*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_* *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *A RUBUCE TAKE* (K'addarata) *Book 02* Page 01 Cikin mugun mutuwar jiki kasala da kuma fargaba ta hada kalmomin "Wacce irin matsala kuma umma?,na shiga uku" "Malam baiga komai akan yarinyar ba,komai ya rufe masa,bai hangi ciki ba,kamar yadda babu tabbacin babu shi". Goshinta hafsat ta dafe,tana jin yadda zuciyarta ke tafasa,a zahiri tayi mugun tsanar yarinyar,ta zame mata qarfen qafa sosai,tanason kuma ta zama barazana ga rayuwarta,cikin tsananin fusata tace "Umma,yayi mata koma meye,duk abinda ya dace da ita da zai d'ai d'aita rayuwarta ayishi,banason ganinta kwata kwata cikin gidan nan,yanzu haka fa abban mimi ya biya mata hajji,aikin hajji zasu tafi" ta qarashe maganar tana barkewa da kuka,don abun yayi mata ciwo ba kadan ba. Salati umman tata ta sake kamar tana gaban hafsat din "Kina raye kina kallo?,lallai sai munyi da gaske,sai mun tashi tsaye akan yarinyar nan" *A B B A S* "Ya salam" ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki, kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare da samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad. Ido suka hada shi da ita,ta narke fuska sosai,dab take da sakin kuka,suna hada idon kuma sai rauninta ya bayyana muraran,yasan tabbas yau akwai daru,amma koma meye a shirye yake daya shanyeshi,ciki a jikinta?,cikin da yasha yi mata wayo yana gaya mata ba tarayyarsu ce zata saka tayi ciki ba,shan ruwa a qoshi ne?,yasan lallai zai sha tuhuma. Hannu ya miqa mata alamun ta taho har yanzu murmushi kwance bisa fuskarsa,amma sai ta kauda kai hawaye na ziraro mata,yasan za'a rina,yau saita Allahu,ya dinga danne dariyarsa sannan ya.miqe tsam ya isa gabanta,ya tsaya daga gefanta yana riqe da hannunta yana murzawa a hankali cikin nasa,idanunsa akan na dr "Yanzu ya za'a yi?,ina fatan bazai bada matsala ba wajen tafiya" "Bana jin gaskiya,zanyi qoqari ayi mata komai ku wuce tare,tunda bai nuna ba" ta fada ita kanta tana mamakin watannin cikin,da kuma yadda ya boye kansa da kyau,iya ganinka ba zaka hangeshi jikinta ba. Komai da akeyi kawai tana binsa da ido ne, hankalinta gaba daya bai jikinta tunda akayi zancan ciki,tsoro da fargaba gaba daya sun hadu sun lullubeta,har suka gama komai yana riqe da hannunta,ya bude mata gaban mota ta shiga ya maida murfin ya rufe ya zagaya mazauninsa shima. Ai yana shiga tana fashe masa da kuka,kamar wadda ke jira,ya dakata daga kunna motar ya waiwayo yana dubanta "Ya salam ya Allah.....menene kuma?,ko wani abun na miki ciwo?" "Wallahi idan abba yaji ka yimin ciki sai ya kashemu ni da kai" duk yadda yaso ya riqe dariyarsa amma wannan karon ya gaza,dariya ta kubce masa,har sai da yasa zara zaran yatsuntsa ya toshe bakinsa kada cibi ya zama qari,sai yaushe zata gama girma ne?,ashe har yau da sauran quruciyar nan tana nan?,ta yaya zai bullo mata,sai kawai ya juya fuskarsa zuwa kalar alhini shima yana dubanta "Innalillahi......yanzu ya kike ganin za'a yi?" Da farko dariyarsa ta qular da ita,amma yanzun maganar da yayi saita wanke wancan "Nima ban sani bafa....duk kaine ka jawo,saida nace banaso,kace wai idan nasha ruwa ne zaizo" ta fada yana harararsa,saiya narke fuska kalar tausayi ya langabar da kai "To ai nima na zata hakanne,kuma ma kinsan me?" Kaita girgiza tana sharar qwalla,sai ya juyo yana fuskantarta sosai "Sanda kika gudu kano?" Saita gyada kai tana dubansa "Abba da kansa ya kirani yace nayi wannan abun fa da bakiso din" dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu fado tana kallonsa a tsorace,ya jijjiga mata kai "Da gaske nake" ya sake fada yana danne dariyarsa,bai ankara ba ya takai masa duka tana sake fashewa da wani kukan a sakalce "Allah abbana ba dan iska bane da zaice maka haka" sosai yau din take sashi dariya,ya kare dukan da daya hannun yana dariya tare da fadin "Allah.....Allah kinji nace Allah" ta sanshi farin sani,kaifi daya ne,baya qarya,yana fadin hakan sai kunya ta kamata,ta kifa kanta a cinya tana juya yadda abban nata zaice haka,yanzu.kowa.kenan yasan abinda suke aikatawa?,tana jinsa yanata magana amma bata dago ba bare ta amsa,yana dariya qasa qasa ya tashi motar sukabar asibitin,ransa fes,zuciyarsa qal,wani farinciki daya jima rabon da yaji irinsa ya cika masa zuciya,har hakan yana bayyana kansa saman fuskarsa. Saida sukayi nisa a tafiyar yace "Kona ajjiyeki gidan hajiya?" Ya fadi hakanne saboda yadda yaga sam.batason zaman gidan nasu,saita girgiza kai da sauri "Aah,nidai ka kaini gida" murmushi ya subuce masa,ya gane mai take gudu,kada hajiya ta gano tana da ciki,daga haka yabar zancan ya dauke kan motar suka nufi gida. Sanda ya tsaida motar da kansa ya dauki hand bag dinta yana riqe da ita zuwa ciki,ta langabe kai tana kallonsa "Ka bani,zan iya dauka" kai ya girgiza idanunsa cikin nata,yana jin wata qaunarta tana fusgarsa "Ban yarda ba baby,dama naji a jikina,wannan rashin lafiyan akwai dalili,muje kawai,ko na daukeki?" Ya fadi shima yana langabar dakai,kunya ya bata,ta kauda kanta gefe tana gulmarsa cikin ranta,wai shi kam bayajin kunya ne ma wai?,kamar ba ciki yayi mata ba?. Kamar yasan maganar da takeyi ya saki murmushi kadan,ya kama hannunta ya matsa kadan yana cewa "Muje baby". Sanda suke shiga din akan idanun hafsat dake tsaye bakin window,tunda suka fita ta kasa zama,zuciyara nata qiyasta mata gurare daban daban da zasu iya zuwa,tana goye da shukra dake ta faman rigima,ji take kaman ta yago yarinya ta ajjiyeta,qunqunin yarinyar har tsakiyar kwanyarta,idanunta suka sauka kan handbag din widad da hannayensu dake sarqafe waje guda. Wani matsanancin qunci zuciyarta ta shiga,duk yadda taso daurewa amma ta kasa,ta saki ashar,kasheta mutanen nan sukeson yi?,bayan abinda abbas din ya aikata mata shine zasuci gaba da sabgarsu kamar ma ba'a yi mata komai cikin gidan ba?,ba zata iya dauka ba,dole kowa yasan an tabota,sai kawai ta kunce yarinyar ta aza saman kujera ta nufi qofa da wani irin mugun sauri. Idanunsa ya lumshe kadan,yana tsaye saman kanta yana mata wani duba dake cike da shauqinta,ko yaya ta motsa sai taja hankalinsa "Zan dan fita,amma bazan jima ba zan dawo,me kike buqata?" Ya qarashe fada yana ritsata da idanunsa masu matuqar kwarjini da jan hankali,sai tadan rufe idanunta kadan ta girgiza kai "Babu komai" "Really?" Ya tambayeta yana dubanta,kai ta sake gyada masa "Okay.....zan tafi" ya sake maimaitawa,saita sake lumshe idonta,tasna me.yakeso,amma jikinta a mace yake murus,ta gyara zamanta sosai ta nutse cikin kujerar sannan tace "A dawo lafiya" "Au 'yar hakace yau?" Murmushi tayi kawai tana boye fuskarta,saiya saki wani murmushin,ya duqa kadan a tausashe yayi kissing goshinta sannan yace "Take care of yourself" kai ta jinjina,sai daya juya sannan ta bishi da kallo,zuciyarta na gaya mata wai da gaske ba abun kunya sukayi ba,ta dora hannunta saman cikinta a hankali tana shafawa cike da mamaki da kuma tsoron cewa wai ciki ne a jikinta. Dai dai sanda muryar hafsat ta ratso har cikin falon nata da wani irin amo,sai ta bude idonta a hankali tana saurarenta sanda take magana cikin rawar murya "Wallahi bazan yafe wannan zaluncin ba,sai Allah yayi min sakayya" wani mugun tsaki widad din taja tana tabe baki gami da gyara kwanciyarta cikin kujerar,ita gaba daya mutuncin matar ya gama zubewa a idanunta,tunda take bata taba ganin yadda akema babba rashin kunya ba kamar yadda itadin taga tana yiwa abbansu mimin,ko babu komai aiya girmeta,kuma ko ummu da take tsohuwa ai tana ganin yadda take girmama alhaji,har tabar gidansu bata taba gani ta karba abu daga hannunsa daga tsaye ba,ko ya fada tace a'ah, miqewa tayi cak tana daukar jakarta ta wuce bedroom dinta,haka kawai taji batason jin wata hayaniya kusa da ita. Hannu daya abbas ya sanya cikin zallar bacin rai ya fincikota,ya riqeta gam yana tafe riqe da ita,bai tsaya ko ina ba sai da yakai sassanta ya watsar mata da hannun cikin falon,da yatsa ya nunata "Wannan ya zamana shine lokaci na qarshe da zaki qara gangancin cewa zaki shiga sashenta ko zaki tabata,daga lokacin da kikayi wannan kuskuren zaki fahimci baki da wayo,tunda na fahimci sauna ce ke shashasha wadda batasan girmanta ba" sosai maganarsa ta doketa kamar saukar mashi saman zuciyarta,ita din abbas yake cewa sauna shashasha? "Kowanne suna kakeso ka kirani dashi,daidanka ne,amma bazan fasa neman haqqina ba" "Idan kika fasa neman haqqinki kin raina Allah" kalmar da tasa ta bishi galala da kallo har ya fice,sai ta sake fashewa da kuka,dole tayi iya yinta taga ta tarwatsa farincikinsu,ba zata zauna ita kadai bacin rai ya hallakata ba. Yana tafe zuciyarsa cike da bacin rai,mahaifin hafsat shi daya yake tunawa,mutumin kirki da kowa ya yaba halayyarsa kafin barinsa duniya,yana sonsa yana girmamashi,har yau yana tuna haquri na qarshe daya bashi a kanta kafin barinsa duniya da 'yan awanni,yaja wani dogon tsaki,xuciyarsa na ayyana masa hukunci kala daban daban da zai iya dauka a kanta. A hankali kuma yaji yana sauka musamman daya tuna kyautar da Allah yayi masa a yau daga wajen halitta mafi soyuwa cikin rayuwarsa,sai yaji dukkan haukan hafsat din wani abune mara muhimmanci da zai iya tattarasu ya watsa kwandon shara,idan ta gaji ta sauke kamar yadda ta saba. *******Cikin kwanakin da sukayi cikin gidan kafin tashinsu saudiyya dan qaramin yaqi aka dinga gwabzawa tsakanin abbas da hafsat din,kullum cikin kuka qorafi da masifa,dai dai sanda 'yan abun nasa suka motsa(miskilanci),yayi watsin tsiya da ita,tamkar ma ba dashi take ba. Ta fannin widad ma sai tayi kamar batasan me ake ba,dama ita dimma ba baya bace wajen miskilancin,bare a yanzun da take mugun jin xafin mummy hafsat din haka kawai,ta tsani ta ganta tare da uncle din nata,tana dannewa ne tayi kamar bai dameta ba tunda batasan ainihin me yasa takejin hakan ba,uwa uba ko meye zatayi saidai ta jiyota daha sashensa sashenta ko.farfajiyar gidan,bata doso sassanta,wannan yasa bata dameta ba,a kullum tunaninta da zuluminta sanda kowa zaisan tana da ciki,cikin wata irin wauta dake sanya abbas din ya qunshe kansa yayita mata dariya,a fuska kuma ya tayata jimami da alhini kamar gaske. A lokacin hafsat din ji take kamar zata mutu,yaqi kulata sannan widad din da taso rage zafi da ita ya mata shamakin da ko giyar wake tasha ba zata doshi sassanta ba,ta sanshi farin sani,yana da kawaici yana da alkunya,amma duk sanda ka sake ka turashi inda bai kamata ka turashi din ba.....to kuwa abinda zai biyo baya bashi da sauqi. Duk haukar da hafsat din keyi hakan bai canza komai ba,don kuwa kwanakinsu biyar suka wuce kano,kai tsaye kuma sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na mallam aminu kano. Sosai widad din tayi mamakin ganin 'yan gidansu acan suna jiransu,tayi farinciki sosai amma kuma abinda tasan tana tattare dashi ya hanata sakewa,sai qumbiya qumbiya takeyi,duk kuwa da cewa cikin abaya sakakkiya take da hijabin daya tsaya mata iya qugu saqar qasar indonesia,wanda ya sake fitar da zallar kyanta da kuma yadda ta sake cika ta kuma sake yin kyau. Duk wani motsinta yana kan idanun abbas har sukayi sallama da 'yan gidan nasu,suka kuma bi ayarin tawagar mai girma governor din bauchi wadda kusan duka iyalinsa ne da manya manyan qusoshin gomnati da matayensu. A darare take gaidasu saboda rashin sabo,uwa uba kusan duka sun girme mata,sa'annin yayyenta ne aurarru,saidai suna da tsananin kirkin daya gaza boyuwa,kallo daya zakayi musu kuma kasan wayayyun mata ne da suka goge da sanin rayuwa,idan akace wayewa bawai wayewa ta rashin kunya rashin da'a da rashin kamun kai ba,a'ah.......wayewa ta ma'ana da sanin darajar kai da kimar kai wadda ke gauraye da ilimin zamani. Yadda yaga taqi walwala kafin tashinsu sai yaji duk ba dadi,tana tsaye batasan da isowarsa wajen ba "Suma fa duk sunayi..... qila jiya da daddarema duk sai da sukayi kafin mu taho nan" abinda taji an fada kenan a kunnenta,da mugun hanzari fararen idanunta a waje ta waiwaya,duk da tasan duk duniya babu mai gaya mata hakan kanshi tsaye sai uncle din nata.....uncle abbas dinta,shi dinne,tsaye a bayanta dab da ita,hannayensa zube a aljihun wandon wata lafiyayyar suit da tunda ya sanyata ta gaza dauke idanunta daga kansa har suka iso nan,murmushi ne kwance saman fuskarsa yana jifanta da wani kallo da su kadai sukasan ma'anarsa,saita langabe kai a shagwabe tana dubansa gami da yi masa nuni da mutanen dake gabansu kadan tana masa alamar kada suji fa,kafadunsa duka biyu ya daga ya watsa hannayensa in i don't care manner,ya sake matsowa kadan yana yin qasa da muryarsa "Wannan tsoron naki xai sa kowa ya sani" ya furta yana duba agogon hannunsa "Feel free,u are safe dear,okay?" Saita gyada a hankali,ya aika mata da wani murmushi na musamman sannan ya juya,saita sauke ajiyar zuciya ta bishi da kallo. Batakai ga waiwayo ba taji maganar daya daga cikin matan mai suna hajiya sha'awa "Badai har kun fara kewar juna ba?" Kunya sosai ta kamata,saita girgiza kai da sauri,kafin ta amsa mata sauran sun iso,cikin mintuna qalilan ta shige cikinsu ta kuma fara sakewa,saboda yadda suketa qoqarin janta a jiki tare da sakata a hirar su,hirar data dinga jin kamar ta girmeta,saboda hira ce ta manyan mata,amma ta qarfi da yaji haka suke sanyata a ciki.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *A RUBUCE TAKE* (K'addarata) Book 02 Ta hadu da mutane masu karamci,don haka bata wani jima ba ta sake sosai a cikinsu,zamu iya cewa tafiyar ta zame mata wani mabudi na alkhairi tare da sake sanin wacece ita,wanne aiki ne a gabanta?,wanne muhimmanci abbas ke dashi a rayuwarta wanda abaya duka hankalinta bai taba mata hasashen hakan ba,duk kuwa da yadda take jinsa sosai a jikinta zuciyarta da ruhinta. Abun ya fara ne daga yadda suka maidata kamar qanwarsu,koda a aikin hajjin kowa qoqarin tallafarta tare da nuna mata abubuwa yakeyi,musamman daya zamana ita daya ce farkon zuwa wajen,cikij taimakon Allah sukayi hajjinsu lafiya suka gama,sai ya zaman lokacin komawa gida nigeria kadai ya rage musu. A sannan taga kowacce hankalinta ya tattaru kan mijinta da sukazo tare,a lokacin suka lura da yadda ita din bata maida hankalinta sosai akan hakan kamar yadda su sukeyi,hajiya sha'awa ita ta fara fahimtar hakan,wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,tuntuni suka gane quruciyar dake dawainiya da ita,wadda wasu abubuwan take gaza yinsu,babu wadda taji kunyarta acikinsu,dukka suka hadu kamar yadda zasu yiwa qannensu uwa daya uba daya suka fara dorata akan sabon saiti.....sabon karatu da sabon darasi. Bata taba jin kunyar wasu mutane kaf rayuwarta ba irin yadda suka sanyata jin kunya,amma ta dole sukayi mata ta sake ta kuma soma bin karatun nasu. Abinda bata sani ba kusan kowannensu tasan halayyar hafsat ciki da bai,wannan yasa hatta gidan babu wadda tayi masa zuwa uku, lokacin da sukaga widad din a mazaunin kishiyar hafsat qaunarta da tausayin yadda zata iya zama da ita ya shigesu,wannan yasa suka samu qarfin gwiwar dora mata abubuwa masu nauyi da yawa,wadanda sukasan koda bayan rabuwarsu zai zauna a kanta ya kuma bi jikinta. Ranar farko kuma karo na farko da taji itama tanason kasancewa da mijinta kamar kowacce mace,ta dauki waya ta kirashi,a sannan suna tare da sauran abokansu da basu taho da matansu ba,saidai dukka kewarta ya isheshi,bayason ya fiya takura mata ko matsanta mata ne kawai,duba da situation din da take ciki,amma he really needs her,kullum kwanan duniya sake shigewa rayuwarsa takeyi. Cikin karsashi ya daga kiran,saidai muryarta kawai ya kashe masa jiki,ya jingina da kujerar yana saurarenta sanda take magana dashi cikin narke murya "Bakayi kewata ba ko uncle?" Maganar tata tadan tabashi,har sai daya murmusa "Har bansan yadda zan misalta miki ba babyn uncle,kawai dai baison takurawa maman baby dama babyn" har ranta taji dadin amsarshi "Indai hakanne to kazo mu tafi,yau a wajenka zan kwana" mutuwar zaune yayi yana mamaki,widad dinshi ce ke fadar haka da bakinta?,ya rasa amsar da zaya bata har sai data sake cewa "Hello" "Than you baby,gani nan zuwa" abinda ya iya fadi kenan jikinsa yana dan rawa kadan,wanda ba lallai ne kai ka fahimta ba "Ina zuwa" kawai yace musu yana barin wajen. Kiran wayarsa ya shigo wayarta sanda ta fito daga wanka,tana tsaye jikin madubin dakin nasu tana mulke jikinta da wasu oil perfumes da hajiya fanna ta bata sanda zasu fice subar mata dakin,hajiya khairi ke tsokanar hajiya fanna "Allah dai yasa ba kyautar turaren banza kikayi mata ba,wala'alla ki dawo ki sameta nade a gado ma tayi baccinta" "A'ah ai ba za'ayi haka ba,na tabbatar karatunmu yana shiga,nidai ina ganin canji" qas tayi da kanta tana murmushi,dukkaninsu kunyarsu takeji,tunda sun girmeta,tana jinsu suna tsokanarta har suka fice. Wayar ta daga tace masa gata nan fitowa,ta gama shirinta a nutse,ta dauki duk wani abu da takega ya dace da wanda taga suna dauka suma idan zasu fita din,ita kanta tana jin banbanci da canji a tattare da ita,ta kammala komai a nutse ta fito. Ko sau daya baiji ya qosa da jiranta ba har ta iso,kasa magana yayi sanda qamshinta ya gaurayeshi,sai ajiyat zuciya mai nauyi daya sauke kawai,suna shiga dakin ya maida qofar ya rufe da wani irin zafin nama,ko ina na jikinsa yana daukan rawa. Zaucewa ya kusa yi sanda widad din ta miqa masa kanta yadda yakeso,ta kuma hada da bashi gudunmawa,sai kansa gaba daya ya kunce,jikinsa ya dauki rawa tako ina ya fita mata a hayyancinsa. Bawai shi ba,ko ita din a yau ta gane da banbanci,ta fahimci kuma maganganun su hajiya fanna,bayan komai ya kammala wata kunya ta kamata,yayin da shi kuma ya hanata sakat,bakinsa kuma ya kasa yin shuru,ya dinga zuba sumbatu ya kasa tsuke bakinsa,domin kuwa ta shammace shi fiye da kima,ta kuma kaishi wata duniya da tunda hajiya ta kawoshi sararin duniyar nan bai tana zuwa can din ba,ko sanda yake kidansa yayi rawarsa shi kadai yaya ya qare?,bare yanzu data bashi tallafi ta kuma miqa masa kanta kacokam. Wannan canji na widad ya tabashi fiye da kima,ya sake kuma cusa wata irin zazzafar soyayyarta a zuciyarsa,ya sake susucewa,har abun yake bawa widad din mamaki,yadda ya dinga cire kudi yana mata siyayya abun sai ya dinga daure mata kai,wanne irin so uncle din nata yake mata haka?. Ranar da suka fita siyayyar data sake sanya widad sallamawa abbas rayuwarta da jikinta......ta sake yaqini da yadda yake yawan fadin yana sonta,cikin shagon gold ya mallaka mata wata sarqa da farashinta yakai naira dubu dari tara da hamsin. Kanta ya daure sosai,a wauta da quruciya irin tata tace ba zata karba ba,sai bayan taje dakinsu da ita su hajiya sha'awa suka dinga mata dariya "Karki qara cewa ba zaki karba ba,tunda ya siya baifi qarfinsa bane,kuma tukuici ne tabbas yake baki,lallai soyayyar da yake miki tana da girma da fadi,saiki sake kula ki kuma tabbatar duk abinda yakeso kina aikatashi sau da qafa,tabbas gaba saikin mallaki abinda yafi haka muddin zaki sallamawa mijinki tare da tsare duk wani abu da yakeso,ki kuma guji wanda bayaso" ta jima a kwance tana tariyo rayuwarta ta baya,da kuma abubuwa da suka faru a yanzu,ko addu'a ce da ummu da mommynta suka yita jaddada mata ta yiwa kanta mijinta da kuma rayuwar aurenta?,ba shakka akwai tasirin addu'ar data dinga yi tuquru,sai gashi tanata ganin abubuwan da ada bata iyasu ba batama san dasu ba. Ranar da suka qara fita siyayya gefe ta koma kawai tana kallonshi,yadda ya zage yana siyan kayan babies kamar yasan me za'a haifa,har sai data gaji da ganin yadda yake diban kaya kamar baisan ciwon kudinsa ba tayi magana "Uncle" ta fada a narke "Baby" ya amsa bayan yabar dukkan abinda yakeyi ya waiwayo yana duban idanunta farare masu haske sosai,wanda suka dan qara girma kadan "Wai don Allah bakajin kunya?,ciki fa ka yiwa mace" dariyar da bai shiryawa ba ita ta kubce masa,nutsatstsiyar dariya mai wani irin siririn sauti da tasa fararen haqoransa bayyana,sakalci da shirmen quruciya dai a cikin jinin widad qilan yake,sai tayi kaman ta daina sai wataran ta sakankance ta yanko maka wata wautar,kallonta yake kawai yana dariyarsa,yama rasa wacce amsa zai bata. Turo baki gaba tayi ganin yadda yaketa mata dariyar yana kuma kallonta "Kaiko a jikinka,ka yiwa mace ciki kuma kana siyan kayan jarirai,bakajin kunya ma mutane su gane". Takowa yayi gaba kadan ya tsaya a gabanta yana kallonta,ko yaushe qara kyau takeyi tana zama wata balarabiya,ba wanda zai kalleta ya yadda ta iya hausa,hakanan babu wanda zai kalleta ya yarda akwai ciki a jikinta "To ko mutanen duniya zasu fara boye kawunansu ne?" Kai ta daga ta kalleshi don bata gane me yake nufi ba,saiya kashe mata ido daya "Ai kowa ma ta yadda wannan cikin ya samu ta haka yazo,ciki harda ni dake da......." Da sauri ta rufe masa bakinsa bayan ta danyi dage kadan,saita janye hannunta da sauri "Kuma me ya kawo wannan maganar?" "Kece mana" ya amsata yana qunshe dariyarsa "To naji,amma bakasan fa me za'a haifa ba kake diban kaya" "Ko meye kika haifa wuud(qauna/soyayya matsananciya) inaso,idan ana haifar rabin mutum ma kika haifamin zan karba hannu bibbiyu" ido ta zaro tana kama haba "Rabin mutum?,wai?" Yadda tayin ta bashi dariya,sai.ya janyeta cikin hikima sukaci gaba da zaban kayan unisex a tare,ya kuma tura mata option na zabar favourite colors dinta a dabarance,ta zaba din sosai,duk da tanayi tana waiwaye kamar wadda ke aikata wani abu ba dai dai ba. **************Karfe sha biyu da mintuna na dare motarsu ta tsaya qofar gidansu na bauchi,a sanyaye widad din ta maida bayanta jikin kujera tana kallon gidan,wani mugun tsanar gidan na shigarta sosai,tana jin kamae ta balle murfin motar ta fice ta kama hanyarta,inda zai bata zabi....da salin alin zatace masa ya kaita gidan hajiya ko gidan uncle muhsin,to amma koda ta fada din tasan ba lallai yayi hakan,don zaice mata ne dare yayi,ko baya ga haka ma.....iya kusancin da suka samu a yanzu a tsakaninsu,bata tunanin zai bari tayi nesa dashi. Shi ya fara fita daga motar yana cewa "Ina zuwa" saita gyada kai kawai,tana jin yadda qirjinta yake bugawa,tana iya hangensa daga inda suke zaune a motar ita da umar qaninsa daya daukosu,yanata knocking. Tun yana qwanqwasa a hankali har ya koma bubbugawa da dan tsauri,wasa wasa sai gashi sun kwashe mintuna masu tsaho yana bugawa,amma qofar ko gezau,babu alamun za'a bude musu gidan,har umar dake zaune cikin motar ya miqe ya fita ya soma tayashi bugun. Tun ransa bai baci ba har ya soma baci,don ba cikin gida ba......muddin dai ba wani abu bane ya samesu ba a irin bugun da yakeyi yasan har maqota sun jishi,sannan ma ba ita daya bace a gidan,idan ita bata ji ba saboda tayi ciki......shi kuma lawal fa dake kusa kusa?(dan dan uwanshi daya dauko sanda zaiyi tafiya). "Kira number lawal ka hadani dashi" ya fada yana duba agogon hannunsa,umar ya fidda waya ya fara kiransa,amma wayarsa na a kashe,sabanin ta hafsat daketa ringing kuma ba'a daga ba,a handsfree take don haka yaji me computer ta fada, kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sunji motsi ana tambayar waje,abbas ya tsaya kam yana riqe da qugunsa yana kallon qofar,umar ne ya amsa mata da "Mune" sai aka fara buda qofar gidan a hankali kamar mai ciwon hannu*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *A RUBUCE TAKE* (K'addarata) *Book 02* Page 03 Sakin qofar tayi tayi gaba,abbas din yabi qofar da kallo sannan ya taka zuwa cikin gidan,ya cimmata sanda take juyawa abinta zuwa ciki,daure da zanin atamfa saman wata kodaddiyar rigar baccinta daya jima yana ganinta jikinta,jin takunsa ya sanyata dan dakatawa kadan ta waiwayo,suka hada ido. Duk da dare ne da kuma qarancin haske,amma tana iyabhangen yadda taga yayi wani mugun fresh,qamshinsa ya cika wajen,ya mata kyau,amma data tuna a yanzun tare da wa yake sai taji komai ya gushe mata,kishinta ya motsa sosai,wanda tunda umar yazo ya dauki motar da zummar daukosu tahau kan zafinta,ita tunda suke tare dashi bata taba ganin yayi kyau da gogewa irin hakan ba,kuma ba wannan bane ai zuwansa aikin hajji na farko ba "Me kikeyi mintuna kusan nawa muna tsaye muna bugu?" Ya fada ransa a dan bace "Bacci ne fa ya daukeni" ta fada murya a cunkushe tana bata rai,sai ya janye idanunsa yana dan jan qaramin tsaki "Ta yaya zaki kwanta kinsan muna hanya?, at least dai ai kya tsaya kiga shigowata" ya fada yana qoqarin buda gate din gidan da kansa yana yiwa umar maganar ya shigo da motar ciki dare yana qara yi. Ranta ya sosu,ta tura kayan baki gaba tana jin kamar ta maida masa magana,ason ranta ta shige ciki,amma sai taji tana son tsaiwa taga yarinyar,ta sake tabbatarwa babu cikin da a kullum ta kwanta cikin mafarkinta take ganin kamar tana dashi. Tana tsaye daga gefan har umar ya shigo da motar ya fakata a parking lot na gidan,ya kasheta sannan widad ta buda murfin motar ta fito tana jin ranta da zuciyarta duka babu dadi. Rawa qafafun hafsat suka danyi,ta kadu sosai da yadda taga yarinyar ta sake canzawa,sanye take da wata lafiyayyar abaya baqa sidik mai sulbi, balarabiya sakkk!! Haka ta koma,hasken fatarta sai daukan ido yakeyi,ta sake cika sosai,ta zama cikakkiyar mace,kai bazakace widad din da aka mata aure da qananun shekaru bace,duka cikin watannin da basu wuce biyu da tafiyarsu ba irin wannan gagarumin sauyin na babu zato bare tsammani?. Kasa amsa gaisuwar da take mata tayi,gaba daya a rude take har umar yayi musu sallama ya fice daga gidan bayan abbas ya masa izinin tafiya da motar ya kawo masa ita gobe. Gajiya gami da tsanar data yiwa gidan ya sake kashe mata jiki,ta kallai abbas "Uncle bacci nakeji fa" yadda tayi maganar a mugun shagwabe ya taba ran hafsat sosai,saidai a wajen widad din hakan ba komai bane,don kusan a haka yanzun ta saba magana dashi "Muje sashena,nasan bangarenki akwai qura kam yanzu,dare kuma ya riga yayi bare ki gyara" ya amsa mata a tausashe yana mata wani irin sassanyan kallo da ya riga ya saba yi mata shi,har baisan yana fidda kansa da kansa daga idanunsa ba. Turqashi!.....me abbas din yake nufi?,taje sashensa ta kwana?,aiko sama da qasa zata hadu ba zata bari hakan ta faru ba,wannan ba komai bane ba face zallar rainin hankali,ta gama fadi tashin gyaran sashen saboda shi sannan yace wata ce zata kwana?,uwa uba ma watansa nawa basa tare,hakan yana nufin zai karbe kwananta na yau ya bawa yarinyar?. Taku biyu sukayi tasha gabansu,dubansu takeyi kai tsaye "Ba inda zata ta kwana wallahi,bazan dauki wannan rainin wayon ba" ta fada tana fidda idanunta. Ido yadan qanqance yana dubanta "Me kikeyi ne haka?" "Abinda idonka ya gane maka" kafin abbas din ya sake cewa komai widad ta zame hannunta a hankali ta fara takawa zuwa shiyyar sashenta,shi da hafsat din dukansu suka bita da kallo,sai ya motsa da sauri yabi bayanta,yayin da hafsat ta rakasu da ido qirjinta kamar zai qone saboda zafi da tsananin kishi. A qofar sassanta tana gwada keys din hannunta ya cimmata "Me zakiyi a ciki?" Murmushi ta sake masa a nutse "Zan shiga na kwanta ne uncle dare yana sake yi" ta fada a narke "Amma ai ba'a gyare yake ba,nace muje part dina ki kwanta a can kafin safiya" a nutse ta girgiza masa kai,fuskarta still da murmushi "Zan kwanta a nan din uncle,awa nawa ne gari ya waye?,kada ka damu,kana buqatar hutu,kaje ka huta" gaba daya saita gama kwance masa kai,abinda ya kamata ace hafsta dince tayi ita ta gaza sai 'yar cikinta,wani irin qauna da kimar yarinyar ya sake qaruwa a idanunsa,ya santa gwanar tsoro ce,kawai dai tayi hakanne don ta samar masa da kwanciyar hankali da nutsuwa,ya fuskanci wannan din kusan a dabi'arta yake,batason hayaniya sam,sai ya rasa me zaice mata,ya matsa ya karba keys din ya gwada na qofar ya bude sannan ya tura yayi gaba tana biye dashi. Sosai wajen yayi qura,da kansa ya dinga saka tsintsiya yana kade mata hanya har zuwa bedroom dinta,sai daya tabbatar ta gama komai ta kwanta sannan ya baro sashen. Runtse idanunta tayi zuciyarta na matsanancin bugu da tsoron dake shigarta kamar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito,tana ji har cikin Zuciyarta kamar ana tunkudata ta fice,amma can qasan zuciyarta tana kiran sunan Allah kadan kadan,abinda ya kawo sauqin yanayin da takeji din wanda keta azalzalarta kamar ana gaya mata cikin kunnuwanta. Bai samu Hafsat din a wajen ba,sai bai wani damu ba,har yanzu Zuciyarsa tana cike da mamakin halayenta, kullum babu sauyi?, sai sake ta'azzara al'amuranta sukeyi?,da wanann tunanin ya isa sassansa. Ba laifi babu datti hakanan babu qura,yaci gaba da takawa har dakin gadonsa,yana tura kansa,sautin sheshsheqar kukanta yana masa maraba. Dauke kansa yayi kamar bai ganta ba,baqinciki yana cika masa zuciya,baiga me akayi mata ba da zata zauna a daren daya dawo yana buqatar ya huta ta tusashi da koke koke ba,idan ita bai rufeta da fada ba bazata sashi gaba tana masa kuka ba,sai kawai ya fara rage kayan jikinsa ba tare da yabi ta kanta ba,rabin hankalinsa yana ga widad da yadda yaga taqi sakewa,lallai tsoronta ya dawo,irin tsoron daya ninka na baya,sai wani bangare na zuciyarsa ya bashi ko juna biyun da take dashi ne,qaramin murmushi ya kubce masa sanda ya tuna da ajiyarsa dake jikinta,dai dai sanda muryarta ta ratsa kunnensa cikin sautin kuka "Da wannan wulaqancin da kakeyimin gwara kacemin ka gaji da zama dani na tafi gid......." "Hey..... stop it dallah!" Ya katseta da mugun sauri cikin bacin rai yana dubanta,bacin ran data gani a idanunsa sun ninka nata don haka dole tayi shuru tana binsa da kallo "Banason rainin wayo da wulaqanci cikin daren nan,hutu nake da buqata,idan qorafi ya shigo dake ki tashi ki fita ki bani waje,idan kin fita idan kinga dama ki wuce gidan ban riqe miki qafa ba" sosai.maganar ta daga mata hankali sannan ta bata mata rai,ta sake fashewa da kuka ta miqe tana daukan yusra ta fice a dakin,yaja tsaki yabi bayanta ya kulle qofarsa ya dawo ya wuce bandaki,gaba daya ta gama fita a kansa,fushinta ko kukanta ya daina damunsa sam. Wannan abun daya faru a daren ya sake tunxura zuciyarta,ta kasa kuma bacci sai data kira ummanta,cikin daren suka qulla abubuwa masu yawa da suke saka ran zasu aiwatar,ko akan widad ko akan abbas din,duk wanda nasararsu ta fada a kansa. *********Da qyar ta wayi gari da wani irin matsanancin tsoro daya haifar mata da ciwon kai,inda Allah ya taimaketa washegarin saiga su nujood harda hajjaaa sunzo mata,ta samu tadan sake,daga qarshe hajjaa ta tafi tabar mata nujood ta tayata kintsa sashen da sauran gyare gyare,wannan ne ya sanyata tadan warware,saidai komai a darare takeyinsa,koda abune yayi babban faduwa yanzu zata firgita,har nujood ta fahimta ta tambayeta "Hakanan nakejin haka,nima bansan dalili ba" "Saikiyita kiran sunan Allah da addu'a" "Inayi,daqyar nayi bacci jiya" "Zan karbo miki addu'ar yawan firgita a wajen ya sayyadinmu" da haka suka fada wani zancan,tana ci gaba da addu'a cikin ranta duk sanda taji irin hakan,da haka ta dinga samun sassauci cikin ranta. Dawowarsu daga saudiyyan sai komai ya sake canzawa,gaba daya hafsat din ta tattara sanya idanunta da komai ta aza akan abbas da widad wadda bata sakata a lissafinta ba kwata kwata,don abinda yake gabanta shi ya dameta,saidai duk wata tijara da abubuwan da zatayi tana jinta daga farfajiyar gidan,ko idan guri ya hadasu,ko daga kai ta kalleta batayi bare akai ga jallin tanka mata,tunda bata taba tararta gaba da gaba ta kama sunanta ba tun sanda abbas din yaja kunnen hafsat,ita a yanzun kawai burinta abbas yace ta shirya su koma kaduna,gaba daya ta tsani garin wani muguwar tsana,duk ranar da ba girkinta bane da qyar take iya bacci saboda wani irin tsoro da yake shigarta,da qyar take hana kanta fita a wasu dararen,saidai ta zauna bakin qofar falo tayita kuka tana jin fita kawai takeson yi. A WANI DARE karfe sha biyu da rabi na dare,har ya shiga sassansa ya kwanta ya tuna kamar yau din da daddare batasha magungunanta na anti natal ba,ya sauko daga gadon hafsat na gefe tana kwasar baccinta ya fito. Kamar mutum ya dinga hangowa daga nesa,sai ya sauya yanayin tafiyarsa cikin hikima da dabararsu ta jami'an tsaro,bai wani jima ba ya gane widad dince ke nufar qofa,cikin wani irin zafin nama ya cimmata cikin takun da basu gaza biyar ba,saiji tayi caraf an riqota,ta waiwayo suka hada ido,cikin matuqar kaduwa yace mata "Ina zaki da daren nan?" Kamar jira takeyi ta fashe da kuka "Fita nakeson yi,banason gidan nan uncle" mamakinsa ya qaru,to duka me yake kawo haka?,wannan shine karo na biyu daya taba ganinta zata fita din. A tausashe ya kama hannunta yana son maidata ciki,saita kuma saka kuka "Don Allah uncle" shuru yayi ya zuba mata ido,yadan lumshe idanunsa hadi da budesu "Muje ciki magana zamuyi" dole ta sakar masa hannun ya riqeta zuwa ciki. Bakin gado dukansu suka zauna yana dubanta "Me yake faruwa?" "Banason gidan nan" ta amsa masa kanta tsaye tana qwalla "Me yasa?" "Tsoro nakeji" shuru ya danyi,ya ciro wayarsa yana son kiran dr,saidai yaga dare yayi,amma duk da haka yanajin ya zama dole ya kirata din. Bugu daya ta daga ya nema afuwan tashinta,tace batama jima da shigowa daga aiki ba sannan yayi mata tambayar "Kwai matan da ciki yake sakasu jin zaquwa gajiya da tsanar waje" saita fara masa bayani,yana fahimtarta yana kuma nazartar widad dake zaune a gefansa ta cure waje daya,ya karanci bayananta,to amma a abinda yake gani a tattare da widad din kamar nata yanayin ya dan sha banbam da wadda dr take qoqarin masa bayani "Amma ba komai,with time zata daina ne" daga baya sukayi sallama yayi mata godiya,sai ya miqe yana kallon widad "Bari na kawo miki mimi,hakan yayi?" Kai ta gyada masa a hankali sannan ya juya a nutse ya fice,ta bishi da kallo tana sauke ajiyar zuciya,rabon da yarinyar ta kwana a wajenta harta manta,gaba daya uwar ta hanata kwana a wajenta. Yana buda qofar hafsat din na farkawa,ta bishi da kallo ganin ya shigo ne daga waje,ina yaje?,badai satar kwana aka fara yi mata ba?,saita miqe ta zauna tana kallonsa sanda ya duqa zai dauki mimi daga gadonsu dake gefe,don yau din a nan bacci ya daukesu,sai yace ta barsu kawai "Bacci take fa" "Na sani,zata tayata antynta kwana" ya amsa mata ba tare daya kalleta ba,wani abu ya darsu a ranta "Me ya samu antyn nata?,naga yanxun ita daya take kwana bata ko nemanta ko?" "Basai wani abu ya sameta zasu kwana wajenta ba ai,tunda yaranta ne itama" ya amsata yana rufe yarinyar da dan qaramin lallausan bargonsu,wanda zamansa a dakin ne kawai yasa bargon ya tsira da mutuncinsa ya kuma dade da kyansa. Bai sake ce mata komai ya juya ya fice,sai ta bishi da kallo qaramar dariya tana qwace mata,ashe har yanzu da sauran abun nan bai gama sanewa ba,tanason wannan aikin tabbas!, jaddada shi takeson ayi kafin a wuce zuwa matakin gaba,bata qaunar hada inuwa daya da yarinyar kwata kwata. Sai da kwanciyar tace tayi mata sannan ya tashi yana kallonta "Ki shirya kayanki jibi zamu koma" wannan shine albishir din da yafi faranta mata rai,duk da ason ranta bataqi ma yace gobe zasu tafi ba,amma babu komai,goben ai a wajenta zai kwana,bata da damuwa. *H U G U M A* *Arewabooks: Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 04 Batasan ma tsautsayin da ya sanyata ta yarda da shawarar zama a bauchin ba ta barsu shi da ita a kaduna,sai a yanzu da mamarta ta zauna ta lissafa mata abinda ka iya faruwa acan alhalin ita din tana nan zaune batasan meke gudana ba,ciki kuwa zata iya tara dukiya da abun duniyar da ita da suka kusa haura shekara bakwai bata sameta ba. Sai yanzu ta yarda komai na babba yafi na yaro,ta kuma gasgata dukkan abinda babba ya hango yaro ko yahau bishiyar rimi bazai hangoshi ba,don haka ta hadiye dukka maganganunta taci gaba da zare pampers din data cika ta tumbatsa "Ai basai ka kashe kudinka kayi wata siyayya ka ajjiye a nan ba,nima wannan karon dani za'a tafi" cup din hannunsa ya ajjiye ya miqe a nutse "Wannan tsohuwar magana ce da muka jima da gamata,ki rubuta list ki turamin" ya qarshe maganar yana aje mata kudin cefananta "Allah bazan zauna ba" ta fada kanta tsaye,shi kuma daya fita baima ko nuna yaji ba ya fice abinsa. Yadda yayi matan ya qona mata rai sosai,ta tabbatar akwai gagarumin dauki ba dadi da zai biyo baya kafin ta samu bauqatarta ta biya,sai ta dauki wayarta kawai tayi kiran ummanta ta gaya mata yadda sukayi "Ai gaba da gabanta,baba ma da babanshi,ki kira babarsa ki gaya mata,itace dole zata turasashi kuma yabi" fuska hafsat din ta yatsine "Nifa matar nan ban yarda da ita ba,sonshi take fiye da kowa cikin yaranta,munafuka ce kawai,umma....na gaji da kaishi qara,don Allah don annabi ayi a kammala aikin nan,nafison idan nace eh ta zauna kawai" ajiyar zuciya ta sauke "Hafsatu.....da mijinki da kishiyarki aikinsu dole sai an dinga binsa a hankali,idan kuma ba haka ba yace za'a yi hasara masu yawa" "Ko hasarar mecece can ta matse musu ayita indai buqatata zata biya" "Aah.....ke bari kiji,daga bangarenmu ne hasarar,shi yasa nace abi a sannun,inda daga gurinsu ne ina ruwan wani?,da tuni aikin gama ya gama ai" sun jima akan wayar suna tattaunawa,duka saqa ca a mugun zare da yadda zasu ida mugun nufinsu. Har ta ajjiye wayar ta tuna da yaya baraka,dabarar kiranta takai mata qara a wannan karon ta fado mata,kai tsaye tayi kiran nata,bugu uku ta daga. Suna gama gaisawa ta fashe mata da kuka,sannan ta rattabo mata abinda yake faruwa,bayan ta qawata zancan da qarya da gaskiya,yaaya barakan ba komai ta sani akan lamarin gidan abbas din ba,tunda itace babba a dakinsu itama ba shiga zancan takeyi ba,a yadda hafsat din ta gaya mata maganar sai taji ranta ya baci sosai,saboda rashin adalci zalla data hango,sannan hafsat din tayi sara akan gaba,don bata jima da jin tsegumin da ake na tafiyarsu widad din hajji akabar hafsat a gida ba "Zan sameshi nayi magana dashi,basaima hajiya taji ba,ki kwantar da hankalinki,wannan ma ai rashin adalci ne,ita widad din da gwal aka yita da zaiyita yawo da ita gari gari ke ya barki tsugunne da 'ya'ya?,ya ajjiyeta a tafi dake wannan karon,ko kuma ya hada kanku duka ya tafi daku,shi yaga zai iya" maganar tayi mata dadi,don haka sai tahau shirinta abinta,duk da shirin ya hadu da cikas,kusan kowanne kaya nata suna da naqasu,da qyar take tsintar wanda zata iya dauka a ciki. °°°°°°°°°Yana daga zaune saman carfet tana kai kawon dire masa abincinsa,duk inda ta gifta sai ya bita da ido,yana jin wani abu yana tsarga masa dangane da ita,a yanzun data sallama masa kanta yadda yakeso,sai.yakejin kamar shi kadai yayi sa'ar mace a duniya,komai na matsalolin hafsat a yanzun baya musu kallon da yake musu ada. Boom Short ne a jikinta da wata armless turtle neck shirt wadda ta kama jikinta,dukka kayan black ne,wannan ya qara fitar da haskenta sosai,ga wani kyau me jan hankali,ya kasa dauke idonsa daga kanta,ba wanda zai kalleta yace akwai juna biyu a jikinta,yabi tsaho da kuma qibarta ya boyeshi tsaf. Zuwanta na qarshe ta ajjiye masa strawberry juice data hada masa,zata miqe ya kamo hannunta da kyau ya kuma jawota jikinsa a tausashe yayi mata mazauni saman cinyarsa yana cewa "Na gaji da wannan qwalelen da aketa min tun daxu,ko yaya dai ai kyazo naji duminki ko?,kinsan kuma nayi missing dinki fa" ya fada yana saka hannunsa ya ware gashin kanta,ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana shaqar azababben qamshinta daya sauya daga aihinin wanda ya sani "Ya sub....hanallah.......babyn uncle so kike ki kasheni.....wannan qamshin......" Sai ya kasa qarasawa ya sake cusa kansa sosai a jikinta,sumarta tana yiwa kansa da fuskarsa rumfa, yayin da ita kuma ta saki siririyar dariya tana riqe kansa da kyau saboda saukar hucin numfashinsa. Basu ce komai.ba sukaji an tura qofar falon da mugun qarfi,a firgice weedad ta maida dubanta ga qofar,shi kuma ya zaro kansa daga inda ya boye fuskarsa yana kallon bakin qofar da idanunsa da suka sauya launi. Hafsat ce,baya tayi.kamar zata fadi,tunda take bata taba mummunan gani irin wannan ba, widad ce saman cinyar abbas din?,ko ita ba zata iya tuna when last da tahau cinyarsa kamar haka ba,wani abu me zafi ya taso ya riqe mata qirji,ta fada zuqar numfashi da qyar. Motsawa widad din tayi da nufin zamewa daga kan cinyarsa,sai ya janyota ya gyara mata zama sosai akam cinyar tasa yana zagaye qugunta da hannayensa,yayin da idanuwansa ke kan fuskar hafsat yana kallonta cikin bacin rai,ita kuma widad din take kallo,tana jira taga ta sauka,amma sai taga ko motsi batayi ba,saima shirin jingina da take da jikinsa,saboda yadda ya hanata sauka daga cinyar tasa,kunyar yadda ta gansun kuma tana tabata,duk da haushi da taji na yadda ta shigo musu babu ko sallama "Wajenka nazo" ta fada murya a tsaye,tana fatan widad ta sanya baki a maganar ko zata samu hanyar da zata dake ta fa huce takaicinta "Fita waje ki jirani" "Yaaya baraka ce tace na kawo maka waya tanata kiranka baka dauka ba" ta fada a kausashe tana jin yadda hawaye keson kunno kai cikin idanunta tana hanasu zuba,wannan cin fuska da rainin da yarinyar tayi mata har ina,tana zaune sosai saman cinyar mijinta kuma tana kallon qwayar idanunta?. "Ki fita nace ki jirani" ido ta zuba masa kamar zuciyarta zata fado,ita yake kora a gaban qaramar yarinya?,saita jinjina kai ta fice fuuu kamar zata tashi sama. Da sauri ya sanya hannu ya sake tarota sosai cikin jikinsa,ya maida gashinta gefen kafada yana sake zura kansa gefen wuyanta "Un..... uncle" ta kirashi murya a rarrabe, fuskarsa kawai ya dago dab da tata yana kallon fararen qwayar idanunta "Kace mummyn mimi ta jiraka a waje fa" "Ba zata jirani ba,tafiya zatayi" "Amm....." "Shshshs......" Ya fada yana dora yatsarsa akan labbansa yana duban qwayar idanunta "Kada kicemin komai,sannan daga yau,duk sanda ta sake shigo miki waje irin haka muna tare kikace zaki matsa ko zaki tashi,zan hukuntaki ne,ai bata nema izininki ba kafin ta shigo miki waje.........ko ban fada miki ba nasan dole ki sani,a nan ne kadai wajen da nake samun nutsuwa da kwanciyar hankali,kawai sai na bari lissafina ya dagulemin?,nayi wasa da damata kamar yadda tayi wasa da tata?,come-on.....forget her, let's continue to enjoy" ya fada yana sake shige mata. Sai daya gama rage zafinsa sannan yace ta dauko masa wayar,ta dauko ta miqa masa cikin girmamawa,ya saki murmushi yana cewa "Thanks" sannan ya buda wayar yana duba me kiran. Yaya baraka dince,sai kawu hassan,kowanne miscall bibbiyu yayi masa,baibi takan yaya baraka ba,tunda har sunanta ya fita a bakin hafsat yasan akwai wata a qasa,bare yana sane da maganarsu ta daxu,sai ya fara da kiran kawu hassan. Cikin girmama juna suka gaisa,sannan ya shigar masa da zancan baraka ta sameshi da batun iyalinsa kan komawa kaduna,ya yiwa kawu hassan din bayanin komai,yayi shuru yana nazari "Duk dadai mun gama magana da hajiyarku,kusan abu daya muke gani,kayi.haquri ta biku kada duniya ta zageka,kuma ita kanta kada ta sake daukar cewa kana hakanne don rashin adalci,don rashin kyautawa bata kyautata ba,amma ko yanzun ma baka da tabbas din zata zauna idan taje din,tunda mai hali baya fasa halinsa,don haka ka zuba mata ido,taje din". Koda suka gama waya da kawun hajiya ya kira,itama kusan abinda tace dashi kenan,dole ya sauko daga dokin naqin da yahau,saidai baice mata zataje ko bazataje din ba,ya barta tana ta raba ido da taraddadin zai yarda ko zaiyi halin nasa na kafiya,saida asubahin ranar da zasu tafi tunda girkinta ne yace ta shirya da wuri zasu wuce. Jikinta na rawa take kintsa abinda zata iya,qarfe goma na safe sale ya gama fidda kayansu duka an zuba a booth din motarsa,dole ya canza motar komawa saboda wadda suka saba zuwa da ita kamar zasu matsu da yawaga yara biyu ga hafsat din ga widad gashi. Ta riga kowa fitowa ita da yaran,ta buda gidan gaba ta shige ta watsa yaran a baya "Kya zauna a cikinsu,dama nan ne yafi dacewa dake" ta fada a ranta,don dama ko sama da qasa zasu hadu batajin zata yarda ta barwa widad din gidan gaban. Batasan ma me yake faruwa ba,ta fito abinta a shirye tsaf cikin wata atamfa dinkin A shape budadde sosai,duk da yadda hafsat din take ganin ta qurewa ado sai data raina kanta,sai dataji ta muzanta,ta zuba mata ido.tana fatan Allah ya kawo wani mummunan sanadin da zai dakushe wannan kyan da kullum kwanan duniya yake mata barazana cikin idanunta. Tun bata qaraso ba taja hankalin abbas dake tsaye jikin motar yana amsa waya ba tare da yakai ga shiga ba,ya bita da kallo tun daga can harta kawo bakin motar,yaran duka suka fito suna mata oyoyo tasa hannu ta rungumesu cikin jikinta,mimi tace "Anty qamshi,qamshi kike,ki sakamin turaren nima" "Yanzu kuwa.babbar qawa" ta fada tana zuge hand bag din dake maqale a hannunta,ta fidda qaramar kwalbae turare mai kyan gaske ta fara fesawa yarinyar "Ranki ya dade.....mu baza'a san mana qamshin ba?" Abbas data gama kashe masa jiki da adonta ya fada yana turo hularsa gaban goshinsa. Zata iya cewa hatta kalar murmushi hajiya fanna sun koya mata,daya daga ciki ta aro ta aike masa dashi tana juya fararen idanunta,saqonta kuwa ya isa,don kasa takawa yayi ya koma a dole ya manne bayansa da motar yana jin qafafunsa sun saki "Idan ba'a fesa maka ba wa za'a fesawa" sai ta tako a hankali ta matsa gabansa ta fara fesa masa turaren daga wuyansa zuwa qirjinsa,sanyinsa da qamshinsa ya ratsa fatarsa,ya saki ajiyar zuciya,sai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa yana cewa "Kada fa ki jawo hannun agogo ya koma baya,zan iya kasa tuqin nan f........" Bai qarasa ba uban horn din motar ya karade gidan,a tare suka juya zuwa ga motar,yayin dasu mimi suka tsorata saboda yadda ta danne horn din har baka iya jin abinda wani ke fada. Hafsat ce da komai ya faru a gaban idanunta,abinda suke fada ne kawai kunnuwanta basa iya jiyowa,sabida Glass din side din a rufe yake,ta cika tayi fam kamar zata fashe,ita zasu rainawa hankali su shanya a cikin mota?,zame hannunsa yayi ya tako a nutse ya buda murfin motar yana kallonta "Idan tafiya tafiya,idan zama zama,ya zaku tsaya gaban yara kuna abu iskanci iskanci?" Ta fada tana huci,tana jin kamar ta fita ta kamo widad ta shaqeta. Kamar ransa zai baci sai kuma murmushi ya kubce masa,ashefa ita duk irin wadan nan abubuwan a rayuwar ma'aurata iskanci ne a wajenta,kuma shi har ga Allah ya manta da ita "Yi haquri mommy" yana fadin haka ya maida.murfin ya rufe,bai dai fasa ba,sai daya koma ta fesa.masa turaren sannan suka dawo cikin motar,xuwa sannan tayi nisa wajen juya kalmar.mommy daya jefeta da ita,aiba haka yake gaya mata ba,yanzun kuma daya fada me yake nufi kenan?,babu me amsa mata,haka suka cika motar da karadinsu widad na biye musu tana kume jefo abbas a ciki shima yana shiga sabgartasu,har ta dinga jin kamar sunyi watsi da ita ne kawai,kamar babu ita ne a cikin motar gaba daya, abun da ya isheta saita dakawa mimi tsawa "Banason shegen surutu,ki kama min bakinki a wajen" yarinyar tayi tsuru tsuru,sai ta bawa widad din tausayi,ta lura tana yine saboda ita,taja yarinyar jikinta ta fara mata hira qasa qasa,sai gashi ta ware,abbas da yaji shuru yace "Wai me aka gayawa mamana ne tayi shuru haka?" "Daddy labari ake bani me dadi" mudubin gefansa ya saita yadda zai hangesu da kyau,suka hada ido ya kashe mata ido daya "Retired za'a yimin?,ba haka mukeyi dake bafa" baki tadan murguda masa,abinda ya fusgi hankalinsa kenan,don bai taba gani tayi ba sai yau,har sai da murmushi ya subuce masa ba tare daya shirya ba,yayi mata sign na tuba yakeyi saita dauke kai tadan qara volume kadan na muryarta,motar ta dauki shuru suna biye da ita. Tarihi take basu na daya daga cikin sahabbai,kusan ya zauna sosai a kanta saboda alhaji na yawan yi.mata shi,sosai tarihin yake shigar abbas din yana mamakin yadda ta riqe komai exactly,hafsat da takejin muryar widad din kamar tana watsa mata ruwan zafi taja tsaki karo na kusan goma "Nifa gsky an shiga hakkina" "Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar ta sigar ko in kula "Lallai ne kowa sai yaji abinda take fada?" "Ba lallai" ya fada yana zura hannunsa aljihun motar,ya ciro wata mini laptop da earpiece ya xube mata ba tare da yace da ita komai ba,sai tabi kayan da kallo kafin ta maida kansa,saidai tuni yaci gaba da abinda yakeyi kamar ma baiyi komai ba. *H U G U M A* *Arewabooks: Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 05 Kafin sukai kaduna zuciyarta kamar xata fashe,bata samu sauqi ba saida bacci ya daukesu mimi,widad kuma ta sanya earpiece abinta ta kunna data tahau watsapp. Saidai duk da hakan hankalinsa yana kanta,bini bini ya juya ya gani,ta rasa da wacce siga zata masa magana juyawan da yakeyi tana jinta kamar a qahon zuciyarta yake soka mata abu mai tsini,amma yadda taga ya tsare gida tasan bata isa ma tace komai ba,haka ta dinga cinyewa kamar ta zuqo kaduna ta rage nisan tafiyar suyi su isa,saidai wannan abun ba zata barshi ba,dole taci uban yarinyar da kyau. Qarfe biyu da mintuna suna cikin gidan,kowa na gidan na maraba da dawowar abbas din,kasancewarsa mutum me kirki da kyauta,ma'aikatan gidan suka kwashe kayansu zuwa falon gidan. Shi ya buda musu parlor din ya koma don gyara parking,hafsat ce a gaba,tana tafe tan qarewa parlor din kallo,komai na parlor din ba wanda ta sani bane,an canza abubuwa da yawa da wani irin tsari me kyau,komai qal kamar basuyi tafiya sun bar gidan ba,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,tana tuna lokacin data sanya qafa tabar gidan,tana jin duk duniya babu yadda abbas zaiyi da ita. Awancan lokacin tana jin babu matakin da zai iya dauka,babu wata mace da zata iya shiga rayuwarsa,ashe babbar matsala ce zata biyo baya,yanzun gata ita kusan sa'ar diyarta ta fari inda auren wuri tayi zasu goga kishi. Gaba widad tayi abinta,ta buda dakinta ta shige,tunda komai nata yana ciki,lokuttan baya kafin kusanci ya samu tsakaninta da abbas din ta koma dakinsa a nan take kwana,da kallo hafsat din ta bita tana jin kamar ta jawota,ganin yadda ta barta tsaye a falon,wato ta samu dakin zama kenan,taja wani mugun tsaki tana kallon dakin nasa dake kulle,sai ya shigo kenan zai bude mata dakin,ta koma ta zauna saman kujerar tana sauke shukra dake bacci,yaran nata guje guje da murnar zuwa gurin da suka jima basu zo ba. Duka duka part din bedroom biyu ne,a dole abbas din ya budewa hafsat nasa bedroom din suka saka kayansu. Tana daga gefan gado tana bawa yusra yusra mama tana qarewa dakin kallo shima,komai neat,qamshin shegiyar yarinyar ya kama dakin da kyau,da qyar take iya hadiye yawu saboda wani abu daya tokare mata wuya,ta cirr yusra data koma bacci ta kwantar da ita gefe,sai hannunta ya fada saman wani.abu mai taushi,ta janye hannun tana dubawa da sauri. Baby pink rigar baccin widad ce wadda ta barta saman gadon garin sauri ranar da zasu bar kadunan,ta daga rigar tana qare mata kallo,bata da maraba da tsirara,saboda duk inda muhallin tsiraici yake neat ne a wajen da wani silk yard duka jikin rigar,nannade rigar tayi tayi wurgi da ita cikin tsananin bacin rai,ita za'a yiwa iskanci?,sai ta miqe ta fara bincike dakin,tun daga drawer dinsa zuwa toilet. Da qarfi ta buda murfin wardrobe dinsa,idanuwanta ba zasu juri ganin kayansu a cakude waje daya ba,brassiere dinta da qananun kayanshi,kai tsaye ta miqe ta fita a dakin da nufin zuwa ta gaya mata tazo ta kwashe kayan nata. A falo sukayi kacibus dashi yana shigowa riqe da hannun nawwara,ya bita da kallo "Ina zuwa?" Kallonsa tayi qirjinta kamar zai fado saboda radadin da zuciyarta keyi mata "Zuwa zanyi na gaya mata tazo ta kwashe kayanta a dakin" wani nutsatsen kallo ya bita dashi sannan ya gyara tsaiwarsa "Ki barni da kaina zan gaya mata,sannan ma dole ki samu kayanta cikin dakin tunda batasan da dawowarmu tare ba" galala ta bishi da kallo kanta yana daurewa,ita abbas ke cewa ba'asan da zuwanta ba?,to banda ma iskanci da fidda sabon salo,tana cewa ita din sanda tana nan dankwalinta baya bari a dakin,kome ta bari sai ya sanya ta tattarasu ta fiddasu a dakin kafin ya rufe ya wuce aiki,shine yanzu zata samu kayan yarinyar cike a dakinsa,kayan ma na rashin arziqi da rashin kunya?. Bai wani nuna ya lura da yanayin data shiga ba ya miqa mata nawwara "Ki dafa musu wani abun suci kafin ku gama kintsa gidan,yunwa sukeji" bai tsaya jiran amsarta ba ya wuce ciki yana janye da luggage dinsa. (Widad) Tun shigowarsu gidan tare duka taji gidan ya canza mata,batasan me takeji game da biyosu da mummyn mimi tayi ba,amma dai tasan har ranta hakan bai mata wani dadi ba,saidai idan ta tuna matarsa ce itama kamarta sai tayi qoqarin dannar zuciyarta,duk kuwa da cewa tanajin mugun qunci duk sanda taga wani kusanci a tsakaninsu,haka ta dinga qoqarin shanyewa,ta gyara dakinta zuwa toilet dinta tsaf,tanata son fitowa ta gyara sauran sassan gidan amma tana ta jin motsin yaran,batasan ko suna amfani da falon ba,sai dataji shuru sannan ta fito. Tuni falon ya fara watsewa da tarkace,bata saba ganinsa haka ba,duk sai taji wani iri,ta tattare musu shirginsu guri guda ta kintsa falon,tana gamawa hafsat din na fitowa daga kitchen dauke da plate din wata cakurkudaddiyar jallop din taliya yaran na biye da ita. Tsaki taja tana shigowa falon tare da kallon yadda ta gyarashi,itafa batason irin wannan sanaben tsiyan,daga dan tashinsu an wani hau shara?,saita watso dukka kayan qasa tayi abun zama dasu,ta ajjiye musu plate din a qasa suka fara cin taliyar,mimi na cewa "Anty kizo muci" harara hafsat ta maka mata "Tunda ita ta dafa man ba uwar iyayin tsiya" qaramin murmushi widad ta saki,itakam wannan taliyar ko matse bakinta akayi batajin zata iya hadiyarta,ko kadan bata bata sha'awa ba "Na gode mimin daddy" saita juya ta wuce dakinta,zuwa yanzun duk wani girma da mutuncin hafsat babu abinda yayi saura a idanun widad din,ta zare kayan jikinta ta shiga wanka. Yana shigowa daga sallar azahar ya zauna falon yana tambayarta abinda ta dafa,sanda ta zubo ta kawo gabansa sai yaji duk yunwar da yakeji.tayi qaura babu ita a cikinsa,ya kalli abincin da kyau ya girgiza kai ya kawar gefe,bazai iya saka wannan "Ina antynku?" Ya tambayi su mimi "Tana daki" shi kansa yau din gaba daya sai yakejin wani iri,ba da wannan yanayin suka saba dawowa kaduna ba,kewarta duka ta isheshi,a kadunan yake samun kanta fiye dako ina,don tafi sakewa sosai a nan din,sai ya miqe tsam ya nufi dakin nata,yayin da hafsat dake zaune a wajen tunda sukaci abinci bata motsa ba bare tayi haramar gyara kayan da sukazo dashi da kuma dakin ta bishi da kallo. Duk yadda taso ta daure sai ta kasa,ta buda baki cikin qunci "Ina zaka?,girkina ne fa?" A nutsensa ya waiwayo yana kallonta "Wani abun nace miki zanje nayi?,idan girkinki ne ki maida hankali wajen tunanin abinda zaki dafa mana da dare" tasan magana ya gaya mata a fakaice,sai tayi shuru tana sake rakashi da idanu,kamar ta tashi ta tari gabansa,har ya murda handle din ya waiwayo yace mata ta sama masa black tea ta hada masa da wani abun da zaici. Maida qofar yayi ya rufe a hankali ya jingina da jikin qofar yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya dakin ya gauraye da qamshin shower gel air freshener spray dinta,ya zuqi iska ya fesar yana kallonta,tana daure da towel tana mulke lallausar fatarta da kyawawan mayukan gyaran jiki da suke qarawa fatarta kyau da glowing. "Ki daina kallona da wadan nan idanun naki don Allah,kada ki sa na kasa qarasowa mana madam" ya fada yana kallon yadda ta tsareshi da ido ta cikin madubi,ba shiri murmushi ya kubce mata,duk yadda kuwa takejin ranta a quntace,amma shi dinma a yanzun kallo daya tayi masa ta karanci kamar akwai 'yar qaramar damuwa a fuskarta. Dab da bayanta ya tsaya,ya dauki cumb yana taje mata kanta a tausashe,yadan ja kadan saboda yana son tsokanarta,fuskarta yakeson gani sosai,sai ta yamutsa fuska "Asshhh" ta furta tana shagwabe masa,ya saki siririn murmushi "Idan ba haka nayi miki ba naga alaman rowar fuskar nan akemin yau" siraran labbanta ta tura gaba "Idan baka gani ba ai zakaga ta mummyn mimi" farko bai gane me take nufi ba sai daga baya, siririyar dariya ta qwace masa,yaja kujerar madubi ya zauna,ya jawota cikin zafin nama zuwa saman cinyarsa ya zaunar da ita,dukkansu wani shock sukaji cikin jikinsu,ya dora hannunsa saman cikinta "Idan naga ta mummyn mimi sai akace naga taki?,sunanku ma aiba daya bane,matsayin taki daban matsayin tata daban" matsayin da yace din sai ya kumbura zuciyarta,ta fara qoqarin zamewa "Tunda itama mai matsayi ce ai duk daya ve da tawan" dariyar da yake riqewa ta qwace masa "La'ila....lallai yarinyar nan,zoki gayamin......kin iya kishi dama wai?,dama tun rannan nake ganin alamu,ashe nayi hasashe dai dai......yaushe kika fara son uncle din naki haka?" Duka hannuwanta ta saka ta zagayesu a qeyarsa tana kallon idanunsa sosai "Ranar da kayimin ciki mana" mutuwar zaune yayi,ya nutsa idanunsa cikin nata yana mata wani irin narkakken kallo,inama zata zauna a haka?,ta yakice sauran kunyar da tayi ragowa tattare da ita?,that's all he needs,yana buqatar kulawa da soyayya kamar ba za'a mutu ba,sai kawai ya sanya dukka hannuwansa ya mata masauki cikin jikinsa ya matseta gam yana sauke numfashi "Bansan lokacin dana fara sonki ba,kishin da nake naki kuma inajin zai iya kasheni......inaso kici gaba da kishina,kiyita kishina kiyita kishina,na miki alqawari wani abu na musamman" Murmushin jin dadin ya kubce mata,wannan satar amsar hajiya fanna ce ta bata ita,ta jima tanason gwadawa amma tanajin nauyi da kunyarsa,sai gashi.....yayi aiki,tana iya jin bugun zuciyarsa ya qaru sosai. Bugun qofar da akeyi shi ya tilastata zare jikinta daga nashi tana kallonsa,wani abu ne da basu saba dashi ba,muddin suna kaduna a irin wannan lokacin ba wani abu dake disturbing dinsu*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 06 Hannu ya miqa mata yana dubanta da idanunsa da sukayi laushi,saita noqe kafada alamun a'ah,ya sauke hannunsa muryarsa adan shaqe yana tambayar "Waye?" "Nice" kakkausar muryar hafsat ta bayyana,ya miqe cikin wata irin kasala hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya isa bakin qofar yasa hannu ya bude mata. Idanu suka zubawa juna shi da ita,ita din tanason karantar cikin wanne yanayi yake,yayin da shi kuma yakeson jin ba'asanin bugun qofar "Tazo ta kwashe kayan nata" sai daya lumshe idanunsa ya lumshe ya budesu lokaci guda sannan ya amsa mata a nutse "Meye damuwarki ne?,badai kinyi complain ba?" Mugun haushi ya cikata,yadda ya bata amsar sam shi bashi da damuwa ma kenan "Eh.....amma dai kasan yau din kwana na ne da zakazo har cikin dakinta ku rufe qofa" sai daya dubi bayansa wato cikin dakin ta gefan idanunsa sannan ya maida dubansa kanta "Stop it hafsat......kisan irin abinda zaki dinga fada,yara kin sani suna jinki" "Eh ai.hakkin......" "Dalla ya isa......bacemin agun" ya fada cikin bacin rai ganin bata da niyyar yin shuru,gasu mimi dake zaune daga falo ta fara calling attention dinsu. Ido ta zuba masa cikin bacin rai,saita jijjiga kanta da qarfi ta juya da sauri tana barin wajen saboda hawayen da suka ciko mata idanu,cikin bacin rai yaja siririn tsaki ya koma da baya cikin dakin,zuwa sannan har widad ta nema doguwar riga ta saka. Wani kyan yaga ta sake masa fiye dana dazu,yasa hannu ya dan shafi cikinta kadan wanda shima har yanzu yake mamaki idan ya tuna tuna akwai d'a a ciki "Ki shiga dakina ki dauke abubuwanki masu muhimmanci,mamansu mimi zata aje kayanta" ido tadan lumshe sannan ta kauda kanta tana jin wani abu ya soki zuciyarta,a taqaice dai an koreta daga dakinsa mummy Hafsat din ta tare kenan "To" ta amsa masa ciki ciki tana dan tura baki gaba,ya fahimceta sarai,qaramin murmushi ya kubce masa,yadda take kishin nan nasa yana nurgeshi sosai,sai ya.miqa hannu ya jawota jikinsa "Bamu rabu ba babyn uncle,ko yaushe ina cikin gidan nan,ranar girkinki kuma zamu kasance tare anan har sai kince kin gaji" da sauri tadan tureshi tana dariya "Nifa ba haka nake nufi ba,kuma ma bance komai ba uncle" dariya ya saki cikin jin dadi,Allah baya hadawa bawansa zafi biyu,idan ya rageka ta wani bangaren saiya sanyaya maka ta wani,sam bata daukar abubuwa da zafi,uzuri guda daya kacal ya isa ya wankeshi a wajenta. Shi ya taka mata har dakin gudun fitina,yana tsaye ta hada kayanta tsaf ta baro dakin,shima duk sai ya dinga jin ba dadi,har ya fara tunanin sauya muhalli wadatacce muddin hafsat din ta dage da zaman kadunan. Kamar jira take widad din ta fita a dakin ta fito daga bandakin data shige sanda taji motsin shigowarsu,gudun kada widad din taga hawayen da takeyi ta rainata, qorafi taso dasa masa kan wanda ta fara dazun amma bai bata fuska ba,hasalima sai ya fice daga gidan abinsa,dole ta tattara dukka wani quncinta ta adanashi waje guda,don ko widad dinma tana cikin dakinta tana sabgarta,bata ganta ba bare ta juye a kanta. Da dare shi ya kira widad din akan tazo suci abinci,hafsat din tanata wani cika tana batsewa kamar wadda tayi wani abun kirki,shinkafa ce da miya 'yar kullum,sai nama da bai gama rusuna ba cikin miyar. Wata armless chiffon gown ce a jikinta ruwan zama, tsahonta duka duka iyakarsa qauri,ko sauko mata batayi ba sosai,hafsat din ta bita da kallo ranta kamar zai fashe,ta cika tayi fam a rigar saboda cikinta da yabi jikinta sosai zuwa qirjinta,ita batayi don wata hafsat ba,tayine saboda sabo,ire iren shigarta kenan dama a kadunan,da wuya ka ganta da atamfa. Da qyar take zuba abincin,ta gama ta turawa kowa tabar widad da zuba nata,kadan ta zuba,don ko a ido ma ta dinga jin abincin bai mata ba tun batakai cikinta ba,aikuwa da qyar tayi loma biyu ta miqe,ya bita da kallo yana tambayar ba'asi "Na qoshi ne uncle" ta fada adan shagwabe,yasan inda matsalar take,shi kansa da ya saba cin wannan collabo din nata yana ci ne kawai don babu yadda zaiyi,bare widad din da bata saba ba. "Amma.....me zakici?" Tadan juya fararen idanunta cikin dan tunani "Zan duba wani abun ko cikin fridge ne" kai ya gyada "Make sure kinci wani abun kafin ki kwanta,karki sake ki kwanta da yunwa" ya fadi yana dan jin damuwa a ransa,ya dauko abinda ya zame musu damuwa duk su duka,kai ta gyada "In sha Allah uncle" sai ta fara takawa zuwa cikin dakinta,yayin da hafsat ta kasa daurewa taja wani mugun tsaki mai masifar qara "Ayidai mu gani" kallonta yayi baice komai ba yaci gaba da cin abincinsa ganin widad din ko waiwaye batayi ba bare tasan abun ya shafeta,sai yarinyar ta sake burgeshi,yasan ta tsani taja masifa aqi tanka mata,yanzu zata sake haukacewa "Sai wani rawar qafa kake a kanta,idan banda daurewa qarya qarqashi,ayi abincin tace wani wai bataci,sannan kai ka biye mata da zancan ta nemi wani abun taci tsabar ciwa mutum fuska" tayi maganar muryarta tana rawa. Sosai ya kalleta kafin ya aje spoon din hannunsa "Ki shiga taitayinki hafsat,ni ba haka na saba rayuwata a Kaduna ba,nutsuwa da kwanciyar hankali sosai nake samu,ba zaki zo ki hanamin wannan ba,indai kikace irin wanan halin zaki dauka to ki tabbatar ba zaki taba jin dadi na ba" daga haka ya miqe shima yabar mata wajen. *******Kwanakin girkinta guda biyun nan ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi,itadai widad bata fasa sabgoginta ba kamar yadda hajiya fanna ta bata shawara,illa iyaka ganinta ma wuya yakema hafsat din bare ta takaleta,wuni a daki baya yi mata wahal,tayi kallo ko tayi chart ko ta buga game,idan ta fita falo daukar abu tazo yi zata dauka ta wuce abinta,yaran suna son zuwa wajenta amma uwar ta kasa ta tsare,idan ta bari sun rabeta to uban yana gidan ne babu yadda zatayi tana shakkar hanasu. Abbas din yana ta qoqarin ganin tana fitowa ta sake a cikinsu amma taqi bada wannan damar,don ta sake sanin ciwon kanta zuwa yanzu,uwa uba kuma kishin hafsat din itama takeji sosai,musamman ta ganta ta fito daga dakin uncle din nata sai taji kamar zuciyarta zata fashe,tafi ganewa tayi zamanta a dakinta tayi sabgoginta,ko abincin darenma na washegari tsakura tayi tabar falon,hafsat din nata binta da harara kamar idanunta zasu fado,amma ita bata ma kalleta ba bare tasan me takeyi. ********Kwanansu biyu da dawowa widad din ta karbi girki,ranar tunda safe datayi wanka ta shirya cikin wata farar wide leg jumpsuit,sai baqar gatsby cap data dora saman kanta. Duk sa cewa tayi shigarta ne kawai normal bada wani manufa ba amma wani mugun kyau tayi,shigar ta karbeta sosai,saika dauka wata baturiya ce,musamman yadda sassalkan gashinta ya fita ta qasan hular kan nata. Ta lura da lalacewar falon kwanaki biyu kacal,saboda haka can ta fara fita bayan ta zura lallausan bedroom slippers dinta. Yadda take tsammani haka ta samu falon,a wargaje tarkace kota ina,haka ta dinga kawar da duk abinda tasan bai kamata ya zauna a falon ba tana killaceshi,cikin mintuna qalilan ya fara daukan saiti. Tana tsaka da aikin hafsat ta fito dauke da qaramin mug da plate dinsa,suka hada ido widad ta janye kallonta daga kanta tana ci gaba da aikinta,wata irin harara da widad din batasan tana yi ba ta zabga mata,taja wani dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,gaba daya yarinyar ta gama shige mata rayuwa,banda tsabar raini me ya hadata da taba mata falo?,ko tana tunanin itama tana da power ne irin yadda ita take da ita? "Iyayin banza da wofi kawai" ta fada tana wuce widad din,wadda tabi bayanta da kallo,saita samu kanta itama da cillama bayan nata harara kafin ta maida dubanta ga qofar dakin uncle din nata,wanda a yanzu ya zama nasu shida hafsat din,wani zafi takeji a zuciyarta,tunda mommyn tazo komai ya sauya a tsakaninsu,a baya kullum suna manne da juna,amma yanzun ta shiga tsakaninsu,siririn tsaki taja data tuna uncle din nata yana dakin,tare suka kwana,kuma duk wani abu da yake mata itama mummyn yana mata kenan?,tana shaqar wannan daddadan qamshin nasa?,tana jin wannan lallausar fatar tasa?,yana bata wannan soft kiss din irin wanda yake bata?,sai taji ranta ya baci amma tayi saurin koren shaidan yadda anty madeena ta koya mata. A kitchen kuwa tsaki hafsat din tayita ja a jajjere,yau abbas din zai raba musu kwana da yarinyar?,saita zube cups din kawai ta fito tabar kitchen din. Wuceta ta sakeyi ta gefanta kamar zata gogeta,ko daga kai widad din batayi ta kalleta ba taci gaba da aikinta,ba jimawa aka turo qofar dakin,bata juya wajen ba,amma duk da haka lallausan qamshinsa ya gaya mata waye. Tsaye yake daga bakin qofar yana qare mata kallo cikin police uniform dinsa dake matuqar qara masa kyau da wani irin kwarji na musamman,hannayensa cikin aljihunsa fuskarsa ta wadata da murmushi,duk kuwa da cewa bata ma san da tsaiwarsa ba,tun tana basarwa hadi da qin kaon qofar har zuciyarta ta gaza,tana jin saukar idanunsa a dukka jikinta,yana kuma haifar mata da kasala sosai. A gajiye ta daga fararen manyan idanunta ta sauke masa,idanuwansu suka gauraye waje guda,sai shima ya gaza.....ya zaga da tsaiwa a nan ba tare daya iskota ba,ya fara takowa a hankali har yanzu ya kasa dauke idonsa daga kanta "Good morning babyn uncle" fuska tadan narke kadan ta karyar da wuya,kishi nason taso mata amma tana danneshi,uwa uba kuma ya mata wani irin kyau me taba zuciya "Morning uncle din baby" maganar tata ta sanya murmushi ya subuce daga labbansa,kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai hafsat din ta fito daga dakin,dauke da briefcase dinsa, idanuwanta a kansu har ta iso ta miqa masa jakar,ya karba yana gyara rufinta "Ina kwana?" Ta fada tana russuna masa cikin girmamawa "Lafiya lau baby,kin tashi lpy?" "Lafiya uncle" ta amsa masa a narke tana karyar da wuya,ya gyara jakar yana mata duban tsakiyar ido,yana jin kamar ya jawota ya rungume cikin jikinsa,shi wani mutum ne da muddin yana so ba kasafai yake iya boyeshi ba,ba soyayyar mutum ba,soyayyar komai ma "Ba wani matsala ko?" Kai ta gyada tana dan murmushi, idanunsa kawai sun wanke mata komai a ranta "To shikenan sai na dawo" "A dawo lafiya uncle,Allah ya tsare" "Ameen babyn uncle" tsaiwar mashi cak sunan ya yiwa hafsat a tsakiyar ranta,wanann zallar iskanci ne da wulaqanci,a gabanta suke irin wadan nan abubuwan?,sai kawai tayi fuuuu tayi gaba,hakan ya bashi damar qarasa sallamarsa a nutse ya fice yana qorafin tayi masa qauro,ai ba irin wannan sallamar suka saba yi,tana ta masa dariya hadi dace masa aiba ranar girkinta bane,yayita juya zancan cikin ransa,wato har ta fara rarrabewa da wani girkinta da ba girkinta ba,yadan daki sitiyarin motar kadan,shikam wannan tafiyar da hafsat ta tauyeshi da yawa. Aikinta taci gaba da yi,saidai sanda ta shiga kitchen ta gane hafsat ta jiqa mata aiki,komai a qazance,sak dai yadda ta saba barin sassanta na bauchi,saita zage ta shiga gyara haiqan,wanda tun batayi nisa ba taji cikinta ya wani cure kamar an sakar mata dutse,ta miqe tana dora hannunta saman cikin,tana mamakin wani dan tudu da take iya ji cikin nata yayi,idan ta kalli kanta cikin madubi kuma bata iya ganin komai,saita koma da baya ta huta kadan sanann ta qarasa. Duka abinda akeyi hafsat tana falo ta kasa ta tsare,wata irin dakiya ce ta zoma widad din,bata fasa aikace aikacenta ba kamar yadda bata bi ta kanta ba,da taga bata ko lura da zamanta ba saita fara zirya tana qananun maganganu daga kitchen din zuwa falo,burinta yarinyar ta tanka,ta samu ta likideta ta fake sa rashin kunya tayi mata. Tana jiyo su mimi daga falo suna nemanta ta daka musu tsawa ta zaunar dasu waje daya,saida suka fara kukan yunwar da suka farka da ita sannan ta wuto kitchen din daukar musu abinci,sannan harta gama kintsa kitchen din,tana adana kayan cefanen da tun randa suka dawo hafsat din ta karbi girki abbas din yayosu masu yawan gaske,amma haka nan hafsat din ta barsu,komai saidai ta farka ta diba yadda ranta yakeso ta barshi a wajen,hatta da kayan miyansu haka ta wurgasj fridge babu gyara. Zuciya tazoma hafsat din iya wuya,me yarinyar ke nufi,duk abinda ta fita a girki ta barshi ta sauya masa fasali daga yadda yake wai ita zata karba girki,har tazo fita ta dawo baya a zafafe "Ke nifa banason iyayin banza da wofi,duk kin kama abubuwa kin sauya musu waje kamar kinfi kowa iyawa?" Tana ware tomatoes din da suka lalace ta daga kai ta dubeta,ido tadan zuba mata ba tare da tace komai ba "Dake nake magana kika zuban ido,ba zaki zo gidana kice zaki isheni da kinibibi bafa" sai a sannan ta janye idanunta,qasa qasa tace "Gidanmu dai" "Qunquni kikemin?,me kika ce?" Ta tambayeta a zafafe "Gidanmu dai" ta amsa mata kai tsaye tana kallon qwayar idanunta. Wani abu ne ya saukar mata a kanta mai nauyi,mamaki yayi bala'in cikata,yanzu haka har tana da qwarin gwiwar maida mata magana haka kai tsaye?,lallai tayi sake,tayi kuma barci kwana biyu "Zaizo me daure miki gindin ya gaya min idan shine ya gaya miki gidan nan kema gidanki ne" sai tayi gaba widad ta rakata da ido tana tabe baki,sai kuma ta gwada yadda tayi maganar sannan ta saki dariya,ita abinda ke bata mamaki,mummy hafsat din babba da ita,amma kullum aikinta tsaiwa taja magana tsakaninta da ita,taja tsaki tana sake tabe baki taci gaba da aikinta.