Babba jikinta ne ya yi sanyi dan tasan sarai Fulani zata iya aikata abin da ya fi wannan ma, amma kuma ya akayi Shukra tasan da wannan abubuwan to ko ta fara tsafi ne kamar yadda tayi tsammani. Shi kansa Maleek ba ƙaramin mamaki ya yi ba amma kuma ya akayi ita ta san da wannan abun, sannan kuma anya ba sharri take san ƙagawa Fulani Babba ba tun da dama cen ba jituwa suke yi ba. Maryo ce ta yi wata ɗariya sannan ta ce. "Ni da kika ganni bana ƙwai na sai da zakara ki gama matse-matsen hawayenki wannan kukan yanzu kika fara, dan wallahi sai na bankaɗa sirrin ki na ɓoye kowa ya gane kalarki da ke da munafukan cikin masarautar nan, kin ƙaryatani kin ce sharri na yi miki ko?" Fulani Babba tayi zuru saboda tashin hankali cikinta ban da rugugi babu abin da yake yi. Kasa amsa tambayar da Maryo tayi mata tai sai binta da take da kallo tana fargabar karta ƙara bankaɗo wani mugun ƙullin da ta ɓoye shi. Maleek ya tamke fuska yace. "Shukra dan Allah kizo mu wuce banasan waɗannan abubuwan da kike yi, wannan abun fa kamar kina neman tada hankalin masarauta ne." Maryo itama tamke fuska tayi tasa farin ƙyalle data wanke shi bai gama bushewa ta goge jinin da ya ɗigo daga hancinta ta ce. "Ai dama babban burina kenan in tayar da hankalin Masarauta a fahimci bambamcin ina nan da bana nan, ka bar wahalar da bakinka dan duk faɗin masarautar nan mutum biyu ne zasu iya dakatar dani daga aikata abin da nayi niyya." tana gama faɗa ta wuce ta wajen damɓasheshiyar kujerar da Fulani Babba take zaune, ƙirjin Fulani ne ya shiga bugawa ba ƙaƙƙautawa saboda fargabar abinda zata zaluƙo. Da sauri Maryo ta sa hannu ta riƙo hannun Fulani ta ɗaga ta daga kan kujerar, ganin haka yasa Maleek takawa zuwan gurin da niyyar janye ta, tana juyowa ta ce. "Hurmin ga ajiya na baku" Maleek duk yadda yaso ɗaga ƙafarsa ya ƙarasa gurin kasawa ya yi, Maryo ƙafa ɗaya tasa ta ture kujerar wata ƙwarangwal ɗin mage suka gani a tsugunne da alama da ranta aka ajiye ta agurin har ta mutu ta bushe a haka, Fulani Babba shiru tayi gumi na keto mata sai a lokacin Maryo ta kalli Maleek ta ce."Ku sake shi" Fulani da Baiwarta juyawa suka yi dan su dai basu ga kowa ba, amma sun tabbata bokan da ya bata sa'a to da makarai take aiki. Maleek ƙarasawa ya yi gurin ya ga busasshiyar magen nan, Maryo ta kalleshi ta ce. "Ganin buzu a masallaci ya isa tinkiya tayi karatun ta nutsu, idan wannan kawai bai hankaltar da ku ba akwai wasu ƙullin a gaba amma wannan da kanta zata kunce su, idan kuma tayi gaddama sai na tara mutanen garin nan sannan na kunce su da kaina." Ta juya tana kallan Fulani da gumi ya gama wanke mata fuska ta ce. "Na baki wunin yau ko ki samu Sarki Abdallah ki sanar da shi da iyalansa abin da kika aikata musu ko kuma na fallasaki da kaina hatta da mutuwar Mai babban Ɗaki" A firgice Fulani Babba ta ɗago tana kallan Maryo, Maryo tai mata murmushi ta ce. "Kina mamaki ne? Ai ni ginshiƙin dutse nake kowa yayi karo dani shi zai faɗi. Idan kin aiwatar da abin da na umarce ki akwai wani a gaba dan kinsan ƙullin naki da yawa." Maryo na gama faɗa ta wuce fuuuuu kamar zata tashi sama. Tana tafe Maleek na bin ta a baya kamar jela duk inda suka wuce sai dai kaga ana binsu da kallo, dan ma ba ƙaramin tsoron Maleek suke ji ba hakan yasa suna ganinsa kowa zai ci gaba da aikin da yake yi, sai sun wuce kaji ƙananan maganganu na tashi. Suna shiga sashen su Maryo ta shige ɗaki ta datse kofar duk yadda yaso ta buɗe haka ya ƙaraci tsaiwarsa ya bar gurin har sai da Bayin gurin suka fara fahimtar halin da suke ciki. Yana nan tsaye saƙo ya iso masa daga fadar Mai martaba, jiki a sanyaye ya wuce fadar dan yasan ba akan komai za'ayi masa wannan neman na gaggawa ba sai akan matarsa. Yana zuwa ya yi sallama cikin fadar ya shiga ya zaune daga cen gefen Sarki Abdallah, Maleek yace. "Allah ya taimakeka ance kana nema na" Sarki Abdallah ya numfasa yace. "Maleek mun aika kiranka ne ba dan komai ba sai dan muna ganin kamar akwai matsala tattare da iyalinka." Galadima da ke gefe ya gyaɗa kai, Maleek ya russuna yace. "Haka ne Ranka shi daɗe nima na fahimci haka, saboda na ga canje-caje daga yanayin mu'amalarmu da ita." Sarki Abdallah ya jinjina kai yace. "Dan haka ya zama wajibi a nema mata magani saboda gudun abin da kaje yazo, yanzu kana gani da ba'a kusa me kake tunani zai faru da Waziri" Maleek ya kai kallonsa ga Waziri da har lokacin da alama bai gama dawowa dai-dai ba. Maleek yace. "Insha Allah za'ayi yadda kace" Sarki Abdallah ya kuma gyara zama yace. "Abu na gaba da nake so da kai, ka yi bakin ƙoƙarinka wajen ganin ka hanata fitowa waje har sai ta samu lafiya." Maleek ya gyaɗa kai ya russuna cikin girmamawa yace. "Insha Allah ranka shi daɗe" daga haka Sarki Abdallah ya sallami Maleek sannan suka ci gaba da tattaunawa. Galadima ne ya kalli Takawa yace. "Allah ya taimake ka nifa lamarin yarinyar nan ina ganin kamar harda makarai" Waziri da ke gefe yace. "Wallahi babu wani makarai nina fi zargin aikota akayi kawai ta halakani" Sarki Abdallah yace. "Waziri bana tunanin wani zai turo Shukra ta kashe ka, saboda idan ta kashe ka ribar me zata samu tunda ita ba kowa gareta ba, nafi aminta da maganar Galadima saboda ga dukkan alamau akwai shafar jinnu a jikinta." Waziri da yake ganin kamar sun take gaskiya ne ya rufe baki cikin takaici. Sarki Abdallah ya kalli Galadima yace. "Galadima a nemo masu magunguna saboda a tari matsalar da wuri kar matsalar ta nemi gagarar kundila." Galadima ya amsa sannan suka ci gaba da tattaunawa Bayan kwana biyu zaman Maryo da Maleek ba wata matsala sai dai babu mai kula wani a tsakaninsu daga gaisuwa sai gaisuwa abin da yake haɗa su kenan, Fulani da farko ta so ta samu Sarki Abdallah da maganar amma da ta yi wani tunani sai ta barshi dan ra'ayin kanta saboda wani shiri da take ƙullawa. Da safiyar ranar Laraba Maleek ya tafi da Maryo ɗakin baya da aka tanada saboda masu magani anan zasu dinga dubata, suna zuwa Maryo ta nemi guri ta zauna tana ƙarewa Mai ganin kallo. Wani ɗan busasshen saurayi ne yana maƙale da jakarsa fa maganjɓi, zama ya yi ya fara ciro da kayan aikinsa. Daga cikin jakar yaga hayaƙi na fitowa lokaci ɗaya suka ga wuta ta kama Jakar, tana ƙoƙarin lasar Mai maganin. Maleek baya ya ja cikin ta'ajibi Maryo kallan Mai maganin ta yi ta ce. "Idan na kuma ganinka ƙafarka a gurin nan ba jakarka ba hatta kai kanka sai na ƙone ka." tun bata gama faɗa ba Mai maganin ya fice a guje ko waiwaye baya yi. Sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakin Abu da Saif dan bashi da abokiyar hira sama da Abu, itama kuma haka yanzu hatta shan iska idan zai fita sai ya nemi rakiyar Abu suna tafe suna hira har suje gurin da zasu je. Kamar kullin yauma Abu ce ta shirya cikin kayanta masu kyau, Fulani Zaliha ce ta bata kuɗin kayan kwalliya su jagira da gazal harda kuɗin kallabi saboda na Abu sun ɗan yi ƙaranci. Har ta fito tsakar gida Saif ya dakatar da ita suka tafi tare suna tafe suna hira, duk inda suka wuce a cikin gidan sai anyi gulmarsu saboda wasu har sun fara yi musu wata fassara, wasu suce soyayya suke wasu kuma suce shaƙuwa ce kawai kowa dai da abin da yake faɗa. Kai tsaye kasuwar rimi suka wuce Abu take ta siyayya har ta kammalla, wasu kayan Saifa ne yake riƙe mata wasu kuma ita take riƙewa. Kamar almara ta hango Maryo gaban wani me sayar da kayan ƙore da jigidar mata, sakin baki tayi da murnarta tana nunawa Saif ta ce. "Maryo! Yaushe kuka zo?" Saif yace. "Wace Maryo kuma" gurin da take nuna masa ya kalla hango ya yi tsaye itama su take kallo, nan take ya tsuke fuska Abu ta matsa zata ƙarasa gurin da sauri ya riƙe hannunta yana cewa. "Wallahi idan kika matsa daga nan sai ranki ya ɓaci" juyowa tayi ta kalleshi idanta cike da hawaye ta ce. "Maryo ce fa ƴar uwata" fisge hannu tayi da niyyar zuwa gurinta amma ga mamakinta sama ko ƙasa haka ta nemi Maryo ta rasa. _LITTAFIN ANY BAIWA CE NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [17/11/2021, 11:17] Ameera Adam🌚: 30... Kurɗawa ta dinga yi cikin mutane tana laluben Maryo haɗe da ambatar sunanta, tana gaba Saif yana biye da ita yana kiranta. Idanunta ne suka ciko da ƙwallah ganin har zuwa wannan lokacin babu Maryo babu alaminta, gefe tana tana zubda hawaye ta ce. "Maryo ina kika shiga ne me yasa kika tafi ne?" Saif ya ƙaraso gurinta fuska a ɗaure yace. "Baza fa ki ganta ba." Abu ta goge ƙwallar idonta ta ce. "Saboda me?" Saif ya ɗaga kafaɗarsa alamun shima bai sani ba sannan yace. "Da tana so ki ganta da baza ta tafi ta barki ba kinga kuwa tana sani ta ɓoye miki, dama ke kika damu da ita ban da haka da ta damu dake bazata..." da sauri ta katse shi da cewar, "A'a wallahi akwai dalilinta na san ɓoye mini. Maryo ba yadda ka fassara ta take ba, na fi kowa sanin wacece ita amma..." Shima katse ta ya yi yana tsareta da dara-daran idanuwansa yana faɗin. "Wuce mu tafi ina ga ta fara yi miki gizo ne dan da ita ce a yadda kika faɗa kinga bazata tafi ba" Ganin zata ɓata musu lokaci yasa ya riƙo hannunta suka wuce tana tafe tana waiwaye, har sai da ya ga sun bar wajen kasuwar sannan ya sakar mata hannu. Har lokacin Abu hawaye take dan zuciyata taƙi aminta da cewar wai gizo Maryo take yi mata, suna ƙarasawa gida a gaggauce ta ƙarasa gurin Fulani Zaliha ta ajiye kayan da suka siyo kai tsaye ta wuce sashen Fulani Maryama. Sallama ɗauke a bakinta ta shiga sashe sai da ta fara shiga wurin Fulani Maryama ta gaisheta, sama-sama Fulani