ƁOYAYYAR MANUFA ©️Maimuna Tijjani Iyam Bismillahir rahamanir rahim da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, maƙagin rayuwata. Wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da aron numfashin da ya bani na rubuta wannan littafin na ƁOYAYYAR MANUFA. Bayan kammala littafin MATAN AREWA. Ina roƙon Allah da ya tsare mini hannayena, wajen rubuta abinda zai zamu cutar ga al'ummar musulmai tare da tarbiyar su. Page 0️⃣1️⃣ _______________________________________ Fizgar da aka yi wa hanayena tamkar za'a tsinke su daga gangar jikina, ya sanya hankali da nutsuwata da suka yi ƙaura daga gare ni dawowa. Sai a lokacin na sama zarafin calla wani uban ƙara mai matuƙar sauti, dukan da aka rufe ni dashi ta ko'ina ya sanya sautin kukan nawan dishashewa. Jefar da aka yi da ni gefe guda ya tilasta mini runtse idanuna da jinin dake zuba daga goshina da na ke jin wani azabar zogi. Yana wanke mini fuskata, jin raɗaɗin da ya ratsa kwanyata shi ya tabbatar mini da cewar haƙata bata cimma ruwa ba. Fatan mutuwar da nayi wa kaina ubangijina dake da ikon sarrafa rayuwata bai amshe ta ba. "Kin cuce ni Aishatu na yi da-na-sanin auren ku da Abdul-hameed. Ashe ajalinsa ne yake zaune da ita". Zancen da suka yi dirar mikiya kenan a kunnuwana, da na gaza tantance takamanmen mamallakin muryar. Sai dai tabbas amon ba baƙuwa bane ga kunnuwana. Dishi dishi idanuna suke gane mini 'yan uwan mijina Abdul-hameed da suke tsaye cirko cirko a kaina babu alamar ranƙwafawa, tamkar sun haɗiye taɓarya. Na gaza kare kaina daga dukan da suka cigaba da yi mini, balle na sama yawun da zan sarrafa wajen furta kalaman kare kaina daga mummunar zargin da suke jifa na dashi. Cushewar da numfashi ya fara yi tare da maƙalewa a ƙirji ya sanya idanuna fara gano mini baƙin duhu yana gilmawa. Jiniyar motar 'yan sandan da na ji ya yi dai dai da tsananta bugun da ƙirjina yake yi a raunane. Surutai da koke koke suka ƙara karaɗe wajen kafin na ji an ɗago ni cak an dire ni akan ƙafafuna da suke rawa. Hannayena duka biyu aka sanyawa wani abu, da nake kyautata zatona cewar ma'aikatan tsaro ne suka sanya mini ankwa. Kamar yanda na ji wata murya tana faɗin"ga ta nan ita ce ta kashe shi". Da ƙarfin rabussamawati aka finciko ni kukan tagwayen 'ya'yana Ashraf da Arfat 'yan watanni takwas a duniya da na same su bayan na shafe shekara cur da watanni a gidan mijin, suka dira a kunnuwana. Da ya tursasa mini wartsakewa nan take. Jin sun ƙammame ni ya sanya ni sakin sakekken ajiyar zuciyar da ya tafiyar da kukan zucin da nake yi. Ina ji ina gani aka ɓanɓare su daga jikina ni kuma aka jawo ni izuwa waje. Maƙil ƙofar gidan yake da mutanen da suke yi mini tofin ala tsine tare da Allah wadarai da halina. Kukan da ya zo mini da ƙarfin gaske da kuma jan dogon numfashin da nayi, ya yi dai dai da lokacin da na daina fahimtar komai. Saboda daina bugun da ƙirjina ya yi. Sai buɗe ido na yi na gan ni kwance cikin wani ɗakin da na ƙarewa kallon tsaf. Tabbas asibiti ne ga kuma ƙarin ruwa a maƙale a hannuna. Kuka na fashe dashi mai tsuma zuciya fahimtar da na yi cewar tabbas har yanzu ina raye cikin duniyar da ƙunci da halin ƙaƙayi kayi suke yi mini dabaibayi, yunkurar da na yi da nufin tashi zaune na ji kamar an riƙe mini hannuna ɗaya. Shi ya sa ni kai dubana izuwa ɓangaren, ankwa ne saƙale a hannun a saka a cikin gadon da nake kwance a kai. Dole na koma na kwanta don izuwa yanzu na rasa ƙarfin tashin, tuna abubuwan da suka wakana da nake jin wanzuwar su tamkar a cikin mafarki ya sanya kaina sarawa. "Innalillahi wa inna ilaihir". Shi kaɗai bakina ya yi nasarar furtawa ina cije leɓena, wata irin ƙaddara ce wannan ta gilma a cikin rayuwata?. Tare da rushe duk wani gini da foundation ɗin da na yi, wajen ganin inganta rayuwar aurena da ta 'ya'yana masu tasowa. Hannuna da aka sanyawa ƙarin ruwan na ƙurawa idanu, raina a jagule wai da wannan hannun na yi amfani wajen daɓawa Abdul-hameed wuƙar da ta yi sanadin rayuwarsa. Kaicona! Tabbas na yi saƙa da mungun zare. Na yi saurin rufe idanuna da yake gano mini Abdul-hameed kwance cikin jini. Na daɗe cikin wannan yanayin har izuwa lokacin da aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo, maza ne biyu ɗaya sanye da rigar likitoci ɗayan kuma cikin cikakken shirgar 'ya sanda. Duba ni likitan ya yi sannan ya juya haɗe da faɗin"za ku iya tafiya da ita tunda ta farka". Take na ji kaina ya juya na daina fahimtar komai, har wata ma'aikaciyar 'yan sanda ta shigo. Ta since mini ankwan ta riƙo ni muka fice daga ɗakin. Duk da idanuna suna ƙasa amma tabbas ina ji a jikina irin kallon da jama'ar wajen suke bi na dashi har aka shiga dani motar 'yan sandan muka bar cikin harabar asibitin. Tunda na shiga cikin motar hawaye suke kwaranya daga idanuna, zuciyata na yi mini wani irin zogi da suya. So na ke na sama ƙwarin gwiwar tabbatarwa kaina cewar a zahiri abubuwan da nake kallon su tamkar mafarki suke faruwa. A ofishin 'yan sandan da ya cika da ma'aikatan gidan jaridu motar ta tsaya aka fito dani, tunin suka yi mini rubdugu tare da jefo mini tambayoyi wani na bin wani. "Me za ki iya cewa akan zargin kashe mijinki da ake yi miki?". Tambayar da na ji ta har cikin kwanyata daga bakin ɗaya daga cikin 'yan jaridun kenan. Ma'aikatan tsaron suka hana su ƙarisowa gare ni tare da shigar da ni cikin ofishin. Mahaifiyata tare da yayyena maza biyu Hamma Abubakar da Hamma Adnan idanuna suka yi tozali da su tsaye a cikin ofishin. Muna haɗa ido na ji wasu hawayen masu ɗumi su na fareti a bisa dandamalin fuskata. Fuskar Ummata ta kumbura tsimtim, ga damuna da firgicin da ya bayyana ɓaro ɓaro a fuskokin su. Da sauri ta iso gare ni tare da tallafo fuskana tana faɗin" me yasa, me yasa?. Me yasa kika aikata wannan ɗanyen aikin?". "Umma wallahi ban aikata ba, ban kashe Abdul-hameed ba. Ku yarda da ni". Na faɗa cikin dushashewar muryata da bata fita sosai. Kafin ta kai ga furta mini wani kalmar wani ɗan sanda ya kaɗa ƙeyata izuwa cikin cell. Cikin kuka Umma ta zube akan gwiwoyinta haɗin da cewar"don Allah ku bar ni na yi magana da ita 'yata ce ƙwalli ɗaya jal". Cikin halin ko in kulawa da rashin tausayi ya furzo mata zancen da ya sanya duk gaɓoɓin jikin sakewa. "To tun wuri ma ki cire ta daga ranki ki manta da cewar kina da wata 'ya mai kamar ta. Domin wannan kam na tabbatar da cewar ana zuwa kotu, hukuncin kisa alkali zai yanke mata. Ku yi ta haihuwar 'ya'ya sakaka kamar fari ku ka sa basu tarbiyyar da ta dace su zo su zama annoba ga al'umma gabaɗaya. Da haihuwar irin wannan ai gwara ɓarin cikinta". Duk da babu abunda na fi buƙata a yanzu fiye da mutuwata, sai dai ganin yanda zancen nashi ya ƙara sanya Umma da 'yan uwana cikin wani tashin hankali. Na yi takaicin kasancewa ta a raye, nayi nadamar ganin wannan ranar a cikin rayuwata. Ranar da na jefa duk wani makusancina cikin mungun yanayi. Kalman na san ya sanya Umma yanke jiki ta faɗin a wajen sumammiya, ma'aikatan suka dakawa su Hamma Abubakar tsawa tare da umartar su da su ɗauke ta su fice daga wajen. Dole na zame nayi zaman 'yan bori dirshan a ƙasa. Izuwa yanzu na kasa yin hawayen ma sai kukan zuciya da nake yi. Kaina ya shiga sarawa tamkar zai rabe gidan biyu. Duniyar ta yi mini zafin da komai na cikinta ya gundure ni, jikina ya ɗauki rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki. "Ban kashe Abdul-hameed ba, ban kashe Abdul-hameed ba". Zancen da nake maimaitawa kenan a cikin zuciyata domin nauyin da bakina ya yi mini. Da nake jin ba zan iya furta ko kalma ɗaya ba, ban san iya tsawon lokacin da na ɗauka ina faɗin wannan kalmar ba. Har izuwa lokacin da aka buɗe cell ɗin, ban ɗago kaina ba sai dai na ji tsayiwar mutum a kaina. Na fita daga hayyacina sam babu nutsuwa a tare da ni tun ina furta cewar ba ni na kashe Abdul-hameed ba a cikin zuciyata har sautina ya fara fita. "Ki nutsu". Da sauri na ɗago kaina ina ƙarewa jami'in ɗan sandan dake tsaye a kaina, na ce"ba ni na kashe shi ba wallahi ban kashe shi ba". Bai ce dani komai ba sai da ya tsuguna akan ƙafafunsa a gabana sannan ya furta"na ji ba ke kika kashe shi ba, meye sunan ki?". Na sauƙe ajiyar zuciya" Abdul-hameed". Sai da ya ƙare mini kallon tsaf kana ya juya ga ma'aikacin dake bayan sa ya ce"a kai ta ta yi wanka, ta canza kaya sannan a bata abinci ta ci. Kafin nan ta dawo hayyacinta sai da amsa mana tambayoyinmu". "Ok sir". Ya furta cikin tsantsar biyayya tare suka fice sannan wata mace ta shigo. Ta kai ni na yi wanka sannan na canza kaya, abinci kam inda ta dosara mini shi ko kallon shi ban yi ba. Hawayena sun kafe ko ina kukan basa zuba, tabbas ina cikin tsaka mai wuya. Halin da mahaifiyata take ciki a yanzu shi ya fi ɗaga mini hankali fiye da makomar tawa rayuwar, domin ni kam na san shan ruwana ya ƙare a cikin wannan duniyar. Sai da dare ya tsala na ƙara shiga mawuyacin halin, tunanin yarana da abincin su yake zuba daga jikina ya tsaya mini a rai. Ko yanzu su na wani hali oho, ko sun ci ko basu ci ba duk ban da masaniya akan hakan. Sai da gari ya waye wannan ma'aikaciyar ta dawo, sai da ta gama jefa mini kallon tsana kafin ta soma yi mini magana a tsawace"yanda na ajiye abincin haka kika bar shi kenan?, in kin ci ma kanki ki ka yiwa ba wani ba. Munguwa kura da fatar akuya. Allah wadaran ki". "Ina so na yi salla". Tabbas na ga tsantsar mamaki a bisa fuskarta ta taɓe tare da faɗin"kin san da wanda za ki yiwa sallan, amma kika manta dashi a lokacin da zuciyarki take yi miki saƙa da mungun zare. Duk wanda ya kashe rai shima hukuncin kisa ne akan sa kin san da hakan?". Ban ce da ita ko kanzil ba har ta gama ta fita bayan ta tsirtar da wani tsaki mai dogon zangon. Waige waige na soma yi ko zan sama ƙasan da zan yi taimama dashi a cikin ɗakin, amma ban ga alamar sa ba dole na miƙe ina jin wani jiri yana ɗeba ta na zo jikin ƙarfe ɗakin da yake bani damar hango inda ma'aikatan suke tsatstsaye. Sai da na yi baki ya fi a irga sannan wani ya zo inda nake, tare da yi mini gargaɗi kar na ƙara damun su. Dai dai lokacin da wannan ma'aikacin ya shigo wajen duk suka miƙe suna sara masa cikin girmamawa. Ya tambayi dalilin tsayiwata a wajen suka sanar masa, take ya basu umarnin samar mini da ruwan alwala, hijabi da kuma sallaya. A zaune na yi sallan saboda bana iya miƙewa akan ƙafata jiri yake mayar da ni ƙasa, na kasa furta komai illa rawar da bakina yake yi na ɗaga hannayena duka biyu sama. A hakan wannan ma'aikacin ɗan sandan ya shigo ya iske ni, duk tambayoyin da ya yi mini babu wanda na amsa domin ba na jin ko na yi yunƙurin amsa masa zan sama haɗin kai daga bakina wajen furta zancen dake zuciyata, ko zan rage zogin da nake ji. Ganin ba zan iya amsawa ba ya tilasta masa ficewa daga ɗakin, haka na cigaba da zama na kwana na wuni a wajen kafin aka zo ka sanya mini ankwa a duka hannayena aka fito da ni izuwa wani ɗaki. Ina shiga na ga Umma da Hamma Adnan zaune, da gudu na isa gare ta na durƙusa a gabanta, tare da ɗaura kaina akan cinyarta. A hankali take bubbuga bayana hawayen da suke kwaranya daga koramar idanunta, suna sauƙa a bayan wuyana. "Aishatu". Ta furta kalmar sunana cikin karayar murya, a karo na farko da taɓa ƙirana da Aishatu kai tsaye babu sakayawar da ta saba. Ban iya amsa mata ba saboda kukan da ya ci ƙarfina. Ta cigaba da cewa"kowa sai faɗin albarkacin bakinsa yake yi akan ki, wasu sun ce kishi ne ya rufe miki ido kika ɗauki wannan hukuncin. Me yasa kika aikata haka?". Kukan na cigaba dashi da dukkan ƙarfina kafin na yi nasarar ɗauko kaina da ya yi mini nauyin gaske, na sauƙe rinannun idanuna akan fuskarta." Ban kashe shi ba ban kashe ba. Umma bai mutu ba fa. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u". Hamma Adnan ya furta yana dafe goshinsa, daga ni har Umma kuka muke babu mai lallashin wani. "Time up, lokacinku ya yi ku tashi ku fita". Ma'aikacin ɗan sandan dake tsaye a kan mu ya furta a zafafe tare da ƙirar wacce ta shigo da ni tazo ta maida ni. Da sauri na rarrafa gaban Hamma Adnan na ce" ina Baffa?". Kafin ya amsa mini har ta shigo ta ɗago ni zamu fice. Amsar da ya ba ni ya tsaya Ni tsayawa cak. "Ki yi haƙuri Baffa ya ce bai zai tako yazo inda kike ba". ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam Page 0⃣2⃣ ____________________________________ Har aka komar dani cikin cell ɗin ban san inda nake cilla ƙafafuna ba, ina shiga jiri ya makani da ƙasa. Na dafe ƙahon ƙirjina da yake bugawa a raunane, zuffa yana tsatstsafowa daga dukkan mafitar gashin dake jikina. Take numfashina ya fara yi sama sama, ina jin ƙirjina tamkar an ɗaura mini dutse tsabar nauyin da ya yi mini. A hankali na soma buɗe idanuna da suka yi mini nauyi ina motsa jikina da ya sake. Lumshe idanuna nayi hawaye suna bin gefe da gefen fuskana, ƙwaƙwalwata tana tariyo mini amsar da Hamma Adnan ya ba ni. Zuciyata ta ƙara karyewa. Rayuwar ya ƙara ficewa daga raina gabaɗaya tunda mahaifin da ya haife ni ma ya yanke mini wannan hukuncin ba tare da ya ji daga gare ni ba, to ina ga sauran al'ummar da nake rayuwa a cikin su?. Take zuciyata ta ayyana mini kawai na amshi abunda ake zargina dashi domin shi ne kawai mafita a gare ni. Sai da nayi kwana biyu a asibiti ƙarƙashin kulawar ma'aikatan lafiya da kuma jami'an tsaro, a rana na uku aka wuce dani kotu. Tun daga sauƙa na daga cikin motar 'yan sandan jama'a suka yi mini ca tamkar zasu cinye ni ɗanye. 'Yan jaridu kowa na san samun abun yaɗawa, sauran jama'a na yi mini tofin ala tsine da jifa na da munanan alkaba'i, sai da 'yan sandan suka kewaye ni daga dukan da mutane suke kawo mini sannan muka shiga cikin kotun. A tarihin rayuwata kaf ko ƙofar ofishin 'yan bijilanti ban taɓa zuwa ba, amma ƙaddara ya sa ni yau ni ce da kwanan ofishin 'yan sanda har da zuwa kotu. Maƙil kotun yake da jama'a bayan a nuna mini cikin inda zan tsaya, na soma rarraba idanu ko zan gano wani nawa. Can na gano Hamma Adnan da Hamma Abubakar sai kuma Baba Alhaji ƙanin Abbanmu da 'yansa Hamma Ahmad da Anwar su kenan waɗanda na sa ni cikin dandazon jama'ar da suka yi tururuwa a kotun. Ban hangi ko kare daga dangin Abdul-hameed ba. Magatakardar kotun ne ya tashi ya gabatar da shari'ar tare da miƙa wasu takardu ga Alkalin, sai da ya gyara zaman farin gilashin dake zaune akan karan hancinsa kana ya ce"lauyan gwamnati ya gabatar da kansa". Ya miƙe yana cewa"sunana barrister Adam Lawan lauyan gwamnati daga chamber na ɗari uku da ashirin da biyu, na gode ya mai girma mai shari'a". Sai da Alkalin ya yi wasu rubuce rubuce kafin ya ɗago ya kuma faɗin"lauyan wacce ake zargi ya gabatar da kan shi". Babu wanda ya tashi da sunan kare ni hakan ya haifar ƙananun surutai. Sai da Alkalin ya tsawatar ta hanyar buga karamar gudumar dake hannunsa. "Ina lauyan da zai kare ki?". Ya jefo mini tambayar da ya sanya ni haɗiye wani miyau mai kauri daga maƙoshina da ya bushe, tamkar tafkin da ƙasa ya tsotse ruwan cikinsa. A sanyaye na furta "ya mai girma mai shari'a ba ni da lauya". Shuru ya biyo bayan zancena na tsawon daƙiƙu kafin ya furta"sakamakon rashin lauya daga ɓangaren wacce ake ƙara, an ɗaga wannan shari'ar zuwa ashirin da takwas ga watan afrilun shekaran dubu biyu da ashirin da huɗu". Yana dasa aya ya buga gudumar kowa ya miƙe, sai da ya fita ta wani ƙofa sannan mutane suka fara fita. Aka sa mini ankwa aka tisa ƙeyata. Har yanzu harabar kotun a cike yake da jama'a, su Hamma Abubakar suna tsaye suna jiran fitowata. Suka iso gare ni da hanzari. "Ki yi haƙuri kin ji ki ta addu'a, in sha Allah zamu sama lauya kafin zama na gaba". Furcin Baba Alhaji ke nan yayin da za'a tusa ni a cikin motar na yi saurin riƙe hannun Anwar gam ina sakin wani kuka marar sauti. Suma kukan suke yi Baba Alhaji yana lallashin mu, haka aka sanya ni cikin motar ina hangen su har suka ɓacewa ganina. Ba'a mayar da ni ofishin 'yan sanda ba aka wuce da ni gidan ajiye ɗaurarru. Na ci kuka tamkar raina zai fita na rasa inda zan sanya raina na ji sanyi, kwana huɗu cur a wajen babu wanda yake zuwa inda nake sai 'yan sandan da suke kawo mini abinci da kuma ruwar yin alwala. Ina takure a ƙurriyar ɗakin na kifa kaina a bisa gwiwoyina, tunanin lokutan da muka ƙarar tare da Abdul-hameed na nunawa juna so da tattali suna ziyartar kwanyata. Zuciyata ta kasa yarda da cewar ya mutu gani nake yi kamar da zarar na fita daga nan zan same shi cikin ƙoshin lafiya. "Ke taso kina da baƙi". Na ji a furta da muryar da sai da kaina ya sara, jikina babu ƙwari na miƙe domin tun bayan faruwar lamarin nan ban sanya koda ƙwayar abinci a cikin cikina ba illa ruwan da nake kurɓa inda zan yi alwala. Kamar bugaggiya haka na fito ina haɗa kaya izuwa wani ɗaki mai ɗauke da kujerun zama guda huɗu, Hamma Abubakar da Hamma Ahmad da wani mutum sai kuma ɗan sandan dake zaune su kenan a cikin ɗakin na ƙarisa na zauna. Hawaye yana gudu a fuskana na furta" ina Umma?". Ina ina jiyo sakekken ajiyar zuciyar da ya saka a ƙoƙarin ɓoye damuwar dake kan fuskarsa ya ce"tana gida kuma ta ce a gaishe ki". Idanu na ƙura masa don fuskarsa ta bayyanar da gaskiyar da ya ɓoye cikin furcinsa, ya gyara zamansa yana fuskanto ni sosai"wannan abokina ne barrister ne sunansa Aliyu, shine wanda zai taimaka mana akan case ɗinki kar ki ɓoye masa komai ki sanar dashi iya gaskiyarki kin ji?". Kaina na ɗaga masa" da gaske ne Abdul-hameed ya mutu da gaske ne? Wai ni na kashe shi?. Idanunsa taf da ƙwalla sai dai juriya da taurin rai irin nashi ya hana su tsiyaya, cikin sigar son kwantar mini da hankali ya ce"ai kowa jiran lokaci yake yi, duk wanda lokacinsa ya yi dole zai mutu". Yana gama faɗin haka ya tashi da sauri ya fice daga ɗakin Hamma Ahmad yana rufa masa baya, da kallo na bi shi har ya maido da ƙofar ya rufe. "Aishatu". Na ji barristern ya furta da hakan ya sanya ni kai dubana gare shi sannan na rusunar da idanuna. Me ya hana Umma zuwa kotu?, Abdul-hameed yana raye ko kuma da gaske na kashe shi?, meye dalilin ƙwallar idanun Hamma Abubakar?. Menene yake ɓoye wanda ban sa ni ba?. Jerin gwanon tambayoyin da na jefa wa kai kenan da na gaza cimma amsoshin su. Har izuwa lokacin da barristern ya katse mini hanzari ta hanyar faɗin"Abubakar ya sanar da ni wasu abubuwa game dake, amma zan so ki in ji daga bakinki wani yaya auren ku da Abdul-hameed ya kasance?".. Zazzafan iska na furzar daga bakina kana na sama zarafin cewa "an ce ni na kashe shi kuma nima kashe ni za'a yi". Da sauri ya tari numfashina"bincike ne zai tabbatar da ke ce ko kuma saɓanin hakan, hakan zai yiyuwa ne kawai idan kin bani haɗin kai wajen amsa tambayoyin da zan miki kin ji?". Kaina na ɗaga masa alamar na ji sannan ya ƙara maimaita mini tambayar a karo na biyu. Dogon numfashi na ja na fesar ina jin dukkan abubuwan da suka wakana cikin rayuwata, ya na dawo mini sabo bil a idanuna. Alhaji Ahmadu Sanda shine cikakken sunan mahaifinmu, asalinmu fulani ne usul da aka san su da kara da kuma alkunya, kafin kasuwanci ya sanya iyayenmu baro mahaifarsu. Mahaifinmu da muke ƙira da Baffa mutum me tsananin zafi da kuma tsayawa akan ra'ayinsa komai wuya komai runtsi. Su biyu iyayen su suka haifa shi da ƙaninsa Baba Alhaji, tun kafin samuwar mu 'ya'yansu suka ƙudurce a ransu cewar aure haɗi zasu yiwa 'ya'yansu, domin ɗaurewar zumunci koda bayan ransu. Hamma Abubakar ne babban gidanmu da ya gado zafi da tsananin Baffa, sannan Hamma Adnan da yake da sauƙin hali da yawan mutane sun fi tsammanin ɗan Baba Alhaji ne. Saboda yanda ku san dukkanin halayya da ɗabi'unsu yake kwaf da kwaf, fiye ma da 'ya'yan da ya haifa a cikinsa ga son tsokala. A cikin 'ya'yansa Hamma Ahmad ne kawai suke kamanceceniyar ɗabi'u dashi. Ni ce auta kuma mace ɗaya tal a tsakanin 'yan uwana, na ci sunan kakata ta wajen Umma. Hakan ya sanya bata taɓa ƙiran sunana kai tsaye ba tare da ta sakaya ba, saboda zallar jinin fulanin dake gudana a cikin jikinta. Hamma Abubakar shi yake ƙiran ta da Umma sanda yake ƙarami saboda yaran makwabtan mu da suke wasa tare haka suke ƙiran iyayensu mata. Ya bi bakin su har muma muka zo muna ƙiran ta da sunan 'Ya'yan Baba Alhaji biyar mata uku maza biyu, Hamma Ahmad, Adda Azima, Adda Abida. Sannan Anwar da yake tsara na, da tsakanimu 'yan watanni ne, sai kuma auta Abasiyya. Muna da rufin asiri dai dai gwargwado da kuma wadatar zucin da muke gudanar da rayuwarmu dai dai ruwa dai dai tsaki. Akwai tsantsar ƙaunar juna a tsakaninmu, mun tashi da tarbiyyar da ya zama abin sha'awa ga mutanen unguwanmu. Unguwa ɗaya muke zaune sai dai kowa da gidan shi, a gidan su Abasiyya na taso domin daga yaye na koma can bacci ne kawai ke dawo dani gida. Mun shaƙu sosai da Anwar fiye da sauran 'yan uwana domin shine muka taso tare. Tare aka samu a makaranta haka nan tare muke zuwa. Sana'ar gidan mu shine kasuwanci don su Hamma Abubakar suna ƙare makarantar sakandiri suka koma kasuwa. Tare muka yi sauƙa da Anwar a lokacin muka kammala ƙaramar sakandiri ya soma bin su Hamma Abubakar kasuwa. Zaune nake na tisa kwanukan wanke wanke dake gabana ina shaɓar kuka har da shiɗewa, Allah ya sa ni a aiki gida gabaɗaya babu wanda na ƙi jini fiye da wanke wanke. Sau tari in an sa ni Abasiyya nake lallaɓawa ta yi mini, ni kuwa na goya ta na zagaye filin gidan tsaf da ita. Ban ji shigowar sa ba illa jin ƙarar kujerar da ya jawo ya zauna a kai, na yi saurin ɗago idona ina kallon Anwar ɗin da shi ma ya kafe ni da ido. Ruwan wanke wanke na ɗeba a hannuna na watsa masa a fuska ina faɗin "me kai kuma ka tsura mini ido kamar wani maye".@ Dariya ya yi yana goge ruwar da na watsa masa ya ce"in da ni maye ne ai da tunin na gama dake yarinya, waya taɓa ki kike wannan kukan?". "Umma ce ta sa ni wanke wanke". "Umma ce ta sa ni wanke wanke ". Ya faɗa yana kwaikwayon muryata da hakan ya ƙara ƙular dani matuƙa. Na ɗauka kwanon samira da nufin jefa masa ya yi saurin kama kunnesa yana faɗin"afuwan Boɗɗiam(kyakkyawata) bari na taya ki". "Da ka wanke kanka". Na faɗa ina goge hawayen da ya ɓata mini fuska, muna hira har ya gama wanke kwanukan tsaf, ya kai madafa ni kuma na soma share wajen. Dai dai sanda Umma take fitowa daga ɗaki ta saki salati tana cewar"oh! Hande min boni 'yar nan ba ki yi wanke wanken nan ba?. Wacce irin malalaciya ce haka?". Ajiye tsuntsiyar hannuna na yi na ɗaga hannuna zan fara rantse rantse akan ni na yi, ta dakatar da ni"kar ki ce min komai duk abinda zai fito daga bakinki ƙarya ne, ina ɗaki na ji sallamar Anwar kuma na tabbatar shi ya wanke kwanukan nan". "Umma ita ta yi na dai taya ta mun ƙarisa ne". Anwar ya furta yana fitowa daga madafan, jijjiga kanta kawai Umma ta yi ta ɗauki bota ta shiga banɗaki. Na sa ki dariya har da ƙyalƙyallewa har Umma ta fito daga banɗakin ban tsagaita ba ta rufe ni da faɗan, wai na dunga sausauta muryata duk gidan ya ɗauki dariyata ba. Ban ce komai na cigaba da sharan ta juya ga Anwar"ya kasuwan?". "Kasuwa alhamdulillah, Baffa ne ya aiko ni daman na kawo cefane". Ya ƙare zancen yana mata nuni da baƙar ledar da take bisa tabarmar dake shinfiɗe a ƙofar ɗaki, da sai yanzu na lura da ita. "To Allah ya amfana, ka kama hanya ka koma kar ka biyewa yarinyar nan da shiriritarta". Dariya na kuma saka don ni sam bana ganin wuyar yin ta na ce"ai yanzu ma ina gama wajen Abasiyya za ni". "Allah ya shirye ki". Ta faɗa tana komawa ɗaki, Anwar ya katse mini hanzari da faɗin"Boɗɗi zan koma zan taho miki da abin daɗi". Kaina kawai na ɗaga masa ya fice yana sakar mini da murmushi, ina gama sharan na zagi hijabina na nufi gidan su Anwar. Ina shiga na hangi Adda Azima tana shaya kayan da ta wanke gefe guda kuwa Adda Abida na hura wuta sai mahaifiyarsu Dada ake zaune Abasiyya tana mata tsifa. Da gudu na isa wajen Abasiyya na wafce kifiyan dake hannunta ina faɗin"matsa ki bani wuri ni zan mata". Dada sai faman faɗin"ku yi hankali" take yi amma kamar bada mu take yi ba, sai ture ture muke yi. Sai da Adda Azima ta daka mana tsawa sannan muka nutsu, na ji tamkar na saki fitsari a wandona domin ba kaɗan ba tsawa yake firgita ni. "Ba kya ji ne ana yi muku magana?, kar ku nutsu a wajen nan ku gani". Zunɓuro baki na yi ƙasa ƙasa ina cewa" halin su ɗaya da Hamma Abubakar shiyasa su Baffa suke son haɗa su aure, su je can su ƙarisa da masifa". ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 0️⃣3️⃣ Dole Abasiyya ta saduda ta bar mini na yi wa Dada tsifar, sannan muka koma gidanmu tare bisa umarnin Dada. Da ta ce mu koma muje mu taya Umma aiki mun baro ta ita ɗaya. Sai bayan sallan isha'i su Baffa suke dawowa gida, tabbas iyayenmu maza sun yi katari da samun iyalai masu tsananin biyayya a gare su. Domin ko tsinke suka ajiye babu mai ƙetarewa. Zaune duk muke akan ƙatuwar tabarmar da Umma ta baje mana a filin tsakar gidan, mun kunna fitilar ƙwai da ya haske wajen. Abasiyya, Adda Abida da Anwar duk muna zaune tare dasu. Baffa da Baba Alhaji kuwa suna zaure suna cin abincin. Ranƙwashin da na ji a kaina ya sanya ni saurin haɗiye raguwar dariyar da nake yi babu ƙwau-ƙwautawa. Ina dafe wajen na ɗago kaina da nufin tsala ihu, ganin Hamma Abubakar tsaye a kaina ya haɗe rai tamkar magribar ɗinya ya tursasa mini cinye kukan da nake shirin saka. Cikin ƙanƙace idon da ya zamo ɗabi'arsa a duk lokacin da zai yi faɗa, ya nuno ni da 'yar manuniyar tsayarsa yana cewa" wai ke sai yaushe za ki yi hankali ne? ba ki san cewar muryar mace shima al'aurarta bane?. Sam ba ki iya zance cikin hankali ba sai faman ƙyalƙyala dariya kike". Tsif wajen babu wanda ya tanka masa illa riƙe hannuna da Abasiyya ta yi dam a cikin nata. Ƙwafa ya yi ya fice yana faɗin"Umma na wuce gidan Baba". Sai da na tabbatar da cewar ya fice na saki wani uban ƙara kai ka ce yankar nama jikinsa ake yi, Anwar, Abasiyya da Adda Abida suke ta faman lallashina, Umma kam ko kallona ba ta yi ba. Tsananta kukan da na yi ya sanya Hamma Adnan da Hamma Ahmad da suke cikin ɗakin fito a tare suna tambayar meke faruwa. Cikin tsantsar ɓacin rai tattare da furucinsa Anwar ya ce"Hamma Abubakar ne ya ranƙwashe ta wai don kawai tana dariya da ƙarfi". Su ma lallashina suka yi, ban yi shuru ba har Baffa ya ƙwala ƙirar Anwar ya je ya shigo da kwanukan abincin da suka gama ci cikin gidan. Sannan su ma suka shigo Baba Alhaji ya ce"to jiniya waye kuma ya taɓo ki?". Muryana har yana shaƙewa"Hamma Abubakar ne". Na fashe da wani kukan sai Abasiyya ce ta ƙarisa musu. Baba Alhaji ya fara faɗa akan ba ya son ana ranƙwashi gwara a kama ni a zane ni. Da kyar na yi shuru ina sauƙe ajiyar zuciya a kai a kai. Baffa ya ce"ina kuka baro Azima kuwa?". Umma ta yi murmushi tana faɗin" ai tunda Abubakar ya nuna yana sonta shikenan ta ya ye shigowa gidan nan, ko za ta shigo bata yarda mu haɗu". Murmushi Baffa da Baba Alhaji suka yi suna haɗe baki wajen furta"Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi cikin wannan lamarin". Duk muka amsa da amin. "Kai kuma meye sai wani haɗe fuska ka ke yi, me aka yi maka?". Hamma Adnan ya jefawa Anwar da ya ke ta cika yana batsewa tambaya, Umma ta amshe zancen da faɗin"to har sai an masa wani abu, ai tunda aka taɓa 'yar gaban goshinsa daman yau babu zaman lafiya". Kamar jira yake yi ya fara furzo da zancen dake cikinsa, idanunsa taf da kwantattun ƙwalla"fisabillahi Umma ko me tayi sai ya yi mata irin wannan ranƙwashin idan ya juyar mata da ƙwaƙwalwa fa". Sai da ya yi ƙwafa ya cigaba da"tashi Aishatu mu tafi a gidanmu za ki kwana". Da sauri na tashi riƙe da hannun Abasiyya ina yi wa Umma a kwana lafiya, har mu kai ƙofar fita Adda Abida ta dakatar damu ta hanyar faɗin"to Anwar wannan fusata haka ko za ka rama mata ne?". Harara ya juyo ya watsa mata"ai don ya fi ƙarfina ne, amma wallahi da wani daban ne sai ya sha mamaki". Dariya suka tuntsure dashi Hamma Adnan ya ce"ashe ma duk ƙarya ce". Hamma Ahmad dai murmushi kawai yake yi don shi bai cika yawan magana ba, in ya zauna a waje har ya tashi ba za ka ji bakinsa ba. Ko da muka je muka iske Hamma Abubakar da Adda Azima, zaune a bisa tabarma a filin tsakar gidan su na zancen. Tun a zaure daman Anwar ya ce damu in mun shiga kar mu kula su, mu wuce ɗakin Dada. Yanda ya kitsa mana haka muka aiwatar ni da Abasiyya kai tsaye muka wuce ɗakin Dada da muka tarar tana kishingiɗe bacci ya fara ɗaukarta. "Kai lafiyarku?". Ta furta tana tashi zaune daga kishingiɗewar da ta yi tare da mirtsike idanunta. Sai ƙunƙuni nake yi sai Abasiyya ce ta yi mata bayani ita ma tayi mini faɗa ta sigar lumana akan na dunga sausauta amon muryata yayin magana. Wai mace ƙwarai da kamewa aka san ta a ko yaushe. Ba mu fita daga ɗakin ba sai da muka tabbatar da Hamma Abubakar ya tafi. Kwana biyu a jere Anwar ya ɗauka yana fushi laifin Hamma Abubakar har Adda Azima da ba ta san hau ba balle sauƙe ya shafa. Sai da ya ƙira shi ya nusar dashi illar abunda nake yi sannan ya ɗan sauƙa. Don mutum ne mai tsananin ƙaunar gudan jikinsa a ko'ina kuma a ko yaushe, matuƙar ka taɓa ɗan uwansa sai ka ga ɓacin rai a fuskarsa. Ranar na tashi da matuƙar zazzaɓi ko kaina bana iya ɗagawa, ranar a gidanmu muka kwana. Kafin su Baffa su tafi kasuwa suka shigo suka duba ni dukkansu, Anwar kam an kaɗa an rawa ya ƙi fita kasuwa dole su Baffa suka bar shi. Ranar a kusa da ni ya wuni ko motsi nayi sai ya tambaye ni ko jikin ne, kwanana uku cikin wannan yanayin a wunin na huɗun na ji ɗan dama-dama. Muna tilawar al-qur'ani tare Anwar a barandar ƙofar ɗakin Hamma Abubakar da Hamma Ahmad da ya komo gidan mu da zama gabaɗaya, duk ɗago idon da zan yi sai naga idanunsa a kaina. "Lafiya? ni fa bana son kallon nan, da idanunka manya abun tsoro". Murmusawa ya yi ya ce"ai kin fi ni manyan ido Boɗɗi". Taɓe baki na yi ina rufe ƙur'anin hannuna na ce"faɗa kawai ka ke yi, ai ko a makaranta in an gan mu tare cewa ake yi kamar ba gidan mu ɗaya ba. Su na ce mini 'yar baƙa". "To ai farin fata bashi yake nuna mai shi kyakkyawa bane, hasken kawai muka fi ki amma kowa cewa yake yi ai kin fi mu kyau Boɗɗiam". Yatsina fuskana na yi domin a tsakanin su gabaɗaya ni ce baƙar fata, farare ne tas hatta su Baffa da gwagwarmayar rayuwa ta sanya fatar su dafewa sun fi ni haske. Daren ranar bayan dawowar su Baffa daga kasuwa suka tattauna batun auren Hamma Abubakar da Adda Azima, mu na laɓe muna leƙo su daga cikin gida. Yayin da Dada take basu tabbacin Adda Azima ta amince da wannan haɗin. Tsabar murna ni da Abasiyya muka rungume juna tare da rugawa da gudu muka nufi ɗakin mu muka faɗa kan katifarmu muna sakin dariya. Raina fes zan rabu da masifa da ranƙwashin Hamma Abubakar. A bakin su Hamma Adnan muke jin cewar an sanya bikin nan da mako biyar, babu jan wani dogon lokacin domin tuwana maina za'a. Dakan ɗaka shiƙan ɗaka. Tunin aka fara shirye shirye na tanadin abincin da za'a ci a hidimar bikin. Su Baffa suka ware mishi jari na shi na daban suka bashi saɓanin da da duk suke tare a rumfa ɗaya. Duk da kan ahalin a haɗe yake amma su Baffa ba su lamince da zama tare da suruka a gida ɗaya ba. A cewar su haka ne mabuɗi kowacce fitina dake tasowa tsakani iyali, idan ba ayi dace da surukar ƙwarai ba. Wani ƙaramin gidan dake layin gabanmu da aka sanya a kasuwa su Baffa suka saya a can zasu tare da zaran an ɗaura auren. Shirye shirye ake yi gadan gadan, kafin lokacin komai da za'a buƙata a yayin bikin sai da su Baffa suka samar dashi. Lefe kuwa Hamma Abubakar ne ya haɗe abinsa tsaf babu sisin kowa a ciki da kuɗin da yake ajiyewa. Na sallamar da su Baffa suke musu a kasuwa. Tunda aka sanya bikin na koma gidan su Anwar da kwana har lokacin ya matsu. A 'yan kwanakin nan za ka fahimci yanda Baffa da Baba Alhaji suke cikin tsantsar murna da annushuwa da ya bayyana a fuskarsu ɓaro ɓaro. Duk wayewar gari sai su sawa Hamma Abubakar da Adda Azima albarka tare da addu'ar samun dawamammen zaman lafiya a tsakanin su. Tun ana sauran kwanaki goma bikin dangi suka fara zuwa, tsabar murna na rasa inda zan tsoma kaina balle samun matsuguni ɗaya. Ina son ganin jama'a haka domin ba'a taɓa yin wani taro a gidan mu da aka yi irin wannan cikar ba. Sai dai yanda kowa yake faɗin cewar tamkar ba daga tsantson Umma na fito ba, saboda duhun fatata ya sanya ni suƙurewa. Ana gobe ɗaurin auren aka yi kiɗan kwarya a kofar gida, daren ranar bamu runtsa ba ni da Abasiyya tsabar murnar ganin wayewar garin gobe. Mu saka ankon atamfar da Hamma Ahmad ya yi mana har da su Umma da Dada. An yi bikin sosai yayin da dangi da abokan arziki suka yi mana kara, gidan babu masaka tsinke ko'ina jama'a ne. Bayan isha'i aka ce a fito da amarya za a kai ta gidanta duk yanda nake faɗin cewar ba zan yi kukan rabuwa da Hamma Abubakar da Adda Azima ba. Tsintar kaina na yi da zubda ƙwallar da ban san su na zuba ba, sai da Adda Abida ta ankarar da ni. Haka aka kai amarya ɗakinta ango ya tare su Baffa suka ce babu kwanan gidan amarya, ana kai ta kowa ya juyo aka bar ta da nasihohin da su Dada da Baffa suka yi mata. Washe gari tun farar safiya muka fara shirin zuwa gidan ba don sauƙar ruwan sama da ya yi mana cikas ba, a tsarin mu hantsi a can zai iske mu. Ina tsaye ina ɗaura zanina na buɗe ƙafafu. Na soma dariya ina faɗin" kai wallahi Adda Azima kam za ta ga masifa da bala'i. Hamma Abubakar mungu ne na ƙarshe da tayi laifi zai hau zuba mata ranƙwashi". Dariya muka kuma tuntsirewa dashi ni da Abasiyya, muka gama shiri muka fito. Zamu tafi Umma ta ce dole sai mun tafi tare da wasu 'yan mata biyu da suka zo daga gumel, ba su sama zuwa gidan amarya ba jiya. Ba don raina ya so ba muka haɗa tafiya dasu, basu iya hausa sosai don fullanci yafi zama a harsunansu. Cikin yaren fullancin na ji su na cewar"wannan 'yar kam akwai duhun fata, kamar ba tsantson fulani ba". Ɗayar ta kwashe da dariya"ni fa farkon ganinta na tsorita, domin kwaryar idon ne kawai fari a jikinta sai kuma hakwaranta". Duk da bada yaren muke magana a gida ba, amma sau tari Baffa da Baba Alhaji dashi suke zance musamman in muna zaune a wajen ba sa son mu fahimci abinda suke faɗa. Su kan sauya harshe, a haka muke tsintar ɗaya da biyu har muka fara fahimta me suke faɗi sai dai ba ma iya maidawa. Take na ji raina ya tukunzuma zuciyata har wani tafasa take yi. Muka haɗa ido da Abasiyya da ita ma ta fahimci me suke faɗa, idanuna cike da hawayen da nake ɓoyewa na takaici na yi sauri na yi gaba na bar su a baya. Abasiyya ta biyo bayana tana cewa"meye haka kuma?, kin yi gaba kin bar mu". "Ku yi tafiyarku na yi tawa". Ina gama faɗin haka na ruga da gudu na miƙe layin, maimakon na karya kwana sai na miƙe na sama wani ɗan lungu na zauna, na kifa kaina da gwiwa ina kuka. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimunah Tijjani Iyam _____________________________________ Page 0️⃣4️⃣ Sai da rana ya iske ni a wajen ya fara dukana sannan na ɗago kaina ina ƙarewa fatar hannuna kallo. Raina cike da takaicin yanda mutane suke sukar halittar da maƙagin rayuwata bai yi shawara da ni, yayin ƙera ni ba. Goge fuskana na yi duk da ba yau na saba jin an ce dani baƙar fata ba. Amma abin bai taɓa sukar raina irin na yau ba. A zuciyata nake ayyana rashin mutuncin da zan shuka musu, na miƙe na soma tafiya sai na da ƙure lungun da ya ɓullar da ni izuwa wani babban layi. Na fara waige waige don na rasa inda zan nufa ya kai ni gidan, ware idona nake ko zan gano layin da na fahimta amma babu alamar hakan. Kasancewar ban ko'ina na sani cikin unguwar ba duk yawona bai wuce gidan su Anwar. Baya na koma da nufin dawowa inda muka rabu da su Abasiyya, ina tafe kaina a ƙasa na ji ƙarar wucewar wata motar da ta wuce ta gefena da matuƙar gudu fiyuuu. Ɗago kan da zan yi ya fancakalo mini ruwar kwatan da ya kwanta a wajen a fuskata. Na tsaya cak na kasa komai illa hawayen da yake sauƙa daga idanuna. Har cikin bakina ruwan ya shiga na tofar da miyau, ina bin motar da ta faka a gefe da harara. Ji nake yi kamar na je na shaƙo mai motar ko zan huce takaicin da ya tusa mini a raina. Sai da aka ɗau mintuna kafin aka buɗe ƙofar motar mazaunin driver aka fito, na yi saurin yin ƙasa da kaina cike da kunyar halin da fuskata take ciki. Ganin wasu masu talla da suka tunkaro inda nake tsaye zasu wuce, har suka wuce ban ɗago kaina ba. "Assalamu alaikum sannu baiwar Allah". Na ji a furta cikin kammalalliyar murya ma'abociyar nutsuwa, take na ji tsikar jikina ya tashi domin ban taɓa tsayiwa da wani namiji akan hanya ba, bayan 'yan uwana da suka kasance muharramaina. Ban sa ni ko fahimtar hakan ne ya san shi ƙara sausauta murya ya ce"baiwar Allah afuwan ban lura da ke a wajen ba, na ɓata miki jiki da ruwa". Sai a lokacin na ɗago kaina na sauƙe akan sa, ba za'a sanya shi a layin farare ba kamar yanda ba za'a ƙira shi da baƙi ba. Sajen fuskarsa da kuma farin shaddar dake jikinsa su kaɗai na kalla na rusunar da idanuna ƙasa. Komawa inda ya ajiye motarsa ya yi ya ɗauko gorar ruwa ya dawo ya miƙe mini, ba tare da na ɗago kaina ba na karɓa na soma wanke fuskata. Ina gamawa na miƙe masa gorar ruwan na soma tafiya, ƙafufuna har suna harɗewa cikin zanina. Da sauri ya biyo bayana ya sha gabana tare da cewa"baiwar Allah kina ji na?". Hawaye suka zubo daga idanuna ya ƙara sausauta murya ya ce"afuwan baiwar Allah". Kaina kawai na ɗaga masa na raɓe zan wuce ya kuma shan gabana, jikina ya soma rawa ganin yanda mutane suke wucewa ta wajen, rashin sabo ya sanya ni ganin kamar cewar kowa ni yake gani. "Allah yasa ba ni na yi sanadiyar zubar hawayen nan ba, domin ba zan yafewa kaina ba sanya hawayen wani zuba a dalilina". Cikin sarƙewar harshe na furta "zan wuce". Ya haɗe hannayensa da yake riƙe da gorar ruwan wajen guda, tare da marairaicewa"ki yi haƙuri". Da sauri na bi gefe na wuce cikin sauri tamkar zan tashi sama. Ina waige na ga yana tsaye baya biyo bayana na sa ki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, sai da na ƙure layin ina hango inda muka rabu da su Abasiyya na ji hankalina ya kwanta. Ban ankara ba naji an danna mini horn ɗin mota a bayana da ya sanya cikina juyawa, na cigaba da tafiya da sauri. Ya zuge gilashin motar muka haɗa ido na kawar da nawa gefe guda, muryarsa suka yi ƙafofin kunnuwana dirar mikiya. "Ban sa ni ba ko afuwan nawan ya sama karɓuwa". Izuwa yanzu kam gabaɗaya na gama tsorita ina tina yanda nasihar Dada da take ja mana kunne ni da Abasiyya. Akan cewar kar wani namiji ya yi mana magana a hanya mu tsaya, duk wanda muka gani da babbar mota ɗan yankan kai ne. Ji nake yi kamar na saki fitsari a wando tsabar tsoritar da nayi. Gudu gudu sauri sauri nake tafiya ba tare da na kuma kallon gefen da yake ba, sai da na iso wajen na gane hanyar gidan Adda Azima. Ina isa na iske mutane cike a filin gidan kamar an jefo ni haka na faɗo cikin gidan. Muka haɗo ido da Abasiyya da take miƙo abinci a mutane tare da wasu mata biyu. Na galla mata uwar harara na zari buta na shiga banɗaki. Ina fitowa na saki ajiyar zuciyar samun nutsuwar da na yi, na je kusa da Adda Abida na zauna. Ta kallo ni ta ce"ke kuma ina kika tsaya sai yanzu?". Turo baki na yi na ce" ɓata mini rai suka yi" ta jijjiga kai ta kuma cewa"za ki je ki haɗu da Hamma Abubakar ne, don ya shigo yana neman ki. Haka nan ma Anwar yanzu ya bar gidan nan". Taɓe baki na yi don yanzu yunwar cikina ce ta dame ni don ko abincin bamu ci ba muka fito. Na miƙe na je na karɓa abinci na soma ci Abasiyya ta zauna a kusa dani, na saki dogon tsaki ina kawar da kaina gefe guda tare da mayar da hankali ga cin abincin da nake yi. "Ki yi haƙuri mana, Adda Abida ma da ta yi musu faɗa akan abinda suka faɗa miki". Ban kula ta ba ta ɗaura da"kin ji 'yar uwa?". A zafafe na furta"malama kar ki sanya ni na ƙware ki bar ni haka nan". Murmushi tayi don inda sabo ta saba da halina na masifa da rashin barin ta kwana, sai da na cinye abincina tas ba wanke hannuna na shiga ɗakin Adda Azima ita ma ta tsare ni da tambayar inda na tsaya na ce da ita canza hanya na yi nabi tawa hanyar suma suka bi tasu. Sai bayan sallan asr sannan muka koma gida gidanmu muka wuce, lokaci baƙin nisa duk sun fara watsewa ya rage saura tsirarun mutane ne suka yi saura. Bayan sallan magrib ina zaune a bisa sallayar da na iddar' Anwar ya aiko ƙirana. Da muryana ta na tashi domin yau tun wayewar gari ban sanya shi a cikin idanuna ba, na fita na iske shi a zaure tun kafin na isa na turo baki gaba, ya saki murmushi yana faɗin"waya taɓa mini Boɗɗita?". Na yi ƙwafa na soma sanar dashi duk abinda ya faru a hanyar zuwar mu gidan Adda Azima. "Duk da kasancewar ki bakar fata ai ke kyakkyawa ce shiyasa nake ƙiran ki Boɗɗiam. Farare dubu nawa ne munanan da baƙaƙen ma suka fi su kyawu?, ke kyakkyawa ce. Ki rubuta ki ajiye wani masoyinki zai tabbatar miki da haƙiƙanin gaskiyar maganar da na furta miki a yanzu". Dariyar da yau gabaɗaya ban yi kamar ba na saka har da sunkuyawa ƙasa, sosai nake yin ta. Ya dakatar da ni da faɗin"ki nutsu ga Hamma Abubakar shigowa". Babu shiri na miƙe tsam ina rarraba idanu da hakan ya sanya shi sakin dariya. "Matsoraciyar banza me zai kawo Hamma Abubakar kuma a wannan lokacin, ai yana can tare da amaryarsa". A bayyane na saki ajiyar zuciya ina jefa masa harara ina cewa"tsoritar da musulmi dai haramun ne". "Tsakanin jiya da yau kin lura da hauhawan annurin su Baffa?". Ya furta yana gyara tsayiwarsa. Na numfasa kana na amsa da "ƙwarai kuwa suna cikin matuƙar farin ciki". "Allah ya ƙara haɗa kanmu Boɗɗiam". Na yi fari da idona kana na ce "amin Hamma Anwar" ya yi taƙaitaccen murmushi haɗi da faɗin"ina kika tsaya yau da kuka fita?, don naje gidan Hamma Abubakar aka ce ba ki ƙariso ba". Ban san dalilin faɗuwar da gabana ya yi ba idanuna ya kawo ruwar ƙwalla, na sanar dashi komai game da wannan mai motar da ya fancakala mini ruwan kwata a fuskana. "Kar ki ƙara sauraran irin mutanen nan. Ko gaba irin haka ya faru ki yi tafiyarki kawai". Ban amsa masa ba illa kafe sa da idon da na yi, don ganin yanayin da ya yi maganar da gabaɗaya annurin fuskarsa ya gusa. Idanunsa har sun koma launin ja, cikin sanyin jiki na soma faɗin"ni fa ban kula shi ba, ko da ya bani haƙuri ma ban tanka masa ba. Shi ne ya yi ta bina a baya". "Naji ki shiga gida sai da safe". Yana ƙare faɗin haka ya fice daga zauren ya bar ni tsaye sororo kamar sokuwa. Haka na koma ciki jikina gabaɗaya babu ƙwari tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, ko da na kwanta na kasa bacci ina ta tunanin ko na faɗa wani abu ba dai dai bane, duk da Anwar yana da saurin ɗaukar zafi da kuma zuciya amma baya taɓa nuna shi a kan 'yan uwansa musamman ni. Da na zama tamkar Hussaina a gare shi. Washe gari 'yan biki kowa ya watse gidan ya zama sharau. Na nufi gidan Baba ina sako kai muka yi kiciɓus dashi zai fita na matsa da sauri na bashi hanya ina faɗin "ina kwana an tashi lafiya?". Ba tare da kalle ni ba ya amsa da"lafiya ƙalau". Na marairaice muryar tamkar mai shirin yin kuka" ban san me na yi maka ba jiya ka tafi ranka a ɓace". Ya zaro ido waje"ni na ce miki raina ya ɓaci?". "Yanayinka ne ya nuna haka ai". Ya sauƙe ajiyar zuciya kafin ya furta" kawai ji nayi ban ji daɗi ba da kika sanar da ni, yanda ya ɓata miki fuska da ruwan kwata". "To ai ya bani haƙuri fa". Na faɗa cikin shagwaɓan da ya tilasta masa sakin dariya duk shan kunun da yake yi. Ya ɗago idonsa ya kalle ni ya ce"to ai ya bani haƙuri fa". Na yi rau rau da ido zan yi magana ya tari numfashina"shikenan ya wuce kin ji?". Cike da jin daɗi na sakin murmushi ina cewa "to na gode yanzu ina zaka je". "Kasuwa su Hamma Ahmad tunin sun wuce". Addu'ar dawowa lafiya da cimma abinda aka je nema na yi masa, ya amsa cike da jin daɗin da ya bayyana akan farar fuskarsa. Ya wuce ni kuma na shige ciki ina shiga Abasiyya ta soma yi mini dariya. Ko tambayar lafiyarta da nake yi bata amsa ba ta cigaba da dariyarta, na watsa mata harara ina tsarkin tsaki. Sai da ta tsagaita ta soma cewa"ai daman yanda Hamma Anwar ya shigo gidan nan a daren jiya, sai da na yi zargin cewar da walakin goro a miya. Ashe ke kika tunzuro shi". Ban kula ta don ba ita ce a gabana na faɗa ɗakin Dada. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________ Page 0️⃣5️⃣ Tun bayan auren Hamma Abubakar na ƙara sakewa a cikin gidan. Sai dai ko wacce safiya kafin ya wuce kasuwa sai ya zo gidan ya gaishe dasu Baffa haka nan bayan sallan isha'i kafin ya wuce sai ya zo ya yi musu a kwana lafiya. Kasuwancin su Baffa sai ƙara hafɓaka yake yi domin yanzu tunin likafa ta cigaba. Hamma Ahmad da Hamma Adnan ma an ware musu nasu rumfar daban da suke sayar da atamfofi, Anwar ne kawai yake tare dasu Baffa. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya lokaci yana juya, yayin da kullum muke ƙara kwanakin mu suke ƙarewa ba tare da mun sa ni ba, balle tanadin guzuri. Sai ma burin da ya ke ƙara cika mana rai. Sai da Adda Azima ta cika watanni uku cur a gidan miji sannan ta zo ganin gida, ranar tsabar murna rasa inda zamu tusa kanmu muka yi inda Abasiyya, mu kawo mata wancan mu kawo mata wancan. Duk abinda ya faru kuwa a gidan ko aka yi duk sai da muka sanar da ita. Ta yi ɓul-ɓul kuma ta ƙars yin wani haske na musamman jikinta kamar ka latsa jini ya fito. Sai da suka dawo daga kasuwa Hamma Abubakar ya zo ya ɗauke ta. Wayewar garin ranar da muka buga lissafi da Adda Abida na cikar auren su watanni bakwai da 'yan kwanaki. Hamma Abubakar ya ƙira a gigice wai ta yi ɓari har sun wuce asibiti, ta sha wahala matuƙar don har wankin ciki aka yi mata bayan ta sha jinya ta dawo gida ta yi sati biyu sannan ta koma ɗakinta. A lokacin kowa ya fahimci take taken Hamma Adnan da Adda Abida suna son juna, ya kai matakin da har basa iya ɓoyewa ko zaman 'yan awanni ka yi tare dasu zaka fahimta. Tabbas su Baffa sun yi matuƙar farin cikin jin haka daga iyayenmu mata domin zama na musamman suka haɗa dukkan mu muka bayyana, su na ta sa mana albarka da addu'ar Allah ya ɗaurar da zumunci a tsakanin mu ko bayan ransu. Umma ta aike ni na sayo mata sugari ta damawa Baffa fura, layin sharau domin an shiga sallar isha'i. Na je na tarar da shagon a kunne na nema waje na zauna ina wasa da 'yan yatsun hannuna. Har aka yi sallama aka fara fitowa tun daga nisa na hango mai shagon da hakan ya sa ni saurin miƙewa ina karkaɗe jikina, na gaishe shi ya amsa sannan na sanar dashi abinda nazo saya ya buɗe shagon ya ɗauko ya bani na karba tare da miƙa masa kuɗinsa. Sauri sauri nake yi saboda yanda maza suka fara cika layin, ban ankara ba na ji na bangaji mutum. Na yi saurin ja da baya tare da tsugunawa ba ɗauko wayar da ta faɗi ƙasa ba ɗago zan miƙa masa kenan idanunmu suka sarƙafe a cikin na juna. Take na ji jikina ya ɗauki rawa ganin zan kuma yasar da wayar ya sanya shi karɓa"ke ce?". Ban kula shi ba na fara tafiya ya soma jerawa da ni"tun wancan lokacin nake ta addu'ar Allah ya ƙara haɗa ni dake domin na nema afuwarki. A layin nan kike?". "Ya riga ya wuce tun lokacin na sanar da kai, don Allah ka daina bi na". "Me yasa?". Ya jefa mini tambayar da ya sanya ni ƙara saurin da nake yi tamkar zan kife akan hancina, idanuna rau rau na ce"za a yi mini faɗa a gida idan aka gan ni da ka...". Ban rufe bakina ba na hangi Baffa da Baba Alhaji suna nufo gida suna tafe suna tattaunawa da limamin masallacin. Bayan su kuwa su Hamma Ahmad da Adnan ne sai Anwar da yake daga gefe tare da wani abokinsa na cikin unguwar. Babu shiri na sa ki ledar sugarin ya faɗi ƙasa, na ɗaura hannuna a ka"shikenan na shiga uku". Na sunkuya na zari ledar da yake yoyo ba ruga gida da gudu domin na tabbatar da cewar duk sun ganni. Ina shiga na ɓarke da kukan da ya tilasta Umma yanke addu'ar da take yi ba tare da ta kammala ba. "Ke lafiyarki?, ina aiken da na yi miki ko kuɗin kika sayar?". Kafin na kai ga bata amsa su Hamma Ahmad suka shigo. "Ke meya fitar da ke a wannan lokacin, sannan waye wancan da muka tsaya dashi?". Cikina ya bada ƙarar ƙululu sai da na haɗiye wani miyau mai ɗaci"Umma ce ta aike ni na sayo mata suga, shi ne na gan shi a cikin layin daman tun lokacin auren su Hamma Abubakar ne ranar an yi ruwa ya fancakala mini ruwan kwata a jikina shi ne wai yake bina zai ba ni haƙuri". Hamma Ahmad ya yi ƙwafa yana nuna yi da 'yar manuniyar yatsarsa"shi ne kuma ba ki taɓa faɗawa kowa ba". "Na faɗawa Anwar tun a lokacin". Na furta ina nuni da Anwar ɗin dake tsaye a bayan su. "To ki nutsu ki ji ni, wallahi kika kuskura na ƙara ganin ki ki sanya ƙafa kin fita daga cikin gidan nan a irin wannan lokacin sai kin yi mamakin matakin da zan ɗauka. Duk wani aike a ba wa Anwar ya je ya siyo". Furucin Hamma Adnan kenan yana saka kai ya shige ɗakinsu, Hamma Ahmad ya kallo ni yayin da yake rufa masa baya"ki kiyaye". Na ɗaga masa kaina da sauri. Umma da tun ɗazun ba ta kuma cewa komai ta zo ta ɗauki ledar sugar tana faɗin"kin kyautawa kan ki". Haka na cigaba da kukana Anwar yana lallashina ina jin gyaran muryan Baffa dake alamata mini zai zo na yi zumbur na shige ɗaki. Sai da aka jera kwanaki biyu muna wasa 'yar ɓoya dashi, faɗawa kuwa na sha shi a wajen Umma tamkar za ta yi aron baki. Bayan abun ya lafa ina zaune a ɗakin kwananmu ina shafa mai a fatata mai duhu. Na ji sallamar Abasiyya. Umma ta amsa mata kana ta ɗaura da"ke dai kam Abasiyya tufarkalla, ba kya taɓa shigowa gidan nan ba tare da sallama ba". Na san gugan zana Umma ke son yi mini don haka na ɗago labule na leƙo"ita ma ɗin munafurci ne sai da ta tabbatar kina tsakar gidan, sannan ta ƙirƙiro sallamar ta shigo da ita". Umma ta sa ki dariya tana miƙewa, na gallawa Abasiyya harara na koma na cigaba da sha mai ɗin. Ta shigo ta zauna tana kallo na har na saka kayana na ɗage mata ido ɗaya alamar lafiya. Ta sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ta ce"lafiya ƙalau Hamma Ahmad ne ya aiko ni na ƙira ki". Na taɓe baki "shine kika zo kika wani tsare ni da ido" . Bata ce dani komai ba illa murmushi da ta saka, ta jira ni na sanya hijabina muka sanar da Umma kafin muka fita. Ɗakin dake zauren gidansu Abasiyya ta ce mini yana ciki, na yi sallama sai da aka amsa sannan na ɗaga labulen na shiga. Yana zaune akan ɗaya daga cikin kujeru biyu da suke ɗakin, na zauna a ƙasa nisa dashi kaɗan na ce"an ce kana nema na". Ina ina jiyo sakakken ajiyar zuciyar da ya sauƙe da matuƙar ƙarfi kana ya soma cewa"haka ne wani magana nake so mu yi dake". Na ɗaga kaina alamar ina sauraron sa. "Su Baffa ne suka umarce ni da na zo na nema amincewar ki, idan kin amince mun daidaita kanmu. Suna son a haɗa tare da na su Adnan". Babu shiri na ɗago kaina ina yi masa wani kallo cike da son ƙarin bayani game da furcinsa da ya yi mini a dunƙule. "Amincewata akan meye kenan?". Ya ɗan yi jim kafin ya furta sunana a kasalance"Aishatu". Na amsa a sanyaye sannan ya cigaba da" na daɗe da fahimtar cewar son da nake miki ya wuce na 'yan uwantaka, ina miki so irin wanda nake fatan yin rayuwa dake har ƙarshen rayuwata idan kin bani dama". "Ka yi mini afuwa har yanzu ban gane abinda kake son ka faɗa ba". "Ina son ki Aishatu". Take tsikar jikina ya tashi na ɗago ido na yi masa kallo ɗaya sannan na kawar da nawa idanun gefe guda. Tsawon ɗakiƙu ashiri cikin mu babu wanda ya ce ko kanzil, kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa. Na ji muryarsa ya katse mini hanzari. "Ki je ki yi tinani sannan ki yi istikata. Ina son ki sanar dani duk abin da ke ranki game da ni kar ki ɓoye min komai. Babu wanda zai yi miki tilas akan abin da bakya so" Da mutuwar jiki na ɗaga masa kaina sama alamar na ji. Sai da ya bani damar tafiya sannan na tashi na fice daga ɗakin. Ko cikin gidan ban shiga ba na koma gida jikina gabaɗaya babu kuzari tamkar kazar da aka jefa da ruwar gishiri. Ban tarar da Umma a tsakar gida ba don haka kai tsaye na shige ɗakin kwanan mu na zauna na zabga tagumi da hannu biyu. Allah ya sani ban taɓa koda mafarkin yin soyayya da Hamma Ahmad ba balle har ya kaimu ga yin aure. Bugun zuciyata ya tsananta ba zan iya kallon tsabar idon shi na ce dashi ba zan iya aurensa ba. Sai dai tabbas zan cutar da kaina cutarwa mafi illa domin zan yi rayuwa ne ba tare da farin ciki koda na sakan ɗaya ba. Ban ankara na ji hawaye yana gudu a bisa fuskata, na kwanta na yi lamau ina ta tinane-tinane. Haka ranar na wuni tamkar marar lafiya ko Umma na kasa faɗawa ba. Sai bayan sallan magrib Anwar ya shigo lokacin muna ci abinci da Abasiyya, ya gaishe da Umma sannan ya zauna akan dakalin ƙofar ɗakin mu. "Yau lafiyarki kuwa?". Muryarsa ta dawo ni duniyar zahiri daga duniyar tunanin da na faɗa. Kallon shi kawai na yi ba tare da na ce komai ba na tsame hannuna daga kwanon abincin na koma gefe. Ya kuma cewa"Umma ba ta da lafiya ne?". Ta yarfa hannunta alamar bata sa ni ba tana tashi ta shige ɗaki. Ya dawo kusa da ni ya tsuguna akan ƙafafunsa ya ce"Boɗɗiam menene yake damun ki?". Maimakon na bashi amsa sai na tsinci kaina da sakin hawaye. "Subhallahi kuka kuma Boɗɗiam? Menene yake faruwa?". "Wata magana nake so yi". Na faɗa tare da ɗago kaina wasu hawayen suna ƙara zubo mini. Ya juya ya ga Abasiyya da tayi shuru tana sauraron mu ya ce"tashi ki ɗauki abinciki ki bamu guri". Ta tashi ta shige ɗaki ta ba mu waje. Ya gyara tsugunan da ya yi ya furta" ina jinki menene?". Na rasa ta inda zan fara sanar dashi domin na rasa makama, ya sausauta muryarsa ƙasa ƙasa ya ce"ki gaugauta sanar da ni zuciyata bugawa take yi da ƙarfi". Na zuƙe majinar kukan da yazo mini kafin na sama zarafin faɗin"su Baffa ne suka ce Hamma Ahmad ya zo ya nema amincewata, idan mu daidaita kanmu a haɗa tare da na su Hamma Adn...". Ban ƙarisa ba sakamakon firgicin da na ke iya hangowa a fuskarsa. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam Page 0️⃣6️⃣ ______________________________________ Na kafe shi da ido ina faɗin"lafiya me ya faru?". Bai amsa mini ba ya dafe goshinsa da jijiyoyin kansa suka fito ɗarau ɗarau, kana ya furta"me kika ce?". Na kuma tsare shi da wani kallon da ya fi kama da na rashin fahimta. "Su Baffa suka ce Hamma Ahmad ya nema amincewata, idan mun daidaita tsakaninmu a haɗa tare da su Hamma Adnan". Na maimaita cikin sanyin jiki kamar yanda ya buƙata ina sunkuyar da kaina ƙasa. Sai da ya ɗauki wasu mintoti kafin ya furta"to ke kuma meye kika ce masa?". Na ja dogon numfashi na fesar"ban ce masa komai ba amma shi dai ya ce mini na je na yi istikata, sannan kar na ɓoye masa duk abinda na ji a raina game dashi". "Kina son sa?". Ya jefa mini tambayar da ya tilasta mini ɗago kaina na yi masa kallo ɗaya kafin na amsa da faɗin"bani da amsar wannan tambayar domin nima kaina ban sa ni ba". "Ki yi istikatan kamar yanda ya faɗa miki in sha Allah khairan ne". Muryarsa a shaƙe ya ƙarƙare zancen yana miƙewa tsaye na bi shi da kallo"muna magana kuma ka tashi". "Yau gabaɗaya bana jin daɗi ne, tun ina kasuwa nake jin kaina yana min ciwo. Zan je na nema magani". "Akwai magani a wajen Umma ai bari na karɓo maka". Da sauri ya dakatar da ni"a'a ki bar shi kawai". Yana ƙare faɗin hakan ya juya da nufin ficewa daga cikin gidan, ɗaga ƙafan da zai yi ya sauƙe ya faɗi. Na sa ki ƙara a gigice kafin na isa wajensa ina ƙwala ƙiran Umma. A tare suka fito da Abasiyya suka iso wajen tare da tambayar lafiya. Hawaye su na gudu a fuskata na ce"kawai ya tashi zai tafi ne ya faɗi". Umma ta na jera masa sannu Abasiyya kuma tunin ta zare kallabin kanta tana yi masa fiffita dashi. Ya tashi ya na zaune riƙe da kansa, Umma ta ce na ɗebo ruwa a ƙwarya na kawo mata. Na tashi da sauri na je na ɗebo na kawo mata ta fara tofa wasu addu'o'i a ciki, kafin ta miƙa masa ta ce ya sha akan nasan. Ya karɓa ya yi kamar yanda ta ce, duk sannu suke jera masa wani na bin wani ni kam na kasa cewa komai illa hawaye na ke yi. "Lafiya kuwa Anwar me ya faru?". "Jiri ne daman tun a kasuwa ina jin ciwon kai". "To Allah ya sauwaƙe tashi ka koma ka zauna, sai ka sha magani". Kamar wanda ta watsawa wuta ya zabura da faɗin"a'a zan tafi zan je na sha maganin sai na kwanta". Sai da ta kalle shi sosai kana ta ce"babu inda zaka je a cikin wannan yanayi koma ka nema waje ka zauna". Babu yanda ya iya haka ya koma ya zauna ko sallan isha'i a gida ya yi, ana fitowa daga masallaci Hamma Abubakar, Adnan da Ahmad suka shigo a tare. Hamma Abubakar shi ya fara tambayar Anwar dalilin da ya bai gan shi a masallaci ba. Abasiyya ta yi caraf ta sanar dasu abinda ya faru ganin ya ƙi faɗa kai tsaye sai hanya hanya yake yi. Duk sannu suka yi masa kafin Hamma Adnan ya shi ɗaki ya ɗauko masa wani magani ya ba shi ya sha. Tunda suka shigo na kasa ɗago kaina na kalli inda suka zauna, amma jikina yana bani tabbacin cewar idanun Hamma Ahmad yana kaina don haka na kasa samun nutsuwa. Na tashi na koma ɗaki, daren ranar ban iya runtsawa kamar yanda na kasa faɗawa kowa damuwar dake raina. Na kasa tantancewa shin ina son Hamma Ahmad ko a'a, shin a ɗan uwa na ɗauke shi ko kuma masoyi. Har gari ya waye raina a cunkushe ban fito daga ɗaki ba sai da na ji gyaran muryar Baffa ya fito zai tafi kasuwa su Hamma Ahmad suna gaishe shi, sannan na fito. Na tsuguna na gaishe shi ya amsa mini fuskarsa da fara'a, kafin ya soma tambayar jikin Anwar a wajen Abasiyya da ta shigo yanzun. Ta ce da sauƙi amma har yanzu ma yana kwance a ɗaki, duk addu'ar samun lafiya muka yi masa suka fita da nufi zuwa duba jikin nasan. Ɗaki na koma na yi kwanciyata duk abin duniya ya ishe ni duk tambayar da Abasiyya take mini ban tanka mata ba, har ta gaji don kanta ta yi shuru. Sai da na ji Umma ta ɗago labulen ɗakin tana shaida mana za ta je dubo jikin Anwar sannan na miƙe ina faɗin"nima zan je". Tare duk muka fita muka nufi gidan bayan mun gaisa da Dada muka shiga ɗakinsa, yana kwance lulluɓe kirif da bargo. Muka zauna muna yi masa sannu ya ɗago kansa ya dube mu yana ƙoƙari tashi zaune. Idanunmu suka sarƙafe cikin na juna ya yi saurin ɗauke na shi, na cigaba da kallon shi da muraɗi ko zai ƙara ɗago idonsa amma ya ƙi yarda mu haɗa ido. "Da Umma kuke tare ne?". Ya katse shurun da ya karaɗe ɗakin, na ɗauke idona daga kan shi ina sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. "Tare muke da ita". Abasiyya ta amsa masa kansa ya jinjina, na yi saurin tare hawayen da suke ƙoƙarin zubo mini. "Ke kuma lafiyarki? Kukan nan fa?". Abasiyya da ta ankara da ni ta furta kaina na jijjiga mata alamar ba komai ta taɓe baki tare da ficewa daga ɗakin. Cikin sanyi jiki da na murya na ce"ya jikin?". "Da sauƙi". Ya amsa mini a gajarce, na kuma faɗin"ka yi haƙur...". Ya yi saurin katse ni"ba ki yi min komai ba". Hawayen da nake matsewa suka zubo"na kasa sanar da kowa Anwar". Ina iya jiyo sakakken ajiyar zuciyar da ya sauƙe kana ya soma cewa"ki kwantar da hankalinki domin kowa ya sa ni, ko jiya Dada sun yi zancen da Baba da ya shigo". "Me yasa jiya ka faɗi bayan na sanar da kai maganar nan?". Cije leɓansa ya yi alamar ya fara gajiya da zancen ya ce"babu na ce miki babu komai". Yanayin yanda ya yi maganar ya sanya ni miƙewa na fice daga ɗakin, Dada da Umma suka bi ni da kallo sa'ilin da nake faɗawa ɗakin kwanan mu. Ina ji Umma na faɗin ko dai jikin Anwar ne ɗin ya yi tsananin da ya sanya ni kuka. Labulen ɗakin da iska ya ɗage shi ya bani damar hango su yayin da suke tashi suka nufi ɗakinsa. Sai da muka baro gidan tare da Umma sannan na fito daga ɗakin. Washe gari bayan ba iddar da sallan asubahi ina zaune akan sallayan da al-ƙur'ani ajiye a gabana na kasa buɗewa balle ba karanta. Umma ta shigo ta zauna kusa da ni sai da na daidaita nutsuwata kana na gaishe ta cike da girmama ta amsa mini tana ɗaurawa da"menene yake damun ki cikin kwanakin nan duk kin canza?". Na jijjiga mata kaina alamar babu, ta kamo hannuna ta sanya cikinta" 'yar nan ni mahaifiyarki ce babu wani abinda za ki ɓoye min. Fuskarki ta daɗe da bayyanar da damuwar da kike ɓoyewa a cikin ranki, shuru ba ya taɓa zama mafita domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Zancen haɗin aurenku da Ahmad shi ne yake sanya ki cikin damuwa?". Da sauri na ɗauro idona cike da mamaki na sauƙe a fuskarta. "Kema kin sa ni kenan Umma?". Ta sakar mini murmushi kana ta ce"na sa ni Baffanku ya sanar da ni kuma na yi na'am da wannan haɗin. Ahmad ɗan uwanki ne da ko bai aure ki ba shi mai iya tsayawa akan dukkan lamuranki ne, ko muna nan ko a bayan idonmu. Ki amsa masa domin ku ƙara fahimtar juna". "Ba na jin son sa ne ko kaɗan a raina". Na furta ina sunkuyar da kaina cike da kunya, ta sanya hannunta ta tallafo fuskata tare da faɗin"idan kika ba shi dama zai koya miki yanda soyayya take, har kema ki fara son sa". Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe mai ƙarfi. "To". Na furta can ƙasan maƙoshina ta shafi kuncina tana sami mini albarka cike da jin daɗin amsan da na bata. Tana fita na zabga tagumi wataƙila idan na bi maganarta na bashi daman sannu a hankali son sa nima ya shige ni. Sai da hantsi ya fito sannan na fito waje domin baccin da ban samu na yi shi daren jiya bane, na fashe shi da asubahin ba tare da na sani ba. Sanda na fito har su Baffa sun tafi kasuwa. Na taya Umma aikace-aikace, kwaɗon zogala musamman ta yi ta ce na kai wa Anwar kafin da yammaci tazo ta ƙara duba jikin nasan. Na iske Dada da Adda Abida a tsakar gida na gaishe su sannan na shiga ɗakin Anwar. Yana zaune idanunsa akan rufin ɗakin ya yi nisa cikin tunanin da ya faɗa, ina sanya ƙafata kunnuwana suka jiyo mini zancen da ya tsaya ni yin mutuwar tsaye jikina gabaɗaya ya fara rawa. "Ina son ta wallahi ba zan iya jurar ganin ta a gidan wani ba ni ba, ko da kuwa wanene. Allah ka mallaka min wannan baiwar takan domin kai kaɗai ka san irin tsananin son da nake yi mata". Yana ƙare zancen hawaye suna rige-rigen zubowa daga idanunsa, ganin kwanon zogalen na ƙoƙarin faɗuwa daga hannu ya san ni dosara shi a wajen na ƙarisa shiga ɗakin. Har na zauna bai san da kasantuwa ta a cikin ɗakin ba sai na ƙira sunansa, ya yi figigi ya dawo hayyacinsa yana goge hawayen da suka ɓata masa fuska. "Wacece ka ke so haka Anwar? Da son ta ya jefa ka cikin wannan halin?". Tabbas na ga alamar firgici akan fuskarsa da kuma ruɗewa, ya gyara zaman sa da kyau"ni kuma? Babu wacce nake so ko mun taɓa wannan maganar dake?". Na yi masa kallon gefe ido na ce"baka taɓa ba yanzu dai kunnuwana suka jiye mini kana faɗa". Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce"ban ma san na faɗi hakan ba, wataƙil zafin zazzaɓin da nake ji ya sanya ni sumbatu". Ba don na yarda da furucinsa ba na jinjina kaina ina faɗin"Allah ya sauwaƙe". Na tashi na ɗauko kwanon na ajiye masa a gabansa tare da cewa"ga zogale Umma ta aiko maka, ta na maka sannu kafin anjima ta shigo". Da hanzari na juya na fice kamar zan kife na faɗa kan cinyar Adda Abida ina rero kukana. Babu tambayar da basu yi mini ba amma na ƙi cewa dasu komai, Dada da ta fusata ta fara balbale Anwar da masifa da tambayar sa ko wani abun ya yi mini ya ce a'a. Na saddaƙar tare da ƙudurin ba wa Hamma Ahmad dama kamar yanda Umma ta ba ni shawara. Bayan mun yi sallan magrib muka fito tare da Abasiyya, a ƙofar gida muka tarar da Baba Alhaji zaune a bisa tabarma da wani matashi a gabansa ya duƙar da kansa ƙasa yana sanye da fararen kaya tas. Ban tsaya wani ƙare masa kallo ba domin abinda yake gaba na ma kaɗai ya ishe ni, muka tsuguna muka gaishe da Baba sannan muka wuce cikin gidan. Ta wuce ciki ni kuma na tsaya ina sallama a ɗakin dake zaure sai da ya bani iznin shiga sannan na shiga a hankali bakina ɗauke da siririyar sallama. Bayan na gaishe shi kowa ya yi shuru, ya katse shurun da faɗin"an gama wasan ɓuyan da ake yi da ni kenan, yau an kawo kai?". Na ƙara yin ƙasa da kaina ina wasa da yatsun hannuna. Sautisa ya kuma dira a kunnuwana a karo na biyu"to ina jin ki". Kunya ya hana ni samun ta inda zan fara yi masa bayani, take wani dabaran ta faɗo mini na miƙe na ce"daman zan ba wa Abasiyya saƙo ne ta ba ka, shine na zo na sanar da kai". "To ina maraba da wannan saƙon". Ya faɗa yana ƙara yalwata annurin fuskarsa, ina fita na saki nauyayyar numfashi. Ɗago idon da zan yi na ga Anwar tsaye a gabana ya kafe ni ido, sosai yake mini kallon da sai ya tsorita ni. Na yi masa alama da hannuna akan lafiya, bai tanka mini ba illa girgiza kansa da ya yi ya fice. A gidan na kwana washe gari muka je gaida Umma ni da Abasiyya. Na yi zaton su Baffa sun tafi kasuwa domin ba su taɓa kai wa irin wannan lokacin a gida ba, da mamakina na gan su zaune a filin tsakar gidan kusa da garken tumakai. Umma na zaune daga gefen su akan kujera, sallamar da muka yi ya sanya su zubo mini idanu. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 0️⃣7️⃣ Muka tsuguna muna gaishe su gabaɗaya cike da tarbiyar da suka ɗora mu a kanta ɗorar, suka amsa mana a tare yayin da Baffa da Baba Alhaji suke miƙewa. "Ki yi mata bayanin komai". Umma ta ɗaga kai" in sha Allah a dawo lafiya Allah ya tsare ya bada abinda aka je nema". Tun tasowar mu muka buɗe ido muke ganin yanda Umma da Dada suke zazzagawa Baffa da Baba Alhaji addu'ar, yayin da duk zasu fita neman halali. Ba sai sun furta cikin kalmomin baki cewar suna jin daɗin addu'ar ba domin fuskar su ya riga da ya bayyanar da labarin zuciyoyinsu. Muna addu'ar a dawo lafiya muka yi musu suka fice, sannan muka koma kan tabarman muka zauna. Umma ta kallo ni ta na sakin ajiyar zuciya"ku share filin gidan, sannan ke kuma ki zo ki same ni a ɗaki in kun gama. Za mu yi magana". Take na ji ƙirjina ya harba da matuƙar ƙarfi, a sanyaye na amsa da"to". Muka miƙe muka ɗauki tsintsiya muka fara sharan. Muna gamawa na nufin ɗakin Umma da sallamata ba ta amsa mini a zahiri ba illa idanun da ta tsura mini har na yi wa kaina mazauni a ƙasa kusa da ƙafafunta. "Ga ni". Sai da ta washe wasu tsawon daƙiƙu kana ta ce" 'yar nan jiya wani bawan Allah yazo wajen Babanku da zancen neman iznin fara tsayiwa dake, a matsayin saurayi da budurwa". Take na ji wani zuffa mai maiƙo ya karyo mini, ban ɗago kaina ba har ta ɗaura"Baffanku ya yi faɗa sosai akan me yasa ma ya saurare sa bayan ya ji abinda yake tafe dashi, ya kuma ce a sanar dake ki ba wa Ahmad dama domin babu fashi haɗawa da na so Adnan da suke so a yi tare". "Wallahi ni bana kula kowa kema kin sa ni, kuma babu wanda ya ce zai zo gidan mu". "Na yarda da ke amma dai ki kiyaye sosai don Baffanku ya fusata ainun, ya kuma shaidawa Babanku idan ya dawo ya sanar dashi cewar an yi miki miji kuma auren ba zai ɗau lokaci ba za a ɗaura ". Na faɗa tunanin to waye wannan mai zarra da ƙarfi halin da ya iya tunkaran iyayena kai tsaye?. A iya tinani ban taɓa tsayiwa da wani ba balle har ya san gidanmu ya zuwa iyayena da wannan maganar. Zancen murya ya katse mini hanzari. "Ba ki da mijin da ya wuce Ahmad don haka ki karkara dukkan hankalinki gare shi". Ban iya cewa da ita komai ba sai jinjina kaina da nayi, ta sa mini albarka tare da umarta ta da na tafi. Haka na fito jikina tamkar wacce aka zarewa laka, duk wunin ranar na ƙarar dashi wajen tunanin waye wanda ya zo wajen Baba Alhaji jiya, har zargi na yi kodai wannan matashin da muka tarar dasu jiya tare ni?. Take zuciyata ta ƙaryata hashashen ƙwaƙwalwata babu ta yanda za a yi wannan matashin da ya murza shadda mai wakilya ya zo neman iznin fara zance da ni, duk da ban ga fuskarsa ba amma ban bari ba yaudari kaina da tunanin mallakan irin sa a matsayi abokin rayuwa ba. Sai da muka je kwanciya na sanar da Abasiyya ta faɗawa Hamma Ahmad cewar na bashi dama, haƙiƙa farin cikinta ya ƙara ruɓanya babu abinda yake yi mini sai godiya tare da jadadda mini cewar gari na wayewa zata fara yi masa albishir da wannan daddaɗan labarin. Haka na kwana cikin fargaba da tatardadin da ban san dalilin tsintar kaina a cikin sa ba, muna cin abinci Hamma Ahmad ya shigo ina jin muryarsa gabaɗaya ya yi faɗu da ya haddasa mini runtse idanuna. Na miƙe da sauri na shige daƙi ina jin Adda Abida da Abasiyya suna yi mini dariya. Na sauƙe ajiyar zuciya jin da na yi yana yiwa Dada sallamar ya tafi kasuwa. Ya ɗago labulen ɗakin ya kare ni da ido na yi saurin rusunar da nawa ƙasa, ina iya jiyo saurin dariya da ya yi taƙaitacciya kana ya furta"sai ki fito cigaba da cin abincinki, tunda dodon da kike gudu ya tafi". "A'a ni fa ba kai nake gudu ba".Na faɗa cikin inda-inda bai. "Shikenan in na dawo da dare zamu yi magana kar ki yi bacci da wuri". Kaina kawai na ɗaga masa ya saki labulen ɗakin ta juya dai-dai sanda ruwar ƙwallar da suka wadaci koramar idanuna zubo. Haka na wuni kamar marar lafiya gabaɗaya na rasa gane kaina, ana ƙiran sallan magrib fargaban da na wuni a ciki ya tsananta. Na zari hijabina zuwa duba jikin Anwar da har yanzu yana kwance, kiciɓusu muka yi dashi Ai shiga gidan yana dawowa daga masallaci. Muka haɗa ido ya yi saurin ɗauke nashi tare da ƙoƙarin shigewa na yi saurin riga shi shiga, tare da tsayawa a gabansa. Har yanzu idanuna suna kan fuskarsa na ce"wai me ye yake faruwa na kasa gane kanka gabaɗaya, wani laifin na yi maka ne?". Sai da ba cire rai da samun amsarsa kana ya furta"ba komai tun ba yau ba na faɗa miki ba komai". "Ba gaskiya kake faɗa ba wallahi wannan ba gaskiya bane, bayan ka san ina cikin tsaka mai wuya na taskun da su Baffa suka jefa ni. Shi ne kai ma ka bijiro da wannan halayyar da waye kake so na zauna na sanar dashi damuwata ya fahimce ni?. Bayan da kai kaɗai zuciyata ta aminta da ta ji sirrin dake adane a cikinta". Na faɗa idanuna suna kawo ruwar ƙwalla, jingina ya yi da bango yana cije leɓansa tare da runtse idanunsa kana ya buɗe su tar a kaina. "Ki yi haƙuri wallahi ba zan iya sanar dake abinda yake damuwa ba a yanzu, kawai ki taya ni da addu'a Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar". Yana ƙare faɗin hakan ya shige cikin gidan ya bar ni tsaye a wajen, sai da na yi kokawa da numfashina da yake sarƙewa kafin na ja ƙafafuna na ƙarisa cikin gidan. Ban tarar dashi a tsakar gidan ba da nake kyautata zatona cewar ɗakinsa ya wuce. "Akwai abinda yake damun yaron nan, gabaɗaya ya canja". Dada ta furta cike da kuma Adda Abida ta karɓe zancen da faɗin" nima na lura da kanka dubi fa wani ramar da ya yi kamar wanda ya kwashe watanni yana jinya". Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ina jin wani ɗaci a raina, sai bayan isha'i Hamma Ahmad ya aiko ƙirana na je. Yake shaida mini ya ji saƙona a wajen Abasiyya kuma ya gode tare da yi mini alƙawarin ba zan taɓa da na sanin bashi damar kasancewa abokin rayuwata ba. Cike da kunya nake amsa masa, ya rako ni har zauren gidanmu ya ce na fara shiga shi zai biya wani waje kafin ya shigo. Wasa-wasa asaran rai haka aka makonni biyu, babu abunda ya sauya zani na daga matsayin da na ajiye Hamma Ahmad a zuciyata na ɗan uwana. Duk ƙoƙarin kyautata mini da yake yi da bani kulawa bai sanya na ji son sa a cikin zuciyata ba. Gefe guda ga rashin sake mini fuska da wasa da dariyar da Anwar yake mini da ya fi komai jefa ni cikin damuwar da ya haifar mini da yi wata 'yar rama. A lokacin na fara yin sallan istikata na neman zaɓin Allah kamar yanda Dada ta umarce ni na yi, tare da roƙo na da na sanar da ita duk canjin da na ji a raina. Haka na yi har na tsawon kwanaki bakwai, zuciyata ta kasance tamkar dutsin da ba ya jin shuri da ƙafa balle zunguri domin har yanzu bana jin koda ɗigon soyayyar Hamma Ahmad a cikin zuciyata sai dai na kan yi masa kara ina dannewa saboda alaƙar 'yan uwanta mai ƙarfi da yake tsakani. Ranar da na yi kwana biyu da gama sallar neman zaɓin Allah Dada ta aiko ƙirana, ban yi ƙasa a gwiwa ba na gurfana a gabanta. "Na ƙira ki ne na ji shin ko an sama canji, bayan istikatan da kika gudanar?". Na sunkuyar da kaina ƙasa domin Allah ya sa ni ba zan iya kallon tsabar idon Dada na furta mata cewar bana son ɗanta ba, alhalin ita bata da burin da ya wuce faranta mini da ganina cikin walwala. Ganin na kasa cewa komai ya sanya ta ƙara faɗin"ke nake sauraro kar ki ji nauyin sanar dani komai, domin aure ba abun wasa bane. Dole sai da so da ƙauna a tsakani domin su ne ginshiƙin da yake riƙe aure har ya yi tsawon rai, kar ki yi duba da matsayin Ahmad a gare ni hakan ya sanya ki ɓoye abinda ke zuciyarki". "Zan iya zama da Hamma Ahmad koda kuwa babu son sa a cikin zuciyata, zan yi wannan sadaukarwa a gare shi domin kuwa ya cancanci fiye da hak..". Tun kafin na ƙarisa ta yi sauri kwaɓa da faɗin"kul kul kar ki soma wannan tunanin, cikin dukkan lamuran zaɓi Allah yana kan gaba shin ki na jin son sa a cikin zuciyarki ko kuma a'a?". Take na ji wani zuffa yana tsatstsafowa daga jikina na ƙara yin ƙasa da kaina cike da kunyarta. Na ji hannayenta a bisa nawa"Aishatu sanar da ni komai kar ki ji nauyina, yanda na su Azima suke a wajena kema haka na ɗauke ki. Kuma na yi miki alƙawarin cewar ba zan taɓa bari ki auri wanda babu shi a zuciyarki ba. Domin na san ɗacin dake cikin haka tamkar gudanar da rayuwa ce cikin duhun makanci da babu san ran zuwan haske ta wani ƙofa". Sai da ta sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya mai bayyanar da damuwar dake danƙare cikin ƙalbinta kana ta cigaba da"ban taɓa ganin sa ba sai bayan an ɗaura mana aure, na yi biyayyar iyaye na zauna dashi kuma na yi masa biyayya dai-dai gwargwado tare da ƙoƙarin sauƙe duk haƙƙinsa da Ubangiji ya ɗaura mini. Sai dai har muka haifi Ahmad ban taɓa jin soyayyarsa a cikin zuciyata dai-dai da rana ɗaya ba sai dai hakan bai hana yi bashi girmansa da yin biyayya da dukkanin umarnin sa ba, na kan shiga ɗaki na ci kuka har na godewa Allah. A haka ba rayuwa har muka haifi 'ya'ya biyar dashi har yanzu da nake yi miki wannan maganar da ban taɓa sanar da ko wani mahaluki ba. Ba zan so ki yi irin wannan rayuwar ba". Sai a lokacin na iya ɗago idona na sauƙe su akan fuskarta da idanunta suka tara ruwan hawaye. Tabbas Dada ta cancanci a ƙira ta da jarumar mace kuma jajirtacciya a cikin jerin matayen wannan nahiyar gabaɗaya. "Dada zan yi biyayyar iyayen ni ma zan zauna dashi kodan na cigaba da samun albarkan iyayena". Sai da ta yi jim kana ta furta"yarinya ce ke kuma zuciya bata ƙashi kar ki je garin nemar yarda iyaye ki jefa kanki da rayuwarki cikin garari. Ki bar zuciya akan abinda bata so domin babu irin kyautatawan da bawan Allahn nan baya min amma hakan bai canja komai ba". Gabaɗaya jikina ya gama yin mutuwa na gama narkewa cikin tsantsar mamakin yanda zaman auren su yake. Na ƙara yarda da sahihacin wannan karin maganar na Hausa "mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo". Ta ɗago haɓarta"kar ki damu in sha Allah zan san abin yi akan hakan". Kaina kawai na ɗaga mata hawayen da ban shirya musu ba suna zubowa daga idona ta sanya hannu tana share mini su. Lumshe idona na yi cikin raina ina ƙara jinjina ƙarfin soyayyar da Dada take yi mini da babu algus a cikinsa. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 0️⃣8️⃣ Tun bayan da muka zanta da Dada na rage damuwar da na azawa kaina, Anwar ma ya sauƙo ya fara sakar mini fuskata sai dai jikinsa babu cigaba kullum ji-i-yau. Bana taɓa mance safiyar wata asabar da kai tsaye zan iya ƙira da baƙar rana mafi muni a rayuwata. Kafin su Baffa su fita kasuwa suka ƙira mu gabaɗayanmu muka haɗu a filin tsakar gidanmu akan babban tabarma. Baffa ya yi gyara murya yana cewar" mun taru a nan ne domin tabbatar da wani babban lamari da muke saka ran ya sama alkhairi a gare mu gabaɗaya in sha Allah. Mai babban suna shin kun daidaita tsakanin ku da Aishatu?". Hamma Ahmad yake nufi domin haka yake ƙiransa a ko yaushe, kasancewar sunansa ya ci. Wajen ya ɗauki shuru kowa yana dakon sauraron abinda zai ce. "Mun samu daidaito sai dai na ce ta yi istikata har yanzu bata sanar da ni canjin da aka samu bayan gudanar da hakan ba". "Shin bayan gudanar da istikaran da kika yi kina jin Ahmad a cikin ranki ko kuwa?". Baffa ya watso mini tambayar da ya sanya hanjin cikina kaɗawa, na kasa cewa komai illa ƙasa da na yi kaina jikina yana rawa. Na ji muryar Dada sun sauƙa a ƙofofin kunnuwana. "Ta gudanar da istikara da nufin neman zaɓin Allah, amma sai dai har yanzu bata jin Ahmad a cikin ranta. A tunani zai fi kyautuwa a bata zaɓi ta zaɓa wanda take so. Domin zaman aure da wanda babu shi a zuciyarka wallahi abu ne mai wahalar gaske musamman idan aka yi duba da ƙaranci shekarunta. Kar aje garin neman ido a rasa gir.." Baffa ya tari numfashinta" bata son shi daman tun asali na fahimci haka". Ta buɗe baki da zumar kare ni ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu"ba ta son shi ne kawai, domin na lura tun lokacin da muka ba shi damar yaje ya nema amincewarta. Gabaɗaya ta canza ta daina walwalar da ta saba balle gudanar da lamuranta kamar da. Ba ki da mijin da ya wuce Ahmad matuƙar ni ne haife ki kuma in na isa dake". Cikin tsananin ɓaci rai ya yi maganar da hakan ya sanya ni ƙasa yin wani ƙwaƙwaran motsi. Baba Alhaji ya ɗaura da faɗin"ash ash asha yaya ban so ka furta hakan ba. Ya kamata a karɓa uzurinta domin uzuri ne mai ƙarfi da ya kamata a saurara. Istikata fa aka ce ta yi sallar neman zaɓin Allah kuma bayan gudanar da hakan ya kasance cewar bata jin sa a cikin ranta. Hakan yana nufin babu alkhairi cikin wannan haɗin koda kuwa an yi shi, kamata ya yi mu yi hamdala mu godewa Allah ya hakan ya bayyana tun gabannin a kai ga ɗaura auren". "Dama tun can ba son shi take yi ba shiyasa ta yi amfani da wannan hanyar wajen bijirewa zaɓinmu". "Don Allah Yaya ka sanyawa zuciyarka ruwan sanyi da lumana, a bi komai a sannu idan hankali ya ɓata hankali ake sanyawa a nemo shi. Wallahi ko an ɗaura wannan auren babu abinda za a dunga cin karo dashi sai tarin da-na-sani da nadama a yayin da lokaci ya ƙure mana, kar mu bari ɓaci rai ya sanya mu mance da ilmin addinin da muke dashi . Neman zaɓin Allah akan duk wani abun da kake ƙoƙarin yi abun ne mai matuƙar kyau domin Annabinmu ma ya umarce mu da yin hakan a dukkan lokacin da muke son aikata wani abu. Tunda lamarin ya kasance haka ni ina ganin akwai mu ba wa wancan bawan Allahn da ya taɓa zuwa neman iznin fara zance da ita dama, mu yi bincike a kansa idan an same shi da dukkan nagartattun halayya sai mu bashi damar turo manyansa". So nake na ɗago kaina amma sam na kasa domin ba zan iya haɗa ido da Baffa a wannan yanayin ba, cikin wani irin yanayin da tunda Umma ta haifo ni na zo duniya ban taɓa kunsa a cikin makamancinsa ya soma ba wa Hamma Ahmad haƙuri. "ka yi haƙuri mai babban sunan ni nayi maka alƙawarin aura maka Aishatu ba tare da na san hakan zata kasance ba, ta watsa mini ƙasa a ido tare da karyar mini da zuciya. A yau da ina da wata ɗiyar bayan ita da babu abinda zai hana na aura maka ita daren yau ɗin nan ka ɗaure ta ku tafi. Babban burina na aurar da ita ga ɗaya daga cikin 'ya'yan ɗan uwana ɗaya jal da ya rage min a duniya, domin na yi imanin komai runtsi komai wuya da tsanani da yanda rayuwa za ta juya zai riƙe ta bisa amana zai kuma samar mata da rayuwa mai inganci. Shuru ya biyo bayan zancen na san na ƙarshe, babu shiri na ji wani kuka mai ƙarfi ya kubce mini. Na rarrafo na iso gaban Baffa cikin kuka na ce"ka yafe mini ka yafe mini Baffa, wallahi ba zan taɓa watsa maka ƙasa a ido ba. Ba zan taba baka kunya ba akan ko menene matuƙar ina da damar yin sa in zai saka farin ciki zan yi shi komai wuyarsa". Da ƙyar na iddar da zancen saboda sarƙewa da numfashi yake yi, da kuma kukan da nake yi da dukkan ƙarfina. Sai da aka kwashi wasu mintuna kafin Baba Alhaji ya furta"tashi ku shiga ciki". Ya ƙare zancen yana nuni da ni da Abasiyya. Muka miƙe muka shige ɗakin kwanan mu, a cikin labulen na tsaya don ba zan iya samun kwanciyar hankali ba matuƙar ban ji abinda aka yanke ba. "Don Allah ni dai roƙo na mu bi komai a hankali, mu yiwa yarinyar nan adalci mana kar mu tauye mata haƙƙinta don kawai zuciyoyinmu su yi fari. Yaron nan shi ya ce ta je ta yi da istikara to menene laifinta bayan gudanar da hakan ta ji cewar ba ta son shi. Bamu ilmi fa mu Yaya duk yanda muka kai ga son haɗa yaran nan aure babu wanda muka iya matuƙar Allah bai tsara su zamo ma'aurata ba. Ko yanzun mun cika burin mu tunda mun haɗa zuri'armu aure, ga Abubakar da Azima sannan in sha Allah ga Adnan shima da Abida shin ko hakan kaɗai bai isa ya sanya mu godewa Allah ba?". Furucin Baba Alhaji kenan da ya tursasa mini sakin nauyayyen ajiyar zuciya ina sulalawa ƙasa na zauna dirshan. Na kifa kaina akan gwiwata ina sakin wani kuka marar sauti. Na fahimci tunanin Baffa shi ne daman can bana son Hamma Ahmad tabbas haka ne amma bayan da na yi istikata haƙiƙa na ji ya ƙara cirewa daga raina. Har na ji motsin su Baffa su na ficewa ban ji Umma ta ce ko kanzil ba, na yi tunanin fitar su zai sanya ta shigowa ta ji daga gare ni sai na ga saɓanin hashashena. Abasiyya ma ficewa ta yi ba tare da ta ce da ni komai ba, hakan ya sanya ni ƙara sakin wani kukan mai ƙarfin gaske. Ban san tsawon lokacin da na ɗauka zaune a wajen ina kuka ba, har sai da na ji ana ƙiran sallan zurh sannan na tashi ina jin wani jiri yana ƙoƙarin mai da ni ƙasa. A daddafe na fito na yi alwalan na koma ciki na yi salla ina jin wani zazzaɓi mai zafi na ƙoƙarin rufe ni. Jin motsin Umma ta ta tsakar gida ya tilasta mini fitowa, tana zaune tana tsintar yakuwa na iske ta na zauna ina yi mata sannu ba ta tanka mini ba. Ban ƙara tsintar kaina cikin tafkin mamaki ba sai da na kai hannu zan ɗauki yakuwan domin tsintar da dakatar da ni"ajiye min kayana ban nema ki yi min ba, ki je ki yi kwanciyarki kawai". Kamar yanda maƙeri yake dukan ƙarfe haka na ji tamkar ana sanya guduma ana dukan ƙirjina. Idanuna cike da hawaye na ɗago ido na kalle ta sam ba ni take kallo ba ta mayar da hankali ga abinda yake gabanta. "Umma don Allah ku yi haƙuri wallahi ba laifi na ba ne, ba n...". Tun kafin na dire zancen ta katse ni" bana buƙatar jin komai daga gare ki 'yar nan". Hawayen da suka ciko mini kurmi idanu zubowa. Na kai hannu zan riƙo nata ta janye ban san lokacin da ya cilla wani uban ihu ba ina faɗin"na shiga uku ni kam na shiga uku". Na tashi a zabure na faɗa ɗaki na ɗauko jikan da na kasa sanya shi a jikina, na lulluɓa shi a kafaɗata. Kamar zautacciya haka na fita ina tafe ina kuka na ɗaura hannayena a kaina. Na faɗa cikin gidan tamkar wacce aka jefo Dada da Adda Abida suka tashi a tare su na tambayata lafiya. Na isa ga Dada ina kwantar da kaina a kafaɗata. "Me ya faru?". Ban amsa ba ta har muka zauna na zamar da kaina izuwa kan cinyarta, a hankali take bubbuga bayana tana mai cigaba da cewa"me ya faru ne? Ko Umman naku ce ba lafiya?". Sai a sa'ilin na ɗago fuskata muryata har ta dishashe"Umma ta daina Kula ni yaya zan yi Dada?". Na ƙare zancen ina ƙara fashewa da wani kuka tare da mayar da kaina kan cinyarta. "Ki yi haƙuri a hankali zasu fahimta cewar ba laifinki bane, dole yanzu da suke cikin ɓacin rai sai kin yi haƙuri da su". Ban tanka mata illa sausauta kukan da nake yi da yi, haka ta cigaba da kwantar mini da hankali tare da nuna mini cewar komai zai daidaita da iznin Allah. Zancen da Adda Abida ta furta ya sanya ni ɗago kaina babu shiri tare da zube rinannun idanuna akan fuskarta da take yatsina shi yayin maganan. "Ai daman duk tsuntsun da ya ja wallahi shi ruwa yake duka. Ta yaya daman za ki yi tsammanin cigaba da samun yanda kike so bayan kema ba ki yi musu abinda suke so. Ki yi ɗamara domin wannan shi ne wasa farin girki". Tsawa Dada ta doka mata da ya tilasta ta haɗiye raguwar zancen ba tare da ta furzo mini su ba. "Ba ki da hankali ashe Abida? Ko kin manta wacece kike gayawa wannan kalaman?. Kema ashe duk taron tsintsiya ne babu shara, ke dole aka yi miki da Adnan? In ce dai sai da kika furta kina son sa sannan, to me yasa ita ma ba za a bata damar zaɓan wanda take so ba, laifi ne don ta faɗa abinda ke zuciyata? Kar ki kuskura na ƙara yin kin maimaita irin haka don ranki zai yi mummunan ɓaci, tashi ki ba ni waje shashasha kawai". Ba tare da ta ko kalle gefen da nake ba ta tashi ta shige ɗaki, na riƙo hannun Dada gam na riƙe"kin gani kin gani ko Dada. Kowa wani kallo daban yake yi mini yaya zan yi da raina, ina zan sanya kaina na ji sanyi don Allah Dada ki faɗa mini". Lallashina ta cigaba da nusar da ni cewar duk abinda ya yi farko tabbas ƙarshensa yana nan zuwa. A jikinta na wuni ko nan da can bata motsa ba saboda zazzaɓin da ya rufe. Ko abinci na kasa ci ruwa ina sha nake dawo dashi. Tunda na zo Abasiyya bata kula ni ba balle tazo inda nake har ta yi mini sannu ko taya ni jimanin halin da nake ciki. Sai da aka yi sallan Asr, magrib ta fara kawo kai Dada ta ce na je ni gida bai kamata duk abinda Umma ta yi mini na guje ta na ƙi komawa ita ma in aka yi salla zata shigo su yi magana. Na ɗan dakata ko Abasiyya za ta ce zata raka ni amma na ga babu alamar za ta motsa daga inda take, dole na ja ƙafafuna na yi gida. Ko sannun da na yi mata yanzu ma bata amsa ba, na ji wasu hawaye suna rige-rigen fitowa daga idona. Zan yi magana ta ɗaga mini hannu dole na haɗiye zancen a cikina na tashi duk da bana jin daɗin jikina na ɗauki tsintsiya na fara share tsakar gidan. Ina gamawa ana ƙiran sallan magrib. Na yi sauri sawa Umma ruwa a buta na ajiye mata sannan nima na zubo wata butar na fara. Ina shafar kai na ji an yi kutubal da butar gabana na ɗauro da sauri don ganin waye. Na miƙe a sanyaye ganin Abasiyya tsaye a gabana tana kuka. Kafin na kai ga tambayar ta me ke faru, ta riga ni fara magana. "Hankalinki yanzu sai ya kwanta za ki kashe shi ki huta, wallahi kin ba ni mamaki da kika saka yin Wannan sadaukarwa ga Hamma Ahmad kin san tsananin farin cikin da ya shiga kuwa sanda na sanar dashi cewar kin amince masa. Amma duk da haka sai da kika karya masa zuciya ga shi can ya yanke jiki ya faɗi a kasuwa a dawo shi bai san inda kansa yake ba, wallahi idan kika yi sanadin da ya mutu ko ya kamu da wani ciwon ba zan taɓa yafe miki ba". ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 0️⃣9️⃣ Kafin na yi magana Umma ta riga ni furta"me ya same shi?". "Yana can an dawo dashi daga kasuwa ya faɗi ko motsi ba ya yi". Ko hijabin Umma ba ta gama sawa a kanta ba ta kamo hannun Abasiyya za su fice, na zabura zan bi su har mun isa zaure Umma ta juyo ta yi mini wani kallo tare da tsawan da ya sanya ni saurin sunkuyar da kaina ƙasa jikina yana rawa tamkar mazari. "Ina za ki je? Ko so ki ke ki je ki baƙin cikinki ya ƙarisa shi? Idan kika leƙa ko ƙofar gida ba da yawuna ba". "Don Allah ki bar ni na je". Na faɗa ina ƙoƙarin isa gare ta zan kama hijabinta ta yi saurin buge hannuna suka fice, a wajen na durƙushe akan ƙafafuna ina sakin wani kukan mai tsuma zuciya. Na sha kuka a wajen har sai da kaina ya fara sarawa, da ƙyar na ja ƙafafuna na tashi na koma ciki ina tafe ina haɗa hanya tamkar bugaggiya. Na faɗa ɗakin kwananmu ina mai cigaba da sakin wani kukan, ina jin kaina yana sarawa da matuƙar ƙarfi, a gigice na sauƙe wahalallen ajiyar zuciyar da ya tafiyar da kukan da nake yi. "Ya Rabbi". Na furta haƙwarana suna datse harshena, wani hali Hamma Ahmad yake ciki shi ne babban abinda nake buƙatar sani a halin yanzu fiye da komai. Sai na yi yunƙurin tashi domin na je na dubo shi sai na tuna gargaɗin Umma a gare ni dole na koma na zauna. Ganin zaman ba zai fishshe ni ba ya sanya ni tashi na je na fita na yo alwala nazo na fara gudanar da sallan magrib sannan na ɗaura da nafila. Na daɗe ina yin sallan da ban san adadin yawan raka'o'in da na yi ba, sai da aka yin ƙiran sallan isha'i sannan na tsagaita. Na yi sallan isha'i sannan na kwanta akan sallayan ina maida numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceto rai. Na kasa motsa lwa daga wajen haka nan izuwa yanzu na kasa yin hawayen da nake yi ina jin daɗi a cikin ƙalbina. Har karfe tara ya buga babu wanda ya shigo hakan ya sanya ni komawa zaure na zauna ina jiran dawowansu. "Me kike yi a nan wajen?, tashi ki shiga gida". Na yi Muryar Hamma Adnan tamkar a mafarki, na yi figigi na buɗe idona ina ƙoƙarin miƙewa ya komar da ni na zaune. "Ina yake ina Hamma Ahmad ɗin?". Na faɗa cikin dushashewar muryar da yake nuna cewar mai shi ya ci kuka ya ƙoshi, sai da ya ƙare mini kallon tsaf kana ya furta"jikinsa da sauƙi sosai, ko awa biyu ma bamu yi a asibitin ba aka sallame shi. Ƙarin ruwa kawai aka yi masa sai kuma magangunan da aka ba shi". A bayyane na sauƙe ajiyar zuciya"Alhamdulillah ina so na je na duba shi, amma Umma ta hana ni". "Ki kwantar da hankalinki ai jikin ma da sauƙi, su Umman ma yanzu zasu dawo tashi ki shiga gida". Ciki muka koma yana tambayata na ci abinci na ce masa a'a da kansa ya zubo mini abincin ya ajiye mini tare da umartata akan na soma ci. Sai da ya yi mini jan ido kafin na kai lomar farko cikin bakina. Ina cikin ci Umma ta shigo duk muka yi mata sannu da zuwa, ba ta amsa mana da kalamai ba illa ɗaga mana kai da ta yi tana shigewa ɗaki. Da ƙyar nake haɗiye abincin ta maƙoshina da nake jin tamkar ina haɗiyar ciyawa mai cike da ƙarangiya. Hamma Adnan shi ya yi ta kwantar mini da hankali ta hanyar furta mini cewar jikin da sauƙi, ko da na yi shirin kwanciya sam bacci ya gagari idanuna sai faman juyi nake yi idanuna ƙas tamkar na soyayyan kifi. Furucin da Abasiyya ta guntso ta fesa mini suna amsa-kuwwa a nau'rar naɗar sautina. Tabbas a 'yan tsakanin nan Hamma Ahmad ya nuni mini kulawa tsantsa sai dai a ba a yi wa zuciya dole musamman wajen tusa soyayya. Yanda na ga rana haka na ga dare ƙiran sallan assalatu farko kuwa a kunnuwana ya fara sauƙa na tashi jikina sam babu ƙwari na je na yi alwala. Na zo na fara sallan ina iddarwa na kifa kaina a bisa gwiwana raina cike da tarin damuwar da na kasa warware shi. Sai da gari ya fara yin haske na fito na fara yin sharan filin tsakar gidan, babu wasu kwanukan wanke-wanke domin daren jiya ni ɗaya jal na cakali girkin da Umma ta yi, don haka kwano ɗaya na wanke. Na zauna a dakalin ƙofar ɗakin kwananmu na zabga tagumi da hannuwa bibbiyu. A haka Baffa ya fito ya iske Umma ta na biye dashi a baya suka fito, na zube a gabansu tamkar baiwa ina gaishe su fuskokin su babu yabo babu fallasa suka amsa mini ba tare da sun ƙara cewa da ni komai ba. Hakan ya sanya ni tashi na koma mazaunina na zuba musu ido suna zantawa akan jinyar Hamma Ahmad ɗin. "Allah dai ya kiyaye gaba amma tabbas an auna sa'a. An kuma tsallake rijiya da baya domin yanda mai babban suna ya yanke jiki ya faɗi a rumfarsu babu wanda ya yi tsammanin abin zai zo da sauƙi haka. Haka aka kawo mana shi ranga-ranga tamkar matacce". Umma ta jinjina kai cike da damuwar da ta bayyana ƙarara akan fuskarta"Amin kam Allah kuma ya bashi lafiya ya sauya masa da mafi zama alkhairi a gare sa". "Amin zan fita kasuwa amma da wuri zan dawo". Addu'ar Allah ya kiyaye ta yi masa kamar kullum har zai fice na yi saurin katse shi da faɗin"Baffa idan ka ba ni izni ina so na je na duba jikin nasan, tun jiya na so zuwa Umma ta ce na dakata". Sai da ya yi jim kafin ya amsa mini a gajarce da hakan ya bani tabbacin cewar har yanzu yana fushi da ni kamar yanda Umma ma take fushi dani. "Za ki iya zuwa". Na zame daga zaunen da nake na zuba gwiwoyina a ƙasa ina godiya. Hamma Adnan ya fito suka fita tare. Sai da na ɗauko hijabina zan fita na je zan yi sanarwa Umma. Na tsuguna a gabanta"na shirya zan je". "Ki saka kunne ki saurare ni da kunnen basira saura idan kika je ki ƙara furta masa wani zancen da zai ƙara haddasa masa wani jinyar. Wallahi akan Ahmad za ki ga tsananin ɓacin raina da ba ki taɓa ganina tunda kika zo duniya". "To in sha Allah za a kiyaye". Na tashi na fita ina tafe ina hawaye har ba isa gidan, Abasiyya ce kawai a tsakar gidan tana jan ruwa a rijiyar da sai babu ruwa a famfo ake buɗe ta. Fuskata da maɗaukakiyar mamaki na kafe da kallo don a kalla na yi sallama ya fi baki uku amma ko a jikinta wai a muntsine kakkaura bata amsa mini ba. "Abasiyya kina ji ina sallama kika share ni?". Sai a lokacin ta ɗago ido ta yi mini kallon da na kasa gano manufarsa, ta zara gugar cikin rijiyar tana jawo ruwar ta ce"ai ba dole sai na amsa a fili kin ji ba, tunda ina da damar amsawa a cikin zuciyata". Wasu hawaye suka kwaranyo mini" Hamma Ahmad fa?". Ta buga mini tsaki"yau kuma baƙuwa kika zama a cikin gidan?. Ina ce da in kin zo kai tsaye kike shiga duk inda kike so". "Allah ya ba ki haƙuri, Abasiyya ki yi haƙuri". Ta buɗe baki za ta fara zance cikin tsiwa, na ji ƙarar sauƙar mari da ya bada sautin tas. Ihun da ta saka suka sanya ni saurin ɗago idona don ganin wanda ya ɗauke ta da wannan marin. Anwar ne tsaye yana huci ya nuna ta da 'yar manuniyar yatsarsa"ke kina da hankali kuwa? Wannan ba ta fi ki ba ne?. Ko hauka kika yi?. Ki nutsu ki koma cikin hankalinki domin komai ya faru gaba take dake". Ta yi jifa da gugar hannunta ya faɗa cikin rijiyar tana a sakin kuka tare da shigewa ɗaki. Ya tako ya iso gabana"ki yi haƙuri in ji?". Kaina kawai na ɗaga masa"daman na zo duba jikin Hamma Ahmad ne". "Ki shiga yana ɗakin zaure". Kaina na kuma jinjina masa, na juya na nufi zauren kamar kullum sai da na yi sallama ya bani iznin shiga sannan na shigo na zauna a inda na saba zama a duk sanda na zo ɗakin. Kafin na yi magana ya riga ni"na yi fushi tunda sai yanzu ma za ki zo duba ni". Na ƙara yin ƙasa da kaina"tun jiya na so zuwa sai kuma su Umma suka zo, babu wanda za a bari a gidan shiyasa amma yaya jikin?.". Ina jin taƙaitaccen murmushin da ya saka da ya fi kama da na dole kana ya ce" ba komai kar ki damu, jiki da sauƙi alhamdulillah". Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya cikin karayar zuciya na furta"ka yi haƙuri Hamma Ahmad wallahi ni ma ba yin kaina ba n...". Ban ƙarisa ba ya katse ni"ba komai Aishatu na yarda cewar Allah ne bai yi za mu zama ma'aurata ba kuma na fahimce ki. Kawai kin san zuciya bata da ƙash,i na kasa ɗaurewa ne a lokacin har hakan ya afku". Ya tsagaita kana ya sauƙe numfashi ya ɗaura da"ko wani gaskiya tana da ɗaci sai dai tabbas tana kwantar da hankali. Ni na roƙe ki akan kar ki ɓoye min komai ki ke ji a ranki game ni, to bai kamata na ga laifinki bayan ki sanar da ni abinda ni da kaina na roƙa ba. Ina miki fatan alkhairi da kuma addu'ar Allah ya ba ki miji na gari wanda zai so ki so na gaskiya koda rabin irin son da nake yi miki ne". Hawaye suka zubo daga idona ina musgutawa na ce"ka yi haƙuri ba zan taɓa daina baka haƙuri ba Hamma Ahmad, har ƙarshen numfashina". Sai da na cire rai da samun amsa daga gare shi sannan na ji ya soma faɗin"ban riƙe ki a zuciyata ba Allah ne shaida, sai dai dole zan shiga cikin yanayi amma duk abinda aka sanya haƙuri, dangana da miƙa wuya ga Allah komai zai wuce har ya zama tahiri. Zan tsaya tsayin daka a matsayina na ɗan uwanki wajen ganin kin auri duk wanda kika kawo kina son shi matuƙar da ya cike dukkan sharruɗan da ake nema yayin ɗaura aure". "Na gode kai ma Allah ya ba da wacce ta fi ni". Dariya ya yi sosai mai sauti"ba na jin akwai wacce zan iya ƙara so a rayuwata balle har soyayyar ta kai mu ga yin aure. Zan zauna haka na yi ta bautawa ubangijina har na iske wa'adina". Jikina ya yi sanyi ainun da ina da dama da na sharewa Hamma Ahmad hawaye domin kuwa ya cancanta ta ko wacce fuska. Sai dai ba ni da wannan ikon domin Sarkin da ke da iko da mu ya riga ya tsara komai. [9/13, 20:07] Maimunatu Iyam: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IPa4qxjMSC6Ke1K7zC3R0t ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 1️⃣0️⃣ Tun bayan faruwar lamarin na daina ganin fara'a akan fuskar Umma, idan ina zaune a waje kuwa komai zan yi ba za ta ɗago kai ta kalle ni ba balle ta ce da ni ci kanki. Na zage damtse duk wani aikin gidan kafin hantsi ya fito na kammala shi duk a ƙoƙarin farantawa Umma. Amma a banza tamkar ana ƙwalawa bebe ƙira babu abinda ya sauya zani. Ranar ina zaune na zabga tagumi bayan sallan magrib ni ɗaya Umma ta shiga wajen Dada. Domin tun bayan faruwar abun ba ta je ba a cewar ta wai kunyarta take ji da nauyin haɗa ido da ita. Hamma Abubakar ya shigo ina jin ya yi sallama na zabura ina ƙoƙarin miƙewa na shige ɗaki ya dakatar da ni. "Ina za ki je? Koma ki zauna". Na koma inda na tashi na zauna na sunkuyar da kai ina sauraronsa." Aishatu kin kyautawa kanki kenan?. Ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yanzu ga inda za ki sama kwanciyan hankali ana nuna miki gabas kina nausawa kudu, me ye aibun Ahmad wani halinsa ne ba ki sani ba? Ba ya shaye shaye, ba ya nema matan banza sannan bai taɓa kusantar zina ba da duk wani abinda Allah ya hane mu da aikata shi, kema shaida ce yana da ƙoƙarin ibada da kuma hidimtawa addini da ƙarfinsa da kuma aljihunsa. Shin bai da siffofin da duk wata macen ƙwarai take buƙata daga wajen ɗa na miji ne ko meye kin faɗa min?". Da sauri na girgiza masa kaina alamar a'a, hawaye suna gangarowa daga idanuna. Ya yi taku uku ya iso inda nake zaune ya nuna ni da 'yar manuniyar yatsarsa"to wallahi duk wanda za ki aura saɓanin Ahmad ba za mu taɓa farin ciki da aurenki ba". Muryata a shaƙe na furta"ku yi haƙuri Hamma Abubakar wallahi ba laifina bane". Kafin na rufe bakina na ji ya ɗauke ni da wani gigitaccen marin da tsabar azabar da na ji ya ratsa ni ko kuka na kasa yi, ina dafe kuncina da yake yi mini zogi. Ya ɗaga hannu da niyyar ƙara zabga mini Hamma Ahmad da Adnan suka shigo. Hamma Adnan ya yi saurin janye ni gefe ya riƙe ni, na kwantar da kaina a jikinsa na kasa kukan sai ajiyar zuciyar da nake sauƙe a kai a kai. "Me ye haka me ye haka Abubakar? Me ta yi maka da zaka yi mata wannan marin?. Baka tunanin nasiha da nusarwa za su fi yin aiki ga masu shekaru irin nata fiye da duka?". "Ta cancanci komai wannan yarinyar ba ta san halacci ba". Hamma Abubakar shi ma ya furta a zafafe, a lokuta da yawa idan ya hau dokin fushi da zuciya Hamma Ahmad sausatawa yake yi har sai ya sauƙo. Amma a wannan karon ɗaga masa murya shima ya yi. "Me ye laifinta don ta faɗa abinda yake ranta? ko kuma ku za ku zauna mata da ni bayan auren?. Kai auren dole aka yi maka ko kuma sai da aka nema amincewar ka?. Me yasa haka Abubakar me yasa kuka ƙasa fahimtar cewar tabbas akwai wata ƁOYAYYIYAR MANUFA na Ubangiji shiyasa duk haka ya faru". Sai da ya tsagaita kana ya cigaba da faɗin"in dai a kaina ake yi mata wannan musgutawan ba zan taɓa yafewa kaina ba har abada, kuma na gwammace na yi nisan zangon da garin nan akan kullum ina shigowa idanuna suna yi min tozali da wannan cin zalin da kuke yi mata babu gaira babu dalili. Idan tsoron lalacewar zumunci kuke gudu to abinda ta yi shine daidai kuma shi ne zai ɗaurar da zumuncin dake tsakani. Ka yi tunanin da ace sai bayan auren ta fara nuna alamomin ba ta sona me zai faru?". Har ya yunƙura zai ƙara yin wani maganar kamar wanda aka riƙewa baki sai kuma ya yi shuru, yana jijjiga kansa. "Kin ga abinda kika jawo ko?". Hamma Abubakar ya furta mini cikin daka mini tsawar da ta sanya Hamma Ahmad zabura ya isa gare shi tare da cin kwalarsa ya riƙe tamau. Idanunsa sun sauya launi yake faɗin"ka san yawan rantsuwa ba halayyata bane, amma na rantse da Sarkin da ba shi da abokin tarayya idan ka ƙara ɗaga mata murya ko ka kai hannunka jikinta da sunan duka sai na yi maka lakani Abubakar". "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Don Allah ku yi haƙuri ya isa haka nan". Hamma Adnan ya furta cike da damuwa a tattare da muryarsa. Babu abinda nake yi sai kuka na zube ƙasa akan gwiwoyinta tare da haɗe hannayen waje guda alamar roƙo. So na ke na ce da su suyi haƙuri amma sam na gaza samun haɗin kai daga wajen bakina domin na rasa yawun da zan sarrafa a cikin bakina har na iya furzo zancen wajen. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Me zan gani haka me yake faru?". Muryar Umma ta yi wa kofofin kunnuwana sallama, duk tambayar lafiyar da take musu ba su bata wani gamshashshen amsa ba sai ce mata su ke ba komai. Shi ma Hamma Adnan kawai yake iya ƙarfin halin furta mata hakan. A matuƙar fusace Hamma Ahmad ya fice yana dafe goshinsa duk muka raka shi da kallo. Hamma Abubakar ya nema waje ya zauna dafe da kansa. "Wai me yake faruwa ne? Kun bar ni a cikin duhu?". "Umma ki kwantar da hankalinki zamu yi maganar daga baya don Allah ". Hamma Adnan ya furta ya na ɗago ni na miƙe tsaye daga durƙushewar da na yi akan gwiwoyina. Da ido ya yi mini alamar akan na shige ɗaki jiri yana kwasata idanuna suna gani mini gilmawar baƙin duhu na shige ɗakin tare da faɗawa kan katifar kwanciyarmu. So nake yi na yi koda hawaye ne amma sam hakan ya garare ni, ji nake yi tamkar zuciyata za ta ɓallo allon ƙirjina ta fito waje tsabar damuwar da ya yi yawa a cikinta. Da na rasa samun ta inda zan warware shi. Filin gidan tsit bana iya jiyo motsin komai, har aka yi ƙiran sallan magrib ban iya tashi domin na je na yi alwala ba. Saboda nauyin da dukkan gaɓoɓin jikina ya yi mini ko yatsar hannuna bana iya motsawa shi. Ji nake yi tamkar na fita a gude na yi hauka ko zan ji sausaucin raɗaɗin da nake ya na ƙartar zuciyata. Ban ƙara tabbatarwa kaina cewar ina cikin tsaka mai wuya ba sai yau da wannan rikicin ya afku. Tun da na yi wayo na iya bambamce tsakanin fari da baƙi, nake iya rabewa tsakanin hagu da damana. Na san so, ƙauna da kuma shaƙuwar dake tsakanin waɗannan 'yan uwan biyun duk da Hamma Abubakar yana da zafi da zuciya Hamma Ahmad ya kasance tamkar ruwar ƙanƙara mai iya kashe duk wani wutar zafin zuciyar Hamma Abubakar. Ba su taɓa sa'in sa da junansu ba balle har ya kai su ga matakin ɗagawa juna murya ko bayarwa juna martani da zafafan kalamai. Sai gashi yau a ta dalilina sun yi abinda a tarihin bai taɓa faruwa a tsakanin su. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u!". Na furta ina mirginawa tare da dafe ƙirjina da nake jin tamkar ana soka mini tsinin mashi, juyi kawai na cigaba da yi da tunanin samun ɗauki amma babu ko alama. Tun daga lokacin na daina fahimtar komai sai sauƙar ruwar sanyi na ji ya na ratsa jikina. Na yi figigi na tashi a zabure ina sauƙe numfashi a wahale. Na damƙe hannun Dada da idanuna suke gano mini dishi dishi"Dada ki taimaka mini zuciyata zata fashe". Tofin wasu addu'o'in da take yi mini a bayyane ta cigaba da yi, hakan ya sanya ni komar da kaina kan cinyarta ina sauƙe numfashi. "Ki na ji na. Na tsayar da ƙwayar idona akan fuskarta tare da ɗaga mata kaina alamar e. Ta gyara mini zaman kaina dake jikinta"me ya same ki? Me ya yi zafi haka Aishatu ke kuwa?". "Zuciyata zafi take yi mini". "Ki yi haƙuri za ki iya tashi ki zauna?". Kaina na ɗaga mata ina cije leɓena na tashi na zauna na jingina kaina a jikin bango tare da lumshe idona, wasu hawayen masu ɗumi suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina. "Ki cire komai a ranki, kamar yanda na sha faɗa miki a baya cewar komai zai wuce". Na kasa cewa komai na gyaɗa mata kaina ta umarce ni da na fito na yi alwala. Umma ta na zaune kan tabarma na yi mata sannu da ba ta amsa ba. Kamar zan kife haka na ɗauki buta na shiga banɗaki. Waje na nema na zauna na ci kuka har na godewa Rabbana sannan na wanke fuskana na fito. "Yaya kuke son yarinyar nan ta yi ne? Ko so kuke ku ɗaura mata wani ciwon na daban da ba a san dashi ba?. Duk kun juya mata baya babu mai kula ta balle sauraron damuwarta a fahimce ta har ayi mata uzuri. Dubi fa halin da na shigo na tarar da ita a sume ba ta san inda kanta yake ba, in ba don Allah ya rufa asiri na shiga ba yaya kenan lamarin zai kasance?". Zantukan Dada kenan da na fara cin karo dasu yayin da nake fitowa daga banɗakin. Har na iddar da alwalan ba ta tsagaita ba kamar yanda Umma ba ta ce da ita komai ba. A zaune na haɗe sallolin magrib da isha'in na yi su domin ba ni da kuzarin iya tsayawa akan ƙafafuna da suke tangal tangal. Sosai na yi addu'ar neman sauƙi kana na shafa a sanyaye. Sanda Dada za ta tafi ta ce da ni na fito na bi ta domin ba zan zauna ni ƙadai wani abun ya kuma faruwa babu mai damuwa da duba lafiyata ba. Ko da muka je gidan Adda Abida da Abasiyya babu wanda ya yi mini kallo arziki balle yi mini yaya jiki duk da yanda Dada take ƙara kambama ciwon da yanayin da ta tarar da ni. Anwar ne kawai ke ta jeranta mini kalmar sannu kamar zai yi ƙwalla. A nan na kwana cike da kulawar Dada da Anwar, kafin na tashi ya saka mini ruwan zafi har ya kai mini banɗaki ya sanar da ni na fito na tarar da mutum a banɗakin. Abasiyya ce ta fito sanye da hijabin da take shiga wanka dashi, ya bi ta da wani kallo"da wani ruwa kika yi wankan?". "Ruwan da yake cikin banɗakin". "Sai ki wuce ki je ki dafa wani ruwan domin a Aishatu na ajiye wannan". Ta zaro ido waje"da wannan ɗanyar itacen zan dafa ruwan wanka?, sai dai zuwa anjima in an kawo bushashshen itac...". "Ki wuce ki yi abinda na sa ki". Ya faɗa a tsawace dai dai sanda Hamma Ahmad yake kutso kai cikin gidan, ya tambayi me ke faru Abasiyya da ta ɓarke da kuka na sanar dashi. Bai goyi bayanta ba shi ma ya ce ta je ta dafa wani ruwan zafin ta kai banɗaki. Na yi ƙasa da kaina domin bani da ƙarfin halin iya haɗa ido dashi bayan duk abubuwan da suka faru, na tsinkayo muryarsa yana faɗin"idan kin gama ina neman ki". Kaina kawai na ɗaga masa ya fice ya bar ni da sauƙe tagwayen ajiyar zuciya. Ɗakin Dada na nufo da na iske ta tana faɗa a Abasiyya tare da bata rashin gaskiya, sai da na yiwa kaina mazauni domin ba zan iya jure tsayiwarwa. Kana na sausauta muryata na ce"ki yi haƙuri Dada tsakanin mu da Abasiyya ai ya wuce haka. Nima sau nawa nake zuwa gidan nan ya ɗauki kayanta ba yi amfani dashi, kuma babu yanda ta iya sani dole da ta yi haƙuri da ni don yau kawai ta aikawata aikata wannan a bisa kuskure don Allah ku yi haƙuri". Kanta ta jinjina"shikenan Allah ya yi muku albarka". Na amsa da kalmar Amin sannan ta ɗaura da tambayar yaya jikin nawan, na ce da ita alhamdulillah. Sai da na ɗaura wani ruwan na yi wanka na sha kunun tsamiyar da Abba Abida ta dosara mini a gabana, sannan na nufi ɗakin zaure domin amsa ƙiran da Hamma Ahmad ya yi mini. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 1️⃣1️⃣ Kamar ko yaushe sai da na yi sallama ya amsa mini sannan na kutsa kai cikin ɗakin. Na zauna tare da gaishe shi cikin sanyin murya, sai ya ja ɗau lokaci sannan ya amsa mini yana ɗaura da"yaya jikin nakin?" "Da sauƙi alhamdulillah". Ina iya jiyo numfashin da ya fesar da ƙarfi"na kasa riƙe kaina ne, ina kasa sarrafa fushina matuƙar maganarki ake yi Aishatu. Ban san ina da rauni ba sai yanzu ban san zuciyata a kusa take ba sai bayan faruwar wannan lamarin". "Ku yi haƙuri Hamma duk laifina ne ni ce silar faruwar komai". Ya yi saurin katse ni"babu laifinki ko kaɗan in ma da mai laifi to bai wuce ni ba, da na kasa danne fushina a lokacin har abinda ya faru ya afku". Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe, sannan ya cigaba da faɗin"ɗazu mun yi magana da Baba akan cewar wanda ya zo da maganar neman iznin fara zancen da ke zai zo yau. Za su tattauna da su Baffa sannan su bashi damar ganawa da ke, don haka ki zama cikin shiri sannan ki kasance mai nutsuwa, ban da rawar kai da rashin kunyar 'ya'yan zamani". Sai da ya sausata amon muryarsa"Aishatu ke ce ta farkon da zata fara tsayiwa da wani saurayi a wannan ahalin. Don haka dole za ki fuskanci wasu ƙananun ƙalubale da ba za a rasa ba, shawarata gare ki shi ne ki riƙe mutuncinki kar ki bari wani ya yaudare ki da wasu kalamai ko wani ƙale-ƙalen duniya, duk da ba a yabon ɗan yau amma zan iya bugan ƙirji a gaban ko waye na san ba za ki zubds mutuncinki akan abun duniya ko kuma ki wofantar da tarbiyyar da iyayenmu suka ɗaura ki a kai ba". Sunkuyar da kaina ƙasa na yi hawaye suna gangarowa daga idanuna"Hamma Ahmad ni fa babu wanda ya taɓa cewa yana sona, balle ya zo wajen su Baba". "To ai hakan da ya yi shine daidai kuma hakan ne ke nuna cewar daga babban gida ya fito kuma yake bayyanar da cewar ya san abinda ya kamata. Ba mutunci bane ga duk wanda ya san mutuncin kansa ya tari mace a hanya ya furta mata kamar so, ba tare da ya tuntuɓi magabatanta ba. Tabbas ko daga haka ya nuna cewar shi na daban ne". Zazzafan iska na fesar daga bakina ina musgutawa tare da gyara zamana. Tabbas Hamma Ahmad ya cika cikakken ɗan uwa kuma masoyi na haƙiƙa, firgici nake ciki sosai domin ban san wanda zan gani ba. Bana kula kowa a cikin samarin unguwan domin ko su Hamma Abubakar ne ba su cika shigowa da abokansu gidan ba, balle na ce ɗaya daga ciki ne ya ganni har ya gurfana a gaban Baba. Kwantar mini da hankali ya yi ta yi, har na ɗan ji nutsuwa ya ziyarci sashin ruhina. Ya shaida mini cewar yau da wuri zasu dawo daga kasuwa don haka na zama cikin shiri. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na shiga cikin gidan kaina tsaye na wuce ɗakin Dada, na sanar da ita komai itama kwantar mini da hankali ta yi sosai da kalamai masu daɗi da kyawawan misalai. Ta ƙarƙare da yi mini addu'ar Allah ya yi mini zaɓi mafi zama alkhairi a gare ni da kuma fatan alkhairi. Haka na wuni da zazzaɓi ina kwance lilif fargaba da tsoro sun gama yi mini mamaya. Ko sallama na ji an yi sai na ji faɗuwar gaba. Ina iddar da sallan magrib kuwa na kifa kai da gwiwa, Dada ta ƙwalo mini ƙira na miƙe ina jin hajijiya yana kwasa ta na je na durƙusa a gabanta. "Yau za ki yi baƙo kin sa ni?". Na ɗaga mata kaina jikina duk ya yi sanyi ƙalau. "To ki nutsu ban da rawar kai inda kin fita, ki saurare shi sannan ki kama kanki da kuma mutuncinki kin ji ni?". Take na ji hawaye sun ciki mini koramar idanuna"to in sha Allah". Ta sanya mini albarka tare da umarta na tashi. Har muka gama cin abinci da Abasiyya babu wanda ya cewa wani abu har Baba Alhaji ya shigo. Duk muka yi masa sannu da zuwa ya amsa mana fuskarsa a washe. Na tashi na wanke hannuna zan shige ɗaki ya ce na dawo na zauna, kamar yanda faɗa hakan na yi na koma na zauna. "Ki ɗauko mayafinki kina da baƙo a waje". Ƙirjina ya buda da ƙarfi na miƙe a sanyaye, ban taɓa tsayiwa da wani saurayi ba da sunan zance haka nan ban taso na buɗe ido na ga su Adda Azima na yi ba, don haka abun sai ya zamo mini sabon al'amari a gare ni. Cikin matsanancin faɗuwar gaba na isa inda aka shimfiɗa tabarma. Muryar da ya sauƙa a masarrafar jina suka sanya ni ƙara gwalo idanuna wajen. "Kai ne?". Na furta ina nuna shi da yatsata ya ɗago idonsa ya sauƙe akan fuskarta da firgici, tsoro da ruɗu suka bayyana akan ta"ƙwarai ni ne ki zauna mana". "Me ya kawo ka gidanmu?. Me yasa ba zaka daina bi na ba?. Ko lokacin baya sai da aka yi mini faɗa akab tare ni da ka yi don Allah ka yi haƙuri ka bar ni". Na ƙare zancen ina haɗe hannayena waje guda alamar roƙo, tare da yunƙurin juyawa da nufin barin wajen. Zancen da ya furta suka tursasa mini tsayiwa cak tamkar dasasshen itace na kasa gaba balle baya. "Yau da iznin iyayenki zan yi magana dake, domin sai da na nema izninsu kafin na yi wannan zuwan. Don Allah ki ba ni lokaci daga cikin lokacinki domin ki ji abinda yake tafe da ni". Na faɗa duniyar tunani da nazari me yake nufi da cewar da iznin iyayena ya zo nan?. Na juyo a birkice"ban gane me ye kake nufi ba?". "Ki zauna sai na sanar dake za ki fi fahimtana". Na sauƙe gigitaccen ajiyar zuciya a bayane, na yi ƙasa da kaina "ka ce da iznin iyayena ka zo nan?". "Ƙwarai kuwa da za ki yi haƙuri da kin ji abinda yake tafe da ni". A hankali na tako na ɗosana akan tabarmar zuciyata tana dakan lugadai. Ya gyara zamansa kana ya soma faɗin"na san za ki mamakin ganina a gidanku ko?". Na ɗaga masa kaina ya cigaba da"tun lokacin da Allah ya haɗa fuskokinmu na ɓata miki jiki da ruwa a bisa kuskure na ba ki haƙuri kuma ba ki saurare ni. A lokacin na ajiye motata ba bi ki a ƙafa har na ga gidan da kika shiga, da yamma bayan na dawo daga aiki na bi ta layin ko zan ganki amma ban sama ganin ki ba. Tun daga lokacin nake ta addu'ar Allah ya sa na ƙara yin tozali da ke, Allah bai nufa ba sai lokacin da na tsaya na yi sallan a wannan masallacin na gan ki, a lokacin na ga gidan da kika shiga. Bayan na tafi na yi bincike akan gidanku har na sama wasu bayanai na zo na iske mahaifinki ya ce zasu gudanar da bincike a kaina daga baya zasu neme ni". Ya tsagaita sannan ya ɗaura da"tun daga ranar da ya ce na je sai sun neme ni nake kwana cikin zulumi da fargaba, sai dai na dage da addu'a da kai kukana ga Allah. Kwanaki biyu da suka wuce ya nemi da na zo na yi farin ciki sosai da ya shaida min cewar sun ba ni damar fara zance da ke mu fahimci juna kafin na turo magabatana". Zuciyata tana ɗillin ɗillin na ce"daman kai ne wanda su Baffa suke faɗa?". "Ni ne Aishatu kina mamaki har yanzu ko?". Na daga masa kaina. "To ki daina mamaki domin zuciya bata taɓa nisa da abinda take so". Na yi shuru ba tare da na ce dashi komai ba, ya kuma faɗin"ina fatan ban makaro ba wani bai riga ni ba ko?". Na ƙara yin ƙasa da kaina, ya yi ɗan murmushi"shuru ma magana ne, hakan yana nufin dole na ƙara zage damtse kenan na yi shirin yin yaƙi da gaske". "Yaƙi kuma?". "E mana Indai zan mallaki zuciyarki ai abun da ya fi yaƙi ma zan yi shirin yin sa". Yanda ya yi zancen cikin barkwanci ya sanya ni yin takaitaccen murmushi. Zancensa ya kuma ratso kunnuwana "don Allah ki ɗago kan ki ki kalle ni". Na ɗago idona caraf muka haɗa ido na yi saurin yin ƙasa da nawa. "Allah ya sa na sama karɓuwa a cikin zuciyarki, domin tun ranar da na ɗaura ido akan ki nake jin cewar na sama abokiyar rayuwa in Allah ya yarda". Na ɗago kaina da nufin furta abinda yake raina na hango Hamma Ahmad da Hamma Adnan suna nufo wajen, jikina ya soma rawa ban sa ni ba ko lura da hakan ne ya sanya shi jefo mini tambayar lafiya?. Tare da juyawa yana kallon inda na ƙurawa ido. Miƙewa na ga ya yi tun kafin su ƙariso ya isa gare su, suka fara gaisawa ta hanyar yin musabaha da juna ciki raha da girmama juna tamkar sun san juna. Na kasa ɗago ido na kalli Hamma Ahmad don wani nauyinsa nake ji na musamman. "Ina ji da wannan ƙanwar tawan fiye komai don haka ka riƙe min ita da amana da kuma gaskiya. Don ina iya jure komai a kaina amma idan aka taɓo ta bana jurewa". Furucin Hamma Ahmad kenan cikin sigar zolaya suka sa ki dariya tare da Hamma Adnan. "Ina sha Allah za ka same ni fiye da yanda kake zato". Ya faɗa cike da girmamawa. Suka yi masa godiya sannan suka wuce cikin gidan, ya dawo inda ya tashi ya zauna yana faɗin"waɗanda 'yan uwan nakin sun burge ni basu da matsala". "Dukkansu yayuna ne". "Na ga kammani ai". Ina wasa da yatsun hannuna na ce"ai kuwa kama gama dasu ko kaɗan, sai dai kawai jini duk inda yake baya ɓoya". "Kuna kama mana sosai ma kuwa". Na kawar da maganar ta hanyar faɗin"zan shiga ciki dare yana yi". "Haka ne amma gashi har zamu rabu ba ki tambayi ko da sunana bane amma ni na san na ki sunan". Cike da jin kunya na ce"to yanzu na tambaya". "Sai da na roƙo". Na yi masa shuru ya katse shurun ta hanyar faɗin"sunana Abdul-hameed". Kaina na jinjina masa kana na ce "na gode a huta gajiya zan shiga daga ciki". Muka miƙe tare ya sanya takalmarsa sannan ya fara ƙoƙarin naɗe tabarmar na katse shi da faɗin"da ka bar shi ma". Sai da ya naɗe tsaf kana ya ce "ba komai yanzu sai yaushe zan dawo?". "Sai dai ka tambayi su Hammana duk abinda suka ce haka za ayi". "To shikenan nan kafin ina son na sama gamshashshiyar amsa daga gare ki". Na saki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ina gyaɗa masa kaina. Ya miƙa mini tabarmar na karɓa sannan ya yi mini sallama, na wuce gida. Sai da na tsaya a zaure ina sauƙe numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceto rai. Na shafe tsawon mintoti kana na ja ƙafafuna na ƙaria shiga cikin gidan ina shiga Baba Alhaji yana ƙoƙarin fita na yi saurin matsawa na bashi hanya. Abasiyya da Adda Abida duk suka zubo mini idanuna har na ajiye tabarmar dake hannuna na zauna, tare da sadda kaina ƙasa duk kunya ta ishe ni. "Baƙon ya tafi kenan?". Dada ta furta ɗaga mata kaina na yi alamar e, Hamma Adnan ya karɓe zancen da faɗin"amma zama a wannan wajen bai kamata ba domin hanyar wucewar mutane ne. A mutunci bane tsayiwa da saurayi a hanya irin haka, don haka gaba ki shigo dashi zaure". Kunya ya hana ni amsa masa na tashi na shige ɗaki, har mun kwanta Abasiyya ta tashe ni na murtsike idanuna ina faɗin"lafiya?". "Ina kuwa lafiya bayan duk abinda kika aikata babu alamar nadama ki kunyar hakan a tare ke. Wallahi kin ba ni mamaki, wai ke ko nauyin Hamma Ahmad ba kya ji akan idonsa ki shigo kin dawo daga zance da wani". Wani ɗaci na ji a raina na kai hannu zan riƙe hannunta ta yi saurin zamewa. Na ƙura mata idanu tamkar yau na soma ganinta"Abasiyya yaya ki ke so na da raina?. Da kin san yanda nake ji na tabbatar da cewar za ki yi mini uzuri". "Ƙarya kike yi kawai son zuciyarki kika fifita fiye da komai. Ba ki damu da halin da za ki jefa kowa ba ke dai kawai farin cikinki shi kika sanya a gaba". Ban san sanda wasu hawaye masu zafi suka rige- rigen fitowa daga idanuna suna fareti a bisa kuncina. Shin da wani yaren zan yi amfani dashi wajen fahimtar da ita har ta fahimci ni ta daina jifa na da waɗannan miyagun zantukan?. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 1️⃣2️⃣ Haƙuri kawai na bata na koma na kwanta na juya mata baya, na kasa tsayar da ruwan hawayen da yake kwaranya daga idanuna. Zuciyata sai tafasa take yi numfashina yana cunkushewa waje guda. Dole na tashi na zauna tsam saboda tarin da ya sarƙafe ni sosai nake yin tarin kamar zan shiɗe. Na mirgino daga kan gado zuwa ƙasa na kwanta luf, ina jin wani tsaki mai dogon zangon da Abasiyya ta saka. Kafin asubahi wani zazzaɓi mai zafi ya rufe ni sai rawar ɗari nake yi. Dada da Anwar suka tashi hankalinsu a kaina da Hamma Adnan muka je chemist aka ba ni magani tare da tsira mini wasu allurai. Wunin ranar gabaɗaya ban iya tsinana komai ba sai kwanciya, washe gari na ɗan ɗaga Dada sai kumbar baki take yi akan rashin zuwan Umma duba ni duk da ta aika a sanar da ita cewar ba ni da lafiya. Sai da na yi sallan zuhr na lallaɓa na je gaida Umma domin jiya ban je ba. Tsakar gidan wayam babu kowa don haka kaina tsaye na wuce ɗakinta, tana kishingiɗe na iske ta nayi sallama sannan na shiga na zauna. A ladabce na gaishe ta ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa. "Ya jikin nakin?. Jiya Adnanu ya zo yana sanar da ni cewar kun je chemist". Na amsa muryata ƙasa ƙasa"da sauƙi alhamdulillah". Ta jinjina mini kanta tare da ɗauke idonta daga kaina, na ja jikina na motsa kusa sosai da ita. "Umma don girman Allah ki sausata mini wallahi fushinki a gare ni ba ƙaramin tashin hankali yake saka ni ba. Yana hana ni sukuni na gwammace ki yi mini ko wani irin hukuncin ne komai tsauri da tsananin sa zan jure. Idan akan maganar Hamma Ahmad ne wallahi ni na amince ki zaɓo mini ko waye ko yaya yake na amince zan aure sa kuma na yi masa biyayya dai-dai gwargwado matuƙar hakan zai sanya ranki ya yi fari". Na ƙarƙare zancen ina kifa kaina akan hannayenta da ba riƙe a cikin nawa, sai da ta ɗau lokaci kafin ta furta"ba ni da matsala da duk wanda za ki aure 'yar ba, amma abinda nake hange miki shine a cikin wannan zamanin da gurɓatattu suka yawaita ba lalle ki sama nagartaccen namiji kamar Ahmad ba. Ba lalle ki sama wanda zai so, ya riƙe ki bisa amana kuma ya mutuntaki da mu kanmu ba kamar sa. Ina yi miki sha'awar auren sa ne saboda kyawawan ɗabi'unsa". Sosai zantukanta suka ratsa kwanyata tare da haifar mini da nutsuwa a dukkan jikina. Wasu hawayen suka kuma zubowa daga idona. Na gagara raba tsakanin harshe da haƙwarana balle na sama damar cewa da ita wani abu, na daɗe kaina a sunkuye kafin ta ɗago ni tana goge mini fuskata. Murmushin da ta ƙawarta fuskarta dashi da na daɗe ban gan shi ba ta sakar mini, da hakan ya sanya ni jin rangwamen zogin da yake sokar raina. Ta yi mini nasiha mai tsoritarwa da ratsa jiki sosai akan na kula da wanda yake zuwa wajena domin mafi yawan mazan wannan zamanin babu Allah a cikin zuƙatansu. Duk da ba na jin daɗin jikina amma zage damtse na yi. Na yi duk wasu aikace aikace, sai da na yi sallan magrib na tashi zan tafi sallamar Hamma Abubakar ya sanya ni daburcewa domin tun bayan lokacin da wannan saɓanin ya gifta tsakanin su da Hamma Ahmad ban ƙara yin tozali dashi ba. Kiana a ƙasa na gaishe shi ya amsa mini a gajarce, na yi sallama a Umma zan fice ya dakatar da ni da faɗin"gobe da yamma ki zo gida ina son ganin ki". "To". Na amsa dashi ina jin wani matsanancin faɗuwar gaba, ranar baccina ragagge ne domin duk yanda na so fahimtar da Abasiyya ta kasa fahimtana balle ta yi mini uzuri. Na ci kuka sosai a banɗaki wayewar safiyar ranar da na shiga wanka, sai dai na ƙi bada ƙofar da Dada za ta fahimci wani abu tsakaninmu da Abasiyyan domin ba ta yi mini a gabanta, tsakanina da Adda Abida kuwa yanzu harara ce da kallon banza. Idan na zauna a inuwar da take zaune kuwa za ta tashi ta bar mini wajen. Da Anwar muka je gidan Hamma Abubakar, tunda muka fito daga gida ban ce komai ba sai faman tunane-tunane nake yi. Ya tafa hannunsa tare da ɗage mini ido ɗaya alamar lafiya. Na sauƙe sakekken ajiyar zuciya"ba komai kawai na kasa samun nutsuwa ne da wannan ƙiran da Hamma Abubakar ya yi mini". Sai da ya yi ɗan jim kafin ya furta"ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu komai". "Zan so ya kasance cewar babu komai ɗin, amma na san idan na sakankance akan hakan ma yaudaran kaina zan yi wanda ba shi da wani amfani". Ya kallo ni tare da faɗin"me yasa kika ce haka?". "Saboda kowa fushi yake yi da ni". "Har da ni?". Ya furta cikin salon kwaikwayon muryata. Na san manufarsa bai wuce domin ya sanya ni dariya ba duk ƙoƙarin da na yi murmushi kawai na iya saka gajera da iyakarsa kan fuskata, domin bai kai har zuci ba. "Ki amsa min mana". "E to kai ɗin ba zan iya cewa komai ba domin ban ga alama ba. Ko kuma kara kawai kake yi mini ban sa ni ba". Ya yi turus yana kallona"ashe za ki iya yin wannan tunanin a kaina?. Wallahi ban taɓa jin haushinki don kin ƙi Hamma Ahmad ba. Abinda na yi imani dashi shi ne duk zakaran da Rabbana ya nufa da cara to fa ko ana muzurai ana shaho sai ya yi". Na ɗan murmusa"haka ne". Muka karya kwanar da zata sada mu da gidan ya soma faɗin"ina ta jira ki ba ni labarin sabon saurayin nakin amma na ga kin tsuke bakinki kin yi shuru, ko dai an canja ni a matsayin mafi kusa dake a cikin yan'uwanmu ne ni nan ban sa ni ba?". Na kallo shi sannan na yi ƙasa da kaina"wallahi ban sama sukunin yin maganar da kowa bane ma". "Saboda kowa ya canja miki a gidan ko?". Na jijjiga masa kaina da sauri, ya ɗaura da"kar ki yi min musu domin ina lura da duk abinda yake faru ba, kuma daman ina son na ba ki haƙuri ban sama damar zama dake ba sai yanzun". Na ƙirƙiro murmushi na dasa a fuskata"babu komai ni kam, wataƙil ko ni ce a matsayin su na yi makamancin abinda suke yi ko ma fiye da haka". "Ba dai wannan Aishatun da na sa ni ba, domin ni a sanin da na yi mata sam hakan baya daga cikin halayyata". Yanda ya lanƙwashe murya wajen furta zancen ban san lokacin da dariya ya suɓece mini ba, sai da na dara sosai har idona yana kawo ruwar ƙwalla. Ya dakata da tafiyar da yake yi tare da naɗe hannayensa a ƙirjinsa ya ƙura mini idanu"idan ki na wannan walwalan ƙara kyau kike yi akan kyan da kike dashi, don Allah ki cigaba da yi ko wani yanayi za ki shiga kar ki daina kin ji?". Na ɗaga idona na kalle shi har yanzun ni yake kallo na yarfa hannu da hakan ya sanya shi ɗan lumshe idanunsa, muka cigaba da tafiyan. "Ina jin ki". Ya katse mini zancen zucin da nake yi, na fesar da iska daga bakina ina hango ƙofar gidan Hamma Abubakar ɗin na ce"ba zan iya cewa komai akan sa ba, domin na yi mamakin ganin sa da kuma abinda yake tafe dashi". Ya yi saurin katse ni"daman kin san shi ne?". Na jijjiga masa kaina"shine wanda nake baka labari ya fancakala mini ruwan kwata da daɗewa, Anwar wai shi ne yazo yana so na na ma rasa yanda zan yi". "Ki nutsu ki yi shawara da zuciyarki duk abinda kika ji kin fi samun nutsuwa a kansa to bakya buƙatar neman shawarar wani. Matuƙar kin yaba da halayyarsa kuma su Baffa suka gudanar da bincike akan sa aka sake shi da dukkan nagartattun halayya, kin ga ke kam ai kin da ce. Amma kafin ki ba shi ko wacce irin amsa ki tabbatar da cewar ki yi istikata". Ya ɗan tsagaita yana kallona dai dai sanda muka iso ƙofar gidan." Allah ya ba ki ikon fahimtar masoyinki na gaskiya, wanda tsananin son da yake yi miki ba zai sanya shi ya cutar dake ko da na daƙiƙa ɗaya bane". Cike da rashin fahimta na watsa masa idanuna, ya sakar mini murmushi domin shi ma ya lura da cewar ban fahimta ba. Yana gaba ina bin sa a baya muka shiga cikin gidan. Muka tarar da Adda Azima tana hura gawayi cike da farin ciki ta tarbe mu kamar wasu baƙin da suka taho daga wata uwa duniya. Haka take ta jeranta masa sannu da kuma dire mana kofin ruwa a gabanmu, ta tsiyaya mana tare da miƙawa kowa. Sai da na jiƙa maƙoshina da sanyayyen ruwan sannan muka haɗa baki wajen gaishe ta, ta amsa mana fuskarta tamkar gonar auduga. Ta na rufe bakinta sallamar Hamma Abubakar yana ratsa ƙofofin kunnuwanmu. Muka yi masa sannu da zuwa sannan muka gaishe shi ya amsa mana a gajarce yana shigewa ciki tare da ƙiran matarsa. Muna zaune a wajen ya fito ya yi wanka ya ƙara komawa ciki. Na cigaba da hurawa Adda Azima gawayin har ya ruru na aza mata sanwa. Ta fito tare da faɗin na shiga yana yi mini magana. Ƙirjina ya buga da ƙarfi muka haɗa ido da Anwar. A sanyaye na yi sallama ya amsa mini sannan na kutsa kai ciki na zauna a ƙasa ina ƙara yi masa sannu. Sai da ya ƙarar da wasu mintoti sannan ya ce"na ƙira ki ne akan maganan wanda yake zuwa wajen ki, Baba ya ce tare da na Adnan da Abida za a haɗa. Tun kafin su ba shi damar ganawa dake aka fara gudanar da bincike akan sa. Cikakken sunan sa shine Abdul-hameed Abba ma'aikacin ne mai rufin asiri da ya kasance mai sana'ar zanen gidaje a ƙarƙashin wata ma'aikata da take aiki da injiniyoyi ƙwararru. Mahaifinsa ya rasu shekaru huɗu da suka gabata, yana da yayye mata biyu da kuma ƙaninsa na miji guda ɗaya jal. Shi yake kula da mahaifiyarsa da kuma ƙaninsa bayan aikinsa kuma shi yake juya dukiyar da mahaifinsu su ya bari. Ya sama kyakkyawan shaida daga mutanen unguwansu, sai dai Ahmad ya yi masa fintinkau da zarra akan kyawawan dabi'u sai kawai shi ya fi shi da abin duniya ne, ban sa ni ba ko hakan kika duba ki ka zaɓe shi akan Ahmad". Da sauri na ɗago idona da suka kawo ruwar ƙwalla"wallahi tallahi ban zaɓe shi akan Hamma Ahmad ba hasalima ni ban san da cewar ya zo wajen Baba ba. Ban da motar da na ganshi da ita wallahi ban san da duk wani abinda ya mallaka bayan ita ba". Ya kawar maganar ta hanyar faɗin"yanzu dai kina son sa kuwa?". Na yi shuru sai da ya daka mini tsawar da ya sanya Adda Azima shigo sannan na ce"nima ban sa ni ba sau ɗaya kawai muka yi dogon magana dashi". "Hamma don Allah ka yi haƙuri a bi komai a hankali". Ta furta cikin kwantar da murya bai kula ta ya miƙe tsaye yana faɗin"na ba ki nan da mako biyu ki sanar da ni amsar tambayata". Yana dasa aya a nan ya shige cikin uwar ɗaka, Adda Azima ce ta hau aikin lallashina da kwantar mini da hankali. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 1️⃣3️⃣ Haka na kwana cikin zulumi duk da Anwar da Adda Azima sun kwantar mini da hankali sosai amma na gaza samun nutsuwa. Sai da aka yi kwana biyu wani yammaci Dada ta ce da ni in shirya ina da baƙo. Sai bayan sallan magrib ya zo, Dada ta ba ni tabarma ta ce na shinfiɗa masa a cikin zaure. Na ƙarba na yi kamar yanda ta faɗa. A zauren muka zauna na gaishe da shi muryata ƙasa ƙasa, ya amsa mini tare da ɗaurawa da faɗin"kwana biyu yau cur ban yi tozali da ke ba, ina ta so na ƙira Hammanki na tambaya kuma ina jin kunya". Na ƙara yin ƙasa da kaina"to yanzun yaya aka yi kazo?". "Gaban kaina na yi kawai na zo don ba zan iya jurewa ba, ban sa ni ba ko na yi laifi. Amma na sanya a raina cewar kafin na tafi zamu yi magana dasu na ji lokacin da ya dace ina zuwa". Na jinjina masa kaina hakan ya bashi damar cigaba da cewa"ina fatan yau kafin na tafi na sama amsa daga gare ki domin wallahi zuciyata ta kasa samun sukuni". Ina wasa da dogayen yatsun hannuna na ce"zan zo ka ba ni lokaci na gudanar da istikara kafin na ce da kai komai". Ya yi ɗan jim kafin ya furta"hakan yana da kyau domin nima kafin na tunkari iyayenki sai na yi na kuma sama nutsuwa da ke, ina fatan na ji alkhairi daga gare ki". "In sha Allah". "Ba ki nema ji ki komai dangane da ni ba shin ko hakan baya cikin tsarinki ne?". "Iyayena sun yi bincike akan ka daga gare su na ji duk wani abun ya dace na sa ni a game da kai". A jikina nake jin idanunsa suna kaina yake faɗin"to ba ni labarin abinda kika sa ni na ji". Na ɗago kaina na saci kallonsa ta gefen ido kafin na sama damar soma faɗin"na san sunanka, sana'arka da kuma inda kake zaune. A binciken da iyayena duka gudanar an same ka da dukkan ɗabi'u kyawawa. Wanda hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwar bari na, na saurare ka". Sai da na tsagaita ina furzar da iska daga bakina na cigaba"ban taɓa tsayiwa da wani saurayi ba kuma ban taɓa ganin ɗaya daga cikin 'yan uwana tana yi ba, ni ce ta farko saboda haka nake cike da fargaba. Ban taɓa soyayya ba sai a wannan karon don Allah kar ka cutar da zuciyata kar ka zalunce Ni ta hanyar amfani da raunina na 'ya mace.". "Ɗago idonki ki kalle ni". Na yi kamar ban ji shi ba sai da ya ƙara maimaita zancen a karo na biyu, sannan na ɗago idona na sanya a cikin nasa. "Ban taɓa cutar da wani ba balle ke da kika yi rassa a cikin zuciyata. Ban zo gaban iyayenki da nufin yaudara ba face auren da ko yau suka buƙata a shirye nake". Sosai kalamansa suka ratsa ni tare da yin tasiri a dukkan sassan jikina, na kasa cewa komai tamkar wacce ruwa ya cinye ta. "Ki ba ni dama zan tabbatar miki da cewar ni na daban ne a cikin sauran maza". Murmushi kawai na yi masa shima ya maido mini dashi"ke kaɗai ce mace a gidanku?". Na jijjiga kaina"A'a a wajen su Baffa dai ni ce kawai mace, amma ina da yayu biyu mata na wajen Babanmu Sannan akwai ƙanwata Abasiyya". "Ban taɓa ganin su ba". "To sau nawa ma kazo gidan? Kuma Adda Azima ta yi aure lokacin bikinta ne ka fancakala mini ruwa zamu je gidanta. Sannan Adda Abida ma aurenta saura kaɗan da Hamma Adnan". Sai da jera kalaman masha Allah sau uku sannan ya ce"ke kuma da waye bikinku?". "Hamma Ahmad sai kuma Allah bai nufa ba". "Wataƙila rabona ne ya rantse shiyasa kika ga ba ayi ba". Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe sai can ya furta"ni kuma ni ne babban ɗa na miji a gidanmu ina da yayu biyu mata sannan ƙanina ɗaya, muna zaune tare da mahaifiyarmu domin Allah ya yiwa mahaifinmu rasuwa da daɗewa". Cike da jajantawa na ce"Allah ya jiƙansa". "Amin". A wannan zuwan nasan mun ɗan tattauna sosai mun kuma ƙara sanin junan mu, da zamu yi sallama ya ce ba zai dawo ba sai na gama gudanar da istikara ya zo ya ji amsa idan Allah ya nufa sai ya turo iyayensa. A kan haka muka yi sallama ya tafi na dawo na sanar da Dada yanda muka yi, ta ce hakan ma daidai ne na yi istikaran. A daren ranar na fara gudanarwa kafin na gama cike kwanakin na ji sauyi sosai a cikin raina. Haka nan kawai na tsinci kaina da matuƙar son ganin sa. Na fayyacewa Dada komai ta yi hamdala tare da sanya mana albarka. Washe garin ranar da na gama kuwa ya cika alƙawari ya zo shi, Dada har da ba ni ruwa a sabon ƙofin da ta siyawa Adda Abida na taru ta ce na kai masa. Na tsiyaya masa tare da yi masa bismilla ya nuna mini a ƙoshe yake. Ina gyara zamana na ce"sai dai ko in baka shan ruwan rijiya ne, amma wanda ya yi tafiya ai dole zai buƙaci ruwa". "A'a ina sha sosai ma hasalima shi na sha na girma kawai na zaƙu da son jin amsata ne daga gare ki". "To ka fara shan sannan na sanar da kai". "Hakan ya yi miki?". Na gyaɗa masa kaina ya ɗauki kofin ruwan ya sha kaɗan sannan ya ajiye ya ce"ina jin ki". Na rusunar da kaina ƙasa"na ji a raina cewar kai ne alkhairi na ina farin cikin sanar da kai cewar ka sama gurbin a cikin zuciyata". Ina ƙare faɗin haka na miƙe da sauri zan shige cikin gidan ya dakatar da ni da kalamansa. "Ina koma za ki je? Ai dole ki dawo mu raba wannan farin cikin domin ya yi min yawa Ni ɗaya na yi shi". Ban amsa ba na dawo na zauna kaina a ƙasa. "Na gode da samun wannan damar kuma ina mai tabbatar miki da cewar ba za ki taba yin da na sani ba. Zan wadata ki da dukkan abinda wata 'ya mace take da buƙata daga wajen ɗan miji dai-dai ƙarfina. Ki sanar da gida cewar idan an ba ni dama zan turo iyayena a yi maganar aure". Kaina na ɗaga masa kafin na amsa cikin faɗin"da Hammana zaka kuyi wannan maganar". Daga haka ban ƙara cewa komai ba har ya miƙe muka yi sallama domin wani kunyarsa ce ta yi mini mamaya. Sai washe gari na sanar da Dada ta yi murna sosai ta faɗawa da Baba Alhaji ya ce zasu yi magana da Baffa. Ranar ina zaune ina dama furar da Hamma Adnan ya shigo da ita ya ce a damawa su Baffa. Anwar ya shigo da kallo na bi shi har ya zauna akan tabarmar dake shimfiɗe a wajen na ce"lafiya? Ko baka jin daɗi ne?". Ya laune leɓansa"lafiya ƙalau wani labari mai daɗin ji nake tafe miki dashi". Na waro idanuna wajen"to wani labari ne wannan?". Ya gyara zamansa yana fuskanto ni sosai sannan ya ce"yanzun nan iyayen Abdul-hameed suka tafi sun zanta da su Baffa kuma an bashi auren ki za a yi tare da na su Hamma Adnan". Ban san lokacin da na saki ludayin da nake dama furar da ita ta faɗi ƙasa ba, na dafe ƙirjina ban san dalilin tsintar kaina cikin matsanancin faɗuwar gaba ba. "Lafiya?". Kaina kawai na iya ɗaga masa ina maimaita kalmar hasbunallah a cikin raina a ƙoƙarin samarwa kaina da nutsuwar da na rasa. Na ɗauki ludayin na wanke sannan na cigaba da damun da nake yi. Abasiyya da take zaune a gefe ta taɓe baki gami da faɗin"uhmm duk wanda ya ƙi ji dai to ba zai ƙi gani ba, kuma kowa san cewar tusa bata hura wuta". Ta miƙe tsam ta shige ɗaki tare da banko labulen, ko kaina ban ɗago na ganta ba balle na ce da ita wani abun na gama abun gaba na shige ɗaki. Bayan sallan isha'i Baffa ya ce kowa yaje shi yana neman sa, babban tabarma aka shimfiɗa a filin tsakar gidan duk muka zazzauna. Ya yi gyaran murya sannan ya soma magana kamar haka"mun tattauna da iyayen yaron da ke neman auren Aishatu kuma mun ba su aurenta, daidai lokacin da muka sanya na Adnanu haka ita ma za a yi nata. Sai dai ina so ku shaida wani zance ɗaya gabaɗayan ku". Ƙirjina ya hau dakan lugudai na matse jikina wajen guda, kowa ya yi shuru Baffa kawai ake saurara da ya cigaba da faɗin" Aishatu za ta auri wanda take so bayan ta bijirewa zaɓinmu, ina so ku shaida ba zan laminta wani ƙorafi daga gare ta ba bayan an ɗaura aure a kai ta ɗakinta. Duk abinda zai yi miki ƙi yi haƙuri ki haɗiye tunda ke kika zaɓe shi. In ba sakin ki ya yi ba ban yarda ki ɗauko ƙafarki ki zo gidan nan da sunan yaji ko kin kawo ƙarar sa ba". Shuru ya karaɗe wajen ni kuwa faɗuwar gaban da nake ji ya kuma tsananta, wata zuciyar tana raya mini cewar na buɗe baki na ce dasu na fasa auren amma hakan ma na san ba zai zama mafita ba. Domin Baffa ba zai taɓa laminta ba, ba ya yin magana biyu a rayuwarsa kuma ba ya yin zance ya janye duk abinda ya furta sai ya aiwatar. "In sha Allah Yaya hakan ma ba zai faru, mu yi musu fatan samun zaman lafiya a cikin auren su". Furucin Baba Alhaji kenan da ya sanya Baffa gyaɗa kansa kawai ya yi shuru. Baba Alhaji ya ɗaura da" za a yi bikin nan da wata ɗaya don haka duk wani shirye-shiryen da za ku yi sai ku fara shi tun daga yanzu". Umma da Dada suka amsa a tare, a haka taron ya watse na je na kwanta gabaɗaya ina ji na wani iri. Na rasa me yake yi mini daɗi. Washe gari ya kasance ranar juma'a ana ƙwalla rana mai zafi sosai, bayan an sauƙo daga juma'a 'yan mazan gidan mu gabaɗaya suka shigo. Hamma Ahmad ne yake shaida mini cewar ina da baƙo a zaure. Na sako hijabina na fita na iske shi yana zaune har an shimfiɗa masa tabarma na gaishe shi ya amsa mini yana bi na da kallo. "Na kwana cikin murna da godewa Allah daren jiya da iyayena suka shaida min cewar an bani ke". Ban ce dashi komai ba ya cigaba da"ina so na yi miki wani tambaya". Na musguta"ina jin ka". Sai da ya ɗan ɗau lokaci kana ya ce"shin za ki iya zama da uwar miji a gida ɗaya?". Ban san sanda na ɗago idona na yi masa kallon ido cikin ido ba kafin na janye nawa. "Me yasa ka yi mini wannan tambayar?". "Ina son na ji daga gare ki naki ra'ayin game da hakan". Na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina"a tunanina idan har ina son ɗanta da ya tsaga jikinta ya fito to dole ita ma na so ta. Idan zan iya jure halin tawa uwar na zauna da ita ko yaya take to tabbas zan iya zama da mahaifiyarsa domin ita ma mahaifiya ce a gare ni". Ya ƙura mini ido na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya saki numfashin da nima sai da na ji sa"tabbas da mata sun kasance masu irin tunani da kaifin basira irin na ki da an zauna lafiya a ko wani ahali. Tabbas na cika mai sa'a da na same ki". "Amma har yanzu ban gane manufar yi mini tambayar ba". Na faɗa ina matsa hannuna waje guda. Ya sausauta muryarsa ya ce"saboda tare zamu zauna da mahaifiyata, ni nake kula da ita tun bayan rasuwar mahaifinmu. Hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar na yi nisa da ita. Zan so ki taimaka min wajen tabbatar da wannan abun". Gabaɗaya na ji jikina ya mutu murus a irin labaran da su Umma suke yi na kan suna faɗin irin ƙalubalen da ke tattare da zama gida ɗaya da suruka. Wannan dalilin ne ya sanya Baffa warewa Hamma Abubakar matsuguninsa daban tun bayan aurensa. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 1️⃣4️⃣ Ƙiran sunana da ya yi shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga tunanin da na yi nisan kiwo a cikinsa. "Lafiya kuwa?". "Lafiya ƙalau". Ya yi nisa kafin ya furta"na san mata da yawa suna gudun zama da uwar miji. Amma ba kowacce ba ce take zama matsala. Mafi akasari an fi samun matsala daga mijin ta hanyar nuna bambamci a tsakanin su. Da a ce kowa zai tsaya a matsayinsa in sha Allah babu wani ƙalubalen da zai bijiro". Na yi ƙasa da kaina a hankali na furta"haka ne kam, ni kam daga gare ni bani da matsala game da hakan". Ya yi hamdala tare da faɗin"na gode matuƙa Allah ya tabbatar mana da alkhairi". A sanyaye na amsa da"Amin". Har muka yi sallama na koma cikin gida zancensa suna yi mini yawo a cikin kwanyata. Bayan mun gama cin abincin dare na iske Dada a ɗakinta tare da Adda Abida. Na sanar da ita komai ta jinjina kanta kafin ta furta"zama da uwar miji tabbas yana da nashi tarin ƙalubalen dole kuma sai kin kasance mai takatsan-tsan. Wasu iyayen mijin su kan kasance masu katsalandan a cikin harkokin gidan 'ya'yansu, wani matsala kuma daga wajen matayen take tasowa, domin su kan nuna cewar su ne akan gaba fiye da kowa. Suna mance irin wahalhalun da uwarsa ta yi dashi ya girma har ya taka matsayin da suka gan shi a kai har ya aure su". Sai da ta tsagaita kana ta cigaba da faɗin"ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu wani abun da zai faru. Ki kasance mai biyayya da kuma alkunya, ki so 'yan uwansa ki kuma ɗauki mahaifiyarsa tamkar wacce ta tsuguna ta yi naƙudarki ta haifo ki. Idan kika sanya haka a ranki ba za ki taɓa yi mata ba daidai ba, dole wataran ta yi abinda zai sosa miki rai domin duk ɗan adam aziji ne tara yake bai cika goma ba. Ki zama mai kiyaye dukiyar mijinki kar kina yin almubazaranci, ki na ƙoƙarin ɗaura shi akan hanya sannan ki nuna masa cewar 'yan uwansa suma suna da haƙƙi akan sa. Ki rungumi 'yan uwansa tamkar waɗanda kuka fito ciki ɗaya dasu domin su zasu zame miki maɓoya a yayin da kuka sama saɓani da shi, ki zama mai kyau kuma kar ki bari abin hannunki ya rufe miki ido. Matuƙar kika riƙe waɗanda abubuwan da na lissafo miki za ki zauna da ko waye lafiya ƙalau babu wani tashin hankali". Na kasa cewa komai jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwar gishiri. Ban ɗago kaina ba har izuwa lokacin da Adda Abida ta furzo zancen da ya sanya ni kallon ta, ta gefen idona da ya kawo ruwar ƙwalla. "Tabɗijam lalle mutumin daga yin auren kenan zai haɗa ki da uwarsa?. Kina yarinya ƙarama ina za ki iya da wannan ɗawainiyar bayan na shi ga kuma na uwarsa". Dada ta yi saurin kwaɓar ta"haramun ne zama gida ɗaga da suruka Abida?. Kar na ƙara jin yin makamancin wannan maganar". Ba ta kuma cewa komai ba ta ja bakinta ta tsuke, Dada ta cigaba da faɗin"kar ki ji komai Aishatu ki sanar dashi kin amince da hakan, ki hidimta mata dai-dai gwargwado sai ki ga kimarki da darajarki ta ƙara yaɗuwa a idanun mijinki". "In sha Allah na gode sosai Allah ya ƙara girma". Na furta muryata ƙasa ƙasa bata fita da kyau, ta amsa tare da sanar da ni cewar zata faɗawa Umma. Hamma Ahmad ya ƙira ni muka zanta ya ce duk abinda nake buƙata na sanar dashi, kar na ji nauyin sa duk wani abunda na gani ina so na faɗa masa zai saya mini ko menene kuma ko nawa ne. Cikin sati biyu muka yi sabo da Abdul-hameed sosai ban san meye so ba sai a kansa, tabbas ya iya kulawa ya kuma san matakan sace zuciya tare da narkar da ita. Kullum cikin takatsan-tsan nake dashi amma ko da wasa bai taɓa yi mini maganar banza ba, bai taɓa yunƙurin kai hannunsa jikina ba. Kullum burinsa bai wuce a ɗaura aure a kai masa ni gidansa ba. Ko yaushe cikin faɗa mini yanda yake ƙaunar mahaifiyarsa da yanda yake burin kyautatawa da hidimta mata. Gadan gadan bikin ya matso Hamma Ahmad kullum cikin nan da nan yake yi da ni, Anwar kuwa kwana biyun nan kullum cikin jinya yake da aka kasa gane kansa. Hamma Adnan ya haɗe lefensa tsaf sai son barka, a unguwar Hamma Abubakar ya yi gininsa. Ranar da hantsi dangin Abdul-hameed suka kawo lefen gidanmu. A gidan Baba aka sauƙe su wata da na ji ana ƙiran ta da Anty Adama ta dage akan sai dai a ƙira ni su ganni. Na sanyi hijabina na fito filin tsakar gidan na tsuguna na gaishe su gabaɗayan su. Suka amsa suna bi na da kallo kafin Anty Adaman ta furta"ke ce amaryar Abdallah nan?. Ikon Allah sai kallo wannan mitsitsiyar yarinyar ya tashi hankalinsa a kanta kamar zai zauce, kullum cikin zancenta Aishata kasa Aishata kaza Allah ya kyauta". Na sunkuyar da kaina na kasa cewa komai, Adda Azima ta riƙo hannuna ta ce na koma ciki. Ko da na zare hijabin kaina neman waje na yi na zauna tare da zabga tagumi da hannu bibbiyu. Sai da suka tafi da yamma Umma ta zo ganin kayan. Ya yi ƙoƙari sosai da kuma bajinta na gani na faɗa, a karon farko sai da su Dada suka tsorita da yawan kayan. Da ya zo nake sanar dashi kayan ya yi yawa har iyayena suna magana akai, ya nuni mini cewar yana da shi ne shiyasa ya yi mini, da bashi da shi ai dole ya haƙura. Ya gyara zamansa yana fuskanto ni sosai ya ce"da su Abba zasu amince ma da har kayan ɗaki zan miki, ke kaɗai nake buƙata a kawo min gidana". Na yi saurin dakatar dashi da faɗin"tab ai kuwa dai ba zasu taɓa amincewa ba, ko yaya ne sai sun yi mini daidai ƙarfinsu wanda bai wuce zarafi ba. Ka yi haƙuri kawai". "To shikenan amma idan an kai ki gidana ai ina da damar saya miki komai". Na ɗaga masa kaina ina faɗin"ƙwarai kuwa". "Ina so na je na gaisar da su Umma". Sai da na murmusa kana na ce"tab Umma da kunya ai ba za ta taɓa bari ku haɗu ba, wataƙil sai bayan an ɗaura". Shima murmushin ya yi tare da sauya akalan zancen. Mun yi zance sosai har Anwar ya shigo ya iske mu suka gaisa sannan ya shiga ciki ya bar mu. "'Yan uwana suna ta yabon ki da suka kawo lefe, cewar kunyarki ta burge su". "Na fito na gaishe su amma ban gane su ba". Ya yi ɗan dariya kana ya ce"Anty Adama da Anty Alawiyya duk sun zo kuma sun ganki, bari ki ga hotunan su". Ya ƙare zancen yana zaro wayarsa daga aljihunsa ya soma latsa kana ya miƙo mini hotunan mata biyu ne a tsaye sai wata babbar macen da nake kyautata zaton cewar mahaifiyarsu ce a zaune, yana daga gefen hagunta sannan wani wanda suke tsananin kama dashi yana zaune daga gefen dama. Fuskokinsu gaɓadaya washe da ƙayataccen murmushin dake bayyanar da cewar zuƙatansu wanke yake tas da farin ciki. Shiga iri ɗaya suka yi na shadda ruwar ƙasa da ya amshi jikinsu hatta aikin dake jikin shadda iri ɗaya ce. Na kasa janye idona daga kan su na ce"masha Allah wannan dai na ganta ranar". Na ƙare zancen ina nuni da Anty Adama. "Ita ce babbarmu sannan Anty Alawiyya ni sai kuma auta Al'amin". Na miƙa masa wayar ina faɗin"Allah ya ƙara haɗa kawunanku waje guda". Ya amsa da amin cike da jin daɗin addu'ar. Haka muka yi sallama cike da kewar juna. Ana saura sati ɗaya bikin na koma gidan Adda Azima a cewar ta so take ta yi mini gyara sosai, saboda ta lura da wani gani ganin da dangin Abdul-hameed suke yi mini. Kafin a rufa kwanaki biyar na yi fes da ni fatata ta yi kyau har wani ƙyalli nake yi. Sau ɗaya Abdul-hameed ya zo gidan muka yi magana akan kuɗin da zai ba ni na gyaran jiki da kuma abincin ƙawaye. Na nuna masa cewar ban san komai game da hakan ba, don haka na ƙira masa Adda Azima suka yi zancen da ita. Dangi na nesa da na kusa tunin suka fara cika gidan don ba na wasa ba Dada ta yi gayyata, takanas ta ɗauki ƙafa taje har garin su ta kai gorona da na Adda Abida. Baba da kansa ya saya mana leshi da turmin atamfa guda ɗaiɗaya ya ce mu yi fitar biki dashi, a cewar sa kar a taɓawa kowacce kayan lefenta musamman ni da nake da dangin miji dole zasu sanya ido akan kayan da suka kawo. Adda Azima ta ba da aka yi mana ɗinkin kayan iri ɗaya, ranar juma'a da karfe biyun rana bayan an sauƙo daga sallar juma'a ya kasance dai-dai lokacin da aka ɗaura auren. Bamu san me ya faru ba sai ji muka yi wai an wuce da Anwar da asibiti ya yanke jiki ya faɗi a masallacin. Hankali gabaɗaya ya tashi amma an hana kowacce zuwa Hamma Abubakar ya ce da sauƙi ruwa kawai aka ƙara masa kuma yana tunanin ma zuwa yamma za a iya sallamarsa. Aka kai mu wajen Umma da Dada suka yi mana nasiha sosai sannan aka wuce damu wajen Baffa da Baba su ma nasihar suka ƙara yi mana. Baffa yana kan bakansa na cewar ko meye Abdul-hameed ya yi mini har na tako gidansa da sunan kawo ƙara ko zuwa yaji ba zai laminta ba. Hakan ya ƙara dagula mini lissafina na ƙara tsananta kukan da nake yi kamar zan shiɗe. Na ƙamƙame Umma ƙam a jikina da ƙyar aka raba mu. 'Yan uwanta su suka je yiwa Adda Abida jere 'yan uwan Dada kuwa suka je mini jere. Komai iri ɗaya aka yi mana mun sha kukan mu kafin aka raba mu aka wuce da kowa gidanta. Ba ni da ƙawa ko ɗaya don haka da ni sai dangina da abokan arziki. Har motar ta ja burki ban tsagaita da kukan da nake yi ba tabbas na ƙara gaskatawa cewar aure yaƙin mata, in ban da hakan mai zai raba ni da uwata aka kawo ni nan cikin mutanen da ban san so ba. Haka aka fito da ni sanye cikin laffaya da alkabba a kai da Baba ya sanya mana ni da Adda Abida. Za a shiga da ni a wuce dani izuwa sashina aka ce sai an fara kai ni wajen Amma mahaifiyarsa. Aka wuce da ni can kaina a ƙasa yake amma ina iya hango mutanen da suke cike a falon da ya ƙawatu da abubuwan alfarma da more rayuwa tun kafin na zauna wani daddaɗan ƙamshi ya bugu hancina. Aka zaunar da ni a ƙasa sannan suka gaishe da kowa. Kafin na gaishe su wata murya ta daki kunnuwana, cikin isa da izza aka furzo zancen a dake. "Wannan ce amaryar abu kamar an roƙo?". Shuru ya ratsa wajen na tsawon daƙiƙu kafin wata ƙanwar Baffanmu ta furta"ita ce ranki ya daɗe". Ta taɓe baki"madalla ɗauke ta ku kai ta sashinta". "To ranki ya daɗe ga amana nan sai an haɗa da haƙuri yarinya ce. Don Allah idan ta yi ba daidai ba a nusar da ita, dole sai da kwaɓa wani lokacin". Ba ta amsa ba sai wata dake kusa da ita ne ta amsa cikin faɗin"in sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya ya kawo ƙazantar ɗaki". Duk suka amsa da amin kafin aka ɗauke ni aka wuce da ni sashina. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 1️⃣5️⃣ Kaina yana ƙasa muka shiga sashin dangina suka rangaɗa guɗa. Aka kai ni har cikin uwar ɗaka. Adda Azima ce ke ta kwaɓar waɗanda suke girmama zancen da Amma ta yi. Sai da ango da abokan suka shigo sannan suka tsagaita, suka damƙa amanar amarya a hannun angonta tare da ƙara yi mana nasiha da nusar da mu cewar shi aure ɗan haƙuri ne dole sai mun kai zuciya nisa kuma mu kasance masu yiwa juna uzuri a ko yaushe. Sai da suka biya kuɗin sayan baki sannan aka buɗe musu fuskata, aka yi addu'a abokansa suka ce mutane su fito su fara mayar dasu. Duk sallama suka soma yi mini domin Bana ya ce babu kwana a gidan amarya ana kai ta cikin ɗakinta kowa ya dawo gida alabashi gobe aje a gano ta. Na yi kuka tamkar raina zai fita har sai da na ji idanuna sun yi mini wani nauyin gaske da ko buɗe su bana ƙaunar yi balle kallon haske. Tabbas Abdul-hameed ya cika cikakken masoyi domin ya bani duk wani kulawan da ta dace, duk da ya fahimci ina cike da tsoro, fargaba da kuma rashin sabo amma ya yi dabara wajen tafiyar da ni akan yanda nake. Da safe kafin ya shigo ɗakin kasancewar ba a nan ya kwana ba, na yi wanka na shirya cikin sigar riga da zanin atamfa na ɗaura hijabina a kai. Na zauna na yi shuru duk kewar 'yan uwana ya ishe ni kwana ɗayan da na yi ban gan su ji nake kamar na shekara ban sanya ta a cikin idona ba. A haka ya shigo ya same, ban ji shigowar sa ba illa zaman da ya yi a kusa dani tare da tafa hannunsa. "Lafiya tunanin me kike haka?". Na rusunar da kaina ƙasa"babu komai ina kwana an tashi lafiya". "Lafiya ƙalau ya kwanan baƙuta". A sanyaye na amsa da"alhamdulillah". "Ya kuma kuka?". Na yi shuru ban amsa masa ba ya yi gyaran muryar sannan ya cigaba da faɗin"a tsarin wannan gidan Amma ta tsani ta yiwa mutum magana ya yi mata shuru tabbas aikata hakan yana jawo tsananin ɓacin ranta. Don Allah kar ki aikata hakan a gare ta". Take naji gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau na gyaɗa masa kaina alamar na ji sai kuma na tuna da zancen nasan na yi saurin ɗaugo kaina ina faɗin"to in sha Allah zan kiyaye". "Allah ya bada iko". Na amsa cikin faɗin amin ya miƙe ya ce da ni na fito falo kafin ya yi wanka ya shirya mu je mu gaida Amma. Yanda ya umarce ni hakan na aikata na zauna zaman jiran sa a falon. Kujerun da aka yi mini sun zama abun tausayi a cikin falon saboda girmansa da kuma ƙawatuwarsa. Ga wakeken filin da ya yi saura. Ƙamshin turaren da na ji ya bugi hancina shi ya sanya ni ɗaga kaina caraf idanunmu suka haɗe cikin na juna, na yi saurin ɗauke nawa. A hankali ya tako ya iso har gabana tare da sa hannunsa ya tallafo fuskana ya ɗago ta. Tsam na matse idanuna na ƙi yarda na buɗe na kalle shi. Shafo goshina zuwa kuncina ya yi tare da hura mini iska a idanuna. Ya riƙo hannuna ya miƙar da ni tsaye ya na faɗin"mu je". A hankali nake takawa har muka fito daga cikin sashin. Babban gida ne mai ɗauƙe da part uku na Amma ya fi kowanne girma sannan namu da wani a gefensa. A tare muka yi sallama yayin kutsa kai cikin falonta aka amsa sallamar ciki ciki. Muka zauna a ƙasa sannan muka haɗe baki wajen gaishe ta. Sai da ta ja dogon lokacin kafin ta amsa mana tana kafe ni da ido"Abdallah yaya naga aamryar takan duk ta yaƙwane haka, jiya da aka shigo da ita nan ta fi haka daɗin gani da kuma hasken fata". "Amma wataƙil dai kallon tsoro kika yi mata a daren jiyan shiyasa, amma ba wani canjawan da tayi. Ta ma kwana da zazzaɓi ne saboda kukan da ta yi". Sai a lokacin na yi nasarar zame hannuna daga riƙon da ya yi mini ina ɗan janye jikina gefe kaɗan. "Kuka kuma na meye?". "Kukan rashin sabo da kuma rabuwa da gida". Ya bata amsar kansa tsaye da hakan ya sanya ta sakin dariya mai matuƙar sauti kana ta furta" ai yanzu ko yarinya 'yar shekara goma aka yi wa aure zaunawa take yi lafiya lafiya babu wani tashin hankali, balle wannan da zata iya haura goma sha shida". "Haka ne amma ko wa da irin halittansa ". Ba ta ce kuma ba illa jinjina kanta da ta yi tana ɗaukar wayarta ta fara latsawa tare da karawa a kunnenta. "A fito da abin karin kumallo ga ango da amarya har sun fito". Yana gama faɗin haka kit ta katse wayar. "Kin yi karatun zamani kuwa?". Tambayar ta ya katse mini zancen zucin da nake yi. Cike da girmamawa na ce"na yi amma ban yi nisa ba". "Yanayinki kuwa bai yi kama da na wacce ta taɓa zaman aji ba. Kin yi girki?". "Na iya dai-dai gwargwado". Ina rufe bakina aka yi sallama ta amsa sannan aka shigo ta dire kulolin abincin da ta jere a cikin wani kwando sannan ta gaishe da Abdul-hameed nima na gaishe ta ta amsa mini har da yi mini taken amarya mai maganar zuma. Ta koma sannan ta dawo da wasu kayan ta jere. Ta durƙusa har ƙasa ta ce "ranki ya daɗe komai ya kammala". "Ki je ki ƙira Al'amin da Alawiyya". "To ranki ya daɗe, me za a ɗauro da rana saboda baƙin da zasu iya zuwa?". Sai da ta ɗau lokacin kana ta furta"bana son gaggawa Asabe ki bari ranar ta yi tukunna sai a fara tunanin abinda za a yi". Kamar za ta yi mata sujjada ta ce"tuba nake uwargijiyata". Ba ta kul ta ta miƙe ta fice jim kaɗan Anty Alawiyya da Al'amin ɗin suka shigo. Suka gaisa da Abdul-hameed ni kuwa suka yi banza da ni. Hakan ya tabbatar mini da cewar jira suke na fara gaishe su. Don haka na sausauta muryata na gaishe da Anty Alawiyya sannan Al'amin kafin ya amsa Abdul-hameed ya yi saurin faɗin"kai yanzu sai ka amsa don baka da kunya?". "To meye abin rashin kunya don ta gaishe dashi ya amsa. Ai girman bishiyar kuka kawai ake gani amma gabaruwa ita ce babba, ko a ido ai Al'amin ya fi wannan yarinyar". Amma ta tsara zancen daki daki, kowa shi yake ɗibar abunda yake son ci ni kam ko motsawa daga inda nake na kasa yi, shi ya zuba mini ya kuma yi mini bismilla. A hankali nake kai abincin bakina, tunda muka fara cin abincin babu wanda ya ce ko kanzil har muka kammala. Asabe ta dawo ta tattare kwanukan tare da gyara wajen. "Alawiyya ki je sashin Abdallah ki ɗauko min hotunan kayan da iyayen matarsa suka yi mata". Wani irin yanayi na ji ya baƙunce ni shin tozarta ni Amma take son ta yi ko kuma nata salon ne haka shine abinda na gaza fahimta. Bai ce komai ba shima har Anty Alawiyyan ta miƙe ta fita ta dawo tare da nunawa Amma hotunan kayan da ta ɗauko. Ta kalla sosai sannan ta ajiye wayar tana taɓe baki"waɗanda kayan ba su yi ba dole za a mayar musu da abun su, don ba zan ji kunya ba sanin kanka ne yau ƙawayena a sauran dangi zasu zo ganin amarya da kuma ganin ɗakinta. Ai ga irin bajintar da iyayenta suka yi mata, idan aka zo aka tarar da wannan kayan ai na ji kunya. A fitar dasu maza a mayar musu zan sanya a zuba wasu da suka dace". Ƙirjina ya harba da ƙarfi idanuna yana hasko mini hotun ƙatuwar saniyarsa da Baba ya sayar domin yi mana waɗanda kayan. Gabaɗaya sai na ji zaman wajen ya gundure ni babu abunda na fi buƙata kamar na ga na bar wajen na keɓe ni ɗaya. "Iyayenta sun yi ƙoƙari wajen yi mata wannan kayan, maimakon a mayar musu dashi mai zai hana a sanya su a ɗaki guda har da kujerun tunda ɗakin zai ɗauko. Amma kowa fa zai so yaga yana amfani da wani abu dai da zai dunga tunawa da wani nasa musamman iyaye". Duk da a cikin lumana da kuma tsantsar biyayya da kwantar da murya ya yi mata zancen, sai na ji ta ɗaga murya sama tana faɗin"na gama yanke hukunci wannan kayan mayar musu da abun su za a yi, idan kuma kana so ka nuna min cewar ban isa na zartar da hukunci akan lamarin gidanka bane to bismilla". Cikin sanyin jiki da na murya ya ce"kin isa, ba na faɗi haka da nufin ɓata miki rai bane Allah ya huci zuciyarki". A gajarce ta amsa da"Amin". A take a wajen ta umarce Al'amin da yaje ya yi wa masu gadi jagoranci izuwa sashin sun fitar da komai, a deɓo kayan dake cikin sashin dake kallon namu a mayar dasu cikin namu. Sannan haka ya miƙe ya fice ina jin zuciyata tana yi mini wani irin azabban zogi. Ƙwalla suka ciko mini koramar idanuna na yi saurin mayar dasu. Muna nan zaune a wajen Al'amin ya dawo yana shaida mata an cire komai, ta jinjina kanta tare da cewar"za ku iya tafiya, bayan sallan zuhr ki zama cikin shiri domin za a baƙi kuma zasu ganki". "To in sha Allah a tashi lafiya". Na amsa mata sannan muka tashi muka fito ban san sanda hawayen da nake dannewa suka kwaranyo ba lokacin da na yi tozali da dukkan kayan da iyayena suka yi mini an fake su a gefe waje guda. Hatta kayan katakon basu tsira ba duk da jajircewar da Hamma Ahmad ya yi wajen ganin an zaɓo mini mai ƙarko kuma na ke ce raini. Ka kallon kayan da aka sauya a cikin falon ban yi ba na wuce ɗaki da sauri, ya rufa mini baya. Na zauna na zabga tagumi ina hawaye. A kusa dani ya zauna tare da naɗe dukkan ƙafafunsa wajen guda ya ce"ki yi haƙuri Aisha zama da Amma tabbas sai ma haƙuri mai haƙuri ma sai mai tsananin haƙuri. Don Allah ki taimaka mini wajen yi mata biyayya domin a yanzu ita kaɗai ta rage mana mahaifin mu ya rasu. Duk bana iya ƙetare umarninta ko kuma na yi mata musu akan komai amma ba hakan bane yake nuni da cewar zan bari ki tozarta a cikin gidan nan. Wallahi ina son ki kuma ba zan taɓa jure ana wulaƙanta ki akan idona ba". Cike da ƙarfin hali na ɗago idona da har yanzu yake tsiyayar da ruwar ƙwalla na sauƙe akan fuskarsa ina faɗin"abu ne mai kyau yin biyayya ga iyaye musamman uwa domin babu wani abinda za ka yi ka biya ta kwantankwancin rabin ɗawainiyar da ta yi da kai". "Ba za a mayar da kayan ba, za a sanya su a cikin ɗayan sashin tunda baƙi kawai ake sauƙa a cikin sa". Kaina kawai na jinjina masa ya ƙara matsowa dab da ni har muna jin fitar numfashin juna, ya kai bayan hannunsa yana share mini hawyen da suke fareti a bisa kuncina. Na lula duniyar tunani shin wani irin zama zan yi a cikin gidan nan da tsarin mutanen cikinsa ya sha bambam da na sauran gidaje. Shin ta yaya zan saba da halin Amma da ragowar 'yan uwansa?. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 1️⃣6️⃣ Sosai ya yi ta aikin lallashi na, ganin yanda ya ke nuna damuwarsa a fili ya sanya ni danne zuciyata da nake jin tana tafasa na nuna masa babu komai. Ko da wasa ban ƙara bari ya fahimci cewar abin yana damuna ba. Ya shirya ya ce dani zai je wajen abokansa da suka kwana yau duk za su wuce su yi sallama. Irin addu'ar da Umma take yi wa Baffanmu yayin da zai fita kasuwa irin sa na yi masa. Sosai ya ji daɗi ya sumbaci goshina sannan muka yi sallama. Na zauna a falon ina ƙarewa Kayan cikinsa kallo kaya ne na alfarma wanda kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da hakan. Launin ruwan toka da kuma dogayen labulaye ruwan ƙasa, haka kawai na ji raina a dagule ba rasa me ke yi mini daɗi, duk kyawun kayan sai na ji ba su wani burge ni ba balle ƙyalƙyalin su ya ɗaɗa ni da ƙasa. Ban motsa daga wajen ba sai na ji sallamar 'yan uwana kafin na miƙe har sun shigo. Da sauri na isa gare su tare da rungume Adda Azima tsam a jikina. Dangin su Baffa ne da na Umma da kuma na Dada. Sai Adda Azima da kuma Abasiyya. Na gaishe su cike da girmamawa duk suka amsa mini fuskokinsu a washe. "Ikon sai illahi ke kuwa Aisha ina kika samo waɗanda kujeru masu laushin tsiya?. Kana zama yana lotsewa da kai". Furucin Goggo Azumi kenan da take matsayin uwa ga Umma domin ita ta riƙe ta har ta aurar da ita bayan rasuwar iyayenta. Na kasa cewa da ita komai illa ƙasa da na yi da kaina ina murza yatsun hannuna da aka feshe shi da ƙunshi. Adda Azima ta taɓo kafaɗata tare da faɗin"ina kayan ki suke?". "Su na wancan sashin". "Kamar ya suna wancan sashin?". Goggo Azumi ta yi saurin katse ta da faɗin"me ye haka Azima?. Ai ke abin ki taya ta murna ne ma da farin ciki Allah ya yi mata ilhama ta tsinci dami a kale, a wannan zamanin wani na mijin ne zai yi wannan ɗawainiyar ga matar. Ya sauya nata komai lokaci guda, ke dai 'yar nan wallahi sai don barka Allah ya rufa miki asiri ya rage naki ki yi wa kanki karatun ta nutsu, ki yi masa biyayya dai-dai iyawarki". Har yanzun ban ɗago kaina ba na ce amsa cikin faɗin"in sha Allah ". Suka tashi suka shi shiga ɗaki, banɗaki da kuma kitchen duk suka gani suna ta yaba ƙoƙarin Abdul-hameed da gwaɗa tsaruwar kayan da aka zuba. Adda Azima ta ja ni ɗaki tare da titsiye ni da tambayar"ki faɗa min gaskiya Aisha ke kika buƙaci wannan kayan daga gare shi, ko kuma kin raina ƙoƙarin su Baffa ne wajen ganin gazawan su game da kayan da suka yi miki?". Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya mai matuƙar ƙarfi da kuma sauti kana na sama zarafin faɗin"wallahi Adda ko ɗaya ni ban roƙe shi abinda kike zargi na dashi ba, mahaifiyarsa ce ta ce kayan basu yi wai zata ji kunya a wajen ƙawayenta inda suka ga kayan shi ne ta ce a cire su a sanya waɗanda". "Ke Aishatu ki ji tsoron Allah mahaifiyarta san ce ta ce haka?". Na ɗaga mata kaina cike da son tabbatar mata da gaskiyar zancen ina mai ɗaurawa da"haka ta ce, da farko ta ce a mayar da kayan gida shi ne ya bata haƙuri aka bar saka su a wancan sashin". Ina iya jiyo bayyananniyar ajiyar zuciyar da ta sauƙe kana ta riƙo hannuna ta riƙe game cikin nata"kar ki gayawa kowa wannan maganar ko da kuwa Umma ko Dada ne suka buƙacin jin inda kayan ki yake ki shauda musu canza miki wasu ya yi, naki an adana miki su. Kar ki faɗawa kowa cewar mahaifiyarsa ce ta ce a cire kayan kin ji?". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau na ce"to in sha Allah zan yi yanda kika je". "Ina fatan babu wani matsala ko?". Sai da na yi dogon tunani sosai kafin na ce da babu komai. Ta jinjina kanta tana sakar mini hannuna dake saƙale cikin nata. "To mu zamu tafi, don Baffa ya yi gargaɗin cewar kar a daɗe a gidanki saboda tare kuke da 'yan uwan mijinki kar suka kamar wani abu ne ya kawo mu". Na yi saurin riƙe hannunta da hakan ya sanya ta komawa ta zauna daga yunƙurin miƙewar da ta soma yi. "Don Allah ku zauna a nan zuwa bayan zurh akwai mutanen da zasu zo, ta ce na zama cikin shiri. Ban san yanda zan yi ba ni kam". "Ki kwantar da hankalinki za ki iya in sha Allah. Wasu kalan baƙin ne?". "Ƙawayen ta da wasu daga cikin dangin su". Ta ɗan yi jim kana ta ce"shikenan bari na yi magana a Goggo Azumi ko ni sai na zauna nan su kuma sai su wuce gidan Abida. Don itama ba a koma mata ba tun daren jiya". "To". Muka fito tare da ita izuwa falon sanda muke shigowa ya yi dai-dai da lokacin da Asabe da wasu mata biyu suke shigowa da kulolin abinci da lemukan gora masu sanyi. Suka gaisa da dangina sannan suka fice. Sun ci sun sha sannan suka fara haramar tafiyan bayan sun yi sallan zurh, a lokacin Adda Azima ta ce na yi wanka. Ta sanar da Goggo Azumi abinda ke gudana ita ma ta yi na'am akan ta zauna ɗin tare dani. Wata doguwar rigar atamfa kalar ja da aka ɗinka mini daga gida, shi ta fidda mini ta ce na sanya. Ta ɗaura mini kallabi sannan ta zaɓo mini wani laffaya ruwan madara daga cikin kayan lefena ta naɗa mini, ta gyara mini fuskana tsaf tare da feshe ni da turare ba fito na yi cas da ni. Na ƙara fito a matsayin amarya daga sama har ƙasa. Na kalli kaina a madubi ina jinjina kaina, na juyo ina kallon ta ina cewa"ki cire kayan da za a rabawa dangi da kuma naku daga cikin kayan lefen". Ta waro idanu"ke rufa min asiri, ko safiyar yau sai da Baffa ya yi gargaɗin cewar bai yarda an taɓa komai daga cikin wannan kayan ba. Don haka ki bar kayanki". Take na ji ni a wani irin yanayi na daban na zauna a bakin ƙaton gadon ina cewa"Baffa fushi yake yi da ni har yanzu, wallahi ko wani irin farin ciki nake yi inna tuna hakan sai na ji gabaɗaya na nema walwalata ba rasa". Ta tausasa amon muryarta"ba ya fushi dake kuma a sannu a hankali komai zai wuce kamar babu wani abun da ya taɓa faruwa in sha Allah". Sallamar da aka yi a ƙofar ɗakin ya dakatar da ni daga maganar da na yunƙura da nufin furtawa, Adda Azima ta amsa Asabe ta shigo ta durƙusa har ƙasa "Hajiya ce ta ce azo a sanar dake in kin shirya ki fito baƙinta sun iso". "To za ku tafi tare ko kuma za ta biyo bayan ki ne?". "A'a zata iya biyo bayana kawai na zo sanar da ita ne". "To ga ta nan fitowa". Adda Azima ta amsa mata, har ta fice daga ɗakin ban ɗauke idona daga gare ta. Adda Azima ta ƙara gyara mini laffayan tare da jawo shi ya ɗan rufe mini rabin fuskata. Ta riƙo hannuna muka fito bayan ta gama jaddada mini cewar na nutsu kuma kafin na yi komai na yi tunani na kuma san yanda zan na amsa musu magana. Muna jiyo tashin maganar mutane a falon ƙasa ƙasa. Cike falon yake da jama'a muka shigo muka zauna wata mata ta rangaɗa guɗa, muka gaishe su a ladabce duk suka amsa mana. "Wacece amaryan a cikinku?". Adda Azima ta yi musu nuni da ni, matar da tayi zancen ta yamutse fuska"yanzu Hajiya duk kyau, nasaba, dukiya da ilmin Abdul-hameed ya rasa wacce zai aura sai wannan yarinyar. Wannan raino zai yi ko meye?". Duk suka saka dariya kafin Amma ta furta"kin san ance so gamon jini shi kuma wacce ta yi masa kenan". "Haka ne kam". Ta kuma faɗa a daƙile, raina ya soso sosai amma na danne zuciyata. Nasiha suka yi mini a taƙaice sannan suka fara cin abincin da Asabe ta jere su a nan cikin falon sashina. Har suka kammala ba su ce da mu mu tashi mu tafi ba. Haka nan muma ba mu gosa ba sai da suka tashi tafiya suka buƙaci lambar asusun ajiyata na ce dasu bani dashi. Sosai suka ta yin mamaki kwatankwacin irin mamakin da wanda ya ga wani da bai iya wani aikin ibada kuma baya neman sani akan sa. Suka ajiye mini wasu kuɗaɗe suka tafi bayan na yi musu godiya da fatan sauƙa lafiya. Su na gama fita na janye laffayan daga kaina zan yi magana Adda Azima ta yi saurin taran numfashina"ki yi haƙuri shine kawai abinda zan iya faɗa miki, domin ki kaɗai za ki riƙe ki ci riba a rayuwarki". Wasu hawaye suka gangaro mini"ki kai kuɗin a su Umma babu abinda zan yi dasu. "A'a ki ajiye a wajen ki, ki fara nunawa mijinki tukunna. Alabashi sai ki yi duk abinda kike da niyya ki yi dasu". Lallashina ta yi ta yi da ba ni haƙuri, na sha jin ana yiwa amarya huɗubar haƙuri a mafi yawan lokuta sai dai ban yi tsammanin cewar tun daga wayewar ranar da aka kai ni gidan mijin zan ci karo da hakan ba. "Ya jikin Hamma Ahmad?". "Uhmm da sauƙi yau dai ya ɗan ɗaga har ya fito waje". Na dafe ƙirjina"na shiga uku daman sosai ne rashin lafiyan". Sai da ta gyara zaman ta kana ta ce"da sauƙi dai kawai za a ce". Na yi shuru ban ƙara cewa komai halin da yake ciki ya yi mini tsayiwar ƙayar fiki a raina. Sai da ta yi sallan Asr sannan Abdul-hameed da wani abokinsa ɗaya suka shigo suka gaisa sosai da Adda Azima. Ya sanya aka mayar da ita har gida bayan ba yi sallan isha'i na zauna akan sallayan na zuba tagumi. Ya zo ya zauna a gabana tare da naɗe dukkan ƙafafunsa waje guda tamkar mai zaman tahiya. Ya ɗage mini gira" wannan tagumin fa na menene?". Na sauƙe numfashi tare da yin ƙasa da kaina"babu". "Ban rabo ki da iyaye da 'yan uwanki don na dunga saki tagumi ba, ina so na ganki kullum cikin walwala sannan bana son ki na ɓoye mi duk wani abunda yake damun ki don Allah kin ji?". Na gyaɗa masa kaina alamar na ji, ya yi ɗan murmushi kana ya ce"kin amsa na ji". "To in sha Allah". "Yauwa don kin ga bayan amanar ki da iyayenki suka ba ni, ranar ɗauri aure da safe Hamma Ahmad ya roƙe ni da na kula dake sosai na kuma zamo bango a gare ki da za ki jingina dashi a duk lokacin da kika shiga wani matsala. Na kuma yi masa alƙawarin ƙawata rayuwarki da farin ciki marar yankewa". Ji na yi tamkar an sanya igiyar kirtani an dai daure ni dashi. Na gaza cewa dashi komai cikin raina ina ƙara jinjina matsayin Hamma Ahmad a gare ni. "Baƙin Amma sun zo ina fatan komai ya tafi dai dai, ba zan iya tambayanta ba shiyasa na tambaye ki". Zancen sa ya katse mini hanzari, a hankali na furta"babu wani abu komai lafiya har kuɗi ma suka ba ni masu yawa". "To Alhamdulillah ina can ina tunanin abinda zai faru". Ya yi ɗan jim kafin na ji hannayen sa akan nawa, na ɗago idanunmu suka sarƙafe cikin na juna na kasa ɗauke nawa kamar yanda shi ma ya kafe ni da nashi. "Danginki ba su ce ina kayanki ba da suka zo?". Na yi nasarar yanje nawa ido gefe guda"basu ce komai da suka tambaya na ce dasu yana ɗayan sashin". "Kin zaɓin ki ɓoye musu gaskiya kenan?". Na furzar da iska daga bakina"in dai ina sonka ai dole na zama mai kare ta a ko yaushe a kuma gaban ko waye". Ban yi aune ba na ji ya jawo ni jikinsa yana ga furta mini kalaman godiya. A nan sashin muka ci abincin daren, washe gari da safe bayan mun shirya muka je gaishe da Amma a nata sashin. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________ Page 1️⃣7️⃣ Na ga saƙonni ku na addu'o'in da kuka yi mini bisa rashin lafiyan da na yi, na gode sosai da kulawan ku a gare ni. Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci. ********************* Tana zaune akan lallausan kafet ɗin da yake malale a cikin falon tana karatun wani ƙaramin littafin addini a hannunta, da siririn farin gilashi akan karan hancinta. Ta ɗago ido ta yi mana kallo ɗaya tare da mayar da kanta ƙasa. Muka ƙariso muka zaune tare da yi mata sannu. Sai da ta ja lokacin kafin ta rufe littafin ta ajiye gefe gudu kana ta amsa gaisuwar tamun. "Sai yanzu ka sama fitowa?". Ya yi ƙasa da kansa yana ɗan sosa ƙeyarsa ya ke faɗin"Amma wallahi mun makara bamu tashi da wuri ba". Ta jinjina kanta"ko sallan asuba baka fita ba lafiya?". "Sanda na tashi har an shiga sai kawai na yi a gida". Ta yi shuru na wasu daƙiƙu kana ta furta"ba laifi hakan ma ya yi". Tana rufe bakinta Asabe ta yi sallama tare da dire kulolin abincin da ta riƙo a hannunta, ta kuma komawa ta ɗauko plate. Na yunƙura da nufin taimaka mata muryar Amma ta dakatar da ni. "Koma ki zauna ba aikin ki bane". Jikina ya yi sanyi ƙalau na koma mazaunina na zauna tare da yin ƙasa da kaina, sai da Anty Alawiyya ta shigo na ɗago na gaishe ta ta amsa mini tana yatsina fuska. Sai da muka gama cin abincin Asabe ta dawo ta tattare kwanukan tare da gyara wajen tsaf. Na bi ta da kallo sa'ilin da take ficewa daga cikin falon babbar macece sosai don a ƙalla za ta iya yin sa'ar su Umma. "Ka yi magana da Aminu ne?". "E na yi kuma ya shaida min cewar har yanzu yana son matarsa, ba zai kuma sake ba akan wannan dalilin. Ni a gani ne ta yi haƙuri kawai ta koma kan 'ya'yanta". Na shuru ina sauraron su domin na ƙasa fahimtar zancen. Amma ta yi gyaran murya kana ta ɗaura da faɗin"Alawiyya ba zata koma gidansa ba matuƙar wannan matar tana ciki sai dai ya zaɓa ko 'yata ko kuma matarsa". Sai a lokacin na soma gane kan zancen duk dai akan Anty Alawiyya ce da tun ɗazun ta yi shuru tamkar ruwa ya cinye ta. Ina iya jiyo ajiyar numfashin da ya sauƙe ya ce"shikenan zan sanar dashi hakan". Haka suka cigaba da tattaunawar su har ya miƙe yana musu sallamar zai fita. A daƙile ta ce dashi ya dawo lafiya haka nan ma Anty Alawiyya. Al'amin kam daman bamu yi karin kumallon dashi ba. "Tashi ki raka mijinki". Na tsinkayi muryar Amma a sama, na miƙe a hankali na bi bayansa har ya isa wajen motarsa yana tsaye alamar shi ma ni yake jira. Ya kafe ni da ido da hakan ya sanya ni yin ƙasa da nawa ina wasa da yatsun hannuna. Ya yi murmushi tare da faɗin"haka aka ce miki ki zo ki sani a gaba ki yi shuru ki kasa cewa dani komai?". "Amma ce ta ce na raka ka". Ya ɗan matso kusa da ni ya sunkuyo da kansa kaɗan ta yanda tsayin mu ya daidaita dashi ya ce"to shikenan sallame ni na tafi". Na watsa masa idanuna ya ɗage mini gira yana ƙara faɗin"ina ji fa". "Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya ya kuma dawo da kai lafiya. Allah ya tsare ka da dukkan abin ƙi ya haɗa ka da dukkanin alkhairin dake cikin wannan rana. Ya azurta ka da halal ya kuma nisanta da haram komai ƙanƙantarsa". Ya kasa cewa da ni komai illa tsura mini idon da ya yi babu ko ƙiftawa, sai da na yarfa hannuna a fuskarsa sannan ya dawo dai-dai yana sakin wani ƙayataccen murmushin da ya ƙara fito da ainihin kyawun zubin tsukakkiyar fuskantar da sajensa ya kwanta ya yi luf. "Na gode da wannan tarin addu'o'in nakin gare ni, idan Allah ya dawo da ni lafiya sai na ba ki wani babbar tsaraba". Ya ƙare zancen yana lakace mini kunci, har ya shiga cikin motar ina tsaye a wajen. Ya zuge gilashin motar yan kallona ya ce"ki matsa kar na ƙara fancakala miki ruwa". Sosai furucin nasan ya sanya ni sakin dariya, na matsa gefe ya ja motar ya fice daga cikin gidan. Na sauƙe nauyayyen ajiyar zuciya kana na koma sashina na kwanta, raina cike da kewar yan uwana. Ban san sanda bacci ya ɗauke ni sai jin sallamar Asabe a ƙofar ɗakin ne ya farkar dani, na yi miƙa ina sakin salati sannan na zo na duɓe ƙofar. "Hajiya ce ta ce a zo a sanar dake an kammala girkin rana, idan kina buƙata a shigo miki dashi". Na ƙirƙiro murmushi na dasa a fuskata"sannu da ƙoƙari Baaba, amma a bari zuwa anjima kafin shi ɗin ya dawo sai a shigo dashi". Ta ɗan kallo ni ta ce"ai baya dawowa cin abincin rana ban sa ni ba dai ko yanzu zai fara". Na yi saurin wayincewa na ce"to shikenan a shigo dashi a iya na mutum ɗaya". "To" Ta amsa dashi tana ɗaukar hanyar ficewa, na mayar da ƙofar na rufe ina furzar da iska daga bakina. Jin ana ƙwala ƙiran salla ya sanya ni ɗauro alwala na gabatar da sallan zurh sannan na ɗan calcakale abincin da Asabe ta shigo dashi. Gabaɗaya sai nake ji na wani irin domin a gida sam ban saba cin abinci ni ɗaya ba. Wanka na yi na saka wani doguwar rigar yadin material na nufi sashin Amma. Tana kan sallaya tana lazimi na tarar da ita na zauna har ta gama muka shafa addu'ar tare. Tana tashin na yi saurin miƙewa na naɗe sallayan na ajiye, sai da ta zauna sannan na zauna ina yi mata sannu da huta, ta amsa mini. "Lafiya?". Tambayar da ta watsa mini ya cikina kaɗawa. "Daman na zo ne ko kuma buƙatar ayi miki wani abun sai na yi miki". Sai da ta yi ɗan jim tana ɗauka makunnin na'urar sanyaya ɗaki dake cikin falon ta kunna shi, kana ta furta "ba na buƙatar komai sai dai ina so na yi miki wasu tambayoyi". "Na yi alƙawarin sanar dake dukkan gaskiyata akan dukkan tambayar da za ki yi mini". Ta jinjina kanta"yaushe kuka haɗu da Abdul?". "Mun haɗu dashi a lokacin bikin Hammana a hanya ya fancakala mini ruwan kwata a jikina, tun daga lokacin yake bibiyata har ya zo gidan mu ban sani ba". Shuru ya biyo bayan zancen nawan na ƙarshe, har sai da na fara zargin ko na faɗi wani abun da bai dace bane. Sai can ta ta ce dani"iyayenki sun so haɗa ki aure da ɗan uwanki amma kika bijire kika auri zaɓinki. Me yasa kika zaɓi Abdul akan wanda ya kasance jininki?". Take na ji wani maiƙon zuffa ya kwanta a goshina cikina ya bada ƙarar ƙululu. Ta saki taƙaitaccen murmushi "kina mamaki inda na zama wannan bayanan ko?". Na jijjiga kaina alamar a'a kana na aro jarumta na yafawa kaina na soma faɗin"ban yi mamaki ba domin duk wasu iyaye idan ɗan su zai yi aure sukan gudanar da nasu binciken, kamar yanda dangin amarya ma suke yi nasu". Na tsura mini ido tamkar ɗan sandan dake titsiye ɗan fashi cikin sigar son gano gaskiya. "Bani amsar tambayata". Na ja dogon numfashi na fesar"ban zaɓi Abdul-hameed akan Hamma Ahmad face dama can Allah ya rubuta cewar Abdul-hameed shi ne mijina a duniya tun kafin samuwar ruhina a bayan ƙasa. Na yi imani da cewar babu wanda yake aurar matar wani domin da Hamma Ahmad mijina ne babu wata ƙaddarar da zata haɗa ni da Abdul-hameed". Shuru ta yi ba tare da ta ce da ni ko kanzil ba illa ɗauke kanta da ta yi ta zuba idanunsa ga tvn dake aiki a cikin falon. Yanda ta basar da ni tamkar bata saurara na ko kuma bata san da wanzuwa na a wajen ba. Sai da na cire rai da samun amsa daga gare ta kana ta furta"haka ne maganarki, zan sanar dake wani abu da na ƙudurci faɗawa duk wata matar da Abdul zai aura ya yi zaman aure da ita". Gabana ya yi ras na dake ina gyara zamana da hakan ya bata lasisin ɗaurawa da"Abdul-hameed a cikin 'ya'ya shi na daban don haka nake ɗaukar duk wani abun da ya shafe shi azimun. Ina bashi dukkanin wata kulawa fiye ma da yanda mata zata kula da mijinta, ki riƙe shi hannu bibiyu domin samun irin sa a cikin wannan zamani abu ne mai wahalar gaske. Abin da nake son sanar dake shine Abdul-hameed ba zai zauna da mace ɗaya tal tamkar rai duk lokacin da na ga wacce ta yi min kuma hankalina ya nutsu da ita zai ƙara aure ya kawo matar cikin gidan nan". Tsabar harbawan da ƙirjina ya yi ban san lokacin da na runtse idona da ƙarfe ina cije leɓena ba tare da kokuwa da numfashina da yake maƙale mini a ƙirji. "Lafiya dai?". Sai da na yi ƙoƙarin dai dai nutsuwata na furta"lafiya". "To ina fatan kin ji abinda na faɗa?". Na ɗaga mata kaina"na ji kuma ina addu'ar Allah ya bashi ta kirki wacce zata kula miki dashi kamar yanda kike yi". A daƙile ta amsa mini"Amin". Tana rufe bakinta Al'amin ya shigo falon tare da zubewa akan kujera ya toshe dukkan kunnuwansa da earpiece yana bin waƙar. "Tashi ki ji ki fara shirin tarban mijinki". "To Hajiya a tashi lafiya". Hannu kawai ta ɗaga mini na tashi na fice daga falon. Har na isa sashin ina saƙa da warwara cikin raina yayin da maganganun natan suke yi mini amsa-kuwwa a nau'rar naɗar sautina. Shifit na zube akan gadona ina mayar da numfashi a hankali idanuna zube akan rufin ɗakin da ya zamo shamaki tsakanina da sararin samaniya. Na daɗe kwance a wajen har sai da na ji an yi ƙiran sallan asr sannan na tashi na yi alwala nazo na gabatar da sallan. Al-ƙur'anin dake ajiye saman dirowar dake gefen gadon na ɗauka na fara karantawa ban tashi ba har aka yi ƙiran sallan magrib na sallan. Ina naɗe sallan na hange shigowar motar Abdul-hameed cikin gidan, na tsaya ta jikin tagar ina kallonsa ya fito daga cikin motar da waya maƙale a kunnensa bakinsa yana motsi da hakan ya tabbatar mini da magana yake yi sai dai bana iya jiyo abinda yake faɗa. Sai da ya gama wayar ya juyo na yi saurin ja da baya, a tunanin nan zai shigo amma ina leƙawa sai naga ya nufi sashin Amma. Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina tausar zuciyata da take cike da mararin son ganin sa. Tuna furucin Amma na ɗazu ya sanya dukkan gaɓoɓin jikina yin sanyi, wata zuciyar ta ce dani gwara ma ki saba tun yanzu domin idan ya yi auren kina gani sashin wata zai shiga su kwana tare gwara nan wajen mahaifiyarsa ya je. Na danne zuciyata na tashi na shiga banɗaki na yi wanka tare da ɗauro alwala na fito, na sha mai kaɗan a jikina sannan na saka kayana na ɗaura hijabi a kai na yi sallan isha'i. Na gyara fuskata duk da baƙin fatata amma na yi fayau da ni na ɗaura kallabi tare da shafa humrar da Dada ta ba ni, na buɗe ƙofar ɗaki zan fita muka yi kiciɓus dashi zai shigo . Na yi saurin ja da baya ina bashi hanya ya shigo, ina ɗago idona muka haɗa dashi ya kashe mini ido ɗaya. Tare da miƙa mini hannunsa na yi ƙasa da kaina don na fahimci abinda yake nuni. Ya ranƙwafo daidai kunnena ya yi mini raɗa"kin yi kyau kamar a sace a gudu". "Na gode". Na furta a hankali ya riƙo hannuna muka zauna a bakin gado ya kafe ni da ido da har sai da na fara tsorita da irin kallon da yake yi mini. Na ɗage masa idona ɗaya alamar lafiya, ya sa ki murmushi yana cewa"na kwaso gajiya sosai a wajen aiki". "To bari na haɗa maka ruwa ka yi wanka ka ɗan huta". Ban jira amsar sa ba na miƙe na shiga banɗaki na haɗa masa ruwan wanka tare da ajiye masa komai na buƙata. Kafin ya fito na ciro masa wasu kayan na ajiye masa akan gado na fita na koma falo ina jiransa. Jim kaɗan ya fito yana waya abu ɗaya na tsinta a cikin zancen kafin ya katse wayar shine"ka san yanda zaka gyara gidanka tun kafin abubuwa su fi ƙarfinka". Ya katse wayar sannan ya ƙira Asabe"a shigo mana da abinci". Har ya zauna ina bin shi da kallo bai ce da ni uffan ba ya jingina kansa jikin kujerar tare da lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa. Na ɗan matso kusa dashi na ce"lafiya kuwa?". Ya ɗaga mini kansa haka nan kawai na ji ban gamsu ba na ƙara faɗin"don Allah ka sanar dani me ke faruwa, idan kuma bani da hurumin jin abinda yake damun ka ne sai na taya ka da addu'a. Allah ya warware maka matsalar". Nan ma shuru ya yi ya jawo ni jikinsa na kwantar da kaina akan ƙafarsa, jin ana buga ƙofar falon ya sa ni tashi naje na buɗe Asabe ce riƙe da kwandon da ta jerin kuloli a ciki ba karva tare da yi mata sannu na shigo dashi. Har na zuzzuba abincin yana nan zaune inda na bar shi bai motsa. Na jawo hannunsa ya sauƙa ba tura masa plate ɗin gabansa don tare na saka mana, a hankali yake ci kamar wanda aka yi masa dole. "Ban san da waye ka yi waya ba, amma na tabbatar yin wayar ne ya jefa ka cikin wannan yanayin". Ya ajiye cokalin hannunsa yana fuskanto ni"mijin Anty Alawiyya ne wallahi ina jin kunya da nauyinsa sosai amma Amma ta dage akan sai zai na ce masa ya aikowa Anty Alawiyya takardarta ko kuma ya zaɓa tsakanin ita da amaryar da ya yi". Muƙut na ci abincin ya wuce da ƙyar ta maƙoshina, lalle Amma tana son nata da kuma kishin su. Nata 'yar ba zata zauna da kishiya ba akan hakan ta gwammace a sake ta, amma shi ne ni take ambata mini cewar ko ba daɗe ko ba jima Abdul-hameed sai ya ƙara aure ba zai zauna da mace ɗaya ba. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________ Page 1️⃣8️⃣ Sai na cika satikai biyu cif a cikin gidan sau ɗaya na yi waya da Umma da wayarsa na tambayi jikin Hamma Ahmad ta ce mini da sauƙi. Ban taɓa ɗaura girki ba kullum Asabe ce ke kawo mana daga sashin Amma, ban taɓa nuna damuwata akan hakan ba balle na nuna masa ina son na yi girkina da kaina. Kamar yanda shima bai taɓa cewa da ni komai akan hakan ba. Na fahimci cewar duk cikin 'yan uwansa babu wanda yake son Amma da tausayinta kamar sa, baya taɓa tsallake kara idan ta ajiye. Sannan ba ya yi musu da ita akan dukkan abinda ta ce dashi idan ta kalli balbela ta ce baƙa ce bin ta yake yi a haka ya ce babu abinda ya kai ta baƙi. Bayan gaisawa har yanzu babu wani zancen da ya taɓa shiga tsakanina da Anty Alawiyya balle kuma Al'amin. Basa zama inda nake balle hira da ni tun da nazo gidan basu taɓa shigowa sashina ba. Ranar wata juma'a ya ce mini na shirya zai dawo da wuri zamu je wani waje, haka na wuni da tunanin idan zamu je. Sai da na yi sallan zuhur sannan na yi wanka na shirya cikin shigar doguwar rigar atamfar da ta sauƙa mini har ƙasa, na ɗaura kallabi ina zauna ina jiran sa. Na daɗe zaune sai can na ji ƙaran shigowar motarsa na miƙe da sauri na naje jikin taga na tsaya ina leƙansa, kamar yanda na yi tunani sashin Amma ya fara shiga sai dai bai daɗe ba ya fito. Na saki labulen tagar na fito falon domin tarban sa, muka sakarwa juna murmushi yana ware mini hannayensa na gane nufinsa bai wuce naje gare shi ne, don haka na kauce na wuce na kawo masa ruwa na tsiyaya masa a kofi na miƙa masa ina yi masa sannu da zuwa. "Afuwan matar kirki na bar ki kina ta jira ko?". Ya faɗa yana zame kofin daga bakinsa, na ƙara ƙawata fuskata da annuri "a'a ban ma daɗe da yin shirin ba nima". "To shikenan nima bari na je na shiryo". Ya miƙe tsaye tare da miƙa mini hannunsa na riƙe muka wuce ɗakinsa, kafin ya rage kayan jikinsa na haɗa masa ruwan wanka na fito ya shiga. Na ciro masa wani shadda kalar sararin samaniya na ajiye masa akan gado sai ya yi daidai da irin zanen dake cikin atamfar dake jikina. Na ciro masa hula, agogo da maɓallin hannun rigar na ajiye masa kana na koma falo na zauna. Babu jimawa ya fito yana gyara zaman hular akan sa na yi masa murmushi ina ɗaga masa yatsan hannuna alamar ya yi kyau. "Mu je ke ma na ciro miki kayan da za ki saka, kamar yanda kema kika ciro min". Na waro ido ina duban kayan jikina"ai ni na gama shiri na ni kam". "Wannan bai yi mini ba". Kafin na ce wani abu har ya shige ɗakin na bi bayan sa, yana tsaye a gaban wadrobe ɗin kayan yana dubawa. Ya zaro wata abaya da mayafinta irin kalar shaddar dake jikinsa sai shi ya yi ɗan duhu haka. "Yauwa wannan nake so ki saka". Babu musu naa karɓa na shiga banɗaki na saka na fito, ya bi ni da kallo sannan ya ce na zauna a gaban madubi da kansa ya shafa mini hoda ya saka mini kwalli sannan ya shafa mini man leɓe. Yana ƙoƙarin ɗaura mini mayafin rigar a kaina na kauce"yanzu duk gyara fuskana da na yi kafin ka dawo bai yi ba kenan?". Ya lakace mini karan hanci yana faɗin"ya yi sosai ma, kawai ina so yau na hutar dake ne ni zan shirya ki gabaɗaya tunda na dawo da wuri". Ban ce dashi komai ba har ya gama ɗaura mini mayafin, ya ɗauko wani mayafin mai girma da kauri ya naɗa mini a kaina. Sosai shigar ya yi mini kyau na fito na yi ɗas da ni. Hatta jaka da takalmin da zan saka shi ya zaɓa mini ya riƙo hannuna muka fito falo ya ce sai mun yi hoto. Sai da muka gama yi muka nufi sashin Amma tana zaune kamar kullum a inda take zama, muka yi mata sannu ta amsa Al'amin yana gefenta yana latsa waya. "Fita zaku yi na gan ku da wannan shirin?". Ya ɗan shafa goshinsa"e zamu fita amma ba daɗewa zamu yi ba". Sai da ta taɓe baki ta furta"kuma muna shirin cin abinci yanzu". Ya yi saurin faɗin"ku ci kawai ba komai zamu tsaya a gidan abinci mu ci". Sosai ta tsura masa idanun da ya sanya shi rusunar da kansa ƙasa. "Bana son ina magana ana katse ni kafi kowa sanin hakan". "Afuwan tuba nake Amma". Ta yi banza da shi sai can ta ce"ku tashi ku bani waje". Tabbas na san matsayin uwa darajar ta da kuma kimarta daban yake, kuma tana haƙƙi babba akan 'ya'yanta amma na yi mamakin yanda ya maraice tamkar zai fashe da kuka yana bata haƙuri cikin roƙo da magiya, furucin da ya yi a ƙarshen zancen sa ya sanya ni ɗago idona na yi masa kallo ɗaya na maida kaina ƙasa. "Ba katse ki na yi ba domin bana fatan ganin ranar da zan katse miki zance a rayuwata. Idan ba ki amince ba sai mu fasa fitan mu bari sai wani lokaci". "Ba zan hana ku aiwatar da abinda kuka shirya ba, amma ka kiyaye katse ni idan ina zance gaba". Da rawar jiki ya amsa"in sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba". Sai da zamu fita na ce"a tashi lafiya". Ko kallon kirki ban ishe Al'amin va domin tun zaman mu har muka miƙe bai ce mana ƙala ba. A motarsa muka fita yana toƙin a hankali kamar wanda aka sanarwa da saƙon mutuwa. Na kallo shi game da faɗin"ka yi haƙuri ka daina saka damuwa a cikin ranka". Ina iya jiyo yanda ya furzar da iska daga bakinsa, kana ya sama zarafin cewa"a rayuwata babu abinda na ƙi jininsa, nake gudunsa da kuma kiyaye faruwarsa kamar ɓacin ran Amma. Bana iya jurewa ko kaɗan". "Ba ta yi fushi da kai ba. Ta dai nusar da kai ne a lokacin da kake ƙoƙarin kauce hanya. Kuma na lura a cikin yan uwanka kafi kowa kiyaye ɓacin ranta da ƙoƙarin son faranta mata". Bai amsa mini ba sai da ya karya kwana kana ya ce"na kasance irin mutanen da ba basa iya ɓoye soyayyar su akan duk abinda suke so ne". Na jinjina kaina"na ga alama". Mun ɗan taɓa hira kafin muka isa gidan cin abincin muka cika cikinmu. Mu ka ƙara ɗaukar hanya sai a lokacin Allah ya bani ikon tambayar sa inda zamu je. "In har kin yarda da ni to kawai ki zauna ki yi shuru. Idanunki zasu gane miki inda zamu je". Yanda ya faɗan hakan na yi na zauna na yi shuru. Ya tsaya ya sayi bandir ɗin lemukan gora da abaya da kankana aka saka masa a bayan motar, muka cigaba da tafiya. Ina ganin ya shiga layin mu na ɗago na kalle shi, ya ƙi yarda ya kalli ni. Har ya faka motar a ƙofar gidan Baba bai kalla inda nake ba. Ya riga ni fita ya zagayo ya buɗe mini ƙofar ban fito ba na ce "daman nan zamu zo?". "E ko baka so mu zo ne?". Na jijjiga masa kaina na fito ya ce na shiga idan na yi masa iso sai ya shigo. Ina sanya ƙafata a cikin zauren muka yi kiciɓus da Anwar zai fita. "Anwar". Na faɗa muryata yana rawa saboda wani mummunan ramar da ya yi marar daɗin faɗa da baki. Shi ya fara ɗauke idonsa daga kaina yana cewa"yanzu kika zo?". Na gyaɗa masa kaina. "To ki ƙariso mana". Yana gaba ina bin sa a baya muka ƙarisa shiga cikin gidan. Dada tana zaune akan tabarma tana sauraron rediyo, Abasiyya na gefe tana wanki. Da tsantsar murnar da ya kasa ɓoyiwa akan fuskarta Dada ta tarbe ni tamkar za ta maida ni ciki don soyayya, sai nan da nan take yi dani. Bayan na gaishe ta ta amsa mini fuskarta kamar gonar auduga ta ɗaura da"yaya mijinki nakin"?. "Lafiya ƙalau, tare dashi muka ke yana waje". Salati ta saka kamar wacce nayi wani zunubi. "Aishatu Allah ya nuna min ranar da za ki yi wayo, yanzu ku zo tare da mutum amma ki bar shi a waje a tsaye. Anwar je ka shigo dashi". "Shi fa ya ce na fara shigowa Dada". Ta yi mini daƙuwar tare da sanya Abasiyya ta miƙo mata hijabinta daga ɗaki ta sanya. Aka shimfiɗa masa sallaya akan tabarman da muke zaune. Duk yanda Anwar ya dage masa akan ya zauna akan sallayan, ƙi ya wa ya yi ya zauna akan tabarman ya gaishe da Dada cike da girmamawa. Ta amsa tana tambayar "Allah ya sa dai ba ita ta ɗaga maka hankali sai kun zo ba?". Ya yi murmushi tare da faɗin "A'a mun yi waya da Adnan ne yake shaida min har yanzu Hamma Ahmad yana kwance jikinsa ya ƙi daɗi. Shine na ɗauko ta muka zo duba shi". "Wallahi Ahmad kam yana jin jiki sai dai addu'a, abu ya ci ya ƙi ƙarewa. Yau ne ma ya ɗan ɗaga don tunda ya fita masallacin juma'a har yanzu bai dawo ba". Ni da shi muka haɗe baki wajen faɗin"Allah ya bashi lafiya". "Amin". Ta amsa dashi kafin ya furta"bari na je masallaci ana ƙiran salla kafin ya dawo". Tare da Anwar suka fita, jim ƙadan yara suka fara shigowa da kayan da ya saya aka zuba masa a mota. Dada ta rufe ni da faɗa na hau yi mata rantsuwa akan ni ba ni ce ya saya ba hasalima ban san nan zamu zo ba. Salla nima na yi na fito na zauna na kwantar da murya na ce"ni kam Anwar shi ma jinyar ya yi ne naga duk ya rame?". Sai da ta saki sakakkiyar ajiyar zuciya ta ce"babu jinya akwai damuwa ya ɗauka ya ƙwallafa a cikin ransa. Babu irin tambayar da Baffanku da Babanku ba su yi masa ba amma ya ƙi faɗan abinda ke damun sa. Daga ƙarshe ma cewa ya yi wai karatu yake so ya cigaba dashi baya son zaman garin". Ƙirjina ya duba da ƙarfi"don Allah Dada ki sanya baki a hana shi". "Nima zan so hakan ya faru. Amma sai na fahimci kamar ba zai sama kwanciya ba matuƙar yana nan ɗin, gwara kawai a bar shi ya tafi mu cigaba da yi masa addu'ar. Allah ya yaye masa duk wani damuwar da yake damun sa". Na kasa cewa komai illa tagumin da na zabga ta janye hannuna ta riƙe"ki kwantar da hankalinki ki yi masa addu'a kawai, Allah ya kawo masa mafita". Kaina kawai na iya ɗaga mata domin jikina gabaɗaya ya mutu murus ta kuma cewa"ki tashi ki je ɗayan gidan kafin su dawo. Abasiyya ta raka ki". Tare da Abasiyya muka fito da tunda nazo ban ji muryarta ba illa gaisuwar da ta yiwa Abdul-hameed. "Har yanzu fushi kike yi da ni Abasiyya?". "Me kika yi min da zan yi fushi dake?". Na taune leɓena"shi ne nima abinda ban sa ni ba, amma don Allah ina mai ba ki haƙuri ki yafe mini idan na yi miki wani laifin cikin rashin sani ne". Ganin ba ta da niyyar kula ni ya sanya ni cigaba da"na yi kewar ki sosai wani lokacin sai na yi tunanin ki. Ko meye kike yi oho. Don Allah ki daina fushi da ni". Na ƙarishe zancen ƙarshen cikin maraice murya, ta kallo ni dai dai sanda muka iso ƙofar gidan. "Nima nan kullum cikin kewarki nake yi 'yar uwata". Fuskarta ɗauke da annurin da ya sanya na ji zuciyata ta yi fari ƙal ban sa lokacin da na rungume ta ba akan layin ina yi zayyana mata irin kewar ta da nayi da kasancewa tare da ita. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________ Page 1️⃣9️⃣ Umma ta na zaune muka iske ta tana dama fura, na tafi da guda na cike da murnar na rungume ta. "Ash ash!. Sai kin yi miki ɓari ne?". Na sake ta ina zaunawa a kusa da ita, ji nake yi tamkar na shafe wasu shekaru masu tsawo ban sanya ta a cikin idona. Na gaishe ta a amsa mini fuskarta ɗauke da annurin da ya sanya zuciyata samun nutsuwa. "Ina Baffa da su Hamma Adnan?". "Tunda suka fita masallaci har yanzu ba su dawo ba". Na jinjina kaina ta katse miki hanzari ta hanyar faɗin "lafiya kuwa 'yar nan?". "Lafiya ƙalau, mun zo duba jikin Hamma Ahmad ne tare dashi muke zo". Na ƙare zancen ina karɓan ƙwaryan na cigaba da dama mata furan"na daɗe ban sha fura ba, gabaɗaya kwaɗayinta nake yi". Abasiyya ta yi caraf ta cafke zancen"ai kuwa sai dai ki ci kan ki. Domin wannan furar na su Baffa ne". Na galla mata harara "wannan ɗin kuma shi ya burge ni, kuma ko kin ƙi kin so sai na sha". Ina gamawa na ɗauko kofi na zuba na fara sha ina yi mata gwalo. Sai da na shanye tas na siɗe bakina, muka yi alwala muka yi sallan asr. Ina zaune akan sallaya Umma ta shigo ta zauna a bakin gadonta mai rumfa"yaya gidan na kin komai lafiya ko?". Na yi ƙasa da kaina"lafiya ƙalau babu wani matsala". "To madalla ki nutsu ki ƙara riƙe kanki ki san inda kike. Duk abinda za ki yi tarbiyan gidanku za ki nuna don haka ki san abinda kike yi, kuma ki riƙe gaskiya akan komai". "In sha Allah, mun gode Allah ya ƙara girma". "Amin". Ta amsa mini dashi tana sanya mini albarka, mun ɗan zanta kafin su Baffa suka shigo Abasiyya ta shinfiɗa musu tabarma. Ina daga ɗakin nake jiyo muryar Abdul-hameed yana gaishe da Baffa da Baba Alhaji, Umma ta sanya hijabi ta fita suka gaisa. Na miƙe na bi bayanta na zauna a kan dakalin ƙofar ɗakin ina gaishe da Baffa da Baba Alhaji. Suka haɗe baki suka amsa mini suna tambayata ko da wani matsalar na ce da su babu komai. Da zamu tafi tamkar na tsala ihu Umma sai ƙara nanata mini kalmar haƙuri take yi, da nusar da ni cewar ibadar Ubangiji nake yi don haka dole sai na yi haƙuri wajen neman aljannata. Kuɗin da Abdul-hameed ya ajiye su Baffa fir sun ƙi karɓa dole ya ɗauke abin sa, muka koma wajen Dada duk muka tarar da su Hamma Abubakar a nan. Muka gaisa sannan na kallo Hamma Ahmad da gabaɗaya ya canza ko maƙiyi ya yi ido biyu dashi dole ya tausaya masa, idan kuwa mai saurin hawayena sai ya yi masa ƙwalla. "Sannu Hamma Ahmad". Ya yi ƙaƙalo murmushin ƙarfin ya dasa a fuskarsa ya ce"sannun ki ƙanwata". "Ya jikin?". "Da sauƙi alhamdulillah ". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi saboda ganin yanayin da yake ciki na kuma faɗin"Allah ya ƙara sauƙi". Duk suka haɗe baki wajen amsawa da kalmar amin. Tabbas Hamma Ahmad bai kasance mutum mai yawan zance da shiga cikin jama'a ba amma fuskarsa baya taɓa rabuwa da annuri. Duk da yana cikin jinya wannan dabi'ar bai yasar da ita ba. Ban san lokacin da na fara hawaye ba sai da naji Dada na faɗin"kai ɗan nan kaga ɗauki matarta ku yi tafiyar ku, kafin ta fara wannan kukan natan da bata jin lallashi". Bai amsa mata ba illa murmushin da ya yi yana satar kallo na, na ƙi yarda mu haɗa ido. "Haba! Ke fa yanzu babba ce ko dai ba ki sa ni bane?. Ki daina kuka akan komai kin ji?" Hamma Adnan ya furta cike da kulawa a tattare a cikin kalamansa, kaina kawai na ɗaga masa. Dada ta kawowa Abdul-hameed dammiyar fura sai da su Hamma Abubakar suka saka baki sannan ya sha ya yi hamdala. Ya ce zai jira ni a waje na shirya na fito mu wuce magrib tana kawo kai. Suka yi sallama da Dada, su Hamma Abubakar dukkan su suka miƙe zasu raka shi. Na yi saurin faɗin"Anwar ba ri mu yi magana mana". Na tashi na yi bayan sa muka tsaya a zaure, sai da na sauƙe numfashin da nake jin tamkar wani abu aka sanya aka yi tokare mini ƙirjina kana na sama zarafin faɗin"don Allah ka sanar da ni abinda yake damun Hamma Ahmad na san kai kaɗai zaka iya yi mini wannan". Ya yi ɗan jima kafin ya ce"a asibiti an ce ciwon zuciya ne da kuma yawan tunanin da yake yi, amma tunda aka ɗaura shi akan wasu magungunan abin da sauƙi". Na dafe ƙirjina"na shiga uku ciwon zuciya?". Na ɗaga mini kansa yana ɗaurawa da"ƙwarai kuwa amma fa ki kwantar da hankalinki. Ai yanzu ma da sauƙi sosai". Na jingina bayana a jikina gini ina jin wani zogi a cikin zuciyata. Duk tausasan kalaman da ya ke yin amfani dasu wajen kwantar mini da hankali basu yi tasiri wajen tsirkar mini da sanyi a sashin ruhina ba. "Me yasa kake son yin nisa da garin nan?". Na faɗa idanuna ɗauke da kwantattun ƙwallar da suke jiran ƙiris su kwaranyo. "Saboda na sama kwanciyar hankali Aishatu". "Don Allah ka yi haƙuri ka zauna a nan na roƙe ka" ya yi mini kallon ido cikin ido kafin ya ce"me yasa zan zauna?". Na yi ƙasa da kaina da hakan ya bashi damar cigaba da faɗin"in na zauna hakan zai sanya ki cikin farin ciki?". Da hanzari na ɗaga masa kaina alamar e. Ya sa ki taƙaitaccen murmushi"to shikenan zan duba na gani". Sai a lokacin hawayen da nake matsewa suka zubo na ce"na gode sosai bari mu yi sallama da Dada". Na koma cikin gidan muka yi sallama da Dada da kuma Abasiyya da nake jin kamar kar mu rabu da ita. Ina ta tambayar ta yaushe zata kawo mun ziyara ta ce dani kwana kusa. Kafin mu tafi sai da Hamma Ahmad ya ja ni gefe yana tambaya ta ko ina da wani matsala na shaida masa babu komai. Haka muka tafi raina cike da kewar 'yan uwana. Muna isa gida ko ciki bai shiga ba ya fita masallaci saboda ƙiran sallan magrib ɗin da aka fara yi. Tsam na tsaya babu shiri na saki jakar hannuna ƙasa ina ware idona akan Al'amin da ya yi ɗaɗɗaya da kayan wadrobe ɗin yana yi mini bincike........ "Time up Barrister lokacin ka ya cika". Furucin da jami'in ɗan sanda da yake zaune cikin ɗakin ya yi kenan, da tilasta mini dakatawa dole. Na zame daga kan kujerar da nake zaune ina sakin wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro saboda tuno rayuwata ta baya da nayi. Kafin na yi arangama da wannan mummunar ƙaddarar da ta datse mini duk wasu igiyoyin sadar da farin ciki a cikin rayuwata. Ta ɗaiɗaita jin daɗina tare da yin fatali da kwanciyar hankalina da nutsuwata. "Ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, sai mun haɗu a kotu a zama na gaba". Ƙirjina yana harbawa da matuƙar ƙarfi, tamkar mai lalurar numfashi haka numfashina yake ja. Muryata ta dushashe na kasa cigaba da yin hawayen. A hakan idona ya fice na kasa cewa komai aka mayar da ni cikin ɗakin da aka ɗauko ni. Na yi imanin cewar izuwa yanzu kam ruwan hawayena sun ƙare domin sam na gaza yin kuka da hawaye. Addu'a kawai nake yi Allahu ya ɗauki rayuwata ko zan sama salama don a wannan yanayin mutuwar ce kaɗai hutu a gare ni. 'Ya'yana su kaɗai nake da tsananin buƙatar gani da kuma sanin halin da suke ciki, ko yanzu suna ina oho. Haka na wuni na kwana cikin wannan halin bana iya cin komai balle wani abu ya iya wucewa ta maƙoshina. Ko rufe idona na yi hotun Abdul-hameed ɗauke da ƙayataccen murmushi a fuskarsa kawai nake gani . Idona biyu nake kwana yanda naga rana haka nan nake ganin dare bana runtsawa. Bana bambamce wuni da dare domin ba na fita ko ina, na yi imanin cewa da mutane sun irin yawan son da nake yiwa mijina da ba zasu zarge ni da zan iya cutar dashi ba balle raba gangar jikinsa da numfashinsa. Ban san adadin kwanakin da na ɗauka a haka ba, sai da aka zo aka fitar da ni ɗakin da ake ganawa da mutane. Dishi dishi idanuna suke iya gano mini Hamma Ahmad da yake zaune, ba kasa zama akan kujerar na durƙushe akan gwiwata. "Aishatu". Ya ƙira sunana cikin muryar dake bayyanar da tsantsar tashin hankalin da yake ciki. "Kar ki yi kuka addu'a za ki yi". Na ɗago rinannun idanuna na zube su akan fuskarsa"Ina Umma? Ina su Ashraf?". "Duk suna nan lafiya ki kwantar da hankalinki. Muna zo sau huɗu tare da Baba ana hana mu ganin ki, sai yau aka bani mintuna ashirin na gana dake kafin gobe a koma kotu. Don Allah na roƙe ki ƙanwata ki faɗi dukkan gaskiyar ki akan lamarin nan kar ki ɓoye komai, Barrister Aliyu ya tabbatar mana da cewar zai taimaka miki". Na ji wani ɗaci ya gauraye mini dukkan kusurwan bakina"Hamma bana buƙatar wani taimakon da ya wuce addu'ar ku a halin yanzu. Gwara nima a kashe ni na huta domin na tabbatar ko an bar ni ba zan yi tsawon rai ba zan mutu". "Kar ki ce haka in sha Allah Indai da gaskiyar ki babu abinda zai sa a kashe ki". Sai a lokacin na sama damar sakin wani gigitaccen kuka mai sauti bil haƙƙin nake kukan, ina nadamar kasancewata a cikin wannan duniyar haka ina ji ina gani aka fitar da ni daga ɗakin. Haka na kwana idona biyu washe gari aka zo aka sanya mini ankwa aka fitar da ni, babu masaka tsinke a harabar kotun ko ina ka wulga mutane ne cike maƙil. Aka fito da ni daga motar kafin na ankara na ji ruwan duwatsu a jikina, jami'an tsaron suka kewaye ni tare da umartan mutanen su ja baya. Da ƙyar nake ɗaga ƙafata da nake jin cewar tamkar baya jikin gangar jikina. Na ƙarisa inda aka nuna mini domin tsayiwa. Na hangi Anty Adama da Al'amin a cikin 'yan zaman kuton suna gefen 'yan uwana da kallon banza, ina jin kaina yana juyawa na ɗauke idona daga kan su. Magatakardar kotun ya gabatar da shari'ar da za a saurara sannan ya miƙawa Alkalin takardan. "Lauyan wacce ake zargi ya gabatar da kansa". "Sunana Aliyu Sanusi lauyan wacce ake zargi. Na gode ya mai girma mai shari'a". Ya yi wasu rubuce rubuce sannan ya ce"lauyan gwamnati ko kana hujjan da zaka gabatarwa kuto?". Da karsashi ya miƙe"ƙwarai kuwa ya mai girma mai shari'a, zan so inspectorn da aka sanar da su kisan da Aisha ta yi ya bayyana a gaban kuto". Wannan jami'in ɗan sandan ya taso ya fito gaban kuto, sai da Barrister Adam ya tako ya matso gabansa kafin ya ce"zan zo ka sanarwa kuto yanda kuka tarar da faruwar lamarin bayan da aka ƙira ku". "Misalin ƙarfe ukun yamma aka ƙira mu aka sanar damu cewar an yi ƙisan kai a wannan unguwar, muka je tare da sauran ma'aikatan mu muka tarar da mamacin kwance cikin jini da kuma wannan baiwar Allahn a gefe cikin yanayi da ɗimuwa, mun miƙa gawar sashin bincike yayin da ita kuma kuma ajiye ta a wajen mu kafin muka miƙa ta kuto". Kuton ya ɗauki hayaniya mai shari'ar da ya dakatar da suturun tare da umartan Barrister Adam ya cigaba da tambayoyinsa. "Za ka iya komawa ka zauna mun gode, yanzu kuma zan so likitan da ya yi bincike akan gawar marigayi Abdul-hameed ya bayyana a gaban kuto". Wani farin mutum mai diri ya fito gaban kuton, Barrister Adam ya soma faɗin" a irin ƙwarewar aikin ku na likitoci, meye bincikenku ya nuna muku shi ya yi musabbabin rasuwar marigayi Abdul-hameed?". "A binciken da muka gudanar ya nuna mana cewar caka masa wani ƙarfe mai kafi aka yi dangin su wuƙa da dai sauran su. An caka masa a ƙahon zuciyarsa har sau biyu, sannan a jikin wuƙar da aka yi kisan da ita tambarin hannun wajen ake zargi muka sama". Kan ka ce kwabo kotun ya rikice da suturu, kaina ya soma juyawa ina ganin abubuwa yana rabuwa bibiyu a idanuna. Bisa furucin da wani dattijo ya guntso ya furzar, tsabar takaicin dake karzan ransa har ƙwalla ya yi. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Me yasa masifa da bala'i ba zasu addabe mu ba?. Mata babu tausayi a cikin zukatansu ko na misƙala zarratin, ki ɗauki wuƙa ki daɓawa mijinki don tsabar zalunci. Allah wadaran ki da haihuwar irin ki gwada mutum ya ƙare rayuwar sa babu 'ya'ya babu jika". ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________ Page 2️⃣0️⃣ Ɗif ji da ganina suka ɗauke na wucen gadi. Na dafe katagon da ya kewaye inda nake tsaye. Saboda jirin da yake neman kwaɗa ni da ƙasa. Ina kokuwa da numfashina da yake maƙalewa a ƙirjina da yake yi mini matuƙar zafi da zogi. "Barrister ci gaba da tambayoyinka". Alkalin ya furta bayan da dakatar da surutun da ya ɓarke ta hanyar buga ƙaramar gudumar dake hannunsa. "Da waɗannan hujjojin na sakamakon binciken ƙwararrun likitoci da ya nuna tambarin hannun Aisha ɓaro ɓaro a jikin wuƙar da aka yi kisan Abdul-hameed dashi. Nake roƙon wannan kotu mai alfarma da ta gaggauta yanke mata hukunci domin ya zama izni ga raguwar mata masu irin halinta". Zance Barrister Adam kenan cike da ƙwarin gwiwa, kafin ya gabatar da godiya ya koma ya zauna. Sai da Alkalin ya ba wa Barrister Aliyu damar yin tambayoyi ga likitan da jami'in ɗan sandan idan yana dashi sannan ya tashi yana gyara rigar aikin sa dake jikinsa. Jami'in ɗan sandan ne ya fara fitowa domin shi ya buƙaci fara gani. "Zan so ka sanarwa kotu yanayin da kuka iske Aisha a lokacin da kuka isa gidan?". "Mun same ta cikin yanayi na riɗimuwa da karaɗuwa, domin har kwanciya a gadon asibiti ta yi kafin a kawo ta nan". "Da wannan kalmar na riɗimuwa da kaɗuwa nake son na yi amfani na fahimtar da kotu cewar tabbas akwai wani ƁOYAYYIYAR MANUFA a cikin wannan lamarin. Duk wanda yake da ƙwarin gwiwar iya ɗaukar wuƙa ya daɓawa mutum a ƙahon zuciyarsa har sau biyu, bana tunanin bayan ya aikata hakan za a tsinci shi cikin irin wannan yanayin har da zai haifar masa jinyar da za ta kwantar dashi a gadon asibiti, ina roƙon wannan kotu mai alfarma da ta ƙara mana lokacin wajen samo tarin hujjojin da zan gabatar a gaban ta". Shuru ya karaɗe ilahin wajen tamkar babu wani halitta mai numfashi a cikinsa, har izuwa lokacin da Alkalin ya soma faɗin"bisa rashin hujja daga ɓangaren lauya mai kare wacce ake zargi, zamu ɗaga wanna shari'ar zuwa ranar uku ga watan mayun wannan shekarar da muke ciki. Za a cigaba da tsare ta a gidan ajiye ɗaurarru har ranar da za a dawo kotu". Kowa ya miƙe tsaye akan ƙafafunsa har sai da ya fita sannan aka fara ficewa. Kowa yana tufa albarkacin bakinsa game da lamarin, 'yan jaridu suka yi miki rubgudu da ƙyar aka sama hanyar da aka sanya ni cikin motar aka komar da ni inda aka ɗauko ni. Na shiga cikin matsanancin tashin hankali fiye da wanda nake cikinsa a yanzu, furucin Barrister Adam yana yi mini yawo a cikin kwanyata. Shin da gaske ne kenan na kashe mijina na kasha Abdul-hameed?. Da hannuna na daɓa masa wuƙar da ta yi sanadin rayuwarsa?. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u". Shi kaɗai kawai na iya furtawa ina dafe kaina da yake juya mini. Kwance take jikinta ya ɗaukoi zafi tamkar garwashi, Dada da Adda Azima zaune kusa da ita. "Sun dawo daga kotun ne?". Ta tambaya cikin muryarta da ba ta fita sosai. "Ki yi haƙuri ba su dawo ba ki kwantar da hankalinki". A bayyane ta sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya"ina son naje na gan ta. Wallahi a yanzu babu abinda idanuna suka fi buƙata gani kamar Aishatu". Cike da kulawa gami da tausayawa Dada ta riƙo hannunsa tare da taimaka mata ta tashi ta zauna ta jingina kanta jikin matashin da ta sanya mata a bayan ta. "Tabbas na san kin yi haƙuri amma ki ƙara haƙuri, addu'ar ki ta fi buƙata yanzu fiye da komai kuma ko a ina kika yi mata sai Allah ya kawo mata mafita. Domin alƙawarin Allah ne addu'ar uwa baya taɓa faɗuwa ƙasa banza". Lumshe idanunta ta yi tana cije leɓanta"ina ji a jikina zamana da Baffan yaran nan ya zo ƙarshe. Tunda ranar da aka kawo ni cikin gidansa da jajayen sawu nake bin umarnin sa, ban taɓa ƙerata kara idan ya ajiye ba, ban taɓa yin musu da shi ba balle aikata abinda zai kai mu ga yin rigima. Tabbas zaman tare dole za a saɓa domin ko harshe da haƙori suna saɓawa amma Allah ne shaida na kiyaye dukkan wani abun da baya so tare da ɗabbaka abunda yake so ko da kuwa ni ɗin zan cuto. Amma akan 'yata ya kasa yi min uzuri ya ƙasa fahimtar raunin dake cikin ƙirjina ya jefa ni a tsaka mai wuya ta hanyar ba ni tsauraran zaɓi". Ta ƙare zancen hawaye suna rige-rigen zubowa daga idonta. Adda Azima da ta kasa cewa komai ganin Umma na kuka gabaɗaya sai ta kashe mata jiki. Ta miƙe ta fice daga ɗakin tare yarce hawayen da suka zubo mata. Cikin tausasan kalamai Dada ta soma faɗin"tabbas duk inda ake nemar jajirtacciyar mace wajen farantawa mijinta da nisantan abinda baya so kin kai a buga misali dake cike da alfahari. Tun da ya furta miki cewar idan kika je wajen ta a bakin auren ki ba tare da ya ji nauyi ko duba 'ya'yan dake tsakaninku ba . To babu makawa zai iya aiwatar da abinda ya furta, tunda Babansu ya yi masa magana ya ƙi sauraron sa a wannan karon ya kai maƙurar hawa dokin zuciya, ki yi haƙuri ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki yana sane da ke bai manta dake ba, ita kuma Allah ya kawo mata ɗauki ". Sallamar su Hamma Ahmad ya katse Umma daga maganar da ta yunƙuro da nufin furtawa, sai suka zauna sannan ɗaya bayan ɗaya suka yi mata sannu. Bata amsa musu ba ta fara faɗin" kun dawo daga kotun? Ina ita Aishan an sake ta ne?". "Ki kwantar da hankalinki Umma, ai yanzu aka fara shari'ar sannu a hankali ake bin komai". Hamma Abubakar ya furta cikin kwantar da murya da zummar kwantar mata da hankali , saboda yanayin jinyar da take ciki da tun faɗuwar da ta yi a ofishin 'yan sanda ta suma ta ba ƙara yin lafiya ba har yanzu. "Ku sanar da ni gaskiya ko da kuwa munin zancen zai yi silar da za a kai ni kushewa, sai na fi samun nutsuwa fiye da ku ce za ku ɓoye min". Duk shuru suka yi domin gabaɗaya sun rasa ta inda zasu fara zayyana mata lamarin. Hamma Ahmad ne ya yi ƙarfin halin faɗin"tabbas Aishatu tana buƙatar addu'ar kowa a cikin mu, zaman da aka yi yau ya nuna babu alamun nasara daga ɓangaren mu. Amma Allah baya bacci matuƙar tana da gaskiya ba zai taɓa bari ta tozarta ba. Domin ko da da sakan ɗaya zucuyata bata taɓa aminta cewar za ta iya kashe mutum ba balle Abdul-hameed, mutumin da ta nunawa tsantsar so ". A wannan karan Dada ce ta furta"innalillahi wa inna ilaihir raji'u!. Allah ya dube yarinyar nan da idon rahama, ya bayyana duk abinda yake ɓoye". Suka haɗe baki wajen faɗin"Amin". Kafin Hamma Adnan ya ce"mun yi magana game da yiyuwar su bamu yaran su zauna a wajen mu kafin muga abinda Allah zai yi, amma mahaifiyarsa ta hana a cewar ta jikokinta ba za su taso su sama irin tarbiyyar da uwarsu take dashi ba. Ba Baffa kaɗai ba hatta Baba Alhaji ya fusata su ce kar ɗaya daga cikin mu ya ƙara tunkarar su game da yaran mu bar su dasu tunda su ma jikokinsu ne". "Ashsha! Ai in hankali ya gushe hankali ake sanyawa a nemo shi. Ban da abin su ai hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar". Cike da takaici Dada ta yi zancen tana jijjiga kanta. Anwar da tun da suka shigo bayan sannun da ya yiwa Umma bai ce ko kanzil ba. Ya tashi da nufin barin cikin ɗakin ɗaga ƙafan da zai yi bai sauƙe ba ya yanke jiki ya faɗi a wajen sumamme. A rikice duk suka yi kansa suna ƙiran sunan shi tare da jijjiga shi. Hamma Abubakar ya shafa masa ruwar da Adda Azima ta miƙo a fuskarsa sannan ya saki gigitacciyar ajiyar zuciya mai matuƙar ƙarfi yana ƙare musu kallo. Sannu duk suka shiga jeranta masa wani na bin wani, kafin suka fara tambayar me ke damun sa. Dagewa ya yi akan babu komai lamarin da ya fusata Dada ta zabga masa mari cike da ƙonar zuciya"ka cigaba da riƙe damuwarka a cikin ranka Anwar. Tunda mu ba mu kai ka sanar da mu abinda yake damun ka ba. Idan kana tunanin ba za mu iya magance maka ita bane ai addu'a ya kore komai, ko shi kaɗai muka duƙufa da yi maka zaka sama sassauci". Tana dasa aya ta fice daga cikin ɗakin cikin matuƙar ɓacin rai, Adda Azima ta rufa mata baya tana bata haƙuri. Da kallo Hamma Ahmad ya bi Anwar da ya miƙe ya fice daga ɗakin bayan ya gama sauraron nasihar da Umma ta yi masa. Tun faruwar lamarin Adda Azima da Adda Abida a nan gidan suke wuni sai dare su koma tare da mazajen su, Abasiyya kuwa ta na can garin su Baffanmu inda take aure. Babu wani dogon maganar da yake shiga tsakanin Baffa da Umma daga gaisuwa sai bin juna da ido. Tsaye Hamma Ahmad yake a ƙofar ɗakin zauren da Anwar yake ciki ya kafa kan shi da gwiwa tare da lulawa cikin duniyar tunanin da ya yi nisan kiwo a cikinsa. Har ya ƙarisa cikin ɗakin bai san da wanzuwar sa a wajen ba, sai da kai hannunsa ya taɓo kafaɗarsa sannan ya dawo cikin hayyacinsa. "Hamma yaushe ka shigo?". "Na daɗe ina tsaye. Yau ina son ka sanar da ni damuwar da ka ɗauki tsawon shekaru kana ɓoyewa a cikin ranka Anwar". Gyara zamansa ya yi yana naɗe ƙafafunsa wajen guda kana ya ce"babu abinda ya ke dam...". Tun kafin ya dire zancen ya dakatar dashi "ko yaushe haka kake faɗa, amma ni na san cewa akwai komai. Akwai abinda yake damun ka Anwar. Kar ka ɓoye min domin na san komai". ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________ Page 2️⃣1️⃣ Fuskarsa ɗauke da maɗaukakiyar mamaki Anwar ya waro idanunsa ya ce"me ka sa ni Hamma?". Taƙaitaccen murmushi ya saka"na daɗe da fahimtar cewar son Aishatu kake yi na jima da gano hakan. Shaƙuwar da ke tsakanin ku da kowa yake ɗauka a haka a ɓangarenka rikiɗewa ya yi ya koma soyayyar da take wahalar da zuciyarka, tun kuna ƙanana kake bata kulawa kana iya yin faɗa da kowa a kanta. Hasalima ko Umma ce ta yi mata faɗa sai an ga canji akan fuskarka. Ban tabbatar da cewa kana son ta ba sai bayan auren ta da Abdul-hameed, duk ranar da ka gan su tare sun zo gidan nan sai ka kwana da jinya. Ka kasa haƙurin rashin ta zuciyarka ta gaza karɓa ƙaddara Anwar, shiyasa a wancan lokacin ka nema amincewar iyayenmu da su baka dama ka yi nisa da garin nan". Kansa ya jijjiga yana faɗin"Allah ya tsari zuciyata da son macen da kake so Hamma. Wallahi na gwammace son ta ya yi ajalina akan na yi tarayya da kai a wannan fagen. Ban taɓa tunanin haka za ta kasance ba, nasha tashi cikin dare na yi kuka a mahaliccina don samun mafitar damuwar da nake ciki. Zan iya sadaukar da komai a gare ka". Dafa kafaɗarsa Hamma Ahmad ya yi yana kallon fuskarsa yake faɗin"ni ya dace na yi maka wannan sadaukarwa. Ni ya kamata na yi fatali da farin cikina domin ɗaurewar tsawon ran naka, na so a ce zan iya maida hannun agogo baya, na so ace zan iya goge duk abubuwan da suka wakana na yi amfani da tsaftaccen alƙalami wajen rubuta wani. Da sai na tabbatar da cewar ka mallaki Aishatu a matsayi mata". Dafe kansa da jijiyoyin kan suka fito suka yi ɗara-ɗara Anwar ya yi yana faɗin"wani irin jarabawa ce wannan Allah yake jarabce mu da ita?". Ba zan taɓa iya aurar macen da kake so har cikin zuciyarka ba , ba zan iya yi maka wannan butulcin ba. Kowa kai ya sa ni kan sonta don haka kai ne kafi cancanta ka mallake ta fiye da kowa, Hamma Ahmad ka yafe min na kasa samun ikon sarrafa zuciyata ne. Kar iyayenmu su ji wannan zancen". Jawo shi jikinsa ya yi tare da kwantar da kansa akan cinyarsa yana shafa sumarsa. Tsawon wasu mintoti cikin su babu wanda ya yi magana. Sai can Hamma Ahmad ya yi ƙarfin halin faɗin"ba ka yi min laifi ba domin kai ma ba yi kanka bane kuma babu wanda zai ji wannan maganar. Na yi maka alƙawarin matuƙar Allah ya yi ikonsa ya kuɓutar da Aishatu da wannan sarƙarƙiyar zan ba ka duk wani guduwama wajen ganin ka mallake ta". Da saurin Anwar ya ɗago idanunsa da suka sauya kala ya zube su akan fuskar Hamma Ahmad da shi ɗin ma shi yake kallo. Ya ɗaga masa kansa alamar son tabbatar masa da sahihacin zancen da ya yi har cikin zuciyarsa hakan take. Bai bashi damar cewa komai ba ya miƙe ya fice daga ɗakin, ya bar shi cike da zallar ruwan mamakin da ya shayar dashi. Da ƙarfi ya kaiwa iska naushi yana buga kansa a ƙasa"hande min boni na shiga uku. Me yasa na kasa riƙe kaina? Me yasa zuciyata ta kasa daure rashin ki Aishatu?. Tabbas na ji tsananin kunya, kuma zuciyata ba ki yi min adalci ba, ta rasa wacce za ki faɗa soyayyar ta sai wanda ɗan uwana yake tsananin so kaico na". Haka ya ƙarar da wuni cikin wani halin da shi ma kansa ba zai iya faɗin abinda ke damunsa cikin kalma ɗaya ba. Na ƙara shiga cikin tashin hankali, na fita daga hayyacina ina da yaƙinin ko maƙiyana ya gan ni sai ya zubar mini da ƙwalla. Sau ɗaya Barrister Aliyu yazo domin ganawa da ni, na kasa cewa dashi komai dole ya haƙura ya tafi. Ranar da aka mayar da ni kotu kamar yanda na yi hashashe harabar kotun a cike ya ki maƙil da dandazon jama'a. Da ƙyar aka sama hanyar da aka shigar dani izuwa cikin kotun. Anty Adama, Anty Alawiyya da Al'amin su na fara hanga, gabana ya yi wani mummunar faɗuwar da ya tursasa mini runtse idanuna da ƙarfi. Alkalin ya buƙaci Barrister Aliyu da ya fara gabatar da hujjan da ya buƙaci kotun ta bashi lokaci domin haɗo su. Ya miƙe ya gabatar da godiya sannan ya ɗaura da"zan so Amira 'yar aikin gidan marigayi Abdul-hameed ta bayyana a gaban kotu". Sai a lokacin na buɗe idona ina bin Amira 'yar aikin da Abdul-hameed ya kawo mini da kallo yayin da take fitowa ta tsaya a gaban kotun, Barrister Aliyu yana isa gaban ta sai da ya gyara tsayiwarsa ya ce"kotu za ta so ta ji alaƙar ki da marigayi da kuma wacce ake zargin ita ta kashe shi". "Ni ma'aikaciya ce a gidan marigayi, ina taya matarsa aikace-aikacen cikin gida". "Kwana kike yi a gidan ko kuma zuwa kike idan kika gama aikinki ki tafi?". Ta ɗaga kanta tana kallon shi"farkon zuwa na ba na kwana sai da ta sama ciki ne na dawo gidan da kwana". "Ko za ki iya bayyanawa kotu yanda zamantakewar aurensu yake?". Sai da ta ja numfashi mai dogon zango kana ta furta"ban taɓa ganin macen da take tsantsar son mijinta kamar yanda Antyna take son yallaɓai ba. Ban taɓa ganin su na musu ba balle tashin hankali, idan ya furta baya son abu kuwa to ta bar aikata wannan abun har abada. Duk wani abunda zai sanya shi cikin farin ciki tana ƙoƙarin aikata shi, ba ta barin sa cikin damuwa domin idan yana cikin wani hali har tana fin sa shiga damuwa. Na sha ji da kunnena yana faɗin cewar shi kam ya yi dacen mata a gidan duniya da yake fatan su rayu tare har a gidan aljanna, rayuwar auren su abun sha'awa ce kuma abun kwaikwayo da raguwar ma'aurata". Daga haka ta tsagaita tana yarce hawayen da suka kwaranyo daga idanunta. Barrister Aliyu ya soma faɗin"ya mai girma mai shari'a tabbas akwai lauje cikin naɗi a labarin da Malama Amira ta zayyana a gaban kotu. Babu wani abun da ya taɓa haɗa su, ba a taɓa jin kansu ba balle ayi musu sulhu tun da suka yi aure, zai yi wuya haka siddan ta ɗauki wuƙa ta ɗaba masa ba tare da wata ƁOYAYYAR MANUFA ba". Ya ƙare zancen yana komawa mazauninsa. Shuru ya karaɗe kotun, Alkalin ya furta"ko lauyan gwamnati yana da tambayar da zai yiwa malama Amira?". "Ƙwarai kuwa ya mai girma mai shari'a". Barrister Adam ya furta yana miƙewa da takun alfarma ya isa gaban ta Kana ya soma faɗin"ko za ki bayyanawa kotu ranar da lamarin ya faru kina ina?". "Ranar yallaɓai ya tashi da azumin nafilan da suke yi tare da Anty a duk ranakun litinin da alhamis, ranar bai fita ko ina ba saboda Anty ta tashi bata jin daɗi a gida ya wuni. Ta gama shayar da 'ya'yanta ta bar ni tare da su a ɗaki zan shirya su ta fita wajensa. Bayan wani lokaci na fara jiyo ihun sa". Ya yi saurin faɗin"me yake cewa a cikin ihun?". "Faɗi yake yi me na yi miki za ki kashe ni Aisha, na kasa fita domin da farko na zargi kunnena da tashin tace sautin da ya jiyo min. Sai da na jiyo kukan mahaifiyarsa da 'yan uwansa na fito na tarar dashi kwance cikin jini baya motsi. Ban don ina cikin gidan abun ya afku ba, ko mahaifiyata ce ta ce da ni Anty za ta iya ɗaukar makami ta yanki jikin yallaɓai ba zan yarda ba balle har ta daɓa masa wuƙa". Ta ƙarƙare zancen wasu hawayen suna biyo kuncinta, sallamar ta ya yi ta koma ta zauna kana ya fara cewa"ta tafi wajen sa kuma bayan wani lokaci aka ji ihunsa yana ambata sunanta akan kar ta kashe shi, tabbas Aisha ita ce babbar abar zargi a cikin wannan lamarin. Duk tarin soyayyar da ta nuna masa bashi yake nuna cewar ba zata iya aikata laifin da ake zargin ta da shi ba, zai iya yiyuwa a lokacin da ta je wajensa ta ji yana waya da wata zuciya ta ɗebe ta. Ta aikata wanan aika-aikan". Da saurin Barrister Aliyu ya miƙe"objective my lord! Lauyan gwamnati yana amfani da tsauraran kalamai wajen son jingina dukkan laifin ga Aisha, bayan har yanzu zargi kawai ake yi ba a tabbatar ba". "Ka kiyaye Barrister Adam". "In sha Allah, zan zo kotu ta bani damar yiwa A'isha wasu tambayoyi". "An baka". Ya iso gabana ya tsaya tare da furta kalmar sunana , ban amsa ba illa ɗago idona da nayi na sauƙe akan fuskarsa da shi ɗin ma ni yake kallo. "Wani irin zamantakewa ku ka yi da marigayi?". Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya, idanuna yana hasko mini dukkan abubuwan da suka gabata ɗaya bayan ɗaya. Take na fara jin tamkar yanzu abubuwan suke faruwa. ******* Turus na yi ina sakin jakar hannuna ta faɗi izuwa ƙasa, yayin da muka haɗa ido da Al'amin da ya gama birkita gabaɗaya ɗakin. "Lafiya? Wani abun kake nema?". Na furta cikin rawar jikina da na murya. Ya yi mini wani kallon da ya tsananta rawar da gabaɗaya jikina yake yi. Ya buda tsaki yana nufo inda nake tsaye"ke har kin isa ki titsiye ni da tambayar me nake nema don na shigo sashin ɗan uwana. Bana son shishshigi a lamura na don haka ki kiyaye kuma bakinki ƙanin ƙafarki kin ji ni?". Da hanzari na gyaɗa masa kaina alamar na ji tsabar tsoritan da na yi na kasa buɗe idona na kalle shi har ya fice daga ɗakin. Na fi mintuna uku tsaye ban motsa ba kafin na yi nasarar furzar da iska daga bakina. A hankali na tako cikin ɗakin na zauna a bakin gado ina kallon yanda ya yi kaca kaca da ɗakin. Na jewa kaina tambayar da na gaza cimma amshoshin su. Shin me ya kawo shi har cikin ɗakin baccina? Me yake nema haka? Me yasa ya gargaɗe ni da cewar bakina ƙanin ƙafata?. Sai da na ji masallacin dake kusa sun iddar da sallan magrib sannan na zabura na tashi, na shiga banɗaki na yi alwala na zo na gabatar da sallan. Ban yi dogon addu'a ba na shafa na ɗaura hijabina a ƙuguna na fara tattare ɗakin. Sai da na mayar da komai mazauninsa na zauna ina mayar da numfashi lokacin har an shiga sallan isha'i, na tabbatar ana iddarwa Abdul-hameed zai dawo don haka ina yi sallan isha'i na shiga wanka. Doguwar rigar material na saka na yafa mayafi na fita sashin Amma, domin ta sanya dokar zama a sashinta a irin wannan lokacin kullum. Har ya riga ni shigowa na iske su suna tattauna game da maganar komawar Anty Alawiyya ɗakin ta, ina sako ƙafata Amma ta canza zancen izuwa wani daban. Da dama da na koma sai sun gama sannan na shigo amma babu dama domin sun riga da sun ganni. Na tabbatar ganin nawan ne ya sanya ta sauya zancen domin har yanzu basu ɗauke ni ɗaya daga cikin ahalin su ba. Na yi saurin yin ƙasa da ido ganin Al'amin zaune a cikin falon, na zauna ina yi musu sannu da hutawa suka amsa mini fuskar su babu yabo babu fallasa. "Sai yanzu kika sama shigowa?". Amma ta jefa mini tambayar kai tsaye, na rusunar da kaina"na yi wasu gyare-gyare ne shi ya riƙe har ban farga da lokaci ba saboda gajiya". "Hala da kuka fita da motar a hanya kuka ajiye ta, kuka ƙarisa a ƙafa ko?". Anty Alawiyya ta gwatsalo mini zancen. Na jijjiga kaina"a'a ba haka nak...". Amma ta katse ni"yaya kuka baro mutanen gidan nakun?". Na ji daɗi a cikin raina domin ko ba komai yau ɗaya ta tambayi lafiyar wani nawa. "Suna nan lafiya sun ce a gaishe ku". Ta jinjina kanta tana gyara kishingiɗewa da ta yi ta ce"in ce dai ba haka kuke je musu hannu rabbana ba?". Wani irin na ji tambayar na yi zargin so take yi ta bugi cikina da kuma auna mizanin tunanina don haka na furta"mun je musu da daidai abunda ƙarfinsa ya kai". Ta yi mini shuru tamkar ba ta ji abinda na furta ba. Sai can ta ce"madalla". Ina ɗago idona muka haɗa ido da Al'amin ya yi mini wani kallon da na gaza gano ma'anar sa, zuciyata ta buga da ƙarfi me bawan Allahn nan yake nufi da ni ne?. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 2️⃣2️⃣ Kwana biyu a tsakani ina juyayin lamarin na Al'amin duk da dama can babu maganar da take haɗa mu. Amma yanzu ko a bisa kuskure muka haɗa ido dashi sai kallon banza sai harara. Kaina ya ɗaure da kaina na ƙara birkita kayan ɗakina kaf da nufin gano abinda Al'amin yake nema amma ban gan komai ba. Na kasa yin maganar da Abdul-hameed domin ban san ta inda za fara ba. Da sallama na shigo falon ina dire kofin ruwan da na kawo masa a gaban sa, na yi masa sannu ya amsa mini fuskarsa tamkar gonar auduga. Cike da sha'awa nake kallon zanen foundation ɗin gidan da yake zanawa. "Gaskiya kuna ƙoƙari sosai". Na faɗa ina ƙara kallon zanen, ya murmusa kana ya ce"bashi da wani wahala ai". "Haka dai ka ke gani don ka iya". Ya miƙa mini alƙalamin"karɓi ki yi kema za ki tabbatar da rashin wuyarsa da nake faɗa". Na waro idanuna waje"tab ai sai dai na ɓata maka". Ya saki dariya mai sauti yana ɗaukar kofin ruwan da na ajiye masa ya kafa a bakinsa. Sai ya shanye tas ya ajiye ya turo mini zanen gabana yana faɗin"kin ga wannan structure ɗin gida ne mai hawa biyu ako wani hawa akwai ɗakuna huɗu, falo ɗaya, banɗaki biyu da kitchen sai kuma filin tsakar gidan. Yanzu idan na kai wannan zanen ma'aikata zasu duba shi kafin a miƙawa magina su kuma samar dashi kamar yanda na nuna miki". Na jinjina kaina cike da gamsuwa da maganar nasan na ce"wani aikin sai mai shi, ban taɓa tunanin idan za a yi gini sai an zana shi a fefa ba kafin a tsara shi". "E to kin san kullum ƙara samun cigaba ake yi technology yana shigowa. Shiyasa yanzu idan kin lura akwai bambamcin tazara mai yawa tsakanin gine-ginen da da kuma yanzu". Ya ƙare zancen yana jawo ni jikinsa na tuno baki gaba zan yi magana ya ɗaura mini yatsarsa akan leɓena yana faɗin"shit". Dole na yi shuru domin na lura a duniya kaf babu abinda ya fi tsana kamar gardama tunda na fahimci hakan na yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa yin musu dashi ba. Yawon da yake yi da hannunsa akan fuskata yana zarcewa izuwa tudun wuyata ya hana ni cewa ko kanzil. Sallamar Asabe ya sanya mu dawowa cikin hankalin mu na yi saurin janye jikina ina matsawa gefe guda, har ta riga ta shigo cikin falon kanta yana ƙasa ta gaishe shi. Bai amsa ba ya fara faɗin"lafiya za ki shigo kan mu haka? Akwai wata matsalar ne?". "Afuwan ranka ya daɗe, Uwargijiyata ce ta zo na ƙira mata Aisha" A bayyane ya tsirtar da siririyar tsaki"je ki zata biyo bayanki". Kanta har yanzu yana ƙasa ta fice. Ya juyo ya kalle ni"ki je ƙiran Amma bari nima na tashi na shiga wanka na fita wajen aiki". Kaina kawai na ɗaga masa zan miƙe ya yi saurin riƙe mini hannayen yana lumshe idanunsa ya ce"ki dawo da wuri". Na yi fari da idanuna na miƙe na fita tare da nufar sashin Amma, babu kowa a falon sai Anty Alawiyya da na iske ta na waya. Na yi mata sannu ta zare wayar daga kunnenta ta amsa mini a gajarce ce ta ce da cewa da ni na haura sama Amma na jira na a ɗakinta. Gabana ya faɗi ya yi ras tun da aka kawo ni gidan ƙafafuna basu taɓa wuce cikin wannan falon ba a sashin natan. Haka nan kawai na tsinci kaina cikin matuƙar fargaba na haura benin ɗakuna uku ne ɗaya a tsakiya biyun kuma daga gefe, na tsakiyan da yake kallona na nufi na tsaya daga ƙofar ina yin sallama. Sai da na yi baki huɗu har zan juya na koma kasa na sanar da Anty Alawiyya cewar ban gano ɗakin ba, sai na ji an amsa mini tare da bani izinin shigowa. Na turo ƙofar a hankali tana zaune a bakin tankamemen gadon da ya ji bargonan alfarma tana kallon hotuna. Na zauna akan kafet na yi ƙasa da murya na ce"sannu da hutawa". Kanta kawai ta ɗaga mini na kuma cewa"Baaba Asabe ta sanar da ni saƙon ki shiyasa na yi hanzarin zuwa". Duk da kaina yana ƙasa amma jikina ya bani cewar tabbas ni take kallo, sai da ta ja dogon lokacin kana ta ce"ina mijinki?". "Na bar shi zai shirya ya fita wajen aiki". Ta jinjina kanta tana ajiye hotun dake hannunta akan dirowar dake kusa da gadon"wani aiki zan saka ki".Na gyara zamana ina sauraronta da kyau. "Ɗauki wancan ledar garin magani ne da nake son ki zuba mishi a cikin ruwan wanka". Ƙirjina ya buga da ƙarfi tamkar zai fito waje. Na ɗago kaina ina kallon ta ita ɗin ni take kallo na ce"magani kuma? Na menene?". Kai tsaye ta furta mini"ki kwantar da hankalinki ba na cutarwa bane, ina da damar da zan iya aiwatar da hakan ba tare da sanin ki ba amma na zaɓi na sanar dake domin kema zuwa gaba za ki haifa kuwa za ki zama uwa. Za ki so 'ya'yan da za ka haifa su yi miki biyayya to wannan ƙulin maganin yana daga cikin abubuwan da zasu taimaka wajen samun cikakken biyayya daga 'ya'ya". "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Ki yi haƙuri Amma kamar asiri ne fa wannan. Abdul-hameed ya kasance mai tsananin biyayya a gare ki akan dukkan komai, wallahi ko yaushe cikin labarta mini yanda yake son faranta miki yake duk tashin daren da zai yi sai ya yi addu'ar Allah ya ba shi abinda zai kula dake. Don Allah Amma kar ki aikata haka a gare shi gwara ki yi masa addu'ar Allah ya sanya tausayinki a cikin zuciyarsa ya bashi ikon sauƙe haƙkinki dake kan sa". Tunda na fara maganar ta ɗauƙe kanta daga kaina har na kai aya bata ce da ni uffan ba. Kwantattun hawayen da suka ciko idanuna suka zubo na yi saurin kai bayan hannuna na share su. Har na cire rai da samun amsarta na ji ta furta" ban ƙira ki na sanar dake sirrina don ki karanto min wannan zantukan nakin ba, yaushe kika haɗu shi da zai nuna min cewar kin fi ni son sa?. Ni na ɗauki cikin Abdul-hameed na yi naƙudarsa na shayar dashi na yi ɗawainiyya dashi har ya kai munzalin iya bambamce tsakanin hagu da damarsa. Babu wanda zai nuna masa soyayya fiye da wanda nake yi masa". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau sai ko meye zata faɗa mini bana jin zan iya aikata abinda take so na yi. Zancenta ya katse mini hanzari"zan iya aiwatar da hakan ko da sanin ki ko akasin hakan, amma tunda kin bijire tashi ki bani waje zan nema wani hanyar". Wata zuciyar ta ya mini cewar idan ma ban amshi wannan tayin da ta yi mini ba, to tabbas zata bi ta wani hanyar kamar yanda ta faɗa don ganin ta cimma ƙudurinta. Haƙiƙi na yi imanin cewar babu wata uwar da zata so ganin ana cutar da ɗan da ya rayu a cikin cikinta ya tsaga naman jikinta ya fito balle a ce ita da kanta ta iya cutar dashi. Na sauƙe bayyanannen ajiyar zuciya kafin na zama zarafin faɗin"shikenan zan yi duk abinda kika sa ni in sha Allah". "Da kin kyautawa kanki. Yanzu ba za ki gane duk abinda zan faɗa miki ba sai lokacin da kika haifa kika ajiye 'ya'ya a gaban ki". Ban ce da ita komai ba na kai hannu na ɗauki ƙulin maganin, ta ƙara jaddada mini cewar a ruwar wanka zan zuba masa. Na fito na tsaya ina juya ƙulin maganin a hannuna zuciyata cike fal da wasi-wasi. Tuna cewar Abdul-hameed yana jira na ya sa ni ɓoye maganin a cikin aljihun doguwar rigar dake jikina na sauƙa ƙasa da sauri. Murmushin da ya bayyanar da fararen haƙwaranta Amma ta saka a bayyane ta furta"da alama wannan ba za ta yi wahalar kamuwa ba". Lokacin da na sauƙo Anty Alawiyya ta tashi daga falon. Jin na yi karo da mutum ya sa ni saurin ja da baya. "Ke ba ki da hankali ne?". Al'amin ya furta a zafafe yana watsa mini wani kallon tsana tare da karkaɗe inda na jikina ya taɓa shi. "Ka yi haƙuri ban lura bane". Na faɗa ina ficewa daga falon da sauri ina jin kalmar bagidajiyar da ya jefa mini amma ban waigo ba na nufi sashina. Sai da na fara shiga ɗakina na ɓoye ƙulin maganin a cikin kayana sannan na wuce ɗakinsa. Yana tsaye yana kallo cikin harshen turanci na iske shi, na haɗe hannayena waje guda alamar ban haƙuri sannan na nufi wajen kayansa na ciro masa komai. Daidai sanda ya gama wayar yana ajiye ta na isa gare shi ya zauna ina murza masa mai a fatarsa. Ya riƙe hannuna hakan ya sa ni ɗago idanuna na yi masa kallon ido cikin ido. "Me kuka tattauna da Amma?". Na yi ƙasa da idona ina cigaba da shafa masa man na ce"tattaunawa ce irin ta uwa 'yarta, sai kuma shawarwarin da ta ba ni da zasu amfane mu gabaɗaya wajen tafiyar da zamantakewar mu". "Allah Sarki Amma tana son duk wani abunda nake so. Shiyasa kullum nake addu'ar Allah ya bani ikon faranta mata". Jikina a sanyaye na ce"Amin". Sai da ya shirya tsaf na rako shi har jikin motarsa muka yi sallama kamar kullum na na yi masa tarin addu'o'i. Sai da na ga ficewar motarsa sannan na koma ciki kaina tsaye na wuce ɗaki. Na kasa zama sai safa da marwa nake na yi, na kai mafi na kai bango kamar yanda na gaza gano manufar Amma na son aikata hakan. Shirif na zube akan gado ina mayar da numfashi Indai ba so take yi ya fara yi mata sujjada ba dukkan wani biyayya yana yi mata, zan iya rantsuwa da ban taɓa ganin ɗan dake yi wa mahaifiyarsa irin biyayyar da Abdul-hameed yake yi wa Amma ba. A kwanakin nan hatta abinci ya koma ci tare da ita a cewar sa daman can tare suke ci, duk da tana da direbanta amma idan zata fita ko ina yaje sai ya dawo ya kai ta kuma ya jira ta kammala dukkan uzurinta kafin ya dawo da ita. Shi yake yanke mata kumba duk sati. "Rabbi inni lima anzalta alaihi min khairin faƙir". Na furta ina dafe kaina, daidai lokacin da na ji sallamar Asabe na tashi da sauri na fito. Ganin wacce take bayanta ya tursasa mini murtsike idona ina faɗin"Abasiyya". Na isa na rungume ta sai da muka zauna Asabe ta ce"daman uwargijiyata ce ta ce na yi mata jagoranci, sannan idan akwai abinda za a dafa mata sai ki sanar". "Ki dafa mata abunda da ba zai ba ki wahala ba kuma wanda ba zai ɗau lokaci ba". "An gama ranki ya daɗe". Ta furta yayin da take ɗaukar hanyar ficewa bayan mun gaisa na kawo mata ruwa ta sha. Fuskarta ɗauke da murmushi ta ce" 'yar uwa kin yi sa'ar uwar miji ke kam, duk yanda muke tsammani ba haka bane. Ban taɓa tunanin har yanzu akwai irin uwayen masu ɗaukar matar ɗansu tamkar 'ya'yan su ba". Cike da tashin fahimta na ce"kin haɗu da ita ne?". "Sosai ma kuwa da Hamma Ahmad ya ƙira mijinki ya sanar dashi zuwa na aiko har gida aka zo aka ɗauke ni. To da muka iso sashinta aka fara shiga da ni. Mun yi hira sosai da ita babu ruwan ta kamar dama can mun san juna da ita, ni kam har cikin raina sai na ji ta burge ki kuma kina ji a jikina ke za ki zama ɗaya daga cikin misalin da zai karya alƙanin da ake yiwa uwayen miji domin ke kam kin yi dace". Fuskata ɗauke da maɗaukakiyar mamaki na ce"Da Amma kuka yi dogon hira?". Ta gyaɗa mini kanta"ƙwarai kuwa". Na sauƙe numfashi ba don na yarda da maganarta ba na zako wani zance. Domin ni kam tun ranar da aka kawo ni cikin gidan ban da yau da buƙartarta kanta ya sa ta ƙira ni ba ta taɓa yi mini maganar cikakken mintin biyu ba. Mun sha hira sosai da Abasiyya har take labarta mini kowacce rana da yammaci idan Abdul-hameed ya dawo daga wajen aiki sai ya tsaya a gida ya duba jikin Hamma Ahmad. Na ji wani daɗin sanyi yana mamaye mini raina. Asabe ta shigo da soyayyiyar dankali da ƙwai ɗin da ta dafa mata, na yi mata sannu. Mun wuni tsum da ita a bakinta nake jin Adda Azima tana jiki kuma bata da lafiya na yi murna sosai. Bayan mun yi sallan Asr Asabe ta shigo ta ce yallaɓai ya ƙira waya ya ce za a mayar da Abasiyya gida ga direba yana jiran ta. Babu irin dagewan da ban yi ba amma ta ƙi karɓar kayan kwalliyan da na ɗeba mata daga cikin kayan lefena. Na rako ta sashin Amma domin ta yi mata sallama. Ta bata turamen zannuwa har biyu da mayukan shafawa a cewar ta tunda ni ban bata komai ba. Haka muka yi sallama ta tafi bayan na gama bata saƙon gaisuwar ta gaishe mini da kowa, sashina na koma na cigaba da tunani daga inda na tsaya. Sai bayan sallan isha'i Abdul-hameed ya shigo wanka kawai ya yi muka tafi sashin Amma muka ci abinci. Na lura da wani kallo na daban da take bi na dashi tun shigowar mu da na kasa gano manufarsa. Sai da ta miƙe za ta shige ɗakinta duk muka yi mata a kwana lafiya ta amsa tana ɗaurawa da"Abdul ka same ni a ɗaki ina so magana da kai". Har ta yi gaba ta juyo"kar ki jira shi a nan, ki je ki fara tanadin karɓan da za ki yi masa". A kunyace na ce"To a tashi lafiya". Ta amsa a gajarce ya miƙe ya bi bayanta, ganin daga sai Anty Alawiyya da Al'amin a falon ya ni tashi na yi musu sai da safen da basu amsa mini ba na fice izuwa sashina raina cike da fargaba. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________ Page 2️⃣3️⃣ Idanu ta zuba mishi kusan mintuna biyar ba ta ce dashi komai ba. Tayi imanin cewar ko zai kwana a zaune a wajen ba ta ce dashi komai ba, ba zai taɓa gusawa ba sai ta bashi umarnin haka nan ba zai tambaye ta dalilin ajiye shi da ta yi ba. Sai da ta gama ƙasaitarta ta furta"me ka sani game da halayyar matarka Aishatu?". "Na santa da kyawawan hali da kuma tarbiyya game da girmama duk wanda yake gaba da ita, tana da ilmin addini. Waɗanda halayyan natan su suka ja hankalina zuwa gare ta, kuma zuciyata ta kwaɗaitu da son mallakar ta a matsayin abokiyar rayuwata ta har abada". Ta sa ki taƙaitaccen murmushin gefen baki"wannan iya halayyan da ta bayyana ka gani kake faɗa, na ga alama baka da masaniya akan zahirin halayyarta na ɓoye". Da sauri ya ɗago idanunsa da ya yi ƙasa da su"ɓoyayyan hali kuma Amma? Shin wani abun aka ce miki ta aikata ko kuma kika gani da idonki?". "Ya zama dole a gare ni na zama mai sanya ido akan duk wani abunda yake kusantanka. Ka san da cewar yau matarka ta yi baƙuwa?". Kansa ya jinjina ya ce"ƙwarai kuwa da sani na ta zo, amma wannan ba baƙuwa ba ce domin 'yar uwarta ce. Ki sanar da ni inda akwai wata matsalar zuciyata bugawa take yi da ƙarfi". Dariya mai sauti ta saka tana ƙara fuskantarsa ta furta "yaro yaro ne. Abdul-hameed har yanzu kai yaro ne. To ka kasa kunne ka saurari abunda zan faɗa maka da kunnen basira, 'yar uwar matarka da tazo yau ta zo mata da wani ƙulin magani domin mallake ka. Lokacin da Asabe ta shiga domin kai mata abin taɓawa ta ji tana zayyana mata yanda zata barbaɗa maka maganin a cikin ruwan wanka, kuma ka san adadin shekarun da na ɗauka tare da Asabe tun kafin kazo duniya take yi min hidima kuma ba ta taɓa yi min ƙarya ko faɗin abin da bashi kenan ba". "Aishan?". Ya furta muryarsa yana shaƙewa waje guda. Cike da tabbaci ta ɗaga masa kanta tana daurawa da"na san dole za ka yi mamaki domin ni ma da farko zancen ya sa ni cikin kaɗuwa. Amma ka sanya mata ido sosai za ka tabbatar da gaskiyar zancena, sannan in da hali ka sanya dokar hana kowa kawo mata ziyara saboda gudun afluwar matsala a cikin auren ku. Gidanka ne matarka ce kana da damar yin komai ba tare da kowa ya ce da kai komai ba". Sai da ya share maiƙon zuffan da yake tsatstsafowa daga goshinsa kana ya sama damar raba tsakanin haƙwaransa da suke karo da juna. Kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri yake faɗin"na yarda da Aisha matuƙar yarda na aminta da ita, irin amintar da ko a cikin mafarki zuciyata ba ta taɓa kawo min tunanin za ta iya cutar da ni ba. Wallahi Amma ba don ke kika sanar da ni wannan maganar ba ko duk jikina kunnuwana babu wanda zai sanar dani hakan na yarda". Cike da jin daɗi ta ce"ai idan mutum ne ƙafafu biyu ne zai aikata fiye da haka ma. Na sanar da kai ne don ka ƙara sanya ido sosai ba wai don na lalata maka aure ba sai ka nutsu ka san abin yi". Musgutawa ya yi yana naɗe dukkan ƙafafunsa wajen guda tare da sakin sakekken ajiyar zuciya. "Na gode da kulawar ki a gare ni. In sha Allah zan sanya ido amma wallahi bana tunanin Aisha za ta iya cutar dani ko da kuwa a cikin rashin sani ne. Anya Baaba Asabe ba wani maganar daban ta ji suna yi ba?". Harara ta watsawa masa"so me sanya idanu su makance, na baka damar ka yi bincike idan ka tabbatar da saɓanin abinda na faɗa maka. Sai ka sama bakin ƙaryata Asabe. Dafe kansa da yake sarawa ya yi cikin ransa yana karanto hasbunallahu wa ni'imal wakil.Tabbas yana cikin tsaka mai wuya zuciyarsa ta kasa aminta da cewar Aishansa za ta iya cutar dashi ta wannan hanyar. Amma sai dai ya san babu wani dalilin da zai sanya Amma furta masa zancen da bai faru ba. "Me ye ribarta idan ta aikata hakan a gare ni Amma?". "Wannan kuma wani ƁOYAYYAR MANUFA ce da ta ɓoye a cikin ranta". Da ƙarfi ya cije leɓensa yana ƙoƙarin miƙewa ta yi saurin dakatar dashi tare da tsiyaya masa ruwar dake ajiye a kan dirowar gefen gadon ta miƙa masa. Tare da umartarsa da ya shanye bai yi mata musu ba ya karɓa ya kafa a bakinsa, sai da ya shanye tas ya ajiye kofin ya yi mata sai da safe sannan ya fice yana jin wani irin nauyin da ƙirjinsa ya yi masa. Tunda na baro sashi Amma na zauna na kafa tagumi ina tunanin yanda zan yi da ƙulin maganin da ta bani. Na tsayar da matsaya akan gobe da safe yana fita sallar asubahi zan fito na haƙa rami na burne shi. Don ko yanzu da yake cikin ɗakina hankalina ba a kwance yake ba, sai na fitar dashi daga cikin gidan sannan zan sama sallama kuma zuciyata za ta fi gasuwar cewar ba zai cuto ba. Wanka na yi na shirin cikin shigar bacci na zaunan jiran sa. Asabe ta kawo mini kayan haɗin shayin da yake sha a kowani dare kafin ya kwanta. Filas ɗin ruwan zafi ne sai gayen shayi da kuma taceccciyar farar zuma. Na ɗauko kofi na ƙaramin cokali na ajiye masa da duk wani abunda zai buƙata, na tisa kayan a gabana ina kallo. Ina son naga nima ina girkawa mijina abincin da zai ci ko zai sha da hannuna kamar yanda sauran mata suke hidimtawa mazajen su don samun tagomashin lada daga wajen Ubangiji. Sai dai ba ni da wannan damar domin har yanzu babu kayan abinci a sashina ruwa da lemuka ne kawai a cikin firiji. Jin motsin taɓa ƙofa ya sa ni dawowa cikin hayyacina daga tunanin da na zurma. Yanda ya shigo mini ya sanya gabana yin wani mummunar faɗuwar da zai da na dafe ƙirjina. Kamar bai gan ni ba ya ɗauki hanyar wucewa ɗakinsa, na yi saurin miƙewa ina shan gabansa. "Lafiya kuwa?". Duk da yanayin da yake ciki a hargitse sai da ya yi ƙoƙarin sakar mini da murmushi da ko haƙwaransa basu bayyana ba. Bai iya furta mini komai ya raɓa ta gefe na ya shige ɗakin tare da turo ƙofar ya rufe. "Na shiga uku!". Na furta ina ƙara dafe ƙirjina da yake yi mini gudun famfalaƙi. Tunani barkatai suka fara ziyartar kwanyata ni dai a iya sa nina na bar shi za su haura sama da Amma zasu tattaunawa kamar yanda ta ce, daga haka ban san me ya faru ba da ya jefa shi cikin wannan yanayin. Ko dai wani ne ya rasu ko kuma ɗaya daga cikin su babu lafiya?. Na yi saurin ƙaryata hashashen zuciyata, tare da zabura nima na nufi daƙin. Yana zaune akan gado ya juya bayansa tare da dafe kansa. Na tako a hankali na iso na tsuguna a gabansa a nutse na furta"Allah ya huci zuciyan sadaukin mazaje, ka sanya ni cikin tsoro ina fatan kowa lafiya daga cikin gidan?". Kansa kawai ya iya yin ƙarfin halin ɗaga mini na ƙara da cewar"ki gaggawa ka sanar da ni menene yake faruw..". Ban ƙarisa saboda rawar da jikina ya soma da ban san lokacin da na zame na zauna dirshan ba, idan na yi rantsuwa na tabbatar babu kaffara a kaina idan na ce da ya ɗako idonsa ya kalle ni ban da ɗigon baƙi ko kaɗan a cikin ƙwayar idonsa ba. "La-la-la-lafiya?". Na furta maganar a rarrabe kamar 'yar koyo. Sai da ya ja lokaci cikin wata iriyar murya ya ce"ki yi haƙuri ki bani lokaci ina son kasancewa ni kaɗai". Yanda ya yi maganar na tabbatar da cewa idan bakina ya yi kuskuren ƙara cewa wani abu babu tantanma zai iya rufe ni da mahaukacin duka. Don haka na nemawa kaina salama na tashi na fito sai dai na kasa barin ƙofar ɗakin nan na zauna na ci kuka har na godewa Allah. Wata zuciyar tana raya mini na je na sanar da Amma halin da yake ciki sai na fasa. Haka na zauna a wajen da tunanin zai neme ni komai dare har bacci ya kwashe ni. A hankali na soma buɗe idona da ya yi mini nauyin gaske ga ciwon kai da jikin da ya rufe ni, saboda ƙiran sunana da na ji an yi tare da taɓo kafaɗata. "A nan kika kwana?". Na yi zumbur na miƙe ina kallonsa kafin na yi magana ya yi saurin taran numfashina da faɗin"ki je ki yi salla idan na dawo daga masallaci zamu yi magana kin ji?". Kaina kawai na ɗaga masa ina matasa na bashi hanya ya wuce na bishi da kallo wasu hawaye masu ɗumi suna gangaro mini. Ba zan iya jan ƙafana izuwa ɗakina ba don haka na shige ɗakinsa na yi alawala. A zaune na yi sallan asubahin saboda rashin kuzarin da nake ji a jikina. Na ɗauko al'ƙur'ani na fara karanta shafi biyu na yi na rufe don sai zabga kwaɓa nake maimakon samun lada sai na ɗebowa kaina zunubi. Sai ƙarfe bakwai ya shigo kamar yanda yake yi a kwanakin nan da ya taso daga sallan asubahi sashin Amma yake wucewa. Har ya shigo ɗakin ya ja dirowa ya ɗauki wasu kuɗaɗe ya fita ban ɗago kaina ba. Ina jin sa yana ji wa Al'amin kashegi akan ya rage wasa da kuɗin. Ya dawo ya zauna ɗan nesa da ni kaɗan ya furta"tashi za mu yi magana".Na tashi daga kwanciyar da na yi akan gardumar ina tattara dukkan nutsuwata gare shi. "Ba zan gaji da sanar dake cewar kina son ki ba zuciyata ta aminta dake aminta na sosai. Idan ki ka cire Amma ban taɓa yarda da wani mutum kwantankwacin yanda na yarda dake ba. Da ke kaɗai zuciyata ta aminta da na ƙarar da rayuwata tare dake. Na ba ki amanar kaina,dukiyata da kuma duk wasu abubuwan da suka kasance mallakina na kasance tamkar raƙumi da akala a gare ki da kike da ikon jan ragamana zuwa ko wani direction. Idan kin ga dama ki bar ni na mutu idan kuma kin so ki tarairaye ni". Dam na ji ƙirjina ya buda da matuƙar ƙarfi yana yi mini dakan lugudai. Bayan ya tsuƙa numfashi ya fesar da iska ya ɗaura da"mu maza bamu da wahalar sarrafawa a hannun mata matuƙar suka hano rauninmu babu boka babu malaman zasu mallake mu. Ina yi miki tuni da ki sanya tsoron Ubangijin da baya bacci a cikin dukkan lamuranki, Don Allah matata kar ki yi amfani da son da nake yi miki ki cutar da ni kamar yanda mata suke yi a yanzu". Haƙwarana suka datse harshena zuffan ya jiƙa mini jikina da yake rawa. Duk yanda na so furta zancen da yake bakina lamarin ya faskara. Na kasa cewa komai illa ƙasa da na yi da idanuna da ya kawo ruwar ƙwalla saboda ɗaurin da ya yi mini da zantukansa da na kasa warwarewa. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 2️⃣4️⃣ Ban ɗago kaina ba sai da na ji shi dab da ni har ina iya jiyo bugun da ƙirjinsa yake yi. Ya kai hannunsa ya tallafo haɓana na matsa idona gam ya hura mini iska a fuskata yana yi mini raɗa a kunnena"buɗe idonki ki ganni". Ban buɗe sai da ya kuma faɗin"kin san bana son gardama ko?". A hankali na buɗe tare da faɗin"tambaya ɗaya zan yi maka don Allah ka sanar dani gaskiyar abinda yake zuciyarka game da hakan". "Na yi miki alƙawarin sanar dake dukkan gaskiyata akan duk abinda kika tambaye ni matuƙar na sa ni". "Wani alama ka gani na cewar zan iya cutar da kai?". Ya juyo fuskana idanunmu cikin na juna kana ya furta"har cikin zuciyata na yi imanin cewar ba za ki taɓa iya cutar da ni ba, shiyasa duk abinda za a sanar da ni game da ke wallahi zuciyata ba zata aminta dashi ba". Na yi rau-rau da ido "wallahi son da nake yi maka ba zai taɓa barin na cutar da kai ba Abdul-hameed. Ko wani na ga zai cutar da kai sai inda ƙarfina ya ƙare balle kuma ni da kaina ma cutar da kai". Ya sakar mini da laulansan murmushi"na yarda dake matata Allah ya ƙara kare mu daga dukkanin wani abun ƙi". Jikina a sanyaye na amsa da Amin. Ina ɗaurawa da "jiya ka bani tsoro sosai ban taɓa ganin ka a cikin irin yanayin da ka shigo jiya ba". "Tuba nake yi ranki ya daɗe, wani labari na ji da ya kiɗima ni na wata matar da ta mallake mijinta ta hanyar sirri ta raba shi da kowa nashi. Labarin ya taɓa min zuciyata sosai shiyasa kika ga na yi miki wannan maganar yanzu don Allah kar ki bari sheɗan ya yi rinjayi akan ki ki faɗa sahun irin waɗannan matan". Jikina ya ƙara yin sanyi lamau"in sha Allah, Allah ya kiyaye mana imaninmu". "Amin" Sai da ya yi yanda ya yi ya fitar dani daga halin zulumin da nake ciki. Na ƙara jin so da tausayinsa a lokaci guda yana ƙara shige mini raina. Kamar ko wace safiya na haɗa masa ruwan wanka ya shiga kafin ya fito na gyara ɗakin tare da ciro masa kayan da zai sa na ajiye masa akan gado da duk wasu abubuwan da zai buƙata. Na koma ɗakina nima na shirya ina zaune gaban madubi na faɗa duniyar tunani maganunsa sun tsaye mini a rai tamkar ƙayar kifi. Ta cikin madubin na ke sa tsaye a ƙofar ɗakin ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa na saka ɗan kunnena na juyo ina kallonsa. Ya kashe mini ido ɗaya yana faɗin"kin yi kyau kamar a sace a gudu". Na murmusa"kai ma ai haka ne". Hannunsa ya miƙo mini na sanya nawa a ciki muka fita izuwa sashin Amma. Duk zaune a falon muka iske su suna zaune, sallamar da mu ka shiga da ita ya sanya su zubo mana idonsu har muka zauna. Duk yanda na so ƙwace hannuna daga cikin na sa na kasa saboda riƙon da ya yi mini gam. Muka haɗe bakin wajen gaishe da Amma ta amsa mana a gajarce sannan Anty Alawiyya. Asabe ta gama jere mana komai na karin kumallo, sai a lokacin ya zare hannunsa daga cikin nawa ya koma kusa da Amma tana zuba musu abincin, take Al'amin ya ce shima tare dasu zai ci, Anty Alawiyya ma kuwa ta ce ba za a barta a baya ba. Ta ƙwala ƙiran Asabe ta kawo musu babban plate suka zuba a ciki. "Ki zuba abinda za ki ci mana". Na yi muryar Amma kamar daga sama, na buɗe kular na zuba wainar farar shinkafa da miyar kayan ciki na soma ci. A hankali nake tauna kamar mai ciwon baki yana wucewa ta maƙoshina da ƙyar, babu wanda ya yi magana domin a dokar gidan Amma ba a yin magana yayin da ake cin abinci kowacce magana ce sai an jira an kammala sannan a yi ta. Sai da muka kammala Asabe tazo ta kwashe kwanukan tare da gyare wajen na bita da kallo a kaina ina jinjina ƙarfin halinta na tsayawa neman halaliyarta don rufawa kanta asiri. Na so tashi na taimaka mata da ɗebe kwanuka gargaɗin da Amma ta yi mini akan na daina shiga harkar da bai shafe ni a cikin gidan ya sanya ni dakatawa. "Yaya kuka yi da Aminu? Ka san bana juran wulaƙanci". "Mun yi magana dashi ya ce a bashi lokaci ya yi tunani" Da sauri ta katse shi"wani irin tunani? Ai tunani ɗaya ne shine ya zaɓa ko Alawiyya ko amarya da ya yi. Don matuƙar ina raye ba zan taba barin wani nawa ya zauna da kishiya ba na zan zafin hakan na san irin tarin raɗaɗin da hakan yake haifarwa a cikin zuciya". Ya yi ƙasa da muryarsa"abun duk bai kai ga haka ba. Amma haƙuri kawai za a yi ta koma ɗakinta ta kula da 'ya'yanta ko don tarbiyarsu a zamanin nan kana kan 'ya'ya ma yaya aka ƙare balle baka kusa dasu. Idan fa ya sake ta dole amaryar ita za ta riƙe yaran kuma duk tarbiyyar da ta zo dashi haka su ma zasu tashi dashi ". Sai da ta gyara zamanta tana cije leɓanta kana ta ce"ba ka san zafin kishiya ba Abdul-hameed. Ni da ubangijina mu kaɗai muka san irin halin da na faɗa lokacin da dangin mahaifinku suka hura masa wutar sai ya ƙara aure don kawai na haifo 'ya'ya mata har guda biyu ". Daga haka ta yi shuru yana sadda kanta ƙasa na saci kallonta ta gefen idona tabbass akwai abinda yake yi mata ciwo a ranta. Maganar da Anty Alawiyya ta soma yi ya tursasa mini ɗauke idona daga kanta. "Amma ki yi haƙuri Ni kam kawai a bar ni na koma gidan mijina" Tana ƙare faɗin hakan ta miƙe ta bar cikin falon. Duk suka raka ta da ido kafin Abdul-hameed ya hau ba wa Amma haƙuri da lallami. Wani takaici ya tokare mini ƙirjina domin na gaza gano haƙurin meye yake ba ta. Sai da ya ga ta yi murmushi sannan ya sama sallama. Ta ce Al'amin ta je ɗakinta ya ɗauko mata wani leda akan gadonta, babu jimawa ya dawo ya ajiye mata saƙon a gabanta ta turo miki shi tana faɗin"ɗauki waya ce tunda naga shi mijinki nakin har yanzu ba shi da niyyar saya miki". Kafin na yi magana ya riga ni"ina da niyya daman ina so ƙarshen satin nan na ɗauke ta muje ta zaɓo da kanta". "Ai yanzu kam na hutar da kai". Ya sa ki murmushi yana sosa ƙeyarsa. A nutse na furta"mun gode sosai Allah ya ƙara girma". "Kun gode ke da waye?". Na yi ƙasa da kaina na ƙara cewa"na gode Allah ya ƙara buɗi". "Amin zasu iya tafiya na sallame ku". Na ɗauki ledar wayar muka fita sai da muka isa wajen motarsa ya ce na buɗe wayar na yi kamar yanda ya ce. Sabuwa ce dal launin ruwan toka ga santsi kamar jikin kifi. "Allah ya sakawa Amma da alkhairi". "Amin". Na amsa dashi muka yi sallama dashi na koma sashina. Baccin da ban yi daren jiya bane na fanshe shi yau, ban tashi ba sai lokacin da ake ƙiran sallan zuhr na yi miƙa ina karanto addu'ar tashi daga bacci. Na yi alwala na yi salla na fito falo na ɗauki ruwa a firiji ina tsaye ina sha na ji ana sallama a ƙofar falon na bada iznin shigowa. "Barka da hutawa ranki ya daɗe, dama uwargijiyata ce ta ce nazo na sanar dake lokacin cin abinci ya yi". Kaina na jinjina mata na ce "to gani nan fitowa". Ta fice na bi bayanta duk da bana jin yunwa amma ya zama kamar dole a kaina na fita domin rashin fitan zai zama matsala a gare ni. Sai da muka shiga sashin take sanar dani cewar wai ta ce na fara samun ta a ɗakinta tukunnna. Ƙirjina ya hau dakan lugadai na haura saman ina ɗar ɗar. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi sallama aka amsa mini tare da bani iznin shigowa na tura ƙofar a hankali na shiga. Tana zaune akan garduma da alama salla ta iddar. Na zauna ina yi mata sannu. Ba ta amsa mini ba sai da ta zare hijabin kanta ta koma bakin gado tá zauna kana ta ce da ni"kin aiwatar da aikin da na sa ki?". Na fara inda-inda domin ba zan ta yanda zan fara ba. Ta ƙara maimaita mini muryarta babu alamar sausauci. Na haɗiye wani miyau mai kauri kafin na sama zarafin furta "ban aiwatar ba daman yanzu nake so nazo na same ki game da maganar. Ba zan iya munafurtarki ba gwara na faɗa miki gaskiya daren jiya Abdul-hameed ya shigo cikin wani yanayin da ban gane gan shi ba, ko da na tambaye shi dalili zai ya ce mini wani labari ya ji akan wata mata ta zubawa mijinta maganin mallaka ta raba shi da dukkan danginsa. Na yi tunani mai zurfi yanda ya nuna ƙyamar abun a fili don kawai ya ji labarin wata can da bai sa ni ba to ina ga in ya gano mu?". Na ƙara sausauta amon muryata"don Allah Amma ki yi haƙuri da wannan abun. Ke uwa duk wani addu'ar da za ki akan sa ba zai taɓa faɗuwa ƙasa banza ba tare da Allah ya amshe ta ba. Ko cigaba da yi masa addu'ar Allah ya sanya tausayi da jin ƙanki a cikin zuciyarki". Sai da ta ɓata wasu mintoti kafin ta ce"ba za ki iya ba kenan?". "Ba zan iya kara yarda da amincewar da ya yi da ni bane, ina mai ba ki haƙuri". Yi tayi kamar ba ta ji ni ba ta jawo wayarta da gilashinta ta maƙala a idonta tana latsa wayarta sai da na gaji kana ta furta"ke ji ɗauko min maganin ki kawo min". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu alamar ba ta son ji komai daga gare ni. Dole na miƙe na koma sashina sai dai me?. Magani ya ce ɗauke ni a hankali domin babu shi babu alamarsa, na fito da kayan wajen gabaɗaya amma ban gan shi ba. Na sauƙe wahalallen ajiyar zuciya ina kama ƙuguna da tunanin abin yi. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 2️⃣5️⃣ Dafe goshina da yake tsatstsafo da maiƙon gumi na yi ina cije naman leɓena. Ban daddara ba sai da na ƙara fito da kayan wajen kaf na ƙara dubawa, amma ban yi tozali da abinda nake nema ba. Babu wanda yake shigo mini ɗaki daga ni sai mijina wanda ko da sakon ɗaya zuciyata ba ta taɓa dasa mini wasi-wasi akan sa. "Ya Rabbi". Na furta ina kwasar kayan ba mayar dasu na fito gabana yana tsanata bugu na nufi sashin Amma. Na haura sama sai da nayi sallama ta amsa mini sannan na kutsa kai cikin ɗakin tare da yiwa kaina mazauni na yi ƙasa da kaina. Domin na rasa ta inda zan fara, na ji muryarta mai cike da taƙama da izza ya bugi kunnuwana. "Me yasa kika daɗe? Ina maganin?". Cikina ya bada ƙarar ƙululu, na musguta kana na zama zarafin faɗin"wallahi ban san yanda aka yi ba, da hannuna na ajiye shi amma yanzu babu irin dubawan da ban yi amma ban gan shi ba". Da mamakina sai naga ta saki dariya mai sauti na ɗauro kaina tare da sauƙe idanuna da ƙwalla ya kwanta a cikin su akanta. "Aisha kina da yawan rantsuwa". Shuru na yi ina ɗauke idona daga kanta da hakan ya bata damar cigaba da"babu wanda yake shiga sashin ki balle har ya yi miki bincike ta yaya za a ce kin rasa shi?" Zan yi magana ta ɗaga mini hannu dole na haɗiye zancen kare kaina da nake son furtawa. "Bana buƙatar jin komai daga gare ki tashi ki ba ni waje". Jikina a sanyaye na tashi ina faɗin"a tashi lafiya". Sai da na fito daga sashin hawayen da suka ciko ƙoramar idona suka kwaranyo, ban yi wani yunƙurin dakatar dasu kamar yanda ban iya samun kuzarin kai hannu na share su ba. Ina shiga sashina na zauna a falo ina tunanin yanda aka yi na rasa ƙulin maganin nan, wani takaici ya tsaya mini a wuya wataƙil Amma za ta yi tunanin na yi amfani da maganin ne nake ɓoye mata. Ko ma ta yi mini kallo mai fuska biyu. Ƙiran sallan Asr ya tursasa mini tashi na yi alawa na yi salla, na ɗauko wayar da ta bani na buɗe ina kallonta, har da sabon layin MTN a cikinta. Ina kunnawa ta kawo na fara latsawa ban yi nisa ba na ajiye ta don ban iya komai da ita ba. Har su Adda Azima suka yi aure basu da waya haka nan ma su Umma. Yayunmu maza da su Baffa su suke da wayoyi. Na yi baya na jingina a jikin kujerar da nake zauna tare da lumshe idona, ina son ganin Ummata ko don na furzar mata da tarin zantukan da suke ƙunshe a cikin raina. Shin daman haka kowacce suruka take ko kuma ni ce kawai nake da rabon fige kazar wahalar da bani da alhakin yanka ta?. Jin an banko ƙofar falon an shigo da gudu ya sa ni saurin buɗe idona. Ina kafe kyawawan yara guda biyu ma mace da namiji da suka nufo suka faɗo kan cinyata. Yanda suke ƙyalƙyala dariya dake bayyanar da zuciyar su wanke take fes da farin ciki, ya hana ni ɗauke idona daga kallon burgewan da nake yi musu. Macen ce ta fara ɗago kanta tana nuna ni da yatsarta ta ce"ke ce ko Anty?". "Ni ce waye?". "Ke ce Antyn da Amminmu take faɗa mana". Na ware idona cike da rashin fahimta"waye Ammin nakun?". Namiji ya yi saurin faɗin"ke ce matar uncle Abdul. Amminmu ta ce muna shigowa sashin nan zamu gan ki, ke ce ko?". Sallamar da aka yi shi ya hani ni yin maganar da na yi niyya, Anty Adama ce cikin shiga ta alfarma leshin ya yi mata ɗas a jikinta sai zabga ƙamshi take yi ta nufo cikin falon. Fara'ar dake kan fuskantarta ya sanya ni nima ƙawata tawa fuskantar ina yi mata sannu da zuwa. Sai da ta zauna sannan na gaishe ta ta amsa mini tana ɗaura da"Afrin da Aryan sarakan zumuɗi har kun riga ni shigowa" A tare yaran suka saki murmushin da ya ƙara fito da kyawunsu. "Anty 'ya'yanki ne?". Ta ɗaga mini kanta na ce"Allah ya raya su bari na kawo muku ruwa". Ina kai aya na miƙe na kawo musu ruwa da lemo da suke cikin firiji na haɗo musu da kofofuna na ajiye musu a gaban su. Muka ƙara sabon gaisuwa da ita, ruwan kawai ta sha kana ta ce"mu kam tun ranar biki kin ji mu shuru ko? Wallahi a daren ɗaurin auren muka yi tafiya sai jiya Allah ya yi dawowar mu. Yau kuwa na ce a gidan amarya zamu wuni". Kunya gabaɗaya ta yi mini dabaibaya domin ban taɓa ko tambayar ta a wajen Abdul-hameed ba. Na saki murmushi"Ayya sannu da hanya". "Yauwa mun same ku lafiya, ya fita ko?". "E ya fita amma zuwa bayan magrib zai dawo". Ta jinjina kanta tana zolaya da cewar"ai dole ya dawo gida tunda yanzu ya ajiye mace". Murmushi kawai na yi mata ina ta biyewa su Aryan da suke ta yi mini shirmen tambayoyi ina masu amsa daidai da fahimtar ƙwaƙwalwa da shekarunsu. "To ya isa haka. Maza kuje sashin Amma ku gaishe ta kafin na shigo". A guje suka ruga suka fita.Ta sa ki ajiyar zuciyar da sai da na jiyo sautinsa daga inda nake zaune. "Tun ranar da aka kawo ki gidan nan nazo mu tattauna da ke amma hakan bai yiyuwa ba. Tunda muka je gidanku kai kayan lefe na ga karancin shekarun ki, na tabbatar da cewar za ki fuskanci tarin ƙalubale a zaman ki a cikin gidan nan. Abdul ɗan uwana ne amma na san babu macen da za ta iya jure zama dashi sai mai haƙuri da kuma fahimta, ba shi da halayyar kule-kulen 'yan mata amma duk wata budurwa r da ya yi sai sun ɓata a dalilin Amma yana fifitata akan komai da kowa a rayuwarsa, wanda yin hakan ba laifi bane amma fa kowa yana da matsayinsa. Kullum addu'ata shine Allah ya haɗa shi da mace ta gari wacce za ta fahimce shi, wacce za ta kishin soyayyar da ya ke yiwa Amma ba zai rufe mata ido ba balle har ta cutar da shi, ta hanyar aikata abinda zai raba tsakanin su". Daga haka ta tsagaita, na gyara zamana ina fuskantar da kyau. "Amma uwata ce amma ko ni na san ba zan iya jure halinta ba a matsayin suruka, amma son da take yiwa Abdul shi ya kawo haka tun muna ƙanana take nuna kulawa akan sa da sanya ido akan dukkan lamuransa da mutane da yawa suke fassara haka a mizanin cewar tana fifita shi a kan mu. Ta jure abubuwa da yawa kafin ta same shi, ta haɗiye baƙin cikin mai ɗinbun yawa da ba kowacce mace ba ce zata iya yin hakan. Har yau ina tuna irin gori da gugar zanar da ta fuskanta daga dangin mahaifinmu akan ta kasa haifo ɗa namiji. Haihuwar Abdul shi ya wanzar da farin cikin da dishashe a cikin rayuwarta". Sai da ta sausauta amon muryarta kana ta ɗaura da"haƙuri zan ba ki akan duk abinda zai faru a yanzu, da zaran Amma ta amince dake to babu kamar ki a wajen ta". A bayyane na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina naɗe ƙafafuna waje guda."wallahi Anty har cikin raina ban taɓa kallon abunda Amma take yi da wani fuskan na daban ba. Kuma na san ko zan mutu na dawo ba zan taɓa yaudarar kaina wajen yin tarayya da ita a cikin zuciyar Abdul-hameed ba. Ina da yayu maza abinda ba zan so matansu su aikatawa uwata ba to tabbas ba zan yi shi ga wata uwar ba". Tabbas na hangi tsantsar farin cikin da kalamaina suka dasa a fuskarta. Godiya ta yi ta jeranta mini kamar za ta yi aron baki. Ta ba ni wasu shawarwarin kana ta shiga sashin Amma don ta ce suna zuwa nan suka fara shigowa. Na zabga tagumi da hannu bibiyu ina nazarin zancenta daki daki. Kenan duk abubuwan da Amma take aikawata a gare ni son ɗanta ne ya rufe mata ido? Kenan ta mance da cewar nima ɗiyar wasu ce. Ban taɓa samun fuska daga wani a cikin gidan mun yi dogon zance ba sai yau, duk da zuciyata tana yi mini kokonto amma na yi iya ƙoƙarin kana kaina zargin komai da zuciya ɗaya na faɗa mata duk abinda na ce. Ganin magrib ta fara kawo kai ya sa ni tashi, na maida hulolin kujerun da su Aryan suka faɗar a ƙasa. Sai da na yi salla na karanta wasu ayoyi daga cikin suratul Muminun sannan na tashi na yi wanka na shirya cikin shirgar doguwar rigar kamfala, na yafa mayafi a kaina na fito za ni sashin Amma. Ina fitowa Abdul-hameed yana shigowa da motarsa sai da na tsaya ya gama daidaita fakin sannan na isa gare shi. Ya kafe da lumshashshun idanunsa da babu komai a cikin su face tarin gajiya da kuma buƙatar hutu. "Sannu da dawowa ranka da daɗe, da alama ka ɗebo gajiya zai fi kyau ka shiga ka fara yin wanka ka ci abinci. Sannan sauran abubuwan su biyo baya". Ya saƙalo ƙafarsa ɗaya waje yana kwantar da kansa jikin kujerar motar da ya yi baya da ita ya ce"Amma kawai nake da buƙatar gani yanzu". "Hakan ma ya kamata". Ya miƙo mini hannunsa na riƙe sannan ya fito muka shiga sashin muna yi sallama Afrin da Aryan suka rugo da gudu suka rungume shi. Tunin ya sa ki hannuna ya ware musu hannayensa suka faɗa jikinsa. Na lura yaran akwai surutu ba na wasa ba don tunda muka shigo bakinsu bai huta ba. Tare suka ci abinci da Amma sannan suka fara hirar su na mutanen da ban ma san su ba. Jifa jifa Anty Adama take sako ni a cikin hirar. Da ya tashi zai je ya yi wanka Anty Adama ta matsa mini akan cewar na bi shi, idanun da Amma ta tsura mini suka hana ni sakat ban tashi ba har yaje ya dawo ba, suka cigaba da hirar su. Na zauna shuru duk zaman ya gundure ni tunanin nawa ahalin ya fara zuwa mini. Nima da yanzu ina cikin 'yan uwana suna hirarmu cike da nishaɗi. Sai wajajen ƙarfe goma mijin Anty Adama ya ɗauke ta, na rasa abinda zan ba wa su Aryan na cika da kunya. Sai da muka je makwancinmu ya koya mini yanda zan yi amfani da wayar, ya sanya mini lambobin duk wasu wanda zan buƙata. Washe gari bayan ya fita aiki wuni na yi ina waya da Umma in na gama da ita na ce a kaiwa Dada. Naso na tattauna lamarin Amma da ya ɗaure mini kai da Dada domin ba zan iya maganar da Ummata saboda alkunya irin ta fulani. A tashin farko Dada ta daka mini birki tare da alaƙanta hakan wai da sharrin sheɗan dake son dasa mini wasi-wasi a cikin raina. Haka na jera kwanaki biyar cif ina ɓuɗuye a cikin kayana amma ban sama ƙulin maganin nan ba. Wata safiyar ranar juma'a bayan Abdul-hameed ya fita aiki Amma ta aiko Asabe ta yi ƙira na, tunda ta sanar dani gabana yake faɗuwa domin ban san me zan tarar ba. Duk lokacin da tayi mini irin wannan aiken sai na faɗa cikin fargaba da zulumi. ƁOYAYYAR MANUFA ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________ Page 2️⃣6️⃣ Da mamakina da na isa cikin ɗakin natan na tarar da Abdul-hameed zaune a gabanta, rabuwar da muka yi dashi tun fitar safe da ya yi ya kuma shaida mini zai wuce masallaci kafin ya dawo. A hankali jikina tamkar wacce aka zarewa laka akan na yi wa kaina matsuguni sannan na yi musu sannu dukkansu. Shuru ya ratsa ɗakin na tsawon wasu daƙiƙai kafin Amma ta yi gyaran murya ta na faɗin"tambaya nake so na yi miki don tabbatar da wani abun da ni na fahimta da kaina". Cikina ya bada ƙarar ƙululu na sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na ce"to Hajiya". "Shin anya kina gamsar da mijinki kuwa ta fuskar shimfiɗa?". Dam dam ƙirjina ya buda ƙarfi, wani kunya da nauyinta suka ƙara rufe ni. Na kasa cewa komai saboda yanda zancen yazo mini a baranbakau. "Ke nake sauraro". Ta ƙara jefa mini tambayar da ya tilasta mini furta"ba zan iya cewa komai akan hakan ba, domin shi ya fi dace ya amsa wannan tambayar". Ta yi wani ƙasaitaccen murmushi da na gaza gano manufarta kafin ta ce "to kai ka ji abinda matarka ta ce ko?". "Na ji komai Amma. Haƙiƙa ina samun nutsuwa daga wajenta, ta kowacce fuska tana ƙoƙarin sauƙe haƙƙina da yake kanta". Basarwa ta yi kamar ba ta ji shi ba. Sai da ta zare gilashin dake kan karan hancinta ta ce"ka dai faɗi son ranka ne kawai, amma kowa ya gan ka ya san babu batun nutsuwa a tare da kai. Na lura matarta bata wadatar da kai don haka ka sa a ranka cewar dole ka ƙaro wani auren. Don ba zai yiyu in zuba ido ina gani wannan dalilin ya sanya ka faɗa harkan banza ba". Da sauri ya katse ta"wallahi ba ki fahimta bane duk yanda kike tunani ba haka bane. Muna samun farin ciki daga junanmu muna sauƙe haƙƙin juna. Mace ɗaya nake da burin rayuwa da ita kuma Aisha ce". A sanyaye ya ƙare zancen da yake bayyanar da tsantsar gaskiyarsa kenan har cikin ransa. Zuciyata ta hau tafarfasa wani ɗaci ya gauraye mini dukkan kusurwan bakina. Wani irin cin fuska Amma ke son yi mini na tattauna wannan zancen akan idona? Zancen da ta ɗaura dashi ya dakatar dani daga zancen zucin da nake yi. "Ba ra'ayinka nake son ji ba, hukuncin da na riga na zartar nake faɗa maka. Watanku biyu da kwana biyu amma ko alamun ɗaukar ciki babu a tare da ita, dole ka yi aure dole ka kawo wata mace cikin gidan nan. Ba cin fuska nake yi miki ba ina son ki kwana da sanin hakan ne tun yanzu, kafin tafiyar ta yi nisa ki ce an yi miki rufa-rufa". Miƙut na haɗiye miyau ɗin da ya wuce ta maƙoƙarona da ya bushe tamkar ƙasar sahara, kana na yi jaruntar sakin murmushin da ya tsaya iya kan leɓana na ce"babu komai Amma ai addini ya ba shi damar ya auri wasu matan uku bayan ni, ba ni da matsala da aurensa". "To Allah ya sa abinda kike faɗa har cikin zuciyarki haka yake". Na cije leɓena"har cikin zuciyata hakan yake". Taɓe baki ta yi"Allah ya yi muku albarka ku tashi na sallame ku". A zuciyata na amsa ina miƙewa na fice daga ɗakin ba tare da ko kalle inda yake ba. Kaina tsaye ina shiga sashina na ɗauki hanyar ɗakina ya riƙo hannuna na kwafce. Ina shiga na faɗa kan gado ina sakin wani kukan da nake jin ciwonsa har cikin raina. Ina jin shigowarsa da zaman da ya yi a kusa da ni ya kasa cewa da ni komai, ban motsa daga inda nake ba balle na ce dashi wani abu. "Ki yi haƙuri, ke kaɗai nake so kuma da ke kaɗai zan rayuwa domin ke kaɗai ce a zuciyata. Ba zan iya haɗa soyayyarki da kowa ba, kar ki sanya maganar Amma a ranki balle har ta dame ki". Da sauri na ɗago kaina ina kafe shi da idanuna da suke tsiyayar da ruwar ƙwalla na ke faɗin"kar na saka a raina fa ka ce? Da gaske kenan bana wadatar da kai dole sai ka auro wata ka kawo cikin gidanka?". Yanda nake yi maganar numfashina yan fizge ya sanya shi riƙo ni gam ya manna ni da jikinsa, duk yanda na so ƙwafce kaina na kasa hakan. Kamar mai raɗa yake cewa"ki yi haƙuri shi ne kawai kalmar da zan iya furta miki a yanzu. Dole sai kin taimaka min wajen yiwa Amma biyayya". A wahale na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi saboda dukan da furucinsa suka yiwa kunnuwana kwatankwacin irin yanda maƙeri yake dukan ƙarfe. "Shin da gaske baka samun nutsuwa da ni?". Sai da jijjiga mini kansa kana ya furta"ina samun dukkanin abinda nake buƙata daga gare ki ɗari bisa ɗari". A bayyane na tagwayen ajiyar zuciya ina lumshe idanuna"ina so gobe idan ka yi mini izini na je gida". "In ce dai ba akan wannan maganar kike son zuwa gida ba?". "Tun kafin maganar daman ina da niyyar tambayarka". Sai da ya yi jim kana ya ce"ba zan hana ki ba amma ki bari gobe asabar ba zan daɗe a wajen aiki ba in na dawo sai mu je". Sai a lokacin na buɗe idona daga lumshe su da na yi"inda hali ina so naje na wuni tare dasu". Sai da ya ƙara motsawa dab da ni kamar zai mayar dani cikinsa, muryarsa ƙasa-ƙasa kuma zancensa a raunane yake faɗin"don Allah alfarmar da zan nema a gare ki kar ki sanar dasu wannan maganar. In sha Allah zan shawo kan Amma har komai ya daidaita". Wasu hawaye suka ƙara ciko mini idanuna na ɗaga masa kaina alamar na ji. Sai dai har cikin raina nake jin cewar ba lalle na iya yin abinda yake buƙatar na yi ba, dole na sanar da iyayena halin da ake ciki kamar yanda shima dukkan komai yake sanar da tashi uwar. Sai da aka yi sallan Asr sannan ya fice daga ɗakin bayan ya gama yi mini lallashi da lallamin da basu yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba. Yana fita na kifa kaina a bisa gwiwa ina sakin wani gigitaccen kuka, sosai nake yin kukan da jin cewar gabaɗaya zaman gidan ya gundure ni. Ji nake yi kamar na ruga a guje na fice daga cikinsa. Shin Indai haka zafin kishi yake to tabbas nawa babba ne kuma ya sha bambam da na sauran matan duniya. Domin jin ƙirjina nake yi tamkar ana sanya tsinin mashi ana sukana. Babu abinda yake yi mini yawon a kwanyata sai zancen Amma. Da ƙyar na tashi na shiga banɗaki na kwance fuskana tare da ɗauro alwala, na fito na tsaya a gaban madubi ina ƙarewa ƙiran halittar jikina kallo. Ban kasance irin matan da marubutan ƙagaggun labarun hausa suke siffantawa ba, ba ni da hasken fata amma ina da kyawun fata mai laushi. Ba ni da cikar ƙirji sai dai ina da kyawun zubi, tsayi da kuma gashi. Ba za a sako ni a cikin kyawawan mata ba amma ina da kyawu daidai irin nawa. Na ja ƙafafuna da suka yi sanyi ƙalau na saka hijabi tare da fuskantar alƙibla na tada da kabbara. Na daɗe kan sallayan ina addu'ar neman mafita da samun sauƙin halin da nake ciki, ban saka rai da shigowarsa a wannan lokacin ba domin na san ko ya dawo to sashin Amma zai wuce. Sai bayan sallan magrib zai shigo ya yi wanka mu koma sashin natan tare domin cin abinci. Ina sallan magrib ya shigo har ya shirya cikin wasu ƙananan kaya marasa nauyi. Sai da ya jira nima na yi wanka sannan muka nufi sashin BASARAKIYA kamar yanda zuciyata ta raɗa mata sunan. Ba a yi wani dogon zama ba yau ana gama cin abincin ta haura sama. Na yi iya ƙoƙarin sarrafa kaina ta hanyar danne kishin dake ci na, na nunawa Abdul-hameed komai ya wuce. Daren ranar baccina ragagge ne tunani barkatai sun ƙi barin ƙwaƙwalwata ta sarara. Kafin ƙarfe goma mun gama shirinmu tsaf har mun shiga sashin Amma zamu yi mata sallama, ta tare mu da faɗin"ina zuwa haka?". "Za ta je gida ne". Ya amsa yan sosa ƙeyarsa tare da rusunar da kansa ƙasa. Ta jinjina kanta tana ɗauka remote ta canja tashar da take kallo ta ce"kai kuma fa ina zaka je?". "Zan kai ta ne daga nan mu gaisa da mutanen gidan na kwana biyu ban tsaya ta can ba". Zancen ta yi ya tursasa mini ɗago kaina babu shiri. A karon farko da na yi mata kallon ido cikin ido. "Direba ya kai ta ko kuma ta hau adaidaita. Kai ɗin ka zauna akwai maganar da zamu yi mai muhimmanci". *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️Maimuna Tijjani Iyam _________________________________ Page 2️⃣7️⃣ Ƙasa na yi da ido ƙirjina yana bugawa tare da kasa kunnen ina tsimayan amsar da Abdul-hameed zai ba ta. "Amma bana yin ja-in-ja ko kuma musu akan dukkan maganarki. Zan so ki yi min wannan alfarman na kai sai na dawo mu yi maganar". "Tashi ka je". Ƙara sausata amon muryarsa ya yi cikin kwantar da kai da ban baki yake faɗin"ki yi haƙuri Amma ba nufina na ɓata miki rai bane. Bari direba kawai ya kai ta". Su kaɗai suke kiɗansu suke rawarsu domin tunda suka fara zancen ban ce uffan ba. Ta ƙwala ƙiran Asabe ta ce ta je ɗakinta ta kawo mata jakanta babu jimawa ta dawo. Ta ciro wasu kuɗaɗe sabi fil da ko irga su bata yi ba, ta dire su a gabana tare da faɗin"ɗauki wannan ki yi musu tsaraba". "An godiya Allah ya ƙara girma". "Amin". Ta amsa mini dashi a daƙile muka fito tare dashi, zai fara yi mini magana na dakatar dashi"kar ka damu ba komai". Sosai ya gargaɗi direban da ya yi toƙi cikin nutsuwa. Sai da motar ta fice daga cikin gidan hawayen da suka kwanta a cikin kurmin idaniyata suka sama damar kwaranya. Ban yi yunƙurin hana su zuba ba, har sai da motar ta faka a ƙofar gidan mu bisa kwatancen da Abdul-hameed ya yi masa muka iso gidan. Na ɓalle marfin motar na fice na nufi gidanmu tare da sallama ɗauke a bakina. Muryar Anwar ce ya amsa sallama na ƙarisa shigowa cikin gidan. Yana zaune tare da Umma yana tsince mata zogala na isa da sauri raina cike da murnar ganin uwata na faɗa jikinta. "Hande min boni. 