[8/3, 12:57 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *1.* _Na_ *Rahma Kabir*✍🏾 Mototaci ne guda uku suke tafe bisa hanya aguje, dukansu gilas d'in motocin masu duhu ne, mota ta farko dake gaba bodyguard ne a ciki. Sai na tsakiya motar d'auke yake da tsadaddun 'yan mata su uku wanda ba zasu wuce shekaru Ashirin da biyu (22yrs) ba a duniya. *'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin wak'ar tamkar sune suka rerata, sunayi suna rawa da jinsu da kad'a kai, kana ganin su kaga 'ya'yan gata, cike suke da farin ciki fal da nishad'i, domin ba suda wata damuwa ko matsala a rayuwansu. Motan baya itama na bodyguard ne, suke marawa motan Queen baya. Wani Matashin Saurayi wanda bai wuce shekara Talatin ba (30yrs), yake tafiya cikin sauri domin ya amso wa Ummansa nik'an masara da k'anwarsa Khadija ta kai ta aje, saboda zata wuce tallan kwai, hankalinsa yayi nisa sosai cikin tunani, baisan yahau kan titi ba. Meena ce taja mugun burki, ji kake k'iiiii kad'an ya rage ta buge shi, Aryan tsayawa yayi cak ya runtse ido yana fad'in *Innalillahi wa inna ilaihir rajuun* jira yake motan ta bigeshi domin ya riga ya sadak'ar motan zata kad'eshi, Cikin b'acin rai Queen Basma, Leema, Meena duk suka fito a motan, haka bodyguard suka yi parking akan hanya suka fito rik'e da bindigogi, cikin k'ank'anin lokaci suka had'a gosilo, mutane suka fara taruwa, ganin bindiga ne yasa kowa ya kama kansa, Queen Basma ta k'arasa kusa da Aryan bodyguard suka take mata baya, tsadadden k'amshin turarenta ne ya dawo da hankalin Aryan jikinsa, domin ji yayi wani k'amshi na ratsashi, bud'e ido yayi a hankali yayi tozali da kyakkyawar fuskan Queen wanda saida gabansa ya fad'i, nan take tsoro ya ziyarce shi, kallon k'asa da sama Queen Basma ta bisa dashi cike da jin haushinsa, kyamansa taji saboda wani irin warin zufa dake tashi a jikinsa, tattaro miyon bakinta tayi ta tofa masa a jikinsa tare da toshe hancinta da hankacif, juyawa tayi ta kalli d'aya daga cikin bodyguard d'inta, cikin sauri ya k'araso, Aryan baiyi aune ba bodyguard d'in ya kifa masa kyakkyawan mari guda biyu, Leema ce ta k'araso cikin isa tace "Hee, Marin ma kad'ai ya ishe shi" sai ta juya tana kallonsu Meena tana murmushi, ta kuma cewa "babies mu wuce kar mu b'atawa kanmu lokaci akan wannan mahaukacin, kunsan duk muna da abinyi a gabanmu". Dakyar Aryan yaja k'afansa zuwa gefen hanya, zuciyansa cike da k'unci, su kuma su Meena suka shiga mota suka wuce. Tsananin damuwa ne Aryan ya tsinci kansa a ciki, sai ya fara zancen zuci yace, "shi dai talaka kullun shi wulak'antacce ne a idon jama'a, Allah kai ka haliccemu kayimu ma banbantan jinsi, kaine mai girma, ka saka mini da kyakkyawan sakayya" wani guntun hawayen ya sauka a kuncin sa, ba abinda yake k'ara masa bak'in ciki sai irin yanda Queen Basma ta tofa masa miyau, murmushi yayi na k'arfin hali ya girgiza kai a fili ya furta "Rayuwa ce" sai ya wuce inda zashi. Sai gabda Magrib ya kaiwa Umma nik'an masaran, ya sameta ta rafka tagumi, sallaman da yayi shine ya dawo da ita daga duniyar tunani data fad'a, nisawa tayi ta amsa tace "Aryan ya akayi ka dad'e ga ruwan sanwan ya tausa harya fara k'onewa" zama yayi a tabarma dake tsakar gidan yace "Umma kiyi hakuri naje basu nik'a ba saida na jira suka nik'a shiyasa na dad'e" Umma tace "Allah sarki, ba damuwa tunda mun samu nik'an yanzu zan gama insha Allah" Nan ya zauna yana mata hira tana aikinta har aka kira sallan Magrib ya wuce masallaci. Ta b'angaren su Queen Basma kuwa gidan hutawanta suka wuce, musamma tasa aka gina mata shi dan hutuwa. K'aton gida ne babban flat wanda ya k'unci kayan alatu a ciki, ginin zamani aka yi shi a tsakiyar babban fili, filin gidan za a iya pakin mota goma, sai daga can gefe ruffa ne mai d'auke da kujeru da table a tsakiya, an tanaji wannan wurin dan hutuwa, wurin zagaye yake da shukokin furenni masu fidda k'amshi mai dad'i, sai kuma daga bayan gidan katon swimming pool ne wanda aka sanya masa ruwa mai kyau da tsafta, in ka kalli ruwan har kashe ido yake dan haske, lokaci-lokaci ake jenye ruwan ana sauya wani. Daga gaban swimming pool d'in akwai wata yar k'aramar k'ofa wanda sai sadaka da cikin garden(lanbu), ya k'unci bishiyoyi na kayan marmari (fruits) da kuma kujeru na hutu dan shawakatawa, wurin ya had'u matuk'a. Suna shiga cikin gidan suka shiga babban falo, basu zauna ba sai ko wacce ta nufi d'akinta kamar yanda suka saba, falo ne mai d'auke da d'akuna guda biyar ko wanne da ban d'aki a ciki (toilet), d'akin faro shine na Leema wanda aka k'awata shi da kayan Sarauta a matsayinta na gimbiyar 'yar Sarkin Kano. D'aki na biyu shine na Queen Basma wanda aka kawatashi da kayan more rayuwa, an kashe mak'udan kud'i sosai, a matsayinta na 'yar shugaban k'asa. Sai d'aki na uku na Meena ce, wanda shima aka k'awata shi da dukiya, amma bai kai na Queen ba, a matsayinta na 'yar gomna. D'aki na hud'u kuma an sanya masa kaya dai-dai misali, sun bar d'akin na masaukin bak'insu. Sai kuma d'aki na biyar, tsadaddun kayan motsa jiki ne a ciki, wanda ko wani lokaci sukan mota jikinsu a ciki. Sai katon kitchen dake gefe yaji kayan amfani. Wannan gidan musamnan Basma tasa mahaifinta president ya gina mata shi, bayan dawowarta daga k'asar England karatu, kasan tuwar sunyi karatu tare da Leema da Meena yasa ta sanya ko wacce aka shirya mata d'akinta dan soboda tsananin shak'uwar su kullun suna tare. Queen ce ta fito daga ita sai best da pant ta d'aura towel a k'ugunta, hanyar k'ofar baya tabi ta bud'e, direct wurin swimming pool ta wuce, tana isa ta cire towel d'in ta fad'a cikin ruwan ta soma iyo, suma su Meena haka suka fito cikin shigar da Basma tayi, cikin ruwan suka shiga suma suka fara wanka, ko wacce na abinda ya shafeta. Sun kai misalin Rabin awa a ciki kana Meena ta fita a ruwan, ta zauna a kujeran hutawa dake bakin swimming pool d'in, wani jaka naga ta d'auka ta zage zip d'insa, sigari ta ciro tare da leta, sai ta kunna mata wuta ta hure, kana ta kwanta a bayanta tana zuk'ar sigarin tare da fidda hayak'i sosai ta hanci da baki. Leema ma fita tayi ta zauna a kujeran hutuwa nesa da Meena kad'an, wayarta ta d'auka ta fara chart da abokin harkanta, murmushi take zubawa ita kad'ai da alama tana jin dad'in hiran. Queen Basma tana cikin ruwan ta tsaya da wankan cikin fad'a tace ma Meena "Malama kinsan na hanaki wannan shirman muddun ina wuri ko, ya zaki kunna sigari ya rik'a cutar damu, kuma kinsan bana son warinta" cike da d'aure fuska Meena tace "To maida damuwarki zan kashe shikenan?" sai ta kashe ta jefar, bud'e jakanta ta kuma yi ta d'auko kwalban syrup tace cikin gatsali, "in kin hanani shan sigarin to ba zaki hanani shan wannan ba, don ita ba hayak'i". Basma take ta fito cikin ruwan ta d'auki towel d'inta tare da gallawa Meena harara tace " kanki kike cutarwa" taja tsaki ta wuce cikin falo. Meena itama ta bita da harara bata ce komai ba, Leema ta kalleta ta kwashe da dariya tace "wow ina son fad'anki da Basma, domin kullun sai kinyi abinda bata so a wurin nan, ita kuma kullun sai ta tanka miki". Tsaki Meena taja tace "Ke kuma 'yar sa ido, to ya isheki, kije ki cigaba da iskancin ki, gwara ni bana bin maza" ran Leema ne ya sosu, ta d'aure fuska, nan take sarauta ya motsa mata, tashi tayi tabi bayan Basma. Meena ta bita da dariya tace "na dai rama". Leema ta samu Basma sanye cikin riga iya cinya ya kamata, ta sanya wakar music sai tikar rawa takeyi tana mota duk sassan jikinta, tsaki Leema tayi tace "zaki damu mutane da wannan wak'ok'in shirme" cikin fad'a Basma tace "ina ruwanki, naga kowa yanayin abinda ya dameshi ne, ki shiga d'akinki kiyi chart da samarinki ban takuraki ba, nima ki barni inyi rawata", hararanta Leema tayi bata tanka mata ba, Meena ce ta shigo falon idunanunta sunyi jawur saboda ta shawu, joining d'in Basma tayi suka cigaba da rawa ba tare da ta canza shigar dake jikinta ba. Saida aka kira sallan magrib kana Basma ta kashe wak'ar, duk suka wuce d'aki, wanka ta fara yi tare da d'auro alwala, jallabiya ta sanya wacce take sallah dashi ta sanya hijab ta tayar da sallah, bayan ta idar tayi duk azkar da ake karantawa da yamma, ta d'aura da Addu'a, Al'Qur'ani ta shiga karantawa cikin muryanta mai zak'i, tana zaune a haka har aka kira sallan Isha'i, sai ta rufe Al'Qur'ani ta gabatar da Sallan Isha'i. Bayan ta idar ta mik'e ta sauya shiga cikin doguwar riga har k'asa yar kanti, ta kamata sosai tun daga samanta har k'ugu, daga gwiwa ya bud'e kad'an har k'asa an masa tsagu. Ta busar da gashinta da hand dryer, ta sanya mai ta kamashi da ribon a tsakiyan kai, ta bar jelan gashin yana reto a bayanta, ta d'auko hular mulki na Queen ta aza a saman gashinta, turare ta fesa masu dad'in k'amshi, ta sanya siririn sark'an goal a wuyanta tare da d'an kunne, a gogon hannu ta sanya da zobe, tayi kyau sosai, sai ta sanya takalmi dogo mai igiya, haka ta d'aureshi har k'auri, saida ta k'arewa kanta kallo a madubi sosai kana tayi wani murmushi wanda yake k'ara fidda kyanta, sai ta nufi falo cike da takun k'asaita. Kallon-kallon su Meena da Leema suka yi saboda irin had'uwar da Basma tayi, sai suka ga tasu wankan ba komai bane saboda Queen ta lashe duka wankansu. D'aukarta photo suka farayi kala-kala, suna mata kirayi tare da kurantata, a kullun Basma in dai zasu fita zuwa club irin wannan shigan takeyi, amma fa ko wani shiga da kalarsa domin sai afi watanni bata maimaita wani shigan da tayi ba, ko wace rigan daban. Bayan sun gama d'aukarta photo, nan suka had'u suka yita selfee, suma su Meena sunyi kyau ba laifi, shigan dogayen riguna sukayi tare da barin sumarsu ya zuba a bayan su, kansu ba d'ankwali, dogayen cover shoe suka sanya sunyi kyau sosai amma fa basu kai Basma ba. Fita sukayi suka shiga mota dukansu a seat d'in baya suka zauna suka sanya Basma a tsakiya, driver ya jasu, tare da bodyguard suna gaba, da kuma masu rufa musu baya sai club. Aryan ya dawo daga sallan Isha'i, ya samu su Umma a tsakar gida kan tabarma suna cin abinci, shima zama yayi a shinfid'ar da yake mai girma ne, Khadija ta mik'e ta isa kitchen ta kawo masa abincinsa, bud'ewa yayi tare da cewa "nagode Dija", sun kammla cin abinci dukansu sai Aryan ya kai dubansa inda Dija ta zauna yace "Khadija meyasa in kika fita tallan kwai bakya dawowa gida da wuri" marai raicewa tayi tace "Yaya Aryan wallahi ba kasuwa ne shiyasa nace bari na k'ara lokaci ko zan saida duka, ka gafa tun shekaran jiya Umma ta dafa min amma har yau bai k'are ba" shuru yayi na 'yan dak'ik'a kana yace "ai Dija mutum baya wuce rabonsa, ni dai dan Allah ki rik'a dawowa da wuri kuma duk inda kike ki tuna matsayinki da rik'e mutuncinki" "tom Yaya Aryan insha Allah zan kiyaye" Umma na jinsu tace "Aryan gwara ka rik'a mata fad'a, d'azu ma sai bayan magriba ta dawo" yace "ai Umma wallahi ni da ina da hali da Dija ta daina tallan nan sam bana sonta" Umma tace "to Aryan ya zamuyi, haka Allah ya rubuta mana, ya zancen rumfanka an gyara kuwa?" gyara zama yayi yace "Umma ba kud'in gyara shiyasa na koma gefe ina aikina inna samu kud'in zan gyara, gashi yanzu cinikin sai Addu'a tunda Lawal ya dawo kusa dani ya kwashemin customers d'ina" Umma tace "karka damu insha Allah in kud'in kwai ya taru zan baka ka gyara runfar, batun kuma Lawal ka rabu dashi kowa rabonsa zai ci, muyi ta Addu'a Allah ya kawo mana karshen wannan hali da muke ciki". Duk suna amsa da Ameen kana suka cigaba da hiran duniya. *Muje zuwa...*🤔 *_Rahma Ce_* [8/3, 12:58 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *2.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Su Basma suna isa club, suka wuce cikin hol d'in, mutane ne sosai a ciki maza da mata, daka gansu kaga 'ya'yan manya, tsautsayi ne zai kai d'an talaka wurin, kid'a da sauti ke tashi kowa na zaune, kamar yanda suka saba zuwa suna da nasu wurin zama na musamman, duk suka zauna, aka cike musu wurin da kayan motsa baki, wani kyakkyawan Guy ne yazo kusa dasu suka gaisa Amma banda Basma domin bata shiga harkan Maza, Leema ce ta mik'e saurayin mai suna Jalal ya rik'ota ta kugunta suka wuce tare da hiransu na masoya, fita sukayi a wurin suka wuce cikin hotel da club d'in ke ciki. D'akinsa ya bud'e suka shiga, kamar suna jirace da juna suka fara kaiwa juna sak'onni, nan da nan suka rikice suka lula duniyar shashanci, Allah ya shirya Ameen, nan na fito na basu guri. Ita kuma Meena ta mik'e ta wuce group d'insu na mashaya, wurin mata ne da maza a had'e, suna ganinta suka fara ihu, wuri suka bata ta zauna ta fara aikawa da syrup. Queen itama Abokan rawanta suka matso kusa da ita nan suka d'unguma zuwa saman dandamali, nan fa kowa hankalinsa ya tashi ganin Basma ta hau, hayaniya ya k'aru suka fara ihu domin sunyi missing ganin rawan Basma, aka d'aura mata best wak'arta na music d'in labarawa, Queen Basma ta soma rawa mai ban mamaki tamkar ba jikinta take k'aryawa ba, sai wuri ya kuma hautsibewa da ihu, dama abinda Basma keso kenan, mutane suka fara mata yayyafin kud'i masu taya ta rawa suka k'ara dagewa farin ciki ne ya rufe su domin sunsan yau zasu kwashi kud'i. Dan in sun gama Basma cewa take a basu kud'in su raba. Sai da taci rawa mai isarta kana ta sauka ta samu guri ta zauna tana maida numfashi, sauran 'yan rawar suma suka sauka, aka kwashe kud'in su tas aka basu, farin ciki ya gama rufesu domin yau sun samu kud'i sosai, suna alfahari da Queen data zama star d'insu. Sai misalin k'arfe ukun dare suka dawo gida, ko wacce ta nufi d'aki ta kwanta, nima saina tayasu rufe k'ofa nace saida safe. *Washe gari* Da misalin k'arfe takwas na safe Aryan yayiwa Umma sallama ya wuce kasuwa kamar kullun, yana isa rumfansa hawaye ya ciko fal idonta, girgiza kai yayi saiya bud'e k'aton buhu da yake kasa kayan miya, haka ya karkasa tumatur, tarugu, sai tattasai, samun wuri yayi ya zauna daga inda rufin shagonsa ya kifa ya rab'e, sai ya rafka tagumi ya fara tuno rayuwansu. *ASALIN ARYAN? "* Sunan mahaifinsu Aliyu, Asalinsu fulanin Gombe ne, mahaifinsa ya rasa Iyayensa tun yana k'arami, a wurin k'anin Baffansa ya tashi Malam Mu'azu, ya had'ashi da yaransa su biyu Aisha da Ibrahim ya rik'e. Matarsa Inna Amina suna kiranta da Inna Lami ta rik'e Aliyu Amana tamkar ita ta haifeshi, duk inda Aliyu yake Khalil na wurin, sun tsaku sosai makaranta tare suke zuwa, ga k'anwarsu Aisha suna ji da ita. Wata rana Inna Lami ta aiki Khalil kasuwa shuru-shuru bai dawo ba har aka d'auki tsawon lokaci, abu kamar wasa Khalil ya b'ace anyi niman duniya amma ba amo ba labari, Malam Mu'azu da Inna Lami sun shiga tsananin damuwa, tun ana kwana d'aya da b'atan Khalil har ya d'auki tsawon wata ba'a ganshi ba balle aji labarinsa. Haka su Inna suka runguma Aliyu da Aisha suka barwa Allah lamarin sa da Addu'an Allah ya bayyana musu Khalil ko a mace ko a raye. Aliyu kuwa har rashin lafiya yayi saboda rashin d'an uwansa. *Bayan shekaru* Aliyu ya gama diploman sa a b'angaren kasuwanci, yana da shekaru 26. Aisha kuma tana da shekara sha takwas Malam Mu'az ya had'a Aliyu da Aisha auren zumunci, basu damu ba dama suna son junansu saboda akwai shakuwa mai k'arfi a tsakaninsu, Ana d'aura musu Aure sai suka tare a wani gefe daga cikin gidansu. Bayan wata biyar da aurensu wani abokin Malam Mu'azu yazo Gombe mai suna Alhaji Sani, Malam yayi masa kyakkyawan tarba, d'aya tashi tafiya ya rok'i Malam akan ya bashi Aliyu ya tafi dashi Abuja tunda yayi karatu, ya d'auke shi aiki a companyn sa, da farko Malam bai yarda ba, amma daga baya saiya amince bisa sharad'in sai dai Aliyu ya tafi da matarsa, Alhaji Sani ya amince, cikin kwana biyu suka shirya sai garin Abuja. Alhaji Sani mutum ne mai kirki, ya siyawa Aliyu k'aramin gida mai d'aki ciki uku da kicin da ban d'aki, sai kuma filin tsakar gida k'arami madaidaici a unguwar suleja, ya kuma siyan masa mashin da zai rik'a zuwa aiki. Farin cikin wurin Aisha da Aliyu baya misaltuwa, Aliyu ya fara aiki a company Alhaji Sani a matsayin Massinger. Sukan ziyarci Gombe duk bayan watanni biyu ko uku tare da alkhairai masu yawa. *Bayan wani lokaci* Aisha ta haifo d'anta Namiji suka sanya masa suna Aryan, Aryan ya tashi cikin kulawa da gata na iyaye, sun sanya shi makaranta mai kyau da tsada, Aryan yaro ne mai hazak'a b'angaren boko da islamiya, ga kuma natsuwa, gashi da kyau sosai, da ka ganshi gaka Asalin bafula tani, hakan yasa yayi farin jini sosai a makarantansu. Aryan yana da shekara takwas Aisha wanda Aryan yake kiranta da Umma ta haifo 'Yarta kyakkyawa khajida, tun tana k'arama Aryan yake matukar son k'anwarsa duk abinda ya samu tofa na Khadija ce daya sanya mata suna Deeja. Arya ya kammala secondary school Khadija na primary 5, mahaifinsa ya nima masa makaranta a kadpoly Kaduna ya tafi ya fara karatun computer science, cikin ikon Allah da mai da hankali ya kammala, shekarunsa uku a makaranta ya dawo da cirtificate d'insa na diploma, ya koma Abuja lokacin Deeja ta shiga jss3 a secondary. Wata rana Aliyu ya wayi gari da matsanancin ciwon ciki Abu kamar wasa, zuwa yamma yace ga garinku, wannan family sun shiga tashin hankali sosai da rashin Mahaifinsu, karma ace maka Aryan da yayi mugun sabo da mahaifinsa, mutanan Gombe suka zo saida akayi arba'in sannan Inna ta tafi, sun so su Umma su tattara su koma Gombe amma Alhaji Sani yace su barsu anan, yana so Aryan ya cigaba da aikin Mahaifinsa, haka suka amince badan ransu yaso ba. Aryan ya fara zuwa aiki a company Alhaji Sani, tunda ya fara zuwa ya fara samun matsaloli, wasu daga wurin aikin suka sanya masa ido saboda sunga yanda Alhaji sani ke nan-nan dashi. Daga karshe suka yi masa sharri bayan shekaransa guda da fara aiki Alhaji Sani ya koreshi. Aryan yayi kuka sosai rayuwa tayi musu k'unci abinda za suci wuya yake musu cikin k'ank'anin lokaci duk suka rame suka lalace, Khadija ta daina zuwa makaranta domin ba kud'in school fees, Allah yasa ba haya suke ba domin da gidan su kawai suka tsira. Dole yasa Aryan ya fara bige-bige, Umma kuma ta soma wankau a gida da haka ne suke samun abincin da zasuci, Aryan yayi yawon niman aiki Amma bai samu ba, wani wurin inya je sai suce mai Digree suke nima, ba suda kud'in da zai koma karatu dole yasa ya soma dako a kasuwa. Allah ya taimakeshi ya samu baro yana amfani dashi wajen dakon. Da wannan kud'in baron ne ya samu ya kafa runfa a cikin kasuwa yana biyan kud'in hayan wurin, ya fara saida kayan miya, abu kamar wasa sai sana'ar ya amshe shi, da haka Deeja ta koma makaranta ya cigaba da biya mata school fees, Umma kuma ta daina wankau saboda sanyi ya fara mata illa, sai ta samu jari ta fara dafawa Deeja kwai tana saidawa, in ta dawo makarantan boko saita fita tallan kwai, da yake duk sunyi saukar Al'Qur'ani, boko kawai take zuwa. A daddafe Khadija ta kammala secondary school, tunda ta gama Aryan yaso nima mata school of health ta cigaba amma ba kud'i, burin Khadija ta zama babban likitan mata amma ba hali. Samari sosai take da su amma Yaya Aryan ya hanata hira, saida Umma ta sanya baki ya fara barinta tana fitan ma wani malaminsu na ialamiyan da ta gama mai suna Musa. Soyayya sosai suke yi, sun fara zancen Aure Iyayen Musa suka hana shi aurenta saboda akwai yarinyar da suka zab'an masa, wannan dalilin ne ya kawo k'arshen soyayyan Dija da Musa. Tun daga nan Dija ta tsani soyayya burinta yanzu bai wuce ta samu ta cigaba da karatu. Aryan yazame mata uba duk abinda 'ya budurwa take buk'ata Aryan ya tsare mata shi, ta maida hankali sosai wajen tallan kwai. Aryan runfansa ya rufta tun daga wannan ranar komai ya dagule masa cinikinsa yaja baya, wata biyu kenan da rushewan rumfansa. Ana cikin hakane mak'ocinsu Malam Lawal yaje ya kafa tashi rumfan kusa dana Aryan da hakane Malam Lawal ya kwashewa Aryan customers, ya zamana Aryan saiya fita kasuwa ya dawo gida baiyi cinikin kirki ba. Aryan saurayi ne matashi mai cikar kamala, yanada tsayi amma dai-dai misali, yanada kauri, kuma fatarsa mai haske ne, yanada dogon hanci da dara-daran ido, bakinsa dai-dai da fuskansa, Namiji ne mai cike da kwarjini ga faffad'an k'irji, suman kansa luf-luf yake tamkar d'an India, in ya d'auki lokaci baiyi aski ba gashinta yana taruwa wanda zai iya kamawa da ribom, gashi da santsi sosai. Hakane kesa kullun Kansa da Hula baya son sumansa na fitowa, ba kowa yasan sumarsa haka yake ba saboda baya fita ba hula, sai dai in yaje masallaci wurin yin Alwala sai mutane su gani. 'yan Matan unguwansu Aryan sun rud'e sosai akansa, suna haukan sonsa, shi kuma bai san ma suna yi ba. Shekarunsa Talatin (30yrs) a duniya har yanzu baida budurwa, baima kallon mata balle ma su birgeshi, shiyasa ranar da sukayi ido hud'u da Basma gabansa ya fad'i domin shi Sam baya kallon mata, amma fuskan Basma ya kasa b'ace masa a ido saboda wulak'ancin da tayi masa. A yanzu kullun burinsa bai wuce ya samu kud'i ya farantawa Ummansa rai da k'anwarsa abin sonsa. *Cigaban Labari...* Malam lawal ne ya kwad'a ma Aryan sallama, firgigit ya farka daga dogon tunanin da ya shiga, cikin sark'ewan murya yace "Naam Malam Lawal ashe harka iso" cikin dariya Malam Lawal yace "tun d'azu nazo, nayi maka magana naga gaba d'aya hankalinka ya yi nisa ince dai lafiya?" murmushi yayi yace "lafiya lau Malam Lawal, ya kwanan iyalin?" "Lafiya lau, d'azun nan naga Deeja zata aiken Ummanku, sai na tambayeta ko ka wuce? sai tace aika fita da wuri" "eh wallahi na fito da wuri, da yake na biya wajen saro kayan miya" "Ok, Allah ya bamu sa'a da kasuwa mai Albarka" "Ameen Malam Lawal". Nan suka cigaba da tattaunawa akan maganar kasuwan. B'angaren su Queen Basma sai goma na safe suka farka, ko wacce ta fito cikin shigan mu ta Hausawa, Leema ta sanya leshi riga da zani rafa, Meena ta sanya shadda doguwar Riga, Basma kuma ta sanya atamfa super, d'inkin Riga da siket, ba k'aramin kyau sukayi ba, ko wacce da gyale a kanta, hakan da suka yi sai suka bani mamaki, gaba d'aya kamar ba sune jiya suka yi shigan dogayen riga sai kace ba 'ya'yan Musulmai ba, suka tafi zuwa club. Queen ce tace "Ni zan tafi gida domin a yanzu haka ana jirana domin yin breakfast, in kuma za kuje tom sai mu tafi tare" Leema ta yatsine fuska tace "Ni bazani ba saboda Momynki akwai takura gwara-gwara Ammi, dan haka hotel d'in da muka sauka ni da Meena zan wuce" Meena tace "kai Leema kiyi hak'uri muje kawai kinga fa sunsan muna garin nan bai kamata muje wani guri ba tunda duk Family ne mu ba bare ba" Queen ta yi hanyar fita tace "ban takurawa kowa ba, in kun so ku fito mu tafi in kuma kun k'i ko wacce ta kama hanyar inda zata, yau dai ba mai kwana min a wannan gidan, nima gidan Ubana zani na kwana" tana gama fad'an haka tasa kai ta fice, tsaki Meena tayi tace "In kina tak'ama da mulki muma fa gidanta muka fito, kinga Leema mu wuce gidan President d'in inya so in munyi two days sai ki koma Kano ni kuma na wuce Kaduna, domin wallahi ina missing Family na" Murmushi Leema tayi tace "hmmm wallahi nima hankalina ya koma gida fa, yanzu fa iyayenmu sun d'auka yau ne zamu dawo daga Dubai da muka tafi, bacin yau satinmu d'aya da dawowa, muna biyewa Queen bayan ita iyayenta sun ga dawowarta a ranar, muko munyi k'arya sai yawo muke bamu nan bamu can" Dariya Meena ta kwashe dashi tace "kefa saboda Jalal kika tsaya anan" hararan wasa Leema tayi mata tace "Ke kuma saboda mashayarku kika tsaya, saboda kinsan in kika koma gida Yaya Jamal zai takura miki ba shiga ba fita" duka Meena ta kaiwa Leema saita goce ta fice da sauri tana dariya. Haka su dukansu suka d'unguma zuwa babban gidan Shugaban k'asa. *WACECE QUEEN BASMA?...* _*Rahma Ce*_ [8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *3.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *WACECE QUEEN BASMA?* 'Yace a wurin Alhaji Mukhtar Bukar Bulama, wanda yake shugabancin k'asarmu Nigeria a yanzu. Asalin Mahaifinsa d'an Maiduguri ne Kanuri, mahaifiyarsa kuma mai suna Asma'u 'yar Gombe ce Fulani, Alhaji Bukar Bulama babban d'an kasuwa ne, yana fita k'asashen waje sosai, ya jima baiyi aure ba saboda yanayin kasuwancinsa, Mahaifin Asma'u Alhaji Salis, abokinsa ne k'ud da k'ud wanda a sanadin kasuwanci abotansu ya had'u, ganin Ahaji Bukar Bulam baiyi aure ba yasa Alhaji Salis ya bama Alhaji Bukar auren 'yar tilo d'aya Asma'u. Suna zama a cikin garin Kaduna a Unguwar Rimi, Alhaji Bukar an sanshi sosai, Mutum ne mai tausayi da taimakon talakawa, yaransa biyu a duniya Mukhtar da Halimatus Sadiya, sun taso cikin gata da kulawa kuma Asma'u tayi k'ok'ari sosai wajen basu tarbiyya mai kyau. Mukhtar yana gama primary mahaifinsa ya turashi karatu k'asar Germany a can ya fara secondary school d'insa. Tafiya ya kama su Alhaji Bukar zuwa Gombe sanafin rasuwan mahaifiyar Asma'u, bayan sunje basu dawo ba har akayi Addu'an bakwai kana suka kamo hanyar Kaduna, basu fita daga Gombe ba akan hanyarsu suka bige wani yaro, cike da tashin hankali suka nufi Asibiti dashi, aka karb'esu emergency, an samu yaron ya farfad'o, amma baya iya magana sai zaro idonsa yake waje, Likita ya basu tabbacin yaron ya samu Matsala a kwakwalwansa, hankalin Alhaji Bukar yayi masifar tashi, sunyi iya bincike ganin an gano iyayan yaron amma shuru ba a gano ba, da haka ya d'auki yaron ya wuce dashi Kaduna da nufin in ya samawa yaron lafiya ya maidashi wurin Iyayensa. Alhaji Bukar suna dawowa da kwana biyu ya shirya zuwa kasar Germany da iyalensa domin duba lafiyan Yaron daya bige, wanda baya iya magana. Da isarsu da kwana biyu cikin ikon Allah Yaron ya soma magana, sunan shi kad'ai ya iya tunawa Ibrahim, amma banda haka bai tuna komai ba, Likitoci suka tabbatar musu da Yaron ya samu mancewar kwakwalwa (loosing Memory). Abin ya damu Hajiya Asma'u sosai hakan yasa Alhaji Bukar ya bar Ibrahim a wajen Mukhtar ya fara karatu shima, sai suka tarkato suka dawo Nigeria. *Bayan shekaru mai tsawo* Su Muktar sun dawo Nigeria wanda dukkansu sun gama karatunsu sun samu aiki, har zuwa lokacin Ibrahim bai dawo cikin kwakwalwansa ba. Sadiya kuma tana karatu a KASU, tun dawowar su Mukhtar Allah ya daurawa Sadiya son Ibrahim, Abu kamar wasa har mahaifiyarsu ta ganeta saita kwab'eta, abinda basu Sani ba shima ta wurin Ibrahim d'in ya kamu da son Sadiya, daga bisani ya bayyana mata zuciyanshi suka fara soyayya. An sanya bikin su Ibrahim da Sadiya ba b'ata lokaci, wanda Alhaji Bukar yace ta cigaba da karatunta a d'akin mijinta, Mukhtar shima yana soyayya da k'anwar Sarkin kano mai suna Fatima, soyayya tayi k'arfi wanda hakan yasa aka had'a bikin su duka a kayi. Anyi biki sosai na manyan Attajirai, ko wacce ta tare a sabon gidanta da Alhaji Bukar ya siya musu a unguwar sunusi. Wata rana Alhaji Bukar ya shirya tafiya k'asar Dubai shida Mahaifin Asma'u, domin kula da kasuwancinsu dake can, a hanyar dawowarsu jirginsu yayi hatsari suka rasu. tashin hankali ba'a sanya masa rana, wannan Family sun shiga cikin damuwa da k'unci na rashin jigonsu, Hajiya Asma'u ta zama ba Uwa ba Uba ba Miji sai sauran danginta da yaranta. Hakan ya girgizata wanda haka yasa ta samu ciwon hawan jini. Su kuma su Mukhtar sun rasa Bango abin jingina watarsu. Ibrahim yayi kuka matuk'a domin da bazar Alhaji Bukar yake taka rawa, har yau baisan shi waye ba ko danginsa, yasan dai su Hajiya Asma'u basune iyayensa ba, ya kasa tuna komai na danginsa. Bayan Addu'an Arba'in duk dangi suka watse, an rab'e musu gadonsu, Muktar ya had'a duka dana k'anwarsa Sadiya dana Ummansu ya cigaba da kasuwanci dasu sannan yana aikinsa. Shi kuma Ibrahim sun bashi wani kaso mai tsoka daga dukiyar nasu kamar yanda mahaifinsu ya rubuta a cikin dairy d'insa, Ibrahim ya amsa yana godiya harda kukansa, daga nan shima ya cigaba da business. Hajiya Fatima matar Muktar ta haifi d'a Namiji mai suna Ahmad, bayan shekara guda ta kuma samun ciki, bata so ba amma dole ta hak'ura saboda Alhaji Mukhtar yana son abinsa, haka ya d'auki Ahamd ya bama Ummansu ta cigaba da rik'onsa. Bayan wata tara ta kuma haifo d'anta Namiji mai suna Abubakar suna kiransa da Naufal. Sati biyu da haihuwarta Allah ya azurta Alhaji Ibrahim samun k'aruwa da d'a Namiji wanda suke sanya masa suna Jamal. Sun raini 'ya'yansu cikin Kauna da soyayya, sun basu tarbiya sosai domin kud'insu bai hanasu tsayawa bisa tarbiyyan yaransu ba. *Bayan shekara biyu* Hajiya Fatima ta kuma haifo 'ya mace suka sanya mata Asma'u suna kiranta da Husnah. Ta b'angaren Hajiya Sadiya ita bata k'ara haihuwa ba tana rik'e da d'anta Jamal. Alhaji Mukhtar ya rik'e mukamin Commissioner har kujera uku, soyayyar da ya samu wurin Mutane yasa ya fito takaran gomna, cikin ikwan Allah ya samu. Ta b'angaren Ibrahim shima yana ta samun mukamai a wurin aikinsa dukiyarsu sai hab'aka take ta ko ina. Alhaji Mukhtar ya k'ara aure da 'yar wani hamshak'in mai kud'i a garin Kano 'yar Alhaji Buba mai Naira itace 'yarsa tilo guda d'aya mai suna Maryam, anyi Biki sosai na manyan Mutane, Alhaji Mukhtar ya tare da ita a gidansa na Gomnati, gida d'aya ya had'asu da Hajiya Fatima, suna zaune zaman lafiya ba tashin hankali. *Bayan shekara Hudu* yana kujeran Gomna, Hajiya Maryam ta Haifi 'yarta mace k'atuwa ga kyau, suka sanya mata suna Basma, Basma ta taso cikin gata da soyayyan iyayenta, Yaya Ahmad yana sonta sosai tun tana k'arama suka shak'u sosai, bata shiri da Yaya Naufal, Anty Husnah kuwa duk inda zata suna tare, tun tana k'arama ta koma hannun Hajiya Fatima, Nono kawai ke kaita gun Momynta. Itama Hajiya Sadiya ta k'ara haihuwar 'ya mace aka sanya mata Ameena suna kiranta da Meena, tserayen wata biyu ne tsakanin haihuwar Basma da Meena. Yaya Ahmad da Yaya Naufal kusan tare suka wuce k'asar Malesia karatu, Yaya Ahmad yana karanta Medicine Yaya Naufal yana karana Biochemistry. A lokacin Anty Husnah tana secondary school. Basma kuma tana primary. Hajiya Fatima wanda suke kira da Ammi ta gama sangartata duk wani rashin ji ta sani, ga tsokanar fad'a a makaranta, duk wani kiriniya tare suke yi da Meena da yake makarantar su d'aya. A daffafe suka kare primary saboda irin kai k'aransu da iyayen yara keyi, kasantuwar iyayensu manya ne shiyasa ba'a koresu ba. Hajiya Maryam ta k'ara haihuwar yara Maza 'yan biyu Anwar da Na'im, anyi shagali sosai da haihuwarsu, su Basma kuwa murna har kunne. So tari Hajiyar Maryam wanda suke kira da Momy bata ragawa Basma tayita mata fad'a hakan yasa Basma bata son kwana a b'angarenta sai wurin Ammi saboda Ammi na kula da ita bata son b'acin ranta. An d'aurawa Anty Husnah aure da Jabir d'an senator, sun had'u a makarantar Abu Zaria inda ta fara karatu, an d'aura auren tana cigaba da zuwa makaranta. A wannan shagalin bikin ne akayi taron da ba'a tab'a yiba, mutanan Gombe, Maiduguri, kano duk sun hallara, matar Sarkin Kano yayan Ammi, Hajiya Murja tazo bikin wanda ta taho da 'yarta mace sa'ar su Husnah mai suna Haleema suna ce mata Leema, tun daga nan su Basma aka samu kawa, da zasu tafi Leema ta kafe saita zauna wurin Ammi, haka mahaifiyarta ta barta mai martaba Sarki Abdallah ya amince Leema ta zauna wurin Ammi domin yasan gidan Gomna Muktar Bukar Bulama akwai tarbiyya. Abdullahi shine ya gaji sarautar gidansu bayan rasuwan Babansu, Yayane ga Hajiya Fatima, uwa d'aya uba d'aya suke, yana da mata biyu Hajiya Sa'a itace Uwar gida tana da yara biyu duk Maza Adam shine babba sai Shureym shine k'arami, sai Amaryansa Murja yarta guda d'aya ce itace Leema, sun d'aura son duniya sun azawa Leema kowa na dangi yana sonta, tun tana k'arama ta taso cikin sarauta, gimbiya Leema 'ya ga Sarki Abdallah. Hajiya Sa'a Mace ce yar k'arya da son duniya ta shigewa Hajiya Maryam Momyn Basma, amma Momy tak'i sake mata saboda halayyarsu bai zo d'aya ba, Hajiya Sa'a basa shiri Sam da Ammi wato k'anuwar mijinta, hakan yasa Momy tak'i sake jiki da ita. Hajiya Sa'a ta sangarta Shureym da gata, ta d'aura son duniya ta bashi saboda tana ganin shine zai gaji kujaran Babansu, shiyasa tun yana k'arami take kiranshi da Prince Shureym, hakan yana masa dad'i sosai. Adam shi kuma Mutum ne salihi ba yida hayaniya hakan yasa nasu yazo d'aya da Hajiya Murja, a wurinta yake komai. Shureym yana America yana karatun Engineering, shiko Adam Madina ya tafi karatunsa bangaren Islamic studies. Basma, Meena, Leema duk makarantar d'aya suke secondary, a part d'in Ammi suka tare domin Ammi ita bata kwab'a musu, Meena ta kwaso kayanta ta dawo gidansu Basma gaba d'aya. Alhaji Ibrahim Baban Meena ya samu cigaba sosai, wanda yaita samun K'arin girma a wurin aikinsa, ya tura Yaya Jamal karatu inda su Yaya Ahmad suke k'asar Malesia yana karanta Business admin. Gomna Muktar Bukar Bulama ya sauka a kan kujeran Gomna bayan shekara takwas daya shafe akai, ya k'ara samun kurajeran Sanator wanda ya wuce Abuja, sai weekend yake dawowa gida Kaduna. Dukiyarsu na gado sai hab'aka yake yi. Su Yaya Ahmad sun gama karatunsu gaba d'aya duk sun dawo, Yaya Ahmad ya fara aiki a babban Asibiti dake garin Abuja, Yaya Naufal kuma ya karb'i kasuwancin Abbansu ya cigaba da juyawa. Yaya Jamal ma dukiyar Dadynsa ya cigaba da rik'ewa. Ta b'angaren Mutanan Kano kuwa Yarima Adam ya dawo ya fara lecturing a BUK, shi kuma Shureym bai riga ya kammala masters d'inshi ba. Su Basma an zama 'yan Mata sun gama Secondary School yanzu suna England suna karatu. Basma na karanta Micro Biological, Leema tana karanta Pharmacy, Meena kuma tana karanta Low. Tunda suka koma England rayuwarsu ta k'ara sauyawa, sun had'u da 'ya'yan turawa da kuma 'yan k'asashe daban-daban, Basma tunda ta soma karatu saita natsu ta zama mara son magana, amma fa akwai tsiwa in aka tab'ota, Meena kuma akwai shegen surutu, Leema kuma akwai ji dakai da kuma k'asaita na Sarauta. Sunyi farin jini sosai saboda suna da k'ok'ari sosai. Meena ta had'u da wata yar ajinsu ta koya mata zuwa club, abu kamar wasa Meena in bata je club ba bata jin dad'i, tun su Leema na mata k'orafin ta daina zuwa har taja ra'ayin Leema ta fara zuwa. Abu na farko da suka koya shine Meena ta shiga group d'in 'yan shaye-shaye, tun bata iya ba harta kware sosai wajen zukar sigari da shan kwayoyi. Leema kuma Mace ce mai yawan sha'awa, in Meena ta jata cikin group d'insu saita kasa sakewa a haka harta had'u da Jalal suka fara soyayya tun bata sakewa harta sake dashi, Jalal ya fara fita da ita yawo kullun sai sun fita. A hankali yayi ta jan ra'ayinta gareshi, tun tanak'in amince masa harta bashi kai bori ya hau. Tun daga nan suka d'inke da Jalal, ya mai da ta tamkar Matarsa shine mutum na farko da yasa fara sanin ta a 'ya mace. A hankali Leema ta raba shi da duk 'yan matanshi, Basma kullun cikin musu nasiha take akan sun gurb'ata tarbiyyan da iyayensu suka yi musu dasu gyara halinsu. Meena tayi murmushi tace "ke bazaki gane ba, meye amfanin zuwanmu k'asar waje bamu waye ba, ai wannan itace wayewar, kinga ni shaye-shaye kawai nakeyi ita kuwa Leema da Jalal take harka, kinga ta samu abinda zuciyarta take so". Basma tayi tsaki tace "Allah ya kyauta" Murmushi Leema tayi tace "ki shirya yau muje club dake Allah za kiji dad'in wurin sosai" Basma tace "Kun dameni da zancen club d'in nan, yau dai zani inga abinda akeyi a gun shikenan kunyi farin ciki ko?" cikin farin ciki suka ce "wow munyi Murna kema zaki shigo sabon rayuwa ki huta da rayuwan duhun kai" Sunje club gaba d'ayansu, yanda Basma taga wurin sai ya sanyata farin ciki musamman data ga 'yan rawa sai hakan ya kwanta mata arai, dan a duniya Basma tana son rawa, kawai sai ta mik'e ta nufi wurin rawan ta hau, cike da mamakin mutane suka bita da kallo, ji tayi k'afarta ya k'asa d'aukarta, dan gani tayi ido ya mata yawa bazata iya ba, su Meena ne suka fara kiranta "common Besty ki fara" nan kowa ya fara ihu suna mata kirari dan ta fara, nan kanta yayi chargy taji wani k'arfi da dakewa saita fara rawa cikin salo naban namaki, sai wurin ya kaure da ihu, dan tayi matuk'ar burgesu, ba wanda yayi tsammanin ta iya rawa haka, hatta su Leema sunsha mamaki. Nan aka fara mata yayyafin kud'i kan basma ya k'ara kato saida tayi sosai kana ta sauko, koda ta samu guri ta zauna sai mai wurin ya kawo mata kud'in data samu bud'en bakinta tace ya barshi. Murna sosai yayi ya mata godiya. Tun daga wannan rana Basma ta fara zuwa club burinta bai wuce taje tayi rawa a yi mata kuwwa a fasa mata kai. Musamman ta shiga makarantar koyan rawa babu irin wanda ba a koya mata ba hatta na larabawa. *_Rahma Ce_* [8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *4.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 An shirya gagarumin gasa na rawa a k'asar England, Basma na d'aya daga cikin masu fafatawa. In ta dawo daga school babu abinda take yi sai gwajin rawa, su Leema suke k'ara mata k'arfin gwiwa. Ranar taro, k'aton hol cike yake mak'il da mutane maza da mata, ko wanne yana mazauninsa, ga kuma masu tantance rawar daga gefe, zaune suke akan kujeru na alfarma, ga dogon table a gabansu an d'aura kayan motsa baki da kuma abin sha, masu fafata gasar su Hamsin ne, a ciki ake son a finda zakara guda d'aya wanda aka tanada mak'udan kud'i da key na mota sai kuma hular Queen na rawa ga wanda taci, sai na biyu dana uku kyautar kud'i. Gasar maza da mata ne, Ganin yawansu da Basma tayi sai zuciyarta ya tsinke ta karaya, gani take ba zata ci ba, jere suke akan layi wannan na bin wannan, sun sanya riga top mai dogon hannu sai kuma wando dogo pencil ya matse jikinsu, rigan ta kama su daga sama zuwa ciki, k'asan kuma ya bud'e, tsayinta ya kawo rabin cinya. Wasu sun sanya hula a kai wasu kuma sun baje gashin su a baya, shigar Basma tayi mata kyau, ta dunk'ule gashinta ta sanya hula, ba wani makeup a fuskanta amma tayi kyau sosai. Basma itace ta goma sha shida a cikin jerin layin. D'aya bayan d'aya suke fitowa suna gwada rawan su, alkalai suna dubawa tare da rubuta makin, 'yan kallo kuma suna ihu in rawar tayi musu kyau ga masu gwajin. A haka layi yazo kan Basma, cikin salo da kwarewa ta fara rawa mai ban sha'awa, a hankali take komai cikin nutsuwa, lauye duk sassan jikinta take yi tamkar roba, ta d'auki tsayin minti ashirin tana rawa, nan fa hol ya kaure da ihu da alama rawarta ya birge su. Alkalai suka dakatar da ita suka ce ta tafi, na gaba yazo ya nuna nashi. Da haka har aka gama tantance rawar su Hamsin. Daga cikin alkalai wani ya mik'e yace cikin harshen turanci, zasu cire mutane goma daga cikin su, domin fafatawa na k'arshe, washe gari zasu yi rawa a cikinsu za'a tantance Mutum na farko dana biyu har zuwa na uku da sauran numbers. Nan fa hol yayi tsit ana son aji su waye zasu shiga gasa ta k'arshe. An fara kiran Mutum na farko da haka har aka je kan Mutum na tara, Basma bata ji sunanta ba sai ta sadak'ar da ta rasa gasar, wanda basuji sunan su ba sai kuka wasu kuma damuwa ya bayyana a fuskokinsu, Basma bata an k'araba taji an kira sunanta Basima MB a ta goma, da yake da haka tayi regista da sunan ta basima MB, saboda basaja, kuma ita ba 'yar k'asan ba ce. Ai hol saiya kaure da ihun su Leema da Meena sauran Mutane ma suka tayasu ihun. Da haka aka tashi taro Maza hud'u mata shida sune zasu fafata a washe gari. *Washe gari* Hol ya cika mak'il da Mutane fiye dana jiya ma, nan kowa ya samu guri ya zauna, yau shigan dasu Basma sukayi kusan irin na jiya ne sai dai an sauya launin kalan kayan da suka sanya jiya. Alk'alai suka baza ido, na farko ya fito ya fara fafatawa, har aka kai na biyar, daga nan sai aka tafi hutun tak'aitaccen lokaci. Bayan an dawo aka d'aura har zuwa na k"arshe ta fito wato Basma, nan ta soma kafa tarihi domin rawar ta na yau yasha ban-ban dana jiya, Basma ta dage iya iyawanta, sai baza rawa take tamkar ba ita ba, inba ka mata kallon caf ba bazaka shaida Basma ce ba, domin tayi shiga na b'adda kama. Saida tayi rawa sosai sannan aka dakatar da ita, alk'alai sun fita a hol sunje had'a marking, sai da suka b'ata kimanin rabin awa kana suka dawo kan high table suka zauna, sun fara fad'an sakamako daga na goma ne, har suka zo kan na shida ya rage saura mutum Hud'u, Basma na ciki, a haka har suka fad'i na Hud'u dana uku, saura Basma dawata 'yar k'asar England d'in, sai aka tafi hutun rabin sa'a, nan fa kawayen su Basma suka rufe ta da Murna Addu'a suke Allah yasa itace mai nasara. Burin Basma ko na biyu tazo zatayi farin ciki tunda ta kafa Tarihi a fagen rawa. Koda aka dawo daga hutun takaitaccen lokaci, hol d'in yayi shuru ana jiran aji wacce tayi winning, mai fad'an sakamako saida yayi shurun minti biyar kafin ya furta first position Basima MB kece ki kai nasara, d'ayan kuma ta zama na biyu, hol d'in ya kaure da kuwwa, nan take aka d'aurawa Basma Hular Queen, wannan dalilin ne yasa Basma take amsa sunan Queen Basma. Sunyi hotuna kala-kala hatta gidan TV na k'asar sun nuna gasar a TV. Taro ya watse, su Meena cike da farin ciki suke, kana ganinsu kasan yau suna cikin murna, har gidan da suke zama aka kaiwa Basma motarta da kuma kud'in data samu. Tun daga wannan lokacin su Leema fankama da d'aga kai ya k'aru, Basma kuwa sunan ta sai da ya shiga cikin k'asar England sosai, kowa na sonta har wani respect d'inta ake. Ana saura shekara d'aya su gama karatunsu su dawo k'asarmu, Mahaifin Basma ya fito takaran shugaban k'asan Nigeria, Mahaifin Meena ma ya fito takaran Gomnan jahar Kaduna. Abu kamar wasa da lokacin zab'e yazo duk suka ci zab'en. Mahaifin Basma President Mukhtar Bukar Bulama sai kuma Gomna Ibrahim Abubakar, yana amsa sunan Alhaji Bukar wanda ya rik'eshi. Farin ciki wurinsu Basma ba a magana musamman suka dawo Nigeria akayi bikin rantsar da iyayensu, tun daga wannan lokacin sai suka chanza salo suka k'ara sauya rayuwansu ga mutane, suka keb'e kansu, musammam aka samu ascot suka bi su Basma England suna basu kariya, feeling da d'agawa ya k'aru a wajensu Leema. Su Basma sun kammala karatunsu sun dawo gida, ta matsawa president saiya gina mata gidan huta a Abuja, haka ya sanya aka mata k'erarren gini aka zuba kayan da ta buk'ata, koda suka dawo Abuja suka sauka, domin yanzu Alhaji Mukhtar yadawo Abuja da iyalensa suna gidan shugaban k'asa, su Meena da Leema suma nan suka sauka, sun k'i komawa gidansu saida suka shafe wata guda kan suka wuce gidajen iyayensu. Akwai wani lokaci da Basma ta tafi kano hutu, tunda Hajiya Sa'a ta ganta saita k'udurta wa ranta Prince Shureym ya samu mata, tayi alkhawari yana dawowa zata turashi yaje gun Basma su dai-daita koda baya sonta, burinta Shureym sai 'yar babban mutum zai aura. Saboda wannan k'udirin nata ne yasa ta k'ara shigewa Momy mahaifyar Basma, dole yasa ta shirya da Ammi, domin tasan tabbas sai tabi ta wajenta tunda Basma a hannunta take, Hajiya Sa'a bini-bini tana Abuja, kasan tuwar su Ammi basu san nufinta ba sai suka sake mata suka saba sosai, zumunci ya k'ara kulluwa mai k'arfi. Duk wannan abinda Hajiya Sa'a takeyi Shureym bai sani ba yana can America, shi a can ya had'u da wata 'yar Yola mai suna Safeena, soyayya sukeyi sosai, sunyi wa juna, Alkwari aure in sun dawo k'asarmu. Hajiya Sa'a tayi k'ok'arin had'a Basma da Shureym a waya suna gaisawa, da kyar ta shawo kan shureym bayan tayi masa bayani akan Basma, ya amince amma da sharad'in zata barshi ya auri Safeena, haka ta amince masa, ita dai burinta Shureym ya auri *'Yar Shugaba* a matsayinsa na D'an Sarki. Da dubara Hajiya Sa'a ta soma tusa maganar a wajen iyayen Basma, kuma su a zuciyarsu hakan yayi musu dad'i sosai. Basma kuma suka fara soyayya da Shureym kamar gaske. Leema kuma ta kamu da son Yaya Jamal amma shi ko kad'an baya sonta baya ma shiga hanyarta, Duk da haka bata daina harka da Jalal ba. Meena kuwa soyayya take da Yaya Naufal kamar zasu cinye juna. Su Basma koda suka dawo Abuja basu sauya rayuwar da suka fara ba a England, da zarar sun tafi gidan Hutu tofa bazasu dawo gida ba sai sunje wani babban club dake cikin garin Abuja, sunyi abinda ran su ke so, sannan su koma gidan Hutu su kwana ba tare da kowa ya san rayuwar da suke ai katawa ba. *Hmmm adai jure zuwa rafi...* Bayan sun dawo da shekara guda, Meena ta tafi Abuja, Leema ma ta bar kano ta tafi Abuja da nufin zasu Dubai siyayya. Duk suka had'u, suka shirya tsaf suka tafi Dubai, achan ma saida suka lalubo babban club can suka b'arje lokacin su, da zasu dawo su Meena da Leema basu gaya ma iyayensu zasu dawo ba, Queen ta kira aka zo a ka d'aukesu a airport, direct hotel suka je suka kama Leema da Meena domin so suke su wataya kan su koma gida, ita kuma Basma gida ta wuce sai ta cewa iyayenta su Meena suna gidan hutunta. A fitan da Basma tayi ta fita d'auko su Meena a hotel don suje gidan hutunta, bayan ta d'auko su ne a hanyar zuwa gidan Hutu ne suka had'u da Aryan har suka kusa bigeshi, Basma ta tofa masa miyau takuma sanya aka mareshi. *Cigaban labari...* Basma sun wuce gida gaba d'ayan su, bayan sun isa sai suka wuce part d'in Abbansu domin tasan breakfast d'insu yayi ready a can, suna shiga duka iyayan nasu suka bisu da kallon sha'awa a nutse suka k'arasa suka kwashi gaisuwa, President dake zaune a dining ya kalle su yace yarana kun girma fa sai aure tunda kun gama karatu, dariya duk suka yi, Basma a tsagwabe tace "Ni Abba ba yanzu zanyi Aure ba sai na kai 25yrs tukunna lokacin na kara wayo" duka mutanen falon suka sanya dariya amma banga Momy da take doka mata harara, koda suka had'a ido da juna sai tayi saurin kauda kai, dan tasan laifin da tayi. Nan suka zauna suka karya duka, bayan sun gama ne Abba yace "Basma ki sameni a falon sama" Cikin farin ciki tace "to" kana ta mik'e tabi yansa, Ammi ma bayansu ta bi, Momy kuma ta kalli su Meena tace "wai ku yaushe za kuyi hankali ne, kun dawo amma kunk'i zuwa ku kwana anan ko? sannan nayi waya da Hajiya Sa'a tace ai ke Leema baki samar musu kin dawo ba, ke kuma Meena Maminki ma bata san kin dawo ba, to wallahi ranku duk sai ya b'aci, inna sanya k'afar wando d'aya daku, ku tashi kuje sashi na ku jirani gani nan zuwa, in ba haka ba saina ci muntuncin ku" Sum-sum suka mik'e suka tafi part d'inta, su Na'im da Anwar suka mik'e suka ce "Momy mun tafi Makarantan hadda" Da murmushi a fuskanta tace "To sai kun dawo ku mai dankali sosai banda wasa" suka ce "to" sannan suka wuce. Momy ta danna k'araurawar kicin, da gudu ma'aikatan kicin d'in suka fito tare da risinawa, umarni tayi musu dasu kwashe kayan abincin su gyara wurin, cikin sauri suka mik'e dan cika umarninta. Momy ta mik'e tayi wurinsu Basma. Ta same su Ammi zaune suna jiran fitowar Abba, koda ya fito sai ya samu guri ya zauna yace "Basma nayi waya da Mai Martaba ya sanar dani dawowar Shureym gobe insha Allah, dan haka sai ki tsumayi zuwansa domin a nan zai fara sauka in yayi mana kwana biyu zai wuce Kano" sunkuyar da kai tayi k'asa tace cikin ladabi "To Abba" Ammi tace "sai ki d'auki su Meena a mota kuje kuyi siyayya dan had'a masa kayan tarba" Momy tayi tsaraf tace "su Meena yau d'in nan zan turasu su koma gida, domin duk iyayensu basu san sun dawo ba" ido bude Ammi tace "kaji min ja'iran yara, shiyasa suka k'i kwana anan, to Allah ya shirya mana su" duk suka amsa da "Amin" Abba ne ya ciro bandir d'in kud'i na 'yan dubu-dubu ya mik'awa Basma yace "Ga wannan kud'in ko kinada bukatar wani abu" cikin natsuwa tace "Abba akwai kud'i a account d'ina fa" "Eh nasan dasu wannan cash ne ai" Basma cikin farin ciki ta amsa tayi godiya, saita mik'e ta fito tabar iyayan nata anan ta nufi sashin Momy. Can ta samu su Meena sunyi jugum-jugum, kwashewa tayi da dariya tace "wow yau kun shiga hannu Momy mai fiddaku sai Allah" hararenta Leema tayi tace "ai duk ke kika ja mana, munce bazamu zo ma kika wani damemu, gashi yanzu ta tsaremu, dama ni ita nake ji, dan ta cika takurawa Mutane" ta k'arasa maganar dayin tsaki, kan basma ta basu amsa sai ga Momy ta shigo, zama tayi ta zuba musu ido tace "ku shirya yanzu nan driver zai kaiku airport, ke Leema ki wuce Kano a jirgin sama, Ke kuma Meena jirgin k'asa zaki bi ki sauka a Kaduna". Leema kamar zata yi kuka tace "Momy ki bari gobe in Allah ya kaimu sai mu tafi" Momy tace cikin fushi "rufemin baki yau d'in nan zaku tafi, maza ku tafi driver suna jiran ku" jiki na rawa suka mik'e suka fita saida suka biya gidan hutun Basma da kuma hotel d'in da suka sauka suka kwashi kayansu kana suka tafi Airport sai gida. Momy ta kai dubanta ga Basma tace "Wato ke Basma har yanzu ba kida hankali ko? bana hanaki kwana a wannan gidan hutun ba, shine kika kwana jiya baki sanar dani ba saboda Ammi ta d'aure miki kiyi yanda kika ga dama ko" cikin shagwab'a tace Momy "wallahi dare tayi ne shiyasa ban dawo ba" "dalla can yimin shuru, ni tunda kika tafi England kika dawo kedasu Leema kuka sauya hali, na rasa me kukeyi a wannan gidan" da sauri ta d'ago tace "babu abinda mukeyi fa, hutawa kawai muke sai wanka a swimming pool" "ok naji, yanzu dai na sanya abokan naki sun tafi, naga dalilin fitanki kullun, gobe in Allah ya kaimu zan aike ki gidan hajiya Aisha k'awata" cikin sauri ta katseta tace "Momy gobe ne fa Shureym zaizo kinga bai kamata na fita ba, ki aiki su Na'im mana pls" hararanta tayi tace "bazan aike su ba, ke nake so ki tafi, tashi ki bani wuri" cikin shagwab'a Basma ta mik'e tare da buka k'afafunta ta fita a sashin Momy harda kwalla, ta nufi part d'in Ammi. Momy ta girgiza kai tace "ohh ni Maryamu ka haifi d'a amma Baka haifi halinka ba, Allah ka shirya min Basma" tana gama fad'an haka sai ta mik'e ta shiga d'akinta. *Muje zuwa...* _*Rahma Ce*_ [8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *5.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *washe gari* Basma ta tafi aiken Momy da misalin ƙarfe sha biyu na rana, gidan hajiya Aisha ta tafi ta kaimata saƙon Momy. A hanyarta na dawowa ne saita wuce gidan hutu ta ɗauko wasu kayanta kana ta kama hanyar gida, escot na biye da ita a baya, ta hau kan babban hanya bata ankara ba ta bige wata Yarinya, cike da tashin hankali ta koma bakin hanya tayi parking, bodyguard suka fito a motansu suka nufa wacce ta bige, saboda tsoro Basma ta kasa fitowa, sun ganta kwance cikin jini a sume, cikin sauri ɗaya daga cikin ascot ɗin ya isa gun basma yace "Hajiya Yarinya ta suma fa" cikin sarƙewan murya tace "ku sata a motanku a seat na baya, sai kuzo ku biyu ku shiga tawa motan tunda ku huɗu ne" cikin sauri ya amsa "yes Madam" ya tafi tare da cika umarnin data basu. General hospital direct suka wuce, aka wuce da ita emergency room, cikin sauri Basma ta ɗauki wayarta ta kira Yaya Ahmad ta shaida masa suna cikin asibity ta bige wata yazo da sauri, baifi minti biyar da kiranshi ba saiga shi yazo yace "ina take?" cikin damuwa tace "tana emergency room" bata kaiga ƙarasawa ba ya wuce ciki. Zarya ta shiga yi hankali ta a tashe ganin ma ashe ba ƙaramar Yarinya ta bige ba budurwa ce, an ɗauki kusan minti talatin kafin duka likitocin suka fito, da sauri Basma ta tari Yaya Ahmad tace "Yaya ta farfaɗo kuwa?" ciki da tausayawa ƙanwar tashi ganin yanda ta burkice yace "ta farfaɗo yanzu dai ta samu barci kuma anyi mata dressing inda taji ciwo, nan da awa guda zata farka insha Allah". Da ƙarfi Basma tayi ajiyan zuciya tace "Alhamdulillah" sai Yaya ya jefo mata tambaya yace "in kika je ne har kika bigeta?" gefe ta koma ta samu wuri ta zauna, shima binta yayi ya zauna, nan ta bashi labarin yanda ya faru. Ya girgaza kai yace "Allah ya kyauta gaba, amma meyasa kikayi driving da kanki" murmushi tayi tace "Yaya Ahmad wlh kawai hakanan naji ina sha'awar tuka kaina" Dariya yayi yace "hmm su Basma rikici, kije gida kawai saiki turo Shugaban mai kula da sashin Ammi Baba kulu tazo ta zauna da ita, tunda ke yau nasan kinada baƙo ya kusa sauka ma", murmushi tayi tace "tom Yaya Ahmad bari naje anjima zan dawo insha Allah" "ok sai kin dawo, ki kula da kankifa" "insha Allah Yaya zan kula" suka rabu cikin farin ciki. Tana isa gida taje ta samu Baba Kulu ta sanar da ita saƙon Yaya Ahmad, driver zai kaita, cikin sauri Baba kulu ta tafi. Basma tasa masu aikin Kicin na ɓangaran Ammi ta sanar musu abincin da za suyi mata na tarban baƙonta. Sai ta nufi sashin Momy ta samesu zaune da Ammi suna magana ta gaishesu kana tace "Momy na kai mata saƙon tace za kuyi waya" Momy tace "ok, amma naga kin daɗe ko kin biya gidan hutun naki da kika saba?" murmushi tayi tace "a'a Momy wallahi a kan hanyar dawowa na gida, na bige wata, yanzu haka tana asibity, na tura Baba Kulu ta zauna da ita zuwa anjima zan koma" cikin tashin hankali Ammi da Momy suka hada baki "subhanallah da fatan dai abin da sauki" murmushi tayi tace "da sauki kamar yanda Yaya Ahmad ya sanar dani shiyasa na taho ma" Ammi tace "to Allah ya bata lafiya ya kuma tsare na gaba" duk suka amsa da "Amin". Saita shiga ɗakinta dake sashin Momy. Tana Shiga ta faɗa makeken gadonta wayarta ta jawo ta duba taga miss call ɗin su Meena, kiranta tayi bugu buyu ta ɗauka, Meena bata jira Basma ta yi magana tace "wlh Basma ba kida kirki, jiya ko ki kiramu kiji ya muka sauka" cikin natsuwa tace "Afwan ya habibty, nima Momy saida tamin faɗa, haushin haka yasa ban kiraku ba" Nan dai suka shirya, Basma ta bata labarin accident ɗin da tayi, Meena ta mata Allah ya kyauta na gaba kana suka kashe wayar. Basma ta kuma kiran Leema itama mita tayi mata ƙorafi kamar yanda Meena tayi nan ta bata haƙuri suka yi hira kana suka yi sallama. Bayan sallan asri Basma tayi wani wanka ta sanya baƙar jallabiya mai ɗauke da kwalliya pink color, tayi rolin da gyalen abayan, saita fito, abinci ta ɗauka a baske kamar yanda Momy tasa aka dafawa mara lafiyan, saita shiga mota driver ya jata zuwa asibity. Ta nufi ɗakin da aka sauyawa mara lafiyan, ta shiga ta sameta zaune jingine da pillow, idonta a lumshe da alama tana hutawa ne, Baba Kulu ta amshi kwandon abincin tace "sannu Basma" cikin fara'a Basma ta ce "yauwa Baba Kulu, ya mai jiki, "da sauki, ta farka tun ɗazu amma fa kuka take tayi min, wai ita zata tafi, da kyar na lallashe" cikin kulawa Basma ta kai dubanta ga mara lafiyan, wuri ta samu gefen gadon ta zauba ta kama hannun mara lafiyan tace cikin sanyin murya "baiwar Allah ya jikin da fatan dai babu wata damuwa" idonta cike da hawaye tace "lafiya lau ni naji sauƙi, ni dai ku taimaka ku kaini gida, wlh nasan hankalin Umma na da Yaya a tashe yake in basu ganni ba" cikin nutsuwa Basma ta kuma cewa "kiyi hakuri, ya sunanki?" cikin damuwa tace "Khadija" girgiza kai tayi a laman gamsuwa tace "kiyi haƙuri kici abinci zan kira likita yazo ya bamu sallama saina kaiki gida" cike da fara'a tace "nagode Hajiya" Basma tayi murmushi tace "sunana Basma ba Hajiya ba" itama Khadija murmushi tayi kawai batace komai ba. Baba Kulu ta sanya mata tuwon semo miyar agushi, ga wani plet ɗin ta sanya mata farfesun kayan ciki ta kuma zuba mata drink na 5alive a cup, a kan gadon ta jera mata, cikin kulawa Deeja tace "nagode Baba" dama da ɗan yunwanta ta fito zuwa wurin saro kwai, bata kaiga siyo bane Basma ta bigeta, saita buɗe ciki ta kwashi girki Basma sai kallonta take yi, a zuciyarta tana yaba kyawun khadijan sai dai a irin shigan da taganta dashi ya tabbatar mata masu ƙaramin ƙarfi ne, hakanan taji Kadijan ta kwanta mata a rai saboda ta lura tanada sauƙin hali, bayan ta gama cin abincin suka kawo mata wurin wanke hannu ta wanke kana ta kalli Basma tace, "Hajiya au, kince sunanki Basma ko" ta gyada mata kai alaman eh, ta cigaba dacewa "ke nake jira ki kira likita in tafi gida, wlh Ummata zata damu da Yaya Aryan, murmushi Basma tayi mata ba tace komai ba a zuciyarta tana maimaita sunan Aryan, hakanan taji sunan tayi mata daɗi. Wayarta da ɗauka ta kira Yaya Ahmad bai ɓata lokaci ba yazo, yace "Basma ashe kin dawo?" "eh Yaya Ahmad na dawo, dama Patient ɗinka ce tace a sallameta zata gida" dubansa ya kai wurin Khadija yayi mata murmushi yace "haba dai kiyi haƙuri ki kwana gobe zaina sallamaki" Deeja ta zaro ido waje tace cikin tsoro wlh Ummata nake ji da Yaya Aryan, kuyi hakuri Ku sallameni" shima Yaya Ahmad cikin zolaya ya zaro ido yace "tafɗi, ni bazan sallameki ba sai gobe in Allah ya kaimu" ai sai Deeja ta fara fidda kwalla, Basma tace "Yaya kaga kuka take yifa, ka sallameta kawai sai a bata magunguna, in yaso ni da kaina zan dawo maka da ita sai ka kara dubata" cikin fara'a yace "Basma rabu da ita wasa nake mata, dolena na sallameta kafin ta nima hanyar guduwa" dukansu sai suka sa dariya amma banda Deeja da ta sunkuyar da kai ƙasa tana murmushi. Yaya Ahmad ya rubuta mata sallama yace "Basma zaki dawo da ita nan da kwana biyu" "OK Yaya insha Allah zan dawo da ita". Nan Yaya Ahmad ya kira driver ya kwashi kayan su yasa a mota, ya kalli Baba Kulu yace "Baba kuje gida ni zan kaisu Basma", cikin kulawa Baba Kulu tayi godiya kana ta tafi. Ya kai dubansa ga Basma yace "muje ko, da fatan ta sanar miki da inda take" "Ok, Yaya ba damuwa zan tambayeta a mota". Sai suka kama hanya, Yaya Ahmad ya shiga dasu shopping complex ya siya mata kayan ciye-ciye, kana suka ɗauki hanyan gidansu Deeja. Aɓangaren su Umma kuwa Yaya Aryan zaune yake a gidan yayi jugum, Umma ma tayi tagumi tace "wlh hankali ya tashi har yanzu ace bata dawo ba? ban taɓa aiken Deeja ta dad.