Maryama ta amsa fuska a tsuke ta ce. "Lafiya me kika zo yi a nan?" A ɗan duburburce Abu ta ce. "Dama nazo na gaishe da Inna ta ne." Fulani Maryama ta taɓe baki ta ce. "Ba fa koyaushe na fiye san a dinga yi mini zarya a sashe ba, dan haka ki kiyaye idan ba haka ba zan sa a dakatar da zuwanki." Abu ta russuna ta ce. "Za'a kiyaye Allah ya taimake ki." Fulani Maryama kamar ba za ta amasa ba sai kuma ta ce. "Ki gaggauta zuwa kiyi abin da ya kawo ki dan ina da abin da zansa ta tayi mini" Abu ta russuna ta miƙe ta godiya. Abu na shiga ɗakin Inna Habi ko kyakkyawar gaisuwa basu yi ba, cikin raɗa tace. "Inna wallahi na yau a bakin kasuwa naga Maryo wai kafin na ƙarasa na neme ta na rasa" zaro idanu waje Inna Habi tayi cikin zumuɗi ta ce. "Me yasa baki mata magana ba?" Abu hawaye ta fara yi tana bawa Inna Habi labarin yadda sukayi, jiki a sanayaye Inna Habi ta ce. "Abu kuma kina ganin maganar Saif bata hanya kuwa? Gani nake Maryo zata zo amma taƙi ƙarasowa gidan nan? Idan Maryo bata Adamawa ai da tuni munji labari daga gurin Takawa. Ina ganin yawan tunaninta ne yasa kika fara ganin tana miki gizo." Motsi suka ji daga bakin ƙofar Fulani Maryama da sauri Abu ta ce. "Inna sai anjima ni zan wuce dama cewa nai bayi nazo na gaishe ki" Baiwar Fulani Maryama ce ta ce. "Inna Habi Fulani ta ce kije ki matsa mata ƙafa." Inna Habi jiki na rawa ta ce. "To muje" Abu cikin tausayi ta kalli Mahaifiyarta tana jin tausayinta dan tabbas tasan bata jin daɗin zaman gurin Fulani Maryama, ta so ace ita take zaune a ɓangarenta Mahaifiyarta na sashen Fulani Zaliha amma babu yadda ta iya, jiki babu ƙwari kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Zuciyarta babu daɗi ta koma sashen Fulani Zaliha, tana shiga ta wuce kan katifarta ta kwanta tana tunanin halin da ƴar uwarta take ciki. Akan idanunta suka wuce suka tafi lokacin da take leƙensu tana daga wani ɗan lungu a ɓoye, lokacin da ta fito daga gurin da take ɓoye a dai-dai lokacin Saif ya juyo suna haɗa ido ya watsa mata harara hannunsa riƙe da na Abu, da sauri ta koma lungun ta ta jingina ta bango ƙirjinta na bugawa nan take taji wani abu na sukarta a zuciya, hawaye ne suka zubo mata saboda gabaɗaya rayuwar tayi mata zafi. Tana nan tsaye taji an dafa ta ta baya da sauri ta juya dan ganin wanda ya dafa ta, wata tsohuwa ta gani suna haɗa ido taji gabanta ya faɗi tsigar jikinta ta shi, ɗauke idanunta ta yi saboda bazata iya ci gaba da kallonta ba, tsohuwar ta katse mata tunani da cewar. "Ki ƙara haƙuri. A rayuwa dukkan tsanani yana tare da samu, da sannu ƙuncin rayuwa zai yaye miki ki dai karki cutar da kowa ki zauna da kowa lafiya, karki shiga haƙƙin wani ki riƙe Allah da manzansa indai kika riƙe wannan zaki ci ribar rayuwa." gyaɗa mata kai tayi ta sunkuyar da kai tana goge hawaye tana ɗago da kai ta nemi tsohuwar ta rasa, ba ƙaramin tsoro ta ji ba da sauri ta bar gurin jikinta har rawa yake saboda tashin hankali. Wannan karan tsoro ne ƙarara ya bayyana akan fuskar Maleek yana san ya yi mata magana yana tsoron kar shima wani abun ya same shi, daga waje wani Dogari ne ya leƙo yace. "Allah ya taumaki Yarima labari ya ishewa Takawa akan tafiyar mai maganin, yanzu haka akwai wani Sarkin wanzamai yana bakin ƙofa idan ka bada umarni a shigo da shi yanzu, Mai martaba yace shima zai jarraba tashi basirar." Maleek yawu ya haɗiya mai ɗaci dan shi kansa ƙarfin halin zama ya yi a ɗakin da take, ajiyar zuciya ya sauke yace, "Ba damuwa a ce ya shigo" yana gama faɗa suka haɗa idanu da Maryo lokaci ɗaya ta sakar masa murmushi wanda ya sa cikinsa murɗawa ba tare da yasan dalili ba, dan ya yi imani da Allah wannan murmushi da take yi ba lallai ya zame musu alkairi ba. Yana nan tsaye Mai maganin ya shigo hannunsa rataye da jakar wanzancinsa, Dattijo ne dan da alama zai yi shekara hamsin zuwa hamsin da biyar. Cikin girmamawa ya russuna ya gaida Maleek sannan ya kai dubansa ga Maryo da ke zaune a gefe ta harɗe ƙafafuwanta, suna haɗa ido ta miƙe ƙafafuwanta sannan ta ce masa. "Idan zaka iya zan baka wani aiki, nima ba hurumi na bane da na aiwatar da shi tun tuni." Wanzamin kallanta ya yi yana ƙarewa yanayinta kallo ya ɗan tsorata da yadda ya kalli yanayinta, cikin ƙarfin hali yace. "Wane aiki ne? Idan bai gagara ba na aiwatar da shi" Maryo a hankali ta tako ta ƙarasa gabansa, Maleek dake ƙoƙarin zama yana kallonsu cikin mamaki, dan ya yi tsammanin shima wutar zata saka masa. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta sa hannunta ta shafo hawayen idonta, hawayen ta dangwala a ƙasan tabarmin kaba. Nuna masa tayi ta ce, "Wannan abun nake son kaje ka tonr mini shi a fadar Daulatul Ujuran zan baka kyautar abubuwan da baka taɓa tsammani ba, zan baka sirrikan daga cikin irin ayyukanku, dan Allah wannan kaɗai zaka iya yi mini ka ceci rayuwata da ta Mijina." Maleek ido ya zuba musu dan shi dai babu abin da ya iya gani a gurin yana tabarmar gurin take haka yake kallanta, yana tsaka da tunani yaji Wanzamin yace, "Allah ya taimakeki wannan fa ba ƙaramin aiki bane, kuma maganar gaskiya nikam ina jin tsoro saboda kin ce kema ya gagareki, ina gudun halin da rayuwata da na iyalaina zamu shiga." Maryo ta share hawayenta ta ce, "Ba wai ya gagareni bane saboda ba zan iya ba, a'a kasan yadda ahalin Bidayatul jinn muke da kowanne irin rami. Da ace idan na shiga zan iya cimma burina babu yadda za'ayi na nemi agajin wata halitta, don Allah ka taimaka ka ceci muradin da aka jima ana ƙoƙarin cimma burinsa." Wanzamin sharce gumin kansa ya yi yace, "Gaskiya wannan aikin yafi ƙarfina haka zalika ni banma san ke zan yiwa magani ba, da babu abin da zai sa na zo gidan nan." Maryo ta miƙe ta koma gurin zamanta na farko ta ce, "Na baka lokaci kayi nazari dan na fahimci duk gidan nam babu wanda ya fahimci halin da nake ciki" Maleek idanu ya zura musu dan gabaɗaya kansa ya kulle, Wanzamin ya gyara zaman jakarsa sannan yace, "Ya kamata ki sanar da su dan su fita daga hurumin da ba nasu ba, wannan yaƙin naki ne ki daina tunanin wani zai iya taimaka miki idan ba haka ba bazaki taɓa nasara ba, ki bar tunanin zan iya yin wani abu akai domin kin fi kowa sani waye Zulik da mugun halinsa, matsawar yana raye bazai taɓa barin wani yaga wallensa ba. Ke kaɗai ce bazai iya cutarwa ba dan haka ke kike da yaƙin kuma kike da nasarar a hannunki." Maryo cikin gamsuwa da jawabinsa ta ce. "Alƙawari na ɗauka san raɗin kaina bazan waiwaye su ba, ba zan koma gurinsu ba har sai lokacin da suka fahimci cewar ni ba tasu bace, sai sun tabbatar da cewar kama da wane bata wane. Ina so su fahimci bambamcin dake tsakanin fari da fari-fari idan yaso dan kansu sai su yanke hukuncin da ya dace da kansu, amma ko da soyayyarsa zata kashe ni tabbas bazan taɓa kunyata baiwar Allah da ta taimaka mini a lokacin da bani da kowa ba, ta yi mini sutura a lokacin da nake tsirara ta maye mini gurbin uwa da uba a lokacin da nake marainiya gaba da baya." Wazamin ba ƙaramin tausayinta ya ji ba a hankali ya miƙe ya ɗauki jakarsa yace, "Zan yi ƙoƙarin na wayar da kansu akan su san halin da ake ciki har game da masu maganin da suke nema ido rufe, ina miki fatan nasara akan abin da kika sa a gaba." yana gaba faɗa ya zagaye ramin da ta nuna masa har ya kai bakin ƙofa ya juya ya ce mata, "Ki ƙoƙarin ɓatar da tasawirar ramin nan domin kinsan mugu bai da kama, bana fatana a ƙara miki wani ƙullin akan wani dan kinsan cikin gidannan ma maƙiyanki sunfi masoyanki yawa." ficewa ya yi daga ɗakin yana sauri kamar zai tashi sama. Maleek da ya jiƙu da mamaki ya kalli Maryo da ta ƙarasa bakin gurin da sa ɗigon hawayen tana shafe gurin da hannunta, bayan ta gama shafewa ta kai hannunta kan gashinta ta shafa akan gashinta ta ƙarasa yi tana girgiza kanta. Wanzamin na fita bai zame ko ina ba sai fadar Sarki Abdallah, yana shiga ya nemi guri ya russuna cikin girmamawa ya ƙara gaida Sarki sannan ya ɗan jim dan yanasan sanar da shi abin da zai ɗaure musu kai, sai dai bai san ta siffar da zasu karɓi maganar ta shi ba. Sarki Abdallah ne ya kalli yanayinsa ya kalli wasu Dogarawa ya umarce su da su basu guri, fadar ta rage daga Ciroma, Galadima sai Ɗan more. Sarki Abdallah yace. "Ɗan Wanzam ya ake ciki ina fatan jin nasara daga bakinka" Wanzamin ya gyara zama yace. Allah ya taimakeka ka gafarceni amma labarin ba me daɗi bane, kuma ina fatan wannan jawabin nawa zai warware wasu wasin da kuke ciki dangane da abin da na sani zan sanar da ku. Maganar gaskiya wannan yarinyat duk wani Mai magani da zaku kira sai dai yaci kuɗinku dan babu wata nasara da zai samu a kanta, shekaru goma da suka wuce akwai wani abokina wanda ya kasance yana daga cikin jinsin aljanu, ya bani labarinta dan haka zan sanar da ku idan kuna da buƙata." Sarki Abdallah mamaki ne ya kama shi ya kallai Wanzami ya gyaɗa kai, Wanzamin ya ci gaba da cewa. "Wasu dubannin shekaru da suka wuce..." Yanzu sai kuna hakuri wallahi sbd rashin wuta bana samun caji akai akai idan kun lura yawan typing ya ja baya ku karɓeshi yanda ya samu pls😥👏🏻 _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [19/11/2021, 19:26] Ameera Adam🌚: 31... SHEKARU DUBU ƊAYA DA ƊARI BIYAR BAYA Ƙorama ce mai cike da yalwar tsuntsaye da kala-kalar korayen ganyayyaki mabambamta, ban da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi a gurin sai tsirarin kukan hallitun dake cikin ƙarƙashin ruwa. Waɗannan kukan hallitu kaɗai sun isa zaburar ko tsoratar da duk wata hallitar