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 07 Wuni hafsat din tayi tana zirga zirga cikin gidan,bata falo bata kitchen,ita kuwa widad hakan bai hanata zagewa ta shiryama uncle abbas dinta abinci lafiyayye ba, hafsat din na zaune daga falo sanda qamshin ya fara mata sallama,ta baza qofofin hancinta, Zuciyarta na gaya mata ko daga babban sashen hajiya na gidan qamshin ke fitowa?,to amma data nutsu da kyau saita gane daga kitchen din gidansu ne,mamaki ya daskarar da ita a wajen,ta gaza daurewa ta nufi kitchen din kamar zata dauko wani abu. Qamshin da tayi arba dashi yafi na falon,ta gefan ido take kallon yadda yarinyar keta aikin girkinta komai da komai tsaf,kai bakace girki takeyi ba,zarcewa tayi da dauko ruwa zuciyarta na wani irin tsalle daga qirjinta saboda zallar kishi,ta dauka ruwan ta juyo ta fito,saita ajeshi kawai gefanta ranta yana baci. Tako ina yarinyar ta bata mata tsari,komai na yarinyar canzawa yakeyi ko tace tama canza totally,komai nata a yanzun na cikakkun matan aure ne,yaushe ta iya girki mai bada matsiyacin qamshi haka?,cikin wadanne watannin ne da bata banbancesu ba?. Tana tsaka da wannan nunqufurcin da tunanin harta gama komai ta kuma fito daga kitchen din zuwa dakinta,a nan yaran suka ganta,suka ruga da saurinsu suka bita dakinta,a sannan bata da kuzarin hanawa,don tayi nisa cikin tunani da lalubowa kanta mafita. Sosai yaran suka sake suna wasansu a dakin nata,ta fidda chocolates ta basu ta shiga wanka,ta fito tana baza qamshin shower gel dinta mai taushin qamshi,ta tsaya gaban madubi ta soma gyara kanta. Tunda wuri yake qoqarin yaga ya kammala duka aikinsa ya dawo gida,duk wani motsi da zaiyi tana maqale cikin ransa,haka yayita kokawa da ayyuka don ya samu dawowa gida da wuri ya kasance da ita,amma hakan bai yiwu ba,sai yamma liqis sannan ya samu ya ture wasu ayyukan ya fito. Sai daya tsaya ya siya dukka nau'in fruits din da yasan tana so,ha hadama yaran da kayan kwadayi sannan ya dauki hanyar gida,cikin ransa yana jin wani zallar nishadi da farinciki,wata walwala da baisan tushenta ba ita ke wanzuwa saman fuskarsa,lokaci lokaci yakan saki murmushi idan ta fado masa a rai,a haka har ya cimma gida,yadan dannan hon mai gadi ya dage masa qofar. Sautin hon din motarsa daban yake a kunnuwan widad,ta lumshe ido dai dai sanda ta gama shirya kanta tana duban kanta da kanta cikin madubi "Ga daddy nan fa ya dawo" tace da yaran tana dan dubansu,wani shauqi da qaguwar riskarsa tana ratsata,sai takejin kamar tayi shekara ne bata rab'i uncle din nata ba "Yau sai na riga kowa zuwa taro daddy" mimi ta fada tana tattare kayanta,murmushi widad ta saki "Zamuga waye zai riga wani" sai ta dauki turare ta sake feshe jikinta,sannan ta nufi qofa da sauri tana yiwa mimi gwalo,wannan ya sanyata zubda kayan ta miqe tana qyalqyala dariya "Allah anty saina rigaki" ganin yarinyar ta biyota sai ta dan saka sassarfa tana mata dariya tayo gaba mimi din ta rufo mata baya. Dai dai sannan hafsat da taji muryarsa daga waje suna gaisawa da ma'aikatan gidan ta fito falon,daga kujerar dake daura da bakin qofa ta zauna,ta yadda idan ga shigo idanuwanta zasu iya gane mata komai,uwa uba ma tasan babu wanda ya isa ya keta idanunta ya tsallaketa ya isa gareshi,ta baza dukka idanunta tana qarewa gyaran da aka yiwa falon zuciyarta kamar ta fito,lallai ba shakka sai taci uban yarinyar,sai tayi maganin dukka wannan kinibibin nata,taja qwafa tana karkada qafafunta. Yana doso part din ransa yana sake yin fari,tun bai isa falon ba ya tabbatar ya koma saitinsa yadda yakeso,qamshi mai sanyi ke hudowa ta tsakanin labule da qofar yana fitowa har harabar gidan,ya buda qofar falon a nutse bakinsa dauke da sallama,hafsat din ta miqe tana dan sakin murmushi tare da amsa masa sallamar. Taku biyu tayi zuwa gaba da niyyar amsar jakar hannunsa muryar widad hade data mimi ta karade falon. Hankalinsa da nata gaba daya ya koma kansu,sanda suke rige rigen tarbarsa kowa yanason ya fara isa a tsakaninsu. Sosai ta fusgi hankalinsa ta kuma tafi da dukkan nutsuwarsa,yadda take tahowa da sassarfa yaji ya masa kadan,ya fara takawa shima ha ruskesu,cikin sa'a ta riga mimi isa,ya bude hannunsa ta fada jikinsa tana fadi cikin dariya "Oyoyo daddyn mimi" sosai yake kallon fuskarta da narkakkun idanunsa dake kanta,yasa hannu ya daga fuskar tata yana murmushi wanda yafi kama da dariyar farinciki "Kinwa 'yarki wayo ko?" "Dama na gaya mata,sai na rigata" saita jefawa mimi gwalo,yarinyar ta tabe baki kamar zata saki kuka,sai widad din ta miqa mata hannu tana sakin dariya "Taho.....taho mimin dadd......" Sautin kuka shi ya maida hankalinsu duka ga hafsat,duk sai sukayi sak suna dubanta,har ga Allah abbas din ya manta da wanzuwarta a wajen gaba daya,widad tasan tana gurin amma batajin zata iya fasa abinda ta saba yiwa uncle din nata,uwa uba kuma dazu da taji yana cika baki da tinqaho akan uncle din,abun ya bata haushi amma saita qyale kawai,tana ji a ranta zuwa yanzu ko meye mommy hafsat din tayi mata ta daina qyaleta. Kuka sosai takeyi,kafin abbas ya samu damar cewa wani abu ta juya da sauri ta nufi dakinta,batason yarinyar taga hawaye har haka a fuskarta saboda gudun raini. Bayan wucewarta sai suka koma kallon kallon a tsakanin,a nutse ya zare widad daga jikinsa yana cewa "Ina zuwa" yabi bayan hafsat din,tabe baki widad tayi ta dauki.jakarsa daya aje a wajen suka wuce dakinta ita da mimi,yarinyar nata murnar tare daddy ya tarbesu,saidai sama sama widad din ke amsawa,don dukka hankalinta nakan abbas din. A nutse ya tura qofar dakin ya shiga,tana daga zaune bakin gadonta tana sharar qwalla,ya taka ya isa gabanta ya tsaya kawai kallonta hannayensa goye a qirjinsa "Me akayi miki?" Ya jefa mata tambayar data sakata dago kai idanu jiqe da qwalla ta dubeshi,wani baqinciki ya tokare mata wuya,wato baisan me yayi ba? "Bakasan me kayimin ba abban mimi?,ko yaushe baka da burin da ya wuce ka wulaqantani ka tozartani a gaban yarinyar nan,nice na fara welcoming dinka,amma tana fitowa ka kasa tarata ka koma kanta saboda tsabar cin fuska" iska ya furzar daga bakinsa yana gyara tsaiwarsa "Yanzu wannan shine abinda yakai ayi masa kuka?" Shuru tayi bata amsa ba tana ci gaba da goge qwalla,baisan yadda takeji ba a yanzun,da bai tsaya kanta yana magana fada fada ba "Dole sai kinyi haquri kin dauke kai,akwai banbancin shekaru a tsakaninku, infact ma ta riga ta saba ita kadai take rayuwa a gidan nan,wasu abubuwan sai a hankali zata dainasu" saiya fara takawa zai fita a dakin,ta bishi da kallon takaici,bataso ya shigo dakin ya fita haka da sauri,tana so ko yaya ne ta bata masa lokaci yadda zata dasa zargi a zuciyar yarinyar,tunda ta lura zuwa yanzu zaman kishi sosai takeso suyi,ta wuce wancan lokacin da zata dinga juya ta da raina mata wayo yadda taso. Sunansa ta sake kira,cike da qosawa ya tsaya ya waiwayo,saita taso ta iso gabansa ta fada jikinsa ta fashe da kuka sosai,ba yadda ya iya haka yasa hannu ya tallafeta,rigimar hafsat din tayi yawa,matsaloli kala kala marasa tushe balle makama,qanqanin abu saita hurashi ya zama babba,har yau ta kasa gane girmanta balle ta riqeshi. "Bansan me yasa kakemin haka ba,bakasan yadda nakeji a zuciyata ba" ta fada cikin kuka,tilas ya bata lokaci yana lallashinta tare da nusashe da ita cikin hikima,saidai abinda bai sani ba,duk abinda yake fada tana bi ta bayan kunnenta ne,burinta kawai ya jima a dakin. Ta samu yadda takeso kuwa,don ya jima yana jan hankalinta kafin ya baro dakin bayan ya umarceta data sake gyara dakin, saboda tuni ya fara fita daga kamanninsa a kwanki uku kacal,baya jin kuma zai jura,ba kamar bauchi bane,a yanzun bashi da wani dakin daban da zaice zai kebance a cikinsa. Bacci ya dauke mimi sai widad dake zaune gefan gadon,ta cika tayi fam,bata taba jin bacin rai irin wannan ba,shi yasa sam ko ganin mummy hafsat din batasonyi,tana jin wani zafi a zuciyarta duk sanda ta fahimci ko taga sun kebe,koda yayi sallama saita zumbura baki ta miqe ta nufi toilet kawai tana amsa masa ba tare daya tsaya a nan ba,qaramin murmushi ya saki bayan ya kalli agogo,sai a sannan ya fuskanci laifinsa,ya qarasa bakin gadon ya duqa ya dauki mimi ya maidata wajen hafsat sannan ya dawo dakin,ya jingina da mirror yana jiran fitowarta. Kamar bata ganshi ba sanda ta fito daga bandakin,ya bita da kallo yana sake tantance kyan da tayi,wani abu na motsa masa a ransa game da ita,a strong desire,idanunsa na zagawa bisa jikinta,bomshort din jikinta yayi masifar fidda shape na qugunta,kaman ana fusgarsa haka yaji,ya isa gareta cikin sassarfa ya jawota jikinsa. Abun yazo mata a bazata,wanann ya haifar da motsi a cikinta,abinda yayi matuqar firgitata tunda bata bata taba ji ba,a zabure ta saki ihu da ya sanya abbas riqeta da kyau yana lalubar abinda ya faru,hafsat kuma dake maqale a bakin qofa tana jiran jin taqaddamar da zata faru a tsakaninsu sanadin dadewarsa a dakinta ta sake gyara tsaiwarta da kyau,dadi yana cikata da jin ihun widad din,may be ta masa wani rashin kunyar ne yaji bazai iya jurewa 'yar cikinsa tayi masa haka ba ya kaiwa bakinta bugu. "calm down.....menene?" Kasa amsa masa tayi sai hawaye da ya fara bin idanunta,ta kama hannunsa ta dora saman cikinta,dai dai sanda motsin ya ratsa tafin hannunsa ya aika saqo kwanyarsa,sai kuma ya tsaya cak. Sosai ya shiga mamaki da tunani,ya dubeta cikin mamaki "Yaushe ya fara irin wannan motsin?" "Bai taba yi ba sai yau" ta fada tana sharbe hawaye,qaramin murmushi ya saki,saita saki baki tana kallonsa "Karki damu,zan kira dr yanzu nayi mata bayani,zauna a nan ki nutsu,don't bother". A nutse ya zaunar da ita sannan ya lalubi wayarsa ya fara neman number din dr maryam,daya daga cikin personal doctor dinsa.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 08 Bai jima yana kira ba aka daga,suka gaisa cikin yanayi na sanin juna,sannan yayi mata bayanin dalilin kiran nata idanunsa akan widad da dukka ta sauya lokaci daya tayi wani laushi,idanunta cike da tsoro. "Indai cikin yakai watannin da zaiyi motsi ai zaiyi dama,hakan kuma alamu ne na cikin lafiyayye ne,watansa nawa?" Kai ya girgiza "Bansan watanninsa ba" Dan murmushi ta saka mai sauti "An gaisheku gaskiya,ina ganin gobe ka kawota asibitin sai ayi mata scanning da komai da komai,har EDD dinta sai mu gani,amma kace mata kada ta damu,babynta ya fara rayuwa sosai cikin qoshin lafiya ne" godiya yayi mata ya ajjiye wayar,ya saka hannayensa a aljihun uniform dinsa daya kasa cirewa tun shigowarsa gidan, idanunsa a kanta yana sakar masa murmushi,duk da cikin tsoro take amma hakan bai hanata basar dashi ba,zata miqe ya kamo hannunta da sauri ya sakata cikin jikinsa yana sansanarta kamar wata 'yar mage,yunqurin tureshi takeyi amma yaqi bata dama "Ka koma wajen hafsa kawai" ido ya fidda yana dariya "Yau kuma?,hafsa zalla?" "Eh sunanta ne ai" ta fada tana dan murguda bakinta,har qasan zuciyarta tana jin kishi yana tsunkulinta,juyo da ita yayi suna fuskantar juna "Yanzu dai na gane,kishi ne kikeyi,to ayimin afuwa" kafada ta maqale "Ni ban haqura ba,saidai idan zaka kaini na siyo ice cream" kai ya girgiza bayan ya fidda ido "So kike ki debarwa babyna sanyi?,bayan dr tace da alama lafiyayye ne?" Fuska ta kwabe ta langabar da wuya,yadda tayin tilas tasa yace "Shikenan ki shirya,amma yau kawai" cikin farinciki ta amsa masa,tuni har ta manta komai ta fara shiryawa,shi kuma ya fara rage kayan jikinsa don ya shiga ya watsa ruwa,wanda already ta hada masa,yana shiryawa shima yana tsokanarta akan cikin,ita kuwa kunya takeji,saida tayi masa kamar zatayi kuka sannan ya qyaleta. Sai da qafafunta suka gaji da tsaiwa bata sake jin komai ba,uwa uba da taga lokaci yana matsowa na fitarsa zuwa masallaci,dole taja jikinta tabar gurin tsakanin kokwanto da rashin tabbas na samuwar matsala a tsakaninsu,saita koma dakinta tabar dan space tana leqensa,har ya fito daga dakin tsaf dashi ya wuce masallaci yana baza qamshi,saita koma bakin gadon ta zube tana riqe da kanta,idan akwai abinda ta tsana a duniya shine taga walwala da zaman lafiya na gudana a tsakaninsu,dole ta sake kashewa tsinanniyar yarinyar kudi,dole ta sake aiki a kanta. Sai da yasa yara suka kirata sau uku akan ta fito suci abincin dare sannan ta fito,dai dai lokacin da widad ta fito daga kitchen dauke da babban try data zuba. Kofta(ire iren abincinsu ne na 'yan yemen da ake sarrafashi da nama). Hafsat din na shirin zama sai taji qafafuwanta zuwa bayanta ya sage,da qyar ta danni zuciyarta ta zauna zuciyarta na wani irin tuquqi da suya,wannan zallar cin fuska ne kawai abbas din yaso yi mata,banda haka ta yaya zai kirata cin abinci jikin yarinyar da wadan nan kayan?,duk kuwa da cewa ta dora wata 'yar kyakkyawar farar riga mai budadden gaba,amma hakan baikai ga boye dukkanin adonta ba. Da ido kawai take bin abincin,sunata walwalarsu tsakaninsu,abbas din yana tsokanar mimi widad na tare mata,ta gama serving kowa suka fara ci a nutse. Har qasan zuciyarsa yakejin nutsuwa tana saukar masa,ba shakka lafiyayyen abinci mai daddadan dandano ma rahama ne a rayuwa,bashi ba,hatta mimi ta soma santin abincin,abun ya taru.ya yiwa.hafsat yawa,duk yadda qamshin abincin ya karade falon yake tsinkar da yawu amma sai taji ya fice mata aka,ta ture plate din ba tare da tace komai ba ta saba yusra a kafadarta,tana gyara zaninta daya tattare. Sai da yakai lomar kufta din bakinsa sannan ya daga kai a nutse ya dubeta "Ya haka?,ina zuwa?" "Bazan zauna a nan ba tarbiyyar yara na ta lalace ba,don ba wajen zama bane,ta saka wasu kaya fingil fingil yarana suna zaune suna kallonta?,ke nawwara......mimi ku tashi muje" ta fada a tsawace,haushin yadda yaran ke wasoson abincin yana sake qureta Bata fuska dukkaninsu sukayi,saboda sudai suna jin dadin abincin sosai "Mommy ki zauna kici,da dadi wallahi" mimi ta fada fuska a narke,abunda ya sake hasala hafsat din ta kwaza mata tsawa,sai abbas din ya daga mata hannu "Kinga ya isa,jeki abinki ke daya" yadda yayi maganar tayi mugun baqanta mata,nan da nan hawaye suka cika mata idanu,sai ta girgixa kai kawai tayi gaba da sauri hawayen nason subuce mata. Ko tunata babu wanda ya sakeyi,abunda yayi masifar baqanta mata rai kenan,don tayi tsammanin zai biyo bayanta kamar dazun,saidai a maimakon haka ma sai tashin motarsa da taji,koda ta fito Parlor din wayam babu kowa,saita zauna anan hawaye na qwace mata,ya wankin hula yake shirin kaita dare?,saita miqe zumbur ta koma dakinta tana lalubar wayarta. Cikin kwanakin girkin widad din gaba daya hafsat ta tsangwami kanta,ta rasa nutsuwa bare sukuni,bata daki bata falo,komai widad din zata aiwatar idanuwanta suna kai,hakan ko kadan bai damu widad din ba,don zuwa yanzu ta fahimci meye ma'anar kishiya da abinda zamansu yake nufi ita da hafsat din,ko daya idanunta bai sanya widad din ta fasa duk abinda ta saba yi ba,hasalima yi tayi kamar bata gane ba,kamar dai har yau wautar quruciyan ne ke dibanta,abinda ke masifar hargitsa hafsat din,tana ganin kamar abbas din yana biyewa duk abinda takeso ne,yana kuma fifitata a kanta,wannan ya sanya ya ta sake cin alwashin wargatsa komai da lalata duk wani farinciki na widad din kota tsiya kota tsiya tsiya,sam ba zata gajiya ba. Ta gaza shuru ta gaza haquri da yadda yarinyar ke gudanar da komai kamar wata babbar mace,cikin kwanakin komai na gidan tsaf yake a kammale,bata bari komai ya lalace ko a barshi wasarere,tun daga cikin kitchen zuwa parlor dinsu,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin ganin ta watsa komai,widad din taja yaran a jiki,ta koya musu yadda zasu bar waje da kyansa bai lalace ba,ta koya musu koda sweet suka sha inda zasu saka ledan,abun ya yiwa hafsat din ciwo,tayita jaraba tana fadan su yar amma qememe sai suqi,kada ma mimi taji labari,maganar anty widad awajenta kamar fadar Allah,hafsat tayi dukan tayi banbamin ta hanata zuwa duk inda take amma kamar turi,abun ya soma taruwa yana mata yawa,ta rasa inda zata taro,yaran ko abbas din?,dole ta zauna ta fidda kudi sosai ta turawa ummanta,tana hasashen samun mafita. *******Yammaci ne lis,inda suke zaune cikin falon ita da yaran suna kallo,duk da cewa girkin hafsat dinne,amma ko alamun shirin dora girkin dare batayi ba,hasalima tana daki kwance abinta. Hakan gaba daya ba damuwar widad bane,don dama da qyar take kaiwa labari da abincin hafsat,wani irin girki mara tsari mara fasali kuma,sam ko a ido bashi da wani qayatarwa bare kakai ga bakinta,Allah ya bata wani irin kurman ciki da har yanxu ya gaza nunawa a jikinta,saidai can cikin jikinta tana jin wasu sauye sauye da ita kanta tasan wani muhimman al'amari ne yake tunkarota,takan zauna tayita lissafin scanning din da dr tayi mata,wai cikinta watanni shida harda kwanaki,ta sha ganin ciki amma itadai ba haka taga ana ciki ba,tasha tsayawa gaban madubi amma bata ganin komai idan ba turoshi gaba tayi sosai ba,duk da yana motsa mata sosai amma yabi jikinta da kyau,ya qarawa breast dinta cika ne sosai,abinda ke matuqar daukar hankalin abbas kenan kamar zai zauce mata. Waya ce a hannunta tana duba wasu sabbin recipe da Chief deeja Berver ta basu,tana yi tana murmushi,saboda yadda take fahimtar komai kamar a gabanta akeyi,har ya fada hasashen yaddaa gobe zata tashi kan gidan da nau'in kalolin sabbin girke girke. Taji qarar bude qofad sarai,amma bata ko kalli bakin qofar ba,don tasan wacece,sai taci gaba da duba wayarta kawai ba tare da tako motsa ba. Idanuwan hafsat din a zube fes akanta,ko wacce rana tana kwana ta tashi da mamakin yadda yarinyar ta gaza tabuwa,duk kuwa da kudin data kashe akanta,sai wata 'yar qaramar nasara data samu,wadda har yau wannan nasarar bata gamsar da ita ba,don bata ga wata alama ta shiga damuwa ko qunci daga wajen yarinyar ba sam,duk kuwa da cewa a yanzun tana iya juya wasu abubuwa na gidan,wanda a kwanaki ko watannin baya bata isa ta juyasu ba. "Ke mimi..... nawwara,uban me kuke zaune kukeyi a nan?" Ta jefawa yaran tambaya tana zare idanu a kansu,cikin tsoron kada ta hanata zama mimi ke kallonta,yayin da nawwara tayi qirmisisi abinta "Baba me gadi ne ya kawo kayan abba,yanata buga qofa shine na bude masa" "Da kika bude masa kuma sai kika samu waje kika zauna?,ina kayan suke?" "Suna dakin anty widad". Wani abune yazo ya tsaya mata a rai,ta kalli widad da har yanzu bata kalleta ba koda sau daya,miskilancin yarinyar yana qona mata rai,tanaso tayi mata cin mutunci wasu lokutan,amma bata kulata ma bare ta bata dama "Ke.....ki tashi ki debo kayan wankin abbansu ki kawomin nan" cak ta tsaya da danna wayar,saita daga kai a hankali karon farko ta kalleta,daga samanta cukurkudadden gashinta data daura dankwalin atamfa,zuwa jikinta dake sanye da rigar atamfar da wuyanta ya yima yawa,ta sauko ga fallen zaninta wani kalar atamfar daban. Kamar zata fashe da dariya amma kuma bacin ran da take ciki ya zarta tayi dariyar,don cikin kwanakin kawaici kawai takewa hafsat din,ta dauka har yanzu wai widad din dai data sani ce?,cikin kwanakin gaba daya ta fito da wata sabuwar gadara cikin gidan,komai ta taba komai zata gyara ko zatayi amfani dashi sai ta tsoma mata baki,tana tutiyar cewa gidanta ne,yadda takeso haka za'a yi,yadda taga dama haka takeson ta gani. Koda ranta ya baci bata taba tsaiwa tabi ta kanta ba,abu daya ta lura kamar abbas ya kasa dai daita hakan,abinda ita kuma takejin tazo maqura,ba zata lamunta ba itama. "Dakina nima akwai wajen ajiya" amsar data bata kenan a taqaice taci gaba da danna wayarta,abinda ya harzuqa hafsat din kenan "Ba shawara nake baki ba,umarni ne" sake sauke wayar tayi ya dubi idanunta da kyau,ta gaji da rainin hankalinta,kusan fiye da rabin komai da komai na abbas yana dakinta,tunda shine asalin dakinsa,amma ko sau daya bata taba nuna damuwa ko tayi qorafi ba,shine yanzu "Ajiyar ce akace miki ni ban iya ba?,wai meye damuwarki?,naga dai kayan mijina ne ko?" "Miji?,ni kike cewa mijinki ne?,turqashi!,wallahi saina nuna miki isata,saina nuna miki ni wacece,kuma wadan nan kayan saikin fiddosu" ta fada tana nunata da yatsa,kamar ma batasan me take ba, saita bawa banza ajiyarta taci gaba da abinda takeyi,ita abinda bata sani ba,tana jin zafinta fiye da yadda ita takejin nata,tana kishin uncle abbas fiye da yadda ita take kishin nasa,saidai ita an gaya mata,matsayinsu daya hasalima gaba take da ita,dole tayi respecting nata,amma ko daya bataga alamun daukar girma a wajenta ba. Banbami tahau yi tana sauka akan yaran,ta tattarasu ta wuce kitchen dasu,widad ta tabe baki taci gaba da abinda takeyi,saidai can qasan ranta zuciyarta tana mata zugi,ta gaji da rainin hankali irin na hafsat din,ta kuma daina daga mata qafa. Ko daga kitchen din tana jiyo masifarta da kuma mitarta,ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga bisani ta kashe girkin data dora ta dauki yusra suka fito "Sai maganinki,bazan zauna qaramar yarinya dake kina maidamin magana ba kamar sa'arki" abinda ta fada kenan tana ficewa daga falon. Gyara kwanciyarta ma tayi tana maida hankalinta ga kallo,tsahon mintuna kusan goma sha biyar saiga maari matar me gadinsu tayi sallama,widad ta miqe ta zauna cikin fara'a da yake mutuniyarta ce sosai,suka gaisa sannan tace "Hajiya ce tace ayi kiranki" mamaki sosai ya kama widad din,hajiya kuma?,irin hakan bata taba hadasu ba illa iyaka gaisuwa "Bari na fito muje tare" ta fada tana miqewa tayi daki,maari tabi bayanta da kallo cikin tausayawa yarinyar,Allah ya hadata da BAK'AR KISHIYA. Tana sallama ta hangi hafsat daga zaune tana bawa yusra nono,a nutse widad din ta qarasa tana gidata,sama sama ta amsa mata fuska a hade,tun daga nan sai itama widad din ta kama kanta. "Kinsan alaqata da babanki?" Ta fada kai tsaye,saita dubeta sannan ta girgiza kai,tadai san suna da alaqa amma batasan wacce iri bace,kwanaki da ummu tazo mata suna yawan zama suna hira,hakanan itama tana aiko mata da abinci kullum "Kamar qanwa nake a wajen babanki,wannan dalilin ya sanya nayi kiranki,mummyn mimi ta kawo qararki,ki shiga taitayinki,banason rashin kunya da diban albarka,kizo ki sameta da mijinta da komai nata amma ki dinga qoqarin nuna kinfi kowa iyawa?,ki dinga yi mata isa da gida?" Wani abu ne ya taso mata,taji sam ba zata iya daukan zancan ba,don haka ta runtse idanu tayi nesa da tunaninta na tsahon wasu mintuna kafin daga bisani ta miqe "Ai bansan gidanta bane ba,amma yanzu na sani" abinda tace kenan ta soma takawa tana yin gaba,duk sai suka bita da ido,nauyi da kunyar yadda yarinyar tayi yana kama hajiya,yayin da hafsat ranta ya baci,ta kawo qarar wajenta ne saboda taji akwai alaqa a tsakaninsu,amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba. Ranta yanatason ya baci amma tana qoqarin dannewa,tayi nasarar korar wannan,taci gaba da sabgoginta,bata ce ga sanda hafaat ta dawo ba,ta daiji motsinta cikin kitchen da kuma qananun mitocinta qasa qasa. Kwance tayi a dakinta har aka kira magrib,ta shiga toilet dinta ta sake wanka sannan tayi alwalar sallar magariba,wanna din sunnarta ne,ta riga ta saba koda bata da girki sai tayi wankan nan ta canza kaya,abinda hafsat din tayita son ganin ta hanashi faruwa,a cewarta ba ranar girkinta bane,don me zata dinga fitowa tana mata kwarkwasa da turare da kwalliya,saidai bata samu wannan nasarar ba. Ana idar da sallah taji alamun shigowar abbas din,duk sanda ya shigo gidan koda motarsa na anesa,ko motar office ce ta ajjiyeshi daga nesa sai taji hakan cikin jikinta,har zuwa sanda ya shigo sassan nasu, tanajin muryar su mimi suna masa oyoyo,taso tashi amma sai taji duka bata da interest akan hakan,kuma ma tasan bazai wuce minti uku bai qaraso dakinta ya dubata ba,don haka taci gaba da zama tana qarasa addu'o'inta da bata rabo dasu. Tun tana zuba ido harta soma qosawa,shuru bataji sake jin motsinsa ba,ta kalli agogo minti kusan ashirin kenan,tana sauke ido yayi dai dai da tashin muryarsa daga parlor yana kiran sunanta,duk sai taji banbarakwai,abinda bata saba dashi ba,amma kuma yau da gobe sai Allah,sai ta miqe a nutse tana gyara hijabinta sanan ta nufi qofa,gefe daya tana jin yadda cikinta yake qara tauri,wanda ita daya keji da ganin hakan.[5/8, 2:56 PM] Sweet sis: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 10 Kamar ta bawa mimi kudin ta maida mata,sai taga kada tayi asara,ta bata kudin kuma tazo batayi musu girkin ba,don haka sai ta ajjiye kudin tanata qananun mitoci. Tun tana saka ran ganin widad din ta shigo sashen har ta fidda rai,don yamma ta riga tayi,ga yunwa suna ji ita da yaran,dole ta shiga kitchen ta dora dafa dukan shinkafa. Tana kitchen din tana fama ga magrib ya kawo jiki widad ta dawo,dakinta ta wuce kai tsaye,bata bi ta kan jagulallen parlor din nasu ba,tana mamakin yadda suke iya hargitsa guri har haka suci gaba da zama a cikinsu abinsu hankali kwance. Ta taho da sauran faten tsakin daxu,da zafinsa don a wani warmer mai kyau da hajiya ta bawa maari yake a ajjiye,saita hada ruwa me zafi ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka ta gasa jikinta sosai,ta dawo ta zura wata armless riga da iya tsahonta gwiwa,ta wadata jikinta da turare,ta sake jona humidifier sannan ta dawo tana laluben hijabin da zatayi sallar dashi wanda zai saukar mata har qasa. Sosai yau ya hado yunwa da kuma gajiya a jikinsa,ya tabbatar zai samu dukkan wani hutu da kulawa hadi da kwanciyar hankali daga gurinta,wannan yasa ya hada dukkan yunwarsa ta yinin ranar,bai wani tsaya yaci cikakken abinci ba,don yasan zai tarar da irin taste din da yake muradi,har fiye ma da yadda yakeso. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya kashe motar tasa,ya waiwaya baya ya dauko ledar fruit din da ya siyo da chocolate nasu mimi ya fito,ya kashe motar sannan ya nufi cikin gidan. Tun kafin ya qaraso ya fara buda hancinsa yana tsammatar samuwa sassanyan qamshin nan dake masa maraba a duk sanda girkinta ya shiga,saidai babu shi ba alamarsa,duk da haka yaci gaba da takawa cikin hope da kuma karsashi. Sosai mamaki ya cikashi sanda ya yaye labulen falon ya sameshi a tarwatse,komai yana zaune zaman kansa,sai su mimi dake ta hada hada da kayan ciye ciye na leda irin wanda yake siyowa ya jibge musu,ko ina tarkacen kayan ledojin da tsinken sweet ne,dukansu suka watsar da abinda yake hannunsu suka nufoshi suna rige rigen qarasowa,ya tsugunna ya tarbesu gaba daya. Miqewa yayi yana dauke da nawwara mimi na hannunsa,yaji motsi a kitchen,don haka zuciyarsa ta bashi widad ce,sai ya wuce kitchen din dasu kanshi tsaye yana amsa tarin tambayoyinsu da suketa damunshi dasu. Tun bai gama shiga kitchen din ba idanu da hancinsa suka gaya masa ba widad bace,hafsat ce sanye da doguwar rigar wani material ruwan qwaiduwar qwai,sulbinsa ya sanya dinkin da aka masa a wasu sassan ya zazzame yayi zare zare,tana goye da yusra daketa mutsu mutsun son a sauko da ita,ya qarasa yana amsar yarinyar,ta sauke masa ita tana masa sannu da zuwa muryar a cunkushe. "Ina antyn nasu?" "Tana dakinta mana" hafsat ta amsa adan fusace tana juya dafadukan data fara kamawa "Lafiyarta qalau?" Juyowa tayi kamar ta banka masa harara,amma kwarjinin nashi idanuwan sun shallake nata "Aiba wannan ya kamata ka fara tambaya ba,kamata yayi ace ka tambayi wanda ya bamu abinci wunin yau,ta shige daki saboda ta samu daurin gindi tayi kwanciyar ta wuni guda ta barmu da yunwa ni da yara" sam hankalinsa bashi akan maganarta, zuciyarsa da tunaninsa sun karkata kan sanin lafiyarta da abinda ya hanata fitowa wunin yau,sai ya juya yana sabe da yusra ya fice a kitchen din. Ana fara knocking ta gane shine,ta riga ta saba da komai nasa,hatta takun takalminsa ya banbanta dana kowa,tana kuma iya banbancewa,ranta yadan quntata,itakam ko son ganinsa batason yi,space take da buqata, batason takura,to amma batason tayi wani abu na rashin girmamawa a gareshi gaban yaransa,dole ta ajjiye qaramar hular da take qoqarin sanyawa sassalkar sumarta daketa sheqi saboda yadda tayi oiling dinta da mai,tana tura baki da shagwababbiyar fuskarta ta isa qofar ta bude masa,sai taja ta tsaya daga bakin qofar,kamar wadda aka zo gayawa saqo take jira a gama gaya mata a fita ta kulle qofarta. Tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa wani abu ya tsarga masa,yadda batasaka brassiere ba amma hakan bai hana na shanunta tsaiwa kyam suna nuna kansu ba,lafiyayyun cinyoyinta sun fita sosai ta cikin tsingilalliyar rigar,yadda ta turo bakinta gaba kuma ya qarasa kunnashi,soft pink lips dinta daketa sheqin lip gloss,sai yaji kamar ya jata cikin jikinsa ya kama bakin ya tsotse,amma yusra na kafadarsa,tilas ya daure,ya qarasa gefan gadon ya zauna ya dora yarinyar saman cinyarsa "Sannu da zuwa" shuru ya ratsa maimakon ya amsa mata,ya tsareta da ido yana jin yadda kallonta kawai yake saukar masa da kasala "Banda na shigo na nemeki bakisan ma na dawo ba kenan?" "To me zanzo nayi maka?,bayan maganar matarka kawai kake ji" ta fadi haka cikin ranta,amma a fili saita sake tura baki gaba tana yamutsa girarta hadi da sarqafe yatsunta waje daya tana ballaqasu "Zonan" ya fada a tausashe yana nuna mata kujerar madubin dake gabansa,ta kalli wajen sannan ta kalleshi,ko yaushe girma da kimarsa ke sakata ta kasa masa musu ko wasu dabi'u da basu kamata ba,ta sauke hannuwanta ta dawo inda ya nuna matan ta zauna,wannan karon idanunta cikin nasa tanason jin abinda zai gaya mata kuma. Rage kaifin nasa idanun yayi kadan daga kanta sannan ya magantu "Ya akayi gidan ya zamana yau duk a hargitse,infact ma yau girkinki ne amma baki fito kwata kwata ba,ko yanzun ma antynki ce cikin kitchen din" wani haushi ya kamata,aiki?.....a nan tafi kauri kenan, idanunta ta lumshe kadan tana daukesu daga kansa,abinda ya sake fusgarsa da wani madaukakin shauqi zuwa gareta,duk da ba tayi bane don ta burgeshi ko kuma da wata manufa "Gida a hargitse?,ina cewa mummyn mimi tana cikin gidan,amfanin zaman mutum biyu kenan,idan dayan ya gaza ko ya gajiya sai dayan ya tallafa masa.......girki kuma ni na daina girki,na bar mata komai da komai harda kwanana" mamakin widad din sosai ya kamshi,yadda tayi maganar ya tabbatar da gamewar hankali a jikinta,don tana maganar ne with seriousness in her sound,baibi takan maganarta ta farko ba,maganarta ta qarshe tafi fusgar hankalinsa tare da tabashi,don abune da bayajin ko sama da qasa zata hadu zai amince da hakan "Kin daina girki?,meye dalili?,da kuma izinin wa kika dauki wannan matakin?" Sake tura bakinta gaba tayi sosai tana hade fuska,ta kuma kaucewa dubansa "Saboda gidan da mijin duka nata ne,so komai da yake cikin gidan yafi cancanta ya zama nata" sai yanzu ya sake gano inda ta dosa,can qasan ransa murmushi ya kubce masa,kishi take da gaske.....ta kuma ji haushin abinda yayi mata kenan fiye da yadda ma shi ya zata,amma bayason ta dore da haka don haka ya miqe yana dora yusra a kafadarsa "Ki shirya komai kamar yadda kika saba,banason dawo da zance,abinda ya wuce ya wuce" sai ya taka yana ficewa a dakin. Sam maganarsa bata bawa zuciyarta sassauci ba,saima tunzurata da yayi,bazai iya daukan mataki ba kenan kwata kwata?,indai haka ne itama bataga dalilin da zai sanyata saukowa ba,don haka yana fita sallar magariba ta sakawa dakinta key tayi sallarta ta jirayi isha'i ta bada ita sannan ta haye gado ta nutse cikin duvet hankali kwance. Sai daya dawo daga masallaci sannan ya zarce dakinta don ya samu ruwan nan nata me wani irin dumi da qamshi don yayi wanka,ruwan da ita kadai tasan yadda take hada masa shi,don koshi ya hada da kansa baya jin dadinsa kamar haka. A nutse ya tsaya yana knocking a bakin qofar,tana jinsa ta share,saita saka earpiece ma a kunnenta,don haka batasan adadin awannin ko mintunan da ya dauka yana bugun ba. Sosai ransa ya quntata,don yadda yayi tsaye yana bugun har mimi taji ta fito ya tabbatar tana jinsa,ya kirayi sunanta kusan biyar shuru,dole ya juya dakinsa dakin kuma hafsat,tana zaune a qasa ta tara kayan qazantar yusra tana waresu,ya wuce gaban cupboard dinsa yana rage kayan jikinsa. Binsa tayi da kallo ta tabe baki,ita da zasu tabbata a haka sai tafi kowa farinciki,duk bugun akan kunnenta akayishi,tana sane tayi bakam "Ba kwananta bane?,ya na ganka a nan dakin?" Ta jefa masa tambayar da tasan amsarta. "Na sani,hadamin ruwa zanyi wanka" ya fada muryarsa da wani irin laushi daya bata mata rai,komai na yarinyar tabashi yakeyi,saka masa damuwa yakeyi,duk qoqarinta na kau da hankalinsa amma baya wani tasiri yadda take da buqata,ita sau nawa suna irin wannan sabanin,amma ko a fuska bata taba gani yayi laushi irin haka ba,komai dadewar da zasuyi,sai yanzu akan qaramar yarinya kwana uku kacal amma duka ya canza?. Da tunani iri daban daban ya shiga wankan,sam ruwan baiyi masa ba,hasalima ya cika zafi da yawa,yaja tsaki ya saki famfo akai,sai kuma yaso salance masa,ya sake jan wani tsakin yana komawa cikin bathtub din ransa duka a jagule. Koda sukazo cin abinci ma yasa mimi ta bubbuga mata,duk da yadda hafsat ke faman hada rai tana ganin ya girkinta ne batayi ba ita ta zauna tayi kuma saboda gata wai a kirata taci,itama mimin haka ta qaraci bugunta ta haqura ta dawo jiki a sanyaye "Bata bude ba" sai ya shafa kanta "Inajin tayi bacci" a yadda yake jinsa koda lafiyayyen girki hafsat din tayi abincin bazai masa dadi a baki ba,bare tafashi kadan hafsat din wadda ta cuccure waje daya,kamar gidan da aka yiwa gorin man girki,bayan komai a wadace yake a store dinsu,zuciyar tata ce dai haka. Da qyar yayi loma hudu ya ture abincin,ya maida hankalinsa ga news da ake haskowa a channel din al_hadath,duk da a badini fiye da rabin hankalinsa yana kan qofar dakinta,duk bayan mintuna biyu saiya kalli qofar dakin,amma ko motsinta daga ciki baiji ba bare ya sanya ran zata bude ta fito. Har yaran sukayi bacci hafsat ta debesu takai daki ta dawo tayi masa sallama yana zaune a wajen,sanda sha daya na dare ta buga sai ya tashi yana sake gwada bugun,a lokacin tuni tayi bacci,bugunsa ne ya tasheta,ta sauko a hankali ta wuce toilet abinta,tayi fitsari ta sake alwala ta dawo ta kuma kwanciyarta. Wannan karon yaji motsinta shigarta bandaki zuwa fitarta,hakan ya nuna masa tana jinsa,bata kuma da niyyar bude masa,ya koma da baya ransa yana baci,ya juya yana nufar dakinsa. Dadi ya kama hafsat dake labe,saita koma bakin gado ta zauna tana kada qafa a hankali,itakam gaba ta kaita,dole yau ya kwana dakinta,sannu a hankali dai gida yana shirin dawowa hannunta sai yadda ta juyashi, murmushin nasara da farinciki ya kubce mata. [5/8, 2:56 PM] Sweet sis: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 09 Yana zaune saman kujera sanye da uniform din nan nasa dake qara masa kyau da kuma kwarjini,ko boots din qafarsa baikai ga cirewa ba,hafsat na tsaye daga gefansa,hannayenta goye a qirjinta,fushi ne kwance saman fuskarta. Idanunshi a kanta,wani abu daya kasa tantance meye yana tsinkulin zuciyarsa,mabanbantan abubuwa guda biyu daketa faman gogayya da juna,har ta iso ta zauna gefan kujerar dake daura dashi tana masa sannu da zuwa. "Me ya hadaki da hafsat.....har kikayi mata rashin kunya?" Maganar tazo mata a bazata,mamaki ya kamata,ta dubi hafsat din suka hada ido,sai hafsat din ta aike mata da saqon harara,ta daure ta shanye sanann tace "Ni bansan yaushe nayi mata rashin kunya ba" "Kina nufin bakisan maganar kayan da kika kwashe ba?" Ta tambayeta kamar wata diyar cikinta,sai abbas din ya daga mata hannu "Ya isa.....me yasa kika kwashe kaya da aka dawo dasu daga laundry?" Cak ta tsaya ta zuba masa idanu,mamaki yana kasheta,duk yadda taso hana taruwar qwalla a idanunta amma ta gaza,saita gyada kai tana hadiye wani abu mai tauri daya tsaya mata,cikin rawar murya ta fara masa bayani "Baba mai gadi ne ya kawo su,tana.bacci yace a kwashe maka kada yara su tattaka,don ma debe shine nayi laifi?,ina cewa kusan kaso uku cikin hudu na kayanka suna dakinta a wajenta,na taba magana?" Sosai ta taba zuciyarsa yadda hawaye ke sauka saman fuskarta,tana kuma maganar muryarta tana rawa cikin sautin kuka,yanason yace ta tashi taje,tayi dai dai amma kuma kamar ana ingiza zuciyarsa,kamar kuma ana hura masa bacin rai haka yakeji. "Tashi kije ki debosu!" Yadan fada a kausashe,idanunta ta sanya cikin nasa mamaki yana sake daskarar da ita,totally uncle abbas din canzawa yakeyi cikin kwanakin,ba yau ya fara ba amma na yau yafi qona mata rai da tsaya mata a rai,ba yau ya fara ba,cikin kwanakin ko meye hafsat din tayi gaskiya yake bata,yana kuma qoqarin goyuwa da bayanta,sai ta miqe tsam cikin matsanancin bacin rai,ta dauke idanunta daga kansa ta maida ga hafsat,sai taga tuni yanayin fuskarta ya sauya zuwa madaukakin farinciki. Janye idanunta tayi daga kan fuskokinsu gaba daya,ta kuma juya da sauri ta nufi dakinta, abbas ya rakata da idanu yana jin kamar ya bita amma kuma wata zuciyar na gaya masa yayi dai dai,sai yaci gaba da kallon qofar da kuma tsammanin fitowarta. Cikin bacin rai ta fara tattara dukka wani abu da tasan nashi ne cikin daki,bata bar komai ba koda kuwa agogo ne,tana hade kayan hawaye na fita a idanunta,ta tsani rashin gaskiya,ta tsani a bata rashin gaskiya a rayuwar ta,ta tsani batayi abu ba ace tayi,tana jin kamar ta mutu idan akayi mata haka. Debo kayan ta fara yi hannu bibbiyu,ba ruwa ta da wadanda suke zubewa ta riqosu zuwa falon,tana zuwa batayi wata wata ba ta watsar dasu a wajen ta juya da sauri taci gaba da debo sauran tana zubarwa a wajen,ran hafsat ya sosu sosai,wanne irin raini ne wannan?,ta tsammaci zaice wani abu,sai taga bai ko motsa ba yana kallonta ne kawai,yana karantar zallar fushin dake fuskarta,wanda bai taba ganin irinsa ba a tattare da ita ba "Wai baka ganin abinda yarinyar nan takeyi?,kaga fa yadda take watso mana kaya?" Maganartata yayi da gama kwaso kayan,ta juya abinta da nufin komawa dakinta "Widad" ya kirata a tausashe,bata ko waiwayo ba bare ta saurareshi,don kuka takeyi sosai ta wuce daki abinta. Cikin qarfin ikon Allah ya miqe da wani irin zafin nama,zuciyarsa yaji kamar zata fashe da kukan da widad din keyi,ya tuna meye a jikinta,ta yaya zai barta tana irin wannan kukan?,sai ya nufi dakin da wani irin sauri wanda yasa hafsat ta zaci zuwa zaiyi yayi maganinta,ya dauki mataki akan abinda tayin yanzu,don haka ta saki wata qaramar dariya cikin nishadi da jin dadi,ta tako cikin rashin damuwa ta fara tsince kayan tana dibansu zuwa dakinta,sai a sanann ta lura da mimi dake sharar qwalla "Ubanki kike a wajen?,wato an saka uwarki kuka shine kikazo kika rabe a nan kina naki kukan,zaki tashi ki wuce ciki ko sai nayi ball dake?" Ba shiri yarinyar ta zame ta wuce daki tana tura baki gaba hadi da ci gaba da goge qwalla. Rub da ciki takeso tayi kukanta yadda takeso ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma tudun da takeji a cikinta ya hana,dole sai saman pillow ta dora fuskarta tana sakin kuka sosai. Jiki a matuqar sanyaye ya qarasa shigowa dakin,sai ya kasa qarasowa ya tsaya daga bakin qofa yana kallonta,shi kansa baisan me yake damunsa ba,baisan me yasa yake wasu abubuwan ba,duk da abinda yakeyi din bata taba nuna damuwarta ba,koda ta nuna mintuna kadan take sakin fuskarta kamar ba'a yi ba,sai ayau data nuna fushinta har haka. A nutse ya qaraso ya zauna gefanta,tunda ya buda mata qofar daki tana jinsa amma bata nuna tasan da shigowarsa bama,hannu yasa a tausashe ya zare pillow din ya maye gurbinsa da tattausan tafin hannunsa,sai tayi saurin kawar da fuskarta daga wajen kamar ya dora mata wuta,yasan halin kayarsa,ta iya rigima a duk sanda taso ko aka tabota,don haka yayi amfani da dukka qarfinsa ya azata saman jikinsa. Dukka qarfinta ta sanya ta zame a jikinsa,bai gaji ba ya sake maidota yana kiran sunanta tare da qoqarin son su hada idanu amma taqi bashi wannan damar. Kin zama tayi bare ta saurareshi ba,haka ya gaji da son yin magana da ita ya haqura ya fice yana sauke ajiyar zuciya,ransa gaba daya a jagule babu dadi. Da kanta ta lallashi kanta,saidai a ranar ta yiwa kanta hukunci qauracewa abbas din da dukka abinda ya shafi hafsat dama cikin gidan,ba zata iya gani ba bazata iya jura ba,duk jarumtar ta abun ya taba ranta,tana iya bakin qoqarin bashi farinciki da son ganin walwala da nutsuwarsa.....gefe guda yana bawa hafsat go ahead tayi duk abinda yake shine dai dai,yana kuma mara mata baya,ta yaya ita tata zuciyar zata samu nutsuwar bashi nutsuwa?. Washegari ranar girkinta ne,tun safe tana kwance a dakinta wanda tun dare ta saka muqulli ta rufe abinta,tana da abubuwan ciye ciye da yawa a dakinta da bata rabo dasu,don a lokacin abbas da ya shafe babin fita da iyalinsa zuwa wasu guraren shaqatawa a baya,a yanzu widad din ta dawo masa da wannan dabi'a tasa,ko rana daya hafsat din bata taba yunqurin binsu ba,sai mugun haushi da takaicin da take fama dashi,har zuwa sanda zasu dawo cikin gidan,takan ce ita tafi qarfin zuwa nan wajen. Zamu iya cewa borin kunya ne takeyi,don tun sand yake marmarin kaita take watsa masa qasa a ido,take nuna tafi qaunar ya bata abinda za'a kashe a wajen ta adana,har abun ya fita a kansa,ko ssnda ta haifi su mimi yana son kaisu amma bai samu wannan qwarin gwiwa daga wajenta ba,don haka sai a jima bai fita da yaran ba sai sanda ya samu hutu mai tsaho,gaba daya ita din opposition na rayuwarsa ne totally,bata kuma taba sawa a ranta ta sauya wani tsari yanayi hali ko dabi'a tata saboda shi ba,saboda a samu dai daito da zama me dorewa. Tana jin motsinsu daga parlor din amma bata ko motsa ba bare tayi yunqurin fitowa,ciye ciyen da tayi a daki ya dauketa fes,don dama bata iya cin abinci me yawa,yana zaune dining area amma hankalinsa yana kan qofar dakinta,jiya da abun ya kwana dashi ya tashi,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin mantar dashi da wasu salo da sam baibi jikinta ba bare ya dace da ita,don ba dabi'arta bane. Ya kammala shan tea din da babu qamshin komai a ciki saina Lipton da milo,ya ajjiye cup din ya miqe yana sauka daga wajen,hafsat din na zaune tana kallonsa batace komai ba,tanason ganin ya za'a qare,ya isa qofar dakin nata ya tsaya a nutse ya fara knocking yana amsa wayar data shigo masa a lokacin. Taso ta shareshi taqi bude qofar,saboda Wani mugun zafinsa da takeji har cikin ranta,amma sai taga hakan bai kamata ba,tunda tasan a lokacin kowa yana parlor,ta kuma tabbatar hafsat din tana ganin komai da zai faru,don haka ba'a son ranta ba ta miqe a hankali tana gyara zaman yaloluwar rigar jikinta ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofar. Tana bude masa ta saki qofar ta koma,yabi bayanta da kallo tsigar jikinsa tana zubawa,ko kadan baya gajiya da ita,baya qosawa da ita,kwanaki biyun da basu tare mugun yunwar ta yakeyi,yaci gaba da kallonta yana dan hangen cikinta daya turo kadan,wanda sai ka saka ido da tsananin kula zaka iya ganinsa. Guri ta samu ta zauna ta gaidashi ba tare data kalli fuskarsa ba,yanata qoqarin su hada ido amma taqi "Ya jikin naki?" "Lafiyata qalau" ta amsa masa a shashance,ya sake duban fuskarta sosai yadda taketa basarwa,sai ya ajjiye mata kudin cefane yayi mata sallama ya fice. Dashi da kudin gaba daya tabi da kallo, zuciyarta ta tsinke kuka yaso qwace mata amma ta danne,ta kalli agogo sannan ta miqe ta shiga bandaki ta watsa ruwa,ta fito taa shirya cikin dinkin doguwar ruga bubu gown ta yane kanta da madaidaicin mayafi ba tare data daura dankwali ba,fuskarta tayi kyau,ta sake wani fresh da haske mai daukan idanu,inda ya ajjiye kudin cefanen ta isa ta dauki kudin,sannan ta qarasa inda wayarta take ita dauketa tare da daukan wasu abubuwan masu amfani sannan ta fito falon. Babu kowa,sai ta zarce kitchen,ta dan samu abinda zataci wanda bazai mata wahalar narkewa ba,don yanzun matsalar da take fama da ita kenan. Ta gama ta dauraye cup din ta maidashi inda ta dauko tana kallon yadda kitchen din ya hargitse,kamar ba kwanaki biyu baya ya koma hannun hafsat din komai fes bisa tsari,saika dauka watanni aka dauka ba'a gyarashi ba. Baki ta tabe ta fice abinta,yau daga kitchen din har Parlor din babu inda zata sama hannu,itama tasan dadin jikinta,kawai dai tanayin komai ne don samun walwala da nutsuwarsa,tunda ta fuskanci babu abinda ke daga masa hankali a rayuwa irin qazanta,amma tunda bai gani itama ba zata dinga wahalar da rayuwarta ba,zata barsu shida hafsat din tasa. Tana isowa falon sukaci karo da mimi "Ina kwana anty?" "Oyoyo mimin daddy,kin tashi lafiya?" "Lafiya lau anty,yau duka baki fito ba" "Banajin dadi ne,ungo wannan ki kaima mommynki kice kudin cefane ne inji ni" ta hada dukka kudin da abbas din ya bata ta sanyashi a hannun mimi,sai da taga ta shiga dakin sannan ta fice abinta harabar gidan. Kai tsaye boys quaters ta nufa wajen maari matar baba mai gadi,sosai taji dadin ganinta kuwa,don bata taba zuwan mata ba,ko yaushe widad din tafi ganewa zamanta daki tayi kallo ko chart,ta marabceta sosai suka fara dan taba hira,tun widad din bata sake ba har ta saki jikinta suka shiga hira sosai,kasancewar hajiyan bata nan,babu wani aiki cikin gidan haka suka wuni tare. Maari din saita tuna mata da latifanta,cikin awanni kadan ta gane tana da kirki matuqa da jan mutum ajiki,har tafi tsohuwar me aikin hajiyan data dinga tayata kwana sanda abbas yake tafiya bauchi ba tare da ita ba. Tayi musu faten tsakin masara da yasha gyada da yakuwa,batayi zaton zata iya ci ba,sai gashi taci sosai sunata hira,kirkin widad da yadda take girmama kowa cikin rashin nuna qyama ya sanya maari ma taji ta shiga ranta,ba kamar hafsat din ba,dake dagawa izgilanci da wulaqanta na qasa da ita. Hafsat na tsaka da barci taji mimi na qwala mata kira saman kanta,da qyar ta bude idonta tana jan mugun tsaki,kafin daga bisani kuma ta buda hancinta sosai saboda warin bayan gida da take jiyowa,dole ta wartsake ta miqe sosai ta zauna tana duban mimi "Ban hanaki idan ina bacci ki dinga tashina ba don ubanki?" Kebe fuska yarinyar tayi kamar zata saki kuka "Ai ban tasheki ba harma su nawwara sukayi kashi,yanzunma anty ce tace na kawo miki kudin cefane" "Kudin cefane kuma?"ta tambayeta da mamaki,saita jinjina kai,ta miqa mata hannu ta saka mata kudin,ta waresu tana irgawa. To me yarinyar take nufi?,nufinta ta ajjiye girki kenan saboda abinda ya faru jiya?,aiko ba zata sabu ba,ita dinma ai ba jaka bace da zata zauna tayita girka musu suna ci.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 10 Kamar ta bawa mimi kudin ta maida mata,sai taga kada tayi asara,ta bata kudin kuma tazo batayi musu girkin ba,don haka sai ta ajjiye kudin tanata qananun mitoci. Tun tana saka ran ganin widad din ta shigo sashen har ta fidda rai,don yamma ta riga tayi,ga yunwa suna ji ita da yaran,dole ta shiga kitchen ta dora dafa dukan shinkafa. Tana kitchen din tana fama ga magrib ya kawo jiki widad ta dawo,dakinta ta wuce kai tsaye,bata bi ta kan jagulallen parlor din nasu ba,tana mamakin yadda suke iya hargitsa guri har haka suci gaba da zama a cikinsu abinsu hankali kwance. Ta taho da sauran faten tsakin daxu,da zafinsa don a wani warmer mai kyau da hajiya ta bawa maari yake a ajjiye,saita hada ruwa me zafi ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka ta gasa jikinta sosai,ta dawo ta zura wata armless riga da iya tsahonta gwiwa,ta wadata jikinta da turare,ta sake jona humidifier sannan ta dawo tana laluben hijabin da zatayi sallar dashi wanda zai saukar mata har qasa. Sosai yau ya hado yunwa da kuma gajiya a jikinsa,ya tabbatar zai samu dukkan wani hutu da kulawa hadi da kwanciyar hankali daga gurinta,wannan yasa ya hada dukkan yunwarsa ta yinin ranar,bai wani tsaya yaci cikakken abinci ba,don yasan zai tarar da irin taste din da yake muradi,har fiye ma da yadda yakeso. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya kashe motar tasa,ya waiwaya baya ya dauko ledar fruit din da ya siyo da chocolate nasu mimi ya fito,ya kashe motar sannan ya nufi cikin gidan. Tun kafin ya qaraso ya fara buda hancinsa yana tsammatar samuwa sassanyan qamshin nan dake masa maraba a duk sanda girkinta ya shiga,saidai babu shi ba alamarsa,duk da haka yaci gaba da takawa cikin hope da kuma karsashi. Sosai mamaki ya cikashi sanda ya yaye labulen falon ya sameshi a tarwatse,komai yana zaune zaman kansa,sai su mimi dake ta hada hada da kayan ciye ciye na leda irin wanda yake siyowa ya jibge musu,ko ina tarkacen kayan ledojin da tsinken sweet ne,dukansu suka watsar da abinda yake hannunsu suka nufoshi suna rige rigen qarasowa,ya tsugunna ya tarbesu gaba daya. Miqewa yayi yana dauke da nawwara mimi na hannunsa,yaji motsi a kitchen,don haka zuciyarsa ta bashi widad ce,sai ya wuce kitchen din dasu kanshi tsaye yana amsa tarin tambayoyinsu da suketa damunshi dasu. Tun bai gama shiga kitchen din ba idanu da hancinsa suka gaya masa ba widad bace,hafsat ce sanye da doguwar rigar wani material ruwan qwaiduwar qwai,sulbinsa ya sanya dinkin da aka masa a wasu sassan ya zazzame yayi zare zare,tana goye da yusra daketa mutsu mutsun son a sauko da ita,ya qarasa yana amsar yarinyar,ta sauke masa ita tana masa sannu da zuwa muryar a cunkushe. "Ina antyn nasu?" "Tana dakinta mana" hafsat ta amsa adan fusace tana juya dafadukan data fara kamawa "Lafiyarta qalau?" Juyowa tayi kamar ta banka masa harara,amma kwarjinin nashi idanuwan sun shallake nata "Aiba wannan ya kamata ka fara tambaya ba,kamata yayi ace ka tambayi wanda ya bamu abinci wunin yau,ta shige daki saboda ta samu daurin gindi tayi kwanciyar ta wuni guda ta barmu da yunwa ni da yara" sam hankalinsa bashi akan maganarta, zuciyarsa da tunaninsa sun karkata kan sanin lafiyarta da abinda ya hanata fitowa wunin yau,sai ya juya yana sabe da yusra ya fice a kitchen din. Ana fara knocking ta gane shine,ta riga ta saba da komai nasa,hatta takun takalminsa ya banbanta dana kowa,tana kuma iya banbancewa,ranta yadan quntata,itakam ko son ganinsa batason yi,space take da buqata, batason takura,to amma batason tayi wani abu na rashin girmamawa a gareshi gaban yaransa,dole ta ajjiye qaramar hular da take qoqarin sanyawa sassalkar sumarta daketa sheqi saboda yadda tayi oiling dinta da mai,tana tura baki da shagwababbiyar fuskarta ta isa qofar ta bude masa,sai taja ta tsaya daga bakin qofar,kamar wadda aka zo gayawa saqo take jira a gama gaya mata a fita ta kulle qofarta. Tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa wani abu ya tsarga masa,yadda batasaka brassiere ba amma hakan bai hana na shanunta tsaiwa kyam suna nuna kansu ba,lafiyayyun cinyoyinta sun fita sosai ta cikin tsingilalliyar rigar,yadda ta turo bakinta gaba kuma ya qarasa kunnashi,soft pink lips dinta daketa sheqin lip gloss,sai yaji kamar ya jata cikin jikinsa ya kama bakin ya tsotse,amma yusra na kafadarsa,tilas ya daure,ya qarasa gefan gadon ya zauna ya dora yarinyar saman cinyarsa "Sannu da zuwa" shuru ya ratsa maimakon ya amsa mata,ya tsareta da ido yana jin yadda kallonta kawai yake saukar masa da kasala "Banda na shigo na nemeki bakisan ma na dawo ba kenan?" "To me zanzo nayi maka?,bayan maganar matarka kawai kake ji" ta fadi haka cikin ranta,amma a fili saita sake tura baki gaba tana yamutsa girarta hadi da sarqafe yatsunta waje daya tana ballaqasu "Zonan" ya fada a tausashe yana nuna mata kujerar madubin dake gabansa,ta kalli wajen sannan ta kalleshi,ko yaushe girma da kimarsa ke sakata ta kasa masa musu ko wasu dabi'u da basu kamata ba,ta sauke hannuwanta ta dawo inda ya nuna matan ta zauna,wannan karon idanunta cikin nasa tanason jin abinda zai gaya mata kuma. Rage kaifin nasa idanun yayi kadan daga kanta sannan ya magantu "Ya akayi gidan ya zamana yau duk a hargitse,infact ma yau girkinki ne amma baki fito kwata kwata ba,ko yanzun ma antynki ce cikin kitchen din" wani haushi ya kamata,aiki?.....a nan tafi kauri kenan, idanunta ta lumshe kadan tana daukesu daga kansa,abinda ya sake fusgarsa da wani madaukakin shauqi zuwa gareta,duk da ba tayi bane don ta burgeshi ko kuma da wata manufa "Gida a hargitse?,ina cewa mummyn mimi tana cikin gidan,amfanin zaman mutum biyu kenan,idan dayan ya gaza ko ya gajiya sai dayan ya tallafa masa.......girki kuma ni na daina girki,na bar mata komai da komai harda kwanana" mamakin widad din sosai ya kamshi,yadda tayi maganar ya tabbatar da gamewar hankali a jikinta,don tana maganar ne with seriousness in her sound,baibi takan maganarta ta farko ba,maganarta ta qarshe tafi fusgar hankalinsa tare da tabashi,don abune da bayajin ko sama da qasa zata hadu zai amince da hakan "Kin daina girki?,meye dalili?,da kuma izinin wa kika dauki wannan matakin?" Sake tura bakinta gaba tayi sosai tana hade fuska,ta kuma kaucewa dubansa "Saboda gidan da mijin duka nata ne,so komai da yake cikin gidan yafi cancanta ya zama nata" sai yanzu ya sake gano inda ta dosa,can qasan ransa murmushi ya kubce masa,kishi take da gaske.....ta kuma ji haushin abinda yayi mata kenan fiye da yadda ma shi ya zata,amma bayason ta dore da haka don haka ya miqe yana dora yusra a kafadarsa "Ki shirya komai kamar yadda kika saba,banason dawo da zance,abinda ya wuce ya wuce" sai ya taka yana ficewa a dakin. Sam maganarsa bata bawa zuciyarta sassauci ba,saima tunzurata da yayi,bazai iya daukan mataki ba kenan kwata kwata?,indai haka ne itama bataga dalilin da zai sanyata saukowa ba,don haka yana fita sallar magariba ta sakawa dakinta key tayi sallarta ta jirayi isha'i ta bada ita sannan ta haye gado ta nutse cikin duvet hankali kwance. Sai daya dawo daga masallaci sannan ya zarce dakinta don ya samu ruwan nan nata me wani irin dumi da qamshi don yayi wanka,ruwan da ita kadai tasan yadda take hada masa shi,don koshi ya hada da kansa baya jin dadinsa kamar haka. A nutse ya tsaya yana knocking a bakin qofar,tana jinsa ta share,saita saka earpiece ma a kunnenta,don haka batasan adadin awannin ko mintunan da ya dauka yana bugun ba. Sosai ransa ya quntata,don yadda yayi tsaye yana bugun har mimi taji ta fito ya tabbatar tana jinsa,ya kirayi sunanta kusan biyar shuru,dole ya juya dakinsa dakin kuma hafsat,tana zaune a qasa ta tara kayan qazantar yusra tana waresu,ya wuce gaban cupboard dinsa yana rage kayan jikinsa. Binsa tayi da kallo ta tabe baki,ita da zasu tabbata a haka sai tafi kowa farinciki,duk bugun akan kunnenta akayishi,tana sane tayi bakam "Ba kwananta bane?,ya na ganka a nan dakin?" Ta jefa masa tambayar da tasan amsarta. "Na sani,hadamin ruwa zanyi wanka" ya fada muryarsa da wani irin laushi daya bata mata rai,komai na yarinyar tabashi yakeyi,saka masa damuwa yakeyi,duk qoqarinta na kau da hankalinsa amma baya wani tasiri yadda take da buqata,ita sau nawa suna irin wannan sabanin,amma ko a fuska bata taba gani yayi laushi irin haka ba,komai dadewar da zasuyi,sai yanzu akan qaramar yarinya kwana uku kacal amma duka ya canza?. Da tunani iri daban daban ya shiga wankan,sam ruwan baiyi masa ba,hasalima ya cika zafi da yawa,yaja tsaki ya saki famfo akai,sai kuma yaso salance masa,ya sake jan wani tsakin yana komawa cikin bathtub din ransa duka a jagule. Koda sukazo cin abinci ma yasa mimi ta bubbuga mata,duk da yadda hafsat ke faman hada rai tana ganin ya girkinta ne batayi ba ita ta zauna tayi kuma saboda gata wai a kirata taci,itama mimin haka ta qaraci bugunta ta haqura ta dawo jiki a sanyaye "Bata bude ba" sai ya shafa kanta "Inajin tayi bacci" a yadda yake jinsa koda lafiyayyen girki hafsat din tayi abincin bazai masa dadi a baki ba,bare tafashi kadan hafsat din wadda ta cuccure waje daya,kamar gidan da aka yiwa gorin man girki,bayan komai a wadace yake a store dinsu,zuciyar tata ce dai haka. Da qyar yayi loma hudu ya ture abincin,ya maida hankalinsa ga news da ake haskowa a channel din al_hadath,duk da a badini fiye da rabin hankalinsa yana kan qofar dakinta,duk bayan mintuna biyu saiya kalli qofar dakin,amma ko motsinta daga ciki baiji ba bare ya sanya ran zata bude ta fito. Har yaran sukayi bacci hafsat ta debesu takai daki ta dawo tayi masa sallama yana zaune a wajen,sanda sha daya na dare ta buga sai ya tashi yana sake gwada bugun,a lokacin tuni tayi bacci,bugunsa ne ya tasheta,ta sauko a hankali ta wuce toilet abinta,tayi fitsari ta sake alwala ta dawo ta kuma kwanciyarta. Wannan karon yaji motsinta shigarta bandaki zuwa fitarta,hakan ya nuna masa tana jinsa,bata kuma da niyyar bude masa,ya koma da baya ransa yana baci,ya juya yana nufar dakinsa. Dadi ya kama hafsat dake labe,saita koma bakin gado ta zauna tana kada qafa a hankali,itakam gaba ta kaita,dole yau ya kwana dakinta,sannu a hankali dai gida yana shirin dawowa hannunta sai yadda ta juyashi, murmushin nasara da farinciki ya kubce mata.