'Yar nan Allah ya shirye ki". Dariya na ƙyalƙyale dashi ina ɗago kaina daga jikinta"Ina kwana na same ku lafiya?". "Lafiya ƙalau ya gidan nakin?." Na amsa mata da lafiya ƙalau ina maida dubana ga Anwar na ce"ɗan saurayi ya kake?". Harara ya watsa mini"ke kin san dai na fi ki ko?". Na juya masa idona kafin na yi magana ya tari numfashina da faɗin"tare kuke dashi ne?". Sai da na sadda kaina ƙasa kana na furta"a'a ni kaɗai na zo". Koda da ban ɗago kaina ba amma muryar da ya yi magana da ita ya tabbatar mini da cewar walwalarsa ta daɗu. Hira muka kacame dashi sosai har sai da Umma ta tashi ta koma ɗaki ta bar mu, muka tsince zolayan tsaf na ɗaura a wuta sannan na dawo na zauna. "Duk da kina ƙoƙarin ƙawata fuskarki da murmushi domin ɓoye damuwar dake ranki. Ni na gano hakan a tattare dake. Shin kina da wata matsala ne?". A bayyane na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi ina gyara zamana da kyau. Tabbas Anwar ɗan uwa ne na gari a gare ni amma ta yaya zan fara sanar dashi damuwata?. "Shurun da kika yi yanzu hakan ya ƙara tabbatar min da hashashen zuciyata, kina da damuwa Boɗɗiam". Sai da na yi ƙarfin hali wajen danne kukan da yake shirin kubce mini kafin na sama zarafin iya furta"babu abinda ke damuna in ma akwai to addu'arka kawai nake da buƙata". Sai da ya yi jim kafin ya ce"kullum kina cikin addu'ata a dare da rana, nima ki taya ni da addu'ar Allah ya ƙara min ƙwarin gwiwar iya jure rashin da zuciyata ta yi da ba shi da madadi". Cike da rashin fahimta na watsa masa idanuna ya sakar mini da murmushin da kai tsaye na gane na ƙarfin hali ne. Har zogalan ya dahu na sauƙe na kwaɗa mana muka ci ina nuna masa sabon wayata, ya yi mini son barka tare da yi mini gargaɗin yin ta-ka-tsantsan game da sharrinta haka nan ma Umma. Na yi salla snnan muka fita wajen Dada sosai ta cika da murnar ganina. Na waiga ina faɗin"ina Abasiyya fa?". "Tana can gidan Azima bata ji daɗi ba ita ma". Na jinjina kaina"Allah dai ya raba lafiya". "Amin". Suka haɗe baki mun ɗan taɓa hirar da har ta mantar da ni rabin damuwar da na fito daga gida da ita. Bamu sama damar keɓewa da Dada ba sai da na shiga ɗaki zan yi sallan Asr bayan ta shigo ta zauna ta ce dani"ina fatan babu wata matsalar ko?". Tamkar ta sanya kifiya ta soki zuciyata haka na ji zuciyata ta raunana. Kwalla suka ciko mini idanuna taf suka tsiyayo a bisa kuncina. Cike da kulawa take cewa"subhallahi kuka kuma? Me yake faruwa?". "Dada ina cikin matsala". Mamaki ƙarara a bisa fuskarta"matsala tun daga yanzu?". Na jinjina mata kaina"mahaifiyarsa ta ce aure zai ƙara domin ba zai zauna da mace ɗaya tal ba. Tana zargin wai bana samar masa da nutsuwa yanda ya kamata, sannan har yanzu babu wani alamar samun ƙaruwa daga gare ni. Wallahi tun lokacin da ta furta wannan maganar na kasa samun kwanciyar hankali ko murmushi sai dai na yi na yaƙe. Na rasa mafita da abin yi baya taɓa ketare umarninta akan komai". Na ƙare maganar ina ƙara fashewa da wani sabon kukan tare da kifa kaina akan cinyarta, shuru ya karaɗe ɗakin sai sautin kukana da yake tashi a hankali. "Yin biyayya ga iyaye mussamman uwa wajibi ne, don ya fifita uwarsa akan komai da kuma kowa akan ba laifi bane. Maganar ƙarin aure kuma ki cire shi a ranki tabbas da akwai ciwo amma idan kika miƙa lamuranki ga Allah mabuwayi haƙiƙa sauƙi zai zo miki ta inda ba ki taɓa zato ba balle tsammani. Ki yi biyayya ga mijinki ki kuma kyautata masa ta hanyar sauƙe dukkanin haƙƙinsa dake kanki. Kar ki damu da duk abinda 'yan uwansa za su yi miki ko kuma su ce da ke. Ke dai kawai ki kyautata musu domin ita kyautata ta na juya tsana zuwa soyayya". Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar wacce aka zarewa laka. Muryata har ta fara dishashewa na furta"a lokuta da yawa sai in ta tunanin kamar ɓatawa su Baffa da na yi ne, hakan yake faruwa da ni". Sai da sauri ta kwaɓe ne"kul kar na ƙara jin kin furta haka. Babu wanda yake auren matar wani ba ki ji ana cewa matar mutum kabarinsa ba?". Kaina na ɗaga mata na ce"ba sa hira da ni har yanzu bare nake a tsakanin su. Na rasa da waye zan yarda a cikin su". Sai da ta ɗago kaina tana goge mini hawayen da ya ɓata mini fuskana kana ta ce"ki yi haƙuri wasun su na da wahalar sabo kafin su sa ki jiki da mutum ba da wuri ba. Amma inda kika yi haƙuri komai zai wuce ke dai kawai ki tsarkake zuciyarki kuma kar ki nufi kowa da komai face alkhairi.". Sai da ta numfasa ta ɗaura da"dole ki koyi warware matsalolin aurenki da kanki cikin siyasa da dabara". Haka ta yi ta aikin lallashina gami da kwantar mini da hankali. Na ji wani rauni a cikin zuciyata na tabbatar da na sama Dada a matsayin suruka da na dace a gidan duniya. Ina da yaƙinin da ba ni da wata damuwa domin za ta nuna mini tsantsar soyayyar da babu algus a cikinta. Zancen da ta ɗaura dashi shi ya fizgo ni na dawo hayyacina daga duniyar tunanin da na lula. "Amma na yi mamaki da kika ce mahaifiyarss ce ta ce zai ƙara aure, matar nan tana da kirki matuƙar domin ta sha yin aike a gidan nan. Duk juma'ar duniya kuwa sai direban gidan ya kawo abin sadaka". Zantukanta suka shayar da ni ruwan mamakin da ya hana ni yin ƙwaƙwƙwaran motsi balle iya raba tsakanin haƙwarana da suka haɗe da juna. Meye nufin Amma a gare ni kenan? A gaban iyayena da mijina za ta nuna tamkar ta fi kowa sona alhalin fuskar da take nuna mini ya sha bambam. Na so sanar da Daada zancen ƙulin maganin nan amma jin abinda ta faɗa yanzu akan Amma da irin tarin yabon da ta ɗaura da yi mata, sai suka sake mini gwiwa na kasa taɓuka komai. Na so zuwa gidan Adda Azima na gano ta amma Daada ta hana ni a cewar ta wai ban tambayi izni daga gare shi, na zamo mai tsaya a inda aka umarce ni dole na haƙura ba don raina ya so ba. Na numfasa kafin na ce"ni kuwa ya maganar tafiyar Anwar?". Ita ma sai da ta sauƙe numfashi kana ta furta"ba ni da ta cewa akan hakan sai dai kawai na dage da yi masa addu'a". Na tsinci kaina cikin wani irin yanayi"don Allah Daada a hana shi wannan tafiyar". Na ƙare zancen ina marairaice murya kanta kawai ta ɗaga mini tana sakar mini murmushi. Muna cikin haka Anwar da Hamma Ahmad suka yi sallama, muka haɗe baki ni da Daada muka amsa musu. Hamma Ahmad ya kafe ni da ido"yaushe a gari in ji maƙi baƙi?". Ya furta yayin da yake yi wa kansa matsuguni, na saki murmushi"ɗazu na zo". Muka hau gaisawa da juna kafin Daada ta amshe zancen da faɗin"ki yi masa faɗa ko zai ji har yanzu ya ƙi ya fito da wacce zai aura, kullum Babanku a kaina yake juya laifin wai ni nake goye masa baya". "Ya kamata kam izuwa yanzu ka bar mana gida, mun gaji da ciyar da ƙato". Anwar ya furta cikin sigar zolaya da ya sanya Hamma Ahmad saurin kai masa dundun a bayansa yana haɗe fuska tamau. Cikin sanyin jiki da na murya na soma faɗin"gaskiya kam yanzu ya dace ace kai ma ka ajiye iyali. Sai darajarkaya ƙara cika na zama babban mutum".Ya zubo mini idanu sai da na ji wani yar a jikina. "Hmm! In dai ba zaɓa min za ku yi da kanku a ɗaura auren a kawo min ita ba. To ni kam babu wata macen da idanuna za su iya kalle balle saƙon ya kai ga ƙwaƙwalwata har sonta ya yi tasiri a cikinsa. Ki yi haƙuri Daada ni kam ina ga kamar ba ni da rabon yin aure a duniya ne". Duk muka yi tsit tamkar ruwa ya cinye mu. Saboda kashe mana jiki da ya yi da kalamansa da yana kai aya ya miƙe ya fice daga ɗakin. Duk da kallo muka tara shi kafin Daada ta furta"Allah ya kyauta". Da zancen Hamma Ahmad na wuni a cikin raina har lokacin da direba ya zo ɗauka na. Lokacin da Anwar ya shigo yake sanar da ni na fito an zo ɗauka na. Na yi tunanin Abdul-hameed ne domin har a Daada cewa na yi shi zai zo ya ɗauke ni har fura ta ce na dama mishi. Kuɗin da Amma ta ba ni na raba biyu na ba wa Ummata da Daada, sai da na jira dawowar su Baffa muka gaisa. Sannan muka tafi ina jin tamkar an sauƙe mini wani abu mai nauyi daga ƙirjina. Tattaunawar da muka da Daada ya samar mini da nutsuwa haka nan na ƙudurce aiki da dukkan shawaran da ta ba ni domin ina da yaƙinin ba za ta taɓa cutar da ni, ko ɗaura ni a hanyar da ba ta dace ba. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 2️⃣8️⃣ Ina isa sashina ana ƙiran sallan magrib na faɗa banɗaki na ɗauro alwala sannan na zo na tada kabbara, ban tashi daga kan sallayan ba sai da na yi sallan isha'i. Sannan na shiga wanka na fito na shirya cikin shigar abayar da ta sauƙa mini har ƙasa. Ina ƙulle igiyar rigar na tuna cewar lalle Abdul-hameed yana sashin Amma, nasihar Daada ya fara dawo mini cikin kwanyata. Da sauri na ɗaure na ɗaura mayafin rigar a kaina tare da ɗaukar wayata na fita sashin. Dole nima na dunga kutsa kaina cikin su ba zan ƙara jiran sai an zo an ƙira ni kafin na je ba. Al'amin tsaye nake hangowa a cikin inda ake ajiye motoci da waya saƙale a kunnensa da dukkan alamo waya ya ke yi. Na zo dai dai ta wajen zan wuce kunnuwana suka jiyo mini abinda ya hautsina hanjin cikina. "Ku tabbatar da cewar kun aiwatar da aikin nan yanda ya kamata. Yana cikin garin har yanzu". Haka nan kawai jikina ya ba ni cewar ba lafiya ba, kamar yanda zancen suka sama matsuguni a cikin curin ƙaramar ƙwaƙwalwar dake cikin ƙoƙon kaina. Da saurin na ja ƙafafuna na bar wajen ina maimaita kalmar auziya a cikin raina. A hankali na yi sallamar da ya sama amsawar Anty Alawiyya a daƙile tamkar an yi mata dole, sai da na zauna kana na yi wa Hajiya Amma sannu da kuma ita Anty Alawiyyan suka amsa mini ba yabo babu fallasa. Sai dai na lura da cewar kamar wata maganar suke tattaunawa a tsakanin su da shigowata ya sanya su dakatawa. "Kin sama dawowa kenan?". "E wallahi na dawo, kuma sun ce a gaishe ku gabaɗaya". Kanta kawai ta jinjina mini tare da kawar da kanta gefe. Rashin ganin Abdul-hameed a wajen ya sanya zuciyata faɗawa cikin wasi-wasin anya lafiya kuwa?. A duk irin wannan lokacin to tabbas za a same shi tare da Amma. Kuma ko wucewata yanzu na ga motarshi a cikin gidan. Ta gefen idona nake ƙarewa girman falon kallo ko zan gano shi amma ban kai ga cimma hakan ba. Domin da yana cikin falon to haƙiƙa da na gan shi. Bayan na gama sa-toka-sa-katsi da zuciyata da take ingiza ni akan na tambaye inda yake a wajen Anty Alawiyya na ɗago kaina da hakan ya yi daidai da shigowar Al'amin cikin falon. Ya haɗe fuskarta tamau kamar magriban ɗinya, da kallo Amma da Anty Alawiyya suka bi shi dashi har ya zauna da dukkan alamo akwai tarin zancen a bakin su. Da ido Amma ta yi masa alama akan lafiya ya jijjiga mata kansa yana ƙara ɗaure fuska. Tsakin da Anty Alawiyya ta tsirka ya ja hankalin izuwa gare ta sai dai ba su bar mini wani alama ɗaya da zan iya gano ƁOYAYYIYAR MANUFAr da suke ɓoyewa ba. A zabure na dawo cikin hayyacina saboda sallamar Asabe ya na ji shi tamkar a tsakar kaina ta ƙwala shi. Ta zube gaban Amma"uwargijiyata girki ya kammala". Kanta kawai ta ɗaga mata da hakan ya ba ta damar miƙewa ta fara ɗebo kulolin abincin tana jere su a gaban mu. Kowa shi ya zuba abinda zai ci ni kam na kasa kai koda cokali ɗaya na abincin cikin bakina. Babu irin nau'in tunanin da bai zo raina ba a wannan lokacin har izuwa lokacin da na ji muryar Amma sun bugi kunnuwana. "Kin yi magana da mijinki ne yau?". "A'a". Na furta a sanyaye ina ajiye cokalin hannuna. "Meye amfanin wayar hannunki kenan idan ba za ki ƙira mijinki ki ji lafiyarsa ba?". Na yi ƙasa da kaina"na sha'afa da wayar ne ma don tunda na fita tana cikin jakata". Sai da ta ja lokaci mai tsawo kafin ta ce"to mijinki ya yi tafiya na aike shi can wani ƙauye, wataƙila gobe ki jibi ya iya dawowa". Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe muryata ƙasa ƙasa na furta"Allah ya dawo dashi lafiya". "Amin" Ta amsa dashi tana mai cigaba da cin abincinta, gudun kar ta ƙara yi mini wani zancen ya sanya ni ɗaukar cokalin ina tura abincin da ƙyar ba don son raina ko don ina jin danɗanon abincin a bisa harshena ba. Muna gamawa Asabe ta zo ta ɗebe kwanuka tare da gyare wajen. Al'amin ya buga mini wani hararar da babu shiri na rusunar da idanuna ƙasa. "Malama ki tashi ki bamu waje zan tattauna da mahaifiyata da 'yar uwata". "Bana son rashin hankali Al'amin ka dunga bin komai a hankali". A karon farko da Amma ta yi mini magana cikin sanyayyiyar murya mai cike da taushi ta ce da ni"Aisha tashi ki je ki kwanta na sallame ki". "Na gode, a tashi lafiya". Cikin su babu wanda ya ce dani ko kanzil har na miƙe na fice. Ban san inda nake cilla ƙafata ba har na isa cikin sashina na zube akan kujera a falo ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Ina Abdul-hameed ya je? Me yasa bai sanar da ni ba? Wannan dalilin ne ya hana shi zuwa ɗauka na kenan daga gida?. Da sauri na dafe goshina saboda matsanancin sarawan da kaina yake yi mini, halin da yake ciki kawai shi nake son sa ni. Don haka na tashi zaune ina lalumar wayata. Sai da na dubo har ƙasar kujerar babu ita babu alamarta. Babu shakka a falon Amma na baro ta. Na fito tare da nufar sashinta har na ɗaura hannu a jikin ƙofar tare da yunƙurin furta sallama zancen da suka yi wa kunnewana dirar mikiya suka sanya ni yin mutuwar tsaye, babu shiri na jingina da bango saboda rawar da ƙafafuna suka yi mini da nuna bijirewarsu ga jimirin ɗaukar nauyin gangar jikina. "Wallahi tunanina gabaɗaya ya tsaya cak na rasa ma inda zan dafa. In har ba mu gudanar da wannan aikin a yau ba to tabbas ba zamu ƙara samun wannan damar ba. Dole mun karɓa wannan muhimman takardun daga wajensa". Tsabar tashin hankalin da na dulmiya a cikinsa, na ma gaza tantance takamanmen mamallakin muryar da aka yi zancen da ita. "Wasu takardu kenan?". Na jefawa kaina tambayar da ba ni da amsarta kuma bani da mai amsa mini ita. Na daɗe tsaye a wajen jikina yana karkarwa, jin an dafa kafaɗata ya tursasa mini dawowa hayyacina daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa. Asabe ce tsaye a gabana tana bi na da wani irin kallon da ya fi kama da na tuhuma hakan ya sanya ni saurin gyara tsayiwata ina goge fuskana. "Ke lafiya?". "La-la-la-lafiya wayata na manta a ciki na zo ɗauka". Sai da ta ƙare mini kallo kafin ta miƙo mini wayata tare da faɗin "ga ta nan yanzu uwargijiyata ta ba ni ta ce na kawo miki". Da hanzari na karɓa"na gode, don Allah zan nema alfarma mana ko za ki zo mu kwana tare wallahi tsoro nake ji ba zan iya kwana ni ɗaya ba". "Ba zai yiyuwa ba domin uwargijiyata ba za ta bani damar yin hakan ba. Ki yi haƙuri kawai ki je ki yi kwanciyarki. Sannan ki taya mijinki da addu'a domin yana buƙata". Take jikina ya ƙara yin la'asar kaina kawai na jinjina mata na ɗauki hanyar barin wajen. Na so na tambaye ta ko tana da masaniya akan inda yake amma wata zuciyar ta gargaɗe ni ba da kowa zan yarda ba. Sai da na murzawa ƙofar falon ɗan makulli na kashe duk ƙwayayen wutar falon kana na wuce cikin ɗaki na zauna. Lambarsa da ya sanya mini da kansa na laluma tare da danna masa ƙira bayan na sanya ƙiran a amsa-kuwwa na tisa wayar a gabana ina kallonsa. Har ƙiran ya katse ba a ɗauka ba na ƙara dannawa a karo na biyu shima babu amsa. Na ƙira ya fi sau goma amma duk ba a ɗagawa dole na haƙura ba don na sama abinda raina yake so ba. Ban ankara ba na ji ruwan hawaye suna gudu a kuncina. A bayyane na furta"Allah ya kare ka da kariyarsa a duk inda kake mijina". Domin sam zuciyata bata aminta da inda yake ba, haka na kwana ina zabura da mungayen mafarke-mafarke idona biyu yanda na ga rana haka nan na ga dare na kasa runtsawa. Ƙiran assalatun farko kuwa tamkar a kunnuwana ladanin ya ƙwala shi, ban tashi daga inda na yi sallan ba na ɗaura daga inda na tsaya daga ƙiran wayansa amma har yanzu ba a ɗauka. Na rasa yanda zan yi har tunanin ƙiran gida na yi na sanar dasu halin da nake ciki. Amma na ji zuciyata bata nutsu da hakan ba. Haka na wuni a ɗaka ban fita ko ina ba sai bayan sallan zuhr na ji ana buga ƙofar falon da sai yanzu na tuna da cewar ban buɗe ta ba. Na tashi jikina babu ƙwari na je na buɗe Asabe ce tsaye a ƙofar. "Uwargijiyata ce ta ce a zo a duba lafiya ba ki fito ba har yanzu". Na murtsike idona da babu komai a cikinsa face bacci kana na ce"lafiya ƙalau na makare amma yanzu zan fito". A gurguje na yi wanka na shirya na fito duk su na zaune a falon a iske su na gaishe su suka amsa mini. "Lafiya ba ki fito da wuri ba? Ko duk kaɗaicin rashin mijinki a kusa dake ne?". Kaina na jijjiga mata ina ɗaurawa da"A'a kawai an sama akasi na makara ne". Ba ta ƙara cewa da ni komai illa mayar da idanunta da ta yi akan TVn dake aiki a cikin falon. Asabe ta ajiye mini abincin karin kumallona a gaba domin har sun yi nasu. Caccakala na yi na ɗebe kwanukan na kai kitchen na ajiye. Tana tare da wasu yan mata biyu suna ta aikin abincin rana, sannu na yi musu sannan na juya na fice ina jin daya daga cikin 'yan matan tana labartawa Asabe cewar tun ranar da ta fara ganina ta ji tana tausayina. Sashina na wuce na yi kwanciyata na ƙiran layin Hamma Abubakar muka gaisa amma na kasa sanar dashi damuwata. A madadin hakan sai ɓugewa na yi da tambayarsa jikin Adda Azima ya shaida mini da sauƙi. A falon na yi sallan magrib na shafa doguwar addu'ar da na yi da hakan ya yi dai-dai da shigowar mutum cikin falon. Da hanzari na kai dubana izuwa ƙofar shigowa. Zumbur na miƙe jikina har wani rawa yake yi tamkar mazari take idanuna suka kawo ruwar hawaye na furta"kai ne?". Kafin ya ba ni amsa tunin na isa gare shi tare da kifa kaina a ƙirjinsa ina sakin kuka. Shafa kaina yake yi a hankali kamar mai raɗa ya ce"ki yi haƙuri ki daina wannan kukan ba ga ni dawo ba. Tafiyar ce ta zo min a bazata shiyasa". Muryata har tana shaƙewa na furta"na ƙira wayanka ya fi a irga amma ba a amsawa, na faɗa tunani da yawa ko bacci na kasa yi". "Na manta wayata a falon Amma shiyasa idan kika ƙira ba a ɗagawa, sai yanzu da na dawo ta bani ita". Da sauri na raba jikina da nasa ina ƙare masa kallo fuskata da maɗaukakiyar mamaki na ce"ka bar ta a wajen Amma?". Cike da bani tabbacin zancensa ya ɗaga mini kansa da hakan ya yi musabbabin jin miyau ɗin bakina kaf ya tsaya tamkar rijiyar da ta yi shekaru aru-aru da kafewar ruwan cikinta. Sai da ya taɓo ni na dawo hayyacina ya kuma ɗage mini idonsa ɗaya alamar lafiya?. Ƙasa na yi da kaina na ce"ina kaje?". " Zan sanar da ke amma yanzu na fi buƙatar na yi wanka tukunna". Ban ƙara faɗin komai ba na wuce ɗakinsa na haɗa masa ruwan wanka ya shiga. Na ciro masa duk abinda zai buƙata na ajiye masa akan gado na dawo falo na zauna. Ba zan iya yin komai ba sai na sama amshoshin tarin tambayoyin da suka tsaye mini a rai tamkar ƙaryar kifi a maƙoƙwaro daga gare sa. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 2️⃣9️⃣ Ban ankara da fitowarsa daga ɗaki ba sai ji nayi ana hura mini iska a fuskata da hakan ya tilasta mini ɗan lumshe idanuna ina buɗe su akan fuskarsa. Alama ya yi mini da ido akan lafiya, na sauƙe gigitacciyar ajiyar zuciya kafin na kai ga furta abinda ke nuƙurƙusan raina da ruhina sallamar Asabe ya ratsa ƙofofin kunnuwanmu. Ya amsa mata ta shigo ta dire kulolin abincin da ta sako cikin wani ɗan kwadon. "Yau nan aka kawo mana abincin ke nan?". Tambayar da ya yi mata ya sanya ta dakatawa ta ɗago kanta tare da faɗin"yau uwargijiyata ta ce a kawo muku abincinku nan, don ka sama ishashshen lokacin da matarka. Sannan ta ce a sanar da kai ko ka dawo daga masallaci ka wuce wajen matarka ta sallame ka sai gobe idan Allah ya kaimu mu na cikin rayayyu". Ta gefen idona nake ganinsa na lura da wani murmushin jin daɗin da ya saka yana murza hannunsa. Na san tatsuniyar gizo bata wuce labarin ƙoƙi ko shakka babu na san ganin hakan ya yi a matsayi nuna kulawar Amma a gare shi. Har ta gama ajiye kulolin ta fice ban ce ko kanzil ba. Ya jawo ni jikinsa idanunmu suna cikin na juna ya ce da ni"menene yake damun matata na gan ta wani kala?". "Magana nake son mu yi mai muhimmanci". Kansa ya gyaɗa mini alamar yana saurarona da hakan ya bani lasisin ɗaurawa da"ina kaje? Domin na lura tun dawowa ta jiya akwai damuwa da fargaba tare da Amma da kuma su Al'amin game da tafiyar da ka yi". Sai da ya ɗan janye jikinsa daga nawa kafin ya furta"zan sanar dake komai, amma ba ri na je masallaci na dawo sai mu yi maganar". Kaina kawai na iya yin ƙarfin halin ɗaga masa, ya lakaci kuncina yayin da yake miƙewa, da kallo na bi shi har ya fice kafin na sa ki bayyanannen ajiyar zuciya. Sai da na ji an shiga sallar isha'in sannan na tashi daga falon. Alwala na ɗauro na yi sallan sannan na yi wanka na shirya cikin wasu kayan marasa nauyi da takura, ina buɗe kulolin abincin ya shigo na tashi da sauri na je na karɓa sallayan hannunsa ina yi masa sannu da zuwa. Tare muka ci abincin a kwano ɗaya abinda da rabona dashi tun kwanakin biyun amarcina. Sanin ƙa'idarsu na cewar idan ana cin abincin ba a yi ko wacce iriyar magana, ya sanya ni tsuke bakina har sai da muka gama cin abincin na tattare kwanukan na dawo na zauna. Ya riga ni farawa da faɗin"to yanzu bari na amsa miki tambayarki Gimbiyata. Ƙauyenmu naje can garin mahaifinmu domin ganawa da wasu danginsa akan wani gonarmu dake can". Na yi ƙasa da kaina"amma na ji Al'amin yana maganar karɓo wasu takardu". "E akwai wani gonarmu da services ɗin kamfanin MTN ya faɗa a ciki suka buƙaci a sayar musu dashi shine takardun da na tafi dashi". Duk da ya sanar da ni iyakacin abinda na tambaya amma zuciyata ta kasa nutsuwa, a sanyaye na ɗago kaina ina faɗin"don Allah idan akwai wani abun da ya dace na sani game da kai ka sanar da ni". Yanda ya ƙura mini manyan idanunsa ma'abota girma ya tursasa mini janye nawa idanun daga gare sa. Sai da ya yi nisa kafin ya furta"kin san abubuwa da yawa a game da ni amma zan ƙara buɗa miki hanyar saboda yanzu kin zama ma'ajin sirrina". Daga haka ya dakata tare da furzar da iska daga bakinsa ya cigaba da faɗin"tun muna yara muka fahimci akwai takun saƙa tsakanin mahaifiyarmu da kuma dangin mahaifinmu, a da ba haka Amma take ba macece mai matuƙar haƙuri, kawaici, zurfin ciki, da kuma kara.Yau da gobe ya sa ta canja, ta fuskanci ƙalubale masu yawan gaske saboda haihuwar 'ya'ya matan da take yi. Ta haifa biyu basa zuwa da rai sannan Anty Adama da kuma Anty Alawiyya, a lokacin dangin mahaifinmu suka lashi takobi matuƙar ta ƙara haihuwar ɗiya mace sai sun ba wa ɗan uwansu mata ya aura wacce ta ke da ƙwayayen halittar haifo 'ya'ya maza. Allah ya ƙaddara kasantuwana a cikin Amma har ta haife ni, ta nuna min son da kowa ya shaida har ake ganin kamar tana nuna fifiko a tsakanina da ragowan 'yan uwana. Mun rayu cikin tsangwaman dangin uba saboda Allah ya rufa masa arziki fiye dasu". Sai da ya gyara zamansa ya cigaba daga inda ya tsaya"jin labarin faɗuwan services ɗin kamfanin MTN cikin gonan ya sanya Amma tura ni ƙauyen babu shiri, domin su sun dage akan ba za a sayar da gonar ba duk da kuwa alkhairi da riban da za a samu, to in ji dalilin fargaban da kika gani a tare dasu game da tafiyata". Ƙirjina ya yi tsalle ya dawo kwatankwacin yanda gero ke hautsinawa yayin da ake casarsa a cikin turmin. Na yi nisan kiwo cikin tunanin da na faɗa, tabbass idan Amma ta fuskanci dukkan wannan ƙalubalen da ya labarta mini ta cika a ƙira ta jaruma. Sai dai me ye dalilinta na son jefa ni a makamancin halin da bata ji daɗin kasancewa a cikinsa ba?. Haƙiƙa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne amma mafi yawan mata su suke zamowa matsalar junansu ba tare da sun farga da irin illar da hakan yake yi a rayuwarsu ba. Jin ya ƙira sunana da babban murya ya sanya ni dawowa cikin hayyacina, da ido ya yi mini alama akan lafiya na gyaɗa masa kaina. "Ki daina sanya kanki a cikin damuwa Amma da sauran 'yan uwana sun yi min tsantsar soyayya. Ba zasu taɓa iya cutar dani ba ki saka haka a ranki". Ban iya cewa dashi komai ba, ya cigaba da ja na a jikinsa. Daren ranar dai shi ya yi kiɗansa kuma ya yi rawarsa domin na kasa taɓuka komai. Washe gari kafin ya tashi har na gama duk wani abun da zan yi, na zauna a bakin gadon na zuba masa ido. Yana buɗe idonsa muka sakarwa juna murmushi ya tashi ya zauna na matso gabansa muka gaisar da juna. Sosai ya yaba da kwalliyata na haɗa masa ruwan wanka tare da ajiye masa duk abun buƙata akan gado na koma falo zaman jiransa. Ina latsa wayata amma sam hankalina ba nan yake ba, so nake yau nima na girkawa mijina abincin da zai ci da hannuna. So nake na ciyar da shi daga abinda na sarrafa amma sai dai babu damar yin hakan don har yanzu babu wani na'u'in kayan abinci ko ƙwayar gero a cikin sashin. Ganin ya fito ya sanya ni ture wannan tunanin a gefe na tarbe shi tare da yaba kyawun da muka yi. A wayarsa ya ƙira Baffa muka gaisa har da Umma haka nan ma Baba sai zuba mana albarka yake yi. Cikin nishaɗi muka fito muka nufi sashin Amma muka gaisar da ita ta amsa mana fuskarta a sake. Sai da muka gama cin abincin ta kallo shi haɗin da faɗin"kamar bakinka da magana". Ƙasa ya yi da kansa yana ɗan sosa ƙeyarsa"e daman za mu sama hutun ƙarshen shekara ne a wajen aiki, shine nake son mu yi wani ɗan tafiya tare da Aisha". "Zuwa ina?". "Da na ce ko cairo". "Cairo? Da wannan ɗin za ka je cairon?". Al'amin ya ƙara jinjina zancen yana taɓe baki. Da sauri ya ɗauro kansa da nufin maida masa da amsa Amma ta tari numfashinsa"ku dakata da tafiyar sai wani lokaci. Ka san da har yanzu ba wai an raba gado bane juya su kawai kake yi don haka ka dunga sanin abinda zaka yi hidimar iyalinka dashi". Kalamanta suka soki ƙahon zuciyata da take azalzala akan na ɗago na galla mata kallo amma na danne. Na maimaita zancen a raina daman ba su yi rabon gado ba kenan?. "Ina lura da dukkan abinda nake kashewa na daga kuɗi. Hasalima Amma ai account ɗin da riban wancan kasuwancin yake shiga daban yake kuma in dai ƙudin da zai shiga ko ya fita sai kin sa ni". Banza ta yi dashi kamar ba ta ji abinda ya faɗa ba, sai can ta ce"yau idan ka taso daga aiki ina so ka je gidan mijin Alawiyya ta kwaso min 'ya'yan nan gabaɗayansu ka kawo min su nan". "Innalillahi! Haba Amma ai duk abin bai yi zafi har haka ba. Don Allah ki yi haƙuri ko da Anty Alawiyya ba za ta koma ba a bar yaran nan su taso a gidan ubansu, ko mai lalacewar tuwo ba a canja masa suna". Carab Al'amin ya karɓe zancen"ni fa daman tun can Amma mutumin nan bai taɓa burge ni ba. Kawai dai Yaya Abdul ne ya dage har aka yi auren nan wai don yana yayan abokinsa". A harzuƙe Abdul-hameed yake faɗin"ka dakata min haka nan Al'amin. Sau nawa zan ja maka layi akan idan ina maganar da Amma wanda bai shafe fa ka daina yi min katsalandan?". Tsam Amma ta miƙe ta na kakkaɓe hannu"ga ka gashi idan kun ga dama ku cinye kanku. Na tashi na baku guri". Tana dasa aya ta haura sama ɗakinta. Abdul-hameed ya rufa mata baya yana bata baki. Tagwayen ajiyar zuciya na saka ina kallon Al'ain da ya ɗauke kansa tare da nuna halin ko in kula da fushin da Amma ta yi, sai ma zaro wayarsa da ya yi daga aljihunsa yana latsawa. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________ Page 3️⃣0️⃣ A sanyaye ya sauƙo na bi shi da kallo yayin da ke ƙarisowa cikin falon. Da ido ya yi mini alama akan na taso na miƙe ya figi hannuna da ƙarfi ya fara ja na muka fice daga cikin falon, sai da muka isa tsakiyar falonmu kana ya saki hannuna ya zube akan kujerar zaman mutum uku dafe da goshinsa. A tsuguna a gaban kujerar tare da ɗaura hannuna akan hannunsa da yake bisa goshinsa. "Ka kwantar da hankalinka ka ji?". Sai da na cire tsammani da samun amsa daga gare shi kana ya furta"hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar Amma tana fushi da ni, ba zan taɓa samun nutsuwa ba". Na zame daga tsugunan da na yi akan ƙafafuna na yi zaman dirshan akan kafet ɗin"ai baka aikata wani abunda zai sanya ta fushi da kai ba". Sai da ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman nawa kafin ya ce"na aikata mana ba ki ga yanda ta bar cikin falon a fusace ba?". "Na ga ni, amma idan akwai wanda ya dace ya shiga wannan yanayin to Al'amin ne. Domin da bai tsoma baki a maganar da bai shafe sa ba da duk hakan bai afku ba. Hamma Abdul ya kamata ka daina ɗaurawa kanka laifi akan komai". Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da ya sauƙe yana matse hannunsa dake ƙasan nashi bai ce da ni komai ba, ya saki hannuna ya tashi ya zauna yana matse hannayensa da ya haɗe waje guda yayin da yake miƙewa ya nufi ɗakinsa na yi saurin dakatar dashi da faɗin "wajen aikin fa?". "Babu inda zan iya fita matuƙar Amma ba na fushi da ni, ko nake ba zan iya taɓuka komai ba". Yana gama faɗin ya shige ɗakinsa na bi bayansa da kallo raina cike taf da tsantsar mamaki . Ni dai ban ga laifin da ya aikata da za ta ɗau fushi dashi ba hasalima Al'amin shi ne mai laifin ba shi ba. Take zuciyata ta fara harbawa da ƙarfi ina soyayyar da kowa yake faɗa cewar Amma tana yi masa?. Anya akwai uwar da za ta yi wa ɗan da ta haifa irin hakan kuwa?. Tsam na miƙe a ƙoƙarin ƙaryata hashashen zuciyata mai munin gaske. Ranar wuni na yi ina lallashinsa da ba shi baki. Ko da muka je cin abincin rana Amma ba ta fito ba haka nan ma na dare haka muka ci babu ita. Sai ƙarfe sha ɗayan dare ya shigo ɗakina don tunda muka gama cin abincin ya ce da ni naje na kwanta sai jira fitowar Amma. Washe gari ma sai da ya makara wajen fita aiki, tun yana bani tausayi har lamarin ya koma ba ni haushi. Kwana biyun nan gabaɗaya kaɗaici ya dame ni idan ya fita ya bar ni bana yin komai har ya dawo. Daga yin kallo sai danna wayar da wani lokacin ma mancewa nake yi da ita. A ranar da ya dawo bai shigo ba har sai da lokacin cin ya yi na fito, na tarar dashi zaune a tsakiyar wasu yara biyu duk maza sai suturu suke ta zuba masa. Na yi wa Amma sannan ta amsa mini ba tare da ta ko kalle inda nake ba. "Afuwan kinga ban shigo ba ko?". Ban ce dashi komai ba ya cigaba da "waɗannan 'ya'yan Anty Alawiyya ne zasu cigaba da zama a nan zuwa wani lokaci". Murmushin dole na ƙaƙalo na dasa a fuskana. Muka ci abinci muka gama na yi mamakin ganin yanda Amma ta zage tana tambayar yaran irin zamantakewar da mahaifinsu yake yi da sabuwar amaryar da ya yi, yaran da babban cikin su bai wuce shekaru shida ba sai fayyace mata zancen yake yi. Ba su yi wani dogon hira ba ta sallame mu muka yi mata sai da safe, har mun yi shirin kwanciya ina zaune a gefensa yana latsa laptop ɗin dake gabansa ya ce"ina son yara a rayuwata sosai". Na yi taƙaitaccen murmushi"ai yara abin so ne daman kana da na 'yan uwa. Kafin Allah ya baka naka". "Ai su ba ni da cikakken iko akan su tunda ba mahaifinsu bane ɗan uwana". Na jinjina kaina cike da gamsuwa da maganarsa kafin na ce"ni kuwa me yasa Anty Alawiyya ba za ta yi haƙuri ta mance komai ta koma gidan uban 'ya'yanta ba?". Sai da ya ajiye laptop ɗin akan dirowar dake gefen gadon kana ya furta"matsalar ba daga gare ta bane domin ita ma tana son komawar idan kin lura, sai dai Amma ce ba za ta bari ba a cewar ta 'yarta ba zata zauna da kishiya ba". Na furzar da iska daga bakina haɗi da faɗin"kana yi wa Amma dukkanin biyayyar da ko wani ɗa na gari zai yi wa Mahaifiyarsa kuma ita ma na san tana alfahari da hakan. Amma fa akwai wai gaɓar da ya dace kana nusar da ita ko kuma jawo hankalinta, yanzu ko rabuwa suka yi tana da yaƙinin cewar za ta sama marar mata wanda zai aure ta kuma ya zauna da ita tal ita kaɗai?" Jim ya yi kamar mai nazari sai can ya ce"haka ne lokuta da yawa ina son aikata hakan amma bana iyawa, ban san me yasa ba". Hannuna na ɗaura a saman nasa ina murzawa a hankali"saita lokacin da nake cikin nishaɗi za ka yi sai ka yi mata zancen cikin kwantar da kai". "Tsarki ya tabbata da Sarkin da ya sanya mace ta gari ta zama silar samun nutsuwar mijinta". Ya furta yana shafa goshina da gashina ya kwanta ya yi luf. Haka rayuwa ta cigaba da lafiya lokaci yana juyawa kwanakinmu yana daɗa ƙarewa. Kullum muna ƙara kusantar mutuwa ba tare da mun farga ba balle mu yi tanadin guzuri. Har na cika wata takwas cur ban taɓa yin ɓatan wata ba Adda Abida lokacin cikinta har ya fito ya yi mata ɗas. Adda Azima kuwa tunin ta kuma yin ɓarin da har yanzu Allah bai bata wani rabon ba. Kullum sabon lamari Amma take fitowa dashi a cikin kwanakin nan komai Abdul-hameed ya yi baya yi mata gwaninta, ta maida shi tamkar bawata biyayyar da yake yi mata kuwa kullum ninkuwa yake kamar zai yi mata sujjada. Dukiyarsu kuwa baya zarar ko sule ba tare da ta tuhume shi dalilin fitar kuɗin ba. Tausayinsa ya mamaye mini raina mussamman da Amma ta bijiro da zancen dole ya ƙaro aure tunda ni ba zan iya haifo masa 'ya'ya ba. Kwance nake a falo na yi zurfi sosai cikin duniyar tunanin da na faɗa, na ji tsayiwar mutum a kaina da sauri na tashi. Na zabura ina murtsike idona don tabbatar da abinda idanuna suka gane mini. Anty Azima, Adda Abida da kuma Abasiyya na rungume su tsam a jikina tsabar murna na ma rasa inda zan tosa su. Na kawo musu ruwa da lemo a dire musu a gaban su sannan muka hau gaisawan yaushe rabo. "Amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida". Abasiyya ta faɗa cikin sigar zolaya na wurga mata pillown dake kan kujerar ita ma ta dawo mini dashi, Adda Azima ta yi saurin faɗin"ke ki rufa mana asiri kar ki yi mata asara". "Asarar meye?". "Ɗan dake cikinta mana". Kunya ya tursasa mini yin ƙasa da kaina"ni kam Adda ba ni da komai". Dariya kawai ta yi dake alamta mini cewar ba ta gamsu da zancen nawan ba. "Ina Hamma Ahmad da Anwar fa?". Na furta a ƙoƙarin kawar musu da zancen. Duk suka yi shuru sai Adda Abida ce ta amsa mini da faɗin"Hamma Ahmad yana nan Anwar kuwa ya tafi can Jigawa wajen Goggo". Na ɗago kaina ina kallonta"yaushe ya tafi?". "A ƙalla zai yi wata guda". "Haba Adda shi ne babu wanda ya gaya mini. Kuma fa muna waya da su Baffa da su Dada amma duk ba su faɗa mini ba". Na ƙare zancen muryata tana rawa. "Tafiyar ce tazo a gaggauce shiyasa amma ai zai na zuwa gida". Duk sai na ji yanayina ya sauya ban ƙara fahimtar hirar da suke yi ba har sai lokacin da Adda Azima ta ce Abasiyya ta tashi ta taya ni ɗaura girki a mijina. Na san ta faɗi haka ne don fitar dani daga yanayin da na faɗa. Jikina a sanyaye na ce"ba na yin girki daga sashin mahaifiyarsa ake kawowa". "Ban gane bakya yin girki ba? Kina nufin har yanzu ba kya girkawa mijinki abincin da zai ci sai an girka an ba ku?. Cabɗijam! Lalle Aishatu ba ki da lissafi". Furucin Adda Abida ke nan a zafafe tamkar za ta kai mini bugu, na sausauta muryata na ce"tsarin su ne haka kuma shi ma bai taɓa ƙorafi akan hakan ba". Ta yi saurin tarar numfashina"daman ta yaya zai yi miki ƙorafi tunda ya gano cewar ke shashasha ce ba ki san inda yake yi miki ciwo ba. Ki tsaya kallo ruwa kwaɗo ya yi miki ƙafa kina nan kina zaune kin sake baki a ƙwace miki miji a banzan a wofi, tun wuri ki san inda dare ya yi miki kwaci mijinki a hannunki. Yo ni Allah na tuba akwai wacce ta isa ta yi min haka ne ai dama tun lokacin da ya ce gida ɗaya zai haɗa ku da mahaifiyarsa na san cewar za a rina wai an saci zanin mahaukaciya". Da hanzari Adda Azima ta kwaɓe ta"ke Abida ya isa haka. Yanzu idan wani ya ji fa me kike tunanin zai faru? Ai sai a ce mun zo har gidanta muna zuga ta, don Allah mu bi komai a sannu". "Adda Azima ai abin ne da ciwo. Wallahi tun wuri kafin abun ya yi nisa ki yawa tufkar hanci. Bijirewa za ki yi ki nuna kina son a damƙa miki ragamar girkin mijinki, idan kuwa ta ƙi sai ki yi gaban kanki". Jijjiga kanta kawai Adda Azima ta yi, mun wuni tsum tare dasu sai da muka yi salla na shigar dasu sashin Amma suka gaisa, ta sanya Asabe ta bi yo mu da abinci da abin sha. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________ Page 3️⃣1️⃣ Tunda suka tafi nake bitan zantukan Adda Abida a cikin kwanyata. Tabbas nima ina son na ga ina girkawa mijina abinda zai ci da hannuna da kuma amfani da basirata, ƙaruwar ajiyar zuciya na sauƙe tunawa da na yi duk tsawon zamana a cikin gidan har yanzu ban san abincin da ya fi so ki kuma abin shan da yafi burge shi ba. Banko ƙofa da shigowar 'ya'yan Anty Alawiyya shi ya yi nasarar dawo da ni hayyacina daga tunanin da na yi nutsu a cikinsa. Kai tsaye suka wuce ɗakinsa su na leƙawa, fuskana tamau kamar hadirin gabas na ce"lafiya me kuke nema haka?". Cike da tsiwa babban Ansar ya furta "Amma ce ta ce mu zo mu duba mata ko uncle Abdul ya dawo". Na taɓe baki"to tunda kun ga baya nan ai sai ku koma ku sanar da ita abinda idanunku ya gane muku ko?". Ina dasa aya na miƙe fuu na shige ɗakina cikin ƙonar zuci. Dole sai na shafawa idanuna toka na koya maida martani akan komai da an ce mini kule na ce cas. Sai da na yi sallan magrib sannan na ɗaga wayata na ƙira mijina, kai na tsaye na furta"me kake buƙatar ci yau?". Da mamaki cike fal da furucinsa ya ce"duk abinda kika tanada min". Na yi murmushin jin daɗi"to shikenan Allah ya dawo mini da kai lafiya". "Amin ya Allah". Da haka muka yi sallama na fito na nufi sashin Amma, babu kowa a falon sai ƙarar na'urar sanyaya waje. Don haka kaina tsaye na wuce kitchen na tarar da Asabe ta kammala komai tana gyara wajen. Sannu na yi mata ina ɗaura da"Baba Asabe girki nake so na ɗauro, ko za ki taimaka ki nuna mini yanda zan yi amfani da komai?". Sakake ta yi tana bi na da idanu da alama mamakin furucina ne ya hana ta motsawa, na ƙara ware idanuna akan ta ina maimaitawa a karo na biyu. "Uwargijiyata ta riga da ta faɗi abinda za a girka kuma har na kammala. Dokar gidan nan ne idan aka sauƙe sanwa ba a kuma ɗaura wani". Ko a jikin wai a muntsine kakkaura na taho izuwa tsakiyar kitchen ɗin na fara buɗe dorowowin ina dubawa. "Mijina ne yake buƙata kin ga kowa ko ita Amman ba zata so na saɓawa umarninsa ba. Dambu nake so na yi akwai zogale?". "Akwai jiya an kawo". "Madalla! Yana ina na fara aikin da wuri". Ta nuna mini inda yake na ɗauro na fara figewa, kafin wani lokaci na gama haɗa komai na haɗin dambu. Ta kunna mini gas ɗin kasancewar ban iya amfani dashi ba na ɗaura cikin wata tukunya da aka yi ta musamman don turara dambu. Sai da na tabbatar komai ya kammalu na ce"don Allah ki dunga kula mini dashi zan je na yi wanka". "To ai ko dan wannan daddaɗan ƙamshin da yake tashi ma, ba zan so na yi nisa dashi ba". Murmushi kawai na yi na fice na koma sashina ina jin wani farin ciki na musamman na mamaye mini raina, a gurguje na yi wanka na ɗauro alawa na gabatar da salla. Na shirya cikin doguwar rigar atamfata mai kalar sararin samaniya na kashe ɗauri tare da feshe jikina da turare. A wajen ajiye motoci na ga motarsa da hakan yake bani tabbacin cewar ya dawo, tun kafin na ƙarisa shiga falon nake jin yanda suke hirarsu cikin raha da son juna. Na yi musu sannu sannan na zauna ina ankare da wani kallon da Al'amin ya bi ni dashi ta gefen ido yana cire leɓe. Sam na ƙi yarda mu haɗa ido da Abdul-hameed duk ƙoƙarin da yake yi, Asabe ta yi sallama tare da jere mana kulolin abinci a gaban mu da ido ta yi mini nuni da kular da girkina yake cikinsa na ɗaga mata kai alamar na gane. Kamar kullum ya ɗauro plate zai zuba musu shi da Amma na yi saurin faɗin"ka manta alƙawarin da ka yi mini ne?". Ya ɗage mini ido alamar bai gane ba, na jawo kular gabana tare da buɗe ta kafin na ce"yau ai abinci ka yana hannuna don haka bismillah". Na ƙare zancen ina ɗaukar wani plate na soma zuba masa na tsiyaya masa man ƙuli tare da sanya masa yajin da ya daku ya yi luƙui. Ya kafe ni da ido kamar yanda sauran ma suka yi, kafin ya yi magana Anty Alawiyya ta riga shi da faɗin"wa ya yi wannan girkin?". "Ni ce na girkawa mijina nima ina son yau ɗaya dai ya ci girkin hannuna". Za ta ƙara yin wani maganar Amma ta ɗaga mata hannu alamar ta dakata, sannan ta karɓe zancen cikin faɗin"da iznin waye kika yi wannan girkin?". Na yi ƙasa da kaina"da izninsa na yi domin sai da na tambaye sa kuma Amma ban yi zaton aikata hakan zai zama laifi ba domin a ganina kyautatawa ne na yi gare shi. Kuma ina da tabbacin ke ma za ki so duk wani abunda zai faranta masa". Na ƙarƙare ina ɗago idona domin karantar yanayin fuskarta da ya cika da tsantsar mamaki da ya kasa ɓoyiwa sai da ya bayyana. Sai da ta ɗau lokacin kana a gajarce ta furta"kai ka taba iznin shiga madafa ta yi maka girki?". Inda-inda ya soma yi ganin hakan ya sanya ni saurin yin caraf na cafke zancen da faɗin"kullum nuna mini hanyar da zan samar masa da farin ciki da kwanciyar hankali ki ke yi. Kuma girki yana ɗaya daga cikin ababen da yake ɗaurar da ƙauna tsakanin ma'aurat...". Tsawar da ta doka mini ya tursasa mini haɗiye raguwar zancen tare da runtse idanuna da ƙarfi saboda bugun da ƙirjina ya yi. "Ina sauraron ka". "Ni na ba ta izni". "Menene dalilinka na yi hakan?. Shin abincin da ake yi ne ba ka so ko kuma ba ayin sa yanda kake so ne?". Da hanzari ya jijjiga kansa"ko kaɗan ba haka bane tabbas ina samun duk abinda nake so. Ganin ba ta taɓa bijirowa da zancen tana son girka wani abu bane sai a wannan karon shiyasa na bada dama". Ba ta ce dashi ko kanzil ba ta tashi daga kishingiɗewar da tayi ta jawo kular farar shinkafa da miyar da ta sha ganye ta fara zubawa a plate. Har ta fara cin abincin ba ta ce dashi komai ba kamar yanda shi ma ya kasa kai koda loma ɗaya na dambun da na zuba masa. Na haɗiye wani miyau mai ɗacin gaske daga maƙoshina kana na furta"bismilla ka ci mana". Sai a lokacin Amma ta ce "ban yarda da dambun nan ba, ba ta cokalin ta fara ci tukunna". Ƙirjina ya yi wani wawan bugun da ya sanya ni watsa mata wani kallo ba tare da sanin da na yi ba. Ta ware mini idanunta cike da son tabbatar mini da zancen ta, na kasa aiwatar da komai sai hawayen da suka fara gudun famfalaƙi a bisa kuncina. "Idan babu wata ƁOYAYYAR MANUFA to ki fara ci tukunna kafin Abdul-hameed ya ɗanɗana". Anty Alawiyya ta furta cike da gatsali da hakan ya ƙara ƙarfin gudun hawayena. Cikin rawar jiki da na murya na furta"wallahi ba zan taɓa iya cutar da Abdul-hameed ba, ko wani naga zai cutar dashi sai inda ƙarfina ya ƙare balle kuma ni da kaina ". Al'amin ya yi saurin daka mini birki"salla malama ki yi abinda aka umarce ki kawai, daga magana za ki fara wani koke-koke a muta....". Marin da Abdul-hameed ya ɗauke shi ya shi ya hana sa dire zancen da ya ɗauko tiryan-tiryan cike da tijara, idanunsa har wani ƙankancewa suka yi yake faɗin"ka san da wacce kake magana kuma ki ita ba ta kai ka girmama ta ba ai za ta ci darajata. Aisha ta wuce duk wani wulaƙancin daga gare ka, abinci ne domin ni ta yi shi kuma ko meye ta saka a ciki zan ci shi". Salatin da Amma ta rafka tana tafa hannu gami da riƙe haɓa ya sanya shi yin ƙasa da kansa. "Ba shakka Abdul-hameed macen za ka fifita akan ɗan uwanka da kuka kwanta a cikin mahaifa ɗaya? To abinci ne na ce ba zaka ci shi ba". "Duk yanda kika ce haka za a yi ba zan taɓa yi miki musu ba. Amma matuƙar Al'amin bai daina furta mata ki wani irin magana ya zo bakinsa ba za mu sama gagarumar matsala dashi. Kowa ya tsaya a matsayinsa shi ɗan uwanane ita kuma matata cikin su babu wanda zan yarda ɗaya ya ciwa mutunci na kyale". Sai da ya miƙe tsaye ya cigaba da"sai da safe na barku lafiya, tashi mu tafi". Ya faɗa yana maida dubansa gare ni jikina a sanyaye na miƙe na bi bayansa ina tare sabbin ƙwallar dake ƙoƙarin kwaranyo mini. Ina jin Ansar yana faɗawa mahaifiyarsa cewar zai ci dambun tana kwaɓarsa da cewar wai ba abun ci bane. Kamar jira kukan yake yi ina sanya ƙafa cikin sashinmu ya kufce mini mai matuƙar ƙarfi. Na durƙushe akan gwiwata ina sakin kukan da dukkan ƙarfina, ya tsuguna a gabana tare da jawo ni jikinsa ya ƙanƙame ni gam saboda rawar da jikina yake yi. Ya soma hura min iska a goshina haɗi da faɗin"don girman Allah ki yi haƙuri Aisha in sha Allah haka ba zai ƙara faruwa ba. Kar ki sa wannan abun a ran ki na roƙe ki matata". "Daman duk zaman nan 'yan uwanka basu yarda da ni ba? Daman duk tsawon wannan lokacin kallon wacce za ta iya cutar da kai suke yi mini?". "Shit". Ya furta yana ɗaura ɗan yatsansa akan leɓena"kar ki ce haka babu wanda yake zarginki a cikin 'yan uwana. Ko yau da kika hakan ya faru haushin rashin sanar da ita da kika yi ya sanya ta aikata komai, ina mai ba ki haƙuri". Shuru na yi masa ba don na yarda da zancen nasan ba, na koma sauƙe ajiyar zuciya a kai a kai. Ya tallafo haɓata"ki yi haƙuri na miki alƙawarin ba zan taɓa barin ki wulakanta ba". Kaina kawai na iya ɗaga masa ya kai hannunsa yana share mini hawayen fuskana yana faɗin"bari na yi wanka sai mu je gidan cin abinci mu ci abincin ko?". Bai jira amsata ba ya miƙe tare da ɗauka ta cak ya yi ɗakinsa da ni ya dire ni akan gado. Ya shiga banɗaki ranar ko ruwan wanka ban iya haɗa masa ba na tusa kallabina a cikin bakina a ƙoƙarin hana sautin kukan da nake yi fita, sai da na yi mai isa ta sannan na tashi na nufi wajen ajiye kayansa. Inda yake ajiye t-shirt da wandunan jeans na nufa, ya kwana biyu bai sanya su ba na fara ciro su ina duddubawa. Ina ɗago wani wando na ji wani abu ya faɗi, ban jiyo ba sai da na ajiye shi akan gado sannan na waigo. Gabana ya yi wani mummunar faɗuwa sakamakon abinda idanuna suka yi mini tozali dashi, jikina yana rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki na sunkuya na ɗauki ƙulin maganin ina jujjuya shi a hannuna. Babu ko shakka wannan shi ne ƙulin maganin da Amma ta bani ta umarce ni na sanya masa a cikin ruwan wanka wanda na neme shi ko sama ko ƙasa na rasa shi. Abinda na alkince shi a cikin ɗakina cikin kayana me ya kawo shi ɗakin Abdul-hameed?. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________ Page 3️⃣2️⃣ Jin kamar zai buɗo ƙofar ya fito ya sa ni saurin sanya ƙulin cikin aljihun rigar atamfar dake jikina. Na juya da sauri zan fice na je falo na jira shi ya dakatar da ni ta hanyar faɗin"ina koma za ki je?". "Zan je falo na jira ka ne". Ya tako ya sanya hannunsa ya riƙo ni ta baya yana yi mini raɗa a kunne"ki dawo ki shirya ni". Na juyo idanunmu suka haɗe waje guda wata zuciyar ta ayyana mini na ciro ƙulin maganin na nuna masa tare da tambayarsa inda ya samo ta, sai na yi wani tunanin yanda ya nuna mini komai ya wuce na haɗiye kawai. Sai a lokacin na hango ashe ko rufe wajen kayan ban yi ba. Na shirya shi tsaf sai zabga ƙamshi yake yi. Na ɗage masa ido ɗaya alamar ya yi bala'in kyau, ya kai hannu zai riƙo ni na yi saurin gaucewa ina sakin murmushi domin na san manufarsa. Ƙirar wayarsa da aka yi ya bani damar zillewa na koma ɗakina, kai tsaye banɗaki na wuce na je ƙulin maganin a cikin toilet na kunna ruwa ya raka shi. A bayyane na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina jin tamkar an sauƙe mini wani dutsi mai nauyi da aka ɗaura mini a tsakar kai. Fuskana na gyara da kukan da na yi ya ɓata, na yafa mayafina na fito a falo na bar wayata na ɗauka muka fito. Na yi tunanin zai ce mu fara leƙa sashin Amma sai na ga saɓanin tunanina kai tsaye muka bar cikin unguwar, ya kunna ƙira'ar sheik Sudais a cikin rediyon motar. Wani gidan cin abinci muka je wajen shuru babu wani hayaniyar ɗaga hankali, wani teburin da aka tsara shi da wasu wutar kyandir muka zauna aka jere mana na'u'in kalolin abinci da abin sha a gaban mu. Cike da farin ciki muka ciyar da kanmu cike da tsantsar ƙaunar junarmu. "Har yanzu abin nan yana damunki ko?". Na jinjina kaina"ya riga da ya wuce ai tun kafin mu fito daga gida na riga da na mance shi". Kafin na ankara na ji hannunsa a bisa nawa na ɗago idona na sauƙe a fuskarsa, ya zame daga kan kujerar da yake ya tsuguna akan gwiwarsa a gabana. Cikin sanyin murya mai cike da taushi ya ce"Aisha ina son ki wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba don Allah ki kasance da ni har izuwa ƙarshen numfashina". Jikina gabana ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. "Na yarda da duk wani abunda zai fito daga bakinka. Ina sha Allah babu wani abinda zai raba mu sai dai ikon Allah". Ya kafe ni da ido na turo baki"don Allah ka tashi kaga mutane fa sai kallonmu suke yi". "To ni ina ruwana domin ni bana ganin kowa sai ke a idanuna". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo ya tashi ya koma kujerar da ya tashi. Mun yi hira sosai da hotuna a wajen babu adadi sannan muka baro waje, na jingina bayana a jikin kujerar motar ina faɗin"wash duk jikina ciwo yake yi mini". "Lalle kuwa! Gwara ma ki zage domin ba gida muka nufa ba". Da sauri na wartsake na buɗe idona tar a bisa titin tabbas ba hanyar gida ya nufa ba, na kallo shi"ina zamu je?". Sai da ya karya kwana sannan ya ce"ziyara". Ban ƙara cewa komai ba na ɗauki wayarsa dake kan cinyarsa na fara ganin hotunan da muka yi, ban ɗago kaina ba har sai da na ji ya faka motar ya fita ya zagayo ya buɗe mini na ƙi ɗago kaina na kalle shi. "Za ki fito ko in fito dake?". Da sauri na zaro ƙafata na fito ina cuno baki, ya wuce gaba ina biye dashi a baya. Muna shiga gidan wani mutum ya fito fuskarsa kamar gonar auduga suka gaisa da shi nima na gaishe ya amsa mini yana tafawa da Abdul-hameed ya ce"wato Madam ta ɓoye ka ko a office baka ganuwa". "Kai bari kawai Auwal". Ina biye dasu har cikin falon muka zauna yana faɗin bari ya yi wa matarsa magana, jim kaɗan suka fito na matar ta tsaya tana riƙe haɓa"uncle Abdul lalle kuwa wata sabon gani. Yau kai ne a gidanmu amarya ta ɓoye ka". "Haba Mamana ke ma shaidar da za ki yi min ke nan?". Ta nema waje kusa da mijinta ta zauna kana ta ce"to ai gaskiya ne shurun ya yi yawa jiya nake cikiyarka a wajen Daddyn Junior". Murmushi ya yi ya ce"tuba nake Mamana yanzu dai na wanke laifina don ga amarya na kawo miki". "Masha Allah Allahumma barik. Sannu da zuwa amarya". Na yi ƙasa da kaina ina faɗin"yauwa". Ruwa da abin taɓawa ta jere mana a gaban mu cikinmu a cike yake amma yanda ta nuna damuwa da matsawar cewar lalle sai mun ci ko kaɗan ne ya sanya mu san ruwan. Hirar wajen aiki Abdul-hameed suka ɓarke dashi da ya sanya ta miƙewa ta kamo hannuna tana cewa"ba ru mu ba ku waje su yi hirarku don ba fahimtar wannan yaren muke yi ba. Amarya tashi mu shiga daga ciki". Duk dariya suka saka kafin Abdul-hameed ya furta"ni kuwa ina Jinior na ji gidan shuru". "Yana can wajen Umma". Ta faɗa yayin da muke barin cikin falon muka shiga wani ɗaki muka zauna muka ƙara gaisawa kana ta cigaba da faɗin "abin mamaki wai yau uncle Abdul ne har da mata". Na rusunar da kaina ƙasa"kin san ikon Allah babu abinda ya bari kuma komai in lokacinsa ya yi dole za a yi sa". Ta gyara zamanta muna fuskantar juna"haka ne domin iko Allah ne kaɗai ya isa juya wannan lamarin". Na ɗago kaina fuskana ɗauke da mamakin furcin da ta na ce"ban gane inda kika dosa ba?". Ta numfasa kana ta ce"wallahi ba ni da wani mummunan nufi amma kin ga daga ni har mai gida da ragowar abokansu babu wanda ya yi tsammanin Abdul-hameed zai yi aure nan kusa. Abokansu babu wanda bai ajiye 'ya'ya ba, haihuwata na fari bai zo da raina ba na biyu kuwa sunan Abdul-hameed aka sanya muna ƙiran sa da Jinior". Na jinjina kaina"daman an ce aure da mutuwa lokaci gare su matuƙar ya yi babu makawa sai an yi su " Ta taɓe baki tare da cewa"haka ne, ki yi haƙuri da abinda zan faɗa miki yanzu Abdul-hameed har da ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya sun yi soyayya, Amma ta kafa musu ƙahon zuƙa sai da ta raba su yanzu haka tana gidan mijinta da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe. Shiyasa duk matan abokansu muka sha mamakin jin cewar ba 'yar uwarsa ya aura ba bamu yi tunanin Amma za ta bar shi ya auri wata daban ba". Duk da maganganunta sun yi mini nauyi a ƙirjina amma na yi ƙarfin halin ƙirƙiran murmushi na dasa a fuskata, cikin sanyi na furta"dama duk lalume muke yi a cikin duhu, Allah ya riga ya tsara komai ". "Tabbas haka ne gashi kin zama mai sa'ar samun uncle Abdul". Yanda ta yi zancen cikin zolaya ya tursasa mini sakin wani taƙaitaccen murmushin ina yin ƙasa da kaina. Daga haka ta canja zancen muka koma wani daban mun sha hira kamar mun san juna har album ɗin hotunan bikinsu da na sunan Junior ta nuna mini, sun yi bala'in kyau tufarkalla. Bamu baro gidan ba sai ƙarfe goman dare saura, Asiya matar Auwal ta cika mini leda shaƙe da kayan shafe shafe na mata mijinta ya ɗaura mini da naira dubu biyar, na yi godiya sosai da yabawa da karamci da mutuncinsu. Haka muka taho bayan Asiya ta yi miki alƙawarin kawo mini ziyara ta musamman muka yi musayar lambobin juna. Sanda muka iso gidan dare ta tsala don haka kai tsaye muka shige sashinmu muka ja ƙofa, daren ranar mun farantawa juna sosai na kuma sama yabo na bugawa a jarida daga wajen mijina. Washe gari koda muka isa sashin Amma muka tarar har sun gama yin karin kumallo. Daga gaisawar da muka yi mata ta amsa a daƙila ko kallon kirki ba ta ƙara yi mana ba har izuwa lokacin da ya ƙwala ƙiran Asabe ta zo da hanzari tare da zubewa a gabansa. "Ina abin karinmu fa?". Sai da ta saci kallon Amma kafin ta furta"uwargijiyata ba ta bada umarnin ɗaura girkin yau da ku ba". "Subhallahi!". Ya furta a razane yana cigaba da"me ya faru haka Amma?". "Hukunci ne na riga da na yanke tunda ka fi yarda da matarka fiye da kowa kana girka maka kawai kana ci hankalin kowa a kwance". "Wallahi ba haka nake nufi ba don Allah ki fahimc..." Da wani irin sauri ta dakatar dashi"babu abinda zaka ce na janye hukuncin da na riga na yanke. Sanin kan ne bana yin magana biyu, don haka zuwa anjima za a kai duk wani abun buƙata sashinka sai tana girka maka". Shuru ya yi tamkar wanda ruwa ya cinye shi ya ɗagawa Asabe hannu alamar ya sallame ta, shuru ya karaɗe girman falon sai can na furta"Allah ya huci zuciyarki Hajiya". Ban iya jin abinda ta furta ba sai dai tabbas na ga leɓanta ya yi motsi. Haka ya tafi wajen aiki kamar wanda aka yi wa mutuwa. Har fa cikin raina na ji daɗin wannan hukuncin da ta yanke ko babu komai nima zan sama 'yancin girkawa mijina abinda yake so a ko wani lokaci ba sai na jira an shigo mana dashi ba. Bayan ya tafi na ƙira Asiya muka gaisa na lura akwai ta da surutu ba na wasa ba, bayan sallan zuhr direba ya yi sallama na je na buɗe masa ya ce za a shigo da kaya. Na'u'in kayan abinci kusan komai an kawo sai da suka gama shigarwa na je na duba, ina cikin store ɗin na ji wayata na ruri a falo na fito da sauri. Kafin na iso ƙiran ya katse ban san dalilin tsintar kaina cikin matsanancin faɗuwar gaba ba ganin sunan Abdul-hameed ya fito cikin wayar. Na bi bayan ƙiran akalla kusan sau uku amma baya tafiya na ajiye wayar zan koma store ɗin, na ji ƙarar shigowar saƙon da ya sanya ni dawowa na buɗe. Da lambar Abdul-hameed aka turo saƙon da ya sanya ni zaman 'yan bori dirshan ina dafe ƙahon zuciyata tare da karanto saƙon a bayyane. "Aisha ki je gida sai na neme ki". *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________ Page 3️⃣3️⃣ Take na ji wani zuffa yana tsatstsafowa mini daga dukkan mafitar gashin dake jikina, jikina ya yi lajab da ruwa. Rawar da jikina ya soma yi ya sanya wayar faɗuwa daga hannuna. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'u!". Kawai na yi nasarar furtawa ina sauƙe gauruwan ajiyar zuciya mai matuƙar nauyin gaske, me yasa Abdul-hameed zai yi mini haka? Me na aikata masa? . Me ya faru bayan lafiya ƙalau salin ƙalin muka rabu dashi ya fita wajen aiki. Zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsikarawa matsilli na fito a zabure na nufi sashin Amma a riɗime. Anty Alawiyya kawai na iske a falon tana kallo ta bi ni da ido da yi mini alaman lafiya. Na yi ƙasa da kai na ce"Amma tana ciki ne?". "Lafiya?". Kamar na kurma ihu saboda Amman kawai nake da buƙatar gani a yanzu na amayar mata da zancen da yake sukan raina. "Ki haura sama tana ciki" bata gama rufe bakinta ba na bar wajen, a ƙofar ɗakin na tsaya ina ƙwanƙwasawa tun ina yi a hankali har na zage ƙarfina ina dukan ƙofar sai can ta amsa mini sallamar da nake kwaɗawa. Na shiga ɗakin kamar wacce aka jefo daga sama muka haɗa ido, da alama daga wanka ta fito don mai take murzawa a jikinta tana zaune a bakin gadonta. Na ƙariso na zauna na fara inda-inda, ta riga ni furta"Lafiya? Na gan ki duk a birkice?". Idanuna ya kawo ruwan ƙwalla muryata yana sarƙewa na ce"wani saƙo na ga ni da ya tada mini da hankali". "Wani kalan saƙo ne?". "Saƙo ne aka turo mini da lambar Abdul-hameed cewar wai na je gida sai ya neme ni. Na ƙira layinsa don ji daga gare shi wayarsa ba ta tafiya, na san baya aiwatar da komai ba tare da sanin ki ba shiyasa na zo na tambaye ki sahihacin saƙon". Ban tsinci komai a fuskantar ta hasalima biris da yi da ni duk da muhimmancin zancen da na zo mata dashi, sai can a gajarce ta furta mini"na ga saƙon". Na laluma jikina babu waya sai a lokacin na tuna tsabar rikicewar da na yi na mance wayar a falo ban fito da ita ba. A hankali na furta"na bar wayar a falo bari na je na ɗauko". Ban ɓatawa kaina lokaci wajen jiran amsarta ba domin ban yi tunanin samun sa daga gare ta ba, na miƙe har na kai ƙofar fita na ji ta furta"Aisha ki sama mai nutsuwa" kaina kawai na ɗaga mata na fito ina yi kiciɓus da Anty Alawiyya tana shigowa, da gudu-gudu na isa sashina na ɗauko wayar na fito. Jikina har rawa yake yi na miƙa mata wayar ta sanya hannu ta amsa tana karanta saƙon a bayyane. Ban ankara ba na ji wasu hawaye masu zafi su na gudun famfalaƙi a bisa dandamalin kuncina, sai da ta _kammala tsaf ta sauƙe numfashi kana ta ce"to yanzu me kike so daga gare ni?". Na kai hannu na share hawayen fuskana kafin na sama damar faɗin"na ƙira wayansa ba ya tafiya ne ko za ki ƙira shi". "Babu abinda zan iya yi akan wannan lamarin Aisha, na yanke hukuncin zare hannuna daga lamarin aurenku. Abdul-hameed mijinki ne kuma yana da ikon zartar da duk wani hukunci game da lamarin gidansa. Indai za ki ji shawaran da zan ba ki to kawai ki tafi tunda ya shi ya nema hakan, ko dan jan mutunci da darajarki". Ban san sanda wani gigitaccen kuka ya kubce mini ba na kai hannuna na toshe bakina. Babu wanda ya ce dani ci kanki a cikin su har na yi mai isa ta na tsagaita don kaina na miƙe ina jin wani jiri yana ƙoƙarin maida ni ƙasa. "Na gode, idan na aikata miki wani abu da ya ɓata miki a tsawon zaman da muka yi. Ina neman yafiyarki". Ta ɗago idanunta ta kalle"babu abinda kika yi min". Ta ƙare zancen tana miƙo mini wayata dake hannunta na karɓa na fice, ina isa sashina na zube a ƙasa ina jin wani irin zafi a cikin zuciyata. Kamar mahaukaciya haka na dunga ƙiran layin Abdul-hameed amma baya shiga dole na haƙura na ajiye wayar. Na shiga ɗakina ina bin ɗakin da kallo da tunanin yanda zan tunkari iyaye da wannan lamarin mai girman gaske, zancen Baffa ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu na dafe ƙirjina hawaye suna zubowa daga idona. Hamma Ahmad shi ya fara faɗo mini a rai na zabura na ɗauki wayata na danna masa ƙira. Har ƙiran ya katse mai ɗauka ba ina shirin danna masa ƙiran a karo na biyu ƙiransa ya shigo wayata da sauri na ɗauka ina jin muryarsa na fara kuka. "Subhallahi! Aishatu lafiya? Me ya faru?". Na kasa cewa komai jin hanyar wuyata nake yi kamar an sanya igiyar kirtani an zarge mini wuyata, sai da na fizgo numfashina kafin na sama zarafin faɗin"kana gida ki kasuwa?". "Ina kasuwa amma lafiya?". "Su Baffa fa?". Muryarsa fal da damuwa ya ce da ni"daga ni sai Adnan". "Ga ni nan zuwa". Na faɗa wani kukan yana ƙara yunƙuro mini dole ba kashe wayar na ci kuka har na godewa Allahna, har aka fara ƙiran sallan Asr ina durƙushe a wajen. Na ƙyar na iya miƙewa akan ƙafata na sauƙo da ƙaramin akwatin laifena na zuba kayana, dubu biyar da jiya mijin Asiya ya ba ni da su na yi amfani na hau abin hawa na isa kasuwa. Na nufi shagon su Hamma Ahmad ban iske kowa a shagon ba na yi sallama a wani dake kusa da wajen na tambaye shi ya ce sun tafi masallaci sun ce idan na iso na shiga na jira su. Na yi masa godiya na shiga na zauna. Jin ana ƙwala ƙiran sunana da ƙarfi shi ya dawo da ni izuwa duniyar zahiri daga na tunanin da na lula, na sauƙe sakekken ajiyar zuciya ina ɗauke idona daga kallo ɗaya da na yiwa fuskar Hamma Adnan. Sai da suka zauna Hamma Ahmad ya ce"lafiya me ya faru? Tunda kika ƙira ni hankalina ya kasa kwanciya sai saƙe-saƙe nake yi". Ya ƙare zancen yana tsayar da idonsa akan akwatin kayana dake kusa da ni. "Magana fa ake yi miki". Hamma Adnan ya furta da hakan ya sanya ni yi ƙasa da kaina ina faɗin"cewa ya yi wai na taho gida". "A wani dalilin? Me kika aikata masa? Wani laifi kika yi masa da zai ce ki taho gida?. Ko takardarki ya ba ki?". Ya jere ya watsa mini tambayoyin na girgiza masa kaina ina ɗaurawa da" saƙo ya turo mini ta cikin waya, na ƙira layinsa ya fi a irga baya tafiya. Na sanar da mahaifiyarsa ta ce babu abinda da za iya yi akai kawai na tafi ɗin". Duk suka yi shuru na tsawon wasu daƙiƙu kafin Hamma Adnan ya furta" da ta ce ki taho kuma da yake ke shashasha ce sai kika ɗauko ƙafa kika kwaso kaya kika taho ko?. Ai tsayawa za ki yi ki jira shi ya dawo cikin gidan ki ji daga bakinsa". Ya ƙarƙare yana fiddo wayarsa daga aljihunsa ya shiga dannawa layin Abdul-hameed ƙira, ya ƙira ya fi sau goma layin ba ta tafiya ya ajiye wayar tare da cewa"na ƙira ba ta tafiya amma zan ƙara gwadawa zuwa anjima. Ahmad yanzu me ye abin yi ka yi shuru baka ce komai ba". Ina iya jiyo sautin da ajiyar zuciyar da ya sauƙe ya bada kafin ya furta"ai na rasa abinda zan ce ne, amma tabbas kin yi wauta da kika taho ba tare da kin ji ta bakinsa ba. Dole yanzu za ki koma mu zauna dashi sai mu tattaunawa". Wasu hawayen masu ɗumi suka gangaro daga idona"baya dawowa Sai bayan sallan magrib ko mun je yanzu ba lalle bane mu same shi". "Shikenan yanzu ki tashi ki je gida wajen Abida inda mun tashi daga kasuwa zamu biyo ta can". Hamma Adnan ya furta cike da taushi cikin kalamansa. Kaina kawai na ɗaga masa ya zaro Naira ɗari biyar ya ajiye mini akan cinyata, a sanyaye na ce"akwai kuɗi a wajena". Bai ce da ni uffan ba amma kallon da ya yi mini kaɗai ya isa na fahimta nufinsa. Har cikin kasuwar Hamma Ahmad ya sanya yaron shagon ya taro mini adaidaita na hau ya kai ni gidan Adda Abida. Tana wanke shinkafar tuwo na iske ta, fara'ar dake bisa fuskarta da ta juyo dashi ya rikiɗe izuwa mamaki ganina da ta yi da akwatin kaya a hannu. "Lafiya na gan ki da wannan kayan?". Ban ce da ita komai ba sai da na nema waje na zauna na ce"zan yi miki bayani amma yanzu bari na fara yin salla". Na tashi na ɗauki bota na yi alwala na shiga ɗakinta na gabatar da sallan Asr na daɗe ina addu'ar samun mafita da makarin warware wannan ƙullin da ya cakuɗe mini kafin na shafa addu'ar, dai dai lokacin da sallamar Adda Abida ya ratso kunnuwana. Ta zauna tare da kafe ni da ido"me yake faruwa ne? Ina shi Abdul-hameed ɗin?". Na cije leɓena na sanar da ita komai, ta riƙe baki cike da takaici ta soma cewa"lalle wannan lamarin akwai ɗaure kai matuƙa, amma kuwa ita ma uwar tashin ba ta san dattaku ba. Yanzu idan 'yarta ce zata so haka ya kasancewa da ita ne da har za ta ce babu abinda za ta iya yi a kai, yanzu ki zauna ki jira dawowar nasun sai mu ga abinda halin zai yi". Kaina kawai na gyaɗa mata. Ta fice ta bar ni na kasa taɓuka komai illa tunanin da na yi nisan kiwo a cikinsa. Zuciyata zafi take yi mini tamkar ana watsa mini garwashin wuta na tisa wayata a gaba ina kallon saƙon hawayen suna tsere a idona. Har aka yi sallan magrib ban tashi daga wajen ba Adda Abida ta zo ta iske ni a yanda ta fi ce ta bar ni. "Aishatu haƙuri za ki yi kar ki je ki ɗaurawa kanki wata damuwar akan namijin da uwarsa ma ba ta damu dake ba. Ake samun mutuwar aure ma kuma a cigaba da rayuwa kamar babu wani abun da ya taɓa faruwa balle kai da gida kawai ya ce ki zo. Ki tashi ki ci abinci sai kin yi wanka kafin su iso". Na haɗiye miyau da ƙyar ya wuce ta cikin bushashshen maƙoshina "Adda wallahi ni kam ko yunwar ma bana jin ta, zan yi salla kawai na jira isowar su". A fusace ta furta mini"za ki kashe kanki Aishatu za ki ɗaurawa kanki hawan jini a banza da wofi idan akan namiji ne wallahi. Ki tashi ki yi abinda na ce dake tun na saɓa miki". Ba ni da zaɓi face aiwatar da umarninta dole na tashi na ɗeba ruwa na je na yi wanka sai da na ɗauro alwala sannan na shiga ɗaki na yi salla, na caccakala abincin da ta ajiye mini a gabana ina wanko hannuna na dawo ɗakin ko zama ban yi ba na ji sallamar su Hamma Ahmad. Gaba ya yi ras. Adda Abida ta yi musu sannu da zuwa tare da shimfiɗa musu tabarma ina hangen su daga inda nake laɓe a bayan labulen ɗakin. Suka ce a ƙira ni na yi saurin komawa na zauna Adda Abida ta ɗago labulen ta ce na fito. Na fito na zauna tare da yi musu sannu da zuwa, Hamma Adnan ya buƙaci da na nuna musu saƙon da na ce ya turo mini ɗin na miƙa musu wayata suka gani. "Na ƙira wayarsa har shugowarmu cikin gidan nan amma baya ɗauka, ba zamu sako Baffa cikin wannan lamarin ba domin ina da tabbacin cewar ba ki mance yanda kuka yi dashi ba". Take jikina ya mutu murus komai ya fice fit daga raina. Hamma Ahmad ya ɗaura da faɗin"kin tabbatar cewa kuma babu wani abunda kika yi masa?". Na gyaɗa masa kaina ya cigaba da"shikenan ki zauna a nan ki kwana zuwa gobe sai mu je can gidan mu same shi, kafin nan Abubakar ma ya iso. Ina fatan dai babu wata matsalar ko?". Ni kuwa nake da tarin matsaloli ma ba matsala ba, na furta a cikin raina a zahiri kuwa cewa na yi"babu wata matsala". Da haka suka sallame ni, ko da dare ya tsala na kasa runtsawa ban yi tunanin za a kai har wannan lokacin bai neme ni a waya ba sai gashi abin yana nema zarce tunanina. Na kasa yin hawayen illa soyar da zuciyata take yi mini furcin Baffa na cewar ko yankan namar jikina Abdul-hameed yake yi kar na kuskura na zo gida da sunan yaji ko kawo ƙara sai yawo suke yi mini a cikin kwanyata *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 3️⃣4️⃣ Yanda na ga rana haka na ga dare idanuna ƙas tamkar na soyayyan kifi na kasa runtsawa. Akan sallaya Adda Abida ta zo ta iske ni bayan na iddar da sallan asubahi, na gaishe ta cikin harshen fulanci ta amsa mini cike da kulawa kana ta furta " ba ki yi bacci ba daren jiya ko?". Na sunkuyar da kaina"na kasa yi ne". Sai da ta yi jim kafin ta ce"ya kamata izuwa yanzu ki nemawa kanki mafita akan waɗannan abubuwan da suke faruwa. Na yarda kina son Abdul-hameed amma fa wani lokacin ki dunga nemawa kanki 'yancin, ƙiyayyar uwar miji da danginsa wallahi ba ƙaramin bala'i yake haifarwa ba ko da kuwa kin yi dacen samun miji mai ƙaunarki". Ban ce da ita komai ba illa laƙwashe ƙafafuna da na yi waje guda ina sauraron zancen da ta ɗaura dashi. "Idan kika koma ɗakinki ki yi duk wani mai yiyuwa wajen fito da maƙircin 'yan uwansa a fili ya gani kuma ya shaida". "Adda ni ba su bane a gabana, tunda na tabbatar da cewar mijina yana sona ai shikenan". Riƙe haɓa ta yi cike da mamaki"haka da yawan mata suke ɗauka amma in har ba ka yi dacen dangin miji ba to wallahi ba kya taɓa jin daɗin zaman aure, ko haihuwa kika yi ƙiyayyar nan sai ta shafi 'ya'yanki" A bayyane na sauƙe wata shirgegiyar ajiyar zuciya mai nauyin gaske kana na sama damar faɗin"ganin nake yi kamar bijirewa zaɓin su Baffa a gare ni shine musabbabin faruwar waɗannan abubuw..." Da sauri ta kai hannunta ta toshe mini baki tana cewa da ni"har ki ce haka domin wani baya taɓa auran matar wani, kuma ai matar mutum kabarinsa". Haka ta yi ta lallashina gami da kwantar mini da hankali da daɗaɗan kalamai masu taushi, sai da muka yi karin kumallo sannan Adda Abida ta ce na fito ga Hamma Abubakar ya iso, duk su ukun suna zaune a bisa tabarma na iske su na gaishe da su suka amsa mini a tare. "Me yake faruwa tsakaninki da mijinki?". Hamma Abubakar ya jefa mini tambayar muryarsa a kaurare. Ban yi ƙwauron baki ba a feɗe masa biri har wutsiyarsa, ya jinjina kansa"ƙira wayarsa yanzu". Na dannawa lambarsa ƙira amma ba ya tafiya har yanzu. "Ɗauko kayanki ki fito ki tafi, ki jira shi ya dawo ko bangon duniya yaje shi ya dawo. Ya sanar dake dalilin cewa ki zo gida da ya yi. Idan kuma sakinki ya yi sai ya sanar". Furcin Hamma Abubakar ke nan cikin ƙololuwar ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a cikin muryarsa, Hamma Ahmad ne ya amshe zancen da faɗin"ya dai kamata mu jira zuwansa tukunna mu ji ta bakinsa kafin ta koma". "Ba za ta zauna ba ko ka manta furcin da Baffa ya yi ne akan auransu?. Ta koma idan har sakinta ya yi ya bata takardarta a wannan sa'in sai da ta dawo ". Wasu hawayen da nake jin sauƙar su a bisa fatana tamkar tafashashshen ruwan dalma suka shiga wanke mini fuska , na gaza cewa uffan saboda yanda haƙwarana suka datse harshena. Na tashi na shiga ɗaki na ɗauko akwatina na yi wa Adda Abida sallama muka tafi. Tare da Hamma Ahmad da Hamma Abubakar muka je gidan, gabana yana tsananta bugu na yi sallama a ƙofar falon Amma. Aka amsa tare da bada iznin shigowa ni na fara shiga duk suka zubo mini idanu tamkar sun ga wani baƙuwar halitta. Na rusuna na gaishe da Amma ba ta amsa mini illa kallon mamakin da ta cigaba da bi na dashi har izuwa lokacin da na ce "tare nake da yayuna suna son magana dake". "Su na ina?". Ta faɗa a gadarance, na yi ƙasa da idona kafin na ce"su na waje". Da ido ta yi mini alama akan su shigo na fito na yi musu iso, ta sallame kowa daga mu sai ita. Hamma Abubakar ya musguta tare da cewar"Hajiya mun zo ne mu ji dalilin tura ta gida da Abdul-hameed ya yi, kuma mun neme sa a waya ba ma samun sa shiyasa muka ɗauko ta muka dawo da ita". Gabana ya tsananta bugu saboda banzan da Amma ta yi masa. Na san Hamma Abubakar da zafin zuciya da saurin fusata. Muka haɗa ido dashi na yi saurin janye nawa. Sai can ta ce"nima bai sanar da ni dalilinsa na yin hakan ba amma za ku iya jiran dawowarsa sai ku tattauna dashi". A wannan karon Hamma Ahmad ne ya yi magana"zamu je mu dawo, domin dole mun zauna dashi. Ita dai yanzu za ta koma ɗakinta". Kafaɗarta ta ɗage musu alamar duk yanda suka yi dai-dai ne, sallama suka yi mata domin ko kaɗan ta ƙi basu fuskar tattauna wani zance da ita game da lamarin balle har a sama hanyar da za a ɗinke ɓarakar. Sai da muka fita Hamma Adnan ya sauƙe numfashi kafin ya ce"anya ba zamu tafi da yarinyar nan ba kuwa? Mu jira har sai ya zo don mu ga gudun ruwansa". "Haka ne amma dole ce za ta samu mu bar ta nan, domin idan har wannan labarin ya iske kunnuwan Baffa to duk ranmu sai ya ɓaci. Ki yi haƙuri ki shiga ki zauna in sha Allah zamu yi magana dashi kin ji?". Jikina a mace na ɗaga masa kaina ina jin wasu hawayen su na ciko mini koramar idanuna. Nasiha su ka ɗan yi mini kafin suka tafi tare da yi mini gargaɗin duk abinda ya ƙara faruwa nan gaba, kafin na bar gidan na sanar dasu a waya tukunna. Haka suka tafi suka bar ni raina cike da zulumi, na ja saƙararrun ƙafafuna na koma sashina yana nan kamar yanda na bar shi wanka na fara yi na gyara ɗakina tare da mayar da kayan da na zuba cikin akwatin. Na zauna na zabga tagumi cike da rashin sanin matsayin aurena a halin yanzu. Firgitit na dawo cikin hayyacina saboda rurin da wayata ta soma yi, da azama na ɗauko ta ganin sunan Asiya ya bayyana cikin screen ɗin wayar ya sa ni furzar da iska daga bakina domin na yi zaton Abdul-hameed ne. A hankali na yi sallama ta amsa mini muka gaisa kana ta ce"ya ke ma na ji muryarki wani kala yanzu mijinki ma ya bar gidan nan shi ma kamar marar lafiya". "Mijina? Abdul-hameed ke nan fa ?". Na faɗa da wani irin sauri har ina nema zamewa daga kan kujerar da nake zaune. "E shi fa yanzu suka fita da Auwal. Ya zo ya ce yana buƙata na nema miki 'yar aiki wacce za ta taya ki aikace-aikace". Na taune leɓena da ƙarfi tamkar ba namar jikina ba, sai da na fizgo numfashina da ƙarfi na sama lasisin faɗin"to fa sai ki samo mana mai nutsuwa". Sai da ta dara sosai ta ce"irin wannan kashedin dai shi ma ya yi ta yi min, in sha Allah zan nema miki ko a cikin yaran maƙota da suke shigo min. Idan an samu zan sanar dake". "To godiya muke mun haɗa ki da aiki. Ina mai sunan mu fa?". "Yana can wajen su Umma". Saƙon gaisuwata na bayar gare sa sosai kafin muka yi sallama. Na manne wayar a ƙirjina na so na tambaye ta ƙarin haske game da yanayin da yake ciki sai na gudun kar ta zargi wani abu. Wuni na yi ina sarƙa da warwara cikin raina na kasa assala komai har aka yi sallan magrib. Ina ta tsumayin ƙiran su Hamma Abubakar amma su ma shuru kamar an shuka dosa kunya ni kuwa ta hani na ƙira su na tambaye su yaya ake ciki. Ina zaune kan sallaya bayan na gama iddar da sallan isha'i na ji ƙarar shigowar motarsa kamar zan kife akan hancina na tashi na tsaya ta jikin taga ina leƙansa. Ya yi fakin ɗin motar ya fito sannan ya zagayo ta kujerar mai zaman banzan ya ɗauko jakarsa, na ƙara ware idona akan sa domin kamar tun kayan jiya da fita dashi har yanzu shi ne a jikinsa. Har sai da ya ɓacewa ganina ya shige sashin Amma sannan na bar wajen na koma na zauna. Ban yi tsammanin shigowarsa nan kusa ba don haka na yi zama na a ɗaki raina duk a jagule. Kamar an ce ɗaga kanki ina ɗagowa idanuna suka sauƙa akan fuskar idanunsa ƙar a kaina ya naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa. Na gyara zamana domin ko kaɗan ban ji ƙarar buɗe ƙofar ba balle motsin shigowarsa. Duk takun da zai yi yana ƙara matso ni sai bugun zuciyata ya tsananta fiye da kima da tunani.Ya yi wani tsuguno mai ban sha'awa akan ƙafarsa a gabana yana ƙawata fuskarsa da annurin da ya sanya mamaki bayyana a bisa razananniyar fuskata "Afuwan tafiya ce ta kama ni ta gaggawa a wajen aiki kuma inda muka je babu network ba zan iya ƙira ko amsa ƙira ba". "Ta-ta-tafiya kuma?". Na furta kalmar a rarrabe tamkar mai koyan magana. Ya ɗaga mini kansa"ƙwarai kuwa akwai wasu NGO da suka ɗauki nauyin ginawa waɗanda iftila'in ambaliyan ruwa ya rutsa da su a cikin Borno. Sun kawo aikin ofishinmu shi ne aka wakilta ni nake na ga wajen. Motata ta sama matsala sai da Auwal ya ɗauko ni aka gyara sannan na dawo". Na ji wani sanyin daɗin ya ziyarci sashin ruhina, na saki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ina jin raina saƙayau. A raunane na ce"na ga saƙon da ka turo mini hankalina gabaɗaya ya tashi na ƙira wayanka kuma ba ya tafiya. Har su Hamma su ma sun jarraba amma ba ya shiga". Da mamakina sai na ga ya waro idanunsa waje alamar mamakin zancena yake yi ya ce"wani irin saƙo?". Ma galla masa harara ina ƙarawa da watsa masa kallon uku saura kwata. Na ɗauki wayata dake kusa da ni na shiga wajen saƙon na haska masa a idonsa. Ya karɓa ya karanta bai ce komai sai da ya zame daga tsugunan da ya yi ya zauna dirshan. Ya ɗago idanunsa da suka sauya launi ya zube su a fuskana"yawan rantsuwa bai kasance daga cikin halayyata ba, amma na rantse miki da Sarkin da bashi da abokin tarayya ba ni da masani game da wannan saƙon. Ban tura ko wani irin saƙo da wayata ba hasalima a mota na bar wayata da wayar wajen aiki nake amfani har na je na dawo". Na ɗaga masa hannuna alamar ya dakata mini haka nan"lambarka ce fa aka turo saƙon dashi kuma ka ce baka da masaniya akan saƙon". "Wallahi ban san yaushe aka turo ba ban kuma san waye ya turo ba ki yarda da ni". Na kasa cewa komai don ya gama ɗaure ni da jijiyar jikina, sai da na karɓa wayata na miƙe tsaye idanuna taf da hawaye na ce"ka ƙira Hamma Abubakar dashi za ku yi magana". Ina dasa aya na shige ɗakina fu na ja ƙofar na rufe. Na jingina a jikin ƙofar ina sauraron bugun da zuciyata yake yi tamkar zai ɓallo allon ƙirjina ya fito waje ya daka rawar disko. Na daɗe a haka kafin na fara sulalewa izuwa ƙasa dai-dai lokacin da wayata ta soma ruri ba tare da na duba mai ƙira na ba ɗaga tare kara wayar a kunnena. "Aishatu kina ji na?". Na ji muryar Hamma Abubakar daga ɗayan ɓangaren sun yi dirar mikiya a kunnuwana. "Ina ji Hamma". "Yanzu mun yi magana da mijinki abin mamaki ya yi min rantsu da abinda zai kashe shi cewar ba shi ya turo wannan saƙon ba kuma bai san wanda ya turo ba". Hawayen idanuna suka zubo na share su kafin na furta "haka nima yanzu yake shaida mini amma zuciyata ba ta nutsu da hakan ba". Ya yi shuru kamar mai nazarin wani abu kafin ya ce"kar ki damu tunda ya ce bai aikata ba shikenan a bar shi a hakan. Ki yi haƙuri ki manta komai ki nuna mana kema daga ɓangarenki komai ya wuce, sannan Aishatu ki dade da addu'a tabbas akwai wata ƁOYAYYAR MANUFA na Ubangiji a cikin aurenki da Abdul-hameed ". Jikina babu kuzari gabaɗaya na amsa da"in sha Allah Hamma na gode Allah ya bar zumunci". "Amin amin ". Da haka muka yi sallama yana ta nanata mini kalmar na dage da kai kukana ga Allah. Na zame wayar daga kunnena zuciyata cike da mamakin wannan abin al'ajabin da ya fi yi mini kama da almara. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________ Page 3️⃣5️⃣ Na yi iya ƙoƙarin danne komai tare da mance komai, ta hanyar nuna masa cewar komai ya wuce. Sai dai cikin raina na ƙudurce sai na gano abin da yake wakana a cikin ƙasa, ba zan taɓa samun nutsuwa ba kuma ba zan taɓa fita daga zulumi ba sai na gano wanda ya turo mini wannan saƙo da layin Abdul-hameed. Kwanaki biyu tsakani Asiya ta ƙira ni ta ce an sama yar aiki, za ta taho mini da ita na gan ta idan ta yi mini. Bayan sallan zuhur kuwa sai ga ta ƙira ta ina ɗagawa ta sanar da ni cewar ga ta a bakin gate. Na yafa mayafina na fito na shigo da ita. "Sannu da zuwa kin ɗebo rana". Na faɗa ina miƙa mata kofin da na tsiyaya mata ruwan sanyi, ta karɓa tana faɗin"wallahi akwai rana kam". Ta kai kofin bakinta ta sha kusan rabin ruwan sannan ta ajiye. "Ga ta na cika alƙawari na kawo miki ita har gida". Sai a lokacin na bi natashiyar yarinyar dake zaune kusa da ita tana riƙe da Junior"masha Allah ai kuwa muna godiya, in ce dai kin san ta kin kuma san iyayenta?. Don kin san yanzu duniya ta lalace ". Sai da ta murmusa ta furta"ai sai da na yi bincike sosai, 'yar maƙwabtarmu ce. Ba ta da matsala idan kin zauna da ita za ki ba ni labari". Na jinjina kaina ina tsayar da ido akan yarinyar"sannu baiwar Allah yaya sunanki?". "Amira". Zancen da Asiya ta ɗaura dashi ya katse mini hanzari"ya ce ba kwana za ta yi ba ma ai, zuwa da komawa ne". A bakinta na ji hakan domin bamu tattaunawa dashi akan hakan ba. Na miƙawa Junior ya maƙe kafaɗa alamar ba zai zo ba. Wasu tambayoyi na yi wa Amira ta amsa mini su tsaf, na lura yarinyar tana da nutsuwa sosai da kuma hankali. Na tashi na ɗora girki farar shinkafa na yi da miya, na zubo mana muna ci. Ansar suka shigo kallo ɗaya na yi musu na mayar da hankalina ga abincin dake gabana domin ko basu furta ba na san abin da yake tafe dasu. Umarnin Amma su ka zo aiwatarwa na duba Abdul -hameed yana nan ko ya fita, ba su ce da ni uffan ba haka nan ban ga suna da niyyar gaisar da Asiya ba, sai faman zazzare idanu suke yi tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya. "Waɗanda fa Aisha? Wani abun suke nema ne?". Na kora ruwa sannan na amsa mata da faɗin" 'ya'yan yayarsa ce". "Shine kika bar su suna faɗo miki falo haka? Yo ai ko ɗakin uwarka ne zaka shiga za ka yi alamar a san da shigowarka balle nan, kuma ba su iya gaisuwa ba sai zazzare idanu a mutane". Na yi ƙasa da kaina tare da cewa"kin san kowa da irin yanayin ƙuruciyarsa". Da sauri ta katse ni"wani irin ƙuruciya? Rashin kwaɓa da tsawatarwa dai". Na ɗago ina kallonta"kin ga don Allah Asiya ki rufa mini asiri, mu bar maganan nan haka nan. Yanzu sai su ɗeba su kaiwa Amma wannan zancen abu ya zama babba". Cak ta ajiye cokalin dake hannunta fuskarta ɗauke da maɗaukakiyar mamakin ta ce"waɗannan? To ki yarda kawai koya musu haka aka yi babu wani ƙuruciya. Wallahi fuska suka samu shiyasa suka miƙe ƙafafu har da samun damar yin sanya, tun wuri ki taka musu burki me ye haka?". Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina gyara zamana kafin na ce"ba za ki gane bane, amma barin su da nayi ɗin shi ne akwai mafita a gare ni". A bayyane ta tsirtar da tsaki mai dogon zango tana cewa"tun ice yana ɗanye ake lanƙwasa shi idan ya bushe sai dai a karya shi. Ai yanda kika ɗaura su akan hakan zasu ɗaure". Shuru na yi mata da hakan ya bata lasisin cigaba da faɗin"kin ganni ina da baki da kuma surutu amma sam ba ni da munafurci. Iya gaskiyar abin da ke a cikin raina nake faɗa. Ba na wani ƙunbiya-ƙunbiya. Da Allah ya ƙaddara Azinatu ce a cikin gidan nan a matsayin matar Abdul wallahi da sai mun mayar da Amma kan kashinta". Ban bar ta ta dire zancen ba na yi saurin kai hannuna na rufe mata bakina. "Kin ga don Allah mu bar maganar nan haka nan. Amma dai kamar uwa take a gare ni, yanda zan yi haƙuri na jure duk wasu halayyar ytawa uwar ita ma haka zan yi haƙuri da na ta". Wani kallo da na yi mini na ba ki san abin da kike yi kana ta ce"shikenan tunda haka kika ce, amma ina tabbatar miki wataran da kanki za ki ɗaga waya ki ƙira ni ina neman shawarata ". Murmushi kawai na yi mata muka cigaba da cin abincin na tattare kwanukan, lokacin su Ansar suka fice. Alawala suka yi sannan na shimfiɗa musu sallaya suka yi sallan Asr sannan suka fara haramar tafiya. Fitowarmu ya yi dai-dai da fitowar Amma da Al'amin daga cikin lambun dake kusa da sashin na tan. Muka ƙarisa Asiya ta gaishe ta, ta amsa fuska babu annuri, har bakin gate na yi mata rakiya sannan na koma. Ko zama ban yi ba Ansar yana faɗin wai Amma na ƙira na, na rasa dalilin da a duk lokacin da aka isar mini da saƙon Amma nake tsintar kaina a cikin matsanancin faɗuwar gaba ba. Yana gaba ina biye dashi har cikin falonta, na yi wa kaina mazauni tare da yi mata sannu. Kallon da ta tsura mini ya sanya hantar cikina kaɗawa na yi saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. Muryarta a kaurare ya sauƙa a na'urar naɗar sautina. "Kamar Asiys matar Auwal na ga kun fito tare ko?". Na gyaɗa mata kaina. "Ciwo bakinki yake yi da ba za ki yi amsa min ba?". Da rawar jiki na ce"e ita ce". "Daman tun can kun san juna da ita ne?". Na jijjiga kaina haɗe da cewa"a'a ranan nan ne muke kai musu ziyara tare dashi". Ta yi shuru babu alamar za ta amsa mini sai da na gaji da zama na ji duk ƙafafuna sun sake kana ta ce da ni"to ki kasa kunne ki saurare ni da kyau daga yau na datse duk wani mu'amalar dake tsakaninku da ita. Da kin san wacece Asiya da ba za ki yi marmarin kusantar inda take ba balle haɗa inuwa ɗaya da ita". Cike da tsoro na ɗago kaina"wani halin take dashi Amma?". "Ta so haɗa ƙanwarta da Abdul ta hanyar cusa masa ita ta ƙarfi da ya ji. Sai na tashi akan ƙafana sannan na raba su, idan kika sake mata kina nan zaune za ta ɗaura ki a keken ɓeran da zai yi sanadin fitar ki daga cikin gidan nan. Ƙanwarta ta maye gurbinki". Na sauƙe numfashi mai ƙarfi "zan kiyaye in sha Allah na gode". Hannu kawai ta ɗaga mini da ke alamta mini cewar ta sallame ni. Na koma sashina na kwanta ina bitar zantukanta. Ko da Abdul-hameed ya dawo na sanar dashi zuwan Asiya da abin da ke tafe da ta, ya ce idan yarinyar ta yi mini to babu matsala ko gobe sai ta fara zuwa aikin. Ni dai kam na yaba da nutsuwar Amira don haka na sanar da Asiya cewar za ta iya fara zuwa aikin. Ta fara aikinta za ta zo ta wuni da yamma ta koma, mun shaƙu sosai da ita domin sam ba ta da wani matsala duk a shekaru zamu iya karawa da ita. Amma ko bisa kuskure ba ta taɓa ƙiran sunana kai tsaye ba tare da ta maƙala mini kalmar Anty ba. Mun yi zaman wata biyu cur da ita babu wani abun da ya taɓa shiga tsakaninmu. A lokacin aurenmu ya cika watanni goma cur, bana mance wani yammacin da na fito zan shiga sashin Amma, a harabar gidan na hange Anty Alawiyya zaune da wani su na zance. Kallo ɗaya na yi musu shi ma ya kasance a bisa kuskure ne na ɗauke kaina raina cike da takaici, wai da aurenka kana sauraron wani daban. Babu kowa a falon sai su Ansar su na guje-gujensu su na tambaye su Amma su ka ce ta shiga ɗaki tana fitowa, waje na nema na zauna ina latsa wayata ina kallon hotunan da muka yi a gidan cin abincin nan. Ansar ya zo ya ɓoye a bayana yana faɗin"ki cewa Aysar ya bar min abu na". "Me ye abun?". Na faɗa ina ajiye wayar hannuna ya miƙo mini SIM ya ce"ga shi tsinta na yi wai ya ce na shi ne". "Idan an tsinta abu ai neman me shi ake yi, ka kai wa Ummanka in ta shigo sai ta nema mai shi ko?". "A shara fa na samu, ba mai amfani bane". Ya gatsalo mini zancen a kwaɓe, na yi murmushin takaici da tausayin gurɓataccen tarbiyyar da aka ɗora su a kai. Na karɓa na cire SIM ɗina na sanya wanda na karɓan a ciki. Ma'ajiyar lambobi na shiga babu komai sai mu number na latsa, lambobin da suka bayyana ya tursasa mini ƙara ware idona sosai. Lambar Abdul-hameed ce ta bayyana na fita na ƙara shiga don tabbatar da abin da nake gani. Tabbas shi ɗin ne na fara jeranta lambana zan ƙira na tuna cewar na cire SIM ɗin, wata dabarar turawa kaina saƙo ya faɗo mini na rubuta sallama na tura a layina. Na cire wannan na mayar da nawa ina kunna saƙon ne ya fara shigowa ga lambar Abdul-hameed ɓaro-ɓaro ya bayyana fau. Na dafe ƙirjina babu shiri ina ji tamkar zai tarwatse na saci kallon su Ansar na ga duk sun zuba mini na jiyamu. Na saisaita nutsuwata kafin na ce "ka ce a ina ka sama wannan layin?". "A cikin shara na samu". "Ka daina ɗaukar abu a cikin shara babu kyau, zan jefa dashi. Na yi maka alƙawarin idan uncle Abdul ya dawo zan ce ya kai ka siyayya ya sayo muku wasu kayan wasan masu yawa" . Banza duk suka yi da ni kamar basu yi na'am da zancen nawan ba, sai da na ƙara maimaitawa a karo na biyu cikin tashin murya kafin Aysar ya ce"ni kam na yarda". "Nima na yarda amma na wa zai yi na Aysar yawa ko?". Da sauri na furta "ai ko girma ma ka fi shi dole naka ya fi nashi yawa, amma fa idan kuka faɗawa Amma ko Mommyku cewar kun tsinci SIM a cikin shara zasu yi muku faɗa. Kuma Amma ta ce babu inda za ku je siyayyan". "Na kulle bakina". Suka furta a tare, na sauƙe wahalallen ajiyar zuciya. Da haka muka rabu dasu suka fice waje. Har Amma ta fito na gaishe ta na baro sashin ban dawo dai-dai ba. Sai bayan da Abdul-hameed ya dawo muka ci abinci muka nutsa yake sanar da ni yanda suka yi da su Hamma Abubakar. Na hange zallar gaskiyarsa kwance cikin idanunsa sa'ilin da yake ƙara nanata mini cewar ba shi da masaniya game da wannan saƙon. Na lanƙwashe ƙafafuna wajen guda"ni kam ɗazu ne nake kallo, na ji wani abun mamaki. Daman mutane daban daban su na iya mallakan SIM guda ɗaya?". "Sosai ma kuwa ana samun irin haka. Don akwai wasu tagwayen da muka yi jami'a tare dasu kamfanin suka je aka yi musu SIM guda biyu amma mai ɗauke da lamba ɗaya kowa ya riƙe guda". Na jinjina kaina cike da tashin sanin inda zan dafa, shin na sanar dashi ko kuma na bar abin a cikin raina?. Na nuna masa SIM ɗin ko kuwa?. Na fayyace mishi abin da zuciyata take zargi?. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________ Page 3️⃣6️⃣ Sai da ya taɓo kafaɗata na dawo cikin hayyacina, da ido ya yi mini alama akan lafiya na yi ƙasa da kaina. Ina shawara da zuciyata da take dakan lugudai. Dole na samawa kaina mafita akan abubuwan da suke faruwa kuma ni ɗin dai ni zan tashi na yi yaƙin nemawa kaina 'yanci. "Daman wani magana nake so mu yi" Na furta bayan na gama sa-toka-sa-katsi da zuciyata. Ya gyara zamansa alamar yana saurara ta, na ciro SIM ɗin da na sanya a bayan wayata na miƙa masa tare da cewa"ɗazu na shiga sashin Amma na tarar da su Ansar suna rigima akan SIM wai tsinta suka yi a cikin shara. Shine na karɓa na gwada a wayata don tabbatar da cewar mai amfani ne ko akasin hakan, babu komai a cikinsa sai lambar layin da ya yi daidai da naka, don tabbatar da hakan har saƙo na turawa kaina ya zo mini da lambarka". Ya waro idanunsa cike da mamaki ya furta"lambata kuma na ga ni" Na miƙa masa layin da kuma saƙon da na turawa kaina, ya karɓa ya ga ni. Ya sanya layin a cikin wayarsa tare da jera lambata ya ƙira. Take ƙiran ya shigo wayata da lambarsa, ya sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi da kuma sauti kafin ya ce"tabbas lambata ce take fitowa. Amma yaya aka yi hakan ya faru?". Na daɗe masa kafaɗata alamar ban sa ni ba, ya cigaba da "kwanaki an tura miki saƙo da lambata wanda ba ni da masaniya akan sa yanzu kuma ga bayyanar wannan layin shima. Wai me yake shirin faruwa ne?". Ya ƙare zancen yana dafe goshinsa cike da damuwa. Na sausauta amon muryarta a nutse nake faɗin"sai fa ka kwantar da hankali tare da haɗe nutsuwarka waje guda sannan mu iya cimma mafita". Na saci kallonsa kana na cigaba da cewa"ya kamata mu faɗawa kanmu gaskiya Abdul-hameed ka yarda ko akasin haka 'yan uwanka ba sa ƙaunar tarayyata da kai, ƙiri ƙiri sun fito sun nuna mini manufarsu. Su zarge ni akan abincin da na girka maka yanzu kuma ga batun wannan layin da ina da tabbacin da shi aka tura mini wancan saƙon". Da wani irin saurin ya ɗago kansa yana zube idanunsa da suka fara canza launi a bisa fuskata. Duk da ƙirjina yana bugawa fiye da kima ga kuma tsoron da ya yi mini mamaya a cikin zuciyata ban ɗauƙe idona daga kansa ba ban kuma razana da kallon da yake yi mini ba. "Me kike nufi Aisha? Ki na so ki ce min ɗaya daga cikin 'yan uwana kike zargi da tura wannan saƙon? To a wani dalilin ke nan sannan me ye ribar su idan suka aikata abin da kike zargin su dashi". Na matse yatsun hannuna waje guda kafin na furta"ba zargin su nake yi yaƙini nake dashi akan abin da na faɗa. Idan ba rami me ya kawo batun rami?. A sashin Amma fa aka sa ma wannan layi....". Ban gama ba na ji ya ɗauke ni da wani gigitaccen marin da sai da idanuna suka gano mini gilmawan baƙin duhu, hakan ya tursasa mini haɗiye raguwar zancen don dole. Na dafe kuncina na ɗago idanuna da ya cika taf da ƙwalla ina kallonsa zan yi magana ya ɗaga mini hannu alamar na dakata. "Ki na da damar da za ki iya ɗauka zarginki akan kowa amma kar ki yi kuskuren sako Amma a cikin zancenki". Ya furta cikin ƙanƙace ido dake alamta ya kai ƙarshen gejin fusata da harzuƙa. Ruwan ƙwallar da suka ciko ƙoramar idanuna suka zubo, cikin kukan da ya kubce mini na ce"mari ni ka mara?. Ba komai na gode". Na kai aya ina ƙoƙarin miƙewa ya yi saurin fizgo hannuna na faɗa jikinsa ya sanya dukkan hannayensa ya riƙe ni gam. Duk yanda na so raba jikina da na shi na kasa domin riƙon da ya yi mini ba na wasa ba. Har wani zafi nake jin ƙirjina yana yi mini tsabar tashin hankalin da ƙuncin da zuciyata take a ciki. Ya kawo bakinsa dai-dai kunnuwana tare da cewa"ki yi haƙuri ki yi haƙuri matata. Wallahi na kasa jurewa ne da kika ambaci sunan Amma. Na roƙe ki ba don ni ba ko don ɗaurewan zaman lafiya a tsakanin mu, ki san yanda za ki yi magana akan dukkan abin da ya danganci Amma". Ajiyar zuciya kawai nake sauƙewa akai akai kamar wacce ta yi gudun ceton rai. Ya soma shafa kaina a hankali, ban iya cewa dashi komai saboda wani irin nauyin da nake jin bakina ya yi mini. Na kasa yarda cewar hannunsa ne ya sauƙa a jikina da sunan duka akan abin da bai taka kara ya karya ba. Washe gari na tashi da wani mungun zazzaɓi ko ɗan yatsata bana iya ɗagawa. Na so ƙiran Hamma Ahmad na sanar dashi abin da ya faru amma zuciyata ta gargaɗe ni da cewar na koya riƙe sirrin aurena na kuma san yanda zan magance matsalata. Ina kwance akan sallayan da na yi sallan asubahi na kasa motsawa, na ji shigowarsa har ya zauna a gabana ban ɗago kai na kalle shi ba. "Me yake damunki?". Ya furta muryarsa cike da tausayawa na so na yi banza da shi amma na kasa yin hakan. "Babu komai". Ya kai hannunsa saman goshina kafin ya zarce izuwa tudun wuyata. Yana cewa"ba ki da lafiya ne?". " Lafiyana". Na faɗa ina ƙoƙarin tashi ba zauna duk da tsananin ciwon kan da yake addaba na. Zai riƙo ni na janye hannuna ina matse jikina waje guda. Ya haɗa hannayensa waje guda alamar roƙo"don Allah ki yi haƙuri ki daina wannan fushin da ni, wallahi ba zan iya jurewa. Sanar da ni damuwar". "Babu komai kuma Ni lafiyata ƙalau, ka shirya ka tafi wajen aiki kar ka makara". Ya furzar da iska daga bakinsa"idan akan maganar jiya n....". Da sauri na tare shi ta hanyar faɗin"ka daina dawo da hannun agogo baya ya riga ya wuce har abada". Ina dasa aya nan na fice daga ɗakin, na koma ɗakinsa na jingina jikin ƙofar ina sakin wani kuka marar sauti kafin na isa ga wajen ajiye kayansa ba fito masa komai na ajiye masa na fito, muka yi kiciɓus dashi na matsa da hanzari ina ba shi hanya ya wuce. Na ƙudurce a raina cewar ba zan yi faɗa dashi ko na yi fito na fito dashi ba. Amma dole na nusar dashi kuskuren da ya tafka, ba zaɓa ladabtar dashi ta hanyar janye jikina daga gare shi. Kafin ya fito na haɗa masa ruwan shayi da soyayyan ƙwai na ajiye masa a falon. Dai-dai zan shige ɗakin na ji muryarsa kamar daga sama. "Don Allah tsaya ki saurare ni". Na juyo fuskana a haɗe"na tsaya don girman wanda ka ambata". Ya tako ya iso har gabana ya na zura dukkan hannayensa a aljihun jamfar dake jikinsa. "Ki yi haƙur....". Na ɗaga masa hannu"ya wuce, ga karin kumallonka ka ci kafin ya huce Allah ya tsare a dawo lafiya". Na ƙare zancen ina ƙoƙarin shigewa ɗaki ya riƙo ni na fizge. Lokacin sallama da shigowar Amira muka ji yo shi a tare, na yi wuf na shige ɗakina na bar shi tsaye a wajen. Sai da na ji ƙarar fitar motarsa sannan ba fito na iske Amira tana gyara falon, ta gaishe ni na amsa mata ina ƙoƙarin sake fuskana da babu annuri. Har ta gama ta yi mopping wajen ban ce da ita komai ba, ta zo ta durƙusa a gabana. "Anty lafiya kuwa?". "Lafiya kawai yau na tashi ba na jin daɗi ne". "Allah ya sauwaƙe". Na ɗaga mata kaina, ranar wuni na yi ban leƙa ko ƙofar sashina ba ko zuwa gaisar da Amma ban yi ba duk da zuciyata ta ba ƙoƙarin nusar da ni rashin dacewar hakan, amma na yau dai na danne. Ban fita sai da nayi sallan Asr na shiga sashin tare da Amira. Ta na kishingiɗe a wajen zamanta na kullum kullum. Na rusuna na gaishe ta, ba ta amsa mini ba sai ma tambayar da ta jefo mini. "Me ya faru tsakanin ki da mijinki". "Babu abin ya ya faru a iya sa ni na, amma wani abun kika gani ko ya faɗa miki?". Babu shiri ta yi mini wani kallo da alama ba ta yi zaton samun irin wannan amsar daga gare ni ba. "Na daɗe ban gan shi cikin irin yanayin da ya zo min a safiyar yau ba. Tabbas na san akwai wani abun da ya faru da ya jefa shi cikin wannan yanayin". Sai da ta ƙara kaurara amon muryarta ta ɗaura da"kar ki yi amfani da son da Abdul-hameed ya ke yi miki ki cutar dashi, Allah ya rufa miki asiri da samun miji irin sa don haka kar ki yi wasa da damarki". Zancenta su da daki ƙwaƙwalwata tare da munana zuciyata. Na gyara zamana"tabbas da ni dashi duk mun yi sa'ar samun juna". Ina ankare da kallon da ta yi mini ta gefen idonta ba tare da ta ce da ni komai ba. Haka nan kawai na tsinci kaina da faɗin"ina Anty Alawiyya fa da su Ansar?". Kamar ba za ta amsa ba sai can kuma ta ce"su na ciki". Na miƙe ta yi saurin faɗin"ina za ki je?". "Zan je mu gaisa ne, don wataƙila sai gobe na kuma shigowa". "Kar ki damu in ta fito zan sanar da ita zuwanki". Na maida dubana ga Amira ina bada umarnin tashi mu ta fi. A falo muka zauna Amira ta yi ƙasa da kanta tana cewar"Anty tun da na shigo yau na iske kuna ja-in-ja da yallaɓai da kuma yanayin da ki ke ciki, na ji gaɓadaya jikina ya yi sanyi. Gashi har lokacin tafiyata ya gabato ba ki dawo kamar da ba, don Allah in wani abun na yi miki ina mai neman afuwarki". Da ƙarfi na furzar da iska daga bakina ina zamewa na jingina bayana jikin kujerar da nake zaune"babu abinda kika yi mini Amira. Kamar yanda na gaya miki kawai yau na tashi ba na jin daɗi ne". "Shikenan Anty daman ina so na yi miki wata tambaya, amma ina tsoro ki ce na zaƙe da yawa ko saka kaina cikin abin da bai shafe ni ba". Na gyara zamana da kyau ina sauraron ta"tun ranar da na fara zuwa gidan nan aiki kafin na shigo wajenki, mai gadi ya kan ce da ni Hajiya tana nema na idan na ce tambayoyi take yi mini akan yanda kuke zaune da Yallaɓai". "Ba komai Amira kar wannan ya dame ki, babu abin da zai dawwama komai zai wuce wataran ai sai labari. Shi yasa nake kawar da kai akan abubuwa da dama". Cike da gamsuwa ta amsa mini da"haka ne kam, Innata ta ce na gaida ki sosai". Na ƙirƙiri murmushin dole na yaɓawa fuskata yayin da nake amsawa. Ko da ta tafi ta barni na kasa taɓuka komai a wajen na zauna ina tunanin wanda zan ƙira na sanarwa damuwata. Tabbas duk wanda ya fito daga tsantson fulani a san shi da matuƙa kunya musamman akan lamarin da ya shafi aure wannan dalilin shi ya hana ni sanar da Umma abin da yake faru tuntunin. Hamma Ahmad na ƙira na irge masa komai tabbas shi ma ya shiga ruɗu sosai, haƙuri ya yi ta ba ni shawarwarin cewar na dage da kai kukana ga Allah. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________ Page 3️⃣7️⃣ Sai na jera kwanaki bakwai cur bana shiga shirginsa, duk wani abun da na san zai buƙata tun kafin ya nema nake tanada masa shi. Girki kuwa ina kammalawa zan ajiye masa na shige ɗaki ba zan fito ba sai na ji ƙarar ficewar motarsa daga cikin gidan, ko kuma shigowar Amira. Fitowata daga wanka ke nan bayan na gama girka masa karin kumallo na dawo ɗaki, na yi saurin isa ga wayata da take faman ruri na yi turus ganin baƙuwar lamba ce, sai da ya kusa katsewa ba kara tare da maƙalawa a kunnena. "Ki zo sashina ina son ganin ki yanzu". Na ji muryar Amma sun sauƙa a ƙofofin kunnuna, ta na dire faɗin zancen git ta kashe wayar. Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya gabana yana tsananta bugu da tarradin abin da zan tarar. Sai da na gama shiryawa tsaf na ɗauki wayata na fito, duk su na zaune a falon sallamar da na yi ya sanya su zubo mini idanu har na yi wa kaina mazauni tare da gaishe da Amma. Ba ta amsa mini illa fara faɗin da ta yi"har nan na ƙirawo ki na tambaye ki me ke faruwa tsakaninki da mijinki amma ki ka nuna min cewar ba komai. Sai gashi yanzu da kan sa ya kawo min kukansa cewar ba kya kula shi". Na gyara zamana sosai "Amma kamar yanda na sanar dake ne babu wani abu a tsakanin mu. Ko yanzu ma mun rabu dashi cikin farin ciki da kewar juna". Na ƙare zancen ina satan kallon Abdul-hameed ta gefen ido da mamakin zancen nawan ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa fuskarsa. Ta yi masa wani kallo da ya fi kama da na tuhuma kafin ta furta"kai me kazo ka faɗa min?". Ya sunkuyar da kansa ya na sosa ƙeya"kamar yanda ba faɗa miki ne kwana biyun nan ba ta shiga harkata, komai nake da buƙata ajiye min shi take yi ta koma ciki. Shiyasa na kawo kukana gare ki ki taya ni ba ta haƙuri idan wani laifin na aikata a gare ta". "To kin ji abin da ya ce" "Na ji dukkan abin da ya ce, manufata na ba shi lokaci na lura kamar kwana biyun nan yana kwaso gajiya daga wajen aiki ne gashi ba ya dawowa da wuri shiyasa na ke basa lokaci ya huta". Sai da ta ja dogon lokacin kafin a ƙasaitance ta furta"wannan ba huruminki ba ne, ya tabbatar a kanki dole ki samarwa mijinki nutsuwa. Idan kuma kin fara gajiya dashi ne za ki iya fitowa ki faɗa, domin Abdul bai rasa gata ba bai kuma cancanci wulaƙanci ko wata iriyar mace ba balle Aisha". "Gaya mata dai, ban da so ma da kwashe-kwashe me ye haɗin kifi da kaska?". Furucin da Al'amin ya yi ke nan ya na yatsina fuska duk da na ji zafin zancen amma ban ce komai ba, na sunkuyar da kaina ƙasa ina godewa Ubangijin da ya tsaro mini yin rayuwa a cikin waɗannan mutanen. Sai da ta ƙare zancenta da suka yi kama da kashedi kafin ta sallame mu, tare muka fito ki kallonsa ban yi ba na ɗauki hanyar komawa sashina ya yi saurin shan gabana. "Wai don Allah menene? Yaya ki ke na yi da raina ne?. Yanzu fa a gaban Amma kika nuna ba komai yanzu kuma mun fito za ki canja min". Yanda ya ƙare zancen cikin maraice tamkar mai shirin fashewa da kuka ya yi matuƙar taɓa mini zuciya ainun. Tabbas na shaida irin son da Abdul-hameed yake gwada mini, ba zan iya yin dogon fushi da shi ba na tabbatar ko share shi da na yi na tsawon waɗannan kwanakin ya gano kuskurensa. "Ai kamar yanda na faɗa a gaban natan ne komai ya wuce". Ya matso gab da ni tare da ranƙwafo da kansa"hukuncin da ki ka yi min ya yi tsauri da yawa, don Allah ki dunga sausauta min. Na gane kuskurena kuma in sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba". Kaina kawai na gyaɗa masa saboda yanda ya matso ni na kasa cewa komai illa ƙamshin turarensa da nake shaƙa. Ganin alamar yana ƙoƙarin zarcewa ya sa ni saurin zillewa ina ɗaga masa hannu alamar sai ya dawo, ina juyowa na hango Al'amin ya na fitowa sai da muka haɗa ido na juya da saurina na isa ga Abdul-hameed da yake ƙoƙarin shiga mota. Duk da ya zarce ni sosai a tsayi na yi ɗage na manna masa kyakkyawan sumbata a ƙuncinsa ina kashe masa ido ɗaya, zai kamo ni na kauce da hanzari muna sakarwa juna murmushi. Sai da ya ja motarsa ta jfice daga cikin gidan, na juyo ina watsawa Al'amin da ya yi mutuwar tsaye ya kasa gaba balle baya wani kallo. Na wuce ta gefensa ina baza takuna raina ƙyal kamar farar azurfa, ko banza na bashi amsar zancen da ya yaɓa mini a ciki. Babu jimawa Amira ta zo tare muka yi karin kumallo da ita sannan ta gyare sashin tsaf, muka zauna mu na hira ina nuna mata hotunan bikinmu. Sai yabawa take da faɗin Masha Allah. "Anty duk sun fi ki haske amma kin fi su kyau". Na bushe da dariya mai ƙarfi sai da na tsagaita na ce"kallon tsoro kika yi musu har kyawun ma sun ɗara ni, ba ki ga duk su na kama ba ni ce dai kamar rabe a tsakanin su". Ita ma dariyar ta yi ta ce"kallon ƙurilla fa na yi musu". Haka muka sha hirar mu sosai kafin muka ɗaura girkin rana. Ina jin daɗin daɗin zama da Amira sosai wani lokacin ganin ta nake yi kamar Abasiyya. Cikin kwanakin nan mun dawo kamar yanda muke da mijina babu abinda muke yi sai kulawa da tattalin juna. Izuwa kam kan mage ya waye domin ba na ƙwauron baki wajen mayar da martani da ba da amsa dai-dai da tambayar da aka yi mini, sai dai duk furucin da zan yi bana taɓa jefa kalmar rashin girmamawa ko cin fuska ga Amma, domin ko ba komai ita uwa ce kuma in zan yiwa Abdul-hameed adalci dole na ɗauki uwarsa tamkar tawa kamar yanda shi ma yake mutunta tawa kamar ita ta yu naƙudarsa. Duk safiya bayan fitarsa da zazzaɓi nake wuni ga kasala da kuma rashin ɗanɗanon da bani dashi. Ina kwance a falo na ji sallamar Amira na amsa tare da bata iznin shigowa. Tana daga bakin ƙofar ta ce"Anty ki na da baƙo a waje". Na ɗago kaina da ƙyar"waye ne? Kuma ni yake nema?". "Ya ce dai ki leƙo ki ganewa idanunki". Tsiririin tsakin na saka don Allah ma ya sa ni bana ƙaunar motsa jikina ko kaɗan sai ya zama dole, ina leƙowa idanuna suka yi mini tozali da abun da ya tilasta mini jin wani karsashi a cikin jikina. "Anwar". Fuskarsa tamkar gonar auduga ya ce"Boɗɗiam". Hawayen farin ciki suka ciko mini idona na maida duba ga Amira"yaya ne wanda kika hotunan mu rannan". Ta ɗaga mini kanta alamar ta gane, ya shigo ya zauna na dunga jere masa lemuka a gabansa tare da umartar Amira ta ɗaura girki yanzu. Cike da zumuɗi na ɗaga wayata ya katse ni da faɗin"wa za ƙira kuma?". "Zan ƙira shi ne na sanar dashi yau muna da babban baƙo". Dariya kawai ya yi ni kuwa na cigaba da dannawa layin Abdul-hameed ƙira sai da na ƙira sau biyu bai ɗauka ba na ajiyewa wayar. "Na ƙira ma bai ɗauka ba ina ba ya kusa. Yaushe ka zo? Kai kuma tafiya kamar ana koranka babu sanarwa balle a yi sallama". Murmushin ya ƙara saka haɗe da faɗin"jiya da yamma na zo, wallahi tafiyar ce ta zo min a matsayin zaɓi na ƙarshe babu yanda na iya shiyasa". Na jim ina sunkuyar da kaina ƙasa, lura da canzawar yanayina ya sanya shi ɗaurawa da"wani kyakkyawan albishir na zo miki dashi, wanda idan kika ji shi sai kin yi min kyauta". "To wani irin albishir ne wannan?". "Ki canka" Na ɗaga kaina sama ina nazari da ƙarfina na ce"ko dai Hamma Ahmad ne zai yi aure?". "Hamma Ahmad kam ai sai dai mu taya shi da addu'a, domin ko batun aure ma shi ba ya yi. Ki dai ƙara nazari ko za ki canka dai-dai". "Ba wani cankan da zan iya kawai ka faɗa mini". "Adda Abida ta sauƙa lafiya, ta haiho ɗiyarta ta mace". Ban san sanda na zame daga kan kujerar da nake ba ina faɗin"da gaske?". Ya ɗaga mini kansa alamar tabbatar mini da zancensa. "Shi ne komai babu wanda ya ƙira ni ya gaya mini?". "Tun jiyan aka so ƙiranki a gaya miki na ce a bari zan zo da kaina na sanar dake". Wani sanyin daɗin ta rufe ni na rasa inda zan tsoma kaina tsabar murna, ji nake yi kamar na yi tsuntsuwa nake na ga Adda Abida da abin da ta haifa, na san Hamma Adnan bakinsa har ƙeya don farin ciki. Ina ta zuba masa surutu har Amira ta gama girkin ta kawo, na yi na yi dashi amma ya nuna mini ba zai ci komai. Babu yanda ban yi dashi ba amma ya ƙi ruwa da lemon kawai ya sha. Na ɗauki plate na fara zuba mishi abincin na cika taf na miƙa masa. "A ƙoshe nake Aishatu alhamdulillah". Na harare sa"har kazo gidan da bake ka tafi baka ci komai ba". Ina rufe bakina idanuna suka sauƙa akan Amma da Al'amin da suke tsaye a ƙofar falon ta ciki sun zubo mini idanuna da dukkan alamo sun daɗe tsaye a wajen ba tare da na farga ba. Bai karɓa ba na ajiye plate ɗin a bisa teburin dake kusa da kujerar, su ka ƙariso tsakiyar falon. Ba zan iya tuna ranar da Amma ta shigo sashin ba tun wayewar ranar da aka rako ni gidan a matsayin amaryan Abdul-hameed da suka zo da ƙawayenta ganin kayan ɗaki. "Aisha". "Na'am sannu da shigowa". Anwar ya zame daga kan kujerar da yake ya ɗan rusuna yana gaishe ta cike da bata cikakken girmanta. Ba ta amsa ba ta soma faɗin"wanene wannan kika shigo dashi har cikin falon mijinki?". Ƙirjina ya harba da ƙarfin gaske"Amma ɗan uwana ne ya zo sanar da ni Adda Abida ta sauƙa lafiya". "Duk cikin danginku a rasa mace ƙwara ɗaya jal da za a wakilta ta zo ta sanar dake haihuwar sai wannan jibgegen ƙaton za a turo?. To me ye amfanin wayarki da ba za a ƙira ƙi ba?. Da ya sanar dake shine aka ce ya nema waje ya zauna har kuna ja-in-ja dashi akan ya ci abinci". Cikin taushin murya Anwar ya ce"Allah ya huci zuciyarki Hajiya, na ga kamar ba ki fahimta ba ne ɗan uwanta ne ni". "Wani irin ɗan uwa ke nan yi min bayani". Ya ƙara tausasa amon muryarsa"iyayenmu maza wa da ƙani suke". "Amma ka san cewar akwai aure a tsakanin ku da ita ko? Domin kai ba muharraminta bane. Kun aurar da yarinya amma kin hana ta samun kwanciyar hankali a gidan mijinta sai bibiyar rayuwar gidan aurenta kuke yi. Zuwa ka yi ka hure mata kunne ta cigaba da wulaƙanta mijinta don ɗan uwanka ya rasa ta watau kowa ma ya rasa ko?". Zan yi magana Al'amin ya daka mini wata gigitacciyar tsawar da ta tilasta mini haɗiye zancen da nake yunƙurin furzowa. "Dalla ki rufewa mutane baki munafukar banzan munafukar wofi, me ye kuma za ki ce mana bayan abin da idanunmu suka gane mana?". Da wani irin ƙarfi Anwar ya miƙe daga rusunawar da ya yi yana ƙarewa mini kallo"daman irin wannan zaman ki ke yi Aishatu?". Ban amsa masa ya ɗan matso kusa da Al'amin na riƙo bayan rigarsa ina jijjiga masa kaina alamar kar ya yi amma bai saurare ni ba. "Waye kai da kake siffanta ta da waɗannan munanan kalmomin?". A gadarance ya ce"ƙanin mai gidan ne ni, ka ga kuwa na fika iko a cikin gidan". Ya cije gefen bakinsa kafin ya cigaba da faɗin"da kun san irin sadaukarwa da tarin ƙalubalen da Aishatu ta fuskanta akan auren yayan nakan don tabbatar da ɗaurewa farin cikin da kwanciyar hankali a rayuwarsa. Da ta zama abin girmamawa, mutuntawa da karramawa a gare ku. Ni na kawo kaina cikin gidanku don haka dole na jure komai daga gare ku". Ya juyo gare ni muryarsa har wani ja yake yi tsabar ƙololuwar ɓacin ran da ya kai ya ce"zan tafi". Yana gama faɗin haka wuf ya juya ya fara tafiya. "Da ka tsaya ai, in ban da ƙaddara me ye yaya Abdul zai yi da wannan. Ya haɗa mu da dangin jaraba dangin da ko riƙon aure ba su iya ba". Furucin Al'amin ke nan da ya sanya Anwar dawowa da wani irin sauri kamar iska ne ke jan sa, ya shiga nuna shi da 'yar manuniyar yatsarsa yana cije bakinsa sai dai ya gaza cewa uffan. Ya fizgo hannunsa kamar zai tsinke shi daga gangar jikina ya fara ja na ina turjewa ina kuka ina faɗin"don Allah Anwar ka tsaya, ka yi haƙuri a gyara komai a nan". Amma kamar ana ƙwalawa bebe ƙira ki waigowa bai yi ba balle ta saurare ni, muna fita muka sama adaidaita muka hau. Na fashe da wani irin matsanancin kuka har jikina rawa yake yi, bai ce da ni ki kanzil ba har adaidaitan ya tsaya a cikin layinmu. Ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya miƙa masa sai da ya fita ya ce"fito". Na ɗago idanuna da naji sun yi mini nauyi sosai zan yi magana ya ɗaga mini hannu, ya sanya hannunsa ɗaya ya jawo ni na fito. Dai-dai lokacin da aka sallame sallan Asr a masallacin dake kusa da gidanmu mutane suka fara fitowa, ya cigaba da jan hannu da sauri sau dai abin da muke gudu muke ƙoƙarin kauce masa ne ya faru. Muna isowa ƙofar gidan muka yi kiciɓus daBaffa da Baba Alhaji su na dawowa. ********************* Dai-dai nan Barrister Adam ya dakatar da ni ya juya yana kallon mai shari'ar da ya tallafi ƙuncinsa ya na kallona da hawaye su ka gama jiƙa mini fuska. Cike da ƙwarin gwiwa ya maido da kallonsa gare ni ya nafaɗin"kin guji auren ɗan uwanki ki auri Abdul-hameed yayin da kika tarar da abin da ba ki yi zato ba a cikin gidansa. 'Yan uwanki sun ba ki shawarar kar ki juri irin abubuwan da mahaifiyarsa da 'yan uwansa suke yi miki ta hanyar nuna miki ki zama robar wando ta yanda za ki iya kama ƙudun kowa. Sai kika yi amfani da hakan kika kashe shi, ki ka mayar da mahaifiya da 'yan uwansa marayun dole domin shi ya maye musu madadin uba. Ki ka ɗauki wannan mataki wajen rama abin da suka yi miki haka ne?". Tsabar cin ƙarfina da kukan ya yi na kasa cewa komai, ƙafafuna suka fara rawa ina jin kaina yana juyawa tamkar sitiyarin mota a hannun ɗan koyo. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________ Page 3️⃣8️⃣ Kotun ya kaure da hayaniya kamar cin kasuwa, kowa ya na tufa albarkacin bakinsa. Sai da mai shari'ar ya dakatar da surutun tare da ba wa Barinsa Adam damar ci gaba da tambayoyinsa. "Zan so ki amsa min wannan tambayar. Me yasa kika yi amfani da son da marigayi ya ke yi miki ki ka cutar dashi?". Da hanzari Barrister Aliyu ya miƙe haɗe da faɗin"objective my Lord! Lauyan gwamnati ya na ƙoƙarin tsorita wacce ake tuhuma ta hanyar jefa mata tsauraran tambayoyin da zai iya kiɗimata ta furta abin da ba shi ke nan ba". "Lauyan gwamnati ka kiyaye". Ɗan ranƙwafar da kansa Barrister Adam ya yi alamar girmamawa sannan ya cigaba da faɗin"zan so Alawiyya ya ga marigayi ta bayyana a gaban kotu". Sai a lokacin na yi ƙarfin halin cira kaina na bi ta da kallo zuciyata ta na yi mini ƙuna da raɗaɗi na ba wasa ba. Ya tako ya isa gabanta ya na gyara zaman baƙar rigar dake jikinsa ya furta" me ki ka sa ni game da Aisha da marigayi, ina nufin ko akwai wani abun da ya haɗa su kafin faruwar lamarin?". Ta yi sama da kanta alamar ta na nazari kafin ta ce"tabbas akwai, domin a lokacin ana shirye-shiryen kai kuɗin aurensa". "Wani irin shirye-shirye?". "Zai ƙara aure to lokacin ana shirin kai kuɗi gidan su yarinyar da zai aura". Ya jinjina kansa da alama ya gama samun abin da yake so jin daga gare ta, ya cigaba da maganan ba bana jiya jin abin da yake furtawa illa ganin bakinsa ya na motsawa da nake yi. Ya gabatar da godiya ya koma ya zauna. Mai shari'ar ya yi jefawa Barrister Aliyu tambayar ko yana da tambayar da zai yi wa Anty Alawiyya. Ya miƙe a nutse ya iso gabanta yana ƙare mata kallo"a labarin da yar aikin gidan marigayi da wanda matarsa da ake zargi da kashe shi ta gabatar a gaban kotu. Ya nuna cewar tabbas akwai ƙauna mai ƙarfi a tsakanin su, sannan akwai kulawa na musamman da suke gwadawa junansu. Me ya sanya Abdul-hameed bijirowa da zancen ƙarin aure?". "Ai kyautatawa ba ta hana magidanci ƙarin aure, lokaci ne ya yi shi yasa zai ƙara". Ya yi wani murmushin gefen bakin kafin ya ce"kina da aure?". "Ba ni dashi". "Me ya fito dake daga gidan mijinki?". "Fifita kishiyata ya yi sama da ni". Ya zube idonsa akan ta"tunda ya bijiro da zancen ƙarin aure shin matarsa ta taɓa nuna rashin hankalinta game da hakan?". "A'a". Murmushi ya kuma yi tare da faɗin"lokacin da aka yi kisan ki na cikin gidan". Ta gyaɗa kanta da hakan ya ba shi damar ɗaurawa da"kun haɗu dashi ranar da lamarin ya faru?". "E ya shigo gaishe da mahaifiyarmu, bayan ya koma sashinsa muka fara jiyo ihunsa". "Da ku ka ji ihun me kuka yi?". Ya gyara mayafinta da yake zamowa kafin ta amsa masa da"garzaya muka yi izuwa sashinsa muka tarar dashi a kwance jikin jini, ita kuma ta na gefe da wuƙar da sallamarta ta koma mazauninta. Ya ɗaura da faɗin"ya mai girma mai shari'a ƙarin auren da marigayi ya bijiro dashi ba shi zai sanya Aisha hallaka shi, tunda kamar yanda yayarsa ta batyana a gaban kotu cewar ba ta taɓa nuna tashin hankalinta game da auren ba. Ba zan gaji da faɗin cewar haƙiƙa akwai wata ƁOYAYYAR MANUFA a cikin wannan kisan ba". Wasu ƙananun magana suka fara tashi tsakanin yan zaman sauraron shari'ar da suka yi ka kotun. Ina hangen su Hamma Ahmad ji nake yi kamar na ruga a guje na isa gare su na tuntsire da kuka ko zan ji sausaucin zogin dake sukar ƙahon zuciyata. "Kotu ta ɗaga wannan ƙara zuwa ranar goma sha bakwai ga watan Mayun shekarar dubu biyu da ashirin da huɗu. A sannan duk ɓangarori biyun su taho da gamshashshiyar hujjar da za ta gamsar da kotu, har izuwa lokacin da za a dawo za a cigaba da tsare Aisha a gidan ajiye ɗaurarru, ba tare da beli ba". Ya na ƙare zancen ya buga ƙaramar dake bisa teburinsa ya miƙe ya fice ta wata ƙofa. Sai da ya fita sannan ragowar jama'a suka fara ficewa. Aka mayar mini da ankwan da aka cire mini da za a shigo da ni cikin kotun. Aka fito da ni jama'a suka fara kawo mini hari na duka da jifa jami'an 'yan sandan su na kare ni. Kamar sassaƙeƙƙen gunki haka na kafu a wajen tamkar an dasa ni idanuna ƙar akan dukkanin yayuna mazan da kuma Ummata da take yarce hawayen da suka yi mata lijif a fuska. Na sauƙe wani gigitacciyar ajiyar zuciyar da ta tafiyar da kukan zucin da nake yi. Ban yi aune ba na ji wata jami'a mace ta fizgo ni da ƙarfin rabbussamawati na kaucewa jifan da wasu fusatattun matasa suka ke yi mini da manyan duwatsu. Cikin kumfar baki su ke faɗin"sai mu kashe ta tunda an ƙi barin doka ya hau kanta, tun zaman farko ya makata an yanke mata hukunci kisa ta hanya mafi muni da tozarci. Amma an bar ta har yanzu ta na cigaba da shaƙar iskar numfashi sai bayan wani lokaci a fito a cewa jama'a ta na matsalar ƙwaƙwalwa an sake ta". Su na zancen su na ƙoƙarin ƙara kusanta da tare da kawo mini duka ta ko ina. Hamma Ahmad da Umma suka ratso su na kare ni, Hamma Abubakar ya na tsaye ya kasa komai illa hawayen da yake sake. A farin sanin da na yi masa mutum ne mai dauriya da juriya komai girman abu ya na iya danne shi a cikin ransa. Ba ƙaramin abu bane yake sanya hawayen idanunsa tsiyaya, sai gashi yau a dalilina ya na zubar da ƙwalla cikin ƙonar zuci. Duka da goran da wa ni ya kawo mini Umma ta yi saurin tarewa, ya sauƙar a goshinta take jini ya ce sallama alaikum. Jami'an su ka ƙara ƙaimi wajen ba ni kariya sai dai lamarin ya ci tura sai da suka tarwatsa tarin jama'ar ta hanyar jefa borkonon tsohuwa sannan aka sama sararin jefa ni a cikin mota. Aka fige ta da karfin gaske muka bar cikin harabar kotun. Sai da aka mayar da ni cikin ɗakin da aka ɗauko ni na sama ƙarfin sakin kukan da yake nuƙurƙusan rai da ruhina. Na rasa abin da zan yi na ji daɗi a halin da nake ciki, babu abin da nake yi wa kaina sai fatan mutuwa. Idanuna sai hasko mini yanda jini yake zuba daga goshin Ummata a lokacin da aka jefa ni cikin motar. Tabbas ɗan kuka shi ke jawa uwarsa jifa. Da saurin Hamma Ahmad ya riƙe Umma saboda ƙoƙarin zubewan da take yi tana tangal-tangal. Borkonon tsohuwar da aka jefa a wajen ya tarwatsa dandazon jama'ar kowa ya fara yin ta kansa. Da ƙyar suka fito da ita daga cikin harabar kotun suka tsaya neman adaidaita. Ba su samu ba ga zubar da jinin da take yi har yanzu, faka motarsa Barrister Aliyu ya yi a dai-dai gabansu tare da zuge gilashin motar. "Ku shigo mu je asibiti". Ya furta yana kallon gefen da Umma take. Shigar da ita suka yi kai tsaye suka wuce asibiti mafi kusa, sai da aka yi mata ɗinkin a wajen tare da wasu allurai sannan ta sama bacci. Hamma Abubakar ya sauƙe numfashi ya na kallon Barrister Aliyu da tunda ya kawo su bai tafiya ya ce "Barrister anya Shari'ar nan akwai alamun za mu yi nasara kuwa? Wallahi duk na sare". "Ai ka san ita Shari'a saɓanin hankali ne. Kamar mai cike ne babu wanda ya san abin da ke cikinta sai wanda yake da ikon akan komai da kowa. Amma na yi muku alƙawarin matuƙar Aisha ta na gaskiya sai iya inda ƙarfina ya ƙare akan wannan case ɗin, ku kwantar da hankalinku sannan ku cigaba da yi mata addu'a". Duk shuru suka yi kamar ruwa ya cinye su sai Barrister Aliyu ne ya cigaba da kwantar musu da hankali. Bai tafi ba sai da Umma ta tashi ya sauƙe su a gida, Baffa ya na zaune a cikin ɗakin zaure kasancewar tun bayan faruwar lamarin fita ko nan da can ya gagare shi, ya na sauraron rediyon da ya kunna sai dai daga kallo ɗaya za ka fahimci cewar hankalinsa a nan yake ba. Sannu su Hamma suka yi masa amma ko waigowa bai yi ba balle amsawa musu. Da ido Hamma ya yi wa Anwar da Hamma Adnan alama akan su shiga gida tare da Umma. Shi da Hamma Ahmad su ka zauna nan wajen Baffa za su yi magana. Da hanzari Adda Azima da Adda Abida suka miƙe ganin yanda suka shigo. Suka nufo su cikin tashin hankali kasancewar duk Baffa ya hana su zuwa gabaɗayansu. "Tun ɗazu muke zaune muna jiran dawowarku, hankalinmu gabaɗaya ya tashi ganin abin da ya faru a kotu da muka gani a waya". "Shigar da Umma ciki ta kwanta, ina Dadar?". "Yanzu ta fita zuwa gida, don tun bayan tafiyanku jama'a suka cika ƙofar gidan nan su na hayaniya". Adda Abida ta furta ta na kama hannun Umma ta shigar da ita ɗaki ta kwanta. Ta fito ta iske Hamma Adnan da Anwar zaune. "Wallahi tsabar tashin hankalin da na shiga na ma kasa cigaba da ganin Shari'ar da ke haskawa. Zuciyata ta karaya sosai ganin yanda lauyan gwamnati yake ragargaza duk hujjojin da aka bayar domin kare ta". Zantukan Adda Azima suke da tsantsar damuwa da ya sanya Anwar miƙewa tsam ya tashi ya bar wajen yana riƙe kansa duk suka bi shi da kallo. Don baya Umma da ta kasance mahaifiya a gare ni babu wanda ya kai shi shiga tashin hankali da damuwar abin da ya afku. Sun daɗe su na tattauna har Dada ta shigo ta shiga ta duba jikin Umma da take kwance lilif. Sannu ta yi mata cike da kulawa kana ta furta"shi yasa tun farko na ba ki haƙuri akan ki ƙara yin haƙuri tunda Baffansu ya ce kar ki je ki yi haƙuri kawai. Ki cigaba da yi mata addu'a". Ba ta ce da ita komai ba illa jinjina kanta da ta yi cikin ƙarfin hali"wallahi ba zan iya ba ne, babu ta yanda za a yi zuciyata ta sama nutsuwa ina zaune a nan alhalin ita kuma ta na can". "Ina tunanin abin da zai je ya dawo ne shi yasa tun farko na hane ki". Ta na rufe bakinta muryar Baffa ta na sauƙa a ƙofofin kunnuwansu yana ƙwaal ƙiran Umma. Dada ta riƙo ta su ka fito su Hamma da su Adda Azima da Abids duk su na zaune a wajen. Sai da ya ajiye butar da ya iddar da alwalan sallan magrib da ita sannan ya ce"ya jikin nakin?". "Da sauƙi". Ta furta cikin ƙarfin halin nuna cewar babu komai. A yarfe ruwan dake bisa goshinsa kana ya furta"zan faɗa a gaban kowa don su zama shaida. Na sanar dake cewar duk ranar da ki ka sanya ƙafa ki ka fita daga cikin gidan nan da sunan zuwa wajen Aishatu to a bakin aurenki. Sai gashi kin aikata hakan don haka zama ya ƙare tsakaninmu, na sauwaƙe miki sai dai ki yi zaman 'ya'yank......". Da wani irin azama Hamma Abubakar ya yunƙuro Baffa ya ɗaga masa hannu"na riga na furta". Ya na ƙare faɗin hakan ya juya zai fice Anwar da yake zaune a ƙofar ɗaki ya jawo jikinsa Ya zo ya riƙe ƙafarsa ya na faɗin"don girman Allah Baffa kar ka yi mana haka. Umma ta kasance mai biyayya a gare ka akan komai kuma a ko yaushe a wannan karon zaɓin da ka bata ya yi tsauri da yawa ne da har ta kasa jure shi". Adda Azima da Abida suka fashe da kuka mai ƙarfi. Umma ta ƙara tako uku ta iso gabansa, numfashinta ya na fizgo da ƙarfi ta ce"tunda lokacin da na yanke hukuncin halaltar zaman kotun da za ayi. Na sa a raina cewar na gama zama da kai, ban taɓa tunanin hakan daga gare ka ban taɓa tunanin za ka aikata hakan ga 'yar da ta fito daga tsatsonka ba". "Don Allah ku yi haƙuri". Zancen Dada ke nan da ya sanya Umma cigaba da faɗin"ki bar ni ki bar ni yau na sanar dashi abin da ke ƙunshe cikin raina. Wallahi ba zan iya cigaba da zama dashi ba, ko Aishatu ta kuɓuta ko akasin hakan". Tana gama faɗin haka ta juya za ta koma ɗaki ta yanke jiki ta faɗi jirif. A ruɗe duk suka rufo a kanta su na faman ƙwala ƙiran sunanta amma shuru babu wata gaɓar dake motsawa a jikinta babu alamar numfashi a tare da ita. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 3️⃣9️⃣ Da ƙyar su Adda Azima suka ɗaga ta saboda sakewan da jikinta ya yi, suka mayar da ita kan tabarman da suke zaune. Dada ta ce Hamma Adnan ya deɓo ruwa ya kawo mata a cikin ƙwarya ta shafa mata a fuskarta sai da ta shafa masa sau biyu kafin ta ja dogon numfashi mai ƙarfin gaske da ya ba wa ƙwallar da suka ciko mata idaniya damar kwaranya a bisa kuncinta. Sannu duk suka hau jeranta mata wani na bin wani. Kafin Hamma Abubakar ya ce"Azima ku fito da ita mu tafi asibiti". "Ba sai mun je ko ina ba, ku haɗa min kayana kawai ƙauye zan je". "Don girman Allah Umma ki yi haƙuri. Ki zauna har a sasanta komai, idan kin je ƙauyen wajen waye za ki je a ina za ki zauna? Babu wasu ba dangin kusa da suka rage a cikin ƙauyen, kuma idan kin je ki ce dasu me ye". Furucin Hamma Ahmad ke nan cike da damuwa. Dada ta amshe zancen da faɗin"gaskiya kam babu inda za ki je, ko da aure ko babu ai yanzu an ruga da an zama ɗaya. Ki yi zamanki a cikin gidan nan domin babu inda za ki je da ya fi nan". "Ɗaga ni na tashi Abida". Umma ta furta tana cije leɓanta alamar ta na cikin ciwon matuƙa. A hankali ta soma faɗin"don Allah Umma ki yi haƙuri in kika bar gidan nan ina za ki je? Na tabbatar ko akwai to hankalinki ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar ki ka yi nisa da nan, ki bari Baba ya dawo a sasanta komai". "Dukkanku babu wanda bai mallaki hankalin kansa ba a cikinku. Don haka duk inda naje ba ni da fargaba akan ku mussamman idan na tuna cewar ko da ni ko babu ni ba za ku yi kukan rashina ba domin ga Dadarku nan". Duk shuru suka yi saboda kashe musu jiki da zancen na Umma ya yi. Anwar dai ya gaza cewa komai har yanzu ya na durƙushe inda Baffa ya zame ƙafarsa daga riƙon da ya yi masa ya fice, ya kasa motsawa wani irin zafi ƙirjinsa yake yi masa da ya wuce kima. Hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai yake ta maimaitawa cikin ransa. Ko a cikin mafarki babu wanda ya taɓa kawo irin wannan ranar za ta zo cikin rayuwarsu, ranar da Baffa zai furta wannan furcin ga Umma da ta kasance mai matuƙar biyayya a gare shi. Ahalin da suke rayuwa cikin tsantsar farin ciki, walwala, son juna da kuma nunawa juna kulawa yau su ne ƙaddarar ƁOYAYYAR MANUFA ta share duk waɗannan ababen. Babu irin magiya, roƙo, ban baki, lallashi gami da lallamin da ba su yi wa Umma ba amma fir ta nuna ba za ta iya cigaba da zama a cikin gidan ba. Da ƙyar ta yarda za ta koma gidan Hamma Abubakar da zama domin a son ranta ƙauyen dai ta so komawa ko jiran dawowar Baba Alhajin da Hamma Adnan yake ta ƙiran wayansa ba ta shiga ba su yi suka tafi tare da Adda Azima da Anwar. Figigi na zabura tamkar wacce aka tsigarawa matsilli ina kurma ihu ina faɗin"Umma". Wani jami'in 'yan sandan ya zo wajen da hanzari ya na tambayar me ke faruwa. Wasu hawayen suka ciki mini idaniya na haɗo na kalle shi hawayen su na zuba na ce"don Allah Ummata nake son gani. Na roƙe ka ƙira mini ita ko a waya ne." Kallon da ya jefa mini ya tursasa ni saurin janye idona daga kan sa. "Ba hawaye idanunki za su na fitarwa ba, ko jini ne wallahi ni dai kam ba zan ji tausayinki ba. Balle har na nema miki sauƙi, babu wanda zai shigo ya ganki a nan wajen a yanzu sai dai lauyanki. Don haka tun wuri ki cire ran sake ganin kowa idan kun haɗu a kotu bayan an yanke mi ki hukunci ku yafi juna da su". A wulaƙanci ya yaɓa mini zancen cike da ƙyama da kuma kyara. Ya na gama faɗin hakan ya joya ya fice babu jimawa ya dawo ya buɗe ɗakin ya danƙwafa mini akwanon abinci da ruwa a gabana ya fice. Na jifa kaina ina ƙara sakin wani kukan marar sauti sai dai haifar da zogi a cikin rai. Tunanin Umma ya ƙara ruru wutar tashin hankalin da nake ciki ina jin zuciyata tamkar za ta fashe. A bayyane na furta"wallahi ban kashe Abdul -hameed ban kashe ba. Abdul-hameed bai mutu ba". Na ƙara fashewa da wani matsanancin kukan idanuna su na hasko mini hotonsa cikin farar kaya ƙyal ya na baza kyakkyawan murmushin da yake bayyanar da wushiyar dake tsakanin jeranrun fararen haƙwaransa. Ƙunci ya mamaye mini zuciya izuwa yanzu na daina kuka da hawaye sai dai na zuci mai tsananin ƙuna. Ba na iya runtsawa ba saboda zafin da ƙirjina yake yi mini ga wani tarin da ya turnuƙe mini rai idan ya na yi kaki maimakon miyau jini nake tofarwa. Kwana biyu tsakani babu wanda ya zo wajena sai a yinin na uku Barrister Aliyu ya zo ganawa da ni har cikin ɗakin da nake ya shigo ya yi zaman dirsham a gabana. Dishi-dishi idanuna suke iya gane mini shi, kunnuwana da su na jiyo mini sautin muryarsa can ƙasa ya furta kalmar sunana. Na ɗago idona da ƙyar na yi masa kallo ɗaya ina mayar da kaina ƙasa. "Sati biyu cakal kotu ta ƙara mana a koma zama na gaba, wanda nake hashashen idan a ba yanke miki hukunci a wannan zaman ba to a zama na gaba dole hakan zai faru. Saboda jama'a sun fusata sosai akan case, idan aka cigaba da jan case ɗin za su iya ɗaukar doka a hannunsu su illata ki ko ma su hallaka ki. Hatta ni kaina da an ƙira ni a waya an yi min barazana akan na fita daga cikin case ɗin. Na yi iya ƙokarin ganin na bibiyi diddigin lambar da aka yi ƙiran dashi amma babu wata kafar yin hakan, rayuwar Iyaye, 'yan uwanki da duk wasu makusantarki su na cikin hatsari. Tambayoyi biyar zuwa shida zan yi miki domin tabbatar da wani hashashen zuciyata". Ban iya cewa dashi komai saboda nauyin da bakina ya yi mini da ya hana ni samun damar cewa ko kanzil. Shurun da na yi ya ba shi damar ɗaurawa da"ki ƙarisa min labarin zaman aurenku da marigaya a taƙaice". Na ja dogon numfashi na fesar ina haɗiye miyau ɗin da ya taro a bakina kana na zama zarafin faɗin"Lokacin da Anwar ya taho da ni gida Baffa ya daka tsalle ya dire akan ba zan zauna a gidan ba sai dai in saki na ya yi. Da ƙyar da tsiɗin goshi Baba Alhaji ya jawo hankalinsa ya bar ni na zauna, ban koma ba sai da aka yi sunan Adda Abida wanda ta ci sunan Ummanmu Aliyatu. Sosai Hamma Ahmad ya nunawa Anwar ɓacin ransa akan me yasa zai taho da ni gida bayan ya san furcin da Baffa ya yi game da aurena. Ban koma ba sai da alamomin samuwar ciki suka bayyana a gare ni saboda wani rashin lafiyan da na yi na tsawon kwanaki uku , aka kai ni asibiti aka tabbatar da samuwar cikin sati biyar a jikina. Da kansa Baffa ya ƙira Abdul-hameed ya ce ya zo ya ɗauke ni mu tafi ba zan yi renon ciki a gida ba hakan aka yi na koma ɗakina tare da nasihar Umma da kuma Dada. Daga lokacin Baffa ya hana koma zuwa gidana, ko da na koma na tarar da Amira ba ta zuwa aiki da na nema jin dalili bayan na ƙira Asiya na sanar da ita ta shaida mini cewar bayan tafiyata gida Al'amin ya yi ƙoƙarin keta mata haddi shi yasa ta daina zuwa. Da ƙyar na shawo kan mahaifiyarta har ta dawo aiki, na fuskanci tarin ƙalubale daga wajen Amma da sauran 'yan uwansa a lokacin mijin Anty Alawiyya ya aiko mata da takardar saki kamar yanda ta daɗe ta na buƙatar hakan daga gare shi. Cikin ya na ɗan watanni biyar laulayi ya sako ni a gaba ba na iya taɓuka komai hakan ya sanya Amira dawowa gidan da kwana, na sama dukkan wani kulawa daga mijina. A lokacin Amma ta bijiro da wani sabon hali sai ta saita lokacin dawowarsa ya yi sai ta ƙira ni sashinta ta ce na zauna ba ta bari na na tafi har sai dare ya tsala. Ranar da naƙuda ya taso mini na sha baƙar wahala tamkar ba zan yi raina ba sai ba yar da wasiƙa nake yi. Sai da aka yi mini aiki aka ciro mini 'yan tagwaye, tsabar farin ciki da nuna godiyarsa ga Allah Abdul-hameed har azumi ya yi. Sai dai haihuwar ta zo da wani abu na daban domin yaran sun kasance dukkan su zabiya ne, Amma ta shafe idonta da toka ta ce sam ba jinin ɗanta bane domin a danginsu kaf ba a taɓa haiho zabiya ba. Sai da aka kai ruwa rana sannan ƙorar ta lafa bayan an gudanar da gwajin ƙwayar halittar da su ka nuna cewar yara dai na ɗanta ne. Tunda muka dawo daga asibiti ba ta shigo baSai ana gobe suna ta shigo tare da Anty Alawiyya suka zo ɗakina wai sun zo ganin yara da kanta ta sa aka yi musu kuɗuba, washe gari babu wanda ya sanar da mu sunan yaran sai da yammaci muka ji sunan mahaifiyarsa da na mahaifinsa aka sanya bayan mun gama magana dashi akan sai ɗau ɗaya nima na ɗau ɗaya, Adda Azima ita take ta tausa ta akan kar na tada hankalina akan hakan na yi addu'ar Allah ya raya mini su kawai. Tun su na cikin zanin goyo Al'amin yake gwada musu tsana da ƙiyayya a bayyane, a cewarsa wai ƙyamar ganinsu yake yi balle kuma ɗaukar su idan ya matso kusa dasu kuwa har kakakin amai yake ji. Na sha matuƙa wahala akan 'ya'ya kullum mijina cikin ba ni haƙuri yake tun ina ganin laifinsa idan wani abun ya faru har na dawo jin tausayinsa domin na fahimci ba laifinsa bane. Hamma Ahmad shi yake tsaye akan lamarin aurena duk wani matsala idan ta taso kafin na sanar da kowa shi nake fara ƙira na sanarwa. Mun zama ƙawaye sosai da Asiya lokuta da dama ta na taimaka mini da shawara akan abin da ya shige mini duhu, na yi gwagwarmaya har yarana su kai wata uku Amira ita ke taimaka mini da aikace-aikacen cikin gida, har wannan lokacin Hamma Ahmad bai yi aure ba har maganin aljannu ake karɓo masa da tunanin ko aljana ce ta aure shi ta hana shi aure amma duk a banza. Na yi ƙoƙarin haɗa shi da Amira amma abin zai yiyuwa ba. Amma ta tsiro da cewar tun bayan haihuwata na dawo ƙazama ko wulgawa na yi sai an ji ƙarnin nono a cikina. Yara kuwa daman ta ce a daina shigowa dasu sashinta. Lokacin da su ka watannin biyar cif a duniya wani iftila'i ya faɗawa Abdul-hameed ya yi asaran wasu maƙudan kuɗin a kasuwancinsu, na ga tashin hankalin da ba na fatan ƙara ganin makamcinsa a cikin rayuwata domin Amma da raguwar 'yan uwansa sun gaza fahimtarsa hasalima shi suke zargi da salwantar da kuɗin. Hatta gaisuwarshi sai da Amma ta daina amsa ta fita daga duk wani abun da ya shafe shi gabaɗaya, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba". Daga haka na tsagaita ina zuƙe majinar kukan da ya zo mini kana na ɗaura da" na sanar da Hamma Ahmad halin da ake ciki. Ba tare da sanin kowa ba ya sayar da shanayansa biyu da ya mallaka da suke ƙauye suka haɗa baki da mai kula dasu akan ya faɗawa su Baffa cewar sace su aka yi. Ba tare da sanin kowa ba ya damƙa mini kuɗin ya ce na bawa Abdul -hameed, ranar na yi kuka na yi kuka kamar raina zai fita na ƙara tabbatarwa kaina cewar lalle samun ɗan uwa kamar Hamma Ahmad babu dace ne a rayuwar nan ta duniya. Mamaki sosai na hanga a fuskar Abdul-hameed lokacin da na bashi kuɗin tare da zayyana masa yanda aka same su sai na ga hawaye su na fita daga idonsa. A take a wajen ya ƙira Hamma ya ce ba zai iya karɓan wannan kuɗin ba amma ya nuna masa cewar babu komai yi wa kaine, da kuɗin ya yi amfani wajen mayar da asaran da aka yi kasuwanci ya cigaba da tafiya. A wannan lokacin Amma ta bijiro da cewar lalle zai ya ƙara aure domin ya sama 'ya'yan da suka amsa sunansa kuma cikakkun ba irin wanda na haifo masa. Idan na ce ba na kishin mijina wallahi na yi ƙarya amma na yi ina ƙokarin dannewa wajen mayar da komai ba komai ba. Da kanta ta zaɓo masa matar da zai aura aka shirya kai kuɗi gidan su, sai dai hakan bai sai dai-dai da sakon ɗaya ya sauya mini ba illa ma ninka kulawar da ya yi a gare ni". A nan na ƙarƙare ina cigaba da kukan ya taso mini ina ganin komai a idanuna tamkar yanzu su ke wakana. Ina jiya jiyo sautin ajiyar zuciyar da Barrister Aliyu ya sauƙe kana ya ce" sorry" ya zaro handkerchief a aljihunsa ya miƙo mini na karɓa na goge fuskana. "Ranar da lamarin ya faru za ki iya tuna wani abu muhimmi da ya faru?". "Babu wani sabon abu da ya faru, na bar Amira da yara ta na shirya su na fito falo wajensa kasancewar ranar ban ji daɗi ba bai fita ko ina ba gashi kuma ya na azumi". Ya yi ɗan jim kafin ya cigaba"ki dai ƙara tunawa babu wanda ya ko ya shigo inda kuke je?". Na yi shuru ina nazari sai can na furta"Asabe ta zo ta ce da ni Amma ta na ƙira na". Da sauri ya tari numfashina"za ki iya tuna abin da ya faru da kika je sashin natan?". Na gyaɗa masa kaina"damammiyar madarar da aka sanya zuma a cikinta ta saka Asabe kawo mini. Ta umarce ni da na shanye ta tas a gabanta saboda samun wadataccen ruwan maman da zan shayar da yarana da suka fara darawa". "Daman ta saba ba ki madarar ne ko kuma wannan ne karon farko?". "Wannan ne karon farko, saboda a lokacin abincin da suke samu daga gare ni ba ya isar su. Sai an haɗa musu da madara". Ya miƙe tsaye tare da goye dukka hannayensa a bayansa ya na zagaye ɗakin yana faɗin"babu wani abun da ya faru bayan kin sha madarar?". "Babu komai, na dawo sashina muka cigaba da hirarmu da Abdul-hameed". Ya yi shuru ya cigaba da zagaye ɗakin da yake yi a zabure ya jefo mini tambayar"wa ya kawo miki madarar kika ce?". Na ɗaga kaina na kalle shi"Asabe 'yar aikin Amma". Ya jinjina kansa haɗi da haɗe hannayensa waje guda yana faɗin"na sama abin da nake nema. Zan tafi yanzu amma zan dawo kafin a koma kotu". Kaina kawai na ɗaya masa ya juya ya fara tafiya har ya kusa ficewa ya waigo da faɗin " kin yi dacen ɗan uwan da samun kamarsa sai an tona Hamma mutumin kirki ne". Yana faɗin haka ya fice ta bar ni rusar kuka. *ƁOYAYYAR MANUFA* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________ Page 4️⃣0️⃣ Motarsa da ya faka ta a waje Barrister Aliyu ya nufa yana tafe ya na nazari a cikin ransa, da tunanin ta yanda zai ɓullowa wannan lamarin mai tsarƙarƙiya. Ya na shiga motar ya maida ƙofar ya rufe tare da jingina bayansa jikin kujerar dake zaune yana lumshe idanunsa. Jin an saita shi da wani abu a kansa ta baya ya sanya shi saurin buɗe idanunsa a zabure jikinsa ya na rawa. "Idan ka juyo sai na harba kunaman bingiran nan na fasa kanka. Kashegi na zo na ƙara yi maka a karo na biyu idan ba ka ajiye wannan case ɗin da kake yi na Aishatu ba rayuwarka da ta iyalinta matarka da ta je gidansu haihuwa duk ku na cikin babban hatsari". Runtse idanunsa ya yi jin ya ambaci matarsa da ta shiga cikin watannin haihuwarta. Zuffa ya na kwanciya a bisa goshinsa ya ce"matsalarku da ni ba da matata ba kar ku sako ta cikin wannan case ɗin". Ƙara danna masa bindigan ya yi cikin kakkauran murya ya furta"kuskuren da kake son yi na ganin ƙarfi da yaji ka wanke ta. Shi ya shafi matarka da kake tsananin so, idan ka ɗauki gargaɗin da na yi maka ka ajiye wannan case to ka yi kyan kai, idan kuwa ka yi kunnen uwar shegu to ka yi kuka da kanka". Ya na gama faɗin hakan ya buɗe motar da sauri ya fice tare da shigewa wata motar da ta faka a wajen yanzu. Da ƙarfi aka figi motar aka bar wajen, ya fito da sauri ya na bin motar da kallo ko lamba babu a cikin motar da dukkan alamu sabuwa ce ko kuma since lambar aka yi. Dafe kansa ya yi ransa cike da damuwa a tarihin aikinsa na lauyanci bai taɓa cin karo da case mai sarƙarƙiya kamar wannan ba. Bai taɓa gudanar da shari'ar da ta jefa rayuwarsa da ta iyalinsa cikin hatsari ba sai wannan. Da hanzari ya koma cikin motar ya ɗauko wayarsa ya fito ya ɗauki hoton bayar motar sannan na ya fara ƙiran layin matarsa Asma'u, sai da ƙiran ya kusa katsewa ta ɗauka cikin sanyin murya ta yi sallama bai amsa ba illa sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi da ya yi. Jin muryarta kaɗai da ya yi ya samar masa da nutsuwa ya kuma goge masa mummunan hashashen da zuciyarsa take yi masa. Kashe wayar ya yi ba tare da ya ce da ita komai ba ya kifa kansa a bisa sitiyarin motar. Waye wannan da yake yi masa barazana a waya da har ta kai ta kawo ya fito masa yau a zahiri tare da yunƙurin ɗaukar rayuwarsa?, Me yasa yake son ya ajiye wannan case ɗin mai girman gaske? . "Waye wannan! Waye wannan?". Ya furta a bayyana ya na kaiwa iska naushi, ya daɗe a wajen da tunanin yanda aka yi ya san inda yake da kuma hanyar da ya bi ya shigo cikin motar bayan da hannunsa ya rufe ta kuma yanzu da ya fito sai da ya danna makulli kana ta buɗu. Da ƙarfi ya figi motar bai tsaya ko ina ba sai ofishin 'yan sanda, bai fito ba ya na zaune cikin motar ya ƙira layin Inspector Ammar wanda case ɗin Aishatu yake a hannunsa kafin a miƙa ta kotu. Mintuna ƙalilan tsakanin ya fito ya buɗe ɓangaren mai zaman banza ya shiga. "Barrister lafiya kuwa?". Sai da ya furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakinsa ya na shafa sajen fuskarsa kana ya ce"Ammar akwai matsala bayan wannan lambar da na turo maka an ƙira ni dashi an yi min barazana game da wannan case ɗin. Yau kuma har cikin motata aka shiga aka sanya min bindiga akan ƙara jaddada min na ajiye wannan case ɗin, matuƙar ina ƙaunar zaman lafiyar matata da abin da take ɗauke dashi a cikin cikinta". "Ya salam! Ina fata dai ba su cutar da kai ba?". Kansa ya ɗaga masa ya na latsa wayarsa ya nuna masa hoton bayan motar da ya ɗauka. Ya karɓa ya na gani a tsanake sai da ya gama kallo tsaf kana ya ce"ka tura min hoton ta what's app za mu yi bincike akan motar da kuma mamallakinta in sha Allah za mu gano ko waye ne ka kwantar da hankalinka, sannan kar ka ɓoyewa matarka komai ka sanar da ita ta yanda da zaran ta ga wani abun da ba ta yarda dashi ba za ta ƙira ta sanar da kai". Kansa Barrister Aliyu ya jinjina cike da yaba ƙoƙarin Ammar ɗin ya ce"I trust you inspector na yarda da kai". Murmushi ya yi masa tare da faɗin"ya ya ake ciki game da zaman da za ayi a kotu, akwai alamun nasara kuwa?". "In sha Allah akwai alamun nasara domin na fara hango wani haske game da lamarin. Gobe ina so na je na gana da mahaifiya da 'yan uwan marigayi". Gyara zamansa inspector Amma ya yi sosai yana sauƙe ajiyar zuciyar da ya tokare masa ƙirji. A sanyaye yake faɗin"wallahi na daɗe ban ji labarin da ya yi matuƙar ɗaga min hankali ba irin labarin rayuwar yarinyar nan, yarinya ƙarama amma ta haɗu da jarabawar rayuwa". Cije leɓansa ya yi da ƙarfi kana ya sama damar faɗin" shi yasa nake son tsayiwa tsayin daka wajen ganin na yi duk mai yiyuwa don ganin ta buƙuta, idan ka ga halin da mahaifiyarta take ciki sai ka zubda mata da ƙwalla". "Allah ya taimaka, in sha Allah za ka sama duk wani gudumawan da kake bukata daga gare ni ". Murmushin ƙarfin halin Barrister Aliyu ya saka ya na miƙa masa hannu su ka yi musabaha, bayan Inspector Ammar ya ba shi wani nau'rar da duk inda yake ya danna ta saƙo zai iso masa. Daga cikin ofishin gidansa Barrister Aliyu ya wuce ya yi wanka tare da sauya shiga zuwa marasa nauyi ya zauna ya na nazarin labarin da na ƙarishe masa ɗazu, daki-daki ya ke breaking ko wani jumla. A zabure ya furta"i get it". Ya ƙare zancen ya na jawo wayarsa ya shiga latsa lambar Asma'u. Tunda Umma ta dawo gidan Hamma Abubakar duk dare ba ta iya runtsawa da wani azababben ciwon kan da yake ta'azzaranta. Sawun Baba sau huɗu gidan ya na bata haƙurin ta koma ko zaman 'ya'yanta ta yi kafin lamarin ya dai-dai. Amma ta nuna cewar tun da ya furta zama ya ƙare tsakaninsu to ita ma kuwa babu abin da zai ƙara haɗa ta zama inuwa ɗaya dashi. Sai a lokacin Abasiyya ta zo don farko Hamma Adnan ne daman ya hana ta zuwa saboda tsohon cikin da take ɗauke dashi haihuwa ko yau ko gobe. Ba don ransa ya so ba dole ya haƙura ya bar ta, ya bata lokacin har zuwa lokacin da za ta huce. Ko kaɗan bai ga laifinta akan hakan ba. Da Yamma Barrister Aliyu ya zo duba jikin Umma. Ba don ya ƙara musu wani tashin hankalin akan wanda suke ciki ya sanar dasu barazanar da ake masa ba sai ya zama dole su sa ni. Cike da damuwa Umma ta furta"ɗan nan ka yi matuƙar ƙoƙari da halacci a gare mu wanda ba za mu iya biyanka ba hasalima bamu da abin da zamu iya saka maka dashi. Kar ka saka iyalinka cikin matsala a dalilinmu gwada kawai ka ajiye case ɗin kamar yanda suka buƙata ka yi, na yi imanin idan Aishatu ta na gaskiya Allah ba sai taɓa bari ta wulaƙanta ba, ko kashe ta aka yi sai gaskiya ta yi halinta sai kuma an gane cewar tabbas an cutar da ita". Ta ƙarishe zancen wasu hawaye su na gudun famfalaƙi a bisa kumburarriyar fuskarta da ta yi him tamkar kwaɓin famken da ya ji sinadarin yis. "Umma ba zan taɓa ajiye wannan case ɗin ba har sai na tabbatar da gaskiya ta yi halinta. Kar ki damu da duk irin matsalan da zan shiga domin hakan aikinmu ya gada, addu'arki kawai muke buƙata". Shuru Umma ta yi don ta gaza samun kalaman da za ta yi amfani dasu wajen saka masa irin alkhairin da ya yi musu. Maganar da ya cigaba da ya yi ya dawo da ita duniyar zahiri da ga kogin tunanin da ta faɗa. "Gobe ina son na je na gana da dangin marigaya. Domin samun amsoshin wasu tambayoyin daga gare su" Jinjina kanta kawai ta yi daga haka ba ta ƙara cewa uffan, su ka cigaba da tattaunawa da Hamma Ahmad da Abubakar game da lamarin ƙiran sallan magrib ne ya sanya su fice. Washe gari tun safe Barrister Aliyu ya yi dirar mikiya a ƙofar gidan marigayi Abdul-hameed. A waje ya ajiye motarsa ya fito ya na ƙarewa zubin gidan kallo, ya tako ya iso bakin gate ɗin a hankali ya fara ƙwanƙwasawa daga ciki aka ce waye ne. "Ɓako ne". Sai da aka yi ɗan jim kafin aka buɗe suka gaisa da mai gadin, ya nuna masa ID card ɗin sa tare da yi masa bayanin wanene shi da kuma abun da yake tafe dashi. "Allah sarki Hajiya! Wallahi kullum ta na cikin addu'ata Allah ya fitar da ita wannan sarƙarƙiyar da ta faɗa ciki ". Sosai Barrister Aliyu ya ke ƙare masa kallo kana ya ce"Amin, a yi min iso wajen Hajiyar". Gaba ya wuce ya na bin sa a baya har bakin sashin Amma, kana ya dakata shi kuma ya shiga. Ya zura dukkan hannayensa a aljihunsa ya na ƙara kallon farfajiyar gidan a ransa yake ayyana cewar tabbas wancan sashin dake kallon na Amman shi ne wanda A'isha da Abdul-hameed suka rayu a cikin sa. "Waye ne yake son ganin Amman?". Ya ji an furta da ya sanya shi saurin waigowa ya na ƙarewa matashin da ya furto zancen a gantsale ya na harare- harare. Hannu Barrister Aliyu ya miƙa masa su yi musabaha ya ɗauke kansa, janye hannunsa ya yi yana faɗin"Hajiyar ta na ciki ne? Ina son ganawa da ita". "Ta na ciki lafiya?". ID card ɗinsa ya yi masa nuni dashi daga haka bai ƙara cewa komai ba. Da sauri mai gadin ya bar wajen saboda kallon da Al'amin yake jifarsa dashi. Ya na doso ƙofar falon sautin tsala ihu ya fara sauƙa a ƙofofin kunnuwansa. Akan yaran da suke yashe a falon idanunsa suka fara sauƙa, alamar ihun da suka yi dole cikin biyu akwai ɗaya ko faɗuwa suka yi ko kuma ɗauke su aka yi da gigitaccen mari. Zama ya yi har yanzun ya kasa ɗauke idonsu akan su. Ƙarar sauƙowar mutum daga matakalan benin shi ya tursasa shi kawar da idonsa daga kan yaran. "Me ya sama waɗannan yaran suka cikawa mutane kunne kamar jiniya?". Al'amin ya furta a tsawace, take cikin 'yar aikin dake tsaye ta na share abin da ya fashe a wajen ya fara rawa. Cike da tsoro ta ɗago ta furta"lallashin su nake ta yi tun ɗazu, madarar ma sun ƙi sha". Tsaki ya saka dai-dai sanda Amma da Anty Alawiyya suka ƙariso suka zauna a kujerar dake kallon wanda Barrister Aliyu yake zaune. Sosai yake nazarin yanayin yaran da kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci cewar lalle su na cikin takura da tashin sakewa. "Kai ne kake so magana da ni?". Furucin Amma ke nan da ya sanya shi dawowa hayyacinsa daga shagala da kallon su Ashraf da ya yi da har yanzu su ke kukan. Da ido Amma ta yi wa 'yar aikin alama akan ta ɗebe su ta fice daga falon, da rawar jiki ta aiwatar da umarninta. Sai da ya yi gyaran murya ya ce"ƙwarai ni ne Hajiya lauyan dake kare Aishatu a kotu". "Mun gane ka ai". Anty Alawiyya ta furta ta na musgutawa cike da son jin abin da ke tafe dashi. Murmushi ya yi kafin ya ce"ya ƙarin haƙuri kuma? Allah ya jiƙansa". Suka haɗe baki wajen amsawa da kalmar Amin, kafin ya ɗaura da"wasu tambayoyi ne ke tafe da ni". Jinjina kanta Amma ta yi alamar ta na ji da sauraronsa. "Tun da aka fara zaman wannan shari'ar Hajiya ba ki halalci zaman kotu ba, ko me ye dalili? Shin daman akwai wani uzurin da hana ki halaltar zaman shari'ar kisan ɗanki?". Cike da ta-ka-tsantsan ta furta"tun ranar da Abdul-hameed ya bar duniya ban ƙara kwana ɗaya da lafiya ba, saboda kaɗuwa da kuma zafin rashin da har yanzu bai bar ni ba wannan dalilin shi ya hana ni zuwa kotu. Sai da ya ƙare mata kallo kana ya ce"Allah ya ba ki lafiya, 'yar aikinki Asabe zan iya ganinta?". Tabbas ya lura da yanayin firgicin da ya sauƙa a fuskokin Al'amin da kuma Anty Alawiyya. Sai dai tsabar iya taku irin na Amma sam ta ƙi barin kaɗuwar da ke zuciyarta ya bayyana a bisa fuskarsa. Cikin tsantsar iya takunta ta soma faɗin"ta je gida ganin 'ya'yanta". "Tun yaushe?". Ya katse ta da hanzari. "Tun washe garin ranar da aka yi sadakan uku". "Ko zan iya sanin garin da take ɗin". Cikin nuna ko a jikinta ta ɗage kafaɗarta"me zai hana, nan ne babu nisa garin abuwa gidan tsohon sarkin noma". Ta na ƙare faɗin hakan ta fashe da kuka mai ƙarfi har da shashsheƙa. "Aisha ta cuce ni, ta raba ni da Abdul. Ta bar min wani babban giɓi a cikin zuciyata da babu wanda zai iya cike min shi. Tsakanina da ita Allah ya isa yanda ta sanya zuciyata ƙunci ina addu'ar Allah ya ninka maka sau dubu". Rarrashinta Anty Alawiyya ta soma yi"ki yi haƙuri Amma in sha Allah sai ta girbi abun da shuka, ai kowa ya san hukuncin wanda ya kashe rai a kashe shi ne". Taƙaitaccen murmushi Barrister Aliyu ya yi ya na yin ƙasa da kanta ta gefen idonsa yake ƙare wa girman kallo ya ce" Hajiya shi fata na gari na lamiri ne". "Malam ko don irin hakan bai taɓa faruwa da wani na ka bane shi yasa kake faɗin haka?. Anya ka san raɗaɗin da zuƙatanmu suke a ciki kuwa?". A fusace Al'amin ya yi zancen da kumfar baki Shafa fuskarsa Barrister Aliyu ya yi kana ya ce"ko bai taɓa faruwa a kaina ba zan iya fahimtar hakan. Anywhere na gode da lokacin da ki da kika ba ni, ni zan tafi". Kanta kawai ta ɗaga masa ya miƙe har ya yi gaba, Al'amin ya furta"to mu ma mun gode". Da hanzari ya waigo haɗi da cewar"kamar na taɓa jin muryar nan a wani waje". "Ni-ni-ni-ni? Ba ni ba ne malam". Murmushi kawai Barrister Aliyu ya kuma saka a nutse ya furta"sai mun haɗu a kotu, na bar ku lafiya". Miƙewa Anty Alawiyya ta yi ta leƙa ta tabbatar da ya fice kafin ta dawo ta zauna cikin tashin hankali ta furta"me kike ƙoƙarin aikatawa Amma?. Anya kin san me kika aikata kuwa?. Sanar da shi inda zai sama Asabe fa ki ka yi, bayan kin san akwai sirrinmu da yake ɓoye a wajenta mai muhimmancin gaske". Murmushi mai sautin gaske Amma ta saka ta na gyra zamanta ta ɗan zamo daga kan kujerar da take zaune kana ta ce"yarinya ce ke har yansu Alawiyya shi yasa kika kasa gano ƁOYAYYAR MANUFAta ta sanar dashi hakan. Idan muka ɓoye masa zai nemo to gwada mu sanar dashi da bakinmu domin gujewa matsala". Ta dafa kafaɗarta ta mai cigaba da cewar"ki kwantar da hankalinki na yi muku alƙawarin yanda wanda ya mutu ba ya taɓa dawowa haka sirrin da muka ɓoye ba zai taɓa tashi duniya ta ji ba". "Afuwan na katse muku zancen da kuke yi, makullin motana na mance na dawo ɗauka". A tsorice duk suka waigo jin furucin Barrister Aliyun a bazata. Ya tako ya iso wajen kujeran da ya zauna ya ɗauki makullin tare da ƙara yi musu sallama, har ya fice babu wanda ya ce da shi uffan a cikinsa illa kallon da suke bin sa dashi. Iska Al'amin ya kai wa naushi ya na miƙewa a fusace yake nuna Amma da manuniyar yatsarsa"Amma kin ga ni ko wallahi mutumin nan zai zame mana babban matsala. Shi ne fa wanda kwanaki biyu da suka wuce na sanya masa bindiga a kai na ja masa warning, kin ga gashi yanzu ya gane ni". Ita miƙewar ta yi"shi yasa na hane ka da aikata komai ba tare da sa ni na ba. Ina so kafin ya kai ga garin abuwa a tabbatar da cewar Asabe ta bar cikin wannan duniyar, sannan kar a bar wata alamar da zai karkato da zargi kanmu ". "Dama umarninki kawai nake jira amma da na daɗe da kawar da matar nan. Don duk lokacin da na tuna cewar ta san sirrinmu hankalina ba ya kwanciya. Hatta 'ya'yana su Ashraf ni fa ƙaunar ganin su nake yi b...". Marin da Amma ta ɗauke shi da shi cikin ƙankance ido ta ke faɗin" ka yi iya abin da na faɗa maka, ka bar min sauran komai a hannuna". Kansa ya ɗaga mata ya na dafe ƙuncinsa cikin tafasar zuciya. Cikin kwanakin nan babu abun da nake yi wa kaina fata face mutuwa tun kafin a gurfanar da ni a gaban kotu. Wataƙila a yanke mini hukuncin da zai sanya zuciyar Ummata buga, ta jefa 'yan uwana cikin wani yanayi. A na gobe sauran kwanaki biyu Barrister Aliyu ya zo ganawa da ni, nan ya sanar da ni wani BIYAYYAR MANUFAR da ya ƙara hautsina mini tunanina. Ya ƙara jefa ni cikin wani mungun yanayi. Ban dawo dai-dai ba har ranar da aka komar da ni kotu, da ƙyar aka sama hanyar da aka shigar da ni cikin kotun Saboda yawan mutanen ya zarce na ko wani lokaci. Umma da duk yayyuna maza sun hallara a cikin kotun har da Baba Alhaji. A wannan zaman bayan Anty Alawiyya, Anty Adama da Al'amin hatta Amma ta halaccin zaman. Har Alkalin ya shigo Barrister Aliyu bai zo ba. Ina jin tashin zance daga cikin 'yan zaman kotun su na faɗin Barrister Aliyu karaya ya yi shi yasa bai zo ya na gudun a kayar dashi a case ɗin. Barrister Adam da magoya bayansa su ka fara farin cikin ganin alamar nasara ta na gare su. Hankalin kowa ya na kaina na kasa ɗago kaina zuciyata ta harbawa a raunane. Na gama cire buri game da cigaba da zama a cikin wannan duniyar, zuciyata ta na raya mini cewar daga nan nima kashe ni za a yi . Jin wani hayaniyar ya na tashi ya tursasa mini haɗo kaina da nake kunyar haɗa ido da Umma da kuma sauran yayuna. "Alhamdulillah ga shi nan ya ƙariso". Na ji an furta daga ɓangaren da kunnuwana suke ji yo mini. A gaggauce ya ƙariso gaban kotun ya na ɗingisa ƙafarsa"afuwan ya mai girma mai shari'a ina mai ba ta haƙuri akan rashin zuwa na akan lokaci. Saboda wasu abubuwan da su ka taso da suka tursasa faruwar hakan". "Hakan ya na faruwa ba ka da matsala Barrister Aliyu, kai kotu take saurara ka gabatar da hujjojinka". Rusunar da kansa ya yi alamar girmamawa"tabbas yau ina tafe da hujjan da zai warware duk wani ƁOYAYYAR MANUFA. Na fayyace abin da kowa ya daɗe ya na dakonsa. Zan so kotu ta ba ni damar shigo da Asabe da take waje tare da jami'an tsaro". Hatta ni kaina sai na razana da jin sunan wacce ya ambata. Mai shari'ar ya ba shi dama kamar yanda ya buƙata. Aka shigo da ita ta na tafiya da ƙyar da bangejin da aka kewaye kanta da shi, an naɗe hannunta a ƙasan ƙirjinta alamar karaya. Ta tsaya a gaban kowa, shuru ya ɗauki wajen. Har zuwa lokacin da Barrister Aliyu ya soma faɗin"kotu za ta so jin abin da kika sani game da wannan case ɗin domin warware mana zare da abawa". Maimakon ta ba shi amsa sai ma fashewa ta yi da kuka tare da cewar"tabbas ina ɗauke da sirrin da zai warware duk wani ƙulli". Ta dakata a nan ta share fuskarta da ɗayan hannunta mai lafiyar kana ta nuno ni"Aishatu ita ce ta yi kisan Abdul-hameed, sai dai ba ta cikin hayyacinta domin sai da ana gusar mata da hankalin ta hanyar sanya mata wani sinadari cikin madarar da ta sha. Ya fitar da ita daga hayyacinta ta yanda a lokacin duk abun da aka umarce ta ta yi shi za ta aikata ko menene saboda ba ta cikin hayyacinta". Shuru ya ƙara karaɗe wajen, Barrister Aliyu ya gyara tsayiwarsa"su waye su ka gusar mata da hankalin? Sannan me ye faru bayan shan madarar da ta yi?. Me ye manufarsu ta aikata hakan?". Shuru ta yi ta na zazzare idanu alamar tsoro da firgici ƙarara a bisa fuskata. Ta kasa cewa komai har sai da ya ƙara cewa"kar ki ji tsoron komai domin ki na ƙarƙashin kulawar hukuma". Sai da ta ja lokaci kafin ta fara yunƙurin buɗe bakinta za ta yi magana ba ta kai ga furta abin da yake cikinta ba ta faɗi a wajen sumammiya. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! A nan na kawo ƙarshen liffafi na farko, sai mun haɗu a littafi na biyu wanda yake ɗauke da amsoshin tarin tambayoyin da suka tsaya muku a rai. Shin Abdul-hameed ya mutu? Me ya faru bayan shan madarar da Aishatu ta yi? Ta ya ya zai kasance cewar ita ta kashe shi?. Menene sirrin da su Amma su ke tsoron Asabe ta tona shi ga duniya?, Anya Amma ita ce mahaifiyarsa?. Me dalilin bambamcin da take gwadawa tsakaninsa da Al'amin?, dukiyar da ya ke juyawa wanene mamallakinta?. Menene makomar rayuwar Aishatu? A wani irin rayuwa 'ya'ya da maraicin uba ya faɗa musu da ƙarancin watanni za su taso? Tsakanin Hamma da Anwar wa ye zai ƙara da Aisha? Idan ta tabbatar A'isha ta kuɓuta daga wannan sarƙarƙiyar da wani ido Baffa zai kalli Umma?. Duk za ku sama amsoshin waɗanda tambayoyin cikin littafi na biyu akan N500 kacal. Da a fara posting ɗin a ranar goma sha biyar ga watan Nuwamba. Domin ƙarin bayani, shawara, ko kuma neman littafi na biyu za ku iya tuntuɓa ta akan wannan lambar kamar haka 07038908713.