bil'adama da tai gangancin halartar gurin, saboda tsari da yanayin gurin bai daidaitu da zubi da mazaunin hallitar da ta kasance Bil'adam ba. Ilahirin hankalinta ya tafi ga tunanin abin da yake faruwa dangane da makomar rayuwarta, a hankali take ɗaukan waɗansu irin duwatsu masu kama da ruwan zaiba tana jefawa a cikin ruwan, dukda a lokacin hawaye ne ke malala a saman fuskarta. A hankali ya tako ya ƙaraso gurinta cikin shauƙin so da ƙauna ya rungumota jikinsa ya fara yi mata magana cikin harshe yaren su na Jinnu. "Har bis kilman dilfaskinbat miladu war kibtinga rautiku filsin yaytarku lilbaitu wurgas yaftis gurman?" (Barka da hutawa Sarauniyar duniya shin akwai wani abu da bai yi miki daɗi ba dangane da zaman ki a gurin nan?" (AI MUN ƊAN TAƁA YARENSU KO😂) Hawayen idanuwanta ne suka ci gaba da malala kafin tayi wani yunƙuri yasa hannunda yana goge mata fuskarta yana cewa, "Zubar hawayenki dai-dai yake da zubar dalma a dandamalin zuciyata" a gaggauce ta ɗago tana kallonta dan ita kanta sheda ce dangane da abinda ya faɗa sai dai wannan jiginanniyar ƙaddarar ba lallai ta bar cikar burinsu ba, murya a sanyaye ta fara magana cikin irin yarensu na aljanu duk da kasancewarta cikin jinsin Bil'adam. "Ka mayar da ni gida kar su neme ni su rasa" hancin ta ya ja yace, "Idan sun tambayeki ai sai ki ce musu kina gurin mijinki" sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, "Kasan Kaka ya hanani daɗewa a gurin nan sabo da yana tsoron abin da kaje yazo, kafi kowa sanin yadda ƴan uwanka suka ɗauke ni basa sona basa ƙunata, ina tsoronma wata rana karsu fara farautar rayuwata, amma na kasa haƙurƙurtar da zuciyata akan soyayyarka me yasa? Meyasa bazasu duba irin soyayyar da mukewa juna ba?" A wannan karan kukanta ne ya tsananta saboda yadda kalaman suke fitowa daga ƙasan zuciyarta, rungumota ya yi yana lallashinta yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa. Sai da ya lura kukan nata ya fara tsagaitawa ya kalleta yace, "Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Ki daina kuka saboda hakan shi zai ƙara raunatar da tawa zuciyar, kin fi kowa sanin yadda nake ƙaunarki kuma bana tunanin ƙiyayyar da suke nuna miki zata iya tasiri a zamantakewar mu, kedai mu ci gaba da haƙuri wata rana sai labari." Da sauri ta fisge hannunta ta ce, "Har sai yaushe labarin zai zo ne sai yaushe zasu daina cin kashi a kaina yadda suka ga dama, dan Allah kayi wani abu mana me zai hana mu tafi wani gurin domin muyi rayuwarmu" sunkuyar da kai ya yi sannan ya ɗago da kai yana yi mata wani irin murmushi sannan yace, "Kinfi kowa sanin ni kaɗai Mahaifina ya mallaka kuma a yanzu yana cikin halin rashin lafiya, shin idan na tafi na barshi nayi masa adalci kenan?" Nine maganin masarauta Mahaifina yana da tarin ƴan uba kina ganin zasu kula da shi? A kan idonsa ma meye basa yi mana balle ace na tafi na barsu su biyu shi da Mahaifiyata." Cikin gamsuwa da kalamansa ta ce, "Tabbas hakane amma wannan shirun da kake yi a kodayaushe bazai fusshemu da komai ba." Murmushi ya yi mata yace, "Karki damu wata rana sai labari." gyaɗa masa kai tayi sannan ya sumbaci kumatunta, miƙewa ya yi yana riƙe da hannunta suka fara tafiya, suna gabda fita daga ƙoramara daga bayanta taji an fyaɗe ta tafi ta kifa ta faɗa kan cikinta, ƙara ta ƙwalla tana dafe baya cikin azaba, da sauri ya ƙarasa riƙeta Allah ya taimaka ma bata ji ciwo sosai ba, a hankali ta ɗago ta kalleshi suna haɗa ido ya wurga mata kallan tsana yana cewa. "Wannan cikin har abada bazaki haifeshi da sannu sai mun salwantar da ku gabaɗaya." Hawaye take yi a hankali ya ɗagata yana kaɗe mata kayan cikinta, faɗuwarta jinta ya yi har cikin jikinsa saindai babu yadda ya iya, hannunsa ya ɗora akan cikinta yace. "Ina fatan babu abin da ya shafi abin da yake cikinki" gyaɗa masa kai tayi tana sauke ajiyar zuciya. Ɗaukanta ya yi cak yace, "Rufe idonki" tun bai ƙarasa faɗa ba ta rufe saboda tasan gida zai mayar da ita. Tsaye yake da ita a cikin bukkar da babu komi a cikin sai gadon tabarmar kara da buzun damusa a shimfeɗe, kwantar da ita ya yi ta buɗe idonta, ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta yace ina tare da kai babu abin da zasu iya yi miki da ke da abim da yake cikinki" murmushi ta yi tana gyaɗa kai motsi suka ji daga baya, nan take Yace. "Ina zuwa." Yana gama faɗa ya zama gizagizo ya bi ta jikin bango ya koma cikin ragar da ta kasance mazauninsa, Kaka ne ya shigo ƙugunsa ɗauke da tafka-tafkan ganye waɗanda suka zame masa kamar makari ne na rufe al'aurarsa. Tsaye ya yi akanta yana ƙare mata kallo duk sai ya ji yanayinsa babu daɗi, dan gani yake duk wani abu da zai faru da ita kamar shine silar komai. Tsugunnawa ya yi yana kallon busassun hawayen idonta, a hankali ya fara yi mata magana cikin tausasawa, "Kyauta! Kiyi haƙuri" juyowa tayi idanunta na cikowa da ƙwalla bata tanka masa ba, ya russunar da kai ƙasa kamar me nazari ya ci gaba da cewa, har gobe bazan daina ganin kaina a matsayin mai laifi ba saboda ta silata ce kika faɗa cikin wannan halin da kika tsinci kanki, ka yafe mini dan na tabbata haƙƙinki bazai taɓa barina ba matasawar baki yafe mini ba" ɗagowa tayi tana kallonsa murya na rawa ta tashi zaune ta ce, "Kaka dan Allah ka daina faɗin haka kana sa ina jin babu daɗi a zuciyata. Na tabbata kayi haka ne ba dan komai ba sai dan ka sama mini gurbin da zan fi samun kwanciyar hankali, kasan duk duniya bani da kowa bayan kai. Kaine kaci kashi da fitsarina tun da ni da kai na saba bansan iyayena ba da kai na buɗi ido, na tabbata bazaka taba zaɓa mini abin da zai cutar da ni ba." Hawaye ya fara saboda ba ƙaramin daɗi yaji ba yadda Allah ya dasa mata tausayinta a zuciya, katse tunaninsa ta yi da cewar, "Kowanne abu da zai faru da bawa na tabbata yana daga cikin ƙaddararsa, ni wannan ita ce tawa ƙaddarar, ni kaina ina shiga cikin ɗimuwa da tashin hankali idan na tuna halin da jinina zai fuskanta idan babu ni" Tana zuwa nan a zancenta hawaye ya ci gaba da tsiyaya daga idanunta, Kaka shima hawayen yake cikin tausayawa a zuciyarsa yake jin inama a ce haka bata faru ba, me yasa ko kaɗam bai yi hangen abin da zai faru a gaba ba. Me yasa bai bari ta kai munzalin da zai yi shawara da ita ba? Waɗannan tambayoyin yake jerawa cikin zuciyarsa yana jin nadama da dana sani, kamar tasan abin da yake zuciyarsa ta ce, "Kaka banasan ka dinga jerawa zuciyarka tambayoyin da zasu saka cikin ɗimuwa da tashin hankali, Ka sani duk duniya bani da kowa sai kai" ta ɗan shiru tana jin zuciyarta na ƙara raunata sannan ta ci gaba da cewa, "Sai kuma Mirdad, ku kaɗai nake kalla naji daɗi, idan kuma wani abu ya faru da kai ya kake so nayi?" Goge hawayen idanunsa ya yi yace, "Na miki alƙawarin haka baza ta taɓa faruwa ba amma kema sai kin cire damuwar dake zuciyarki, kinsan fa ba ki kaɗai bace ko kina so ki jawa Jaririn da ke cikinki matsala, kina so ki haifo yarona yana tagumi?" murmushi tayi ta girgiza masa kai sannnan ya miƙe yace, "Amma ɗazu naga kamar bakya nan ina kika je" Ɗan duburburcewa ta yi ta ce, "Naje gurin Mirdad" ɗan canja fuska ya yi cikin damuwa yace, "Ki dinga hankali fa ina gudun kar su cutar da ke" Gyaɗa masa kai ta yi sannan ya fice daga cikin bukkar ya nufi bakin wutar da take ci kamar a maƙera. Zaune ya yi a bakin wutar ya ƙura mata ido yana kallo yana tunanin rayuwarsa ta baya da tushen mafarin shigar jikarsa cikin wannan matsala. ASALIN LABARIN KYAUTA Damina shine ainihin cikakken sunan Kaka asalinsa Maguzawa ne yana da Mata Dela dukkanninsu haifaffun garin Kano ne, iyayensu su Fatake ne wanda bincike bai tabbatar da asalin garin da suka fito ba, Mahaifin Damina dana Dele abokaine dan haka suka haɗa su aure. Damina ya taso da wata baiwa tun ranar da mahaifiyarsa ta fahimci tana ɗauke da cikinsa, a ranar da ta fahimci haka a ranar Bayan Mahaifinsa ya fita farauta Allah ya bashi nasara ya farauto wani ƙasurgumin Zaki wanda ya samu nasarar halakashi tun kafin ya kawo shi gida. Tun daga wannan ranar sai abubuwaa nasara ya dinga samunsa wanda basu taɓa tsammani ba, daga wannan lokacin sai suka fahimci Duk tinkiyar da shigo sashen Dela sai to babu jimawa zata samu ciki, kuma idan ta tashi haihuwa sai dai ta haifi ƴaƴa uku, huɗu har akwai wacce ta haifi ƴaƴa biyar. Lokaci ɗaya zance ya ƙaraɗe cikin ƙauyen Goron dutse cewar Dela na ɗauke da cikin Ɗan baiwa, tun daga wannan lokacin aka ɗinga ririta Dela hatta aikin gida bata yi akwai masu zuwa su yi mata, wannan magana ba iya nan kaɗai ta tsaya ba har sai da je kunnen Sarkin lokacin wato Sarkin Kano Rabo Juma Dogon gida, ba ƙaramin murna suka yi ba saboda a ganinsu sun samu Ɗan baiwa dan haka wasu al'amuran nasu zai zo da sauƙi. Akwana a tashi har Allah ya sauki Dela lafiya ranar da ta haifeshi kuwa aka wuni aka kwana ana tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, dan a wannan lokacin tun da damina ta kama ba'a taɓa tafka ruwa mai yawa kamar na ranar ba, hakan ne yasa suka saka masa suna Damina, kuma tun da aka haifeshi yaƙi kama Mama duk yadda aka bashi ƙi ya yi, dan a lokacin har Nonon akuya dana Saniya aka taso aka bashi amma yaƙi karɓa, sai ruwa suke bashi haka ya ci gaba da rayuwa.Damina yana girma harkokin baiwarsa na ƙara bunƙasa har ya kai shekara goma sha takwas, tun daga wannan lokacin yan garin suka mayar da shi wani babban jigo daga rayuwarsu, dan a lokacin ba dan sun bada ƙarfi wajen bautar Rana ba wasu daga cikinsu da tuni sun fara