ɗe haka ba, gashi kaje har wajen masu kwai bata ba labarinta, sunce ma bata jeba, Allah yasa ba sace min 'ya akaya ba" ta ƙarasa maganar tana matsar kwalla, Yaya Aryan cikin damuwa yace "Umma kiyi haƙuri insha Allah za'a ganta, bari na ƙara fita in duba ko Allah zaisa muji wanda yaganta" ya miƙe tare da cewa "Umma saina dawo" ta amsa da "to Allah yasa a dace". Sun shigo Layin su Deeja saita tace "Ku saukeni a nan in ƙarasa, nagode Allah ya saka da alkhairi" Basma ce ta juyo da sauri, da yake tana kusa da Yaya Ahmad dake tuƙasu, tace "haba dai Khadija, ki bari mu kaiki har gida mana", cikin dishewar murya tace "a'a Ku bari kawai na tafi" cikin kulawa Basma tace "daga nan zuwa gidanku da nisa?" tace "a'a ba nisa nan sama ne kaɗan" Basma ta kai dubanta ga Yaya Ahmad tace "Yaya saukemu anan mu ƙarasa, ƙila bata so wasu suga an sauketa a mota ne" cike da kallon tuhuma yace "kinsan dai ba tare muke da escot ba" Basma ta gyaɗa kai "na sani Yaya Ahmad, insha babu abin da zai faru" "Ok, kuje bari na jira ki anan, amma karki daɗe, tace "Tom Yaya na tnx. Sun kama hanyar gidan su Deeja, suna zuwa ƙofar gidan Deeja tace "ga gidan mun kawo" Basma tace "Ok mu Shiga" Deeja tana shiga ta hango Umma zaune tasha kuka idonta yayi ja, da ganinta tana cikin damuwan rashinta ne, da gudu ta ƙarasa ta faɗa jikin Umma tace "Umma na dawo" cikin damuwa Umma tace "Khadija ina kika tsaya tun d.ɗazu kin asamu hankalinmu a tashe?" tace "Umma tafe nake da baƙuwa" da sauri Umma ta kai dubanta hanyar waje ta hango Basma tsaye tana kallonsu, da sauri ta miƙe tace "lale sannu da zuwa, ƙaraso ciki mana" da murmushi a fuskarta ta ƙarasa, wuri ta samu ta zauna kan tabarma cikin nutsuwa tace "Umma ina yini" nan suka gaisa kana ta yiwa Umma bayanin duk abin da ya faru, Umma tayi godiya da kulwanta sannan tace "sun yafe ba komai, nan dai Basma ta miƙe tayi musu sallama tare da aje musu bandir ɗin 'yan budu ɗai-ɗai har dubu Hamsin, ga kuma siyayyan da Yaya Ahmad yayi mata, Umma cike da tsoro tace " 'yar nan mun yafe ki d.ɗauki kuɗinki" cikin fara'a Basma tace "Umma nima 'yar kice, wannan kyauta nayi ma Ummata, kiyi haƙuri ki amsa" da farin ciki Umma tayi mata godiya, sai suka rakata har ƙofar gida, kana ta wuce su kuma suka shiga gida. Basma ta tafi cike da tausayinsu ganin irin gidan da suke ciki, hakanan taji a zuciyarta tana son ta taimaka musu, amma tana tunanin ta wace hanya zata taimakesu, da haka tayi nisa cikin tunani bata ankaraba taji tayi karo da mutum, da sauri ta ɗago ta kalle shi, ido Huɗu suka yi da juna, nan take zuciyarta ta buga, haka shima nashi ya buga, Aryan sarai ya gane ta, haka itama ta gane shi, cikin yanayi na ko in kula Aryan yace "Ke ba kida hankali ne zaki riƙa tafiya ba kya kallon hanya, ko makauniya ce ke da kike tafiya bakya kallon gabanki, ko har gefen hanya kina takama dashi ne?" cike da jin zafin abinda ya gaya mata, wato ma ya ganeta ta faɗa a zuciyarta, tace cikin tsiwa "Kaine ba kada hankali ƙazami kawai, kuma kaine makaho da baka ganin kan hanya" cike da ƙunan zuciya ya d'aga hannunsa ya kwashe ta da mari, abinda bai taɓa yiba kenan ya daki mace, nan fa mutane suka fara taruwa, Basma ta dafe kuncinta tace "ni ka mara? kasan ko wacece ni?" yace "Na mareki koke wacece, kiyi abinda za kiyi, kina tsammanin zan mance baƙar fuskarki ne? Mara tunani kawai, dalla ɓace min da gani" ya ƙarasa maganar cikin zare mata ido, nan take tsoranshi ya mamaye mata zuciya, cikin kuka gudu-dugu Basma ta bar wurin tana ƙoƙarin isa wurin motansu. Shi kuma yabi bayan ta da kallo yayi kwafa sannan ya cigaba da tafiya. Tunda take ba'a taɓa wulaƙanta ta irin na yau ba, tana isa ta faɗa mota, Yaya Ahmad cikin tashin hankali yace "lafiya Basma me aka miki? meya faru? haka ya jero mata tambaya babu amsa, illa a cikin kuka tace "Yaya Ahmad muje gida, muje gida". Cikin tashin hankali ya tada mota ya figeta a guje. Aryan yana tafiya ya fara tunani, a wani ɓangare na zuciyanshi yana farin cikin rama marin da yayi, wani ɓangare kuma yana gargaɗinsa, meyasa ya mareta, nan take wannan tunanin ya rinjayi wancen sai yaji zuciyansa yayi masa ba daɗi da haka ya ƙarasa gida. *Basmatyyy ansha mari ooo 😉 ko kunga laifin Aryan daya rama? muje zuwa...* *Rahma Ce* [8/3, 12:59 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *6.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Ya Ahmad saida ya bari sun kusa gida sai ya samu guri yayi parking, ya kalli Basma yace "Basma ki gaya min me ya faru? dan bazani gida dake a haka ba" share hawayenta tayi ta fara bashi labarin duk abinda ya faru, bata ɓoya masa komai ba tun farkon haɗuwanta da Aryan, saida ta gama tsaf kana ya gyara zamansa ya fuskanceta da kyau yace "Basma gaskiya baki kyauta ba, domin ke kika ja komai ya faru, meyasa idonki zai rufe saboda samun duniya ki wulakanta Mutum, Allah da kanshi ya karrama ɗan Adam ya fifitamu akan Aljanu, Basma yanzu halittan Allah ya cancanci wulakanci? haba Basma ban san yaushe kika sauya halinki ba, kina taƙama da mulki da kuɗi ko, to wallahi Allah zai iya amshesu daga hannun mu ya bama wasu, ki sani wannan duniyar ba matabbata bace munzo cin kasuwa ne, duk kuma abinda muka shuka shi zamu girba a makomarmu, Basma na lura tunda kuka tafi England ke dasu Meena duk kuka sauya hali" Jikin Basma ne yayi sanyi sosai, tabbas maganganun sa sun ratsata, cikin mutuwar jiki tace "Yaya Ahmad wallahi yanzu hankalina ya dawo jikina tabbas ban kyauta masa ba, nagode daka tunatar dani da kayi, lallai na shagala da ruɗin duniya, Yaya Ahmad bansan me ya shiga kaina ba" saita ƙarasa maganar tana kuka, murmushi yayi yace "Ai shi Allah mai gafara ne, inaso duk lokacin da kika ƙara haɗuwa dashi, to ki bashi haƙuri" tace "to Yaya Ahmad insha Allah zanyi yanda kace" wannan karan dariya yayi har haƙoransa na fitowa yace "yauwa ƙanwata farin cikina, yanzu bani labarin yanda kika ƙarasa a gidansu Khadija" murmushi tayi ta soma bashi labari, masha Allah yace, kana ya tada motan suka wuce gida suna hira cikin nishaɗi tamkar Basma batayi kuka ba. Yaya Aryan yana isa gida ya tadda Umma riƙe da kuɗi tana juyasu a hannunta, da sauri ya ƙarasa yace "Umma wannan kuɗin fa? Khadija ta dawo kuwa? dan na zaga sosai ban ga mai kamarta ba, na tambaya ba wanda ya ganta" murmushi Umma tayi tace "Khadija ta dawo yanzu ta shiga bayi, ashe wai wata Yarinya ce ta bigeta a mota suka kaita asibity" nan dai Umma ta labarta masa abinda ta sani, Yaya Aryan ya jinjina lamarin yace "to Allah ya kyauta nagaba, yanzu duk wannan kuɗin su suka bada?" "eh su suka bayar, harda siyayya ma suka yi mata na kayan ciye-ciye" kafin yayi magana Khadija ce ta fito daga wanka tace "sannu da zuwa Yaya Aryan" "yauwa Khadija" nan suka gaisa itama ta ƙara bashi labari, Umma ce ta miƙa masa kuɗin tace "ga kuɗin saika gyara runfarka daga nan ka biya kuɗin haya, sauran kuɗin ka siya mana kayan abinci" Amsa yayi cikin natsuwa yace "Allah ya saka da alkhairi, bari na fita in duba Muntari kafinta sai mu fara maganar gyaran" "to Aryan saika dawo, Allah ya muku albarka" duk suka amsa da "Ameen" kana ya fice. Bayan sallan Magrib jirginsu Prince Shureym ya iso, yana sauka a jirgi motoci na jiransa, ya ƙarasa su tafi gidan president. Bayan sun kai ya wuce falon shugaban ƙasa ya gaisheshi, kana ya wuce part ɗin Ammi ya gaisheta, ya shiga wurin Momy itama ya gaisheta, saiya wuce part ɗinsu Yaya Ahmad can ne masaukinsa, yana shiga falon sai ya faɗa wani ɗaki, wanka yayi ya kimtsa saiya gabatar da sallan Magrib, yana idarwa aka kira sallan isha'i, ya tashi ya gabatar, sai da ya kammala gaba ɗaya, kana ya tashi ya fita falon ya zauna, TV ya kunna sannan ya ɗauki wayarsa ya kira Safeena hira suka shiga yi na kewar junansu. Ɓangaren Basma kuwa, ta sanya aka kawo masa abinci aka jera a kan kafet dake tsakiyar falon, wanka tayi ta sanya doguwar riga na leshi, tayi ɗaurin Maryam Babangida, tayi kyau matuƙa sai ƙamshi takeyi. Basma doguwa ce kaɗan tanada ƙiba shima kaɗan, sai fatarta akwai ɗan duhu mai haɗe da haske, ita ba baka ba ita ba fara ba, tsaka tsaki, sai kuma tana da Boobs dai-dai da jikinta maca ce mai hips sosai, mazaunanta yayi dai-dai da jikinta, cikinta a ɗame yake tamkar bata cin abinci, Basma akwai shape mai kyau da diri. Fuskarta ɗauke yake da dara daran idanu, bakinta ɗan ƙarami ne pink color, sai dogon hanci da yayi tsini har baka, in tayi dariya dimple ɗinta sai ya lotsa, gashin giranta tamkar anyi mata kabin, Basma tanada yalwataccen gashi har gadon baya, mai silɓi da baƙi sosai, Basma ta haɗu domin ko ba makeup fuskarta a haɗe take, Allah ya gama halitta anan. A fili in ka ganta za kayi zaton za tayi nauyi amma ana ɗaukarta shagwal take, kyau dai ta haɗa na Barebari da kuma Fulani. Masu karatu ya kuka hango kyawun Basma, abin ba acewa komai lol😃. A hankali take taku, saboda dogon takalmin dake ƙafarta, a haka ta isa part ɗin su Yaya Ahmad, ta same shi yanata waya ganinta ne ya sashi saurin kashe wayar, galala yayi yana kallon halittar Allah, haɗiya miyau yayi a zuciyansa yace "gaskiya Basma kin haɗu, dole in fara lasar zumanki kan muyi aure, dan bazan jure ganinki haka ba" a fili kuma yace "walcome my Baby" ya buɗe hannu domin taje tayi hugging ɗinshi, rungume hannunta yayi ta gyara tsayuwa, domin ba zata iya abinda yake nufi ba, miƙewa yayi ya isa gab da ita kamshin turarensu ya gauraye gurin, kama hannunta yayi sai ta runtse ido, ƙoƙarin rungumeta ya shiga yi, da sauri ta janye tace "miye haka Yaya Shureym, ka bari kaci abinci mana" dariya yayi yace "afwan gimbiyata ganinki ne duk ya ruɗani, muje ki zuba min" suka je suka zauna, ta zuba masa abincin ya soma ci, yana santi duk a haukansa ya ɗauka ita tayi. Bayan ya kammala ci, saiya miƙe yaje ya wanke bakinsa ya dayo, ita kuma ta zauna akan kushum tana jiran dawowarsa, daya dawo saiya zauna kusa da ita, hannunta ya kama yace "Basma ina sonki sosai, gobe ina son zamu fita zaki rakani wani guri da yamma" tace "ok Allah ya kaimu". Wasa ya farayi da yatsun hanunta, yana mata magana rad'a-rad'a, janye hannun tayi tace "haba Prince ka bari mana" sosa k'eya yayi yace "haba my Basma ya kike yi kamar baki waye ba, ina ce a England kika yi karatu, ai nasan duk kin waye da irin wannan ai" gaban tane ya fad'i tana tambayar kanta "shin me wannan yake nufi?" a ranta, bata ankara ba taji ya rungumeta yana kokorin yi had'a bakinsu guri d'aya, ai da sauri ta fara kiciniyar kwatar kanta, shi kuma ya rik'eta gam, Sallaman da Yaya Ahmad yayi ne ya shigo, shine yasa yayi saurin sakinta, ita kuma ta mik'e da sauri tayi k'ok'arin barin d'akin da gudu, Shureym ne yake kiranta amma ina ta fece a guje, haka ta isa part d'in Ammi tana haki, Allah yasa bata tadda kowa a falon ba, saita wuce d'akinta ta fad'a kan gado, runtse idonta tayi tana mai ambaton Allah, tsanani damuwa ta shiga, yanda Yaya Ahmad yazo ya gansu shine matsalanta. Acan kuma Yaya Ahmad yace "haba Shureym wallahi ba girmanka bane yin haka, iskancin da kake yi a can America sai kace zaka gwada a kan k'anwarka, kuma akan matar da zaka aura?" shafa kansa yayi yace "to meye? ai aurenta zanyi, kuma ma kasan duk abinda zanyi bazan wuce gona da iri ba" tsaki Yaya Ahmad yayi yace "Allah ya shiryeka" bai jira Mai zaice ba ya fice a falon. Bayan Basma yabi, yasan tabbas tana part d'in Amminsa, can ya wuce ya sameta a d'akinta ta kwanta, jin an shigo mata d'aki ne yasa tayi saurin d'agowa ta zauna, Yaya Ahmad ya rufe d'akin, ya jawo wata kujera ya zauna ya fuskanceta, sunkuyar da kai tayi k'asa tana wasa da hannunta, kiran sunanta yayi yace "Basma, ban sanki da hali haka ba, ko da yake nasan shaidani ne shi, amma kuma duk da haka da laifinki Basma, kinje har d'akinmu a wannan shigar kuma ba mayafi, sannan kuma daga ke sai shi, kin san cikon na ukun ku shaidan ne, Basma mace da Namiji ba aso suna keb'ewa haka, in dai ba mata da miji bane, ki daina d'aukar Shureym a matsayinmu, domin mu jininki ne, shi kuma aure zai shiga tsakaninku, dole kiyi taka tsan-tsan dashi domin na fiki sanin waye Shureym". Dago jajayen idonta tayi tace "Yaya kayi hak'uri ba laifi bane, shine ya matsamin, ina k'ok'arin kwacewa ne kazo ka samemu a haka" "eh, Nagani ai, ina so in dai zaki sashinmu, tofa ki tafi da su Na'im da Anwar, karki yarda kina keb'ewa dashi ke kad'ai" tace "to Yaya Ahmad, insha Allah zan kiyaye" "yauwa k'anwata" nan yayi ta mata nasiha har ta saki jiki sukayi barkwanci, kana yayi mata saida safe ya wuce. Basma ji tayi duk Shureym d'inma ya sire mata a rai, bata zata haka yake ba, amma ta d'auki alkhawari za tayi maganinsa. *Washe gari* Da misalin k'arfe 4:30pm na yamma Basma ta shirya cikin riga da sket na kanti, ta sanya lafaya, ba k'aramin kyau tayi ba, yau ta fito a 'yar Maiduguri sosai, fitowa tayi su Anwar da Na'im suna biye a bayanta, suma sunyi shigan kananan kaya sunyi kyau, shekarunsu zai kai 16yrs, har motan Prince suka isa, sai ga shi ya tawo, tun daga nesa yake washe baki harya k'araso, ganinsu twins ne yasa yace "My Basma kin ga yanda kika yi kyau kuwa" murmushi tayi ba tace komai ba, yace "ba dai da su twins zamu tafi ba?" da murmushi a fuskanta tace "tare Zamu tafi, ko akwai Matsala ne?" bata rai yayi yace "amma ai kinsan ba haka mu kai dake ba ko?" kafin ta bashi amsa twins suka ce "Haba Yaya Shureym me mukayi da ba za'a damu ba, mu gaskiya sai munje" Basma ma tace "in ba zamu dasu ba sai dai a fasa tafiyan" k'ara tsare gira Shureym yayi, sai ya bud'e mota bai ce komai ba, haka su ka tafi tare badan ransa ya so ba, har suka dawo Prince bai saki fuska ba. Siyayyan kayan kwalama yayi musu suka dawo, Basma ko a zuciyarta sai dariya take yi. Bayan Sallan Isha'i, Yaya Ahmad ya shigo falon Ammi, bai sameta a falon ba, saiya wuce wurin Basma ya sameta tana danna system d'inta, rufewa tayi suka gaisa, ya samu guri ya zauna tace "Yaya Ahmad kasan yanda nayi yau da mutuminka kuwa?" cikin dariya yace "wa kenan?" tace "Yaya Shureym mana" nan ta kwashe yanda suka yi ta bashi labari, aiko sai ya kwashe da dariya yace "good k'anwata, yanzu ma ko yace kije side d'inmu karki je, kice yazo falon Ammi kuyi hiran, kinga ai ba zai yi shakiyanci anan ba" dariya itama tayi tace "sosai ma kuwa, ai ba zai yi ba, maganinsa zanyi ai tunda shi shaid'ani ne" dariya yayi yace "Mijinki ne dai ba ruwana, yauwa gobe ne fa zaki kawomin patient d'ina ko?" Tace "eh, insha Allah gobe ne zanje har gida na d'aukota, "to Allah ya kaimu" "Ameen". Nan suka yi sallama ya wuce. *Washe gari* Da misalin k'arfe goma na safe, Basma ta shirya ta fita cikin shigar doguwar riga na atamfa ya kamata daga sama k'asa ya bud'e, babu wani kwalliya a fuskanta, ta shiga motanta sai d'aya daga bodyguard d'inta yazo zai yi magana tace "yau ni ka d'ai nake jin fita ba dad'ewa zanyi ba" daga wannan bata sake magana ba ta tada mota tayi gaba. Yau ak'ofar gidan tayi parking ta shiga a nutse, ta samu Deeja tana wanke-wanke, da sallama ta shiga, Deeja ta mik'e da sauri tace "sannu da zuwa Anty Basma" Basma ta amsa cike da fara'a, tabarma ta d'auko ta shinfid'a mata ta zauna, tace "Deeja ina Umma" tace "Umma ta fita mak'ota dubiya yanzu zata dawo, bari na k'arasa wanke-wanke kan tazo" Basma ta mik'e tace "bari na tayaki" da sauri Deeja tace "a'a ki barshi nagode" ai sai ta b'ata rai tace "baki so na samu lada ne nima?" "a'a inaso ki samu, gani nayi daga nin ki baki saba da wahala ba" dariya tayi tace "haka dai kika gani" haka ta sanya mata hannu tana d'auraye kayan tana kifewa a kwando suna kuma hira. Yaya Aryan ne yayi sallama ya shiga, ai sai gaban Basma ya fad'i, da sauri ta waiga aiko tsaraf suka had'a ido nan take gabansu ya fad'i dukansu, mamaki ne ya kama Aryan, sai da suka yiwa juba kallon tsayin minti uku, kana ya je ya zauna kan wata kujera, Deeja ce tace "Yaya ba kaje kasuwan bane?" yace "naje, wani Abu nazo amsa gun Umma" "ok, aiko ta fita amma bazata dad'e ba" a sanyaye Basma ta k'arasa taya Deeja wanke-wanke, ta koma ta zauna, Deeja ta d'au kayan ta kai kicin ta dawo ta zauna gefen Basma, tace Basma ga Yayana Aryan" "ok" tace, Deeja ta kai dubanta ga Yaya Aryan tace "Yaya Aryan ga Basma nan, wanda na baka labari, yanzu ma tazo muje asibity ne a k'ara dubani" murmushi yayi na gefen baki yace "ok na ganta" sai Khadija taji abin yayi mata wani iri yanda Yaya Aryan yace, Basma tace "ina kwana" tayi maganar a sanyaye, amsawa yayi a dak'ile, sai ya mik'e yace "Deeja zan koma, anjima zan dawo, dan yau ba zan dad'e ba a kasuwan" "To adawo lafiya" Basma ta bi bayansa da kallo. Saita juya tace "dama wannan ne Yayan naki?" da murmushi Deeja tace "eh" Umma ce tayi sallama sai duk suka amsa, nan Basma ta gaishe ta, ta kuma bayanin komawansu asibity, Umma tayi godiya tace "to sai kun dawo" Deeja ta d'auko hijabi ta sanya suka wuce. Umma da mamaki tace "ikon Allah, Basma sam bata kyamarmu". *Rahma Ce* [8/3, 5:01 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *7.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Basma da Deeja suna tafe a hankali a cikin mota, Basma ta kalli Deeja tace "Deeja dan Allah ina son ki bani tarihinku a tak'aice in ba damuwa" murmushi Deeja tayi tace "ba damuwa Anty Basma" nan ta fara bata labarinsu tas a takaice, har suka isa Asibiti zancen suke yi, Basma tana girgiza kai alaman tausayawa sosai. Bayan sun isa Asibiti, suka tadda Yaya Ahmad a office d'insa, ya duba Deeja ya k'ara bata wasu maganin kana ya sallamsu yace "an gama ba zata k'ara dawowa ba" Basma ce tace "ok Yaya godiya muke" murmushi yayi mata yace a cikin harshen yaran barebari, "Basma, Khadija tana da kyau, ko kin lura da haka kuwa?" da murmushi a fuskanta ta mayar masa cikin yare, "sosai ma kuwa, haka Yayanta yake kuma yama fita kyau, ita tafi kama da Ummansu" murmushi yayi yace cikin sigar wasa "to kina ganin inna zab'eta tayi?" zaro ido tayi waje tace "Yaya talakawa ne fa, amma kana ganin su Ammi zasu yarda?" dariya yayi sosai yace "mai zai hana suk'i yarda, damu dasu duk d'aya muke a gurin Allah, face wanda yafi wani imani, kawai ke zaki wayar da ita sosai ta zama kamar yanda kika waye, sannan zan sata a makaranta tayi karatu, kinga ai shikenan ba mai hanani aurenta" murmushi tayi tace "hakane Yaya Ahmad, ni ai wallahi ka sani farin ciki sosai, dama kuwa kasan abin da nake shiri kenan na maidata makaranta" dariya yayi yace "to na rigaki buk'atar samun Ladan" itama dariya tayi tace "yauwa Yaya Ahmad, ya za ayi ka samar ma Yayanta aiki a company Abbanmu, yana da diploma a computer science, kaga in an d'aukeshi sai ya koma karatunsa, yayi digree da masters, kuma yana aiki ana biyansa salary mai kyau" murmushi yayi yace "shawara mai kyau, kinga mun taimaka su, tunda suna cikin buk'atan haka, kuma dama amfanin Arzikin kenan, in ka samu ka bama na k'asa da kai, zansa ma a k'ara yiwa unguwarsu titi, zamu d'auki matasan unguwan marasa k'arfi mu sanya su a makaranta, dan naga unguwar akwai mabuk'ata sosai" tace "da kyau Yaya Ahmad, wannan shawaran yayi, Allah ya bamu ikon yi" yace "Ameen" duk wannan hiran cikin yaransu na barebari suke yi, Deeja tayi shuru tana saurarensu amma bata fahimtar me suke cewa, computer science d'in da Basma tace, shine ya bata damar fahimtar k'ila hiran da sukayi da ita ne, take gaya masa. Mik'ewa Basma tayi tace "Yaya bari mu tafi" murmushi yayi yace a cikin harshen labaraci "ki kulamin da Matata, karki sake ki gaya mata ba yanzu ba tukun, kuma ina so ki b'oye musu asalinmu, saboda su samu damar sake jiki damu" murmushi tayi tace itma cikin larabci, "ai Yaya bazan fad'a ba, zance musu Mom d'nmu da Dad basa k'asarnan suna Canada, muke Nigeria da sauran family d'inmu, kuma gidan hutuna shine gidan iyayenmu, kaga bazasu gane ba" Cikin harshen turanci yace "good girl" tana dariya suka fita, Deeja dai jinsu takeyi, tad'an so ta fahimci hiran amma bata gane ba saboda batajin labarci sai kalmomi kad'an take iya tsinta. Suna tafe a hanya suna hira a yanzu Deeja ta saki jiki sosai da Basma, koda suna kusan sa'a amma akwai girmamawa na musamman da Deeja kewa Basma, Basma tace "Deeja samu shiga kasuwa siyayya" tace "to Anty Allah ya kaimu lafiya". Sunje Babban shago na saida kayan kanti, side d'in maza suka fara shiga, riga da wando ta siya kala biyar k'ananun kaya, sai manyan kaya shadda da material na maza kala biyar d'inkakku, sai su singilet da gajeran wando guda biyar-biyar, sai takalmi kala hud'u, huda kala biyu, da kuma turare masu k'amshi har kala Hud'u, sai a gogo kala biyu. Aka sanya kowanne a jaka, ta bada kud'i aka sanya musu a mota. Suka shiga side d'in mata nanma kaya ta sanya Deeja ta zaba kananu da kuma lesshi da atamfa, hatta gyale, takalma da d'an kunne duk ta siya mata, sannan ta siyawa Umma nata kayan kala uku da mayafi, takalmi da d'an kunne da sarka, harda turare, Siyayya suka yi sosai kana suka wuce gida. Suna isa suka fara shiga da kaya, Umma ai bud'e baki tayi tana kallon kayan cike da mamaki, saida suka shigo dashi tas, Basma ta ware na Yaya Aryan tace "Deeja ina d'akin Yaya Aryan yake?" Deeja tace "shine can da yake kallonki" tace "d'akin abude yake?" "Eh a bud'e yake kullun" Umma kallonta take kawai ta kasa magana, Basma ta nufi d'akin ta bud'e, ba laifi d'akin ba wari yana k'amshin turaren wuta na tsinke, sai dai d'akin akwai datti da tarkacen kaya, aiko shiga tayi ta bud'e k'ofar, ta fara kauda kaya kana ta samu tsintsiya ta share d'akin, har wani gumi ta had'a abinda ba'a saba yiba, Deeja tazo zata tayata tace ta barshi itama zata iya, tana gama sharan ta kakkab'e zanin katifar ta gyara kana tazo ta kwashi kayan data siya masa ta aje gefe guda, ta fito tana sharce zufa, Umma ne tace "Sannu da k'ok'ari Basma Allah ya miki albarka, ya baki miji nagari, yasa ki gama da duniya lafiya" ta k'arasa maganar tana matsar kwalla, Murmushi Basma tayi ta k'arasa kusa da Umma, zama tayi gefenta a kan tabarma tace "Umma na d'aukeki Uwa a gareni, duk abin da na muku na yiwa kaina ne domin Uwata nayi mawa, kuma Umma meye amfanin kud'in da za'a tara a aje ba'a yi taimako dashi ba, ki d'auka tamkar ke kika haifeni Umma, domin Allah ya riga ya had'amu, iyayena basa nan suna k'asar waje dagani sai Yaya na Ahmad da kuma sauran danginmu, lokaci-lokaci suke zuwa nan domin mu munk'i zama dasu, munfi son zama a k'asarmu, Umma iyayenmu suna bamu kud'in wanda bamu san me zamu yi dashi ba saboda yawansu, kinga kuwa danna bayar wa Alumman Annabi bamu Fad'i ba" Da murmushi a fuskan Umma tace "kwarai kuwa Allah ya saka da alkhairi" "Ameen Umma, kuma nayi magana da Yaya na yace zai mai da Khadija makaranta, yace in gaya muku kafin yazo" Umma cike da farin ciki mara misaltuwa ta rungume Basma, Deeja kuwa tsalle tayi ta dawo kusa da Basma, godiya ta shiga zuba mata sosai tamkar ta biya mata saudiya. Haka sukaita murna suna zuba mata godiya, Basma ta d'auko takadda a jakarta ta shiga rubuta short note, ta bama Yaya Aryan hak'uri akan abinda tayi masa. Tana gama rubutawa ta mik'e ta je ta sanya letter a cikin d'aya daga cikin jakukunan kayan data siya masa, kana ta fito ta d'auki Jakarta tayiwa su Umma sallama, Umma har k'ofar gida ta rakota tana shi mata da albarka tare da addua, Deeja kuwa har mota taraka ta. Basma na isa gida wanka ta yi ta dad'e cikin ruwan zafi tana gasa jiki domin yau ta kwaso gajiya, tana fitowa ta shirya ta wuce part d'in Momynta, ta same ta zaune bisa dadduma ta idar da sallan La'asar, zuwa tayi ta kwanta ajikinta cike da shagwab'a tace "Momy kin jini shuru yau baki nime ni ba?" murmushi tayi tace "ai kwanakin nan naga kamar kinyi hankali ne, kodan basu Leema ne k'ila" dariya tayi tace "kai Momy, dama can ma haka nake, hala su Na'im suna islamiya?" "eh suna can, wai ke kuwa yaushe rabon naga kina karatun al'Qur'ani?" murmushi tayi tace "Momy ina karantawa bayan sallan Magrib da kuma in zan kwanta barci, a wata sau biyu nake saukewa fa" "Masha Allah haka nake so ki rik'a kula da ibadarki sosai" "tom Momy zan kula insha Allah, Momy dama ina son muyi magana akan yarinyar dana bige rannan, sunan ta Khadija" nan ta shiga bama Momy labarinsu kaf da kuma abubuwan da tayi musu, da ma taimakon da take shirin yi musu ita da Yaya Ahmad, Murmushi Momy tayi na farin ciki tace "Basma ban tab'a tunanin kinyi hankali irin haka ba sai yau, wannan abu da kike yi tunani ne mai kyau, nima zan bada tawa gudun mawar akai, sai muyi tarayya a cikin Ladan gaba d'aya, zanga Ahmad saimu tattauna akan gyaran unguwar da taimakon mutanan unguwar, Allah ya bamu ikon yi da iklasi" tace "Ameen Momy, kin amince in cigaba da taimaka musu kenan?" "sosai kuwa na amince, ai in dai wannan ne sai inda k'arfi na ya k'are wajen baki goyen baya, kuma mun taimaka wa Abbanku ne, tunda shike Mulkan k'asatar nan" "hakane Momy" kamar zata gayawa Momy k'udirin Yaya Ahmad akan Deeja saita fasa, saboda ta d'aukar masa alkhawari akan bazata gayawa kowa ba. Haka suka cigaba da hira na 'Ya da Uwa har barci ya d'auke Basma, Momy kuma ta cigaba da lazumi, sai gabda sallan Magrib ta tasheta, sannan duk suka nufi d'aki. Yaya Aryan ya dawo da yamma lis, ya samu Umma tana tuka tuwo, ya gaisheta kana ya nufi d'akinsa, yana tura k'ofa ya shiga yaga daki fes an gyara, bai k'ara tsinkewa ba saida ya hango jakukuna a gefe, da sauri ya juyo ya kalli Umma yace "Umma waya shigan min d'aki kuma jakukunar waye a ciki?" Murmushi tayi tace "ka shiga ka duba akwai sak'on bayani a ciki" Deeja ce tayi tsaraf tace "Yaya Aryan kayanka ne da" bata k'arasa ba Umma tayi mata dak'uwa tace "yi min shuru a wurin nan, ya shiga ya gani mana da kansa, ya tsaya yana tambaya" jikinsa a sanyaye ya koma d'akin, zama yayi dirshen a ledan d'akin, ya shiga fidda kayan dake jakukunan d'aya bayan d'aya, harya isa jakan da huluna da agogo ke ciki, yana ciro hula sai letter ya fad'o, da sauri ya aje hulan ya shiga bud'e letter, gyara zama yayi ya soma karantawa kamar haka *Assalamu Alaikum* *"Yaya Aryan nasan zaka yi mamakin ganin sak'o na, da farko ina mai baka hak'uri akan duk abin da na yi maka kwanaki, hak'ik'a nayi kuskure, kuma naji kunya d'azu sosai, saboda bansan kaine Yayan Deeja ba."* *"Yaya Aryan wannan kayan naka ne, a matsayina na k'anwarka na siya maka, karka d'aukesu a matsayin na raina maka ne, wallahi nayi maka dan Allah ne, domin a yanzu ka zama Yaya a gareni."* *"Dan Allah kar kace ba zaka sanya kayan ba, domin in kayi amfani dasu, hakan ne zai nuna min ka yafemin akan abinda ya faru tsakanin mu, kuma ka d'aukeni k'anwarka. Hakan zai sanya ni farin ciki sosai Yaya Aryan."* *Kanwarka Basma Bulama.* Nagode. Wani irin yanayi Yaya Aryan ya tsinci kansa a ciki, komawa yayi ya d'aura kansa bisa katifa, ya kuma karanta sak'on, yayi ta maimaitawa kusan sau biyar, mamaki ne ya cika shi, zuciyarsa yana harbawa a hankali, ji yayi duk kasala ya rufeshi, lumshe idonsa yayi ya shiga tariyo abinda ya faru a tsakaninsu, nan take yaji ta burgeshi yanda take nuna isa kamar wata *'YAR SHUGABA* salonta ya bashi mamaki yanda tayi saurin sakowa ta bashi hak'uri, sai yaji zuciyansa ya wanke babu sauran jin haushinta da yake yi, hakanan ya tsinci kanshi da k'ara son ganin ta, yana kissima ya salon zai sauya tunda yanzu sun shirya ba fad'a, murmushi yayi wanda ya k'ara bayyana kyawunsa, a bayyane yace "nima naso na baki hak'uri, saboda irin k'ok'arin da kika yi akan Deeja, baki cancanci mari a guna ba Basma, kawai dai munyi abun a cikin rashin sani ne, koda ke kika rafa tsokana ta, amma duk da haka zan ja aji, domin ki gane ni d'in Namijin gaske ne" Dariya yayi wanda ya bayyana fararen hak'oransa, ya tashi zaune ya k'ara duba kayan, duk sun kwanta masa arai, godiya yayi ma Allah, kana ya mai da kayan mazauninsu ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallan Magrib. *Rahma Ce* [8/3, 5:02 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *8.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *Bayan mako guda* Yaya Aryan yanata zuba ido yaga zuwan Basma amma shuru, wani lokacin har tashi yake a kasuwa da wuri domin yazo ko zasu had'u, cikin da bara yake tambayan su Umma akan Basma tazo? sai suce bata zoba, wasa-wasa har aka shafe sati d'aya, sai rashin zuwan nata ya fara sa shi damuwa, Addu'a yake Allah yasa lafiya. Ta b'angaren Basma kula kalau take, domin a cikin satin Yaya Shureym yazo, sun sha soyayya shiyasa bata samun lokaci sosai ba na zuwa gidansu Deeja, domin kullun yamma suna fita da Yaya Shureym dasu Na'im, sai Magrib suke dawowa. Hakan yasa bata samu damar zuwa ba, amma fa tana tunaninsu da kewar Umma sosai, ta d'auki aniyar siyan musu waya, in bata samu zuwa ba ta rik'a kirasu. Yau ya kama ranar Juma'a, bayan Sallan La'asar Basma da Yaya Ahmad suka shirya zuwa gidansu Deeja, Basma tayi shigan lafaya mai kalan fari da green, Yaya Ahmad kuma ya sanya sky blue na shadda hula bak'in dara da takalmi bak'i, sunyi kyau sosai. suka kama hanya suka tafi a mota ba tare da escot ba, hira suke cikin nishad'i tare da kwanciyar hankali, a haka suka isa gidan. Bayan sun isa Basma, ta fito tace "Yaya bari na gaya musu tukunna saika shigo" ya kalle ta da murmushi yace "ba damuwa ina jira". Cikin natsuwa ta Shiga gidan, duk kan su suka amsa, cike da fara'a Umma ta tarbeta, Deeja kuwa tasowa tayi ta amshi jakan hannunta tana mata sannu, Yaya Aryan kuwa basar da ita yayi tamkar bai ganeta ba, Amma fa a zuciyansa yana yaba kyawun da tayi, dauriya kawai yayi ya matse, zama tayi a kan tafarma sai da suka gaisa da Umma kana suka gaisa da Deeja, ta kai kallonta wajen Yaya Aryan tace "ina yini Yaya Aryan?" farin cikin ne ya mamaye zuciyansa jin yanda ta kira sunansa yayi masa matuk'ar dad'i, a fili kuma ya amsa fuska ba yabo ba fallasa a dak'ile, daga nan bata k'ara cewa komai ba domin jikinta yayi sanyi yanda taga ya amsa mata, sai duk ta jita a takure, Waigawa tayi wurin Umma tace "da Yaya Ahmad muke yana waje, nace bari na sanar muku kafin ya shigo" Umma ta fad'ad'a fara'an fuskanta tace "Allah Sarki ai da ya shigo tunda duk gida ne, Kai Aryan tashi ka shigo dashi" da sauri ya mik'e ya fita, cikin minti uku saiga su sun shigo, ya zauna a tabarman da Yaya Aryan ke zaune shima ya zauna gefensa, cikin natsuwa ya gaida Umma, ta amsa cike da farin ciki, Deeja ne ta fito daga d'aki sanye da gyale ta kawo masa ruwan pure water a cikin plet ta aje a gabansa, sannan ta gaishe shi, cikin kulawa ta amsa, Basma na satan kallonshi, taga sai wani kallon Deeja yake kamar zai had'iyeta, ita ko Deeja batasan yana yiba, nan ya shiga yiwa su Umma bayanin zuwansa, yace "Umma kan zancen makarantar Deeja ce, insha Allah ranar Monday zasuje tare da Basma tayi mata registration, saboda yanzu ana farkon fara d'aukan sabbin dalibai, sannan kuma na d'auki Aryan zai yi aiki a company Abbanmu, In ba damuwa" Aryan cikin natsuwa yace "Ayi haka kuwa? wannan dawai niya ai zata yi yawa, ga Deeja ga kuma ni" murmushi Yaya Ahmad yayi yace "d'an uwa karma damu duk yiwa kaine" Aryan yace mun gode Allah ya saka da Alkhairi" Umma ma godiya tayi harda yan kwallanta, Deeja ko murna ne kan murna, itama godiya tayi. Nan fa hira ya b'arke sunata zan tawa, Amma fa banda Basma data takure, saboda irin nuna ko in kula da Yaya Aryan yayi mata, bayan minti talatin da zuwansu, Yaya Ahmad yace zai je wani wuri inya dawo zaizo ya d'auki Basma, nan yayi musu sallama Yaya Aryan ya rakashi waje, Basma ne ta juyo wurin Deeja tace "saiki shirya ranar Monday da wuri zanzo domin mu tafi makarantan, ina so mu gama registration a ranar ne" cikin farin ciki tace "insha Allah tun Asuba zan tashi na shirya da wuri" Umma tace "da dai ya fi miki da wannan shegen barcin asaran da kike yi, to yanzu ga makaranta nan saiki cigaba da barcin mu gani" duk suka sanya dariya, Yaya Aryan ne ya shigo yace "Umma wai ina furan ne? wallahi yunwa nakeji" da sauri tace "af kaga na manta, da an dama Ahmad yasha kan ya tafi, ke Deeja d'auko min kwanan furan nan da kuma kindirmo had'e da sugar" taje ta d'auko, nan Umma ta dama fura da nono da yawa, ta fara zubawa Basma a cup ta aje a gabanta, sannan sauran ta zuba musu. Deeja ta mik'awa Yaya Aryan nashi yace "mik'o min sugar na k'ara" ta mik'a masa ya k'ara, ya juya da kyau ya fara sha, duk suka fara sha banda Basma, Umma tace "ya dai Basma yau na ganki wani iri ko lafiya?" dariya tayi tace "Umma lafiya lau zan sha" Yaya Aryan ya mik'e ya shiga d'aki d'auko wani abu ya bar furan a wurin, yana shiga Basma tayi sauri ta d'auko furansa ta fara sha, Umma da Deeja suka sanya dariya ba tare da sunce komai ba, sun zuba ido suga drama ya Aryan zaiyi, yana fitowa yaga wurin wayam ba cup d'in furansa. D'ago kan da zai yi, ya hango Basma tana sha hankalinta kwance, murmushi kawai yayi ya matsa kusa da ita yace, "bani furana ai ba naki bane wannan" ko d'agowa bata yi ba, ta cigaba da sha, Khadija ce ta kwashe da dariya tace "kai Yaya tunda ta d'auka naka sai kayi hak'uri ka d'auki nata kasha" d'aura fuska yayi ya harareta, sai ta gimtse dariyan da takeyi, Umma dai uffan ba tace ba, k'arshe ma tashi tayi ta shiga kicin dan ta duba tukunyarta, aiko tana shiga kicin ya saka hannu ya wafce kofin furansa, sai Basma ta sa kukan harda shagwab'a, ga hawaye na malala, mamaki ma ta bashi, Amma saiya dake ya koma ya zauna, murza gyad'a mai gishiri yayi, ya zuba a furan ya cigaba da sha, Umma ce ta fito daga abin mamaki, d'aure fuska tayi tace "Aryan ba dai amsa kayi ba?" da murmushi fuskansa yace "Umma ai ba nata bane nawa ne fa, shiyasa na amsa" d'aure fuska ta kuma yi tace "banson shirme ita ma ba k'anwarka bace, shine baka barmata ba" aiko Basma ta samu goyon baya, sai ta kuma narkewa cike da shagwab'a tace "Umma ni nashi zan sha ki ce masa ya bani" Umma taso tayi dariya Amma sai ta dake tace "Aryan bata naka kayi hak'uri kasha nata" shima cikin yana yi na shagwab'a yace "Umma nawa nake so na sha" Umma ganin zasu sa mata hauka sai ta shige d'aki ta basu guri, domin tasan da gan-gan Aryan yayi haka, zuciyarta ne ya fara mata zargin wani abu. Deeja ta dinga dariya a b'oye, haka Yaya Aryan ya shanye furan, harda lashe kofi, Basma na gefe sai kumbure-kumbure take yi. *Nace ohhh su Basma ko ina akaje sai an raba hali lol.*😉😄 Deeja ta mik'e ta shige bayi, Yaya Aryan ya mik'e ya matsa kusa da ita ya d'auki furanta yace a hankali yanda Umma ba zata ji ba, "Ga naki kisha kar kuda ya shanye miki, domin nima ban koshi ba, in baza ki shaba sai na shanye" hawaye cike a narkakkun idonta ta d'ago, sai suka had'a ido, ai gaba d'aya saita saukar masa da kasala, sun d'auki tsawon minti biyar suna kallon juna, ita tana masa kallon tuhuma "meyasa baka yafemin ba" shi kuma yana mata kallon "da sauranki ban hak'ura ba" Shine ya katse kallon ya limshe idonsa, kana ya bud'e ya sakar mata wani shu'umin murmushi, da sauri ta sunkuyar da kai domin tabbas duk gangar jikinta ya amsa, bai kuma cewa komai ba, ya aje cup d'in a gabanta, ya sanya takalmi yace da k'arfi "Umma na fita saina dawo" a cikin d'aki ta amsa masa "adawo lafiya". Yana fita Basma itama ta sanya takami ta bi bayan sa. Shi dai yaji ajikinsa Basma zata biyo shi, sai ya d'aure fuska ya cigaba da tafiya, sai da ya d'anyi nisa da gida kana ya juyo fuska d'aure, yace "lafiya kike bina?" Cike da damuwa tace "ba kaga sak'ona bane" yayi guntun murmushi yace "inna gani me zan miki" marai raice fuska tayi tamkar zatayi kuka tace "Yaya Aryan na baka hak'uri Amma kayi burus, kamar ma na k'ara zuga ka ne" ya kuma d'aure fuska yace "da yake kin raina min hankali ba, zaki wani rubuta min a takarda, to ki sani bai min ba, kaya kuma suna nan na aje, duk lokacin da kika ga dama zaki zo ki d'auka" Cikin rashin jin dad'in abin da ya ce mata tace cikin tsiwa, "dan ma na baka hak'uri, wlh banda kaci darajan su Umma ba abinda zaisa na baka hak'uri, tunda wancen bada hak'urin bai maka ba, yanzu nace Yaya Aryan kayi hak'uri komai ya wuce" dariya ya kwashe dashi yace a ransa "wannan Yarinya ba tad'a kunya zanyi maganinta" a fili kuma yace "a haka zaki bani hak'uri kina min masifa? malama banda lokacin ki yanzu, sai anjima" ya juya zai tafi da sauri ta sha gabansa tace cikin marai raice fuska "Yaya Aryan kaine kake hasalani, to naji zan baka hak'uri, Yaya Aryan kayi hak'uri bazan sake ba" sai tayi shuru, murmushi yayi yace "to naji na hak'ura Amma kad'an, ki wuce gida sai anjima" bai jira me zata ce ba ya wuce da sauri, ita kuma murmushi tayi, tace a fili "Aiko zan maganinka". Bayan sallan Magrib Yaya Ahmad ya dawo, kai tsaye ya shigo gidan, ya same su duka a tsakar gidan, ya kuma gaishe da Umma, ya kalli Basma yace "kin shirya mu wuce ko?" tace "na shirya" Umma tace "ka tsaya kaci tuwo mana, itama yanzu ta gama ci" da sauri ya dubi Basma yace "da gaske kinci?" dariya tayi tace "eh mana na ci" yace "tafd'i, aiko yau za ayi ruwa da k'ank'ara, keda bakya k'aunar tuwo" dariya duk suka yi tace "eh yau dai naci na Umma na mai dad'i" Yaya Ahmad ya mik'e yace "Umma wallahi a k'oshe nake, sai dai wani lokacin inna zo" Umma tace "Ba komai Allah ya kaimu" Basma ma mik'ewa tayi ta d'auki jakanta, suka yi wa Umma saida safe, Deeja tayi musu rakiya har mota. Basma ta ciro waya Android mai kyau ta bawa Deeja tace "ki rik'e a hannun ki, zan dinga kiranku da shi, ina jin lafiyanku" ta amsa tayi godiya sosai. Yaya Ahmad ne ya kalli Deeja yace "Hajiya ba magana ne" murmushi tayi tace "akwai, ai d'azu mun gaisa" yace "hakane Amma ai gaisuwa bata yawa" "eh hakane, to ina wuni Yaya Ahmad" yace "bazan amsa ba tunda saida na rok'a" d'ago kai tayi suka had'a ido sai ya kanne mata ido d'aya, da sauri ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi tace "ayi hak'uri Yaya Ahmad bazan sake ba" dariya yayi yace "karki damu, masu suna Deeja basa laifa dama, amma a wurina" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, a yanzu dai ta fara gane ina Yaya Ahmad ya dosa, domin duk had'uwansu saiya tsokaneta. Nan suka yi sallama ya ciro kud'i bandir d'in dubu d'ai-d'ai ya mik'a mata yace "ga wannan ki sha sweet" sai tak'i karb'a, sai da Basma ta sa baki, kana ta amsa tayi godiya, sannan suka wuce. Yaya Aryan sai bayan sallan isha'i ya dawo, bai samu Basma ba, sai hakan bai masa dad'i ba, domin yana son fad'ansu dan yana masa dad'i. Bayan ya gama komai ya shiga d'aki da nufin kwanciya, sai ya ga d'akinsa a gyare, murmushi yayi domin yasan wacce ta gyasa masa, sauya kayan jikinsa yayi ya sanya na barci, ya kwanta akan katifansa, yayi d'ai-d'ai akan filo, ya d'aura kansa baifi minti goma ba yaji baburetin k'ark'ashin filo, da sauri ya mik'e cike da tsoro yana tunanin menene haka, Sam tunaninsa bai kawo masa waya bane, saboda shi baida ita, da sauri ya finciko filon yaga ko miye, waya ce android babba mai kyau a shinfid'e ya gani, mamaki ya cika shi, tace "wannan yarinyar ko mayya ce sai haka, kullun sai ta barni da mamaki, nasan ba kowa ba ne sai Basma" Wayan ne yaga yana haske da alama kira ne ya shigo, da sauri ya matsa kusa ya d'auka ganin Basma a zanen kan wayan ne, yasa shi murmushi yace "mayyar k'anwata" d'agawa yayi ya kara a kunne bai ce komai ba, itama bata ce komai ba har tsayin minti uku, ganin ba zaiyi magana ba yasa tace "Yaya Aryaaan" tsigan jikinsa yaji ya tashi, irin yanda ta kira sunansa taja k'arshe, a kasale yayi murmushi wanda sai da taji sautinsa, itama murmushi tayi tace "dama zance maka ne kayan d'akinka sunyi datti, zanin gadonka yana bukatar wanki da labule, kayi k'ok'ari ka bayar a wanke maka ko kai ka wanke, domin tsafta cikon addini ne, dan d'azun dakyar nake shak'ar numfashi, saboda yanda kayan ke tashi ya kuma had'e da k'amshin turare" Tsananin fushi Yaya Aryan yayi, cike da b'acin rai yace "wai ke ni sa'anki ne? wallahi inda kina kusa sai na miki marin dayafi na rannan, mara kunya kawai" kwashewa tayi da dariya tace "haba Yayana Aryannny, daga gyara kayanka ai ba zai zama sauke mu raba ba, Allah dan ni ban iya wanki bane, dana wanke maka, shiyasa nace bari na gaya maka a wanke" Murmushin takaici yayi yace "ko kin wanke saina sake wankewa" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace "kuma wannan wayar ta miye zaki aje min a d'aki?" tace "dan na rik'a jin muryan Yayana, shiyasa na aje a gun" a wannan lokacin gyara kwanciyansa yayi gaba d'aya lamarin Basma ya daina bashi mamaki, tana da saurin hasala mutum, tanada saurin sakko da mutum in yayi fushi, Yarinya kamar mai Aljanu, a nushe yace "to Yayan naki yace bai so, ki zo ki d'auki kayanki" cike da shgwab'a tace "uhum ni ban yarda ba, ina son jin muryan Yayana ne, ba zan amsa ba" murmushi ne ya sub'uce masa yace "shi kuma Yayan naki baya buk'atar jin muryanki, dan haka ba zai yi amfani da wayan ki ba, ni saida safe barci nake ji" sai ya gimtse kiran. Saiya rungume wayar a k'irjinsa, haka nan ya tsinci kanshi cikin nishad'i. Basma sam bata ji dad'in gimtse kiran da yayi ba, hakanan ta tsinci kanta da k'ara son jin muryansa, sake kiransa tayi, baburetin d'in wayar ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya shiga, sai ya d'aga kiran, cikin kasalan murya yace "Basmaaa, ki barni nayi barci mana" sai taji wani yarrrr, tsigan jikinta ya tashi, gaba d'aya sai ta ji wani irin nutsuwa ya shigeta, tace cikin irin yanayin muryan da yayi magana tace "eh bazan bari ba sai munyi hira" cikin tsokana yace "ke wai mayya ce" tace cikin tsiwa "eh mayya ce Amma a gunka kai kad'ai" dariya yayi sosai yace "to nama na d'aci gareshi yarinya dan yafi k'arfin ki" itama dariya tayi tace "namanka dai zak'i zaiyi kanma a ce hancinka zai d'auki romo sosai" dariya duk suka kwashe dashi a tare, kana cikin dariya yace "kwalelen ki Yarinya" itama cikin yana yin farin cikin tace "ba wani kwalele Yaya Aryany" nan dai sukai ta hira cikin nishad'i- nishad'i da fad'a-fad'a. Sai misalin sha biyun dare suka yi sallama, sun rabu cike da kewar juna, da rashin jin dadin rabuwansu. Aryan da kyar barci ya d'auki shi, yanata tunani bar katai a kan Basma. itama ta b'angaranta da tunaninsa ta kwanta, cike farin cikin duk suka kwana. *Tofa anya kuwa? 🤔muje dai zuwaaa....* *Rahma Ce* [8/4, 5:17 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *9.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *Washe gari* Da misalin k'arfe hud'u na yamma, ya Aryan yayi wanka, sai ya d'auki d'aya daga cikin kanyan da Basma ta siya masa ya sanya, yayi kyau sosai da yake k'ananun kaya ne, sai ya d'auki hulan sanyi ya sanya a kansa saboda gashin kansa. Ya fito yace wa Umma sai ya dawo, Deeja tace "Yaya Aryan kayan nan ya maka kyau, amma meyasa ka sanya hulan nan, ai daka cire zaka fi kyau" murmushi yayi yace "Deeja banyi aski bane, kinga sumana ya taru shiyasa na sanya" murmushi tayi tace "hakane, to sai ka dawo" kana yasa kai ya fita. Tafiya yake bai san ina zashi ba, ya mik'e hanya sanb'al saida ya kai k'arshen layin su kana ya karya kwana, tafe yanke yana tunanin Basma da irin hiran da suka yi jiya, bai ankara ba wata mota ta taho a guje, gadan-dagan tawo kansa, ai ba shiri yayi tsalle ya koma jikin bangon wani gini saura kiris ya fad'a kwata, ya razana sosai, Basma dake cikin motan me zata yi inba dariya ba, da yake motan mai bak'in glass ne, Aryan ya kafa wa motan ido yana jiran wanda yake ciki ya fito, saida ta gama cin dariya sosai, kana ta bud'e ta fito, ido Hud'u suka yi sai ta kwashe da dariya, iya kuluwa yayi sai ya tamke fuska, cikin fushi yace "dama kece kika son bigeni da gan-gan ko? anya Basma ba kida Matsala a kwakwalwa ba kuwa" yana fad'an haka saita tsaida dariyanta tace cikin tsiwa "haba Yaya Aryan ya zaka kamanta ni da hauka, nifa da wasa nayi maka, tun daga nesa na hango ka nace bari na dan tsokane ka, ashe Yaya Aryan haka kake da tsoro" saita k'ara kwashewa da dariya, a yanzu shima dariyan yayi domin Basma ta kai mak'ura wurin shak'iyanci, tace "Yaya Aryan dama fa wurinka zani, ka rakani wani wuri" kallonta yayi tare da tsare gira yace "ni sa'anki ne, kije ki samu Deeja tana gida ita saita raka ki, amma ba dai ni ba" ai nan da nan Basma tayi fuskan tausayi tace "Yaya Aryan ni kai nake so ka rakani" yayi murmushi yace "to bazani ba" b'ata rai tayi kamar zatayi kuka tace "haba Yaya Aryan kayi hak'uri muje ba zamu dad'e ba" ganin zata fara masa kuka yace "to muje". Nan suka shiga mota suka fara tafiya, ta sanya wak'ar larabawa yana yi a hankali, ta juyo tace "Yaya Aryan kayi kyau amma abu d'aya ya b'ata wankanka" murmushi yayi bai tanka mata ba, ai bai aune ba sai yaje ta janye hulan kansa ta b'oye a dayan gefenta, da sauri ya juyo yace "wai ina wasa dake ne?" tuni Basma ta shagaltu da kallon sumansa saura kad'an ta buga motan dake gabansu, da sauri ta gyara tuk'in ta mai da hankali kan hanya, Yaya Aryan ya kwashe da dariya yace "Yarinya taga suma ba irin nata ba ta rikice" dariya kawai tayi bata ce komai ba har suka isa wurin shak'atawa. Parking suka yi duk suka fito, suka jera ba tare da sunce ma juna komai ba, shi dai binta kawai yakeyi, sun isa wani wurin da aka zagayeshi da furanni masu k'amshi, wuri sanyi ga iska mai dad'i, kujerune a ciki da table a tsakiya duk suka zaune, weta ne ya zo da sauri ya tambayesu abinda za a kawo musu, Basma tace "ice cream da shawarma da kuma drink" ta kalli Yaya Aryan tace "Yaya me za'a kawo maka" yace "duk abinda zaki ci shi zanci" murmushi tayi ta gaya ma weta ya tafi kawo musu. Suna fuskantan juna Yaya Aryan yace "dama nan wurin zaki kawoni" dariya tayi tace "eh, saboda in dan saka ka waye, dan naga kamar baka waye ba" hararanta yayi yace "kece dai baki waye ba da kike sanya k'ananun kaya ki fito ko ajikinki wai irin kin had'u" da sauri ta kalli jikinta tace "Yaya kana nufin banyi kyau ba ne?" "eh baki kyau ba saboda shigan bata dace dake ba" tace "Yaya Aryan, na sanya ne saboda naga a mota nake" riga da wando ta sanya sun kamata sai dai rigan ya sakko har gwiwanta amma duk shape d'in jikinta ya fito sai ta yi rolling da gale a kanta ta rufe gashinta" yace "eh, ai ba shiga bane na musulunci mace tayi ta fita" jikinta ne yayi sanyi tace "To insha Allah bazan sake yin shigan na fito ba, amma zan rik'a sanyawa a gida" murmushi yayi yace "da dai yafi miki" tace "Yaya Aryan sumanka tayi maka kyau, meyasa kake rufewa?" ya kalleta suka had'a ido sai da suka kalli juna na tsayin minti uku, kana ya sauke ajiyan zuciya yace "Basmaaa" sai duk jikinta ya mutu ta sunkuyar da kai k'asa, sai taji ta cigaba da magana, "bana son barin suman, kuma yawan askewa yana k'ara yawansa, shiyasa nake yawo da hula, saboda in mutane suka gani suna yawan min magana akai" murmushi tayi tace "Yaya Aryan dan Allah karka aske, zan siyo maka mayuka na maza, da zaka rik'a gyarawa, wlh har sheki zai rik'ayi, ba kaga yanda mazan India suke yi bane" murmushi yayi yace "ni Basma bana son sumar dan a takure nake" marairaice fuska tayi tace "to ko zaka aske, karka aske duka ni ina son ganinka dashi" hararenta yayi, kan yayi magana an kawo musu shawarman. Sai wayar Basma ce ta d'auki k'ara, da sauri ta d'auka ta kara a kunne, tace "My Shureym" saita shagwab'e fuska ta fara shagwab'a, "bayan kasan ina missing d'inka, shine duk yau baka kirani ba ka manta dani" ta b'angaren Shureym kuwa ya shiga lallashinta. Aryan zuciyansa ne ke dukan uku-uku hankalinsa ya tashi, amma saiya dake, ya cigaba da cin shawarman, amma abin mamaki kamar yana cin magani sam baya jin dad'in sa, sunkuyar da kai yayi k'asa, zuciyansa nayi masa zugi, numfashinsa yana fita da k'arfi, dakiya kawai yayi. Basma sun d'auki tsawon minti sha Biyar suna wayan, daga bisani suka yi bankwana ta kashe wayar. Ta kalli Yaya Aryan tace "Yaya kayi hak'uri na d'auki waya ban nima izini ba" d'agowa yayi idonsa ya kad'a ya d'anyi ja, sai yayi mata murmushin yak'e yace "karki damu bakomai" murmushi ta mayar masa, ta mik'a hannu ta d'auko sauran shawarman da ya rage ta soma ci ko ajikinta. Sam bata lura da sauyawan yanayin sa ba, saida ta gama tace "Yaya Aryan" ya d'ago ya kalle, tace "bari muyi salfee mana?" murmushi gefen baki yayi yace "ni bana hoto" shagwab'e fuska tayi tace "ni dai dan Allah muyi" bata jira me zaice ba ta mik'e ta zo bayanta ta tsaya, shi kuma yana zaune, aiko ta kashe musu photo har uku, shi dai fuskansa ba yabo ba fallasa, gaba d'aya zuciyansa a takure yake, tace "gaka kuwa yanda mukayi kyau?" ta nuna masa, ya kalla shima kanshi hoton ya ma kyau yace "yayi kyau" tace "Yaya muje gida yamma yayi sosai". Bayan sun kama hanya, ta ciro hulansa ta bashi tace "Yaya Aryan, gobe in Allah ya kaimu zanzo mu k'ara fita" murmushi yayi yace "Allah ya kaimu" haka ta sanya wani wanka da music na soyayya, sai bin wakar take, shi ko kwantawa yayi a bayansa yana sauraren wak'ar da muryarta ,gaba d'aya ya shiga wani duniya wanda shi kanshi bai san wani irin duniya ya lula ba. Ta sauke shi suka yi sallama, kana ya wuce cike da damuwa a zuciyansa, itama ta wuce cike da farin cikin a zuciyarta mara misaltuwa. Da dare misalin k'arfe goma da rabi, Basma ta kira Yaya Aryan, yana kallon kiran yak'i d'auka, ta kira shi ya kai sau goma amma yak'i d'agawa, haka nan yaji ba zai d'auka ba, domin shak'uwar da zuciyansa yake da Basma, ya fara bashi tsoro kuma ga dukkan alamu ya soma shiga wani hurumi da ba nashi ba, dole ya d'auki matakan kaucewa damuwa. Basma kuka ta shiga yi hawaye wannan na bin wannan, iyaka damuwa ta shiga, da kyar barci da d'auketa. Haka ma ta b'angaren Yaya Aryan, k'arshe ma tashi yayi ya gabatar da sallan nafila yayi Addu'a akan, Allah ya k'are masa zuciyansa da irin abinda ya soma raya masa game da Basma. *Washe gari* Basma da ciwon kai ta tashi, ta samu ta karya tasha magani sannan ta koma barci. Ta wurin Yaya Aryan kuwa ya samu sassauci game da abinda yake ji, ya shirya ya tafi kasuwa kamar yanda ya saba kullun, amma a k'asan zuciyansa yana tuna masa hiran Basma da Shureym sai damuwa ya ziyarce shi. Da misalin k'arfe biyar ya dawo daga kasuwa, da sauri yayi wanka ya shirya ya fita, unguwar ya bari gaba d'aya saboda baya so su had'u da Basma. Ta b'angarenta kuwa ta zo tayi parking in da suka had'u jiya, tayi ta kiran wayan ba'a d'auka ba, kuma ta jira shi bai zo ba har kusan k'arfe shida na yamma, abinda bata sani ba Aryan yana hangen motanta ya b'oye a wani shagon aski, hakanan yaji tausayinta kamar ya fito sai kawai ya basar, haka ta hak'ura zuciyarta na mata zafi ta tuka motan a hankali, idonta na zubda hawaye, ta shiga damuwa na rashin zuwan Yaya Aryan, a haka ta isa gida kamar mara lafiya. Shima Aryan cikin damuwa ya wuce gida bayan tafiyarta, koda Umma ta ganshi ta tambaye shi ko lafiya? yace mata kansa ke ciwo, sai tayi masa sannu. Yau da wuri ya dawo gida ya kwanta, yau ma yak"i d'auka wayarta, a haka ko wanne ya kwana cikin damuwa. *Washe gari Monday* Basma da sassafe ta fito tazo gidansu Deeja, ta samu Deeja ta shirya suka gaisa da Umma, Aryan yana d'aki yana jinsu amma yak'i fitowa, dauriya Basma tayi tak'i tambayar ko yana nan, suka yiwa Umna sallama suka wuce University dake cikin Abuja, da yake ansan da zuwansu basu sha wani wahala ba wajen yin registration d'in, kuma dama president yasa hannu, Deeja an d'auke ta ba tare da zana wani exam ba, ta samu Medicine b'angaren mata (gynecology). Zuwa k'arfe biyu sun gama komai, sai suka kama hanyar gida. B'angaren Yaya Aryan, ya tafi company su Basma, ya had'u da Yaya Naufal kamar yanda Yaya Ahmad ya gaya ma Naufal d'in, Yaya Naufal yayi masa interview, ga mamakinsa duka Yaya Aryan ya amsa masa, gashi dai ba digree gareshi ba amma ya amsa masa duk tambayoyinsa. Ya duba takardunsa sosai, cikin k'asaita da mulki yace "sunana Naufal, a yanda na gwadaka kuma na duba takardunka gaskiya komai yayi yanda muke so, mun d'auke ka aiki, sannan bayan kamar watanni zamu turaka ka k'aro karatu kayi degree da masters, ga wannan kud'in kuma ka samu ka siya kaya na zuwa office, dole ne ka rik'a shiga mai kyau domin zaka rik'a ganawa da manyan mutane, office d'inka shine na b'angaren computer, kai ne mai shigar da komai in an fitar da kaya ko an shigo da su, da fatan ka fahimta" Yaya Aryan cike da farin ciki yace "na fahimta, nagode Allah ya saka da alkhairi" duk wannan bayanin cikin harshen turanci suke magana, kana Yaya Naufal ya rakashi katon office d'insa, mai d'auke da kujeru na alfarma da katon table, ga AC, ga fridge, kai har toilet akwai a ciki, komai dai normal, Yaya Naufal ya gama nuna masa komai ya fice, Yaya Aryan ya zauna kan kujeran table d'in ya juya yana kallon kud'in da aka zubama office d'in, sai hawaye ya soma zarya a kuncinsa, farin ciki da begen son ganin Basma ne ya bijiro masa, ba dan Allah yasa sanadin ta ba, da ba zai tsinci kansa a irin nan wurin ba. Suna isa Basma ta fad'a d'akin Yaya Aryan ta kwanta bisa katifansa, cikin kankanin lokacin barci ya d'auke ta. Deeja ce ta shigo taga tana barci, taso tashinta ta koma d'akin su, amma saita kyaleta ta cigaba da barcin, ta koma wurin Umma tace "Umma Basma fa barci takeyi, da zan tasheta ta koma d'akinmu saina barta" Umma tace "kyaleta ta kwanta ta gaji ne, kinsan yaran masu kud'i basu saba da wahala ba, kuma ma ai d'akin Aryan yafi namu gyaruwa zata fi jin dad'in barcin anan". Khadija tace "hakane kuma" sai suka cigaba da aikin su na girki, Umma na rangad'a musu, tuwon shinkafa miyar kub'ewa d'anya wanda yaji nama. Da misalin k'arfe uku da rabi, Yaya Aryan ya dawo gida daga company su Basma, ya zauna bisa tabarma a tsakar gida, ya gaisa da Umma, kana yace "Khadija kun gama registration d'in?" tace "eh, Yaya mun gama komai, Monday mai zuwa zan fara zuwa d'aukan lectures" yace "masha Allah, Allah ya taimaka" duk suka amsa da "Ameen", Umma tace ya kuka yi ne a wurin da kaje?" murmushi tayi yace "Umma komai Alhandulillah, an min interview, kuma na ci, musamman suka bani office nawa ni kad'ai, nine zan d'inka shigar da komai na company" kud'i ya ciro daga aljihunsa yace "wannan kud'in budi D'ari biyu ne, sun bani na siya kayan sawa kawai na zuwa office, saboda zan d'inga ganawa da mutane, masu amsan yakan company" baki Umma ta bud'e tace "ikon Allah, wannan Abu haka, gaskiya ba abinda za mucewa Basma da Yayanta sai Allah ya saka musu da gidan Aljanna" duk suka amsa da "Amin" Yaya Aryan yace 'gobe insha Allah zan fara zuwa aiki, albashi na kuma dubu d'ari biyu duk wata" ai Umma sai kabbara, ta yiwa annabi salati s.a.w, hawayen farin cikin ta soma fiddawa, Deeja tace "Umma ba kuka za kiyi ba, waraka Allah ya kawo mana dan haka saimu gode masa". Nan ya mik'e ya shiga d'akinsa, ai sai yaci karo da Basma tayi d'ai-d'ai bisa godonsa, gashin kanta ya baje a bayanta, da gani barcin gajiya take yi, murmushi kawai tayi yace a ransa "Basma rigima, wato ba tad'a wurin barci sai d'akina" Wasu kaya ya d'auka, ya fito ya shiga bayi, Basma da tun shigowarsa ta farka tabi bayansa da kallo tana murmushi. Bayan ya fito daga wankan ya wuce d'akin Umma ya sauya kaya, masallaci ya wuce dan yin sallan La'asar, suma su Umma suka gabatar da nasu sallan. Basma ta fito tayi alwala ta shiga d'akin Umma tayi sallah, anan Deeja ta kawo masu tuwo suka ci tare, bayan sun gama ta shirya zuwa gida ta yiwa su Umma sallama ta fito, Deeja ta rakata mota ta wuce. Tafiya take a hankali zuciyarta cike da son ganin Yaya Aryan, aiko tana yin kwana ta hangeshi tsaye inda ta d'auke shi rannan, farin ciki taji a zuciyarta kana ta d'aure fuska tamkar ba ita ba, ta k'arasa tayi parking mota, ba tare da ta ce masa uffan ba ya bud'e motan ya shiga, yana shiga ta tada motan suka wuce ba wanda wace wani Abu, ko wanne da abinda zuciyansa ke saka masa. Yaya Aryan ya katse shurun yace "Basma" juyiwa tayi ba tare ta tace komai ba, sai hawaye ya fara zuba a idonta, ta juga ta cigaba da tukasu.... *Hmmmm wannan abu ya fara bani tsooloooo😉😂 koya zasu kwashe...