[5/10, 2:11 PM] +234 816 811 4418: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 11 Yana turo qofan dakin ta kalleshi,irin kallon mamakin nan wanda tuni ta shiryama hakan "A'ah,abban mimi ba kwanana bane" idanunsa ya zube fes akan fuskarta,yana iya hangen wani abu fake behind her face,sai ya lumshe ido kadan ya gyada kai "I know" sai ya qarasa ya dauki duvet dinsa da pillow ya juya ya fice yana ja mata qofa. Da kallon mamaki ta bishi,saita miqe ta nufi qofar yana leqensa,saman kujerun parlor din ya shimfidashi ya yada pillow din ya kwanta bayan ya rage hasken qwan falon,ranta yayi mummunar baci,wato ita bai isa ya kwana gurinta ba,saboda kwanan gimbiya ne?,har ta buda qofar zata iskeshi a falon wata zuciyar ta haneta,saita koma da baya ta maida qofar ta rufe. A wannan daren haka kowa cikinsu ya kwana,kowa da irin abinda ke kai kawo a zuciyarsa. *******Tun daga ranar suka koma 'yar haka dashi,sai sa'ar gaske yake iya sanyata a qwayar idanunsa,tuni ta ajjiye girkinta dama komai da komai,iyaka ta gyara bedroom dinta da kanta,idan tana da ra'ayin hira ta kira wanda takeso cikin 'yan uwanta,ummunta anty deena ko anty madeena koma mom dinta,ko kuma ta fice wajen maari susha hirarsu,ita kuma dake mata kallon me qaramin ciki tayita mata dafe dafe na abubuwan gargajiya,wanda da gudu widad din ke ci,don wasu abubuwan ma ta manta dasu sam,ummu ke musu lokaci lokaci a gida dama. Ba wanda ta taba gayawa abinda ke faruwa,don sai taji abun baya ma wani damunta gaba daya,yammaci tana yi dab da zai dawo zata koma dakinta ta kulle. Yadda hafsat take ganin damuwa qarara tattare da abbas din sai hankalinta yayi mugun dagawa,bata taba zaton baka ya damu da yarinyar ya kuma bata muhimmanci mai yawa cikin rayuwarsa ba irin wannan lokacin,ta auna ta auno......taga kaf zamansu bata taba irin wannan sakarcin ya damu da ita haka ko yabi ta kanta ba,hasalima wani lokacin saidai ta bude qofar ta tarar ya koma wajen aikinsa ya ajjiye mata dan note. Kishi sosai ya tasata a gaba,ta daina jin dadin gidan gaba daya,ba zata iya jure ganin soyayya da damuwar abbas akan wata diya mace ba a gaban idanunta tana raye ba,sai ya zamana bata da aiki sai mita da qorafi "Gaba daya qaramar yarinya na neman rikita maka lissafi,totally ka canza abban mimi,ba ita ta zabi haka ba,aiba wansa ya tilastata,saika qyaleta idan ta gaji ta watsar.....banda ma iyayin banza da samun waje,mema akayi mata?" Sai taja qaramin tsaki. A sannan yana shiryawa ne bayan ya fito a wanka,sanda take wannan maganar ma yanata bulayin neman wankakkiyyar singlet da zaisa duka babu,ya watsar dana hannunsa yana duban idanunta "Kin gaza ta abubuwa masu yawa,wannan ya sanya dole nayi kewar kebance kanta da tayi daga wajena,abubuwan da kika kasa ita din duka bata daukesu a komai ba.......ki jiqamin singlets dina da hypo zan wanke da kaina,na gaji da siyan sabbin undies,idan kin gama ki gyara parlor zuwa cikin dakin nan,idan Fresheners dinmu ne suka qare ki gayamin,idan na fita zan shigo da wasu,banason na dawo na samu gidan nan a yadda yake" daga haka ya juya yaci gaba da shiryawa. Turqashi!,ita yake kafawa misali da widad din?,daya kafa mata misali da ita gwara ya buga mata misali da mutuwarta,sai ta rikice masa gaba daya itama,tana ganin bata da wani amfani a wajensa,baya ganin kimarta sam a cewarta,gaba daya saboda yarinya guda daya jal ya rasa walwalarsa ya rasa sukuni,yanata qoqarin shawo kanta tana wahal dashi,ita kuma da take iya bakin qoqarinta a kansa baya gani,bai dauketa da daraja ba. A hankali sai damuwa ta fara yi masa yawa,tako ina ba dadi,widad itace sanyin idaniyarsa,ita ta zamewa rayuwarsa wani bango da zai jingina ya samu relief a duk sanda wani damuwa ta sakoshi gaba,ba damuwar hafsat kadai ba,hatta damuwoyi da matsalolin gurin aiki,don rigimar hafsat ya riga ya saba dasu,to amma a yanzun da suka hadu da juya bayan widad sai abun yayi masa tsauri da yawa,dole ya dauki hutun kwana biyu don ya samu ya gyara komai,bauchin da zasuje ma ya daga tafiyar sai satin gaba,bayason su tafi bauchi a haka,yasan bazai fahimci komai ba har suje su dawo. Ranar farko wuni yayi a parlor din gidan shi da yaran,salla ce kadai take fiddashi,gaba daya zaman yayishi ne a bisa dole,don yadda widad din ke bashi kulawa ta musamman a duk sanda zaiyi wunar musu a gida irin haka bai samu koda quater din wannan daga hafsat ba,saidai ya share ya maida hankali ga yaransa da kuma gyaran bedroom dinsa da hafsat din ta tasamma sauya masa kamanni da halayen baqar qazantarta,ya gama sukayi gyaran parlor tare da yaran,baiko nema sa hannunta ba,saita fake da girki a kitchen. Duk bidirin da akeyi widad din tana jinsu tana daki a kwance abinta,tunda ta fuskanci wunin gidan zaiyi sai taqi yarda ma ta bude qofan bare ya ganta,ta kunna data tayi chart sosai irin wanda ta jima batayi ba,daga baya ta koma youtube ta vidmate ta dauko K dramas da chinese masu yawa na soyayya ta shiga kalla abinta,abinda ya rage mata tsahon wunin sosai. Da mamaki ya kwana,washegari bayan ya tattara su dukka ya kaisu wankin kai,don ya gaji da kallon buyagin kan hafsat din da bata damu ta gyara ba,daga nan yace ayi mata harda manicure and pedicure "Amma dai.....da kudin yaran ka bari a hannuna,sai nayi musu su a gida" ko ta kanta baibi ba ya tashi motar yana cewa "Idan kun gama let me know,zanzo na daukeku" yaja motar abinsa,don tuni ya tura kudin komai ta Account din kamfanin, gurin da widad ke zuwa ne,kuma gyaransu yana da kyau,already yana da details nasu dama saboda yadda ta saba da zuwa wajen duk bayan wani lokaci. A masallaci ya fara tsaiwa yayi sallar azahar sannan ya qaraso da motar cikin gidan. Duk da yasan babu kowa cikin Parlor din amma hakan bai hanashi yin sallama ba,kai tsaye ya doshi dakinta,yana jin cewa yau zaiyi maganinta,murdawa daya ga mamakinsa qofar ta bude,ya tura ya shige,ajiyar zuciya mai tafe da numfashi mai nauyi ya sauke, sassanyan qamshin nan da yayi mugun kewa shi ya fara masa maraba,ko ina na dakin fes dashi yana bada qamshin nan daya cakude ta turarukan jikinta,he missed her badly..... He missed komai da ya shafeta. Ba kowa a dakin sai ya tura qofar toilet din,itama wayam ba kowa,saidai da alama ba'a jima da gama amfani dashi ba,farare qal qal din undies dinta shanye a ciki suna digarda ruwa fari tas da alama sun wanku da kyau,sai qamshi suke fiddawa dasu da toilet din gaba daya. Da baya ya koma yana tunanin ina zata,ya tabbatar ba zata fita daga gidan ba ba tare da ya sani ba,tunani ya fado masa,saiya koma da baya yayi boys quaters. Dai dai sanda tayi rashe rashe abunta a dan qaramin parlor din maari tana cin dumamen tuwo miyar kuka,har tsakiyar kanta takejin dadin tuwon,maari na daga bakin famfo tana dauraye kwanukan da baba mai gadi ya gama cin nasa abincin,suna dan hira kadan kadan taji sallama daga bakin qofa. Sam hankalin widad baikai kai ba,tuwonta kawai take azawa cikinta, maari ta aje kwanon taja mayafi ta leqa,sai taja da baya cikin matuqar girmamawa da jin nauyin abbas ta soma gaidashi,ya amsa mata a mutunce yana tambayarta widad din,tace masa tana ciki "Zaka iya shiga yallabai" ta fada tana rabeshi ta fice a sassan ta wuce sashen hajiya,don dama akwai gyaran da zata mata yau din,gobe ko jibi zasu dawo daga balaguron da sukayi,tayi hakane don ta karanci kamar akwai 'yar matsala ko sabani a tsakaninsu,batason saka baki ne a abinda bai shafeta ba,kuma ba'a yi mata tayin shiga ba. A nutse yake ratsa tsakar gidan nasu har ya isa qofar rumfar tata,idanunsa ya zube a kanta yadda take cin tuwon nata kamar ta samu nama,harma batasan ya iso wajen ba,ya qare mata kallo a nutse,kallon da bai samu yi mata shi ba tsahon sati kusan biyu,ta sake wani mugun cika,hatta da idanuwanta sun qara haske da girma,farinta ya sake daduwa kamar jini zaiyi tsartuwa a jikinta,duk da akwai madaidaicin hijab a jikinta,amma hakan bazai hanaka ganin yadda qirjinta ya cika fam ba,daga inda take zaune kuma baka isa ka nuna ciki a jikinta ba,abun yana mugun daure masa kai,yadda cikin yabi jikinta sosai,kamar bayason a ganshi,ya lumshe idanunsa kishinta yana cikashi,haka ta sake cika amma kullum take baro dakinta tana wuni a nan?,ko waye da waye suka taba kallon masa ita?. Tayi matuqar fusgar hankalinsa,wata kewarta mai zafi ta dinga taso masa,sai ya gaza jurar ci gaba da kallonta,ya tsugunna ya zare takalminsa,sannan ya miqe ya saka kansa rumfar maari,duk da ba haka yaso ba,amma yana jin kamar wani magnet ke jansa zuwa gareta. Sai daya kusa isowa gareta sannan turarensa ya ankarar da ita,tana dagowa idanunsu suka sarqafe waje daya,ta tsame hannunta zata miqe,ya saka dukka wani zafin namansa ya riqeta gam,ya kuma jawota zuwa jikinsa suka zube a wajen,bai tsaya wata wata ba ya hade bakinsu guri guda ya fara sauke mata french kiss mai zafi,wanda ya sanya cikin lokaci kadan jikinsa ya dauki rawa gaba daya,kamar wanda aka watsawa ruwan qanqara a lokacin hunturun sanyi,yayin da bugun zuciyar widad din ya qaru qwarai,har tana jin yadda abinda ke cikinta ya takure ya cure waje daya kamar yasan abinda ke gudana tsakanin mamarsa da abban nasa. Sai da yiwa zuciyarta laga laga,ya luguiguitar da ita,ya kuma sauke duk wani fishi dake maqare a zuciyarta sannan ya saketa yana maida numfashi,abun ya zame musu kamar wani faamin ciwo ne da tayar da tsohuwar soyayya da kewar juna da sukayi na nisantar juna da sukayi tsahon satittikan. Saida bugun zuciyoyinsu suka daidaita sannan ya sauke mata kallonsa da wani irin zazzafan kallo dake saka mutum a shauqi,tayita kauce masa tana jin nauyin yadda ta sake masa jiki haka ba tare data iya kare kanta ba,tabbas ta karbi saqo yadda yakeso,don yaga alamun haka a tattare da ita "Widad...." Ya fada muryarsa a mugun sanyaye,bata iya amsa masa ba,shima kuma bai damu ta amsa din ba ya dora da cewa "Fushi kikeyi dani?......wanne irin fushi ne haka widad?,so kike zuciyata ta buga?" Statement dinsa na qarshe ya sakata dago kai da sauri ta kalleshi,ya samu yadda yakeso,ya kuwa riqe qwayar idanunta da kyau ya hanata motsawa. Fuska ta narke cikin salon shagwabar nan tata da yayi mugu mugun kewa "Ba kai bane ba....." Kawai sai ta fashe masa da kuka,gaba daya ta ida rikitashi "Ya salam" ya fada yana matsowa gareta gaba daya yahau aikin lallashi baji.ba gani,har zuwa sanda zuciyarta tayi sanyi "Pardon me please,I assure you it may not happen again" ya fadi hannayensa hade da juna,shi kansa yana mamakin yadda ya dinga misbehaving nata a lokacin,baisan me ya shiga kansa ba,amma a wannan lokacin sai zuciyarsa ke bashi kawai hafsat keda gaskiya,yasan ya mata abubuwa marasa dadi da yawa wannan shine kusan na biyar ko goma,amma ko a fuska tana qoqarin cinyewa,iyaka ta tura masa baki ya kama bakin yadan ciza shikenan an wuce wajen,a wannan karon ne itama ta gwada masa tata matantakar. Kai ta gyada tana sharar qwalla,sai yakejin kamar tana yankar naman zuciyarsa ne "Don't cry mana,haba babyn uncle,It really hurting me when I see you crying" ya qarashe maganar yana tayata sharar hawayen. Fadan masoya hutu inji hausawa,cikin qanqanin lokaci ya wanke kansa a zuciyarta,daga qarshe dai jawa maari qofar sassanta tayi tabi mijinta. Tun daga parlor ya fara sauke mata dakon lodin soyayyarta daya dauka bashi,ta kuwa sakar masa kanta yayi yadda yakeso da ita,harma fiye da yadda ya zata,saboda sabon karatu data sakeyi wajensu fanna,kuka ya dinga mata saboda gaba daya ya gaza controlling kansa,duniyar da widad ke kaishi a duk sanda yake tare da ita......wata irin duniya ce mai nisan gaske da babu a inda yake nasarar zuwa nan idan bata bangaren widad din ba,'yar gaske ce ta wannan bangaren,mai madaukakiyar baiwa da ni'imar da ita kanta bata gama fuskantarta ba. "Me kuma nayi maka uncle kake kuka?" Ta fada tana tura baki gaba,fuskarta a tsakiyar tafin hannunsa,idanunsa jiqe da lema ya girgiza kai yana murmushi "Komai ma widad,komai ma kinyimin" saita zare ido,ya dora hannunsa saman lips dinsa yana fidda mata fararen mayanyan idanunsa "Shshshs.....ba zaki gane ba ko meye zance miki yanzu, I don't know how to stop my self from crying duk sanda na kasance tare dake,bazan iya misalta dad....." Tasan me zaice,kalmar kuma na masifar bata kunya,hakan yasa tasa tafin hannunta da sauri ta rufe lausasan labbansa tana boye kanta,sai ya dora nasa hannun saman nata yadan ciji tafin hannun nata kadan "Wayyo hannuna" ta fada tana janye hannun cikin shagwaba tare da yarfar dashi gefe,ya lakuce mata hanci "Shagwababbiya kawai" suka saki dariya a tare. Tare sukayi wanka,ta shirya cikin doguwar riga umbrella shape data bude sosai,mayyar dogayen riguna ce ita din,wanda hakan ya taimaka sosai wajen sake sirranta cikin dake jikinta,shi ya taimaka mata ta gyara shimfidar gadon da ya yamutsa,hatta da pillows a qasan gadon ya tsinto mata su,tanata tsokanarsa yasha mur cikin wasa yana basarwa "Duk aike kika jawo". [5/10, 2:11 PM] +234 816 811 4418: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 12 Sam ya manta da batun dauko hafsat daga wajen saloon,yana biye da widad din suna gyara parlor zuwa kitchen wadanda sukayi mugun kewarta,don duk gyaran da hafsat din zatayi bayayin kamar na widad,ya rasa meye dalili. Tayi masa kira ya kusa guda bakwai,ta cika tayi fam,cikin ranta tanata fadin inda waccar sadakar yallan yakai ai bazai manta ba,tilas ta tare musu drop na keke napep ta kawosu gidan. Dai dai sanda suke kitchen shi da ita,yau jin kansa yake fes,bai gane nauyin yadda yayi rashinta ba sai yanzu data dawo da kulawarta a kansa,ko cikin kitchen dinma taso ya zauna falo ne,amma sai ya kalleta sosai yana saka qwayar idanunsa cikin nata "Bazan iya ba.....kinsan yadda nayi missing kallon kyakkyawar fuskar nan?" Ya qarashe maganar yana shafar gefan fuskarta,inda wani kwnataccen baqin gashi mai sulbi ya mamaye wajen,sai murmushi ya subuce mata,ita da Allahnta ne kawai sukasan yadda ta dinga kokawa da zuciyarta a kansa,bata sake sanin yadda ya samu gurbi cikin rayuwarta ba sai a yanzu data sake riqeshi da muhimmanci......sai da su hajiya fanna suke ankarar da ita game da muhimmancin kula da mallakar hankalinsa ta kyakkyawar hanya irin wannan da take kai yanzu. Kusan tare suke aikin,yaqi ya zauna,saidai gaba daya a rikice yake,yayi yayi tabar aikin yau zaima kowa takeaway amma tace dashi cikin narkewa da karyar da wuya a shagwabe "Dole nayi belin kaina na biya bashin abincin da ban ciyar da kai ba" sosai maganarta ta burgeshi,ta kuma samu kyakkyawan gurbi a zuciyarsa,ya sakar mata wani tattausan murmushi,yana jin kamar ya bude qirjinsa ya maidata ciki,bai taba tunani akwai so mai zafi irin wannan ba. Dan qaramin ihu ta saki tana yarfe hannu,ya watsar da lettuce din hannunsa da yake gyarawa ya nufota, hannun ya kama yana dubawa "Taji miki ciwo?" Saita zame hannun a hankali "Ba sosai bane,na tsorata ne" ta fada a shagwabe,kai ya girgiza "No,ban yarda ba gaskiya.....ajjiye muje,na yafe girkin yau" maqale kafada tayi "Su mimi fa?" "Kowa zai qoshi,baki da damuwa" kafin ta ankara ya sanya hannu ya dauketa cak da hannu biyu "Wai wai wai......kilo dinki nawa baby?.....wait......waima......how many months baby na yake yanzu?" Ya tsaya cak yayi maganar cikin rada. Duk sanda zai mata maganar cikin sai kunya ta kamata,musamman idan ta tuna wautar data tafka,da irin wayon daya dinga mata a sannan na cewa sai ansha ruwa an qoshi ake samun ciki. Kanta ta boye a faffadan qirjinsa tana dariya qasa qasa "Bazan gaya maka ba,nima saina rama" dariya suka saki gaba daya a tare sanda suke shigowa parlor din,hakan yayi dai dai da shigowar hafsat ita da yara gaba daya. Mutuwar tsaye tayi,ta tsaya cak tana kallonsu,sanda ya zaunar da ita saman kujera one sitter ya tsugunna gabanta kan gwiwoyinsa hadi da dora kansa saman cinyarta bayan ya kama hannunta yana sake dubawa......sai taji gaba daya kamar rufin sama ne zai rufto a kanta,jakar hannunta data saka pampers na nawwara da sauran tarkace ta silale daga hannunta ta fadi,ta bada dan sauti abinda yaja hankalinsu kenan. Da sauri ya miqe yana nufarta hadi da fadin "Subhanallahi" sai yasa hannunsa ya kama kunnuwansa ya riqe duka biyun yana kuma fadin "Am so sorry......nayi laifi ko?,bansan za'a gama muku da wuri haka ba,me yasa baki kirani ba?" "Wanne irin nau'in kira kakeso nayi maka abbas?, miscall nawa kake buqata daga gareni kafin ka amsa wayata?" Ta jefa masa tambayar tana kallonsa da idanunta da suka fara zubar da ruwan hawaye,tanajin wani zafi a qirjinta kamar zuciyarta zatayi bindiga. Goshinsa ya dafe,shaf ya manta wayar na a silent "Ya salam.....i forget to......." "To what?!,kada kacemin komai,don babu abinda zaka gayamin da zai sakani yarda da kai,kawai ka shirya cimin mutunci ne,oho.....dama shi yasa ka turani gyaran gashi ni da yara don ka samu kebewa da matarka?,me yasa baka gayamin ba?,ai da ban dawo yanzu ba bare naga cin amanar da kuke aikatamin" "Cin amana kuma?" Widad ta fada cike da zallar mamaki, saboda nauyi da kalmar tayi mata,me yasa hafsat din take abu kamar kwancan hauka?, uncle abbas din kwartonta ne ko kuwa?,ita bataga dukka abinda yake faruwa a gidan ba,oh.....hala ma dadi abun ya mata kenan?,shi yasa a jiya fanna keta mata fada kan matakin da ta dauka,tace sam baiyi ba,zata sake nesanta kanta da mijinta ne hadi da kawo kusanci tsakaninsa da hafsat din,ta gani,ta gani kam "Ke ba dake nake ba,kiyimin shuru tun ban cimmaki na lallasaki ba" wani murmushi widad din ta sake,hankali kwance ta girgiza kai "Wuce nan......wuce nan wallahi,me jiya ma tayi ballantana yau?" "Ya isa....ya isa" abbas ya tsaidasu yana daga hannunsa,hafsat dake kallon widad kamar wata sakarya cike da madaukakin mamaki yadda yarinyar ke kallonta kanta tsaye,ba alamun tsoro ko shayi a tattare da ita,ta dauke dubanta daga kan widad ta mayar kan abbas "Kaga abinda ka jawomin ko a wajen diyar cikina?.....shikenan b......burinka......yac.....cika" tana kaiwa qarshe kuka ya kubce mata,sai tayi dakinta da gudu gudu ba tare data dauke jakarta a wajen ba. Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai mimi da nawwara suka shigo da gudunsu hannuwansu dauke da leda babba "Daddy.....kaga abinda abban kaduna ya bamu,yanata sallama bakaji ba,yace zai dawo anjima" idanunsa dauke dauke da damuwa da bacin rai ya bude yana kallon yaran,abban kaduna amini ne ga mahaifinsa,kuma shine a yanzu ya bashi part daya cikin gidan suke zaune,saboda yana kallonsa tamkar dan cikinsa. "Me aka samo mana" widad ta fada cikin qoqarin kawo raha da kawar da bacin ran data fuskanci ya taba zuciyarsa,ta karba ledar ta bude tana biyewa yaran tare da sako abbas din a ciki. Cikin mintuna qalilan tayi nasarar kore masa bacin ransa,shima ya zauna cikinsu ana rabon kayan wasan yara fal leda da chocolates masu yawa daya kawo musu,sai da aka kusa kiran sallah sannan ya nufi daki yace zai daura alwala,su shirya idan ya dawo zasu fita yayi musu takeaway. Murna yaran suka hauyi,nawwara tace baei ta gayama mommy sai mimi ta jawota "Kina gaya mata zata hanamu zuwa,don Allah kada ki gaya mata kawai kiyi Shuru" Tsaf ta shirya cikin gold laffaya data sake fiddata a jinin larabawa sosai,sanda ta fito parlor din narkewa abbas yayi a wajen yana binta da wani kallo mai nauyi,ko nawa ne.....kuma komai yawan kudi bayajin qyashin kashewa ya siya mata wasu kaya daya gani suka burgeshi ko kuma kayan gyara,saboda ya sani,komai ta saka yana dacewa da ita fiye da yadda ya gansu. Yatsunta ta murza saman fuskarsa tana murmushi "Yallabai" murmushin shima ya saki yana gyara tsaiwarsa "Wudd(so,qauna,soyayya mai zafi)" kai ta langabe gefe,tana jin dadin sunan sosai "Ka yima mommyn mimi magana sai mu wuce gaba daya,kada a dauko mata abinda batajin cinsa" "Saidai ke ki kirata" ya amsa mata yana shafa gefan sumar fuskarsa zuwa habarsa,gaba daya ta gana tsumashi,bai taba ganin mutumin da ciki ya boye sosai a jikinsa,ya kuma yi masa mugu mugun kyau ba kamarta. Kafada ta daga,ta kuma taka a hankali ta nufi dakin. A nutse tare da sallama ta tura qofar ta shiga,da sauri hafsat ta daga kanta tana mamakin jin muryar yarinyar cikin dakin,sai data shiga sosai yadda zata ganta da kyau sannan tace "Maman mimi..... uncle yace ki shirya ki samemu a mota,zamu dan fita shan iska" widad tayi maganar cikin wani salo me aji da gayu. Ashar hafsat din ta saki sannan ta miqe tsaye kamar kububuwa "Ga hanya nan ki ficemin daga daki tun baki raina kanki ba,ke har kin isa na shiga rigar alfarmarki don zan fita da mijina,idan kunje kada ku dawo" fuska tadan yamutsa cikin nuna yanayin alhini "Ayyah....me yayi zafi?,Allah ya baki haquri" widad ta fada qaramin murmushi yana qwace mata,wanda hakan ya sake tunzura hafsat, saita tako kamar zata yo kanta,widad din ta juya ta fice abinta. Ta samu duk sun fice daga parlor din babu kowa,don haka ta tsaya taci dariyar da taketa dannewa "Inda ta kamaki da kinci qaniyarki" ta gayawa kanta da kanta tana ganin tsaurin ido da qoqarin da itama tayi dariya na sake qwace mata. Ta jima tsaye tana duban bakin qofar bayan fitar widad din,ta hango soma wanzuwar raini qarara a tsakaninta da yarinyar,banda haka a baya yaushe ma ta isa ta isko falonta indai ba ita tayi kiranta ba sanda ta maisheta ma'aikaciyarta?,balle har ta samu sararin da zata shigo har daki ta gaya mata magana mai kama da jirwaye,saita koma ta zauna tana huci,ta sake tashi tana laluben su mimi,daga bisani ta fahimci dasu akayi tafiyar,domin kuwa ga kayansu nan tun na safe zube a falon,kenan har canjin kaya tayi musu,ta lailayo ashar ita daya ta dura "Zasu ci ubansu ne,gobe ko dakinta akace su kalla ba zasu sake ba" saita koma daki kwanyarta cike fal da tunani, itakam dai banda uwa uwace,da tace anya ummanta tana mata abinda ya dace da dukka iyayen kudaden da take turawa da sunan za'a yi mata aiki irin wanda takeso?. Widad da kanta ta zaba musu wani eatery suka sauka a can,kowa yayi order din abinda ransu yakeso,yau kam mimi kamar tayi me saboda dadi,don sam a gidansu bata saba ganin wannan rayuwar ba,shi kansa abbas din ba qaramin dadi yakeji ba duk sanda ya debo familyn nasa sukayi fita irin wannan,suna cin abincin suna raha a tsakaninsu,bayan sun kammala yayi musu takeaway suka tafi dashi,ya tsaya wani supermarket ya hado musu da sauran kayan qwalam. Tayi zarya daga dakinta zuwa falon bayan fitarsu sau babu adadi,jiran dawowarsu kawai takeyi,suna sallama tana fitowa daga dakin,sanye da wata riga ruwan madara mai dan qaramin hannu daga can saman kafada,a saman rigar ta daura fallen zani. A yadda taga abbas da widad din sun shigo a tare suna dariya ya sake hassalata,tana isa tsakar falon tasa hannu ta janyo mimi ta zuba mata mari "Gidan ubanwa kika tafi?, daga yau idan akace ki sake binta ba zakiyi marmari ba,saikin gayan uban wa ya baki umarnin fita....." Tayi maganar tana sake cakumo yarinyar kamar ta samu babba,ta kuma ware yatsunta zata sake zuba mata masu,abbas ya dakatar da ita a tsawace "Kina dukanta ba zaki sauke hannunki ba zan rama mata,kuma da izinin ubanta mahaifi ta fita" ya amsa mata cikin tsananin fushi shima. Idanunta dake cakude da bacin rai ta daga ta kalleshi "Me ka shawo a waje?,'yata zan hukunta kakemin shamaki?,to wallahi ba wanda a isa ya hanani hukuntata,tunda ba wanda ya haifa min ita" tayi maganar tana sauke kallonta akan widad da takejin inda za'a bata bindiga yanzu,a kuma bata damar kashe mutum guda daya tak a duniya ita zata harbe,bata sauke dubanta ba abbas ya zare yarinyar daga hannunta yana cewa "Idan kina haukarki kiyi ke daya,karki sake kice zaki huce kishin haukarki akan yarinyata,don abun bazaiyi miki kyau ba" sai ya miqata ga widad dake tsaye tana kallon zallar hauka daga wajen mummy hafsat din. Ganin ya miqata ga widad saita zabura "Karki sake ki tabamin 'ya don baki da iko da ita,idan kinji haushi kema ki haifi taki" waiwaya abbas yayi yayi mata alamar su wuce daki abinsu,kwnataccen murmushi ta sake masa a shagwabe "Take it easy sir.....banason ka qare da ciwon kai please" kai ya gyada yana lumshe ido "I Will handle it in sha Allah" saita kama hannun mimi suka wuce dakinta,suna tafiya tana shafa mata wajen tare da lallashinta,akwai qauna sosai tsakaninta da yarinyar,tana son widad din sosai,wannan yasa itama widad din duk cikin 'yan uwanta tafi sonta,uwa uba ma kama da takeyi da uncle abbas dinta. Shihewarsu daki da mimi ya sake hargitsa hafsat din,ta fashe masa da kuka tana masa hauka sosai,widad dake daki batasan ainihin abinda ke faruwa ba,don bata tantance abinda hafsat din ke fada,amma tashin muryarta da hayaniyarta ta tabbatar har harabar gidan ta isa. Batasna ya suka qarke ba,wajen goma da rabi ya shigo dakin,sosai kansa yake sarawa,qasan zuciyarsa yana ambaton sunan Allah,mutum ne da baya qaunar hayaniya ko kadan,ga hafsat kuma wannan din ba komai bane,ya duqa yasa hannu ya dauki mimin "Ka barta uncle ta kwana a nan" kai ya girgiza kadan "No.....i need space,i want to be with you..... only you" jin abinda yace sai bata qara magana ba,bashi ba,ita kanta tasan tayi tsananin kewarsa,tana kuma buqatarsa,ba zata bari kuma haukar hafsat ya bata musu wannan daren ba kamar yadda hajiya sha'awa tasha gaya mata "Akwai hanyoyi da yawa da kishiya zata iya sace miki kwana,bawai saita hanyar dauke miki miji ya kwana a dakinta ba". Ko inda take zaune tana gursheqen kuka bai kalla ba ya kwantar da mimi daketa baccinta saman gadon,ya gyara mata kwanciyar gami da tofeta da addu'a,ya tsaya sosai bisa qafafunsa yana duban qofa "Ko qwarzane na gani da safe a jikinta,wallahi wallahi ki kuka da kanki" daga haka ya fara nufar qofa "Ai da saika barta wajen uwar daka sake mata" Ta amsa masa tana sakin wani kukan baqinciki daga zuciya zuwa maqoshinta. Kamar yadda ta saba bata barshi ya kwana da wani bacin rai ko tunanin hafsat ba gaba daya,ta dauke dukka wani tunani da hankalinsa zuwa wata duniya ta daban,ta sakar masa ragamarta gaba daya,ya fanshe dukka wata gajiya bacin rai da kuma bashin daya dauka a kanta,shi kansa yasan ya bata aiki da yawa,bashi da wani sauran aiki sai lallabarta da tattalata da ya shiga yi tamkar wani sabon qwai. [5/10, 2:11 PM] +234 816 811 4418: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 13 *W A S H E G A R I* K'arfe shida da mintuna na saafiya ya baro masallaci,bayan ya gama 'yan addu'o'insa. Daga bayansa yaji tafiya,kafin ya waiwaya an ambaci sunansa,tuni ya gane muryar sai ya rage tafiyar da yakeyi yaja baya kadan hadi da waiwayawa. Karasowa mutumin yayi fuskarshi qunshe da murmushi ya miqawa abbas din hannu,maimakon ya bashi hannun shima sai ya rusuna yana gaidashi cike da matuqar girmamawa. Kin amsa masa yayi har sai da sukayi musabahan,duk da har yanzu abbas bai miqe tsahonsa ba saboda bashi girma "Ban sani ba ko yara sun gaya maka saqona" yayi murmushi "Eh abba.....sunce kazo zamu gaisa" "Eh.....to ma sha Allah,na sake dawowa amma ban samu ganinka ba dai,mu qarasa gidan,inason magana da kai" tare suka jera da mutumin,suna tafe suna dan taba hirarrakin da suka shafesu,har suka isa cikin gidan. Bayan gaisawa da ma'aikatan gidan,kai tsaye suka wuce setting room dinsa. Sunansa abban ya kira yana duban fuskarsa "Nazo jiya sau biyu kamar yadda na gaya maka,saidai duk zuwan da nayi din na iske rikici ne da hayaniya tana fitowa daga gidan har harabar gidan nan,ya akayi kabar gidanka yake neman zama haka?,me yake faruwa?" Gyara zamansa abbas yayi yana sunkuyar da kansa,abban kamar mahaifi yake a wajensa,babu abinda zai boye masa,don haka ya gaya masa komai. Shuru yayi na wasu mintuna sannan ya sauke ajiyar zuciya "Ba yadda za'a yi ka ajjiye mata biyu a guri irin wannan sannan kayi zaton samun kwanciyar hankali,muddin kanason zaman lafiya saidai ka raba musu muhalli,wannan shine kawai hanya daya da zaka samu dai daito akan irin wannan matsalolin,daya bataga 'yaruwarta ba bare wani abu ya biyo baya" kai abbas yake jinjinawa yayi, masa godiya sosai,lallai shawarar abban tayi masa qwarai,ya kuma bashi mafitar da shi a kansa ma bai kawo hakan ba "Amma.....ita hafsatu meye ya dawo da ita kaduna idan ba zallar neman fitina bama?" Abban ya fada cikin mamaki, saboda fes yasan halinta ya kuma san abinda ya wakana wancan karon,abbas din yayi qasa da kansa,yama rasa wacce irin amsa zai bawa abban,Allah shine masanin gaibu,kuma shi daya yasan yadda yakeji a qirjinsa game da dabi'a da halayyar hafsat din,shi kadai yasan irin haqurin da yakeyi da ita "Kada ka damu,kaci gaba da addu'a,sannan kaci gaba da jajircewa,Allah ya kawo mafita ya shige gaba" Ranar bai fita aiki ba,gaba daya sai yaji bashi da kuzarin fita aikin, widad din ta gama kashe masa jiki da xuciya da soyayyarta,a irin abinda take masan,yaso ace gidan nasu kamar daa ne sanda suke daga shi sai ita. Rashin fitarsa aiki ya sake harzuqa hafsat din qwarai,ta sake birkicewa sanda ya fiddo kaf kayansa dake dakin widad da wanda yake dakinta,ya kuma raba komai yace kowacce ta dauka,ranar kamar zata ara hauka "Wallahi na yarda.......yarinyar nan mallaka da asiri takeyi mai matuqar qarfin da yafi nawa" hankalinta ya tashi sosai,tana ganin abubuwan kamar suna fin na baya lalacewa da jagwalewa,ta rasa inda zata tsoma ranta ranar taji dadi,tanason tayi waya kuma tana shakkar kada ya shigo ko wani ya jita,dole ta dinga hadiyar bacin ranta ita kadai zuciyarta kamar zata fashe. To tun daga ranar abbas din ya fara neman wani gidan ba tare da sanin kowa a cikinsu ba,satin gaba kuma da zasuje bauchi hutu,zuwansu na farko bayan tahowarsu dukka gaba daya kaduna. Daren da suka isa da qyar widad takai safiya cikin gidan,saboda wani birkicewa da tayi,an dasa ma zuciyarta wani mummunan tsoron gidan,kwanan zaune tayi tana rusa kuka,tana jin kamar ta fita da gudu tanar cikin gidan,wani irin qunci ne ya cika mata qirji,tana jinta kamar wadda aka jefa cikin dokar daji ita daya. Sosai hankalin abbas ya tashi lokacin da ya biyo da asuba dubata ya sameta firgai firgai,tana ganinsa ta fada jikinsa ta saki kuka,tambayar duniya me yake faruwa ta gaza yi masa bayani,abu daya dai take fada "Banason gidan nan uncle don Allah,ka kaini wajen hajiya ko gidansu nujood" ko fita a part din ta hanashi,bata wani damu da jarabar hafsat da zata iya biyo baya ba saboda zamansa a part din nata ranar kwananta,haka shima abbas din,ba wannan bane damuwarsa,abinda ya sauya widad din yasa ta firgice haka ke bashi mamaki,bayan yasan lafiya qalau suka baro kaduna. Ko part din bai bari ba ya sanyata ta shiga toilet tayi wanka,wankan ma da da tace tayi idan sunje gidansu nujood yace aah,kafin ta fito ya shirya mata jakarta da kansa,ta fito ta shirya agurguje kamar wadda ake jira suka fito ya kulle mata sashen da kansa,yanata binta da kallo cike da mamakin abinda yake damunta. Sai data shiga motar sannan yace mata yana zuwa,ya juya zuwa sashen hafsat. Da sauri ta bar bakin window din,ta koma saman dining tana ci gaba da gyara kwanukan data zuba akai,duk da ba wani abun kirki ta dafa ba,a cewarta ta gaji,ba zata iya wani dogon aikin abincin safe ba. Amsa sallamarsa tayi kamar bataga komai ba,ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo, already ya saba ba kasafai yake gaidashi da safe ba,wani lokacin yayi mata gyara wani lokacin ya watsar da ita "Zan kai widad gidan muhsin kada ki jini shuru" "A dawo lafiya" ta amsa masa ba tare data dubeshi ba hankali kuma kwance,tana jin wani dadi yana ratsata,sai ya shafa kan yusra dake kwance cikin kujera sannan ya juya ya fice. Yana fita taja wani mugun tsaki sannan ta saki dariya "Habaaaaa yarinya,ki hanani sakewa a can a nan ma ki hanani?,Allah ya raka taki gona,da ikon Allah ma kin fita kenan ba zaki sake dawowa ba" ta sake rufe zancan nata da tsaki,tabar aikin da takeyi din ta koma saman kujerar tana karkada qafa,a duniya ita daya tasan yadda yarinyar tayi mata karen tsaye a rayuwa,duk yadda takai ga zuba iskancinta bata taba fuskantar matsala irin wannan daga wajen abbas ba sai yanzu,ta sake jan wani tsakin "In sha Allahu sai nayi maganinki,bazan gaji ba wallahi" ta fadi a fili kamar ita da wani suke magana. Kamar cirar qaya haka taji bayan fitarsu daga gidan,sai taji komai yana raguwa cikin kanta, nutsuwarta tana dawo mata a hankali a hankali. Sanda suka isa gidan ta shiga ciki mamaki ne ya kama hajjaa,koda ta tambayeta lafiya?,ce mata tayi ba komai,kawai ta gaji da zaman gidanne. Cikin mintuna qalilan ta sake sosai kamar ba ita ba,zuwanta ya yiwa yaran gidan duka dadi,ta ware sosai abinta,har zuwa sanda abbas dake setting room sunata hira da uncle muhsin,irin hirar da suka jima basuyi irinta ba ya tashi tafiya,ta miqe ta yafa mayafin abayarta ta fice don suyi sallama. Idanunsa qur bisa qofar,kamar daman jiran isowarta yakeyi,ta yaye labulen ta shigo a hankali,saiya miqa mata hannunsa,ta kama a hankali ya jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinyarsa. Hannusa guda daya ya dora saman cikinta,kamar yasan me akayi yayi wani zillo,tadan motsa da sauri tana zare ido,don har yau ta kasa sabawa da irin wannan motsin,abbas da yaga irin yadda ta motsa sai ya saki murmushi "Kin gani ko?,shi kansa yana cewa zaiyi kewar babansa,amma mamansa kamar bata damu ba" ya qarashe maganar yana langabe mata kai kamar wani maraya me neman agaji. Yadda yayi din ya bata dariya,tadan saki siririyar dariyar data bayyanar da fararen haqoranta dake burge abbas sosai,ta saka hanuwanta duka biyu ta riqe kansa cikin tafukan nata tana dubansa "Mamansa zatayi kewarka fiye da yadda shi zaiyi......" "Amma me yasa kika zabi kibar gidan?,kinsan yadda nakeji duk lokacin da na juya cikin gidan naga babu ke a cikinsa?,widad.....duk gidan da babu ke a cikinsa shida kango daya suke a wajena. ,inji a zuciyata kina gidana wata babbar rahama ce a wajena,kallonki yana bani dukkan nutsuwa da zuciya da ruhi suke buqata.....ban taba kasancewa tare dake ba.....koda wata mu'amala bata shiga tsakanina dake baba tare dana samu nutsuwa ba" yadda yake tsara mata kalaman da yadda yake karanta mata su cikin kunnuwanta sai suka kashe mata jiki,ta matsa a hankali ta kwantar da kanta saman kafadarsa tana rufe idanunta gami da jin yadda bugun zuciyarta ya bugawa a nutse,irin bugun da bata samu irinsa ba daren jiya. Ita kadai tasan irin yadda take fighting da wani mugun tsoro..... tsoro irin wanda bata taba jin irinsa ba..... qunci da damuwa da wata irin qaguwa na tabar gidan,ta matsa a wajen,tana jin kamar tana taka qayoyi a qafafunta duk sanda take taka kowanne sashe na gidanta,amma batasan ya zata gaya masa ba,ya zatayi masa bayani,tunda ita daya takejin hakan,ta sani tana addu'a kuma tana samun sauqi lokaci lokaci. Sun jima a haka suna shan dumin jikin juna,kafin ya dagata yana duban fuskarta "Gobe ne kwananki,zanzo na daukeki,babu cin bashi" narke masa tayi,ya dora yatsantsa saman labbansa "I will bring you back,right?" Murmushi ta sakar masa sannan ta gyada kanta,tashin hankalinta dama yace zata ci gaba da zama har zuwa sanda zasu koma Kaduna. Kwana daya tak tayi yazo ya dauki abarsa,hajja nata tsokanarsa ko surukuta babu?,bai amsa ta ba illa binta da yayi da miskilin murmushinsa. Hafsat ta sake sosai ganin widad bata gidan,hankalinta kwancw tana ganin zata ci gaba da riqe abbas muddin suna bauchi saidai idan sun koma kaduna,a can dinma tunaninta ya fara karkata.....me zai hana tayi wani abu a kaine kwatankwacin abinda ke wakana yanzu?. Sosai shawarar ta zauna mata cikin kai,don a yanzun da take zaune ita daya cikin gidan sai takejin kamar bata da sauran matsala a duniya. Ba qaramin kaduwa tayi ba lokacin da ta fara jiyo qamshi na fita daga part din widad din,qamshin turaren wuta da na abinci duka lokaci guda,sam sam batasan sun shigo gidan ba,daga ita har abbas din,zuciyarta tayi wani irin nauyi,mamaki ya kusan kasheta "Wannan wacce irin musiba ce" ta furta a fili kamar zata zunduma ihu,duk ta inda take hangen nasara sai alamun nasarar sun fara bayyana kansu sai komai ya rushe. Kasa jurewa tayi ta aika yaran su gano mata abbansu yana nan,baya nan din don tunda ya ajjiyeta ya fita yace zaije ya dawo,saidai sun dawo mata da tsarabar lafiyayyen samosa da yaji nama carrot dankali da wadatacciyar albasa. Samosan yana daya daga cikin abinda take mugun so,qyuya son jiki da rashin maida hankali a koyi girki yasa bata iya ba,duk da suna da komai na amfani a gidan da zata iya yi da kanta,sa'annan son kudi da son abun duniya kuma baya barinta ta siya a wani waje,saidai idan anci sa'a ta fita wani gurin sha'ani ta samu a can taci. Duk sonta dashi yau din quncin zuciya da kuma tsanar widad din ya hanata ci,duk da yawan wanda ta bawa yaran,suka sanya abinsu a gaba suka cinyeshi tas suka sha ruwa,duk sai suka hau bacci. [5/10, 2:11 PM] +234 816 811 4418: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *UCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 14 Tun daga ranar sai ya zamana duk sanda sukazo kadunan gidan hajja take sauka abinta,don a yanzun ta yiwa gidan hajiya qaura,mugun kunyarta takeji saboda cikin da yake jikinta,ranar da hajiyan tayi mata addu'ar Allah ya raba lafiya kamar zata mace a wajen saboda kunya,taso qwarai ma ya dinga barinta kaduna,amma yaqi,saboda hajiyan nayin fada duk sanda yazo babu ita,bugu da qari shi kansa bazai iya wadan nan kwanakin tana wani gari yana wani ba,a haka rayuwar taci gaba da juyawa,har suka share watanni uku,mugun nufin hafsat din bai cimma gaci ba yadda takeso take kuma tsarama ranta,saidai a wasu abubuwan da dama ubangiji kan yiwa bawansa talala ya barshi da zabinsa. *_B A Y A N W A T A U K U_* Sanye take da wata farar gown ta wani cotton material dake da wani irin ado mai qyalli na golden din zare,ta bude sosai daga qasan rigar,hade take da mayafinta mai dan yalwa,tana tsaye gaba madubin dakin nujood tana shafawa fuskarta farar powder,nujood din na saman gadonta daga bayan widad din,hannunta dauke da littafin da widad din ke karantawa,tana tsaka da karatun abbas yayi kiranta kan cewa zai shigo. Yadda widad din keta qalqale jikinta yasa nujood ta kasa yin shuru "Ni banga amfanin wannan qaqale qaqalen da kiketa yi ba,just yaushe kikayi wanka ma?,wannan skin din naki da baya riqe dauda kwata kwata?,a wannan kyan da cikinki ya sakaki kikayi indai baso kike ki matso muninki ba don Allah kibar face dinki haka" murmushi ya qwacewa widad din ta juyo tana kallonta "Uncle abbas ne fa zaizo,ke waya gaya miki ana wasa da lokuttan da za'a kebe da miji,kin mance kishiya gareni?" Dariya sosai nujood ta kece da ita sai itama widad din ta saki dariyar,ta tashi ta zauna sosai saman gadon "Ni wanna kishiyar taki ita da zero duk daya,kinsan Allah tun bankai haka wayo ba nake tunanin uncle abbas me aji,dan gayu wanda bai rasa komai ba.....me ya gani a tattare da wannan wai?,wai kinsan tun asalinta qazama ce?,da sallah abba yayi yayi muje gidan uncle abbas muqi,ya rasa dalili in gaya miki,baisan idan munje wuni muke da yunwa ba,bata iya dafa mana abinci saidai ta hadamu da kayan tarkace,ci banza ci wofi,ga uban wanke wanke da wankin undies da zata hadaka dashi" sauke hannuwanta data goya widad tayi tana jinjina kai,qazantar hafsat din ita kanta tana matuqar daure mata kai,harta kama jikinta,don ko kumbarta ka kalla kasan akwai burbushin qazanta a tattare da ita "Allah ya kawo mata sauqi" "Ai wannan ba zata daina ba har ta mutu" "Banason wulaqanci,mamar yaran masoyina ne fa" widad ta fada tana jifan nujood da hararar wasa,saita fidda ido "Wai yaushe kika zama rasa kunya ne?,komai naki uncle abbas,baki da aiki sai maganarsa?" Fararen idanunta ta juya kafin ta saukesu akan nujood "Kin manta shine rayuwata?,a kansa na fara sanin soyayya qauna kulawa da tattali,a kansa na fara sanin rayuwa, ga kuma d'a ko 'yarsa a jikina" baki sosai nujood ta kama tana gwalalo ido "Na shigesu,widad yanzu kinfi qarfina,Allah yasa dai nima gab nake da auren nan bare ki sani a uku" dariya suka sake qyalqyalewa da ita "Wai nikam......mamar mimi tasan da cikin nan?,banji har yanzu ta nuna kowanne reaction ba" baki widad ta tabe,har zuciyarta bata qaunar zancan matar,ita a yanzun ta mijinta kawai takeyi "Idan nace miki muna iya sati daya bamu hadu ba zaki yarda?" "Haba dai?" Juyawa widad tayi tana zizarawa idonta kwalli "Bata da aji gaba daya matar,da farko kallon mamata ma nakeyi mata,bana iya.musu ko qanqani da ita,ta cutar dani taso gurgunta rayuwata ta hanyar yin amfani da quruciyata,to a yanzun kuma meye yayi saura tsakanina da ita,ina kishin uncle sosai,shi yasa bana hada inuwa daya da ita,har muzo bauchi mu gama zamanmu bama sake haduwa sai a mota idan zamu koma,to me zai hada ni d........" Maganarta ta katse sanda kira ya shigo wayarta,ta duba fuskar wayar tana murmushi "Uncle dina ya iso....."kafin ta daga wayar kiran ya katse,dai dai nan hajjaaa ta turo qofa tana gaya mata tayi ta fito ga uncle abbas dincan a setting room "Saina dawo" ta fada rana zira wani plate white shoes na fata daya dace da qafarta "Allah ya kiyaye hanya Juliet matar romeo" "Babanki ne dai" ta amsawa nujood ta fice tana dariya,itama dariyar ta saki tana bin widad din da kallo,gaba daya rayuwarta da uncle abbas din burge nujood take,wata qauna da soyayya yake bata irin wadda bata iya boyuwa,duk inda kayi musu kallon farko zuwa.na biyu zaka fahimci hakan "Ashe dama uncle din nan dan duniya ne" ta fada qasa qasa a fili tana dariya, saboda ta tuna sanda yake zuwa gidansu,tsakaninsu dashi gaisuwa,sai qarancin fara'a da kuma tsare gida da yake dashi,amma fa duk da haka dama can din shi mai kirki ne da yawan kyauta. A nutse tayi masa sallama da sassanyar muryarta wadda ta tanadeta musamman sabodashi,kasa amsa sallamar yayi,saima ya miqe tsaye cak yana jiran isowarta. Hannuwansa ya bata duka biyun,ya kuma jawota zuwa jikinsa yayi mata kyakkyawan masauki,ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi yana tura kansa cikin mayafinta da kyau,tare da shaqar daddadan qamshin da take fiddawa. Ya jima a haka shi da ita suna jin dumin jikin junansu,kwana biyu tal amma yana jin kamar ya shekara ba tare da ita bane "Ka zauna uncle" tayi qarfin halin fada,saiya dago fuskarsa ya hade da tata "I missed you har bansan yadda zan kwatanta miki ba" "I missed you too uncle" ta fada tana qanqameshi sosai,sai ya saki murmushi tare da ajiyar Zuciya gaba daya,yana jin dadin yadda kullum widad din ke sake zama cikakkiyar mace data karanci abinda yafiso da wanda bayaso,tamkar yana mata sharinga wani part na qwaqwalwarsa ne. Ita ya fara zaunarwa sannan ya zauna a gabanta,ya dauko dukka qafafunta ya dora saman cinyoyinsa yana matsawa a hankali hadi da sauke mata wani narkakken kallo kamar zai cinyeta. Kusan ta saba da irin wannan yanayin,duk da yana azama zuciyarta wani sabon naiyi ne,amma ko tace ya koma saman kujera ya zauna bazai zauna ba,yakance yana matuqar jin dadin hakan,duk da tana zaune sai data rusuna da dukkan girmamawa tace "Barka da yamma yallabai" "Barka kadai yallabiya maman biyu" saita zaro ido "Uncle.....kanason na mutu ko?" Kai ya girgiza da sauri "No.....idan kika mutu babynuncle......na tabbatar a ranar nima zan biki,just kawai ina sha'awar twince dinne,amma tunda bakiso shikenan" ya fada yana dariya cikin ransa,ta wani bata fuska kamar shine mai bayarwa ko kuma yace lallai twince din zata haifa. "Ya bakaso dasu mimi ba?" Ta sake tambayarsa "Ban qarasa gida ba,daga sokoto direct nan nayo.....ba zama ma zanyi ba,ki koma ki dauko abinda zaki dauko mu wuce gida" fuska ta narke masa sosai tana kallonsa "But uncle.....a wajen mummyn mimi ya kamata ka sauka,kuma ma ka manta.....gobe fa na gaya maka zasu wuce kano anty madeena ta haihu,inason na bisu,i missed ummu alort,nayi missing kowa,abba na....su Aarifa da kowa" "I know.....i know,bance kuma ba zakije ba,amma ina buqatar ki cike ragowar kwananki,kwana daya nayi miki aka kirani sokoto,kin tuna?" Baki ta turo masa gaba,a kwanakin gaba daya ciwon mara ne yake damunta,abunka da rashin kan gado fa rashin sanin makama irin na masu haihuwar fari saitake ganin duka takurarsa ne ya jawo mata,don kamar wanda aka qarawa qaimi a kanta,baya iya daga mata qafa a dukka kwanaki biyun da zaiyi a wajenta,shi kansa yasan tabbas tana qoqari,wannan ya qara mata matuqar kima da martaba mai tarin yawa a idanunsa,abinda wadda ta linka shekarunta ta gaza qanqanuwa da ita tana iyayi,kai bama ita ba,hatta da muhsin yanzun ganin girmansa yake qwarai da gaske "Uncle a daina tuna baya fa" "Wannan tuna bayan ya zama dole ai" ya fada yana lumshe ido,yana zagaye lips dinta da suka dan qara tudu kadan da yatsun hannunsa "Nidai nidai" "Baki zuwa?,sai naje na kaima mummyn mimi kwanan naki" ya dauka zatace bata yarda ba,don ya gama sallamawa kan yadda take kishinsa,saidai kishi ne irin na hankali da sanin ya kamata,wanda zakayi zaton wasu shekaru gareta masu yawa,amma sai yaji yace ta yarda. Kicin kicin kuwa yayi,ya kasa ya tsare yace ta shiga ta fito yana jiranta,cikin sa'a Allah ya jefo da uncle muhsin,ya goya masa baya ya tayashi koro qaryarta,harda guzurin "Kada ka yarda gobenma ta wahalar dakai,zasu biyo ta nan gidan su dauketa basai tazo ba". A mota ta dinga masa fishi,bai damu ba ya biye mata kawai,ya yita yawo da ita ya cikata da qwalaman kayan toshiyar baki,bakin kuw aya tosu,ta tasa kayanta a gaba ta dinga ci,saidai a yau din bata wani ci da yawa ba taji ta qoshi. Yau dinma bayan widad din kawai hafsat din ta gani sanda shiga sashenta,mugun kishin da takeji a ranta ba kasafai ma yake barinta take iya mata wani kallo mai tsaho ba,don duk sanda tace zata zurafafa kallonta zuciya na ingizata ta aiwatar da abubuwa masu yawa,wanda ta tabbatar muddin ta aikata hakan sakamakon bazai mata kyau ba,takanji kamar ta samu wani ruwan guba da zai bata mata fuska ta watsa mata,ko tayita dukanta har dai ta galabaitar da ita,ko kuma ta shaqeta har sai ta daina motsi "Baqar matsiyaciya" ta fada a ranta,tana sake jin qwarin gwiwar ci gaba da jarraba sa'arta akan widad din har sai sanda ta cimma nasara. K'arfe sha biyu na rana suka sauka garin kano,cikin gidansu,gidan dake da tsohon tarihin a wajen widad,gidan da tayi wata rayuwa ta gata shagwaba da sangarta,batasan me kalmar matsala ke nufi ba,batasan bacin rai ko damuwa ba,a lokacin ko baka sonta bata jin zafin abun saboda zallar quruciya da rashin damuwa da ire iren wadan nan abubuwan. Duk yadda zuciyarta ke matuqar dauki da son ganin ummunta amma qafafunta da suka dan tasa saboda zaman mota sunqi bata dama,tana hanya kafin ta qarasa su nujood suka dinga wuceta suna mata dariyar sai sun rigata ganin ummu,ta kuwa kebe baki shagwabar ta motsa,hannunta riqe da bayanta dake dan motsa mata lokaci lokaci ta isa falon ummun,dai dai sanda nujood ke dariyar "Saida kowa ya gama gane miki ita sannan kika iso" tureta gefe ummu tayi ta miqe tana cewa "Ba wanda ya rigata gani na,ni na fara ganinta,kuma itama ni ta fara gani" sai widad din tayi qaramar dariya tana jefawa nujood harara hadi da cewa "Munafuki dai baiji dadin halinsa ba wallahi" ta fada jikin ummunta,ummu ta riqeta da kyau,farinciki ya cika zuciyarta gaba daya,widad dinta kullum girma takeyi,kullum kuma alamu suna nuna soyayyar mijinta a jikinta,ta zama wata babbar mace kamar ba ita ba,idan ka ganta zaka musanta shekarunta,ga kuma albarkar aure a tattare da ita,duk da batasan watanninsa ba amma tasan dai ya fara mata nauyi,Allah zai cika mata burinta na ganin dan widad a duniya?,saita share hawayenta cikin dabara ta zaunar da widad din a nutse tana fadin "Me yasa kikayi tafiyar mota ga qafafunki nan sun tasa" "Bazan iya jurewa ba ummu,a taho kano a barni?" Saita girgiza kai tana dariya,kai itama ummun ta girgiza "Ki shiga ciki to ki fidda kayan nan,ki watsa ruwa sai a dumama miki qafar ki shafa man zafi,kici abinci saiki kwanta ki huta" "Duk ita kadai ummu?" Aafiya dake shigowa ta fada,cikin madaukakin farinciki suka rungume juna ita da widad "Wai ashe dai da gaske mun kusa zama iyaye" ta fadi tana kallon cikin widad da wahalar tafiya tasa a yau din ya fito sosai,kamar damar ranar yake jira,kamar jira yake su shigo kano din. Da sauri ta kwabi Aafiya, saboda ita har ga Allah kunya takeji idan akace ciki ne da ita,sai taji kamar ta nutse "Ba abinda ummu fa zata miki,tafi kowa ma murna,randa aka gaya mata ko abincin kirki kasa ci tayi" ta fada tana sheqa dariya,don dukkansu sunsan danbarwar boye cikin data dinga yi,sai suka sanya dariya gaba daya qasa qasa. To wanka da hutu dai baiyiwu wajen widad ba,don gidan nasu cike yake da baqi kasancewar jibi sunan yarinyar da anty madeena ta haifa,baqi anata shigowa,yan uwa da abokan arzuqi gidan a cike yake,wannan ya shigo wannan ya fita,anata hirar yaushe gamo,sai widad din take jin ranta fes,kamar bata da sauran matsala,hatta da wayarta ta mantata a jaka gaba daya. Jin hajjaa zata fita ziyarce ziyarce danginta da nasu uncle muhsin din sai widad din tace zatace,ummu ta kasa ta tsare tace ba inda zata fita,ta marairaice mata da kyau "Don Allah ummu ki barni naje,yaushe rabona da kano,koda zamuje aikin hajji kwana nawa duka nayi,da muka dawo kuma ko gidan nan uncle bai barni na shigo ba muka wuce bauchi" "Ki barta taje ummu,ta dan tattaka ma,tunda acan nasan ba wani waje kike zuwa ba" anty halima dake wajen ta roqar mata ummun. Yawo sukayi sosai harda tafiyar qafa,kafin su dawo kuwa jikinta ya soma gaya mata,a ciwon mara da bayanta ya sake qaruwa time to time,a haka take cinyewa ganin idan ya motsa yana daukan wasu mintuna masu tsaho sai basake motsa mata ba. Basu suka dawo ba sai ana gab da sallar magariba,kai tsaye ta wuce dakin da ummu tasa aka gyara mata ta fidda kayan jikinta tayi wanka da ruwa me mugun dumi wanda mutuniyarta latifa ta hada mata. Tana fitowa daure da towel taji marar tata ta sake riqewa da kyau,saita lallaba ta zauna gefan gado tana cije lebe har zuwa sanda ya lafa mata,ta yunqura zata miqe don ta shirya ta sake ficewa, hankalinta yayi gaba saboda sautin hirarraki da take jiyowa daga falon ummu sai taji ringing din wayarta,ta dafe baki tana mamakin yadda yau wuni sur ta manta da wayarta,suna gama waya da mommynta kiran abbas ya shigo,tunda sukayi sallama ta maidata jakar,tasa hannu ta dauko jakar da aka aje mata saman pillow wanda duka tasan aikin latifarta ne,ta buda ta ciro wayar. Ido ta zazzaro ganin tarin miscall din abbas kusan guda ashirin,ta bude pattern din tana yunqurin kiransa sai gashi ya sake kira. Ajiyar zuciya ya fara sauke mata kafin yayi mata sallama,ta amsa tana jin kewarsa a take tana saukar mata "Kin dagamin hankali sosai,banda yanzun muka gama waya da naadir ya tabbatarmin lafiya da tuni na kamo hanyar kano" ido ta zaro cike da mamaki "Uncle?,da gaske?,kano fa kace?,don kawai ban daga wayarka ba?" Murmushi ya fidda mai sauti,ko yaya zaiyi mata bayanin girman matsayinta a idonsa ba lallai ta gane ba,saidai kwanyarta ta dauki iya abinda zata dauka "Wudd..." Ya kirata da sunan da kaf duniya shi daya yake kiranta dashi,ta amsa masa a tausashe "Matata fa.....da yarona ne suke neman bacemin,yaya zan saka wasa?" Dariya ta subuce mata mara sauti,saita jinjina kai "Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana" "Inason hakan musamman ya zamana tare dake zamu mori lafiyar da kuma nisan kwanan" kunya tadan kamata,yadda uncle din yake mata kamar baya tuna cewa ya ninkata a shekaru,ita din sa'ar 'yar abokinsa ce,ba ruwansa da wanann,kwata kwata baya iya boye mata soyayyar da yake mata. Wata irin hira mai sanyi sukeyi shi da ita,sau uku latifa na leqota taga waya takeyi saita koma,basu rabu ba har sai da mararta ta tsikareta tace "Wayyo Allah" cikin matuqar kulawa yake tambayarta lafiya,data gaya amsa yace ta ajjiye wayar taje taci abinci ta kwanta ta huta sosai,gobe sur yakeso ta yini a gida kada ta sake fita,shima a goben tun asuba zai fita shida Samuel zasu sokoto,tayi masa kyakkyawar addu'ar nan tata dake qara masa qwarin gwiwa sannan suka rabu. Doguwar rigar da tasan ba zata takura ba ta sanya,ta zura hula ta sakawa qafarta socks sannan ta fito.[5/11, 12:23 PM] +234 802 297 0646: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 15 Parlor din kuwa cike yake da surukan ummu da jikokinta,saboda wasu a nan zasu kwana sai ranar suna ko washegari zasu tafi,duka kowa baida matsalar wajen da zai sauka,don gidan nasu badai girma da yalwar masaukin baqi ba. Cikinsu ta zauna latifa ta kawo mata abinci akaci gaba da hira da ita,bataci mai yawa ba ta ture tana yatsina fuska,don ciwon mara da bayan kamar ma yafi na baya. Ummu dake ankare da ita tace "Lafiya?,mene?" "Baya na ne yaketa ciwo ummu" "Ehaan,kaji ba,shi yasa nace kiyi zamanki kika qi,saiki tashi ki shirya bari a yiwa wani cikin yaran nan magana ya dauko mota kuje asibiti" kai ta girgiza "Aah,kawai a bani man zafi na shafa har qafafuwana ma" "Basai taje asibiti sun jagulata ba ummu,tunda naga cikin kamar bai isa haihuwa ba ai,a bata.man ta shafa,zai ware,idan bai ware bama sai suje" anty halima ta fada cikin kulawa. Ummu da kanta ta shafa mata ta kuma tasata a gaba kan ta wuce daki ta kwanta ta huta hakanan,a hadu gobe,tunda hirar tasu bata qarewa,dole badon taso ba ta wuce dakin tayi musu sallama,su kuma suka rakata da sannu. To abu kamar wasa maimakon ciwo yayi baya sai yake qara gaba,tun tana daurewa daga kwance harta miqe ta zauna sosai,kafin wani lokaci mararta ta dauka itama,ta hada gumi sharkaf duk da ac din dake aiki a dakin. Cikin ikon Allah ummu ta leqa dakin da kanta ganin nujood da zasu kwana dakin tare bata gama tata hirar ba bare ta shiga,da sauri ummu ta qaraso tana mata sannu "Bayan ne?" "Harda marata ummu" ta fadi muryarta na karyewa tana dafe da marar saboda wani irin ciwo da take mata. Daga nan inda take bata matsa ba ta fara qwalawa latifa kira,kiran da yaja hankalinsu anty halima suka shigo. "Amma fa kamar mai naquda,kuma cikin kamar baiyi girman da zata haihu ba" Mmn muhassana matar uncle dinta ta fada "Shine nima abinda na gani,inaga ki shirya keda halima ku bita,kome mene zasu fada,Allah ya sawwaqe" ummu ta fadi tana dafe da widad din,kamar ta cire ciwon daga jikinta,ba jimawa naadir yace ya fidda motar,anty madeena na riqe da ita suka fice kowa na mata sannu. Babban private hospital ne daya hada qwararrun ma'aikata a cikinsa,kai tsaye sukayi amfani da file din mommyn muhassana tunda a nan suke ganin likita,kuma family file ne dasu,aka turata labor room bayan sun gama nata gwaje gwaje da tambayoyi. Idanu ta dinga rarrabawa sanda sukayi maganar ta cire pant dinta,bata fahimci me za'a yi ba,ta cire ta tsaya suka buqaci ta kwanta ta kuma bude su gwadata. Qwalla ta dinga yi sosai,ga zafin ciwon mara dana baya ga kuma budetan da nurses sukayi "Labor kikeyi,kuma nan da asuba zuwa wayewar gari zaki iya haihuwa,don yanzun haka kinkai 4cm" abinda suka gaya mata kenan,abinda ta gayawa su anty halima. Mamaki sosai suka dinga yi,don duk kowa kallon cikin suke baifi watanni biyar ba,tunda bai fito ba sosai,ba jimawa suka bata gado da daki,anty madeena kuma tayi waya gida ta gayawa su ummu,nan da nan saiga 'yan gidan sun fara zarya zuwa,itakam widad batasan ma me akeyi ba,don tana labor room private room da aka bata,basu sukabar asibitin ba sai sha biyu na dare,aka bar anty halima da anty deena. *_A R U B U C E T A K E_* K'arfe takwas na safiyar ranar Allah ya bawa widad ikon haifo santalelen d'a namiji mai kama da abbas SAK!,tamkar yayi kakin yaron ya ajjiye,ko kuma photocopy dinsa akayi yana yaro aka ajjiye,wannan kusan itace kalmar da kowa yaga yaron ke fada "Tabdi,wai don Allah a wanne waje wannan yaron yaje ya boye kansa?" Tambayar da anty haleema ta yiwa mommyn muhassana kenan "Kin rigani ne a fili,na rigaki a zuci halima,ciki a ido dan qarami amma yaro tubarkalla ma sha Allah?,wacce addu'a kikeyi ne widad?" Widad dake jingine da jikin gado idanunta a lumshe murmushi kawai ta saki cikin jin nauyi,babu abinda take tunawa sai iein gwagwarmayar da tasha,wai dama hakan kowacce mace keji a sanda tazo haihuwa?,amma duk da hakan duniya cike take da 'ya'ya?. A safiyar ranar asibitin yayi wata irin cika da 'yan uwa da abokan arziqi,duk wanda ke asibitin a ranar ya fahimci lallai haihuwa ce me kima da daraja aka yiwa wannan family,bata wani jima ba suka sallameta bayan sun tabbatar da komai nata lafiya. Ita a cikin jikinta take jin wani banbarakwai,idan ta dubi kyakkyawan jaririn mai fuskar uncle abbas dinta taga wai a yanzun danta ne itama,mallakinta. *A B B A S* Yana tsaye sakiyar parlor din yana saka links din hannun rigarsa,yanayi yana duba agogo gami da dubansu mimi da nawwara da suka sanya yusra a gaba suna mata wasa,su a lallai ga manyan yayye. Lokaci lokaci yana kallon qofar kitchen dinta,ya danja tsaki yana yarfe hannuwa,shikam gaba daya yayi dana sanin sanyata aikin ma,da yasan haka zata jawo masa yayi late da da kansa zai shiga ya hada breakfast dinsa yadda ya saba wasu lokutan,ta sani fa yau din zaiyi tafiyar,amma ta kwanta tana bacci abinta babu abinda ya dameta har sai da ya tasheta, just ruwan baqin shayi da soyayyen qwai amma ya gagara ta kammala masa,a lokacin widad ke ransa,yaji wata muguwar kewarta ta saukar masa,sai yake tunanin zaiyi wuya idan bai biya ya taho da ita ba idan ya tashi dawowa daga sokoto. Wayarsa dake aje saman briefcase dinsa ta dauki tsuwwa,ya sunkuya ya dauki wayar yana duba me kiran,ya dan saki fuska ganin muhsin ne,jiya jiya suka gama waya dashi,ya danyi mamakin kiran,to amma maybe wani abun ya taso ne,saiya daga wayar ya saka a kunnensa. Agurguje suka gaisa ya sanar masa da saqon kiran "Ni zan tayaka murna....ko kaine zaka tayani?,...ko duka mu taru mu taya juna?" Dan murmushi ya sake,fararen jerarrun haqoransa suka bayyana "Eheen......me ya faru?" "Kayi d'a,ni kuma nayi jika,widad ta haihu" unexpected maganar yazo masa,sai ya fidda idanu waje "Bama haka dakai muhsin" "Kuma yau ba zamu fara ba,ka samu d'a na miji alhmdlh" "Allahu akhbar,Allahu akhbar,Alhamdulillah, Alhamdulillah" shine abinda bakinsa kawai ya iya maimaitawa cikin wani irin yanayin madaukakin farincikin da shi kansa baisan adadinsa, uncle muhsin yayi masa barka don tabbas yasan ya fishi cancantar ayi masa barka,ya kuma ce yana jiran goron albishir dinsa sanann ya katse wayar don ya barshi yayi sharing farincikin wa danginsa. Wayar kamar zata fadi a hannunsa haka yaji,ya rasa da wa zai fara sharing wannan abun farincikin,sai kawai ya kamo.su mimi ya rungumesu cikin jikinsa yana ta maimaita hamdalar da tun dazu taqi barin bakinsa "Daddy menene?" Mimi ta tambayeshi tana kallon fuskarsa "Antynku ta haihu yanzu" wani irin tsalle ta buga cikin farinciki tana kallon nawwara "Nawwara mun sake samun baby,anty ta haihu,yanzu mun koma mu haka ko daddy?" Ta fada tana daga yatsunta guda hudu,kai ya jinjina mata murmushi yaqi barin fuskarsa,bakinsa kuma ya gaza rufuwa "Bari naje na gayawa mummy" tayi maganar tana zame jikinta daga na abbas din,ta kuma ruga kitchen da gudu. Ta gama zuba ruwan tea a flask kenan mimi ta fado kitchen din,ta juyo ta zabga mata harara "Ban hanaku wannan guje gujen ba?,saikun fadi ku ishi mutane da koke koken banza" "Anty ce ta haihu mummy" da sauri ta juyo tana dubanta "Wacce antyn?" "Antyn nan gidan,anty widad" wata mummunar faduwar gaba da tunda take zata iya cewa bata taba jinta ba banda randa abbas ya sanar mata qarin aurensa ba taji,ta zaro dukka idanunta tana kaiwa bakin mimi bugu "Kijimin yarinya da shegen jawowa kai masifa,shashasha wadda batasan ciwo da matsalar 'yan uba ba,baku da 'yan uba a cikin gidan nan,kada na sake jin kinyi wannan maganar" dafe bakinta yarinyar tayi duk da Allah ya taimaketa bata sameta da kyau ba "Wallahi mummy d........" Tsawa ta daka mata ba tare data barta ta gama fadin abinda zatace din ba "Fitarmin a kitchen masu shegen surutun da zai halakaka idan bakayi wasa ba"(subhanallah,yana da kyau mu dinga iya bakinmu akan yaranmu,komai qanqantar kalma mu kiyayeta mu guji fadarta akan yara saboda tsanani girma da kuma saurin tasirinta a kansu). Bin yarinyar tayi da kallo harta fice sannan taja tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta kuma juya tana ci gaba da rufe flask din,saidai har a sannan qirjinta bugawa yakeyi. Komai ta shirya kan tray,duk da ba wani abun azo a gani bane,amma.bataso takai masa wani abun yace babu kaza ya sake sakata tashi "Maimakon ya wuce ya samu eatery akan hanya yayi breakfast dinsa shima" ta fada cikin ranta tana gunguni,har yanzu zuciyarta ba dadi idan ta tuna abinda mimi ta fada,dole ta kwabi yarinyar don kada ma ta sake magana irin wannan,kada wataran ta fada da bakin mala'iku,'yan ameen suna kusa su amsa. Cikin tray din ta dauko flask da cups din ta fito daga kitchen din,dai dai sanda suke waya da yaaya bara'atu bayan sun gama waya da hajiya "Yanzun ina shirin tafiya sokoto muhsin ya kirani ya gayamin" shuru ya danyi fuskarsa daukr da wani irin murmushi da zai fayyace maka farincikin dake zuciyarsa bazai misaltu ba,ya sake murmusawa sanann yace "Eh wallahi.....an samu baby boy". Cak komai nata ya tsaya da aiki na wucin gadi,kunneta yayi toshewar data kasa jiyo abinda yaci gaba da cewa,kalamansa zuwa ga yaaya bara'atu sai taji kamar ba hausa bane wani yare yake daban,sai ta dinga jinta kamar a duniyar mafarki ko kuma daga bacci ta tashi,daga bisani kuma kamar wadda babbar mota tazo ta daka haka taji kowanne sashe na jikinta ya saki,har kwanukan hannunta suka zame suka tarwatse a wajen,qarar faduwarsu da kuma fashewar flask din mai cike da ruwan zafi yaja hankalinsa daga wayar kan wayar da yakeyi,ya miqe da sauri yana katse wayar hadi da furta [5/11, 12:23 PM] +234 802 297 0646: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 16 "Subhanallahi, garin yaya?" Bayan ya iso yana duba kayan,komai ya tarwatse ya hade waje daya,saita duqa da hanzari jikinta yana dan rawa tanason boye hadiye tashin hankalinta,ya duqa shima yana tayata tattare wajen sannan yace "Qanwarki ta haihu......" Ya fada yana tattare wajen ba tare daya ko kula da yanayin da fuskarta take ciki ba "Ta samu d'a namiji ba......abinda ni hafsat na gagara baka har kaje ka qara aure don ka sameshi,burinka ya cika" ta fada da wata irin shaqaqqiyar murya sai kuma ta saki tarkacen data fara kwashewa ta wuce daki tana sakin boyayyen kuka mai bala'in cin rai,komai ya qarasa lalacewa kenan,yaushe akayi cikin?,yaushe harya girma?,sannan data tashi haihuwa ma ba mace ba?,namiji?,saita quma kanta da bangon dakin wanda har tsakiyar kanta taji zafin buguwar da tayin,amma radadi da zafin dake cikin zuciyarta ya zarta wanda taji. Da kallo ya bita sanda take wucewa dakin,mamakinta yana kasheshi,banda yasan bata da aljanu da tabbas wasu lokutta sai yaga ruqiyya ce tafi dacewa da ita,yanzun a batun haihuwar widad din meye abun daga hankali?,harda qirqirar batun d'a namiji da 'ya mace?,bashi karan kansa ba,ko a cikin danginsa ba wanda ya taba zancan mata take haifa,hakanan tsahon zamansu bai taba kawo wannan tunanin a ransa ba banda yanzu data furta,don shi a wajensa d'a duka d'a ne,yadda ake haifar namiji haka ma mace,sai wanda Allah ya sanya yafi wani albarka kawai. Yadda yaran sukayi carko carko suna kallonsa yasa bayan ya gama sharar wajen ya wuce dakin nata bayan ya zaunar dasu a falon,kuka ya sameta tanayi sosai hadi da safa da marwa,ta kasa zama waje daya,ya isa tsakiyar dakin a nutse hannayensa zube a aljihun wandonsa yana kallonta "Hafsat,ki nutsu mana,duka wannan abun na meye?" Sosai tayi qoqarin saita kanta, batason ya karanci yaron da aka haifa takejin buri da muradin mutuwarsa yana ratsata "Na nutsu fa kace,wai meye ka maidani abbas?, yarinyar tayi ciki harta haihu ban sani ba sai ranar data haihu din?" Mamaki ya sake kamashi,lallai idan mutum bashi da abun fada to fada yakeyi da kowa ma "To naji,amma relax please,kin saka yara duka hankalinsu ya tashi,yanzun dai tunda ta haihu ai ya wuce ko?,sai kiyi haquri" ya rufe da bata haquri duk don bayason tashin hankali. Kuka ta sake fashewa dashi ganin wani lafiyayyar nutsuwa da walwala shinfide saman fuskarsa "Ko yaushe cutata kake abbas,ko yaushe zaluntata kakeyi" abinda ta fada kenan,kalmomi biyun da ya tsana kenan a rayuwarsa,ko zai yarda da komai amma bazai dauki kalmar cuta ko zalunci ba akan wani,babban dalilin da yasa yake da abokan adawa sosai akan aikinsa, don baya yarda a zalunci kowa,mai gaskiya ne kai ko mai laifi,kowa sai an tabbatar masa da hakkinsa. Ganin yadda ta birkice ba bisa gaskiyarta ba sai kawai ya juya ya fice daga dakin ba tare daya sake bi ta kanta ba,ta sake tunzura ainun sanda tashin motarsa,data leqa falon ba kowa duka ya tattara yaran ya fice dasu banda yusra da tayi bacci ya kwantar mata da ita saman couch ya tareta da pillow don kada ta fado,saita sake rushewa da kuka,a fili tana cewa "Widad ta haihu?,kuma d'a namiji?" Ta fadi hakan ya kusa sau biyar,tanason idan wai mummunan mafarki takeyi Allah ya taimaketa ta farka,saidai still sake samun tabbacin cewa idanu biyu take tayi,musamman da taji muryar sagir dan yayansa daya dauko yake zaune a gidan,saboda samun security na gidan idan suna kaduna. Yana tuqi a hanya amma tunani barkatai yana zuwan masa,lamarin hafsat ya fara sakashi a kokwanto,ko a labari bai taba ganin mace mai baqin kishi irinta ba,ya maida dubansa gasu mimi dake ci gaba da murnarsu ta samun dan uwa,wanda a gidan basu samu sukuni ba saboda gargadin da hafsat din tayi mata,yaran fici fici dasu,ko wanka babu amma haka ya daukosu saboda yasan idan ya barsu a gidanma akansu zata huce idan ba'a yi wasa ba. Yana tsaida motarsa gaban gidan hajiya ya bude yace su shige ciki,da gudunsu kuwa suka fella,ya dauke idanunsa daga kansu yana murmushi bayan sun shige din,wayarsa ya ciro ya sake trying number widad amma taqi shiga, shikam bayajin yau zai iya kwana bai sanyata cikin idanunsa ba,don haka ya shiga kiran number din suraj karo na biyu "Yaya dai angon qarni" "Don Allah idan ba wani muhimmin uzuri gareka ba,ka ajjiye komai kazo kayimin rakiya kano" "Da zafi zafi haka?" "Kaima kasan bazan iya jurewa ba" ya amsa masa yana murmushi "Bani nan da awa daya" "Godiya mai kima" ya fada yana jin dadi,suraj din aboki ne na gari dake tsaya masa cikin kowanne irin yanayi. Suna gama wayar mimi ta fito da gudu tana kiransa "Wai ka shigo inji hajiya" "Gani nan mimin daddy" ya fada yana dariya hadi da kashe motar,ya fito suka jera zuwa cikin gidan tana riqe da hannunsa tana gaya masa zasuyi party dasu nawwara da qawayenta "An gama mimi na" ya bata amsa yana murmushi hadi da shafa kanta. Da waya a hannu ya samu hajiya,ya tsugunna yana sake gaidata duk da sun gaisa dazu ta waya. A nutse ta amsa masa tana kallonsa,cikin muryar nan dak cike da dattijantaka tace "Wai meye yake faruwa a gidanka Abbas?" Tayi maganar cikin qosawa,sai ta kasa jira yace komai ma "Me dame kake boyewa matarka" sosai ya dubi hajiyan,yasan kwanan zancen "Hafsat ce ta kawo qara ta hajiya?" Ya tambayeta a sanyaye,saita gyada masa kai,tana jin tausayinsa yana kama ta,ya hadiye wani abu mai tauri sannan yace "Wai na boye mata cikin widad,ni kaina ban dauka lokacin haihuwar yayi ba,saboda duka scanning dinta da awon da ake mata bata cemin komai" yayi maganar da sound na damuwa da takaicin dabi'ar hafsa. Zama hajiyan tayi a gefansa sabanin dazu da take zaune,sannan ta fara masa magana da harshe irin na uwa,tana tausarsa da kalamai masu kwantar da hankali da suka sanya jikinsa mugun sanyi,saboda yadda hajiyan ke masa magana kamar wadda ke bashi wasiyya ne "Kaci gaba da haquri,ibada kakeyi,kuma nasan tabbas Allah bazai taba wofantar da kai ba,bazai kuma tauye maka ladanka ba,wataran sai labari,kuma wadan nan abubuwan da dukka nake gaya maka ko bayan raina zaka tuna,nidai abu daya da nake godewa Allah,widad da Allah ya baka,ko babu ni nasan zata kula dakai....in sha Allah" "Hajiya ki daina fadin bayan ran nan don Allah" ya fada yana son katse zancan,sai tayi murmushi kawai "Bara'atu harta kirani tayimin zancan zuwa kano" "Eh nan da awa daya zamu tafi ni da suraj in sha Allah,su kuma ina ganin saisu bari ko bayan kwana biyar ne ko shida ko ranar suna" "Ba laifi hakan yayi,Allah ya tsare" Kaye kaye ta masu uban yawa hajiya ta hadama widad din,a yau tana jin zuciya da ruhinta fes,tana sake godewa Allah da ya bata iko tayi wannan hadin,ko ba komai abbas din ya samu wani sassaucin rayuwar gidansa ta wani gefen. Sun dauki hanyar kano a lafiyayyar motar abbas din,daga shi sai suraj,wanda suraj ke tuqin,hira sukeyi sosai a junansu,wanda kusan fiye da rabin zancan na widad ne, zaiyiwu wuya kawo yanzu muddin akwai shaquwa da aminci irin wanda yake tsakaninsa da suraj kuyi dogon zama baiyi maka maganar widad ba "Ka godewa Allah daya baka wani bangere da zaka dinga samun sassauci,amma koni.ina ganin qoqarinka,tabbas inda nine keda hafsat,da tuni na jima da qara mata mai" murmushi abbas yayi sannan ya miqe ya zauna sosai,ba daga bakun suraj kadai.yake jin wannan maganar ba,sai ya dan dubeshi kadan sannan ya maida dubansa ga titi "Saki ba shine hanyar maslaha kadai ba,bai kamata saki ya zama wani abu mai sauqi ga kowanne magidanci ba,idan hakan kuwa ta kasance al'ummarmu zata zama bata da wata makoma,tunda kowacce al'umma gidan aure shine tushenta,tunda daga can ake samar da nau'i na dan adam,nagartacce ko gurbatacce,wanda daga baya shi zai fito ya zama madubi na al'umma,imma malami jagora ko shugaba,mun ruguxa gidajen aurenmu da aure aure da sake sake,me muke tunanin zamu tsinta a gobemmu?,idan kayi qoqarin gyara ko canza matarka hakan bata samu ba,ba saki bane kawai hanyar da zaka samu gyara,infact idan ma bakayi wasa ba,sai ya bude qofar wata barnar,wani lokaci ya kamata mu dinga duba da wasu abubuwa kafin afkuwar saki,kamar makomar yaranmu,da wanne ido zamuyi musu bayani sanda suka budi idanu sukaga babu iyayensu a tare dasu?,wanne alkhairi matar nan ta taba yi maka a rayuwarta komai qanqnatarsa?" Kai suraj yake jinjinawa,ya jima baiga mutum kamar abbas dinsa ba,ko yaushe yana gayawa kansa da kansa abbas din na dabanne,samun irinsa sai an tona,inda hafsat zata gane waye take aure,lallai ba shakka zata fahimci a duniya tana cikin mata masu sa'ar da ba kowa ke samunta ba. Misalai kala kala yaci gaba da bashi,wadanda suka fahimtar da suraj abbas ya fishi gaskiya da kuma hangen nesa,saidai a halittarsa bazai fa iya daukan abinda shi yake dauka ba. Wayarsa da tayi qara ita ta katse zancan,ya daukota daga inda ya zurata yana duban me kiran, al'ameen ne abokin aikinsa,sai ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da sallama "Oga.......kasan an saki signal kuwa?" Abinda ya fara cewa dashi kenan bayan sun gama gaisawa "Ah.....haba,yaushe?" "Jiya cikin dare,ban kwanta ba sai dana duba list,saiga sunanka a farko farko,You have been promoted to DSP.....congratulations" sosai labarin ya tabashi,saboda baisan ma abinda ke faruwa ba banda al'ameen din ya gaya masa yanzun. Hajiya ya fara kira ya gaya mata,tayi masa addu'a sosai cikin zallar farinciki da fatan ci gaba da samun nasara,widad itace tazo ata biyu,don a yanzun a duniya bayan hajiya widad itace number two dinsa,ya gaza haquri har sai ya isa,tayi amsa addu'a sosai data burgeshi, shigen addu'ar da hajiya tayi masa,sai yaji zuciyarsa tana qara sanyi tare da samun nutsuwa a ransa. "Lallai muhammad yazo da alkhairi da albarka" suraj ya fada yana murmushi,kai abbas ya jijjiga sosai,yana tuna sanda ya samu promotion sanda maganar aurensa da widad din ta taso,haka Allah yake al'amarinsa,yana tsara komai bisa yadda yakeso ya kasance. Daga sanar masa haihuwar zuwa isarsu kano duka duka ba'a cika awanni uku ba, lokacin da sukayi ido biyu da widad din sai yaji gaba daya duniyarsa ta dawo sabuwa,tausayi girma da kimarta suna sake ratsashi,ya sanya hannu biyu ya karba yaron idanuwansa suna qishirwar ganinsa. Wata irin qauna da soyayyar yaron mai qarfi ta saukar masa sanda idanunsa suka sauka akan fuskar da marabarta da tashi shekaru ne kawai "Subhanaka rabbi.....maa a'azama sha'anik, Hasbunallahu wani'imal wakil" ya fadi zuciyarsa na bugawa da soyayyar yaron,ya daga kai yana duban widad da wani irin narkakken murmushi "Yau wannan babyn ta zama uwa.......wannan babyn ta zama maama,babyn uncle ta zama maman baby" kunya sosai ta kamata,ta kama hannunsa ta kifa fuskarta a ciki tana dariya qasa qasa. Tamkar abbas bazai bar gidan ba,yana jin kamar yayita zama yana kallon yaron nasa dama widad din gaba daya,saidai abisa tilas yayi musu sallama saboda tafiyarsa sokoto da dole ta koma washegari. Bai bar garin kano ba sai da ya tabbatar hatta da magi da widad zatayi amfani dashi ya tanadar mata,duk da cewa bata rasa komai ba a gidan,ga jibge mata komai na amfani,banda kayan sawa na barka nata dana baby wadanda musamman ya sake sabuwar siyayya banda wadda sukayi a saudiyya,wanda kowa ya gani sai ya shaida irin soyayya qauna da kuma yadda take da muhimmanci cikin rayuwarsa. A ranar ya yiwa yaron huduba da suna muhammad muhsin,wanda zabi ne ya baiwa widad kuma ta zabi sunan uncle muhsin din "Hakan yayi miki?" Saita gyada kai tana murmushi "Uncle muhsin ya bani komai a rayuwa da yayi silar wanzuwar rayuwata tare da taka,ya bani komai da ya bani kai" ta furta kalaman da wani irin sanyi,har cikin zuciyarta tana jinta cikin mata masu sa'a data samu abbas. Kalamanta sun sake gina mata matsayi mai girma cikin jiki da zuciyarsa cikin qanqanin lokaci,ya saki wani tattausan murmushi "Ni zan fadi haka widad,ya kawowa rayuwata alkhairi,ya kuma yarda ya kawowa rayuwata dauki a sanda take gab da dulmiyewa,samunki wani babbar tagomashi da baiwane daga Allah, ubangiji na ya gama yimin komai,babu abinda zance dashi sai godiya mara yankewa har ya zuwa qarshen numfashi na". ********JEGO widad takeyi sosai,irin jegon da ake kira jego ja ainihi,don hajiya umma kakarta ta wajen mahaifiya wadda ta haifi mommynta ce ta taso takanas daga katsina ta taho yi kata zaman dabaro,tace damar da ba'a basu ba lokacin bikinta ba yanzu zasu nuna tasu bajintar. Nan sashen ummu ta sauka cikin dakin da aka warewa widad din,zamansu gwanin sha'awa,gurin sai ya zama majalisar gidan,abinda ya qarawa widad dadin zaman gidan kenan,sai 'yan qananun abubuwa dake damunta,rashin sabo da raino,da kuma shayarwa da sai an tsaya a kanta take shayar da yaron saboda tsoro da rashin sabo. Gyara iya gyara widad tana shansa,jego take irin na da wanda a wajenta yake kamar takura ce,har sai da anty madeena tace da ita "Ki godewa Allah,ke yar gata ce gaba da baya,irin wannan gyaran da kulawar mata da yawa suka rasa,wanda daga ita ne kika samun sbauwar daraja da kima idan kin samu kula da gyara me kyau,daga itane kuma komai yake qwace miki ki kasa fahimtar inda mijinki ya dosa idan kinyi sakaci da ita". Ta sake yarda da haka bayan hajiya fanna tazo mata barka,daga cikin abinda ta kawo matan itama kayan gyara ne 'yan maiduguri masu shegen kyau,ta kuma jadda mata lallai lallai tayi duk abinda tsaffin suka ce mata,domin sun fita sanin me sukeyi,yadda taga kuma suna kula da ita itakam hakan ya burgeta. Fadin irin alkhairin data dinga samu ma bata baki ne,abun sai ya zamana kamar lokacinne aka yiwa abbas din haihuwar fari,abokan aikinsa kota ina,basajin tafiya daga bauchi zuwa kano ganin jariri,abun har mamaki ya dinga bawa kowa. To amma ba abun mamaki bane,duba da dabi'a da halayyar abbas din,mutum ne mai tsananin kirki kyakkyawar mu'amala da kuma budadden hannun alkhairi ga kowa,haka suka yita karbar jama'a,har akayi kwana biyar,aka fara shirin gagarumin suna. *********Ita kadaice a zaune a falon nata tana yankan farcenta da wannan karon da kanta tayi amannar yayi datti yadda ya kamata,don babu ko sirkin jan lalle a kansa ko baqi balle ya taimaka ya boye datti ko tsahon da yayi. Gaba daya tunda akayi haihuwar takejin wani gagarumin sauyi yana tunkarar rayuwarta,tana fuskantar motsin kowa,kowa cikin family kamar rawar jiki yake da haihuwar,abbas kuwa duk da dama can nutsatse ne,komai nasa kuma bisa tsari da dacewa da kuma mutuntaka yakeyinsa......amma walwalarsa ta qaru dari bisa dari,jifa jifa tana tsintar hirarsa da yaransa akan sabon qaninsu,abinda yake matuqar quntata mata,ya kuma jefata cikin baqincikin da yake sake sakata cin alwashin da takejin muddin ranta ba zata sauke ba,sai taga abinda ya turawa buzu nadi. Ko a yanzun ma da take zaune ita kadai a gidan sai yusra,ya kwashesu suna wajen tailor dinsu karbo dinkunan suna,sunan da batajin ko sama da qasa zata hadu zata bar yaranta suje,badai a gobe zai wuce kaduna ba saboda tasowar wasu ayyuka masu matuqar muhimmanci?,taga wanda zai tareta da maganar zuwansu kano.