bautawa Damina, lokacin da ya kai shekara goma sha takwas dai-dai Aljanu suka faa buɗe masa ido, har suna taimaka masa wajen bayar da magunguna da warkar da marasa lafiya. Hakan ne yasa ya fara killace kansa a wata bukka da Mahaifinsa ya tanadar masa, wacce a cikinta ne ake kai masa ziyara yake bada magunguna, tun tana bayar da magani har mata suka fara kawo masa tayin buƙatarsu dangane da kishiyoyinsu, sannu a hankali Damina ya rukiɗe ya koma Boka dan duk abin da kake buƙata kana zuwa gurinsa zai sanar da kai abin da yake tafe da kai, kuma bazaka bar gurin ba sai da biyan buƙatarka. Ana cikin haka wata mata tazo da ƴarta nemar mata maganin farin jini tun da Damina ya ƙyalla ido yaji ta kwanta masa, wani garin magani ya basu akan tayi wanka da shi tun daga ranar yarinyar me suna Laraba ta kamu da mutuwar sansa, lokacin da iyayenta suka fahimci haka sai suka shiga ɗimuwa saboda a tunaninsu ta ɗauko Dala ba gamo, amma wani abun mamaki ana tararsa da maganar sai ya yi na'am da ita. Ba'a ɗauki lokaci me tsayi ba aka sha bikinsu Laraba ta tare a gidan iyayen Damina, bayan wani lokacin Laraba ta haihu ta haifi Ɗanta kyakkyawa namiji wanda suka saka masa suna Nomau, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Damina babu wurin da labarinsa bai karaɗe ba, ba iya garin kano ba har sassan garuruwan da ke makwabtaka da garin na Kano sun san da zaman Damina. Shekara Nomau goma a duniya iyayen Damina suka rasu tare da wasu daga cikin mutanen dake kusa da su sakamakon ambaliyar ruwan da ta same su. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Nomau ya cika shekara Ashirin da biyar cif a lokacin girma ya fara kama, Damina kuma a wanann lokacin aka yi wa Nomau aure da matarsa Tani, bayan bikin Nomau da Tani babu jimawa Damina ya nemi alfarma gurun abokinsa Ɗan sarkin fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa, sai da Aljanin ya gama jin buƙatar Damina sannan yace. "Buƙatarka da ci gaban baiwarka ga sauran zuri'arka zata cika matsawar ka yarjewa tawa buƙatar, nikuma na yi maka alƙawarin wannan taimako da muke yi maka kana bada magunguna zamu ci gaba da buɗewa zuri'arka haska tun daga kan Ɗanka Nomau har zuwa ƙarshen zuri'arka, amma da sharaɗin zaka bawa Ɗana auren abin da yake cikin sirikarta Tani." BARKA DA JUMA'A🤹🏻‍♀️ _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [21/11/2021, 16:24] Ameera Adam🌚: 32... Ban yi dogon tunani da nazarin abin da gaba zata haifar ba na amince da buƙatar Aljani Mardidas, ba ƙaramin daɗi Aljanin ya ji ba kuma tun daga ranar duk lokacin da zai ziyarce ni tare yake zuwa da Ɗansa me kimamin shekara goma a duniya wanda na yiwa alƙawarin jika ta, ni duk a tunanina hakan da na yi ne zai sa baiwar da nake da ita ta karkasu har zuwa kan zuri'ata ta ƙarshe, Sai dai wayo da dabarata sam basu tasirantu da abin da nayi tsammani ba, saboda lokacin da cikin Kyauta ya kai wata bakwai a lokacin ne Nomau ya kwanta wata gajeriyar jinya kuma be daɗe a kwance ba rai ya yi halinsa. A lokacin hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba saboda duk duniya Nomau kaɗai na mallaka a matsayin ɗana, ga shi sannu a hankali girma ya fara kamani. Fargaba ta ɗaya kada na tsufa na rasa madafar dafawa wannan hali da nake ciki yasa na nemi agajin abokina wato Mirdidas, lokacin da yaji bayanina ya tausaya mini matuƙa saboda duk kusan matsalarmu ɗaya da shi, shima Ɗansa ɗaya a duniya hakan ce ta sa ya kawo mini wata shawara wanda a lokaci nayi kasaƙe ina sauraronsa cikin yarensu na jinsin Jinnu, kasancewar idan na juya baki muna magana da shi sai ka rantse nima na fito daga cikin tsatsonsu ne. "Shawarar da nake ganin zata kawo maka mafita ba wata ce Damina illa ka tara mutanen garin nan tun da suna ɗaukar zancen fiye da tsammani, ka ce musu kayi harsashen za'a dinga samun hasara duk shekara dan haka bayan kowa ya yi noma, duk mutum ɗaya zai sauke maka buhun gero ɗaya, masara, da dawa ɗaya. Sannan ga waɗanda basa noma sai ka gindayawa muku su dinga kawo maka kayan sarrafawa, suma daga cikin ka zaɓi wani aiki da zasu dinga gudanar maka na ka,matarka da sirikarka. Sai dai ka gargaɗesu da cewar wannan kaya da zasu kawo maka zaka ajiye ne mu mutanenka mu dinga ɗauka saboda rabonmu ne, ga tabbatar musu da cewar ga duk wanda ya kuskurewa haka to tabbas annobar zata faɗa kansa. Haka zaka yi dan ka samu rayuwarka ta inganta cikin sauƙi, kuma ni nan zan taimaka maka akan duk mutumin da ya bijirewa umarninka." Ba ƙaramin jin daɗin jawabinsa na yi ba saboda ko kaɗan wannan dabarar bata zo mini ba, godiya nayi masa sannan muka yi sallama. Kamar yadda muka yi da Mirdidas haka na tara jama'ar gari na yi musu bayani dalla-dalla kamar gaske kuma duk cikinsu babu wanda ya misa mini, dan dama ko kaɗan ban kawo akwai wanda zai bijiremini ba duba da komai na faɗa musu yana faruwa kuma ina iya basu maganin warkar abun. Tun daga wannan lokacin abinci dai sai dai na bawa wani, dan abinci na wata shekara har tarar da na shekara baya yake yi, wannan shawara yasa na ƙara riƙe amini na hannu bibbiyu kuma amintakarmu ta ci gaba da tafiya lafiya kalau. Ranar Juma'a aka haifi kyauta kuma a ranar ne aka yiwa Abokina Mardidas naɗin sarauta dan haka murnar ta haɗe mana, an naɗa sa a matsayin Sarkin fararen alijun ƙarƙashin ƙasa, wato kujerar mulkin da mahaifinsa ya yi murabus ya bar masa. Wannan dalili yasa ya nemi alfarmar saka mata suna Kyauta saɓanin Jummai da muka yi niyyar saka mata. Haka yarinya ta taso gwanin birgewa da ban sha'awa kuma tun da aka haifeta koyaushe Mirdad na tare da ita, shi yake yi mata wasa da duk wasu abubuwan ɗebe kewa shi yake mata, har ɗaukanta yake yana kaita cen duniyarsu domin ta saba da yanayinsu tun da alƙawarine cewar matarsa ce halak malak, Shiyasa ko da Kyauta ta fara wayo bata damuwa idan ya tafi ita dan sai ta shafe kwana biyu har zuwa uku a gurinsu, sai dai su ajiyewa Uwarta me siffarta a zuwan ita ce, Shekarar Kyauta bakwai annobar amai da gudawa ta sauka a nahiyarmu hatta ni bata kyale ba, dan ba ƙaramar wahala na sha ba. Ta wannan sanadin ne akayi asarar rayuka masu yawa ciki harda Mahaifiyar Kyauta da me ɗakina, wannan mutuwar ba ƙaramin taɓani ta yi ba dan ba ƙaramin so da ƙyauna nake yi wa Laraba ba, babu yadda muka iya haka muka haƙura. Kyauta ta taso cikin gata da kulawa gaba da baya duk da kasancewarta marainiya amma tafi dubbanin masu iyaye gata, shekararta goma sha biyar aka sha bikinta da Mirdad. Sai dai dama tun kafin bikin take mini ƙorafin ƴan uwansa basa ƙaunarta, dan har akwai masu iƙirarin zasu kasheta, danma Mahaifin Mirdad wato Mardidas na tsaye tsayin daka yasa suke shakkun aikata mata wani abun, sai gori, tsangwama da wulaƙanci ba wanda bata sha. Dalilinsu na yin haka wai dan ta kasance jinsin bil'adam ce, kuma suna ganin irin fifikon da Mardidis yake yi akanta fiye da ƴaƴansu, saboda ba ƙaramin ƙaunarta yake yi ba sakamakon tsananin san da ɗansa yake yi mata. Kuma babban damuwarma so suke Mirdad ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴansu saboda jikansu samu damar ɗane karagar mulkin da kowa yake fatan ace jininsa ne akai, da farko bansan da wannan matsalolin ba har sai da fa fara zama a cikinsu take sanar dani halin da ake ciki. Abokina Mardidas na samu da maganar cikin jin kunyata ya bani haƙuri tare da nuna mini kawo ƙarshen matsalar cikin kwanaki ƙalilan, haka na kawo ido na sa amma ƙasan zuciyata babu daɗi duba da yanayin waɗanda take rayuwa da su amma babu abin da zan iya dan na lura a duk duniya idan aka cire ni babu wanda Kyauta take ƙauna kamar Mirdad. Mardidas ne ya tayarwa da ƴan uwansa da suke Uba ɗaya bore saboda dama shi kaɗai mahaifiyarsa ta haifa, ganin haka ya sa suka shirya masa zagon ƙasa da ƙulle-ƙullen makirci har ya kwanta wata irin jinya da ni kaina na kasa gano irinta, wannan dalili yasa shima ya yi murabus ya barwa Ɗansa Mirdad karagar mulkinsa wato mijin Kyauta, kuma anyi haka babu jimawa Kakan Mirdad mahaifin Mardidas ya mutu. Wannan ya ƙara wutar ƙiyayyarsu a zuciyar Kyauta dan dole ba dan ta so ba yasa ta haƙura da zaman cikin jinsun su saboda lamarin ya yi tsanani, sai dai wani abun ɗaure kai da ban mamaki kuma abin farinciki a gurina bayan na fahimci Kyauta na ɗauke da juna biyu, duk lokacin da wani daga cikinsu yayi niyyar cutar da ita, ko da bai aiwatar ba wannan abin da ya yi niyyar yi mata shi ba kuma sai abin ya faru da shi, wannan ne ya ɗan rage mini damuwa saboda na rage fargabar ko zasu cutar da ita, a gefe ɗaya kuma nake ƙara godewa Abokina Mardidas dan buƙatata ta biya tun da gashi jikata tana ɗauke da cikin ɗan baiwa kamar ni. Dalilin dawowarta gida gurina kuwa dan ta samu nutsuwa ne a matsayin da na me juna biyu, saboda ko da babu wani abu da zasu yi mata ya kamata ta samu hutu daga tarin baƙin cikin da suke ƙunsa mata. Daga ɓangaren abokina Mardidas tun ina samu na kai ziyara duba shi muna samu muyi magana da shi har ta kai ga ƴan uwansa na yi mini baraza da rayuwa ta, kuma a wannan lokacin hatta Ɗansa na cikinsa baya iya ganewa saboda zafin ciwo, wani abin farinciki da ko tunowa nayi da mutuwa ta bana jin fargaba yadda Mirdad yake tsananin ƙaunar Kyauta da bata kulawa nasan bana numfashi zai riƙe mini ita amana, tun da dai a duk duniya Kyauta bata da kowa sai ni sai kuma Mirdad, a gefe ɗaya kuma hankalina na matuƙar tashi idan na tuna kar ƴan uwan mahaifinsa su cutar da Mirdad kamar yadda suka cutar