🤔* *Rahma Ce* [8/4, 5:19 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *10.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Wani wajen shak'atawa ta kaisu ba wancen na farko ba, sun samu k'asan wata bishiya suka zauna kan kujeru, ga table a tsakiya, an kawo musu drinks ne da ruwa, Basma ko kallon Yaya Aryan batayi ba kuma tak'i magana, jikin Yaya Aryan yayi sanyi sai ya kwantar da murya yace "Basma fushi kike dani?" kallo d'aya ta mishi a fak'aice sai ta kauda kai gefe, murmushi yayi yace "haba k'anwata ki daina fushi dani mana, bana son ganin b'acin ranki, burina in saki farin ciki har k'arshen rayuwana" d'agowa tayi suka had'a id, idonunta fal da hawaye suna gabda zubowa, da sauri Yaya Aryan ya tara hannunsa a fuskanta domin hawayen ya sauka bisa tafin hannunsa, cikin wani irin murya wanda shi kanshi baisan yanada ita ba, mai dad'i da zak'i yace "Basma karki min asaran hawayenki ya kai ga zuba a k'asa, ba tare da na sharesu ba, ki yafe ma Yayanki, ba zai zake b'ata miki raiba" murmushi tayi na jin dad'i, saita runtse idonta hawayen suka sauka bisa hannunsa, Yaya Aryan ya koma ya zauna, suna kallon juna ya d'aga hannunsa zuwa bakinsa ya lashe digon hawayen ya shanye, Basma saita tafa masa rap rap rap, cike da farin ciki tace "wow, Yaya Aryan yau kawai na tabbatar da cewa ka d'aunke ni jinin jikinka kuma 'yar uwanka" murmushi yayi yace "ke ce baki sani ba amma tun ranar da kika bani hak'uri na d'auke ki a haka, kawai dai na d'an nuna miki ni din Namiji ne" hararansa tayi na wasa tace "ohoo dama shiyasa ka ke basar dani domin kaga rauni na ko, amma ba komai tunda ka fahimci yanda na d'auke ka" dariya yayi yace "sosai na sani, Basma kin zama haske a rayuwana da Ahalina, sanadinki Umma da Deeja da Ni kaina muna farin ciki, kin mana abinda ban san dame zan biya ki ba face Allah ya baki miji nagari, ya kuma baki Aljannah" murmushi tayi najin dad'in abinda yace har cikin taranta, Abu d'aya ne taji ya mata wani iri lokacin da ta tuno da Yaya Shureym, tambayar kanta ta shiga yi, "yanzu inna yi aure shikenan Yaya Shureym ya rabani da Yaya Aryan kenan?" Nan danan taji zuciyarta ya mata wani iri, ganin ta lula duniyar tunani, sai Yaya Aryan ya matso da fuskansa ya hura mata iskan bakinsa, nan take ta dawo hayyacinta, sai duk suka zubawa juna ido, suna baiwa junansu wasu sak'onnin cikin kwayar idonsu, suna karantar wa juna sirrin zuciyansu, sun d'auki tsawon minti biyar kana Yaya Aryan ya kashe mata ido d'aya, da sauri ta sunne kai k'asa alaman jin kunya, a gaskiya duk wanda ya gansu a wannan yanayin, babu abinda mutum zaice illa Aryan da Basma masoya ne. Yaya Aryan ya d'auko kujeransa ya dawo kusa da ita, da muryansa mai dad'i yace "k'anwata meyasa ba kya jin kunyar kallon kwayar ido na? ke ce mace ta farko da take iya kallon ido na harta karanta wasu sirri dake ciki, domin ido naya d'aya daga cikin abinda kewa mutane kwarjini" murmushi tayi kawai ba tace komai ba, ya cigaba da cewa "Amma na fahimci idanunmu sun fara sanin sirrin dake cikin juna, kema haka idonki yake kamar nawa" Basma sunkuyar da kai tayi k'asa, bata tab'a jin nauyi ko kunyar wani namiji ba sai akan Yaya Aryan, wasa take da yatsun hannunta, ta kasa motsi mai k'arfi, gaba d'aya tanajin ta a cikin sabon yanayi da bata tab'a jiba game da wani d'a namiji sai akan Yaya Aryan, a yanzu kunya da kwarjininsa ke tasiri a jikinta, Yaya Aryan ya kira sunansa yace "Basma kinyi shuru ko yau ba kya jin tsokana ne, magana da kuma fad'a?" murmushi tayi tace "ai Kaine kake magana, tun d'azu kake wasu bayanai da ban fahimcesu ba" murmushi yayi yace "kina so ki sansu?" tace "eh ina so" yace "to d'ago fuskanki ki kalleni, zaki fahimci abinda nake nufi acikin ido na" ta d'auki minti d'aya kafin ta d'ago fuskanta, suka had'a ido ko wanne fuskansa da murmushi, sakonni suke zubawa zuciyoyinsu, ko wanne idonsa yayi tamkar mangyada aciki, bugun zuciyarsu yana buguwa a hankali, zan iya ce muku suna bugawa kusan a tare, idonun su yana k'eftawa a hankali tamkar ba zasu rufe ba, numfashinsu yana fita a hankali kamar basa cikin duniyarmu, sun d'auki tsawon minti bakwai, kana Basma ta yi ajiyar zuciya ta sun kuyar da kai, shima Yaya Aryan ajiyan zuciya yayi, cikin wani irin murya kamar yana rad'a yace, Basma kin fatimci abinda nake nufi yanzu?" murmushi tayi kawai ba tace komai ba. Wayar Basma ce tayi ringing, Yaya Shureym ne ya kirata, a wannan lokacin sai taji sam bataji dad'in kiran nasa ba, kamar ba zata d'aga ba, saita d'auka suka gaisa, yau hiran nasu sama-sama suka yi, hakanan taji bata son magana dashi, bayan ta gama ta kashe wayar juyowan da zatayi sai taga ba Yaya Aryan a gun, gabanta ne ya fad'i, ta fara tunanin ko ta b'ata masa raine akan d'aukar wayan, mik'ewa tayi ta hangoshi can yana wasa da ganyen wata bishiya, wurin ta k'arasa tace "Yaya Aryan" da sauri ya juyo idonsa ya kad'a ya d'anyi ja, kan ta kuma magana ya d'aura hannunsa bida leb'ensa yace "shiiii, kin gama wayan?" cikin yanayin rashin jin dad'i tace "eh Amma kayi hak'uri" murmushi yayi yace "hak'urin me zanyi, ai baki laifi ba, da mijinki kike waya fa to me zaisa raina ya b'aci" gabanta ne taji ya fad'i "dammm", hakanan taji maganar da yayi bai mata dad'i ba, tace "Yaya Aryan ba mijina bane fa kawai dai saurayina ne" murmushin yak'e yayi yace "Amma ai aure za kuyi" yana gama fad'an haka yayi gaba ya barta a tsaye, Basma ji tayi zuciyarta ya mata ba dad'i, hawaye ne ke son zubo mata, da sauri tabi bayansa tasha gabansa tace cikin shagwab'a. "Yaya hawayen zai zubo" dariya ta bashi Amma ya dake, yace me ya kawo hawaye, keda kika gama shan soyayya da mijinki" ai tuni hawayen ya soma zuba, sam bata k'aunar Aryan na fad'an haka, matsawa yayi gab da ita cikin salon muryansa mai kashe jiki yace "wlh karki kuskura hawayenki ya sauka k'asa, domin saina mugun sab'a miki, hawayan Basma mai daraja ne a gun yayanta Aryan." Da sauri ya tara hannunsa biyu yace "duk lokacin da kike jin kuka koda bama tare ki rik'e kukan, sai mun had'u kiyi shi akan hannnu na, domin in maida shi cikina". Murmushi tayi tace "tom na bari Amma saika daina cemin Yaya Shureym shine Mijina" dariya yayi sosai yace "dama a kan shi zaki min asaran hawayanki tom karki k'ara" yatsansa yasa ya lakuto hawayenta ya sanya a baki yasha, saida ya raba fuskan da hawaye kana yace "muje gida". Sun kama hanyan zuwa gida, Basma tace "Yaya Aryan wlh da za'a barni dana kwana a gidan ku" Murmushi yayi yace "saboda me zaki kwana mana a gida?" "saboda kawai in tashi inga Yaya Aryan, in nayi kuka ya shanye min hawayena" dariya yayi sosai yace "tom bazan k'ara sha ba, kuma mun b'ata" fuskar tausayi tayi yace "wlh bamu b'ata ba, muna nan a tare, Yayana ba fad'a" duk suka kwashe da dariya. Cikin farin ciki da nishad'i suka isa gida, a wannan rana kamar karsu rabu ko wanne yana jin kewar d'an Uwansa. Tun daga wannan rana Yaya Aryan da Basma suka d'inke, rana d'ai-d'ai ne basa fita wurin shak'atawa. Aryan ya kama aiki gadan-gadan wanda a sanadin zuwansa company ya k'ara hab'aka, Deeja kuma tana ta zuwa makaranta, a yanzu soyayya take sosai da Yaya Ahmad a waya, wani lokacin yakan zo hira, Basma ta rako shi, itama dan su sha hira da Yaya Aryan. Umma da Yaya Aryan sun san soyayyan Yaya Ahmad da Deeja, abinda ke basu tsoro shine, kar gaba iyayen su Basma suk'i yarda ya aureta, domin su talaka ne, Yaya Ahmad ya gyarawa su Deeja gida, anyi fenti an gyara gidan yayi kyau, an zuba musu sabon furniture's. Yaya Aryan ya siyan musu kaya da komai na abincin, da kud'in albashinsa na farko dana biyu, yanzu ko sun fita da Basma shi yake musu siyayya, ya sauya waya ya mai dama Basma nata. Shak'uwa mai k'arfi ya shiga tsakaninsu, Basma ba tada abokin hira sai Yaya Aryan, video call, charts da kuma zuwa wurin shak'atawa, duk tare suke komai, gaba d'aya ta sauyawa Yaya Shureym, wayansa da kyar take d'agawa, shima da yake yanada wacce yake so sai ya daina damuwa da ita, dama shi abinda yasa ya rik'e wuta, ko zai tusa mata son shi ya samu yana rage zafi da ita. Bayan wata uku Basma da Yaya Aryan lamarinsu ya wuce tunanin kowa, basu tab'a furtawa juna kalmar So ba, Amma kuma idanun su, sassan jikinsu, jini, b'argo, da tsoka sun gama zama d'aya, sun tabbatar da in ba d'aya ba rayuwa, amma duk da haka zuciyansu yak'i ya basu damar yarda da abida jikinsu ke fad'a musu. Yau ya kama Lahadi, Yaya Aryan da Basma suna zaune bisa dadduma a wurin shak'atawa, hira suke na nishad'i, wayar Basma ya d'auki k'ara, cikin rashin damuwa ba tare da ta duba mai kiran ba saita d'auka tare da sanya hands free, muryan Yaya Shureym taji yace "My Basma nazo yanzu ance kin fita kina ina ne? ni fa yau na zo muyita ta k'ara, gaba d'aya kin sauyamin kin shareni, kin barni da missing d'inki, Basma ina cike da shauk'inki mai yawa, dan Allah Basma ki bani had'in kai ko da sau d'aya ne muyi rayuwa, wlh bazan bari kowa ya sani ba, kuma kinga Aure za muyi, inma kina tsoro miyu a k'asar nan saimu fita England muje can mu huta" Tsoro, fargaba, damuwa ne suka ziyarci Basma, wani zafafan hawaye ke fita a idonta, jikinta ya d'auki rawa, sam bata zaci abinda zai ce mata ba kenan har tabar wayan a hands free, Yaya Aryan mik'ewa Yayi da sauri ya fizge wayan ya bugata da k'asa, komai na waya ya tarwatse, Basma toshe kunne tayi saboda k'aran fashewan wayan, Yaya Aryan sai huci yake kamar wani zaki, sanya takalmi yayi ya fara tafiya, ya rasa ina zai sanya ransa yaji sanyi, ya d'anyi nisa a tafiyan ya shiga cikin mutane, da gudu Basma ta ruga ta rungumeshi ta baya tana kuka, tace "Yaya Aryan wlh ban tab'a yin wani Abu ba, Yaya Shureym ya sha kawo min farmaki da irin wannan maganar amma nak'i amincewa da k'udurinsa, wlh tun lokacin ya fara fita a raina ni sam bana Sonsa" Aryan ya b'abb'are hannunta daga jikinsa, ya juyo da ita gabanshi ya tsinketa da kyakkyawan Mari guda biyu, nan da nan hankalin mutane ya dawo gunsu, Ya matsa gab da ita yace "Basma kalli ido na ki gayamin abinda kika gani a ciki yanzu" idonta na zubda hawaye ta dafe kumatunta tace "Yaya Aryan kayi hak'uri wlh ban aikata komai ba" cikin fushi da fad'a ya daka mata tsawa yace "Basma me kika gani a idona ki gayamin" tace "idonka yayi ja" yace "Basma kukan zuciyana ne ya bayyana a idona, kina son ki kasheni ko" ya k'arasa maganar muryanshi na rawa, ido ta zaro waje tace "Yaya Aryan ni bazan kasheka ba" lumshe ido yayi ya bud'e, cikin kasalalliyan murya da rauni yace "Basma ina sonki, ina k'aunarki" idonsa ne ya kawo kwalla yana gabda zubowa, sai Basma ta tara hannunta tace cikin kuka "Yaya Aryan nima ina sonka, ina k'aunarka, kaine rayuwata, karka min asaran hawayenka, wanda ban tab'a ganinsa ya fitaba sai yau, ka gau-gauta mayar min da sauran ka adana min su, sai lokacin farin ciki ka fiddamin su" sai hawayen ya d'iga a hannunta, bakinta takai ta shanye su, hannunsa ta kama tana jansa suna tafiya, Yaya Aryan binta yayi da kallon mamaki, gaba d'aya Basma ta bashi mamaki da maganarta. Mutunan dake gurin sai suka fara tafa musu, lallai sun bada salo da kowa yayi sha'awarsu, haka suka bar wurin su ko ajikinsu, kowa na fad'an albarkacin bakinsa. Bayan sun kama hanyan gida Yaya Aryan yace ta samu guri tayi parking za suyi magana, bata masa musu ba ta samu guri tayi parking, yace "Basma ina so ki sani tun ranar dana fara tozali dake da kika tofamin miyau, wani Abu ya d'arsu a zuciyana akanki, a da ina tsammanin k'iyayya ne, sai daga bata na gane ashe So ne, ban tab'a jin d'an d'anon So akan wata mace ba, sai akanki Basma, dan Allah Basma ki kulamin da kanki da rayuwanki, domin kece rayuwata" Farin ciki ne ya lullub'e Basma, yau ta gasgata abinda gan-gan jikinta yake gaya mata akan Yaya Aryan, tace cikin jin kunya "Yaya Aryan karka damu, insha Allah zan kula maka da kaina da kuma mutunci na, kai ne rayuwata nima, kai kad'ai nake gani a idona na kasance cikin farin ciki, dan Allah ka rik'e min Amanar zuciyata, domin kaine mutum na farko da ya bud'e shafukan So da K'auna a ciki, kuma har abada kai ne mutum na farko kuma na k'arshe ba na biyunka" Murmushi yayi yace "Kinsani farin ciki Murmushi na, amma fa ina da kishi, sai ki san yanda za kiyi da Shureym" murmushi tayi tace "my Aryan karka damu zan gayawa ya Ahmad komai". Cikin farin ciki suka k'arasa gida, yau Yaya Aryan ji yake ya sauke wani abu mai nauyi a zuciyansa, haka ma Basma yanzu ta tabbatar Aryan nata ne. *Da dare* Basma ta tafi wurin Yaya Ahmad ta sameshi yana aiki a system d'insa, sai ta gaishe shi, kana ta samu guri ta zauna tace "Yaya Ahmad nazo muyi magana ne" cikin kulawa yace "ina jinki Basma" gyara zama tayi ta soma gaya masa duk abinda Yaya Shureym ke gaya mata, hankalinsa yayi matuk'ar tashi, nan ya shiga niman number Shureym, amma bai shiga ba, cikin yanayi na damuwa ya shiga yi mata fad'a akan meyasa bata gaya da wuri ba, fad'a da nasiha yayi mata sosai kana yace "ina ganin zan gayawa su Momy a sanya bikin kawai ayi kowa ya huta" da sauri Basma ta kalli Yaya Ahmad bakinta har yana rawa tace "Yaya Ahmad wlh bana sonsa bazan aureshi ba na tsaneshi" ta k'arasa maganar cikin damuwa... _*Su Basma da Aryan an shiga lanbun masoya, gaskiya fa salon soyayyanku ya bada kala, koya kuka ce masu karatu...*_ *Rahma Ce* [8/5, 6:45 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *11.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Yaya Ahmad yace "Basma auren ki da Shureym dole za'ayi shi, tunda iyaye sun riga sunyi magana, kuma da an d'aura shikenan zai daina wannan iskancin nashi" hawaye ne ya sauka a kuncinta tace "Yaya Ahmad bana fatan auren Yaya Shureym ni ina da wanda nake so, kuma in ba a bani shima wlh Yaya zaku rasani, domin zan mutu" a razane ya kalleta yace "Basma kina da hankali kuwa? waye kike So haka? waye shi kuma d'an gidan waye?" Cikin kuka tace "ni Yaya Aryan nake so, kuma in ban aureshi ba zan iya mutuwa" a razane Yaya Ahmad ya mik'e tsaye yace cikin kad'uwa, "a'a Basma, a'a Basma, karki ce za kiyi sanadin rabuwar family d'inmu, kinsan yanda Shureym yake a wajenmu, yaron Yayan Ammi ne, karki ce za kiyiwa Ammi haka, plss ki d'auka mafarki kike da sanin Aryan, ki gaggauta cire Aryan a ranki" a razane ta d'ago ta mik'e tsaye tace "Yaya Ahmad bazan iya ba, wlh Yaya Aryan nake so" da gudu ta fita daga d'akin tana kuka, lanbun gidan ta nufa taje ta zauna, kuka take kamar ranta zai fita ba tare da sauti sosai ba, Yaya Ahmad cikin sauri ya isketa a gun, dan yasan tabbas ba zata koma part d'in Ammi ba a haka, zama yayi gefenta ya kama hannunta shima a zuciyarta yana gasgata lallai Basma da Aryan ta dace, domin Mutumin kirki ne ga Addini da sanin yakama, a d'an zaman da yayi dashi baiga wani aibu a gunsa ba, sai dai matsala d'aya ne, su Ammi ba zasu yarda Basma ta kawo wani Mijin ba, sai Shureym, sannan kuma Aryan ba d'an kowa bane shi, baya tunanin su Ammi zasu yarda ta auri talaka. Yace "Basma nima ina son ki auri Aryan, amma kin san hakan bazai yuwuba a wurin su Ammi" cikin kuka tace "Yaya zai wuyu tunda ina sonsa, kai zaka taimaka na aureshi kamar yanda zan taimaka maka ka auri Deeja" nisawa yayi yace "karki damu zanyi wani Abu a kai, ki bani lokaci" sassauta kukan tayi ta share hawayenta tace "Nagode Yaya Ahmad, Allah ya mana jagora" "Ameen" yace, kana ya rakata part d'in Ammi ya koma d'akinsu cike da tunani barkatai, da damuwa fal zuciyansa. Lallai yana tausayin Basma kuma yana sonta fiye da kansa. dole yayi k'ok'arin sama mata mafita, da wannan tunanin har barci ya kwashe shi. *Bayan kwana biyu* Basma sun cigaba da soyayyansu, wanda a yanzu basa b'oyeta ko a gaban waye, Umma ta kad'u sosai data fahimci haka, kiran Yaya Aryan tayi, ta masa fad'a akan yabi a hankali Basma ba tsaran aurensa bane, dole ya iya takunsa, hankalin Aryan ya tashi yace "Umma wlh ina son Basma ki mana addua, domin Addu'anki yana da matuk'ar tasiri a garemu" Umma tayi ajiyar zuciya, ta sanya musu Albarka, can kasan zuciyarta tana tausayawa yaranta, domin tasan iyayansu Basma ba zasu yarda da auren su Deeja ba, saboda su d'in ba kowa bane, talaka ne futuk. Haka Yaya Shureym ya k'araci zama a gidansu Basma bai samu fuska a gunta ba, ko ya kirata bata d'agawa, haka ya tattara ya koma Kano. *To bari na waiwayi wajensu Leema da Meena.* Leema tana kano a takure take, domin bata samun sakewa sosai kullun tana gida, in zata fita saida kuyangi da dogarai, hakan yasa taji duk zaman Kano ya gundureta, ta fata tunanin komawa Abuja, in sha'awarta ta motsa kamar za tayi hauka, wataran a sace take fita tayi b'adda kama taje su had'u da Jalal, su gama shek'e ayarsu ta dawo gida a gau-gauce. A daddafe ta iya kaiwa har wata hud'u a Kano, yanzu ta gama shirya kayanta da yawa domin komawa Abuja, in kuma ta koma bata tunanin dawowa, sai dai ta rik'a zuwa tana gaishe da iyayenta. Haka ma b'angaren Meena, Alhaji Ibrahim mahaifinta mutum ne mai sanya ido sosai kan yaransa, hakan ne yasa Meena bata fita saida dalili mai k'arfi, Yaya Jamal ya sanya mata ido shima domin yaga take-takenta akwai rawar kai, Meena in son shan syrup ya motsa mata, rufe kanta take yi a d'aki taita kuka tana buk'atar abinda zata sha, dakyar barci ke d'aukanta, in ta farka shikenan ta dawo dai-dai, hakan yasa ta samu wani shed'ani d'an unguwarsu, suka tsadance yana siyo mata syrup a sace ya kawo mata, sai ta bashi kud'i mai yawa, haka zatai ta maneji dashi harya k'are, gaba d'aya zaman Kaduna ya gundureta, saita soma had'a kaya dan komawa Abuja gaba d'aya, ita sam ba zata zauna a Kaduna ba, waya sukayi da Leema, suka gayawa juna matsalansu, nan take suka yanke shawaran barin gidan iyayensu a gobe in Allah ya kaimu, domin ci gaba da rayuwan freedom da suka fara a England. *Washe gari* Da safe Meena tayi sallama da iyayenta, dama ta riga ta sanar musu zata koma Abuja, jirgin k'asa tabi, daga gidan president aka aiko mota ya d'auke ta. Leema ma haka ta sauka a airport, mota daga gidan President yazo ya d'auketa. Dukansu suna zaune a falon Ammi suna shan farfesun kifi, Ammi ne ta fito tace "Leema wai ku baza ku zauna guri d'aya ba, baku nan baku can, ni dai naga alama aure kuke so, bari anjima zan samu president in sanar masa, sai a sanya rana mu fara shiri kowa ya huta" bata rufe baki ba Leema tace "taf wlh Ammi aure ba yanzu ba, munyi k'anana" Meena tace "gaskiya kuwa aure sai mun kai 30yrs" Basma dai murmushi tayi kawai domin ita a yanzu auren take so amma fa da Aryan d'inta, Momy ce tace "lallai yaran nan da sauranku, wlh baku isa mu zuba muku ido ba har kukai lokacin da kuke so, aure kam kuma fara shiri" tana gama fad'a ta mik'e ta wuce d'aki, turo baki su Meena sukayi, su a dole basa so, Basma ce ta kallesu tace "dama dai kun bar wannan shirman, domin dai aure shine riban ko wace mace" tana gama fad'a ta mik'e ta wuce d'aki tana murmushi, kallon mamaki suka bita dashi, daga bisa ni suka tafa Leema tace "nifa Basma ta sauya, ko ke baki ga a lama ba? Sam ba ji da kai, ba shan k'amshi, duk wani mulki ta aje, anya babu wani abu a k'asa kuwa?" Meena tace "ita ta sani dai, dan ni ba zanyi aure yanzu ba" haka suka mik'e tare, d'akin Basma suka Shiga sun sameta bisa gado tana chart, ba wanda ya kulata suka haye gadon suka fara hiran yanda suka yi missing zuwa clup, yau sunyi masa shiri na musamman, Basma na jinsu bata ce musu k'ala ba. Bayan sallan la'asar suka shirya sai gidan hutun Basma, Basma bata bisu ba, sun wuce tare da escot, ita kuma ta wuce wurin masoyinta, suka had'u a in da suka saba had'uwa, suka wuce wurin hutawa domin su samu yin hira mai dad'i. Sai misalin k'arfe shiga na yamma suka yi sallama da Yaya Aryan ta wuce gidan hutun da sauri, domin tana son yin wanka a swimming pool, dan ta kwana biyu bata yi ba. Tana isa ta samu su Meena a wajen, haka itama ta shiga ta soma wankanta, Leema ce tace "Besty wai yane naga duk kin sauya ne, ko akwai abinda ke damunki ne?" murumushi tayi a ranta tace "soyayyan Aryan ya sauya ni" a zahiri kuma tace "Me kika gani besty, ina nan a Queen Basma kamar yanda kuka sanni" Meena ce tayi caraf tace "ba wani nan, da akwai abinda ke going wanda bakya so ki gaya mana, sam ban gane sauya wanki akan zancen aure ba, ko kuma soyayyar Yaya Shureym ke fizgarki" nan take Basma ta b'ata rai, bata ce komai ba, ta cigaba da wankanta, Leema da Meena suka had'a ido sai suka kwashe da dariya, hiransu suke bata tanka musu ba, harta gama ta bar su ta nufi d'akinta. Magrib ya gabato ba halin yin rawa, shiyasa ta wuce d'aki dan gabatar da Sallah akan lokaci. Bayan k'arfe takwas na dare kamar yanda suka saba fita, yau ma cikin shirin doguwar riga masu fidda tsiraici su Leema suka sanya, Basma harta d'auko wata yalolon riga wanda duk rabin cinyarta a waje yake, sai zuciyarta ya karaya saboda da tunawa da tayi da Yaya Aryan, dole yasa ta maida ta d'auko wata doguwar riga mara tsagu, kuma mai kauri ta sanya, duk da haka tana jin wani iri, zuciyarta na gaya mata kamar taci amanar Yaya Aryan, haka dai ta shirya, ta taje sumanta ta sakeshi a bayanta, ta d'aura hular Queen, sai ta fito a Queen Basma tamkar yanda take a da, tayi kyau sosai, haka sukaita d'aukar photo kafin nan suka wuce. Kamar yanda suka saba, Leema dama Jalal yana Abuja, cikin k'ank'anin lokaci ya bayyana, yazo suka tafi cikin hotel, Leema kuwa cikin group d'in su na mashaya ta nufa, nan suka soma ihu da kalamai masu dad'i, da irin missing d'inta da suka yi, Basma dai yau a d'arare take ta kasa sakin jikinta, duk hankalinta yaki kwanciya gani take kamar Yaya Aryan zai bayyana a gurin, dakewa tayi ta mik'e ta nufi saman step da abokan rawarta, suka fara cashewa cikin salo mai ban sha'awa. A can gida kuma, Momy ta shiga part d'in Ammi domin ta kira su Meena, zata sanya su aiki a system d'inta, koda ta shiga wayam, da yake Ammi yau ita ke da girki tana part d'in president, mamaki ne ya cikata, sam bata san sun fita ba, kiran wayansu tayi amma duk a kwashe, girgiza kai tayi tace a fili "wato Basma bata tashi rashin da'a sai su Meena sunzo, yau kenan a gidan Hutu zasu kwana, anya yaran nan suka aikata Alkhairi kuwa? amma zan d'auki mataki" sai ta ja tsaki ta fice rai b'ace. Sai misalin k'arfe sha d'aya na dare Basma ta dawo hayyacinta, tunda ta soma rawa saita manta da duniyar da take ciki, Aryan ya fad'o mata a rai a zabure ta fita daga hol d'in ta shiga mota ta rufe, wayarta ta ciro ta kunna, sak'oninsa ne suka fara shigowa har kusan biyar, kan ta kaiga bud'ewa kiransa ya shigo, a tsora ce ta d'auka tamkar mara gaskiya tace "My Aryan lol, afwan wayana ta mutu ba chrgy ne" murmushi yayi tare da ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah tunda lafiya kike, amma Basma baki tab'a min k'arya ba sai yau" damm gaban Basma ya buga, a tsorace tace "k'aryan me nayi baby lol?" yace "saboda tunda nake dake wayoyinki basu tab'a mutuwa babu chrgy ba sai yau, domin wayoyinki uku ne kuma layi daban-daban" jikinta ne ya d'auki rawa cikin rawar murya tace "am am dama" tsawa ya saka mata "yimin shuru karki b'atamin rai, ina kika je?" nan take fitsari ya kamata tace "naje gidan Hutuna ne ni da su Meena" murmushi yayi yace "good, to kinga abinda ya sa kika kashe waya, saboda yau su Meena sunzo har kin fara mantawa dani, haba Basma kinsan kuwa halin da kika sani dana ji wayarki a kashe" marairaice murya tayi ta shiga bashi hak'uri, ajiyar zuciya yayi yace "Basma babu komai banyi fushi ba, sai dai zan rubuta wannan ranar a cikin tarihin rayuwana, ranar da Basma ta fara min k'arya, amma ki kiyaye, kuma ki tabbatar kin ware min lokacina, domin na lura sai na dage miki akan su Meena, dan naga zasu rage soyayyar mu" murmushi tayi ta kuma bashi hak'uri da kalamai masu dad'i har ya sakko, sukayi hira mai dad'i, hakan ya d'auke su har kusan k'arfe d'aya, kana suka yiwa juna sallama. Sai misalin k'arfe uku na dare suka koma gida, ko wacce d'akinta ta nufa ba ko tub'e kaya duk suka fad'a gado sai barci. Yau kusan kwana biyar kenan su Basma basa kwana a gida, kullun sai sunje club, Basma tana k'ok'arin ki yayewa Yaya Aryan, domin time d'in wayansu na dare nayi take fita a hol, taje susha hira a waya. Ta b'angaren Momy kuwa abin yana matuk'ar damunta, in suka fita da yamma sai da safe suke dawowa gida, sam bata nuna musu ta sani ba, kuma bata gayawa kowa ba, yau tayi shirin bin diddiginsu, Yaya Ahmad ta kira yazo sameta a d'aki, suka gaisa, bayani ta shiga yi masa akan su Basma, mamaki k'arara ya bayyana a idonsa, domin bai tab'a tunanin hakan zai faru ba, duk yawan security dake gidan, Momy ta gama gaya masa tsaf, tace "ina so yau kaje gidan hutun Basma, ka gano min meke faruwa" ajiyar zuciya yayi yace "insha Allah Momy zanje, domin ni abin nasu ma mamaki ya bani, a ce wai harda Basma, duk yanda akayi su Meena ne suka sauya ta" murmushin takaici Momy tayi tace "ba ruwansu duk halinsu d'aya, ko da can ma haka suke yi" "To Allah ya shiryesu, bari mu gani zuwa dare in basu dawo ba, sai na d'auki Naufal muje tare dashi". *Rahma Ce* [8/5, 6:46 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *12.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *Da Dare* Bayan sallan Isha'i, Yaya Ahmad ya nufi d'akin Momy ya tambaya ko su Basma sun dawo, Momy ta shaida masa masu dawo ba, da mamakin hakan yabar part d'in Momy, ya kira Yaya Naufal a waya yace masa ya fito ya raka shi wani guri, cikin sauri ya fito suka kama hanya. Ta b'angaren Basma kuwa sun gama shiri tsaf sunyi hotunan da suka saba, sai suka fito haraban gidan suka shiga mota, mai gadi ya bud'e musu gate, d'aya bayan d'aya suka fice, wanda yayi dai-dai da shigowan Yaya Ahmad layin, ganin motocin su ne, sai Yaya Naufal yace "to ai gasu nan sun fito ina ga gida zasu" Yaya Ahmad yace "ai kuwa, amma bari mubi bayansu mu tabbatar da gidan zasu" da sauri ya juya akalan motansa yabi bayansu, tafiya suke da gudu kamar zasu bar gari, sun zo dai-dai kan kwanar da zai sadasu da gida, sai Yaya Ahmad yaga sun mik'e, da mamaki ya juya ya kalli Naufal yace "ka gani ko, ba gida zasu ba, duk yanda akayi akwai inda suke zuwa yaran nan, Amma dai bari muje" sun cigaba da bin bayansu har su Meena suka isa hotel d'in. Sun shiga ciki sunyi parking motocin, Yaya Ahmad yayi parking motonshi a waje, da sauri ya fito Naufal na biye dashi a baya, da shigansu sai suka hango su Basma cikin wani shegen shigan tamkar zasu gasar kyawawa, tafiya suke tamkar ba zasu taka ba, har suka shiga cikin club d'in, mamaki da tsoro ne ya lullub'e su Yaya Ahmad, binsu su kai a baya, escot na ganin su Naufal duk suka fara b'arin jiki, d'aya daga ciki bakinsa ya d'auki rawa yace, "sir sannu da zuwa" Yaya Ahmad ya masa wani mugun kallo ya wuce su, har cikin hol d'in suka bi su Basma, suna hangen inda suke zauna, Yaya Ahmad yace "Naufal ga key je gida da sauri ka d'auko Momy da Ammi, kace kawai suzo, dan bai kamata ace mu kad'ai muka gansu ba" cikin sauri Yaya Naufal ya amsa ya wuce, Yaya Ahmad ya samu wani kujera ya zauna daga baya duk yana hango su, bayan kamar minti ashirin saiga Jalal yazo ya kama hannun Leema suka bi ta wata k'araman k'ofa ta gefe suka fita, da sauri Yaya Ahmad ya bi bayansu, a hankali yake binsu tambayar b'arawo, har suka isa d'akin hotel d'in da Jalal ya kama, suna shiga ya dawo, jikinsa ne ya d'auki rawa saboda tsabar b'acin rai, yana dawowa hol d'in ya hangi Meena cikin wani group maza da mata suna d'aga kwalaben syrup, bai tsinke da lamarin ba saida ya hango Basma kan step tana kwasan rawa iya k'arfinta, da karairaya jiki, ai tuni wasu zafafan hawaye suka cika masa ido bai taba tsammanin haka ba, lamarin ya girgiza shi, wayansa ne ya soma ringing da sauri ya fita hol d'in, ya duba ashe Yaya Naufal ne sai ya d'aga, ya sanar masa sun zo, da sauri ya isa wurin motocin harda escot d'in su Momy, Ahmad ya kasa magana hannun Momy ya kama suka wuce cikin hotel d'in, haka su Ammi suketa binshi har suka isa d'akin da Leema ke ciki, kwankwa k'ofan yayi, daga ciki Jalal ya bud'e daga shi sai best da gajeran wando, Yaya Ahmad ya runtse ido ya bud'e, Jalal ya na musu kallon mamaki yace "lafiya wa kuke nima?" daga ciki ne Leema ke cewa cikin d'aga murya "baby waye ne? kazo mana wlh ina cike da buk'atarka fa" ai da k'arfin Yaya Ahmad ya bangaje Jalal ya kusa kai ciki, su Ammi ma suka rufa masa baya, a razane Leema ta mik'e tana ja da baya harta kai jikin bango, Allah yasa bata cire kayan jikinta ba, idonta ne kamar zasu yo waje saboda tsananin furgici, su Momy da Ammi sai suka hau salati, abin ya girgiza su, Yaya Naufal saboda fushi baisan sanda ya zaro bel d'insa ba ya shiga jibgar Leema, ai Jalal na ganin haka ya fice a sittin, Leema ta kasa ihu domin tashin hankalin da take ciki ya wuce na jin azabar dukan da Yaya Naufal ke mata, da kyar Ammi ta kwaceta tace su fita, haka suka fito cikin tashin hankali. Momy tace "ina su Basma suke" Yaya Ahmad yace "muje in kaiku" ya musu jagora har cikin hol d'in, saboda dan dazon mutane da kyar suka samu hanyar shiga, Yaya Ahmad ne yace "Momy ga Basma can" yayi mata nuni da inda take kwasan rawa, Ammi ne tace "innalillahi wa inna ilai hir rajiun, mun shiga uku ni Faitima" idon Momy ne ya kawo kwalla, sai tayi saurin shanyewa tace "ita kuma Meena tana ina?" cikin mutane Yaya Ahmad ya kusa dasu, ya kaisu hargun da take, suka tsaya ta bayanta, Momy ta dafata, Meena ta juya da niyyar kwararo ashar domin ta riga tayi tatil, ganin Momy a bayanta ne yasa ta mik'e zunbur tace cikin maye "Ke ya kike min kama da Momy ce" wani wawan mari Yaya Naufal ya sakar mata saida taga taurari, a gigice ta kalle shi, ai tuni hanjin cikinta suka hautsine sai taji cikin ta ya murda, nan da nan jikinta ya d'auki b'ari, ta kasa magana sai rufe baki tayi, idonta tamkar zasu fad'o k'asa saboda tsoro, Momy ce ta kama hannunta suka fita waje, a cikin mota suka sanya ta kusa da Leema, sannan suka k'ara komawa cikin hol d'in. Yaya Ahmad yabi ta baya ya hau kan step d'in, ya kutsa cikin masu rawan yaje ta bayan Basma ya ya jawota ta baya, ya rad'a mata magana a kunne "In kin gama rawan ga su Ammi can suna jiranki" sai yayi mata nuni da in da suka tsaya" ai a razane Basma ta juyo, ganin Yaya Ahmad ne yasa tayi luuu zata fad'i k'asa, da sauri ya tallabota ya kamo hannunta suka sauka akan step d'in, mutane suna ta ihu yau Basma ta kula Namiji, a tunaninsu saurayi ne ta samu, suna sauka suka fita a hop d'in, su Momy suka rufa musu baya, ba wanda yayi magana duk suka shiga mota suka wuce gida. Suna isa gida suka wuce part d'in su Yaya Ahmad, d'aki ya bud'e musu suka shiga, Yaya Naufal ya shiga dukansu saida ya musu lis sannan ya fito ya sanya key ya rufe su, Momy suka wuce part d'in president. Sun zauna dukansu a falon, sai gashi ya sauko ya zauna, Yaya Ahmad suka gaishe shi, sannan suka d'aura da bayanin abinda ya faru, mamaki ne ya ziyarci Abba mik'ewa yayi ya shiga safa da marwa a falon, sunan Basma yaketa ammabato yana girgiza kai, komawa yayi ya zauna, ya d'auki wayarsa ya kira number gomna Ibrahim mahaifin Meena, suka gaisa kana ya sanar masa da "gobe in Allah ya kai mu suzo akwai family meeting na gaggawa" cikin ladabi ya amsa masa da ""to suna nan zuwa" sai suka yi sallama ya kashe wayar, gomna Ibrahim ya kalli mahaifiyar su Meena ya labarta mata abinda president yace masa, duk suka cika da mamaki suna Allah-Allah gari ya waye su wuce Abuja d'an jin ko lafiya. Haka Abba ya kira sarkin kano yayi masa umarnin da suzo suma domin family meeting, cikin kulawa ya amsa da alkawarin suna tafe, Abba ya kalli su Ammi yace "kuna gidan nan ace yaran nan suke fita suna wannan iskancin" cikin damuwa Momy tace "yallabai kayi hak'uri, amma iyaka kulawa munayi, kuskuren da akayi shine yanda aka basu daman fita ko ina da mota ba mai kwab'a musu, an basu escot duk da haka ya zama aikin banza, Allah ya shirya mana su" duk suka amsa da "Ameen" Abba yace "lallai laifi nane dana nuna musu gata, kanma ace Basma na sakar mata komai, a gani na Yarinya ce mai hankali kuma mun bata tarbiyya ga kuma ilimi na addini, ashe shirme mukayi, amma insha Allah daga yau zan d'auki tsastsauran mataki" yana gama fad'an haka ya haye sama cike da b'acin rai, su Momy suka bishi da kallo yau ran maza ya b'aci, haka zuka watse a falon cike da damuwa. B'angaren Yaya Aryan yanata kiran wayan Basma, gata a kunne amma anki d'auka, ya kira ya kai sau ashirin amma ba a d'auka ba, hankalinsa yayi matuk'ar tashi, yana ji a jikinsa akwai abinda ya sameta, dak'ar barci ya d'aukeshi tare da yin mafarkai barkatai marasa tushe. Basma kuka suke ba k'auk'autawa, kanma ace maka Meena da Leema tamkar zasu had'iye ransu, yau dai dubunsu ya cika, suna tsoron gamuwansu da iyayensu. *Washe gari* Da misalin k'arfe goma na safe, gida ya cika da dangi, an cika babban falon bak'i, abinci kala-kala aka jera, duk suna zazzaune, mai martaba da iyalensa Hajiya Sa'a da Hajiya Murja, sai gomna Ibrahim shima da matarsa Hajiya Sadiya, sai kakansu Ahmad Kaka Ma'u, sai su Momy da Ammi, President yana gefe shima, nan suka bud'e taro da addua, president ya soma bayani akan had'uwansu yace "Mun had'u anan ne domin in sanar maku da cewa, na sanya aurensu Basma nan da wata d'aya, Basma da Shureym, Meena da Naufal, Leema da Jamal, bisa sadaki dubu D'ari, ina so duk sai ku fara shiri daga yau" Cike da mamaki iyayen suke kallon juna, gomna Ibrahim ne yace "Yallabai yaushe muka yi magana da kai akan batun aurensu, kace sai nan da shekara d'aya, amma me ya kawo sauyawan wannan lamarin" cike da fad'a Ammi tace "wannan hukunci shine dai-dai, domin yaranmu suna gab da lalacewa ko ince summa lalace" falon ne ya hautsine da magana ko wanne yana tambayan meya faru, nan Ammi ta kira Yaya Ahmad yazo ya labarta musu komai, ai mai Martaba yafi kowa shiga tashin hankali, cike da b'acin rai yace "a kira yaran dukansu" cikin k'ank'anin lokaci suka shigo sanye da kayan da suka fita jiya, salati iyayen nasu suka saki kowanne mamaki ya gama cika su, sai suka zauna, nan mai Martaba ya soma musu fad'a daga k'arshe ya shiga nasihi, ya kuma kafa musu doka. "Daga yau na yanke fitanku waje" ya kai dubanshi ga Momy yace "ke Maryam ina son yaran nan su zauna a part d'inki" ya cigaba da cewa "sannan kuma na haramta muku amfani da waya, kuma koda lanbun gidan nan na hana kuje gun, daga part d'in Mominku sai part d'in Ammi da president, Ku tashi Ku bani guri mutanen kawai" President ne ya dakatar dasu, suka koma suka zauna, yace ma Yaya Ahmad daya kira su Yaya Naufal, yaje ya kirasu. Nan duk suka shigo da yake duk sun zo da iyayensu, Anty Husnah Autan Ammi wacce take aure d'an senator, Yaya Naufal, Yaya Ahmad, Yaya Jamal. Yaya Shureym, Yaya Adam duk suka samu guri suka zauna, Gomna Ibrahim shine ya fara magana yace "Ku yaranmu ne, kuma ba zamu yanke muku hukuncin da zaisa muku damuwa ba, duk yanda kuka kai ga lalacewa baza mu k'iku ba, dan haka mun yanke aurenku nan da wata d'aya mai suwa za ayi insha Allah, kai Shureym an bada sadakin Basma, kai Jamal kai da Haleema, kai kuma Naufal kai da Ameena, dama tuntuni mun yanke haka domin mun fahimci kuna son junanku, sai dai yanzu saboda wasu dalilai mun dawo da zancen baya, za'a d'aura muku aure nan da wata d'aya mai zuwa, kai Ahmad da Adam kuyi k'ok'arin gabatar mana da wanda kuke so domin a had'a bikin gaba d'aya". Yaya Naufal a ransa sam baiji dad'i ba saboda Meena ta gama fita a ransa, Yaya Jamal ma ransa ne ya b'aci dan Gaskiya baya son Leema ya tsani halinta, biyayya kawai zaiwa iyayensa. Basma ita kuma kuka ta fashe dashi tace "Wallahi Abba bana son Yaya Shureym, karku had'a auren nan" wani mari Yaya Naufal ya sakar mata wanda ya k'ara gigitata, kuka ta shiga yi sosai tace "wlh zan mutu bana sonsa, dan Allah karku min haka, na tuba bazan sake ba" Lamarin ba k'aramin mamaki ya bama iyayen masu ba, domin sun san Basma soyayya suke yi da Shureym, ta b'angaren Shureym baiyi mamaki ba, domin k'ila tana k'inshi ne saboda abinda yake ce mata, tsoronsa karta tona masa asiri. Momy ce ta dakawa Basma tsawa, sai ta shiga natsuwanta, duk suka fito suka bar iyayen nasu, Basma tana fita tayi hanyar waje da gudu, ai da gudu su Naufal suka bita suna gargad'in masu gadi "karku barta ta fita". Kamata sukayi suka kaita d'akin Momy suka rufe, ihu take tana buga k'ofa "kun daina sona kuna so na mutu, Yaya Aryan kazo ka ceceni zasu rabamu wayyo na shiga uku, wai ba mai Sona ne a gidan nan" surutai take ta yi kamar mahaukaciya, Ammi ce ta shigo falon zata bud'e k'ofar, president na shigowa yace "karki kuskura ki bud'e ta, yau ina so ta nuna mana karshen hauka, kuma wlh na rantse aure tsakaninta da Shureym ba fashi" yana gama fad'a haka ya fice. Kaka Ma'u ce ta sanya aka bud'e d'akin ta shiga, Basma ta rungumeta tanata sambatu, Addu'a taketa tofa mata, a tunaninta ko akwai jinnu a lamarin, lallashinta ta shiga yi har ta samu tayi shuru, tana ajiyan zuciya, da haka barci mai nauyi ya d'auketa. Bayan komai ya lafa, su Meena da Leema an natsu, sun zama kamar kurame, farin cikin su ma za'a aura musu abinda suke so, sai dai zuciyansu na cike da damuwan waye Basma take so haka? sun tausaya mata sosai. Yaya Ahmad ya wuce d'akinsa, damuwa ne ya shigeshi, yasan dole dama za'ayi haka, kira a wayan Basma ne ya shigo, yana dubawa yaga an rubuta my lol Aryan, kamar bazai d'aga ba saiya d'auka, Yaya Aryan ya fara magana "Basma, Basma me ya sameki dan Allah kimin magana, ina cikin damuwa" hawaye ne ya kawo ma Yaya Ahmad na tausayinsu yace "ba Basma bace Ahmad ne" cikin sauri ya tari numfashinsa "me ya samu Basma dan Allah karka b'oye min" Yaya Ahmad yace "ka kwantar da hankalinka Basma tana lafiya barci take yi" cikin damuwa yace "Basma ba tada lafiya, karka b'oyemin akwai abinda ke damunta" kawai saita fashe masa da kuka.... *Rahma Ce* [8/6, 9:02 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *13.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Hankalin Yaya Ahmad yayi matuk'ar tashi, cikin kulawa yace "haba Aryan ya, kake abu kamar k'aramin yaro, nace maka Basma tana barci inna farka zansa ta kiraka" ajiyan zuciya Aryan yayi yace cikin damuwa, "to shikenan nagode" nan suka yi sallama ya kashe wayar. Basma ta farka da misalin k'arfe biyu na rana, Kaka Ma'u ta sanyata tayi wanka ta sauya kaya marasa nauyi, sallan Azahar ta gabatar kana aka kawo mata abinci, Kaka Ma'u ce ta matsa mata taci, loma uku tayi da kyar kana ta sha ruwa tace ta k'oshi, mik'ewa tayi kamar an tsikareta tace wa Kaka Ma'u tana zuwa sai ta fice, tayi sa'a falon ba kowa haka ta sanya takalmi ta fito haraban gidan, motocin gidan sun ragu da alama sun tafi raka su mai Martaba ne airport, hanyar k'ofar fita tayi tana waige-waige kamar mara gaskiya, masu gadi suka hanata fita, saita fara musu masifa akan su bata hanya ta wuce, ganin ta cije ne yasa suka bata hanya tawuce, tana fita, taga Yaya Ahmad zaune bisa wani dakali daga gefe ashe duk yana jin hayaniyansu, tsayawa tayi cak ta kasa tafiya, Yaya Ahmad ne ya mik'e yazo gabanta ya tsaya cike da tuhuma yace "Basma bakya jin magana, ina zaki bayan an hanaku fita, ya kike so ki zama mara biyayya ne" fashe masa da kuka tayi, girgiza kai yayi ya kama hannuta suka koma cikin gidan, part d'in su ya wuce da ita ya zaunar da ita a gefen sa ya kira sunanta a nutse "Basma kin ga abinda rashin ji ya haifar miki, naso ace haka bai faru ba, dana tsaya miki tsayin daka akan baki auri Shureym ba a baki wanda kike so, Basma meyasa kika aje tarbiyanki kika nima lalacewa haka, bayan kinyi saukar Al'Qur'ani har sau biyu, kina da sani akan littafai Addini sosai, a takaice in aka baki aji zaki iya rik'ewa a matsayin Malama, ya a kayi kika shagala da duniya haka Basma?" Jikinta ne yayi sanyi sosai ta kuma b'arkewa da kuka tace "Yaya wlh mun riga munyi kuskure, kuma wannan rayuwar a England muka koyoshi, insha Allah bazamu sake ba mun tuba, ni dai ka taimakeni karka bari a aura min Yaya Shureym wlh bana sonsa, kafi kowa sanin waye Shureym bai cancanta ya zama mijina ba" ajiyan zuciya yayi yace "na sani Basma amma Abba ya riga ya yanke hukunci, ni shawara a gareki shine ki masa biyayya sai Allah ya sauk'ak'a miki lamarin" "To Yaya kamin Addu'a, amma da son Aryan zan mutu" Tsaki yayi baice komai ba wayarta ya d'auka yayi dailing number Aryan, bugu d'aya ya d'aga, sai ya mik'a mata ta kara a kunne, a cikin damuwa Aryan yace "My Basma kina lafiya kuwa?" kuka ta saki wanda hakan yayi dai-dai da k'ara rikicewansa, cikin damuwa yace "meya faru gayamin mana ko so kike nima nayi kukan". Tuni Yaya Ahmad ya bata wurin domin ya gaji da jin kukan nata, Basma ta shiga bashi labarin komai bata b'oye ba, ai zubbur ya mik'e a tsorace yace "Basma shikenan kinyi sanadin rabuwanmu, shikanan kin jawo mana damuwa mara yankewa" ya k'arasa maganar cikin rawar murya, Basma sai tai k'ara tsinkewa da sabon kuka, Aryan kashe wayar yayi gaba d'aya, Basma taita dialing number akashe, a firgice ta mik'e ta fita da gudu, Yaya Ahmad yana waje, ganin ta a guje yasa ya bita a guje, wurin gate ta nufa, masu gadi suka tare ta, kuka take da magiya akan su barta ta fita, amma suka k'i har Yaya Ahmad ya cimmu su. Kama hannunta yayi gam yana janta, ihu sa saka tana tirjiya, ihun ta ne ya dawo da duk hankulan mutanan gidan duk suka fito a guje, da yake sun dawo daga rakiyan, kafin su k'arasa cikin gidan sosai Basma tayi wani ihu saita langwab'e, a razane Yaya Ahmad ya juyo yaga idanunta sun kafe ta suma, jikinsa na b'ari ya d'auketa tsak ya shiga cikin gida da gudu, a hanya yaci karo dasu momy, nan ya kewaye su ya wuce da ita part d'in president, a falon ya ajeta duk suka shigo ko wanne ya rufa a kanta, Ammi ne keta kiran sunanta amma shuru, da gudu Meena ta kawo ruwa aka yayyafa mata, lumshe ido tayi tare da sauke ajiyan zuciya mai k'arfi, President da kansa yazo ya d'auketa cak ya haye da ita sama, ya kuma yi gargad'in kar wanda ya biyoshi, a zata yayi akan gadonsa ya d'auki wayansa ya kira likitansu. Baifi rafin awa ba sai gashi, ya haura sama ya dubata, allurai yayi mata a ciki harda na barci, yayi wa Abba bayanin "damuwa ce ya haifar mata da suma, yanzu nayi mata alluran barci domin kwakwalwanta ya huta" nan Abba ya mishi kyauta ya fice yana godiya. Su Ammi duk suna falon sun kasa tafiya, Yaya Ahmad ne ya zauna jugum yace "Ammi dan Allah kusa baki a jenye maganar Auren nan, lamarin Basma ya fara bani tsoro" Ammi tace "nima abinda na gama tunani kenan, amma kasan Abbanku baya sauya magana in yayi" Momy ce tace "uhum nikam ina bayan Abbanku, aure kuma da Shureym ba fashi" tana gama fad'an haka ta mik'e tace "Husnah zo muje na had'a miki turarukanki kan ki tafi" Cikin sanyi jiki da damuwa Anty Husnah tabi bayanta cike da tauyawa 'yar uwanta. Sai bayan Sallan Isha'i ta farka, Abba da kansa ya kira Ammi tazo tayiwa Basma wanka ta shiryata, Abinci ta bata da kanta, da kyar take iya cin kad'an, bayan sun natsa Abba ya kira su Meena dasu Momy, dasu Yaya Ahmad duk suka had'u a falon sa, ya soma magana "na taraku a nan ne domin in kuma jaddada muka akan zancen Auden ku, saboda wasu dalilai mun k'ara kwanakin bikin zuwa bayan wata Uku, lokacin Basma ta samu lafiya sosai, Meena tasha maganin Islamic akan kwayoyin da tasha, ke kuma Leema ki samu yin istibra'i" Leema saita sunkuyar da kai k'asa, cike da dana sani, yanzu kowa yasan ita fasik'a ce wa'iyazu billah, maganar zuci takeyi hayawa na zuba a kuncinta. Abba yakai dubansa ga Basma data rakub'e gefe d'aya kusa da Ammi yace "ke kuma Basma ina so ki sani tun da muka haifeki, ban tab'a saki abu kin k'i yimin ba, to ina niman alfarma a gunki a matsayina na mahaifinki, kiyi hak'uri kiyi min biyayya insha Allah zaki nasara a rayuwanki, Basma ke mai biyayya ce a garemu, akwai abubuwa dana auna na tabbatar da yin aurenki ga Shureym shine dai-dai, zumunci ba abun wasa bane, dan haka ki sanyawa ranki salama ki tabbatar min da nine mahaifinki kuma na isa dana saki Abu kiyi min" Kuka ta soma yi amma mara sauti, tashin hakanli ta shiga, domin yau ta riga ta sadak'ar an rabata da Aryan, kwantawa tayi a jikin Ammi tace cikin kuka mai karya zuciya "Abba ina son Aryan ne wlh shi nake so, burina in muku biyayya, Abba kamin komai a rayuwata, k'arshe na sab'a muku, na aje tarbiyyan da kuka bani na soma yin wata rayuwa mara tushe, mai dinbin dana sani aciki, nagodewa Allah da kune kuka ganni da idonku, na tabbatar da labari aka baku baza ku yarda ba, saboda kun bani dukkar yardanku, Abba saboda haka na hak'ura da soyayyar Aryan, amma ku sani zan auri Shureym bisa ga biyayya a gareku ne, domin in cire muku rad'ad'in sab'a muku da nayi, Na amince zan auri Shureym, Aryan ka yafemin" Sai ta k'arasa maganar da wani matsanan cin kuka, da gudu ta mik'e tabar falon, ta nufi d'akin Abba, ta fad'a gado tana rera kuka mai tsuma zuciya. Gaba d'aya illahirin mutanan falon jikinsu yayi sanyi, hatta Abba ya tausayawa 'yarsa abin sonsa, sunyi shuru ko wanne da irin abin da yake sak'awa a ransa, sautin kukansu Meena da Leema ne ke tashi a falon, Kaka Ma'u ce tace "ni kam wannan lamari yana bani mamaki, waye wannan Aryan d'in da yake son raba zumunci" Yaya Ahmad ne yace cikin wasan kaka "ke kuma tsoguwa ina ruwanki, ana Abu na yara kin tsomo baki, sai ki mana shuru" Abba ne ya masa dak'uwa yace "kai ungo naka uwata kake cewa hakan" su Ammi duk suka yi murmushi, nan take fara'ansu ya dawo, damuwan da suke ciki ya ragu, Abba yace "Ahmad ina so gobe in Allah ya kaimu ka tattaro min dukkan takardu da makullan abubuwan da Basma ta mallaka" Cikin dalabi yace "to Abba insha Allah zanyi, Allah ya kaimu" Nan Abba ya sallami kowa, Momy ce mai girki Abba ya cewa Ammi, ta wuce da Basma d'akinta, ta bata kyakkyawan tsaro saboda karta fita cikin dare ba'a sani ba. Shureym bayan sun isa Kano, ya samu Maminsa ya matsa mata akan shifa lallai sai an aura masa Basma in ba haka ba akwai Matsala, Hajiya Sa'a tayi murmushi tace masa "Ka kwantar da hankalinka, aurenka da Basma kamar anyi an gama, ita d'in banza harta isa tace bazata aureka ba, zanje in samu Mai Martaba na k'ara hura masa wuta akan lamarin" dariya yayi na farin ciki yace "to Mami ya maganar aurena da Safeena? Kinsan fa so nake a fara d'aurawa da ita kan na Basma" tace "Karka damu cikin satin nan zan had'aka da sarkin gida da wasu, domin su jagoranci aurenka da Safeena, a cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba, kaga sai a d'aura muku aure kafin bikin su Basma da wata guda, ka ajeta a gidan gonarka, da an d'aura aurenku da Basma ku tarkata ku wuce America, bazaku dawo ba sai ka kammala komai da shekara guda, kaga lokacin komai yayi dai-dai" dariya yayi harda tafawa yace "Gaskiya Mami kin gama min komai in kika min haka, zanyi murna sosai" tunowa da yanda Basma ta nuna masa tsantsar kiyayya yayi, yasa ya cije leb'e yayi wani shu'umin murmushi. *Bayan kwana biyu* Aryan ya lalace yayi duhu, hankalin Umma ya tashi sosai dan kwanan sa biyu ko k'ofar gida baya iya zuwa, sallah ma a gida yake yi, baya iya cin komai sai abu mai ruwa, sai yawan barci. Deeja ce take sanarwa Yaya Ahmad halinda suke ciki domin sam Yaya Aryan yak'i yarda suje asibity kuma yace shi lafiyansa kalau, Ahmad ya shirya yazo, ya samu Umma ya sanar mata abin da ke faruwa game fa Basma da Aryan, bai b'oye mata komai ba, hankalin Umma ya tashi sosai ta tausaya musu, dama tasan za ayi haka, Deeja d'aki ta shiga ta fara kuka, Yaya Ahmad ya sanar mata da zuwan iyayensa nan da ranar Juma'a akan maganar auren Deeja, Umma ta sanya albarka tayi murna koba komai hakan ya rage mata damuwa, nan ya shiga wurin Aryan da kyar ya shawo kanshi suka tafi asibity tare. Likita ya duba shi ya rubata masa magani da allurai, haka akai treatment d'insa, Yaya Ahmad yayi masa siyayyan kayan ciye-ciye, kana ya dawo dashi gida, ya yiwa Umma sallama ya tafi. *Bayan wata guda* Bikinsu Basma saura wata biyu, Yaya Aryan ya warware ya cigaba da zuwa aikinsa, sai dai yanzu miskilanci ya k'aru, baya magana saiya kama dole, baya cin abinci sosai duk ya rame yayi fari, Umma tayi mita da lallashi harta gaji ta kyaleshi, kullun dare baya iya barci sai yayi kuka sosai, kana yayi Nafila ya rok'i Allah kan ya sassauta masa akan lamarin. Abba ya wakilta Abokansa wajen nimawa Ahmad auren Deeja, da yake Ahmad ya sanar da Abba komai tun farkon had'uwansu, Abba ya jinjina lamarin kuma yayi farin ciki da 'ya'yansa, da suka kasance masu tausayi da taimakon na k'asa dasu, hakanne ya k'ara bashi k'arfin gwiwan ya amince da Auren Ahmad da Deeja, a ransa baiji dad'in raba Basma da Aryan ba, Amma yayi alkwarin zai d'aukaka darajan Aryan yanda duniya da 'yan uwansa zasu amfana dashi. Mak'otan su Deeja da mai anguwa sune suka amshi maganar Auren Deeja, iyayen Ahmad da suka zo sun boye asalin Ahmad, suka sanya biki dai-dai dana su Meena, a haka suka gama taron cikin mutunci, kowa ya koma gida. Deeja farin ciki ya lullub'eta, amma inta tuno da Yaya Aryan sai damuwa ya rufeta. A haka suka fara shirye-shieyen biki, Yaya Ahmad ya sanar musu da, shifa Deeja kawai yakeso a bashi, baya buk'atar komai, hatta abincin biki Abbansu ya d'auki nauyi, dan haka kar su takurawa kansu, Umma saboda murna har kuka tayi. B'angaren Basma kuwa, lamura sun dagule mata ta lalace tayi bak'i, duk ta rame inka ganta sai ka k'ara kallonta ka tambaya anya itace Basma 'yar kwalisa kuwa? domin duk ta fice a hayyacinta, kowa na gidan yana tausaya mata, hatta Momy tana jin tausayin 'yarta haka yasa take jawota a jiki, tana lallashinta da maganganu masu dad'i da nasiha, yanzu Basma ta saduda ta kuma hak'ura da lamarin, burinta bai wuce ta k'ara tozali da Aryan ba suyi magana na bankwana. Su Meena an natsu, ana ta bata magunguna na Islamic wanda zai wanke mata dattin kwayoyin data sha. Leema kuwa Momy musamman takwo mai gyara, domin a gyarata, yanda zata dawo kamar budurwa, koda dai ta riga ta rasa budurcinta. *Ni kam nace anbaro shiri tun rani* Shirye-shirye ake ta ko wani b'angare, Abuja, Kano, Kaduna, duk sunata shirye-shieye, biki ne na 'ya'yan manya. *Biki saura wata guda* President ya kira Ahmad suka gana dashi a d'akinsa. Yaya Ahmad ya fita da sauri domin aiwatar da ummarnin Abba. Abba ya kira Momy da Ammi, ya kira duk yaran gidan, kaka Ma'u ita ta koma Kaduna dan tafi jin dad'in zaman can. Yaya Ahmad ya nufi gidansu Aryan, ya samu duk suna gida da yake weekend ne, Yaya Ahmad ya shiga ya zauna a shinfid'an da Deeja ta masa, suka gaisa da Umma, ya kalli Aryan ya kalli Umma yace "Umma mahaifina ne yace inzo in tafi daku gidanmu, domin yana buk'atar ganinku, yace in baku hak'uri akan hakan, yasan shine ya kamata yazo amma bisa wasu dalilai yace da kuje ku same shi" Yaya Aryan ne yace "ok badamuwa yaushe yake son ganinmu?" "Yanzu yake son ganinku" Umma tace "to shikenan bari mu tafi" ta k'ara maganar tana mik'ewa, komawa d'aki suka yi duk suka canza shiga mai kyau, suka rufe gidan suka gida mota. Aryan na gaba Umma da Deeja suna kujeran baya, sun kama hanya suna tafiya, Aryan suna hira da Yaya Ahmad, tafiya sukai mai nisa, tun suna arean talakawa har suka gota arean masu hannu da shuni, Yaya Ahmad yana zullumi a zuciyansa yanda in suka san Abbansu ne Shugaba k'asa ya zasu d'auki lamarin , Yaya Aryan ne ya katse masa tunaninsa yace "Ahmad naga mun doshi hanyar gidan Shugaba k"asa ne, kasan fa ta arean akwai check point kuma ga yawan security" murmushi Yaya Ahmad yayi yace "eh gidanmu dole sai tanan zamu bi, karka damu" haka suka fara ratsa check point ba tare da an tare su ba, security suna d'agawa Yaya Ahmad hannu, mamaki ne ya fara cika su, basu tsinke ba saida suka ga security na bud'e musu hanya suna sarawa Yaya Ahmad, katon tangameman gate d'in fadar shugaban k'asa suka dosa, wanda kan su k'araso an bud'e musu gate, a tsorace Yaya Aryan ya kalli Ahmad bakinsa yana yawa yana nuna shi yace..... *Rahma ce* [8/6, 9:03 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *14.