[5/13, 2:08 PM] +234 704 105 6348: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 17 Sallamar anty ummee ce ta tsinkar mata da zuciya,a sanyaye ta amsa mata,anty ummee din ta shigo idanunta na dan shawagi cikin falon,cikin ranta tana Allah wadarai da halin qazantar ummeen da har yau ta gaza rabuwa dashi. "Ya naji gidan shuru,ina yaran?" Ta tambayeta bayan sun gama gaisawa,kamar jira takeyi sai kawai ta sakewa ummeen kuka "Ke meye haka?,ai sai a dauka wani abu nayi miki daga shigowata" kamar zuciyarta zata fito daga qirjinta sanda take gayawa anty ummeen damuwarta,sai data gama tsaf sannan ta tabe baki "Ai wallahi yanzu yadda kissa ke ci asirin bai isa yayi wannan aikin ba,ke ko masu asirin aida kissar suke hadawa bawai ki tsaya haka sungungum ba,ni ai tunda umma ta gwasaleni saina tsame hannuna,yanzu ki yiwa kanki hisabi,da lokacin da muke kan takunmu da yanzu wanne lokaci ne kikafi samun yadda kikeso?" Shuru tayi tana nazari,ko ba'a gaya mata ba tasan amsar,a wancan lokacin ta samu dukka wata dama da rashin haqurinta yasa ta gaza kaiwa ga gaci ta koma bin malamai,duk da suma nasu aikin tana samun biyan buqata duk kuwa da bamai yawa bace,amma babu jinkiri a hanyarsu,sha yanzu magani yanzu ne(wa'iya zubillah). "Nasan kin riga da kin baiwa kanki amsa,to koda zakibi malamai saikin hada da kissa,saboda haka idan kin shirya bismillah,duk da dai yanzun bani da lokaci isashe,muna shirye shiryen tashi zuwa sabon gidanmu,idan na hada hankalina waje daya saimu tsara yadda zamu gyara komai,muga kuma yadda Allah zaiyi". A ranar saita samu walwala sosai,daga ganin anty ummeen sai taji kamar matsalarta tazo qarshe,ta dan jima a gidan,wanda bata fita a gidan ba sai data yagi wani abu daga jikin hafsat,bata hanata ba,don itama yanzu taimakonta take nema,daga qarshe ma sai data bawa dan riqon gidanta dan yayan abbas din key din motar ta ya maida anty ummeen gida. Sau biyu tana fitowa tana shige kitchen amma tana ganinsa a zaune inda ta barshi,kusan awa guda kenan yana zaune a wajen,yaran suna kwance daga gefansa sunyi barci. Tunda ya dawo ya watsa ruwa ya zauna zaman cin abinci,ta dire masa abincin ta qara gaba,don tun ranar da widad ta haihu haka take masa,zafinsa takeji,saidai ko.sau daya bai taba nuna mata ma ya gane wai fushi take ba,don shidai kaf a abinda ya faru baiga abin yiwa fushi a ciki ba,shi yasa ya tattara ya bawa banza ajiyarta. Cikin zafi yake amsa wayar tsahon awa gudan kenan da gurbataccen turanci (brooking),da alama yana magana da wasu cikin yaransa ne akan abinda ya shafi aikinsu. Fitowarta ta qarshe daga kitchen din ya sauke wayar a kunnensa bayan yaja tsaki,sau da yawa ire iren abubuwan dake janyo musu bacin suna kenan daga wajen al'umma suke musu kallon abu daya,yanzun ya zama dole ya tafi kaduna a gobe "Zoki dauke yaran nan ki kaisu daki" kakkausar muryarsa da amonta babu wasa kwata kwata a ciki ta ratsa kunnenta,saita ratso ta tsakiyar kujerun ta fara daukesu daya bayan daya,shi kuma ya buda warmer din abincin yana qare ma abincin kallo. Bacin ransa ya sake daduwa sosai,ya maida murfin ya rufe,ya koma.ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya,ya dade da sanin irin muhimmancin widad cikin rayuwarsa,amma nisan da tayi dashi a yanzu ya sake haska masa girman da muhimmancin da take dashi ga rayuwarsa. "Idan kinkaita ki dawo" saita tura baki gaba tana cure fuska kamar wadda aka yabawa kashi,tana tsammanin yana buqatar wani abune daga gareta,indai.kuwa hakane yau a jikinsa zata fanshe abubuwa da yawa da ta qudirta,don haka koda takai nawwara sai da taja lokaci sannan ta dawo cikin falon,zuwa sannan ma har ya shiga kitchen ya hada coffe da kansa,don ya gwammace ya shashi ya kwanta akan yaci wannan qaddararren abincin nata. Gefe ta zauna tana hada rai, baice komai da ita ba sai daya gama sha ya dire cup din,ya jawo system dinsa dake cike da rubutu yayi saving ya kasheta,sannan ya bude briefcase din gefansa ya ciro kudade ya ajjiye mata. "Nasan hajiya ta gaya miki gobe zaku wuce kano suna,gashi nan,kudin transport ne dana amfanin gida,nasan zasu isheki harda ragowa ma" ya qarashe maganar ba tare daya dubi fuskarta ba,sai jakarsa da yake rufewa "Ni ba inda zani fa,saboda haka sai sun dawo" wani kallo ya watsa mata bayan ya miqe yana kallon cikin idanunta "Ba shawararki nake nema ba,umarni ne na baki, bijirewa magana ta kuma bazatayi miki dadi ba,banason doguwar magana,gobe zaku kano period" ya juya a nutse yana tafiyar nan tasa majestically kamar bashi da sauran damuwa,duk kuwa da cewa qasan ransa bacin rai ne fal,ga na shirmen da aka masa a office ga matsalar hafsa din da har yau babu alamun gyaruwa ko nutsuwa a tattare da ita sam sam. Dakinsa ya wuce ya ajjiye jakar sannan ya fara hadawa kansa ruwan wanka a mugun gajiye,abinda baisan dashi ba muddin kwanan widad ne,koda ya gama gado kawai ya haye,sannan yaja wayarsa ya kira widad din don ya tabbatar zai samu relief. Ya samu har fiye da yadda yakeso ma,ta sauke masa dukkan wani bacin rai dake ransa,daga qarshe ma video call sukayi ita dashi,ta nuna masa duk wata kwalliyar suna "Wannan ai tsomo ni kawai zakiyi,nayi missing......nayi missing sosai,ina da aiki amma banda haka ya kamata nazo naga kwalliyar sosai" "Za'a yi maka wadda tafi wannan,kada ka damu,ka maida hankali ga aikinka,wanda na tabbatar muhimmncin da kake bashi shine mabudin dukkan wannan nasarorin da kake samu" "Sirrin kuma nasarorin kece ba......nutsuwar da kike bani widad.......I don't know how to explain it to you,you become part of me". Irin wadan nan hirarrakin dake qara dasa kowanne cikin zuciyar dan uwansa su sukaci gaba da gudana,daga qarshe yace a karbo masa muhammad zai ganshi,dole ta ajjiye wayar duk da yadda takejin kunya don yana hannun 'yan suna,ta samu nujood ta lallabata ta karboshi. Ya jima yana kallon yaron ta cikin video call din sannan ya sauke ajiyar zuciya "Bazan iya hana wannan taron sunan ba,amma don Allah..... please na roqeki,ki kulamin da kanki,ki kuma kularmin da yaro na,kada ayita wannan shige da ficen da shi" dariya ma ya bata yadda ya marairaice,kuma yake maganar da gasken gaske "Oh...... dariya ma na baki?, seriously madam......am in pain na yadda za'a kallemin ke a gobe,don Allah ki kula" "Nifa taka ce,mallakinka ce ta har abada,infact ma saboda kai Allah ya halicci widad,no need ka damu,kayi aikinka hankalinka kwance don Allah" maganganu tayi masa masu kwantar da hankali,dole daga bisani sukayi sallama saboda yadda aketa kiranta daga falo. Suna gamawa ya ajjiye wayar yayi addu'ar kwanciya barci,yaja duvet abinsa ko takan hafsat baibi ba. Sanda ta gama baqin ran nata tana zaton zai biyota taga bai biyota ba saita shirya ta taho,koda ta iso tuni ya jima da yin baccinsa,abinda ya qara mata baqinciki da takaici,ta kasa kwanan dakin ta rufe masa qofa ta koma nata dakin. ********Tun asuba ya shirya ya fice abinsa,bai sake tada mata zancan zuwa kano ba alamun zabi kenan ya rage nata. Duk abinta tasan iya lokuttan da take iskancinta,ta sani sarai idan ya kafe bashi da dadi sam,dole ta fara shirin tafiya,bayan ta kira muneera taji qarfe nawa ne tafiyar. A ranar sai data fidda kayan sawarta daga cupboard dinta gaba daya amma ta rasa wanda ya dace ta saka,kowanne akwai nashi illar,sutura iya sutura masu tsada,don abbas baya siyan abun banza,saidai idan ita ya bawa kudin ta siya na banza ta soke sauran kudin,wannan kuwa ko ta kanta baya bi. Wata rigar tasha squeezing,wata bata ga dan kwalinta ba,wata na buga tsami,saboda an saka an maidata cikin kayan ba tare da an wanke ko an barta tasha iska kafin a maidata din ba. Bata taba jin haushin irin abun ba sai yau,so takeyi tayi shiga ta kece raini,amma maimakon taji haushin kanta sai haushin ya tattara akan widad da abbas,kamar dole sai taje sunan?,amma kuma data tuna maganar anty ummee da tace gwara taje ta ganewa idanunta barnar kudin da yayi musu sai taji babu case,taci gaba da bincikawa,da qyar ta dace ta tsamo wata ABC england dark blue,itama a yamutse take,saidai atamfa ce mai laushi cotton sosai,don haka ta fesa mata ruwa ta zauna akai ta samu tadan miqe. Duka mayafanta masu tsada da abbas ke siya sanyasu takeyi cikin kayan siyarwarta ta saida,a nan ma da qyar ta samu wani baqi ta dora,sanann ta laluba jaka da takalmi duka ta yamutsa abinta. Idan kika ganta zakiyi tsammanin amaryar 'yar talla ce daga wani qauyen ranar fitowa daga gidan miji na farko,ga jambaki ja ya kama ya haska baqar fatarta data rasa gyara bare tayi kyan da masu duhun fata keyi idan ta samu kula ba tare da canza launin fata,to amma da yake ba saban bace ta fannin ado da kwalliya,sai take ganin ta gama qure adaka,qarfe goma na safe motar da abbas ya sanya ta kaisu kanon ta iso ta dauketa suka wuce. Daga ita sai gwaggwo mero qanwar hajiyarsu,sannan muneera yaaya bara'atu,sai gwaggwo fanteka da gwaggwo hassana matan uncles dinsa,da kuma qanwar abbas wadda take binsa nasma. Tunda suka dau hanya babu wanda ta kula a cikinsu,saboda kowa fuskarsa babu alamun damuwa ko bacin rai sai ita kadai,har gwara gwaggwo hassana da yake suna da alaqa da ita,takan tabe baki lokaci lokaci ko tayi magana qasa qasa akan tafiyar. A can kano kuwa ko cikin family ranar kowa yasan sha lelen ummu ta haihu,gata tako ina a ranar ya nuna kansa,ba daga wajen mommy mahaifiyarta ba,ba kuma daga wajen ummunta ba,ba daga wajen tsoho mai ran qarfe alh salim ba ko mahaifinta Alhj mahmud da Allah ya dorama son jikan nasa,kamar a kansa aka fara masa haihuwar jika ba,ga kuma mai dungurungum din wato DSP abbas turaki. Wani kalar suna ake gudanarwa,irin sunan da tsiya da babu suke gudu da qafafunsu, komai a wadace,hatta da almajirai da mawadata ranar sun shaida sunan,tun da sassafe widad ke sanya sutura tana canzawa harta fara gajiya,qarfe sha biyu saiga motarsu hafsat tayi landing cikin tsakiyar harabar gidansu widad😂😂😂 _to mai karatu,ya zata kaya ne?,anya kuwa hafsat ayau zata iya cinye kishinta?,kuzo dai mu rakasu ciki mu gani_😂😂🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️ [5/13, 2:08 PM] +234 704 105 6348: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 18 Tun daga harabar gidan ta fara fahimtar daga wanne irin gida widad din ta fito,daga yadda taga abubuwa suna gudana tun daga farfajiyar gidan da aka cika da rumfuna jikinta ya fara sanyi,wani irin kishi da bacin rai yayi mata tsaye a wuya,a haka dai ta daure,ta fita a motar,suna biye da hajjaa data zame musu jagora cikin gidan. Tarba ta girma akayi musu bisa jagoranci anty deena,ta shirya komai yadda zai qawatar da baqin cikin girma da karamci,komai kasa cewa tayi,sai idanunta dake biye da komai na gidan,tun daga falo zuwa wani falon da aka tanada don su kadai,ko da mutum guda bata gaisa ba,sai ido da takebin mutane dashi,sannan ta watsar kamar babu ita a wajen. Komai dake gudana gwaggwo mero na ankare dashi,har zuwa sanda suka kadaita a falon,aka kuma turo musu widad dake shirye cikin wani dandasheshen lace da mummyn ta ta dinka mata,wanda kudinsa yakai dubu sittin. Lace dim shine abu na farko daya fara tsone ma hafsat din idanu,tasan kudinsa sarai tunda sana'arta kenan,wani tashin hankali ya rufto mata,har ta gaza dauke idanunta daga kan lace din,tana jin kamar ta tashi ta yageshi daga jikin widad. Duk yadda taso ta tausa zuciyarta ta amsa gaisuwar da widad din ke mata,ranta fes fuskarta cike da walwala amma ta kasa,daga qarshe ma sai tayi bandaki kamar wadda wata buqata ta kama. Kasa riqe kukanta tayi,sai data matsi hawaye sosai sannan ta fito bayan ta waske da dauro alwala,ta riga kowa tayar da sallah tun farkon muhtarin sallar azahar. Tana kan abun sallah ba tare data waiwayo ba,tana jinsu suna yaba yaron da aka shiryashi cikin wasu irin kaya masu asalin kyau da tsada na qasar saudiyya,kowa ya daukeshi sai ya fadi kyau da kuma tsantsar kamannin dake tsakaninsa da babansa,abinda ya sake dagula mata lissafi kenan. 'yan awannin da sukayi ta shiga quncin da sai data gwammace bijirewa zuwan tayi koma meye suyi da abbas din,idanunta sunga abubuwa kala kala,wadanda da wannan bacin rai tayi guzurinsu zuwa gida. Taro ya watse lafiya cike da tarin alkhairi da yaron ya zoma iyayensa biyu dashi,widad kuma ta shiga ci gaba da samun kulawa irin ta tsaffin da sukaga jiya sukaga yau,gefe guda ga gudunmawar yayyen zamani irinsu anty deena anty madeena,da matan abokai na qwarai irinsu fanna da sha'awa. *_DUKKAN ME RAI MAMACI NE_* Cikin sati biyu kacal muhammad da suke kira da affan ya fara wayo da wani irin girma dake alamta qiba zaiyi,daga shi har mamansa widad fatarsu ta qara gogewa,sunyi wani irin kyau na samun nutsuwa da kulawa,jegonta take hankali kwance,kulawa da soyayya tako ina,kusan ko yaushe suna manne a waya ita da abbas din,sukan shafe lokuta sosai suna hira,irin hirar dake debe kewa da sawa zuciya nutsuwa. Kwana biyu kacal yin wayarsu yadan ja baya,data tambayeshi yace hajiya ce bata jin dadi a kwanakin,a ranar sau biyu tana kiran hajiyan taji jikinta,cikin dauriya da murmushi take amsa mata "Da sauqi fa,kawai abbas ya tashi hankalinsa ne" kiran data mata a washegari da safe wanda shine kiran na kusan biyar hajiyan ta daga suka gaisa,ta tambayi dan jikallen nata wanda yake kamar shi daya ne jika a wajenta saboda yadda takejinsa a ranta "Allah yayi miki albarka widad,ya dafawa al'amuranki,kiyi haquri,kiyi juriya,Allah ya baki ikon kula da mijinki da dukka abinda ma zaki haifa a gaba" bata kawo komai a ranta ba,saima nauyin addu'ar hajiyan ta qarshe,duk da haka saita samu kanta da cewa "Ameeen" suka dan sake gaisawa sannan sukayi sallama da hajiyan. A ranar duka basuyi waya da abbas ba,tadan shiga damuwa amma daga baya ta bayar wataqila yanayin aiki ne,wanda wasu lokutan dama idan ya sakasu a gaba basu da wani sauran sukuni har sai sun gama sannan suke samun sauqi. Washegari affan yana saman cinyarta tana shayar dashi cikin dakinta,ita dashi dukkansu sunyi wankansu fes,sai qamshi suke fitarwa,so take ta gama bashi ya qoshi ta kaiwa latifa shi ta goyashi,kamar daga sama sai taji muryar uncle muhsin daga falo,cikin zumudi ta zare maman daga bakin affan ta sanyashi a kafada tana shafa bayansa,don yana shirin fara rigima ne,don da alama bai gama qoshi ba,tayo falon dashi. A tsaye ta sameshi shi da tsoho me ran qarfe da kuma ummu,yadda dukkansu suka bita da idanu haka kawai sai taji ta tsargu,saboda basu taba yi mata irin wannan kallon ba,duk sai taji qafafuwanta sunyi laushi,ta daure ta qarasa falon tana masa sannu da zuwa,ya miqa hannu yana cewa "Bani takwara na,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta tayaki hada kayanki zamu wuce bauchi" sosai maganar ta daketa,ta dubeshi da kyau "Bauchi kuma uncle?,ina cewa yanzu ka shigo?" Kai ya gyada mata "Eh,rakani zakiyi,flight zamu bi,kuma yanzun haka da nasa a siya mana ticket saura awa daya duka duka lokacin tashinmu yayi" kasa ci gaba da tambayarsa tayi,kawai saita juya tayi abinda yace din,saidai ko latifa dake hada mata kayan batace komai ba,bata tambayi ba'asin irin wannan tafiyar ta gaggawa ba,sai ta sake jin cewa lallai akwai wani abu dake faruwa. Samun kanta tayi da gwada wayar abbas don ta tambayeshi yasan wani abu akan tafiyarta?,ta kuma shaida masa tahowarsu amma amsa daya computer ke bashi wayar a kashe take,dukka.layukansa,da personal da na aikin gaba daya,saita jefa wayar jakarta kawai ta dauki mayafin abayarta ta roller ta fito. Sallama ta dinga yi da mutanen gidan,duk da tana gaya musu zata dawo sai tayi arba'in zata koma,ba wanda yace mata komai daga uncle muhsin har ummu,a haka suka fice a gidan ta cikin motar daya daga cikin samarin gidan da zai saukesu a airport. Tun saukarsu a garin bauchi taji gabanta yana wani irin faduwa mai tsanani,nutsuwarta tana neman barin gangar jikinta,ta dauka irin yanayin da take tsintar kanta ne duk sanda sukazo bauchin,amma saita karancin yanayin ya sha bambam da wannan da take tsintar kan nata a ciki,tayita kokawa da zuciyarta har zuwa sanda taga sun doshi hanyar gidan hajiya. Waiwayowa tayi tana duban uncle muhsin "Na dauka gidanka zamu sauka?" "Aah" ya fada a taqaice,daga haka shi da ita ba wanda ya sake magana,har zuwa sanda suka gangara gefan titi suka shiga faffadan layin dake malale da kwalta. Mummunar faduwa gabanta yayi lokacin da taga jama'ar dake zaune a qofar gidan,qarqashin rumfar tempol,qofar gidan cike yake jama'a,haka ta dinga ratsa mutanen qafafunta kamar ba'a jikinta ba, zuciyarta na wani irin bugu,ta kuma kasa tambayar uncle muhsin komai,burinta kawai ta isa cikin gidan ta gano abinda yake faruwa. Bata tsaya ba har sai data isa falon hajiya da shima yake tanqam da jama'a,sai surutai kadan kadan da kuma koke koke,kamar wata mutum mutumi ta tsaya tana qarewa kowa dake falon kallo,bakinta ya gaza cewa komai "Kamata ki zaunar da ita" taji muryar Gwaggo mero tana fada,sai a sannan ta samu qwarin gwiwar kallon hajja dake sama mata wajen zama bayan ta karba affan ta miqawa yaaya bara'atu "Waye ya rasu hajjaa" "Kiyi haquri ki zauna,hajiya ce Allah yayi mata rasuwa" kamar an qwala mata qarfe haka taji,kunnuwanta suka daina ji na wasu sakanni kafin su dai daita, bakinta da dukka ilahirin jikinta ya fara rawa,Allah ya taimaketa ta kama kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kuka mai tsananin qarfi ya qwace mata,sai kuma numfashinta ya fara sarqewa,ta fara kokawar qwatarsa,daga haka kuma saita daina gane komai. Sanda ta farka cikin setting room ta samu kanta ita da hajjaa nujood da bilkisa matar suraj,suna mata sannu amma sake tanbayarsu take da gaske hajiya ta rasu ko kuma mafarki tayi?. "Allahn da ya fimu sonta ya dauki abarsa,addu'a ce kawai zata nuna zallar soyayyar da muke mata ba koke koke ba" nasihar da suka dinga mata kenan cikin kwantar da kai, saita fashe da kuka sosai tana jerawa hajiya addu'o'i har kamar ba zata tsaya ba,a haka suka miqo mata affan daketa rigima ta soma shayar dashi,amma hawayen fuskarta yaqi tsayawa,duk sanda ta kalli affan din sai taji zuciyarta ta sakeyin rauni,yayi rashin kaaka,kuma masoyiyarsa,wanda tun yana ciki take qaunarsa da begen ganinsa amma Allah bai qaddara hakan ba. Ba shakka hajiyan ta dace,domin dukkan wata siffa dake alamta kyakkyawan qarshe hajiyan ta sameshi,kama daga yanayin yadda ta mutu da cikakkiyar kalmar shahada a bakinta,zuwa yabo data dinga samu daga wajen mutane,gidan kamar xai tsage da jama'a,har maqwafta a cike yake babu masaka tsinke. Ta idar da sallar la'asar tana zaune saman abun sallah,har a sannan qwalla bata bar fita daga idanunta ba,tuni kanta yake sara mata da matsanancin ciwo,husna 'yar nasmah qanwar abbas ta shigo mata da abinci,ta kalleta ta kalli abincin "Ina abbansu mimi ne?" "Ni tun safe ban qara ganinsa ba" hankalinta sai ya qara daukuwa a kansa,tasanshi sarai,tasan irin soyayyar dake tsakaninsa da hajiyan,ya kamata a duba halin da yake ciki,itama tunda tazo bataji an ambaceshi ba,don haka ta miqe ta goyawa husna affan sannan ta canza hijabin jikinta zuwa babban daya saukar mata har qasa ta fita a dakin. Da qyar aka gano mata shi a dakin su umar,sanda tayi sallama ta shiga dakin kasa ganinsa tayi saboda duhun da dakin yake dashi,ta laluba makunnin fitilar dakin ta kunna,haske ya wadaci ko ina,mamaki ya kamata ganinsa zaune saman abun sallar, idanunsu suka hadu waje guda,sai taji wani rauni ya ziyarceta,kuka take da muradin yi amma kuma zuciyarta na gaya mata ba haka ya kamata tayi ba. Takowa tayi a hankali zuwa inda yake zaunen har yanzu idanunsu na manne da junna,fuskarsa ta fada wuni guda,sai wani irin jigata da idanunsa sukayi,dab da zata iso ya shafa addu'a sannan ya miqa mata hannunsa,ta dora nata hannun akai,zai mata masauki saman cinyarsa ta zame ta zauna daga gefansa tana kallon qwayar idanunsa dake cike da wani irin tashin hankalin da ba kowa bane zai iya karanta,tsananin jarumtarsa ya boye komai "Yaushe kukazo?" Ya tambayeta da wata irin murya dake cike da sanyi da jigata,ta danyi gyaran murya kadan don kada ta fashe masa da kuka "D'a.....d'az......" Kasa qarasawa tayi,dukkan wata jarumta ta qare,saita fashe masa da kuka harda sheshsheqa,baice komai ba illa rungume kanta da yayi a qirjinsa yana shafa bayanta,yadda kanta ke qirjinsa haka take jiyo yadda Zuciyarsa ke wani irin bugawa a hagunce. Mintuna kusan biyar ta dauka a haka sanann ta fara qoqarin saita kanta,ta daga kai tana dubansa da idanunsa da suka sauya kala,hannu biyu yasa yana goge mata hawayen sanann yace "Nasan ba wannan ne kukan da kika fara ba,pls karki qara yin wani kukan,hajiya bataso,kiyi mata addu'a" kai ta jinjina cikin aro jarumta,ta gaidashi tare da yi masa gaisuwa,don ya fita cancantar ayi masa gaisuwa,duk kuwa da cewa itama kallon uwa takewa hajiyan,ba zata taba mantawa da gudunmawa da soyayya qauna da kariya data baiwa rayuwarta ba. "Amma uncle,me kakeyi a nan kai kadai a duhu?" "Sallah nayi,baki gani ba sanda kk shigo?" Kai ta jinjina "Na gani,amma idan ka shiga cikin jama'a kamar sai yafi,a nan din tunani zaiyi maka yawa ne" kai ya jinjina kawai "Kaci abinci?" Ya sake girgiza mata kai,saita ajjiye masa affan ta shiga cikin gida ta samo masa abinci me kyau,saidai gaba daya ya kasa ci,ya ture plate din yace "Samomin coffee kawai ya isa" haka ta koma ciki ta hado masa coffee din,a hanya ne suka hadu da hafsat tana shigowa goye da yusra,yadda ta dauke mata kai itama haka ta bawa banza ajiyarta ta shige. Coffee din ya shige cikinsa da qyar,ya kama hannuwanta ya riqe cikin nasa yana cewa "Allah yayi miki albarka" don badon tazo ba yanajin azumin yini biyu zaiyi,don shidai ko qyallin hafsat bai gani ba,duk da ya tabbatar tana gidan,don suna gaban gawar hajiya ta shigo gidan tana runtuma ihun da sai da akayi mata magana. Bata barshi shi kadai ba sai data sashi gaba ya fito daga dakin ya koma cikin mutane,duk bayan wasu lokutta kuma tana sawa ana duba mata shi da yadda yake. To rashin mahaifiya wani rashi ne mai mugun ciwon da fadin radadinsa bazai misaltu ba sai wanda Allah ya jarabta dashi, rasuwar hajiya rashine na dukka dangi dama mutanen unguwa,kowa yaga tsananin jarumtar abbas,don ba wanda baisan irin shaquwa da qaunar dake tsakaninsu ba. A gidan yake kwana shi da widad din,amma daki daban daban,hafsat kuwa yaran take diba su wuce gidan iyayenta su kwana,sai kusan azahar take zuwa har akayi kwana uku. Randa akayi sadakar ukun da safe ne tsananin ciwon kai na rashin bacci da kuma damuwa suka sanya abbas a gaba,dole ya buqaci tafiya gida don ya kwanta ya huta,duk da bashi da tabbacin yiwuwar baccin. Farko hafsat yasa widad ta nemo masa su wuce tare,don yasan gidan kansa yayi qura,sanann widad din tana jego ga kuma mutuwar itama yadda ta bugeta tilas tana buqatar hutu,to amma sama da qasa babu hafsat din ba alamarta,dole yasa widad ta shirya suka wuce gidan. Sosai ta gyara masa bedroom dinsa irin yadda tasan yana so,sannan ta shirya masa dan abinda zaici mai dadi da ruwa ruwa,ta kuma hada masa ruwan wanka mai dumi sosai da qamshi,yayi ya canza kayan,ta sashi a gaba yaci abincin ya kwanta sannan ta baro masa dakin bayan ta sanyashi yayi addu'a. Falon ta dawo taci gaba da gyaranshi,tanayi tana duba affan dake kwance yana watsal watsal da qafa,ya cusa yatsunsa biyu a baki. Doko qofar falon akayi lokaci guda ba zato ba tsammani,har affan dake kwance yadan firgita "Subhanallahi" widad ta fadi tana duban bakin qofar.[5/14, 12:29 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 19 Hafsat ce a wani birkice sanye da hijabi ruwan qasa,fuskar nan cike taf da bala'i,tun sanda ta dawo taji sunyo gida da abbas din hankalinta yatashi,kullum fatarta da addu'arta yarinyar ta tafi kenan,sai gashi ta dawo rayuwarta tsundum "To mayya natacciyar dole,da kika tashi dawowa ai saiki jira girki yazo kanki,bawai ki biyomin miji kihau aikin da ba naki ba" sosai maganar tata tayi mata ciwo,kamar ba zata tanka mata ba,amma saita dago daga gyaran throw pillows din da takeyi ta kalleta "Maita da naci ga miji inajin isace wannan,wadda bata isa ba ko tayi babu riba,mukan da mukeyi alhmdlh akwai riba, miji kuwa babu wata rana da na kebe da zan tsame hannuna daga bashi kulawa saboda na girkina bane muddin yana da buqatar kulawata,ke meye ya hanaki tsaiwa ki bashi kulawar idan har kin damu dashi?" Ta fadi kanta tsaye tana kallon idanun hafsat da mamaki ya kasheta. Turqashi!,anzo wajen,yau ta samu dama,tanajin babu abinda zai hanata cin uban yarinyar yau abinda ta jima tana buri,kamar widad din ta karanci hakan,kuma bataso tayi abinda zai tada abbas di daga bacci,don haka tayi hanyar kitchen da dan saurinta "Dawo mana qaramar mara kunya kiga yadda ake yinta yau a fidda raini" hafsat ta fada tana bin bayan widad,dama abinda widad din keso kenan,don haka tadan daga qafa,tana shiga kitchen din ta tsaya tana ajjiye plate din hannunta,dai dai sanda hafsat ta qaraso ta dora hannunta a kafadar widad da nufin damqota. Tankwabe hannunta widad tayi cikin fushi tana kallonta "Sakeni,karki sake gigin riqeni,idan raini kikeso a fidda ki bari ya gama baccinsa ya fita a gidan ya zaman dagani sai ke,a sannan zan nuna miki cewa jaa da baya ga rago ba tsoro bane,shashasha wadda har yau batasan ta girma ba" ta dire maganar da tsaki mai mugun qarfi. Tsananin mamaki ya sanya hafsat din mutuwar tsaye tana kallon widad,cikin fushi ta yunquro a karo na biyu kafin tace komai widad ta rigata yin magana "Kika sake kika dora hannunki a jikina.... wallahi tallahi sai nayi miki wanka da wannan ruwan zafin,sauna kawai,shashasha"tayi maganar tana fidda manyan fararen idanunta waje a kan hafsat din. Abu makamancin wannan bai taba hadasu da wida din ba,don haka furucinta ya tabata sosai,sai taja da baya tana tafa hannuwa "Ashe da 'yar kalare nake zaune?,dama kanawa 'yan sara sukane mazanku da matanku?,to shi wanda ya baki daurin qarqashin yimin rashin mutuncin bari na tasoshi" saita juya tana haramar fita a kitchen din. Ai widad bata barta takai qofar ba ta sanya hannu ta fincikota saiga hafsat warwas a qasa,ta isa bakin qofar kitchen din ta tsaya riqe da qugunta "Azzaluma mara imani,wanann baccin dai yau sai ya yishi wallahi duk baqincikinki da baqin halinki" sai kawai taja qofar kitchen din ta kulleta aciki,bata da wata hanyar fita kuma saidai tabi ta qofar baya ta kitchen din ta fice,saita isa qofar part din nasa shima ta kulle,sannan ta saki ajiyar zuciya tana jan tsaki a ranta. Sam ta daina ragawa matar,zata nuna mata ita din bakanuwa ce,duk da ba jininsu bace amma kuma cibiyarta na bunne anan,tana jjn surutanta da zage zagenta sama sama har ta daina ji,da alama tabi ta qofar bayan ta fice. Yayi bacci kuwa sosai,don bashi ya tashi ba sai dab da magariba,a sannan widad din tayi wanka a nan sashensa ta sauya shigarta da wani sky Blue din material me kyau,ta daure kanta da band ta kuma dora dan yalolon mayafin material din,affan na kwance daga gefe cikin farar overall yana bacci abinsa shinfide cikin farin towel. Tunda ya fito yaga dukansu sunyi masa kyau uwa da dan nata,karon farko da ya fara ganin mai jego mai tsafta irin haka,abinda bai saba gani ba,idan hafsat na jego idan kaji ana jaga jaga ko itace,duk wani kalar qarni da bashi bashi zaka jishi,idan anyi magana takance jego take,dama wannan ai shine jegon inji hausawa,sallamawa sassanta dama yakeyi gaba daya,saidai tazo nashi da ziyara ta wuce. Ta daga kai daga wayar dake hannunta tana duba saqonnin watsapp suka hada ido,ya sauke mata murmushi yana jin zuciyarsa tana yin sanyi,ya samu nutsuwa kaso hamsin cikin dari daga qunci da rudanin da zuciyarsa ke ciki,ya durqusa a hankali yayi kissing affan dake baccinsa cikin qauna, qamshin da jikin yaron keyi ya ratsa hancinsa,ya daga kai yana sake kallonsa "Kullum kamanninmu da muhammad sake fitowa takeyi" ya fada da sassanyar muryarsa,ta saki dan murmushi "Sosai.......kun nunamin son kai ai" ta fada tana dan masa hararar wasa,sai ya saki murmushi yana cewa "Ba komai,next time by now ya samu yaruwa,ita na tabbatar zatayi miki karar" ido ta fidda sosai tana kallonsa sannan ta langabar da kai "Habba mana uncle....." Kai ya jinjina yana tarar numfashinta "Yes.....inason yara da yawa babyn uncle,mutuwar hajiya tasa naji ina son in tara yara masu yawa sosai,just pray Allah ya bamu nagari da zasuji qanmu"sai ta jinjina kai tana cewa "Ameen". Bai fita sallar magariba ba sai da yaci abinci ya sake wanka,kafin ya dawo ta sake gyare komai,ta budade falon da qamshi yadda zai masa dadin zama. Sai da akayi isha'i ya dawo,ya zauna a falo suna taba hira,yana kan kujera tana zaune a qasa,qafarsa saman cinyarta tana matsa masa qafafunsa a hankali cikin wani salo da ya sake saukar masa da nutsuwa,kamar an jehota saiga hafsat ta sake shigowa falon tana kumbura. Kallo daya widad tayi mata ta dauke kai kamar batasan Allah yayi ruwanta ba a wajen tana ci gaba da tausawa abbas qafarsa,yayin da abbas din ya tsirata da idanu yana kallonta ba tare da yace komai ba "Daddyn mimi,zuwa nayi na gaya maka ka jawa matarka kunne sanna kayi mana tsakan........" "Dakata da Allah"ya fada da kakkausar muryarsa yana daga mata hannu "Bana buqatar wata hayaniya ko tashin hankali,idan ba zaman lafiya bane ya kawoki ba..... please stay away from here" yadda yayi maganar yana nuna kamar ta gundureshi yasa ranta ya quntata sosai "Adalcin da zakayi kenan?,ba zaka tsaya kaji abinda akayimin bama.....dama kaine kakar daure mata gindi shi yasa kullum take kallon mutane sa'aninta,to wallahi......" "Shut up" ya miqe tsaye a zafafe yana nuna mata hanya "Fita banason hauka" hawaye ne suka balle mata "Yanzu a gabanta kakemin haka abbas?,na rantse da Allah......" Wani mahaukacin mari yakai mata wanda widad ta tabbata inda ya sameta saita rasa haqoran gaba,Allah ya taimaketa ta goce,ba shiri ta juya tana fita daga falon,hannunta dafe da kuncin nata cikin kuka kamar wadda marin ya sameta. Hannunsa cikin kana ya zauna yana yamutsashi,ya samu ciwon kan ya ragu amma tana neman maido masa bara bana,miqewa widad din tayi tayi mazauni gefans kamar zata shige jikinsa,da kalamai da hikimomi data koya ta samu nasarar saukeshi,ya dinga sauke ajiyar zuciya yana matsa hannunta dake cikin nasa,ba shakka mace ta gari rahama ce,inda bai samu widad din ba ashe da haka zai qare rayuwarsa cikin wahala da baqinciki?. A daren tason ya barta ta kwana sashenta ta kira hafsat din ta kwana tare dashi,tunda ita din na abinda zata iya masa amma yace bata isa ba,muddin ta tafi ranta sai ya baci,shiba wani abu yake buqata ba a situation din da yake ciki ba,koda batayi masa komai ba kasancewarta a damansa yafi komai kwantar masa da hankali. Kwanan daga fuskanci widad din tayi ya sake ingizata sosai,wutar qiyayya ta sake ruruwa a zuciyarta,ranar tayi kukan fili tayi na boye,ta kuma tsinewa duk wata kishiya dake duniya. Washegarin da akayi addu'ar bakwai suka shirya komawa kaduna bakin aikinsa,yabar widad a nan don ta gama arba'in dinta,taso komawa kano amma muhsin yace tazo kenan,dan tsoho alhj salim ya goya masa baya,hakama abbanta,don dole ta zauna a nan,amma ta koma gidan hajjaa ne saboda yadda gidan har yau yake bata tsoro. ********To sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da tafiya,al'amuran rayuwa kuma sukaci gaba da gudana yadda suke a baya,duk da ciwon rashin hajiya yana zukatansu,amma dole a yadda da hukuncin ubangiji a kuma rungumi rayuwa a duk yadda tazo. Zamanta gidan hajjaa taci gaba da samun kulawa,tana kuma sake gogewa da rayuwa da sanin makamarta. Sanda sukayi arba'in affan yayi wata qiba gwanin sha'awa,yaron kamar ka saceshi ka gudu saboda kyau da wani kwarjini da yake dashi,farat daya yake shiga ran kowa,hakanan itama widad din,kana kallonta zakasan lallai girma da hankali ya soma gameta,ta samu hutu da nutsuwar rai sosai a tattare da ita,ta zama wata big madam,ta kula da jikinta da kyau ciki da waje. Ranar da sukayi arba'in ranar abbas da yammaci ya diro,da safen sunyi waya da tace masa basuyi arba'in ba sai jibi,saboda batason yace mata zaizo,akwai abubuwan da takeson qarasawa,to ashe yana lissafe tsaf da kwanakin. Dariya nujood ta dinga yi mata sanda aka saukeshi a setting room,tana zaune dafa'an a qasan carfet sanye da wata riga me qaramin hannu mai kama jiki kamae robber,sai palazzo pants daya zauna mata sosai ya kuma bude yadda ya kamata daga qasa. Harara ta watsawa nujood din ta miqe tana cewa "Karki bari aji kanmu dake wallahi" tayi maganar tana zare ribbon dinta da yayi sakwa sakwa tana gayara gashinta,duk da cewa itama taji dadi qasan ranta,don ba qaramin kewarsa tayi ba,to amma kuma taso ta kammala komai ne "Bani nakar zomon ba" ta gama gyarawa tsaf ta duqa zata dauki affan nujood ta rigata tana cewa "Rufa masa asiri,kada a jawo masa a matse dan bawan Allah,ku gama gaisawar tukunna sai na kawo miki shi" ta fuskanci jan magana nujood din keji,sai bata sake ce mata komai ba ta juya ta fice. [5/14, 12:29 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 20 A tsaye yake yana fuskantar qofar shigowa falon,hannayensa duka zube a aljihun trouser din dake jikinsa,qananun kaya ne a jikinsa da sukayi matuqar dacewa da lafiyayyar fatarsa da kuma qirar jikinsa dake bayyana halittarsa ta qaqqarfan namiji. Tun kafin ta qaraso ya saka hannunsa ya zare baqin gilashin fuskarsa yana qureta da kallo,totally ta sake canza masa,kamar ba widad dinsa ba,a yanzun wata cikakkiyar mace yake gani,wadda komai nata ya cika goma cif cif,kama daga kyan halitta zuwa qirar jikinta,yanayin takunta mai daukan hankali wanda a baya yafi kama da na shagwaba,a yanzun ya zama wani irin taku me aji. Itama shi take kallo sanda ta shigo setting room din,uncle din nata ya canza,yadan rame kadan amma fatarsa tayi fresh sosai,manyan idanunsan nan masu matuqar kwarjini da fusgar hankalin suna tsaye kyam a kanta,sai kawai ya bude mata hannayensa,batayi qasa a gwiwa ba ta tafi a tausashe ta fada,ya maida dukka hannayensa ya kulleta gam yana sauke ajiyar zuciya yana rufe idanunsa "Welcome back abbas" ya furta da murya can qasa,saita daga kanta sa sauri tana duban fuskarta,dai dai sanda shima ya bude idanunsa ya zubasu cikin nata "Back from where?" Murmushi ya saki,ya kama tsinin hancinta yadan riqe sannan yace "from an unhappy life to a life full of joy and happiness" murmushi ya subuce mata,tayi juyi me kyau cikin qirjinsa,tana sake tuna kalaman sha'awa da tace indai mijinki yana jin kece rayuwarsa,indai mijinki yana jin bashi da sauran farinciki da walwala sai idan yana tare dake,lallai kincika mace,kin amsa sunan daya cancanci a hada miki da yabawa. Matseta yayi gam cikin jikinsa yana sansanarta da kyau,duk sai qamshinta ya ida rikitashi,ya fara kai hancinsa ko ina a jikinta yana sansanawa,kafin Wani lokaci sai ya nemi ya birkice mata gaba daya. Itama da qyar ta saita kanta,tadan tureshi tana cewa "Uncle,gidan surukanka kake fa" dauke fuskarshi yayi daga inda ya boyeta cikin jikinta,yana dan jan hancinsa kamar me mura,ya lalubo nutsuwa da qyar ya azama kansa "Oh.....haka.....ina fata kin shirya tafiya" noqe kafada tayi "Uncle,ban gama shiryawa ba,da saura fa" kai ya girgiza,ba zai iya tafiya ya barta ba a yau din,don shi kadai yasan yadda yakeji,shi kadai yasan irin azbtuwar da yayi watannin data dauka basa tare "Pack your stuff we will go home,ko mu wuce a kawo miki kayan daga baya" duk yadda taso ya bari ko zuwa dare ne amma yaqi,dole hajjaa ta kira uncle muhsin a waya ta gaya masa zasu wuce "Har sai an gayamin banda abinki?, shi da matarsa?,tunda ya tako da kansa yazo ya gaza haquri zuwa randa sukayi dashi ai kinga akwai dalili" "Amma uncle,akwai abubuwan da ba'a gama hada mata ba ko.kayanta ma bata shirya ba" "Kinga please stop it......ta bishi kawai,koma meye a aika mata dashi daga baya,tabar hada kayan sawar nata nujood takai mata su gobe ko jibi" hakanan aka bi umarnin uncle muhsin din,sukayi sallama sun cika da kewar affan tun kafin ma su qarasa barin gidan. Sanda suka isa gidan lawal ne ya buda masa gate yana masa sannu da zuwa,daga haka ya saka kai zai bar wajen,sai abbas din yayi kiransa,ya sanyashi debe dukka kayan da suka shigo dasu,yadan rusuna ya gaida widad,ta amsa tana mamakin yadda yau ya gaidata din ma,don dan dakin hafsat ne,ba wani magana bace take hadata dashi ba wanda ya wuce gaisuwa,gaisuwar ma da sai idan sunyi clashing sosai ba yadda zai wuceta. Ba kowa a gidan dama sai mai gadi,sai kuma lawal din da yana shirin fita suka dawo,don haka bayan ya fice gidan sai ya sake zama shuru. Tare sukayi aikin komai da komai,suka gyara part dinsa sannan suka koma suka gyara nata. Cikin lokaci kadan gidan ya koma fes,iska mai dadi hade da wani lallausan qamshi ya shiga kai kawo,ta gyarawa affan kwanciya saman dan qaramin gadonsa da abbas yasa aka hada masa,sannan ta fidda kayanta ta shiga wanka. Tana gama zare towel din jikinta ya tura qofar toilet din ya shigo,ta waiwayo a hankali suka hada idanu,kowa ya kafe dan uwansa da kallon nan mai cike da shauqi da wata irin qauna mai fusgar hankali tare da kewa,ya zame idanunsa a hankali ya saukesu kan qirjinta,wani abu ya jashi kamar lantarki,sai ya gaza ci gaba da tsaiwa a wajen,ya shigo ciki sosai,ya maida qofar toilet din ya rufe. Kayan jikinsa ya fara zarewa,har yanzu idanunsa yana kanta "Bari nayi joining dinki,ruwanki yafi nawa dumi da qamshi" ya fada yana fidda qaramin murmushi hadi da kashe mata ido daya. Kafada ta maqale a shagwabenta,kamar dai widad din nan da aka kawo masa lokuttan baya da suka shude wadda batasan komai ba "Allah uncle wayo dai,iri daya na hada mana fa,kaje toilet din naka ka dub......" Bata qarashe ba ta tsinceta manne da jikinsa,abinda ya kusa sanyata shidewar numfashi saboda yadda fatar jikinsu ta hadu guri guda,daga nan bakin dukkansu ya mutu ita dashi,wani irin feeling mai qarfi ya dinga kewaya cikin jini da zuciyarsu,sai gashi gaba dayansu kowa ya birkice tsananin ita dashi,wankan da ba'a ida gamashi ba,suka zarce zuwa gadonta daya samu kyakkyawan gyara. Kai tsaye zata iya kiran ranar da second first night dinta,don sai komai ya zame mata sabo kamar bata haihu ba,taci wuya a hannunsa,har shi kansa ya shaida hakan,tana rungume tsam a jikinsa,kwanyarsa cike fal da tunani,dama ana samun hakan bayan d'a ya tsaga jikin mace ya fito?,lallai da gaske mata suna suka tara,kamar yadda suka banbanta a abubuwa da dama haka suka banbamta ta wadan nan guraren. Sati guda sukayi a bauchi suna bare wani amarcinsu,irin amarcin da a baya ma bai sameshi ba,a yanxun ya samu fiye da abinda yakeso,ya samu fiye da yadda yake zato,ya kuma samu fiye da abinda yake tsammani,gaba daya widad din ta gama zama cikakkiyar mace ta kowanne fanni,yana samun fiye da abinda yake buqata daga wajenta,bata fannin kwanciya kadai ba..... a'ah,ta kowanne fanni ma ta cike masa dukka wani gurbi. Wannan yayi matuqar tasiri a rayuwarsa da zuciyarsa,ta sake shiga ransa da wani irin matsayi mafi girma da yakejin kaf kafin duniya a yanzu babu diya macen data takashi. Randa suka cika kwanaki bakwai ranar suka tattara suka wuce kaduna,kai tsaye kuma ya zarce da ita sabon gidan da ya kama mata,ya kama haya ne saboda bashi da tabbacin zasu yita zama a Kaduna,koda yaushe yanayin aiki yana iya canzashi daga kadunan zuwa wani gari na daban. Yayi mata ba zata matuqa,al'amarin kuma da ya faranta mata rai fiye da zatonsa,ko ba komai zata samu sakewa,ta rabu da wata matsalar,zata kuma tattara hankalinta ta kula da mijinta da kuma yaronta yadda ya kamata,gida ne two bedroom,kowanne da toilet a ciki,kitchen parlor da kuma dining area,sai madaidaiciyar harabar da zata iya dauke motar abbas din,yayi matuqar tsaruwa gidan,dole ya burgeka,an shirya komai bisa mizanin hankali da ilimi. *H AF S A T* Batasan cewa zata damu ba da gidan da widad ta koma din ba sai bayan ta koma din,tunda ita da kanta ta zaba cewar ba inda zata motsa daga nan gidan da suke,saidai ita widad din ta qara gaba ta barta,tunda itace babba,babu mai cire gwamnatinta. Murmushi kawai abbas ya saki sanda take wannan bayanin cike da izza fariya da kuma alfahari "Gwamnatinki saidai kuma wata,mai guri yazo mai tabarma dole ya nade abarsa" abbas ya fada cikin ransa,yana matuqar tausayin hafsat din amma ita sam bata tausayin kanta,yana hango mata rasa abubuwa da dama cikin rayuwarta amma ita bata gani,Allah ya sani,ko ra'ayin auren mata biyu baya dashi,ko meye ya faru tamkar itace ta bashi lasisin aikata hakan. Widad kam cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta tsara gidanta ta kuma ci gaba da tafiyar dashi,cike da qwarewa da kuma gogewar da take sake samu daga mutanen dake tare da ita,cikin ikon Allah ta hadu da maqota na qwarai,macace mai matuqar karamci dake kallon widad din kamar qanwarta,jininsu ya hadu qwarai tashi guda,wannan ya sanya widad din taja babbar 'yar matar da ba zata wuce shekara sha daya ba a jiki,aminatu yarinyar nada matuqar hankali,ta iya komai ita kewa mamanta ayyuka da yawa,amma yawan alkhairan widad a garesu ya sanya maman tabar mata ita,rainon affan da sauran 'yan aikace aikace ita take mata,wannan ya sake bata nutsuwa a zaman gidanta,tana dame debe mata kewa kuma ta rage mata ayyuka,saita samu cikakken lokacin tsara duk wani abu da zai faranta ran abbas ya kuma sake zaunar da ita a ransa. Gidanta yana dab da wajen aikin abbas,wanda ko a qafa zai iya takawa ya qaraso gidan nasa,abu na farko kenan daya soma hana hafsat sukuni,ta dinga tunani kala kala,a duk ranar kwananta bata da kwanciyar hankali harma ranar da ba tata ba,tana ganin a yanzu widad din ta fita samun kusanci dashi,kamar ko yaushe suna tare,kwata kwata a lokacin tunaninta bai bata hakan zai iya kasancewa ba,kawai a sannan tanaso ta nunawa widad ta koreta daga mazauninta ne don ta isa,ita kuma ta maye gurbinta,daga iya haka tunaninta ya tsaya. *F I T S A R I N F A K' O* Tunda ta dawo kusa ya daina cin abincin rana a ko ina sai gida,idan ayyuka sun masa yawa sai ya aiko yaransa su daukar masa,idan kuma ya samu chance da kansa yake dawowa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya koma,wani lokaci ma idan akayi sa'a aminatu ta fita da affan ko suna dakinsa sai ya more lokacinsa sosai sannan yake komawa din,a wannan lokacin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali daya jima bai samu irinta ba,don har wata qiba da murjewa ya sakeyi,gaba daya hafsat da matsalolinta ya sanyasu a mala,dai dai da abincinta ba damuwarsa bane yanzu,ita kanta ta lura da wannan sauyin daya sake daga mata hankali matuqa,har take ganin widad din ta fara aiki a kanta ne da 'yan tsubbu don ta janye hankalinsa daga kanta,ko sau daya a tsukakkiyar qwaqwalwarta bata taba shawartarta ta duba inda ta gaza ta gyara ba. **********Tunda ya sallameta a safiyar dazu data fita a girki ranta yake suya,komai nata yanzun ya koma yana shakulaton bangaro dashi,ta kalli inda ta ajjiye masa gantalallen breakfast din da ko ta kansa baibi ba ranta yana sake baci,zuwa azahar ta gaza daurewa,bayan mimi ta shirya kanta ita da nawwara ta zubasu a mota ta ajjiyesu a islamiyya duk da ba ita ke kaisu ba,sai kawai ta dauke kan motar tata tayi hanyar police college.[5/15, 5:51 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 21 Riqe yake da hannunta gam cikin nasa,yana sauraren shagwabarta da 'yar qaramar muryarta mai taushi,murmushi ne yake fita kadan kadan daga saman fuskarsa,har bayason ta dakata daga magiyar da take masa, sosai muryarta take masa dadi,ta narke masa sosai,ita kano takeson zuwa,shi kuma baya jin zai iya barinta a yadda yakejinta cikin rayuwa da zuciyarsa a yanzun tayi nesa dashi. Wata farar long sleeve blouse ce a jikinta fara sol,sai mini side button skirt a jikinta mai tsaga daya baya shima fari sol,ta kame gashinta mai tsaho da sulbi a tsakiyar kanta,jikinta ba abinda yakeyi sai fidda tattausan qamshin turarenta daya hade da kabbasar da takewa kowanne kaya nata da mabanbantan qamshin turare. Tuntuni ta gama haddace yadda yake mutuwar son yaga tayi shigar qananun kaya,wannan ya sanya ta mayar dashi al'adarta,don zata iya cewa ba zata iya tuna sau nawa ta saka atamfa kace ko material a jikinta ba muddin tana cikin gidan,walau ran girkinta ko ba ranar girkinta ba,har ya riga da ya zame mata jiki,hakanan fararen kaya na mugun yi mata kyau,da yake kuma ya hadu da mace mai tsafta idan ta saka saika dauka kowanne sabo ne bata taba sakashi ba. Gidan ba kowa shi yasa ta baje masa tabararta sosai,har yaji kamar bazai iya komawa gurin aiki ba,dama cin abincin rana ya dawo dashi,affan yana wajen aminatu,tun daxun gab fa zata gama abincin rana ta goyashi suka shiga gidansu. Waiwayowa yayi,har yanxu murmushi na bisa fuskarsa yana dubanta,sai ya zare hannunsa daga nata "Baby......wallahi kinason yau nayi satar kwana kenan,da irin wannan shagwabar taki zan kasa kaiwa yayarki kwananta fa" kai ta girgiza tana dan bubbuga qafa "Nidai ba ruwa na,abinda nace kawai inason naje kano,sanya ranar Aafiya za'a yi fa" "Ba yanzu ba baby.....idan bikin ya taso dai zakije" jikinsa ta shige tana fadin "Don Allah.....don Allah" dai dai sanda aka angizo qaramar qofar dake jikin gate din gidan aka shigo. Idanuwanta a kansu,zuciyarta na wani irin bugawa,wannan shine karo na hudu da zuciyarta ke raya mata yana gidan yarinyar,kuma idan tazo din take cimmasa,bata taba kuskuren zuwa bata sameshi ba. Waiwayawa sukayi gaba dayansu suna kallonta,widad ta janye idanunta tana jan tsaki can qasan ranta,ko daya bata sani ba,bata kuma gane dalilin wannan safarar da take musu a gida ba,bayan ita tunda tabar gidanta bata sake koda marmarin taka qafarta ba,idan ta shiga unguwar ma,mutanen da sukayi zaman arziqi tajewa jaje ko taya murna,daga nan kuma bata qarawa ko ina take dawowa gida abinta,duk da tanason ganin mimi amma haka take haqura. Dage tayi sosai,ta mannawa abbas din kiss a goshi a tausashe sannan tace "Allah ya kiyaye hanya,im gonna miss you baby" ta danyi rolling idanunta hadi da daga masa hannu,taja baya a hankali tana takawa zuwa cikin gidan,da gayya take juya mazaunanta da kyau,duk kuwa da cewa koda batayi hakan ba salon tafiyarta ne dake tafiya da abbas din ainun. Tare sukabi bayan nata da kallo shida hafsat din,nashi kallon na zallar qauna tare da jin wani iri,kwana biyu kawai da zaiyi ba tare da ita ba sai yakejinsu kamar shekara dubu,duk da zai leqota a qalla sau biyu a wuni kafin ya tashi a office,yayin da kallon hafsat ke cike da wani mugun baqin kishi,wanda a wannan lokacin inda zata samu dama tabbas saita nakasta wannan surar da akemata barazana da ita. Kasa jure ci gaba da kallonta tayi,sai take ganin kamar taqi sauri ta shige falonta ne da biyu,ta maido dubanta ga abbas din,saidai gaba daya hankalinsa baya kanta,kamar ma ya manta a inda yake tsaye,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,har taji ba zata iya magana ba,sai kawai ta juya da mugun sauri ta koma cikin motarta,wadda ko kasheta batayi ba saboda tsabar sauri ta shiga ta rufe murfin da mugun qarfi,taci ribas ta fice daga layin. Qarar buga murfin motar ne ya dauki hankalinsa,ya juya yana kallon qurar data tayar,sai a sannan ma komai ya dawo masa,yaushe sukayi da ita zata fita?,ya gyada kai ransa na mugun sosuwa,ya taka yana fita a gidan ya nufi tasa motar don ya koma office. Gudu kawai take shararawa a hanya,sauran masu ababen hawa dake bin hanyar sunata binta da kallo,wasu na kaucewa wasu suna Allah wadai da ita,kuka takeson yi amma idanunta sun soye,a bisa qa'ida ai ya shiga lokacin girkinta,karo na hudu kenan tana ganin irin haka,dama wannan shine dalilin da ya sanya ya canza mata gida ya kaita kusa da office dinsa?,zaizo zasu hadu,yau din saidai kowacce wacce. Batasan abbas din ya fita bacin ran fitar da tayi ba tare da izninsa ba,ba kowanne sakarci yake dauka ba ko kuma ya qyale,tunda suke da widad koda wasa bai taba kamata da laifin yin leqe bama bare har takai ga fita,fitarma irin tata mara tushe bare ma'ana,tunda me tazo yi gidan widad din a wannan lokacin?,abinda ta saba?,bin qwaqwafi da bin diddigin yarinyar da ta haifeta?,bai taba jin widad tayi zancanta ko ta damu da lamarinta ba,amma ita ko yaushe damuwarta widad,ko yaushe qorafinta yana kan widad din,sai yaushe ne zatayi hankali?,yaushe zata gyara halinta?. Lokacin da ya koma gida baibi ta kanta ba,hidimarsa ya shiga yi da yaransa,hatta da abincinta ma bai nema ba,ya shiga kitchen ya dafa musu wani bayan ya tambayi yaransa me sukeson ci. Banza ya bawa ajiyarta suka baje a qasan carfet da yaran suka hau cin abincinsu,kamar ma baisan da wanzuwarta cikin falon ba. Ta sake cika tayi fam kamar zuciyarta zata fado saboda yadda take mata ciwo,cikin sa'a za'a ce ko rashin sa'a mimi tace "Mummy ke bakyacin abincin?" "Zan tsinka miki mari,aiba a yunwace kika ganni ba ko?" Sauke idanunsa yayi a kanta a nutse,sannan ya motsa labbansa "Tashi kibar nan gurin" a dan fusace ta kalleshi,amma a kallo dayan ta karanci bacin ran dake kwance cikin qwayar idanunsa,saita miqe da wani irin qarfi tana kade jikinta,amma kuma ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Ki miqomin key din motarki yanzun nan" ya bata umarni nakai tsaye ba tare da ya ko dubeta ba " a mamakance ta juyo tana kallonsa,amma ko kallon inda take baiyi ba,ta dauke kai ta jinjina sannan ta taka zuwa ciki,ta dauko key din ta dawo ta ajjiye masa ta wuce daki wasu hawaye masu zafi suna qwace mata. Koma wanne karin magana bahaushe yayi akan kishiya,koma meye aka fada akan kishiya tabbas ya dace da ita,wasu baqaqen dabi'u da halaye da batasan dame zata kwatantasu ba abbas din ya koyo,saidai koma meye ita ba zata taba bari widad din taga faduwarta ba. *_A N K U M A M A C E T A H A I F I M A C E inji bahaushe_* Watan affan bakwai dai dai wanda yayi dai dai da samun qarin matsayin abbas din ya sake samun wani promotion din daga DSP(deputy Superintendent of Police) zuwa SP(superintendent of police) din gaba daya,wani irin ci gaba da budi yaketa samu tako ina wanda bai zaci samunsa haka a kurkusa ba. Randa aka saki signal sunansa ya fito widad din na falo a kwance,sanye take da wata armless chiffon gown,yatsunta na hannu da na qafa sunsha jan lalle jajir gwanin sha'awa,basu jima da dawowa daga wankin kai ba ita da aminatu,ta dauki affan suka fice sai ita kadai a gidan,gashinta mai tsaho santsi da baqi yayi kyau sai sheqi yakeyi,wannan gyara ne daya zame mata jiki jiddin zaka sameta cikinsa. Yau din ba ranar girkinta bane,sai a gobe zata karba girki,amma ta gama shirya tarbar abbas din tun a yau din,ta gama komai,zuwa yanzun yadda abbas din keyi a kanta ya daina damunta,ta riga ta saba,ya zamar mata jiki,hasalima tausayi yake bata,don ta tabbatar inda yana samun kulawa yadda ya kamata daga wajen hafsat itama zata samu sauqin wani abun,to amma ita daya ce ke iya kashe masa qishirwar komai,ita kadai ke tsaye a kansa take samar masa nutsuwa da kwanciyar hankali. Tunda ya duba sunansa yaga ya fito yaji har cikin jiki da zuciyarsa ita yafi dacewa ta fara sani,a nutse yake tuqa motarsa bakinsa dauke da hamdala da godiya ga Allah fili da badini,don yayi masa dukkan wata baiwar da rufin asiri,kuma dama a rayuwa baka taba samun komai cif cif dari bisa dari. A kofar gidan ya kashe motarsa sannan ya fito,yasa key ya buda gidan yana sanya kai,yau gaba daya aiki ya sashi a gaba,ko zuwa ya dubasun da yakeyi baiyi ba sai yanzun da ya samu break,amma da yake gwanar alkunya ce tare da yi masa uzuri,da sukayi waya ita ta fara bashi uzuri ma kafin ya bata. Lumshe idanunsa yayi sanda ya tura qofar falon,sassanyan qamshin nan na kullum da kullum dai shine a falon cakude da sanyin ac da aka daidaitashi dai dai da buqatar dan adam. A duniya gidanta ne waje na farko da yake fara saukar masa da nutsuwa a rayuwarsa,bazaiqi ya dawwama a cikin gidanta ba kaf rayuwarsa,yasan bazai rasa komai ba,ba kuma zaiyi kuka da Komai ba. Tana daga kwancen ta daga fararen idanunta masu girma ta.kalleshi,ta sakar masa murmushi tana miqewa daga kwancen ta zauna tana dubansa "Welcome home sir" tsaiwa yayi ya moqe kafadarsa kamar qaramin yaro yana kallonta "Ban yarda da wannan qwangen da akeson yimin ba" saita miqe da sassarfa ta isa gareshi,ya buda mata hannuwansa kamar yadda suka saba ta fada jikinsa,ya maida hannun ya lullubeta gam cikin qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,kamar yaron da yayi kuka ya qoshi "Alhamdulillah ala kullin ni'am.......na samu promotion,now am SP abbas" wani irin qanqameshi ta qara yi cikin wata siririyar qara "Seriouse abbin affan?" "Da gaske nake sarauniyata" ya fada a tausashe yana shafa sumarta da taja hankalinsa sosai,qamshin jikinta kuma yana neman birkitashi,yana jin yadda bugun zuciyarta ya qaru saboda murna,zamewa tayi a jikinsa ta kama hannuwansa dukka biyun,ta dinga jera masa addu'ar samun nasara tare da fatan alkhairi mai yawa a rayuwarsa,har sai da qwalla ta cika idanunsa,zuciyarsa ta tabu sosai. Mutum daya...... mutum daya ke tsaiwa tayi masa irin wannan,hajiyarsa,zayaso ace yau tana raye taga abinda ubangiji yaketa yima rayuwarsa. "Zan samu abinci madam" ya fada yana langabe mata kai,a gabanta kawai yake komawa hakan,inda zaka ganshi a fagen aiki zaka dauka bashi bane. Kafada ta noqe tana tura baki gaba "Girkin mummyn mimi ne fa daddyn mimi" girarsa ya daga "Yes i know....amma kinsan banason cin abincin waje baya ina da mata har biyu,gida kuma yanzun yamin nisa,infact ma abincinki nakeson ci,in kuma ba za'a bani ba to shikenan" ya fada yana komawa kamar wani abun tausayi,dole ya sanyata ta saki wata shagwababbiyar dariya "Ni na isa na hanaka abinci?,zauna sosai na zubo maka" tayi maganar tana miqewa,saiya riqo hannunta ta baya,ya kashe mata ido daya "Zafi nakeji,hadamin ruwa nadan watsa tukunna,yau aiki zai riqeni inajin har wajen isha" kai ta jinjina masa,saita sauya akalarta zuwa bedroom dinsa ta hada masa ruwan kamar yanda ya buqata sannan ta fito ta gaya masa ta wuce kitchen. Tana tsaka da shirya masa abincin taji yana kiranta,ta ajjiye warmer din ta fito. Tana tura qofar toilet din unexpected kawai taji an fincikota,ko kula dashi ma batayi ba,bata zame ko ina ba sai cikin bathtub,ta jiqe jalaf har saman kanta,tabi jikinta da kallo sannan ta waiwaya tana kallonsa ta gefe,don tuni ya mata masauki cikin jikinsa "Daddyn mimi......" "Shshshs....."ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa "Karkice komai,minti biyar kawai zakiyi ki tafi,ba abinda zan miki,kawai ina buqatar ki a jikina kamar haka" bata iya masa musu a wannan bangaren,saboda tasan koda ransa bai masa dadi ba bazai nuna mata ba,uwa uba kuma tasan ba inda zai samu hakan sai wajenta,saita lumshe ido kawai ta jingina da jikinsa. Sun kusa mintuna goma a haka sannan ta samu ta zame,haka ta fita da kayanta suna diga,sai data shiga bedroom dinsa sannan ta ciresu,ta dauki bababn towel dinsa ta daura ta nufi qofar fita don ta koma nata bedroom din ta saka wasu kayan. Gabanta yayi mummunar faduwa sansa ta bude qofar dakin,don kwata kwata bata tsammaci ganin mutum cikin falonsu ba,ta kafeta da idanu wani bacin rai yana taso mata,ita din wacce irin dabba ce?,don ta wuce a kirata mahaukaciya,haka kawai saika buda gidan mutane ka shigo babu sallama babu komai?,ba neman izini kamar naka gidan,yau kuwa zata nuna mata ta fita hauka da danyan kai,idan akace ta sake zuwa mata gida ba zata qara ba,saita fasa shiga nata dakin,ta tako a hankali ta nufi gurin tv dake aiki. [5/15, 5:51 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 22 Gifatatan da tayi shi ya fahimtar da hafsat dake zaune tana huci fitowar ta,ta bita da kallo daure da towel din daya bayyanar da kyakkyawar surarta da farar fatarta dake ta glowing mai daukan hankali saboda gyara da mai da sabulan wanka masu kyau data samu. Qamshinta ya cika mata hanci,ta gaza dauke idanunta daga kanta har zuwa sanda ta isa gaban tv din ta kasheta. Kashe tv din tayi sannan ta dawo ta sake wuceta kamar batasan Allah yayi wata halitta ba a wajen,ta sake nufar bedroom din abbas din cikin takun na isa,tana shiga ta maida qofar ta rufe hankalinta kwance. Gefan gadon ta koma ta zauna tana qissima abubuwa da yawa cikin ranta,bata taba ganin mace kidahuma irin hafsat din ba,sau tari idan ta zauna tana nazarin rayuwar abbas din tausayinsa kamata yakeyi,yana da matuqar kirki sanyin hali da qoqarin sauke haqqin da ya rataya a wuyansa,yana da mugun haquri,mutum ne mai nisan haquri sosai da kuma idan aka qureshi fushinsa yakanyi tsahon da ba kasafai yake sakkowa da wuri ba,tako ina babu digon match atare dasu,idan ka kalleta ka kalleshi ba zaka taba zaton miji da mata bane,to amma kuma kowanne bawa da kalar tasa qaddarar,TASHI QADDARAR KENAN. Yayi mamakin ganinta a zaune daya fito,yana goge jikinsa sa towel yana tsokanarta "Ko nazo na qarasa aikina ne kawai mu samu ladan me gaba daya?" Ya fada yana kashe mata ido,saita dan jefa masa hararar wasa yana karya wuya "Naqi wayon.....na yarda ka kashemin jiki,kazo dai ka rakani kitchen saimu debo kayan abincin gaba daya" "As you wish maaaa" yadda yayi maganar sai ya bata dariya,gefe guda kuma tausayinsa ya kamata,tasan yanzun nan jahilar matarsa zata jagula lissafi da kuma nutsuwar da ya samu. Tana gaba yana biye da ita daure da towel shima,yadda widad din ta tsara ma ranta kuwa haka ya kasance, idanun hafsat din a kansu ya fara sauka,saita miqe tsaye cak kamar wadda aka yiwa barin wuta,yayin da abbas ya dubeta cike da mamaki,take zuciyarsa ta fara tafasa "Da izinin waye kika fito?" Ya tambayeta da kakkausar muryar,maimakon ta amsa shi saita sauke dubanta ga widad "Shegiya la'ananniya,dama nasan yana wajenk......." "Dakatamin......karki qara kuskuren kirana da wannan sunan,idan ba haka ba wallahi zakisha mamaki na......tunda kike haukarki kinga na taba bi ta kanki?,saboda ni ba take nake ba,ta mijina nake,shine a gabana,ya samu farinciki da nutsuwa daga gareni,ta yadda zan tsaya gaban kowa na amsa suna na na mace,bawai muna mata ba,sannan zanji gamsuwa ba mata na rako duniya ba" ta qarashe maganar tana watsa mata wani banzan kallo,kallon da ya kusa fin maganar da widad ta yaba mata zafi,sai ta fige mayafinta ta watsar da jakarta "Yau saina nuna miki wace mace wace muna mata" "Karki kuskura ki sake taku ko guda daya idan ba haka ba yau zakiga abinda baki taba gani ba daga gareni" abbas ya fada idanunsa na sauya launi "Wuce" ya juya yana gayawa widad,saita fara taku a nutse fuskarta fes da murmushin d hafsat taji kamar ta watsa mata garwashin wuta a fuska. "Kana gani fa......kana kallon gaskiya kake taketa?,sau nawa ina kamaka a gidan nan abbas?" "Tunda kwartanci nazo yi saiki tsayarmin da haddi,da izinin wa kika fito nace miki!!!" Ya daka mata tsawar da sai da cikinta ya kada,amma taurin zuciya da tsaurin rai ya sakata ci gaba da tsaiwa tana dubansa "Dole ne ka fake a bayan na fita baka sani ba,tunda idonka ya rufe ka manta sanda na gaya maka bani da lafiya ko" kallonta yakeyi yana jin kamar ya yanke mata hukuncin da zuciyarsa ke raya masa ko zai samu sassauci daga abinda yakeji a ransa na zallar bacin rai "Idan kika qara minti daya tsaye a nan wallahi saikin raina wayonki" abinda ya fada mata kenan ya juya ya koma dakinsa. Tana kuka wurjanjan ta fita a gidan ta wuce titi ta samu abun hawa,bata jin zata iya jurar ci gaba da zama a garin kaduna,bata da sauran amfani a wajen abbas,ba wata soyayya ko qauna data rage tsakaninsu. Tsaf ta shirya abincin ta fito dashi bayan ta sauya kayan jikinta,da taga baya falo saita wuce bedroom dinsa. Ko towel din jikinsa bai cire ba,yana zaune a gafen gadon dafe da kansa,ta ajjiye abincin a nutse tausayinsa yana kamata,ta tako a hankali ta zauna gefansa tana dafa kafadarsa hadi da kiran sunansa a tausashe. Hannunsa dake dafe da kansa ya sauke, sannan ya dagashi zuwa gareta yana duban fararen idanunta da nashi idanun da suka rine "Kayi haquri....." "Na gaji widad.....na gaji,nayi duk iya bakin qoqarina,na kuma yi irin haqurin da nake ganin zan iya,shekara nawa?,shekara nawa amma har yau babu sauyi?,har yau jiya iyau,sai yaushe zata canza?" "Mai haquri baya taba tabewa daddyn mimi,kaci gana da haquri ko don yaranka" dan shuru yayi sannan ya fara magana a sanyaye "Ina da dubban hanyoyin da zan hukuntata,amma ta kowanne fanni idan na duba mafi yawan hukuncin da duk zan mata sai ya shafi yarana,inda ace bamu da zuri'a ko daya da ita,wallahi wallahi bazan zauna da ita ba" maganar ta daki widad sosai,don duk wanda yake wajen yadda maganar ta fita daga bakinsa zai fahimci tun daga qasan zuciyarsa ne. Sosai tayi qoqarin kwantar masa da hankali da dadadan kalamai da ban haquri,ta tayashi sukaci abincin tare duk da ba yunwa takeji ba,sannan ta taimaka masa ya sake shiryawa cikin wasu uniform din,don idan ya watsa ruwa da rana kamar haka baya maimaita kaya,takan tsokaneshi da cewa "Ban taba ganin police din da kayan aiki sukewa kyau irinka ba,hakanan ban taba ganin dan sanda mai tsafta kamar ka ba" murmushi yakeyi sannan yadan harareta "Kina nufin qazamai ne kenan?" Takan maida masa murmushin hadi da salute nashi "Afwa nake nema yallabai,ni na isa na fadi haka,kada kasa hukumar 'yan sanda ta kamani" "Waya isa,wane mutum,kina da Abbas turaki" ire iren hirarrakin da suke sakawa basa gajiya da junansu. Relief din da ya samu daga wajenta yasa zuciyarsa ta sauka sosai,ya kuma yi aikinsa cikin sukuni,sanda ya tashi komawa gida sai yaji kamar ya koma gidan widad din,amma hakan bashi yiwuwa,kodon yaransa da kuma hakkin Allah dake kansa. Daya koma din kamar wancan lokacin,baibi takan komai nata ba,hidimarsa yayi dasu mimi,gefan abincinta ma bai kalla ba,saida sukayi baccin ua debesu ya wuce dakinsa dasu,yabar musu gadon ya kwanta saman sofa bed. Da safe da wurwuri ya shiryasu ya wuce aiki,ya ajjiye mata kudin cefane,bayan ya zabge fiye da rabin abinda ya saba batan,yana sane yayin hakan,don yanason ko yaya ne ya horata taji a jikinta. Koda aka tashi daga aikin gidan widad ya wuce,bai koma ganinsu ba yadda ya saba,bai kuma kirata ba,baisan ya akayi ba washegari suna waya da lawal kawai yaji muryar su mimi,tsananin amaki ya cikashi "Suwa nakeji kamarsu mimi?" "Eh....eh sune" yadan fada a daburce,saboda yasan yadda akayi tahowar,baiso kuma yaji wani bayani daga bakinsa ba "Ok,shikenan yayi" abinda ya fadi kenan,don ba hurumin yaron bane suyi kowacce magana dashi ba,suka gama maganar da zasuyi ya kashe wayar. Duk yadda yaso yayi controlling fushinsa amma ya gaza,tattarawa tayi ta koma bauchi ba tare da izininsa ba kenan kwatankwacin abinda tayi masa wancan karon da yayi sanadiyyar haramta mata kaduna kwata kwata kenan?,sai ya sake daukar wayar ya fara kiranta. Sai da yayi mata miscal biyar bata daga ba,abinda bai taba yiwa wani dan adam ba,ya sauke wayar ya shiga gurin rubuta saqo ya aika mata da saqo kamar haka _Ki wuce gidanku har sai na nemeki_ Abinda ya aika mata kenan a taqaice,saqon da yayi mugun gigita mata hankali,ta fara kiransa babu qaqqautawa,amma sai shima yayi biris,daga qarshe ma da kiran yayi yawa sai ya kashe wayar gaba daya,widad dake zaune gefansa tana tayashi shigar da wasu bayanai system dinsa batasan abinda yake faruwa ba,sai da taji yana ta jan tsaki sannan ta kalleshi "What's...." "Shshsh....."ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa yana dan lumshe idonsa,saita dage kafada da gira tana murmushi,bata sake cewa komai ba taci gaba da tayashin,yayi qoqarin shima tattara duk wata damuwar hafsat din ya watsar. Kwana uku rak kawu hassan yayi kiransa,yace a jirashi sai ya shigo weekend,weekend din da baije ba sai da bayan wata guda cif!. Widad sam batasan me ake ba,taga dai ya dawo gidan gaba daya,ta kuma sake samun wata sabuwar zazzafar soyayya da kulawar data dinga sakata jin kunya muddin cikin mutane suke,takan tambayi kanta wai wacce irin soyayya abbas din yake mata?,tasha tambayarsa amma shima baida amsa illa yace "Min indillah" daga qarshe itama haka ta barwa ranta daga Allah ne,saidai tabbas ZUCIYA TANA SON ME KYAUTATA MATA,TANA KUMA QIN ME MUNANA MATA KOMAI SOYAYYAR DA ITA ZUCIYAR KE MASA. Suna sauka a bauchi ya wuce gidan kawu hassan din,don akwai maganganun da zasu tattauna,yanason wannan karon su halarci bikin qara musu girman da akayi,itama bata zauna ba tace zata je gidan uncle muhsin,da fari ya hana don mugun kishinta yakeyi,yace ta jira ya dawo ya kaita. Amma ta kafe da roqo da nacin ya barta,don akwai abinda take shirya masa,batason kuma ya sani sai ranar,daga qarshe da qyar ya yarda idan ya isa gida zai turo umar ya dauki motarsa guda daya ya kaita,ta saki murmushi sanda yake fita "Uncle dina" ta fada qasa qasa cikin murmushi,wani kaffa kaffa yakeyi da ita,hatta da kayan sawarta yanzun ya hanata saka wasu muddin fita zatayi,yafi ganewa kowanne dinki ma ayi mata doguwar riga sakakkiya. Abbas sun tattauna sosai da kawu hassan harma da yaaya sa'id da Bashir akan batun hafsat din,sun tausheshi sosai sun bashi haquri,yace yaji,amma su qyaleshi,ko zai maidata ba yanzun ba,ya fara gajiya yana son shima ya huta,ba wanda ya tilastashi a lokacin,babban wansa yaaya sa'id ne yace "Shikenan,zan nema kawun nata zamuyi magana,amma dai ka daure kaci gaba da haquri ko don zuriar da Allah ya qaddara a tsakaninku" "In sha Allah" ya fada cikin girmamawa,sun qyaleshin,suka ajjiye batun suka shiga tattauna sauran maganganun da ya shafesu. Kafin yabar gidan ya bawa umar key din motarsa yace ya dauko masa su mimi,saboda yanason su koma kaduna tare,ko don makarantar yaran. Abinda yayi matuqar bata mamaki da daga mata hankali kenan,a dauko su mimi fa?,to me yake nufi?,kada fa ya zamana ta fita kenan a gidan gaba daya,kada yarinyar ta zama sanadiyyar fitarta haihata haihata a gidan,ta kadu don irin hakan bata taba faruwa a tsakaninta dashi ba,amma ummanta ta kwantar mata da hankali "Kada ki damu,ki bada yaran,kinsan muddin ina raye bazan bari irin haka ta faru dake ba" hakanan ta daure ta hada musu tsummokaransu. Kafin abbas din ya dawo ita ta rigasu dawowa,ta gyara bangarenta da nashi,ta dora abinci,sanda yaran suka iso ta gyarasu fes ta canza musu kaya,sai gashi sun sake sunata walwala abinsu,musamman mimi data dinga fadin "Nidai wajenki zan zauna anty", murmushi kawai widad tayi "Dama ta wajena ce ke" abbas na zaune yana binsu da kallo,sai yakejin gidan nasa ya sake masa dadi, widad nata kai.kawo tana hidima dasu,affan yana hannun su mimi suna masa wasa,wanda inda mahaifiyarsu na nan basu isa su samu wannan damar ba. Waya ta shiga daki ta amsa,koda ta fito sai ya tsareta da ido,daga bisani kuma murmushi ya kubce masa "Madam.......tsakani da Allah ban yarda dake ba,me kike shiryawa silently" dariya takeson yi amma bataso ta bashi qofar da zai gane plan dinta "Siyar dakai zanyi" tayi maganar tana kashe masa ido daya,wani qawataccen murmushi ya subuce masa yana jin kansa fes cikin wata irin walwala "Girmanki ne,don kin siyar da DSP,har IG ma zaki iya siyarwa,duka girmanki ne" sai dariya ta qwace musu su duka biyun. Washegari bayan ya fita ta kuma tambayarsa zasu fita ita da yaran gaba daya,ya langabe kai a inda yake zaune "Babyn uncle.....ki jirani zuwa dare na kaiki please,wallahi banaso...... inajin kishin ki fita a kalleki,banason kihau motar haya" "Allah uncle ba zamu jima ba,kuma inda zanje din basa fitowa ai da daddare,don Allah ka turon umar ko ko muneer,saika bamu aron daya motar taka ya miqamu ya dawo damu" "Shikenan nan,amma awa biyu kacal na baku" "In sha Allah bazan wuce haka ba" ta amsa masa a ladabce.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 23 Wankin kai da qunshi akayi mata,haka suma yaran duka,sunata murna don ba'a taba musu gyara da lalle irin wannan ba,bata wuce awa biyun ba ta dawo,koda ya dawo gidam ya samesu da gyaran bai kawo komai ransa ba,tunda yasan dama already ita kullum cikin gyara take ta saba (qalubale gareki, keda bakya komai sai sallah ko idan zakuyi biki ko wani sha'ani na taro ya kama,mai gida har ya gane hakan,yara suyita tambayar umma unguwa zamu?,umma biki za'a yi,ba lalle ba gyaran kai babu kitso). *******Karfe hudu na yammacin washegari tayi wata kyakkyawar shiga cikin wani tsadajjen crystal swarovski lace,duk inda ta motsa ko ta gifta daddadan qamshi ne yake fita daga jikinta da wani irin qyalqyali mai daukan hankali. Ta nutsu ita daya daga can bakin gate,ta yadda abbas data kirashi gida urgently bazai gane abinda ke faruwa cikin gidan ba har sai ya shigo. Daga waje ya kashe motar,ya bude ya fito ya kulle yana kallonta cikin mamaki,tace yazo gida yanzu yanzu,yazo kuna ya tarar da ita cikin ido me narkar da zuciya da idanunsa "Wow......amma kin kyauta da kika kirani naga wannan kwalliyar kada nayi missing nata" ya fada yana murmushi,batace masa komai ba sai kama hannunsa da tayi suka shiga cikin gidan. Mutuwar tsaye yayi sanda yaga yadda aka maida harabar gidan nasa kamar wani event center,har yaushe akayi hakan bayan fitarsa daga gidan duka duka bai wuce awa uku ba,ko ina ya daga kai manya banners ne masu dauke da hotonsa cikin full police uniform a tsaye,da wasu rubututtuka na nuna murnar tayashi qarin samun promotion da yayi,ga family saman kujeraru da shigowarsa ta saka kowa miqewa yana masa maraba,a lokacin wani irin sassanyan abu yaji yana tsarga masa akan widad din "Ya rabbb,wacce irin yarinya Allah ya azurtashi da ita?" "Surprise?" Ya fada yana sauke idanunsa a kanta yana lumshesu cike da wani irin shauqi,saita jinjina kai lallausan murmushi yana kubce mata,shima kan ya jinjina,ya kuma kama hannunta da kyau cikin nasa ya fara takawa zuwa ciki suna riqe da hannun juna ya nufi yan uwa dake dakon isowarsa don a gaggaisa kafin a fara ciye ciye na abinda aka tanada a wajen. Cikin wani yanayi me kyau da qayatarwa aka kammala taron lafiya,abu yayi masifar qayatarwa,ya burge masoya, abokan adawa kuma da masu taya hafsat kishi kamar su mutu "Yar qanqanuwar yarinya ta iya kidifiri da iyayi,ta kora sa'ar uwarta uwar gida cikin yaranta gida tazo tana shimfida abinda taga dama" ire iren abinda su gwaggwo hassana da gwaggwo fanteka suke fada kenan,saidai babu bakin cewa komai saidai gulma daga gefe,hakanan kuma sukaci suka sha suka watse. Sai data tabbatar an sallami kowa harabar gidan ta barwa su shazali zasu qarasa gyarawa sannan ta dawo cikin gidan duba yaran,tasan bata da matsala don suna tare da aminatu,tare suka taho wannan karon. Aminatun kam akwai hidima,ba qyuya sam,harta sake musu wanka,affan da nawwara sunyi bacci,ita da mimi ne kadai suna kallo a ipad din widad da abbas din yabar mata kwanan nan,don dama itace bata da ita,hafsat nada tata duk da ta bari yara sun tsoma tatan a ruwa. Bayan ta tabbatar sunci abinci sai ta dauki affan tayi musu sai da safe,don ta gaji tubus,ta kuma ji shigowar abbas din tun kusan dazun ma tana waje tana sallama da mutane. Tana tura qofar suna hada ido,waya yake amsawa,da alama kuma mai tsaho ce,don haka ta daga masa hannu kawai,ta ajjiye masa affan ta kitchen ta hado musu baqin shayi me kayan qamshi sosai,don ya koya mata itama,sanann ta wuce toilet ta hada ruwa mai zafi tayi wanka. Daure da towel ta fito,fatarta sai sheqi takeyi,ya ajjiye wayar gefe ya miqa mata hannunsa,batayi qasa a gwiwa ba ta miqo masa nata hannun,yayi mata mazauni saman cinyarsa yana sansanarta,yana bala'in son qamshinta,ba qaramin burgeshi yakeyi ba "Sannu da hidima madam" murmushi tayi tana saqalo wuyansa da hannunta "Kaine da sannu yallabai,don dukka aikinka ne wannan" da mamaki ya daga kai ya dubeta,don dai shi yasan sisinsa babu a ciki,hasalima baisan zata shirya ba sai daya shigo gidan. "Aikina kuma?" Gira ta daga tana murmushi "Sosai,mun samu kyakkyawar kulawa daga gareka,ka sauke dukkan wani haqqi naka dake wuyanmu,wanann yasa har a cikin zuciyata naji ka cancanci fiye da haka ma,donma ni din ba wata bace,da fin haka naso ya kasance" cikin jikinsa ya qanqameta yana cusa kansa tsakanin qirjinta,abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,ya sauke mata zazzafan numfashin da dole ta riqe kansa da hannunta tana 'yar dariya "Ji nakeyi kamar na maidaki cikina na boyeki,zuciyata har wani irin zafi takemin saboda sonki" yana kaiwa nan saiji tayi ya watsata saman gadon ya kuma maye gurbin towel din jikinta. Washegari ta tsinci alert a wayarta da sunan mijin nata har na naira million daya,ta sameshi a bayan gidan shi daya da wasu takardu data tabbatar ayyukansa yake,da alama za'a baza komar kama wani mai laifi ne "Yallabai kudinka sunyi batan kan shigowa account dina fa,da saninka?" Takardun ya aje gefe,ita daya duk duniya yakema haka idan yana aiki irin wannan "Zonan" yace tana bata hannunsa,saita qaraso din ta zauna "Ba batan kai sukayi ba,sun shiga inda ya dace ne,nawa kika kashe jiya." Fararen idanunta tadan juya kadan "Bazance ba,amma dai bazai wuce three hundred thousand ba" kai ya jinjina "Kice duka tattalin arziqinki kika kwashe" saita saki dariya,kome zata bawa abbas din batajin zatajishi a matsayin asara "To yayi,kudin dana tura duka naki ne,inason ki zauna kiyi tunani ko kiyi shawarar sana'ar da kike sha'awa,inason ki fara kasuwanci cikin gida" sosai ya bata mamaki kamar yadda itama ta bashi mamaki jiya,ta sauko saman gwiwoyinta ta fara masa godiya,ya kamata ya tayar da ita "Ban miki komai ba,saboda ke din kin bani komai" *H A F S A T* Kai kawo taci gaba da yi,wayar hajiya habiba tana hannunta,duk hoto daya da zata bude tashin hankali ne yake sauko mata mara adadi,kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,abbas dinta mijinta da kuma yaranta,duka under control na widad,wacce irin asara take shirin tafkawa?. "Nidai gaskiya kin bani mamaki,am totally disappointed wallahi,ni duk sai kunya ta kamani ma da naga irin abinda akeyi a wajen,sai lawal ne ya bani address na gidan nan,shima yana daga gefe takaici ya isheshi,don dai bashi da yadda zaiyi ne". Kananun qwalla ce suka kubcewa hafsat,tana jin tata ta qare,duk wani abu da zatayi akan widad tayi amma jiya iyau "Aah,ai kuka bai ganki ba,mafita ya kamata ki nema" komawa tayi ta zauna,don gaba daya jikinta babu sauran qwari ko karsashi "Meye ma banyi ba,kissar nayi babu ci,malaman nabi amma sai abun yayi kamar zaiyi tasiri saiya wargaje" murmushi haj habiba ta saki "Malamai kika bi ko muna malamai?,hajiyata kiqi kudinki kizo na kaiki inda zaki mori kudinki,kissa kuma iri iri ce hakanan iyawa ce,ki fita batun yarinyar koda an miki aiki yayi,ko agabansa ki dinga nuna bata gabanki shine kawai" "Wallahi na shirya,ko nawa zan kashe a shirye nake,ai ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba" murmushi ta saki "Gwara da Allah ya ganar dake ai" (hmmm,kodai shaidan ya batar da ita,Allah yasa mufi qarfin zukatanmu,muje dai zuwa masu karatu,aci gaba da haquri,so nake mu sauke dukkan darasin dake ciki,saboda labarina yafi rinjaye da true life story)*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 24 Kafin su gama hutunsu a bauchi ta tattauna da mutanen da suka zame mata tamkar fitila a rayuwarta,su anty deena hajiya sha'awa dasu hajiya fanna,anty deena tace "Kina 'yar kano cibiyar kasuwanci ai baki da matsala,kaya kawai za'a yita kawo miki kina saidawa kina maido kudin ana sake miki sari" su hajiya fanna dake 'yan kasuwa ne suma sukace ba matsala zasu dinga karba,ta zauna tayi shawara da tunani ta zabi kayan da zata dinga saidawa,bata bar bauchi ba saida kayan suka iso,ta raba wasu suka wuce kaduna da wasu. Abu kamar wasa saiga kaya sunata shiga ana hada mata kudinta,hakan yayi mata dadi sosai,a cikin lokaci qalilan ta fara gane amfanin sana'a ga mace. Ta maida kanta sosai ga kulawa da mijinta da yaronta dake shiga watanni takwas,gasu mimi da takejinsu kamar yaran cikinta,bata da sauran matsala sai godiya ga Allah. Watansu daya da dawowa ya dauki su mimi ya maidasu bauchi kan mamarsu ta dawo,bata wani damu ba tunda zuciyarta babu wani mummunan nufi a ciki,saidai bataji dadin tafiyar yaran ba,don hatta mimi taso a barta amma hakan bai yiwu ba. *R U B U T A C C I Y A R K' A D D A R A* K'arfe hudu na yammaci,tana kitchen tana aikin abincin dare,affan yana goye a bayanta,don aminatu bata nan tana islamiyya,yau din ta dauko aiki me dan wahala,favourite foods na abbas din takeyi har guda biyu,don ma aminatu ta rage mata wasu ayyukan kafin ta wuce islamiyya. Knocking taji anatayi sosai,kamar za'a balla qofar,mamaki ya kamata,sam bata qaunar bugu me qarfi haka,taha tsaki ta share bugun ta qarasa juya miyarta sannan ta ajjiye ludayin ta nufi qofar tana tambayar waye da dan qarfi,saidai ba'a amsa mata ba har ta bude qofar. Tsananin mamaki ya kamata ganin abbas a tsaye,ya kafeta da ido kafin ya sanyo kai ciki,saita rabe gefe tana bashi hanya hadi da binsa da kallon mamaki,a hankali kuma ta taka ta bishi a baya jikinta na wani irin mutuwa. Sai da ya gama qarewa falon kallo tsaf sannan ya kalli wayarsa dake hannunsa ya maida dubansa gareta da murtukekkiyar fuskarsa "Ina kika je?" "Ni kuma?,ina zan fita ba tare da saninka ko izininka ba?,ina kitchen ina girki" "kina kitchen kuma?" Ya sake tambayarta cikin yanayi na rashin yarda sosai kwance a fuskarsa,abinda ya bawa widad mamaki sosai "Eh mana,uncle na taba yi maka qarya?" "Amma naketa kiranki baki dauka ba?,kamar kin fita ko kin tafi Wani wajen?" Idanu tadan zuba masa sannan ta sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai kawai ta kama hannunsa suka wuce zuwa bedroom dinta inda tabar wayar a ajjiye. Cak ta dauko wayar ta danqa masa a hannunsa,ya dubeta ya dubi wayar sannan ya bude "A silent take,ni na sakata saboda inason affan yayi bacci,kada kira ya shigo ya tadashi" wayar yadan juya a hannunsa kadan yana sauke ajiyar zuciya a jejjere,sai ya koma da baya ya zauna a bakin gadonta. A matuqar sanyaye ta fice,ta shiga kitchen ta bude fridge ta fiddo zobo me sanyi data hada masa da yaji kayan hadinsu abarba,daya daga cikin nau'ikan zobon data koya a class dinsu da deeja Berver (the best online class da na taba shiga da ya burgeni qwarai qwarai 0907 927 4454). Tason yana matuqar sonshi saboda taste dinsa na dabanne da ba ko wanne gida zaka shiga ka samu irinsa ba,shi yasa bata rabo da yi masa. Gabansa ta dawo ta durqusa ta soma zuba masa sannan ta miqa masa idanuwanta a kansa,bai musa ba ya karba ya kuma shanye tas ya miqa mata cup din,saita koma gefan gadon ta kwantar da affan sannan ta dawo gabansa ta zauna tana tattara nutsuwarta a kansa "Uncle,me yake faruwa?,kwanakin nan gaba daya idan ka kira wayata baka sameni ba sai hankalinka yayita tashi,sannan duka ka gaza nutsuwa a wajen aikinka,me yake faruwa?" Idanunsa ya lumshe yana kada kansa da yakejin ya masa wani nauyi,zuciyarsa kuma tana rabuwa gida biyu "I don't know,kawai dai.......ina tsananin kishinki" shuru tayi tana nazarin maganarsa,a baya yana kishin nata amma ba ta irin hanyar da yanzu yakeyi ba,ya canza kwata kwata,wasu irin halaye yake mata da suke sakata shakku,kamar zargi zargi,to amma tunda ya bata wannan hanzarin bata da hurumin masa hukunci kai tsaye "Ka kwantar da hankalinka uncle,ni taka ce har abada" qaramin murmushi ya subuce masa wanda baikai har zuciya ba,ya waiwaya yana kallon affan dake bacci abinsa hankali kwance cikin cikakkiyar tsafta da kulawa. Bayan wasu kwanaki da yammacin wata litinin,a yau din ba ita keda girki ba,don haka tun bayan kammala sallar la'asar ta gama komai.nata tana zaune,sai kiran ummu ya shigo mata,suka shiga hirarsu sosai tana wasa da hannun affan dake zaune saman cinyarta yana wasa da teether. A qalla sun kusa awa guda,suna gamawa kuma kiran anty fanna ya shigo,suka hau hirar kasuwanci da lissafin kudaden kayan widad din da aka saida wadanda suke hannunta. Daga qofar falonta taji ana knocking,ta dauki excuse tace zata kirata ta aje wayar ta miqe tana bude qofar,aminatu ce sanye da kayan islamiyya,hannunta riqe da waya "Aah,har an taso?" Widad ta tambayeta "Aah anty,yau korar school fees akeyi" dan bata rai tayi kadan "Amma sau nawa zan gaya miki,duk sanda wata ya qare ki dinga tunamin ina baki?" "Mamace tace na qyaleki hakanan,wancan watan kin kawo kayan abinci,yanzu kuma......" Sai maganarta ta katse saboda ringing da wayar hannunta ta fara,duka suka kalli wayar a tare "Wayar waye wannan?" "Wani ne,da uniform irin nasu abban affan,yace sunanshi samuel,oga ne yace wai a kawo miki wayar zakuyi magana" ta gane komai a dan bayanin aminatun,amma sai mamaki ya kamata,tasa hannu ta karbi wayar,kafin takai ga dagawa ta yanke,saita saki qofar ta juya cikin falon jikinta a matuqar sanyaye,abun na abbas har ya fara kaiwa haka?,meye haka mai qarfi ya shiga zuciyarsa dangane da ita?. Tana shirin zama amintu ta sunkuya ta dauki affan tana masa wasa sai gashi ya sake kira,batayi qasa a gwiwa ba ta daga wayar ta sakata a kunne tare da yin sallama. Maimakon ya amsa sai ya fadata da fada,ta runtse idanunta tana jin kakkausar muryarsa har cikin zuciyarta,sai ta miqe tsam ta wuce daki riqe da wayar tabar aminatu da affan a nan. "Ke dawa kuke waya?" Ya tambayeta bayan ya gama fadan rashin daga wayar da wuri "Nida ummu,sai kuma anty fanna" "Shine har kusan awa daya da rabi?" Mamaki ya sake cikata,to meye a ciki?,yasansu kuma dukkaninsu dama idan tana waya dasu tana dadewa "Eh lissafin kaya mukeyi da ita,ummu kuma dama kasan hirarmu ai" Shuru ya danyi sannan yaja tsaki ya kashe wayar. Duk yadda taso danne zuciyarta amma ta gaza saida hawaye ya silalo mata,wai meye hakan?,me yake faruwa?. Sai data dan koka kadan zuciyarta tayi sanyi sannan ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta shafa farar powder sannan ta fito. Har yanzu suna falo ita da yaron,ta bata wayar tace ta maida masa,sannan ta zauna ta dauki tata wayar tana dubawa. Tex ta rubuta masa na ban haquri,duk da abun naci mata zuciya sannan ta tura masa,saita koma ta zauna jikinta gaba daya babu qwari. Falon shuru saboda aminatu ta fita da affan,zuzzurfan tunani ta shiga tanason gano ainihin abinda ya kawo wannan lamarin tsakaninta da abbas din amma ta gaza gano komai,cikin haka ta kwashe awa kusa biyu,ta daga idanunta tana kallon qofa sanda taji ansa key ana qoqarin bude qofar. Tasan waye,don shi kadai keda key din gidan,miqewa tayi cak da nufin shigewa bedroom dinta,motsinsa da taji kadai ya karya mata zuciya,bata kuma so tayi kuka a gabansa,saidai ta makara,bata kai ga isa dakin ba ya shigo,kuma ya ganta,yana dauke da affan,da alama ya tsaya ya karboshi ne. Daga nan inda yake ya tsaya bayan yayi sallama yana kallonta,ta amsa amma bata juyo ba,sai ya tako a hankali ya iso bayanta ya rungume ta ta baya,saita sake masa kuka kawai.[5/17, 5:13 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 25 Kasa cewa komai yayi,sai zuciyarsa dake wani irin tsinkewa,sun jima a tsaye a haka har affan ya fara kuka,sai ya miqa mata yaron ya juya ya koma dakinsa yana jin wani yanayi mara dadi cikin ransa,yanason bata haquri ya kuma lallasheta ya kasa,sai bayan ya zauna cin abincin dare yake sake jadda mata "Ina tsananin sonki,ina kuma tsananin kishinki" bata da amsar bashi,amma batasan wanne irin kishi ko soyayya bane daya rikide yake son komawa ZARGI. Tun daga ranar data fuskanci haka saita daina doguwar waya don kada ya kirata bai sameta ba,hakanan ta daina nisa da wayarta,idan zaiyi kira dubu zata daga,don don kiyaye faruwar wata matsala da take gani kamar tana shirin kunno kai,da tayi hakan sai taga kamar abubuwan sun ragu,kira dai tana jurar dagashi,to amma ta barwa ranta hakan shine maslaharta. Ya koyi dawowa gida akai akai,sabanin baya da abincin rana kawai ke dawo dashi,a yanzu sai yazo gida sau hudu biyar kafin lokacin tashinsu a aiki yayi,tun abun yana mata wani iri har ya koma bata mamaki,tako ina ya koma wani irin tsauri da yake mata kama da ZARGI don yafi gaban kishi,amma tayi qoqarin dannewa,tare da bashi uzuri. Tafiya ta kamashi katsina ta kwana biyu,har sunyi sallama dashi kan aminatu zata dawo gidan ta zauna har sai ya dawo,amma bayan awa uku sai gashi da fahad,dan yayansa ne shima "Zai tayaki zama har na dawo" da to kawai ta amsa masa,don abubuwan nasa sun fada daure mata kai. A tafiyarsa ta kwanaki biyu ya dage da addu'ar Allah ya sassauta komai,ya kawo qarshensa,cikin sa'a daya dawo din sai taga abun ya ragu,satinsa daya da dawowar suka shirya zuwa weekend yadda suka saba,daga nan zasu maida fahad gida. *R U B U T A C C I Y A R K' A D D A R A II* Shigar yammaci suka yiwa bauchin,sanda motarsu take shiga gidan duka yaran suna farfajiyar gidan suna wasa saman kekuna,hafsat na tsaye da wata baquwa da alama sallama takeyi tayo mata rakiya ne. Dukka yaran suka kwaso a guje sukayo kansu suna murna tare da kiran sunan affan,harda yusra dake rarrafe,duka tyai budu budu da jikinta da qurar dake farfajiyar gidan,widad bata barta ta qaraso ba ta isa gaban yarinyar ta dagata tana mata waqa "Allah rayan.....rayan 'yar nan" sai kuwa ta bangale mata baki tana dariya,ta sanya yarinyar cikin jikinta itama tana dariya,duk da ajiqe jikinta yake,fitsari ne ko ruwa itama bata sani ba,yarinyar akwai fara'a sosai,shi yasa take sonta. Ga mamakin widad da hafsat ta dawo daga raka baquwar sai tayo wajensu "Sannu da zuwa daddy" ya daga kai da murmushi yana kallonta "Yauwa sannu da gida maman yara" ta saki murmushin jin dadi kadan,sai widad ta taka kadan ta gaidata. Ba yabo ba fallasa ta amsa mata sannan ta maida kanta ga mijinta suka fara hirarrakinsu,har widad taji tadan qosa da tsaiwar ta dauki qaramae jakarta ta cewa fahad "Shigomin da sauran kayan don Allah" sai tayi gaba ta barsu a wajen. Sai bayan kusan awa guda aka shigo mata da affan,a lokacin har tayi nisa wajen gyaran sashenta,ta karbeshi tana tambayar fahad ina duka yaran "Mamansu ta tafi dasu bagaren abbansu" saita gyada kai kawai tana cirema affan pampers dinsa,don ba kasafai take barinsa dashi ba don ba mai yawan fitsari bane. Ta kama kanta sosai game da lamarin hafsat dama tun ba yau ba,don sai ta gama zamanta a bauchi su koma bata bari hanya ta hadasu ba,to wannan zuwa hutun ma haka ya kasance,hatta dasu mimi ta janyesu,wannan bai damu widad ba,tunda koba komai itama Allah ya bata nata,affan ya isheta suyi sabgarsu a sassansu,ga kasuwancinta dake dauke mata hankali,wani lokacin saita share awanni tana lissafin kaya dana kudade. Uwa uba wannan zuwan ma da sukayi sai takejin jikinta duka babu dadi,yawan bacci da kasala gaba daya,ranar da ta karba girki washegari abbas din yana saman dining tana shirya masa breakfast yana riqe da affan yana masa wasa,ta kammala taja kujerar ta zauna ta fara saving dinsa,idanunshi a kanta harta gama ta daga kai suka hada ido "Lafiya yallabai?" Sai ya dage mata girarsa dukka biyun "Sonki nakeyi" maganar ta bata dariya har sai data murmusa "So na nawa kuma ranka ya dade?" "Na babu adadi,malala gashin tunkiya,ina sonki sosai,ina kuma kishinki widad,da ina da hali ko quda bazan bari ya sauka a kanki ba" ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyi tadanyi rolling idanunta tana kallonsa,ta yarda kai idanma akwai abinda yafi yarda ta yishi akan irin soyyyar da abbas keyi mata "Amma jiya kinsan kinci bashi na,kikayi baccinki kina barni da kewa" murmushi ta sakeyi tana dan rufe bakinta "Amma yallabai,ina jinka fa ka rage zafi sosai fa" fuska yadan bata "Hakan bai gamsar dani ba madam.....bana wani ganewa rage zafi,na ji na kasance tare dake kawai shine magana,kwanan nan kin koyi lalaci da dogon barci,ko so kike na qara aure oho" ya fada yana dan shan mur kamar da gaske. Idanu ta fiddo,saita fara bubbuga masa qafa cike da shagwabar nan tata tana masa kukan qarya "Haka kace uncle?,haka kace?" Dariya ya saki "Wasa naki miki wuddu na" ya dora affan saman dining din yana cewa "Idan na biyewa mamarka bazan fita ba,ina da aiki masu yawa,gobe ma kuma sokoto zan tafi daurin aure,zai yiwu ma mu kwana can sai jibi" "Allah ya nuna mana"ta amsa tana qarasa tura masa sauran breakfast din. *W A S H E G A R I* Tunda wuri ta gama masa komai na tafiyan yana kwance yana bacci,hatta da breakfast da ruwan wanka,sai data kammala ta shiga dakin,suna cikin duvet shi da affan suna baccinsu hankali kwance,ta saki murmushi har qasan ranta tana jin dadi idan ta kallesu,su din sanyin idaniyarta ne,kamarsu kullum qara fitowa takeyi da juna,kana ganinsa basai ka tambaya ba kasan mahaifinsa ne,tadan dora hannunta saman pillow din da yake kai ta soma bubbugawa a tausashe,ya motsa kadan saiya dora hannuwansa saman kunnensa ya rufe. Murmushi ta saki,ta gane ya farka tashi ne bashi da niyyar yi,saita gyara zama ta zame duvet din gaba daya daga fuskarsa,ta kamoshi ya maida fuskarsa,ta sake zamewa,sai kawai ya cakumota gaba daga ya mirginata ya danneta da dukka qarfinsa,sannan ya kama fuskarta ya riqe a tafin hannunsa saitin tasa,ya fara bude manyan idanunsa da suka qara girma kadan saboda barci cikin nata qwayar idanun,suka kuma dan canza launi kadan. "Na meye zaki dameni da tashin sassafe,bayan ke kika gajiyar dani jiya?" Ya fada da muryar bacci wadda tayi mata dadi qwarai cikin kunnuwanta,saita saki murmushi tana girgiza kai "Banda sharri uncle,ka fadi gaskiya" girarsa ya daga mata "Wacce gaskiya ce da tafi wannan,ni wani irin zaqi naji kina......." "Wayyo uncle,don Allah kada ka fada" ba shiri murmushi mai kama da dariya ya qwace masa,sai ya hade goshinsu waje daya "Don Allah ki barni na fadi irin abinda naji,da gaske nake widad,kullum sake dad......" Bata da zabi illa hade bakinsu da tayi waje guda,shi kuma hakan ya zamana kamar ta sake bashi dama ne,sai kuwa ya manne mata da kyau. Da qyar ta qwaci kwanta tana sakin numfashi,ta nuna masa agogo da yatsantsa "Lokaci yana tafiya, everything is ready" tayi tsalle ta fice daga bedroom din don kada ha biyota. Binta yayi da kallo yana murmushi,sai ya waiwaua gefan inda affan yake,sun tula masa pillows basu sani ba,ya gyara masa kwanciya sosai sannan ya fada toilet. Komai ita ta taimaka masa ya gama shi,yayi kyau cikin Wani lallausan yadi ruwan zama,wanda ya sake fitar da haibarsa da kwarjininsa. Widad dake tsaye tana qare ma kwalliyar tasa kallo,tana sake jinsa har cikin jininta tayi.magana qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta bayan ya ajjiye tissue din da ya gama goge sauran maiqon abincin da yaci,saiya zube hannayensa a aljihun wandonsa ya fara takowa inda take idanunsa akan fuskarta "Me kika ce?" Dariya take qoqarin dannewa "Bance komai bafa" da wani irin zafin nama ya kamota ya sakata sosai cikin jikinsa yana sansanarta "Kayi kyau da kwarjini,idan ka fita kamar ba kai ba,kamar ba kaine ka gama danne 'yar mutane dazu dazu ba,ko ba haka kikace ba?" saita zaro ido sosai,batayi tsammanin yaji abinda ta fada ba,girgiza kai ta fara yi "Don't say no.....na riga naji" juyo da ita gabansa yayi "I love you,ina kishinki sosai" ido ta lumshe tana mamakin yadda yake jaddada maganar kishin nan koda yaushe "I love you too" ta amsa masa a sanyaye. Har gaban mota ya rakoshi,tana tsaye suka fice daga gidan bayan ya leqa ya yiwa hafsat sallama,ita din dama can batasan rakoshi ba,saidai idan wani abun zata amsa tayi mantuwa ta biyoshi,ko kuma abinda zata karba din yana cikin motar tasa. *B A Y A N A W A H U D U* Misalin qarfe hudu na yammaci,tana kwancw a falo tana chart,affan yana kwance saman cikinta yayi bacci kira ga shigo wayarta,data duba da kyau sai taga abubakar ne,dan uwa ga mahaifiyarta wanda yake kamar mazaunin uba a wajenta,yana da matuqar kirki,ya kuma dauketa kamar diyar cikinsa. Kwantar da affan tayi,ta zauna sosai tana amsa wayar,suka gaida dashi sannan yace "Muna garinku,amma bamusan inda zamu iso gidanki ba,don wannan shine shigowarmu ta farko bauchi" sosai dadi ya kamata,iya zuwan da takeyi wajen mummynta kawai ta fahimci yadda sukeson mommyn nata,bama ita kadai ba,har su da suka fito daga cikinta "Ta wanne guri kuke?" "FAAZ hotels" "Bansan gurin ba kawu,amma zan tambaya saina taho daku" ta fada cikin murna,karon farko wasu daga dangin mahaifiyarta zasu kawo mata ziyara gidanta. Suna gama wayar ta kira abbas din don ta gaya masa zata taho dasu,saidai cikin rashin sa'a dukka layukansa is switched off,ta kira rose tace ta yiwa samuel magana ko tare suke ya cewa ogansa ya kirata,to amma shima ba tare dashi sukayi tafiyar ba,ta kusa minti talatin tana kira bata sameshi ba,sai ta miqe ta gyara yafen mayafinta ta fito farfajiyar gidan. [5/17, 5:13 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 26 Hafsat da lawal ta hango tsaye jikin motar hafsat din suna magana,da alama fita zasuyi ko kuma sun dawo,ba kasafai takeson shiga sabgarsu ba,amma yanzun dole tayi tambaya taji ta inane wurin yake tunda ba garinta bane,saita sauya akalar tafiyarta zuwa wajensu. Dif sukayi sanda suka ganta a wajen,hafsat ta dauke kai kamar bata ganta ba "Don Allah lawal ta ina faaz hotels yake?" Tambayar data fusgi hankalin hafsat,saita waiwayo ta zubawa widad din ido "Faaz hotel kuma?" "Eh nayi baqi ne zan taho dasu" "Okay" ya fada sannan ya fara mata kwantance inda yake ya qarashe da cewa "Kibi ta nan ahmadu bello way" "Aah,ta sa'adu zungur road kaman yafi" hafsat ta tsoma bakinta,bata kawo komai a ranta ba,cikin tsarkakakkiyar zuciya tace "Yauwa na gode" kamar tace lawal din ya kaita ganin suna rufe motar sun gama uzurinsu da ita amma saita fasa,ta shige part dinta da sauri ga sauya kayanta zuwa abaya wadatacciya tayi rolling,saita saba affan a kafadarta ta dauki key dinta da kudin napep da zai kaita ta fita,tasan ba zata jima ba,duka duka da zuwa da dawowar ba lallai ta wuce awa daya tunda basu da wani nisa sosai. Wani irin duumm yaji kansa yayi,ya sake daukan wayar jikinsa yana rawa ya kuma buda hotunan,itace dai..... widad dinsa ce dai babu canji, itace dauke da affan dinsa,yaron dake tsananin kama dashi "Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ya fada wannan karon har bakinsa yana rawa,kansa ya sara masa yasa hannu bibbiyu ya dafe,wani sashen na zuciyarsa yanata qoqarin kawo uzuri da kariya a gareta,amma wani sashen kuma yana qaryata haka hadi da sukan duk wani hanzari da zuciyarsa ke badawa,sashe mafi qarfi kuma mafi rinjaye kenan. A hankali sai zuciya ta fara ayyano masa irin abubuwan da suka faru a jiyan,ita tafara tashinsa a bacci,ta kuma shirya masa komai na tafiyar tun lokacin tafiyar baiyi ba,ta dameshi kuma ya tashi ya shirya kada yayi latti,hakan yana nufin dama akwai abinda ta shirya zatayi a ranar shiyasa take Allah Allah ya tafi?. Bayan nan yayi kiranta da yammar kusan miscal uku,bata biyoshi kiran ba,har sai cikin dare bayan bacci ya daukeshi,sai da safe yaga miscal,bata kuma sake nemansa ba,me hakan yake nufi,duka wadan nan abubuwan da ido yake gani ya zama gaskiya kenan?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya sake fada kansa yana qara sara masa sosai yayi qas da kansa yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani masifaffen zafi. Yafi awa uku cikin matsanancin halin da baisan dame zai kwatantashi ba,kafin daga bisani wata qaqqarfar zuciya ta yunquro masa,ya miqe ya fara hada kayansa,abinda sam baiyi shirinsa a sannan ba har sai zuwa gobe da safe. Bashi da kuzari ko qarfin halin da zai iya tuqi daga sokoto zuwa bauchi,dole ya nemi daya daga cikin yaransa da sukayi tafiyar tare ya bashi driving din. Tunda suka dauki hanya bai iya katabus din komai ba,sunci rabin tafiyar saiga kiran widad din ya shigo,ya kalli wayar sosai kamar widad dince a gabansa,zuciyarsa na wani irin bugawa,wani sashe na zuciyarsa na bashi izinin dagawa,wani sashen kuma yana hanashi tare da tuna masa girman laifinta a gareshi,daga qarshe daya sashen yayi rinjaye,sai yayi rejecting kiran,yama kashe wayar gaba daya,ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa,kanshi yana ci gaba da sara masa "Widad fa,widad" abinda zuciyarsa keta maimaitawa kenan cike da wani irin zulumi tashin hankali tsoro da kuma fargaba. Cikin mamaki ta sauke wayar tana kallon fuskar wayar sosai,zuciyarta na gaya mata rejecting kiran nata yayi amma ta kasa gasgatawa,saita katse shakka da mamakinta ta sake yunqurin kiransa a karo na biyu,saidai computer ta gaya mata wayar tasa a kashe take. Jim ta danyi,to kodai wayar tasa babu charge ne,ya qare sanda take kiran nasa?,bata sani ba,amma daga qarshe saita barwa kanta cewa hakanne,don baka ta miqe ta soma aikace aikacenta lokaci lokaci tana gwada sake kiransa,saidai babu wani abu daya canza,a kashe din dai take.[5/18, 2:15 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 27 Yamma lis suka sauka a bauchi saboda gudun da yaron nasa ya tsula bisa umarnin ogan nasa "FAAZ hotels zaka kaini" ya fada a wani galabaice,kamar yau ya fara doguwar tafiya a mota "Yes sir" ya fada yana karya kan motar tasu ya dauki titin da zai sadasu da hotel din. Karon farko gabansa yayi mummunar faduwa sanda suka isa gaban hotel din,abind aya jima baiji ba kenan,duk irin hatsarin aikin da zai shiga kuwa,zuciyarsa ta dinga masa saqe saqen munana abubuwa,tana ayyana masa adadin xuwan widad wajen,kamar wanda allurarsa ta motsa ya zunkuda cikin zafin nama ya buda murfin motar ya fice,bayan ya yiwa yaron umarnin ya zauna cikin motar ya jirashi,yanzu zai dawo su wuce gida. Cikin rashin nutsuwa yake takawa zuwa makekiyar qofar hotel din,hannunsa cikin aljihun wandonsa yana qarewa qofar kallo,duk da irin qwarewarsa a wajen aiki,duk da qwarewarsa wajen iya bincike amma a yau kamar an bude kwanyarsa an kwashe dukka wannan qwarewar,komai ya kwance masa,a haka ya isa ga security din dake zaune daga bakin qofar. Sallama yayi masa ya bashi hannu suka gaisa,ya gabatar masa da kansa gami da nuna masa ID card dinsa,ya jinjina kai "To na shiga ciki ne na sanar da manager zuwanka?" Kai ya girgiza da sauri ransa yana masa suya,yau wai shine zai gwada aikinsa akan widad?,yau shine yazo bincike hotel akan widad?,halittar da duk duniya babu ta biyunta a wajensa?. "Ba buqatar haka,personal investigation ne,tambaya daya ce kawai zan maka,idan akwai buqatar shiga cikin sai na sanar maka" "To officer ba damuwa" . Wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana rawa,ya buda hoton widad sannan ya miqa masa yana hadiye wani abu mai tauri a wuyansa,zuciyarsa kamar zata fashe "Zaka iya shaida wannan fuskar?,ina nufin ka taba ganinta a nan wajen naku?" Cira kai yayi daga kallon fuskar,ya shaidata sosai,matar da yayita jiya mamaki da yaji tana hausa,don bai zaci ta iya hausa ba "Tabbas jiya ma na ganta" "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ya furta yana saurin dafe qarfen qofar sanadiyyar jiri da yaji yana niyyar kayar da shi, idanunsa suka rufe na wucin gadi,da qyar ya samu ya daidaita kansa jin security din yana tambayarsa lafiyarsa lau?. "Na gode" ya fada yana karbar wayar daga hannunsa,sannan ya juya da wata irin tafiya yana nufar motar. Koda ya shiga sai ya saka kansa tsakiyar hannayensa yana jin kamar ana masa laguden tashin hankali,wani saqo can qasan zuciyarsa na gaya masa qarya ne,amma wani abu mai qarfi yana taso masa daga wani guri da baisan ina bane,yana gasgata masa abinda yake son ha zarga din "Idan hafsat kishiyace,bata qaunar ta,zata iya mata sharri,shi kuma wannan security din fa?,meye hadinsa da ita da zai mata sharri?,ga shaidu da suka tabbatar kuma da haka?" "Sir.......sai ina?" Muryar yaron ta kutsa tunaninsa "Kaini gida"ya furta ba tare da ya iya daga kai ya kalleshi ba. Farfajiyar gidan babu kowa,sai lawal dake zaune daga bakin gate yana yiwa hafsat CID din shigowar abbas din,ko karbar key din motar bai iya tsaiwa yayi ba ya wuce sashensa,yace lawal ya sallami yaron da kudi masu nauyi ya karba key din ya bayar cikin gida a ajjiye masa. Kansa a sama ya wuce sassan widad,hakanan yaji ko sassan nata bayason kallo bare ya hangeta. Da murnarsa ya kirga kudi ya bashin,ya karbi key din ya wuce sashen hafsat kansa tsaye baki har kunne,lallau yau ya warke,aljihunsa zai jiqe. Tana jin muryar sa ta fito da gudu gudu daga kitchen tana watsa hannaye idanunta a waje,irin na mutumin dake jiran wani kyakkyawan albishir "Ya ake ciki?" Dariya yadan saki "Da alama komai ya kankama fa,sassansa ya wuce yana tafiya da qyar,ga key dinsa nan" "Ma sha Allah,miqomin shi,ina zuwa" ta fada tana karbe key din,saura kadan ta fadi saboda yadda zaninta ke hardeta ya fice daga falon. Ba abinda ya iya cirewa daga jikinsa banda takalminsa,sassan fes wanda yake da yaqinin gyaran da widad din tayi ne randa zata fita a girki,abinda ya sake dagula masa lissafi,da qyar ya iya zama saman kujerar. Duk inda ya kwaso lissafin sai ya wargaje masa,yaji har cikin zuciyarsa yana qyamarta sosai,haske da tagomashin data samu cikin zuciyarsa wani qaqqarfan abu yana shirin tasowa ya lullubeshi fes!!! Ta yadda ko burbushinsa ba za'a samu ba. Sai data dan tsaya ta saita nutsuwarta a bakin part din nasa sannan ta tura qofar tayi sallama,bata ko duna yanayin shigarta ba dake a jikirce,wata rigar kamfala da sukayi anko ce ash color da aka yiwa dinkin half bubu,ta daura zanin atamfa a sama,sai dankwalin kamfalar a kanta data masa wani dauri kamar na 'yan talla. Sosai kamfalar ta fidda duhunta,don dama daqyar tayita,don kala ce dake nuna baqinta,wannan yasa bata cikason abu ash ba. Da qyar ya bude idanunsa ya watsasu a kanta yana amsa sallamarta,sai yaji kansa ya sake sarawa,ya zuba mata ido harta iso gefansa hannun kujerar da yake kai "Sannu da zuwa daddyn mimi" "Yauwa sannuku" "Ya hanya?" "Alhmdlh ya yaran?" "Lafiya lau,sun gaji da jiranka sunyi bacci,yau kayi delay na dawowa,hala ka tsaya wani waje ne?" Kai ya girgiza mata,haka kawai yaji baiso tasan damuwarsa,tunda dama asalan basu saba haka da ita ba,batasan damuwarsa ba,shi daya yake cinye kayansa yayi solving dinta,saiko hajiyarsa Allah ya jiqan rai,ita kuma ba kowacce damuwa yake gaya mata ba,saboda kiyaye lafiyarta "Sokoto to bauchi kinsan tafiyar ba kadan bace" saita gyada kai "Ummmm,kuma fa hakane" daga haka shuru ya biyo baya a tsakaninsu,tanason taji ya sake cewa wani abu, tanason taji koda kalma guda daya daga bakinsa amma yaqi magantuwa,daga bisani ma sai ya miqe yana shirin shigewa bedroom dinsa "Baka buqatar komai?" Bayajin zai buqaci wani abun,amma kuma idan baice komai din ba bazata qyaleshi ya huta ba,a yanzun kadaice kawai yake buqata ko zai samu sararin yin tunanin mafita ga gagarumin ibtila'i ko musibar data afko rayuwarsa "Ki kawomin black tea" "In sha Allah" ta fada da wani yanayi da sam bata saba ba,hakan ya sanya ma abun bai wani karbeta ba. Ta gama shirya komai tsaf sai zaman jiransa da takeyi,tayi shiga irin wadda tasan yana tsananin so,tayi kewarsa kwana dayan nan kacal,ya shiga rayuwarta da yawa,ko yaya suka nisanci juna dukkansu saisun galabaita,ta samu wasu satar amsoshi da yawa a group dinsu na hanyoyin da zaki sake tsayewa mai gida a rai da takeson ta gwadasu a yau din,ita ta yarda da kanta,ta kuma yi imanin ta tsaya a rayuwar uncle din nata yadda ya kamata,amma kullum tunaninta da burinta shine taci gaba da tsaiwa a wannan matakin ba tare data cutar da abokiyar zamanta ba. Har aka idar da magariba tana sake gwada wayarsa amma still a kashe,sai abun ya soma bata tsoro,tayi Shuru saman abun sallah,cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa lafiya,ta qiyasta wasu awanni,indai suka shude bai iso ba,bai kuma bude wayarba zata magantu,ba zata iya jurewa ba. Har isha'i shuru,don haka bayan ta idar da sallar isha din saita zura slipper dinta ta dora babban hijab saman qananun kayan jikinta sabbi fil data saka sabodashi,ta fito farfajiyar gidan tana neman fahad. Da motarsa ta fara yin ido hudu,mamaki ya cikata,sai taja burki kawai tana kallon motar,yaushe ya shigo?,shine tambayar da takewa kanta,amma saita bawa ranta qila tana tsaka da sallah ne yanzu yanzu shi yasa bataji ba. Muryar fahad taji a bayanta,saita waiwaya "Yaushe daddy ya shigo ne?" "Kai ai ya kusa awa biyu inajin" "Ok inajin ya leqo ina ciki" ta fadi yana qoqarin danne damuwa da mamakin nata dai,sai tayi gaba tana cewa yadan duba mata affan a falo kada ya tashi ya fara koke koke. [5/18, 2:15 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 28 Ba kowa a falon,saita saka kai zuwa bedroom dinsa,ta isa bakin qofar ta murdata ta tura tana saka kanta ciki. Dai dai sanda yake tsaye gaban madubu yana goge kansa da fuskarsa da qaramin towel,ya qurawa fuskarsa idanu da kyau,sai kace wanda yake karantar wani sabon abu daya tsiro masa a fuskar,saidai duka ba haka bane, zuzzurfan tunani da ya cika zuciyarsa fal. A hankali idanunsa suka sauka akanta ta cikin madubin dake gabansa,amma sai ya janye idon yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da goge jikinsa. Ko sau daya a tsahon zamansu bata saba ganin haka ba,don haka bata kawowa ranta wai ya ganta ba,saita fara takowa cikin shagwabar nan tata data saba masa tana cewa "Ya da haka uncle?" Ta fadi tana kebe fuska kamar zata sakar masa kuka,duk kuwa da cewa ranta cike yake fal da wasi wasi. Bayajin zai iya kallon fuskarta a sannan,saboda wasu abubuwa da zuciyarsa ke sake saqa masa a kanta,sai ya barta bai tanka mata ba,har ta iso bayansa,ta rungumeshi tsam ta bayan,tana dora hannuwanta saman ruwan cikinsa. Qamshin turarenta da abaya yafi qaunar ji fiye da komai,a yanzun sai yaji dadinsa yana sauyawa zuwa wani abu da yafi qyama hadi da tsanar shaqa "Uncle?" Ta sake kiransa a shagwabe,kanta kwance a gadon bayansa. Ajjiye towel din hannunsa yayi saman madubin,sannan ya saka dukkan hannuwansa biyu ya zare hannunta dake saman cikinsa,har zata fara masa tabarar tata ya waiwayo suka hada ido,sai tayi sak tana kallonsa. Wani abu take gani yana wulgawa cikin qwayar idonsa, irin abinda bata taba gani atare dashi ba,wani irin kallo da ya sanyata jin ta muzanta gaba daya,kallon da ya sakata ta daburce ta kuma rude,sai kuma ya dauke kansa daga dubanta ya taka gaba zuwa wajen drower dinsa don ya fidda kaya,ta taka da hanzari ta cimmasa,ta kama murfin drower din da nufin budewa ta zaba masa kayan kamar yadda ta saba masa amma sai ya dakatar da ita da kakkausar muryarsa "Stop,bashshi kawai" abinda yayi mugun sanyaya mata jiki,yau me ya samu uncle?,me ta aikata masa yake zuwa da baqin halayen da bata taba ganin irinsu tattare dashi ba. Tsabar mamaki yasa tayi sakato tana kallonsa,har ya ciro kayan ya dawo gefan gado ya fara fidda na jikinsa don ya saka wadan nan. Har yau bata iya kallonsa naked don haka ta russunar da idanuwanta,amma jin muryar hafsat daga falo tana doso dakin ya sanyata zabura ta isa gabansa,ta dauki rigar ta fara ware masa fuskarta qunshe da murmushi tana jira ya gama saka boxer din ya karba,a haka idan ka kallesu saika dauka soyayya ake bugawa a lokacin. Sak hafsat din tayi wani idin abu na bugunta "Kan jar uba!,kada dai ace wannan plan din ma score zero point," shine ya fara zuwa mata ka,da kuma irin kudaden xaga narka. kamar ta juya da tea flask din kuma saita fasa ganin ya ganta,ta tufa qofa ta shiga idonta akan widad da babu alamun akwai abinda yake damunta. Cikin son nuna bariki ta qaraso cikin daki "Gashi abban mimi,akwai wani abu da kake buqata kuma?" Kai ya girgiza mata,saita jinjina kai "Alright,idan akwai sai kayimin magana" "Thanks" kawai yace muryarsa can qasa, saita juya tana ficewa kamar babu abinda ya dameta dasu,saidai can qasan ranta tana jin kamar ta juyo ta dawo cikin dakin ta kora widad din. "Ehen......yauwa uncle,ni zan saka maka da kaina please,ka barni na samu wannan ladan" ta fadi a shagwabe da qarfi tana kallon bayan hafsat,dai dai sanda taga tana shirin ficewa a dakin. Aikuwa maganar ta daketa sosai,don da qyar ta iya cinyewa bata waiwayo ba,saita dan qara sauri cikin tashin hankali ta fice ta isa sassanta. Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta,yasa hannu ya damqe rigar dake hannunta "Jiya ina kika je?" Gabanta ya fadi,wani tsoro da shakkar gaya masa ya kamata,saita saki murmushi "Jiya?,bako ina,ina gida" idanunsa duka ya lumshe "Ya Allah,ta tabbata......lallai ta tabbata" "Please do me a favor" ya furta idanunsa a lumshe ba tare daya bude ba,don bayason kallon fuskarta kwata kwata "Name uncle?" "Stay away from here,i need space" gaba daya sai jikinta ya hau rawa,to amma saita hanawa zuciyarta samun rauni "Ok shikenan" ta sakar masa rigar ta juya a sanyaye,harta kusa fita ta jiyo lallausar muryarsa yana cewa "Karki matsawa kanki,ki kwanta a sashenki kiyi baccinki" da qyar ta hadiye wani abu da ya taso mata,ta gyada kai ba tare data juyo ba ta fice da sassarfa. Sai daya tabbatar ya kulle sashen nasa sannan ya dawo ya zauna,wani baqinta na sake ninkuwa a ransa,zarginsa kuma na sake tabbata, widad da baisanta d qarya ba ko misqala zarratin yaushe ta fara qarya?,lallai akwai qamshin gaskiya a dukka abinda yake zargi. Wata baqar zuciya da baisan ta inda ta shiga qirjinsa ba ta dinga kambama abun tare da qara masa muni a idanunsa,wanda daga qarshe ta tayashi yanke mummunan hukunci akan widad din. Karon farko a rayuwar aurensu da Wani abu me suna bacin rai da batasan ta inda ya samo asali ba ya raba makwancinsu a ranar da yake girkinta ne,ranar da babu ranar da uncle din yake zumudin zuwanta irinta,ta rungume affan tsam a qirjinta tana ta juyi,ta lalubi bacci kaf a idanunta ta rasashi,ba irin tunanin da baizo kanta ba,amma saita taushi zuciyarta take gayawa kanta wata damuwa yake ciki wadda qila bayaso su sani,tunda a gabanta hafsat ma ta fice,amma bataso haka ba,batason ya dinga aje damuwa a ransa,tafison suci gaba da sharing problems dinsu tare suna samo solution yadda suka fara tun farko. Sai tsakiyar dare ta samu bacci ya dauketa,kiran sallar farko kuma ta farka a firgice saboda wani mafarki mara dadi da tayi,sanda ta idar da sallar asuba ta fuskanci saqo ya shigo wayarta,data duba saita saki murmushi,zuciyarta na saki daga damuwar data kwana cikinta,ranta yana mata fari sosai _ki shirya around 10 zaki rakani katsina,wani aiki ya tasomin,but basai kin shigo ba,idan kin shirya kawai ki fito gaba daya_ Dadin da taji a ranta yasa ta miqe tun lokacin ta fara shiri,ta fara da hada masa lafiyayyen breakfast,farfesun kaza da yaji spice masu dadi,sannan ta masa hadadden spicy tea,gefe daya ga wani irin chips dake cakude da qwai,sannan ta gyara sashen,tayi wanka,sai a sannan affan ya farka, yaron yana da haquri sosai,ba kasafai yake hanata aiki ba,ta dagashi tana masa miqa hadi da karanta masa addu'ar tashi daga bacci sannan ta rungume shi tana kissing dinsa hadi da tambayarsa "Ka tashi lafiya uncle dina na kaina?,yau kaji baccin ka daban ko?,munyi missing daddy dukkanmu,karka damu,we have a trip tare da daddy,na tabbatar we will enjoy it in sha Allah" saita saki murmushi tana shafan kan yaron,sannan ta miqe dashi ta masa wanka a toilet suka hau shiryawa. Kayan data sawa yaron ya dace sosai sa shigar atamfar da tayi,atamfar tayi mugun karbarta kamar don ita aka bude kamfani atamfa,ita kanta sanda ta tsaya a gaban madubi tana kallon fuskarta a tsakiyar mayafin kanta ruwan zuma sai data burge kanta,ta saki murmushi tana jin dadin yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace me iya dressing me fusgar hankalin mijinta, cikakkiyar macen da duk inda ta shiga za'a waiwaya a kalleta,ta tashi daga sakaltacciyar widad din ummu,ta zama classy madam din abbas turaki. Fahad ne ya shigo yana gaya mata "Uncle yace ki fito anty" "Breakfast dinshi fa,kace a kawo masa na gama" "Okay bari na gaya masa" sai ya juya ya fita,ba jimawa ya dawo ya gaya mata yace he's okay,bazai iya cin komai yanzu ba,sai abun yayi mata banbarakwai,bata taba masa tayin abinci koda ba ranar girkinta bane ya tankwabar bare kuma ranar girkinta,don haka sai ta share wannan maganar ta shirya abincin cikin wani basket mai kyau da daukan hankali,na musamman ne da tasa akayi mata da dukka favourite colors na abbas din don saboda shi din, kome zatayi tana yin sa da colors ko yanayin da tasan zabinsa ne,bata taba duba nata choice din,wannan ya sake sawa ta kama zuciyarsa da kyau. Fahad ta bawa kwandon,ita kuma ta kulle sashen nata,ta saka affan a kafadarta ta fito. A seat din baya yasa fahad ya saka kwandon,karon farko da ya rasa duk wata sha'awa na cin abincinta,bama abincinta kawai ba,gaba daya yayi loosing komai da yakeji a kanta,sanda ya daga ido ya hangeta tana takowa,gaba daya ta haske farfajiyar gidan da wani irin kyau da qamshinta daya fara aika saqon tahowarta kowanne sashe na gidan,ita da yaron sunyi wani kyau na kusamman kamar fure,saiya dauke kansa ya maida gefe,yana jin zuciyarsa na masa matsanancin bugu kamar zaya fado daga qirjinsa,abubuwa hiyu suna gogayya cikin qirji guda daya lokaci guda SO YAYYA DA KIYAYYA,soyayyar nason tasiri,amma wani abu mai nauyi yana tasowa ya danneta yana baiwa qiyayyar damar wanzuwa a farfajiyar qirji da zuciyarsa,zuciyarsa na kwadaita masa ya sake kallonta,don ta fito a kamar da yakeso,amma tsananin haushinta ya danne wannan muradin da ransa ke dashi,don haka kafin ta qaraso ma ya shige cikin motar yana haki qasa qasa. Mamaki ya sake cikata,da kansa a irin wannan lokacin yake takowa ya karba affan daga hannunta ya bude mata motar ta shiga sanan ya miqo mata shi,jiki a sanyaye ta qarasa motar ta bude ta shiga ta zauna, qamshinta ya qarasa baibaye ilahirin motar "Ina kwana uncle" ta gaaidashi tana dan rusunawa,ya amsa a taqaice ya miqa hannu yana karbar affan,tsam ya rungumeshi a qirjinsa hana jinjina hukuncin da zai yanke wanda har yaron zai shafa,amma dai wannan shine maslaha a wajensa,don yana ji a zuciyarsa bazai taba iya zama da fasiqar mace ba "Why widad why?,ta ina na gaza?" Ya fada can qasan ransa yana jin wani ciwo,saiya sunkuya a sanyaye yayi kissing goshin yaron ya saka masa dariya kuwa,sai zuciyarsa ta karye,ya miqa mata shi ba tare daya sake kallon fuskarta ba,don kallon fuskarta na gaya masa wani fa ya taba tabata,wani ya taba rabar wanann jikin nata,wani ya taba kwanciya da ita yadda kakeyi,tunanin da yake sakashi jin kamar zaiyi bindiga. Duk yadda taso yaci abincin ya qiya,dole ta qyaleshi,tayita sako hira a hanyar tafiyar amma yana banzatarwa,ta jinjina kai tana mamakin wacce damuwa ce haka ke damunsa?,don kada fa takura masa daga qarshe sai tayi shuru itama, motar kamar ta kurame,tafiya mara dadi data fara yi dashi tsahon rayuwarsu dashi,har daga qarshe bacci ya dinga daukarta,dama yau din bata samu tayi baccin nata data saba ba. Lokacin da zasu gifta kano sai taji kamar ta sauka yaje ga ummunta,amma dole ta danne,koshi bata cewa komai ba,batason ta dameshi da magana,tunda ta fahimci a yanayin rashin son magana yake. Sai bayan azahar sannan suka isa magariba,ta ware idanunta sosai tana jin kewa da shauqin mommynta,tana jin dama ya ajeta wajenta duk da rakiyar aiki tayi masa,ga mamakinta sai taga ya dauki hanyar gidan nasu,ta kasa haquri sanda taga sun shiga unguwar su "Na gode uncle" kansa kawai ya daure ya gyada mata ba tare da yace komai ba. A qofar gidan yayi parking,cikin sa'a usama daya daga cikin qannenta maza da mamarta ta haifa a gidan ya fito,cikin zumudi da murna ya qarso wajen,suka gaisa da abbas sannan ya fidda mata kayanta "Kakaimin jakar kazo ka karbi affan" saboda yadda taji qafarta da mararta duka sun riqe mata gam. Yana shiga ya fito ya karbi affan din suka shige ciki suka barta,ta buda murfin motar,saidai har a sannan abbas din baice mata komai ba,sai ta dakata da fitar ta waiwayo "To sai yaushe kenan?,sannan a nan zaka sauka?" Kai ya girgiza mata alamun a'ah,ya bude bakinsa da yakejin kamar ya manne yace "Ki zauna kawai,sai lokacin dana gama aikin,zanzo na daukeki" duk da yanayin da yayi mata maganar yana saka mata rashin jin dadi a ranta,saboda ba yanayin daya saba mata mu'amala dashi bane,amma jin zata dan zauna a gidan ya mata dadi,tanason kasancewa sosai da mamarta,don tana jin dadin haka,uwa uba tana qaruwa da abubuwa masu yawa,sajta jinjina kai "Allah ya bada sa'a,yasa a gama lafiya, zamuyi kewarka nida affan" ta fadi a sanyaye da wani abu dake bugun zuciyarta wanda batasan meye ba "Ameen" ya fada muryarsa a qasa "Ba zaka shiga ku gaisa ba?" Tayi masa tayi,abinda bata taba ba kenan sai yau "Later" ya fada a gajarce,saita jinjina kai kawai,ta saka qafarta ta fice a motar jikinta a mugun sanyaye kamar wadda aka zarewa laka.*H U G U M A* Arewabooks:huguma A RUBUCE TAKE (k'addarata) Part 2 Page 29 A nutse ta bude k'ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu. Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina......tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun. A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan? "AKWAI WANI ABU" ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa. Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria..... matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba.....zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa "Waishin meke faruwa?" Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta. Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba.....komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki. Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan. Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita.....duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta. A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana "Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi" cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata.....kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata. Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba "Ina zuwa" tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya. Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar "Assalamualaikum" ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba "Wa'alaikumus salam" mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu.....irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki......irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba. Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa "Ka sauka lafiya?,ya kaje gida" "Me yasa zaki aikata min haka?" Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta "Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqi miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?" Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne "Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?" "Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha'intata WIDAD?" Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa "Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ins kake yanzu?" Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he's safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan "Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?" Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai. "Hotel kuma?" Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya "Bakije bane?,ko zaki shiryamin irin qaryar da kika saba?" "Naje,tabbas naje....amm......" "Ya isa!!!!" Abinda ya fada kenan a tsawace "Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!" Kit! Wayar ta katse "Abban affan,daddy!!!" Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji. "Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???" Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita "Hafsah" taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko.mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar.[5/19, 6:04 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 30 Mummy ce dauke affan da yake faman tsala kuka,kukan nasa daya dinga shiga kunnuwan widad kamar a duniyar mafarki "Karbeshi ki bashi yasha,kamar bacci yakeyi" mummyn ta fada tana miqa mata shi,saidai ko motsawa batayi ba bare tayi azamar karbarsa,abinda yaja hankalin mummyn kenan "Ke widad.... widad lafiya?" A hankali ta ajjiye affan ta zauna tana jan widad din cikin jikinta gami da ambaton "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil" ganin kamar tana neman fita a hayyacinta,addu'o'i ta soma karantawa tana shafa mata a fuska,a hankali sai nutsuwarta ta fara dai daita,ganinta ya fara dawowa dai dai,ta zubawa mummyn idanu wasu hawaye masu zafin gaske suka fara zarya akan fuskarta. "Meyake faruwa?,me ya sameki?" "Mummy cikina ne yakemin wani irin ciwo" "Ya subhanallah" ta fada wani sashen na zuciyarta yana mata wasi wasi,yanayin da taga ta shiga baiyi kama da yanayin ciwo ba,yafi kama da wanda yaga wani mummunan tashin hankalin "Bari na kira saleem sai mu muje kiga likita,ai bai kamata a zauna ba" kama hannun mummyn tayi "Aah mummy,addu'a zakici gaba da yimin,ko yanzun da kika yimin na samu sassauci" kai ta jinjina badon ta yarda da widad da abinda yake damunta ba,a haka ta sakata ta shayar da affan saita sake karbarsa ta fita,saidai fiye da rabin hankalinta yana kan widad din,duk bayan wani lokaci saita leqata tare da tambayarta ya jikin?,akwai abinda take buqata?,saidai tace babu. A ranar yadda taga baqar rana haka taga baqin dare,baqin daren daya zame mata baqiqqirin,yayi mata kuma tsaho tamkar daren mutuwa,tayi dukka Wani qoqari na fahimtar da abbas abinda yake zato ba haka bane amma yaqi saurararta,ta kira har sau ba adadi,ta tura masa tex na bayanai har batasan yawansu ba amma ba abinda ya canza,kafin gari ya waye ta fige ta fita hayyacinta da tashin hankali,kamar yadda shima a nasa bangaren wani irin firgici tashin hankali da razani yaso da'ai d'aitashi,duk sanda ya tuna har lawal ya shaida fitar tata ya kuma bashi tabbacin zuwa take hotel din tana kuma kawo maza sai yaji kamar zuciyarsa ta fashe ya mutu. Sanda mummy ta shigo da safen ja da baya tayi tana salati ganin yadda fuskar widad din tayi jajur da ita ta tasa "Ke tashi,tashi ki gayamin gaskiyar abinda yake damunki" mummyn ta fada tan ajjiye kayan tea data shigo mata dasu,ta nemi gefanta ta zauna ta a nutse tana rutsata da ido. Batasan ba zata iya daukan wannan tashin hankalin ba,batasan zuciyarta ba zata iya jure wannan al'amarin ba sai data dora kanta a kafadar mummyn,a sannan ta sake gasgata uwa rahamace da babu kamarta a doron duniya,tayi kuka tayi kuka,har sai data zagwanye dukkan wasu damuwoyi data jima tana dakonsu a ranta,sannan a hankali cikin wani irin ciwo da zuciyarta ke mata ta furta ma mummyn abinda ke faruwa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta maimaita sau uku cikin mugun gigicewa tana daga widad daga kafadarta "Da wannan abun kike boyewa?,wacce iri ce ke widad?,to ni kaina wannan abun yafi qarfina,yafi kuma qarfin jina da kunnuwana,bazan iya jin wannan abun ni kadai ba,maza tashi"ta fada tana dauko ruwan tea din data shigo dashi "Tashi kisha wannan yanzun nan fita ta kamani,banga ta zama ba" haka ta dinga bata tea din,tana kurba tana jin kamar mutuwa takesha,mararta kamar zata fashe saboda tsananin ciwo,amma wannan ciwon bashi ke damunta ba,salama ne akan ciwon dake danqare cikin zuciyarta. Mummy na bata tea din tana sake maimaita innalillahin saboda yadda batun ya daki zuciyarta,ta sani ta kare kanta da mutuncinta tsahon rayuwarta,dai dai da rana daya kuma bata taba hutawa da yiwa yaranta da jikokinta addu'a kan samun kariya daga zina ba,tayi imanin addu'arta ba zata tashi a banza ba. Da cup din ta fice bayan ta sakata kwanciya sanda taga gumi yana yanko mata ko ina "Ki cire damuwa a ranki,Allah yana tare dame gaskiya muddin kinsan kedin me gaskiya ce,komai daren dadewa Allah bazai bar gaskiya ta tozarta ba" da wannan kalamin na mummy widad ta samu nutsuwa kadan,saidai duk da haka hawaye baibar fita daga idanunta ba,yadda abbas ya rufe idanu kamar yau ya fara saninta,yaqi ji yaqi gani,yaqi tsaiwa ya saurari gaskiyar ta. Shiryawa mummyn tayi tsaf suka fice zuwa gidan yayanta,tabarsu a gidan ita da affan da su saleem,tace su kula da ita su dinga yawan leqata,zasuje su dawo ita da usama. Shi kansa uncle bashir ya kadu da jin batun da mommyn tazo dashi,yayi Shuru yana jinjina maganar cikin ransa "Abinda nake gani,mu basu iska shida ita,shi din na tabbatar tunda jami'in tsaro ne bazai gaza bincike ba,zuwa sannan ya huce ba kamar yanzun da yake kan doron zargi ba,kuma wala'alla ya kammala bincikensa sai mu tuntubeshi muji daga gareshi,zan shigo naga widad din in sha Allah,kici gaba da tausarta komai zai dai daita in sha Allah" mummyn ta gamsu da shawararsa,da wannan kuma ta dawo gida ta shiga kula da widad din,dukkan qoqarinta ta sanaya akanta,bata barinta ta kebe kwata kwata saidai idan ya zama dole gudun kada ta shiga damuwa,saidai abar zuciya da abinda takeso,wata muguwar damuwa keta cin ranta ta can qasa,duk da tana ta qoqarin sakewa saboda yadda take ganin mummyn nata tana wahala da ita. Komai nata mutanen gidan sun bashi muhimmanci,kowa qoqarin ganin ya nuna mata damuwa da kulawarsa yake,amma har yau al'amarin abbas yaqi sakinta,mamakinsa ke cikata a duk sanda ta tunashi,a kowacce rana tana duba wayarta sau babu adadi waiko zataga kira ko saqonsa,kozai bayyana mata ya gano qarya ne sharri ne,ya gano kuskuren fahimtarta yayi,a kullum dakonsa takeyo ko zataga saqon ban haquri,amma shuruuuuu kakeji,babu shi babu dalilinsa. Idan tace zata kwatanta yanayin da rayuwarta ta fada a wannan tsukin ma bata baki ne,wata irin damuwa me cin gangar jiki da ruhi,duk yadda take wuni cikin jama'a idan dare yayi tazo bacci saita kasa,kuka kuwa ta yishi kamar hawayen idanunta zasu qare,wai yau ita uncle dinta ke tuhuma da laifin zina,zina fa?,saita rushe da kuka tana jin kamar ranta zai bar gangar jikinta ta huta. *H A F S A T* Duniya ta zame mata sabuwa,sai takejin kamar bata da sauran wata matsala kuma yanzun,duk sanda ta dubi sassan widad ta ganshi a garqame,ta tafi kuma ba'asan ranar dawowarta ba,tayi rawa tayi juyi duk ita kadai,ta kuma kira habiba tayi mata godiya mai yawa,tare da fadin zasu koma wajen malaminta nan kusa,amma abu daya dake damunta,irin yadda abbas din gaba daya ya canza,bashi da kuzari bare walwala, fara'a kam babu ita,tuni tayi nata waje,duk da qoqarin da takeyi taga ta gyaggara yadda widad keyi amma babu abinda ya canza,sai abubuwa suka fara mata wuya,ga qoqarin ganin ta dauki pattern din widad wanda dukka jiki da zuciyarta suka gaza saboda bata saba ba,ga sauyin yanayin abbas din. Shikam kome baisan yana yi ba,duk yadda yaso ya manta komai ya cisge widad daga rayuwarsa amma ya gaza,abun ya masa tsaye a rai,ya tsaya masa fiye da duk yadda ya zata,ko mutuwar mahiafiyarsa ya dangana amma ya kasa dangana da widad din,ya tsaya a gaban mudubi ya kalli kansa da kansa ya yiwa kansa fada amma ko gezau,yasha rasa bacci cikin dare idan abun ya taso masa amma abu guda zuciyarsa keta nacin bashi shawara "Ki saketa kawai ka huta,ka saketa zaka manta da ita" saidai sam hannuwansa sun gaza rubutu takardar sakin. Irin wannan maganar hafsat din tayi masa,bayan sallar isha'i yana zaune a falonsa yana kallon labaran duniya a tv,ga mai zuzzurfan hankali duba daya zaiyi masa ya gane tunani yakeyi bawai kallo ba,ta turo qofar ta shigo idanunta a kansa,ta dauke kai tana jan tsaki qasan ranta "Haka zakayita yi kazo kuma ka haqura,kun rabu kenan har abada billahillazi" kafin ta qaraso ta sauya fuskarta zuwa yanayi na tausayi "Daddyn mimi,nifa banajin dadin ganinka a haka gaskiya,wannan abun tunda ya riga daya faru,kawai ka sawwaqe mata,saika samu nutsuwar zuciya idan aka rabu gaba daya,badai affan ne zai hada ba?,ka dauko yaronka,na maka alqawarin zan riqeshi tare dasu mimi" kamar wanda wuyansa ya sage haka ya daga kai yana kallonta,wani irin duba ne da yafi kama da duban baki da hankali,duk yadda zuciyarsa ke bashi shigen wannan shawarar amma ai bata taba ma kawo masa ya rabo affan da mamarsa ba,sai kawai ya ajjiye remote din hannunsa ya miqe tsam ya wuce bedroom dinsa. Da kallo ta bishi cikin mamakin yadda abubuwan har yau suka kasa saitan mata yadda takeso "Wai me yake faruwa ne?" Ta tambayi kanta,sai ta miqe tabi bayansa,saidai ta sameshi ya wuce toilet,da alama kuma alwala yakeyi,dole ta fito,ta wuce sassanta ta kirayi habiba ta tsegunta mata damuwarta "Ai dama yace kibi a hankali,don har yanzu zuciyarsa na ga yarinyar,zuciyarsu guri guda take,rabasu sai anbi da nutsuwa da taka tsantsan,don haka kibi a sannu,a hankali komai zai shigeshi ya rabu da ita harma ya manta da ita ba tare da ya sani ba,a yanzun dai gidanne ta barshi har abada,malam yace bazai bari ta dawo miki ba" taji dadi tayi maya godiya,ta kuma koma sashen,saidai tana murda qofar ta jita a kulle,tayita knocking amma ba'a bude mata ba,abun ya mata ciwo yadda a yanzun yake banzatar da duk wasu al'amura nata fiye da yadda take gani a baya,to amma data tuna da zancan da suka gama yi da habiba sai taji zuciyarta ta wanke,ta juya tana cewa "A juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,baqar matsiyaciya yadda kika fiddani daga rayuwarsa,kin bar gidan nan har abada,kuma saikin fita daga zuciyarsa kema haihata haihata" ta fada a fili a hankali kamar me sambatu. Yana fitowa kira yana shigowa wayarsa,kamar bazai dauka ba amma sai ya koma saman sofa bed ya zauna yana daga wayar,daga can uncle bashir yayi sallama jin ya daga wayar,ya amsa masa da muryarsa data zama me sanyi sosai. Gabatar masa da kansa yayi,sai suka sake gaisawa cikin mutuntawa,sannan uncle bashir ya sanar masa da dalilin kiransa. Wani irin zafin tururi ya dinga ji yana taso masa a qirjinsa,ya dinga furzar da iska daga bakinsa,da qyar ya iya controlling kansa kafin ua fara magana "Na sameta da laifin cin amanata ne,tana zuwa hotel tana kuma kawomin maza har cikin gidan aurena,yanzu haka ina da shaida a hannu na,kuma ita kanta ta amsa da bakinta taje" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" uncle bashir ya dinga fadi "Yanzu babu ta inda kake gani za'a gyara lamarin?" "Sai nayi bincike shine abinda zan iya cewa" ya fada a taqaice,don gaba daya bai qaunar maganar,sai yaji numfashinsa yana riqewa. A sanyaye uncle bashir ya kalli mommyn widad "Ya kukayi dashi?" Bai boye mata komai ba ya gaya mata,ta sake maimaita innalillahin da tun zuwan widad bata bar bakinta "Ina zaki?" Ya tambayeta sanda yaga ta miqe "Kiranta zanyi naji waye din yazo kuma da gaske taje hotel din ita?" Daga haka tayi gaba,ta isa qofar dakin ta tura ta budeta, widad ta daha jemammun idanunta wanda ta manta rabon da suga kwalli tana duban mahaifiyarta,tana zaune saman abun sallah,ta hade tafukan hannayenta waje daya,da alama addu'a takeson yi amma ta rasa me zatace "Taso" mommy ta fada tana yafitota,saita miqe tsam tabi bayanta. A nutse ta amsa musu duk tambayar da sukayi mata "Dama shi baisan abubakar ba?" "Zuwansa na farko kenan shida baaba hamisu" duk sai sukayi shuru suna jinjina abun da yadda za'a warwareshi "Bari nayi kiran mahmuda,dole yasan abinda ake ciki,don na fuskanci abun babba ne" uncle bashir ya fada,ya sake fidda wayarsa ya zayyanewa abban komai. Shima dai kiran sunan Allah ya dinga yi "Ku kawomin ita kano" shine abinda ya fada,a washegari mummyn da uncle bashir suka yi mata rakiya zuwa kano,a gidan ummu suka sauka,suna shiga kuma widad din ta fada jikin ummu tana sakin kuma me tsuma zuciya. Wani mawuyacin hali ummun ta shiga,ta dinga goge qwalla zuciyarta fal tausayin widad din tata,ganin yadda tayi wata rama ta sake yin fari faaattt,hatta fatar bakinta a bushe take "Tun yaushe kika shiga wannan yanayin amma ba'a sanar min ba?,kiyi haquri ki kwantar da hankalinki,Allah yana tare dame gaskiya,kuma zai fiddaki ko ba dade ko bajima" haka ummu ta dinga fada cikin tashin hankali da yanayi na tausayi,zuciyarta kamar zata tsaga qirjinta ta fito,tasa aka gyarewa widad din daki,sannan aka shirya mata abinci kamar yadda aka shiryawa mommy da uncle bashir,amma komai widad din ta kasa tabawa,saboda bata iya cin komai,daga ruwa sai lemo,na fata kona gora,ita kanta mummyn tayi tayi ta dinga cin abincin amma baya wuce mata,kota kwatanta ci baya ciyuwa sai tayi amansa. [5/19, 6:04 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 31 Zuwa azahar abba mahmud ya iso,ba dadewa saiga uncle muhsin shima takanas,wanda sam baisan abinda yake faruwa ba sai sannan,suka zauna shida sauran qannensa biyu dake binsa dukka cikin falon ummu,ya dubi widad da fuskar nan tasa dake nuna tsantsar da gaske yake,ya kirayi sunan widad din,wadda duna daya ta yiwa fuskarsa yawun bakinta ya dauke tsaf!!,tasan waye abban,tasan halinsa sarai,baya daukan wasa ko raini,hakanan bayason rashin gaskiya kaf rayuwarsa "Ki gayamin tsakaninki da Allah me ya faru?" Bakinta ne ya fara rawa,cikin kakkausar murya yace "Ki nutsu kiyimin bayani,idan kuma baki da gaskiya ne kiyi gaggawar fadamin basai kin batawa kowa lokaci ba" ta rufe idanunta sosai tana son bawa zuciyarta haquri ta kuma dai dai tata,saita fara gaya masa komai daki daki harta kammala. "Wayeshi abubakar din?" "Abubakar dai fa daka sani" uncle bashir ya amsa masa,sake waiwayawa abba yayi ga widad "Wannan abun da kika fada ayanzun idan baki qur'ani zaki iya dafawa ki sake rantsewa da hakan shine iya abinda ya taba faruwa?" Da sauri ta jijjiga kai "Zan rantse abba wallahi zan rantse" "A bani number wayar abubakar din" ya miqawa uncle bashir wayarsa,ya saka masa number abubakar akayi kiransa. Yadda widad ta fada din haka shima ya fadi,abba yayi masa sallama ya kashe wahar yana duban widad idanunsa tsar a kanta "Ashe kece duk kika jawa kanki wannan,ki gayamin uban da yace miki koni na mutu zaki fita daga gidanki kafin ki shaidawa mijinki,kadin kuma ya baki izni ta hanyar amincewa?" "Nayi kuskure abba,kuma naga indai fita ta uzuri ya kama yana barina ko ban gaya masa ba,saidai idan ya dawo din saina gaya masa....... astagfirullah" ta fada a rude hawaye yana zirarowa saman kuncinta sannan ta fashe da kuka,har affan yana daga kai yana kallon fuskarta sosai,dukka saida kowa a wajen zuciyarsa ta karye, dukkaninsu sunsan halinta,bata qarya ko za'a yanka ne zata fadi gaskiya,tun tashinta haka take. Sosai ran abba ya sosu,ransa ya kuma baci har ya gaza jurewa "Wanne irin aure ne wannan kukeyinsa da zargi?,ina akace anayin aure da zargi irin haka,zina fa?" "Wai ba zargi yakeyi ba,har hujja yana da ita" "Idan ba zargi bane waye ya gaya masa?" "Abokiyar zamanta ce" wani balaeen bacin rai ya tasowa abban, musamman shi da ya taba fuskantar halin makirci irin na mata "Abokiyar zamanta?" Ya maimaita wani bacin ran yana ciyoshi,sai kawai ya kasa sake cewa komai saboda tsananin bacin rai,ya miqe tsam yana cewa ummu "Ta zauna a wajenki ummu" daga haka ya fice,kowa a wajen ya fahimci yadda ransa yayi mummunar bacin rai,na biyunsa kuwa uncle muhsin ne,wanda shima ya miqe ya fita,ya kuma lalubi number abbas din ya kira. Daidai lokacin da yake tsaka da aiki da dukkan qananun police dake qasansa da zasuyi aikin tare. Cikin uniform dinsa dake qara masa kwarjini sosai,fuskarsa a dinke tsaf,a yau din baya ga yanayin aiki da yake sawa ya koma hakan,harda wannan qulalliyar damuwar dake qasan zuciyarsa,wadda ta koma masa abokiyar rayuwar ruhinsa,ya saka hannu a aljihun wandon uniform dinsa ya fidda wayar,ganin sunan muhsin din sai yadan gyara tsaiwarsa,tunda abun ya faru ko sau daya basuyi magana ba,sai ya juya a hankali ya taka yana fita zuwa qofar dan qaramin hall din da suke ganawar sirri. Kan qaramar barandar dake wajen ya tsaya ya daga wayar,suka fara gaisawa kamar komai bai faru ba,sannan a nutse ya jefa masa tambayar abinda yake faruwa tsakaninsu da widad. Yadda ya gayawa uncle bashir haka ya gayawa muhsin din,ransa yabaci shima "Yanzun ka yarda da abinda ita ta fada?" "Bana ce ba,sai nayi bincike kawai,zan sake bincikawa yanzun haka ina katsina ne" kai muhsin ya jijjiga ransa a bace "Saika gaggauta,saboda ran yaaya mahmud ya baci,kuma nasan halinsa sarai" daga haka ya yanke wayar,abbas din ya sauke wayar daga kunnensa yana kallonta,daga can qasan zuciyarsa ana gaya masa bakayi dai dao ba baka kyautawa,wani sashen kuma yana gaya masa shine dai dai,ya rufe idonsa a hankali yana jin kansa yana masa nauyi,a hankali sai ya fara jinsa kamar iska na kadashi hagu da dama,jinsa ya fara yin qasa hayaniyar dake kusa dashi ta fara komawa nesa dashi,sai kuma yaji kamar qafafunsa sun lanqwashe an turashi,ya tafi luuuuu zai fadi,mutumin dake dauke da posting later dinsa ta sauyin gurin aiki daga kaduna zuwa katsinar ya isa gareshi yayi saurin tareshi yana fadin "Subhanallah, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai ya fara neman dauki,wadanda ke kusa suka qaraso suka tayashi riqe abbas din daketa qoqarin daidaita numfashinsa ya kuma miqe ya tsaya da qafafunsa saidai abun yaci tura,sunqi sakinsa don sun tabbatar zai iya faduwa,dole aka dauko motar aiki aka sakashi a ciki suka wuce asibiti dashi. Ummu tafi kowa saninta da sanin wacece ita,hatta da mahaifiyarta ba zata gaya mata wacece ita ba,zamanta wajen ummun an dan samu ci gaba kadan,ta lalubo abubuwan da takeson ci ta saka latifa na tanadar mata su,a yadda ummun ta lura sai taga kamar qaramin ciki ke sake wahalar da widad din,koda ta gaya mata a gigice ta daga kai ta kalleta cikin tashin hankali gabanta na wani irin faduwa "Ciki kuma ummu?" Yadda taga hankalinta yayi mugun tashi saita saki murmushi "Wai hasashe na ne,amma ba lallai ya zamana shi din bane" tabar widad din a haka,don ta fuskanci sanin tana da cikin kamar zai sake zame mata wata qarin damuwa akan wadda take ciki,sai kawai taci gaba da kula da ita a hakan. Kwanansa biyu a asibitin yana jin jiki,a kwana na ukun yaji dama dama,ya kuma nemi sallama amma likitan yace bazai bashi yanzu ba,sai ya huta sosai,saboda stress yayi masa yawa,so yana buqatar ya samu hutu sosai. Daga wajen aiki sun bashi kulawa sosai,sun kuma saka an saka komai a gidan da aka bashi zai zauna a zaman aikinsa,koda suka gaya masa shi sai yaji duka wannan ba damuwa bace a wajensa. Ciki ikon Allah a kwana na ukun yaji ya fara damuwa da yanayin da yake ciki,zuciyarsa ta fara tuhumarsa,ko yaya widad take ba zaka iya zama da ita ba?,ya sadaukar da komai dominka fa. Maganar da wannan raunannan sashen na zuciyarsa ke gaya masa kenan,ya tuna wayarsu ta qarshe da muhsin,wadda daga ita bai kuma kiransa ba,ya kuma tuna yadda ya gaya masa abban ya dauki zafi,mutum me mugun karamci da kirki,sai ya miqe zumbur ya zauna saman gadonsa ya jawo wayarsa. Kai tsaye ya kira kawu hassan,bayan sun gama gaisawa ya fara masa bayanin biko yakeso suje masa "Ikon Allah,hafsatun abun yakai har da sake tafiya gida?" Kai ya girgiza yana jin zafi a ransa "Ba ita bace,widad ce" "Widad kuma?" Kawun ya tambaya cikin mamaki "Eh kawu" shuru ya danyi sannan yace "Allah ya kyauta,amma ya zama dole ka sake zama mai nisan haquri,su mata indai kace ba zaka dinga haquri ba,kowacce ma ba zaka iya zama da ita ba,ko ka auro saisun tafi,kuma zo mu zauna zo mu saba" ya danyi masa fada sannan yace zaiyi magana da ko sunusi ne sai su shiga kanon ko zuwa gobe ne,ya yiwa kawun godiya sosai,yace zai sanya a tura musu kudin da zasu sha mai "Don qaniyarka muba iyayenka bane,har sai ka bamu kudin mai banda alkhairin da kake mana" wani busashen murmushi ya danyi kawai,ya sake masa godiya ya ajjiye wayar. Shuru yayi ya jingina da gadon idanunsa a rufe,wata zuciyar na gaya masa ya kyauta,wata kuma tana tuhumarsa,kanme zai dawo da ita bayan babban laifin data aikata?,bata cancanci ya zauna da ita ba,ya rasa wanne matsaya yake a cikin biyun?. Sai da yayi sallar azahar hafsat ta fado masa a rai,ya dauki wayar yana duba ko akwai kiranta amma babu ko daya tsahon kwana ukun,mamaki ya kamashi,sai ya fara neman layinta. Sai data kusa da tsinkewa sannan ta daga,murya a daqile tayi masa sallama,ya amsa sa muryarsa mai laushi "Sai yau ka tuna damu,ni kamar ma mu ka kama a hotel din nan" ta fada cikin gatse,sai yayi shuru yana jinta ransa na masa zafi,batayi dogon nazarin taji sauyi a muryarsa ba ta dora "Duk masifar ta dawo kanmu,kwana uku kayi tafiya amma ka kasa neman matarka daka bari da yaranka" kansa ya girgiza yana jin ciwo a ransa "Ke bakisan ki kira mijinki kiji ya ya isa ba?,idan kinji shuru bakisan ki karashi kiji me yake faruwa dashi ba?,bani da lafiya ina asibiti kwana uku amma rashin kulawarki yasa bakisan da hakan ba,da irin wannan halin naki wataran sai an kawo miki gawata unexpected" sai kuma jikinta yayi sanyi,ta danyi shuru sannan ta fara magana "Ni wallahi bansan baka da lafiya ba,sannu Allah ya sawwaqe ya baka lafiya" "Ameen" ya amsa can qasa,duk wani karsashinsa babu,sai yaji baya buqatar dogon magana da ita,ya tambayi yara ta hadashi dasu. Kusan su suka debe masa kewa,yayi hira dasu mai tsayi sannan yasa suka kaiwa mamar tasu wayar,ta tambayeshi wanne asibiti yake,daya gaya mata ya dauka zatayi batun zuwa ganinsa,amma sai tace masa kawai Allah yasa kaffara,akan haka sukayi sallama,sai ya kashe wayar,widad ta fado a ransa,yayi imanin inda itace da yanzun haka ta rude masa gaba daya,ya mirgina kansa gefe yana jin zafin zuwanta hotel,sai yaji ko sunansa bayason ji. *********Sai da ya gama shirin fitarsa kasuwa sannan ya fito gaba daya,ya samu baqin da akace masa suna jiransa a falon saukar baqi na gidan. Sukayi gaisuwar mutunci sosai,ya shaida kawu hassan don haka bai buqaci sanin daga ina suke ba,haquri suka bayar kan su din basusan me yake faruwa ba sai daga baya,suka kuma gabatar masa da buqatarsu na abasu bikon widad din tare da alqawarin hakan ba zai sake faruwa ba. Gyara zamansa sosai abba yayi "To naji dadin zuwanku,don dama inata shawarar neman daya daga cikinku,batun ya sake faruwa ko kada ya sake faruwa dama bazai sake din ba,saboda a yanzun bana buqatar kowa ya nemi bikon widad,abinda nake buqata don Allah,ku gaya masa ya rubuta takardar sakin diyata ya aikomin da ita,ko ya turomin ni tunda yana da number ta,magana ta biyu kuma,ku gayawa ita abokiyar zaman tata mai shaida da shaidu cewa,ta shirya shiga kotu dani uban widad bisa qazafin zinar data yiwa diyata,zamu shiga kotu har sai gaskiya tayi halinta,walau gaskiyarta ko kuma gaskiyar tawa diyar" dukkansu sun girgiza sun kuma ji babu dadi,don basu zaci wannan hukuncin daga wajen abban ba,sai suka fara qoqarin bashi haquri "Ai baza'ayi haka ba alhaji" "Me zai hana ayi haka?,na gama magana kuyi haquri bana maimaici,ya bayar da takarda ita kuma ta shirya shiga kotu,'yata ba mazinaciya bace,ba kuma zata sake zaman zargi ba" daga haka ya musu sallama cikin girmamawa yabar musu falon. Dole bayan sun gama jimanta maganganun a tsakaninsu suka fito,kowa sai da ransa ya baci dajin cewa wai hafsat ce ta gaya masa anyi haka harda bashi shaidu,kawu hassan bai rufeshi da komai ba,ya kirashi yayi masa tatas,ya kuma bashi saqon abban ya kashe wayarsa abinsa.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 32 "Hasbunallahu wani'imal wakil,ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" itace ya samu kansa da maimaitawa,jujjuya kansa kawai yakeyi yanajin kamar zai zauce,kamar hankalinsa na shirin yin qaura daga gangar jikinsa ne,wasu irin muryoyi ne daga qasan zuciyarsa ke karanta masa abubuwa iri daban dabanya kama kansa da kyau ya riqe,sai yaji hawaye na shirin fita a idanunsa,kewar hajiya ta mamayeshi,ita daya ce yake iya jingina da ita a duk sand aya shiga matsanancin hali irin wanna,ita daya yake raba yaji snayi ya kuma samu mafita cikin sauqi,gaba daya kansa ya gama kwancewa,yanason yayi wani abu amma sai yaji kamar ana dannarsa,a wannan gabar abu daya ne kadai tunda ya darsu ya kasa barin zuciyarsa,yana son widad ta dawo,koma yaya ne yanason ta dawo,idan ta dawo koma meye sai yafi gabatar dashi a nutse,nesantarsa da tayi sainyakejin kamar bashi da sauran komai da ya rage masa a rayuwa,gaba daya maganin da likita ke bashi da sauran treatment da yake bashi ana bashine kawai badon suna wani amfani ba,a wannan rana da kansa ya kira yace ayi masa allurar bacci,saboda daina gane komai da yayi,kowanne sashe na zuciyarsa da abinda yake umartarsa da ya aikata. Cikin kwana uku ya gaza samun sukuni,gaba daya a rikice yake,yanatabyaqi da zuciyar dake umartarsa da nisantar widad da dukkan wani abu da ya shafeshi,ya dinga naci wa su kawu hassan da basu haquri,ba yadda suka iya,shi din mai alkhairi ne da maida damuwarsu tashi,haka suma suka dinga ziryar zuwa kano neman bikon widad din,zukatansu suma duka babu dadi. Tun abba yana saurarensu tare da jadda musu cewa,shifa takardar sakin widad yake jira bawai batun biko ba,har takai yama daina sauraron kowa a cikinsu,ba abbas da har yanzu yake kwance yana jinya ba,hatta dasu kawu hassan abun ya daure musu kai,don basu tsammaci samun hakan daga wajen abba ba. A yanzun har takai ta kawo baya saurarensu,sai yasa a kaisu dakin baqi suyita zaman jiransa,har sai sun gaji sun tafi. Yanayin da yake ciki na jinya a asibiti ne kawai ya hana su kawu zame hannunsu daga batun bikon widad din,duk yadda suke zaton al'amarin daga wajen abban ya wuce nan,dole suka yanke shawarar tuntubar tsoho mai ran qarfe alhaji salim,suna da yaqinin shi kadai ne zai iya masa magana yaji,shi daya ne zai iya sakashi yayi. *******K'arfe takwas na safiya ne,tana zaune saman kujerar dining din ummu tana kurbar tea mai dumi sosai,a yanzun ta zama wata acici,ita da abinci bai wani dameta ba,amma yanzun tun farar safiya take fara neman abinci,ita kuwa latifa bata gajiya da bata duk kalar abincin da takeso. Cikin kwanakin ta gama amincewa juna biyu ne da ita,bata buqatar zuwa asibiti su gaya mata,don dukkan wasu alamu sun nuna mata,a yanzun ba kamar lokacin cikin affan bane,babu quruciya sosai a kanta bare ta gaza fahimtar komai. Hankalinta a tashe yake sosai da fahimtar hakan da tayi,duka duka watan affan nawa?,sai taji tana shakka da d'ar d'ar na gayawa wani,a wannan situation dinma da take ciki?, yanayin da take ciki na zargin zina daga mijinta,mutumin da ya kamata ace shine mutum na farko da ya fada bata yarda?,sai ya zama shine mutum na qarshe da zai gasgatata?,iya wannan tunanin ya sanyata taji ta qoshi da tea din,ta ajjiye cup din gefe tana ta kokawar yage tunaninsa ta ajjiye gefe kamar yadda ta daukarma ranta,cikin kwanakin ta dan samu nutsuwa albarkacin addu'a da kuma karbar qaddararta da tayi,ta jawo wayarta ta buda tana duba saqonnin customers dinta,don har harkar business dinta ta dawo kai yanzu sosai. Sallamar abban nata ya sanyata daga kai da sauri,ta kuma miqe tana masa sannu da zuwa cike da mamkin fitowarsa da safe haka,saita samu kanta da faduwar gaba,amma ganin baice komai ba sun gaisa kamar ko yaushe yana tambayar abokinsa affan saita saki jiki,ummu ta fito ya tsugunna ya gaidata "Alhajin ya tashi?" "Eh kai yake jira ma,yace zaka kaishi dubiya" "Na iso, za'a sanar mas ako za'a min iso" "Bari na shaida masa" ummu ta fada tana komawa ciki. Ba jimawa ta dawo ta gaya masa yace ya jirashi,minti goma basu cika ba tsohon ya fito a shirye tsaf yana qamshi cikin farin kaya da farin rawani,shigar da yafiyi,ko gaisawa bai tsaya sunyi ba yace suje sa gaisa a mota,ummu da widad sukayi musu fatan dawowa lafiya suka fice yana takewa tsohon baya. Sai da suka dauki hanya sosai sannan tsoho yayi magana "Mamuda an kawo min qararka,surukanka sunce kaqi haquri ka basu bikon diyarka ko?" Nauyi yadan kama abba kadan,mutanen sun masa shigar sauri sunyi kuma mugun shammatarsa,sam hankalinsa baikai zasu nema alhajin ba,da tuni ya musu kandagarki ko ya yiwa tufkar hanci,so yake ya hukunta hafsatun harma da abbas din gaba daya,ta yadda a gaba koda wasa abu makamancin wannan bazasu bari ya sake faruwa ba. Ya muskuta ya dan gyara zamansa zai bada uzuri tsohon ya tari numfashinsa "Kanaso ayi amfani dakai a ruguza auren widad kamar yadda akeso ta faru ko?,wannan abun da kake shirin yi ba komai bane face hanyar cikawa maqiya burinsu,koma waye ya shirya wanna,ya shirya hakanne na tabbatar don yaga bayan auren yarinyar,to inason ka bawa mara d'a kunya,ka turawa koma waye aniyarsa ka maida widad dakinta,sannan ina me baka shawarar ka barwa Allah,duk yadda zaka hukunta wanda yayi mata wannan qazafin baikai hukuncin da Allah zaiyi masa ba,qarshenta kasa a daure maka shi ko?,to daurin da Allah zaiyi masa har yakai wanda zakayi masa?" tunda alhaji ya fara magana gyada kai abba yakeyi cike da gamsuwa "Hakane,in sha Allah za'a yi yadda kace alhaji" "To alhamdulillah,Allah ya tsare gaba,ya basu zaman lafiya dawwamamme,ya kauda sharrin maqiya da mahassada" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu" abban ya amsa masa. Sai bayan sun gama harkokinsu da alhaji ya maidoshi gida sannan yasa aka kira masa widad,a sannan bata jima da gama sallar la'asar ba,tana saman abun sallah tana cin popcorn,wai yunwa takeji bayan duka abincin da taci,tana jira latifa ta gama gasa mata kifin da take sha'awar ci,ta ajjiye popcorn din ta miqe tsam ta fita a dakin. A falon baqi na gidan ta sameshi shi daya zaune "Shigo mana widad din ummu" ya kirata da sunan da ake yawan kiranta,wanda bata taba ji ya kirata dashi ba sai yanzu,ta qaraso kanta a qasa ta zauna gefe. "Allah yayi miki albarka,Allah yayi miki albarka,ya sake tsaremin ke" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu abba,na gode" "Kinsan dalilin da yasa na kiraki?" Saita girgiza kai alamun a'ah "Inason ki gayamin gaskiyar abinda yake ranki,banaso ki boyemin komai" "To abba" ta sake fada tana bashi dukka hankalinta "Kinason ki koma gidan mijinki?" A wani mugun ba zata maganar tazo mata,har sai data daga kai ta kalli abban nata sannan ta saukar da kanta qasa,tun randa taji labarin zaryar da su kawu hassan keyi wajen abban nata,bata sake bari anyi zance makamancin hakan a gabanta ba,don zuwa yanzun ita din bata jin akwai sauran gurbin abbas a zuciyarta,ta soma sabuleshi daga rayuwarta. Har sau uku abba yana sake maimaita tambayar amma ta gaza amsa masa da komai,sai ana ukunne wasu hawaye masu zafi suka zubo mata,yadda abban yake nanata tambayar kamar yana alamta mata ya bada kai bori ya hau,su kawu hassan sun rinjayeshi "Ni bana buqatar komawa gidansa abba,bana so,amma indai kai kana da buqatar hakan,zan maka biyayya abba zan koma" ta qarasa fada kuka yana qwace mata. Sake saka mata albarka yayi sosai tausayinsa yana ratsata,ya dora da cewa "Ni bazan cuceki har abada,bazanso kuma ki shiga takura da damuwa ba,burina dukkanku ku rayu rayuwa ingantacciya me kyau,inaso ki koma gidanki,zan kuma maidaki ne saboda maqiya susan cewa basu isa su raba aurenku ba,kiyi haquri idan hukuncina baiyi miki dadi ba" "Kafi qarfin haka abba a wajena,ka isa dani ta kowavce fuska" tayi maganar siririn kuka yana qwace mata,don tuni ta fara shiryawa kanta yadda zatayi rayuwa ba tare abbas din ba. Maganganu masu dadi da kwantar da rai yayi mata gami da nasiha da jan hankali,har sai da kukan nata ya ragu sosai sannan ya sallameta,bayan ta fita kuma ya kira kawu hassan ya basu bikonta a bisa sharadan da idan ya amince dasu widad zata koma dakinta,idan kuma bai amince ba a shirye yake da karbar takardar sakinta. Na farko abbas din bazai sake hadasu zama gida daya ba tsakanin hafsat da widad,kowacce ta zauna gidanta daban,yace sam zamansu bazai yiwu ba,baya ga banbancin shekaru,irin wadan nan abubuwan da suka fara bullowa a tsakaninsu ba'a san gaba me ta dauki aniyar aikatawa ba,saboda bazai iya dauka da jurar abinda zata bullo dashi a gaba ba idan wannan sun barta da Allah sun qyaleta,na biyu ta kiyayeshi,koda wasa ya sake jin labarin ta aikata abu makamancin wannan to fa duk duniya babu mai tanqwarashi akan matakin da zai dauka dangane da ita,dukkansu sun aminta da wannan sharadin,sun kuma gode masa da har ya nuna dattako ya haqura yayi kawaici akan shariar da yace zasuyi,sun zaunar da hafsat kuma sun gaya mata komai,wadda tuni cikinta yayi bala'in durar ruwa sanda taji batun kai qara kotu,tana tsoron kada ballinta ya tashi,ta tabbatar idan asirinta ya tonu ta ba makawa wannan karon ba asiri ba,ko meye tayi abbas din bazai qyaleta ba,tanason taji cewar kotun za'a je ko an fasa?,amma ta rasa amsa daga wajensu,saboda batason ta matsa da tambayar da zata alamta musu bata da gaskiya,ta wajen abbas kuwa ta kasa jin komai,don ko wayarsa ta kira bashi yake dagawa ba, samuel ne ko wani cikin yaransa,kuma duk sanda zasu daga din zasu gaya mata ne cewa bacci yakeyi,sai suka barta cikin duhu,duhun da ya tafi da dukka nutsuwarta,dare da rana tana zulumin da tsoron ta ina ballin zai tashi?,abu daya yadan kwantar mata da hankali,kudaden data aikawa habiba tace ta koma wajen malamin nasu,ya kuma shaida mata magana ta mutu,har abada abbas bazai sake iya tada zancan ba,kai hatta da komen widad ma,yadda tabar gidan ta barshi kenan yadda yaro ke fita daga cikin mahaifiyarsa,wannan yasa ta saki jikinta taci gaba da sabgoginta. Tana kuka tana komai haka ummu ta gyara mata komai nata ita da anty deena,daban anty deena suka kebe da ita ita da anty madeena suka sake mata lecture kan wasu abubuwan masu amfani,wuni guda,itadai jinsu kawai takeyi tana binsu da idanu,gani take a yanzun tsakaninta da abbas ai sai kallo. A washegari lafiyayyar motar security tazo ta dauki widad tare da affan zuwa garin katsina,sabon muhallin da gurin aiki ya bawa abbas,tanata kuka ganin alhaji ya hana kowa yi mata rakiya "Ku barta ta tafi ita daya,hakan zai bata damar sasantawa da mijinta da wuri,tunda na fuskanci kamar har yanzu akan fushi take". Tafiyar awa biyu da rabi ta sadasu da qofad kyakkyawan madaidaicin gidan,driver ya tsaya yayi hon aka buda qaramin gate din gidan ya saka motar a ciki,ya wuce qaramin parking lot na gidan da bai wuce yaci mota biyu ba ya tsaida motar "Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa anta khairul munzilin" ta fada tana lumshe idanunta sannan ta budesu,bata taba zaton qaddara zata sake hadasu zama da abbas ba,hakanan a yanzu batasan wanne irin zama zasuyi dashi ba. Tana rungume da affan ta nufi qofar da ta tabbatar ta parlor ce,a hankali take takawa,sanye da wata irin doguwar riga 'yar morocco mai sulbi da tayi masifar dacewa da fatarta data fara sheqi tun yanzu saboda qaramin cikin dake jikinta. Yaji shigowarsu sarai amma ya gaza motsawa,yana zaune cikin doguwar kujera hannunsa daya maqale da carbi counter,wanda a yanzun zama tare da shi ne kadai yake bashi sanyi da nutsuwar zuciya,daya hannun nasa kuma wayarsa ce yake duba news akan abubuwan da suka shafi katsina da kewayenta kafin ya gama warkewa ya fara fita aiki. Idanunsa qyar akan qofar sanda yaji an tabata,tana bude qofar idanunsu suka gauraya da juna,kowannensu sai yayi qoqarin janye idonsa daga kan dan uwanta,tayi sallama da siririyar muryarta daga can qasan maqoshinta,wanda banda Allah yasa ya saka kunne da kyau babu ta yadda za'a yi yaji abinda take fada. Amsa mata yayi yana qoqarin fita daga page din da yake karatun,ya aje wayar hannun kujerar da yake kai sannan ya miqe ya nufota. Batasan ya taho din ba,don tunda suka hada ido dashi bata sake marmarin kallonsa ba,ya rame sosai har hakan ya bayyana a fuska da jikinsa,to amma sai taji sam bata damu ba yadda ta saba ji a baya idan bashi da lafiya, taci gaba da takawa zuwa cikin falon,sai ganin mutum tayi yasha gabanta.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 33 Ido suka kuma hadawa,ta sake janye nata idanun tana kuma hade fuskarta tsaf tamkar bata taba dariya ba,sai shima ya basar,yakai hannu kan kafadarta zai karba affan. Ji tayi sam ba zata iya bashi shi ba,don haka ta goce ta hanyar ja da baya,ya kalleta cikin tsantsar mamaki,ya sake takowa ya matso ta sake matsawa baya,sukayi haka har sau uku sai ya gaza daurewa,ya motsa labbansa da dan bacin rai a muryarsa "Yarona nakeson ki bani" "Sai yanzu ka tuna yaronka ne?,aina dauka shima a hotel nayo cikinsa" gam ya runtse idonsa yana jin saukar maganar kan qahon zuciyarsa kamar saukar mashi,karo na farko tsahon tarayyarsa da ita data taba gaya masa wata magana mai gautsi,ko kafin ya bude idanun nasa yaji giftawarta ta gefansa,ya waiwaya ya bita da kallo,ta doshi dakin data gani a bude ba tare data tsaya tambayarsa bedroom dinta ba. Tanata addu'a Allah yasa nata dakin kenan,ta kuwa dace don duka kayanta da aka shigo mata dasu suna ciki,wadataccen bedroom da aka saka komai na buqata daya dace da dakin kwana,ta qarasa a hankali ta kwantar da affan dake bacci saman gado,sannan ta jawo jakarta zuwa tsakiyar dakin,ta budeta ta fidda abubuwan da take buqatar cirewa,ta jefata dukanta cikin wardrobe na dakin,cikin ranta tana jin kamar ba wani zama zatayi ba,kamar na dan lokaci ne zata koma inda ta fito. Agogon hannunta ta cire ta ajiye saman madubi ta shiga bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala,tana fitowa ta hangeshi,tsugunne gaban gadon, hannunsa riqe da hannun affan dake bacci,ya sunkuya a hankali yayi kissing dinsa sannan ya miqe,suka sake hada ido ta kuma kau da kanta tana tabe baki,shima sai ya dauke kansa,amma duk da haka idanunsa na fusgo masa yadda ta wani murje,sai kishinta ya sake motsawa a zuciyarsa,yadan cije lips dinsa kadan,har yanzu zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa akan abinda ya farun,kuma bayajin zata samu nutsuwar har sai ya sakeyin binciken qwaqwaf akai. Kamar yasan me take shirin aikatawa,har yasa qafarsa waje sai ya fasa ya dawo yana dubanta tana rolling mayafinta saman kanta tana jira ya gama ficewa ta saka sakata "Karki kuskura kice zaki kulle qofa,ki barmin yarona ya sake a gidan babanshi yadda yaso,inda ke daya ce sai nace bismillah,kiyita rufe qofar har Allah ya gajisheki" tabe masa baki tayi ta kauda kai ba tare da tako tanka masa ba,sai yaji haushi ya kamashi,yaso ko yaya ne tace wani abun,yaso ta magantu ko baqar magana ta gaya masa amma sai ta qiya,haka ya qarasa ficewa yana wani tsatstsare gida,yana jin Wani abu mai nauyi yana taba zuciyarsa. Bata kuwa fasa kulle qofarta ba,don batason ma ya wani shigo mata daki,don bata da buqatar ganinsa sam sam,zuciyarta wani irin zafi take mata idan ta ganshi,ta idar da sallar la'asar,zuwa sannan jikinta har yadan fara rawa,don bata jure yunwa kwata kwata,don dole ta fita ta laluba kitchen. Akwai komai a ciki,harda ruwan zafi a flask,ta shiga tunanin sassauqan abinda zata dafa kafin ya dawo gidan,sai kawai tayi amfani da ruwan zafin flask din ta tsaida ruwa,ta bare noodles ta zuba,ta kunna daya side na gas din ta soya qwai,cikin minti talatin kacal ta hada komai ta dauko ta wuce dakinta abinta. Tana murza key din yana shigowa,yaji qarar key din,yabi qofar da kallo,ransa ya baci,bata ji abinda ya fada kenan ba?,sai ya taka zuwa qofar dakin,ya daga hannu kamar zaiyi knocking me ya tuna kuma sai ya fasa Ya juya ya wuce kitchen. Wayam ya samu kitchen din,sai tukunyar data dafa noodles wadda ta cika da ruwa ta ajjeta a wajen,da spoon din da tayi amfani dashi wajen juyawa,bawon maggi dana vegetables din data zuba,sai yaji abun yayi masa banbarakwai,tsahon zamansu bai taba ganin tayi girki tabar gurin haka ba. Ci gaba yayi da duba kwanukan kitchen din,ko noodles din bata ajjiye masa ba,ransa ya sosu,haka ya jawo wata qaramar tukunya ya dora baqin shayi,don bashi da kuzari da kuma qarfin jikin dora komai a yanzu,girkinta yake marmari,ya kuma sanya ran ci,sai gashi ko ruwa bata dafa ta ajjiye masa ba. Jikin kitchen cabinet ya tsaya yana shan tea din,sau biyu ya kurba ya furzar,babu dadi sam bakinsa,sai a sannan ya ankara ashe ya cika komai yayi yawa,baisan kuma ya akayi hakan ta faru ba,haka ya kwarar da tea din ya fito yabar kitchen din. Parlor ya dawo ya zauna yana sauke numfashi saboda qirjinsa da yaji ya fara riqewa "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya soma maimaitawa a hankali yana qoqarin cooling down kansa,likita ya gargadeshi game da dorawa kansa stress da damuwa mai yawa,jininsa ya hau an samu kuma ya sauka da qyar,idan kuma bai kiyaye ba zai iya dawowa. Yana tunanin akwai yunwa tattare dashi,ya manta rabonsa da cin abinci cikakke,ta riga ta batashi da taste din abincinta mai dadi,damuwa da rashin samun kalar taste dinta yasa ya watsar da lamarin abinci,dole ya cire waya ya kira daya daga cikin yaransa ya gaya musu irin abincin da yakeso. Ko da aka kawo din ba wani mai yawa yaci ba,cikinsa gaba daya a cushe yake,sai ya ture abincin ya koma ya kwanta kan doguwar kujerar falon,tunani ya masa yawa,a yanzun yake jinsa cikakken maraya gaba da baya. Sau kusan biyar yana ganin kiran hafsat,saidai yabi wayar da kallo,harta gama ringing dinta ta katse,bayason damuwa a yanzu,don haka bashi sa buqatar daga wayarta. Daga bangaren hafsat din sai ta dinga jin fargaba da dar dar,amma indai abinda malam ya gaya mata haka yake,me zai hana abbas din daga wayarta,tunda dai lokaci irin wannan da baya da lafiya ta tabbatar yana gida bare tace ya fita Wani aiki na musamman "Basa qarya a zancensu,tunda ta gayamin hakanne,kawai ki shareshi" zuciyarta ta bata shawara,saita aje wayar taci gaba da sabgarta. Washegari kafin ya fito ta gama duk abinda zatayi a kitchen din ta dawo daki ta rufe abinta,bata kuma sake fitowa ba sai bayan isha'i data tabbatar ya tafi masallaci sallah,ta zube kwanukan ta debi wasu ta koma. Cikin kwanaki uku abinda da dawowarta abinda ya dinga faruwa kenan,wani irin zama sukeyi na shariya da fita sabgar juna,saidai widad din ta fishi daukan zafi sosai,don bata fita a dakin sai idan ya fita sallah,da yake har yanzun bai gama warwarewa ba,yana gida yana sake hutawa,ko aiki bai fara fita ba,da zarar ya fita zata fita ta dafa musu abinda zasuci ita da affan ta zuba a cooler ta koma daki,ko wanke wanke taqiyi,haka ta dinga tarawa kitchen din kwanuka itama. Sau daya da wasa bata taba saka tsintsiyarta ta share falon ba tunda tazo cikin gidan,iya dakin da take ciki kawai take tsaftacewa,tun bai lura ba har ya lura da abinda takeyi shigen na hafsat,don kitchen din ya fara canza launi,haka qura ta fara yiwa gidan yawa,hakanan duk da baida lafiya ya zage ya gyara kitchen din da gidan,yayi tsammanin zata dauki haske ta gyara amma a banza,don ci gaba tayi da batawa tana jibge masa kayan a kitchen din,tun yana ganin zai jure har haqurinsa ya gaza,ya dinga fakonta ta fito amma ko sau daya bata bari hakan ta kasance ba,har ya gama murmurewa ya koma bakin aikinsa. Randa zai soma fita din haka ya hadawa kansa baqin ruwan shayi a tsaitsaye,yana tsaye a falon yana kurba,gaba daya sai yakejin bashi da sukuni,idanunsa qyar bisa qofar dakin,yana jiyo hayaniyar yaron,bama rashin isashen abinci da baya samu ne damuwarsa ba,wata kewarsu da yaji ta fara shigarsa da gasken gaske,tun bayan da ya duqufa da addu'o'in da aminin mahaifinsa ya bashi bayan zuwansa dubashi,ya kasa jurewa ya ajjiye cup din ya taka zuwa dakin. Sai da yayi knocking kusan sau biyar sannan aka tambayi waye a daqile "Kinsan ko waye ai ko ban fada ba" ya amsa mata adan kaurare,sai tayi banza dashi kamar bataji abinda ya fada ba,har sai da ya qosa da tsaiwar ya sake bugawa,amma sai tayi biris dashi "Open the door malama" ya fada da dan hargagi "Dakin 'yar kwanan hotel din zaka shiga?,me zakayi da ita kai da kake da kamilar mace a bauchi?" Runtse idanunsa yayi yana jin zafin sunan data kira kanta dashi sannan ya bude a hankali yana aje numfashi "Stop it......ki budemin qofa kiban affan" "Affan kuma?,ai yarona ne ni kadai" "Widad!" Ya kirata da qarfi,sai taqi amsa masa "Ki budemin qofa nace" nan ma tayi masa shuru,har gwarancin da yaron yakeyi,da alama har yazo bakin qofar ne shima yaji.muryarsa,sai ya zame ya duqa a bakin qofar,yana jin kamar yayi zaana ya tsaga qofar ya shige,ba yaron kadai yayi missing ba,harda mamansa,yana son kallon wannan fuskar tata da ya jima bai gani ba,ya tabbatar ba zata sake ce masa komai ba,haka ya gama tsaiwarsa a wajen,ya juya a hankali ya dauki brief case dinsa ya fita a gidan. Rana ta farko a office dinsa amma bai iya wanzar da komai ba,shi kansa yasan baiyi tabuka komai ba,tunani fal kwanyarsa,gaba daya yana jin kamar an canzashi ne,kamar ba ainihin abbas ba,yaja tsaki yafi sau dubu,ya yarfa hannuwansa har baisan adadi ba,har cikin zuciyarsa yaji bazai iya jura ba,kawai sai ya dauki wayarsa yayi qundumbala ya kira muhsin. Kamar komai bai faru ba suka gaisa,sai abbas din ya samu kansa da bawa muhsin haquri "Ya wuce,amma tabbas saika dage da addu'a abbas,idan ba haka ba mata basu da kirki,zasuyita saka ka kana abu kamar Wani zautacce ko qaramin yaro" ajiyar zuciya ya sauke "Na gode" ya gaya masa "Alfarma nake nema don Allah idan zan samu" "Ba 'yar wannan a tsakaninmu,fadi kawai" "Maman affan nakeson ka yiwa magana,ta hanani ganin yaron gaba daya,ta takureshi a daki, at least ta sakeshi ya dinga fitowa yana samun wadatacciyar iska" ya fada a mugun karye,karayar da shi kansa baisan ya nunata ba,sai dariya taso kubcewa muhsin,ya fahimci wani abu a cikin muryarsa wanda shi kansa baisan yana bada wannan amon ba,ba affan bane,maman affan din yake kewa gami da qishirwar gani "Kada ka damu,zan mata magana in sha Allah" yayi masa kuwa godiya sosai sannan sukayi sallama,ya ajjiye wayar yana sauke ajiyar zuciya,sai yake jin wani sassauci cikin ransa,ya jawo system dinsa zai fara rage wasu abubuwan saboda wani dan karsashi yanzun da ya samu,sai kira ya shigo wayarsa,daya duba sai yaga number hafsat ce. Da kallo yabi wayar yana jin wani abu yana yawo a ransa kafin daga bisani ya daga wayar,cikin salo da kisisinar jin cewa a yanzun ita daya ce a duniyarsa tace "Barka da yamma,ya gida ya jikin?" "Alhmdlh,ya yaran?" "Lafiya lau suke,yaushe zaka shigo?, inaga ya kamata ka taho gida don nafijin dadin kula da kai,ga rashin lafiya sannan kuma kai daya kake zaune ai baiyi ba abun" inda ace yau ya fara sanin halaye da dabi'unta sai yace ta bashi mamaki,wato ita ba zata iya takowa ta iskeshi a inda yake ba inda ace cikin buqatar hakan yake,saidai shi ya dawo ya sameta kenan,bai shirya gaya mata komai a kansa a sannan ba,saboda zuciyarsa ta fara tsara masa wasu abubuwa a kanta,shi yasa ya hana a sanar da ita komai game da abinda yake faruwa,har kuma dawowar widad din "Bazan iya tahowa yanzu ba,sai na warke sosai sannan" "K'nnnnn,ai shikenan,nace pampers din nawwara,kudin makarantar yara duka sun qare fa,naji Shuru" "Zan miki transfer ki siya" ya fada a gajarce,dama abinda takeson ji kenan "To yayi,sai anjima" ta fadi a gaggauce kamar wadda ake jira. Wayar yabi da kallo na wasu daqiqu,sai ya tafi contact nasa ya fara lalubar number wayar umar qaninsa. A ladabce ya gaida yayan nasa yakuma yi masa sannu da jiki "Kana ina?" "Ina kasuwa,muna lissafin qarshen shekara zamu danje hutu" "To yayi,idan kun gama ka ajjiye lissafin a wajenka,zan karba idan na nutsu na duba" "To yaya" "Aiki nakeson na baka,amma banason kowa ya sani,inason ya zama sirri tsakanina dakai" "To yaaya in sha Allah" "Ka hada kayanka ka koma gida na,karka taho har sai ranar da na umarceka,anjima idan na koma gida zan kiraka nayi maka bayanin abinda nakeso kayimin" "To shikenan,in sha Allah" yayi masa sallama,ya ajjiye wayar,saiya sake komawa kan system din,maimakon yayi aikin dake kai,sai kawai ya fita,ya saka sunan FAAZ HOTELS ya fara wani sirrintaccen bincike a kansa.[5/22, 10:12 AM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 34 Tana kwancen saman gadon tana chart affan yana kwance a gefanta yayi bacci abinsa kira ya shigo wayartata,tadan saki murmushi ganin suna uncle muhsin ta zauna sosai ta daga wayar suka gaisa,cikin hikima ya sako mata zancan abbas din,yadda yaga tana kame kame ya fahimtar dashi gaskiyar zancan,sai ya fara yi mata fada cikin nasiha,nasihar data sanyata zubda qwalla,ya kuma umarceta ta buda qofarta,tabar uba da da suyi harkarsu,shi yaron ba ruwansa a fadansu,wannan tsakaninsu ne,bazai hanata hukunta abbas ba muddin zata huce,amma kada ta sako affan a ciki. Cikin share qwalla ta bawa uncle muhsin haquri tare da bashi tabbacin ba zata qara ba,ta ajjiye wayar tana sake jin zafin abbas a ranta,a daketa a hanata kuka?,har yana da qwarin gwiwar kaita qara?,saita gyada kai tana cije lebe,ya kirawa kansa ruwa kuwa,lallai ba shakka zata hukuntashi har sai ya gwammace kida da karatu,saita sake daukan wayarta taci gaba da abinda takeyi. Yayi aikin da yakeson yi sosai,ya kuma hada information masu yawa,wannan yaja masa lokaci,bai fita a office din ba sai da yayi sallar magariba,ko kafin yaje gida ana dab da kiran isha'i. Komai data saba yi a gidanta na kaduna ta miqe tayi,ta tsaftace gidan saboda ita kanta jurewa take,duk da bata rayuwa a falon amma tana jin ya dameta har ranta,sabo da qazanta masifa ne,kamar yadda sabo da tsafta yakebin jini shima,tayi girkinta amma iya cikinta dana affan,ta gama ta kwashe musu,ta gyara kanta da yaronta,saboda batason abbas din ya shigar mata daki saita dawo falon tana jiran shigowarsa ta bashi affan din ta wuce dakinta abinta,aqalla ai tayi qoqari,ta kuma bi umarnin kawun nata,bata watsa masa qasa a ido ba. Ya jima zaune cikin motar bayan ya shigo gidan,murfin motar a bude qafarsa daya a waje yana shaqar daddadan qamshin da tun daga harabar gdan kana jiyoshi, qamshin da gaba daya ya gama kashe masa jiki,bai fito ba sai da yaji ana kiran sallar isha'i sannan ya fita,ya daura alwala a famfon harabar gidan ya wuce masallaci. Rigima yaron yaketa mata,saita sakashi a kafada ta soma zarya dashi,sanye take da doguwar rigar wata atmafa mara nauyi,an mata budadden dinki daga qasa,saman kuma yasha tattara ya zauna dai dai qirjinta. Tana kawowa bakin qofar zata juya yana buda qofar,suka hada ido ita dashi,yayi wani irin kwarjini na musamman cikin uniform din, hular kayan na riqe a hannunsa,saita janye idanun nata ta juya zuwa ciki affan na qijrinta,yabi bayanta da kallo,ya tako a hankali zuwa cikin falon bakinsa dauke da sallama,ta duqa tana ajjiye yaron gami da amsa sallamar tasa muryarta can qasan maqoshinta,saita juya ta nufi dakinta ba tare da ta sake kallonsa ba,tana shiga ta tura qofar,ta koma saman gadon tayi kwanciyar ta gami da jan wayarta ta fara dubawa,saidai zuciyarta adan hargitse take kadan,don bugunta ma ya sauya ba kamar yadda yake a qa'ida ba,kuma ita kanta batasan dalili ba. Tsaye yayi kawai a wajen kusan minti biyu yana duban hanyar,sai ya dauke idonsa yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya a wannan lokacin bazaice yana jin dadin duniyarsa ba,duk yadda yaso ga qaryata hakan da gayawa kansa komai dai dai yake,amma yasan ya fada dinne kawai bawai don dai dai din yake ba. Gurin affan ya qarasa,ya dauki yaron yayi masa wasa sosai sanann ya wuce dashi dakinsa,ya cikashi da kayan wasa ya shiga bandaki ya sake wanka, sanda ya fito harya bingire saman gadonsa yayi bacci,da alama dazun dama kukan rigimar baccin yakeyi,ya saki murmushi yayi kissing goshinsa a hankali ya gyara masa kwanciya yana jin qaunar yaron har cikin jininsa,sai ya tsaya gaban madubi ya shirya cikin qananun kaya,ya shafe jikinsa da turare sanna ya fito. A falo ya fara zama,amma kamar wanda magnet ke jan hankalinsa zuwa ga dakinta saiya kasa samun sukuni,bayason shurunta,kasheshi yakeyi,a qalla ko fada yana da buqatar su dinga yi,duk sanda tayi masa shariya irin wannan baya iya jurewa,bashi da juriya akan abinda yakeso,sai ya taka a hankali ya saka kai zuwa cikin dakin. Tana tsaye gaban wardrobe tana fidda wasu kaya,sau daya ta waiwayo ta kalleshi ta mayar da kanta kamar batasan da wanzuwarsa ba,ya tsaya daga bayanta yana dubanta "Ina abinci na?" Kamar ba zata amsa masa ba,saita zuqi numfashi ta fitar ta bakinta a hankali, zuciyarta tafasa kawai takeyi amma batason tayi wani abu da zai nuna bata ganin qimar uncle muhsin,ta saki kayan hannunta ta juya ta fice ba tare data tanka masa ba,yabi bayanta sai ya sameta saman dining tana serving dinsa. Kujera yaja ya zauna yana bin dukka motsinta da kallo,ko sau daya taqi duban inda yake,kamar ma ita daya ne cikin falon,wani irin fushi ne kwance saman fuskarta ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,yaja ajiyar zuciya me nauyi ya sauke a hankali,dai dai sanda ta gama zuba abincin ta motsa da niyyar miqewa tabar wajen "Dawo ki zauna" ya fada a tausashe cikin muryar bada umarni,bata musa masa ba,kamar yadda bata kalleshi ba,ta kauda kanta zuwa wani sashen daban,yaja abincin gabansa ya fara ci,saidai gaba daya girkin kamar ba nata ba,ta cika masa yaji sosai,abinda tasan yafi tsana kenan,ya lumshe ido yana jin yadda yajin ke ratsa harshensa har kwanyarsa,ya sakeyin loma ya biyu ba tare da ya bari ta gane tsananin yaji da yakeji ba,saidai idanunsa suna kanta,ya tsatstsareta dasu ya hanata sakewa gaba daya,cikin jikinta takejin laifin data masa,amma zuciyarta taqi amsar haka. "Karomin" ya fada yana tura mata plate din,sai ta daga kanta da sauri cike da zallar mamaki ta kalli plate din ta kuma maida dubanta gareshi suka hada ido,idanun nasa da suka dan canza launi saboda tsananin zafin yaji,sai kuma ta janye idon nata ta basar,tasa hannu ta dauki plate din ta qara masa ta tura masa hadi da bashi qeya. Spoon ya sake sakawa ya kuma cinyewa,sanda ya sake cewa ta qara masa sai data zauna sosai ta dubeshi da kyau,bakinta yadan motsa kamar zatace wani abun sai kuma ta fasa,ta sake janyo plate din ta fara zuba masa "Wannan karon ki zuba yafi sauran yawa,muddin ta wannan hanyar zuciyarki zatayi sanyi......zan jurewa ci har sai kince na barshi haka" "Kayita ci,bazance ka barshi ba" ta gayawa zuciyarta hakan. Ta gefan ido ta dinga satar kallonsa ganin yana hanyar cinye uban abincin data sake loda masan,tun tana satar kallonsa harta koma kallonsa kai tsaye,ko sau daya bai kalleta ba yaci gaba da ci,ta kalli idanunsa zuwa sannan sun canza launi sosai,tasan yadda yajin abinci ke masa illa,musamman ulcer da yake da ita wadda idan ta tashi ba qaramar wahala take bashi ba,batasan lokacin data riqe hannunsa ba "Ka barshi haka" ta fada da sauri muryarta tana rawa. Jajayen idanunsa Ya daga ya kalleta dasu,sai ta gaza jurewa kuka ya qwace mata,ta saka dukka hannuwanta biyu ya rufe fuskarta dasu tana sakin siririn kuka. Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya iso gabanta ya tsaya yana dubanta zuciyarsa na wani irin tafasa,kafin yace komai tayi hanzarin bude fuskar saboda wani irin amai mai zafi daya danno mata,yana qoqarin riqeta tana qoqarin zamewa,saboda tasan muddin yaci gaba da riqeta zata wankeshi da aman. Bata iya riqeshi ba kuwa ta fara kwararashi,bai damu da yadda ta batashi ba saboda gaba daya hankalinsa a tashe yake,dama bata da lafiya?,tun yaushe?,duka bashi da wannan amsar,ya riqe hannuwanta sosai daya hannun nasa ya dafe mata bayanta yana jera mata sannu kamar zai ari baki. Shi ya gyara wajen,ya hada mata ruwan dumi ta gyara jikinta da ta bata shima ya gyara nasa jikin,tana kwance tana maida numfashi idanunta a kulle ya qaraso dakin,ya canza kayan jikinsa, boxer ne kawai a jikinsa,qaqqarfar kuma lafiyayyar surarsa ta fita sosai,ya dawo gaban gadon ya durqusa dab da ita ya kama lallausan hannunta ya riqe cikin nasa "Tun yaushe ne baki da lafiya?" "Kada ka tambayeni" ta fada muryarta tana rawa "Why?" Ya tambayeta a mamakance,sai data zame hannunta daga nashi sannan tace "Saboda baka damu dani bama gaba daya bare lafiyata" Tashi yayi ya haye gadon gaba daya,ya jawota cikin jikinsa dukkaninta ya rungumeta tsam,bata da qarfin da zata qwace a jikinsa dole haka ta zauna,a hankali sai taji yadda zuciyarsa ke bugawa da Wani irin qarfi n da ya wuce qa'ida "Tun daga wancan lokacin da abun ya faru haka kullum zuciyata take bugawa,ban taba zaton zankai wannan lokacin ban kamu da ciwon zuciya ba,komai nina aikata miki shi,amma bisa wani umarni da bansan daga inda zuciyata take karboshi ba.......kiyi haquri da dukkan abinda ya faru,ki kuma yafemin,amma nayiwa zuciyata alqawarin bazan bar wannan abun ya wuce a haka ba, kowanne irin tunani nasan zaki iyayi a kaina,dai dai ne bazan hanaki ba,amma ki bani dama......i need a chance don Allah don kuma affan bawai don ni ba" daga wannan maganar ya zame jikinsa daga gareta,ya barta da tunani. Hijab ya dauko mata sannan ya dauko affan "Muje kiga likita,bai kamata ki kwana hakanan ba" shi ya taimaka mata har zuwa bakin mota,sai data shiga ya kwantar da affan a baya sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi. Idanunsa qyar akan allon computer din sanda likita yake mata scanning,yara biyu ne gasunan kwance a mahaifarta har zuciyoyinsu sun fara bugawa. Da sauri ta dauke kanta gefe hawaye yana sauko mata,ta yaya zata iya rainon cikin 'yan biyu?,bayan ko yaye affan batayi ba,a wannan yanayin da take ciki bata jin tana da qwarin gwiwar da zata iya rainon cikin ma gaba daya "Satin cikin sha biyu gashinan,congratulations" Dr anwar likitan mai matuqar kirki da barkwanci ya fada. Abbas dake jinsa kamar a duniyar mafarki ya miqa masa nasa hannun,Allah me yadda yaso a lokacin da yaso,cikin yanayin da yake na daukewar dukkan wani farinciki daga rayuwarsa sai ga hasken farinciki ya ratso daga ubangiji,ya maida dubansa ga widad hankalinsa ya tashi da ganin hawayen da take zubarwa,ya matsa saman kanta yana jera mata tambayoyin akwai abinda ke mata ciwo ne?,saita gyada kai "Bari ina zuwa" Dr anwar ya fada yana fita a office din,hakan ya bawa abbas damar dagata,ta zauna sosai yana riqe da hannunta,saidai ya kasa zama,yana tsaye ne tsakiyar qafafunta yana kallonta "Bani da qwarin gwiwar rainonsu da haifarsu" ta fada tana zubda sabbin qwalla,sai ya dora yatsantsa saman labbansa "Zan baki duk wani qwarin gwiwa da kika rasa,zan baki dukan hope,zamu rainesu tare na kuma tayaki naqudarsu,don Allah ki kwantar da hankalinki na roqeki,ina da buqatarsu,burin kuma hajiya kenan kullum taga tarin jikoki daga wajenki" furta sunan hajiya da yayi ya sake sanya damuwa da karyewar zuciya a zukatansu su duka biyun,sai ya matso ya sanyata cikin qirjinsa yanason saukar mata da nutsuwa. Tun daga wanna lokaci gaba daya ya maido hankalinsa akan widad din,ya bata dukkan lokacinsa ya rage ranakun fita aikinsa,ya hanata yin komai,komai shi yake mata,yayi nata yayi nasa yayi na affan,sai daya gama karantar komai da takeso naci sha da sauransu,wani lokacin har tausayi yake bata,duk da har yanzu ta kasa warewa yadda suke a baya,abinda yake qara masa damuwa cikin qirjinsa kenan,yake ganin kamar komai bai wuce a wajenta ba. Tun randa yaci wannan abincin qirjinsa yake yawan riqe masa da ciwo,amma sam bai nuna mata ba,don so yake ya dawo da dukkan farinciki da walwalarta. [5/22, 10:12 AM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 35 Wannan shine babban damuwarsa kafin ya tunkari abinda yake gabansa. *******Qarfe daya na tsakiyar dare ya farka da wani irin mugun gumi da yake karyo masa,saboda riqewa da qirjinsa yayi da wani irin mugun ciwo,da qyar yake iya jan numfashi,ya laluba hannunsa ya kunna fitilar gefan gado,haske ua gauraye dakin nasa,shi daya yake kwana,bai taba takurata ko sau daya akan su hada makwanci ba,hasalima ta lafiyarta yake,ya sauko daga gadon ya fita waje don ya samu ruwa mai sanyi yasha ko qirjin nasa zai sake,ya tabbatar ciwon da yaketa dannewa ne yau yaci qarfinsa. Haki ya dinga yi sosai bayan yasha ruwan,ya samu hannun kujera ya zauna yana riqe da qirjinsa,a hankali ya fara kiran sunan Allah ganin ciwon yana neman yafi qarfinsa. Tana yawan fama da qishirwar dare,tsakiyar baccinta ta tasheta,ta farka a hankali tana mutsitsike idanu sannan ta zauna sosai tana kallon sashen da abbas din ya zauna dazun,wayam babu shi,ya zauna ne yana karanto mata wasu laifuka cikin system dinsa da wasu suka aikata ya kamasu ya kaisu kotu da hukuncin da kotu ta yiwa kowannensu,batasan sanda bacci ma ya dauketa ba. Ba ruwa a dakin,dole ta gyara farar hular data dora kan sassalkar sumarta ta zura bedroom slippers dinta ta fito. Da farko tsorata tayi jin alamun mutum cikin parlor din,amma kuma sai sautin muryarsa dake tashi can qasa ta gaya mata waye,cikin tashin hankali sosai ta iso gareshi. Gaba daya ta rude da yadda taga ya fita a hayyacinsa,tana ta son ta kira wani cikin mutanensu na nan amma ya riqe hannunta gam ya hanata motsawa,batasan sanda hawaye ya fara zaryar saman fuskarta ba,yanayin yadda yake riqe da qirjinsa ta tabbatar ulcer dinsa data jima bata tashi bace a yau ta tashi,kuma ko bai gaya mata ba ta tabbatar abincin data bashi ne yaci. Sosai hankalinta ya tashi,gani take kamar mutuwa zaiyi a daren,kamar bazai kwana ba,indai hakan ta kasance kenan itace ajalinsa?,abinda ya sake daga mata hankali ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai. Duk da cikin ciwo yake amma hakan bai hanashi jawota cikin jikinsa ba yana dan bubbuga bayanta "Kayi haquri daddy,ni na jawo maka" "Shshshsshsh" kawai yace da ita,sai tayi lamo cikin jikinsa,cikin ikon Allah zufar jikinsa ta fara raguwa,kasa sakinsa tayi,har zuwa sanda taji numfashinsa yana sauka a hankali da alama bacci ya fisgeshi. Har zuwa lokacin bata bar share hawaye ba,ta sake qanqameshi cikin jikinta tausayinsa ya kamata a karo na farko,hajiya ce ta fado mata,tayi imani inda tana raye ko meye zai faru bazaikai tsananin wannan ba,ta tuna maganarta ta qarshe akan abbas da affan "Allah ya baki ikon riqesu gaba daya" har maganar ta bawa widad din mamaki,ashe kusan wasiyya hajiyan ke bata. Dukkansu kukan affan ne ya tayar dasu,da tafiyarsa daya fara koya ya qaraso wajen,sai abbas din ya miqa hannu yana daga kwancen ya daukoshi cak ya azashi saman ruwan cikinsa yana kallon yaron fuskarsa dauke da murmushi "Am sorry son.....na hanaku bacci kai da mamanka ko?" Ya fada a karye,saita miqe ta zauna sosai tana masa sannu kafin ta kalli agogo,an riga an idar da sallar asuba,dole sai hakanan suka yita a makare. Yau din musayar aiki akayi,ta hanashi yin komai tayi dukkan wani aiki kamar yadda ta saba a baya,yana kwance yana binta da kallo,duk inda ta gifta sai wani abu ya motsa ransa,zuciyarsa bata masa dadi da yadda ya zargeta ya dasa bacin rai a ranta,ashe yaransa har biyu suna kwance a mahaifarta. Wuni sukayi ranar a tare,har bayan la'asar tana ta hidimar hada musu abincin dare,affan yana kwance saman cikinsa,tayi tayi ya dagashi saboda qirjinsa amma yace "Ki qyaleshi,yayi missing dina shima" tasan akwai magana a bakinsa amma ta shareshi. Cewa yayi tazo ta dauke affan din,tana isowa yasa hannu ya janyota jikinsa,sannan ya sauke affan a gefe,sosai ya sakata cikin jikinsa yana kallon fuskarta "Da gaske widad....bagarar dani kiketa yi,yau kwanaki nawa da dawowarki,da gaske bakiyi missing dina ba?,hala kin daina sona?" Ya fada murya a karye,hannu tasa tana ture fuskarsa daga tata,saboda wani nauyi yake sakar mata da manyan idanun nan nasa "Daddy bamu da lafiya dukkanmu,ka barmu mu warke cikin salaama" ido yadan lumshe sannan ya budesu ya zubesu fes kan fuskarta,saita janye idanunta tayi kamar bata ganshi ba "Alright.....jibi nakeso na wuce bauchi" ta daga kai a hankali ta kalleshi,ranta yadan quntata kadan da zuciyarta ta tuna mata da hafsat,wajenta zaije kenan?,kamar yasan me take rayawa sai yace "Wani aiki ne mai muhimmanci ya tasomin" "Amma daddy,su office din basusan har yanzu baka gama warkewa ba?" "Saun dauka na gama warkewa sumul,tunda sunsan ina da jarumar mata dake bani kulawar dake warkar da zuciya da gangar jiki,basusan wannan karon ta zama raguwa ba" kanta ta kawar kawai,tasan jan magana yakeso,ya saki boyayyen murmushi,wannan boyayyen fushin nata ya barta ne kawai,yana jiran lokaci,zai sauke mata shi tassss,a yanzun taci albarkacin abinda yake jikinta ne,amma itama ta sani,yasan lagonta fiye da yadda take tsammani,ya kauda shurun da ya wanzu a tsakaninsu "Aikin yana da muhimmancin da bazai iya jikirtuwa ba,saidai kiyimin fatan nasara kawai" ya fada yana lumshe idanu,yana tuna wayar da sukayi dazu da umar dinsa,wadda a qalla ta kwashesu kusan awa guda. "Allah ya bada sa'a ya kuma bada nasara" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu". Bayan ya kwantar da affan sai ya bita kitchen suka kama aikin tare,ba wata doguwar hira a tsakaninsu,amma lokaci lokaci tana kamashi yana satar kallonta,kallon da batasan na meye ba,daga bisani ya gaza jurewa,ya zagayo ta bayanta ya riqe qugunta sosai ya jawota cikin jikinsa, ya dora habarsa saman kafadarta "Wannan cikin yayi miki kyau fiye dana affan,ina fatan zaki bani baby girls masu kama dake this time around" murmushi ta saki tana jin saukar numfashinsa har cikin kunnenta,hakan kuma ya fara tayar mata da tsigar jikinta,saita zame a hankali "Eheeennnn.....gwara ma ka fadi gaskiyar ka,koda baby girls dinne masu kama dakai kakeso,ka dauka ba'a gayamin ba,sanda na haifi affan yadda ya deboka ya dinga maka dadi har baka iya jure fada" siririyar dariya ya saki,ya koma ya jingina da kitchen cabinet yana kallon kyakkyawar fuskarta "Bakisan kin fini kyau ba?,affan namiji ne,duk munina idan yayoni ba matsala,kinga kenan dama baby girls din ne yafi kamata su dauko ki ko?" Yadda ya kira kansa da mummuna ya sanyata dole ta daga kai tana sake dubansa da kyau,suka hada ido yayi wani kalar tausayi kamar ita zata zana masa yaran,sai dariya ta qwace mata. A sirrance ya sauka a bauchi,ba wanda yasan ya iso bauchi sai umar,ya kuma gana da manager din hotel din a ranar bayan ya kama daki a wani hotel na daban. Duk wani dauka na cctv camera dake hotel din saida yasa aka sauke masa,tun daga kwanan watan da kwanyarsa zata iya riqe masa na sanda suka fara zuwa weekend shi da widad,ya wuce dasu dakin hotel dinsa dasu. Sai da ya gama komai ya nutsu sannan ya fara bibiya,komai tiryan tiryan,bayan ya bawa umar wasu yace ya tayashi,amma ya tabbatar sai yana kebantaccen waje kamar haka. Aikin ba wani sabon aiki bane a wajensa ba,yana da kafiya da jajircewa akan aikinsa,idan yasa qahon zuqa akan abu sai ya ganoshi,saidai idan baiyi niyya bako bai sa kansa ba,wannan na daya daga cikin sirrin samun qarin girmansa akai akai,dom haka kuma zama bibiyat dukka motsin hotel din na watanni bai wani jigatashi ba,daren gaba daya ya sadaukar yayi wannan aikin,sai coffe kawai da yake makawa cikinsa. Ya tsaya ya jajirce yayi aikinne bawai don har a sannan akwai sauran zargin widad a ransa ba,a'ah,yayi hakanne saboda ya zamana shima yana da hujja kamar yadda tsarin aikinsu yake. Bai gama ba sai kusan azahar,zuwa sannan idanunsa sun kada saboda tsabar rashin baccin da kallon abu daya,amma duka wannan bai dameshi ba,sai wata nutsuwa data dinga saukar masa "Subhanallahi wabi hamdih,subhanallahil azeem" ya dinga maimaitawa yana lanqwasa yatsunsa,cikin tsakiyar kansa yana sake samun kansa da tuhumar kansa da kansa,tuhumar da tunda ya dawo hayyacinsa yakewa kansa,har yau kuma ya rasa dalilin da yasa ya fita hayyacinsa a wancan lokacin da har yau iya aminta da wannan mummunan zargin wa widad,wanda baisan me zaiyi da zai wankeshi ba,amma ya dora hakan bisa mizanin qaddara da jarrabawar rayuwa da rayuwar kowanne bawa bata rabuwa da ita. Ko kwana daya bai qara a hotel din ba ya hada kayansa gaba daya ya kira umar yace yazo ya kaishi gida,yawan baccin dake kansa bazai samu sakewa yayishi cikin dakin hotel din ba. Yana cikin mota ya kira Ezekiel,daya daga cikin yaransa dake bauchi,ya kuma bada umarnin ya hada yara suje su kamo masa lawal duk inda yake,amma bayason sunansa ya fito a ciki gaba daya,ko don saboda yaaya sa'id(mahaifinsa),ya masa bayanin kalar tuhumar da yakeso ayi masa,ya kuma aika masa da number wayar lawal din,yace kada su karbe wayarsa,muddin ya buqaci kiran wata me suna hafsat su bashi dama ya kirata,sannan ya kashe wayar,ya maida bayansa sosai jikin makarin kujerar yana karkata akalar tunaninsa kan next target.