da Mahaifinsa, idan babu Mirdad babu niwace rayuwa Kyauta zata yi ita da abin da yake cikinta?" Amsar da Kaka ya kasa bawa kansa kenan sai ƙwallar dake tsiyaya daga idanunsa, wasu ƙarare ya ɗiba ya ƙara watsawa cikin wutar sannan ya miƙe a hankali yana takawa har ya koma cikin wata bukka dake kallon wacce kyauta take ciki. Bayan kwana biyu da faruwar wannan nazarin na Kaka ya fara wata irin rashin lafiya, a lokacin Hankalin kyauta ba ƙaramin tashi ya yi ba saboda tun da take bata taɓa ganin Kaka cikin wannan halin ba, ban da kuka babu abin da take yi. Danma Mardid na bata kulawa da yana ƙara kwantar mata da hankali akan damuwar da take ciki. Wata rana tana zaune a gefe Kaka yana fitar da numfashi da kyar gefe ɗaya Mardid ne yake kallansu cikin tausayawa, miƙa hannu ya yayi da sauri Kyauta ta miƙa hannuta cikin tafin nasa hannun. Miƙawa Mirdad ɗayan hannu ya yi shima ya miƙa masa nashi hannun, haɗa hannun Kyauta da na Mirdad ya yi yana runtse idonsa ya fara magana cikin ƙarfin hali, "Mirdad ga amanar Kyauta nan nikam tawa ta zo ƙarshe, ka kula min da ita amana da ita da abin da zaku haifa nan gaba, nasan da yadda ƴan uwanka suka ɗauki Kyauta sai dai nasan haɗuwarka da ita akwai wani ɓoyayyen al'amari, amma a kowanne hali kuke ka taimaka ka riƙe amanar dana baka, sannan ka isar yi mini da saƙo ga mahaifinka koda baya magana amma zai ji wannan wasiyyar da zan baka." wata sarƙa Kaka ya ciro daga wuyansa ya damƙawa Mirdad ya ci gaba da cewa. "Wannan sarƙar Mahaifinka ne ya taɓa bani ita sama da shekara tamanin, shi kasan har yau ya kasa sanar dani inda ya samo wannan sarƙar. Idan kaje karka bari wani yaji wasiyya ta ku kaɗaice daga kai sai Kyauta sai Mahaifinka, ka ɗora masa a ƙirjinsa kace ya yafe mini idan har wani abu ya taɓa haɗa mu mara daɗi, sannan wannan sarƙa ka mallakawa Kyauta ita halak malak ita ce kaɗai abin da zata dinga gani tana tunawa da ni. Ina ji a jikina Kyauta zata fuskanci jarrawabawa kala-kala, sai dai har numfashi ya fita daga jikina a ƙasan zuciyata zan yi ta yi miki fatan ɗaukaka akanki da abin da yake cikinki, duk abin da zaki gani kiyi haƙuri domin rayuwa bata zuwar maka yadda kake son ta kasance maka..." maganar Kaka ce ta katse nan take ya fara kakari da tari kafin su miƙa masa ruwa yace ga garinki nan. Kyauta wani irin kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciya nan take mara da bayanta ya amsa ta shiga murƙususu da alama naƙuda ce ta taso mata gadan-gadan. Kafin Mirdad ya yi wani yunƙuri sai jin kukan Jaririya ya yi ta faɗo, rasa yadda zai yi ya yi nan take wata dabara ta faɗo masa, shafe ganin gawar Kaka ya yi ga mutane yana gurgiza sai ga shi ya rikiɗa cikin siffar Kaka, da sauri ya fice ya nufi maƙotan bukkarsu ya sanar da wata tsohuwa halin da ake ciki, da murnarta ta ƙaraso tana yiwa Kaka barka duk a tunaninta Kaka ne, ta fara gyara Kyauta da ke tsugunne wanda har lokacin ban da kuka babu abin da take yi, musamman idan ta ɗaga ido ta kalli Mirdad dake cikin siffar Kaka wanda tasan ya yi haka ne dan ya kauda shakku a zuciyoyin mutanen da suke ma'amula da su Kaka. Lokacin da aka kwantar da Kyakkyawar Jaririyarta a gefen makwancin Kaka, duk abin da yake faruwa tsohuwar bata lura da gawar Kaka dake gefe ba saboda Mirdad ya kauda ganinta, Mirginawa Jariryar tayi tana mutsu-mutsu hannunta ya hau kan Sarkar da Kaka ya bawa Mirdad ya ajiyeta lokacin da zai kira tsohuwar, Kyauta dake gefe tabi Jaririyar da kallo, Mardid ne ya ƙarasa ya ɗauki yarinyar yana jin ƙaunarta a zuciya sai dai gefe ɗaya yana tausayin Kyauta, ɗaga ta sama ya yi bayan tsohuwar ta fice yace, "Barka da zuwa Muhaibish, tabbas harsashen Kaka da alama bazai tashi a banza ba" Kallan Kyauta ya yi da tai zuru tana kallansa ya ci gaba da cewa, "Kyauta kiyi haƙuri! Na saka mata suna Muahaibish ne saboda na lura mafi rinjayen hallitarta daga ɓangarena ne na jinsin Jinnu, akan idon kowanne bil'adam ne zai ganta a matsayin mutum amma sam ba haka bane." Mahaibish ta diro💃🏻 Su waye zasu biyo ni muje suna😜 _LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [22/11/2021, 15:13] Ameera Adam🌚: 33... A firgice Kyauta ta ɗago da kai tana kallon Mardid hawaye na ci gaba da tsiyaya kamar wacce ta shiga gasar kwaranyar hawaye, wani abu ne ya tsarga mata a tsakar kanta da wani dunƙulallen abu mai ɗaci da tsaya mata a zuciyarta, wannan ne karo na farko da Kyauta tana ji rashin jindaɗin zamantakewarta da Mardid, yanzu ace ƴarta ta cikinta wai ta tashi cikin jinsin aljanu. Mardid ganin yanayin Kyauta ya canja yasa ya tsugunna kusa da ita yana tallafo fuskarta da tayi ja saboda kukan da tasha yace, "Kyauta! Ko bakiji daɗin kasancewarta haka ba?" Ɗagowa ta yi ta kalleshi idanuwanta na ci gaba da hawaye ta girgiza kanta, tana cusa kanta cikin jikinsa tare da fashewa da matsanancin kuka. Runtse idanunsa ya yi yana jin kukanta har cikin zuciyarsa, hannu yasa ya fara bubbuga bayanta kamar yarinyar goye, har sai da ta tsagaita da kukan da take yi sannan ya saketa ya ci gaba da cewa, "Na yi miki alƙawari zan kula da ku na tabbatar bazaki yi maraicin Kaka ba" Gyaɗa masa kai tayi sannan ya sa hannu yana goge mata hawayen idonta yace, "Yanzu ki tashi ki fita ki sanar musu da mutuwar Kaka idan yaso bayan an binne shi sai mu koma cen Masarautarmu da zama" wannan karan tashin hankalinta ya bayyana ƙarara a saman fuskarta har sai da ta ɗan firfito da manyan idanuwanta, ya fahimci halin da take ciki ba ƙaramin tausayi ta bashi ba dan haka ya tattaro jarumta yace, "Karki damu na tabbata babu wani abu da zai faru daku ki kasance jaruma me jarumta karki bari raunin zuciyarki ya yi tasiri a gangar jikinki." Gyaɗa masa kai tayi tana ƙoƙarin ɗauke damuwar fuskarta wanda tsanani damuwar tata ya ƙaryata haka. Kallanta ya sake yi a karo na babu adadi yace, "Je ki kirawo su lokaci na ƙurewa" ya ƙarasa faɗa yana ɗaukar Sarƙar da Kaka ya bashi. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tana zubar da ƙwalla, ta fara sanar wa tsirarun mutanen da suke kewaye a wurin. Tsohuwar da ta gyara Kyauta lokaci ɗaya ta ƙaryata dan gani take wannan kamar wasan yara ne, amma suna tozali da gawar Kaka ba ƙaramin sanyi jikinsu ya yi ba, kuka suke sosai dan Kaka na da matuƙar muhimmanci a cikin rayuwarsu, musumman ga Dattawan da ke rayuwa a wurin, matasan yanki ne basu ɗaukake shi kamar yadda iyaye da kakanninsu suke kallansa ba, duba da lokacin da girma ya kamashi ya tarkata kayan aikinsa wuri ɗaya ya daina duk wasu taimako da yake yi musu na bada magunguna, idan ba gani ya yi mutum na cikin wani irin tsanani ba. Bayan an binne Kaka Mardid ya ɗauki Kyauta suka koma cen Masarautarsu ta fararen aljanu dake ƙarƙashin ƙasa, lokacin da suka shiga hannunsa rungume da Muhaibish Kyauta na miye da shi a baya gabanta sai faɗuwa yake. Yana shiga fadar ya gansu a tsaitsaye wasu na zaune sai dai ga dukkan alamu fuskarsu babu walwala wanda yake nuni da cewar suna cikin gagarumin ɓacin rai, dama ya tabbata sai sun ji labari tun kafin isorwarsu saboda yadda suke bibiyar rayuwarsu, Mardid jinin jikinsa yasha dan tabbas yanayinsu baya rasa nasaba da shi, Mardid ne ya gaishesu cikin girmamawa ganin yadda ya yi yasa Kyauta itama ta gaishe da su. Babu wanda ya tanka mata hasalima gabaɗaya a wurin uku ne suke zaune cikin siffar bil'adam, gabaɗaya sauran jama'ar wurin a rikiɗe suke cikin siffarsu da Jinnu. Wannan sam bai dame ta ba saboda ta yi sabo da ganin wannan hallitun nasu tun tana ƙarama amma wannan yanayin nasu ba ƙaramin razanar da ita ya yi, har sai da tsoronta ya bayyana a fili ƙarara. Mardid ne ya fara takawa wajen Yayan Mahaifinsa dake kwance cikin siffar dorinar ruwar da kan Jaki sai wasu tsili-tsili ƙafauwansa masu kama da ƙafafun zakaran hausa, yana zuwa ya miƙa masa Muhaibish cikin ladabi yace, "Kyauta ta haihu ga yarinyar na saka mata Suna Muhaibish, amma a gafarceni na yanke hukunci ba da saninku ba" A firgice ya ɗago yana kallonsa, wagegen bakinsa ya buɗe me matuƙar muni ya furta, "Muhaibish?" Gyaɗa masa kai Mardid ya yi a ƙufule Junduru ya miƙe yace, "Dole a canza sunan yarinyar nan bazai taɓa yuwuwa a kira ta da suna kamar wannan mai matuƙar muhimmanci ba" Kyauta da ke gefe da ba ta san ma'anar sunan ba amma ko da ba ta san me sunan yake nufi ba, ta fahinci sunan me muhimmanci da matuƙar amfani ne a gurinsu, dan ta tabbata da banzan suna ne baza su taɓa ƙorafi akai ba tun da ta san ba ƙaunarta suke ba, kuma ta san bazasu ƙaunaci abin da ya fito daga jikinta ba. Mardid ya kalli kawun nasa da tsananin mamaki yace, "Saboda me za'a canza sunan?" A hasaale Junduru yace, "Saboda sunan me tsarki ne dan haka bazamu yadda ka banzatar da sunan ga wata bil'adam cen mara galuhu ba, kuma kai kanka ka sani ba kowanne yaro ne yake cin wannan sunan rayuwarsa ta ɗore ba, ka sani kuskuren tsinuwa na bibiyar me sunan nan me yasa zaka janyo mana jafa'i cikin ahalinmu, ka san tarihin Muhaibish tun daga farko har ƙarshe. Ka karanta yadda Boka Bugudur ya kuskurewar bakinsa har ya tsine mata, kanasan tsinuwar bakinsa ta sauka akan ƴar ka ne? Ko kuma so kake tsinuwar ta waiwayo har cikin ahalinmu? Sam ba zai taɓa yuwu ba! Dole ma a canza mata suna" Mardid wannan hakan bai ɗaga masa hankali ba ya gyara tsayuwa yace, "Ina ji a jikina wannan Jaririyar bata daga cikin waɗanda Tsinuwar Boka Bugudur zata hau kanta, ina ji a jikina daban take da sauran ƴaƴa. Jarirai da dama sun rasa rayuwar