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Yace "Ahmad kasan inda ka kawo mu kuwa?" Ahmad murmushi kawai yayi, sai yayi parking mota, ya fito tare da cewa "Umma mun kawo Ku futo" a sanyaye suka fito suna k'arewa gidan kallo, cikin kulawa Yaya Ahmad yace "kumu je" Umma tace "Kai Ahmad wai ina ne nan, gaskiya a tsorace nake" murmushi yayi yace "Umma Ku kwantar da hankalinku bakomai fa" a tsorace suka bi bayansa, direct part d'in president ya kaisu, suna shiga duk mutanan falon suka zuba musu ido, jikin su Deeja sai ya d'au rawa, ido suka saki suna kallon kayan alatu da aka zuba a falon, har suka isa tsakiyan falon, Basma ne ta rugo da gudu ta rungume Umma, ai sai ta fashe da kuka, Umma ta rik'eta gam tana lallashinta, a haka suka k'arasa cikin falon suka zauna a kan kafet, Ahmad yace su zauna a kujera amma suka k'i hawa, Su Ammi da Momy suka bisu da kallo, su Meena ma dasu Yaya Naufal kallonsu suke yi da mamaki, sun gaisa gaba d'aya sai falon ya d'auki shuru, baifi minti goma da zuwansu ba President ya fito, cikin shiga na manya kaya, yana tafiya cike da izza tamkar Baba Buhari ya bayya a cikin bainar Jama'a, sai dai shi Abba bai yi tsufan Baba Buhari ba, lol. Su Aryan suna arba dashi sai cikinsu ya d'uru ruwa, kamma ace Umma da tayi mutuwar zaune, Deeja ko kamar ace mata ket ta ruga a guje dan tsoro. Zama yayi a kan kujeransa na alfarma, Ahmad ne yace "Abba gasunan nazo dasu" Abba ne ya kalli inda suka zauna yace "barkanku da zuwa" baki na rawa suka amsa gami da gaisheshi, Abba yace "Nine mahaifin su Basma, Ahmad shine Babban Yaro na, nasan za kuyi mamaki da haka, Ahmad ya sanar dani labarinku, sai dai Ku bakusan nine Mahaifinsu ba sai a yau" a razane Aryan yake kallon Abba yana magana, ya juya kallonsa ga Yaya Ahmad da Basma, murmushi Yaya Ahmad yayi masa ya gyad'a masa kai alaman eh, Basma Kuma ta sunkuyar da kai k'asa, tunda tayi tozali da Yaya Aryan hankalinta ya tashi, taga ya rame sosai tausayinsu ya kamata tasan lallai an yiwa rayuwansu gib'i. Nan Abba ya cigaba da bayani yace "Aryan nasan komai dake tsakanin ka da Basma, kayi hak'uri da abinda ya faru, ba zan iya hana Auren ta da Shureym ba, domin ina martaba zumunci, dan haka ne na amince da Auren Ahmad da 'yar Uwanka saboda in sanya muku farin ciki, ku tabbatar da bama kyamar talaka, sannan yanzu nayi maka alkhawarin ka kawo duk yarinyar da tayi maka, insha Allah zan zame maka Uba na jagoranci lamarin, sannan nasan a company na kake aiki, yanzu na baka MD na company, sannan zaka Zab'i k'asar da kake so domin kaje ka k'aro karatunka a can" Aryan kuka ya fara yi, yace cikin ladabi, "Yallabai nagode kwarai da karamci, ban tab'a kawowa a rayuwata zanga Shugaban k'asa da idona ba, sai gashi a sanadin soyayyan Basma na ganka, Basma ke haske ce a rayuwanmu, Yallab'ai nagode da duk abinda ka bani, amma ina so ku sani, ba zai iya siyan soyayyan Basma ba a zuciyana, domin an riga an halittamin shi a zuciya, na hak'ura da soyayanta dan nariga na sadak'ar Basma tafi k'arfi na, mun gode sosai da karamci" yana gama magana sai yayi shuru. Shasshek'an kukan Basma ke tashi a falon, kowanne yayi shuru suna zancen zuci. Umma itama tayi godiya tace "lallai Basma da Ahmad kunyi gadon halaye na kwarai wurin mahaifinku, nayi mamaki sosai da yanda kuka shigo cukinmu kuka zauna damu duk girman matsayinku, kun rungume mu tamkar jininku" saita k'arasa maganar da kuka, Deeja ma kuka ta soma yi, falon ne yayi shuru na 'yan dak'ik'a, sai Abba yace "Hajiya kuyi hak'uri ai wannan ba abin kuka bane, kai Aryan ba wai na maka wannan kyauta bane domin ka fansar min da soyayyarka ba, nayi maka ne saboda Allah a matsayin d'an cikina, taso ka amshi wannan takardun, na gidan Hutun Basma ce da kuma takardun motanta guda uku, ni na baka su halak malak, ina so kafin lokacin Biki Ku tare a gidan" Yaya Ahmad ne ya matsa danya Amsa takardun, sai Abba yace "shi nake so ya amsa da kansa, domin shima d'ana ne" jikin Aryan ne yayi sanyi, haka ya mik'e yaje ya amsa tare dayi masa godiya. Momy itama tayi masa Addu'a da Allah ya bashi mata tagari, har a zuciyarta taji tana son Aryan, taso ace ya zama sirikinta. Ammi kuwa ta gama k'ulewa kamar zata fashe dan haushi, Meena da Leema sun shaida Aryan kuma sun yaba da kyawunsa lallai sun dace da Basma, Yaya Naufal da yake yasan Aryan ya tayashi murna, amma har a azuciyansa baya son ya auri Basma domin tafi k'arfinsa. Nan Umma tayita godiya, Abba yace "Hajiya ya isa haka Allah ne ya baku, ina 'yata Khadija?" Kanta a sunkuye tace gani, Abba yace "Masha Allah, Allah ya muku Albarka yasa Albarka a aurenku" ya kai dubansa ga Momy yace "Hajiya Maryam gafa surukarku nan, matar Ahmad" ai sai Momy ta fad'ad'a murmushinta tace "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi, ai tunda tazo ma ba zasu tafi da ita ba, zata zauna anan domin ayi mata gyaran jini dasu Leema gaba d'aya" Abba yace "To shikenan, Abu yayi kyau, bari na fita ana jira na" nan yayi musu sallama ya fice, Ammi ce ya mik'e da sauri tace "Ahmad yanzu ka rasa matar aure sai wannan yarinyan, to ka sani ba da yawuna ba, dan bataimin ba" tana gama fad'an haka ta fice, da mamaki duk suka bita da kallon, Ahmad cike da tashin hankali yace ma Momy, "Momy kinji abinda Ammi tace ko, dan Allah ki shawomin kanta" Momy tayi murmushi tace "karkaji komai zata sakko ne" ta kai dubanta gasu Umma tace "Hajiya kuyi hak'uri rashin fahimta ne" Murmushin yak'e Umma tayi domin abin ya bata haushi tace "ba komai ai" nan Yaya Ahmad yace su tashi ya rakasu gidan da Abba ya basu, Basma ta mik'e tace "Yaya Ahmad zani" hararan wasa yayi mata yace "kinsan dai yanzu bakwa fita, kiyi hak'uri kiyi zamanki a gida" marairaice fuska tayi tace "tom zanyi magana da Yaya Aryan" da sauri Aryan ya juyo yace "a'a Basma magana a tsakani mu ya k'are" yana gama fad'an haka yayi waje da sauri, ai da gudu Basma ta bi bayansa tana kwala masa kira. Ya kusa kaiwa gate, sai ya tsaya tsak amma bai juyo ba, ta cimmasa ta tsaya a gabansa tana haki, kallonta yayi ya kauda kai, hawaye ke sauka bisa kuncinta tace cikin sark'ewan murya "Yaya Aryan guduna kakeyi na zama abin gudu ko, ko ka daina sona ne?" Runtse idonsa yayi ya bud'e su, sun rine sunyi ja yace "Basma dole na gujeki domin ke yanzu ba tawa bace, Basma kin haramta a gareni, magana a tsakaninmu bai dace ba, domin zai tado min da mikin dake zuciyana wanda mai gama warkewa ba, ina Sonki Basma baya musaltuwa, amma ki sani soyayyan da mukayi dake kisa aranki tamkar mafarki ne, ki cireni a zuciyarki kiyiwa iyayenki biyayya" yana gama fad'an haka ya matsa ya cigaba da tafiyan, Basma durkushewa tayi a gurin ta saki wani kuka mai tsuma zuciya, Aryan shima da kuka ya fita gidan, yana fita ya tsaya gefen wani dakali ya durkusa agun ya shiga rera kuka tamkar k'aramin Yaro. Leema, Meena da Deeja ne suka zo suka d'aga Basma, suka wuce da ita part d'in Momy. Umma suka fita itama tana kwalla, a haka suka cimma Yaya Aryan ita da Yaya Ahmad da kuma Yaya Naufal, dafashi Yaya Ahmad yayi, ya d'agoshi ya shiga share masa hawaye tare da gaya masa kalamai masu sanyaye rai. A haka ya sanyashi a mota ya wuce dasu gidan da Abba ya basu. B'angaren Shureym kuwa Mami ta aika Sarkin Gida da wasu mutane garin Yola, an basu auren Safeena, sun kai musu akwati da komai da Shureym ya siya, anyi shagulgulan Biki lafiya an d'auko Amarya. sun sauka a gidanta dake garin Kano wanda Shureym ya gyara shi sosai, komai na jin dad'i akwai a gidan. Sun gama bikin auren sirri, wanda daga Mami sai Shureym sai wanda suka je nema masa aure sune kawai suka sani. An bar Amarya da Ango suna cin Amarci. Momy ta samu Ammi akan batun Auren Yaya Ahmad da Deeja, tayi mata bayani mai gamsarwa, Ammi ta sauko, tace ta hak'uri amma tana son Ahmad ya zauna da matar anan cikin gidan President, ta da sanyawa Auren Albarka, Momy taji dad'in haka sosai, tace zata Sanar ma President domin a gyara part d'in da Ahmad zai zauna. *Biki saura mako guda* Anata shirin biki ta ko ina, mutanan Kano sun tattaro sun wuce Abuja, mutanan Kaduna ma haka, gidan president ya cika da dangi da abokan arziki, kowa kagan shi yana cikin farin ciki. Amare kuwa sunsha gyara sai kyalli suke, a zuwa yanzu su Yaya Naufal da Yaya Jamal sun sauko da k'in da sukewa su Meena, yanzu burinsu bai wuce a d'aura aure ba susha amarci, sai dai a Kasan zuciyan Yaya Jamal yayi alkawarin sake aure da sabuwar budurwa domin shima ya mori aure, dan yasan Leema saura zai samu agunta. Basma ta saduda sosai tayi sanyi, tana tsayawa tayi hira da Yaya Shureym amma a k'asar zuciyanta Aryan yana nan, kullun dare saita yi kuka na rashinsa, Shureym sai rawan jiki yake yi, yana nunawa Basma kuwala ta musamman, dan burinshi bai wuce yaga an d'aura Auren ba, domin yana cike da tsananin sha'awarta, yasan duk k'insa da take yi da an d'aura zata bada kai bori ya hau. B'angaren Safeena, Yaya Shureym ya sanar mata da komai na aurensa da Basma, ta nuna rashin damuwa akan haka, sun tawo Abuja a tare, ya kama mata d'aki a hotel har a gama bikin su wuce America, Safeena burinta bai wuce ana gama shagalin biki ba su wuce America, ta juya Basma yanda ranta keso, domin Shureym ta gama dashi a tafin hannunta yake, sannan tayi alkhawarin Shureym bazai tab'a tarawa da Basma ba in dai tana raye. Amarya Deeja tayi kyau tamkar ba ita ba, hatta Ammi da take k'inta ta yaba da yanda ta sauya, fatarta tayi kyau, kamannin ta da Meena ya fito sosai, a hankali taji ta kwanta mata arai saboda yanda Deeja take mata biyayya da kuma nuna kunya a gareta a matayinta na mahaifiyan mijinta, cikin k'ank'anin lokacin ta nima k'iyayyar da take mata ta rasa, har wautan kanta take gani akan meyasa ta nunawa Yarinya tsana haka. Deeja ta koma gida, ta samu su Ammi a sabon gidansu, domin a nan ne za'a d'aukota a kawota gidan president. *Ana gobe biki* Mutane sun gama hallara, ta wajen su Umma mutanan Gombe sunzo, sai dai mahaifinta Malam ba shida lafiya, dan haka Innarta basu samu zuwa ba sai danginsu, sunata shirye-shirye cikin kwanciyar hankali. Yaya Aryan ya bar K'asan ana saura kwana uku biki, ya wuce K'asar Manaco domin yaji ba zai iya tsayawa bikin ba, koda ya isa k'asar ya kashe duk wayoyinsa ya soma Harkan karatunsa, Basma tana ransa, shi kad'ai yasan irin k'unan da zuciyansa yake ciki, kullun saiya kalla hotunanta da wanda take ita kad'ai da wanda suka d'auka tare a cikin system d'inshi, wani yayi murmushi wani yayi kuka, ya saba da haka, harya zame masa jiki. *Ranar daurin aure* Angwaye sun fito sunyi fas sai shek'i suke yi, ta b'angaren amare kuwa tsayawa fad'an kyawunsu b'ata lokaci ne, Basma koda tana cikin damuwa tayi kyau, tasha kwalliya amma bai haka zuban hawaye a fuskanta ba, duk wanda ya ganta saiya tausaya mata, ta k'ara tsukewa ta rame, ko tayi dariya yake tayi, sam bata farin ciki da wannan auren, Addu'a take Allah ya bata hak'uri da juriya akan auren. Bayan sun idar da Sallah Juma'a limamin masallaci ya sanar da d'aurin Auren yaran President da Gomnan Kaduna, da kuma Sarkin Kano. Biki na 'yayan gata. An d'aura auren Yaya Ahmad da Khadija Yaya Shureym da Basma Yaya Jamal da Haleema Yaya Naufal da Ameena Yaya Adam da Munaya 'yar wazirin Sarkin Kano. Anyi addu'o'i kana aka wuce taron walima a babban hol dake fadar Shugaban k'asa, anci ansha kowa ya shaida wannan aure, na 'yayan manya ne kuma masu gata. Basma tana jin an d'aura ta shiga d'akinta ta kulle kanta, kwantawa tayi a gadonta ta fara kuka mara sauti, hoton Aryan a wayanta take kallo tace "shikenan an rabamu, Yaya Aryan ina sonka Allah ya rabamu, Allah kasamin juriya da hak'uri azuciyata, Aryan na je soyayyarka a zuciyata, zan yi kok'arin yin biyayyar aure ga mijina, Allah ya had'a fuskokinmu yasa na zama matarka a aljanna" saita b'alle da sabon kuka. A haka barci mai nauyi ya d'auketa, ba ita ta farka ba sai bayan sallan La'asar. Wanka ta tayi, ta canza wasu kayan zuwa leshi marun mai fulawa fari, tayi makeup tamkar ba Basma ba, ta b'ata lokaci sosai wajen kwalliya, kana ta aza gwagwaro Fari, ta sanya takalmi mai tsini, turaruka kuwa kamar wanka tayi dasu. Kallon kanta tayi a madubi, ita kanta ta yaba da Kyan da tayi. Ta fito a Queen Basma. A can kuwa cikin gidan hankalin kowa ya tashi ba'a ga Basma ba, an duba duk inda ya kama ta amma ba'a ganta ba, gaba d'aya gidan ya hautsine cikin tashin hankali, a cikin wannan yanayi ne Basma ta fito cikin taku na k'asaita, yau Queen Basma ta fito a sunanta, ai sai kallo ya koma gunta cike suke da mamakin ganinta a rinin wannan shiga, nan take suka fara murna, Basma tayi kyau sosai, masu d'aukan hoto suka fara d'aukanta, Ammi ce ta tawo da gudu ta rungemata tace "Basma ina kika shige ne haka?" dariya tayi tace ina d'akina, nayi bankwana da Yaya Aryan shine barci ya d'aukeni, yanzu na kimsha nace bari na fito a cigaba da shagalin Biki dani" ai baki bud'e Ammi ta bita da kallo tana mamakinta tare da tausayinta. *Rahma Ce* [8/7, 8:33 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *15.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *Da dare* An shirya kayataccen Dinner a katon hol mai d'aukan mutane dubu, manyan mutane sun halarci wannan Dinner, harda wasu yan k'asashen waje sun halarta, Amare da Angwaye sunsha kyau, ko wanne zaune yake da Amaryansa, Safeena na zaune cikin mutane ranta ya gama b'aci, zuciyarta yana mata zafi dan tsananin kishi, tunani ta shiga yi, ita fa Auren sirri aka mata sam ba'ayi irin wannan shagalin ba, haushi ya k'ara cikata, amma tasan matakin da zata d'auka akan Shureym, dan taga yana ta rawan jiki akan Basma. Kowa ka ganshi a wannan lokacin yana cikin farin ciki, amma banda Basma da take cikin damuwa na rashin ganin Aryan agun, dan batasan yayi tafiya ba, sai kuma Safeena da take jin haushi akan mijinta. Anyi taro lafiya an watse lafiya, cikin farin ciki da kwanciyar hankali. *Washe gari* An kai ko wace Amarya gidan Mijinta da misalin larfe hud'u na yamma, Deeja an kawota gidan president a side d'in mijinta, haka Meena ma an ajeta acikin gidan president, part d'insu na gefen nasu Yaya Ahmad, Leema kuma an wuce da ita Kaduna zuwa gidan Jamal da Dady ya siya masa, sai Yaya Adam an wuce da matarsa Munayah, an kaita part d'inta dake cikin gidan Sarki, Basma ita ce tayi saura a gida, itama part d'inta yana gidan Sarki kusa dana Yaya Adam, kasantuwar Yaya Shureym bai gama aikin da suka d'aukeshi ba na shekara biyu, yasa zasu wuce America, su cikasa sauran shekara d'ayan daya rage. Sauran baki kuma suna nan basu soma tafiya ba. Sai Washe gari ko wani Ango ya shiga d'akin matansa, suka fud'e faifan sabon rayuwa cike da So da K'auna. Da safe su Basma suka wuce airport, da kyar aka raba Basma da jikin Ammi, tasha kuka kaman ranta zai fita, Shureym kuwa sai wani kamata yake yana lallashi, sun shiga jirgi Basma na d'agawa iyayenta hannu, ji take kamar in ta tafi bazata dawo ba, haka suka zauna wuri guda, sannan aka rufe k'ofar jirgi, ana rufewa Shureym ya tashi kusa da ita ya kowa gefen hagunsa, kusa da Safeena ya zauna, ta cika ta batse dan haushi, Basma ta bishi da kallo ganin ya zauna kusa da wata mace cike da mamaki, bata iya cewa komai ba, Safeena ce da taga Basma na kallonsu, sai tayi saurin sakin fusha ta juyo fuskanta tana kallon Shureym, sai ta had'a bakinsu guri guda, ai da sauri Basma ta kauda kai, zuciyarta na dukan uku-uku, bakinta na fad'an "Inalillahi wa inna ilaihir raji'un" kwantar da bayanta tayi jikin kujera, ta runtse ido, tsananin radad'i zuciyarta yake mata, bawai kishin Yaya Shureym taji ba, tsabar bak'in ciki da irin tsanar hayayyansa take, a tunaninta k'aruwansa ce, Safeena tana ganin Basma ta kauda kai, sai ta janye jikinta ta fara magana k'asa-k'asa tace "Baby wlh ka b'ata min rai cikin kwanakin nan, naga sai wani rawar jiki kake akan wancen yar iskan Yarinya, to wlh ka sani bazan tab'a raba kwana da ita ba, alkwari ka d'aukan min cewa kai mijin mace d'aya ce, dan haka kai nawa ne ni kad'ai, tunda kace had'in zumunci ne shiyasa na yarda da auren, dan haka da kanta zata gaji da zaman gidanka, harta nima saki tayi gaba" Gaban Shureym ne ya fad'i, hankalinsa ya tashi, amma sai ya dake ya wayince yace "Love ke kad'ai ce a guna, me zanyi da Basma, had'in zumunci akai mana dan bana sonta" Cike da murmushi tace "yauwa Babyna, kamin alkwara ba raba kwana da ita" murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace "na miki alkawari, ai bana son b'acin ran ki, ko me kike so zan miki domin in saki farin ciki" Safeena farin ciki ya rufeta, take nan ta manta da b'acin rai data shiga. Basma kuwa kuka ta shiga yi mara sauti, a haka har barci ya kwasheta. *America* Bayan sun kai, mota biyu ke jiransu, d'aya wanda zai d'auki kayan su, d'aya kuma wanda zasu shiga, Basma jikinta a mace ta bud'e k'ofan bayan mota zata shiga, sai Yaya Shureym ya daka mata tsawa yace "Karki kuskura ki shiga nan, ki shiga gaba ki zauna da driver, ko baki ga ina tare da matata bace?" cikin tsoro Basma ta bar jikin mota cike da tsiwa tace "Matarka ko Karuwa?" Ai bata rufe baki ba ya tawo da sauri ya wanketa da mari, a razane ta dafe kuncinta tace "Ni ka mara akan wannan yar iskan, to Allah ya isa mugu fasik'i kawai" tana gama fad'an haka tabar wurin da gudu, ta shige gaban motan daya d'auki kayansu ta zauna, driver ya tukasu suka wuce. Cike da k'unar rai Yaya Shureym ya girgiza kai yayi kwafa, iya ka k'uluwa Safeena tayi, amma ta share suka shiga mota tana sake-saken irin matakin da zata d'auka akan Basma, Lallai dole saita fahimtar da ita cewa ita matar Shureym ce. Suna isa gidan, ta shiga babban falon gidan Driver ya shigo musu da kayansu, d'akuna uku ne a cikin falon, ko wanne da kaya aciki wanda President yasa aka sanya musu komai na buk'ata aciki, Basma ta zauna akan kushim tana jiran su Shureym su shigo, koda suka shigo sai suka zauna suma, Yaya Shureym ya kira wani kuku, sai gashi da gudu yazo, da yake gidan ai'nahi anan Shureym yake zama, ya Umarcesa daya kawo musu ruwa, da sauri yaje ya kawo musu ya dire musu goran ruwa biyu da cup, yaje zai aje goran ruwa a gaban Basma, sai Safeena ta dakatar dashi cikin turanci tace "kai zonan" jikinsa na b'ari ya isa gurin ya risina, tace "daga yau Ni zaka rik'awa aiki amma banda wacen 'yar iskan, domin Mijina ni kad'ai yake aure" tana kaiwa nan tayi shuru, jiki na rawa Kuku ya amsa mata yabar gurin. Cikin ko in kula Basma ta mik'e tace "Yaya Shureym ina ne d'aki na?" Hararanta yayi yace "ban sani ba mara kunyar banza, wlh nan ba Nigeria bane da zaki min iskanci na d'auka, koda kika ga ina lallab'a ki, dama ina yi ne dan ayi auren, saboda kar in b'atawa Iyayena rai, kuma ki sani bana son ki, biyayya ga Iyayena yasa na aureki" Gaban Basma ne ya shiga bugawa da sauri, saboda tashin hankali, ya cigaba da cewa "kinga wannan sunanta Safeena, itace zab'ina, kuma munyi aure da ita wata guda daya wuce cikin sirri, ba tare da kowa ya sani ba, daga ni sai Mami na data goya min baya, dan haka in kina son zaman lafiya a gidan nan, to dole sai kin bita sauda k'afa, inba haka ba wlh na lahira saiya fiki jin dad'i" Basma durkushewa tayi a gurin, saboda k'afafunta bazai iya d'aukanta ba, ta shiga rera kuka wiwi, sai ya kwashe da dariya yace "wawuya nasan kin d'auka son ki nake ko, tashi dalla ki bani wuri, ki wuce d'akinki shine na gefen hagu, na tsakiya kuma nawa ne, na gefen dama na Safeena ce, kuma na haramta miki shiga d'akina" yana kaiwa nan ya mik'e ya kama hannun Safeena suka wuce d'aki. Basma cikin tashin hankali taja trolley kayanta, ta shiga d'akin daya gaya mata, katon d'akine mai d'auke da katon gado, sai daga gefe an jera kujeru set, sai bayi da kicin a ciki, kalan d'akin da kayan ciki purple da ash color ne, rufe d'akin tayi da key, ta shiga wanka, kanta ta sanyawa ruwa sosai, saboda zafin da yake mata, tayi kuka kamar zata shid'e, daga bisani tayi wanka ta d'auro alwala ta fito, kaya ta sanya mara nauyi, ta sanya hijab ta tada sallah, sai da ta rama duk Sallolin da ake binta kana tayi Addu'a, ta mik'e ta shiga cikin d'in d'akinta, komai data ke buk'ata akwai aciki, dan akwai k'aramin store a ciki, ruwan tea ta dafa, ta zo ta diba cin-cin d'in data tawo dashi a plet, ta zauna taci kana ta d'aura da danbun Namam kaza, bayan ta gama sai ta kwanta akan doguwar kujera, ta runtsa idonta ta shiga tunanin wani irin rayuwa zatayi yanzu, kuma wani mataki zata d'auka akan Yaya Shureym da Safeena wacce yake ik'ira rin matarsa ce, hawaye ne ya sauka a kuncinta, a fili tace cikin kuka "babu wanda ya jamin wannan rayuwa sai ku Abbana, dan haka ba wani matakin da zan d'auka ma, domin ko me ya sameni kune sila" Ta goge hawayenta, ta d'auko wayanta ta shiga kiran Momy, ta sanar da ita sun sauka lafiya, nan sukayi sallama, ta kira President ta sanar masa da sun sauka lafiya shima, haka kuma ta kiranl Ammi ta sanar mata da sun sauka lafiya itama, bayan ta gama wayan, sai ta tuna da Umma, sai tayi murmushi, itama ta kira ta suka gaisa, Umma tayi mata nasiha sosai akan biyayyan aure, kana suka yi sallama, saita kashe wayen gaba d'aya ta gyara kwanciya, bata dad'e ba barci ya d'auketa. *A Nigeria* Mutanan Biki duk sun watse sai dai-dai da suka rage, ta b'angaren Amare kuwa sunata cin Amarci hankalin su kwance, kowa yana cikin farin ciki. Ta b'angaren Yaya Jalal ya samu Leema ta yanda bai yi tsammani ba, domin gaskiya tasha gyara wajensu Momy, duk da dai bata isa ta maida mudurcinta ba, amma dai ya gamsu sosai da ita, Leema ta kasance cikin murna da yanda Jalal ya saki jiki da ita, tamkar babu wani abin da ya faru a baya. *A K'asar Monaco* Yaya Aryan ya cigaba da rayuwa shi kad'ai, da Umma kawai yake waya su gaida, da sun gama saiya kashe wayan. Kullun soyayyan Basma k'aruwa yake a zuciyansa, yanzu da baya ganinta yafi shiga tashin hankali da damuwa, ya k'ara ramewa sosai, burinsa yanzu bai wuce Basma ta kwantar da hankalinta ba, tayi rayuwan Aure cikin farin ciki da annatsuwa. Ya duk'ufa sosai wajen karatunsa, yana k'ok'arin kafa sabon rayuwa. *Bayan mako guda* *A America* Basma tunda ta kulle kanta a d'aki, bata kuma bud'ewa ba har tsawon mako guda, komai a cikin d'akinta take yi, hatta girki da kanta take yi, taci ta wanke kayan data b'ata, tun yin aikin na bata wuya kasantuwar bata saba yi ba, har ta fara sabawa, Allah yasa ta iya girki, domin Momy ta koyawa Basma girki dan gaba zai mata amfani, kamar yanda yanzu ya soma mata amfani. Yaya Shureym suna falo suna hira, Safeena tayi pillow da cinyansa, hankalinsa na kan k'ofar d'akin Basma, hira take mishi amma sam baya tare da ita, sha'awan Basma na d'awainiya dashi, sannan ya fara damuwa da rashin ganinta da baiyi ba, tun ran da suka zo, bai sake tozali da ita ba, Safeena ganin baya tare da ita ya barta tana ta surutu, sai ta d'ago kai tana kallon direction d'in da yake kallo, gabanta ne ya fad'i cikin jin haushi tace "Baby tunanin me kake yi haka? Ko ka fara sonta ne?" Firgigit ya farka, cikin inda-inda yace "ba komai, me zanyi da Basma, Allah ya kyauta" cikin fushi tace "k'arya kake yi, d'akinta fa kake kallo, kana ce min ba komai" murmushin ta kaici yayi domin ya soma gajiya da yawan k'orafinta, kawai ba yanda zaiyi da ita saboda yana sonta, kuma baya son b'acin ranta yace "kedai kin cika kishi, kawai ina tunanin yarinyar nan ne, akan tunda muka zo ban ganta ba, ina tsoron kar wani abu ya sameta, domin in wani abu ya sameta wlh zamu shiga cikin matsala, kinsan *YAR SHUGABA* ce, gwara na rika duba lafiyan ta domin president ya bani amanarta, ko ba komai kuma 'Yar Uwata ce" Safeena cikin nuna ko in kula tace "wannan kaita shafa" tana gama fad'an haka ta mik'e ta shiga d'aki tana jan tsaki, binta yayi da kallo yace a fili "Safeena sarkin kishi" sai ya mik'e ya nufa d'akin Basma... *Rahma Ce* [8/7, 8:34 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *16.* _Na_ _*Rahma Kabir*_ Yana isa d'akin ya shiga bugawa, kwance take bisa gadonta tana kallon tv, koda taji bugun k'ofan, ta d'auki kusan minti uku kafin ta mik'e ta nufi k'ofar ta bud'e, tsaye ta ganshi yana k'are mata kallo, miyau ya had'iye da k'arfi, gaba d'aya hankalinsa ya tashi da ganin Basma cikin k'ananun kaya, hararansa tayi cikin tsiwa tace "Malam lafiya ko da matsala ne" guntun murmushi yayi bai ce komai ba, sai yabi gefenta ya kutsa kai cikin d'akin, zama yayi kan kujeran zaman Mutum d'aya, ya shiga k'arewa d'akin kallo yana shakar kamshin d'akin, wanda ya saukar masa da kasala had'e da tsananin sha'awar Basma, ita kuma tura k'ofan tayi ta koma cikin d'akin ta zauna gefen gadonta ta cigaba da kallon tv, sun kai minti biyar a haka ba tare da wani yace wani abu ba, Yaya Shureym ne ya katse shurun yace "Basma meyasa bakya fitowa falo ki zauna?" Cikin nuna ko in kula tayi banza dashi, yace "magana nake kinyi banza dani" Cikin yatsina fuska tace "naga cewa wannan ba matsalan ka bane, ka je ka cigaba da zama da karuwanka, don ni ban yarda aure ku kai ba, kyamarka nake ma, da zaka taimaka ka tashi ka fita da ka kyauta min" "Iya b'acin rai ransa ya baci, mik'ewa yayi da sauri zai isa inda ta zauna, ai da sauri itama ta mik'e tana ja da baya harta isa jikin bango, kankame jikinta tayi ta runtse ido domin yanda taga ransa ya b'aci ta sadakar zai duketa, gabda ita ya tsaya wanda hartana jin hucinsa, hannunta ya shiga b'amb'arewa a jikinta, a razane ta bud'e ido tana kallonsa, ba tayi aune ba ya rungumeta da k'arfi ya matseta a jikinshi, tirjiya ta shiga yi tana k'ok'arin kwatar kanta, ganin ya rik'eta gam yak'i sakinta, saita gantsara masa cizo a damtsan hannusa, da sauri ya saketa yana yarfe hannu, saita maza ta matsa a gun, yana jiyowa ya nima k'ara kamota, da sauri ta ruga, guje-guje suka fara a cikin d'akin, yana k'ok'arin kamata tana kaucewa. Safeena shiganta d'aki da tayi, tana tsammanin Shureym zai biyo bayan ta, sai taji shuru, ganin haka yasa ta lek'a falo sai taga wayam baya gun data barshi, cike da masifa ta fito ta nufi d'akin Basma, tana bud'e k'ofa sai ta cimmusu suna wannan wasan guje-guje, ai sakin baki tayi tana kallonsu, shiga ciki tayi rai b'ace, Shureym yana ganinta yayi sauri ya tsaya yana sosa k'eya, mugun kallo Safeena tabi shi dashi bata ce masa uffan ba, sai nuna masa hanyar waje tayi alaman ya fita, sum-sum ya fita yana murmushi k'asa-k'asa, yana fita ta gyara tsayuwa tana kallon Basma tace "A hir d'inki da Mijina domin ba sa'anki bane, in kuma ke mayya ce to Mijina yafin k'arfinki, ki shiga taitayinki domin wlh inna kuma ganin haka zan d'auki tsastsauran mataki mafi muni a gareki" tsaki Basma tayi tace cikin fad'a "ai ko wlh da kinga yanda zanyi k'asa-k'asa dake, ke d'in banza ke wacece da zaki zo ki nima shiga tsakanina da Mijina kuma d'an Uwana, kefa ba kowa bace face karuwa mara lasisi mara mutunci, ki gaugauta fita sabgata domin had'uwata dake bazai yi kyauta, kibar ganin ina miki shuru-shuru, jaka kawai" Ai tuni Safeena ta cika ta b'atse, magananun Basma sun tunzurata, bata san lokacin da tayi kukan kura ba ta nufi Basma gadan-dagan, Basma na ganin tayo kanta sai ta shige bayi da gudu tare da sanya key, tana maida numfashi, iya tsoro ta tsorata da Safeena, dan ta girmeta kuma ta fita girman jiki, tace a fili "ko banza nasha dakyar muguwa kawai" Safeena tana ganin ta shige bayi sai tayi kwafa, ta fita da sauri. Ta tada Shureym a d'akinsa, ta shiga surfa masa masifa shi dai uffan bai ce ba, da ya gaji da jin haya niyarta sai ya shige baya danyin wanka ya barta tsaye baki na kumfa, a ransa yace "Safeena akwai masifa, ta dage ta hakikance akan abin da yake halal d'ina, gaskiya bazan d'auki wannan sakarcin ba, domin ko ban son Basma ai ina feeling d'inta, balle ma ina sonta kawai kauda kai nake ina miki biyayya, saboda ina tsananin sonki, amma nasan hukuncin da zan d"auka" Basma sai da ta tabbatar ta fita a d'akin saita fito da sauri ta rufe k'ofarta, ta haye gado tana kwasar dariya, ko ba komai ranta ya mata dad'i tunda ta bak'anta ran Safeena, Jakarta ta jawo na kayan gurinta, lollypop ta d'auko, ta bud'e sweet ta sanya a baki tare da lumshe ido dan dad'in ya fara ratsa ta, nan take ta tuna da sunanta Queen Basma 'yar rawa, tashi tayi ta kunna radio tare da sakin sauti, ta shiga cashewa son ranta tare da tuno rayuwanta na makaranta cike da nishad'i. Yaya Shureym ya fito zai fita, jin wakar da Basma ta sanya yasa shi girgiza kai, a fili ya furta "Basma dangin k'uruciya" sai ya fice, Safeena ma fitowa tayi cikin shirin fita tabi bayansa da sauri ta taddashi harya kunna mota zai wuce, da sauri ta cimmasa ta bud'e gaba kusa dashi ta zauna, tana mai kallonsa cike da shagwab'a tace "haba baby shine zaka tafi ka barni" murmushi yayi yace "ai naga fushi kike dani shiyasa nayi shirin fita in je in wayata kona sarara" kamo hannunsa tayi tace "sorry Baby, d'azu raina ne ya b'aci bazan sake ba" gyad'a kai kawai yayi alaman ya gamsu, sai suka fice daga gidan. *Washe gari* Shureym ya tashi da sassafe yayi shirin office, haka ma Safeena tayi shirin fita, nan suka had'u suka fice a gidan. Basma tana jin k'aran fitan motansu, saita bud'e k'ofa ta fito, d'akin Shureym ta shiga ta gama kallon komai, yanda akayi decoration d'akin yayi mata kyau, kalan fentin coffee brown da milk color, haka ma kalan furniture d'in, d'akinsa ba kitchen sai dai akwai toilet babba wanda yafi nasu Basma. D'akin Safeena ma yanayin d'akin Basma ne, sai dai itama ba Kitchen sai toilet kamar na Basma, kalan fentin d'akin ash da pink ne hakama furniture d'inta, fitowa tayi ta shiga cikin babban kitchen na falo, nan ma ya tsaru sosai, kuku guda biyu ta gani a ciki, cikin ladabi suka gaisheta tare ta tambayan abinda take buk'ata, da murmushi tace "bata buk'atar komai" shiga tayi store d'in ta shiga diban abinda ba tada shi ta kai kitchen d'akinta, kana ta fice farfajiyan gidan, baya ta nufa inda shukoki na furanni suke, ta tsak'i iskan wurin sai taji dad'i a ranta, nan take ta tuno da wurin shak'atawan da suke zuwa ita da Yaya Aryan, idonta ya ciko da kwalla, zama tayi kan wani kujera na katako mai lilo, runtse idonta tayi ta shiga duniyan tunanin Aryan, ta kai kusan rabin awa agun kana ta bud'e ido, ta shiga rera kuka, istigfari tayi ta nima yafiyan Allah akan tunanin da tayi na Aryan Alhalin tanada auren wani akanta, tashi tayi ta nufi d'akinta ta fad'a bayi dan watsa ruwa, ko jikinta zai mata dad'i. Yaya Shureym yana office amma ya kasa aiwatar da komai, gaba d'aya tunanin Basma ya cika masa kai, burinsa bai wuce ya samu Basma ba, agogan hannunsa ya duba yaga k'arfe 11am na safe, mik'ewa yayi da sauri ya d'auki wayansa, jakansa da key d'in mota ya wuce gida. Basma ta fito wanka d'aure da towel a k'irjinta, tana zaune gefen gado cike da damuwa a ranta, tunanin iyayenta da family d'inta takeyi, tunawa tayi da tun ranar da suka sauka ta kashe wayarta bata kuma waiwayan sa ba, murmushi ne ya sub'uce mata data tuna dasu Meena, tunanin ya sukaci amarci ne ya fad'o mata, tace a fili "guys nayi missing d'inku sosai, anjima zan bud'e waya muyi chart" Tana gama fad'an haka taje kusa da dressing mirror ta soma Shafa mai, jin motsin k'ofa tayi sai ta juya da sauri, dan shaf ta manta bata rufe ba d'azun, Yaya Shureym ne tsaye yana jefo mata mayen kallo, gabanta ne ya shiga fad'uwa sam bataji k'ugin motansa ba, takowa ya fara yi yana mata wani shu'umin murmushi, Jada baya ta shiga yi, k'ok'arin isa Waldrop d'inta tayi da nufin d'auko hijabi dan ta sanya, da sassarfa ya cimmata a gurin, jikinta ne ya soma b'ari, hannu ya kai saman k'irjinta inda ta d'aura towel d'in, ta rik'e gam ta shiga kuka tana cewa "meye haka Yaya Shureym dan Allan ka fita" Murmushi kawai yayi ya sanya k'arfinsa ya fisge towel d'in, da sauri ta zukunna k'asa ta shiga kuka da k'arfi, d'aukarta yayi ya jefata kan gado, zanin gadon ta jawo ta rufe jikinta dashi, cire kayansa ya shiga yi, vest da gajeran wandon kawai ya rage a jikinsa, sai ya hau kan gadon, Basma ganin haka ta kuma rushewa da kuka, bai hanashi fasa k'udirinsa ba, zanin gadon ya shiga yayewa amma Basma ta cukukuye jikinta da shi, wani wawan mari ya sakar mata, sai ta tsandara uban ihu, duk da haka baisa ta saki ba, cikin fushi yace "wlh ko ki so ko kar kiso yau saina karb'i hakk'i na" Wani marin ya kuma sakar mata, duk da haka tak'i saki, da k'arfi ya finciko zanin gadon, sai ta k'ank'ame hannunta a k'irjinta, kuka take kamar ranta zai fita, magiya ta shiga yi masa cikin kuka "Yaya Shureym dan Allah ka kyaleni karka kasheni, me nayi maka ne da zaka yi min mugunta" Bige mata baki yayi, bakin ya fashe sai jini, abinda yake son aiwatarwa bai fasa ba, Basma kuwa gunjin kuka take yi, a wannan lokacin tariga ta sadak'ar, cizo ta ganna masa a kunne sai ya saketa ya kai mata naushi a baki, ya shiga dukanta ta ko ina Basma wani wahalanlan ihu ta saki wanda yayi dai-dai da shugawar Safeena falon, dama ta shigo falon da mamaki, saboda ganin motan Shureym da tayi a gida, da sauri ta nufi inda take jin kukan, harta isa d'akin Basma, ta tsaya a bakin k'ofar, dai-dai lokacin Shureym yana k'ok'arin kai ga cika k'udurinsa Basma ta saki wani wawan k'ara, ai da k'arfi Safeena ta tura k'ofan ta buga garam, ta fad'a d'akin ta tuna huci.... *Rahma Ce* [8/8, 5:38 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *17.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 K'aran bugun k'ofar shine yayi dai-dai da Shureym ya dawo hayyacinsa, da sauri ya sauka akan gadon, cikin jin haushi da borin kunya ya kwaci kayanshi a hannu ya fita a d'akin, da gudu-dugu ya fad'a d'akinsa tare da sanya key. Basma kuka take tana cewa "Allah ya isa bazan yafe maka ba, mugu azzazulumi insha Allah harka mutu baza ka cimma burinka a kaina ba" furucin Basma na k'arshe shine ya sanya Safeena ajiyan zuciya, dama fargabanta shine ace ya samu Basma, tasan lallai kashinta ya bushe, gashi Basma ta fita komai na kyawun sura, sannan ta tabbatar Basma bata bin maza lallai zai sameta a budurwa, kallo Basma tayi cikin tausayawa, da sanyin murya tace cikin tsoratarwa "Kad'an kika gani in dai Shureym ne, mugune shi sosai haka yakemin nima, karki k'ara yanda haka ta faru in ba haka ba wataran zai kashe ki, maza tashi ki gasa jiki a toilet, kuma karki sake barin k'ofarki a bud'e, dan Shureym ya wuce yanda kike tunani" tana gama fad'an haka ta fice a d'akin. Basma wani sabon kuka ta saki, da kyar ta iya sakowa daga gadon, tana bin bango harta shiga bayi, ruwa ta had'a mai zafi ta shiga ciki, ta kai kusan rabin awa tana ciki, kana tayi wanka ta fito, mirror taje ta tsaya tana kallon yanda fuskanta ya kummbura, hawaye ne ya sauka a kuncinta mai zafi, fuskan ta tayi ja sosai, gashi kumatunta ya kunbura da leb'enta, idonta yayi k'anana gaba d'aya ya sauya mata kamanni, hawaye ta share tace a fili "Abba Ku kuka jamin" kaya ta sanya marasa nauyi ta cire zanin gadon ta ta sanya wani, taje ta kulle d'akinta ta koma gadon ta kwanta cikin k'ankanin lokaci barcin wahala ya d'auketa. Shureym saida ya samu yayi wanka kafin ya samu nutsuwa, nadama ne ya lullub'eshi akan abinda yayi wa Basma, ga kuma kunyar Safeena da yakeji, wannan dalilin ne ya hanashi fitowa sai kawai ya kwanta har barci ya d'aukeshi. Safeena kuwa ta kasa ta tsare a falo tana jiran fitowan Shureym, jin yayi shuru bai fito ba saita gyara zama ta kunna tv tana kallo, sai bayan k'arfe biyu Shureym ya fito daga d'akinsa, ya had'e giran sama dana k'asa yana hura hanci duk na borin kunya, Safeena tana ganin shi sai ta kwashe da dariya, dan gaba d'aya ya bata dariya sai wani basarwa yake yi, zama yayi gefenta yace cikin fishi "meye kika gani na dariya a jikina?" ya mutse fuska tayi tace cikin tsiwa "wlh Shureym kaji kunya, banda Allah yasa nazo na ritsaka, da ka kashe musu Yarinya, kanata cika min baki akanta, ashe duk burga ce na d'a Namiji, Allah ya kyauta maka, kuma ka sani Basma Yarinya ce imma zaka amshi hakk'inka, to ba da k'arfi zaka amsa ba saika bita a hankali" Tana gama fad'a ta mik'e ta shige kicin, abinci ta zubo masa ta mik'a masa, murmushi yayi ya amsa tare da cewa "Tnx my Baby, banyi tunanin zaki saurin saukowa haka ba" hararenshi tayi ta koma ta zauna tare da d'aura k'afa d'aya kan d'aya, ya soma cin abincin tace "Shureym ina Sonka sosai, bazan iyi dogon fishi da kai ba, da ace d'azun baka rufe d'akinka ba, har na sameka a ciki, da saina sauke maka kwandon rashin mutunci, amma na sauko, sai dai yanzu na daina yarda da alk'awarinka domin nasan watara saika karya shi" zai yi magana ta d'aga masa hannu tace "kai dai ci abinci kawai". Bayan la'asar Basma tayi shigar doguwar riga abaya brown, tayi rolin da gyalen, jaka ta d'auka bak'i ta sanya takalmi bak'i, ta same su a falo bata kalli inda suke ba tayi hanyar fita, da sauri cikin tsawa Shureym yace "ke ina zaki?" tsayawa tayi cak bata juyo ba kuma bata ba shi amsa ba, saida ya kuma maimaita tambayan, amma shuru ta masa, k'arshema tasa kai ta fice, a zuciye ya mik'e zaibi bayanta, Safeena na rik'e hannunsa tace "haba Shureym wani irin abune wannan, ka duketa d'azun ka kumbura mata fuska, ka sani ko asibiti zata je, ka rabu da ita taji da kanta mana" cike da mamaki ya juyo ya kalleta yace "Safeena yaushe kika zama haka? da har zaki tausayawa wannan shaid'aniyar yarinyan' murmushi tayi tace "Shureym ni mace ce mai rauni, dole ne inyi saurin tausaya mata akan irin lahanin da kaso yi mata, tana gama fad'an haka ta d'aure fuska, kana ta wuce d'aki. Basma tana fita ta tari taxi asibiti ta fara zuwa, likita ya dubata ya bata Magani da kuma alluran zazzabin da take ji, daga nan saita wuce wurin wani gidan abinci, zama tayi ta sanya aka kawota drink da snacks, nan taci tana nazarin wani mataki ya kamata da d'auka, a haka ta gama komai saita wuce wani studio na kusa da gidansu, ta shiga ta sanya aka d'auki hoton fuskanta kana aka wanke aka bata ta dawo gida. Bata samu kowa a falon ba saita wuce d'akinta ta bud'e ta shiga tare da sanya key, wani jaka ta ciro ta bud'e da wani k'aramin key, ta ciro diary d'inta ta shiga rubuta abin da ya faru da ita na wannan ranar, sannan ta maida cikin jakan tare da sanya wannan hoton aciki, sai ta maida ta rufe ta ajeshi cikin wani dirowa, ta dawo kan gado ta zauna tare da rafka tagumi. Wannan diary d'inta ne tun ranar da suka sauka a k'asar America, ta fara rubuta duk abinda Yaya Shureym yake mata na muzgunawa a ciki, dan ya zame mata tarihi da zata rik'a tunawa. Wayarta ta ciro a jaka ta kunna, sak'onnin text suka fara shigowa, gaba d'aya text d'in yan uwanta ne, d'aya bayan d'aya ta rik'a karantawa, wani tayi kuka wani tayi dariya, nan take kewar family d'inta ya taso mata, WhatsApp d'inta ta bud'e, sakonni suka fara shigowa, ta mance rabonta da hawa online, group ta shiga na family d'insu, nan fa tayi sallama suka fara amsawa cike da murnan sake ganinta, duk suka gaisa na yaushe gamo, Meena ce tace "ke Besty akwai labari muje group d'inmu" nan suka koma group d'in su mai sunan *Manyan Mata, One family* Leema ma ta shigo can sai ga Deeja ta shigo, yanzu su had'u ne a group d'in, sunata murnan ganin Basma, nan suka shiga hira, Meena tace "kinsan kuwa Leema da Deeja ciki ne dasu" Basma cikin farin ciki tace "Dagaske? kice mun kusa samun yara" "Eh wallahi, two month yanzu" "ikwan Allah, yanzu fa mun kai 3month da aure, lallai abin ba wuya, to Allah ya musu albarka ya rabasu lafiya, to Meena kefa?" Meena tace "Ni nawa 1month ne yanzu" "lallai kuce kun girma, Allah ya inganta" Deeja tace "waya sani ko kema kina da naki a k'unshe bamu sani ba" dariya tayi sosai tace "wace ni, ai in gaya muku banda komai, ina planning tukunna" Leema tace "Malama ki fad'a mana gaskiya kawai" "Hmmm Allah kuwa gaskiyar kenan" nan dai suka cigaba da hira, sun shafe lokaci sosai suna hira, sallama su kayi saboda dare yayi sosai a Nigeria, su kuma Basma yamma ne a nan. Cike da kewar family d'inta ta mik'e ta shiga kicin, abinshi ta shiga girkawa. *Bayan Mako biyu* Basma ta shirya da yamma k'arfe hud'u, tayi shigar riga da wando na Pakistan, tayi rolin da gyalen shi, jaka ta d'auka da takalmi ta ficewarta, yau tayi sa'a ba kowa a falon, taxi ta tare ta nufi wurin cin abinci, yau drink kawai ta sha, saita ciro wayarta ta hau online tana chart dasu Meena, wani saurayi ne mai tsayi kyakkyawa, ya tako a hankali har wurin da Basma ta zauna, ya tsaya tare da yi mata sallama, cike da kulawa ta amsa tare da d'ago kanta, cikin harshen labarabci yayi mata magana yace "In zauna?" murmushi tayi tace "eh" sai ya zauna ya cigaba da magana "Ni sunana Bilal dan k'asar Sudan, nazo nan karatun masters d'ina ne" murmushi tayi cikin larabcin tace "sunana Basma Bulama ni 'yar Nigeria ce" cike da mamaki ya kalleta yace "kina nufin ke 'yar Nigeria ce?" Tace "kwarai kuwa" murmushi yayi yace "nayi miki kallon ke 'yar k'asar labarawa ce, shiyasa ma nazo nayi miki magana, ashe 'yan Nigeria sunajin labarci sosai haka" dariya tayi tace "sosai kuwa munaji, domin muna da makarantu acan na larabci" yace "good, yanzu meya kawo ki America?" murmushi tayi tace "Hutu muka zo tare da family na" yace "masha Allah, in ba damuwa zan iya zama abokinki?" murmushi tayi tare da yin tunani kad'an tace "eh ba damuwa" nan su kayi exchanging contact d'insu, tare da alkawarin zasu had'u washe gari in Allah ya kaimu, nan ya taka mata ta shiga taxi kana ya wuce shima yana farin cikin had'uwa da Basma, cikin k'ank'aninin lokaci ya kamu da Sonta, Basma irin tsarin matar da yake burin aura ce, dama ashe a Nigeria suna da kyawawan mata haka? Tambayan da yayiwa zuciyansa kenan, harya k'osa dare yayi gari ya waye su k'ara had'uwa. Basma tana isa gida ta same su zaune a falon, kallon arziki bata yi musu ba ta wuce su, Yaya Shureym yace "Basma wai ina kike zuwa ne?" cikin b'acin rai tace "inda ka aikeni, kuma ka fita cikin rayuwata in ba haka ba zan maka abinda baka tsammani daga gareni" tana fad'an haka tayi gaba, bud'e murya yayi yace "wlh in kika kaini mak'ura zaki sha wuya, mara kunyar banza" tsaki tayi ta bud'e d'aki ta rufa da k'arfi ya buga gam, kana ta sanya key, tayi wanka tare da d'auro alwalan Magrib. *Washe gari* Ya kama week end, yau Shureym yana gida yana hutawa tare da matarshi Safeena, da misalin k'arfe biyun rana Safeena ta fito, tazo d'akin Basma, bugawa tayi amma kusan minti biyu shuru Basma bata bud'e ba, saida ta kuma bugawa tare da bud'e murya tace "Basma ki bud'e Safeena ce" murmushi Basma tayi ta sauko a kan gadon ta bud'e mata, da murmushi a fuskan Safeena tace "Basma dan Allah kin iya wainar fulawa?" Basma tayi murmushi tace "eh na iya" "to dan Allah kiyi hak'uri ki d'an yi min mana, saboda Kuku basu iya ba, kuma wlh marmarinsa nake, in kuma ni nayi bazan iya ci ba" murmushi Basma tayi tace a ranta "shegiya yanzu haka ciki ne dake, kuma in dai wainar fulawa ce za kici kuwa" tace a fili "OK muje nayi miki" "yauwa sis nagode bari na jiraki a falo" murmushi kawai Basma tayi bata ce komai ba, tace aranta "wato yau kinzo da fuskan arziki kenan, saboda zaki more ni, dole a fake da cemin sis" kicin ta shiga, cikin minti talatin ta had'a mata wainar fulawa, taji kayan had'i kuwa, saita kawo mata harda ruwan sha, ta aje bisa table na falon, Safeena na gani ta Shiga lashe baki, jiki na b'ari ta jawo table ta shiga cin wainar, ai had'iyan farko ya tsaya mata a wuya, da sauri ta tashi da gudu ta fad'a bayin dake falo, ta shiga kwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta, Basma zama tayi a falon tana zuba dariyan mugunta, Safeena a galabaice ta fito ta zauna tana maida numfashi, Shureym ne ya shigo falon yana fad'in "Safeena lafiya har yanzu aman bai tsaya ba, ko zamuje asibiti ne?" cikin kasalan murya Safeena ta nuna Basma tace "kaga wacce ta sani amai, nace ta min wainar fulawa saita zabga masa yaji da gishi, loma d'aya nayi na kasa had'iyiwa saida na amayar dashi" cikin b'acin rai ya kalli Basma yace "dan Ubanki kashemin mata zaki ko, saboda kina bak'in ciki da abinda ke cikinta ko, to wlh maza tashi kije ki dafa mata wani wainar, kuma in kika yi kuskure jikinki zai gaya miki" Jikin Basma a sanyaye ta koma kicin ta kuma b'ata lokaci ta had'o wani wainar ta kawo mata, Safeena ta saki ciki ta soma ci harda lumshe ido dan dad'insa saida ta cinye tas kana ta kora da ruwa. Shureym ya kalli Basma yace "D'auko wancen da kika b'ata ki cinye, dan wlh baza kimin asanar abinci ba" cikin k'unk'unai tace "wlh ni na k'oshi" belt d'in wandonsa ya zaro ya rik'e, yaje ya d'auko plet d'in wainar fulawan ya dire a gabanta yace "wlh sai kinci, in kuwa baki cinye ba jikinki zai gaya miki" ai da sauri ta sanya hannu ta d'ibo, tana kaiwa bakinta, zafin yaji da gishiri ya d'arsu a kan harshenta, ai da sauri ta furzar tare da goge harshen, Shureym ya zuba mata belt d'in a gadon bayanta, ai saita tsandara ihu ta shiga sosa bayan, bai hanashi sake zabga mata belt d'in jikinta ba, ya shiga jibgarta tare da cewa saita cinye shi, Safeena dariya ta shiga yi tare da d'aura k'afa kan table, saida yayi mata lilis kafin ya dena dukanta, kuka take tace "Allah ya isa Shureym, haka kawai ka maidani baiwarka, wlh sai kayi nadaman abinda ka aikatamin, azzalumi fasiki, maci amana" wani wawan naushi ya kai mata a baki, nan take bakinta ya fashe ya shiga zubda jini, da sauri Basma ta dafe bakinta tana kuka, tashi tayi dakyar ta isa d'akinta... *Rahma Ce* [8/8, 5:41 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *18.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Bayi ta shiga ta gasa jikinta da ruwan zafi, domin duk jikin yayi mata tsami, bayan ta fito ta samu ta sanya kaya ta fice zuwa studio, photo ta d'auka aka wanke mata, fuskanta ta fito da kyau bakinta a kubbure, ta dawo gida. Rubutawa tayi a diary d'inta kamar yanda ta saba, kana ta koma ta ajiye shi a mazau ninsa, ta had'a tea tasha kana ta d'aura da pain relief tasha, saita bi lafiyan gado. *Nigeria* Gudu take tana ihu, Abba kawai take kira tana cewa "wayyo Abba zai kasheni kazo ka taimake Ni, Momy na wai bakwa sona ne kuka bari zai kashe ni" a razane Abba ya farka daga barcin tare dayin Addu'a *"A'uzu bi kalimatil lahit taammat min sharri ma kalak'a"* gumi ne ke tsatsowa a jikinsa, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, jingina yayi jikin gado, Momy ta farka a barci saita ganshi zaune, tashi ta yi ta zauna, cikin muryan barci tace "yallab'ai lafiya ka zauna cikin wannan Daren?" agogan dake manne a d'akin ta kalla, k'arfe biyu da rabi na dare, sharce zufa yayi ya dafe kansa cikin damuwa yace "Hajiya Maryam wlh mugun mafarki nayi da Basma, hakan ya nuna kamar tana cikin Matsala" Momy ta gyara zamanta tace cikin natsuwa "Abba wannan aikin shaid'an ne kawai, amma Basma bata cikin matsala, saboda munsan wa muka bama 'yar mu fa, kawai dai kila ka sanya ta a ranka ne saboda rashinta na tsayin lokaci da bata tare damu" ajiyar zuciya yayi yace "a gaskiya jiki na ya bani Basma tana cikin damuwa, insha Allah gobe in Allah ya kaimu da sassafe zanje America dan ganin lafiyar ta" ajiyar zuciya Momy tayi tace "Allah ya kaimu goben nima saina maka rakiya" murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga bayi, alwala ya d'auro ya shiga jero sallan Nafila, itama Momy bata kwanta ba, tashi tayi itama tayi alwala tare da gabatar da nata Nafilan. *Washe gari* Da misalin k'arfe Bakwai na safe su Abba sun gama shirin tafiya, Abba ya hana Momy tafiya yace tayi zamansa ba zai kwana ba shima, Yaya Naufal tare da muk'arrbansa suka wuce airport ba tare da b'ata lokaci ba, dama jirgin President na jiran zuwansu, shiga suka yi suka kama hanya sai America. *America* Basma na kwance a d'aki sai nishi take fitarwa da k'arfi, numfashinta na fita da kyar, ta rufa da bargo amma duk da haka bai hanata jin sanyi ba, sai kerma jikinta yake yi, zufa ne ya lullb'eta hawaye na fita a idonta, a wannan lokacin tana buk'atar tai mako. President suna isa, aka turo motoci daga gidan shugaban k'asar America ya kwashe su, sun gaisa dashi kana suka ci abincin, shi Abba ya kasa cin komai drink kawai yasha, burinsa bai wuce yaga Basma ba, wayarsa ya ciro ya kira Shureym, bugu biyu ya d'auka cikin ladabi yace "Abba ina kwana?" Abba ya amsa fuska sake yace "Shureym gani nazo k'asarku, ina gidan shugaban k'asa, kana ina kazo ka kaini gidanka, domin mu gaisa da Basma" Ai bai k'arasa maganan ba jikinsa ya d'auki rawa, muryansa har tana sirk'ewa dan fargaba yace "Abba naje wurin aiki gani bisa hanya zanzo" "OK saika zo karka b'ata lokaci fa domin yau zan koma" "to Abba, insha Allah gani bisa hanya". Sai suka kashe wayar. Ai jikin Shureym na rawa ya tafi gidanshi, ya kira Safeena ya shaida mata zuwan President, itama hankalinta ya tashi, yana isa ya shiga gidan a sukwane, ya samu Safeena a falo tana kai kawo, da sauri ya kama hannunta yace "kije gidan k'awarki, anjima in sun tafi zan kiraki ki dawo" jiki na rawa ta fice a gidan, d'akin Basma ya nufa ya bubbuga k'ofar amma shuru, hankalinsa a tashe yace "Basma dan Allah ki bud'e, Abba ne ya zo zani na d'auko shi, dan Allah ki rufa min asiri zan gyara mistake d'in dana miki pls Basma, bari naje da sauri kinga ma kirana yakeyi" bai jira amsarta ba ya fice da sauri. Hawaye Basma ta cigaba da fitarwa tace "Bana son ganin kowa, gwara na mutu ma" tsaki taja ta mik'e da kyar ta shiga bayi wanka tayi ta sanya atamfa, riga da sket, bud'e k'ofar d'akin ta tayi, kana ta koma kan gado ta kwanta saboda zazzab'in bai saketa ba. Sun iso gidan Shureym sai rawan jiki yake yi, yana fargaban Basma karta tona masa asiri, koda suka shiga falon sun zazzauna, sai Shureym yace "Abba bari na kirata" murmushi yayi yace "Basma fushi take dani, dan tasan da zuwana, ya kamata ace mun sameta a tsakar gida dan tarbanmu, barni da ita bari naje na lallasheta" Gaban Shureym ne ya buga damm, amma sai yayi na maza yace "OK Abba ga d'akinta chan" ya nuna masa d'akin da hannunsa, Abba mik'ewa yayi da sassarfa ya wuce d'akin, turawa yayi a hankali tare da sallama, Basma na kwance ta runtsa idonta hawaye me zafi ya fito a idonta, kanta ta santa cikin bargo ta share hawayenta, ta amsa sallaman a zuciyarta, Abba matsawa yayi gaban gadon cikin lallashi ya fara magana "haba shalelen Abbanta fushi kike dani, kiyi hak'uri kinji Basma na, aiki ne ya hanani zuwa, wannan tafiyan musamman dan ke nayishi" Kukanta ne ya fito fili, da sauri ya yaye bargon, sai yaga tana rawan sanyi, da sauri ya isa gareta ya dagota, jikinta ne yaji yayi zafi kamar wuta, yace "ya salam Basma ba kida lafiya ne?" Langwab'ewa tayi a jikinsa, da sauri Abba ya d'auketa yayi falo da ita, ai Shureym yana ganinsu, gabansa yayi mummunar fad'uwa, rai bace Abba yace "yanzu Shureym har zaka iya tafiya aiki ka barmin Basma kwance ba tada lafiya?" cikin in ina yace "em em Abba ayi hak'uri, nima na fita nabarta tana barci, ban zata zazzabi take ba" Abba yayi tsaki yace "shirman banza, Amanar dana baka kenan nace ka kula min da ita shine zanzo na ganta haka, Yarinya duk ta lalace ta fita hayyacinta" zama yayi da ita akan kujera ya kalli fuskanta, ai gabansa ne ya dad'i, da k'arfi ya furta "Basma me ya sameki a fuska? ya bakinki ya kumbura haka, me yake faruwa ne wai?" Basma banda kuka babu abin da yake yi. Jikin Shureym ya d'auki rawa cikin sark'ewan murya yace "Abba fad'uwa tayi, santsin tyles ne ya kwashe ta ta fad'i, ina ga fad'uwan da tayi shine ya saukar mata da zazzab'i" Basma mamaki ne ya cikata da irin k'aryan da Shureym yake fad'a, Abba ya kalli Basma yace "wai hakane Basma?" cikin kuka tace "eh" wani nannauyen ajiyar zuciya Shureym ya saki ba tare da kowa ya gane ba, Abba yace "to Shureym zan tafi da ita Nigeria, inta samu sauk'i sosai sai na dawo da ita" da sauri Shureym yace "haba Abba kayi hak'uri, ka barta anan, zan kaita asibiti a dubata da kyau, ko jiyan ma na bata pain relief tasha, bansan jikin nata yayi zafi haka da tun safe munje asibiti" Ajiyar zuciya Abba yayi yace "to shikenan bari mu tafi, sai ka d'auketa yanzu ka kaita asibiti mu zamu wuce kawai, Allah ya sauke" ya kalli Basma yace "Basma su Amminki da Momy suna gaidaki, Yayanki Ahmad ya so zuwa, aiki ya rik'eshi" murmushi tayi tace a hankali "ina amsawa" ta kalli Yaya Naufal ta gaisheshi, ya mata sannu da jiki, duk ta gaisa da wanda suka rako Abba, bandir d'in kud'i mai yawa Abba ya bama Basma yace "ga wannan kud'in in kina buk'atar wani Abu" cikin murmushi tace "Abba akwai kud'i a guna fa" "eh na sani ki k'ara da wannan d'in" godiya tayi masa da kuma Addu'an Allah ya sauke su lafiya, ta bada sakon gaisuwa wurin su Ammi da duk family d'in ta. Shureym ya kamata kamar gaske sai wani lallab'ata yake, haka suka yi musu rakiya har mota, Basma tana d'aga musu hannu tare da zubda hawaye, Abba tausayinta ya kamashi kwalla ne ya faru a idonsa, shanyewa yayi tare da d'auke kansa, har suka bar haraban gidan. Shureym mota ya sanya Basma ya wuce da ita asibiti, likita ya bata Magani da kuma allurai nan akayi treatment d'inta, sannan ya biya da ita wurin siyayyan kayan ciye-ciye, ya siya mata su ice cream, kana suka dawo gida, d'aukanta yayi cak ya kaita d'akinta, bisa kan gadonta ya direta, ya zauna a bakin gadon, yace cikin sanyin murya "Nagode Basma da kika rufa min asiri a yau, nayi nadaman duk abin da na ai kata miki, Basma wlh ina sonki sosai, ke kike ja nake dukanki, pls ki amince mu fara zaman aure kamar kowa" Hararansa tayi tace "Shureym ina so ka sani, a duniya kaine mutumin dana fi tsana, kuma kar kaga na rufa maka asiri, kawai na kyaleka ne saboda Iyayena su suka jamin duk wulak'ancin da kake min, ka mai dani baiwarka mara gata da galihu, wlh ka sani na baka talala ne kayi duk iskancin daka ga dama, wlh nasan akwai limit, wataran ko ance ka min wlh bazaka yi ba, dan haka ka tashi ka fita min a d'aki mayaudari kawai azzalumi" Iyaka fushi ya zuciya, amma dakewa yayi bai furta komai ba, ya fice ad'akin tare da jawo mata k'ofa. Kuka ta saki mai tsuma zuciya tace "Abba kun cuceni, da gatana na zama baiwa, Ina *'YAR SHUGABA* na zama mara galihu" saida tayi kuka mai isarta, kana ta mik'e ta fita falo, kud'in da Abba ya bata ta d'auko su a inda ta bari, d'aki ta koma ta rufe, ta aje kud'in a inda take adana kud'inta, murmushi kawai tayi ita kad'ai tasan matakin da zata d'auka akan Shureym. Safeena bata dawo ba sai cikin dare, ta shiga d'akinta, wanka tayi ta fito tana tsaki, zama yai tace "gaskiya Shureym na gaji da wannan auren boyen, ya kamata a fito da zancen nan kowa ya sani, Ni da Mijina auren halal, amma ina guje-guje sai kace auren tsiya mukayi, to wlh da sake, ka kira Maminka ka sanar mata na gaji da wannan wasan kuran da nake da danginka" Sassauta murya Shureym yayi cikin lallashi yace "Haba my baby love, meye na damuwa? da zaran kin haihu magana zai bayyana a dangi, ran nan nayi magana da Mami ita tace haka, dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzu cikinki ba wata hud'u ba, nan da 5month in kin haihu komai zaiyi dai-dai" Ajiyar zuciya tayi tace "to shikenan baby wlh d'azun naji haushi sosai, kawai an sani yini a gidan mutane" murmushi yayi ya kamota, nan ya shiga jefa mata zazzafar soyayyansa, tuni ya mantar da ita damuwa. *Rahma Ce* [8/8, 5:41 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *19.