[5/23, 10:14 PM] +234 803 416 2581: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 36 Har sun dauki hanyar gida ya cewa umar ya kaishi gidan hajiya,ya sakashi ya shiga da motar ciki ya karbi key din gidan ya bude ya shiga. Komai na gidan yana nan tsaf tamkar tana raye,ba qazanta ba komai,su umar suna kula da gidan yadda ya kamata,har ya bude parlor dinta zai shiga sai ya kasa daurewa,ya fito ya bude dakinsu umar din. Wanka yayi ya sanya boxer da farar riga armless,ya rage hasken dake shigowa dakin ya kwanta,a maimakon bacci sai tunani suka cika kwanyarsa fal,ya dinga bitar halaye da dabi'un hafsat din,yana kuma irgen shekarun da suka dauka a haka ba tare da wani sauyi daga gareta ba,har cikin zuciyarsa yana jin ya fara qosawa,haqurinsa kuma yana dab da qarewa,abu daya yake tunawa yake kuma tausayawa,mimi nawwara da yusra,bayason su girma su kalleshi a matsayin wanda ya gaza wajen samar musu da nagartacciyar uwa. Haka yayita saqe saqe,kansa kamar tsage saboda rashin bacci da tunani,dole ya jawo wayarsa yana dubawa,ya cika da mamaki fal na rashin ganin kiran widad ko sau daya daga jiya zuwa yau,wani abune da bai taba faruwa ba a tsakaninsu saida wannan ibtila'in ya fadowa rayuwarsu,ya gama lalubensa sai ya kirata kai tsaye. Tana zaune riqe da wani qaramin littafin addu'o'i da anty madeena ta hadota dashi tana dubawa tare da qoqarin haddace wadanda suke na ko yaushe suke fi kuma muhimmanci,tun jiyan yana ranta,amma kuma batason bada kanta ta kirashi,tanason ta auna yadda take da matsayinta a yanzu a zuciyarsa,akwai abinda ya sauya ne ko har yanzun tana nan dai a yadda take a wajensa bata motsa ba. Qarar wayar yaja hankalinta,koda ta duba taga sunan data saka masa akan wayar sai ajiyar zuciya ta qwace mata,ta kife littafin ta dauki wayar ta kara a kunnenta. Sassanyar muryarta ta sauka a kunnensa, abinda ya sakashi sakin ajiyar zuciya da sautinta ya shiga kunnuwan widad "Kina azabtar dani da yawa maman affan,na dahu haka na dahu,wallahi nayi laushi over,don Allah kiyi haquri ki sassautawa dan marayan da baida uwa baida uba......sai Allah saike......" "Sai kuma uwar gidansa,sarautar mata" ta tari numfashinsa tana qarasa maganar da ba ita ta daukota ba. Dif sukayi gaba dayansu shida ita,ita tana sauraren amsar da zai bata,shi kuma yana fama da wasu abubuwa data saukarwa zuciyarsa,sai yaji harshensa yayi nauyi,duk wani abu da yayi shirin fada ya kama gabansa,bashi da sauran zabi illa zame wayar daga kunnensa ya kuma kasheta gaba daya ya koma yayi rub da ciki yana sauke numfashi da qarfi. Taji lokacin da wayar ta tsinke,don haka ta cireta daga kunnenta tana kallon wayar,tausayinsa ya darsu a ranta,amma ya zatayi,ta kasa daina jin zafin wai hafsta ce zata hadasu?,har ta isa ta zama silar girgizar yadda tsaftatacciyar qauna shaquwa da soyayyar da suka ginata ita dashi?,wata zuciyar na raya mata ta kirashi,wata tana hanata tare da gaya mata ki barshi ya sake dandanar irin abinda kika dandana,duk da ranta ba dadi hakanan ta shareshi,ta dauki littafin addu'o'inta taci gaba da dubawa. Da qyar ya samu bacci ya daukeshi,saboda maganar data gaya masa tayi masa nauyi da yawa a qirji,ya samu baccin nasa yayi nisan zango,don har missing salloli biyu yayi,ya tashi da hanzari ya daura alwala ya bada su, kafin ya kammala wayarsa ta fara tsuwwa alamun shigowar kira. Miscall uku ne na ezekiel,kafin ya gama dubawa tex ya shigo masa akan idan ya samu miscall dinsa ya kirashi. Sai da ya gama 'yan addu'o'insa sannan ya zauna sosai gefan katifa ya kira Ezekiel din,bugu daya ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa,sannan ya fara bashi feedback akan aikin da ya basu. Tunda ezekiel ya fara bayanin idanunsa a kulle suke yana saurarensa,babu abinda zuciyarsa keyi illa bugawa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai yake maimaitawa a hankali bakinsa yana motsawa,sai da ya gama bayanin tas abbas yayi saluting nasa,ya kuma tattara komai kama daga recording na muryarsa da video ya turawa abbas din ta email dinsa sannan sukayi sallama bayan ya gaya masa kwana biyu yakeso lawan yayi a cell,zaizo da kansa ya fiddashi. Duk da jikinsa yayita bashi hakan,duba da sanya idanun da yasa umar yayi masa kan yanayin mu'amalar dake tsakanin hafsat da lawan din,amma kuma ya girgiza matuqa,yadda har lawan ya iya aminta suka hada baki suka shiryawa widad din wannan tuggun,wanda kai tsaye zai iya cewa shi suka cutar bawai widad ba,duk abinda zai cutar da iyalinsa kai tsaye za'a iya cewa shi ya cutar,bare mummunan al'amari irin wannan,ya jima yana juya dalilin da yasa hafsat din ta sadaukar da lokacinta da kudinta ta sanya akabi widad din har hotel din akayi mata hotunan,me hakan ke nufi?,me takeson ta cimma,tace gyara,amma ta haka ake bin hanyar gyara?. Bai dauki komai ba illa key din motarsa ya fita a gidan ya nufi gida,yana tuqi cikin qarfin hali ne kawai,babu wani karsashi a tuqin nasa,har ya isa gidan,ya wuce parking lot ya ajjiye motarsa. Sashensa kawai ya nufa,don sai yaji gaba daya ya tsani kallon fuskar hafsat,mutum ne tsayayye ma'abocin gaskiya da kuma son aiwatar da ita,wannan ya sanya ya tsani qarya da maqaryacin mutum qwarai da gaske,ya buda sashen nasa ya shige ya maida muqullin ya rufe,sannan ya wuce bedroom dinsa kawai ya fada saman gadonsa qwaqwalwarsa na zayyano masa kalolin hukuncin da zai dace za hafsat,don ta lawan ya tabbatar ko iya haka ya barshi ya zuwa yanzu ya gane Allah daya ne,bare shi dinma bazai qyaleshi haka ba,yabar masa gidansa bari na har abada. *H A F S A T* Tun da rana data aiki lawan take jiran dawowarsa amma shuru wai malam yaci shirwa,tun tana bashi uzuri harta tunzura ta fara fada,ta kuma fara neman layinsa amma anata gaya mata a kashe layin yake,ta zauna tayita masifa tana kumfar baki,ragowar lace din da aka siya na anko ne a wajenta guda daya bai cika ba,ta bashi kudin kan yaje kasuwa ya cikaso mata dayan,gashi sun gaya mata suna hanya amma shuru babu shi ba dalilinsa. Sai data gama fadan ta godewa Allah ta koma taraddadi kuma saiga kiransa,sanda ta daga da niyyar yin sababi sai maganarta ta tsinke sanda taji muryarsa a shaqe kuma cikin tashin hankali yana magana da ita "Ina hannun police,sun kamani ne akan batun maman affan, wallahi bakiga mugun dukan da nakesha a hannunsu ba,yanzu haka basusan da wannan wayar a hannuna ba,sun gama dukana sun fita su hutane na kiraki,don Allah kizo kiyi beli na,ki fitar dani daga wannan masifar da kika jefani a ciki". Wata hajijiya ce ta kwasheta ta jefar,dama da gaske ne kenan?,ashe dai zancen bai mutu ba?,wannan wacce irin masifa ce,tana zaton komai ya lafa,tana zaton ta samu nasara ashe qura tana baya "Idan na sake nazo wannan wajen lawan na zama nama na tabbatar,ka jirani zan nemi abban mimi na gaya masa qarya da gaskiya,zaiyi magana kosu waye na tabbatar zaka fito" saita yanke kiran tabar lawan da waya a hannu cikin matuqar mamakin yadda takeso ta barshi shi kadai a masifar,bayan ita ya yiwa aikin. Sanda taketa yunqurin kiran wayar abbas din a kashe take,dai dai sanda ya kashe wayarsa bayan widad ta yaba masa maganar data masa zafi matuqa,tayita kira a jere amma amsar daya ce,haka ta fito wajen baqinta tana rarraba idanu,fuskarta a yamutse,gumi yana tsattsafo mata ta kowacce kafa ta jikinta "Don Allah ina zuwa" ta fada tana yin waje da hanzari zani a hannu kamar zata ci da baka ta fara kiran wayar habiba tana dosar sassan abbas da nufin fakewa a can tayi wayar,don can dinne bata da haufi dashi,tana da tabbacin babu kowa a ciki bare tayi shakka ko taji dar dar din wani zai iya jinta. Koda ta bude sashen abban din sai data tabbatar ta qule har cikin bedroom dinsa,tsabar hankalinta a tashe yake bata ma yi tunanin yadda akayi qofar bedroom din yake a bude ba,burinta kawai ta isa dakin habiba kuma ta daga wayarta. Sama sama ya dinga jin magana yana tsaye gaban madubin bandakin yana kallon fuskarsa,ya matsawa kansa da tambaya da kuma tunanin son sanin yadda akayi ya yankewa widad wannan hukuncin,ya akayi ya aminta da zancan hafsat,a irin baiwa da Allah yayi masa,a irin matsayi da yake dashi da rank a wajen aiki?, tabbas wannan babbar jarrabawa ce,kuma qaddara ce mai girma,wadda ya godewa Allah da ya taqaita masa komai,bai jarrabeshi da sakin widad ba. Sautin muryar hafsat da ya fara ji yasa ya tako a hankali zuwa gaban qofar,har ya sanya hannu zai bude qofar sai ya fasa,kalamanta cikin rudani da tashin hankali suka fara shiga kunnuwansa "Ina cikin tashin hankali habiba,komai yana iya faruwa dani,wannan maganar dai bata mutu ba yadda malam yace,yanzu haka lawan yana hannun 'yan sanda ba,na tabbatar zuwa yanzu indai sun gama bincikarsa to asirina ya gama tonuwa,don ba lallai ya iya iurewa dukansu wallahi sunana zai fadi,ki taimakamin habiba a sake danne maganar nan,dama hankalina tun ranar da sukayi maganar zuwa kotu ba'a kwance yake ba,ko baccin kirki bana iyayi wallahi,idan har abbas yaji maganar nan bani da sauran dabara kuma sai abinda y........" Gaba daya ya rasa karsashi da qwarin gwiwar tsaiwa yaji qarshen maganganunta,hankalinsa yayi mummunar tashi,bayan sharri makirci da qazafi harda bin malamai hafsat din ta hada dashi?,a yaushe?,kuma yana me?,sai kawai ya buda qofar da wani irin qarfi,qarar qofar taja hankalin hafsat har sauran maganar ta maqale mata a maqoshi. Batasan wanne yanayi ta shiga ba,suma tayi a tsaye ko mutuwa tayi ta dawo?,itadai ta bude idanunta taga abbas a gaban mudubi riqe da biro yana rubutu,ta dinga qoqarin zaqulo kalamai daga qasan maqoshinta amma kalma daya ta gaza fita daga bakinta,har ya kammala rubutun ya iso inda take ya ajjiye takardar a gefanta "Daraja daya zuwa biyu kawai zakici yau a hannuna,na farko iyayen widad tun sunan zallar tauhidinsu,sun miqa ki kotun ubangiji wadda babu wata kotu a gaba da ita,babu wani adalin alqali da yakai ubangiji iya hukunci,to kije ni dasu suka mun barki da wannan,na biyu kuma kinci darajar mimi nawwara da yusra,banason na fito na qara ganin fuskarki cikin dakin nan,idan kuma baki yarda ba......" Sai ya murza yatsunsa kawai ya gewayeta ya fice ya barta a wajen a tsugunne. Dukka hannuwanta ta saka ta kama kanta da kyau ta riqe,sai kuma ta saki kuka mai qarfi kamar wata zautacciya "Haba abbas......daddyn ya zakayimin haka?,ko meye nayi nayi ne saboda kai" sake rushewa tayi da kuka,tana jin abun tamkar a mafarki,yau ita abbas ya saka?,abinda bai taba giftawa ba tsahon zamansu sai a yanzu?,a dalilin wata?,wai shin saki nawa ma yayi mata?,sai ta zabura ta dauko takardar ta warware jikinta yana rawa kamar wadda zazzabi ya yiwa mugun kamu. Saki biyu ta gani a rubuce fes,ta saki takardar tana sake rushewa da kuka,duk da ta samu sassauci ganin akwai sauran igiya daya da tayi saura, saita miqe da sassarfa ta fita daga dakin nasa ta doshi sashenta. Wayam ta tarar babu kowa,ba yaran babu baqinta,ta shiga nemansu kamar zautacciya lungu da saqo na gidan amma babu su,a bakin gate shazali ya gaya mata yaga mai gida ya fita shi da yaran duka a mota,batasan sadda ta sulale a wajen ba ta sake fashewa da kuka,tsoro ya kama shazali ganin yadda take sheqa kuka yau a gabansa,gashi babu damar ya tambayeta ko kuma ya bata haquri saboda yasan cin mutunci irin nata,haka ya koma gefe yana satar kallonta,har ta gama me isarta taja qafafunta tayi cikin gida bayan tayi futu futu da jikinta a wajen. Baifi minti talatin ba sai gata da jakarta tana janta,ta buda motarta ta jefa jakar ta shige itama,ta dannewa shazali wani mugun hon,tuni ya durfafi gate din ya bude mata da hanzari gudun kada ta huce haushinta a kansa. Gidan yaaya bara'atu yakai yaran wadda ta cika da mamakin ganinsa,diyarta budurwa ta kira ta dauki yaran,tace ta hada musu abinci,tuni sukabi bayan mariya ta zuba musu abincin suka sake abinsu sunaci,don dama yunwa ce fal cikinsu,tunda tun rana rabonta da basu abinci,tana ta business dinta,sai kuma wannan tashin hankalin yazo ya ratso na kama lawan,hatta da yusra abinci taci sosai,suna gama ci ba dadewa dukkansu bacci ya kwashesu a wajen. A can falo kuwa Shuru yaaya bara'atu tayi kamar ruwa ya cita,jikinta gaba daya ya gama mutuwa murus,tausayi da kuma namijin qoqarin da abbas yayi na zama da ita har tsahon wadan nan shekarun duka sun gama kasheta,gidan abbas dama duka ba wajen zuwansu bane,don babu fuska daga wajen hafsat din,wannan yasa da yawan dangi suka janye jiki saidai idan an hadu a gaisa,wannan ya sanya da yawa basusan wanne hali yake ciki ba,sai idan taso kawo qorafinta a kansa ta hada qarya da gaskiya ta fada saboda ta bawa kanta kariya. "Inason yaran suci gaba da zama a wajenki kafin na gama settling komai" "Ko har abada zakace ka barminsu ina maraba da haka" ta fada tana girgiza kai zuciyarta tana karaya,tausayin yaran na sake kamata. Murmushi kawai ya saki,yana son yaransa sosai,bayajin zai iya kyautarsu. Daren ranar daga hafsat har ummanta babu wanda ya runtsa,sun raba dare suna jajanta abun,don basu taba zaton zai iya sakinta ba,sun masa mugun qullin da tun aurensa da hafsat din sukayi wannan shirin,tsohon shiri ne da ita kanta hafsat din ta manta anyishi,saboda a sannan zuciyarta najin zata iya zama da abbas ba tare da anji kansu ba,zata kuma iya sauke duk wani hakki nasa,tayi abinda yakeso tabar wanda bayaso,don sanda umman ke mata albishir din anyi abun ma ita bata wani daukeshi da muhimmanci ba. [5/23, 10:14 PM] +234 803 416 2581: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 37 Tun bakwai na safe ya gama shirin barin bauchi ya wuce katsina,sai daya tabbatar yabar gidan hannun umar,yace ya kula da kowanne sashe na gidan,idan ya gama ya rufe gidan,ya kaiwa yaaya bara'atu key din,sannan ya dauki dukka wani abu me muhimmanci ya zuba a motarsa ya fice a gidan. Gidan yaaya bara'atun ya fara isa,tasa aka kawo masa breakfast ya taba sama sama,don shi yanzu kowanne abinci kallon hadarin kaji yake masa indai ba abincin widad ba,bayan ta sallami mai gidanta dake sammakon fita tazo suka zauna,a sannan su mimi na tare dashi,yaran duka babu wata damuwa a tattare dasu,ita mimi ma nata murnar "Daddy har anyi kana wanka munci abinci,daddy aiba yanzu zamu koma gida ba ko?" Sai ya gyada kai yana shafa kanta,tausayin yaran kawai yake damunsa,banda mutuwa babu abinda zai raba uwa da danta,amma da yake Allah ya jarabcesu da shashashar uwa bata wani shiga jikinsu da zasu damu can da ita ba,kawai yana baqincikin su girma su tuhumeshi da rashin samar musu da uwa ta gari,saidai yayi imanin Allah bazai taba tozartar dashi ba,tunda yayi dukkan iya bakin qoqarinsa bisa kyautatawa hafsat din zato ya zabeta a matsayin uwar 'ya'yansa. Duk da yaaya bara'atu tana dojewa amma bai bar mata wahalar yaran ta sisin kwabo ba,komai sai daya ajjiye musu kama daga na islamiyya har zuwa na boko,sannan ya bada wasu kudaden yace a canza musu suturar sanyawa,saboda ya lura da yadda kaf kayansu suka qarasa macewa,harda tsadaddun laces din da ya dinka musu,wanda ko shekara basu rufa ba,don shi baya jiran sai wani lokaci na daban zaiyiwa iyalinsa dinki,kusan ko yaushe cikin yi musu suttura yake. A nan ne tace ba zata karba sisinsa ba, dole ya maida kudin dinkinsu,ya mata sallama ya wuce. Tunaninsa a hanya kaf ya qare kan yadda zai doshi widad da yadda zai hukuntata,don ya gaji da maganar da take yaba masa a fakaice,yanaji a jikinsa muddin taci gaba da haka wataran za'a wayi gari ya samu matsalar hawan jini ko zuciyarsa ta tabu,ta shiga rayuwarsa da yawa,a yanzun kuma ta sake kutsawa nisan inda baiyi zato ba,wannana abun da ya faru sai sake qara mata kima da daraja a idanunsa,ya sake qaunar iyayenta tare da ganin zallar dattakonsu. Tun tana bagarar da batunsa daga ranta har tadan soma jin damuwar rashin jin wayarsa da kuma dawowarsa,amma hakanan dai taci gaba da daurewar tana yakicewa. Ko a yau data tashi duk jikinta babu kuzari sosai,ta gama komanta da wuri wajejen azahar,saita zauna shuru,sai kallo da kuma duba littafi zuwa waya da ta dinga yi,affan baya nan,wata maqociyarta ta daukeshi tun azahar din,babbar macace,dukka yaranta sun girma,shi yasa suke da son qananun yara. Karfe uku da kusan minti talatin da tara ya sauka a cikin gidan,ya sanya motarsa cikin parking lot ya kasheta,ya fito yana yiwa yaron gidan magana ya bude booth na motar ya fidda tsarabar da yayo a hanya ya aje masa qofar falon sannan ya wuce. Knocking yayi,ta dauke fuskarta daga kan littafin dake hannunta,sai ta aje littafin ta miqe a zatonta affan aka dawo dashi,tana gyara wuyan rigar wata bubu ta net da aka yiwa shafin wani irin yadi me kyau daga qasanta,rigar tayi mata kyau sosai,saboda ko ina na jikinta ya a cike yake,babu wani rami loko ko lobawa sai inda yake dama a halittar diya mace haka yake,fatarta lumui lumui,wiyanta ta saka wani ziririn zaren sarqa me qyalli da ya ake qawata wuyan nata,ta riga data saba,ya kuma zame mata jiki,ko yaushe a haka zaka sameta fes tana fidda qamshinta me laushi. A nutse ta bude qofar,ta buda siraran labbanta zatayi magana sai maganar tata ta maqale,yana tsaye gaban qofar falon hannunsa harde a qirjinsa,idanunsu suka gauraya waje daya,sai wani abu ya tsarga ma kowannensu,wani abu ya tasowa widad mai matuqar qarfi da tasiri. Ashe dai qarya ne idan kace ka daina son mutum?,ashe dai qarya ne kace baka damu da masoyinka ba saboda wani sabani ko bacin rai,saita juya da hanzari zuwa ciki,batason ta bada kanta. Baice mata komai ba ya dauki kayan duka ya shiga dasu ciki,ya maida qofar ya rufe,ya tsaya tsakiyar falon yana sauke ajiyar zuciya hancinsa yana zuqar lallausan qamshin da yake bayarwa,qirjinsa yana masa wani irin wasai,duk uban nauyin nan da yakeji cikin qirjinsa a yanzu babu shi,yana jin kamar ya sauke wani uban dutse daya danne masa zuciya. Ya wuwwulga idanunsa bata cikin falon,yasan ba zata wuce bedroom dinta ba,don haka ya wuce kai tsaye. Gaban madubi ta wuce kai tsaye, tayi tsaye kawai tana kallon fuskarta da qirjinta dake motsawa saboda bugun da zuciyarta ke mata,ta lumshe ido tana tuhumar kanta akan yadda take samun sauyi akan abbas din,duk wani alwashinta yana sulalewa yana yin nasa waje. Sam bataji shigowarsa ba,sai sautin muryarsa daga bayanta "Me bakin tsiwa,ina tsiwar taki ta tafi?,kin iya gasama mutum magana ko?,ki barshi da ciwon zuciya kiqi nemansa" ya fada yana kafeta da ido,gami da hukuntata da kallon nan nasa,haka kawai batasan ya akayi ta juye masa kalar shagwabarta data saba ba,saita tura baki gaba taja baya tana qara kusancin dake tsakaninsu "Qarya nayi?,ai banyi qarya ba k......." Kasa qarasawa tayi saboda yadda taku biyu kacal ya hade ratar dake tsakaninsu,yaci gaba da ritsata da kaifaffen kallon nan nasa "Uhmmm......qarasa mana" ya fada yana matsota. Ta hangi fitintinu bama fitina ba fal idanunsa,ta kuma tabbatar yau idan ya kamata zata ji jiki da kyau,don haka ta kulle bakinta taqi tanka masa,saidai duk da hakan bai fasa matsota ba,har ya danga da bangon dakin "Tunda kinji tsoro zan qarasa cire wannan rashin kunyar taki,kin dauka ni age mate dinki ne ko?" Kai ya shiga girgiza masa,saidai kafin tace wani abu yakai mata cafka,yayi mata wata wawuyar runguma har yana takure abinda ke kwance a cikinta,baiyi wata waya ba ya hade bakinsu waje daya,ya fara aika mata da wani zazzafan kiss,wanda ko sau daya ya gaza dauke bakinsa daga cikin nata. Cikin mintunan da ba masu yawa ba ya zare mata dukka wata laka ta jikinta,ya cire dukkan wani zafin rai taurin kai da kuma qwafar data yi masa,cikin qalilan din mintuna ya zautata,ya jefata wata duniya wadda ta mantar da ita wacece ita,ta sukurkuce gaba daya,ta kuma miqa masa kanta,irin miqawar da bata tashi gane cewa ta tafka abun kunya ba sai bayan da komai ya kammala,tana kwance a qirjinsa tana kukan da dai dai yake da nade tabarmar kunya. Tabbas taji jiki a hannunsa,ta kuma biya dukkan bashin soyayya da kewa da suka cima juna,yana maqale da ita tsam a jikinsa yana aikin lallashinta,hannunsa daya kan sumarta yana shafawa a hankali,zuciyarsa fes,nutsuwa tana saukar masa "Ka daina tabamin kai,bayan tunda na dawo baka nema komai a gurina ba,har dai kaje bauchi ka gama bincikenka" ta fada cikin kukan shagwaba tana turo baki gaba. Don dole dariya ta kubce masa,ya rungumeta da kyau jikinsa "Am sorry madam,bansan a matse kike ba ai....."kuka ta fashe masa dashi,ta dunqule hannunta tana dan dukan qirjinsa "To na daina,na fasa fada,nine a matse" ya fada yana kare dukan da take kai masa da hannayensa shima. Sai da ya tsagaita dariyar sannan ya sake gyara mata kwanciya sosai a jikinsa,ya kira sunanta cikin sautin muryar data sanyata daga kai ta kalleshi "Banqi neman komai a wajenki da gangan kodon saboda wata mafita ba,a lokacin kina cikin zafi da radadin abinda na aikata miki,na tabbatar idan na nemi wani abu a wajenki a sannan,abinda zaizo kanki shine jikinki kawai nakeso,ban fara sonki saboda jikinki ba ke shaida ce akan hakan,kuma bazan fara saboda hakan ba in sha Allah,koda baki da komai tattare da ke banajin zan daina sonki har gaban abada" sosai kalamansa suka kashe mata jiki,tayi shuru tana saurarensa,tana kuma sake gasgata zancan nujood da tace mata,abinda uncle abbas yayi din tabbas ba halinsa bane,tafi gasgata asiri ne yake dawainiya dashi,a lokacin tace mata hafsat,saidai ita din har yau bata kawota cikin ranta ba. Sake kiran sunanta yayi bayan ya hade hannayensu guri guda cikin wani irin taushi da sanyi,sai data sake shigewa jikinsa da kyau saboda yadda sautin muryar yaratsa kowacce gaba ta jikinta "Don girman Allah ki yafemin,yafiya irin ta har abada,banason ki sake tuna wani abu makamancin wannan ya taba faruwa a rayuwar aurenmu" Abbas ya cancanci yafiyarta,koba komai uban danta ne wanda ta haifa da wanda zata haifa ma a gaba,ba zata taba mancewa kuma da yadda ya tsayawa rayuwarta ba,ya dauki wautarta da shirmenta,ya raineta har ta zama abun kallo ga kowa ba "Na yafe maka har abada" wani farinciki yaji yana ratsa zuciyarsa,har baisan adadin godiyar daya dinga jera mata ba. Cikin kwanakin komai ya wuce ya kuma zama tarihi a rayuwarsu,ba wanda ya sake tada zance makamancin wannan a tsakaninsu,ta koma masa widad din nan dake rikita duniyarsa,ta sake shigewa rayuwarsa da zafafan sirrikan mallakar zuciyar miji tsaftatacciyar hanya babu boka ba malam,sai addu'a data duqufa da ita haiqan a kowacce sujjadarta akan Allah yaci gaba da mallaka mata abbas din. Da yake zuciyarta akwai haske da tsarki,sai komai yake zuwa mata yadda takeso,abbas din ya samu a gareta har fiye da yadda ta zata,ta sake gasgata cewa addu'a ba qarya bace,hakanan duk macen data sadaukarwa kanta wa mijinta,tabbas zai zama bawa a gareta ba tare daya ankara da hakan ba. Samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da yayi daga widad yasa yake aiki tuquru cikin garin katsina,aikin da ya sake tamfatsa sunansa,ya kuma sake sanya sunansa a bakunan manyansa,suka kuma ji tabbas hazaqarsa da qoqarinsa sun girmi wannan matsayin da yake kai a yanzu. Budi sosai ya dinga shigo masa,hatta da kasuwancinsa kamar an qara masa albarka,cikin lokacin ya rasa wanne tukuici ya kamata ya bawa widad din,ba tare da saninta ko shawara da ita ba ya dallo mata sabuwar mota,ya kuma siya wani babban gida daban acan qasan layinsu dake garin bauchi ya ajjiyeshi reserve. Randa ya danqa mata motar tsananin murna ya sanyata kasa runtsawa,kyau da tsadar motar sai takejin kamae tafi qarfinta kamar ba tata bace "Madam,azo a kwanta hakanan murnar ya isa,ko kin manta bake kadai bace?,anya bazan fasa wannan kyautar ba?" Da sauri ta qaraso ta haye gadon tana dariya "Afwan yallabai,suma babies din naka taya ummarsu murna sukeyi" ya saki murmushi ya yaye rigar baccin jikinta yayi kissing cikinta sannan yaja mata duvets ya rufeta. [5/24, 12:41 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 38 Duk wajen wanda hafsat tasan zata ya yiwa abbas magana ya maidata taje amma abbas yayi biris,yaqi bawa kowa fuska yayi masa zancan hafsat din,suma din kuma suna kunya da nauyin yi masa maganar,saboda kowa yasan irin haquri da wahalar da yasha da ita,a yanzun sai yakejin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali da ya jima baiji irinta a rayuwarsa ba. Duk yadda takai ga bugawa bataga alamun samun nasarar komawarta gidan abbas ba,cikin qasqanci mugun bacin rai da baqinciki mai tsanani ta dauki shawarar da ummanta ta bata "Tunda yanzun itace ke fada masa yaji,babu wata hanya data rage illa mu wanke qafarmu muje kanon,mu samu kakanta shi kadai nakejin yayi saura da zai gaya masa yaji,karkiyi baqinciki,idan kika samu nasarar dawowarki gidan,wannan karon ko komai nawa da naki zai qare saimun salwantar da ita,ko ta fita daga gidan d qafafunta,koshi ya koreta,ko kuma tabar duniyar gaba daya". Washegari suka shirya suka nufi kano ita da ummanta,ummu ta ganesu,ta kuma tarbesu kadaran kadaham,basu gaya mata abinda ya kawosu ba amma sun nemi ganin alhaji tsoho,ta sanar masa tayi musu iso ta kuma basu guri. Yadda ta dinga kuka tana gaya masa qaramin ciki ne a jikinta tana roqon alhaji ya sanya baki ya karyar masa da zuciya,duk da yana sane da komai da yake faruwa,ba kuma wai bayajin ciwo ba,to amma hausawa sunce d'a na kowa ne,kuma har yanzu shi akwai wannan jinin na karamci cikin jikinsa,wannan ya sanya ya tabbatar mata da cewa zata koma dakinta in sha Allah ta riqe yaranta. Murna kamar ta taka rawa ita da umman nata,ta yamutsa fuska bayan sun fito ta goge sauran ruwan hawayen dake fuskarta "Yadda kika qasqantar dani kika sanya na nemi alfarma daga wajen iyayenki,na zubda ruwan hawaye na duk ta dalilinki wallahi bazan qyaleki ba" hafsat ta fada cikin cin alwashi da buri. Sanda alhaji yayi kiran abbas din yana office,yabar dukka aikin dake gabansa ya saurari alhajin. Yayi mamakin jin ta inda hafsat ta bullo,bazai iya musu da tsohon ba koda wuqa ya dora masa a maqoshi,saidai yasan maganin hafsat,idan tasan wata batasan wata ba,don haka bai musa din ba yace ya karbi komen ya maidata,amma alhajin yayi masa alfarmar sanar da ita cewa,daga rana irin ta yau,duk randa ta sake yunquri ko ta daga masa hankali to a bakin aurenta. Alhajin baiso yayi wanna furucin ba,to amma kuma mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,duk mutumin da ya iya irin wannan hukuncin akan uwargidansa duk da zuri'ar dake tsakaninsu......shi kadai yasan irin abinda yake fuskanta. Saida alhaji ya nemi magabatan hafsa sukayi magana ta waya,ya kuma shaida musu sharadin abbas sannan yace musu ya maidata. "Alhmdlh,Allah ya qara girma,ya saka maka da alkhairi yasa a gama lafiya" kawunta da ya cire hannunsa daga lamarin saboda baqincikin hafsat da uwarta ya fada,yanason 'ya'yan yan uwansa,amma hafsat ta fita zakka ko a cikin marasa mutuncin gidan,dukka qoqarin da yakewa rayuwarta yana yine kawai don girman zatin Allah da kuma hakkin zumunta. A washegari ta tattara kayanta ta koma gidan,gidan da har ta debe haso da tsammani daga zamanta a cikinsa. Ranar data koma ta tsammaci zai maido mata dasu mimi,saidai har washegari shuru,washegarin ma data saka rai shima dai shuru,haka ta wuni gidan ita daya kamar mayya,zuwa dare ta kasa haquri,ta daga waya ta kirashi. Dai dai sanda suke zaune a falonshi shida widad da tsohon cikinta da take gab da shiga watan haihuwarta,tana saman kujera yana zaune a qasa,ya dora qafafunta saman cinyarsa yana matsa mata saboda yadda suke yawan kumburar mata,iya girman cikin kawai ya isa ya gaya maka cewa lallai twince dinne da gaske,labari yake bata kan gagarumin promotion din da yake sanya rai za'a yi masa koda wanne lokaci,muqamin CP wato commissioner of police,saidai akwai masu so da yawa,amma yana fatan indai zai zame masa rayuwarsa data iyalinsa alkhairi Allah ya tabbatar masa. A yanzun widad din itace abokiyar shawararsa da baya iya boye mata kowanne sirri nasa,duk abinda ya taso masa zai zaunar da ita yayi shawara da ita,Allah ya hore mata wani irin kaifin qwaqwalwa da basirar da muddin ta bashi shawara yana ganin haskenta. "Waye yake kira?" Ya tambayeta saboda tafi kusa da wayar,ta kalli screen na wayar sannan ta amsa masa tana miqa masa wayar "Mummyn mimi ce" qaramin tsakin da baisan ya fito ba yaja "Ki daga kice mata hutawa nakeyi" kai ta girgiza "A'ah fa,ba ruwana,kayi mata dai bayani" "Bazanyi ba,ke nace ki daga,idan kuma ba zaki daga ba ki gayamin kanki tsaye" "Allah ya baka haquri" ta fada tana girgiza kai,sannan ta daga wayar takai kunnenta Cikin kwantar da murya da kuma laushi tayi sallama ta dora da "Daddyn Mimi yanzu ba yafiya tsakanina da kai kenan" "Sorry,yana hutawa ne yanzun haka,saidai ki sake kira anjima" wata ashar ce ta tasowa hafsat din amma ta haqura ta danneta, zuciyarta kamar zata fito ta bakinta,saboda tsabar wulaqanci ita zai bawa wata ta daga mata waya?,a duniya yanzu cikin wadanda ta tsana babu sama da widad,sai taja mugun tsaki ta dauke wayar daga kunnenta,saidai ashe widad din ta rigata gimtse kiran. Safa da marwa kawai ta dinga yi a falon,da qyar ta taushi zuciyarta da dare ta sake kiransa amma bata sameshi bama kwata kwata,haka ta kwana biyar cikin gidan,ga kayan amfaninta duka sunyi qasa,sai takejin gidan gaba daya ya sauya mata tunda ba haka ta saba rayuwa a cikinsa ba. Tasan yaran suna gidan yaaya bara'atu,koda ta kira tace don Allah tasa a kawo mata su sai tace "Babansu yace zai kirani ya gayan duk sanda za'a kaisu din" kan bala'in ubancan,ita da yaranta ma sai an shata mata layin sanda zata gansu?,me abbas ke nufi da ita ne?,anya zata iya jura kuwa?. "Dole ki jure muddin kinason zama cikin gidan" haka anty ummee tace da ita,haka taci gaba da hadiyar baqinciki,cikin lokaci kadan ta fara rama. Sai da tayi sati uku da dawowa sannan umar ya shigo mata da kayan abinci zallarsu,bata ga alamun nama kifi fruits ko drinks da ya saba hadawa dasu ba,babu kuma kudin da yake dora mata akai,wannan karon ta kasa daurewa ta kirashi "Iya abinda zan iya kenan,idan zaki zauna ki zauna,idan ba zaki zauna ba qofa a bude take" amsar da ya bata kenan ya kashe wayarsa. Tana kuka sosai ta kira anty ummee tana gaya mata,don ta kasa samun ummanta "Ke kin cika gajen haquri,tunda bada yunwa ya barki ba saikiyi haquri ai" ta fada a mugun gajiye,saboda itama yanzun ta kanta takeyi,nata ballin kissar ya fara tashi,miji da sauran danginsa sun fara ramfota. Cikin aljannar kare abbas din ya sakata,dukkan wani abu da bai zama dole a addini ba ya janye mata shi,kudi da yake bata na kashewa da qari da yake mata da sauran wasu kayan alatu da basu zama tabbas ba gaba daya ya janye,yanason ya gani shin da gaske ta rusuna?,saidai a yadda ta fara rawa da kiraye kiraye zuciyarsa ta gaya masa "Mai hali fa baya fasa halinsa". Sai da tayi wata guda da komawa sannan ya shirya zuwa bauchi,wannan karon da widad din za'a je,abinda ta manta rabonta dashi,ta jima sosai rabonta da bauchin,gaba daya ma garin ya fita a ranta tun wancan lokacin,yanzun ma tsaowar bikin nujood ne zai kaita garin,don dole taje tayi kara duk da nauyin da tayi,abun kuma yazo dai dai da saukar 'yar yaaya bara'atu. Ya zame mata dabi'a,a duk sanda zaiyi tafiya bata qasa a gwiwa ita ka shirya masa komai,koda weekend din kuwa zaije bauchi,duk dadai ya jima rabonsa da bauchin,tun bayan kammala bincikensa da sallamar hafsat da yayi. Koda ta gama da qyar ta iya miqewa da taimakonsa hannunta riqe da bayanta tana cije lebe "Anya madam,kodai triples ne computer bai gano dayan ba?" Ya fada cikin sigar tsokana yana boye dariyarsa,harara ta balla masa "Ta ina zasu fito?,yallabai ka barni ma naji da wadan nan guda biyun,bansan ina zaka kai son yara ba" "Yaya ai rahama ne,banqi kowacce shekara na dauki sabon baby cikin gidan nan ba" kukan shagwaba ta sake masa tana yarfa hannu,tayi tayi qafa ta taku takai gareshi ya rufeshi da duka kamar yadda ranta keso amma ta kasa,wannan ya sake hasalata ta sakar masa kuka sosai. Shi da affan suka dinga mata dariya,duk da yaran baisan me akewa dariyar ba amma ya taya babansa,sai daga bisani daya fuskanci da gaske take sannan ya aje affan din yana cewa "Baka kyauta ba affan,kawo hannun taho ki rabu dashi" data samu kanta tana isowa kuwa abbas din ranqwasa saman kansa,ya dafe wajen yana shafawa a hankali,sai tasa hannu ta tureshi gaba daya yayi baya ya fadi. Motarsa ya ajjiye ya dauki tata motar,a ciki suka tsara tafiya bauchin dama,tunda already yana da wata motar a gida,idan sunje sai ya bata abarta tayi ziyarce ziyarce itama. Tunda suka idar da sallar asuba basu koma ba,sun gama shiri tsaf sai suka dauki hanya,sammakon da sukayi ya basu damar isa da wuri,taso ta masa magana kan ya sauketa a gidan uncle muhsin amma sai tayi Shuru gudun ta zama mai yawan qorafi,tasan dai yana sane da sharadin raba musu muhalli. Sun shiga layin sai taga yana fakawa qofar wani gidan na daban,tabi gidan da kallo,yakai girman nasu gidan,a tsare yake kamar dai nasun,ya fita ya bude qofar sannan ya tura gate din,ya dawo cikin motar ya jata zuwa ciki. A parking lot ya tsaya ya kashe motar ya waiwaya yana kallon widad din,ya sakar mata murmushi sannan ya fita a motar,ya zagayo side din da take zaune ya bude mata sannan yace "Welcome to your new home" kallonsa tayi da alamun son qarin bayani,sai ya dage mata dukka girarsa "Eh ga naki gidan.....kin dauka mance?,ni na isa nayi saken mantawa da sharadin abba?,ban shirya rasaki bafa kwata kwata koda kuwa da wasa" yayi furucin yana miqa mata hannunsa,saita dora nata akai murmushi yana qwace mata,ya taimaka mata fita a motar,ya fidda affan ya aza a kafadarsa suka wuce cikin gidan.[5/25, 2:37 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 39 Duk da kayanta ne na wancan gidan nasu amma gidan yayi bala'in burgeta,komai ya tsaru,an kuma shirya mata shi dai dai da ra'ayinta da kuma yadda takeson gida ya kasance,ta dinga satar kallon abbas tana mamakin yadda ya karanci komai nata,me takeso,meye bataso,walwala da damuwarta,sai taji zuciyarta ta karaya,ta samu kanta da addu'ar kada Allah ya kawo abinda zai sake rabasu ko ya saka shakka ko rudani a tsakaninsu har qarewar numfashinsu. Widad din mutum ce mai matuqar qoqari,a tsaye take kan hidimar gidanta,duk da komai a gyare yake amma sai da tayi goge goge,ta kuma samar musu da abinci duk da akwai taimakon abbas din yana kama mata,sannan suka sake wanka gaba dayansu suka shirya don wucewa gidan saukar yaaya bara'atu. Yana riqe da hannunta suka shiga motar tata "Inajin aminatu zanje na roqa abarmiki,wannan aikin yana miki yawa" dadi sosai ya kamata,ta murmusa tana cewa "Amma da ka kyautamin qwarai,inason yarinyar,tana da hankali,amma kuma ranka ya dade,naga kaman baka da ra'ayin daukan mai aiki" kallonta yayi sannan yayi murmushi "Wayon tsiya gareki,nasan me kikeso kice,na farko amintu ai bame aiki bace,qaramin qarfi garesu,daukotan zai zama kamar taimako,kamar yadda tasa aka dauko lawan yaso ya zame mana wani abu daban,na biyu kuma ina da tabbacin ko ire iren aminatu dubu zan cika miki gidanki dasu,ba zaki bari kowacce tayi hidimar mijinki ba,ba kuma zaki sakar musu hidimar gidanki gaba daya sai yadda sukaso suyi ba,munsan aminatu muna da tabbaci akan tarbiyyarta,ba zata batamin yara ba,kuma na tabbatar baki da sakaci da zaki kasa sanya ido a kanta,ko yaya motsinta ya canza nasan in sha Allah zaki kula,zaki kuma tsawatar" shuru tayi tana dan gyada kai,komai yayi wato yana sane,yana kuma da hujja akai "To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ya fada cikin nuna kulawa. Sai da ya ajjiyeta a qofar gidan sannan ya miqa mata key dinta yana jifanta da wani kallo,saika dauka sabon saurayi da budurwa ne "Drivernki ya gama aikinsa ranki ya dade" dariya ta tsuntsire da ita "Godiya nake,zan ninka maka salary dinka" "Da kuwa kin kyautawa dan marayan Allah" ta girgiza kai tausayinsa yana dan tabata "Allah ya jiqansu ya kyauta makwancinsu ya kyauta namu zuwan" "Ameen ya Allah,Allah yayi albarka" ta amsa da ameen ya fita a motar yana gaya mata zai qarasa gidan suraj da yake basu da nisa,idan sun shiga wata sabgar yasan zata iya maida kanta gida,idan kuma ya dawo da wuri sai ya maidata "Koka maidani dawowa zakayi,kasan dai kwanan waye ai" harara ya balla mata,tayi kamar bata gani ba ta wuce ciki tana qunshe dariya tana riqe da hannun affan da ya fara koyon tafiya,wannan yasa ta dinga takawa a hankali cikin kula da takatsantsan. Tun daga qofar gidan jama'a ne,ta dinga gaisawa da mutane sunayi mata sannu saboda ganin yadda tayi nauyi sosai da uban ciki a gaba,yan mata matan suka daukar mata affan din suka kutsa cikin gidan dashi ita kuma ta tsaya tana ci gaba da gaisawa da mutane. Hafsat din na tsakar gida anata rabon tuwon sauka,gaba daya ba cikin sukuninta take ba ganin yadda su mimi suka shiga sabgarsu cikin mutane,ko ta kanta basayi,yaran sunyi fes dasu sunyi haske sunyi qiba "La la la,da gani babu tambaya wannan yaron sir abbas ne" wata qanwar mijin yaaya bara'atu ta fada bayan an shigo da affan ciki "Tubarkalla ma sha Allah,yaro ya debo ruwa biyu,miqomin shi na ganshi" ta miqa hannu tana karbar affan dake fidda qamshi cikin navy blue din jeans da shirt dinsa. Sosai maganar taja hankalin hafsat,gabanta ya fadi ta waiwaya tana kallon yaron dake da yawan fara'a,abinda ya qara masa farinjini kenan,saita dauke kanta wani abu yana tsaya mata a wuya,shi da babansa sukazo lo shi kadai?, indai kuwa shi da babansa ne lallai abun abbas qara ta'azzara yakeyi,har yazo bauchi amma bata da mutuncin da zai gaya mata yazo din?. Bata gama wanann taraddadin ba widad ta danno kai,kamar kunna fitila cikin duhu haka ta haska gurin,da kyakkyawar shigarta me aji,dama tunda can din ita gwanar iya dressing ce,tunda quruciya ballantana yanzu data mallaki hankalin kanta,wata lafiyayyar atamfa ce a jikinta wadda tafi kama da material. Suna hada ido gaban hafsat din yayi Wani mummunar faduwa,faduwar da sai data rufe idanunta don tanajin sautin bugun zuciyarta har kunnenta,kamar ciki fa take gani a jikin widad din,ciki fa,cikin ma tsoho?,saita miqe tana laluben hanya,wanda banda Allah ya kare tayi hanzarin dafa bango da tuni ta timu a gurin ta fadi. Ba wanda ma ya kula da ita suna yiwa widad din maraba,kowa na qoqarin mata godiyar alkhairin da ya samu wannan karon daga wajen abbas din,wanda da yawansu sun tabbatar widad din ce sila,hakan yake kuwa,a wannan karon tayi shirin karbar soyayyarsu ne gaba daya,ribar kasuwancinta ta raba biyu,rabi ta dinga qarawa kowa akan abinda abbas ya saba bayarwar,har sai da suka qare,ita da fahad sukayi,batasan bakinsa bai iya shuru ba sai daya gaya musu,saboda shidai abun mamaki ya bashi,don koda wasa bai taba ganin hafsat din tayi musu haka ba,saidai tayi qoqarin ragewa ma. Mayafi da takalminta ta dauka ta sulale sai gidansu,tsananin bacin rai yasa da tashin hankali yasa ta manta da batun daukansu mimi da jiran zuwan abbas tayi masa kwance kwance ya bata yaranta. Tana shiga gidan ta dora hannu aka ta sakama maman nasu kuka,tayo wajenta hankali tashe "Wani cikinne da ita umma na shiga uku,ta kusa haihuwa fa?" "Ina fatan bakiyi wannan haukar a gabansu ba ko?" Ta fada cikin taraddadi,ta jinjina kai kawai don ta kasa cewa komai "Shikenan tashi muje ciki" yunqurin miqewa tayi amma sai jini ya soma bin qafafunta,ta fidda idanu waje ta qwala qara tana fadin "Wayyo Allah!.....cikina umma" sai kuma tayi baya luuuu ta sume umman tata ta tareta cikin tashin hankali. Kai tsaye asibiti suka wuce da ita,bayan an basu gado anyi gwaje gwaje aka tabbatar da zubewar cikin jikinta,kamar zatayi dan qaramin hauka koma ace qaramin haukan ta dinga yi a asibitin,har sai da haushi ya kama 'yan uwanta. Ta ciwa cikin jikinta buri sosai,tasan abbas din da matuqar son yara,ta gama tsara yadda zai zame mata makamin da zata yaqi abbas ta kuma dawo dashi tsundum cikin rayuwarta. Ba abinda abbas din baiyi ba na hidimar asibitin,hatta da ruwan da yan dubiya zasu sha bai bari kowa ya siya masa ba,ko dama can shi din tsayayye ne,baya dorawa kowa lalurar iyalinsa. Ranar da aka sallameta ranar suke komawa bauchi,don haka duk wani plan dinta ya gama rushewa,umman nata tace kada ta damu,ta bari ta gama jinin biqin nan,sai su shirya ma komai da kyau. ********Shirin haihuwa sosai abbas yake yiwa widad din,siyayya yakema twince din da basuzo duniya ba kamar ba gobe,abun yazo masa akan gaba,saboda wani irin budi yake samu sosai,harkokin kasuwancinsa da yake gudanarwa a gefe kamar ana musu yayyafin alkhairi,haka ta fannin aikinsa,ya tsare gaskiya da amana,hakanan koda cikin yaransa ya kamaka da laifin karbar cin hanci ko rashawa to ka kade,dukkansu sun sani kuma suna kiyayewa dokokinsa. Already likita ya gaya mata,tana cika watanni takwas to zata iya haihuwa daga sannan,kasancewar cikin twince,kuma ba haihuwar fari bace,don haka kullum abbas din cikin shiri yake,tayita dariya saboda yadda yakeyi din,kamar lokacin za'a fara yi masa haihuwa. Ranar da zaije bauchi weekend kamar kada ya tafi,tace sam sai yaje,watansa guda kenan baije ba saboda cunkoson aiki anan katsinan,hakadai ya tattara ya tafin ya barta da aminatu da yasa akaje aka dauko mata ita kafin ya wuce,sai da ya dawo sannan hankalinsa ya kwanta. ********Tun kafin su gama cin abincin dare bayanta da mararta ke ciwo,amma take daurewa tana cijewa,suna gama cin abincin tasa aminatu ta dauki affan suka wuce dakinsu,sai itama tace kwanciya zatayi,don bayan sun gama cin abincin fita ta kama abbas din ta gaggawa,don haka suka rufe ko ina,yana da key din kowacce qofa tasan idan ya dawo zai bude. Tashinta uku xuwa wani irin fitsari da yake takura mata,a zuwa na hudunne ta durqushe a bakin toilet din tana riqe da mararta da bayanta saboda wani mugun murdawa da tayi "Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" ta dinga maimaitawa,sai ta koma ta zauna sosai a wajen. Tun a can yaji jikinsa bai bashi ba,don haka ya katse meeting din,yabar mataimakinsa yace su qarasa,kome ake ciki su gaya masa. Yana buda qofar nishinta ya fara ji,a rude ya qaraso inda take yana tambayarta,amma babu baki,sai kawai ya fara sauko da kayan haihuwar data hadasu jiya jiya ya fidda cikin mota,ya kamata ya kaita mota,ya qwanqwasa dakinsu aminatu ta bude,ya gaya mata su kulle ko ina su kwanta,ya bata dukka keys din na gidan yace zasu asibiti,hankalin aminatun a tashe tayi musu addu'a ya fice. Kafin su isa ya kira daya daga cikin juniors dinsa,suka sameta a asibitin,bayan an dubata aka wuce labor room da ita. Addu'ar data dinga yi ba kadan bace,a wannan karon duk yadda ta zata ba haka bane,ana kiraye kirayen sallar asuba lokacin da abbas ya wuce masallaci cikin hukuncin ubangiji ta haife kyawawan twins dinta dukka maza. Yana kuma idar da sallar kira na shigowa wayarsa,ya daga yana sauraren bayanin da ake masa,tafiyar gaggawa ce ta taso musu shida matimakinsa da wanda abbas din ke bi,shine matsayar tattaunawarsu ta jiya,qarfe shida na safe,don dole ba yadda zaiyi haka ya amsa,don a qa'idar aikinsu ba sabawa umarni,ya baro masallacin yazo ya tarar da alkhairin da Allah ya saukar masa a wannan sassanyar asubar,baki da dukka zuciyarsa sun gaza daina furta godiya ga Allah,yaran kawai ya samu gani suma a gaggauce,haka yabar asibitin cike da kewar yaran da kuma mamarsu. Tun a hanya ya buga waya ya gayawa dukkan wanda ya dace ace ya sani,daga danginsa zuwa nata,gab da zai shiga gida ya kashe wayar don ya samu ya shirya,bai kunna wayar ba sai da suka dauki hanya. Yana kunnawa hafsat ya fara kira don ya fita hakkinta,ko basa tare indai zaiyi tafiya ya saba yana sanar da kowaccensu,bayan ya gama gaya mata tafiyar ya dora mata da batun haihuwar. Uffan kasa cewa tayi,saboda wani qaton abu da ya toshe mata qofofin maganarta,twince?,to maza ko mata?,ko Mace da namiji?,kai koma meye yarinyar ta haifa itakam ta shiga uku. Shurun da yaji yayi yawa sai ya mata sallama kawai ya katse wayar,ya amsa kiran yaaya bara'atu daya shigo masa. [5/25, 2:37 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 40 Jikinta yana rawa ta lalubi layin muneera don jin me widad ta haifa "innalillahi,na shiga uku" shine abinda hafsat ta samu kanta da fada bayan muneera ta tabbatar mata twins ta haifa kuma dukka maza,ta dinga safa da marwa cikin falonta kamar wata zautacciya,kamar kuma wadda ciwon naquda ya sameta,kuka takeyi wurjanjan,tana tsinewa widad a zuciyarta,yarinyar ta gama cutarta,cuta tahar abada,ta gama da rayuwarta gaba daya,haihuwa?,haihuwa tayi?,haihuwar kuma ta yara maza ma?,sai yaushe zata iya ruguza dukkan wannan ginin da widad tayi?,yaushe haqarta zai cimma ruwa?,rayuwa na qara tafiya,tana saqa widad din tana warware mata tana dawo da komai baya,ta gaji da wannan jiran gawon shanun,sai ta kira habiba ta fashe mata da kuka me cin rai ta fara gaya mata. Ajiyar zuciya ta sauke "Abinda nakeso dake kiyi haquri kawai,ko kowa ya kasa yi miki komai boka bagwaare ina mai imanin zai miki komai(wa'iyazubillah),saura wata daya kacal aikinka ya kammala,wallahi kinji na rantse miki,ko hajiya dake kabari inda zata dawo duniya tace masa yayi kaza wallahi wallahi naki zai dauka,kudade kika kashe bana wasa ba kin manta?, fiye da rabin jarinki kika bayar,ta yaya zan bari asara ta hauki?" Bayanan habiba sun sanyaya mata rai qwarai sun bata kuma qwarin gwiwa "Kedai abinda nakeso dake,kici gaba da lallabawa,ki sake ayi komai dake,yadda kome zaizo zaizo da sauqi" "Anya zan iya kuwa habiba?, zuciyata bata da wannan qwarin gwiwar" "Ke matsalata dake kenan, kwata kwata baki iya cinye jarabarki ba,wannan karon kuwa dole kiyi haka ko don amfanin kanki" "Zan jarraba in sha Allah". Wunin ranar haka ya yishi babu wata walwala ko jin dadi,ranta a mugun quntace,a zuciyarta tanata fatan taji wani mummunan abu ya samu yaran kowa ya huta,duk bayan mintuna saita tsine musu su da uwarsu,amma cikin ikon Allah lafiya sumul widad ita da jariranta. Wannan karon ummu ce ta kashe kunya da kanta ta yiwo tattaki katsina,gidan widad din sai ya kasance kullum cikin jama'a yake abokan aikin abbas na nan katsinan,gashi kuma a gida take,garin ummanta,dangi tako ina barkowa suke barka ,haka daga kanon ma,wasu na zuwa barka,wasu kuma sai ranar suna sannan zasu iso,yara dai sunyo goshi sosai kamar affan,kowa yasan yadda twins suke da farinjini daman,widad din taga gata tako ina. Ko yaushe suna waya da abbas din da yakejin kamar yayi tsuntsuwa ya dawo,an katse masa hanzarinsa sosai,don bai gama kallon yaransa,iya kallo guda dayan da yayi musu qaunarsu sosai yakeji cikin rayuwarsa da ruhinsa. Komai ya sakar musu dai dai bakin samunsa,don yanzu babu abinda zaice da Allah sai godiya,hatta da hafsat da yara bai barta ba,sai daya gwangwajesu da dinkunan fitar suna na alfarma har kala uku,ta kalli kayan taja mugun tsaki ta nadesu a waje daya,wannan karon kam koda ba'a ce mata ba tabbas zataje suna,zataje kallon sunan widad na qarshe a gidan abbas din,zata je kuma ko don ta sake ganin yadda zata qara sawa bokanta ya qara tsanantawa da aikinsa. _batasan tuni qaddara tayi mata nata tanadin ba,tanadin da tabbas da tana da masaniya a kansa......da babu abinda zai kaita garin katsina_ _hukuncin Allah,da kaf dube duben bokayen nata basu iso suka gano shi ba,hukuncin Allah TALALA mai kamar sake,lallai qaddarar kowanne nawa A RUBUCE TAKE_ Ana ya gobe suna gidan widad din ya qara cika sosai da jama'a,ba laifi gidan yana da nashi girman,don haka kowa ya samu masauki da wajen zama,duk da dakuna biyu ne,nata dana baqi wanda aminatu ke ciki don na abbas a rufe yake,sai wasu dakunan guda biyu da toilet ta baya. A ranar widad ta gama komai,gyaran kai kawai ya rage mata,tayi wani mugun kyau na fitar hankali saboda yadda jegon ya fara karbarta tun a sannan,da safiyar ranar sukayi waya da abbas din yace ta bari sai azahar taje gyaran gashin,abun mamaki zuwa azahar din taji wayarsa,yace ta fito qofar gida ya miqata. Na'eema da marwa ta dauka, kowacce ta dauki baby daya suka fito,tayi kyau cikin maroon din abaya, fuskarta tamkar madubi. Tunda ta fito ya zuba mata ido yana kallonta ta madubi,ya lunshe ido sannan ya bude,yana tuna muryarta lokacin da take naquda,addu'o'i da salati kadai ke fita a bakinta cikin wani hali,ya sake gasgata lallai haihuwa ba wasa bace,duk dan a baibi uwarsa ba ba shakka ya tabe,hakanan duk namijin da bai girmama matarsa ba kodon darajar yaransu lallai ya cika abun zargi. Buda motar tayi ta shigo,suka hada ido ta saki murmushi "Amma fa ka shammaceni,shine baka gayamin zaka dawo yau ba?" "Bakiji dadi ba da kika ganni kenan?" Shagwabe masa tayi "Sosai ma uncle, Surprise fa kayimin" "Good me jego" a ladabce ta gaidashi,sannan suka gaisa dasu marwa da suka zama 'yammata suma,ya tayar da motar yana tambayarta "To yaya?,meye labari?, Ya akaji da jama'a yan suna?,hope komai dai lafiya ko?". Qasa qasa suke hirarsu cike da wani irin kulawa da juna,kosu marwa dake baya basajin me suke fada kamar masu rada,abinda yayi matuqat burgesu ya kuma tafi dasu,don basu taba ganin irin wannan soyayyar tsakanin miji da mata ba,sunfi ganinta ga saurayi da budurwa,amma yau anty widad da uncle abbas din sun karya musu record. A saloon din ya ajjiyeta sannan yace "Zanje na karbo dinkina gaba da nan,idan na tashi dawowa sai na daukeku mu wuce" "Tom,godiya nake sosai,Allah ya qara girma" ta fada tana dunqule hannu cikin salon jinjina da kuma rusunawa, murmushi ya balle masa,tana bala'in respect dinsa,ko meye zai hadasu bata kasa ganin wannan girman nasa. Yana ci gaba da tuqi yana murmushi,halaye da dabi'un widad din yaketa tariyowa,tun daga aurensu kawo yau,tana da sauqin kai da dadin mu'amala over,bata da fushi ko tsaurara abu indai ba bango taje ba. Ya isa ya samu tailor din ya masa halinsu,don a sannan yake qarashe hade dinkin,yana ganinsa ya rude "Sir.....ayimin afuwa yallabai,tuba nake" sai ya jawo stool ya bashi "Yanzun nan za'a kammala sir" bai zauna ba,yadai harde hannayensa a qirji yana dubansa "Kome zakayi ka dinga qoqarin cika alqawari,shine cikar kamalar mutum,sannan sana'arka,duk yadda ka riqeta haka take zamar maka" "In sha Allah sir" yaci gaba da qoqarin hada masa kayan "Ka zauna mana sir" ya sake masa tayin zama "Karka damu,qarasa aikinka" ya fada a nutse,don shi bayajin tsaiwa duba da yanayin aikinsa. Wayarsa ce dake aljihun trouser dinsa ta dauki ruri,ya saka hannu a hankali yana qoqarin cirota,yana duba me kiran kiran ya katse,saiya fara qoqarin kira sai gashi an sake kiransa. Hafsat ce,ya daga wayar a nutse ya kara a kunnensa "Kana ta wajen ina?,gamu a park kazo ka daukemu" ta fadi kanta tsaye cikin son nunawa wadanda take tare dasu lallai har yanzu itace da gwamnati,fiye da rabinsu jama'ar widad ne ta fahimci haka ta yadda suketa hirarta da fadan alkhairinta tun a mota,hakan ya sake hassala zuciyarta da wani mugun bacin rai. Cikin mamaki yace "Me ya biyo dake titi bayan na tura kudin ticket a siya muku keda yara,yanzun haka fahad inajin yana airport yana jiran saukarkuya dauko ku" baki ta tura gaba hadi da tura dankwalinta ma,haka kawai ga mota tana gani sai ta bari ayi asarar kudin a wani siya musu ticket,kudi ba dubu biyar ba ba goma ba "Kawai haka nafiso,na karba kudin ticket din nayi saving mayi wani abun dashi" yadda take masa magana a tsaitsaye yadan bashi mamaki,don tunda tayi kome ta danyi laushi "Okay,to yanzu haka ina cikin wani uzuri,ki kira fahad din ki kwatanta masa inda kuke sai ya daukoku" daga haka ya datse wayarsa shima. Sai yaushe zata bar son kudi?,yaushe zai saka doka ta daina karya masa kanta tsaye?. Sakato tayi da wayar a hannu,ranta yana mugun baci,batakai yabar duk abinda yakeyi ba kenan saboda ita yazo ya daukesu?,cikin wannan bacin ran ta kira fahad ta gaya masa inda suke din,wanda saboda dan nisan dake tsakanin airport din da station din sai daya dan dauki lokaci,sauran wadanda basuga amfanin abinda tayi din ba sukace tunda ba abun hawa na haya available na zasu tsaya wani jira ba sai kawai suka dauki taxi drop suka wuce suka barta ita da su baaba hassana 'yan kanzaginta,sai da suka jima da wucewa sannan fahad ya iso,tayita masa bala'i amma yayi biris da ita bai kulata ba tunda ya riga yasan hali. Sai da aka gama hada masa dinkin sannan ya dawo ya dauki su widad,tuntuni an gama suna zaman jiransa ne ma "Ba komai,tunda dai ya gama alhmdlh" abinda tace dashi kenan sanda yake bata labarin abinda ya tsaidashi,shi kansa baiji dadi ba,don shima yana da baqi daga wasu garuruwan da sukazo masa saboda yana sanya ran zaiyi walima a goben kamar yadda ya saba kowacce haihuwa,haihuwar affan ce kawai bai samu yayi ba. Tunda suka isa gidan tana farfajiyar gidan a zaune ta kasa shiga ciki,kowa saidai yazo ya wuceta,tun a sannan hidimar da akeyi da yadda taga gidan ya fara tara jama'a ya tsaya mata a rai,kowa yana ciki yana huce gajiya harda su mimi,amma baqin kishi ya hanata sakat. Sanda motar abbas din ta shigo harabar gidan idanunta akai,baqin glass ne,bata lura da waye da waye a wajen a ciki ba sai da suka bude,su marwa suka fara fitowa sabe da yaran dake cikin wani lallausan blue din abun daukan yaran suka nufi cikin gidan,ta qurawa motar ido tanason ganin wadda zata fito,sai bayan kusan minti uku sannan widad din ta fito tana murmushi,da alama wata maganar sukayi da abbas din data bata dariya. "Kan abu ta kazar uba" hafsat ta fada cikin ranta,zuciya tayi mugun dibarta,batasan sanda ta isa gaban motar ba side din da abbas din ke zaune cikin wani mugun fushi "Ai dama odan bakayi haka ba ba kaine abbas ba,idan bakayi haka kai din ba namiji bane,dan kunama.....tabarmar qashi RIGAR K'AYA" ta da cikin madaukakin sautin da yaja hankalin mutanen cikin gida da sauran na farfajiyar wajen,ganin yadda hankula ke dawowa kansu bai saka ta fasa magana ba "Ni dana taho daga wata uwa duniya ka zubeni a station ka kasa zuwa daukata,amma ka dauki 'yar gwal da danyen jego a gaban mota kana yawo da ita,kabi ka tattare a gindinta ita da danginta,kana musu wahala kana musu bauta......wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da.......". Tsawar daya daka mata ta yanke sauran maganar,yayi wata irin fitowa daga cikin motar,Allah ya kissimawa widad ba za'a kwasheta da kyau ba,cikin gaggawa ta shiga tsakani ta dora hannayenta kan qirjinsa tanason yaja baya,ta tabbatar gamuwarsu da hafsat din ba zata taba kyau ba,batason kuma zuciyar nan data taso masa ta sanya ya biye mata ga mutane a wajen. 'yan uwan abbas dake kusa ne suketa yima hafsat fada suna janyeta,ana tsaka da haka kiran dan auta a dakinsu baban abbas din ya shigo yana shaida masa sun bata kwatancen masaukinsu,sai ya kashe wayar yana huci ya juya ya koma cikin motar ya figeta ya fice daga gidan. Iska me zafi widad ta furzar,tabi hafsat da kallo wadda aka janyeta can bayan gidan "Barin hali sai mutuwa"ta fada tana mamakin halin halin tantagaryar hauka irin na hafsat din. Ranar gaba daya a birkice hafsat din ta yini,donma 'yan kanzaginta suna dannarta,da qyar takai ga shigowa falon,saidai gaba daya a hargitse take. A yanzun widad din tafi qarfin raini,kuma tafi qarfin ta keta idanunta ta gaya mata maganar banza,uwa uba kuma tana tsakiyar danginta da hafsat din bataga alamun daukan raini ko wargi daga wajensu ba,haka ta yini har dare a falon tana qunsar takaici,saidai idan abun ya qume mata da yawa ta fita ta matse hawaye ta dawo. Har tayi shirin kwanciya abbas din ya shigo,har yanzu fuskarsa babu walwala,ta kalleshi cikin langabar da kai a shagwabe tace "Angon qarni babu fara'a, gaskiya ba kanta,abunma ko kyau baiyi maka ba" dole ta sakashi dariya,sannan ta gyara zamanta "Kaci gaba da haquri uncle don Allah" "Wanne haqurin?,haqurina ai ya gama qarewa......akwai abinda kuke buqata?,zan tafi masauki wajen baqi na" kai ta girgiza,don babu ce kawai basu da ita,ya tsugunna yayi kissing yaransa duka,harsu mimi da tasa aka debo mata suka kwanta gaba daya su bakwai kenan harda ita,da yake gadon babba ne ba wanda ya matsi wani. Har ya fita tana juya abun a ranta, zuciyarta duka ba dadi,batason bacin ran nan nasa,fatanta ko yaushe mummyn mimi ta gyara halinta ko zai samu nutsuwa. Dakin da su gwaggwo mero suka sauka ya leqa don ya musu sallama,baima san hafsat din tana cikinsu ba sai daya shiga,ya gama yi musu sallama ya miqe ya fice,sai hafsat din tayi zumbur ta dauki jakarta ta biyo bayansa. A tsakiyar falon ta cimmasa,tana riqe da qugunta,zuciya kuma na ingizata tace "Muje masaukin tare,acan nima zan kwana" wani banzan kallo ya watsa mata,yaja mata tsaki yayi gaba,saita sha gabansa cikin kuka "Wallahi na gaji da wanna wulaqancin da kakemin,kamar nima ba matarka bace,yau saidai duk abinda zaka yimin ka yimin,na gaji da wannan rashin adalcin" sosai zuciya ya ciyoshi,ya finciki jakar hannunta yayi wurgi da ita sai gata a bakin qofa "Na fiki gajiya,na gaji dake gaba dayanki,kije na sakeki saki daya,badai shikenan ba?" Wutace ta kawo mata ta kuma dauke mata a take,saita aza hannu aka ta kurma wata uwar kururuwa data zama tamkar shele ga dukkan wani me rai da yake gidan,shelar tata kuwa ta iske kowa,take falon ya fara karbar jama'a dake cikin gidan banda na harabar gidan da kunnuwansu baije wajen ba,a lokacin abbas ya jima da ficewa daga gidan yana jin kamar an zare masa qaya. Faduwa tayi tahau tirje tirje a wajen, gwaggwo hassana ce ta riqeta tana kiran sunan Allah kafin sauran su tayata riqe hafsat,tanata abu kamar wadda ke shirin hawa bori ko kuma tayar da iskoki "Ku cikani,ai kuna gani,a gabanku ya sakeni,saki uku kenan yayimin,saki uku kenan fa". [5/25, 2:37 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 41 Saita sake fashewa da kuka,tana jin kamar ranta zai fita,kamar alqiyamarta aka tsayar mata ita kadai. "Ikon rabbi sai kallo,wannan wanne irin musiba ce?,saki haka bagtatan?,wannan abu nu hassana yafi qarfina" gwaggwo hassana ta fada tana kama hafsat daketa zamewa tana tumuwa a qasa "Kiyi haquri tunda aikin gama ya riga ya gama" amma inaaaaa.....sai hafsat din ta hau zage zage,ta dinga debo ashar tana qundumawa widad "Sai naga bayanki,yadda kika hanani zaman lafiya saida kika cisgeni daga gidana wallahi tallahi kema ba zaki sake jin dadin abbas ba.....na rantse kinci bashi bazan qyaleki ba" gwaggwo mero ce ranta yayi mugun baci,ta sanya widad ta koma dakinta abinta ta dubi hafsat "Sakin nan dai ba ita tayi miki shi ba,hasalima batasan me ya hadaku ba,kuma zaman gidan aure dama kowa ya iya allonsa ya wanke ne,halinka kuma shike sai daka,indai bazakiyi haquri kija bakinki ki karbi qaddaraki ba har zuwa wayewar gari,to don Allah bamason hayaniya da tashin hankali ki wuce kitafi,mu taron farinciki ne ya hadamu" gwaggwo mero ta fada wadda ta jima dama tana juya maganganun da sukayi da 'yar uwarta hajiya na qarshe kan yadda take gasa abbas. Banda tsoron fita da takeyi da daddaren ba shakka saita yayyabawa gwaggwo mero maganganu,don tana ganin a yanzun ta zama munafuka ne, goyon bayan widad takeyi. Ranar wani irin dare mai mugun tsaho da baqinciki hafsat ta gani,ta dinga kuka kamar idanunta zai fado,idan ta tuna wai a yau ta rabu da abbas uban yaranta rabuwa ta har abada?,sai taji kamar mafarki takeyi,lallai namiji qanin ajali ne,namiji tabarmar qashi,namiji bashi da tabbas yau ita ta gani zahiran!!! (To masu karatu kunji fa,nidai nace uhmmmm). Ita kanta widad batayi cikakken bacci ba,idan ta kalli su mimi sai tausayinsu ya kamata,ta dinga kiran wayarsa yaqi dagawa,sai daga qarshe ya daga a dake yace da ita "Meye kike ta kirana?,idan zaki samu guri ki kwanta saboda baqinki na gobe gwara ki kwanta" kit ya kashe wayar,yasan magana zata masa akan abinda bakin alqalaminsa ya riga ya bushe,a daren yau sakayau ya dinga jin kansa,zuciyarsa tayi wani irin fes kamar an fito masa da ita an wanke,hankalinsa kwance yayi baccinsa,irin baccin ma da shi ya jima baiyi ba. Washegari kowa da harkokinsa na bikin suna ya tashi,sai hafsat da jama'arta dake qule a daki,wanda kowa ke mamakin abinda ya hanata tafiya tun sassafe,yadda ta dinga yi a daren jiyan basu zaci hantsi zai daga basu tafi ba. Widad na kitchen tana hada ruwan zafi suna magana ita dasu marwa dasu muneera gwaggwo hassana ta shigo,suka hada ido da widad din ta jefa mata Wani munafukin kallo,widad din ta basar ta gaidata a matsayin matar kawun abbas din,ta amsa mata kadaran kadaham,sai tahau neman abinci,sai data gama diban komai sannan tace "Mudai wannan bikin sunan ba damu za'ayi ba,dole muje mu raka diyarmu da aka kora......yarinya kin samu duniya,ku dama sadakar yalla wuyarta ku shiga gida,saikun fidda kowa,da biye biyen malamai duk sai kunbi kun ishi kowa". Ran widad ya baci da kalaman gwaggwo hassana,itadai tasan ba wani abu daya taba hadasu ballantana tace,akan hafsat din?,ita meye nata a ciki?,ita tayi sakin?. "Gwaggwo ni bansan meye sadakar yalla ba kwata kwata,saboda tsatsona ni balarabiya ce,kuma duk wanda ya kalleni ya kalli ahalina ya sani,malamai kuwa isa ce,kuma na gode da kika shaidamin aikina yayi,zanje na qarawa malamina kudi yaci gaba da aiki kada ya daga qafa" Kuka gwaggwo hassana ta saki tana jan salati wai widad tayi mata rashin kunya,duka kitchen din sai akahau kallon kallo,kowa yaqi tanka mata,don duk sunsan itace bata da gaskiya,haka ta fita tana fatar majina tana kaiwa gwaggwo mero qararta,a cewarta yanzu ita daya takejin maganarta. Suna tsaka da maganar abbas ya shigo gidan cikin wata danyar gezna fara qal,sai maiqo takeyi,ta fidda zatinsa da kwarjininsa gami da kyansa da wani irin kamala. Gwaggo hassanar tana ganinsa sai tayi shuru,ta wuce dakinsu sumi sumi,ya tsugunna yana gaida gwaggwo mero tare da tambayarta me ya faru "Fitina ce kawai sukeson ja kafin hafsatu ta fita a gidan nan" "Bata tafi ba?,zaman me takeyi?" Ya fada fuskarsa a hade,sai ya miqe ya nufi dakin, gwaggwo mero ce ta dakatar dashi "Ka barsu muga iya gudun ruwansu,neman wanda zai tayasu dama sukeyi" . Dole ya haqura da shiga dakin,amma ya kasa ya tsare yaqi barin gidan,daga qarshe ya zauna daga bakin gate yana amsa waya. Abinda baiyi zato bane ya sameshi,wato qarin matsayin da yaketa addu'ar tabbatuwarsa idan da alkhairi,hadi da tafiya course na watanni shida america. Dai dai sanda hafsatu ke fitowa da jakarta fuska qozai qozai ita gwaggwo mero,don gwaggwo fanteka tace ita fa babu inda zata sai an gama suna taci abinda tazo ci,idan sun koma dai tazo gida ta sameta ta sake jajanta mata,bayan sun fita taja tsaki tana gunguni "Yarinyar da ba mutuncin kowa take gani ba, zamanta da yaron nan har yai alkhairin da ita qanwar cikinta ya samemu ta sanadinta,ita da ya shekara kusan takwas da ita har ta gama zamanta bamu sameshi ba,yo na meye zan damu kaina?,saina gamacin qwai kaji da nama,ina gani an tirke sa za'a kayar kawai sai na yiwa kaina na tafi rakiyar sakakkiya?,da yake nice maqunshin gishiri"(😂😂,niko nace gaskiyar ki hajiua fanteka,shi mutum mai yawan alkhairi dama maqiyinsa ma wataran masoyinsa yake komawa,Allah kada ka jarrabemu da hannun 'yan dambe). "Alhamdulillah, Alhamdulillah,Allah ya tayaka riqo,kai nayi farinciki,inama ace yar uwata tana raye taga wannan rana da taketa roqa maka ita" gwaggwo mero ta fada zuciyarta a karye,abinda kuma ya shiga kunnen hafsat kenan wanda ya sakata tsananin rudewa,ko ba'a fada ba tasan wani promotion dinne ya samu,dai dai sanda take fita a rayuwarsa?,wannan wacce irin hasara ce ta tafka. Ko gwaggwo mero dake ban baki tare da musu fatan sauka lafiya basu kalla ba,suna fita wajen gidan ta damqi hannun gwaggwo mero "Na shiga uku mero,ya samu promotion,kuma wallahi babban matsayi ne ya samu wannan karon" ta fada qwalla na zubo mata "Eh to dai hakanan zakiyi haquri,duk wani abun rashin haqurinki ne sila,yqnzu gashi kin bar mata gidan kin bar mata mijin,kin bar mata yaran" maganar gwaggwo hassana saita zama kamar kamar wani fami ta yiwa hafsat din,taji kamar itama tana layin maqiyanta ne,amma dole haka ta danne don tana buqatar dan rakiya,bazaiyiwu ta tafi ziqau ba abun sai yayi mata yawa. Abinka da ba 'yan halak ba,isarsu keda wuya laifin yaso ya koma kamar na gwaggwo hassana ne ma,ummanta tana salati tana komai amma tana fadin su gwaggwon basu kyauta mata ba,ta yaya suna wajen zasu bari ya qarasa tsinke ragowar igiyar da tayi saura?. Abun duniya ya taru ya ishi gwaggwo hassana,ta kama baki kawai tana kallon qarfin halin umman hafsatun,wato shi dai abun arziqi bai karbi kare ba wato,hakanan matsiyaci ko a tandun mai aka sakashi haka za'a fiddashi qamas,haka ta karkade zaninta ta tashi ta wuce gida cikin takaici,abun arziqin da tasoyi ya koma na tsiya,can kuma ga daula da gagarumin bikin sunan da za'a yi ta yiwa kanta rasa rasa,sai ta yiwa gwaggwo fanteka barka da batayi biyu babu ba. ******Kwananta biyu cikin matsanancin hali na kuka da damuwa,har daga qarshe umman nata ta gaji da ji ta zaunar da ita "Nifa wannan koke koken naki ya fara isata,wai shin abbas shine autan maza koko ya aka fara?,kinga fa babu ta inda Allah ya rageki in gaya miki,kin samu a jikinsa kin tara abinda kika tara,ki gama iddarki ki gyagije ki fara zawarci me lasisi,wallahi da gudu zaki samu manema,ai sai wani ya yar wani yake dauka,abu daya zaki.masa ki rama,kema da zarar kin gama iddarki ki rattaba aurenki kawai,shine qarshen baqincikin da zaki cusa masa,yara kuma ya baki abinki,ta nan ma kadai zamu sake samun wasu kudin shigar". Da wannan shawarar suka dinga shige da fice saida aka saka baki aka bata su mimi,kallonsu kawai yakeyi,yasan manufarsu,don haka dukkan abinda ya tashi bayarwa na amfanin yaran qeqe da qeqe yayi musu,na watanni uku cas ba qari babu dadi,haka umman da hafsat din sukayita zaginsa sunayi dashi a gaban yaran,mimi da nawwara saidai su bata rai,babu damar yin magana,don tun randa nawwara tayi magana da yake ta danfi mimi tsiwa uwar ta gwabje mata baki basu sake cewa komai ba,saidai suyita bata fuska,takaici da baqinciki ya ishi hafsa,don ko widad aka zaga a gabansu sai fuskarsu ta canza "Shegu an goga musu baqin hali" haka hafsat din ke fada. Watanni uku aka bawa abbas din kafin tafiyar da zaiyi america, office zasu gama masa dukkan shirye shiryen tafiyar,sun bashi damar tafiya da mata daya da yara uku zasu dauki nauyinsu,idan yana buqatar qarawa kuma wannan saidai yayi a aljihunsa. Hankali kwance cikin wata irin nutsuwa yake dukka shirinsa,yanason tafiya da widad amma baisan ya zata kasance ba,saidai yana mata shirin ba tare data sani ba incase koda zai buqaci hakan,don bayajin zai iya nesa da ita na wadan nan watannin. Gefe guda kuwa widad din ta gaya ma kanta aikine sosai ya sameta,idan a baya su biyu ne yanzun ita daya ce dashi,uwa uba kuma riqe namijin da a baya yake da mata biyu yanzu ke daya ce dole saikin zage damtse kin ninka shirinki,duk da hafsat din akwai ya babu ce,amma dai duk tsiya macace itama. Ta tsaya ta gyara kanta da kyau,ciki da waje ta fara canzawa tana komawa yarinyarta danya shakaf,ta sake shiga classes kala kala da groups groups 'yan gaske na manyan matan da suka fita gogewa a komai, groups na hajiyoyi masu mutunci da tarbiyya da ake mugun qaruwa,ta shiga ne ta sanadiyyar su anty fanna da a yanzu suka zame mata madubi kuma makaranta,gefe guda kuma ga su anty madeena da anty deena da sauran yayyenta da kowannensu yanzu zaman lafiya sukeyi sosai,dama can widad din akwai sauqin kai da bin na gaba da ita koda tazarar shekarunku babu yawa,to har kawo aure bai canzata ba,saima sake riqe yayyenta da kyau datayi. Ga mummynta itama da bata jin kunyar yi mata bayanin komai,widad din kawai gareta diya mace,sauran dukka maza ne,don haka ta sake zage damtse tana gyare yarta tsaf,kama daga tarbiyyar jiki data zamantakewarta da mijinta. Cikin lokaci kadan ta sake gigita abbas din,idan sun zauna bashi da zance sai yace "Kina haihuwa kina sake zama mace,kina kuma sake dada wayo,kina kuma mallakeni wuudd" dariya yake bata "Allah ka daina fadan mallakar nan,banason jinta,kada wataran kayi subutar baki a dauka da gaske mallakar nayi maka". Murmushi kawai yake binta dashi,ta shiga kowanne lungu da saqo na rayuwarsa ta tsaye masa cakkk,yasha rayawa a ransa zama da hafsat da rabon haihuwar su mimi ne qaddararsa,bansa haka,inda ace widad din ya fara samu babu abinda zai sanyashi sake wani aure anan dai gidan duniya,saidai hurul'een na aljanna. Wata biyu kacal ta gama gyaran kanta,idan ka ganta ita da yaranta ko ke mace saita baki sha'awa ta burgeki,yaran su dukka ukun affan da sajid da sajjad (twince dinta)dukansu masu kyau ma sha Allah,sun debo kyau wani daga na widad wani daga na abbas,sai kyansu ya zama wani kala daban me ban sha'awa,bul bul dasu dukansu,idan ka gansu su ukun ba zakace ita ta haifa yara ukun nan ba(daya daga cikin sirrin auren wuri kenan,zaki tara yaranki tunda quruciyarki,baki san dadin jikinki ba,sanda zaki gama haihuwa da sauran qarfinki,sai ayita mamakin wadannan duka yaranki ne,ayita sha'awarku,Allah ya bamu haihuwa me albarka,ya albarkaci wadanda muke dasu). Sai da suka cika cika watanni uku sannan sukayi shirin shiga garin bauchi,suka shirya tsaf da tsarabar da widad din tayi da kudinta,ita da yaran da aminatu da fahad wanda a yanzun yake tare dasu,sun fara gaba ne,abbas din yace washegari zai biyosu,akwai wani case da zai rufe ne a ranar. Zuwa tayi ta tarar an yiwa gidanta sabon gyara,wancan gidan nasu kuma da hafsat ta kwashe kayanta duka anata masa aiki,an canza masa fasali da tsari gaba daya,wani irin gini ake masa na tashin kai. Washegari da azahar ya iso, yaran duka suna wajen aminatu ita kuma tana wajen mai gayya mai aiki tana kula dashi,sai da yayi wanka yaci ya qoshi sannan yace mata su shirya suje suyi gaishe gaishe,ta shirya yaran duk da dama ko yaushe tsaf suke,suka fita gaba daya a sabuwar dalleliyar motarsa daya canza,ita kuma yabar mata waccar. Sun zaga dangi sosai,widad kuma tasha sanya albarka sosai ita da yaranta,bayan sun taho hanya abbas ya kalleta "Waini hajjaju,jarin naki duka kike kwashewa kike kyauta dasu?" Murmushi tayi masa tana narkar da wuyanta,ta masa wani kallo na qasan ido "To yallabai ko me zan basu ai ban fadi ba,danginka ne fa?,abun tutiya wa yarana,kuma ka manta ribar da na samu a wannan shekarar?,ko ka manta ina shirin bude shago?" "Tuba nake,na manta fa da hajjajun gaske nake magana ba da jabun ba" sai suka saka dariya a tare tana dora kanta a kafadarsa bayan ta kaiwa bayan hannunsa duka. "Mu samu wani eatery din muci abinci,banason mu koma gida kice zaki shiga kitchen din nan girki,nidai yau na sauke miki" "Godiya nake" ya fada tana hade hannayenta guri guda,ya sakar mata murmushi,yasan duk da yayi hakan tabbas saifa ta shiga kitchen ba fashi,ko Black tea saita dafa masa hankalinta zai kwanta,dun rintsi duk tsanani bata taba bari rana ta fito ta fadi baici komai daga hannunta ba. Gaba daya ta tattara hankalinta akan baqin mutumin da za'a iya kiransa matashi,don bai qarasa shekarun abbas ba,aqalla abbas din yana iya bashi shekara biyar,tun wancan sati biyun da ta kammala idda ya fara zuwa wajenta,amma tun lokacin taji sam baiyi mata ba,a tsukin maza kusan uku sunzo mata,amma duk wanda ta daga kai ta kalla sai taga baikai mata zatin abbas ba,tana da buri.....tanason bawa mara da kunya,tanason tayi auren huce takaici,tanason tayi auren da za'a san bataci baya ba,zatayi auren da abbas zai ciji yatsa,widad kuma tasan cewa tayi mata nisa,ta kuma yi mata tazara da ratar da bazata taba iya kamota ba.