su da dama wasu ma daga ranar da aka ambace su da Sunan Muhaibish kwana ɗaya basa ƙarawa suke mutuwa, amma wannan bazai karya mini gwiwa ba domin na tabbata akwai wani al'amari ɓoyayye dangane da rayuwarta, amma ka gafarceni Kawu idan maganata ta sosa maka rai" Ai kuwa kamar jira suke haka suka yo masa caaa kowa da abin da yake gaya masa, ban da zagin Kyauta babu abin da suke yi da aibanta ta. Ɗaukan ƴarsa ya yi ba tare da yace musu uffan ba ya riƙo hannu Kyauta da take kuka suka wuce cen sashensa. Suna shiga Kyauta ta saki kukan da take riƙewa tun daga cikin fadar ta su, kallanta ya yi yana jin wani irin babu daɗi aransa, janyo hannunta ya yi ya zaunar da ita yace, "Kiyi haƙuri! Dama nasan haka sai ta faru saboda ba ƙaunarmu suke ba" Kyauta ta kalleshi da jajayen idanuwanta ta ce, "Ka san da haka me yasa zaka saka mata sunan da zai zame mana matsala gabaɗaya, kana ji fa yace mutuwa yara suke itama so kake mu rasata, daga haihuwa ko zafin haihuwarta bai gama sakina ba? Wai ma wacece wannan Muhaibish ɗin da ambatar sunanta na ga duk ya firgita su, wacce irin tsinuwa ce Bokan ya yi mata, baka gudun tsinuwarsa ta shafi zuri'armu gabaɗaya? Gaskiya ka sauya mata suna saboda banasan na zama silar rabuwar kawunanku, gani zasu yi nice nake saka komai tun da dama ba ƙaunata suke ba." Yana gama sauraronta ya sakar mata wani lallausan murmushi kamar babu wani abu da yake damunsa sannan yace, "Ki kwanta ki huta kina buƙatar hutu saboda jikinki babu ƙwari" wani irin haushi ne ya kamata nan take hawaye ya ci gaba da shatata, kallansa ta yi ta ce, "Babu wata nutsuwa da zan iya samu matsawar baka sanar da ni ainihin waɗannan tambayoyin da nayi maka ba" Ganin da gaske take yasa yace, "Muhaibish wata shuɗaɗɗiyar shugabarmu ce, zamu iya kiranta ta uwarmu gabaɗaya a Jinsin Aljanu. Wani abun ta aikata wanda mu mun ɗauke shi a matsayin gagarumin abun kunya, ku kuma a jinsinku wannan abin da tayi ba komai bane. Hasali ƙiyayyar da ƴan uwana suke miki akwai wani ɓurɓushin dalili da suke kallo yasa suka ɗora miki wannan karan tsanar, wanda ya faru ne sanadin ƙaddarar Muhaibish. Macece da wannan tsayuwar tawa bazata wadatar da ni na baki ainihin labarin halayenta na gari ba, sai dai wani kuskure da ta aikata tsakaninta da jinsin bil'adam yasa Babban Bokanmu na wancen ƙaranin ya fusata har ya tsine mata, wannan tsinuwar ce take bibiyar duk wanda ya saka wa ƴarsa suna Muhaibish. Na san zakiyi mamaki yadda jarirai suke mutuwa amma ba'a daddara wasu suke ƙara saka sunanta, labarin me tsayin ne akwai ɓoyayyun al'amura dangane da ita. Sannan bayani ya gabace mu cewar za'a haifi Yarinyar da zata ci sunan Mahaibish matsawar ta haure kwana da wuni bayan raɗin sunan batare da ta mutu ba, wannan yarinyar ita zata kasance Muhaibish ta wannan ƙarnin, bazan ce miki komai akan baiwar da yarinyar zata taso da ita ba, matsawar ya kasance Muhaibish ɗinmu ce. Ina ji a jikina ita ɗin ce ma saboda mafarkan da na dinga yi a cikin bacci na, ki kwanta ki huta kina buƙatar hutu" Kyauta kamar wacce aka zarewa laka a jiki haka ta zaunn daɓas tana tunanin wannan rayuwa da zasu fuskanta. Tana shirin kwanciya ta ji dirowar tafkeken wani tsuntsu a tsakiyar bukkarsu me ɗauke da kawuna biyu, a razane Kyuta ta ja da baya Mardid ya haɗe fuska dan ganin yadda suke neman tsoratar da matarsa. Kafin ya yi wani yunƙuri Tsuntsun ya fara magana cikin harshen jinsin su, "Ka gaggauta fito da matarka domin gabatar mata da wankan al'ada na masu jego ita da ƴarta" ƙirjinsa ne ya buga har sai da yaji ƙafafuwansa suna neman kasa ɗaukansa, "Ta ya zasu ce agudanar mata da wankan al'ada bayan sun san ba jinsun su bace? Anya ba da biyu suka yi hakan ba tun da sun san ba za ta iya ɗauka ba?" Yana cikin tunani ya kuma riskar maganar tsuntsun yana ci gaba da cewa, "Idan kuka ɓata lokaci kasan hukuncinta" yana gama faɗa ya bi ta jikin bukkar ya fice. Ɗagowa tayi ta kalleshi dan bata fahimci wane irin wankan al'ada ne suke zancensa ba, tausayinta ne ya kamashi yana jin anya zai iya ci gaba da zama a cikin masarautarsu kuwa, tuno halin da Mahaifinsa yake ciki da wasiyyar da Kaka ya bashi ya yi, nan take hankalinsa ya ƙara tashi. Katse masa tunani tayi da cewar, "Mu je kiran da suke mana banasan ka ƙara laifi a wurinsu." Motsa bakinsa ya yi a sanyaye yace, "Kyauta ba za ki iya ba, sam ba za ki iya jurewa ba saboda ba al'adarku bace." Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo ta ce, "Ka daina tunanin akwai wani abu na daga al'adarku da zai gagareni tun da ni na amince zan iya zama da kai" Ta ƙarasa faɗa tana riƙe hannunsa suka nufi hanyar waje har lokacin hannunsa na rungume da Muhaibish. Suna fita cen farfajiyar masarautar cike gurin yake maza da mata manya da yara, wani fili aka zagaye wanda wata ƴar ƙoramace a tsakiyarsa. Ruwan jawur yake da wasu ɗaiɗaikun korayen furanni, gefe waɗansu irin duwatsun ne masu ruwan zaiba sai wani farin yashi da yake ta walƙiya yana ɗaukan ido. Kyauta da take jinta cikin ƙwarin gwiwa suna zuwa wurin taji gabanta na faɗuwa, karɓar Muhaibish Luliya tayi ta ɗaga sama sannan ta damƙi yashin ta birsine ta da shi gabaɗaya, kuka take tsalawa kamar ranta zai fita. Duk yadda Kyauta taso dakewa ji tayi ta kasa, cikin kuka ta kalli Mardid da ya sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Ka karɓo min ƴata wallahi kasheta za su yi" girgiza mata kai ya yi yace, "Babu abin da zai yi mata wannan kukan da take yi yana da nasaba da ɗigon jinsin jikinki, sai dai tsorona bansan yadda naki wankan zai kasance ba" Shiru tayi zuciyarta na bugawa tsakanin uwa da ɗa sai Allah, Kyauta ji take inama wankan yashin da suke wa Muhaibish ta karɓeshi ya dawo kanta. An ɗauki lokaci me tsawo ana yiwa Muhaibish wankan al'ada da kala-kalan kayan al'adarsu sannan aka kira Kyauta, tana zuwa da ƙarfin tsiya suka dannata cikin wannan ruwan ƙoramar, wata irin azababbiyar ƙara ta ƙwallah saboda azabar da ruwan yake yi mata a jiki. Jikinta ne ya fara sauya launi zuwa baƙi-baƙi nan take fatarta ta fara darewa. Mirdad na ganin haka ya bazama da gudu da niyyar ciro Kyauta da sauri ƴan uwansa suka shatalo shi suka danne shi suna cewa, "Yadda ake wa matanmu babu abu ɗaya da za'a raga mata." 😥Akwai tausayi wlh _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [23/11/2021, 18:54] Ameera Adam🌚: 34... Mardid da ƙarfi ya shiga fisgewa yana ambatar sunan Kyauta amma bahaushe yace, "Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi." Mardid yana ji yana gani haka Kyauta ta ci gaba da kwarara ihu wanda da alama tana yin sa ne ba tare da tana cikin hayyacin ta ba, Bayan an fito da ita daga cikin wannan ƴar ƙoramar jikinta gabaɗaya ya yi wani fatsi-fatsin baƙi ga fatar jikinta duk ta daddare, ko numfashi da ƙyar take sauke shi sabida wahala idanunta arufe suke jikinta duk ya saki kamar wacce babu sauran numfashi a jikinta. Kwantar da ita suka yi sannan suka ɗauko farin yashin nan suka fara fursuna mata a jikinta, a zabure ta miƙe ta zuba a guje cikin fitar hayyaci tana ta zabga gudu tare da kwarara ihu me ban tausayi. Gabaɗaya kallon gurin da tayi suka yi suna ƙyakyacewa da wata irin dariyar mugunta, Mardid na ganin haka ya zabura cikin ƙaraji yana kwalla ƙara tare da ambatar sunan Kyauta, suna hango ta har ta nufi wajen wani murgujejen dutse kai tsaye ta faɗa kai kanta ya bugu da dutsen ta faɗi cen gefe a sume kanta da hancin ta na zubda jiki. Ɗaya daga cikinsu suka ta sa da sauri ya je ya ɗaukota ya dawo da ita wurin da aka fara kwantar da ita, rirriƙe ta suka yi suka ci gaba da shafe mata jiki da farin yashi. Azabar zafin da ya ratsa cikin jikinta ne ya farfaɗo da ita daga dogon suman da tayi, a zabure ta miƙe wannan karan ko kuka ta kasa yi sai binsu take da wani irin kallo kamar mai taɓin hankali, wani garin koren ganye suka fara fesa mata nan take ta kuma kwanciya jikinta na wata irin karkarwa kamar me jin sanyi. Sai a lokacin suka saki Mardid wanda yake kwance a gurin rai a matuƙar ɓace, da gudu ya tafi gurin ta yana kururuwar kiran sunanta amma ko kallan gurin da yake bata yi ba saboda batasan ma abin da yake faruwa ba. A haukace ya ɗauketa be tsaya ko ina ba sai cen sashensa ya kwantar da ita, yana ƙare mata kallo da yadda jikinta ya saluɓe kamar wacce aka tsoma a cikin tafasashen ruwan zafi. Saboda tsabar firgice ya manta da Muhaibish da ke cen a hanunsu, hannuwansa ya kalla yaga fatar jikinta ce manne akan tafin hannunsa gurin da ya ɗauke ta, rushewa ya yi da kuka yana buga ƙasa tare da jin ƙiyayyar ƴan uwansa a zuciyarsa, sai dai yasan ko yana hauka bazai iya ja da su ba saboda sun fi ƙarfinsa. Ganin kukan bazai fissheshi ba yasa ya miƙe ya bazama tsinkar ganyayyakin da zai haɗa mata magani da shi, ya daɗe da fita sannan ya dawo ya fara murza ganyayyakin a cikin ruwa yana yayyafa mata. Wani irin gurnani take yi tana girgiza kanta, sai dai anci sa'a jikin nata ya daina karkarwa sai wani irin gumi da yake karyo mata, saboda yawan gumin har ɗiga yake a ƙasa kamar tsamowarta kenan daga ruwa. Yana nan zaune yana kallon halin da take ciki Ɗan ƙanin Mahaifinsa ya shigo hannunsa ɗauke da Muhaibish, a fusace Mardid ya karɓeta ya rungume yana kuma fashewa da matsanancin kuka. Kuka ta fara yi ya rasa yadda zai yi mata ruwa ya ɗauka ya bata ta sha sannan ya kwantar da ita ta ci gaba da bacci. Kyauta sai da ta kwana biyar a wannan halin batasan wanda yake kanta ba, a kwana na shida ne ta