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *Nigeria* Abba sun sauka lafiya cikin dare, ya shaida ma su Momy Basma na gaishesu ba wata Matsala. Yaya Naufal ya labaratawa Yaya Ahmad duk abinda ya faru, damuwa ne ya ziyarceshi yace "anya kuwa Shureym na kula da Basma?" Yaya Naufal yace "yana kula da ita a yanda muka gani, kuma ai in da da matsala zata gayawa Abba" murmushi kawai Yaya Ahmad yayi a ransa yace "ban yarda ba dole zanyi bincike akai, dan Basma tana da zurfin ciki, ni kad'ai take gayawa damuwanta ko Momy" a fili kuma yace "hakane, to Allah ya bata lafiya ya k'ara musu zaman lafiya" "Ameen" Yaya Naufal yace, kana ya wuce part d'inshi. *Kasar Monaco* Aryan yayi nisa cikin karatunsa, a yanzu hankalinsa ya kwanta, sai dai har yanzu bai maida jikinsa ba, yana waya dasu Umma da Khadija sai Yaya Ahmad, yanzu ya daina kashe wayansa kullun tana kunne, har yanzu bai dawo cikin walwala ba, baya dariya sai dai yak'e kuma shima saiya d'auro, murmushi ne kawai ya kanyi time to time. Wata rana yana makaranta ya fito daga aji yana tafiya, karo yaci da wata ta tawo a guje bata lura dashi ba, d'agowa tayi cike da tsoro, cikin harshen turanci tace "yi hak'uri wlh ban kula bane" gyad'a mata kai kawai yayi sai ya rab'eta ya wuce, binsa tayi da kallo cike da tunani barkatai, "iya had'uwa wannan guy d'in ya had'u, ko dan wani kasa ne oho? Gaskiya bazan bari ya kub'ucemin ba, dan na kamu da sonsa, kuma shine dai-dai tsarina" Abinda take fad'a a ranta kenan, da gudu ta bi bayanshi, bata san sunanshi ba gashi ya tsere mata, duk da haka bata hak'uri ba, ta cigaba da bin bayansa da gudu ta cimmasa, gabansa ta sha, sai ta tsaya cike da yin nishi tace "Yi hak'uri na tsaidaka, sunana Jidda Bukar, ni 'yar Nigeria ce katsina state, muna zama a Abuja, nazo nan karatu ne, in ba zaka damu ba ko zan san daga ina kake? dan kayi min zubin d'an k'asar India" Murmushi yayi a takaice yace cikin harshen turanci "sunana Aryan Aliyu, Dan k'asar Nigeria" ido ta zaro tace "wow ashe k'asarmu d'aya, wlh gani nayi ba kayi kama da 'yan Nigeria ba, amma nayi murna sosai, cewa nayi bari na biyo ka saboda naga Kana da sauk'in kai, in ba damuwa ko zamu kulla abota" ransa ne ya b'aci, amma saiya dake cikin rashin sakin fuska yace "nagode, amma ba zai yuwu ba kawai, in dai mun had'u sai mu rik'a gaisawa" yana gama fad'an haka ya wuce, binsa ta cigaba da yi tare da yi masa magayi akan suyi exchangen number, tsayawa yayi zuciyansa na tafasa cikin masifa yace "ya isa dan Allah, kiyi hak'uri ina da mata, pls ki fita a harkata, sai wani bina kike kamar naci miki bashi" jikinta ne yayi sanyi bata k'ara furta komai ba sai ta juya ta fara tafiya, tausayi ta bashi sai ya dakatar da ita yace "Jidda kiyi hak'uri ban cika son ana takura min ba" juyowa tayi idonta ya cika da kwalla tace "ba komai na fahimceka" Numbern shi ya karanta mata, kana suka yi sallama. Ta wuce cike da murna shi kuma ya tafi cike da tunanin Basma, ji yake kamar yaci amananta, wani b'angare na zuciyansa yace "bakaci amana ba, itama ai tanacan tare da mijinta" runtse idonsa yayi hawaye mai zafi ya fito masa, ji yayi komai ya dawo mishi sabo, zazzab'i ne ya rufeshi, sai ya tafi gida cike da matsananciyar damuwa. Tun daga wannan ranar Jidda ta mak'alewa Aryan, Sam baya son abinda take masa, yana k'ok'arin janye mata amma sai k'ara shige masa take, ita burinta bai wuce ta samu zuciyar Aryan, ko bazai aureta ba tunda yace yana da mata, zata amince masa su tab'a rayuwa ko kad'an ne, domin tana fama da sha'awansa. Aryan yana gida a kwance da yamma, sai yaji anyi masa knocking, tashi yayi ya tafi ya bud'e, mamaki me ya rufe shi ganin Jidda ce, murmushi tayi masa sai tabi gefensa ta shige d'akin, binta yayi da kallon yana mamakin yanda akayi tasan gidansa, cikin nuna ko rashin damuwa Jidda ta cire mayafinta ta zauna a kan kujera mai mazaunin mutum d'aya, komawa yayi ya zauna kujeran dayake fuskantarta tace "Nasan kayi mamakin yanda akayi na gano gidanka, kasan ance mai son d'an tsuntsun shike binsa da jifa, Aryan wlh ina sonka amma kak'i bani gurbi a zuciyanta" Aryan d'aure fuska yayi yace "Jidda nafiso ki bar alak'anmu da abota kawai, domin bana tunanin zaki samu gurbi a raina, dan na riga na bada soyayyata ga wata" Hawaye ne ya cika mata ido tace "pls Aryan, ni wlh ko kaina kace in baka a shirye nake" mik'ewa tayi ta juya a gabansa ta cigaba da cewa "Kalli surata da kyau, ina da duk abinda mace take dashi a jikinta wanda namiji zai mora, dan Allah ka yarda dani in zama mai d'ebe maka kewa, koda baka sona in har ka yarda min da haka zanyi murna" Aryan cikin b'acin rai ya mik'e nuna mata hanyar waje yace "Jidda natsaki na tsani mata masu irin halinki, ki sani har ki mutu ba zaka samu yanda kike so ba domin nafi k'arfin iskancinki, kuma ki sani Ni ba kalar ki bane, ki gaugauta cireni a cikin jinsin mutanan da kikasani" jiki na rawa ta mik'e zata bashi hak'uri, cikin tsawa ya dakatar da ita "Na ce ki fita" da sauri ta kwashi kayanta ta fita tana mai jin haushin kanta, rufe k'ofarsa yayi tare da sauke ajiyan zuciya, Addua yayi da k'ara niman tsari ga irin wannan matan. Tunanin Basma ya shiga yi, "Yarinya ce mai natsuwa, duk wayewarta a kame take, ga kud'i da jin dad'i na rayuwa amma akwai tarbiyya mai kyau, har abada yanajin ba zai samu mace kamarta ba" hawaye ne ya zubo mashi yace a fili "Basma har abada ina sonki, babun macen da zan aura ta kai matsayinki, nasan haduwata dake wani jarabawa ne a rayuwana, Allah ya rabamu ina tsananin sonki, Allah ka bani wacce zata share min hawaye na". *_Aryan nima na tayaka da cewa "Ameen". Masu karatun bari mu koma k'asar America mu ga wainar da Suke toyawa._* *Bayan wata guda* Basma ta warware, zamansu kuma yana nan zaman doya da manja, da dad'i ba dad'i, kadaran kadahan, Basma yau tasha Riga da wando English wears, saita d'auko gyale tayi rolin iya kyau tayi, jaka ta d'auka ta fito falo, Safeena ta tarar tana shan fruit, Safeena tace cikin tsokanar fad'a "Ayawo yau kuma shigan yan iska kike ji?" Basma bata tanka mata ba, illa tsaki taja ta fice, Safeena ta ce " 'yar rainin wayo, zaki had'u da Shureym shine dai dai da iskamcin ki". Basma na fita taxi ta shiga ta wuce inda suke had'uwa da Bilal, ta sameshi yana jiranta, kallonta yake cike da soyayya yace "Basma kinyi kyau sosai" murmushi tayi tace "nagode muje ko" wurin shak'atawa suka wuce, suna tafe suna hira, Bilal yace "Basma yaushe zaki kaini gidan ku na gaida da Iyayenki, nifa da gaske sonki nake kuma aurenki zanyi, dan har na fara magana da Ammi na" Murmushi tayi tace "ni iyaye na suna Nigeria, yanzu da Yaya na muke a nan k'asar, kuma ina so ka sani gaskiya ina da aure" ai bata k'arasa maganar ba ya juyo a zabure yace "pls my Basma ki daina fad'an wannan maganar imma wasa kike" murmushi tayi tace "Bilal da gaske nake, Mijina dai baya tare dani yana k'asarmu" tab'oye masa hakan saboda bata son yasan komai nata, cike da damuwa ya samu guri yayi parking yace "meyasa kike wasa da aure, Basma na tabbata ke mace ce mai ilimin addini, meyasa bakya amfani dashi, yanzu kusan 1month da had'uwarmu, sauk'in abin ma tun farko kink'i Amincewa dani muyi soyayya, kin ce ke kin d'ukeni brother d'inki ne, dama nike kid'ana da rawa, da tun farko kin gaya min kina da aure da alak'anmu batayi nisa ba, ko kuma dana nasan yanda zan fuskance ki, amma ba damuwa naji dad'i da kika gayamin gaskiya, zan koyawa kaina hak'uri da soyayanki, sai mu cigaba da zumunci" Murmushi tayi tace "nagode da tunatarwa, insha Allah zan gyara muje ko" "yanzu ina muka nifa?" murmushi tayi tace "muje wurin wasa da mota ko?" dariya yayi yace "OK my Friend" dariya tayi tace "abotan harya fara aiki kenan" murmushi kawai yayi ya tada mota suka cigaba da tafiya. Sai k'arfe bakwai na dare Basma ta dawo daga wurin kallonta wasan mota, Bilal ya sauketa a k'ofar gida, hakan yayi dai-dai da cillowar motan Yaya Shureym, ita kuma tana d'aga ma Bilal hannu harya wuce, sannan ta shiga gida. Ta samu Safeena zaune sai d'irkan abinci take, tsaki Basma taja tace "Mutum baida aikin yi sai ya zauna yaita d'irkan abinci kamar jaka, wai dole ita mai ciki" Murmushi Safeena tayi bata ce komai ba domin ta riga ta had'a mata bomb mai kwacenta yau a gun shureym sai Allah. Safeena ta gayawa Shureym daya dawo, k'arya da gaskiya akan fitan da Basma take yawan yi da kuma mummunar shiga, ransa yayi matuk'ar b'aci, fita yayi nimanta wuraren shak'atawa ko zai ganta a can, amma haka ya karad'e yawan nimanta bai ganta ba, dawowansa kenan yanzu daya hangota tana d'agawa wani hannu, ransa ya k'ara b'aci sosai kishi ya rufe masa ido, da sauri ya shiga gidan yayi parking. Falo ya shiga da sauri ya soma kwalawa Basma kira, da sauri ta fito tana fad'in "dan Allah karka fasa min kunne, sai wani kwala min kira kake, sai kace tsohon makawo" a zuciye ya bud'e baki zaiyi magana, sai ga Bilal ya kwad'a sallama ya shigo falon, Basma saida gabanta ya tad'i, amma saita dake tace cikin Fara'a "Friend hala nayi mantuwa ko?" murmushi yayi yace "kin manta da ice cream d'inki kina sauri" "ayya wlh ban kula ba, nagode kuwa sosai" Shureym ai sakin bakin yayi yana kallon ikwan Allah, cikin harshen turanci Bilal yace masa "ina yini big brother" Shureym ya amsa a tak'aice, sai ya fice da sauri. Yaya Shureym zama yayi akan kushim yana cizon leb'ensa, gaba d'aya kishi ya rufe masa ido. Har wani d'aci bakinsa yake masa saboda b'acin rai, Basma tana ganin ya zauna bai ce mata komai ba, sai kawai ta shige d'aki. Shureym ya d'aga wayarsa ya kira Dadyn Kaduna, Gobna Ibrahim, suka gaisa Dady yace "Shureym ya Basma da fatan kuna lafiya?" cikin k'unan rai yace "Dady Basma tana cin Amanta, fita take yi tana hurd'a da wasu maza a waje, yau tun rana ta fita sai yanzu ta dawo, kuma Dady wani saurayinta ne ya kawota gida, yanzu yabar falon mu" a razane Dady ya mik'e yana fad'in "Inalillahi wa inna ilai hir raji'un, Basman ce ta zama haka, to maza ku shirya gobe-goben nan ku tawo Nigeria, zan kira family meeting gaba d'aya zamu had'u a Abuja duka, kayi hak'uri kaji Shureym karka ce mata komai" sai suka yi sallama. Dady ya fara kai koma a falo sai salati yake, Ummin Meena dake zaune itama ta mik'e a tsorace tana tambayarsa "Alhaji lafiya?" kallonta yayi bai ce komai ba, ya shiga niman number Mai Martarba Sarkin Kano, suka gaisa, sai ya shaida masa akwai family meeting a Abuja gobe in Allah ya kaimu, nan suka yi sallama. ya d'aga waya ya kira President, shima haka ya shaida masa kamar yanda suka yi da Mai Martaba, President cikin mamaki yace "Ibrahim lafiya dai ko?" cikin murmushi yak'e yace "Lafiya Kalau sai in munzo zaka ji komai insha Allah" da haka suka yi sallama. Dady ya koma ya zauna, itama Ummi ta zauna, ya shiga gaya mata Abinda Shureym yace masa, cikin salati Ummi tace "wlh k'arya yake yi, ba dai Basman mu ba, sai dai in sharri zai mata, dan ba haka muka tarbiyyantar da ita ba" Cikin b'acin rai Dady yace "karki shaideta domin d'an yau ba a iya masa, kuma ai ba tare dasu muke zama ba, hasali ma ba gari d'aya muke ba, Basma zata iya komai tunda dama bason Shureym take ba" sai jikin Ummi yayi sanyi ta shiga nazarin maganar Dady... *Rahma Ce* [8/9, 5:47 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *20.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Safeena cike da damuwa tace "amma Shureym anya baka jawo tonuwar asirinmu ba, domin in dai Basma taji cewa ka kai karanta ne, tofa zata gaya duk abinda ya faruwa, da kuma dukanta da kake yi" Runtse idonsa yayi ya bud'e, cike da damuwa yace "wlh Safeena raina ne ya b'aci, idona ya rufe sam ban kawo haka ba, sai yanzu da kika tunatar da ni, yanzu ya kike ganin za'ayi" cikin damuwa ta rafka tagumi tace "ina ganin karka gaya mata, kace kawai ana nimanku ne, inya so inta je can taji komai, kuma na fison dama kowa yasan dani a family d'inku dan nagaji da b'oye-b'oye" cike da damuwa Shureym yace "haba safeena bai kamata ace abinnan ya fasu yanzu ba, kawai ki tayani da Addu'a kar asirinmu ya tonu" yana gama fad'an haka sai ya mik'e ya shige d'aki, Safeena ta bi bayansa da kallo, ta yatsine baki tace "ba Addu'an da zanyi, in maganar ta fito karshe dai ace an raba aurenka da Basma, kuma abinda nake so kenan". Shureym yana shiga d'aki ya kira Maminsa ya sanar mata duk abinda ke faruwa, hankalinta ya tsahi ta shiga yi masa fad'a, tace "yanzu kazo kaja asirina zai tonu, a gaskiya ba yanzu naso ace maganar nan ya fito ba, domin hakan zai iyi barazana ga aure na, kuma kaima za ka fuskanci fushin Mahaifinka, gaskiya zan San abinyi" tana gama fad'a ta kashe wayar. Kai komo ta shiga yi a d'akinta tana tunanin hanyar da zata bullowa lamarin, zama tayi tayi dogon nazari, murmushi naga tayi sai ta ce "Allah ya kaimu goben, na samo mafita". Da dare Shureym ya kira Basma a waya, yasan in yaje d'akinta ba zata bud'e ba, yace "ki shirya gobe in Allah ya kaimu zamu tafi Nigeria, Dady ya kirani yace muje akwai Family miteeng, dan haka ki shirya da wuri da sassafe mamu tafi" cike da murna tace "Allah ya kaimu" saita kashe wayar. Mikewa tayi, tayi rawa da tsalle, tana murnan zata ga family d'inta, kaya ta shiga had'awa kamar wacce zata bar garin duka ba dawowa. Zan iyace cewa barci b'arawo shine ya saceta, amma sam ta kasa sukuni, kosawa tayi gari ya waye. *Washe gari* Yau Basma harda yiwa Safeena sallama sai fara'a take mata, Safeena tace "hoo su Basma za'a tafi min da miji sai dariya kike, to Allah yasa in kin tafi karki dawo" harara Yaya Shureym ya galla mata, saita gimtse sauran maganarta tana dariya k'asa-k'asa, Basma kuwa cike da dariya tace "Ameen ya rabb, nima bana fata na dawo, kuma mijinki gaki ga shi, babu abinda zan miki dashi, ni dai na barki lafiya" saita fice tare da jan trolley kayanta. Safeena ta bisu har mota tare da musu Addu'a, haka suka wuce airport, Shureym yana cike da damuwa, Basma kuma cike take da murmushi. *Nigeria* Gidan President ya cika da dangi, sunzo sunata zumunci, da yake ya kama yau rana ce ta Juma'a, mazan gidan duka suka taru suka tafi babban masallacin Juma'a na Abuja. Bayan sun dawo gida, iyayen maza da mata suka had'u a babban falon bak'i na shugaban k'asa, anan aka shirya musu abinci a tsakiyar falon kan babban dadduma daya mamaye falon, yara kuma suka baje nasu liyafar a part d'in Ammi, can suke hidimarsu. Bayan sun gama cin abinci suka shiga hiran zumunci, Abba (President) ya kalli Dady (Gobno Ibrahim) yace "Ibrahim yanzu gamu duk mun had'u gaba d'ayanmu, ina so ka sanar mana musabbabin had'uwarmu anan daka buk'aci muyi" Dady ya nisa ya d'ago ya kalli Abba yace "naso ace Shureym da Basma sun zo tukunna sai kuji bayani a bakinsu, dan dama mun had'u anan ne domin su, na tabbatar suna gab da shigowa" Mai martaba yace "A'a Ibrahim ka fara sanar mana da komai kafin zuwansu" Mami (Hajiya sa'a) tace "kwarai kuwa, ya kamata mu ji komai, domin ni hankali na ya ya shi" Hajiya Fatima (Ammi) tace "gwara ka fad'a kawai domin mu fara tattaunawa akai" ita dai Momyn Basma bata iya furta komai ba saboda nuna kawaici, Hajiya Murja Mahaifiyar Leema ita ma bata furta komai ba, Ummin Meena kuwa shuru tayi cike da damuwa a fuskanta. Dady yayi gyaran murya ya gaya musu duk abinda Shureym ya fad'a masa jiya, ai duka falon sai suka d'auki salati, Momy kuwa wani irin fad'uwa gabanta yayi, idonta ne ya kawo kwalla zuciyarta na mata suya, Abba sun kuyar da kai yayi ya kasa yin magana, duk falon ya d'auki shuru sai k'aran fanka da kukan AC ke tashi, Mami ce tace "hmmm nasan za'a rina saboda Shureym ya sanar min cewa tsawan watannin bikinsu da suka yi, Basma tak'i bashi had'in kai suyi rayuwar aure, akwai ranar da har fad'a suka yi nice na sasanta lamarin, har nayi masa fad'a, akan cewa yarinya ce ya bita a hankali, Shureym tunda yaji su Meena duk suna d'auke da ciki abin ya dameshi, nice nake lallashinsa" Mai Martaba ya katseta da cewa "meyasa kinsan da wannan matsalan yanzu tsawon wata 7 da aurensu, sai yanzu za ki fad'a da kika ji matsala ta kunno kai?" "Mai martaba gani nayi Basma ba son aure tayi ba tun farko, shiyasa nace bari mu lalkab'ata harta hak'ura ta yarda da shi". Ba wanda ya tanka mata sai duk suka yi shuru. Sallaman shigiwar su Basma falon, shine ya k'atse shurun domin kusan yaran nasu duka shun shigo falon suna murnan ganinsu Basma, Yaya Ahmad na rik'e da hannun Basma sai suka samu guri suka zauna a gefe, duk yaran suka zauna, Yaya Naufal, Yaya Shureym, Yaya Adam, Yaya Jamal, Anty Husnah, Meena, Leema, Deeja, twins din Momy k'annan Basma. Falo yayi Albarka, kowa ya zauna duk suka gaishe da iyayensu, sai dai fuskokinsu babu walwala, Basma ta tashi ta isa gaban Abba ta zauna tare da sanya kanta akan cinyansa, cike da b'acin rai ya tureta tare da cewa "tashi ki bani wuri" da sauri ta d'ago ta kalleshi, cikin shagwab'a tace "Abba me nayi kake fushi dani" shuru yayi mata, sai duk jikinta yayi sanyi, takai kallonta ga Momy, saita kauda kai a ranta tana tausayawa d'iyarta, duk tabi fuskokin iyayan nasu babu wanda yayi mata dariya ko murmushi, duk ransu na b'ace, cikin tashin hankali tace "Wai me yake faruwa ne?" Dady ne yace "Ku su Meena Ku tashi Ku fita Ku bamu wuri, Anwar da Na'im kuma kuje d'akinku kiyi karatu, ku kuma mazan ku zauna ayi maganar daku" jikinsu duk a sanyaye su Leema suka fita, Basma ta mik'e zata bi bayanzu Dady ya daka mata tsawa yace "zauna karki sake ki fita, dama zaman danke a kayi shi" kuka ta fara yi ta koma kusa da Yaya Ahmad ta zauna, hannunta ya kama ya shiga lallashinta. Falon yayi shuru na tsawon minti biyar, Dady ya kalli Shureym yace "Shureym ina so ka sanar mana da abinda ka gayamin jiya a waya" "Shureym cike da fargaba da damuwa ya shiga zayyana magana k'arya da gaskiya, bayan ya gama gaya musu abinda ya gayawa Dady sai ya d'ora da cewa "Basma bata jin maganata, ban isa in sata ba ko in hanata ba, zagi iri-iri na cin mutunci babu wanda bata yi min, zata fita da banzan shiga na fidda tsiraici, ban isa inyi magana ba" ai bai k'arasa ba Basma tayi magana cikin d'aga murya da tashin hankali tace "karya kake Yaya Shureym, wlh sharri kake min" takalli iyayenta ta cigaba da cewa "wlh Aba sharri yake min, Ammi yanzu ku kun yarda da bayaninsa, Mai martaba wlh Yaya Shureym sharri yake min, karku yarda da maganar shi" ta rarrafa ta isa gaban Mominta tace "Momy in kowa bai yarda dani ba nasan ke zaki yarda dani" Momy sun kuyar da kai tayi k'asa hawaye mai zafi ya sauka a kuncinta, Abba ne ya mik'e da sauri ya wanke Basma da mari guda biyu, tare da hamb'arinta da k'afansa yace "tir da halinki Basma, acikin zuri'ata kin fita zakka sam baki halinmu ba, kuma in kika kuma yin magana anan wlh jikinki zai gaya miki, mituniyar banza kawai" Dady ne ya mik'e ya kama Abba yace "haba Yallab'ai, bai kamata ka duketa ba" komawa duk suka yi suka zauna. Momy cikin fushi tace "Tunda nake ban tab'a sanya baki a cikin lamarin Basma ba saboda ina nuna kawaici, amma yau zanyi magana, a irin tarbiyyan dana bawa 'yata bana tunanin zata aikata abinda Shureym ya gaya, in kuma ku kun yarda toni wlh Ni bazan tab'a yarda da magan ganunsa ba, dan haka Basma 'yata ce, nice nayi nak'udarta babu wanda zai d'aura mata k'azafin zina in d'auka" Saita mik'e taje ta kama hannun Basma suka yi hanyar fita daga Falon, yaya Ahmad shima mik'ewa yayi cikin b'acin rai ya kalli Shureym yace "D'an iska banza baka isa ka yiwa 'yar Uwata sharri ba, domin nafi kowa sanin mugun halinka, dama mazinaci kamar ka ai dole kaga kowa ma haka yake, Basma nasan abinda zata aika nasan wanda ba zata yi ba, mak'arya cin banza dana hofi" shima sai ya bi bayan su Momy. suna gabda zasu fita Abba ya bud'e murya yace "Maryam wlh muddun kika sanya k'afa kika fita a falon nan to a bakin aurenki, Kai kuma Ahmad wlh in ka fita saina sassab'a maka mutumin b'anza kawai, har zaka zo ka goyi bayan shaid'ayar yarinya nan, tun farko dama ta nuna bata Son shi, dan haka kome aka ce tayi to zata iya aika shi" A gigice Momy ta tsaya ta juyo tana mamakin furucin Abba, mai martaba yace "Subhanallah Yallab'ai wani irin furuci ne haka?" Ammi da Ummi da sauri suka mik'e suka isa wurinta, Momy tana kukan bak'in ciki amma sam bata karaya ba dan tana bayan Basma, gabanta su Ammi suka sha, tare da rik'o mata hannu suka jata har zuwa mazauninta, Yaya Ahmad ya kama Basma ya had'ata da jikinsa yana lallashinta, haka suka isa cikin falon suka zauna. Mai Martaba yayi gyaran murya yace "Dan Allah kuyi hak'uri kar b'acin rai yasa a yanke hukunci cikin fushi, ba tare da bincike ba, ke Basma gaya mana gaskiyar abinda ke faruwa" kuka ne yaci k'arfin Basma tace "Wlh ban tab'a zina ba ban tab'a ba, kune iyayena ku zaku shaideni akan haka, wlh ban tab'a ai'kata abinda yace muku ba ko d'aya daga ciki" kuka ne yaci k'arfinta saita d'aura kanta a cinyar Yaya Ahmad, jikinta ne ya soma kad'uwar jin sanyi nan take zazzab'i ya rufeta... *Rahma Ce* [8/9, 5:47 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *21.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Shuru suka yi suna sauraren kukan Basma, tausayinta ne ya kamasu, Ammi ce tace "to shikenan, ni ina ganin gaba d'aya wannan abun rashin fahimta ne, dan haka sai a sulhunta su komai ya wuce, sai su tafi, Dady yace "kwarai kuwa abinda ya kamata ayi kenan" Mai Martaba ya shiga yi musu nasiha mai ratsa zuciya, daga bisani ya d'aura da cewa "President banji dad'in yanda ka d'auki wannan lamari da zafi ba, da har ka furta mummunan kalma ga Hajiya Maryam, in hankali ya gushe ai hankali ne ke nemoshi, dan Allah mu rik'a kai zuciya nesa, duk sai mu taru muyi hak'uri komai ya wuce, kai kuma Shureym kaji tsoron Allah, in har kana cutar da ita Allah ba zai barka ba" Abba yayi wa mai Martaba godiya, ya soma yiwa su Basma nasiha, bayan ya gama yace "Basma kije part d'ina ki jirani, kai kuma Shureym ka shirya zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe zaku koma, shikenan zaku iya tafiya" Haka suka watse kowa da damuwa a ransa, Amma banda Shureym da Maminsa wanda zuciyarsu yayi haske tunda an kashe magana ba tare da Basma ta tona komai ba, duka Matan suka wuce part d'in Momy, anan suka bar Mazan suna tattaunawa. Yaya Ahmad yabi bayan Basma suka zauna a falon Abba, ya kalleta cikin nutsuwa yaga duk ta rame haske kawai ta k'ara, yace "Basma me Shureym yake miki, ki gaya min gaskiya fa, dan bana son k'arya" guntun Murmushi tayi tace cikin sanyin murya "Yaya Ahmad babu komai, kawai dai kasan halinsa na saurin fushi, anan ne muke dan samu sab'ani, amma bayan haka ba komai" kallonta yake cike da zargin abubuwa kala-kala domin sam bai gamsu da amsar da ta bashi ba, sai yace "shikenan tunda ba zaki fad'a ba, in ya kusa kashe ki saiki fad'a" murmushi tayi tace "Ni ba zai ma kashe ni ba" mik'ewa yayi yace "bari na kawo miki abinci da maganin zazzab'i kisha, dan d'azu naga har kad'uwan sanyi kike yi" murmushi tayi race "wlh Yaya tsabar shiga shock ne ya sani zazzab'i, amma ka kawo min zansha ko kaina zai rage min ciwo" harya fara tafiya sai tace "Yaya d'an tsaya in baka ajiya" zage Jakarta tayi ta ciro wani k'arakin key guda d'aya, sai ta mik'e ta isa wurinsa tace "Yaya dan Allah ka ajemin wannan key d'in inna tashi amsa zan maka magana sai ka bani" d'aga key d'in yayi yace key d'in miye ne wannan?" murmushi tayi tace na sirrina ne, ni dai ka ajemin wataran zan maka bayani akansa" gyad'a kai kawai yayi sai ya fita, tare da juya key d'in a hannunsa, yana tunanin ko na miye. Abba ya samu Basma a sashinsa, zama yayi ya kirata, sai tazo ta zauna gefensa a k'asa, kanta ya d'ora bisa cinyansa, sai ya shiga yi mata fad'a daga k'arshe yayi mata nasiha, kuka Basma take yi mara sauti, a haka Yaya Ahmad ya samesu shima ya zauna ya zubawa Basma abincin ya mik'a mata yace taci, Abba ne ya kalle shi fuska a d'aure ya shiga yi masa fad'a akan abinda ya aikata d'azun, hak'uri Yaya Ahmad ya bashi da alkhawarin hakan ba zai sake faruwa ba, nan suka zauna suka cigaba da hira, har Basma ta kammala cin abincin kana ta mik'e zata fita da kulolin abincin, dakatar da ita Abba yayi yace "Basma barshi Ahmad ya tafi dasu, ki hau sama kiyi wanka jakar kayanki yana d'akin kusa da nawa, anan zaki kwana" rau-rau tayi da idonta tace "Abba ina son inga su Meena da su Ammi ne fa" murmushi yayi yace "anjima in zamuci abincin dare zaki gansu, dan haka kiyi abinda na saki" hawaye ne ya ciko idonta, kawai saita haura sama zuwa d'aki, ta shiga rusa kuka sai da tayi mai isanta kana ta shiga bayi dan tayi wanka, zuciyarta na nazarin abinda yasa Abba ya hanata ganawa da 'yan uwanta. Da dare Momy ce zaune a falon Abba sai Basma, magana Momy ta shiga yi tace "Basma anya kina jin dad'in zama da Shureym kuwa? In yana miki wani abu ki gaya min" murmushi Basma tayi tace "Momy ba komai" kallonta tayi sosai tace "Basma ada ba kya b'oyemin matsalanki, amma meyasa yanzu zaki b'oyemin?" murmushi ta kuma yi tace "Momyna ba komai fa" murmushi kawai Momy tayi tace "to shikenan, ki dai k'ara hak'uri, aure ba abin wasa bane ibada ce ta samun Aljanna, sannan ina mai gargad'inki Basma akan k'in amincewa da kika ki yi dashi a matsayin mijinki, ina ganin shine dalilin da yasa ya k'ulla miki sharri, dan haka a kul d'inki ki tabbbatar kin bashi hakk'insa, mijinki ne kuma halas d'inki ne, nasan baki sonsa amma ki sanya a ranki shine wanda Allah ya zab'a miki, dan haka ki amshi k'addarar ki sai Allah ya baki ladan akan haka, kuma duk inda kike ki rike mutuncinki dana aurenki" Kuka Basma ta shiga yi, tana cewa a ranta "duk yanda zan fahintar daku akan zamana da Shureym ba lallai wasu su gasgata ba, domin ya riga yamin mugun tabo wanda inna fad'a za'a ce na fad'a danna kare kaina ne, bana so kusan komai yanzu sai nan gaba kad'an a lokacin da kowa zai gasgata magana ta" A fili tace "insha Allah Momy zan ki yaye, nagode da kika aminta dani, kika bani yardanki a lokacin da kowa yaki yarda dani, Momy na Allah ya biyaki da gidan Aljanna" rungumeta Momy tayi tare da sanya mata albarka. *Washe Gari* Su Basma sun fito zasu koma America, iyayan nasu suka k'ara musu nasiha, kana gaba d'aya gidan suka tafi rakasu zuwa airport. Basma ta tsaya gaban Yaya Ahmad tace "Yayana zan tafi na barku zanyi missing d'inka sosai" murmushi yayi mata yace "kin san ni kullun cikinsa nake, Allah ya kare ki daga duk kan abin k'i" saita rungumeshi tana fad'in "Ameen" a haka tayi ta bin kowa tana musu bankwana, tana zuwa wurin Abba sai ta rungumeshi ta soma kukan shagwab'a, Abba murmushi yayi yace "Queen Basma ai bata kuka, dan haka ta daina b'ata hawayenta Abbanta kullun yana tare da ita" murmushi tayi na jin dad'i tace "Abba ka daina fushi dani ko?" "kwarai kuwa, ba kiga yau rakiya harda ni ba, ai na huce tun jiya, Abbanki bazai iya dogon fushi dake ba, dan haka ki kwantar da hankalinki, Abbanki na sonki" murmushi tayi tace "nagode Abbana" Bayan tayi sallama da duk family d'in ta, sai suka wuce suka shiga jirgi tanata waigensu, tana d'aga musu hannu. Suna shiga jirgi ta fashe da kuka mai tsanani. Tsanar Shureym ya dad'u a ranta, ayyana irin abinda zata yi ta rama take a ranta, a haka har barci ya kwasheta, sai da jirkinsu ya sauka ta farka. Haka suka wuce gida a tsakaninsu babu um babu um-um. Suna isa Safeena ta rungume Shureym, cike da farin ciki tace "nayi kewarka Mijina, da fatan babu wani damuwa" murmushi yayi yace "babu" cikin tsokana Basma tace "Acici baki ganni ba ne, tom na dawo sai kiyi hak'uri Addu'anki baici ba" d'aure fuska tayi tace "nifa bana son rashin kunya waye acicin?" dariya Basma ta kwashe dashi, Shureym yayi mamakin ta yanda ta saki kamar ba ita bace mai kuka d'azu, tace "haba Anty Safeena meye na d'aukan wuta, nifa ba ruwana da fad'a yanzu, in zaki sauko mushirya tom" murmushi Safeena tayi ta kalli Shureym tace "halan an zane ta sosai shiyasa ta koyi ladabi" murmushi yayi bai ce komai ba, Basma tace "ni dai bari naje nayi wanka nazo muyi hira, dan naga surutunki zai hana ni yin abinda ya kamata" tana gama fad'an haka tayi gaba abinta, tana dariya wanda ni mai rubutu ni kad'an nasan ma'anarsu. Sake baki duk suka yi suna kallon Basma, zama Shureym yayi ya bama Safeena labarin komai, murmushi tayi tace "lallai kace abun yaso ya jawo damuwa, to Allah ya kyauta, shiyasa naga Basma ta sako" Shureym yace "tunda ta sako kema sai ki sako a zauna lafiya, ni fa a gaskiya dama ina son Basma, kawai dai bana son b'acin ranki ne" d'aure fuska Safeena tayi tace "to kayi ta sonta mana sai me" murmushi yayi ya mik'e ya bata wuri, dan yasan ya tsokano fad'a. Basma tana gama shiryawa ta fito falo, danbun nama ta dibo a plet da yawa tana ci, zama tayi a kan kushim tace "Anty Safee ga danbun nama ko zaki ci" galla mata hara tayi tace "kina zaune a gun saki ce min in ci, ki zuba min ki bani in kina son naci" dariya tayi taje kusa da ita ta aje plet d'in tace "mai da wuk'ar, gashinan kici, ni bari na shiga kicin na d'aura mana abinci, dan yanzu ba zan yarda kuku na mana girki ba" Safeena sakin baki tayi tace "ikwan Allah, Basma an girma anyi hankali" juyowa tayi tace "haba Anty Safee, me kika mai dani ne, dama can da girma na" dawowa tayi gabda Safeena sai ta d'auketa photo a wayanta, tana cin dabmun nama, hasken wayar yasa ta d'ago tace "kambu d'aukata kike ko?" dariya tayi ta k'ara d'aukanta, sai da tayi mata kala biyar kana ta dena, tace "zan aje miki ne in kin haihu na nuna miki, a lokacin da kike kwad'ayin Danbun nama" tana gama fad'an haka ta shige kicin tabar Safeena cike da mamaki. Tana shiga kicin ta tsaya ta zab'i hoton da Safeena ta fito sosai a ciki, saita goge sauran, kyakkyawan murmushi yayi, sai ta shiga d'aura abincin daren. *Bayan Sallan Isha'i* Su Shureym ne zaune a dinning Safeena na gefen damansa, Basma na dayan gefen hagunsa, suna cin abincin da Basma tayi musu, delof d'in kuskus da hanta wanda yaji kayan lanbu, sai farfesun kayan ciki da kuma juice d'in kwakwa wanda yasha madara. Santi dukansu suke yi amma banda Basma da taketa musu dariya, tashi tayi ta shiga d'aukarsu photo tace "gwara na d'auke ku in rik'a kallon lokacin da kuke santin abincina na farko da kuka fara ci" basu kawo komai aransu ba sai suka yi ta dariya, Basma murmushi tayi kawai, ita kad'ai tasan me take kitsawa a ranta. Bayan sun kammala cin abinci, suka koma babban falonsu suka zauna, Yaya Shureym ya shiga yi musu bayani "Safeena da ke da Basma Ku duk matana ne, ina so mu mance rayuwar da muka fara a baya, mu dawo mu soma rayuwa na aminci da juna, Basma ki yafemin muzguna miki da nayi, sannan nagode da kika rufamin asiri akan aurena da Safeena da kuma abinda nayi miki, ke Safeena ki d'auki Basma a k'anwarki, ke kuma Basma ki d'auki Safeena a matsayin Yayarki, dan Allah mu kiyayi b'atawa juna rai, dan haka yanzu zan raba muku kwana, ke Basma tunda na aureki ban tab'a kwana a d'akin ki ba, dan haka zanyi miki sati d'aya na amarcin da banyi ba, ke kuma Safeena sai kiyi hak'uri in na gama kwanakin, sai na rik'a kwana biyu-biyu a ko wani d'aki, in kuna da magana sai kuyi" Safeena tace "ba komai Shureym nima na yada makaman yak'i na, na d'auki Basma k'anwata, dan haka na yarda kayi mata kwankin Amarcinta" Basma kuma tace "Nagode Yaya Shureym nagode Anty Safeena, sai dai zan nima afwanku akan cewa, yau na fara period kuma ina yin tsawon kwana shida kafin na gama, dan haka nace me zai hana ka rik'a kwana a wurin Anty Safeena, in period d'in ya d'auke sai kayi min kwana kin Amarci na" saita k'arasa maganar da sun kuyar da kai k'asa, alaman jin kunya, dariya duk suka yi Shureym ya kalle Safeena yace "me kika ce game da bayanin Basma" murmushi tayi tace "sai abinda kace tunda kaine Mai gida" dariya yayi na jin dad'i yace "shikenan mun karb'i uzurinki, in ya so bayan kwana shida saiki amshi girki" farin ciki ne ya lullub'e Safeena, domin dama bata jin zata kwana ita kad'ai a d'aki dan tanada b'ukatar mijinta. Nan dai suka shiga hira, Basma ta mik'e tace "bari na mana salfee" sai duk suka mik'e suka shiga d'aukar hotuna, wani ta d'auki Shureym da Safeena suna dariya ga katon cikinta ya fito, wani yana rungume da Safeena, wani kuma su d'auka su uku selfee, wani kuma Safeena ta d'auki Basma da Shureym. Bayan sun gama Basma ta yi musu sallama ta wuce d'aki, suma d'aki suka wuce dan yin shirin barci. Basma tana shiga d'aki ta rufe da key, tsalle tayi akan gado ta kwanta, tare da yin murmushi, can kuma sai ta fashe da kuka.... *Tofa wai me Basma take shiryawa ne*😳🤭 *Rahma Ce* [8/9, 5:48 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *22.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Da misalin k'arfe uku na dare, Basma ta tashi ta gabatar da sallan Nafila, Addu'a tayi da niman yardan Allah akan abinda take shirin yi, haka ta zauna tayi ta tasbihi, har gabanin sallan Asubahi, kana ta k'ara yin alwala tayi raka'atanil fijri, sannan ta gabatar da sallan Asubahi, azkar ta karanta, sai ta tashi ta nad'e sallaya, idonta a rufe ta fad'a gado, murmushi ta saki, a ranta tace "ashe ma Yaya Shureym mugun wawa ne, da nasan haka yake da saukin kai da tuni nasan abinyi, wai su sun d'auka da gaske period nake, hmm kana tunanin cin zarafin da kayi min da sharrin da kamin kasha ni masilla ne, wlh saina d'auki fansa mafi muni a gareka, azzalumi kawai" tsaki taja saita gyara kwanciya, cikin k'ank'anin lokaci barci mai nauyi yayi gaba da ita. Sai k'arfe goma na safe ta farka, wanka tayi ta shirya cikin riga da sket English wears, ba wani makeup da tayi, fitowa tayi taga su Yaya Shureym suna Karin kumallo, murmushi ta sakar musu saita k'arasa wurin taja kujera ta zauna, gaishe su tayi suka amsa cikin kulawa, tace "kuyi hak'uri na makara ban tashi da wuri na had'a mana breakfast ba" murmushi Safeena tayi tace "Basma kenan, karki damu ai nice da girki, nasa kuku ya had'a mana tunda ni gaskiya bana girki" Basma harta kai hannunta zata jawo food wormer sai ta janye hannunta jin Safeena na fad'in kuku yayi musu breakfast, da sauri tace "gwara da ban zuba ba, dan bazan iya cin girkinsu ba" mik'ewa tayi ta wuce d'aki, shi dai Shureym saurarensu yake yi yana kai loman abinci, a ransa yana yabawa Basma "yanda take k'ok'arin yin abinci da kanta duk irin matsayinta da take dashi na 'YAR SHUGABAN K'asa, amma ita Safeena ba 'yar kowa ba sai iyayin tsiya, k'ilama bata iya bane, dan Ni ban tab'a cin girkinta ba" Maganar Basma shine ya dawo dashi daga zancen zuci da yake, tace "Yaya Shureym bari naje naci abinci" kallonta yayi sama da k'asa yace "amma kinsan yanzu ba zan yarda da wannan fitan naki ba ko" marairaice fuska tayi tace "yaya takeway kawai zanyi na dawo" d'aure fuska yayi yace "ni bawai fitan bane damuwa na, kawai bana so ki had'u da d'an iskan saurayinki d'in nan ne" idon Basma ya ciko da kwalla bata ce komai ba, saita juya zata koma d'aki, dakatar da ita yayi yace "kije amma na baki minti talatin, in kika bari ya wuce, to kinfi kowa sanin hukunci na, bawai na bari bane sanyi kawai nayi" bata tanka mishi ba, ta wuce abinta tana kissima abinda zata aikata mishi. Tana fita studio ta wuce, wayarta ta basu ta nuna masu hotunan da take so a wanke mata, tana gama musu bayani ta wuce siyan abinci. Cikin sauri ta dawo ta basu kud'insu ta karb'i hotunan da wayarta, ta adana su a jaka, kana ta fita cikin sauri, taxi ta tara ya sauketa a gida ta shiga da sauri. Ta taddasu a falo, "sannunku da hutawa" tace, kana ta nufi d'akinta, Yaya Shureym ya dakatar da ita, damm taji gabanta ya fad'i, amma saita dake ta juyo, kallonta yayi yace "amma kinsan kin d'auki kusan minti arba'in ko, daga siyan abinci shine zaki d'auki wannan lokacin" marairaice fuska tayi tace "haba Yaya Shureym, kasan k'asar nan bafa Nigeria bane, duk yanda na tadda layi sai an sallami wanda suka rigani kafin a bani, su ba ruwansu da cuwa-cuwa, kuma bada motan gida na fita ba, da taxi ne" Kallonta yayi a takaice kana ya d'auki telephone ya kira masu gadin gidan, tare da duk ma'aikatan gidan, bayan sunzo yace tare da nuna Basma "karku sake ku bar wancen ta fita a gidan nan sai in na baku izini" duk wannan bayani a cikin harshen turenci yake musu, cikin girmama suka amsa masa kana ya sallamesu suka fita, mik'ewa yayi ya zo inda ta tsaya kana ya amshi ledan take away d'in, yace "muje na taya ki ci" gabanta ne ya shigo dukan uku-uku, burin ta karya buk'aci ganin abinda ke cikin jakarta, haka suka jera suka shiga cikin d'akin, Safeena wani bak'in kishi ne ya tirnik'eta, tsaki taja tace "ni sam bana burin wata mace ta rab'i Shureym, amma shegiyar yarinyar nan ta zame mini k'arfen k'afa, bari mu koma Nigeria saina raba wannan Auren, dan in ba haka ba, Shureym ya sameta kashina ya bushe, dan na shiga uku, dani da banza duk d'aya ne a gunsa" mik'ewa tayi ta wuce d'akinta cike da damuwa. Suna shiga ya fincikota, a tsorace ta kalleshi, jakanta ya amsa, ai Basma Addu'a ta fara yi a cikin ranta domin ta gama tsorata, duk tunaninta bud'e jakar zai yi, da mamaki sai taga ya aje akan dressing mirror din ta, wani ajiyar zuciya ta saki a hankali, dawowa yayi wurinta, hannunta ya kama suka zauna kan kujera, jawota yayi kan jikinsa wanda har tana jin saukar numfashinsa a gefen kuncinta, juyo da fuskanta yayi, suka kalli juna ido cikin ido, sha'awar Basma ce kwance a kwayar idon Shureym, itama kuma tsana ce kwance a cikin kwayar idonta, bata ankara ba saita ji ya had'e bakinsu, ya soma sumbatar ta, duk yanda taso kwace kanta ta kasa, k'arshe hak'ura tayi sai da yayi iya ka yinsa kana ya saketa, kuka taso yi amma saboda karta nuna damuwa saita shanye su, mik'ewa yayi yace "daga yanzu wannan ne irin hukuncin da zan rik'a miki, in dai kika sab'awa umarni na" sai ya fice. Da gudu ta mik'e ta shiga bayi, brush ta soma yi tana dirjan harshenta, tana yi tana kuka, takai kusan minti Sha biyar tana aikin abu d'aya, sai da taji bakinta ya soma yi mata zafi kana ta dena brush d'in, wanka tayi ta fito ta sanya kaya marasa nauyi, saita rufe k'ofarta, ji tayi bata jin yunwa, abincin da ta siyo saita sanya a fridge, d'auko wannan jakar tayi ta ciro diary d'inta, ta shiga rubuta labarin fitanta da Bilal, da harya kawo mata ice cream data manta a motansa, Yaya Shureym kuma daya ganshi ya kulla mata sharri, dama ta rubuta labarin tun farkon had'uwarta da Bilal a cikin diary d'in, saita d'aura da labarin bayan dawowarsu daga Nigeria, haka ta rubuta komai abinda ya faru, sai ta sak'ala hotunan data d'aukesu a cikin diary. Maida shi tayi majiyansa, saita mik'e ta dumama abincin da ta siya a microwave, bayan ta gama ta gabatar da Sallan Azahar sai ta bi lafiyan gado. *Kasar Monaco* Jidda ta matsawa Aryan wanda duk iya wulakanci yayi mata, amma tak'i rabuwa dashi, k'arshe dole ya sakko suka cigaba da mutunci kamar yanda ya buk'ata, don ya sanar mata shi sam ba zaiyi soyayya da ita ba, Aryan yayi waya da Umma ya sanar mata saura wata Uku ya dawo Nigeria, tayi masa Addu'a sosai kana tayi masa fad'a da nasiha akan jin tsoron Allah, yayi mata godiya yace "Umma inna dawo zanje Gombe na dawo dasu Malam da Inna su dawo wurinmu mu zauna dasu" Umma tayi farin ciki sosai tace "gaskiya ne, tunda Allah ya bud'a mana yanzu sai su dawo kusa damu, in ya so duk bayan lokaci sai mu rik'a zuwa Gombe muna gaisawa da sauran dangin mu". Nan suka yi sallama tana sanya masa Albarka. *Nigeria* Abba ya tattauna dasu Ammi da Momy akan zancen Basma, ya bama Momy hak'uri akan abinda ya faru, sun sasanta kansu kana ya gargad'i kowa akan kar abari su Meena suji komai, kamar yanda suka yanke da sauran iyayen kafin su tafi. Haka aka rufe maganar ba tare da sun fitar dashi ba. Deeja ta damu Yaya Ahmad akan ya sanar mata abinda ke faruwa, hak'uri ya bata yak'i gaya mata, duk yanda su Meena suka so jin abinda ke faruwa amma ba suji komai ba a wajen mazajensu, k'arshe hak'ura suka yi da niyyar tambayar Basma, sun kira ta, itama tak'i gaya musu tace "ku kwantar da hankalin ku, za kuji komai nan gaba kad'an" dole suka hak'ura badan sun so ba. *America* *Bayan kwana Hud'u* Ya kama yau kwana biyar kenan da dawowar su Basma, cikin dare Basma ta tashi ta d'auki Jakar da diary d'inta ke ciki, ta gama sanya duk abinda ya kama, ta sanya wayar da take amfani wajen d'aukansu Yaya Shureym a ciki, ta barta a kunne, sai ta sanya dukkan gwala-gwalan zinarinta a ciki da hayan amfaninta, saita ta kulle jakar. Tashi tayi ta shiga had'a kayanta gaba d'aya a cikin trolley guda uku, hatta takalmanta bata bari ba, bayan ta kammala tas, sai ta sanya duka trolley d'in a cikin kitchen dinta ta kulle, Sallan Nafila ta gabatar, ta shiga kwararo Addu'a akan abinda take shirin aikatawa, Allah ya bata sa'a ya taimaketa, Sallan Asubahi aka kira ta gabatar da raka'atanil fajri, sannan tayi Sallan Asubahi tayi azkar na safe, saita tashi ta sanya sallayan a cikin d'aya daga cikin trolley, gado ta fad'a ta kwanta ta soma sharb'an barci. *Da safe* Misalin k'arfe tara na safe, Yaya Shureym yazo yana buga mata k'ofa, kamar bazata bud'e ba saboda barcin da take ji, zuwa tayi ta bud'e k'ofar tace "Yaya Shureym lafiya kake buga min k'ofa? wlh barci ke damuna" cikin murmushi yace "Lafiya lau, ina so ki d'an had'a mana breakfast kafin mu dawo daga asibiti, zan kai Safeena ne ba ta jin dad'in jikinta, daga nan za'ayi mata awon ciki" murmushi tayi tace "tom Yaya Allah ya bata lafiya" fitowa tayi ta tadda Safeena a falo sannu tayi mata saita amsa a yatsine, murmushi Basma tayi tace a ranta "kisha kuruminki Malama, yau zan bar miki mijinki" a fili kuma tace "d'an Baba yana baki wahala, Allah dai ya raba ku lafiya" ta amsa a takaice kana suka wuce. Kitchen Basma ta shiga, ta gayawa kuku Breakfast d'in da take so su had'a musu, kana ta koma d'aki da sauri, ta shiga fito da duk trolleyn ta falon, ta aje a bayan kujera, saita rufe su da wani zani. Wanka ta tayi, ta sanya doguwar riga bak'a mai aiki purple, sai ta yi rolin da farin gyale tayi kyau sosai, d'akinta ta bud'e ta fita farfajiyan gidan da gudu a tsorace tana ihu, da sauri duk ma'aikatan gidan suka fito, cikin harshen turanci ta shiga gaya musu "wani Abu ne a d'aki na Ku taimakeni Ku ciremin" suka tambayeta "me ta gani" tace "Ni bazan gane ko miye ne ba" Da sauri duk suka shiga falon suka soma dubawa, d'akinta suka shiga su duka, da sauri tabi bayansu, k'ofar ta jawo da k'arfi ta sanya key ta rufe su, cikin sauri taja trolleyn kayanta har waje, ta bud'e gate ta fitar dashi, a haka harta fidda kayanta duka, su Ema sai ihu suke akan ta bud'e su, kyalkyacewa tayi da dariya ta d'auki hand bag dinta ta fice abinta, tana fita ta samu taxi ya kwashe mata kayanta sai airport. Suna isa ta ja kayanta, zuwa minti sha biyar an gama checking kayansu sun shiga jirgi, minti goma da shigansu jirgi ya daga zuwa k'asarmu Nigeria.✈ *Su Basma an shuka tsiya😂😜, koya cakwakiyar zai kasance sai kun jini a next page...* *Rahma Ce* [8/10, 5:30 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *23.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Jirgin su Basma ya sauka lafiya, drop ta d'auka taxi, ya kaita asibitin da Yaya Ahamd yake aiki, nan ta bufa, ta ciro trolley d'inta guda biyu da kuma wannan bak'ar jakar da diary ke ciki, ta jasu zuwa cikin asibitin, gefe ta tsaya ta samu d'aya daga cikin masu gadi yana ganinta ya washe baki dan ya ganeta suka gaisa tace "aam Baba Dr Ahmad yana ciki kuwa? cikin ladabi yace "yana ciki, motansa yana cikin wancen barandan yayi parking d'inta" Murmushin jin dad'i tayi sai ta ciro wata farar takarda mai d'auke da wasik'a a ciki tace "Baba Dan Allah ka taimaka ka kai masa wannan kayan, sauri nake jirgi na jirana, ka gane ni ai?" cikin dariya yace "kwarai Hajiya na gane ki" murmushi tayi ta k'irga dubu Ashirin ta bashi tace "Baba ga wannan saika ci goro ko" jiki na rawa ya amsa yayita shi mata da albarka, kiran wani matashin saurayi yayi d'aya ne daga cikin drivern asibiti, yayi masa umarni daya d'auki d'aya daga cikin trolley, shi kuma Baba yayi mata sallama ya sanya wasik'ar a aljiunsa, kana ya d'auki d'ayan trolley da kuma bak'ar jakar suka shiga cikin asibiti. Basma binsu tayi a baya har saida taga sun isa k'ofar office d'in Yaya Ahmad, kana tadan tsaya, tana ganin sun Shiga sai ta juya cikin sauri ta isa bakin gate, taxi ta koma ta shiga, da gudu suka bar unguwar. Mai gadi suna Shiga, Yaya Ahmad ya kalle su cike da mamaki yace "Malam wannan kayan fa daga ina?" da dariya a fuskansa yace "Uwar d'akinta tace na kawo maka" cikin mamaki yace "wace uwar d'akin naka?" yace "Basma mana, ita tace na kawo maka domin tace tana sauri ne ana jiranta, tace in baka wannan wasikar ma" saiya mik'a masa, cike da tsoro da mamaki Yaya Ahmad ya mik'e yace "Basma kuma?" da sauri ya fita a office d'in, Baba mai gadi da d'ayan saurayin suka rufa masa baya, gate ya nufa yana hangen ko zai ga Motan da tazo a ciki, babu kowa bamu alaman wata mota, Baba mai gadi yace "kaga ikwan Allah sun riga sun tafi, acan fa na hangi mota taxi wanda ya kawo ta, nima nayi mamaki dana ganta a cikin taxi" ajiyar zuciya Yaya Ahmad yayi ya shiga wasi-wasi da damuwa, komawa office yayi ya Shiga bud'e jakukunan, tabbas kayan Basma ne a ciki, bak'ar jakar ne ya nima bud'ewa amma arufe take babu key a jiki, zama yayi kamar wanda yayi aikin gajiya, dan jikinsa duk a mace yake, da kuma tsananin fargaba da zuciyansa yake ciki, bud'e wasik'ar ya yi, ya soma karantawa kamar haka... *ASSALAMU ALAIKUM* *Yaya Ahmad da fatan duk kuna lafiya, nasan zaka yi mamaki da ganin kayana ba tare da na bari mun had'u ba, Yaya Ahmad ina cikin damuwa na tsani rayuwar dana ke ciki, dan haka zanyi nesa da kowa ko zanji saukin abinda ke damuna, Yaya Ahmad kafi kowa sanin bana son auren da a kayi min, amma na hak'ura nayi biyayya gasu Abba, na d'auki alk'awarin yiwa Yaya Shureym biyayya in zauna dashi, amma kash sai dai shi a gunsa akwai mugun nufi a zuciyansa game dani, a ranar da muka shiga jirgi zuwa garin America lokacin aurenmu, anan cikin jirgi Yaya Shureym ya fara shayar dani ruwan bak'in ciki, wanda har yau ina cikin shansa, Yaya Ahmad na so gaya maka komai a wancen lokacin, saina ce bari nayi hak'uri bai kamata in fara kai k'ara ba, kuma ma duk abinda zan fad'a ba mai yarda dani akai, sai kai kawai nasan zaka yarda tunda kai kasan halinsa, d'aurewa nayi tun daga ranar dana tafi na bar gida har zuwa yanzu, Yaya Ahmad bari na tak'aice maka bayani, duk kan k'arin bayani da kuma labarin zamana a America yana cikin wannan diaryna na rubuta shi, da kuma wasu hotuna a ciki wanda zasu zame min shaida, duk a cikin wannan bak'ar jakan, akwai kuma wayata a ciki wanda akwai wasu hotuna a ciki, ga system d'ina ka aje min shi, key d'in dana baka rannan ka aje min shine mabud'in wannan jakar, ina so ka kai gida ka bayyana wa su Abba komai dake cikin jakar nan, tare da karanta musu wannan wasik'ar da kuma abinda ke cikin diary na, Yayana nagode da kulawanka, nasan kaida Momy ne zaku fi kowa shiga damuwa, dan Allah ka bama Momyna hak'uri, kuma nayi muku alk'awari duk inda nake zan kula da kaina zan kare mana martaban gidanmu da mutunci na, insha Allah zan kiyaye duk kan hakk'ok'in Allah wanda ya rayata akaina, kuma zan kare igiyar Aure na.* *Hawayena ba zasu daina zuba ba, har sai naji a raina kun yafe min laifin dana yi muku akan tafiya da nayi na barku, Ina sonku duka dangina. Abbana ku yafenin Ammi na kar kuyi fushi dani, zan dawo amma ba nan kusa ba, hasalima a yanzu bansan ina na nufa ba*😭. *Bissalam*🙏 'Yarku Basma... Kafin ya gama karantawa, hawaye ya gama wanke masa fuska, tashin hankali ya shiga mara misali, da sauri ya share hawayensa ya sanya wasik'ar cikin aljiunsa, kiran wani mai goge masa office yayi, ya taya shi fita da trolley, mota ya sanyasu, ya shiga mota zuwa gida cike da tashin hankali. Basma suna isa airport ta biya mai taxi, ta ja trolley d'inta wanda ya rage guda d'aya, saita shiga ciki, ba wani b'ata lokaci suka shiga jirgi sai zuwa k'asar Etopia, jirgunsu na d'agawa taji gabanta ya fad'i, kewar family d'inta ya cika mata zuciya, ji tayi dama jirgin zai tsaya ta sauka, runtse idonta tayi tace a ranta "Anya na yiwa iyayena adalci kuwa? anya na yiwa kaina adalci? shin ya za suji in suka ji labarin na tafi, Allah sarki Yaya Ahmad ban kyauta muku ba" Ajiyar zuciya tayi tace "Shureym kaine silan komai, dole in yi nesa da kai da kuma mugun nufinka a kaina, na tsaneka ba zaka tab'a cimma burinka a kaina ba, kuma so nake ka gane kuranka kasan cewa ni Basma 'yar halak ce" saita ja tsaki ta gyara zamanta. Tsarbi counter ta ciro a hand bag d'inta, ta shiga salatin Annabi s.a.w, nan take taji natsuwa ya ziyar ceta, murmushi tayi saita lumshe idonta kamar mai barci. Yaya Ahmad yana isa gida yayi parking, da sauri ya fito ya kwalawa wani driver kira, cikin sauri yazo, jakan ya ciro ya ce ya d'auki d'aya, shima ya d'auki d'aya ya rik'e da bak'ar jakar, falon Abba ya wuce dasu, suna shiga suka aje, ba kowa a falon sai ya sallami driver. Zama yayi dirshen a k'asan kafet, ya rafka ta gumi tunani yake ta ina zai fara, wayansa ya ciro ya kira Amminsa cikin tashin hankali yace "Ammi kina ina? ki zo ina falon Abba" bai jira me zata ce ba ya kashe wayar, haka ya kira Momy itama, ya kira Naufal, ya kira Husna k'anwarsu, cike da damuwa duk suke fito, duk tunaninsu mutuwa akayi, kiran Deeja matarsa yayi ya kuma kira Meena itama, Ammi da Momy har rige-rigen shiga falon suke, tsayawa suka yi cirko-cirko ganin Yaya Ahmad shi kad'ai a falon, Meena ma cikin sauri ta isa falon haka ma Deeja, duk zama suka yi suna jero masa tambaya, Abba dake sama hayaniyar su yaji sai yayi sauri ya fito, ganin su gaba d'aya a falon ya tada masa hankali, saukowa yayi cike da fargaba yace "lafiya kuka taru anan?" Ammi tace "Yallab'ai, Ahmad ya kira mu yace mu taru anan, ni wlh duk hanlina a tashe yake, bamu san dalilin kiran ba" Ahmad mik'ewa yayi zai fita a falon, da sauri Abba ya tsaida shi "kai ina kuma zaka? bana son shirme, kazo duk ka tayar mana da hankali" hawaye ne suka ga ya sauka masa a kuncinsa, sai ya share bai ce komai ba ya fice, ai iya ka tashin hankali sun shiga ciki, domin basu tab'a ganin hawayen Yaya Ahmad ba da girmansa, danshi mutum ne mai d'auriya, da wuya kaga abinda zai tayar masa da hankali balle ya sashi kuka. Suna cikin zama na damuwa sai ga Yaya Naufal ya shigo, baifi minti biyar ba Anty Husna itama ta shigo, duk suka zauna suka gaishe da iyayan nasu tare da tambayan musabbabin had'uwarsu, kafin su basu amsa, Yaya Ahmad ya shigo ya nufi wurin trolley da suka shigo dashi, ya jawo su zuwa tsakiyar falon, Momy ce taji gabanta ya fad'i duk yanda akayi wani abu ne ya samu Basma dan tasan trolley ta ne. Yaya Ahmad ya zauna ya soma musu bayanin yanda Baba mai gadi ya kawo masa kayan, sannan ya bud'e wasikar ya soma karanta musu, iyaka tashin hankali sun shiga, Abba mik'ewa yayi ya soma safa da marwa, Yaya Ahmad ya gama karantawa ai sai Momy ta fashe da kuka, su Meena ma haka, Ammi ce tayi jarumta tace "innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yanzu wannan kayan ta ne kenan, ta tafi da sauran?" Yaya Ahmad yace "eh na bud'e na duba, ya tabbata kayan Basma ce" Key ya ciro, dama fitan da yayi d'azun shine yaje ya d'auko a d'akin sa, ya sanya ya bud'e jakan, diary d'in ya ciro ya bud'e, shafin farko labarin shigansu jirgi a ranar da suka bar gida a matayinta na Amaryan Shureym, Yaya Ahmad ya shiga karantawa, ai sai duk suka d'auki salati, lokacin da yazo wurin da ya koma kusa da Safeena a cikin jirgi da kuma kissing d'in da safeena ta mishi, basu k'ara tsinkewa ba sai da ya bud'e d'ayan tsafin bayan saukarsu a America, da irin marin da Yaya Shureym yayi mata, kai komai saida ya karanta. Yaya Ahmad ya shiga labarin irin dukan da Yaya Shureym ya fara yiwa Basma, hoton fuskanta data d'auka ya gani ya mik'e ya nunawa Abba, Abba runtse idonsa yayi saboda tsananin b'acin rai. Yaya Ahmad sai da ya karance musu tas abinda ke cikin diary, sun d'auki kusan awa biyu suna aikin sauraren Yaya Ahmad yana karanta musu, lamarin daya fi d'aga musu hankali shine labarin Safeena, da Basma ta bayar a matsayin wai Safeena matar Shureym ne, ga hotuna nan duk sun gani, a cikin jirgi ta k'arasa labarin yanda ta fito daga gidan Yaya Shureym, ta kulle ma'aikatan gidan a d'akinta. Abba wani gumi yaji yana saukar masa, Ammi tayi tagumi tana yiwa Allah tasbihi, Momy ko hawaye ke fita a idonta, ta kasa furta komai sai Addu'a take a ranta, falon yayi shuru sai shasshek'an kukan su Meena ke tashi, hatta Anty Husna kuka take yi, Yaya Naufal hatta shi sai da ya zubda hawaye ganin irin yanda Shureym ya sauyawa Basma fuska saboda duka, Abba ne ya nisa cike da damuwa yace "duk wannan damuwar nine naja, da ban had'a wannan auren ba da duk hakan ba zai faruwa, lallai Shureym kaci mutunci na kuma kaci Amanar zumunci, Amma zanyi maganinka, in har na rasa Basma, wlh kaima saika rasa rayuwanka, kai Ahmad maza ka shirya da kai da Naufal, ku kira min mai Martaba yanzu da kuma Ibrahim su zo yanzu, mu tafi American domin muje muga Matar da Shureym ya aje a gidanshi a ma tsayin Matarsa, na tabbatar Mai martaba bai san da wannan Auren nashi ba" Nan take su Yaya Ahmad suka kira su, suka kuma shaida musu gasunan zasu biyo jirgi, basu sanar musu komai ba, sun dai ce kirane ta tagaggawa daga president. *Bayan awa biyu* Su Mai Martaba sun iso fadar Shugaban k'asa, ba b'ata lokaci ya sanar musu America zasu domin tabbatar da wani lamari, Dady ne yace "to an sanar da Shureym da zuwanmu" Abba yace "bai sani ba kuma ba za'a sanar musu ba, sai dai kawai su ganmu, in munje mun dawo zan sanar muku da komai" Damuwa ne ya ziyarci su Mai Martaba, haka suka kama hanya suka wuce airport, cikin minti sha biyar jirginsu ya d'aga sai K'asar America. Sun bar su Momy a falon sunyi jugum-jugum ko wanne da abinda yake sak'awa a rai, babban damuwar su da tashin hankalinsu shine *ina Basma ta nufa...* *Rahma Ce* [8/10, 5:31 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *24.