[5/26, 6:21 PM] +234 803 416 2581: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 42 Matashin ya sake gyara zamansa yana gyaran murya "Sunana AVM mu'awiya mani adam" da hanzari hafsat ta daga kai tana dubansa "AVM kuma?,air vice marshall kenan fa?,dama babban mutum ne shi din haka me muqami yaketa binta tana wulaqanta shi?,wato Allah yayi tana da rabo,da tayi wasa da damarta,saita gyara zama tana sakin masa fuska sosai harda murmushi "Ayyah,afwa yallabai,inata bata maka lokaci ko?,kasan komai sai Allah yayi" shima murmushin ya saki,da alama tarkon da ya dana yayi kamu "Ba komai,yau ai gashi zamu tattauna sosai" sakewa yayi yana bayyana mata waye shi da irin abinda yake dashi,cikin mintunan da basu gaza talatin ba taji ta gamsu ta kuma amince dashi,kuma lallai ta samu mijin auren da take fata wanda yafi abbas matsayi da dukiya,saidai ya nuna masa kyau,take ta bashi damar turo magabatansa,sukayi dan ciye ciye suka kuma sake tattaunawa,ganin shima din mawadaci ne sai bata boye masa komai ba ta gaya masa irin business din da takeyi,da kuma abinda ta mallaka yanzu haka,don ma tanata fama da ummanta dakeson ta hau kan kudin a dinga murqushewa,banda ta bade idanunta da toka zuwa yanzu Allah ne kadai yasan nawa za'a rugurguza,bayan kudaden abincinsu mimi da ake kawowa suke kashe mu raba,shi yasa taji ta matsu tayi aurenta ta samu inda zata sauke dawainiyarta ta daina facaka da kudinta. Sosai take kashewa kanta kudi,ita ala dole bataso aga ta canza bare ayi tunanin baqincikin barin gidan abbas ne yake damunta,idan tayi aure kuwa tunda ta samu mai farcen susa,zata tsula tsiyarta yadda taga dama,sai tasa widad taji ta muzanta. Ya jima wajen masu biyan kudi sannan ya qaraso wajen motarsa yana mita "Sai suce su basuson Dollar dole saida naira za'a biyasu,bayan ribarsu ne idan aka basu dollar din". Kanta ya sake fashewa ta saki murmushi "Rashin wayewa ne kawai yake damunsu" "Wallahi kuwa,duk da haka saida suka riqe canji na wajen 5k" kamar ta juya taje ta karbo,amma sai taga kamar ajinta zai zuba,haka ta kanne sukaci gaba da tafiya. Tana tsaye tana jiran ya bude mata ta ciki motarsu abbas ta faka daga gefansu,tunda motar ta tsaya hankalinta ya dauku a kanta,don ba qaramin burgeta motar tayi baba jimawa ya bude ya fito cikin wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin zamani. Mummunar faduwa gabanta yayi,abbas din ya canza yayi mugun fresh,ga qiba mai kyau daya hada,fatarsa ta qara haske,gaba daya qamshinsa ya cika wajen. Sanda madam widad kuma ta fito cikin wani fitinannen dinkin bubu sai yawun bakinta ya ida qafewa,abbas din ya sunkuya ya karbi sajjad daga hannunta,sajid yana wajen aminatu shida affan,sannan ya karba hand bag dinta ya riqe suka jera zuwa ciki. "Ina zuwa" tace da AVM mu'awiya tana komawa ciki da sauri saurinta kamar wadda tayi mantuwa,so take ta tabbatar da abinda idanunta ke gane mata,widad dince ta koma kamar wata basarakiya a fadar masarautun larabawa. Can ta gansu suna magana da receptionist din,tana dan jifan abbas din da harara,gurin zaben abinci ne,sun saba kuma irin haka,akwai saboda da fahimtar juna sosai tsakaninsu da ma'aikatan wajen,wani abu ya tsaye nata a wuya, tsabar hassada da baqinciki ya rufe mata ido,ta nufi gurin dason nuna musu itama cikin wadata take,kuma tare take da mijin zata aura "Hello" ta fada tana wani yatsina,tunda abbas ya waiwaya sau daya ya kalleta bai qara ba,a yadda yayi zaka tsammaci ranar farko ne daya taba ganin halitta me kama da ita,kuma basu da wata alaqa ko kusa ko alama,sai ya dauke kansa yanaci gaba da miqa musu atm dinsa kan su cira kudin "Takeaway zaku hada mana kawai,basai mun zauna ci a nan ba" abbas ya fada yana duban ma'aikacin,widad da ta yiwa hafsat din kallo biyu cike da mamakin yadda ta tsomale kamar dattijuwar kaza ta maida dubanta ga abbas tana mamaki,yace anan zasuci amma yanzu ya canza,batadai ce komai ba,dukkansu sukayi shuru sai.muryar hafsat daketa qoqarin mata kwaskwarima,ita ala dole ga ajebo. "Nice wadda muka zauna a wancan table din ni da AVM mu'awiya" "AVM mu'awiya kuma?" Ma'aikacin ya tambayeta cikin mamaki "Yes.....mijina da zan aura,akwai sauran 5k canjinsa dake wajenku.....idan ba damuwa zaku iya riqewa" junansu suka kalla cikin mamaki,saboda sudai sunsan indai wanda take magana akai ne da qyar ya cike musu balance dinsu ma,daya daga cikinsu ne ya girgiza kai "Aah,muba wanda muke riqewa canji,saidai idan bai fada miki dai dai ba,ko bakiji dai dai ba" fuska ta bata ganin suna niyyar yarfata "Me kake fada?,ya anyi muku alkhairi zaku saka ma mutane da sharri?" "hajiya wai me kike fada?,mufa ba wani canji a wajenmu,kije ki sake tambayarsa dai" "Okay,indai kuka sakani zuwa na dawo zaku gane kurenku,zaku gane da matar waye kuke musu" ta fada tana murza hannu,saita juya tayi hanyar fita tana taku dai dai,tanason murza power dinga a gabansu ko don yau ta hanasu barci. Jajantawa suke a tsakaninsu na abinda tayin,abbas dake tsaye yana jinsu yace "Inajin bata da hankali,ko damuwa ce tayi mata yawa" ya fada da salon shaqiyanci dariya tana cinsa yana dannewa,dubansa widad tayi da sauri ta galla masa harara "Hafsat dince bata da hankali?" "Oh.....wai dama kinsanta ne?" Yayi tambayar yana dubanta gami da dage dukka girarsa sama,sakato tayi tana kallon abbas din,sai kuma ta girgiza kai kawai,dai dai sanda suka juya suna barin wajen zuwa inda su aminatu ke zaman jiransu "Dama ai dole kace baka santa ba,kana kishi" wata dariya ce ta qwace masa sosai,ya dinga dariya yana duban widad din,bai tsagaita ba har suka shiga mota ya tayar da ita sannan yace "Bakisan tausayin wanda zai dauketa nakeyi ba?,niko a lahira horon da za'a yimin shine na sake zama da ita inuwa daya bare nan gidan duniya?,sam,haihata haihata,idan taso ta auri sarkin makka ma,ina mata murna,amma nikam abbas turaki har abada,ni kadai nasan me naji me na gani" shuru tayi tana girgiza kai cikin mamaki,wato mace na iya fidda kanta fit daga zuciyar namiji kenan,kamar yadda take iya kafa kanta kwatankwacin yadda ita tayi "Su mimi ne a raina,banajin zan iya ci gaba da bar musu yarana gaskiya,kullum haqurina sake qarewa yakeyi a kansu" "Yaushe zamuje ganinsu?" "Gobe......in sha Allah" "Yayi,Allah ya nuna mana" ta fada itama can qasan ranta da damuwa,Allah ya sani tana son yaran sosai,bataqi kuma a dawo dasu a mallaka mata su ba. Daren ranar kasa bacci gaba daya hafsat tayi,ta dinga zarya tana hango abbas da widad a idanunta,happy family,me zatayi wanda zai bata wannan jin dadin nasu?,bata samu hutu ba saida zuciyarta ta yanke mata abinda zata aikata musu,ta san yadda mata suka tsani riqo,musamman ma riqon dan kishiya,ba abinda zata cusgunawa widad din dashi saidai takai mata yaran,ta qara mata yawan aiki ta hanata hutu,wannan kuma tasan zaiyita hadata fada da abbas din,shikenan hankalinta ya kwanta. Da wannan shawarar ta kwanta, washegari kuwa tunda safe ta soma hada musu kayansu,har sun sanya uniform tace su cire,ummansu nata fada da mita "Dan hanyar samun alkhairin zaki toshe mana?" "Nifa aure zanyi umma,don haka yaci gaba da riqe yaransa,babu me masa wahala,yanacan yana holewa da matarsa mu ya barmu da raino" hakanan badon umman taso ba ta tasasu a gaba,ta sakasu a napep sai gidan abbas din kanta tsaye. Kusan kowacce safiya zaka samu gidan neat dashi,bama gidansu na katsina ba har na nan din,saboda basa kwanciya dama abar gidan da datti,har aminatu ta saba,ya zame mata jiki,duk inda takwas tayi ta gama komai,ta yi wanka ta yiwa affan din kansa wanka,saidai suyi wani abun daban kuma,kosu sake kwanciya bayan sunci abinci,ko suyi game na alphabet din arabic ko na english da dai sauran abubuwa masu amfani. Tsaye tayi a tsakiyar falon tana qare masa kallo,an tsara komai na falon daki daki bisa sha'awa da burgewa,hakanan ya samu cikakkiyar tsafta da kulawa,ba abinda yake fitarwa sai wani irin sassanyan qamshi da ya hade da sanyin ac din dake Parlor din. Muryarta ta ware cikin baqinciki ta kwarara sallama,aminatu dake daki ta jiyota,ta miqe ta fito tana riqe da hannu affan,hannunta daya kuma dauke da sajjad dake cikin wasu fafaren overall,ya cikata fam ma sha Allah,idan ka kalli yaran ba zakace twins bane ba. Tsaiwa tayi tana kallon hafsat din cike da mamakin ganinta a gidan,saita kalleta da harara harara "Ina mutan gidan?" "Antyn tana wajen daddynsu....." "Na sani,dalla malama kiramin shi mai gidan" ido aminatu ta fiddo,tunda take dasu bata taba buga musu qofa ba ai,ba zata iya ba,barema dokar widad dince,indai ba wani babban abu bane ya faru basa kiranta idan tana tare da daddyn "Ba'a kiranta idan tana wajen daddy,kiyi haquri ki zauna ki jirasu,bari na kawo miki ruwa" ta fada cikin nutsuwa irin ta yarinyar tana sakin hannun affan,wanda mimi tayi caraf ta kamoshi "Qani.....ka manta ni ko?,ya naga kana kumatu,muji ko bread ka boye" ta fada tana dariya gami da fara lallatsa masa kumatun,yaron bashi da saurin mantuwa,ya tunata sarai,sai kuwa yahau bagala mata dariya,dukkansu sai suka matso kuwa,abinda ya qarawa hafsat takaici ganin yadda suka yanyame yaron dukansu cike da qauna suna masa wasa,ta daka musu tsawa,duk sai suka koma suka lafe. Sosai aminatu ta cika plate da kayan kaiwa baka ta ajjiye gaban hafsat dake tsaye,tabi kayan da kallo,rai naso amma kuma zuciyar ta hana,baqinciki qyashi da kishi mara amfani ya rufe mata ido,taso ta basar amma ta kasa,saita faki ido ta dauki lemo ta jefa a jaka,ta dan rarraba ido taga hankalinsu bai kanta,ta sake zarar wani abun ta jefa,tana kan jefa na uku ne qofar bedroom din abbas ya bude suka fito shi da ita,sai tayi sauri ta saki abunda ta dauka,saidai tuni sun gani,amma sai sukayi kamar basu gani ba. Riqe suke da hannun juna,perfect match couples da kowa ya kallesu sai sun bashi sha'awa,sanye take da wata rigar wani material da aka yiwa wani kyakkyawan dinki da ya zauna mata sosai a jiki,kanta ba dankwali sai sassalkan baqin gashinta me yauqi wanda kullum bata gajiya da gyaransa da yi masa style kala kala harda nasu bead,yau matseshi tayi cikin band ta kuma yiwa jelar kitso guda daya ta barshi yana yawo a bayanta,jikinta ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turarukan jiki dana hayaqi data tsuma kanta dasu. Shima abbas din shirye yake tsaf cikin qananun kaya wadanda suka sake qara masa kyau da quruciya, hannuwansu cikin na juna,tana riqe da wayarsa da kuma takalmansa da baikai ga sakawa ba da alama wata magana suke me muhimmanci,don kowannensu fuskarsa dauke take da walwala,duk da kusan ko yaushe haka suke su din,zaiyi wuya kaga sabani a tsakaninsu. Kanta ta dauke kamar zatayi aman zuciyarta,saidai a fuska kuma bata nuna hakan ba,amma wannan yanayin ya bayyana har saman fuskar tata "Oyoyo mimin daddy,oyoyo nawwaraty.....a'ah ga baby yusra" widad din ta fada cikin farincikin ganin yaran,suka taho da saurinsu suka rungumesu duka har uban,sai ta sanyasu cikin jikinta sosai,tausayinsu yana ratsata,inama ace abban nasu zai bar mata su. Yana zaune yana gaisawa da yaran nasa daya bayan daya yana bincikar lafiyarsu ba tare daya dubi ko sashen da hafsatun take zaune ba,widad kuma na tsugunne gabansa tana sanya masa takalmi a qafafunsa,sun share hafsat din kamar ba ita a falon,tun bayan sannunku da zuwa da widad tace mata ta amsa da qyar sai itama ta watsar da ita,don a yanzun kuma bataga wani alaqa tsakaninsu ba bare ta dameta. "Yaranka na kawo maka,don nima aure zanyi" maganar data fada kenan cikin gadara,dai dai sanda widad ta gama saka masa takalman,sai ya miqe tsam ba tare da yabi takan maganarta ba yana fadin "Allah yayi miki albarka,zan fita amma idan na taho zan kiraki,karkiyi nesa da wayarki" ido ta lumshe tana gyada kai "In sha Allah daddy" har ya daga qafa saita tsaidashi "Kamar kai mummynsu mimi keson gani" "Ohhhh....." Ya fada yana dan sosa girarsa "Yara ta kawo,kuma tayi abinda ya dace,shikenan ta ajjiyesu ta tafi,idan kuma akwai sauran wani damuwan ki wakilceni kawai dear,nasan zaki iya komai.....i trust you" ya fada yana jinjina kai fuskarsa kwance da murmushi. [5/26, 6:21 PM] +234 803 416 2581: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 43 Sake baki kawai tayi tana kallonsa,ya gama kasheta gaba daya,babu kunya ko kara a lamarin nasa?,sai ya kashe mata idonsa guda daya ya juya ya fice abinsa a falon hankalinsa kwance. Yana gama fita ta waiwayo ga hafsat din "Ki zauna sai....." "Ba zama nazo yi ba,ga yara nan Allah ya karemin su ya kula dasu,idan kuma aka cucesu Allah ya isansu basu yafe ba" wani lafiyayyen murmushi widad din ta sakar mata hankalinta kwance,ta koma ta zauna saman kujerar ta dora qafarta daya kan daya tana kallon hafsat din "Ki kwantar da hankalinki,kowanne tsuntsu fa kukan gidansu yakeyi,mu namu kukan me dadi kyau da ma'ana ne,haka aka koya mana,yara kuwa sunzo gidan ubansu inda yafi dacewa dasu,inda zasu samu kulawar da suka rasa kaf iya tsahon rayuwarsu,na meye kuma zaki damu?,idan ka shuka alkhairi ai baka tsoron ranar girbi......oh......na manta,kina tsoron kada na maidasu 'yan wanke wanke ba?,ko masu yimin shara ko wanki,ko kina tsoron kada na dinga basu wankin kashin su affan ko su sajjad?" Saita girgiza kai "Allah ya tsareni,banason ranar girbi na ta zamemin ranar kuka da nadamar baragurbin shukar dana dasa da hannuna,don haka kije kiyi baccinki harda minshari,zasu samu kulawar da ke kanki kika gagara basu,idan iya abinda ya kawoki kenan sai nace ki gaida gida,na gode da kyautar dan mutum sukutum da kikayimin har rai uku ba tare da nayi naqudarsu ba" saita qwalawa aminatu kira tace ta wuce ciki dasu. A karon farko hafsat tabar gidan jiki a matuqar sanyaye,kalaman widad sun bugeta qwarai,anya batayi gwaari ba data dauka yaranta duka ya danqa mata su?,sai shaidaniyar zuciyarta ta jaddada mata tayi dai dai,dole yaran zasu dameta,kuma shine kawai abinda zatayi ta baqanta musu rai,batasan wannan abun da tayi shine abu na farko data yi wanda ya faranta ran widad ba,don kuwa cikin kwana uku kacal yaran suka fara hawa saiti,farincikinsu ya qaru,dadi kamar suyi me babu ma kamar mimi da taji a duniya an gama mata komai,ta dawo waje antynta. Wannan kawo sun shi ya bawa abbas damar fara musu shirye shiryen tafiya america din gaba dayansu,ya kashe kudinsa sosai amma baiji komai ba,farincikinsa shine kasancewa da iyalinsa,sai a yanzu yakejinsa cikakken namiji kuma cikakken mutum,widad ta hada masa kan iyalinsa gaba daya,idan ka shigo gidan kai kanka sai ya burgeka,komai a tsare bisa doka da tsari,yaran sun soma samun wata cikakkiyar nutsuwa da kuma tarbiyya. Ranar da suka bar nigeria ranar hafsat din ta daura auren da ta dinga fatan abbas din yana nan zata daurashi,to baisan ta daura din ba don tuni jirgi ya lula dasu,koda yaji dinma babu abinda zai dameshi,don a duniya bayajin akwai wanda ya fishi farincikin rabuwa da ita,ya yadda KADDARARSA ce zama da ita,a yanzun kuma yana kyautata zaton yaci jarrabawar da Allah ya saukar masa,shi yasa yayi masa tagomashin rabuwa dashi. Rayuwarsu a america tazo da sabon tagomashi qarin wayewa da kuma budewar ido,don a nan ne widad tayi amfani da result dinta tayi course akan kasuwanci na shekara daya,don sun samu qarin wasu watanni shidan,a nan ta hadu da mutane sosai kala kala data qaru dasu,ta fannin gogewar Rayuwa mu'amala da zamantakewa, nau'in girke girke harma da gyaran kai gyaran jiki da kuma kula da iyali da miji gaba daya,ta samu experience na rayuwa me tarin yawa,bayan sun cika shekara suka tattara suka dawo,dukka yaran sun canza,sunyi dima dima sunyi fresh dasu,sai suka zama wasu ababen kallo,widad business dinta ya kankama,don tayi business sosai tacan,ta kawo kaya a shekarar kamar ba gobe,ta rabawa yan uwanta duka harda dangin miji,kowa ya samu alkhairi yayi murna,don sun qaru da ita,wasu har qaramin jarinsu suka tayar,hannunta me albarka ne sosai da komai ta taba sai ya siyu da tarin alkhairin ubangiji,ne yiwuwa zuciya me kyau da take da ita ne ya zame mata silar hakan. Kai tsaye suka sauka a tsohon gidansu da suka bari ana yiwa sabon gini,wani irin tsari aka yiwa gidan me matuqar jan hankali kamar a turai,masu sannu da zuwa da zuwa ganin sabon gida aka yita tururuwar zuwa, widad nata jin kunya tana boyen qaramin cikin data dawo dashi,a lokacin duka duka shekarar su sajjad daya da wata shida,ita a ganinta sunyi qanqanta da ayi musu qani,duk da sanda ta haifesu affan ma baikai haka ba. kuka ta dinga yi tace ita bataso "Ya kikeso yanzu ayi dashi" "Nidai a zubar" "What!!!" Ya fada da mugun qarfi "Eh lallai na yarda baki da hankali,kuma har yau baki girma ba,bari kiji abun Allah ya kiyaye Allah ya tsare,ko cikin shege nayi miki ai baki isa ki zubarmin da ciki ba" cikin wannan rigimar tasu suka iso nigeria,yana shareta tana shareshi,kowa yana ganin yafi dan uwansa gaskiya. Yau tunda ta tashi batajin dadin jikinta sosai,don haka koda safe ma tana jinsu suna sabgoginsu daga can babban falon gidan amma bata leqo ba,tasan aminatu zataji da komai,ga adda mimi kamar yadda tasa suke ce mata,yarinyar akwai qoqari,duk wani aikin zaka sameta tana taya aminatu,widad din bata taba hanata ba,saboda tana tuna wahalar data ci sanadiyyar rashin iya komai a aikin gida,duk da gatane na goyon kaka,tafison idan ta tashi aurar da mimi din kamar yadda take fata wanda duk zai auresu ya qare rayuwarsa yana shi mata albarka. Tana kwance abbas din ya gama shirinsa,yazo kanta ya tsaya,saita dauke kanta gefe,yakai hannunsa ya taba wuyanta,sai ya sauke ajiyar zuciya jin bawai zazzabin da yake takurata ne a jikinta ba,yana mamakin yadda ta iya shareshi da gasken tsahon kwanakin,sai yasa hannu yadan shafi fuskarta kadan yana fadin "Sai na dawo" "A dawo lafiya" ta fada ciki ciki,sai kuma tabi bayansa da kallo,bayan ya fitanbta lumshe ido tana fidda numfashi mai sanyi. Abbas miji ne na musamman,idan tace na musamman tana nufin hakan,duk yadda sukakai ga fada ko sabani da juna saidai iya kan harshe kawai,amma duk wata kulawa basa fasa baiwa junansu. Agogo ta kalla,qarfe daya saura,ta yunqura zata miqe ihun sajjad ya kawo mata har nan inda take,tasa hannuwanta ta toshe kunnuwanta "Allah ya yiwa aminatu albarka" ta fada idanunta a runtse,batason hayaniya kwata kwata,banda akwai aminatu da mimi da batasan yadda zatayi ba,dole yanzun ta fita,tasan filin dambe aka bude tsakanin affan sajjad da sajid,wataqila yusra na gefa tana tilliqa dariya,nawwara na qoqarin shigarwa affan mutuminta,saita sauko kawai ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da bakinta ta fito ta zura wata sassalkar abaya a jikinta,already da wankanta dama,don bata iya kaiwa haka batayi wanka ba sam,ta zura wasu lausasan slipper kalar abayar ta fito tana daura siririn dankwalin rigar a kanta wanda bai rufe komai a gashin kanta ba. Falon kuwa ya kacame gaba daya,duk sun ruda aminatu kamar tayi kuka,dama gata gwanar sanyi,saida widad tayi musu tsawa sannan suka dakata da abinda sukeyi,sai kowa ya fara shiga taitayinsa,suka matso kowa yana gaidata "Maami ya jiki?" Suka dinga cewa,mamaki ya kamata,oh wato abbas yace musu bata da lafiya kenan?,zai hada mata case,yanzun idan suka dinga mata sannu har sai ta gaji,har sai an fuskanci abinda ke maqale a jikinta "Jiki alhmdlh,na warke ai" "Allah ya baki lafiya maami" mimi ta fada cikin damuwa da kulawa "Ameen mimi na" tattarasu duka tasa aminatu tayi waje daya,ta kunna musu cartoon din da sukafi so,sai aka samu salama kowa ya nutsu,sai sajjad da sajid da lokaci bayan lokaci ake fama dasu ana bari bari. Dining ta wuce ta duba abinda aminatu ta dafa musu,saita zauna daga can saman ta hafa baqin tea tana dan kurba kadan kadan tana kallon yaran,rai shida dukka yaran abbas,ga na bakwai a jikinta,kome zata haifa kuma Alla masani,cikin ranta ta samu kanta da addu'ar Allah ya raya mata su taga girmansu,ya bata ikon ci gaba da tarbiyyantar dasu. Qarar wayarta dake gefe ya katseta,ta duba wayar saita saki murmushi,ummunta ce,ta gyara zama ta daga wayar cikin shagwabar da har yau bata iya daina yiwa mutum biyu a duniya ita,suma kuma har yau bata girma a wajensu,abbas da ummunta. Ta sakankance sosai suna hirarsu kusan rabin awa,sai taga aminatu ta buda qofar falon ta fita,sai gata ta dawo,ta hauro inda widad ke zaune "Maami baquwa kikayi,to mai gadi ya hanata shigowa waisai an gaya miki" mamaki ya cikata,bai tana hana kowa shigowa ba muddin ya yarda dashi sai yau?,da yake qarin matsayin da ya samu yana da me gadi cikin qananun 'yan sanda,hakanan an bashi driver da security "Koma wace a barta ta shigo" ta fada tana maida wayarta kunne,idanunta akan qofar falon har zuwa sanda labulen ya dage fuskarta data jirkice ta bayyana,saita zame wayar daga kunnenta tana cewa ummu "Zan kiraki ummu anjima" "To babu damuwa" ummun ta fada tana a gaida mata kishiyoyinta da masu gidan.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 44 Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn Whatsapp 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549 Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 _______________________________ Har yanzu kallon fuskarta takeyi,tanason tantancewa itace ko ba ita bace. Yadda itama take kallonta haka baquwar,kafin ta janye idanun nata ta maida kan yaranta dake zaune gaban tv sun bata hankalinsu,wasu hawaye masu ciwo suka tsatstsafo mata,dai dai sanda widad ta miqe tana cewa "Sannu da zuwa" gami da gangarowa daha step na dining din "Yauwa sannu" ta amsa mata murya a dakushe,widad ta qaraso wajen can gefe daga inda yaran suke tana fadin "Bismillah zauna" "Har ina iya zama?" "Ba damuwa ki zauna......mimi ga mummynku,nawwara yusra?,maza ku taso,aminatu a kawowa baquwa abun tabawa" duk sai hankulansu yayo kanta,duk suka tsaya suna kallonta da kyau,kamar basu ganeta ba. Itama ido ta tsura musu,hawayen da take riqewa ya silmiyo mata,sai suka miqe dukansu sukayo wajen uwar jiki a matuqar sanyaye,dadi ya kamata,ta bude dukka hannuwanta suna isowa ta rungumesu tana sakin kuka mara sauti. Sun jima a haka,tausayinsu yana ratsa widad,Allah alhakim,Allah mai iko,Allah me gaggawar hukunci mai sakayya da hisabi tun a nan gidan duniya,wai yanxu hafsat ce haka?,kamar wata almajira?,cikin shekara guda kacal,cikin wata mummunar kama da siffa. "Naji dadin ganinku haka mimi,duk da dama raina yana rayamin ba za'a samu wata matsala ba,kuna cikin aminci da kulawa,don na tabbatar ban barku a mummunan hannu ba" hafsat ta fada tana sharce hawaye "Na gode,Allah ya saka da alkhairi,Allah ya biyaki da yadda kika riqemin yarana" ta sake fada tana kallon widad kamar me kunyar su hada ido. Duk mamaki sai ya kama widad din,hafsat dince ke mata godiya har tana yabonta,lallai kaji tsoron duniya kaji tsoron ubangijinka "Ba komai,d'a ai na kowa ne,da dukiya da d'a babu wanda yasan me morarsu sai Allah" "Haka yake" ta fada tana jinjina kai,gami da tuna tata dukiyar data dinga salwanta daya bayan daya,har ta zamana a yanzun bata da komai bata mallaki komai ba. Ta jima da yaran a falo widad ta basu waje suna hira,sunata gaya mata abubuwan da suka faru da kuma zamansu a america,a ranar taji farinciki da nishadin data jima bataji irinsa ba,damuwarta ta ragu qwarai da gaske,ta sake gasgatawa lallai yaran sune sanyin idaniyarta. Data tashi tafiya cikin d'ari d'ari tace da widad "Don Allah zan roqi alfarma guda biyu a wajenki idan zan samu" "Babu wata damuwa,ki fada ko menene" "Don Allah ina roqarki ki yafemin duk abubuwan da nayi miki,sannan ki roqarmin babansu shima ya yafemin,duk da nasan saimai qarfin imani ne zai iya yafewar" "Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe,duk abinda ya faru ya riga da ya faru,shima zan gaya masa,zai kuma yafe din in sha Allah" "To na gode qwarai qwarai....alfarma ta biyu don Allah ki sake roqarmin shi,ya dinga barin yaran nan suna zuwarmin,koda ba kwana ba,ko basu yini bama don Allah" tausayinta ya sake kama widad,kaida yaranka amma saika roqi a baka su ka gansu "Xan gaya masa,kada ki damu kinji" godiya sosai ta sake yiwa widad din,sannan ta miqe tana musu sallama "Gashi ban kawo muku komai ba,kuyi haquri babu dama ne" cikin son kwantar mata da hankali tayi murmushi "Karki damu fa,suna da komai mummyn mimi" kai ta jinjina "Shikenan,na gode Allah ya saka da alkhairi" tsaidata widad tayi ta wuce bedroom dinta,cikin matuqar sanyin jiki da kuma tsoron halin duniya ta dauko hand bag dinta data dawo da ita ta buda,ta laluba kudin ciki,duka duka dubu goma ce tayi mata saura kudin nigeria,saita shiryasu ta fita dasu ta miqawa hafsat. Jikinta na rawa cikin mamakin yawan kyautar da tayi mata tasa hannu biyu ta karba qwalla tana cika idanunta,shekara guda kenan rabonta da riqe kudade irin wadan nan,godiya sosai ta dinga yi mata,sannan ta juya ta fice hawaye wani yana korar wani. Haqiqa duk wanda baiji tsoron Allah ba yana tare da wahala,duk wansa baibi duniya a sannu ba matsala bata qare masa ba,a yau yaran da take banzatarwa gasu tana ganinsu tana qaunar su rabeta,tana qaunar zama dasu amma sunfi qarfinta,don tasan ko sama da qasa zasu hade a yadda taga sun samu kwanciyar hankali da kulawa abbas bazai taba bata ko daya daga ciki ba. Gidanta da take ganinsa kamar mallakinta,ta kasa kula dashi,ta banzatar dashi gashi a yau yafi qarfinta,ta fita ta barwa wadda tazo gidan daga baya. Mijin da take banzatarwa,ta kasa tsayawa ta gyara kurenta,ta kasa tsayawa ta karanci abinda yakeso da wanda bayaso,ta kasa bashi abinda yake muradi cikin rayuwarsa.....gashi qaramar yarinyar da a haife ta haifeta,tazo ta sha gabanta,ta shiga rayuwarsa ta maye masa gurbin komai. Idanunta sun rufe,amma a yau suna bude kansu da kansu,tsantsar kishin banza da jahilci mara ma'ana yasa tabar gidanta, mijinta da yaranta dukka yanzu sun zama mallakin wata,saboda anyi mata kishiya ta kasa haqurin zama a gidanta,ta fita daga raminta ta fada ramin wata,tabar ramin data gina ta fada ramin wata,watar dake gallaza mata ita da mijin da baisan darajarta ba (babban qalubalen dake damun mata, mijinki da yasan darajarki,gidanki da kikasan ciwonsa,yaranki da basu da kamarki,dukka sanadin miji zai qara aure saiki watsar dasu kice saiya sakeki,bayan bai wulaqantaki ba,yayi hakanne saboda wani qarin auren a qaddararsa yake bai isa ya tsallaketa ba,babban abun mamakin kuma shine,sai ka ganta can ta buge da auren wani me matar,wai shin da ramin daka gina da kanka?,da wanda wani ya gina ka shiga zai zamto daya a wajenka gurin samun 'yanci da komai ma?,mata mu nutsu mu yiwa kanmu karatun ta nutsa,kishi yana da ciwo,yana da matuqar zafi,babu komai ke gane hakan sai masu zaune da kishiyoyin,to amma kuma ita addu'a maganin komai ce,sannan duk wanda ya miqa lamarinsa ga Allah,Allah ya isar masa,Allah yasa mu dace,yasa mufi qarfin zukatanmu amen). Widad ta dade tana juya abun cikin ranta,ta dade tana tuna fuskar hafsat,Allah abun tsoro duniya abun tsoro,sai jikinta ya sake sanyi,hakanan ta sake lafkewa akan kujera,tana tuna ko akwai inda ta sabi ubangijinta?,iya tunaninta bata tuna ba,amma saita samu kanta da istigfari,zuicyarta kuma ta sake tsarkaka,tare da sake daura aniyar kula da yaran tsakaninta da mahaliccinta,duk da dama ko sau daya zuciyarta bata taba bata wai ta zaluncesu ba. *H A F S A T* Sai data tsaya a soron gidan ta gyara zaman kudin sosai a jikinta cikin zaninta sannan ta sanya kai cikin gidan qirjinta yana dukan uku uku. Da ita kuwa ta fara hada ido,tana tsaye a gaban falonta,gaban hafsat yayi wata mummunar faduwa,tayi saurin janye idanunta,sannan da hanzari ta doshi dakinta kamar zataci da baka,tasa hannu ta tura qofar ta bude kai tsaye don dama bata kulle qofar ba,saboda bata ma da ikon don zata fita ta rufe qofar dakin nata. Falo ne falle da daki a ciki,kujerunta ne tun na aure,wanda su kadai ne suka tsira mu'awiya bai dauka ya siyar ba,maimakon ta samu guri ta zauna saita maqale jikin window din tana leqen tsakar gidan,tana kallon sahura dake mazaunin kishiyarta tana hararar qofar dakin nata,sai kuma ta daga zaninta ta ciro wayarta tecno keypad. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" hafsat ta fada jikinta yana rawa,tasan yau ta kade daga ita har ganyenta,dama tasan tunda ta fita batayi mata sallama tare da gaya mata inda zata ba yau ba ita ba kwana lafiya cikin gidan,tana jinta tana cewa "Ma'a,kazo gata ta dawo.....oho muku,can ta matse muku" sai taja mugun tsaki ta kashe wayar tana mita. Tunda uwar hafsat ta haifeta bata taba ganin bala'e'iyar mace irin sahura ba,bata gajiya da fada da bala'i,mita kuwa saita kwana tana zarya a tsakar gida tana yinta,dare baya mata kaifi haka rana bata damunta, bala'i idan ta kwan biyu bata yishi ba jinta take kamar mara lafiya,jikin hafsat ya dauki rawa,ta fada dakinta tana laluben kayan da zata sakawa jikinta da suka dan fi wannan kauri,tunda taji tana kiransa a waya lallai yau babu makawa jibga zatasha,babu kuma me qwatarta sai sarki Allaha. Ai hijabi kawai ta gama sawa taji anyi ball da kwanonta dake falon sannan ya fara magana da qarfi "Kina ina munafuka,fito nan nace miki" yayi maganar yana nade danqon dake hannunsa,jikinta na mazari ta fito ta qaraso gabansa ta durqusa,baiyi wata wata ba ya fara lafta mata "Ka tsaya don Allah nayi maka bayani,wallahi ba wani guri naje ba" "Qarya take munafuka,dama ta saba bin maza,kana fita take sanya qafafunta ta fice,saita dai daici kana dab da dawowa sannan takes shigowa gidan nan" . Baiko tsaya jin bayanin bakinta ba ya dinga laftarta,garin qoqarin zillewa kudaden da take maqale dasu suka zubo,sahura ta saki salati,ita da mu'awiya duka suka duqa lokaci daya suna qoqarin dauke kudin,sahura da ta fishi son abun duniya ta rigashi dauka,tahau lissafawa. Dubu tara da dari takwas cif,don tayi kudin mota a ciki "Ka gani ko,tabbacin bin maza ta koma,kaima Allah ya qara maka,ta yaya zaka dauko matar me kudi kace zaka iya riqeta,aiga irinta nan" "Miqon kudaden nan" ya fada yana miqawa sahura hannu,wani kallon banza ta jefeshi dashi "Uban kuturu ma yayi kadan bare na makaho,ka manta kudina daka dinga karba sanda zaka aurota?,ai da haka zan gama fanshe asarata,don ni wallahi mun raba hanya da asara,bana daukarta" daga haka ta soke kudin a brassiere ta fice abinta. Bulalar yayar cikin baqincikin rashin samun nasarar daukar kudin,ya zauna saman kujera yana huci "Tashi ki zazzage jikinki ko akwai sauran wasu kudin" haka ta miqe ta zazzage masa kanta,saidai ko sisi bai fado ba,yaja mugun tsaki "Ki rufewa mutane baki ki daina musu kukan banzan nan" "Wallahi bana bin maza,Allah maawiya sharri takemin" "Dalla rufemin baki,bazan taba yarda ni dake ba...." "Na'am" ya katse maganar yana amsa kiran sahura da taketa qwala masa kan ya fito yaja mata ruwa a rijiya,sai ya fice da sauri kamar wanda zai amsa kiran uwarsa. A wajen ta zube tana kukan baqinciki,dama haka qazafin zina yake da ciwo ?,haka widad taji lokacin data qulla mata sharri?,sau daya tayi mata ita,amma sai gashi ita kuma Allah ya hadata da kishiyar da kullum ta Allah daga fitowar rana zuwa faduwarta saita jefeta da wannan qazafin,saita rushe da kuka tana tuba zuwa ga Allah,tana tuna irin tashin hankalin data saka widad a ciki,bama ita kadai ba,hatta da abbas din,banda kiyayewar ubangiji da zuwa yanzu yana dauke ciwon zuciya ko kuma mummunan hawan jini,tati amfani da irin son da taga yana mata,ta saka an dasa zargi me qarfi a kanta cikin zuciyarsa,sannan ta jefeta da qazafin,ashe duk jifan da kayi wataran kanka zai dawo,bayan saki data rabauta dashi a wancan karon,yanzun kuma gashi tarihi ya maimaita kansa. Duk inda takai ga kaidi da jaraba da bin malamai sahura ta dameta ta shanye,a yanzunma ina taga kudin da zatabi malaman?,abinci ma wataran cikin gidan gagararta yakeyi sai tayi biyayya sannan sahuran zata san mata,tunda kusan fiye da rabin qarfin kula da gidan itace.*H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 45 Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn Whatsapp 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549 Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 _______________________________ Wanne irin hakki ne haka yake binta?,ta shiga uku,mu'awiya mutumin da yazo mata a matsayin air vice marshall,ashe kurtu ne,kurtun sojoji wanda akewa alfarmar daukarsu a aiki,suke dan aike aike wa manyansu,amma tsabar hakki da kuma ranar girbar abinda aka shuka da take dab da fadawa ta kasa ganewa,tun daga yadda yazo mata,ba wasu cikakkun suturu na alfarma da zasu gaya mata wayeshi,babu wasu securities da akasan dukka masu matsayi irin masa na yawo dasu ko da yaushe ko kuma motoci yaci ta gane amma idonta ya rufe, kwanyarta ta toshe, duka batayi wannan tunanin ba,matsayinsa ke mata kuwwa cikin kunne,ta tuna ranar da ya raina mata hankali yasa ta koma eatery karbar canjinsa,data koma masa da batun sunce ba'a binsu kudi sai yace "Ayyah,inatason tsaidaki,ai kina shiga ina ganin alert,sunmin transfer yanzu yanzu" da haka ya shashantar da maganar,ashe duka ya shirya aurarta ne ya cinye duk abinda ta tara da abinda ta mallaka,don yanzun haka bata da komai,ko wayar hannu tafi qarfinta,sai azabar da take qunsa daga hannunsa da kuma wajen kishiya. Watanni shida baya ummarta ta rasu,aka rabon gadon da mahaifinsu ya bari wanda a baya ba'a raba ba saboda ummar ta hana a taba,kowa kuma yana tsoro haka yayi Shuru,nata kason bata sani ba mu'awiya yayi ruwa yayi tsaki ya saida mata,yan uwanta kuma sukace babu ruwansu,sun dauka da hadin bakinta ne,hatta anty ummee yanxu tana gida tana zaman zawarci da nakasar ido daya da mijin ya tsiyayar mata,bayan ya gane dogon lokacin data dauka tana ha'intarsa tare da sanyashi yana cin zarafin uwar gidansa ta hanyar amfani da kissa,ita kanta yanzu ta zama abun tausayi,tayi nadama tayi nadama har babu iyaka,kissa bata amfaneta da komai ba sai dana sani da wahala a rayuwarta,ya karbe dukka yaransa dake wajenta ya danqawa uwar gidansa,ita kuma tana kulawa dasu cikin amana da kulawa (Babu inda ba na gari,babu kuma side din da babu baragurbi,daga iyayen gidan har amaren,saidai mata muji tsoron Allah,mu yiwa Allah mu yiwa muhammadur rasulillahi S A W mu daina wahalar da junanmu,ke idan zaki shiga gidan me mata kiji tsoron Allah,ki tsarkake niyyarki,ki shiga da niyya me kyau,wallahi wallahi idan kikayi haka bata isa taga bayanki kota tozartaki ko ta samu nasara a kanki ba,indai kinyi da zatin Allah,kiyi haquri da wasu abubuwan ki dauke kai a wasu,amma kada ki yarda da cin xarafi,kema uwargida ki sanyawa zuciyarki haquri,ansani kishi yana da ciwo,amma ki dauka haka taki qaddarar tazo,ki sanya Allah a gabanki,ki toshe kunneki daga 'yan gulma da yan bani na iya masu kawo miki labaran da zasu daga hankalinki,karki yarda ki cutar da ita bayan ta shigo koki qoqarin fiddata daga gidan,kada ki manta ko meye kikayi wallahi ba'a cin bashin Allah,duk wanda yaci sai ya biya ko 'ya'yansa sai sun baya,ko bakya raye kinga kin bar musu musiba,ki kama girmanki karki bada qofar da za'a rainaki,ki yawaita addu'a sai kiga Allah ya kwarjantaki an girmamaki ko ba'a so daga ita har mijin,ki dauki girman da Allah ya baki,Allah ya bamu haquri da juriya gaba daya). Tana tsaka da wannan tunanin cikin tsananin qunci da tashin hankalin yadda rayuwa ke gare gare da ita aka bankado labulen dakin,ta firgita ta miqe ta zauna suna kallon kallo da sahura "Badai kin aurar min miji ba?,wallahi babu ke ba sauran zaman lafiya,ki tashi kije ki wanke masa bangon bandaki,yace bai fita ba,bazai dauki wannan qazantar taki ba" daga wannan ta juya ta fita tana karkada mata mazaunai. Ko second biyar bata qara ba haka ta miqe ta fito tun kafin ya dawo yaci zarafinta,jikinta nata ciwo tako ina saboda dukan da tasha,ta qarewa bandakin kallo,babu qazanta ko dis,kawai tiles din jikin bangonne da bata wanke ba,tunda ta fara zaman aure bata taba yiwa bandaki bautar da takewa bandakin gidan mu'awiya ba,bama bandaki ba,gidan gaba daya,wata muguwar tsafta ce dasu daga shi har sahura,kamar masu aljanun tsafta,sanda tazo da qazantarta taci wahala,kyara tsangwama daga baya harda duka kamar diyarsu,sai ayi shara kusan goma a gidan,bandaki kuwa duk bayan awanni haka zata tashi ta wankeshi tasss,tasha wahala sosai,don bata saba ba,zuwa yanzu kuwa ya zame mata jiki,saidai hausawa sukace ba'a sabo da wahala. Tana farawa sahura ta dawo bayanta ta tsaya tana mata gyara cikin masifa,daga qarshe ta dauko kofin bandakin ta dinga sheqawa hafsat ruwan tana dirzawa,tana sane da gayya take hakan,don kusan rabin jikin hafsat din sai data jiqa mata shi,bacin rai yazo mata iya wuya,amma bata isa tayi magana ba yanzu suyi kamar zasu cinyeta danya ita dame gidan,yanzun zata hau mata gorin gidanta ne tunda filin da ginin gidan duka ita ta gina,shi kuma zai hau fadin eh dole ta bita,saboda gidanta ne kuma a gidan ta sameta,don mu'awiyan kamar qarqashin umarnin sahura yake rayuwa. Tunda hafsat ta fita tabar gidan ta barta cikin mutuwar jiki mamaki da kuma juyayi,lallai duniya rawar 'yammata ce,na gaba ya koma baya,muddin bakaji tsoron Allah ba ka shiga uku duniyarka da lahirarka. Sai zuwa yammaci ta samu ta qwarara jikinta ta shiga kitchen,don bata taba saukewa kanta kula da cikin abbas din duk rintsi indai suna a tare. Ita da aminatu ne,don haka cikin sauri ta kammala komai,tabar musu gyaran kitchen din ita da mimi dake da himmar aiki,sannan ta dawo parlor din gidan zuwa bedroom ta tabbatar komai yana kan order,ta kuma cikashi da qamshi ta yadda zai dace da yammacin sannan ta wuce bedroom dinta ta fidda kayan jikinta ta fada wanka. Ta jima a bayi sannan ta fito daure da towel,kome takeyi cikin mutuwar jiki take yinsa,baya ga lamarin hafsat akwai kasala sosai a jikinta,taja kujera ta zauna gaban mirror tana kallon lallausar farar fatarta daketa sheqi. A nutse aka turo qofar bedroom din,ta cikin mudubi suka hada idanu dashi,kamar an manne idanun nasu guri daya,sai kuma kowa ya janye idonsa daga na dan uwansa yana basarwa. Saman sofa bed ya zube kayan hannunsa,ta jawo mai ta fara shafawa "Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki ba tare data kalleshi ba. Dubanta yayi kadan hannuwansa cikin aljihun wandonsa,kamar zai magana sai ya fasa ya amsa mata da yawwa,ya juya kadan ya fara cire kayan jikinshi. Mamaki ya kamata ganin yadda yau ya yada zango a dakinta,neman rigima ne ko kuwa?,daya gama din yaja towel ya daura saman gajeran wandon jikinsa daya tsaya masa iya cinya. A bayanta ya tsaya,ya saka hannunsa ta gefen fuskarta ya shafi wuyanta zuwa fuskarta da zummar jin ko da zazzabin a jikinta? "Alhamdulillah" ya furta qasa qasa harda sakin ajiyar zuciya,sai ya taka ya wuce bandakin,ta bishi da satar kallo,har sai da ya shige sannan ta dauke idanunta,ta saki ajiyar zuciya saita maida man shafawan nata saman madubin kawai ta sanya hannuwanta dukka biyun tayi tagumi. Komai ya tsaye nata a rai,da alama wannan karon abbas din ya fita fushi,hankalinta sam ba'a kwance yake ba,sai yanzu ta sake ganowa azabtar da miji ko sanyashi cikin baqinciki ko yaushe na iya jefa mace cikin jarrabawa,sai taji qwalla ta cika mata idanu,taji kuma ta damu sosai da fadan nasu,wanda bata taba damuwa kamar yanzu ba,don a baya tana ganin kawai wahala zata sha cikin dake jikinta. Sanda ya fito a haka ya sameta,sai ya dauke kansa kamar bai gani ba,duk da qasan Zuciyarsa shima cike take da damuwar fadansu,to amma kuma ya koyi darasi daga zamansa da hafsat,ba ko yaushe kake barin mace da zabin kanta ba,hakanan bako yaushe kake barin mace tayi abinda takeso ko kuma abinda yayi mata suger ba. Yadda ya kauda kai kamar bai kula da taguminta da qwallar dake cikin qwayar idanunta ba sai ya sake sanyaya mata jiki,ta gaza daurewa,sai kawai ta miqe tsaye da sassarfa ta nufeshi,ta fada jikinsa sanda yake ware towel din jikinsa ta ruqunqumeshi. Cak wutarsa ta dauke,saboda tayi masa ba zata,uwa uba kuma yadda fatarta me santsi da laushi ta manne a jikinsa,sai ya gaza ci gaba da riqon towel din ya sakeshi ya fadi a qasa, yasa hannu ya tarbeta cikin jikinsa da kyau amma kuma cikin dakakkiyar murya da kuma basarwa yace "Meye hakan?" Muryarsa na danson yin rawa yana qoqarin daidaitata "Kayi haquri don Allah uncle,wallahi bazan sake ba" "Laifin me kikayi?,ba haka kikeso ba?,so nake dama na gama shiryawa yanzu ina yin sallar isha'i muje a zubar din,kinga nan da next year na auro wata meson haihuwar harta haifamin babies" ji tayi maganar tasa ta soketa sosai,sai kawai ta kasa riqe kanta ta sakar masa kuka sosai tana kwantar da saman qirjinsa hadi da rungumeshi da kyau cikin jikinta tana cewa "Na tuba Allah bazan qara ba" sautin muryarta kawai yana sanya masa nutsuwa,wani bangaren kuma yana sakashi yaji ya buqatu da yawa da ita,sai ya dinga lumshe idanunsa yana jin yadda yanayinsa ke canzawa,saboda sautin kukantan sai ya zame masa kamar fami cikin kunnuwansa da kanta dake kwance a allon kafadarsa. "Ka yafemin don Allah" ta fadi tana qoqarin zamewa ta duqa,yayi hanzarin tattarota zuwa jikinsa,don ko daya bayason ta matsa daga jikin nasa,dumin jikinta ya masifar yiwa jikinsa dadi "Na yafe miki,na yafe miki har abada,but don Allah.....karki sake zancen zakiyi abortion,kalma ce me muni,don zaman aure mukeyi ba dadiro ba,inason kowanne qwayar halitta data fita daga jikina ta bayar da d'a,ko ana ciki sau goma nine ubansa,kuma inaso" ya fadi yana kallon tsakiyar qwayar idanunta ciken mayen so da qauna.[5/28, 7:59 PM] +234 803 416 2581: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 46 *_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_* *LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete* *GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA* _kama daga kan_ Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques _our tittle_ Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram@ Lifestyle_Nig Facebook@ Lifestyleng Tik tok@ Lifestyle_Nig Delivery nation wide _ku tuntubemu ta wannan number_ 08036414048 *Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah* _______________________________ "Na daina uncle" ta fada tana cusa kanta tsakanin qirjinsa tana shaqo qamshinsa mai kwantar mata da hankali,wani ciki ta samu a wannan karon meson qamshin jikinsa,sai ya saki murmushi yana shafa sumarta "Nima kiyi haquri,nasan kinyi missing jikina ko?" Ba kunya ta gyada kai tana sake cusa fuskarta cikin gargasar dake qirjinsa,tsigar jikinsa ta dinga zubawa,shima haqurinsa yakai qarshe,dama shima din kawai basarwa yakeyi tsahon lokacin,sai ya zura hannunsa ta baya ya kwance towel din jikinta ya sulale ya fadi qasa ta koma kamar yadda yake,ya maidata jikinsa sosai suka zama abu daya,kowannensu ya dauke numfashi na wucin gadi sannan suka zuqoshi da qyar,cikin rawar jiki ya dauketa cak ya wuce da ita saman tsaftataccen gadonta da baya gajiya da kwanciya a kai. Ranar dai sai a dakin sukayi sallar isha'i shi da ita,sunyi kewar juna ba kadan ba shi da ita,sun kuma gane yadda suka azabtar da junansu. Suna gaban madubi yana sharce mata gyara mata gashin kanta kafin ta saka kaya ta kalleshi ta cikin mudubin "Uncle" "Babyn uncle" ya amsa mata softly "Don Allah zaka iya yimin wata alfarma guda daya zuwa biyu?" "Kinki qarfin komai a wajena" ta dauki hair mist dinta ta miqa masa ya soma fesa mata sanann tace "Ka yafewa mummyn mimi don Allah,ta roqeni na roqar mata wannan alfarmar" "Na yafe mata,Allah ya yafemu gaba daya" ya fada kansa tsaye,donshi wani lokacin ma mantawa yakeyi ya taba aurenta,sai idan dalili ya ratso. "Na fadi ta biyun?" "Eheen,ina jinki" ya fadi yana buda mata doguwar rigar da zata sanya "Kasan tsakanin uwa da d'a sai Allah,ta roqeni na gaya maka don Allah ka dinga barinta tana ganin yaran nan....." Kallonta yayi da sauri sannan yace "Wait......wai zuwarmin gida ma takeyi ba tare da na sani ba?" "Relax uncle manaaaaa" ta fadi tana juyowa da sauri cikin wata narkakkiyar shagwaba hadi da zube masa fararen manyan idanunta,sai ya dan lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya "Uhmmmm.....u have all my ears" "Bata taba zuwa ba sai yau,kaima ka sani,tunda duka duka yaushe muka dawo qasar uhummm?" "Naji,ni banaso tana shigomin gida,kada ta cutarmin dake wataran,i will send her the kids duk sanda naga ya dace,ama bance zasu kwana ko daya ba,kada ta qara zuwanmin gida please" ido ta lumshe gami da gyada kai,ita komai ma mamaki yake bata,ta yaya zata samu miji irin abbas indai ba mummunar qaddara ba tayi saken da zai kufce mata?,the best husband ever. Sajjad da sajid ne suka fiddasu don dole,suka zauna dukkansu suda yaran a table mat suna cin abincin cikin wani irin yanayi da zai nun maka kyakkyawar rayuwa da mu'amala ta gari da kuma cikakkiyar tarbiyya da suke samu,kai kanka idan kana wajen sai familyn yayi mugu mugun burgeka. ***********Katafaren gidan da ya zama na daban cikin layin shaqe yake da jama'a,gida ne da ya zama mallakin IG(inspector general of police) ABBAS TURAKI,tako ina kana hangen yadda tun daga layin har zuwa bakin titin dazai shigo dakai ainihin kayin ke shaqe da al'umma da kuma ababen hawa na alfarma,ko ina shaqe yake da jama'a,yadda manyan riguna da kuma fararen kaya keta nuna kansu,na wannan yana wane wancan,da kuma yadda busar algaita ke tashi kadai zai gaya maka cewa wani katafaren daurin aure akeyi. Ta cikin microphone din dake fitowa daga masallacin,kana iya jiyo muryar wani qaqqarfan mutum na cewa "An bawa muhammad yasir matawalle auren Dr raheema(mimi) IG abbas turaki akan sadaki naira dubu dari lakadan ba ajalan ba......eh diya ga shugaban duk wani dan sanda dake nigeria" ya sake bayani cikin kambamawa irin na maroqa. Dai dai lokacin da IG abbas ke zaune daga can wani sashe na masallacin cikin shigar alfarma ta farar shadda da babbar riga me asalin tsadar,fuskarsa cike da wani irin haiba kwarjini da kuma cikar kamala,sanarwar data haifar da wanzuwar murmushi saman nutsatsiyar fuskarsa,ya sauke boyayyr ajiyar zuciya yana godewa Allah da ya fara nuna masa auren diyar cikinsa ta farko. *C I K I N G I D A* Wani kebantaccen falo ne dake da matuqar kimar da ba kowa take bawa damar saka qafarsa a ciki ba,falo ne na musamman da aka tanadeshi saboda hutawar IG,yake kuma samun kulawa qarqashin uwar gida sarautar mata wato hajiya widad,kamar yadda komai na IG din yake qarqashin jagoranci da kulawarta,duk kuwa da ma'aikatan dake gidan. Duk girman falon su biyu ne a ciki,ita da amarya mimi dake lullube cikin wata lafiyyayar alkyabba,hannunta dake dauke da Wani irin lalle yana sanye cikin tafin hannun hajiya widad da yasha lafiyayyen jan lalle da bata rabo dashi,wadda tana zaune ne a gabanta suna fuskantar juna,tana karanto mata wasu addu'o'i tana maimaitawa. Ta dauketa ne daga cikin taron hayaniyar jama'ar saboda yadda tunda satin bikin ya kama take fama da koke koke,ita batason tafiya tabar maami,ita ba zata je ba,hankalinta na sake tashi idan ta tuna a yau zatabar qasarta ta haihuwa,zata tafi wata uwa duniyar zaman aure ita da mijin da Allah ya bata wato muhammad yasir. Sai data gama karanta addu'o'in kaf yadda maamin tata ta karanta mata,sai suka hada ido,widad tayi qoqarin danne raunin zuciyarta don kada ta karya ma mimi qwarin gwiwar data samu "Basai nace miki komai ba mimi,bani da haufi a kanki,kowanne d'a namiji zaki iya zaman aure dashi,ki kuma mallaki zuciya da hankalinsa babu boka ba malam" kai mimi ta jinjina,ita shaidace yadda maamin nasu ke tafiyar da mahaifinsu,koke 'ya mace akewa haka sai an samu kanki fiye da zato,wata irin macace da batasan ya zata fasaltata ba,a taqaice ta zame mata wata role model dinta,tana kuma alfahari da ita,hakanan tana kiranta da uwa a duk inda ta shiga a duniya,maamin ta zamewa rayuwarsa alkhairi,dukkan mutumin da ya shigo rayuwarsu daga baya yana mata kallon mahaifiyarsu ce data tsugunna ta haifesu,ta basu abinda dukka uwa ke bawa yaranta,harma abinda wasu uwayen suka kasa bawa yaran nasu,koda wasa bakinta bai taba kiran widad a matsayin uwar riqo ba bare wani suna na kishiyar uwa,kullum kallon mahaifiya suke mata,duk da sunsan asalin wadda ta haifesun,amma ko ita kullum gaya musu takeyi widad dince babarsu,itakam kawao naqudarsu tayi ta kawosu duniya,amma idan suna neman uwa itace. Zamewa tayi ta tsugunna gabanta "Maami ki yafemin don Allah tsahon zamanmu idan na taba bata miki...." Da sauri ta kama kafadunta ta dagota ta zaunar da ita sosai "Bakiyimin komai ba mimi iya zamana daku,kun riqeni kamar mahaifiyarku,saidai nan gaba zakiyimin laifin" da sauri ta daga kai ta dubeta,saita sakar mata murmushi tana jinjina kai "Eh,muddin baki zauna lafiya gidan mijinki ba,muddin bakiyi haquri dashi ba,muddin ya kawo qararki gida ya zamana kece da laifi" "Bazan miki laifi ba kuwa har abada maami,saidai in har ajizanci irin na dan adam" ta fada kuka na qwace mata,idan batayi zaman aure bama ai bata yiwa maaminta adalci ba,ta basu dukkan misalai na rayuwa da zamantakewa a baki da kuma a aikace,su shaida ne sun gani. Juriya da jarumtar nan tata ce kawai ta hanata kuka,tayi qoqari ta saukar da mimi daga kukan da takesonyi tana tsokanarta,dai dai sanda khadijatou (diya mace qwaya daya da widad din ta haifa qanwa ga mimi) taturo qofar a hankali tana baza ido "Na shigo maami?" Ta fada a dan shagwabe tana leqo da kanta "Meye haka kamar munafuka?,shigo ki rufen qofa banason wancan me zuciyar matan(affan) yasan muna ciki yazo su hadu suyita ma mutane kuka kamar cewa akayi idan ta tafi ba zata dawo ba" murmushin yaqe khadijatou kawai tayi,don itama daurewa kawai takeyi,anty mimin she's the part of their lives,ta iya tafiya da qannenta cikin kulawa da qauna,bata fada amma ta iya hukunci,ta iya wasa da dariya amma idan gyara yazo babu wannan wasan,dukkansu sun dauketa kaman abokiyar wasansu,amma kuma suna girmamata sosai,itama ta iya zama da kowa a cikinsu da halinsa,sun taso da shaquwa da qaunar junansu qwarai,ba zaka taba cewa ga wadanda suke uwa daya uba daya ba,yanzun haka khadijatou tafi nawwara jin tafiyar mimin,har gwara yusra ma,itama duk da haka affan ya fita rauni,saboda anty mimin abokiyar sirrinsa ce,kuma abokiyar gulmarsa,sai mimin taji abunsa maami widad bataji ba. "Wai dangin angon sun sakeyin tuni,sha biyu zasu wuce airport din,jirgi qarfe uku zasu bi" ta fada qasa qasa tana satar kallon anty mimin nasu,kai widad ta jinjina "Yayi gamu nan" a sanyaye khadijatou din ta juya ta fice tana matse qwallarta. Hannun mimi maami widad ta riqe cikin nata, suka ratsa falon suka fita ta qofar baya suka wuce kai tsaye suka sashen da aka sauki mummy hafsatu da danginta. Da sallama ta shiga matsakaicin falon sashen,mummy hafsatu na zaune saman kujerun falon,sanye da wani lace wanda widad dince ta dinka mata shi da kudinta,tace koda bataci arziqin abbas na kai tsaye ba tunda tana da igiyar auren wani a kanta ba,amma zataci arziqi sa darajar yaranta su mimi. Da sallama ta shiga,hafsat da dangin hafsat din da suke tare da ita suka fara yiwa widad din sannu,don ko maqiyinta ya yaba mata,yaga yadda ta kasa tsaye ta kasa zaune kamar diyar data tsugunna ta haifa take aurarwa. *_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_* *LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete* *GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA* _kama daga kan_ Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques _our tittle_ Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram@ Lifestyle_Nig Facebook@ Lifestyleng Tik tok@ Lifestyle_Nig Delivery nation wide _ku tuntubemu ta wannan number_ 08036414048 *Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah* [5/28, 9:33 PM] +234 803 416 2581: *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 47 END *_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_* *LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete* *GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA* _kama daga kan_ Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques _our tittle_ Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram@ Lifestyle_Nig Facebook@ Lifestyleng Tik tok@ Lifestyle_Nig Delivery nation wide _ku tuntubemu ta wannan number_ 08036414048 *Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah* _________________________________ Gaban hafsat taje ta tsugunnar da mimin sannan ta zauna daga gefe "Mummyn mimi,ga mimi tazo neman albarka,yau dai Allah yayi zata tafi nata gidan,sai ayi mata sauran nasiha a kuma saka mata albarka" hawaye hafsat din ta fara sharewa,farinciki ne fal zuciyarta na samun uwar riqo ta gari da sukayi,ta tabbatar inda a hannunta suke babu lallai mimi din ma ta samu miji irin muhammad yasir,wanda ba abinda ya fara burgeshi da mimi din sai tarbiyyarta da kuma nutsuwarta,shine babban abinda ya fara jan hankalinsa "Aikin gama gaya mata komai,nikam babu abinda yayi saura da zan gaya mata wanda baki gaya nata ba, abinda zata samu daga bakinki yafi wanda zataji daga gareni,abu daya zan gaya mata shine,tayi koyi dake,tayi koyi dake,tayi koyi dake,don kin zamewa rayuwata alkhairi,kin maida yarana abun kwantace abun sha'awa,kin gyatta tawa rayuwar nima a yanzu na dace da mijin da yasan darajata,kin rabani da mu'awiya,Allah ya hadani da mudassir kin kuma tsayawa rayuwata da jari da sana'a,wanda yayi maka wannan me zakace dashi?" "Babu...babu" shine amsar da yan uwanta da a yanzun suke zumunci ta kuma.kamasu da amana irinsu anty uwani amsar da suka bayar kenan,a yanzun suta riqe ta watsar da irinsu anty ummee duk da suma jikin ta qaura yayi la'asar, rayuwa ta gama karanta musu nata karatun. "Allah ya albarkaci rayuwarki,ya baki ikon yin koyi da babarki widad" shine maganar hafsat na qarshe,akayi addu'a sosai sannan suka miqe don sadata da dangin banbanta su gwaggwo mero sukayi sallama. Sanda akaxo sanyata a mota don su wuce kasa tsaiwa gurin widad tayi,don dukka dauriyarta ta qare,yaran duka affan sajjad sajid khadijatou nawwara yusra al'ameen harda auta fadil kuka sukeyi,sun riqeta kyam sai da IG yazo ya tsawatar musu yana hararar affan "Kai dai kam anyi yaayan banza,ita kanta yanzun mimi din ba kaine yayanta ba?" Akasa dariya gaba daya,sai affan din ya fara ciccijewa kuma yana qoqarin maida qwallar data cika masa ido,ya waiwaya gasu sajjad, identical twins masu kama daya "Ku kuma mage da bera.......kun gama cakar da ita sai yau kukasan yaaya mimin taku ce?, nawwara harda ke?,ranar fa ina jinki kina cewa gwara ta tafi ta barki ki shaqata,ba wanda zanwa jaje ma sai hadizatu" yusra ta yunquro "Daddy nifa..."kafin ya bata amsa al'ameen ma yace "Nima daddy" duk sai suka bawa kowa dariya,kowa so yake ya nuna mimin tashi ce,shi kansa IG a sannan qarfin hali da dauriya kawai yakeyi. Kusan duka motocin gidan aka dauka yiwa mimi rakiya airport,duk titin da suka ratsa sai ansan 'yar IG ce zata wuce,don qarqashin security suke har suka isa. Sai da suka isa din IG abbas ya juya ya juya baiga widad ba,ya saki murmushi qasan ransa,yasan tana can tana kukan data ci masa alwashin ba zatayi ba,basu bar airport din ba sai da jirginsu mimi ya tashi sannan kuma sukayo gida. Sanda ya dawo ya dinga bulayin nemanta cikin gidan amma bai ganta ba,daga qarshe acan part dinsa cikin qawataccen bedroom dinsa ya cimmata,ta gama kukan nata ta wanke fuskarta,tana tsaye gaban madubinsa tana laluben powder da takan ajjiye zata shafa. Sunan hada ido tayi saurin janye idanun nata,ta wani hade rai tasha mur,ita lallai kada yace ta karaya sai da tayi kukan,dariya ta qwace masa ba tare da ya shirya ba,dariyar tasa ta qara raunata zuciyarta,yazo bayanta ta tsaya yana duban qwayar idanunta,sai kawai ta sakar masa kukan shagwaba tana fadawa jikinsa,shagwabar nan da har yau ba abinda ta rage masa a cikinta,bata ganin girmanta idan tana tare dashi,kamar yadda bata ganin girma da shekarun abbas din,har yau tana ganin kamar jiya jiya suka hadu,kamar jiya jiya aka daura musu aure,shi dinma kullum kallonta yake a mitsitsiyar widad din nan,shagwababbiyar ummu,mai yawan tsoro wauta da sakalci. Ya zare babbar rigarsa ya ajjiye gefan gado yana murmushi,ya sanya hannuwansa duka ya ya lullubeta cikin jikinsa,ya sani daman,ba zata iya jura ba,kuma duk duniya a yanzu shi yafi kowa iya lallashinta,yadan hura mata iska a fuska kadan yana cewa "Ai dama na sani,you can't take it......ke kuma da son yara,ai dama na shirya aikin lallashi" sai da yaga kamar kukan bazai tsaya ba sanann suka zauna,ya kama dukka hannayenta yana bata baki,daga qarshe ta buge da murmushi cikin jin kunya tana boye fuskarta saboda wata kalma da ya gaya mata,ya miqe shima yana dariya "Nifa madam aiki yayi kira,ina tunanin nima yau da dare zanbi jirgi na koma abuja,ki taimakeni ki sallami baqinki kiyi qoqari ki biyoni,bana jin dadin gidan sam idan baki kusa" ta riga data saba,duk inda abbas din zashi sai ya ganta a gefansa hankalinsa yake kwanciya,duk inda zashi a nan nigeria ko a waje sai ya tafi da ita,tun tana zolayarsa harta gane haka tsarinsa yake,a jininsa qaunarta take,hafsat ta kasa fuskantar sa tun farko akan irin wannan tsarin nasa abinda ya fara kawo musu matsaloli kenan tun yana qaramin dan sandansa ana yawan masa musayar garuruwan aiki,shi mutum ne dakeson ko yaushe yaga yana tare da iyalinsa,bawai kasancewa ta auratayya ba, a'ah, at least ya dawo daga duk inda yake ya shigo gida ko masauki ya tarar dake,ita data fuskanci hakan sai ta bashi dukka rayuwa da lokacinta,shi kuma ya sakar mata ragamarsa. Bashi da tsanani ko takura sam,mutum ne mai wani irin sauqin hali kawaici da kuma yawan bada uzuri,shi yasa idan kaga yadda sukeyi da 'ya'yansa da yadda yake mu'amala cikin gidansa abun zai daure maka kai sosai,ba zakace shine wannan namijin zakin IG din ba "Zaki biyonin please?" Ya tambayeta cikin karya murya, dariya taso kamata "Habba uncle.......ka girma fa,yau din nan ka aurar da diya ko ka manta?" Mur yadan sha "Hakane fa,zaki biyonin?" Ya fada yana murtike fuska da murya,dariya ta qwace musu a tare saboda yadda yanayinma sam bai masa kyau ba "Zan biyoka uncle,kusan zuwa anjima dama kowa zai wuce gida,na nesan ma gobe zasu tafi,amma ayimin alfarma zuwa jibi saina taho,zan sauka na duba jikin ummu daga can saimu siya wani ticket din,banason ma mu wuce jibin saboda yara duka zasu koma school suma,banason faashin makaranta" fuskarta ya kama yayi kissing goshinta "Na gode,Allah yayi miki albarka,yadda kika kula dani da yarana da sauran dukka dangina,ina roqa miki aljanna madaukakiya tun daga duniya har zuwa lahira" murmushi mai sanyi ya qwace mata,ta kama button din rigarsa tana dan wasa dashi "Kaine sirrin komai uncle,ka cancani fiye da haka,don ka zamewa rayuwata wani alkhairi,tun bansan meye rayuwa ba har na santa,Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwarka yaci gaba da yi maka jagora,ya doraka saman maqiyanka,ya tabbatar da nasara a dukka rayuwarka" "Ameen summa ameen wuddu na" ya fada yana jifanta da wani sassanyan kallo daya sanyata jin kunyarsa,saita fice tana cewa bari ya hado masa abinci,ta tabbatar jama'a basu barshi yaci ba,daga nan kuma ta duba komai ta samu yana tafiya yadda ya kamata,su amina su nujood Aafiya na'eema da muneera na kula da komai,don haka ta wuce kitchen ta dauki zababbun warmers din IG ta soma shirya masa abincin da kanta. *Komai yayi farko yana da qarshe!!* _Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah,dukkan godiya ta tabbata ga Alla madaukakin sarki me kowa me komai daya aramin rai da lafiya har na kawo qarshen labarin A RUBUCE TAKE_ _thank you arewabooks followers for being with me all this while from beginning to end_🥰🥰👏🏽 _Godiya ga tarin masoya mabiya daga kowanne lungu da saqo na media,musamman wadanda basa gajiya da kasancewa tare damu da siyan rubututtukan zafafa biyar ta manhajar watsapp,Allah ya qara danqon zumunci da qauna mara yankewa,ubangiji ya kula da lamarinku_ *Abinda muka rubuta dai dai Allah ya bamu lada,wanda muka kuskure kuma ajizanci ne irin na dan adam,muna fatan Allah zai gafarta mana,ya yafe mana kusakurenmu mu daku gaba daya,sai Allah ya sake sadamu a rubutu na gaba da wasu ZAFAFAN LABARAN idan ubangiji ya bamu aron rai da lafiya* *Na gode na gode na gode* @team zafafabiyar _subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'atubu ilaika_👏🏽👏🏽