farfaɗo lokacin Mardid na tsugunne yana shafa mata maganuguna, suna haɗa ido daɗi ya kama shi har sai da yaji kamar ya rungumeta, sai dai da ya tuna raunin jikinta yasa ya sakar mata murmushi yana mata sannu. Bata amsa masa ba ta yunƙura ta tashi zaune tana bin jikinta da wani irin kallo, sai a lokacin komai ya dawo mata hawaye ta fara yi cikin sanyin murya Mardid yace, "Sannu ya jikin?" Sam bata ji me yace ba sai dai ta ga yana motsa baki, a hankali ta buɗe baki ta ce, "Ina Muhaibish?" Motsa baki ta ga ya yi sai kuma ta ga ya nuna mata cen gefe da ta hango ta tana bacci. Cikin damuwa ta ce masa, "Ni fa bana jin ka bana jin abin da kake faɗa naga dai kana motsa baki." Mardid ya zaro ido yace, "Kyauta bangane bakya ji na ba har yanzu bakya jin abin da nake faɗa?" Ganin ya daina motsa baki yasa Kyauta ta kuma cewa, "Ban san me ya samu kunnuwana ba amma banajin komai" daga wannan lokacin Kunnuwan Kyauta suka daina ji sai dai bakinta na magana, haka ta yi ta jinyar jikinta har ta warware. Haka rayuwa ta ci gaba da gudana cikin azabtarwa da tsangwama, har Muhaibish ta cika goma da haihuwa. Muhaibish ta taso kyakkyawa da ita gwanin birgewa, sai dai itama haka take rayuwarta koyaushe a jikin mahaifiyarta, sai a wannan lokacin ta tabbatar da maganar Mardid akan Muhaibish da yace mata sam ba jinsinta bace, dan ta ga ababuwan da take yi ne ta fahimci haka. Tun da dangin Mahaifinta suka fahimci ita ce Muhaibish ɗin wannan ƙarnin sai baƙin cikin duniya ya kama su, saboda a wannan lokacin da sun niyyar yi wa Kyauta, Mardid ko ita mugun abu tun kafin su aiwatar zai faru da su, a wannan lokacin haka suka dinga asarar rayuka saboda masu ayyana kashe Muhaibish su suka dinga mutuwa. Wanan yasa rayuwarsu ta ci gaba da tafiya cikin jindadi babu tsangwama bare fargabar azabtarwa. Wan Mahaifin Mardid satar jiki ya yi ya tafi cen ƙarshen duniya wurin wani tsohon Bokansu, nan take ya sanar masa buƙatarsa game da Muhaibish. Bokan numfawa ya yi yace, "Buƙata zata biya amma sai ka ziyarci kabarin Muhaibish ka ɗebo ƙasar kabarinta kana zuwa kar kayi magana da kowa ka watsawa ita wannan Muhaibish ɗin, idan ka yi haka duk wani kadarinta zai karye tana ji tana gani babu abinda zata iya aiwatarwa, wata ƙila tsinuwar Boka ta faɗa kanta. Amma akwai yuwar bayan wasu shekaru ruhinta ya wanzu a doron ƙasa, bana jin lokacin ma kana raye" Cikin jindaɗi ya amsa da cewar, "Zan aiwatar matuƙar buƙatata zata biya na ganin dukkansu sun wulaƙanta, ba damuwa ta bace dan sun dawo ko da har uwarta zasu dawo duniyar." Ya jima a wurin Boka suna tattaunawa sannan ya tashi ya nufi kabarin Muhaibish dake tsakiyar duniya a doron ƙasa. Cikin nasara Kawun Mardid ya samu nasarar ɗebo ƙasar kabarin Muhaibish, kamar yadda Boka ya sanar masa haka shima ya aiwatar. Yana watsawa Muhaibish ƙasar ta faɗin gurin a sume sai bayan wani lokaci ta farko, tun daga wannan lokacin Muhaibish ta zama mai matuƙar hakuri duk wata baiwarta ta gushe, haka suka ci gaba da azabtar da su Kyauta da ayyukan wahala da tare da al'adatunsu na jinsin Jinnu, musamman Kyauta da bata daga ciki jinsin su. Shekarar Muhaibish ashirin a duniya Kakanta ya rasu nan suka fara taƙaddamar wanda za'a ɗora, dan sun san muddin Mardid ya hau karagar mulki watarana ita zata mulkesu, sai dai babban tashin hakalinsu sun san ko me zasu yi basu isa su ɗora wani akai ba, tun da sun san duk wanda aka ɗora indai bashi ya cancanta ba a ranar yake mutuwa. Suna ji suna gani babu yadda suka iya haka suka ɗora Mardid akan karagar mulki tare da cin alwashin kawar da ita kafin mutuwarsa, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Muhaibish ta cika shekara ashirin da biyar ba tare ta yi aure ba, saboda gabaɗayansu babu wanda ya amince da haɗa iri da ita, kuma tun da Kyauta ta dawo rayuwar cikin jinsin jinnu bata ƙara hauro doron ƙasa ba, haka daga ɓangaren Muhaibish bata taɓa takowa doron ƙasa ba, tayi gabaɗaya rayuwarta ne a ƙarƙashin ƙasa. A wannan lokacin ne suka ƙara tsananta musu da iziya kala-kala har ta sanadin haka suka tsiyayewa Kyauta idanu ita kuma Muhaibish suka yanke mata hannuwa biyu, Mardid a wannan lokacin ne ya nemi ya yi musu bore amma sai suka nuna masa sam bazai yuwu ba, yana yunƙurin ɗaukan su Kyauta zuwa doron ƙasa suka kanainaye shi, su Muhaish da Kyauta suna tsaye haka suka dinga ciccire gaɓoɓin jikin Mardid gida-gida har yace ga garinku nan, Kyauta da lokacin girma ya fara kamata ban da kuka babu abin da take yi ita da Muhaibishi, saboda tun da taji ƴan uwansu sun fisgosu da ƙarfin tsiya sun fito da su jikinta ya bata akwai abinda zasu aikata musu mummuna, kuka take sosai da wannan ƙuncin rayuwar da suke fuska musamman da ta makance, tun da kafin makancewarta tana ganin abin da yake faruwa dan har maganar kurame suke da su Mardid, saɓanin yanzu da sai antaɓa jikinta take sanin yanayin da ake ciki, sai dai har zuwa wannan lokacin bakinta raɗau yake tana iya magana amma babu damar taji ko ta gani. Kyauta ce ta fara lalubar hannun Muhaibish, sarƙar da Kaka ya bata ta damƙa mata sannan ta fara lalubar kunne ta tayi mata raɗa, jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi saboda firgici da kuma yanayin tsufa. Tana gama yi mata raɗa ta fara hankaɗata tana cewa, "Maza ki tafi dan karsu illata ki kema nasan tabbas bazasu barmu ba" Yayan Mahaifin Mardid da sauri ya fisgo Kyauta ganin haka yasa Muhaibish tabi umarnin mahaifiyarta, da gudu ta juya ta nufi sashensu da sauri ta fara haƙa ƙasar gurin cikin hannuwanta na jinnu masu kama da gatari, sai da tayi haƙa sosai sannan ta tura sarƙar ta rufe sai kuma ta rushe da matsanancin kuka saboda tasan yadda suka kashe Mahaifinta itama da Mahaifiyarta bazasu barsu ba, miƙewa tsaye tayi ta buga ramin ta ƙarfi ta ce, "Ya ke Mahaifiya na san a wanan lokacin bakya numfashi amma na tabbata sai kin dawo domin ki ɗau sarƙarki tare da fansar abin da waɗancen azzaluman suka yi mana" tana gama faɗa ta juyo ta fiti daga gurin anan ta yi cikiɓus da ƴan uwan mahifin na ta da ƙarfin tsiya suka ɗauke ta suka kaita wajen ta gawar iyayenta suke. Tana zuwa ta sami Mahaifiyarta yashe a gefe kayan cikinta sun fito waye ga maƙogaronta shima sun fito da shi, a fusace ta juya gun Yayan mahaifinta da wasu jigajigai Biyar da suka fi tsananta musu ta fara kai musu duka cikin kuka, da ƙarfi suka fisgota suka danneta kallansu tayi tana huci ta ce, "Tabbas wannan abin da kuka aikata tamkar bashi ne na rantse da gawarwakin iyaye na sai na cimma buri da muradina akanku" Dariya suka bushe da ita sannan suka sa hannuwansu suka ɓara bakinta kamar yadda ake ɓare kan tinkiya bayan an yanka ta, wasu daga ciki kuma suka wara ƙafafuwanta suka raba ta gida biyu." Ɗan Wanzam ya ɗago da kai ya kalli Sarki Abdallah cikin ladabi yace, "Allah ya taimake ka kaji ainihin labarinta, kuma maganar da nake maka bana tunanin akwai wani mai magani da zai iya ja da ita. Cimma buri da muradi ne ya dawo da ita banajin zata ƙyale me yunƙurin yi mata karan tsaye." Sarki Abdallah ya yi murmushi yace, "Lallai Wanzan ka iya bada tatsuniya me daɗi dan ko a cikin littafan tatsuniyoyi ban taɓa cin karo da labari me ban ta'ajibi kamar wannan ba" Lamarin da ban tausayi😥 To fa mun dawo labari zamu ji yadda zata kasance mu kafta🤾🏻‍♀️ _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [25/11/2021, 18:56] Ameera Adam🌚: 35... Kamar wanda ya ga sabuwar hallita haka Ɗan Wanzam ya zubawa Sarki Abdallah Idanu sannan ya russunar da kai ƙasa, yana girgizawa kamar na ƙosasshen ƙadangare. Sauya fuska ya yi cikin damuwa yana ɗan jin haushin waɗannan kalamai na Sarki Aminullah, saboda yadda ya ɓata lokaci yana ta kwararo labarin kamar saukar ruwan sama. Amma ace wai duk wannan zantukan na shi sun tashi a banza, sake ɗago da kai ya yi yace, "Allah ya taimakeka ba zan tilasta amincewa da batu na ba, amma ina me bada shawara da abi lamarin yarinyar nan a sannu saboda gujewa hatsarin da baza'a yi saurin shawo kansa ba. Wani abu da na manta ban sanar da kai ba Ranka shi daɗe wannan masarautar da kake gani a cikinta ne Muhaibish suka yi rayuwa ita da iyayenta, ba wai ina nufin a doron ƙasa ba. A'a a dai-dai wannan gurin ta cikin ƙarƙashin ƙasa shuɗaɗɗiyar masarautarsu ta kasance. Allah ya baka yawan rai a wannan karan Muhaibish maganar mutum biyu kawai zata iya ji su dakatar da ita daga abin da tayi niyya, bansani ba suma ko sun ƙara dawowa ko kuma ita kaɗai ta dawo? Amma daga Mahaifiyarta Kyauta sai Mardid su kaɗai zasu iya dakatar da ita daga fitowar da tayi na cimma burinta, babban kuskuren da akayi kawo ta cikin masarautar nan, kuma bana tunanin akwai ƙaddarar da zata iya dakatar da ita. Allah ya taimake ka a dubi maganata da idanun basira, nan fada ce ban isa na faɗi abin da ba haka yake ba" Sarki Abdallah mutum ne me kafiya akan abin da yasa a gaba, dan haka ko da yaji wannan batu na Wanzam bai sa ko dai-dai da ƙwayar zarra yaji zuciyarsa ta sauya daga rashin gasgata Wanzan ɗin ba. Ɗan Wanzam ya gyara zaman Jakarsa sannan yace, "Allah ya baka yawan rai idan an sallame ni zan iya tafiya?" Sarki Abdallah ya bashi umarnin tafiya nan take kuma Wanzam ya maƙale jakarsa a hammata sannan ya yi godiya ga Takawa ya fice daga cikin fadar. Bayan fitowar Wanzam Maleek na rakuɓe jikin bango, haka kawai yaji tausayinta ya kama shi duk da ya rasa dalilin haka. Kallanta ya yi ya ga tana zubda ƙwalla , kansa ya dafe ya rasa ma ta ina zai fara yi