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *Etopia* Basma ta sauka a jirgi, sai rarraba ido take ko za ta ga wanda zata iya tambaya, jikinta yayi sanyi ganin tazo garin da bata tab'a zuwa ba, tsoro da fargaba ne ya cika ta, runtse ido tayi ta bud'e tace a fili "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, laa ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazza zalumin, astagfirullah wa'a tubu ilai" abinda tayi ta maimaitawa kenan a zuciyarta, a hankali ta soma jin k'arfin gwiwa da natsuwa, fitowa tayi bakin hanya ta tari taxi, cikin harshen turanci tace "Hotel mai kyau nake so ka kai ni" cikin harshen turanci ya mai da mata da "to shigo mu tafi". Ya kai ta babban hotel mai kyau, ta biyashi kana ta wuce ciki, kud'in d'aki ta biya, saita ja trolley d'inta, wata daga cikin ma'aikatan Hotel d'in suka yi mata jagora har d'akin data kama. Wanka tayi ta gabatar da duk Sallolin da ake binta, bata jin zata iya cin abu mai nauyi, telephone ta d'auka ta kira cikin holel d'in da a kawo mata coffee da kuma Burger, haka suka kawo mata, ta soma cin Burger taji sam teste d'insa ba dad'i, ajiyewa tayi tasha coffee d'in kawai. Tunanin ya za tayi rayuwa anan take yi, can ta tuno da rayuwarta da Yaya Aryan ta tabbatar da shi ta aura duk haka bazai faru ba, kuma ba zata sha wannan wahalar ba, hawaye ya sauka a kuncinta, tace "ya Yaya Aryan zaiji in yaji labarin na gudu" tunani barkatai tayi kamar zata kunna d'ayan wayarta saita fasa, dan tasan za'a iya nimanta ta layin, cire sim d'in tayi a wayan sai ta adana a cikin wallet d'in ta. Lafiyan gado tabi ta kwanta tana tunanin rayuwa, da haka barci ya d'auke ta. *America* Yaya Shureym sun dawo daga Asibiti, baifi minti 20 da wucewar Basma ba suka dawo, hon yayi amma yaji shuru ba'a bud'e masa ba, ba gate man a wurin, saukowa yayi ya bud'e da kansa ya koma mota ya shigo da ita, bai damu daya rufe gate d'in ba, waige-waige yayi amma bai ga ma'aikatan gidan ba, tsaki yaja sai suka shiga falo. Suna shiga suka fara jin ihu da hayaniya daga cikin falon, bin inda ihun ke fita suka dinga bi har suka isa k'ofar d'akin Basma, kallon-kallo Shureym da Safeena suka yi suna tunanin su waye a ciki, Shureym ne yayi k'arfin hali ya bud'e k'ofar, arba yayi da mai gadi da sauran ma'aikatan gidan sunyi gwimi sai zaro ido suke yi, cike da mamaki ya shiga tambaya su, nan suka bashi amsa, murmushi mugunta Yaya Shureym yayi ya kalli Safeena yace "kinga aikin shaid'aniyar yarinyar nan ko, wato kwana biyu tayi lamb'o ta natsu kamar ba ita ba, amma yau tasa kai ta fita duk dokar dana sa mata, baisa ta fasa k'etare wa ba, ta musu dubara ta fice, wlh yau inta dawo Ni da ita ne, sai nayi mata dukan da tunda aka haifeta ba ayi mata shi ba, kuma yau saina amshi hakk'ina da k'arfin tsiya" Yana gama fad'an haka ya wuce ya bama Safeena wuri, Safeena jikinta yayi sanyi, domin ta fara tsorata da lamarin Shureym akan yanda ya damu da budurcin Basma, kishi ne ya rufeta saita bi bayansa a fusace. Masu gadi haka suka fita sum-sum, dan ba suji duk abin da suke cewaba, a cikin Hausa su kayi magana, sun koma bakin aikinsu. Safeena ta cimmasa a cikin falon, ya zauna sai gumi yake yana kwafa yace "Yarinyar nan ni zata rainama wayo, ni bata bani hakk'ina ba taje bama wancan d'an iskan, wai ta yaya zan yarda ba bin maza Basma take yi ba" Safeena ce tace "Wai kai Shureym meyasa ka damu da Basma ne haka? yarinyar da bata sonka batasan kana yi ba, plss karabu da ita mana ka huta" cikin tsawa yace "ya isa, ya isa Safeena, wlh kika kuma furta kalman in saki Basma sai na miki abin da baki tunani, banda albarka cin cikin dake jikinki da saina huce haushi na akan ki, kuma in baki sani ba ki sani ina matuk'ar son Basma, son da ban tab'a yiwa wata Mace ba, ban yiwa kaina ba, na gaji da danne zuciyana akan Son da nake mata dan kawai in saki farin ciki, tom daga yau na daina b'oyewa ina son Matata sosai" Safeena fatsewa tayi da kuka wi-wi, ta kasa ce masa komai, cikin fushi yace "Malama in zaki min shuru kiyi shuru karki k'ara min damuwa tom" dole ta sassauta kukan, dan tasan halinsa sarai, zai iya mata abin da bata tsammani. Su Abba sun shigo k'asar America gari ya soma duhu, basu b'ata lokaci ba motoci suka zo d'aukansu daga gidan shugaban k'asan America. Suna d'aukansu Abba yayi umarnin da su fara zuwa gidan Shureym, in yaso saisu wuce can gidan president su kwana washe gari su wuce Nigeria. Sun isa k'ofar gate d'in gidan, Abba yace suyi parking a waje su shiga. Ta b'angaren Shureym kuwa suna zaune a falo ransa a b'ace yake, sai duba agogon Hannunsa yake yi har zuwa lokacin Basma bata dawo ba, ya cika yayi mak'il kamar zai fashe dan haushi, ita dai Safeena tayi turus da ciki, tayi tagumi dan yau gaba d'aya Shureym ya saurya mata ba wanda ta sani bane, Suna cikin wannan zaman ne ko wanne da abinda yake sak'awa a rai, sallaman Yaya Ahmad ne ya katse musu dukkan tunanin su, a zabure Shureym ya mik'e idonsa tamkar zasu yo k'asa dan tsoro, Yaya Ahmad fuskansa ba yabo ba fallasa ya shigo, su Mai martaba suna biye dashi a baya, ai nan take Shureym yaji tamkar k'asa ya bud'e ya shige ciki, cikinsa ne yayi wani k'ara alaman ya kulle masa, idonsa tamkar zasu yo k'asa ya kalli Safeena wanda itama ta gama tsurewa tana tsaye, dukansu sun gama shugowa falon, sun kafe su Shureym da kallo kowan ne yana nazarin su, atamke fuskokin su yake tamkar anyi musu mutuwa. Mai Martaba ne ya kalli Safeena yace "Yarinya ke wacece a gidan nan kuma ina Basma take?" Cikin rawar baki Shureym ya amshe maganar "Em em baf baf Baffa Ku zauna mana a kawo muku ruwa" Mai Martaba ya dakatar da shi yace "Banyi magana da kai ba, ke bani amsan tambayata" cikin sanyin jiki da tsoro tace "Ni ma Matar Shureym ce watanmu 8 da aure kenan, anyi bikinmu da wata d'aya akayi aurensa da Basma, kuma Basma tun safe da ta fita har yanzu bata shigo ba, muma zaman jiran shugowarta muke" Cike da tashin hankali Mai Martaba ya kalli su President yace "kunji abinda wannan Yarinya tace kuwa? kai Shureym abinda ta fad'a gaskiya ne?" sun kuyar da kai yayi k'asa ya kasa cewa komai, gumi ne yake karyo masa, tashin hankali ya shiga, hawaye ne ya fara zarya a kuncinsa ya kasa d'aga idonsa. Mai Martaba yace "yanzu Shureym abinda ka aikata mana kenan?" Dady ne ya nisa yace "da kyau Shureym yanzu sai ka fita ka nimo mana Basma mu tafi da ita, shine ran nan harkana iya kawo mana k'aranta, ashe Kaine azzalumi maci amana daka ci Amanarmu" yana gama fad'a president yayi murmushin takaici yace "am Ibrahim Basma bata k'asar nan, a yanzu haka mu kanmu bamu san inda take ba" cikin tashin hankali Dady da Mai Martaba suka ce "what" dama kunsan da haka, wai mai yake faruwa ne?" anan ne Shureym ya soma kuka wiwi yace "Na shiga uku Basma ina kika je, karki min haka, wlh ina son ki dan Allah ki dawo gareni, bazan iya rayuwa babu ke ba" wani wawan mari Yaya Naufal ya sakar masa a kumatu yace cikin zafin rai "mugu azzalumi maci amana, wlh kayi asaran rayuwa Shureym, ka b'atawa k'anwata rayuwa, ka kwashe dukkan farin cikinta, bak'in cikinka yasa ta tafi tabarmu, yanzu bamu san wani hali take ciki ba, kaci amanar zumunci" hawayen bak'in ciki ne ya zubo a idon Naufal, hakane yasa shi dole yayi shuru, kuka Shureym yake sosai yace "Abba Ku yafe min, na yarda nayi kuskure, amma dan Allah karku raba aurena da Basma, ina sonta sosai dan zan iya mutuwa in aka rabamu, dan Allah Ku nimo min Basma" Yaya Ahmad murmushi yak'e yayi dan takaici yace "Baka yi kuka ba tukunna Shureym, wa san yara kake yi" Abba yace "tunda idonmu ya gane mana komai mu wuce makwancinmu" Dady yace "kwarai kuwa, amma Ni fa banga ta barci ba, Basma nake so in san ina ta tafi" Abba yace "karmu damu insha Allah zata dawo cikin k'oshin lafiya, tun d'azu na sanya Commissioner 'yan sanda Mukhtar ayi binciken airport, dan sanin wata k'asa ta tafi, sai mubi bayanta" Yana gama fad'an haka suka fita, sun bar Shureym durk'ushe yana kuka cike da tashin hankali kamar k'ara min yaro, nadama ya rufe shi yana dana sani. Koda ya d'ago ko kallon inda Safeena take baiyi ba, d'akinsa ya wuce ya shiga had'a kayan shi, Allah-Allah yake gari ya waye, yaje office d'insa ya musu sallama ya wuce mahaifansa Nigeria. Safeena ma bata yi k'asa a gwiwa ba wajen had'a kayanta, dan ta tabbata barin su k'asar America yayi, kuma k'afar Shureym k'afarta, koda zai yankata gunduwa-gunduwa ne, sai ta bishi. Abba sun isa masaukinsu, suka ci abincin suka huta, su Dady duk suka kira matayensu akan Gobe in Allah ya kaimu su hallara zuwa abuja dukansu, ki wanne ya wuce makwancinsu. Haka suka kwana ko wanne cike da damuwa, yanzu tashin hankalinsu ina Basma ta tafi. *Washe gari* Basma tana farkawa ta shirya cikin doguwar rigan atamfa, ta sanya farin hijabi ya kawo mata iya gwiwa, ba dan kwali a kanta da yake hijab d'in mai hula ne, kayanta ta gama had'a su, fitowa tayi daga hotel d'in tana Jan trolley d'in ta, airport ta wuce tayi duk abinda ya kamata, saita shige jirgi sai k'asar Saudia, zuciyarta cike da farin ciki domin zata ziyarci d'akin Allah da kuma Masallacin Annabi s.a.w, tasan cewa zata samu farin ciki acan da samuwar dukka nin natsuwa. *Rahma Ce* [8/10, 5:32 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *25.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 *K'asar Monaco* Yaya Aryan tunda gari ya waye yaji gaba d'aya hankalinsa ya koma Nigeria, tunani barkatai ya shiga yi, cikin sauri ya mik'e ya shiga had'a kayansa, yana kammalawa yayi wanka ya shirya cikin Manyan kaya, Shadda ganila ash color ya sanya hula bak'i da takalmi, tare da sanya bak'in tabarau, yayi matuk'ar kyau, hakanan ya tsinci kansa cikin nishad'i, burinsa bai wuce ya ga Ummansa, ya wuce airport sai Nigeria. *America* Su Abba sun kamo hanyan Nigeria, Shureym ya tafi office d'insa ya aje musu komai nasu, ya sallame su, sunyi-sunyi ya k'arasa aikinsa amma yak'i dole suka hak'ura, gida ya koma ya kwashi kayansa, Safeena na biye dashi ba um ba um-um a tsakaninsu, sun shiga mota da duk kayansu, shureym ya sallami duk ma'aikatan gidan ya bama wani abokin aikinsa Key d'in gidan, dama gidan na ma'aikatansu ne, airport suka wuce baifi minti talatin da zuwansu ba jirginsu ya d'aga sai Nigeria. *Nigeria* Yaya Aryan ya sauka lafiya, taxi ya shiga ya sauke shi a gida, yana shiga suka gaisa da mai gadi, ciki ya shiga ya wuce d'akinsa, wanka yayi ya sanya k'ananun kaya, kana ya nufi sashin Umma, bata san da dawowansa ba, domin yana so yayi surprising d'inta, yana shiga falo yaga Iya mai aikinta suka gaisa Iya tace "aiko Hajiya bata nan" zama yayi ya kira number Umma ringing biyu ta d'auka yace "Umma kina ina na dawo ina son in baki mamaki kuma bakya gida, da safen nan ina kika je haka?" murmushi tayi tace "Aryan wani irin ka dawo, ba munyi da kai sai nan da wata uku zaka dawo ba, meya dawo da kai yanzu?" dariya yayi yace "Umma hankalina ya dawo gida ne wlh, kewarku ya cikani sosai, shiyasa na dawo, yanzu kina ina ne?" tace "ina gidan shugaban k'asa wurin Khadija" yace "Da fatan dai lafiya ko?" "lafiya lau, ka k'ara so ka gaishesu mana" "To Umma gani nan zuwa" haka ya mik'e ransa bai masa dad'i, yana ji kamar karya je. Khadija ta kira Umma ta sanar mata da abinda ke faruwa, dalilin zuwan Umma kenan da safen domin tayi musu Allah ya kyauta. Yaya Aryan ya isa gidan president, ya same su Umma a part d'in Momy, zama yayi a k'asan kafet, Kansa a sunkuye ya gaishe dasu Ammi, ganin falon cike da mutane ya sashi jin wani iri, sai ya fito Deeja ta biyo shi a baya. Sun zauna a barandan shan iska dake cikin farfajiyan gidan, nan suka k'ara gaisawa suka shiga hiran zumunci, Deeja bata yi gigin gaya masa abinda ke faruwa ba, Umma ce ta fito ta samesu suna zaune cikin barandan, murmushi Umma tayi, farin ciki ne ya mamayeta Aryan ya dawo da walwalansa, Addu'a tayi Allah ya bashi mata ta gari. K'arasawa tayi wurin tace "Deeja ni zan tafi in Ahmad ya dawo ki gaishe shi" Deeja ta kwab'e fuska kamar za tayi kuka tace "kai Umma baki dad'e ba fa, kuma da kin jira sun kusa k'ara sowa ma" murmushi tayi tace "haba Deeja baki ganin Yayanki ya dawo ne, so nake inje in had'a masa abinci dan nasan da wuya inya karya ma" Murmushin jin dad'i Yaya Aryan yayi yace "kinsan kuwa Umma nayi missing d'in Abinci ki, kuma akwai yunwa a tare dani, ki tafi kawai nima ina bisa hanya" dariya tayi tace "yauwa Aryan saika tawo" nan tayi sallama da Deeja ta wuce ta shiga mota driver ya jata sai gida. Aryan suna zaune a wurin Yace "Deeja lafiya naga gidan naku da taron mutane?" murmushi yak'e tayi tace "lafiya lau, president ne yayi umarni da duk a taru anan, mutanen kano da Kaduna duk sunzo, yanzu jiran isowarsu muke daga America" yace "to Allah yasa lafiya, Nima ina ganin bari na gudu ba zan iya jiran su dawo ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu zanzo na gaishesu" bai rufe baki ba, motoci suka fara shigowa cikin haraban gidan, Deeja tace "laaa gaka sun dawo ma muna zancen su" murmushi kawai yayi baice komai ba, yana kallon mototcin da suke shigowa, da sauri ya mik'e lokacin yaga su Yaya Ahmad sun fito ya isa wurin yana dariya, suka kama hannun juna cike da farin ciki a fuskokinsu Yaya Ahmad yace "Aryan saukan yaushe?" cike da dariya yace "yau na sauka" "to kai da mu kayi waya kace sai nan da wata uku zaka dawo" murmushi yayi yace "wlh naji hankali na yayo gida burina in ganin a Nigeria" gaban yaya Ahmad ne ya fad'i amma saiya dake, ya mayar masa da murmushi yace 'lallai fa kace kana kewarmu" "kwarai kuwa nayi" Nan ya wuce wurin President ya risina zai gaisheshi, Abba shafa kansa, ya kama hannun Aryan suka wuce babban falonsa. Falon ya cika da dangi, Dady, Abba, Mai Martaba, da duk iyalensu, Ammi, Mami, Momy, Umma, Hajiya Murja, Duk suka gaisa, suna cikin wannan zaman ne sai ga sallaman Yaya Shureym a birkice ya shigo, Safeena na biye dashi a bayansa, Mami na ganinsu gabanta ya fad'i damm, a razane ta mik'e tace "Shureym lafiya na ganka haka wurjanjan" zuwa yayi ya rungumeta ya soma kuka wiwi, duk mamaki ya cika mutanan falon banda su Abba dasu suka san komai. Yaya Aryan yana gefen Yaya Ahmad suna hira k'asa-k'asa, Dady ne yayi gyaran murya yace "Kai Shureym samu wuri ka zauna, da fatan duk kun san musabbabin taruwan mu anan, akan Shureym da Basma" ai yana furta Basma Yaya Aryan ya d'ago fuskansa gabansa ne ya shiga dukan uku-uku, mutanan falon yabi da kallo amma baiga Basma ba, dama tun d'azu yake raba ido ko zai ganta, amma shuru ba alamunta, kamar zai tambayi Deeja amma saiya fasa. Abba yasa Yaya Ahmad ya karanta lettern da Basma ta rubuta da kuma diary d'inta, nan ya shiga karantawa iyayen sai salati suke yi dama su Mai Martaba basu san komai ba sun dai je America sunga Shureym da mata, Mai Martaba jikinsa yayi sanyi, yace a ransa "lallai shureym yaci amanansa" k'arin tashin hankalinsa yanda Shureym ya maida Basma tamkar baiwansa. Yaya Ahmad ya gama karantawa, Aryan gumi ya gama jik'ashi, kamar shine yayi karatun, falon ne yayi shuru, Ummi tace "ai biri yayi kama da Mutum, kazo ka kawo k'aranta harda yiwa Yarinya k'azafi, ni dama ban yarda ba, ashe kai ne ke cutar da ita" Mai Martaba yace "ka kyauta Shureym, yanzu amanar da muka baka kenan, kaci amanata da zumuncinmu ban tab'a tsammanin haka daga gareka ba" cikin kuka Shureym yace "Baffana ku yafe min sharrin shaid'an ne" Mai Martaba ya katse shi yace "yi min shuru mutumin banza kawai, yanzu ya akai kayi aure har ban sani ba, wasu iyaye ne ka samu suka jagoranci auren?" Cikin tashin hankali Shureym ya basu labarin yanda aka yi aurensa da safeena, jikin kowa ne yayi sanyi jin cewa Mami itace ta goya masa baya wajen yin aure, Ammi cikin fad'a tace "ai dama Hajiya Sa'a na dad'e da sanin Yayana bai yi sa'an mata ba, kin cika kyakkyawar makira mai raba kan zumunci, ina ce kece kika matsa kika hura wuta dan ganin Shureym ya auri Basma, ashe da mugun nufi a ranki, sannan har kina goyawa d'anki baya ya auri wata, tun farko da ya nuna baya son Basma me yasa zaki matsa ya aure ta, da munsan da haka wlh da ba zamu tab'a bari ya auri Basma ba" Mami ne cikin tsiwa da makirci tace "ya ishe ki Hajiya Fatima, ba zan d'auki cin fuska ba" Mai Martaba ne ya daka mata tsawa yace "Mutumiyar banza, dama duk cikin gidana kece mai bani matsala, kuma kisani kamar yanda kika had'a auren Shureym da wancen Yarinya to tamkar kin datse igiyar aurenki ne, saboda kinsan ba na son zama da munafuki mara tsoron Allah" A firgice Mami yace cikin kuka "haba Mai Martaba tuba nake, dan Allah karka min haka, nasan nayi kuskure bazan kuma haka ba, ka k'ara hak'uri dani, dan Allah ka gafarta min zan gyara halina" Saita kai kallonta ga Shureym ta cigaba da cewa "Kai Shureym maza ka saki Safeena don Mai Martaba ya maida aurena" cikin fad'a Mai Martaba yace "karka kuskura ka furta saki akanta domin wlh saina sab'a maka, aure dai ka riga kayi, sai ka san inda zaka aje musu Yarinya kuma ba dai gidana ba, sannan in kika sanya Shureym ya saki Yarinyan mutane wlh saina tsinke duk igiyar aurenmu dake wanda yayi saura" Abba ne ya katse shi da cewa "haba Mai Martaba, in rai ya b'aci hankali karya gushe, dan Allah ka maida aurenka da Hajia Sa'a ka kuma yafewa shureym, kuskure dai an riga anyi, sannan ni dai zan tsare Shureym har sai anga Basma, dan alkawari na d'auka akan haka" Dady yace "ni dai duk kowa yayi hak'uri a sulhunta, aure dai ya riga yayi, dan haka sai mu jira dawo war Basma, in tace zata zauna da mijinta shikenan, in kuma tace bazata zauna dashi ba, to ba mai yi mata dole" Kuka Momy take wiwi, tace "ni dai Ku aje duk wannan bayani, ku tashi ku nimo min Basma, ba zan jure rashinta ba" Kuka Shureym yake tare da sambatu "Dan Allah Basma ki dawo gareni wlhi ina son ki, bazan jure rashinki ba, Basma nayi miki kuskure ki yafemin" Su Meena ne suke hararanshi shike da jin haushinsa, Yaya Adam ya daka masa tsawa, "Dalla yi mana shuru mutumin banza, haka kawai ka tada zaune tsaye, ana zaman lafiya, duk abinda ka dauko insha Allah kanka zai tsaya, kuma babu abinda zai tab'a zumuncinmu" Aryan ya mik'e tsaye fuskanta a tamke cike da damuwa, baicewa kowa komai ba, ya nima fita daga falon, Yaya Ahmad yace "Aryan ina zaka ka tsaya mana" waigowa yayi idonsa na fidda kwalla, ya bud'e baki zaiyi magana, sai kawai waji wani abu ya tokare masa k'irjinsa, jiri ne ya dibeshi sai ya fad'i k'asa da k'arfi, da gudu Yaya Ahmad ya isa wurinsa, Deeja ce ta saki wani k'ara tace "Yaya Aryannnn" cike da firgici duk suka isa wurinsa, cikin tashin hankali suka wuce dashi Asibiti... *Rahma Ce* [8/11, 6:16 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *26.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Bayan sun kaishi asibiti likita ya duba shi, ya tabbatar musu da damuwa ce ta haifar masa da suma "amma yanzu ya farfad'o, nayi masa alluran barci domin kwakwalwansa ya huta, zuwa anjima inya farka, komai zaiyi dai-dai insha Allah" Bayanin da likita yayiwa su Yaya Ahmad kenan sai ya wuce, zama suka yi suna ta zancen zuci, Yaya Ahmad, Yaya Naufal, da kuma Yaya Jamal sune suka kawo shi asibiti. A can gidan kuma sun k'ara shiga damuwa fiye da damuwar rashin Basma, Dady ya shiga tunanin ina ya san Aryan, lallai fuskansa tayi masa kama da wanda ya sani da dad'ewa, amma ya kasa tuna komai, matsantawan da yayi ma kansa da tunani ne ya haifar masa da ciwon kai, dole ya yakice abin a ransa dan gudun matsala. Awa biyu Yaya Aryan ya farka, sai dai bai iya furta koda kalma d'aya ba, idanun sa sun masa nauyi da kyar yake iya bud'esu a hankali ya rufe, hawaye mai zafi ya gangaro masa a kefen idonsa, Yaya Ahmad ya matsa kusa da gadon cikin sanyin murya da tausasa zuciya yace, "Aryan kayi hak'uri duk kan tsanani yana tare da sauk'i, dan Allah ka sanyawa zuciyanka salama, insha Allah komai zaiyi dai-dai, ka rik'a Addu'a a zuciyanka zaka samu sassauci, yawan damuwa baida amfani domin zai rik'a cutar da lafiyanka" A hankali ya bud'e idonsa, ya fud'e baki zai yi magana amma ya kasa, Yaya Ahmad ne ya dakatar dashi ya d'aga masa hannu yace "karka furta komai, ni dai kayi amfani da shawaran dana baka". Haka suka cigaba da zama a Asibiti sai yamma lis likita ya sallame su. Suka wuce dashi gida tare da magungunansa, suka gaisheda Umma, kana suka yi musu sallama. Umma ta kawo masa abinci faten Irish da naman kaza a ciki, da kyar yaci kad'an kana ta zauna kusa dashi ta dafa kafad'ansa tace "Aryan ya kake abu kamar ma tsatson musulmai ba, banji dad'in yanda kake nuna rashin tawakkalin da kake yi, koda nasan zuciya ba tada k'ashi, daman dalilin dawowarka kenan kazo kaga abin bak'in ciki, amma haka Allah ya rubuta, ni dai ina k'ara jan kunnenka ka cire Basma a ranka, kayi tawakkali da lamarin Allah yanda yazo maka, Basma dai da auren wani akanta dan haka ka cireta a rayuwanka, in dai baso kake ka sanyawa kanka wani ciwon ba, a kullun ina maka Addu'a Allah ya baka mata tagari mai tsoron Allah" Aryan rungume Umma yayi ya soma kuka wiwi, yace "Umma ina k'ok'arin cireta a rayuwata, abinda naji ne ya d'aga min hankali, yanda Shureym ya azabtar min da Basma, yayi mata mugun rik'o, Umma ba zan samu natsuwa ba har sai Basma ta dawo cikin koshin lafiya ta cigaba da rayuwan farin ciki kamar kowa yake yi, dan Allah ki yafemin Umma na, son Basma a jini na yake, cireta a zuciyata abu ne mai wahala, sai dai na miki alkawarin kiyayewa akan haka". Umma ta kwantar da Kansa bisa cinyarta, ta shiga lallashinsa har saida yayi shuru yana ajiyar zuciya. *Makkah* Basma ta sauka lafiya ta kama d'aki a hotel dake kusa da harami, wanka tayi ta kwanta domin ta huta, tunanin rayuwarta takeyi, hakanan taji gabanta na fad'uwa, Aryan ne ya fad'o mata a rai, hoton fuskansa ke mata yawo a cikin kwayar idonta, hawaye ne ya soma zarya a idonta, bata hanasu zuba ba domin hakan ne zaisa taji sanyi a ranta. Takai kusan rabin awa a cikin wannan yanayin daga bisani ta mik'e tayi shirin fita ta wuce cikin masallaci. *Nigeria* An samu bayanai akan Basma ta shiga jirgin k'asar Etopia, sakamakon binciken da akayi a airport, haka Abba ya tura wasu domin dubata a can k'asar na Etopia. Abba ya sanya an sakaye Shureym a cikin wani d'aki dake cikin gidansa, za'a bashi abinci da komai na buk'ata, fita ne kawai bazai yi ba dan har masu tsaronsa aka aje, har sai anga basma. Safeena duniya tayi mata k'unci, kuma gaba d'aya dangin su Shureym sunk'i amincewa da ita, dole yasa tayi d'amaran komawa gidansu Adamawa, da tsohon cikinta gunin tausayi. Dady da Abba sun shawo kan mai martaba da kyar, akan ya maida aurensa da Mami, ba dan yaso ba ya maidata d'akinta, duk sun koma gida, an cigaba da Addu'a Allah ya bayyana Basma. Masu bincike sunyi iya k'ok'arinsu wajen bincika Basma, amma babu nasara, k'arshe hak'ura suka yi suna dawo Nigeria, hankalin su Momy ya kuma tashi, lamarin ya k'ara dagule musu, Addu'a suke kawai da sadaka domin Allah ya bayyana ta. *** *Bayan wata guda* Safeena ta haihu 'ya mace, babu abinda ta samu daga dangin mijinta, iyayenta su suka yi komai, koda ta kira Shureym ta sanar masa, yayi murna sosai sai dai ba halin zuwa, ya kira Maminsa ya gaya mata amma ba halin zuwa itama, saboda tana bisa hukuncin Mai Martaba. Ranar suna Yarinya yaci sunan Kausar. Kowa ya cigaba da harkokinsa, sai dai damuwa yana k'arkashin zuciyansu na rashin sanin inda Basma take, Yaya Ahmad yayi iya k'ok'arinsa ganin an samu labarin gajinta amma abu yaci tura, Momy ciwo riris ya kamata duk tayi bak'i ta lalace, ta b'angaren Shureym kuwa ya zama tamkar zautacce, ba yida magana saina Basma, shi dai burinsa ta dawo ya nima gafaranta su cigaba da zaman aurensu. *Makkah* Basma ta murmure ta k'ara kyau, ta samu natsuwa sosai, sai dai zuciyarta yak'i karaya da takoma gida, gani take har zuwa lokacin su Abba basu saduda ba, tausayin Momy take da kuma Yaya Ahmad, sai Yaya Aryan tasan tabbas sune wanda sukafi kowa damuwa akan rashin ta, kayanta ta had'a ta nufi Madina, ta had'u da wata mata yar k'asar Nigeria tana aure anan madina da mijinta, Hajiya Kaltum itace ta bata masauki a gidanta, kullun a masallacin fiyayyen halitta s.a.w take yini, sai dare take komawa makwancinta, tana ibada sosai kuma zuciyarta ta samu kyakkywan natsuwa. Wani lokacin sai taji kamar ta dawo Nigeria, wani b'angare na zuciyarta ke gargad'inta akan ta k'ara hak'uri da sauran lokaci. *** *Bayan wata guda* *K'asar Monaco* Yaya Aryan ya koma ya cigaba da karatunsa, saura masa wata guda ya dawo gaba d'aya, hankalinsa yana Nigeria kullun cikin tambaya yake ko anga Basma, amsa dai d'aya ne ba'a ganta ba. Jidda ta matsawa Yaya Aryan amma duk da haka bata samu yanda take so ba, k'arshe tayi fushi ta daina kula shi. *Nigeria* Khadija ta sillib'o d'anta Namiji kyakkyawa mai kama da Yaya Ahmad, gida ya cika da yan barka, wannan haihuwar sai ya rage musu rad'ad'in rashin ganin Basma. Kwana biyu da haihuwar Khadija Leema itama ta haihu, sun samu d'iya Mace, nan hidima ya k'aru, Leema gaba d'aya aka d'aukota sai Abuja, Kaka Ma'u itace mai yi musu wanka itada da Deeja, farin ciki baya misaltuwa a wannan family, yanzu Meena ce tayi saura, had'a taron suna suka yi, suka k'ara kwana biyu na sunan Deeja aka had'a da Leema, yaron Yaya Ahmad yaci sunan Abba Mukhtar, suna kiransa da Walid, sai Yarinyar Yaya Jamal sunan Ummi taci Sadiya, suna kiranta da Walida, anyi taron suna an watse cikin farin ciki. *Madina* Basma tana madina tayi sabo sosai da Hajiya Kaltum, Hajiya Kaltum 'yar maiduguri ce kasuwanci mijinta ya dawo dasu Madina, yaransu biyu Nana da Amir. Basma ta fara shirye-shiryen komawa Makka, Hajiya Kaltum ta shiga gyara Basma sosai, dilka dasu gyaran jiki tayi mata, Basma ta k'ara kyau sosai, duk tunanin Hajiya kaltum Basma komawa Nigeria zata yi, shiyasa take gyarata saboda ta sanar mata tanada Aure. Ranar da zata tafi ta bata sauran had'in Magani, harda tsaraba, sannan suka amshi number juna, suka yi sallama cike da kewar juna. Basma ta koma jiddah, hankalinta ta koma gida, zullumi da fargaba ya cikata akan son sanin ya makomar aurenta yake, da haka tace bari ta k'ara kwana ki ta cike wata uku, kafin ta koma Nigeria. *** *Bayan wata guda* Meena ta haihu 'ya Mace kyakkyawa mai kama da ita, farin ciki ba'a magana a gun su, yan barka sunata zuwa, su Leema da Deeja kuma anata wankan jego, gidan ya k'ara cika da mutane, Meena, Leema, Deeja suna zaune suna hira Meena tace "Allah sarki Queen Basma, wlh inna tuna life d'in da muka yi a baya har kuka nake saboda missing Basma da nayi, gashi yanzu duk mun haihu ita ko nata auren bata ji dad'insa ba, kuma duk tafimu kamun kai, amma Allah saiya jarabceta, ga gata da komai amma bai mata maganin matsalanta ba" Leema tace "bari kawai Besty, ai missing ma ba'a magana, naso ace duk wannan shagalin tana nan a kayi, wlh Yaya Shureym ba k'aramin azzalumi bane, bana fatan Basma ta cigaba da zaman aure dashi" Deeja tace "gaskiya ne, amma ni kam ina ganin son Basma a idon Shureym fa, kawai yayi rashin hankali ne a kan lamari, kuma Basma tana da sauk'in kai, muzguna mata da yayi ne yasa tayi masa haka" Leema tace "kunga dai Yaya Shureym d'an Uwana ne Ubanmu d'aya dashi, Amma wlh koda yana son Basma, ni sai na zugata karta koma gidansa, dan basu dace ba" nan dai suka cigaba da tattaunawa. * Yaya Aryan ya sauka a jirgi direct ya wuce gida, ya samu Umma ta yi masa barka da zuwa, abinci yaci kana ya wuce ya watsa ruwa, k'ananun kaya ya sanya, ya fito yace ma Umma ya tafi gidan Abba, zaije yaga yaron Deeja, Umma tace "a dawo lafiya, ka gaida mutanan gidan". Yana isa ya wuce part d'in Abba suka gaisa, kana ya je part d'in Ammi nan ya samu Momy duk suka gaisa, sai ya wuce part d'in Deeja yaga Walid sun gaisa sosai na zumumci, Deeja sai murna take da ganin Yaya Aryan, nan ta rakashi part d'in Yaya Naufal yaga Baby, daga nan ya wuce part d'in Kaka Ma'u yaga Baby Walida yarinyar Leema. Suka gaisa saiya musu sallama ya wuce. Haka nan yau yaji nishad'in son zuwa wurin shak"atawa, yana tafiya a mota a hankali sanyin AC na ratsa shi, wak'ar sudan ya sanya, sautin na duka a hankali. A haka harya isa wurin. * Basma ta sauka a jirgi da misalin k'arfe Bihar na yamma, iska mai sanyi yashiga ratsata, gaba d'aya zuciyarta ta cika da tunanin Yaya Aryan, burinta bai wuce tayi tozali dashi ba, taxi ta d'auka drop ta sanya kayanta a ciki, ta shiga ta zauna, lumshe ido tayi taji tana buk'atar zuwa wurin tsak'atawa kafin ta isa gida, har sun d'auki haryan da zai sadata da gida, saita sanya mai motan ya sauya akalan motan, da ya fara kaita wurin shak'atawa. Suna kaiwa tace wa mai mota, "dan Allah kad'an jirani ina zuwa" yace "to hajita sai kin fito" ta shiga cikin wurin a natse, har saida ta kai inda suka saba zama da Yaya Aryan ta samu guri ta zauna, runtse ido tayi ta shak'i iskan dake gurin, nan take taji k'amshin turaren da ba zata tab'a mantawa ba, waige-waige ta soma yi, amma babu alamansa. Ta b'angaren Aryan yana zaune ta bayan in da Basma ke zaune nesa da ita, ya d'aga kansa sama ya rufe idonsa, da alama ya shiga yin tunani mai zurfi, Basma tashi tayi tana bin inda k'amshin turaren ke fitowa harta hango Aryan zaune agun, murza idonta tayi sosai ta bud'e ta kafa masa ido, ta tabbatar Yaya Aryan d'in ta ne, murmushi ta saki saita gyara tsayuwa, ta b'oye a bayan wata bishiya tana kallonsa, kamar ance ya farka daga dogon tunanin da yake ciki, haka ya farka yana waige-waige, jikinsa ya bashi ana kallonsa, amma sai ya mik'e ya danyi tafiya kad'an saiya dawo ya zauna, iska ke kad'awa sosai a gun, iskan ya gauraye k'amshin turaren su ya bayar da wani k'amshi mai dad'i, lumshe ido Yaya Aryan yayi ya bud'e, Basma sai murmushi take yi zuciyarta ya wanke tas ba sauran damuwa. Yaya Aryan ya kurawa wurin bishiyar ido, yana nazarin tanan ne ake kallonsa, "to waye a gun" ya shiga tambayan kansa, mik'ewa yayi ya doshi bishiyar, Basma na ganin ya tunkaro wurin, saita juya da sauri ta b'oye a bayan wasu fulawawi, koda yazo gurin wayam ba kowa, mamaki ya kamashi yace a ransa "ko dai Basma kemin gizo kamar yanda ta saba min" murmushi yayi sai ya juya zai tafi, da sauri Basma ta fito daga mab'oyarta, Aryan yaji ance "Yaya Aryan" A razane ya tsaya tsak ya kasa motsi mai k'arfi balle ya iya juyawa, ya shiga tambayan kansa "mafarki nake ko gaske ne" domin yaji muryan da ba zai tab'a mantawa ba ya daki kunnensa... *Rahma Ce* [8/11, 6:18 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *27.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 A hankali ya juyo ya fuskace ta, ido cikin ido suke kallon juna harna tsawon minti biyar, Yaya Aryan ya katse kallo tare da sauke ajiyar zuciya a hankali, fuskansa babu yabo ba fallasa, bai furta mata komai ba ya juya zai cigaba da tafiya, cikin sauri ta sha gabansa tace "haba Yaya Aryan ya zaka wuce baka ce min komai ba, yanzu na sauka a jirgi dawo wata kenan, ko gida banje ba naji sha'awar zuwa wurin nan, zuciyata ce ta jawoni ashe kai ne zan gani, dan Allah kace wani abu ko baka farin ciki da gani nane" saita k'arashe maganar cikin shagwab'a. Kallonta yayi sama da k'asa sai ya yatsine fuska yace "ke wacece ban ganeki ba fa?" damm Basma taji zuciyarta ta buga, tace cikin tsoro da sark'ewar murya "Haba Yaya Aryan nice baka gane ba, Basma ce fa" ya d'aure fuska yace "Malama kiyi hak'uri ni ban ganeki ba, zaki iya tafiya" ai Basma cikinta ne taji ya murda, tayi sauri ta dafe tana ambaton Allah, kuka ta b'arke dashi mai k'arfi, cikin kuka tace "haba Yaya Aryan dan Allah karka azabtar da zuciyata, ya zaka ce baka gane ni ba" juyawa yayi ya cigaba da tafiya bai bata amsa, sakamakon hawaye da ya cika masa ido, yayi gaba abinsa ko waiwayanta baiyi ba. Cikin kid'ima Basma ta bar gurun da gudu, mutane sai kallonta suke, mota ta shiga tana kuka, da kyar ta iya lallashin kanta tace wa driver ya wuce da ita, duk abinda take yi akan idon Yaya Aryan. Da sauri ya shiga mota yabi bayansu domin ya tabbatar da gida zata wuce, karta kuma wucewa wani wurin, a hankali yake bin bayansu, hawaye nabin idonsa karatun Alqur'ani ya sanya yana bin karatun a hankali. Basma abin duniya ya dameta, gaba d'aya farin cikin data dawo dashi ya gushe, a haka suka isa gida ta sauka tabiya mai taxi, trolley taja tun daga bakin gate sicurity suka fara mamakin ganinta, gaisheta suke tana d'aga musu hannu, Yaya Aryan tunda ya tabbatar gida ta shiga, saiya wuce gida cike da damuwa, zancen zuci ya shiga yi "Nasan yau na b'atawa Basma rai, Amman hakan da nayi shine dai-dai, dan bai kamata na nuna wani abu ba saboda, da auren wani a kanki Basma". Ma'aikatan gidan suka rugo da gudu suna k'ok'arin amsar trolley ta, d'aga musu hannu tayi sai duk suka matsa, ta cigaba da tafiya jiki a mace, ta isa tsakiyar gidan saita tsaya k'am tana kallon wani part ya kamata ta fara zuwa, tana tsaye tana nazari da tunanin ina zata nufa, saiga Yaya Ahmad sun jero da Khadija tana rik'e da Walid a hannunta, tsayawa tsak suka yi suna kallon Basma daga nesa, Yaya Ahmad ya murza idonsa ya bud'e su sosai danya tabbatar da ita dince, Deeja tace "Yaya Ahmad ko kaga abinda na gani?" cike da mamaki yace "nagani Deeja, nima naso tambayarki, gani nake kamar gizo take min" da sassarfa Yaya Ahmad ya isa wurinta, tana ganinshi ta saki kuka mai cin rai ta fad'a jikinsa, Yaya Ahmad ya rungumeta cike da farin ciki, ya dago fuskarta yace "Basma da gaske kece kin dawo garemu, dan Allah karka sake tafiya ki barmu" d'agata yayi sama yayi juyi da ita, sai ya direta, hannunta ya kama suka wuce part d'in Momy, Deeja rufa musu baya tayi cike da murna. Suna shiga part d'in Momy suna tare da Ammi, sai Leema da take zaune tana bama Walida nono, da gudu Yaya Ahmad ya shiga yana jan Basma saida suka je gaban Momy suka tsaya suna haki, yace cikin murna "Momy ga Basmanki ta dawo" Momy mik'ewa tayi ta rungumeta sai ta shiga kukan farin ciki, ai cikin k'ank'anin lokaci kowa na gidan ya hallara falon Momy dan ganin Basma, murna da farin ciki ba'a magana, tunda daga bakin gate zaka jiyo hayaniyarsu. Anty Husnah a sittin ta tuko motanta tazo gidan, part d'in Momy ta nufa, aka cigaba da murna da ita, sun kira dangi a waya an sanar musu da abin farin ciki, Abba baya k'asar, yana k'asar Russia. Yaya Ahmad ne ya kirashi ya sanar mishi da abin farin ciki, Abba yayi murna yace ya bama Basma wayar suyi magana, Basma ta amsa wayar suka gaisa, Abba yace "Basmata da fatan kin dawo lafiya babu wata Matsala ko?" murmushi tayi tace "Abbana lafiya lau" yace "Basma Allah ya miki albarka, insha Allah nan da mako guda zan dawo, zan shirya miki kaya taccen liyafa dan murnan dawowarki, bana so ki fita ko nan da k'ofar gate, kuma ki gayawa Ahmad duk abinda kike so ya siya miki, in ma kina son fita Ahmad ya kaiki inda kike so ko Naufal" cikin jin dad'i tace "to Abbana Allah ya dawo mana da kai lafiya" ya amsa da "Amin" saita bama Yaya Ahmad wayar, Abba yace ya sanya shi a hand free, ya sanya shi kowa na saurare, Abba yace "jan kunne zanyi wa kowa, kar a kuskura a b'atawa Basma rai a ririta min ita har na dawo, duk wanda yayi k'ok'arin b'ata mata rai jikinsa zai gaya masa, kuma inna dawo saina zab'awa mutum" duka suka kwashe da dariya, daga nan saiya kashe wayan. Basma bata samu kanta ba sai dare, kowa so yake ya zauna da ita suyi hira, hakan ya sanyata farin ciki sosai, sai dai a k'asan zuciyarta tana cike da damuwa akan abinda Yaya Aryan ya mata. Bayan tayi wanka tayi shirin barci ta kwanta akan lallausan gadonta, Kaka ce ta shigo tace "tashi zo muje sashi na kiyi barcin acan" Basma cikin shagwab'a tace "haba Kaka, wlh na gaji ki barni nayi barci na anan" "naki in barki d'in, tashi maza mu tafi" haka ta mik'e tana zunb'ura baki suka fito, suka yiwa Momy sallama suka wuce part d'in Kaka Ma'u. Suna shiga ta wuce d'akin Kaka ta fad'a gadonta, Kaka tace "ki min a hankali karki karya min gado fa, dan mijinki ba iya biya zaiyi ba" Basma ta b'ata rai tace "ni ance miki ina da miji ne?" dariya Kaka tayi ta zauna gefen gadon, ta jawota ta d'aura kanta bisa cinyarta tace "Basma naji duk abinda ya faru, tun farko da sunji shawarata da basu had'a auren nan ba tunda baki so, yanzu gaya min kina so ki koma d'akin mijinki ko a raba auren?" Hawaye ne ya gangaro mata a ido a ranta tace "wanda nake so ma yace bai sanni ba, to meye amfanin raba aure" Kaka ta katseta tace "Ki bani amsa kinyi shuru kina kuka, babu fa mai miki dole akan zamanki dashi, wannan tsakani na dake ne" Basma ta nisa tare da share hawayenta tace "Kaka ni dama na fad'a abinda ke faruwa ne tsakanina da Yaya Shureym saboda kowa yasan rayuwar da nake a gidansa, bawai dan a raba auren mu ba, kuma kaka Yaya Shureym sharri zina yamin shiyasa nima na fasa komai, dan haka zaman aurena yana hannunku sai abinda kuka ce" Tana gama fad'an haka ta rushe da kuka, ta d'auke kanta akan cinyar Kaka, ta mirgina ta gyara kwanciya tana shasshekan kuka, Kaka tayi murmushi tace 'Ni kam Basma banga abin kuka anan ba, sannan ina baki shawara kiyi Addu'a da niman zab'in Allah akan zamanki da Shureym". Basma bata tanka mata ba ta ta share hawayenta tace a ranta "ai kullun cikin Addu'a nake, mafita kawai Allah zai fidda min" Da tunani barkatai barci ya d'auketa. *Washe gari* Basma na dinning tana karyawa sai ga sallaman Yaya Shureym ya shigo, d'aure fuska tayi ko kallon inda yake bata yi ba, harya k'araso kusa da ita ya ja kujera ya zauna yana kallonta kamar sabon maye, sai had'iye yawu yake, Basma ta k'ara mishi kyau ta d'anyi k'iba kamar ba Basmanshi ba, cikin sanyin murya yace "Basma ina kwana kin dawo lafiya?" d'ago kai tayi ta kalleshi kana ta cigaba da cin abincin ta, bata furta masa komai ba, cije leb'ensa yayi yace "Basma dan Allah ki yafemin da duk abinda na miki, dan Allah ki k'ara bani dama domin na gyara kuskuren dana aikata miki, Basma wlh ina son ki karki yarda a raba auren mu plss my baby love" Hararenshi tayi ta mik'e tare ja jan tsaki ta bar wurin, cikin zafin nama yabi bayanta ya kama mata hannu, cikin b'acin rai ta juyo ta wanke shi da mari tace cikin fad'a "karka kuskura k'azamin hannunka ya kuma tab'a fatar jikina, na tsaneka Yaya Shureym bana son ganinka" tana gama fad'an haka tayi gaba abinta tana juya duk sassan jikinta. Duk wannan abin ya faru akan idon Kaka Ma'u, yayi k'okarin bin bayanta, Kaka ta dakatar dashi tace "kai Shureym bani son shirme, kasan dai Basma ba zata saurareka ba yanzu, dan haka ka bari ta huce in dai kana so ta koma gidanka" Zuwa yayi ya durk'usa gaban Kaka yace yana hawaye "Hajiya dan Allah ki taimaka min kisa baki Basma ta koma d'akinta, nayi alkhawari zan gyara kuskurena" Kaka ta dafa kansa tace "kaje zanyi k'ok'ari akai, sannan kayi Addu'a sosai akan in komawarta alkhairi ne Allah ya tabbatar, in kuma akasin hakane to ya zab'a muku mafi alkhairi" haka Shureym ya fita zuciyansa na masa zugi da radad'i akan Basma. Basma, Meena, Leema, Deeja suna zaune a d'akin Deeja gaba d'aya hira suke yi na yaushe rabo, Meena tace "Basma baki bamu labarin ina kika je ba" Basma tayi dariya ta soma basu labarin zuwanta k'asar Etopia da kuma zuwanta Makka, harta k'are basu labarin, Leema tace "lallai kinyi k'ok'ari, da fatan dai kinyi Addu'a Allah ya raba auren ki da Shureym a makka, dan wlh bana fatan ki cigaba da zaman aure dashi" Deeja tace "in kuma shine alkhairin fa?" Meena ta harareta tace "haba Deeja kamar baki taya Yayanki Aryan kishi, kinsan dai shine muradin Basma" Basma ta ya mutse fuska yace "waye kuma Aryan?" a razane duk suka juyo suna kallonta, ta cigaba da cewa, "aini ba Aryan a duniyata yanzu, dan ban sanshi bama" Leema ta kwashe da dariya tace "wlh karya kike yi Malama, ga sonsa ina gani a cikin kwayar idonki kina wani zancen baki sanshi ba" Deeja murmushi tayi tace "Antyna me Yayana ya mikine haka?" Hararansu tayi tace "ban sani ba, kawai dai ban gane wanda kuke magana ba" murmushi suka yi Deeja tace a ranta "yanzu haka akwai abinda ya mata, toma ina suka had'u da har za suyi fad'a? lallai dai akwai wani abu a k'asa" nan suka cigaba da hira Basma dai ita kad'ai tasan ya take ji a ranta game da Yaya Aryan, har yau sonsa bai ragu ba a zuciyarta, k'aruwa ma yake yi, tana azabtar da zuciyarta a kan dole sai ta daina tunanin shi, amma ta gaza yin haka. *Baya kwana Biyar* Yau kwana Biyar kenan da dawowar Basma, gida ya cika da 'Yan Uwa ana hidimar sunan Meena, yarinya taci sunan Fatima sunan Ammi, suna kiranta da Najwah. Da yamma aka shirya waliman suna, family an hallara gaba d'aya a cikin gidan daga can baya, an sanya tempol da fararen kujeru ga kuma table a tsakiya, an yiwa wurin decoration, iyaye Mata da yaransu Maza da Mata sun hallara a wurin, iyayensu maza ne basa wurin, hatta Umma tazo da Yaya Aryan. Sunsha kwalliya sai k'amshin turaren ke tashi, Basma tasha kwalliya riga da siket ta sanya na leshi pink color mai fulawa fari da bak'i, d'inkin ya amshi jikinta, bata sanya gyale ba, tasha d'auri tamkar gwagwaro, sai k'amshi ke tashi a jikinta, ta sanya takalmi mai tsini masu igiya, taku take d'as-d'as kamar wata hawainiya, haka ta isa gurin ta rik'a bin ko wani b'angare tana gaidasu, mai jawabi ya soma jawabi nan fa aka soma ciye-ciye ga sauti na tashi, Basma ce ta fara bud'e wurin da rawa cike da salo dan birge masu kallo, duk wannan abinda take yi bata san Aryan da gun ba. Shureym ya tashi ya fara mata mannin kud'i nan fa wuri ya kaure da ihu, ganin Shureym a bayanta yana rawa sai ta juyo ta galla masa harara tayi tsaki ta fice daga wurin rawan, can baya taje ta samu wuri ta zauna tana maida numfashi, wayarta ta ciro ta shiga bugawa kanta salfee, d'ago kan da zata yi ta waiga gefenta, sai karaf suka yi ido hud'u da Yaya Aryan... *Rahma Ce* [8/11, 6:18 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *28.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Murtuke fuska tayi ta galla masa harara sai ta kauda kai, Yaya Aryan yayi murmushi ya kura mata ido, gaba d'aya ji tayi ta takura a gurin, mik'ewa tayi zata bar wurin, garin sauri takalminta ya turgud'e saura kiris ta fad'i, da sauri Yaya Aryan yace "subhanallah" juyowa tayi idonta ya ciko da kwalla ta kalle shi tana ya mutse fuska alama taji zafi, murmushi ya sakar mata, murguda masa baki tayi ta wuce, wannan karan murmushin da yayi har fararan hak'oransa saida suka bayyana. Anyi taro an washe lafiya kowa yaje gida lafiya. Basma tana zaune a d'akin Momy suna hira da Momy, sai ga Yaya Shureym ya shigo, ya risina ya gaida Momy kana ya zauna, Momy ta mik'e ta basu guri, shuru suka yi na mintuna, Yaya Shureym yace "Basma dan Allah ya kamata ki tausaya min, ina son ki son da bana yiwa kai na, ki yafe min my Basma" fuskarta tamau tace "ina Anty Safeena?" tambayan yazo mishi a bazata, har yakan manta da yana da Safeena, cikin sanyin jiki ya bata labarin barinta gidan da komai da ya faru, murmushi tayi ta mik'e ta isa gabansa tace "ga wayata samin number ta" jiki na rawa ya amsa ya sanya mata sai ya mik'a mata wayan, komawa tayi ta zauna, ta shiga kiran number, bugu d'aya ta d'auka, suka gaisa, Basma tace "nasan baki gane ni ba, Basma ce, na dawo kwana Biyar kenan daya wuce, ina so gobe in Allah ya kaimu ki biyo jirgi kizo Abuja" Cikin farin cikin da borin kunya tace "laaa Basma kin dawo, Alhamdulillahi, sai dai ba kud'i a wurina har yau Shureym bai zo yaga babynmu ba" ta k'arasa maganar cikin damuwa, Basma ta nisa tace "ki turomin number account d'inki zan miki transfer, sai ki siya abin da kike buk'ata kishirya a nutse, ko zuwa jibi sai ki zo" cikin farin ciki Safeena tace "nagode Basma Allah ya saka da alkhairi, dan Allah ki yafemin duk abinda na miki, ni kunyarki ma nake ji" Basma tayi murmushi tace "karki damu komai ya wuce ai" nan suka yi sallama Safeena jikinta yayi sanyi. Shureym duk yana sauraren maganar da suka yi, bayan ta aje wayar ya d'ago cikin fuskan tausayi yace "Basma dan Allah ki saurare ni, ki tausaya min plss" d'aura kafa tayi d'aya kan d'aya tace "wai na ce kamin wani laifi ne? aure ne dai nace ba nayi, ka fita sabgata pls" Tana gama fad'an haka ta mik'e, da sauri ya mik'e ya isa gabanta ya tsaya, kallonshi tashi sama da k'asa ta kauda kai, hawaye ne ya cika idonsa ya soma kwaranya a kuncinta, zuciyarta ne ya karaya cikin sanyin murya tace "Yaya Shureym ni banga abin damuwa anan ba, tun farko kace baka sona Safeena kake so, shiyasa na sanya tazo ka d'auki matarka kutafi, Yaya Shureym jiki na fa kake so ba Ni ba, dan haka nayi Alwashin baza ka samu yanda kake so ba" tana kaiwa nan ta wuce ta bashi guri. Zama yayi dirshen a kan tiles, kansa ya kama yana fidda hawaye sosai, Momy ce ta fito ta k'asaro wurinshi ta zauna tace "Shureym kayi hak'uri in har komawar Basma d'akinka Alkhairi ne zata koma, ka barwa Allah komai" da sanyin jiki ya yiwa Momy godiya ya mik'e jiki ba kwari ya tafi. *Bayan kwana biyu* Safeena ta zo, ta sauka a gidan amma ta rasa wurin wa zata, saboda tasan babu wanda zai amsheta, kiran Basma ta yi a waya ta sanar mata da zuwanta, bayan minti biyar Basma ta fito cike da fara'a ta amsheta, part d'in Momy ta wuce da ita ta sauketa a d"akinta, masu aiki tasa suka kawo mata abinci da kayan motsa baki, zama tayi suka k'ara gaisawa, Basma ta d'auki babyn tayi kama da Yaya Shureym, Yarinyan ta kwantawa Basma a rai taji dama nata ne, hira suka yi sosai Safeena ta nima gafararta da ta yafe mata akan abinda ya faru, Basma ta yafe mata. Wanka Safeena tayi ta sauya kaya, Basma ta sanyata tayi kwalliya tayi kyau sosai, fitowa suka yi ta kaita d'akin Momy suka gaisa, suka je d'akin Ammi nan ma suka gaisa ba yabo ba fallasa, duk suka gaisa da mutanan gidan, daga k'arshe ta kaita d'akin da Shureym yake ta fito ta basu wuri. Safeena tana ganin Shureym, sai farin cikin ya rufeta, duk haushin data d'auka dashi nan take ta huce, Shureym ya amshi babynsu yana kallonta cike da soyayya, anan suka zauna suka sha hira, shi kanshi Shureym yayi missing Safeena, nan suka sha soyayya kamar sabbin ma'aurata, Shureym yace "Safeena ki taya ni rok'on Basma akan ta koma d'akinta" murmushi tayi tace "ba ruwana kunfi kusa, yanda Basma ta sauko ta nuna min babu komai ta yafemin, karka zo ka had'ani da ita ba ruwana" jikinsa ne ya kuma yin sanyi. *Washe gari* Abba ya dawo, gida ya cika da farin ciki, Basma na mak'ale da Abba shi kuma sai ririta ta yake yi, bayan komai ya lafa Abba yayi kiran Family Meeting a washe gari, sannan kuma da murnan taron dawowar Basma, cikin k'ank'anin lokaci aka shiga shirye-shirye. Washe gari musamman aka kira mai kunshi ta zane duk matan gidan, Basma tasha kunshi tayi kyau, musamman suka kira masu makeup suka zo gida suka yiwa Matan gidan hatta iyayensu, tun k'arfe d'aya gida ya gama cika da Family, kowa nata hada-hada, masu abinci musamman aka kira su daga hotel suka kawo abinci kala-kala, duk cinka sai dai ka hak'ura ka barshi. Da k'arfe biyu, Abba suna tare da Dady, Mai Martaba, da kuma iyayensu Mata da Kaka Ma'u, sai Yaya Ahmad da Yaya Adam, sai Yaya Naufal da Yaya Jamal, Yaya Shureym shima yana gun, Basma ce kad'ai sai Anty Husnah. Aka bud'e taro da Addu'a, Dady yayi Bisimillah yace "Yau dai gamu dukanmu mun had'u, ga kuma Shureym da Basma, zamu tattauna akan zancen aurensu, yanzu mu iyaye me muka ga ya dace akan wannan lamarin, meye shawaranmu akai?" Ummi ce ta fara magana Mahaifiyar Meena tace "Ni ina ganin ayi sulhu Basma ta koma d'akinta" ai gaban Basma dam taji ya buga amma saita dake, Shureym wani murmushi ya saki a ransa wanda har sai da ya bayyana a fuskansa, Mami ma tace "Gaskiya ne ayi hak'uri ayi sulhu Basma ta koma d'akinta" Ammi tayi tsaraf tace "Ni ban amince ba" Momy saboda kawaici bata furta komai ba, Maman Leema Hajiya Murja tace "ina bayanki Ammi nima ban amince ta koma ba, yanzu yayi mata haka nan gaba ya kenan?" Dady ne yace "bafa jayayya nace muyi ba, magana ta fahimta nace muyi" Mai Martaba yayi gyaran murya yace "kwarai kuwa, ni anawa ganin a tambayi Basma in ta amince ta koma d'akinta shikenan" Abba yace "gaskiya wannan itace magana, Basma in ta amince zata koma shikenan, in kuma bata amince ba Shureym ya sauwak'e mata, daga yanzu ba zan kuma titasta mata ba" Dady yace "Hajiya Kaka baki ce komai ba?" murmushi tayi tace "ina jinku 'ya'yan nan, in naji ba dai-dai ba zanyi magana, yanzu dai a tambayi Basma in ta amince zata koma" Dady ya kai dubansa ga Basma yace "Basma kinji abin da muke magana akai shin zaki koma d'akin Mijinki Shureym ko kuwa ya sauwak'e miki?" Ta d'auki kusan minti biyu kafin ta soma magana tace "Dady Ni banda magana sai hukuncin da kuka yanke, nasan tabbas ba zaku cutar dani ba" saita k'arasa maganar tana kuka. Shuru ne ya d'auki falon na tsayin minti biyu, Yaya Ahmad yace "Basma karki cuci kanki fa, ki fad'i abin da ranki ke so" Yaya Naufal yace "kai ma kasan zab'inta ai, ba so take ta koma ba, kuma muma bama so ta koma wallahi" Anty Husnah itama tace "kwarai kuwa nima ban goyi baya ta koma ba, kawai ya maida mana Yarinya sai kace baiwarsa" Yaya Adam ne yace "muyi hak'uri, Shureym dai yayi kuskure mu taru mu yafe masa" Yaya Jamal yace "hakane kuskure kam an riga anyi shi, sai dai a koke gaba" Dady yace "ya isa haka, ke Basma ki fad'i abin da ranki ke so kar gaba kizo ki kuka damu" Mai Martaba yace "ina ganin mu basu sati guda su sasanta kansu, in sunk'i sasantawa, sai mu mu d'auki mataki mu kuma zama akai" Nan suka amince da wannan shawaran ta Mai Martaba, Shureym idonta ya ciko da kwalla bakinsa na rawa yace "Abba tunda Basma ta baku zab'i, dan Allah ku bani Matata, wlh ina sonta kuma na gane kuskure na" Dady yayi murmushin su na manya yace "shureym kenan, kaje ka sasanta da Matarka kawai, in kun dai-daita shikenan, saika d'auketa Ku tafi". Basma ce ta gyara zamanta cikin sanyin murya tace "Dady ina son inyi magana" Dady yace "an baki dama" tace "Dama akan zancen Safeena ce matar Yaya Shureym, dan Allah kuyi hak'uri ku karb'eta a matsayin sirikarku, kuskure sun riga sunyi, ku yafe musu itama ta shigo cikin dangi, kunga yanzu sun fara tara zuri'a, bamu san iya adadin zuri'an dake tsakanin su ba, kuskure dai sunyi dan Allah Ku yafe musu, yanzu na kirata tazo dan ku gana da ita" Shureym wani soyayyar Basma yaji yana fusganshi, farin cikin ya lullub'eshi, Dady ya nisa yace "da kyau d'iyar albarka, kinyi tunani mai kyau, kai Shureym kira mana ita tazo nan" nan take Shureym ya kira Safeena, cikin minti goma sai gata ta shiga falon kanta a sun kuye, zama tayi gefen Basma, ta gaishe su, nan suka cigaba da tattaunawa, daga bisani Safeena da Yaya Shureym suka nima gafaransu, nan take suka yafe musu. Suka d'add'auki yarinyar data haifa suka sanya mata albarka, sai a sannan Mami ta nima gafarar Basma akan irin abinda tayi mata, Basma ta yafe mata, nan taro ya watse cike da farin ciki, Mazan suka tafi masallaci dan yin sallan La'asar, matan ma suka wuce b'angarensu dan gabatar da nasu Sallah. k'arfe Hud'u kuma su zauna wurin liyafan waliman dawowar Basma, wanda Abba ya shirya mata. *Rahma Ce* [8/12, 7:11 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *29.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Wuri ya k'awatu sosai, b'angaren iyaye Maza daban tare da abokan Abba, sai iyaye Mata b'angare su daban tare da k'awayensu, yara Maza da Mata suma duk b'angarensu daban, sunata ciye-ciyen kayan kwalan da mak'ulashe, mota ce ta shigo gidan duk hankalinsu ya koma wurin ganin ko su waye a motan, Aryan ne ya fito ya doshi b'angare su Abba, risinawa yayi ya gaishesu, Dady dai yanata kallonsa, Aryan yace "Amm Abba dama jiya naje Gombe na d'auko Kakanni na iyayen Umman mu, to shine suka ce na kawo su ku gaisa tare da tayaku murnan dawowar Basma" Cike da farin ciki Mai Martaba yace "Masha Allah, jeka tawo dasu, sannunsu da zuwa" Abba yace "Umman ku fa?" yace "tana tare dasu a cikin mota" "madallah su k'araso ciki". Aryan ya wuce wurin Motan ya bud'e musu, Malam Baffa ne ya soma fitowa sai Inna, dama suke mazaunin baya, sai kuma Umma ta fito daga mazaunin gaba, Suka jero, Yaya Aryan yana gabansu, Dady ya zabura ya mik'e a rud'e, saboda ganin abinda baiyi tsammani ba a rayuwansa, barin kujeransa ne yayi ya fara tafiya ba tare da ya sani ba, su Abba suka bishi da kallo da kuma kalon inda yake kallo, Dady ya dafe kansa da hannu biyu yana ambaton Allah, wani k'ara ya saki sai ya yanke jiki ya fad'i, cike da tashin hankali su Abba da yaran suka rufa a kanshi. Meena ce ta fara kuka tana fad'in Dady, Dady, Dady, su Umma sun kasa k'arasowa saboda abin ya tayar musu da hankali sam basu gane shi ba. Cikin sauri suka d'auke shi sai a sibiti, zan iya cewa dukan mutanan wannan taro suka dunguwa zuwa asibiti, emergency aka shiga dashi, likitoci uku suka rufa a kansa, cikin wani na'ura suka sanya shi suna ta aikin bincike, Abba ya musu bayani yanda abin ya faru, sun fahimci matsalan daga kanshi ne, sai da suka d'auki awa guda a kansa suna aiki. Daga wajen emergency d'in cike yake da Family d'insu, su Abba sai kaiwa da komawa suke yi, su Leema dasu Basma sai kuka suke, Ummi ma ta kasa dauriya kuka take kashirb'an, su Momy na lallashinta, Abba ne ya juyo yace "yanzu fa Ibrahim Addu'a yake buk'ata ba kuka ba, dan Allah kuyi shuru muji da guda d'aya". Likitoci sun fito daga d'akin, su Abba da Mai Martaba, sai Alhaji Gana Abokin Abba suka tare su, Doctor Jabir ne yace "Yallab'ai muje office, nayi muku bayani" haka suka bi bayansu. Duk suka samu guri suka zauna, Dr Jabir ya kalle su yace "Yallab'ai bincikenmu ya nuna cewa Gomna Ibrahim ya tab'a samun loosing memory, to yanzu akwai abinda ya gani da yasa ya dawo dashi hankalinsa, munyi masa allurai da gwaje-gwaje wanda in ya farka zai dawo hayyacinsa gaba d'aya, kuma rayuwan da yake ciki yanzu ba zai manta ba, zai cigaba da rayuwansa kamar yanda ya saba, wancen tunanin daya rasa shine ya dawo kwakwalwansa" Abba yace "Alhamdulillahi, yanzu zai kai k'arfe nawa kafin ya tashi?" Dr Jabir yayi murmushi yace "zai d'auki lokaci kan ya farka, amma ba matsala bane" "to Masha Allah, Allah ya bashi lafiya" duk suka amsa da "Ameen" Dr Jabir yace "yanzu nasa an canza masa d'aki na summan, kuma za'a iya shiga a duba shi amma dan Allah banda hayaniya, domin bama so a tashe shi, mun fi so ya tashi da kanshi" Mai Martaba yace "bakomai insha Allah za'a kiyaye" nan suka yiwa Doctor godiya suka fito. Da sauri su Yaya Ahmad dasu Ammi suka tare su Abba, dan jin me yake damun Dady, cikin natsuwa Abba yace "Alhamdulillahi ya farfad'o sai dai ya samu barci, da zaran ya farka komai zai yi dai-dai, sai dai likita yayi gargad'i banda hayaniya, Hajiya Fatima ku shiga a nutse ku duba shi, Yaranma duk ku shiga, sai ku fito su Ahmad su maidaku gida" Ammi tace "to shikenan, Allah ya bashi lafiya" duk suka amsa da "Ameen". Haka suka shiga d'akin a nutsu bayan sun gama duba shi suka fito, su Yaya Ahmad suka wuce da matan zuka gida, su Umma ma dasu Baffa Yaya Aryan ya maidasu gida ya dawo. Nan aka k'ara security a asibitin, su Yaya Ahmad suna zaune a wajen d'akin, su Abba kuma suna zaune a ciki, sai Addu'a suke tofa masa. A nan suka yi Sallan Magrib da isha'i, har zuwa lokacin Dady bai farka ba, damuwa ne ya soma ziyartan su kusan awa hud'u har lokacin bai farka ba, Abba ya kuma yiwa Doctor complaining, Dr Jabir ya k'ara basu hak'uri, ya tabbatar musu da zai farka karsu damu. Har misalin sha biyun dare Dady bai farka ba, su Yaya Ahmad, Yaya Naufal, Yaya Shureym, Yaya Adam, Yaya Aryan, Abba, Mai Martaba duk a asibiti suka kwana, Alhaji Gana ya wuce gida shi da sauran Abokan Abba. A can gida kuma Matan hankalinsu a tashe suka kwana. *Washe gari* Da misalin k'arfe goma na safe Dr Jabir ya shigo duba Dady, duk su Abba suna gefe a zaune, Dr Jabir ya duba drip d'in dake mak'ale a hannun Dady, a hankali Dady ya sauke ajiyan zuciya, ya soma bud'e ido tamkar wanda ke tsoron haske harya bud'e duka, Addu'a ya shiga karantawa, murmushi Dr Jabir yayi, Dady ya mayar masa da murmushi yace "Baffana" dan fuskan Baffa ke masa gizo a idonsa, da sauri Abba ya mik'e ya isa baki gadon ya kama hannun Dady yace "Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Mai Martaba Ibrahim ya farka" Cikin muryan mara lafiya Dady yace "Ina Baffana suke? ko basu na gani ba d'azun" cikin rashin fahimta Abba yace "suwa kake magana akai?" murmushi Dady yayi ya kalle Mai Martaba yace "ku kira min Aryan domin ya kawo min Innata da Baffana, da kuma k'anwata Aishatu, kuce masa su tawo tare da d'an Uwana Aliyu" cike da mamaki Mai Martaba ya kalli Abba yace "inna fahimci Ibrahim yana magana akan bak'in da Aryan ya shigo dasu ne jiya, Allahu Akbar Allah Mai iko, kaji wani abin Al'ajabi, ban tab'a tunanin Ibrahim zai dawo hayyacinsa ba, kusan shekaru sama da talatin kenan" Abba murna da farin ciki ya hanashi magana, hamdala da tasbihi yake wa Allah, wayansa ya ciro ya kira Ahmad yace "Ahmad maza kaje gidansu Aryan, ka tawo dasu gaba d'ayansu ka kaisu gida, gamu nan likita zai bamu sallama zamu koma gida" Yaya Ahmad zaiyi magana yace "Ahmad yanzu ba lokacin bayani bane, maza ka tafi ka aiwatar da abinda na saka" Dr Jabir yayi dariya yace "wato yallab'ai kasan sallama zan baku" cike da farin ciki Abba yace "kwarai kuwa me zamu jira, bamu sallama da sauran magunguna su Naufal su tawo dasu, mu kaga tafiyar mu" sai ya tallabo Dady yace "D'an Uwana sauko kaga mu wuce gida, ka samu kayi wanka kaci abinci ka rama Sallolin da ake binka, sai mu zauna Family Meeting yau ka gana da iyayenka" Cikin barin ciki Dady ya sauko yana murmushi, haka suka kai shi har mota suka tafi gida,. Su Yaya Shureym suka amsa magungunan Dady, sannan suka wuce gida. Gidan ya hargitse da Murnan dawowan su Dady, direct part d'in president suka wuce a can duk suka kimtsa suka ci abinci, Dady ya rama sallolinsa Magrib, Isha'i da kuma Sallan Asubahi. Duk sun had'u a falon Abba suna zaune, sai ya jiki suke masa, Ummi sai murna miji ya farka, Meena kuwa baki har kunne dasu Basma, falo ya cika suda iyalensu suna ta hira da barkwanci cikin nishadi da farin cikin, sallaman su Yaya Aryan ne ya katse hiran nasu, Yaya Ahmad da su Umma suna biye a baya, wuri aka basu suka zauna Dady ne ya mik'e ya isa in da su Malam suka zauna, ya durkusa ya had'a hannunsa biyu, Baffa ido ya zaro ya shiga murza idonsa, lallai wannan Ibrahima Khalil ne, an ya ko dai gizo nake gani?" kallon Inna yayi ya cigaba da cewa "wai Ameena kina ganin abinda nake gani kuwa, wannan kamar Ibrahim d'in mu? kamannin fuskansu d'aya, sai dai shi mun masa sanin lokacin da yake k'arami ne" Inna tace "kwarai kuwa Malam nima abinda na gani kenan" falon yayi tsit suna kallon su, Dady yace cikin kuka "Inna, Baffa, Ibrahim d'in ku ne ku daina tantama, ina Yaya Aliyu ina Aisha k'anwata?" Ai gaba d'aya falon sai tsoro ya shigesu, Kaka Ma'u ta taso ta dafa kafad'an Dady ta kalli Abba tace "Muktar ko dai fad'uwan da Ibrahim yayi ya samu matsala a kansa ne?" Murmushi Abba yace "lafiyansa kalau, Allah ya dawo masa da hankalinsa ne, kuma wa'innan Kakannin su Aryan ne kuma sune iyayensa, ganin su da yayi jiya ne ya haifar masa da fad'uwa har yayi dogon suma, hakan ne yayi sanadin dawowan tunaninsa na tun lokacin da yana k'arami da Alhajinmu ya bigeshi ya rasa tunaninshi" Gaba d'aya falon sun girgiza da zancen Abba, amma banda Abba da Mai Martaba sai Hajiya Kaka, sune kad'ai suka San wannan abin, saura duk sun d'auki Dady d'an uwansu ne na jini. Falon ya cika da kabbara tare da yiwa Allah tasbihi, Malam da inna kuka suka sanya, Umma ma haka su Ammi ne suka taso suka shiga basu baki, Aryan mamaki ya cika shi ya shiga zancen zuci "dama ashe Dady Babansu Meena shine Yayan Umma wanda ya b'ata tun yana k'arami, tasha gaya musu, wani lokacin har kuka take yi suna lallashinta" Khadija ce ta taso ta fad'a jikin Dady ta shiga kuka sosai cikin kuka tace "Dady dama kai Abbanmu ne bamu sani ba, Abbanmu ya rasu shekaru kusan bakwai da suka wuce" K'ank'ameta yayi a jikinsa yace "Innalillahi wa inna ilaihur rajiun, Baffa wannan 'ya'yan Aliyu ne ashe? Yaya Aliyu ya rasu? ina Matarsa take?" Malam ya share hawayensa ya nuna masa Umma yace "had'in zumunci muka yi musu da k'anwarka Aisha, wancen Yaro Aryan shine babban d'ansu sai Khadija ga tanan itace k'arama, Aliyu ya rasu da kewarka sosai, wani lokacin da girmansa ma kuka yake yi yana jimamin rashin ka, kullun zancenmu ko ka mutu ko kana raye, bamu tab'a tsammanin zamu sake had'uwa da kai ba" Sai ya k'arasa maganan yana fidda kwalla, da sauri Dady ya janye Deeja daga jikinsa ya isa wurin Umma, kama hannunta yayi ya kaita tsakiyan falon yace "kunga k'anwata Uwa d'aya Uba d'aya muke, na tafi na barsu tsawon shekaru, yanzu gashi Allah ya had'amu, abin mamaki da ikon Allah ashe itace Mahaifiyarsu Aryan, bamu tab'a had'uwa ba" ya waigo ya kalleta yace "Aisha kece haka? ashe Yaya Aliyu ya rasu" kuka Umma ta sanya, saboda nan take zafin mutuwan Mijinta ya taso mata, Dady ya maidata mazau ninta. Abba ne ya mik'e ya kama hannun Dady yace "ba ka rasa Aliyu ba tunda gani a tare da kai, zo ka zauna ka kwantar da hankalinka, wannan kukan da kuke ya isa haka, Farin ciki ya kamata muyi da godewa Allah bisa wannan Al'amari" Dady baima Abba musu ba ya bishi suka zauna, falon yayi shuru sai sasshekan kukan Deeja ke tashi da Umma, su Basma ma kukan suke dan jin wannan bak'on Al'amari, Su Yaya Ahmad tsoron Allah ya hanasu magana, Yaya Aryan kuwa sai ajiyan zuciya yake yi, idununsa sunyi jaaa hawaye yana bin kunshinsa. *Rahma Ce* [8/12, 7:12 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑 _page_ *30.* _Na_ _*Rahma Kabir*_✍🏾 Mai Martaba yayi sallama, duk suka amsa, ya cigaba da cewa "Godiya ya tabba ga Allah ubangijin talik'ai, mai kowa mai komai, wanda ya halicci sammai da k'assa', yayi mu maban banta jinsi, mungode wa Allah ya da yayomu a cikin Musulunci, wannan Al'amari da ya faru babu abinda za muyi sai yiwa Allah Godiya, a yau Allah ya sada Alhaji Ibrahim da Iyayensa" Abba ya amsa da kwarai kuwa, Ummana yau ina so ki bada labarin yanda a kayi kuka tsinci Ibrahim keda Abbana lokacin ina k'asar waje karatu" Kaka Ma'u ta share kwallan daya zubo mata, nan ta shiga basu labarin faruwar lamarin tun daga farko har k'arshe, kukan su Meena ne ya k'aru a falon, Malam ya nisa yace "lokacin da Ameena ta aiki Khalil kasuwa, har yamma bai dawo ba" daganan ya cigaba da basu labarin yaruwansu gaba d'aya bayan ba Khalil, Umma ta d'aura itama da irin rayuwar da suka yi da Abban su Aryan, har zuwa had'uwar su da Basma da irin taimakon da tayi musu, har Auren su Deeja da Ahma, babu abinda ta rage hatta soyayyan Basma da Aryan ta bada labari, tana gama labarin ta cigaba da kuka. Falon ne yayi shuru na tsayin minti, Umma ta taso wa Basma da mikin rabuwa da Aryan, ta mik'e ta isa wurin Umma ta d'aura kanta misa cinyarta, ta cigaba kuka mai kashe zuciya. Abba yace "Alhamdulillah, Basma kece silan komai, sanadin ki gashi dangi mun had'u, Allah ya muku Albarka gaba d'aya" duk suka amsa da "Amin". Abba ya gabatar da duk Familynsa masu Malam Faffa, sai suka sanyawa zuri'a Albarka. nan dai suka cigaba da hira, yara suka fita zuwa farfajiyar gidan, suka baje kolinsu a acan, Aryan dai yana tare da Ahmad suna hira, su kuma su Yaya Naufal b'angaren hiransu daban dasu Yaya Shureym, matan kuma duk suna tare, harda Safeena yanzu ta zama 'yar gida. *Da Yamma* Mai Martaba da Abba, Dady da Malam duk suna hira gaba d'aya, Mai Martaba ya kalli Abba yace "Alhaji Muktar nifa naga iri ina so in za'a bani" Abba ya kalle shi cikin rashin fahimta yace "ban fahimce ka ba" Mai Martaba yayi murmushi yace "K'anuwar Ibrahim nake bara ko zaku bani aurenta" cike da farin ciki Dady ya kalli Abba yace "kasan me yake nufi kuwa? Aishatu Mahaifiyar su Aryan yake maga fa" Abba yace "Alhamdulillahi, abu yayi kyau, ai ga malam nan a kusa sai muyi magana" cikin kawaici na Manya Malam yace "wannan ai maganarku ne, Aishatu k'anwarku ce ku zaku yanke hukunci, ni nawa sai dai nasa Albarka" farin ciki ne ya rufe su dajin kalaman Malam, nan suka yanke hukunci hatta sadaki suka yanke, suka sanya rana mako mai zuwa in an sakko Sallan Juma'a a masallaci, Abba yace Zuwa gobe in Allah ya kaimu, sai mu kirata mu tattauna da ita dan ta sani, nasan ba zata k'i amimcewa ba". *Washe gari* Haka duk suka had'u suka ci abincin safe, da yake su Umma sun kwana gidan president, bayan sun kammala, Abba ya kira Umma yana so suyi magana, ba musu Umma tabi yansa, suka zauna a falonsa na sama, Umma na k'asa gefe, Abba na zaune bisa kujera, Dady ne ya shigo shima ya zauna, ta kuma gaishesu, Abba ya nisa yace "wata magana ce zan sanar miki ban sani ba ko zai miki dad'i, mun yanke shawara ba tare da saninki ba, Mai Martaba yazo mana da wata magana akan yana son ya aureki" Da sauri Umma ta d'ago kai tare da dafe kirjinta tace "Ni kuma?" Dady yayi dariya yace "meye abin firgita, ke d'in fa, kuma mun amince har ya bada sadaki, mun yanke Juma'a mai zuwa zamu d'aura auren ku bayan an sakko Sallan Juma'a" sun kuyar da kai tayi cike da jimami dajin kunya tace "shikenan Allah ya tabbatar mana da Alkhairinsa" Abba da Dady suka had'a ido tare da sakar ma juna murmushi suka ce "Ameen" Abba yace "tunda kin amince, mungode Allah ya miki Albarka, zaki iya tafiya" mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta musu godiya ta fito. Da misalin k'arfe biyu na rana, Dady suka shirya tafiya, yace lallai dasu Malam zai tafi, haka suka shirya hard'asu Umma dasu Aryan, duk suka tafi Kaduna, Deeja banda ita da Meena saboda suna jego, harda kuka lokacin da zasu tafi suka yi, Leema tabi Mijinta Yaya Jamal, Kaka Ma'u ma ta bisu don ta samu K'awa Inna, tace ba zata zauna Abauja ba. Mai martaba ma ya tafi da iyalinsa, domin yin shirye-shiryen bikinsu da Umma, Yaya Shureym ma ya tafi da Safeena Kano. Gidan kowa ya watse, sai su Ammi da Yaransu. Washe gari Abba ya wuce Germany domin halarta wani taro a k'asar. Basma ta koma part d'in Ammi, hankalin kowa yanzu a kwance yake, Yaya Ahmad ya cigaba da zuwa aikinsa, Yaya Naufal ma haka, Meena kuwa anata jego. *Da dare* Yaya Ahmad yana zaune da Basma suna cin abinci a plet d'aya, ya kalleta yace "Basma wannan irin santi da haka, ashe Deejana ta iya girki sosai?" Murmushi tayi tace "wallahi Yaya Ahmad ta iya sosai, kuma kasan haka Umma ta iya girki fa, fried rice d'in nan yamin dad'i, yau zan cika cikina sosai" "ki dai ci a hankali kar kici ki kasa tashi da yin numfashi, kin san ance ana so a kasa ciki kashi uku ne, kashi na farko na abinci, kashi na biyu na ruwa, kashi na uku kuma na numfashi" murmushi tayi tace "hakane kuwa Yaya Ahmad, nima wasa nake maka dana ce haka" nan suka cigaba da cin abincin har suka kammala. Yaya Ahmad yace "Queen Basma" da sauri ta d'ago ta kalleshi tana murmushi tace "ya a kayi ne Yayana" yace "kawai naji kiran sunanki ne, ina so ki gayamin yaushe zaki koma gidan Shureym" a razane ta mik'e tace "komawa gidan ya Shureym kuma?" yace "yes, mako guda aka baku, ku sasanta kanku, kuma week d'in ya kusa k'arewa, ina tunanin kun gama sasantawa ai" Hawaye ne ya sauka a kuncinta, ta koma ta zauna bakin gadonta tace "Yayana wallahi bana son zama dashi, amma in har abinda iyayenmu suke so kenan, zan koma in dai ransu zai yi musu dad'i" Yaya Ahmad ya nisa yace "zanyi wani abu akai" da sauri ta d'ago kai tana girgiza kai tace "a'a Yaya Ahmad kar kayi komai akai, haka Allah ya tsaramin rayuwata, kuma ni yanzu bana son Yaya Aryan ma" sai ta k'arasa maganar tana kuka. Murmushi yayi yace "me Aryan ya miki da har zaki daina Sonsa lokaci d'aya?" Cikin kuka ta bashi labarin abinda yayi mata, dariya Yaya Ahmad yayi sosai yace "Basma har yanzu ke Yarinya ce" b'ata fuska tayi tace "Dariya ma kake min ko?" ta k'arasa maganar cike da shagwab'a, toshe bakinsa yayi yace "nayi shuru, na daina dariyan yi hak'uri yar k'anwata, kinga bari naje na kwanta dare yayi, da safe kisa masu aiki su kawo mana tire d'in abincin nan" "to Yaya Ahmad Allah ya bamu alkhairi" ya amsa da "Ameen" ya wuce. *Ranar Juma'a* An d'aura auren Sarki Abdallah da Aisha (Umma) bisa sadaki dubu Hamsin, sun dawo gida, an yi walima da ciye-ciye, kowa ka ganshi yana cikin farin ciki, Hajiya Sa'a tak'i zuwa saboda bak'in kishi, Hajiya Murja kuwa da ita aka zo Abuja dan shagalin Biki, gidan Umma cike yake da 'yan Uwansu na Gombe, ko da suka ji labarin ganin Dady sunyi murna sosai. *Washe gari* Yaya Ahmad ya samu Mai Martaba a side d'in da President ya ware masa, ya zauna ya gaishe yace "Baffa nazo wurin ka ne muyi wata magana" Mai Martaba ya gyara zama yace "ina jinka Ahmad" Yaya Ahmad ya risina kansa k'asa yace "Abba akan batun auren Basma da Shureym ne, a gaskiya Abba Basma bata son zama da Shureym saboda tana da wanda take so, tun farko Abba ya matsa mata akan sai ta auri Shureym, to ni ina niman Alfarma dan Allah Baffa kayi wani Abu a kai, domin itama ta samu farin ciki a rayuwarta kamar yanda kowa yake rayuwan farin ciki, nasan Basma ba zata tab'a cewa a raba auren nan ba, saboda yin biyayya a gareku, amma kuma Baffa wallahi tana cikin damuwa" ya k'arasa maganan cikin fuskan tausayi. Mai Martaba ya jinjina lamarin yace "ai dama munce suje su sasanta kansu, gashi mako gudan ya cika, kaje karka damu zanyi wani abu akai" Yaya Ahmad ya risina yayi masa godiya kana ya fita. A ranar aka wuce da Umma kano gidan Mai Martaba Sarki, gaba d'aya Matan gidan suka tafi Kano, Mazan ne kawai suka bari, Dady ya koma Kaduna, president ya cigaba da gudanar da ayyukan sa. Umma ta samu tarba sosai wajen dangin su Ammi, anyi taro an watse mutanan Kaduna sun koma, na Abuja ma haka, Aryan dole ya dawo Abuja, Abba ya bashi wani part da zai zauna saboda gidansu ba kowa a ciki sai masu gadi, Malam da Inna suna kaduna, Umma kuma ta koma Kano. Aryan baiso dawowa gidan ba, saboda yasan Basma tana nan. *Rahma Ce* [8/12, 7:13 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *31.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* Mai Martaba ya had'a duk kan iyalinsa ya gabatar musu da Amaryansa Umma, sai kuma ya gabatar da Matar Shureym Safeena, Hajiya Sa'a k'iri-k'iri ta nuna kishi sosai akan Umma, Mai Martaba ya ja mata kunne sosai da gargad'i, dole ta shiga taitayinta dan tasan halinsa sarai. Shureym ya zauna a cikin gidansu na sarauta kusa da part d'in Yaya Adam, d'akin Safeena yana kallon d'akin Basma wanda ya dad'e a kulle bata tab'a zama a ciki ba, Shureym kullun yana sanyawa a gyara d'akin Basma tamkar tana zama a ciki tsaf yake. *Bayan sati biyu* Komai yana tafiya yanda ya kamata, Umma ta soma sabawa da zaman gidan sarauta, suna shiri sosai da Hajiya Murja, Mami ganin ba Sarki sai Allah dole ta sauko suka had'a kai suna zaman lafiya. Mai martaba yaji dad'i yanda suka had'a kai, mulki kuma yana tafiya yanda ya kamata. *Da dare* Mai Martaba ya kira Yaya Shureym domin suyi magana, Mai Martaba yace "na kira ka ne akan maganar Basma, wai shin kun dai-daita kuwa? dan yanzu ana niman wata guda kenan dana ce na baku sati d'aya" Sunkuyar da kai yayi k'asa ya soma sosa k'eya, yace cikin inda-inda "am am Baffa muna kan dai-dai tawa dan ina waya da ita" cikin nuna ko in kula Baffa yace "Kira ta yanzu a wayanka inji, ka kuma sanya min a hands free" Gaban Shureym ya buga damm, cikin tsoro yace "Baffa a k'ara bani lokaci yanda zamu samu damar fahimtar juna" wani kallo Baffa yayi masa sai da cikinsa ya kad'a, cikin d'aure fuska yace "Nace ka kira min ita" jikinsa ya d'auki rawa ya ciro wayar ya danna number ta, Kiran farko taki d'auka harya katse, acan kuwa Basma tana kallon kiransa tak'i d'auka, ya sake kira cike da Masifa ta d'aga ko sallama babu tace "Wai Yaya Shureym meye damuwanka da nine? dan Allah ka rabu dani ka fita rayuwata, baza ka tab'a samun yanda kake so ba dan kasan bana Sonka, Abu d'aya zai za na koma d'akin ka, shine in su Abba sun nuna suna son haka, dan bazan tab'a bijirewa buk'atansu ba" saita fara kuka, jikin Yaya Shureym yayi matuk'ar sanyi, bai iya furta mata komai ba ya kashe wayar. Mai martaba yayi ajiyan zuciya yace "Shureym ka b'ata rawanka da tsalle, da ka rik'eta tun farko da Amana da tuni ta manta da k'iyayyar bata son ka, dan haka yanzu ga wannan farar takardan da bairo, in har na isa da kai kuma ni d'in Uba ne a gareka to ka rubuta mata saki d'aya a ciki, idan da rabon zaku zauna kafin ta fita Idda in ta sauko sai ka maidata". A razane Shureym ya kalli Mahaifinshi cikin kid'ima yace "Dan Allah Baffa karka min haka, wallahi ina son ta, zan shiga mawuyacin halin inna rasata, plss Baffa ka tausayamin" sai ya soma zubda hawaye. Baffa ya tausaya masa amma sai ya danne damuwansa yace cikin Natsuwa "Shureym na riga na gama magana, yana da kyau itama Basma tayi rayuwar farin ciki, kamar yanda da farko kaje ka auri wanda kake so ba bada sani na ba, dan haka itama a bata dama ta auri wanda take So" Shureym yana kuka ya d'auki paper da bairo ya rubuta kamar haka "Basma na sake ki saki d'aya, ba dan bana sonki ba sai dan ki auri cikar burinki, in dai hakan zaisa ki farin ciki, ina son ki Basma Son da babu adadi, da kuma shi zan mutu a raina". Yana gama rubutawa ya mik'e ya fita daga falon yana kuka, Baffa yana kiran shi amma ina yayi gaba cike da tashin hankali. Part d'insa ya wuce, ya shiga a birkice, Safeena na ganinsa haka, ta isa inda ya zauna ta shiga tambayansa, kuka yake wiwi yana dafe da Kansa, cikin kuka yace "Baffa yasa na saki Basma saki d'aya" salati ta saki a fili, a zuciyarta kuma tad'an ji dad'i, wani b'angare kuma ba taji dad'in haka ba, lallashinsa ta shiga yi, da kyar ta samu yayi shuru. Mai Martaba ya d'aga waya ya kira Dady suka gaisa yace "Dalilin kiranka shine, Shureym ya saki Basma saki d'aya, ga takardan a gabana, dan haka ka kira Mukhtar ka gaya mishi, domin wallahi kunyansa nake ji" salati Dady ya saki yace "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu duka" nan suka yi sallama suka aje kan wayan. Dady ya sanar da Abba, Abba bai ji dad'in sakin ba, yaso a lallab'asu su shirya su cigaba da zaman su, Addu'a ya musu da fatan Alkhairi. Abba ya tara iyalensa a falonsa ya sanar musu da sakin da Shureym yayi wa Basma, nan take farin cikin ya bayyana a zuk'atan su Yaya Ahmad, Ammi da Momy ma ba suyi b'acin rai ba, face suka sanyi fatan Alkhairi akan lamarin, Basma wani hawaye ya sauka kuncinta, a ranta tana jin ba dad'i da kuma farin ciki, abin da ya sata farin ciki saboda ta rabu da Shureym kuma bai samu cikan burinsa akanta ba, na biyu kuma damuwar da ta shiga saboda Aryan ya daina sonta *a nata tunanin kenan.* Gaba d'aya dangi kowa yasan da mutuwar Auren Basma, Yaya Aryan koda yaji labari murnushi kawai yayi, a ransa yace "dama nasan zaki dawo gareni, domin insha Allah Basma tawa ce ni kad'ai". Basma ta fara Idda, koda dai Shureym bai kusanceta ba amma babu wanda yasan haka, kullun tana gida sai dalili kesa ta fita, tunda Aryan ya dawo gidan basu tab'a had'uwa ba saboda yayi duk abinda zaiyi dan kar su had'u. Yaya Shureym ya lalace yayi bak'i saboda damuwa, Iyayensa saida suka koma suna tausayinsa, hatta Mai Martaba sai da ya tausaya masa, lallashinsa suke tayi da yi masa Addua, a hankali ya soma sabawa da halin da yake ciki ya soma walwala, Safeena na iya k'ok'arinta wajen faranta masa rai, hakan yasa ya dangana ya barwa Allah, amma a ransa bai hak'ura da ita ba gani yake kamar zata kirashi su dai-daita kansu kafin kwanakin cikar iddarta. Lokacin da Iddarta ta cika, a sannan ne yasan tayi masa nisa, sai ya soma k'ok'arin cireta a rayuwansa. *BAYAN WATA UKU* Basma ta kammala Idda, ta zama free ba data nauyin kowa akanta, Yaya Ahmad shine abokin hiranta dasu Meena, kullun suna had'uwa a part d'in Momy ko Ammi su sha hiransu, wani lokacin su sanya waka Basma ta sha rawa ta tuna da rayuwarsu na da lokacin da take Queen Basma. Yau Basma ta tashi cikin nishad'i, da misalin k'arfe biyar na yamma ta isa wurin shak'awata na cikin gidansu dake can baya, ta zauna wurin furanni da bishiyoyi, system d'inta ta kunna ta fara buga Game, ga lemu mai sanyi tana sha sanyin na ratsata, iskan wurin ya gauraye da kamshin turarenta, sai yana busawa da k'amshi mai dad'i. Yaya Aryan hakanan yau yaji yana son yaje gurin shak'atawan, dan tunda yazo gidan bai tab'a zuwa ba, ya fito daga part d'inshi cikin shigan k'ananun kaya, ga suman kansa yayi luf-luf, robali yasa ya d'aure gashin ta baya saboda sumar tayi yawa bai aske ba, wani k'amshi yake fita a jikinsa mai dad'i, yayi matuk'ar kyau, a hankali yake tafiya rik'e da goran swan harya isa gurin, da farko bai lura da ita ba yazo zai zauna a wani kujera dake fuskantar na Basma nesa suke da juna, d'ago kan da zaiyi sai idonsu ya had'u dana juna, dama tun isowansa k'amshin turarensa ya ziyarci Basma, ta bishi da kalli har yazo zai zauna shine suka had'a ido, ya tsine fuska tayi ta kauda kanta ta cigaba da Game d'in ta. Aryan ya zauna yana mai yin murmushi, swan ya bud'e ya kurba ya maida murfin ya rufe, wayansa ya ciro ya fara dannawa yana yi yana satan kallonta, haka ita tunda ya zauna taji ta ta kura a wurin, tana yi ta d'ago kai, ai bata an kara ba ta d'ago kenan ya d'ago suka had'a ido, Yaya Aryan ya sakar mata murmushi, b'ata fuska tayi ta murgud'a masa baki, murmushi ya kuma yi, rufe system d'in tayi ta mik'e a zuciye zata bar wurin. Da sauri ya mik'e yace da k'arfi yanda zata jishi "My Baby Basma" cak ta tsaya ta kasa tafiya, hakan taji jikinta ya mutu, a hankali ya isa bayanta ya tsaya yace "My Lovely fushin me kike dani?" Idonta ne ya kawo kwalla amma saita dake ta juyo cike da tsiwa tace "kai kuma waye? ko zaka min bayani dan ban wayeka ba" Yaya Aryan yaji ransa ya b'aci yace a ransa "wato yarinyar nan ko me a kayi mata saita rama" a fili kuma ya dake yace "uhum na gane manufarki, kuma banga laifinki ba tunda nine na fara miki haka, amma ni a wancen lokacin akwai dalilin da yasa nayi miki haka" Kallonsa tayi ido cikin ido tace "wani irin dalili ne Yaya Aryan da zaka nuna baka sanni ba? ai ko da akwai aure a kaina kasan Sonka na raina, abinda ma ya bani haushi da mamaki shine, ka san bana k'asar nan, anata niman ina naje, dawowata kenan zuciyata ta kaini gurin, Kai ne Mutum na farko dana fara had'uwa dashi kafin in isa gida, mai makon kayi murna da gani na amma sai ka kware min, ka nuna baka sanni ba, ai ko albarka cin sanaiya ka nuna min inma ba zaka nuna mun dan soyayya ba" Ta k'are maganar hawaye na zuba mata, murmushi yayi na rashin jin dad'in abin da yayi mata, yanzu ya gane yayi kuskure, hak'uri ya shiga bata da kalamai masu dad'i, d'aga masa hannu tayi tace "ba kada kalaman da zaka gaya min har suyi tasiri a raina yanzu, kamar yanda ka daina sona nima na daina sonka" Juyawa tayi zata tafi, wayar Yaya Aryan ya shiga k'ara, yana dubawa yaga Jiddah ce, da sauri ya d'aga ya bud'e murya yanda Basma ta zaji abinda zai ce, yace "hello Jidda ya kike kwana biyu" Ai basma bayi step Biyar ba ta jiyo a fusace, da sauri ta k'ara so ta fusge wayan ta kara a kunnenta, ita kuma Jidda lokacin tace masa "My Aryan ka yadani, pls ka soni ko kad'an ne, nima na bar k'asar Monaco na dawo Abuja, ka gaya min inda zamu had'u akwai maganar da zan maka ne" Basma bata bari ta kai aya ba ta daka mata tsawa tace "kee ki kiyaye ni ki fita hanyar Mijina, wallahi in ba haka ba sai na miki abinda baki tab'a tsammani ba, Yaya Aryan nawa ne ni kad'ai, babu wata 'Ya Mace data isa ta shiga gonata" bata jira me zata ce ba saita kashe wayan. Rahma ce [8/13, 4:09 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *32.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* Yaya Aryan d'aure fuska yayi cikin sigar wasa, itama ta d'aure fuska kamar za tayi kuka, tace "bana buk'atar sanin ko ita wacece, ga wayata kayi amfani da shi in kana buk'atan kiran su Umma, dan nima ina da contact d'in kowa har nasu Kaka Malam, Wayanka kuma sai na d'auki mataki akanta sannan zan dawo mana da shi" Mamakinta ne ya bayyana k'arara a fuskansa, bai yi tsammanin abun har zai kai haka ba, cikin d'aure fuska yace "Malama me kike nufi ne? yanzu fa kika gama ce min baki sona, to meye ne dan wacce take sona ta kira ni, kawai ki bani wayata ki rik'e taki, dan ban yarda da wannan salon naki ba" Ya tsine fuska tayi tace "Yaya Aryan wallahi bazan baka wayan nan ba yanzu" tana gama fad'a ta aje masa wayarta a gefen wani kujera "gashinan in ka tashi tafiya sai ka d'auka" ta wuce fuuu cikin fushi kamar guguwa. Dariyan da yake dannewa ne ya kwace masa, ya shiga dariya harda rik'e ciki, Basma ta kara k'uluwa, tafiya take ranta na suya kishi ya gama rufe mata ido, hawaye ke fita a idonta tana sharewa, a ranta tace "wai wani irin So nake wa Yaya Aryan ne haka? har da zan kasa controlling kaina". Haka ta isa part d'in Ammi, sashinta ta wuce ta kulle kanta, kiran wani security tayi a waya tace "zan turo maka wata number yanzu kaje MTN office a bincika min waye mai number, kuma da cikakken address d'in mai number". Cikin girgamawa ya amsa da to sai ta kace wayan. Ta jawo wayan Yaya Aryan, ta d'auki numban Jidda ta turawa security d'in. Yaya Aryan ya d'auka wayan Basma cike da nishad'i, ji yayi duniyan yayi masa dad'i saboda yanda ya gano babu abinda ya rage Sonsa a zuciyar Basma. Ammi na daga window d'akinta dake sama duk tana hangen abinda ya faru tsakanin Basma da Aryan, bata jin abinda suke cewa, Amma ta fahimci soyayya ta dawo, murmushi tayi tace a ranta "masoya Laila da Majnun, dole zan sanar da president domin a zo ayi bikin nan kowa ya huta tunda Basma ta gama idda". *Washe Gari* Ammi suna hira da Momy tana gaya mata labarin su Basma, Momy dariya tayi tace "Aiko wallahi wata ran zaki ga abinda idonki sai kasa gani in dai yaran nan ne" Itama dariya tayi tace "bari kawai, naje rufe window d'in ne fa, shine nayi arba da su, so nake Anjima naje na samu President nayi masa magana, don a sanya bikin da wuri ayi a gama kowa ya huta" Momy tace "aiko gwara dai ki gaya masa dan ni ba ruwana a ciki kunfi kusa, dan yaranki ne" nan dai sukaita tattaunawa. Da yamma misalin k'arfe biyar Basma ce ta fito cikin shirin fita, Yaya Ahmad da Yaya Aryan sun jero suna hira da alama fita za suyi, da sauri Yaya Ahmad ya k'arasa wurin Basma Aryan na biye dashi a baya yace "Queen sai ina haka kuma haka?" Murmushi tayi tace "Yaya Ahmad Momy ta aike ni zanje yanzu na dawo" Aryan ne ya kalleta yace "Bani waya ta in d'auki wani number" ta kalle shi a tak'aice tace "Gaskiya ban gama abinda nake da shi ba inna gama zan baka" "ok, shikenan amma ba ke kad'ai zaki fita ba ko?" "Ni kad'ai zan fita ko akwai matsala ne?" "Awkai saboda ban yarda kina fita ke kad'ai ba, in dai kina son fita to lallai sai dai driver ya kaiki" Bata tanka masa ba, ya mik'a hannunsa Alaman ta bashi key d'in motan, tana turo baki ta mik'a masa, driver ya kwalawa kira ya tawo da sassarfa, Yaya Ahmad na kallon ikwan Allah, Yaya Aryan ya mik'a ma driver key yace "ga tanan ka kaita duk inda zata je, kuma ka tabbatar magriba ta muku a gida" Jiki na rawa ya amsa da to, sannan suka wuce. Ahmad yana mata dariya ciki-ciki dan abin nasu ya bashi dariya sosai. Basma kamar yanda security ya samo mata address d'in Jiddah haka tayi ta ma driver kwatance har suka kai, driver yayi parking tace "ka jirata nan". Cikin natsuwa ta isa bakin gate d'in gidan, turawa tayi k'ofar ya bud'e sai ta shiga, mai gadi na zaune a kan kujera Basma tayi masa sannu, sannan tace "dan Allah ko nan ne gidansu Jidda?" cikin sauri yace "kwarai nan ne, bata dad'e da dawowa daga anguwa ba" Kud'i Basma ta ciro a jakarta wanda bata san adadinsu ba ta bashi, jikinsa na rawa ya amsa yana mata godiya da Addu'a, haka ta shiga cikin gidan hankali ta kwance ba tare da fargaba ko damuwa ba. K'ofar falon ta tura ta shiga, k'aton falo ne mai d'uke da kujeru da kayan alatu, dai-dai gwargwado sunada kud'i suma ba laifi, wata Mata ta amsawa Basma sallama, cikin natsuwa Basma ta k'arasa ta samu guri ta zauna, Matar ta kafawa Basma ido domin bata wayi fuskanta ba, Basma ta sirinar da kai k'asa ta gaisheta, cikin fara'a Hajiya ta amsa, Basma tace "Momy Jidda na nan kuwa?" "tana nan, bari na kira miki ita" nan take ta bud'e murya ta shiga kwalawa Jidda kira, cikin sauri ta fito sanye da k'anun kaya sun matseta tace "Mama kaya nake sawa fa yanzu na fito wanka" "To bak'uwa kika yi gata nan, shine dalilin kiran naki" Da sauri ta karasa falon ta zauna cike da kallon mamaki tak'ewa Basma, cikin murmushi Basma tace "nasan baki waye ni ba, Amma inna ce miki Queen Basma ce k'ila ki iya sani na" Washe baki Jidda tayi tace "laa kece dama Queen Basma Yar shugaba? ai ina jin sunanki, to ya kike?" "Lafiya lau, dama nazo muyi magana ne akan Mijina Aryan" Damm zuciyan Jidda ta buga, cikun k'arfin hali tace "ban fahimceki ba?" Murmushi Basma tayi ta kai kallonta ga Maman Jidda tace "Momy nazo wurinku ne badan rigima ba sai domin inyi magana da Jidda ta fita hanyar Mijina don Allah" Mamaki ya kuma kama Jidda da Mama, Mama tace "Jidda ko yaron da ki kika min bayanin shi?" "Eh shi take magana" "Basma ta cigaba da cewa "tun jiya bayan munyi waya dake baki fasa kira ba kuma wayar tana hannu na, to na rok'eki da ki fita hanyansa in ba haka ba duk abinda na miki ke kika ja" Ta d'auki wayan Aryan ta kashe, ta zare sim d'in ta cigaba da cewa "wannan shine abinda yake had'a ku kuke magana ko? To bari ki gani" sai ta karya sim d'in tayi masa gutsi-gutsi, kana ta ciro sabon layi data sanya aka yi masa regista tare ta sanya masa duk nombobinsa a ciki, na Jidda ne kawai aka cire, sai ta sanya ta kunna tace "na sauya masa layi" Jidda mutuwar zaune zayi domin yau ta had'u da wacce ta fita son Aryan. Basma ta mik'e ta ciro bandir d'in kud'i na dubu d'ai-d'ai taje ta aje gefen Mama tace "Mama ga wannan kici goro na gode" Mama tace "Allah ya miki albarka, nagode ki gaida manyan" Jidda ta mik'e ta bi bayanta har suka fita farfajiyan gidan, hak'uri ta shiga bama Basma da kuma alk'awarin komai ya wuce ba zata sake shiga hanyar Aryan ba, dama ita ke sonsa bashi ba. Nan dai suka rabu lafiya har mota Jidda ta raka ta, kana ta koma gida cike da damuwa. Mama ta kalleta cikin kulawa tace "ai kinga yanzu kya bari Bashir ya fito auren ki, k'iri-k'iri Yaron nan na Sonki, kika mak'ale ke kina da wanda kike So to yau kin gamu da wacce ta fiki sonshi, dan haka yanzu kya shiga hankalin ki, ni naji dad'in zuwanta ma dan yamin riba, dubu d'ari tabani bashi a rubuce" Marai-rai ce fuska tayi tace "Mama ai yanzu ma hak'uri na bata don mu rabu lafiya, bazan iya ja da 'yar President ba, dama can nayi tunanin Aryan yafi k'arfina, baki ganshi bane Mama gayen ya had'u" "Tafi can ki bani wuri, ni dai ki bama Bashir dama ya fito a yi biki nan ko na huta". Murmushi tayi tace "Mama kenan, to ki kwantar da kankalin ki nima na saduda". Basma tana komawa gida taje part d'in Yaya Ahmad ta same su a can, zama tayi suka gaisa ta ciro wayan Aryan ta mik'a mishi tace "ga wayanka nan na sauya masa layi, kuma numbers d'in dake wancen nayi nasa duk an maida maka su, number Jidda ne kawai bai ciki, kuma nasa an tura ma duk contact d'inka text da cewa wannan shine sabon layinka, MTN office naje acan suka min komai" Yaya Ahmad yace "biri yai kama da Mutum d'azun naga text magana ne kawai banyi ba" Aryan murmushi yayi ya amsa wayan, amma yak'i mika mata nata, tace "ka bani nawa" Hararanta yayi yace "ba yanzu ba" mik'e wa tayi ta ce "shikenan ka rik'e tunda burina dai ya cika, dan na gama yin abinda nake so, Jidda ce kuma ba zata sake kiranka ba dan nayi tattaki zuwa gidansu" nan ta kwashe labari tas ta gaya musu sannan bata jira me zasu ce ba ta fice tana gunguni. Dariya duk ta basu Yaya Ahmad yace "Basma rikici, to kai aiki ya same ka" Dariya Aryan yayi yace "zata gama borinta ta daina" nan dai suka cigaba da hira suna dariya. Da dare Yaya Aryan ya kirata a d'ayan wayanta kamar ba zata d'aga ba, sai taji bazata iya share shi ba, d'agawa tayi tare da yin sallama, ya amsa, sannan suka yi shuru, can k'asan murya yace "My Basma ina part d'in Yaya Ahmad kizo za muyi magana" "barci nake ji" "to shikenan bari naje gidansu Jidda nasan ita zata saurareni" Da sauri ta mik'e cikin masifa tace "gani nan zuwa wallahi karma fita" dariya ya kwashe dashi sai ya kashe wayan. Ta same shi tana d'aure fuska, a hankali ta saki saboda irin soyayya da hira da yake mata cikin farin ciki suka rabu. Ammi ta samu Abba sunyi magana akan zancen su Basma, Abba yayi farin ciki nan take ya kira Dady da Mai Martaba yayi magana dasu. *Washe Gari* Duk zuka zo suka had'u suka yanke sadaki da ranar biki sati biyu mai zuwa, Mai Martaba shine ya biyawa Aryan sadaki, Dady kuma shine zaiwa Basma kayan d'aki, da kuma gyaran gidan da zasu zauna, Abba kuma shine zai had'a masa akwati. *Rahma Ce* [8/13, 4:10 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *33.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* Sun fara shirye-shiryen biki ba kama hannun yaro, Musamman Ummi ta kira wata 'yar Uwarsu daga Maiduguri tazo gyara Basma, an tsumata da turaruka sosai da dilka, dasu kayan k'arin ni'ima, Basma ta k'ara kyau sosai duk in da ta gifta k'amshi ke tashi, in ko ta zauna a wuri sai yayi damshi, an gyara mata sumanta ya k'ara bak'i, silb'i da shek'i yayi kyau sosai. Ammi da Hajiya Murja sune suka tafi Dubai had'o kayan lefen Basma. Akwati dozin guda sha biyu tank'ame da kaya, Ango ma anyi masa nashi akwati biyar cike da kaya. Yaya Aryan yana ta shirye-shirye, Yaya Ahmad shima ba baya ba tare suke aiwatar da komai. Dady yasa an gyara gidan da Basma zata zauna, komai sabo aka sanya a gidan. Sweeping pool d'in an sauya ruwan ciki, lanbun gidan an gyara shi sai k'amshi ke tashi. *Biki saura kwana uku* Gida ya gama cika da dangi, taron Mutane yafi ko wani taron biki da akayi a baya, Mutanan Kano, Kaduna, Gombe, Maiduguri duk sun hallara a gidan shugaban k'asa, ko wanne ya samu masauki. Hajiya Kaka da Inna suka sanya Basma a gaba suna mata Nasiha, Basma sai kuka take yi, Kaka tace "Basma, Aryan Yaro ne mai hak'uri dole sai kin ajiye rashin kunya da tsiwan ki in ba haka ba zaki rik'a shiga hakk'insa" Nan dai su kaita mata, tashi tayi ta mik'e cikin shagob'a tace "Ni kun tasani a gaba sai mita kuke min, ai shima ya kamata ku kira shi kuyi masa fad'an, ni kunga tafiya ta" Kaka tace "kinga ja'ira ko, saina sanya shi ya tsafala min ke mara kunya kawai tafi ki bamu wuri" Inna tace "Hajiya bar Yaran yauzu, wataran nan zata zo wurin ki niman tai mako" Basma tace "Allah ya kyauta" ta fice abinta tana dariya. *Ana Gobe Biki* K'ayataccen walima suka had'a Maza da Mata a wani k'aton hol, aka kira wani Babban Malami yazo ya bada fatawa akan zamantakewar Aure. Matan *Siirrin 'ya Mace* sun hallara, haka ma matan *'Yar Shugaba Fan's* sun hallara, Matan group d'in *Khaleesat Haydar Facebook* suma sun zo, matan group d'in *M Khady Fan's* suma sun iso, *QueenMamu novel group* suma sun iso, *real maidanbu novel group* suma sun halarto, *S.I Kaduna Fan's club* suma suna wurin, *Sophy an vc novel* duk suma sun iso. Wuri ya cika ya batse da mutane kowa ka ganshi yana cikin farin ciki, Amarya ta sanya wani material mai kyau da tsada ta d'aura alkebba a sama, haka ma Ango yasha farin yadi mai kyau ya sanya alkebba a sama. Wuri d'aya suka zauna, wurin yasha decoration, Anci ansha taro yayi dad'i da armashi. Sai misalin Sallan Magrib taron ya watse kowa ya koma gida. Amarya suna hanyar dawowa, zaune suke seat d'in Baya, Yaya Aryan ya matsa kusa da ita ya leka cikin fuskarta, runtse ido tayi alaman jin kunya, cikin murya mai dad'i yace "Insha Allah gobe In Allah ya kaimu, uwar haka kin zama tawa ni kad'ai" Murmushi tayi ta bud'e ido sai ya sauka akan nashi, ido d'aya ya kashe mata, sai ta rufe fuska da hannayenta tana dariya, k'unshin da aka mata a hannu ya kurawa ido kamar zai leshe su, dan sunyi masa matuk'ar kyau, cikin kasalan jiki ya kai hannunsa kan zanan, ya shiga binsu a hankali, nan take jikin Basma yayi sanyi kasala ya diran mata, cikin sauri ta cire hannun a fuskanta ta duk'un-k'une su cikin alkebbanta, murmushi yayi mai sauti. Kansa ne yaji ya rasa masa, runtse ido yayi ya bud'e idonsa sunyi ja, janye jikinsa yayi gefe ya d'aura bayansa jikin kujera, runtse idonsa yayi yana ambaton Allah a zuciyansa, a hankali ya fara samun natsuwa, tunani ya shiga yi "me yasa nake jin irin hakan kwana biyun nan?" basarwa yayi ya jawo wayansa ya nima wayar Yaya Ahamd suka fara magana akan hidimar biki. Basma ko ta mak'ure gefe d'aya, Allah-Allah take su isa gida ta fita a motan, gaba d'aya hankalinta a tashe yake, abinda Yaya Aryan ya mata duk ta susuce. "lallai akwai aiki a kaina, bazan k'ara shan wani Magani ba" Zancen zucin da take yi kenan. *Washe Gari* *_Ranar D'aurin Aure_* Ya kama ranar Asabar Weekend, da misalin k'arfe (10am) na safe, Babban Masallacin Juma'an dake Abuja ya cika da Jama'a, Manyan Mutane ke wurin, hatta daga k'asashen waje Abokan President sun zo d'aura auren su Basma. Unguwar ya cika da motoci da Mutane, Ni kaina na kasa yanda zanyi na shiga Masallacin d'auko muku rahoto, Yaya Ahmad na hango dasu Yaya Naufal d'auke da sink'in goro suna k'ok'arin shiga ciki, da k'arfin na bud'e murya na kira Yaya Ahmad, da sauri ya juyo, mik'awa Yaya Jamal sink'in goron yayi suka shiga ciki, yazo guna da sassarfa yace "Anty Rahma hala Mutane sun hana ki shiga d'auko abinda ke wakana a cikin Masallacin?" Murmushi nayi masa nace "kwarai kuwa, taron Mutanan ne suka min yawa kamar an sauko Sallan idi, yanzu dai bari nabi bayanka ko zan samu hanyar shiga" Dariya yayi yace "Ai dole a baki hanya dan in bakya wurin nan d'aurin auren bazai yuwu ba, domin kece jagoran komai, dan haka biyoni a baya". Haka nabi shi a baya, Mutane na darewa suna bani hanya sai gaisheni suke tamkar sun ga Sarauniya. lol🤪 Muna shiga waliyyan Ango da Amarya suka fara siga, nan take aka d'aura auren *Aryan Aliyu da Basma Mukhtar Bukar* Bisa sadaki dubu d'ari lakadan ba ajalan ba, nan a kaita sanarwa a ka soma raban goro da Sweet da dai duk abin da ya shafi Al'adan bahaushe. A can gida kuwa Yaya Ahamd ya kira Deeja ya shaida mata an d'aura, da sauri ta fita ta shaidawa Mutanan gidan nan fa Mata suka fara sakin gud'a. Amarya na k'urya d'akin Ammi su Meena na tare da ita, ta sha kwalliya tayi kyau har ta gaji, leshi ta sanya Marron da kwalliyan fari, anyi mata d'auri na Amare na head, sarkan gold da dan kunne ta sanya tare da abun hannu sai kyalli suke, k'amshi ke tashi a jikinta, duk inda ta juya sai an kalleta, black beauty yayi fa, nan take suka dinga d'aukarta photo suna turawa a WhatsApp group-group, harda su Instagram. Fitowa suka yi da ita 'Yan Uwa suka mai mayeta sunata gud'a, masu d'aukarta photo nayi, Basma tunda taji an d'aura Auren wani sanyi ya ratsa zuciyarta, hawaye ne ya sauka kuncinta tana murmushi, Leema ce ta goge mata tace "Meye haka kuma karki b'ata kwalliyanki" Murmushi tayi tace "ko na b'ata za'a sake min wata, ku barni nayi kukan farin ciki na samu cikar burkina" Juyawa suka ga tayi ta nufi cikin falo, haka suka rufa mata baya, d'aki ta koma ta cire head d'in ta d'auko sanlaya ta shifid'a ta kuma sanya hijab, dama tana da Alwala sai ta kabbarta Sallan Nafila na Walha, raka'a biyu tayi, ta jima a sujuda na k'arshe tana Addu'a, bayana ta d'ago tayi lamuzi tare da sallama. Ta jima a zaune tana yiwa Allah kirari, Addu'a kuwa tayi su da yawa. Bayan ta idar ta Shafa a'ddu'an tare da goge hawayan da ya sauka kuncinta, farin ciki ya gama rufeta ta mik'e ta maida sallayan da hijab mazaunin su, wasu kayan ta sauya, mai kwalliya ta gyara mata fuska aka kuma d'aura mata wani head d'in, wannan karan shadda ta sanya doguwar riga tasha aiki har k'asa, tayi matuk'ar kyau, su Deeja sai kallonta suke cike da burgewa. B'angarden Ango kuwa suna can sunata hada-hada da Mutane, Yaya Shureym shima ba'a barshi a baya ba ya mance komai ya kama Matarsa Safeena, dashi aketa hidimar bikin, Ango yana tare da Abokai da 'yan Uwa sunata hira. *_Da k'arfe takwas na dare_* Kowa ya gama shirin zuwa Dinner, Amarya ta sanya wani leshi mai matuk'ar kyau da tsada, mai kalan pink da fari sai rashin bak'i a jiki, ta kalmi da pos bak'i, head fari ta sanya, Ango yasha shadda fari anyi mata aiki da bak'in zare yayi kyau sosai, hula bak'ar dara da takalmi bak'i ya sanya. Ango yana bayan seat aka fito da Amarya aka sanya ta a kusa da Yaya Aryan, Yaya Ahmad shine ke mazaunin driver sai Deeja a gefenta, Walid ta barshi wuri Momy. Suka kama hanyar Wajen Dinner. Tunda Basma ta shigo Motan, gaban Yaya Aryan ke bugawa ya nima natsuwansa ya rasa, kansa ne ya soma sarawa nan da nan idanunsa yayi ja, Basma kuwa farin ciki ya cika ta matsawa kusa da shi tayi ta kamo hannunsa, da sauri ya runtsa idonsa saboda azabar da kansa yake masa, Basma ta matsa da bakinta kusa da kunnensa tace "myn yau ba magana ko?" Murmushi yayi ya juyo ya kalleta suka had'a ido, a razane tace "Yaya Aryan meya samu idonka yayi ja haka?" Murmushi ya mata yace "Missing d'inki ne yasa haka" Kunya ne ya kama ta sai ta jaye jikinta ta koma gefe, ajiyan zuciya ya saki a hankali, ambaton Allah ya shiga yi a hankali ya soma dawowa hayyacinsa, lamarin ya fara damunsa tsakanin jiya da yau, kuma hakan bai damunsa sai Basma na tare dashi. A ransa yace "Me yake shirin faruwa dani ne?" babu amsa, dole ya kauda tunanin a ransa. Sun isa wurin dinner. Wurin ya tsaru sosai, mutane sun hallara zuwan Amarya da Ango ya rage, haka suka fito ya sakala hannunsa cikin nata nan take ciwon kai ya dawo, d'aurewa yayi har suka isa mazaunin su kana ya zare hannunsa a nata. Taro ya kayatar kuma anci an sha anyi hotuna, anyi rawa an zubda Naira. Matan *sirrin ya mace group* sai rarraba ido suke yi, haka ma manan *Yar Shugaba novel Fan's group* suma sun cashe sosai. Haka aka gama taro kowa ya koma gida cike da farin ciki. *Washe gari* Da misalin k'arfe Hudu na yamma gaba d'aya iyayen suka had'u a falon Abba, Basma na gefe kusa da Kaka Ma'u, Aryan yana gefen Kaka Malam, nasiha sosai iyayen suka yi musu akan zamantakewar Aure, Basma kuka take yi mara sauti, shi kuma Aryan jikinsa ne yayi sanyi sosai, bayan sun gama Abba yace "Hajiya Fatima ina so da ganan ku wuce da Basma gidanta" Ammi tace "to Yallab'ai" Nan ta kama hannunsa Basma su Ummi na biye dasu suka wuce wurin motocin gidan, Momy dai part d'inta ta wuce ko waiwaye batayi ba, hawayen farin ciki ke fita a idonta, saboda Basma ta auri wanda take so tasan tabbas zata samu natsuwa. Umma ma bata bisu ba tabi bayan Momy. Basma kuka take da kyar suka sanyata a mota kamar wannan ne aurenta na farko, gaba d'aya motocin gidan suka kwashe su aka wuce kai Basma gidanta. Suna kaiwa dama gate d'in abud'e yake haka su kaita parking suna fitowa, falon suka shiga sun tadda su Deeja, Meena, Leema, Safeena, Munayah Matar Yaya Adam, sun kintsa komai na gidan, sun zauna suna jiran zuwan Amarya, Ammi ta wuce da ita d'akinta, ta ajeta kan gado, wani k'aramin kofi ta dank'a mata a hannu tace mata a kunne, "bayan sallan Magrib ki tabbatar kin sha wannan, Allah ya baku zaman lafiya" Basma ta k'ara fashewa da kuka tace "Ammi karki tafi dan Allah" Dariya tayi "A'a Basma, aiko tafiya ya zama dole kuma ai wannan ba shine aurenki na farko ba balle kice baki saba ba, nan da kwana biyu zamu dawo" Sai ta janye jikinta daga na Basma ta wuce tana share hawaye, haka suka tafi suka bar su Deeja, sai dare insu Yaya Ahmad sun kawo Ango sannan zasu tafi tare dasu. *Wai Yaya Aryan yadai?*🤔 *Rahma Ce* [8/13, 4:11 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *34.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* *Bayan Sallan Isha'i* Su Yaya Ahmad sun kawo Ango Aryan, tunda suka shigo gabansa ke fad'uwa ya rasa natsuwan sa, nan su Yaya Ahmad suka yi musu d'an tunatarwa game da aure sannan suka yi musu sallama, da kyar Basma ta saki Meena sai kuka take yi, haka suka tafi tare da yi mata sallama. Yaya Aryan ya rakasu har mota saida yaga wuce wansu kana ya koma cikin falo ya zauna ya cire hulan kansa yana fifita dashi domin duk sanyin AC dake d'akin gumi yake yi, maida hulan yayi ya mik'e ya nufi d'akinsa, ruwa ya watsa tare da d'auro alwala ya sanya farar jallabiya ya fito falo, ya shiga kitchen ya d'auki plet tare da cups, hannunsa rik'e da ledoji ya nufi d'akin Basma. Ya sameta zaune gefen gado fuskarta rufe da mayafi, zama yayi kusa da ita yaji kansa ya sara d'aurewa yayi ya yaye mayafin, d'ago fuskarta yayi cikin murya k'asa-k'asa yace "Amaryata kinsha k'amshi, anya zaki rik'a barina ina fita kuwa? dan k'amshin ki kawai zai rik'a riki tani in kasa fita". Murmushi tayi tace "anya kuwa myn?" Murmushi yayi shima yace "Eh mana, tashi ki d'auro Alwala muyi Sallah" Cikin murmushi tace "ina da alwala ban dad'e da idar da Sallan Isha'i ba" "ok tashi ki mu gabatar da Nafila" ba musu ta mik'e. Sun idar da Sallan Nafila Raka'a biyu ya kama kanta ya mata Addu'a'o'i, kana suka yi Addu'a gaba d'aya suka shafa, kayan ciye-ciye ya zuba a plet d'in sannan ya zuba mata yoghurt a cup ya kai bakinta kamar ba zata amsa ba, ta bud'e bakin a hankali tana sha, haka ya ciyar da ita komai da hannunsa har sai da ta ce ta koshi kana ya rabu da ita yaci nashi. Bayan sun kammala ya kwashe kayan ya maida kitchen ya rufe ya koma d'akin ya tadda Basma ta sauya kayan barci ta kuma shiga bayi ta wanke baki, kwanciya tayi akan gadon taja bargo tana dariya k'asa-k'asa tace "Myn saida safe" Murmushi yayi yace "ok Allah ya tashe mu lafiya" sai ya zauna gefen gadon ya dafe kansa, tunani iri-iri yake yi amma ya gaza sanin ina hankalinsa ya dosa, jallabiyansa ya cire ya za gaya d'ayan side d'in gadon ya kwanta, kansa yana ta sarawa d'auriya kawai yake yi, cikin k'ank'anin lokaci idonsa yayi jaaa, hakanan tsoro yaji ya diran masa, Addu'a ya shiga yi dan neman yardan Allah, cikin lokaci kad'an ya samu rangwame ga yanda yake ji. Jawo Basma yayi tana k'ok'arin zillewa ya d'aurata bisa kirjinshi, gam ya rik'eta suna jin bugun zuciyan juna, cikin rad'a yace mata a kunne "Rashinki yasa dare ya zame min rana bana iya barci, na shiga k'unci da damuwa, ya zanyi in misalta miki Son da nake miki ki fahimci zuciyana, my Queen kin zama b'angare na jikina bazan iya rayuwa ba ke ba" Hawaye mai zafi yana fita a idonsa kansa nayi masa tsananin ciwo, Basma ta d'ago kanta tana kallon fuskansa, cikin kasala da damuwa tace "Myn ka daina min asaran hawayenka, wannan ranar muke jira tazo, dan haka farin cikinka nake so ka nuna min a yau da mai cike da so da k'auna". Hawayensa ta goge masa, rungumeta yayi tsam ajikinsa tare da sakin ajiyar zuciya. Daga nan kuma salon ya sauya, suka lula duniyar masoya, soyayya suke nunawa juna mara misaltuwa, sun gama kamuwa sosai, Aryan yana k'ok'arin kai ga biyan buk'atansa jikinsa ya soma rawa, nan da nan zazzab'i ya diran masa kansa yayi zafi kamar wuta nan take kwayan idonsa ya sauya kala yayi jaa kamar garwashin wuta, cike da tashin hankali ya ja jikinsa yana haki, Basma ta kamo hannunsa domin ta kama kamuwa dan maganin da tasha suna matuk'ar aiki a jikinta, fincike hannunsa yayi da k'arfi ya mik'e jallabiyansa ya maida ya koma gefen gadon ya zauna tare da dafe kai. Kuka Basma ta fashe dashi tanata juyi a kan gadon, kukanta ya k'ara tayar masa da hankali, cikin mutuwan jiki ya mik'e da nufin barin d'akin, jiri ne ya kwashe shi ya zube akan gadon yana rawar sanyi, Basma hankali ta yayi matuk'ar tashi, cikin k'arfin hali ta mik'e ta matsa kusa dashi, a can k'asan mak'oshi Aryan ke fad'in "Basma dan Allah ki matsa a kusa dani mutuwa zanyi, in kina kusanto ni azaba nake ji" Kuka Basma ta fashe dashi da k'arfi tana fad'in "Innalillahi wa inna ilai hir rajiu'n". mik'ewa tayi ta shiga bayi ta d'auraye jikinta tare da yin Alwala. Al'Qur'ani ta d'auko ta zauna nesa dashi ta soma karantawa a nutse tana kuka, dafe kunnuwansa yayi bai son jin karatun amma bai hana karatun na shiga kunnensa ba, a hankali ya soma samun natsuwa, da k'arfi ya saki ajiyan zuciya, juyowa yayi yana kallon Basma hawaye na zuba masa, daina karatun tayi ta aje Al'Qur'ani ta dawo gefensa, fuskanta d'auke da murmushi tace "Myn sannu ya jikin da fatan baka jin komai yanzu ko" Murmushi ya mayar mata ya share hawayensa, mik'ewa yayi yana tangad'i, ta mik'e zata kamashi ya daga mata hannu cikin dishewan murya yace "Kina tab'a ni ciwon zai dawo" ido ta zaro waje tare da toshe bakinta hawaye na fita a idonta, haka ya fita zuwa d'akinsa, wanka yayi ya sauya kayan ya fad'a gado sai barci mai nauyi ya d'auke shi. Basma zama tayi gefen gado tana kuka wiwi ba mai taimakonta, tunani barkatai take yi amma ta gaza fahimtar komai, mik'ewa tayi ta gyara shinfid'ar gadon ta kwanta, cikin k'ank'anin lokacin barci ya d'auke ta. *Washe Gari* Basu suka farka ba sai bayan k'arfe takwas na safe, cikin sauri Basma ta fad'a bayi tayi wanka tare da d'auro alwala, ta gabatar da Sallan aAsubshi tayi dukkan Azkar na safe kana ta tashi ta shirya cikin Riga da sket na atamfa ta d'aura d'ankwali, ba wani make-up tayi ba ta fito falo ta samu Yaya Aryan yana zaune, ta k'arasa falon ta zauna nesa dashi kanta a sunkuye ta gaishe shi, cikin fara'a ya amsa "My Queen hop kin tashi lafiya?" "Lafiya lau Myn, uhum ya jikinka?" "da sauk'i ai na warware" "tom masha Allah, Allah ya k'ara afuwa, amma ka tashi da wuri shine baka tashe ni ba?" "Wallahi naso tashin ki, dan harna isa k'ofar d'akin sai naji gabana na fad'uwa sai na dawo kawai" D'ago fuska tayi ido cike da hawaye tace "amma Yaya Aryan a da baka jin irin haka, meyasa yanzu haka ke faruwa?" tana zubda hawaye. Mik'ewa yayi da sauri ya kamota ta mik'e tsaye, rungumeta yayi tsam ajikinsa, take ya fara jin zafin jiki da ciwon kai, saketa yayi suna kallon juna yace "Basma bansan me yake faruwa dani ba, tun bayan kwana biyu da suka wuce, duk lokacin da kika zo kusa dani ina shiga cikin mawiyacin hali, kaina ya rik'a min wani irin ciwo tamkar zan mutu, jikina kuma tamkar garwashi, a yanzu haka ina jin abinda nake gaya miki a jikinsa" Zuba ma juna ido suka yi, tace "Myn zan kira Yaya Ahmad in sanar masa domin anima maka magani" Kama hannunta yayi yace "karki gaya masa saboda kar mu tada musu hankali, yanzu dai ki cigaba damin Addu'a, zo muje mu karya tun d'azu aka aiko mana da breakfast daga gida" Hannunta ya kama gam suka wuce dinning sunci sun koshi, suna yi suna hira kamar babu wata matsala a tare dasu. Da midalin k'arfe biyu na rana Mutane suka fara zuwa, Yaya Aryan fita yayi ya basu guri. Basma tana tare dasu Deeja a d'aki sai tsiya suke mata, murmushi kawai take yi dan ita kad'ai tasan halin da suke ciki, kamar ta gaya musu amma saita fasa. haka suka yi mata yini sai dare su Yaya Ahmad suka zo suka kwashe su. Basma na gefen Aryan yana nishi sama-sama, abinda ya faru jiya shine ya kuma faruwa yau, kuka Basma take yi mara sauti, Addu'a take yi tana tofa masa, a hankali ya samu natsuwa ya hau saman gadon ya gyara kwanciyansa, yau baijin zai iya tafiya ga shi bai wanke jiki ba, haka barci ya d'auke shi mai nauyi. Basma tashi tayi ta wanke jiki ta d'auro alwala Sallan Nafila ta gabatar tare da jero Addu'a, Allah ya kawo musu d'auki cikin matsalan su. Nima dai na taya su da Ameen. *Bayan mako biyu* Su Basma suna cikin wannan halin babu wani sauyi, duk sun rame sunyi haske, d'an kyau da Amare su keyi su sam ba suyi ba. haka suka shirya suka nufi gida dan su gaishe su, sun isa ko wani part sun gaishe su, President yayi tafiya dan haka basu sameshi ba. Part d'in Yaya Ahmad suka nufa, hira suke sosai Yaya Ahmad ya kalle su yace cikin kulawa "Aryan, Basma anya babu wata matsala kuwa a tattare daku? kunga yanda kuka yi rama sai haske da kuka yi kamar wanda suka farfad'o daga ciwo" Murmushi suka yi, Yaya Aryan yace "Abokina mu da muka yi Auren soyayya ai babu wata Matsala da zai samu damuwa, kawai dai duk cikin Amarci ne muka koma haka, ko ya kika ce My Basma?" Murmushi tayi tace "sosai ma kuwa Mijina, hankalin mu kwance yake ba wata damuwa" Yaya Ahmad yace "to Alhamdulillah naga yanda kuka sauya ne lokaci guda, dole muyi zargin ko da Matsala" Yaya Aryan yace "aiko ba zamu sake zuwa ba sai munyi k'iba sosai, dan d'azu ma Ammi tirkemu tayi, wai me yake damun mu duk mun fita hayyacin mu" Dariya duk suka saka yaya Ahmad yace "Allah kuwa duk wanda ya sanku kafin aure in ya ganku yanzu sai anye kunyi rama" Deeja tace "raman ma sosai kam, kuma abin mamaki gaba d'aya suka yi raman, Allah yasa dai lafiya" Harara Yaya Aryan ya watsa mata "me kike nufi? kina nufin baki gamsu da abinda muka fad'a ba" mik'ewa tayi da sauri tana dariya tace "sosai kuwa, ai daga kai har Basma bakin ku d'aya, kuma shegen miskilanci ne daku" tana gama fad'an haka ta bar wurin da gudu dan kar Yaya Aryan ya mata hukunci. Haka suka gama yinin su sai dare suka koma gida cike da farin ciki, suna isa gida, gabansu ya fara fad'uwa sun riga sun sadak'ar yau ma abinda suka saba fuskanta ne zai faru, sun kuma kasa hak'ura da juna, dan kullun sai Aryan yayi k'ok'arin kusantarta, amma abin yaci tura. Yaya Ahmad yana kwance a d'aki ya juya ya kalli Deeja sai barci take yi, tunanin su Basma ya kasa b'ace masa a zuciya "kuma ya kasa yarda da abinda suka gaya masa, yasan wannan karan Basma ba zata tab'a gaya mishi damuwarta ba tunda tana Son Aryan, sannan kuma yasan yanda Aryan ke Son Basma bazai cutar da ita ba, to me yake damunsu su biyun? meyasa su kayi rama haka?" Tambayoyin da yakewa kansa kenan wanda ya zaga samun amsansu sai a bakin Aryan da Basma zai samu, gyara kwanciya yayi da niyyar gobe in Allah ya kaimu sai je gidan da safe yaga abinda ke faru ko ya matsa musu su gaya masa. Da wannan tunanin ne barci ya d'auke shi. *Lallai Aryan akwai wata matsala a tare da kai, ko meye ne...?* _*Hmmm yau dai dasan na tarwatsa farin cikin Makaranta wannan littafin, sai dai ince kuyi min hakuri haka na tsara labarin, kuma ina da dalili, insha Allah za kuyi farin ciki a nan gaba. Godiya gareku masoyana da irin Addu'an ku gare ni. Ina sonku sosai irin da yawa d'in nan Allah ya kara zumunci. Ameen*_ *Rahma Ce* [8/15, 8:44 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *35.