mata magana, mamaki yake a ransa ta yadda Shukransa duk ta birkice lokaci ɗaya. Karo na farko kenan da yaji tsoronta ya fara ɗarsuwa a zuciyarsa, jiki a sanyaye ya ƙarasa gurinta ya miƙa hannu yana san taɓata sai dai yana jin tsoro. Tattaro jarumta ya yi yasa hannu ya taɓa tana faɗin, "Shukra" Ɗagowa tayi tana kallansa da manyan idanuwanta da suka rune jawur kamar gauta, lokaci ɗaya yaji ya ƙara shiga taitayinsa. Cikin inda-inda yace, "Me yake damunki?" Hawayen idanuwanta ne suka ziraro ƙirjinta na bugawa da ƙarfi sannan ta ce, "Shima yace bazai iya ba. Yanzu haka zaku barni da tabon abin da yake damuna?" Lumshe idanunsa ya yi ya ware su akan kyakkyawar fuskarta yana kallonta da alamar neman ƙarin bayani, sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta ce, "Babu damuwa zan aiwatar da kowane muradi da kaina bana neman taimakon kowa bare a nemi dakatar da ni a lokacin da nake tsaka da cimma burina." Tana gama ta miƙe tsaye ta fara takawa cikin izza da ƙasaita, bin ta ya yi da kallo baki a sake yana mamakin waɗannan bauɗaɗɗun kalamai na ta, daga kwanakin da tayi a cikin gidan yaci ace ya fara sabawa da waɗannan bauɗaɗɗun kalmomin nata, sai dai kodayaushe ta yi doguwar magana sai ya tsinci baƙin kalmomi, kamar wanda aka zarewa laka a jiki haka ya bi bayanta yana kiran sunanta, Maryo tafiya take kamar za ta tashi sama saboda sauri duk kiran da yake mata bata waiwayo ta kalleshi ba ballantana yasa ran zata bashi amsa. Tana shiga sashen su Bayi suka fara zubewa suna gaishe ta amma babu wacce ta kalla daga cikinsu, tana wucewa suka bi bayanta da kallo sannan suka fara yafitar junansu suna ƴan gulmammakinsu. Ƙarasowar Maleek ne yasa suka yi ɗif cikin yanayin rashin gaskiya suka fara yi masa barka da hutawa. Fuska a ɗaure ya kallesu ɗaya bayan ɗaya yace, "Ku fice daga sashen nan gabaɗaya bana buƙatarku har sai na neme ku..." tun bai ƙarasa maganar ba suka fara kama gabansu suna yi masa a fito lafiya. Lokacin da ya shiga ɗakin jiki a sanyaye ya fara kiran sunanta amma shiru yake ji kamar an aiki bawa garinsu, yana shiga uwar ɗakinsu ya sameta kwance a kan fado tayi ɗai-ɗai tana bacci har da minshari, ga wanda bai ga wucewar Maryo ba idan ya yi tozali da ita a yadda take baccin nan zai rantse da Allah ta shafe sama da awa guda tana bacci. Bacci take yi hankali kwance fuskarta tayi fayau sai dai rama da ya lura tayi, wuyanta ban da ƙashi babu komai ya lura ta yi haske amma gabaɗaya da alama bata cikin kwanciyar hankali, tausayinta ne ya kamashi ya ga jikinta duk ya wani ɗalli-ɗallin baƙi-baƙi, mayar da idanuwansa ya yi kan tafin hannuwansa da har wannan lokacin da taruwar jini a jikinsu, lokaci ɗaya damuwa ta mamaye zuciyarsa saboda sabuwar lalaurar da ke tattare da matarsa hasalima tunowa ya yi da irin wasannin da suke yi na soyayya shi da ita, amma sai ga shi yanzu ya taɓa mata hannu ma fargaba yake saboda gudun tsattsafowar jinin da ke fita daga jikinta, a ɓangaren sa kuma raɗaɗin ne yake damunsa daga baya kuma wurin ya yi taruwar jini. Gefenta ya koma ya kwanta babu jimawa shima bacci ya yi awon gaba da shi. Fulani Zaliha aikawa tayi a kira mata Abu saboda tun bayan dawowarsu bata ƙara saka ta a idanunta ba, da sallama ta shigo ɗakin cen ƙasa kusa da Fulani Zaliha ta zaune tana ƙaƙalo murmushi ta ce, "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Fulani Zaliha kallan tsaf ta yi mata ta ce, "Zainab lafiya na ga baki fito ba, kin manta kayanki a wurina ko akwai abin da yake damunki?" Kamar ta soso mata inda yake mata ƙaiƙaiyi hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta, dafa ta Fulani Zaliha ta yi tana kallonta don dama tun shigowarta ta fahimci tana cikim damuwa. Sai da tayi me isarta sannnan ta ɗago da kai ta ce, "Maryo na gani a bakin kasuwa kafin naje wurinta ta ɓace mini, na duba wurare amma babu ita babu alamunta." Fulani Zaliha cikin tausayawa ta ce, "Wace ce Maryo ɗin kuma a ina take?" Abu ta goge ƙwallar idonta ta ce, "Ƴar uwata ce da Ɗan ƙanwar Takawa ya tafi da ita a zuwan matarsa ce, ya tafi Adamawa da ita amma ɗazun nan na ganta. Kuma wallahi ba Matarsa bace hasalima Maryo bata taɓa aure ba tare muka taso a wurin Innarmu." Tana zuwa nan a zancen ta rushe da matsanancin kuka. Fulani Zaliha cikin rashin fahimta ta ce, "Bangane ba matarsa ba ce kuma ya tafi da ita? Kina nufin Maleek ɗan wajen Fulani Fahima da suka koma Adamawa?" Abu da sauri ta gyaɗa kai ta ci gaba da cewa, "Ni tsoro ma nake ji wallahi karta faɗa wani wurin, dan nasan kafiyar Maryo bazata taɓa dawowa gidan nan dan ra'ayin kanta ba, na tsaya zan nemo ta Yaya Saif ya janyo ni muka dawo wataƙila da na gano ta" Fulani Zaliha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "To Takawa yasan ba matarsa bace kuma ya barsu suka tafi da ita, wanne irin lamari ne wannan kamar ba a ƙasar musulmai ba" Cikin Abu ne ya kaɗa sai a lokacin ta lura da irin sakin bakin da tayi, tsoro ne ya kamata musamman da taji Fulani Zaliha ta fara faɗa tana cewa zata samu Takawa da maganar, a tsure Abu ta kalli Fulani Zaliha ta ce, "Allah ya taimake ki dan Allah karki cewa Takawa a bakina kika ji, ina jin tsoron hukuncin da zai yi mini. Amma wallahi ko Inna ta zaki kira ki tambaya zata gaya miki Maryo ba matarsa bace, ko aure ma ba'a taɓa yi mata ba" Jikin Fulani Zaliha sanyi ya yi haɗe da tausayinta, cikin zuciyarta take faɗin, "Wai Mai martaba me yake so ya zama ne, bayan rashin adalcin da yake nunawa har kuma da shiga haƙƙin aure da musulunci. Anya ya cancanci ci gaba da mulkar dubbanin al'umma da.." Abu ce ta katse mata tunani da cewa, "Dan Allah Ranki shi daɗe ki..." Ƙaƙalo murmushi Fulani Zaliha ta yi ta katse ta da cewa, "Karki damu Zainab babu abin da zai faru bazan sanar masa ba, kawai ina mamakin yadda lamarin ya kasance. Kiyi ta yi mata addu'a in sha Allah babu abin da zai faru da ita sai alheri." Abu ta amsa da, "Ameen" Fulani Zaliha sallame ta sannan ta faɗa duniyar tunani da cin alwashin dole ta tunkari Sarki Aminullah da wannan maganar. Yamutse fuska take kamar wacce tayi ta ci kashi, duk wanda ya kalli fuskar Jakadiya zai tabbatar tana cikin matsananciyar damuwa. Tana gabda shiga sashen Fulani Maryama suka yi karo da wata baiwa, da sauri ta dafe goshi tana zabga ruwan masifa, "Kai waɗannan yara dai tir da halinku jarababbu kuna tafe da kawuna a sama kamar raƙuma." Dije da take mulmula goshi ta ce, "Allah ya baki haƙuri Jakadiya ban san kin taho ba" A zafafe Jakadiya ta ce, "Ina zaki sane kina fama da ido yana karuwar akuya, wacce uwar kika ƙunso kike sauri kamar sabon kwarto" Ƙunshe dariyarta Dije tayi dan sun lura kwana biyu Jakadiya acikin masifa take, tana shirin bata amsa Jakadiya ta ce, "Ba magana nake yi miki ba Dije? Idan Uwarki Laraba ce zaki yi banza da ita" Dije ta tsuke fuska ta ce, "Ke dai wayon zagi ne kawai ban da haka me na yi miki da zaki zageni, yanzu ka rama cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa. Haka kawai tsohuwa sai jaraba" tana gama faɗa ta bi ta gefen Jakadiya fuuuu ta wuce. Baki a sake Jakadiya ta bi ta da kallo tana tafa hannu ta ce, "Biri ya yi kama da mutum. Wallahi ba banza ba wannan yarinyar sai mun binkiceta dan naji har wari-warin maza take, ban da haka har ni zata gayawa haka bari na shiga na fito dole mu zauna da Laraba mu lalube ta tass." tana gama faɗa ta shige ciki. Zaune ta samu Fulani Maryama da alama itama tana cikin damuwa, bayan sun gaisa Jakadiya ta saluɓe ɗankwalin kanta ta ce, "Maryama anya Marduska ba aljabu yake turowa suna kankarar naman kaina ba, dubi ki ga wani ɓamɓori kullin ta Allah idan na cire ɗankwalina sai na karkaɗe wannan farin garin, ina gudin a wayi gari aga kaina ya marmashe tass" Jakadiya ta faɗa cikin damuwa. Fulani Maryama bata tanka mata ba itama ta fisge ɗankwalin kanta sai ga wani irin farin gari na marmashewa. Jakadiya dafe ƙirji tayi ta ce, "Maryama! Yoo ai nawa shafar mai ne a haka kike zuwa shimfiɗar takawa gari na zuba? Wai ma kuwa ya kuka ƙare da takawa nasan dai har yanzu ba'a ce bai shafo hallitar kanki ya ji yadda kanki ya koma ba" Juye-juye yake ga gumi yana tsattsafo masa ta ko'ina, firgigit ya farga daga mummunan Mafarkin da yake yi bakinsa ɗauke da Addu'a. Kallanta ya yi har yanzu bacci take miƙewa ya yi jiki ba kuzari ya faɗa banɗaki ya ɗauro alawa zai wuce masallaci, har yaje bakin ƙofa ya dawo ya fara bubbuga fulonta yana tashinta, ganin bata tashi ba har zai iya rasa jam'i yasa ya fice da niyyar idan ya dawo ya tashe ta. Fitarsa harabar gidan ya hangi taron jama'a zagaye a wurin kamar zai wuce sai ya hangi Ƙaninsa Sulaiman, yafito shi ya yi da hannun alamun yazo nan take ya ƙaraso wurinsa. Maleek ya tambayashi, "Me yake faruwa ne naga mutane da yawa.?" Mamakin fuskar Sulaiman ne ya ƙaru, ya juya yana nuna masa wurin sannan yace, "Yaya Me babban ɗaki aka gani zaune a wurin" Wani kallo Maleek ya wurga masa yace, "Baka da hankali, shirmen naku har kan Mai babban ɗaki shekarar baiwar Allahr nawa ta rasuwa ina jin tun baka da wayo ta rasu ka ce mana ita ka gani a zaune, ya akayi ka santa?" Sulaiman yace, "Wallahi da gaske haka naji su Baba Ciroma suna faɗa..." Maleek bai gama jin maganar Sulaiman ba ya hango Mahaifinsa da wata tawaga sun nufi hanyar da mutane ke tsaitsaye. Ina muku fatan alheri🥰 Mu haɗe a comments🤾🏻‍♀️ LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KI ACOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._