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* *Washe Gari* Da k'arfe bakwai na safe Yaya Ahmad ya kama hanyar gidan Yaya Aryan. Yana isa yayi hon Mai Gadi ya bud'e masa Gate, yayi parking ya isa bakin k'ofar falon yayi nocking, Yaya Aryan dake kwance a kan doguwar kujera ya mik'e cikin nauyin jiki ya isa bakin k'ofan ya bud'e, sai yayi arba da Yaya Ahmad, sai da gaban Aryan ya fad'i, matsa masa yayi ya shigo cikin falon duk suka samu guri suka zauna, sai suka gaisa, Yaya Ahmad yace "Ina Basma fa?" Yaya Aryan yace "tana d'aki, lafiya na ganka da sassafe haka?" "Lafiya lau, nazo nayi magana daku ne, dan haka kira min Basma tazo" Bai ce komai ba ya mik'e ya isa bakin k'ofar Basma, sai ya ki shiga ya tsaya bakin k'ofar yana bugawa tare da cewa "Basma, Basma ki tashi ga Yaya Ahmad yazo" Cikin magagin barci ta farka ta mik'e tare da bud'e murya yace "to". Yaya Ahmad duk yana kallonshi, a ranshi yace 'ko me ya hanashi shiga d'akin oho' Yaya Aryan ya dawo ya zauna. Basma ta fito sanye cikin doguwar riga ta yane gyale a kanta, zama tayi a one seater ta gaishe da Yaya Ahmad ya amsa cikin kulawa, shuru ne ya biyo baya na tsayin minti Uku, daga bisani Yaya Ahmad yace "Aryan, Basma nazo domin muyi magana ne, a gaskiya ban yarda da bayanin da kuka min ba jiya, shiyasa na zo Yau dan jiya na kasa barci, Dan Allah karku b'oye min komai" Basma da Aryan suka kalli juna suka had'a ido, Basma zata yi magana Aryan ya riga ta yace "ka yarda da abinda muka ce maka mana domin ba komai" Yaya Ahmad yayi murmushin k'arfin hali yace "Basma in shi ba zai gaya min ba ke nasan ba zaki b'oye min ba, dan haka gaya min me yake faru?" Hawaye ne ya soma zarya a idon Basma, ta d'ago ta kalli Yaya Aryan, sai ya fara gir giza mata kai alamar karta gaya, Yaya Ahmad ya kira sunanta sai ta mai da kallonta gare shi yace "Basma ina jinki" Basma ta share hawayenta ta gaya wa Yaya Ahmad abinda ke damun Aryan, sai dai bata gaya mishi matsalan da suke fuskanta ba yayin saduwa sai ta boye wannan. Yaya Ahmad ya kurawa Aryan ido sai ya sun kuyar da kai zuciyarsa na masa zafi, nan take idonsa suka yi ja. Yaya Ahmad yace "Basma d'auko key d'in motanki ki shirya ki tafi gida" Da sauri duk suka zuba masa ido, d'aure fuska yayi yace "Nace ki tashi kiyi abinda na sanya ki" ya fad'a maganar cikin tsawa, jikinta na rawa ta mik'e tare da fashewa da kuka. Aryan mik'ewa yayi cikin fushi yace "Me kake nufi da ta tafi gida ba tare da izini na ba?" Murmushi yayi yace "Saboda ba kada lafiya, ba zata zauna ba domin tabbas matsalan ka zai iya shafanta" yaya Ahmad ya fad'i hakan ne domin ya tunzura Aryan dan ya tabbatar da ciwon nasa. Aiko Aryan ransa ya k'ara baci. Basma sai gata ta fito tana ta kuka, Yaya Aryan ya tare mata hanya ya kama hannunta gam, kansa ne yayi mugun sarawa sai ya rik'e Kan da d'ayan hannunsa, Basma tace "Yaya Aryan ka barni na tafi ko zaka ji sauk'in abinda ke damunka" Yaya Ahmad ne ya matso wurin ya fintsike hannun Basma, ya kama Aryan ya zaunar dashi tare da kama kansa da k'arfi, Addu'a ya fara tofa masa nan take ya ture Yaya Ahmad suka fara dambe. Basma ihu ta soma security da suke gidan suka fad'o falon a sukwane suka kama Yaya Aryan yana cijewa. Yaya Ahmad ya fad'a kitchen d'in Basma ya d'ibo ruwa a cup ya soma karanta Addu'o'i yana tofawa a ciki, bayan ya gama ya soma watsawa Aryan a jiki, wani k'ara ya saki yana gunji, haka yayi ta watsa masa har sai da yayi shuru yana gunji. Da sauri Yaya Ahmad ya kira Naufal yace "Naufal kana ina ne? ina so kaje gidan Malam Hashim ku tawo tare dashi gidan Aryan Akwai Matsala ne" bai jira mai zai ce ba ya kashe wayan. Cikin tashin hankali Naufal ya mik'e ya fito, gidan Malam Hashim ya wuce ya d'auke shi suka nufi gidan Aryan. Sun isa gidan cikin sauri suka fad'a falon, Aryan yana jin shigowar su ya saki k'ara, Malam Hashim ya kunna karwashin wuta ya sanya wasu Magani a ciki ya soma turara d'akin, Malam Hashim ya fara karanto wasu Addu'a yana tofa masa, Aryan yana gunji ya fara magana "Zan fita, Zan fita, Zan fita, karku k'ona ni" Malam yace Bama buk'atar kiyi magana ki tafi kawai" "Ni bazan tafi ba saboda ina son Basma" Ai Basma sai cikinta ya d'uri ruwa. Malam yace "Meyasa kike son ta sannan baki shiga jikinta ba saiki shiga jikin mijinta?" "Saboda tana burgeni, tun tana k'arama nake bibiyarta don na shiga jikinta amma ban samu hanya ba, saboda a jikinta banida mazauni dan Kakansu Bukar ya shayar da jikokinsa magun guna na tsarin jiki gaba d'aya babu wani jinnu da zai iya cutar dasu" "To meyasa kika Shiga jikinsa bacin Basma kike so?" "Soyayyan Basma yasa na shiga jikinsa, shima na jima ina son shiga jikinsa, ran nan ya kwanta ba tare da yayi Addu'a ba har barci ya d'auke shi. shine na samu hanyar shiga jikinsa, kuma bana so ya kusanci Basma saboda son da nake mata banson kowa ya rab'eta" "Kina mace maye da son shiga jikinsa, wannan ai ba soyayya bace, tunda kina cutar da shi, dan haka zan konaki da Ayar Allah" "Kar ku kona ni zan tafi har Abada bazan dawo ba" Malam ya watsa masa wani ruwan Magani, k'ara ya saki yana birgima nan take yayi shuru kamar ruwa ya d'auke. Aka sanya karatun Al'Qur'ani Suratul Bak'ara, nan take barci ya kwashe shi. *Hmmm duk abinda wasunku ke zargi akan Sihiri akaiwa Aryan kunata zaigin su Mami, to ba Sihiri ke damunsa ba, ba ruwan Mami, Yaya Shureym, balle kuma Jidda.* 🤪 Bayan komai ya lafa Yaya Ahmad ya kira su Ammi ya shaida musu abinda ya faru. Cikin tashin hankali suka zo gidan su Aryan. Sun zauna jugum-jugum suna jiran Aryan ya farka, cikin ikwan Allah kuwa sai gashi ya farka yana mai Ambaton Allah, zama yayi yana kallon Mutanen falon d'aya bayan d'aya, yana kai kallonsa ga Basma da take kuka sai ya yun k'ura da k'arfi yace "My Basma me ya same ki kike min asaran hawayenka" Haka ya isa wurin ta ya kama hannunta ya mik'ar ya zaunar da ita a bisa cinyarsa, sam ya manta da Mutanan dake falon, Momy cikin jin kunya ta mik'e ta fita daga falon, Ammi ma fita tayi tabi bayan Momy, Yaya Ahmad yace "To Love Birds hala ka manta da mutanan dake d'akin ne?" Dariya yayi yace "ba dole na manta daku ba, Pretty na tana kuka" Duk sai suka sanya dariya, nan Malam Hashim ya bashi wasu Magani da zai yi amfani dasu wanka da sha sai hayak'i, sannan kuma ya bashi shawarwari akan ya kula da ibadansa da kuma yawai ta karatun Al'Qur'ani da Azkar, Yaya Aryan yayi masa Godiya, nan suka yi musu sallama gaba d'aya suka tafi Gida. Yaya Aryan ya zauna gefen Basma yace "Babyna Allah yasa na samu lafiya kenan, kin ga yanzu bana jin komai in ina zauna gefenki" Hawaye ta share ta d'aura kanta bisa ciyarsa tace "Myn wallahi na firgita da lamarinka sosai, insha Allah ka warke hakan bazai sake faruwa ba". Nan dai suka samu suka karya, suka sake wanka, Aryan yayi amfani da magun-gunansa, sai suka dawo falo suka zauna suna hira suna soyewa abin gwanin sha'awa. *Bayan Kwana Biyu* Aryan ya warware sosai babu sauran wani damuwa, da dare ya siyowa Basma kayan ciye-ciye, suka baje a falo suka ci abinsu, bayan sun kammala ko wanne ya wuce d'aki domin yin shirin barci. Wani Rigan barci Basma ta d'auko, ta d'aga sama tana kallon rigan, jin-jina rigar take yi tana ayyana wa a ranta 'Anya zan iya sanyata kuwa?' Aryan daya jima da shigowa yana kallonta, yace "Dama kin mai data kin aje, dan kar ta bani wahala wajen cirewa, ki bari gobe in Allah ya kaimu sai ki sanya ki min kwanliya da ita da dare kafin mu kwanta" Da sauri ta juyo dan harta tsora ta, kunya ce ta rufeta akan maganan daya fad'a, maida rigan tayi ta ajiye. Arya yazo bayanta ya tsaya, d'aukarta yayi tsak ya ajeta bisa gado. *Nima daga nan nayo waje, na basu guri tare da yi musu saida safe.* *Washe Gari* Da misalin k'arfe shida na safe, Basma ce kwance bisa jikin Yaya Aryan yana lallashinta akan tayi barci, sai shagwab'a take zuba masa. Da kyar ya samu tayi barcin, sai ya gyara mata kwanciya ya ja mata bargo, ya sauka ya zauna gefen gado, dafe kansa yayi cike da mamakin yanda ya samu Basma a cikakken Budurwa, tambayan kansa yake "Dama Basma bata tara da Shureym ba kenan, lallai Allah kaine Mai cikakken iko, hak'ik'a babu wani Sarki sai Kai, kuma Kaine Majib'icin dukkan Al'amuranmu, Alhamdulillah da wannan babban kyauta daka bani, nasan ba wayauna bane ba kuma dubara na bane". Hawayen farin ciki ne ya sauka kuncinsa, ya shiga jero Addu'a tare da yiwa Allah kirari, saida ya karanto sunayen Allah D'ari ba d'aya, ya cika da salatin Annabi s.a.w, sai ya shafa. Basma ta bud'e ido tana kallonsa, ashe barcin nata bai yi nisa ba, ta taso a hankali ta rugumeshi ta baya tace "uhum, uhum, Myn yunwa nake ji ka bani abinci inci" Jawota yayi ya birkito ta akan jikinsa suna kallon juna, hura mata ido yayi yace "kina kallo na kamar zaki had'iye ni, ko d'an kunyan nan ma" runtse ido tayi yana dariya tace "kai Yaya Aryan ka daina cewa haka mana ba ina sonka bane, Ni dai ka bani abinci zanci" "tom bud'e ido muyi magana, me kike so in miki wanda zai saki farin ciki sosai, Hasken Rayuwata kin bani kyauta mafi girman kyauta wanda yazo min a bazata, Basma nayi mamakin samunki a cikakkiyar..." Bai k'arasa ba Basma ta had'e bakinsu guru d'aya saida suka yi tsayin minti biyar, kana ta zaro bakinta a nashi ta kalleshi ido cikin ido, tace "Myn Kai ne kad'ai nake so, kuma kaine Allah ya zub'a da zaka mallakeni, Yaya Aryan so nake muje Asibitoci, Gidan Marayu, da Gidan Kurkuku mu basu taimako da abinda Allah ya bamu, in kamin wannan kad'ai, zanyi farin ciki sosai mara yankewa". Rungumeta tayi tsam a jinshi tamkar zai maidata cikinsa, wani sabon So da K'aunarta ke k'ara ratsa zuciyarsa yana yad'uwa a duk sassan jikinsa. _*To Readers nasan yau dai na saku farin ciki*_☺ *Rahma Ce* [8/15, 8:45 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *36.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* *Bayan Mako D'aya* Aryan da Basma sun murmure sunyi kyau sun fara kumari, kwance suke bisa gado Aryan yace "My Queen nan da Mako guda Insha Allah zamu je Makkah muyi Umara tare da Honey Moon, amma fa na yin Ibada, sannan Gobe Insha Allah zamuje Asibitoci domin in cika miki alkwarinki" Kallonsa take cike da So da K'auna tace "Myn Godiya nake Allah ya k'ara maka Bud'i na Alkhairi yasa kafi haka" "Ameen My Pretty" sai ya rungumeta tare tayi mata sumba a goshinta. Daga nan kuma suka yi Addu'an barci, cikin minti goma Basma barci ya d'auketa. Shima ba dad'ewa barci ya kwashe shi. Saura kwana Uku su tafi Makkah, suka zagaye dangi tare da yi musu Sallama, har Kano sunje sun kwana d'aya, suka je Kaduna ma suka kwana washe gari suka dawo Abuja, a gidan Abba suka yini kowa na farin ciki da sauyawan su, sunyi kyau da k'iba gwanin sha'awa, sai dare suka koma Gida. Ranar da zasu tafi, harda su Momy suka yi musu rakiya, Basma har kuka tayi saboda kewar 'Yan uwanta. A cikin Jirgi Aryan ya rungumeta a jikinsa yana lalla shinta har barci ya d'auketa. *MAKKAH* Sun samu masauki a hotel d'in kusa da Harami, suka yi wanka a tare sannan suka ci Abinci, Basma ta shirya cikin jallabiya Brown mai ratsin fari a jiki babu kwalliya fuskarta amma tayi kyau, sannan ta shirya Aryan cikin doguwar jallabiya fara da farar hula, ta sanya masa turare, tana murmushi tace "My Aryan ina kishi ka fita domin gaskiya Mata karsu kallen min kai, dan ba k'aramin kyau kayi ba" Murmushi ya sakar mata yace "ai kema kinyi kyau sosai, ji yadda Jallabiyar ta amshi jikinki, nima gaskiya ina kishi dan haka Nik'af zaki sanya" Dariya ta sanya tace "Nik'af? bazan iya numfashi a ciki ba Allah kuwa, ban tab'a d'aurawa ba, Ni koda nayi Islamiyya bana sayawa sai dai ina sanya Hijab har k'asa da safa, amma bana iya sanya Nik'af, kuma ai fuskata ba kwalliya" Dariya shima yayi yace "Ai fuskarki ko ba kwalliya kyanki na nan, amma naji baza ki saka ba, sai dai zaki rik'a d'aure fuska kina bonewa" Dariya ta kyalkyale da shi ta fad'a jikinsa, rungumeta yayi kamar bazai sake ta ba sai da suka yi minti biyu a haka kana suka saki ajiyar zuciya a tare yace "kin ga tashi mu wuce masallaci" Ba musu ta mik'e suka wuce masallaci. Sun duk'ufa wajen yin Ibada da yiwa Allah Godiya bisa Ni'imomin da ya basu, sannan kuma da Addu'an Allah ya k'ara musu zaman lafiya acikin zamansu ya barsu tare har a Aljanna, ya saka wa iyayensu da gidansu Aljanna. Sun rokawa dukka nin Al'umma Musulmi da kuma samuwar zaman lafiya a K'asar mu Nigeria da dukkan Duniya gaba d'aya. Nima dai na taya su da "Ameen Ya Rabbi" *Bayan Mako Guda* Suka wuce *MADINAH* dan ziyaran Masallaci Monzon Allah S.A.W. Basma ta kira Hajiya Kaltum ta sanar mata da zuwansu, cikin farin ciki tace su tawo gidan ta. Anan suka samu masauki da kyakkyawan tarba. Bayan sun natsa, Basma ta kwashe labatinta tas ta bata Hajiya Kaltum, ba k'aramin mamaki tayi ba da labarinta, tace "Ashe Basma ke *YAR SHUGABA* Ce, lallai rauyuwa kenan, da ace da farko na rik'e ki da wulakanci da baza ki Ni meni ba, Naji dad'i sosai kuma Nagode" Nan dai suka cigaba da hira. A masallaci suke kwana danyin Ibada. Satin su biyu a Madinah suka shirya dawowa Makkah, Basma Check d'in kud'i ta rubutawa Hajiya Kaltum masu yawa wanda ni kaina ban san yawansu ba, ta bata ta ciresu a bank, dan cigaba da kasuwancin ta, Hajiya Kaltum tayi mata Godiya harda kuka, kaya ta had'a ma Basma na gyaran jiki, ta kuma had'a mata da guzirin wasu kayan. Cikin farin ciki da kewar juna suka baro Madinah, shima Aryan ya yaba sosai da Mutuncin Hajiya Kaltum. *MAKKAH* Sati guda suka k'ara a Makkah suka shirya dawowa k'asarmu Nigeria. Watan su guda kenan a K'asa Mai Tsarki, Basma sunyi Ibada sosai sunyi kuma Honey moon cikin Soyayya da K'aunar Juna. Haka suka tarkato zuwa K'asarmu Nigeria. *Nace "Allah yasa Basma ta kwaso guziri mai Albarka a Makkah".* Lol☺ *NIGERIA* Jirginsu k'arfe Biyar na yamma ya sauka, su Yaya Ahmad, Yaya Naufal, Meena, Deeja, Na'im da Anwar sune suka je tarbansu. Gidan Abba suka wuce gaba d'aya da kayansu, gida ya hautsine da murnan dawowarsu, a falon Abba duk suka zaune, Abba ya sauko suka gaishe shi, yayi musu barka da dawowa. Nan hira ta b'arke a tsakaninnsu sai gab da Sallan Magrib kowa ya watse, su Basma suka shiga d'aya daga cikin d'akin dake Falon Abba suka yi wanka suka sauya kaya. Bayan Sallan Isha'i a part d'in Abba suka ci Abinci duka mutanan gidan, Yaya Ahmad yace "In kun kimtsa zan mai daku gida" Yaya Aryan yace "Ai ni na kammala, dan na gaji ina buk'atar in kwanta da wuri" Yaya Ahmad yace "Basma ke fa?" Itama tace "Na gama" Yaya Aryan yace "Kayan tsaraban nan a barsu anan washe bari zamu zo, kowa a bashi tsarabansa". Sun shiga Mota sai suka fita gate, Yaya Ahmad ya wuce dasu k'ofar wani Gida dake kusa da gidan Abba, Aryan ya juyo da sauri yace "ina zaka kaimu kuma? Don Allah ka kaimu gida mana, muna buk'atar mu huta, ka bari Gobe in Allah ya kaimu in munzo sai mu shiga nan d'in" Dariya Yaya Ahmad yayi yace "mai kake ci na baka na zub, Ni dai ku zuba min ido kurum" Basma da Aryan suka had'a ido sai basu ce komai ba. Hon yayi Mai Gadi ya bud'e wangameman Gate, shiga yayi tare d'ayin kwana ya d'anyi tafiya kad'an, Manyan flat guda Uku ne a cikin Gidan, ko wanne da gab a tsakanin su, da kuma k'ofar shiga. Parking yayi a flat na tsakiya ya fito, key ya ciro a aljuhunsa ya bud'e k'ofar da zai sa dasu da cikin gidan yace "Ku fito mu shiga mana" Ba musu suka shiga, tafiya suka yi kad'an ya sadasu da k'ofar babban falon, ya bud'e k'ofar da key kamshin turaren wuta mai dad'i ya daki hancinsu, Yaya Ahmad ya shiga suma suka bishi a baya, kujerun Falon su na wancen gidan suka yi arba dashi, cikin mamaki Yaya Aryan yace "Ya naga kayanmu a nan kuma?" Yaya Ahmad ya zauna yana murmushi yace "nan kuka dawo, gaba d'aya kayanku dake wancen gidan mun dawo muku dashi nan, muma nan mu ka dawo, flat na farko na Naufal ne, na biyu naku ne, na uku kuma nawa ne, munk'i tarewa munce sai kun dawo kun fara shiga kafin mu dawo, Abba ya gida mana shi" Cikin farin ciki Basma ta mik'e ta shiga bin d'aku nan tana kallo, murna fal cikinta dan tsarin gidan yayi mata, katon falo ne sosai mai d'auke da d'akuna guda hud'u, ko wanne da toilet a ciki, an kuma sanya Furnitures a ciki, ga katon kitchen a falon da extra toilet. Daga cikin kitchen d'in akwai wani d'aki shine store d'insu, shak'e yake da kayan abinci da masarufi. A takaice gida ya tsaru yayi kyau sosai dan yaji kayan Alatu da more rayuwa. Yaya Aryan ya soma Godiya, Yaya Ahmad yace "Ka rik'e Godiyan ka, in ka bad'u da Abba kayi masa" ya mik'e yana Dariya, Yaya Aryan yayi masa rakiya, suna gabda barin falon Yaya Ahmad ya juyo yace "Basma akwai swimming pool ta baya, akwai kuma Lanbu in kin za gaya ta bayan gidan, za kiga k'aramar k'ofa da zai sadaki da lanbun" Yana gama fad'a bai jira mai zata ce ba ya fita. *Washe Gari* Sun had'u gaba d'aya a gidan Abba, suka yi masa Godiya da gidan da ya sauya musu tare dayi masa Addu'a sosai, sun raba tsaraba gaba d'aya, harda na Mutanan Kano da Kaduna sun ware musu. A ranar su Yaya Ahmad da Yaya Naufal suma suka tare a Gida jensu. *Da dare* Basma da Yaya Aryan suna zaune a falo, Basma tayi pillow da cinyansa yace mata "My Queen akwai wani shawara dana yanke, nasan kema zai miki dad'i in kika ji" Basma ta tattaro natauwarta tace "Ina jinka Myn" "Yauwa Babyna, dama so nake ki had'u dasu Meena ku bud'e wata organization na taimakon Al'umma, Nak'asassu, Almajirai, masu k'ara min k'arfi, marasa lafiya da dai tallafawa Talakan K'asarmu baki d'aya, ta wannan hanyar ne za muyi amfani da dukiyar da Allah ya bamu domin mu nima Lahiranmu da shi, kinga Ni dasu Yaya Ahmad sai mu rik'a jagorantar ku akan abin, amma me kika gani?" Wani farin ciki ne ya rufe ta, sai ta mik'e ta zauna tare da sumbatarshi a kumatu ta gyara zama tace "Yaya Aryan ka sani farin ciki sosai Wallahi, na dad'e ina tunanin wani hanya zanbi dan taimakon Al'umma A matsayina na *'YAR SHUGABA* dan haka wannan shawaran naka yayi, Gobe Insha Allah zan tattauna dasu Meena". " Masha Allah da kika amshi shawara ta, yanzu ki bari kar kiyi magana dasu, zan shirya Meeting a tsakaninmu gaba d'aya, sai mu had'u a anan don mu tattauna, amma kan lokacin zanyi magana da Yaya Ahmad, kuma sunan organization d'in *_QUEEN BASMA ('YAR SHUGABA) FOUNDATION_*. tsalle tayi ta fad'a jikinsa ta fara sumbatarshi ta ko ina, nan ta rikita shi gaba d'aya, d'aukarta yayi tana wucil-wucil da k'afa tare da kyalkyata Dariya, suka shiga cikin bed room d'in su. *_Ni Rahma nayi musu fatan Alkhairi, sai na nufi gidan Yaya Ahmad don naga wainar da suke toyawa._* *Rahma Ce* [8/15, 8:46 AM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *37.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* Yaya Ahmad yana zaune a bakin gado Deeja na zaune nesa dashi tana kuka sosai, cikin damuwa yace "Haba Deeja don Allah ki daina kukan nan haka, Allah ya bamu kyauta banga dalilin da zaisa ki zubar min da ciki ba, Plss Babyna kiyi hak'uri ki daina zancen cire cikin nan" D'agowa tayi ido jajir, cikin kuka tace "Yaya Ahmad yanzu fa Walid bai wuce wata biyar zuwa wata shida da haihuwa, ya zaka ce in bar cikin nan a jikina na, Walid fa zai walaha nima haka" "Ni banga wani illa a shayarwan Walid ba, muddun yana cin abinci, kuma cikin nan watan shi guda ne kinga da sauran lokacin har zai sha na kusan wata biyar fa, in kin yaye shi zan kaiwa Momy shi" Kuka take sosai tace "Nifa Allah zai an cire cikin nan" Cikin b'acin rai yace "Wallahi Khadija in kika kuskura kika cire min cikin nan sai nayi mugun sab'a miki" yana gama fad'an haka ya gyara kwanciyarsa ya kwanta ransa na masa zafi. Kuka take sosai, ganin kuka bazai fissheta ba ta mik'e ta Shiga bayi ta wanke fuska, ta dawo tayi shirin barci, ta kwanta da niyyar da sassafe zata je ta gaya wa su Ammi. *Washe Gari* Da misalin k'arfe takwas na safe, Deeja ce a tsaye a bakin k'ofa, Yaya Ahmad ya rufe d'aki yana ta masifa akan ba zata fita ba, ita kuma ta kafe saita fita, Waya ya ciro a aljihunsa ya kira Yaya Aryan, yana d'auka suka gaisa yace "Aryan dan Allah kuzo part d'inmu kaida Basma yanzu pls" bai jira mai zai ce ba ya kashe kiran. Cike da mamaki Aryan yake bama Basma labari, ba shiri suka fito suka nufi part d'insu Deeja. Nocking su kayi, ya bud'e musu suka shiga suka zauna, sun samu Deeja sai kuka take yi, Yaya Ahmad ya karanto musu abin da ke faruwa, Yaya Aryan ransa ya b'aci sosai cikin damuwa yace "Khadija ina kika koyi wannan halin, ba irin wannan tarbiyan Umma ta baki ba, Wallahi kin bani mamaki, Allah ya baki kyauta ki raina, wasu na can suna nima da kud'insu ido rufe amma Allah bai basu ba, karki zama mai budulci mana, babu abinda kika rasa a wajen Mijinki, in kuma dan Walid ne ai ke Doctor ce kinsan babu wani illa akan haka, karki sa in raina wayonki" Ya k'arasa maganar cikin hasala, Basma ta koma gefen Deeja ta dafa ta tace "Kawata kuma 'yar uwata, don Allah ki sanyawa ranki ruwan sanyi, in dai kula da Walid ne matsalan, na d'auki Alkhawarin zai dinga yini a hannu na, Nono kawai zan kawo shi ya sha, kuma ni zan siya masa abincin yara da ake dama musu kullun dare zan bashi ya rik'a kwana a wurina har ki yaye shi, amma in kin yarda" Deeja ta rungume Basma tace "Na yarda kuma na janye kud'urina zan raina cikin, dama ba wai dan bana so bane sai dan ina tausayin Walid" Nan dai su Yaya Aryan su kayi ta mata nasiha jikinta yayi sanyi, har sai da taji tsanar kanta akan b'atawa Yaya Ahmad rai da tayi tsakanin jiya da yau, tunda suka yi aure basu tab'a samum sab'ani ba, ta mik'e da gudu ta fad'a jikin Yaya Ahmad tana kuka tace "Ka yafe min Mijina wallahi sharrin shaid'an ne da yaso cin galaba a kaina, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba" Cikin farin ciki Yaya Ahmad yace "Ni banyi fushi dake ba, dama burina ki gane gaskiya, kuma Alhamdulillah tunda kin gane, na yafe miki Deeja na" "Nagode Mijina" sai ta mik'e tace "Basma taso muje mu had'a breakfast, tunda kunzo, nasan kuma baku d'aura komai ba k'ilama mu muka tadaku a barci" "A'a, mun tashi ban dai d'aura komai bane" sai ta mik'e suka shiga kitchen. Yaya Ahmad ya yiwa Yaya Aryan godiya sai suka cigaba da hira, anan Yaya Aryan ya sanar masa da zancen Organization da yake so su Basma suyi, Yaya Ahmad yayi na'am sosai da abun, kuma hakan ya sashi farin ciki sosai, sai suka yanke bayan sati biyu mai zuwa za suyi zaman Meeting, Aryan yace zai kira su Shureym da Jamal ya sanar musu da komai. Sai wajen k'arfe Goma suka kammala had'a breakfast d'in, suka jera a kafet d'in tsakiyar d'akin, nan suka baje suka yi hani'an, daga bisani Basma ta d'auki Walid a hannu ta suka wuce part d'in su dashi. *Bayan Sati Biyu* Su Aryan ne zaune a falonsu, gaba d'aya sun had'u don gudanar da Meeting d'in su. Yaya Ahmad ne yayi Sallama tare da gabatar da bayanai akan musabbabin had'uwarsu, Yaya Aryan ya d'aura da bayanai masu ma'ana, nan duk su Yaya Adam suka yi Na'am da lamarin. Suka yanke shawaran za suyi k'ok'arin Registration d'in k'ungiyar, sannan zasu sanar da Iyayansu akan abinda suka yanke, sun san tabbas zasu samu goyen baya sosai. Sun tsara Ranar taro k'arshen wata a Kaduna, a Babban filin Murtala Square dan K'addamar da k'ungiyar da kuma fara bada Tallafi ga Mahalarta Taron. Yaya Shureym yace "Na d'auki Alkwarin samo Ma'aikata Masu Ilimi wanda suke niman aiki, kuma Masu gaskiya har Mutane Talatin ta b'angaren Kano" "Yaya Jamal yace "Nima zan kawo Mutane Talatin ta b'angare na, kunga an samu Ma'aikata Sittin kenan, sai mu yanke musu Albashi Dubu d'ari-d'ari, sannan zamu ware Mutane Talatin wanda zasu rik'a bincika mana halin da Mutane suke ciki na ko wani Jaha, ta kafafen gidan TV, Radio, 'yan jarida, da kuma sarakuna, dakatai. Mai Anguwa da sauransu. Mutane Talatin kuma za su rik'a had'a mana bayanai ta na'urar Computer, a Manyan Office da zamu bud'e Kano, Abuja, Kaduna. A hankali zamu bud'e Offisoshi a sauran Jahohin" Cikin farin ciki suka tafa masa raf-raf-raf. Yaya Ahmad yace "Alhamdulillah wannan Abu yayi kyau, amma ya kamata a samu Mutane Ashirin wanda za su rik'a supplying kaya daga Kasuwanni, Abinci, kayan masarufi, sutura, keken guragu, keken d'inki dana sak'a, da duk kayan amfani wanda Mutane zasu amfana dashi, sannan a samu Mutane Goma Drivers wanda za su rik'a zirga-zirga a duk States d'in da muka shirya bada Tallafi" Nan ma suka yi mishi tafi, Yaya Aryan yace "Da fatan sunan Organization d'in yayi muku? *QUEEN BASMA ('YAR SHUGABA) FOUNDATION*" nan duk suka had'a baki da hakan yayi musu, domin Basma ta cancanci haka. Yaya Adam yace "Wato ni kun maidani sectary mai shigar da bayanai, to ga bayanan dana d'aukar mana gaba d'aya, amma karku manta akwai wanda tallafin kud'i suke nima, wasu kuma na karatu, wasu aiki, wasu Sana'a da dai sauransu, ya zamuyi dasu?". Yaya Ahmad yace "Wow, wannan magana taka yazo akan gab'a, akwai companoni da Abba yake k'ok'arin bud'ewa a ko wani Jaha a fad'in Nigeria, ina ganin zamu bada sanarwa a ko wani taro in za muyi, don masu niman aiki su turo applications d'in su ta email d'inmu, Ma'aikatan mu masu shigar da bayanai sune zasu rik'a dubawa suna zaban wanda suka can-canta" Yaya Aryan yace "Gaskiya ne, kuma zamu duba duk buk'atan Mutane sai muyi musu akan abinda suka raja'a akai, amma bada Sadakar Abinci wannan wajibi ne a duk taron da zamu yi sai mun bada shi" Nan dai suka k'are magana da yin Addu'a akan k'udirinsu. Sunyi Murna sosai gaba d'ayansu, suka ci suka sha da ciye-ciye,. Daga nan suka d'unguwa zuwa gidan Abba dan yi masa bayanin abubuwan da suka tattauna. Iyayan nasu sunyi matuk'ar murna, sun kuma goya musu baya wanda daga K'aramin organization ya koma Babba, don Abba yace za su sanya hannu a cikin lamarin, hatta makarantu za'a bud'e ta k'ark'ashin k'ungiyar, sannan kuma akwai Scholarships da zai bayar, zai tafi a k'ark'ashin *Queen Basma ('Year Shugaba) Foundation* donmin Tallafawa marasa k'arfi zuwa K'asashen waje don cigaba da karatunsu. Mu samman Abba ya k'ara yanke ranar Meeting gaba d'aya Family akan K'ungiyar, kafin k'addamar da taron k'ungiyar. Su Yaya Aryan sunyi murna sosai kamma Basma da ake komai dominta, sun k'ara Mutane Goma wanda za su gudanar da aiki Akan wanda zasu fita k'asar waje karatu in sun samu Scholarship. Ma'aikatan nasu sun zama guda d'ari kenan, Nan suka watse cikin farin ciki kowa ya koma gidansa. Yaya Aryan da Basma suna zaune a dinning suna cin abinci, Yaya Aryan yace "Babyna kinga yanda k'udurinmu yake ta bunk'asa ko?" Ta d'ago tare da kai loman abinci bakinta tace "uhum ai Yaya Aryan Yau farin ciki ne ya rufe ni, Alhamdulillah Ala Kullu Halin, babu abin da zancen sai Allah ya barmu tare, Myn kai Haske ne a rayuwata" Tasowa yayi ya rungumeta ta baya yace "Allah ya miki Albarka Babyna, ya bamu Zuri'a d'ayyiba yasa Aljanna ta zame mana makoma" Ta amsa da Ameen tare k'ank'ame hannunsa a k'irjinta. Amai ne taji ya taso mata ba shiri, da sauri ta toshe bakinta tana yunk'uri, da sauri ya d'uketa ya kaita toilet dake falo, sai da ta amayar da abincin da taci duka har sai da ta fara kakari babu abinda ke fita sai majina, nan da nan ta gala baita, d'auraye mata jiki yayi ya dawo da ita falo, d'aki ya shiga ya d'auko key mota, ya yafa mata gyale ya kama ta suka fito waje, suka shiga mota Mai Gadi ya bud'e musu Gate ya fice da gudu zuwa Asibiti. *Rahma Ce* [8/20, 9:15 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *38.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* Koda suka isa Asibiti direct d'akin Likita suka nufa, nan take aka fara mata tests da sauran gwaje-gwaje, Likita ya tabbatar musu tana d'auke da juna biyu harna tsawon wata biyu, Yaya Aryan farin ciki sosai ya kama shi, hatta ita kanta Basma farin ciki ya rufeta, nan take Likita ya rubuta musu Magani suka siya a pharmacy na Asibiti suka kamo hanyar Gida. Suna tafi bisa hanya Aryan tuk'i yake a hankali kwance cikin natsuwa, wani irin nishad'i suke ji mara misaltuwa, hannunsa ya d'aura kan cikinta, da sauri ta kalleshi sai ya kashe mata ido d'aya cikin wani salo na murya yace "Ki kula min da kanki da Unborn Baby d'inmu plss" Murmushi tayi ta gyara zama tace cikin shagwab'a "Uhum Ni fa nayi k'arama da Haihuwa dan bazan iya ba Haihuwa ba ance da wahala, tsoro nake ji" Waro ido waje yayi yace "To me kike nufi" "Ni dai tsoro nake ji amma ina son cikin sosai" Dariya yayi yana buga sitiyarin mota yace "wow My Basma rikici, bafa wani wahala da kinyi nishi shikenan fa" Hararan wasa tayi masa tace "ai su Meena sun bani labarin wahalan da suka sha wajen Haihuwa, ni dai ka tayani da Addu'a kar ya bani wuya Myn" ta k'arasa maganar cikin shagwab'a. Shafa gefen kumatunta yayi yace "Babyna kullun cikin Addu'a nake miki karki damu, insha Allah zaki Haihu lafiya dashi" murmushi tayi ta amsa da "Ameen". a haka suka isa gida cike da farin ciki. *Bayan Kwana Biyu* Suna kwance Basma tayi pillow da hannunsa tace "Baby ina so karka gayawa kowa ina da ciki, nafi so su ganshi in ya fito" "Saboda me" ya jefa mata tambaya. "Kunya na keji" "Uhum su kunya ko, in ya fito zanga yanda za kiyi" Mirginawa tayi ta kwanji samansa, ido cikin ido suke kallon juna sai ya sakar mata Murmushi, murgud'a masa baki tayi saiya sanya hannu ya kama bakin, kukan shagwab'a ta fara sai ya saki yana dariya, tace "Baby ina son shan agwaluma" "What, ya fad'a da k'arfi, Na manta shi ma" kuka ta shiga rerawa ita lallai fa zata sha agwaluma, marairaice fuska yayi yace "Baby ina zan sameshi bama lokacinsa bane fa" Tashi tayi ta zauna ta fara tsotsan bayan hannunta, a dole tayi fushi, tashi yayi ya zauna shima ya jawota jikinshi, hab'arta ya d'ago yace "Babyna ki fad'i wani abun wanda kika san bazan sha wuyan nima ba pls" murgud'a masa baki tayi tace "Farar k'asa da yalo" Ajiyar zuciya ya saki ya mata kiss a goshi sannan ya sauka bisa gadon yace "zan fita yanzu na nimo miki, inna siya zan bama driver ya kawo miki domin yau ina da aiki sosai a office" Bata ce masa kala ba ya shige toilet dan ya watsa ruwa, itama mik'ewa tayi tabi bayanshi, ta iske shi a bawo yana wanka zuwa tayi itama ta shige ciki, dole ya aje nashi wankan yayi mata sannan ya d'aura mata towel ta fito, Murmushi yayi yace 'Wannan unborn Baby ya sa Basma rikici, in da banyi mata wankan ba ta fara kuka' duk a zuciya yake wannan maganar. Bayan ya idar da nashi wankan ya fito ya taddata ta sanya atamfa d'inkin riga da sket, tayi makeup kamar ba ita ba tayi kyau sosai, tsayawa yayi yana kallonta ta juyo fuska tana dariya tace "Ya aka yi ne ka zuba min ido ko na sauya maka ne?" girgiza kai kawai yayi ya soma shiryawa, dama ta ciro masa kayan da zai sanya, k'ananun kaya ne da suit, zama yayi ta shirya shi, ta sanya masa riga da wando ta d'aure masa belt ta kuma yi sitokin d'insa, ya d'aura neck tie ta santa masa suit, turarukan sa ta shiga fesa masa har saida ya amshe yana fad'an "Ya isa haka ko so kike ki k'arar mini Madam rikici" Murgud'a baki tayi ta matsa ta d'auko gyalenta da hand bag, ta sanya takalmi mai tudu ta d'aura igiyan ta d'auke key motan Yaya Aryan tace "Muje aikin ko" Sakin baki yayi yana kallonta, murmushi ta sakar masa ta kanne masa ido d'aya tare da kama hannunsa tana jaaa, suka fito falo masu aikinta ta basu oder duk abinda take so suyi mata, kana ta cigaba da Jan hannunsa suka fice. Bud'e motan tayi ta zauna mazaunin driver bai iya furta komai ba ya shiga gefenta ya zauna ta sanya key ta tada mota ta fice abinta. Lumshe ido yayi ya kwanatar da kanshi a bayan seat, saida su kayi tafiya mai nisa, tayi parking juyowa tayi a shagwab'e tace "Baby ko baka so in raka ka zuwa wurin aikin?" Juyowa yayi ya kalleta sai ya d'aure fuska cikin sigar wasa baice komai ba, hawaye ne ya ciko idonta cikin rawar murya tace "Don Allah ka yafe min kar fushinka ya in kasance cikin tsinuwar Allah, bana fatan in b'ata maka rai" Hannunta ya kamo yace "Waye yace kin min laifi? nasan fa duk Baby d'inmu yasa ki wannan aiki saboda baya son Momyn shi da Abbanshi su rabu" ya k'arasa maganar yana dariya tare da lakace hancinta, itama dariya ta saki ta tada mota suka wuce wurin aikinsa. Yau dai Basma da Aryan a tare suka yi aiki sai yamma lis suka tashi, kasuwa suka wuce sai da Aryan ya siya mata, farar kasa, yalo, da agwaluma harma da magarya duk ya had'a ya siya da yawa. Cike da farin ciki suka dawo Gida. *Karshen Wata* Ana gobe taronsu gaba d'aya Matasan Maza da Matansu suka had'u a Kaduna gidan Dady suka sauka, shirye-shirye suke wanda a lokacin sun gama samun Ma'aikata sun bud'e manyan office a Kaduna, Kano, Abuja. A Ranar taro anko suka yi Maza fararen shadda Matan kuma atamfa mai ratsin yallow, green da fari. Filin Murtala Square ya cika da mutane domin wannan taro na k'addamar da k'ungiyar *QUEEN BASMA ('YAR SHUGABA) FOUNDATION.* Manyan Mutane Mata da Maza sun halarta da yake abin na 'ya'yan Manya ne, hatta Dady yaje wurin da muk'arabansa, Mai Martaba Sarki shima yaje da Sarkin Zaria ya harta, Abba bai samu halarta ba saboda yayi tafiya, sunyi taro cikin farin ciki da lumana, an baza jami'an tsaro har aka gama babu wani tashin hankali ko hatsaniya, sun raba abubuwa da dama kama daga Abinci, Suturu, Kud'ad'e ga talakawa da nak'asassu, ba k'aramin farin ciki suka sanya a zuk'atan Mutane ba, kowa ya tafi Gidansa yana mai sanya musu Albarka. Bayan komai ya lafa duk suka koma gidan Dady, suka had'a k'aramin walima a gidan da yamma, sun ci sun sha tare da sada hiran zumunci. Washe Gari ko wanne ya kama hanyar garinsu. *Da Dare* Bayan Sallan Isha'i, Basma na zaune a falo tayi dirshen a k'asan kafet tana cin tuwon Dawa miyar Kub'ewa d'anya, Aryan na gefenta yana cin farfesun kayan ciki tare da jelof din cus-cus wanda yaji kayan lanbu. Basma sai surutu take yi tana cin abinci, kuma wannan ba halinta bane, Yaya Aryan tun yana amsa mata sai yayi banza da ita ya daina amsa mata, d'ago kai tayi ta kalleshi tace "Myn shine ka shareni ko?" "To Basma me zance miki, gaba d'aya kin sauya hali, wannan cikin ya sanya miki dabi'u da ba naki ba, cin abinci kike kina surutu, ta yaya abincin zaiyi miki Albarka?" Marairaice fuska tayi tace "To na bari" "Gwara dai ki bari, in ba so kike muyi fad'a ba, kuma ki ci a nutse dan babu mai kwace miki" Ai bai rufe baki ba ta mik'e a zuciye zata bar wurin, da sauri ya kama hannunsa ya soma lallashinta, da kyar ya samu ta sakko, zaman da zata yi ne ya lura da bayan rigarta ya baci da jini, da k'arfi yace "Babyna me ya kawo jini a jikin ki?" A tsorace ta jawo rigan ta gani, kuka ta fara tana fad'an "Shikenan Yaya Aryan cikin ya zube, na bani" A firgice Aryan ya d'auketa ya fice da ita da gudu, mota ya sanya ta ya shiga, a sukwane yabar gidan. Yaya Ahmad ya fito daga part d'in su zai fita, sai yaga fitan Yaya Aryan daga gidan a guje, shima da sauri ya shiga tashi motar ya rufa musu baya a sittin. *A Asibiti* D'akin gaggawa aka shigar da ita, a lokacin ciwon mara ya fara damunta, Addu'a take tana ambaton Allah. A waje kuma Yaya Ahmad ya cimma Yaya Aryan yana tambayan sa abinda ya faru, cikin damuwa Aryan ya labarta masa a takaice, mamaki ya kama Yaya Ahmad yace "Dama tana da juna biyu kenan?" Aryan ya girgiza masa kai alaman Eh. Likita yayi k'ok'ari sosai wajen tsaida jinin, sannan ya d'aura mata drip barci mai nauyi ya d'auketa. Likita ya fito Yaya Aryan ya tare shi, hannunsa ya kama suka wuce office d'insa, Yaya Ahmad yana biye dasu. Duk suka zauna suna sauraren Likita yace "Gaskiya da kyar muka tsawo kan matsalan amma Alhamdulillah cikin bai fita ba, dan haka dole a kikaye dan Mahaifarta ba tada k'arfi, zata samu bed rest, komai yi mata za'ayi game da aikin gida, sannan a kiyaye yawan zirga-zirga da ita, ya zama na ta rik'a natsuwa wuri d'aya har sai cikin ya kai wata biyar daga nan ta fita daga wannan risk d'in" Ajiyar Zuciya Yaya Aryan ya saki tare da godewa Allah, Yaya Ahmad yace "Ina ganin fa jugu-jugun taron jiyan nan shine ya haifar mata da wannan matsalan" dan haka sai mu kiyaye fitanta ko ka maida ta gida wurin su Ammi" Da sauri Aryan ya d'ago kai yace "A'a baza ta ko ina ba zan kula da ita" Yaya Ahmad ya dafa shi yana dariya, kunya ce ya kama shi, ya manta shaf Yaya Ahmad Yayan Basma ne, nan Doctor ya rubuta Magani ya basu sallama inta farka su tafi gida. Sai k'arfe sha d'aya na dare ta farka, cikinta ta shafa ta juyo ta kalli Yaya Aryan tace "Ya fita ko?" tana zubar da kwalla, murmushi yayi mata tare da matsawa kusa da ita yace "Babynmu yana nan yace ba zai sa Momy da Abbanshi kuka ba" Murmushi tayi, ya taimaka mata ta zauna, sai a sannan ne ta lura da Yaya Ahmad a wurin kunya ce ta rufeta tace "Au ashe Yaya Ahmad kazo?" Dariya yayi yace "Ina zaki san ina wurin bacin ta Unborn Baby d'inki kike" Rufe ido tayi da tafin hannunta tana dariya. Gida suka wuce. Tun daga ranar kowa yasan Basma tana da juna biyu, aiki kuma bata komai sai dai taci ta kwanta, tayi b'ul-b'ul da kyau, soyayya kuma tsakanin Basma da Aryan sai abinda yayi gaba. A haka har cikinta ya kai wata tara, cikin yayi k'ato ta kubbura, Haihuwa ko yau ko gobe, Yaya Aryan yak'i yarda Basma ta koma gida shike jikilan komai nata. *Rahma Ce* [8/20, 9:16 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *39.* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* *Cikin Basma Wata Tara Da Sati Biyu* Basma ce a cikin kitchen tana zuba Peppe Meat a plet, fitowa tayi tana jan k'afa da alama cikinta yayi mata nauyi sosai, zama tayi akan kushim ta fara ci tare da cuna baki alamar yaji ya dame ta, haka tayi ta ci tana gumi tare da shan Gwaba juice, haka ta cinye tas tare da lashe hannu, da alama bai isheta ba sai ta kwalawa d'aya daga cikin masu aikinta kira "Uwale, Uwale" da sassarfa ta fito ta risina tace "Hajiya gani" "Yauwa k'aromin peppe Meat d'in nan, ki zuba min da yawa sannan ki d'auko min goran ruwa da cup ki kawo min" Jiki na rawa Uwale ta wuce kitchen ta kawo mata gaba d'aya duk abinda take so, zama ta gyara ta cigaba da cin kayanta tanaci tana shan ruwa saboda bala'in yaji data zuba a ciki. Sallaman su Meena da Deeja ne ya katse ta, ta amsa musu, zama duk suka yi suna yi mata tsiya "kullun in muka shigo sai mun ganki da wani abun kina ci, acici mala'kan tauna" Meena ce take fad'an haka. Dariya kawai tayi musu ta cigaba da cin abin ta, hira suke sosai suna tattaunawa akan taron daya gudana a garin Katsina wanda Basma bata samu zuwa ba, hak'ik'a taron ya k'ayatar kuma sun tattauna akan Matsalolin masu yima Yara k'anana fyad'e, Basma tace Wallahi nayi missing taron kuma ba haka naso ba" Deeja ta lura da yanda Basma take yatsine fuska cikin kulawa tace "K'alli yadai naga tun d'azu kina ta yamutse fuska kodai abin yazo ne?" Murmushi kawai tayi tace "inda yazo kya ganni ina d'irkan abinci" Dariya suka yi mata, Meena ta mik'e tace "Kinga bari naje na shirya Yaya Naufal ya kusa shigowa kunsan da an sakko Sallan Juma'a suke dawowa" Deeja ma mik'ewa tayi tace "Hakane 'Yar Uwa, nima bari naje na shirya kinsan yau akwai yini a gidan Abba bayan Sallan La'asar" Nan suka yiwa Basma Sallama, sai tace "Uhum masu Maza to sai ku tafi kan k'uda ya riga ku" Dariya suka kwashe dashi suka fita. Basma ji tayi cikin ta yayi mata hak'e-hak'e da kar take numfashi, gyara zama tayi ta jingina jikin kushim, a fili tace "Ya Rabb ka rabani lafiya da abinda ke cikin nan, kayi masa albarka da kyakkyawan Albarkanka, Ameen, yau dai cikin nan ya d'aure min sosai to Allah gani gareka" Bata rufe baki ba cikin ya fara tsingulinta, da sauri ta mik'e tana jan k'afa ta shiga d'aki ta d'auko key na Motanta, fitowa tayi ta bama masu aikinta order akan abinda take so suyi mata, sai ta fita tana nishi, gaba d'aya ciwon mara ya soma damunta, driver ta kira yazo ta mik'a masa key Motarta tace "Kaini Asibiti" ba musu ya amsa cikin girmamawa. Kafin sukai Asibiti ciwo ya tsananta salati kawai take yi, da sauri Driver ya kira Nurses suka zo suka shiga da Basma cikin Asibiti d'akin Haihuwa suka wuce da ita, Nurse Sa'a ta dubata tana 8cm, da alama ta jima tana nakud'ar a tsaitsaye inji Nurse d'in, Basma nak'uda ta taso sosai Aryan take kira tare da Abbanta, hawaye ya na zuba, Addu'a take da niman sassauci a wurin Allah. Yaya Aryan yana gun Aiki ji yayi Kansa ya sara masa, gabansa ne ya fad'i, a lifi ya furta Basma, da sauri ya mik'e yabar abinda ya keyi ya soma had'a kayansa, jaka ya d'auka ya sanya hularsa ya fito, Massinger ne yace "Yallab'ai akwai masu jiranka suna wurin Alhaji Naufal" Yana tafiya yace "kace su dawo ranar Monday wani uziri ya taso min". Mota ya shige ya kamo hanyar gida, wayar Basma yaketa kira amma bata d'auka ba, Basma a gida ta bar wayan, hankinsa ne ya kuma tashi, wayar Deeja ya kira ya tambayeta Basma tace "Ban jima da fitowa daga part d'inku ba ina ganin tayi barci ne" Cikin damuwa yace "ok" ya kashe wayar. Basma ta cika 10cm haihuwa ta taso amai ta fara yi, haihuwarta mai fayar baki ne, amai take sosai tana yunk'uri, bayan ta gama aman sai nak'udar ta lafa a hankali barci ya fara fizgarta, hutun minti biyar tayi nak'udar ya dawo, cikin ikwan Allah bata k'ara minti goma ba ta haifo d'anta Namiji mai kama da Aryan sak. Yaron kato sai ihu yake Hamdala Basma ta shiga jerowa da yiwa Allah Tasbihi. Yaya Aryan ya shiga kan layinsu kenan wayarsa ya d'auki k'ara, Likintansu ne ya kira shi ya d'auka suka gaisa sai Likita yace "Madam tazo ita kad'ai Asibiti ba tare da kowa ba sai Driver, yanzu haka tana Labour Room, muna so a kawo kayan Baby" Da k'arfi Aryan yace "ta Haihuwa ne?" Likita yace "A'a tana gab, ku kawo kayan da sauri" Godiya Yaya Aryan yayi masa, sai ya juya akalan Motansa ya nufi Asibiti, wayar Deeja ya kira yace mata "Ki shiga part d'inmu ki had'o kayan Baby, da wanda Basma zata canza, da duk kayan da ake buk'ata a Asibiti sai ku tawo" bai jira amsar da zata bashi ba ya kashe. Farin ciki ne ya rufe Deeja ta fito da sauri, Allah yasa ta idar da Sallah kenan tasa kaya. Had'a kayan tayi ta shiga wajen Meena tare suka tawo suka kira su Momy a waya suka sanar dasu. Basma an ciro Mahaifa an gyara mata jiki, kaya ya rage a kawo ta sauya, Baby ma haka, Yaya Aryan a sittin ya shiga d'akin Haihuwar bai jira an bashi izini ba, Nurse Sa'a ta dakatar dashi "Dan Allah Kaje waje mu gama tukuna saika shigo" Ko saurarenta bai yi ba ya isa wurin Basma ya kama hannunta gam yace cikin muryan tausayawa "Babyna Allah ya saukeki lafiya" tare da matsar kwalla. Murmushi Basma tayi sai ta kai hannunsa wajen cikinta tace "Babynmu baya cikina yanzu dan ya fito" ware ido yayi ya shiga waige-waige, hango gadon Yaron yayi ya isa wurin, ya ganci a cikin towel an k'udun-dune shi, hannunsa na rawa ya kai ya d'auko shi, farin ciki ya sanya shi fitan kwalla, ya shiga jero masa Addu'a tare da godewa Allah, Basma na kallonsu tana murmushin farin ciki cike da so da k'aunar su. Nurse Sa'a ce ta amshi Yaron don su sanya masa kayansa da su Deeja suka kawo, Basma ma sanya kayanta tayi Aryan ya d'auketa cak ya kaita d'akin hutawa na masu Haihuwa. Meena da Deeja suka rufa musu baya, dai-dai lokacin Ammi tazo tabi bayansu. Momy tak'i zuwa saboda kunyar 'Yar fari. *Bayan Sallan La'asar* Aka basu Sallama suka wuce gidan Abba gaba d'aya. A side d'in Ammi Basma suka sauka tare da Babynsu. Nan fa kan ace miye gida ya soma cika da 'yan barka sunata zuwa, Anty Husnah ma da sauri tazo gidan dan ganin idon Basma an zama Mama, tasha tsiya wurin su Deeja, amma kuma sun yabama k'ok'arinta da juriya data iya kai kanta Asibiti. Abba yayi Murna da ganin jikinsa ya amsa Yaron yayi masa Addu'a tare da hud'uba. Duk sun sanar da dangi wanda suke nesa, da yawansu sun d'aura d'amaran zuwa Abuja a washe gari, kuma in suka zo sai anyi suna zasu tafi. Leema kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Abuja don Murna, haka ma Safeena ta k'osa Gari ya waye su kamo hanya, Shureym sai da yaji wani iri aransa yace "Da yanzu wannan Yaron nawa ne, Allah Sarki, na amshi wannan k'addaran tawa, ka yafe min dukkan kuskuran dana aikata". Nima na tayaka da Ameen. *Ranar Suna* Yaro yaci sunan *Aliyu* Mahaifinsu Aryan, Suna kiransa da *Hydar*, ba k'aramin shagali suka shirya ba, wannan hidima ya tara Manyan Mutane Sarakuna da Manyan 'Yan Kasuwa. An shirya k'ayataccen Walima bayan Sallan Isha'i a babban hol dake Abuja, hatta Abba dasu Mai Martaba, Dady duk sunje wurin, har Momy da take kunyar 'yar fari taje wurin, su Kaka Ma'u, Inna, Malam kawai suka bari a gidan, Wata Babbar Malama suka gayyata tazo ta bada Fatawa akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci*. Da farko Tarbiyyan Yara sun rataya akan Uba da Uwa wanda aka samu wannan D'a daga Jikinsu. Uba dole ne ya samarwa 'Ya'yansa Uwa Tagari haka itama Uwa dole ne ta samawa 'Ya'yanta Uba Nagari, Tarbiyya yana farawa ne tun daga ginshik'in Neman Aure. Ma'aurata dole ne a yayin saduwa suyi Addu'a kamar yanda Monzon Allah s.a.w ya koyar damu kafin iyaye su kaiga saduwar Aure, kunga kenan an fara samar da D'an ta kyakkyawa hanya, daga nan lokacin da aka samu cikin wannan d'a, Uwa dole ne ta zama mai hak'uri tare ya yawaita Addu'a don samun d'a Nagari, Uba kaima yana da kyau ka sanya ido ka bata kulawa sosai tare da Addu'a har Allah ya sauketa Lafiya. Wasu Iyayen sukan fara da tsinewa ciki tun kan yazo Duniya, sai kuji Uwa na cewa 'Wannan shegen cikin ya isheni da muntsili' 'Na k'osa wannan jarababen cikin nan ya fito na huta' Wannan cikin kaza-kaza, tun d'a na ciki wata Uwar ke fara lalata shi kafin ya fito Duniya, dan haka jan kunne garemu Mata Ku kula sosai yayin irin wannan halin da kuka tsinci kanku, mugun furuci yana lalata Tarbiyyar Yaro, ki zama mai hak'uri da juriya domin a wannan lokacin kina cikin wani jarabawa ne mai dinbin lada, ki zama mai yin Addu'a da niman sauk'i a wurin Allah yayin da cikin ya dame ki. Sannan bayan an haifi Yaro, Uba zai masa kiran Sallah da hud'uba da sunansa, a wannan lokacin d'a zai hanasu barci wani Uban yaita tsaki yana zage-zage, wata Uwar kuma ma kaji tace 'wane kaza ka cika shegen kuka ai Allah wadaran wannan rikici naka', to wallahi dole sai mun kiyaye fidda mugayen kalami akan Yaranmu. Duk abinda Uwa zata yi dole sai kin sanya ido da hak'uri da kuma Juriya, kuma dole sai kin fara gyara halayyarki kafin ki fara kafa tubalin Tarbiyyan Yaranki. Domin wasu Yaran yayin tasowarsu sukan fara koyan wasu halayya da Uwarsu keyi, koda ace mara kyaune a ganinsu mai kyaune tunda sun ga Uwarsu tayi. Dan haka dole mu Iyaye Mata muna sanya ido a kan Yaranmu domin Mune Makarantar farko ga Yaranmu. Sannan da zarar yaro ya taso nuna masa yin Ibada akan lokaci, koyar dashi Addu'an safe da maraice, na shiga bayi, fita gida da sauran Azkar, kasance mai jansu a jiki kina tunatar dasu Tsoron Allah, ki sanyawa d'anki Tak'awa da kuma Tauhidi, nuna masa yanda Azabar Allah yake a ranar gobe k'iyama in suka sab'a masa, ki tsawatar musu in suna wasa da Sallah, ki jasu a jikinki a nan ne zaki rik'a jin dukkan matsalolin su, rik'a duba takardunsu na makaranta kina ganin abinda yara ke ciki game da karatunsu. Kaima Uba ka ja 'ya'yanka a jikinka banda d'aure fuska, ko daka dawo daga aiki su rik'a gudu suna tsoron fad'anka, zauna dasu tamkar abokanka kayi wasa dasu ka tunatar dasu hakk'ok'in Allah wanda ya rayata akan su. Ka sanya su a makaranta masu kyau, karka zama me kyashin biya musu kud'in makaranta. Sannan mu sani yawan duka baya shirya yaro sai dai ya kangarar dashi, mu rik'a musu fad'a da Nasiha, karmu gaji. Insha Allah duk abinda ya gani na sabon Allah zai guje shi, zai kasance mai gudun B'acin ranku, zai zama kamili nagari abin sha'awa gun kowa, Mutane za su rik'a kwatantaku cikin sawun Iyaye Nagari, haka yaron za'a rik'a kwatance dashi a cikin 'Ya'ya Nagari. Allah ya bamu ikwan Tarbiyyan tar da Yaranmu bisa tafarkin Al-Qur'ni da Sunnah. Ameen ya Rabb Sai k'arfe Goma na dare aka gama wannan Walima, kowa ya koma Gida lafiya. Walimar ya burge Mutane sosai game da yanda Malamar ta bada bayani akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci*. Anan Mami ta gane cewa tayi kuskure wajen Tarbiyyan Shureym, ta kuma d'auki Alkhawarin niman gafaransa, da gyara kuskurenta akan jikokinta. *Bayan Wata Guda* Deeja itama ta sullub'o 'Yarta Mace kyakkyawa mai kama da Basma, ranar suna taci sunan Umma 'Aisha'. Kamar yanda aka yi taron sunan Hydar haka akayi na Aisha, an shirya Walima kyatacce akan *Tarbiyyan Yara A Musulunci* Anyi taro lafiya aka watse lafiya. Inna itace ta zaunawa Deeja har zuwa tayi Arba'in. *Rahma Ce* [8/20, 9:17 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA👑* _page_ *40.* *_Final page_* _Na_ *_Rahma Kabir✍🏾_* *Bayan Kammala Wankan Jego* Basma ta gama wanka, zaune take tasha kwaliya cikin d'inkin riga da sket na atamfa, Baby Hydar yana gefenta ta kwantar dashi, wayarta ce a hannunta tana latsawa da alama charting take yi, Sallaman Yaya Aryan shine ya katseta ta d'ago cikin murmushi tare da kallon so ta amsa masa, isa yayi kusa da ita ya zauna tare da rausayar da kai gefe yace "Babyna kinga yanda ki kayi kyau kuwa, kamar Baby Hydar bai fita a jikinki ba, meye sirrin?" Murmushi tayi wanda ya bayyana farin cikin ta tace "Myn bafa komai, Ni ce dai yanda ka sanni sai dai fa na samu kyakkyawan kulawa wurin Ammi dan haka ita zaka tambaya sirrin" Hararan wasa yayi mata yace "Kinsan dai babu wannan tsakanina da Ammi, a bakinki ya kamata naji komai, yanzu dai mu bar wannan maganar yaushe zaki dawo gidanmu, ina missing d'inki Baby love, da kyar nake iya barci fa" ya k'arasa maganar cikin muryar tausayi. Kanne masa ido d'aya tayi tace "Uhum Myn nifa sai nayi wata biyu zan dawo" Ido ya zaro waje yama kasa magana, da gudu ta mik'e ta bar wurin tana kwasan dariya, girgiza kai yayi ya d'auki Baby Hydar yabi bayanta, d'akinta ya sameta ya kwanar da Baby Hydar ya matsa wurin ta yace "Babyna ko so kike in shiga wani hali?" D'ago fuska tayi tana kallonshi cikin ido tace "Baby nima na kosa na dawo gareka amma bansan ya zanyi ba, bazan iya sanar wa Ammi hakan ba, ka k'ara hak'uri suma sunsan ya kamata na koma karka damu" Ajiyar zuciya ya saki tare da busa iska mai zafi yace "ki shirya zanzo gobe Insha Allah zamu fita" Ido ta zaro waje tace "ina zamu kuma Myn? kunya nakeji" Murmushi yayi yace "Hotel zamu domin ina da buk'atar Babyna in ba so take in fara biye-biye ba" Da sauri ta had'e bakinta da nashi domin bata son ya k'arasa maganar, sai da suka d'auki minti goma kana ta janye jikinta tare da sauke ajiyar zuciya, cikin kasalan murya tace "Myn karka k'ara furta kalman da ya fito a bikinka domin kanada ni, Insha Allah zan kasance da kai a koda yau ba zan gaji da kai ba tunda nima inda buk'atarka, zan shirya mu fita amma gidanmu zamu ba Hotel ba, domin in samar maka farin ciki sweet babyna" saita manna masa kiss a goshinsa ta mik'e, tana mai cewa "bari na kawo maka abinci dan nasan da wiya in kaci na rana". Bud"e k'ofar da zata yi ne taci karo da Ammi, Ammi tace "Ina zaki kike sauri haka?" Sosa k'eya tayi tace "Abinci zan kawowa Yaya Aryan" "Ok ga wannan ki shanye shi zuwa anjima da yamma" ta amsa goran tana godiya. *Bayan Sallan La'asar* Ammi ta sameta a d'aki tace "Basma je kiyi wa Momynki Sallama yau zaki koma gida, da fatan kin gama shirya kayanki?" "Eh Ammi na kammala bayan Yaya Aryan ya tafi" "To madalla" saita fita. Tana isa part d'in Momy ta sameta zaune saman kushim tana karanta wani Jarida, sallaman da tayi ne yasa ta aje Jaridar a gefe ta amsa mata, Basma ta isa gefenta ta zauna tare da kama hannunta tace "Momyna sannu da hutawa" "Yauwa My Basma" "Nazo muyi sallama ne Ammi tace yau zan koma gida" ta k'arasa maganar cike da shagwab'a. Hararan wasa ta mata tace "Basma sai yaushe zaki girma da yin shagwab'a ne?" Murmushi tayi ta langwab'ar da kai gefe tace "Uhum Momy ina dake fa kinga kuwa bazan daina shagwab'a ba, ga Abba da Ammi, ga Dady da Ummin kd dasu Kaka Ma'u duk inada ku fa" Momy tayi dariya tare da lakace hancinta tace "Ki dai ragewa su Hydar" Kunya ya rufeta ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi tare da wasa da yatsun hannunta. Momy ta gyara zama tare da kiran sunan ta, Basma ta d'ago taga babu alamar wasa a tattare da Momy, natsuwarta ta tattaro tace "Na'am Momy" Momy tace "Basma ina son in miki tuni akan hakk'in Mijinki dake kanki, Mata da dama wasu na kuskure akan da zarar Mace ta haihu saita jingine buk'atun Mijinta ta kama na Yaronta kuma wannan ba dai-dai bane, hakk'in Miji shine farko kafin hakk'in 'Ya'ya, A Ranar Gobe K'iyama Allah yana fara tambayan hakk'in Miji ne kafin hakk'in 'Ya'ya, sannan Aljannarki yana k'afar Mijinki inya d'aga ki shiga Aljanna, in kuma ya danne ki auka wuta. Allah yayi mana tsari da wuta Ameen. Dan haka sai munyi karatun tanatsu sosai, Mata da dama suna jingine need d'in Mijinsu da zarar sun Haihu, wata ma ba tada lokacin wani hira da Miji ko girka masa abinci, kullun itace hidimar yaranta ba ruwanta da farin cikin Mijinta ko b'acin ransa, wata ma saboda d'anta saita hana miji hakk'insa, wai adole ita mai d'a, to wallahi mu hankalta Musani shi Miji yanada matuk'ar mahimmanci dole ne mu rik'a kula dasu muna basu lokutanmu domin samun da cewa. Ki ware lokutanki kina tsarawa kanki ko wanne ki fita hakk'insa, Miji da kuma Yaranki, su Kansu mazan suna tausayawa Matan akan wasu hidimomin gidan har suke tayasu ma. "Maza da dama suna fuskanta k'alubale a wurin wasu Matan nasu da zarar Mace ta haihu, ita kullun ba data lokacinsa, wata ma ta daina yin kwalliya, wata kuma tsafta ma ta rage, wata kuma yin abinci ma sai dole, babu wani kyale kyale da Miji zai gani a wurin Matarsa da sai sashi sha'awarta. Da ance wance kaza kin daina abubuwa kaza kin sauya, saita ce hidimar Yara sune suke hanata. Hakan kesa Mazan suna sha'awar Matan dake waje masu kwalliya da kyale-kyale, da ya samu mai sonsa saiki fara damuwa Mijinki ya sauya miki, ke kaza-kaza, bacin kece kika bashi k'ofar yin hakan. Shi dai haihuwa bazai sanya ki zama k'azama ba ko ki zama mara kwalliya da gyaran jiki ba, sai in dama kin sanyawa ranki sangarci, lalaci, son jiki da kuma rashin tunani, dan haka Mata mu kula sosai, dan da wayan matsalolin da wasummu suke fuskanta a gidan aure muke fara bada k'ofar aukuwarsa. Namiji kamar Yaro yake jin kansa, yana buk'atar kulawa da tarairaya, 'yar soyayyan nan ko 'Ya'ya nawa ki kayi baki tsufa da yinshi ba, a kullun kina gyara kina tsafta Mijinki zai rik'a miki kallon yarinya ce". Basma shuru tayi, gaba d'aya jikinta ya mutu tace "Momy yanzu kina nufin da safe kafin in fara indimar Hydar na Babanshi zan fara?" Momy 'yar dariyarsu ta Murmushi tace "kwarai kuwa, ba da safe bama a ko wani lokaci ma, in har Mijinki mai fitan safiya ne dole ki tashi ki fara masa hidima kafin ya fita ki tabbatar ya fita da farin ciki a ransa wanda in ya tuna zai rik'a Murmushi da farin ciki, kinga kin samar masa farin ciki wanda ko ya fita hankalinsa da tunaninsa yana wurinki zai rika Allah-Allah ya dawo gida. Ki zama mai kwalliya, canza shiga iri-iri, karki nacewa shiga guda d'aya, k'amshi karya rabu dake ki zama mai amfani da turaruka masu sanyin k'amshi, kuma kala-kala, karki yarda Mijinki ya fahimci k'amshin ki guda d'aya ne, ya zamana daban-daban, kuma ki tanada masu taushin k'amshi na wanciya barci ne wannan kawai. K'amshi yana d'aya daga cikin sirrin mace wanda zata mallaki zuciyar mijinta cikin sauki. Sannan ki rik'a wa Mijinki Addu'a a fili da kuma a b'oye, in zai fita bishi da Addu'a tare da tarairaya wanda in ya tuna ki ya saki murmushi. Kuma karki kuskura ki sakarwa 'yar aiki hidimar mijinki dan wasu matsalolin daga nan yake farawa, sai jiki ance 'yar aiki ta aure mijin matar gida, wannan duk sakacin matane akan kula da hakk'in Miji. Nasan duk kin sannan wannan abubuwan tuni dai nake miki". Ajiyar zuciya Basma ta saki mai k'arfi tace "Momy nagode sosai, hak'ik'a duk Macen da tayi amfani da shawarwarinki zai mata amfani matuk'a sosai, Allah ya saka Miki da Aljanna yasa ki gama da duniya lafiya, ina alfahsri da samunki A matsayinki na Uwa a gareni, love u much Mom" ta k'arasa maganar tana matsar kwalla. Momy tayi Murmushi tace "Ai Basma lokacin ma yayi mana kad'an, domin na lura da *Anty Rahma* ta k'osa ta gudu ta barmu, ta koma labarin Jannat na cikin sabon littafinta *MAI HAK'URI (shi ke da riba)*. Dariya Basma tayi ta mik'e tace "Momy Anty Rahma tana k'ok'ari sosai ina jinjina mata matuk'a" Momy ta wuce d'aki ta had'o mata wasu magunguna ta bata, Basma ta amsa tana murmushi cike da jin kunya tayi mata Godiya. *Ni Rahma nace kunga Iyayen zamani*😉 Ammi itace ta mai da Basma gidanta, sai gabda Magrib ta barota ta dawo Gida. Yaya Aryan sai bayan Sallan isha'i ya shigo gidan, mamaki ya cika shi yanda k'amshin Abinci ya cika masa hanci daga kitchen, tunani ya shiga yi, yasan tabbas ma'aikatan gidan sun gama aikinsu sun wuce part d'in su, tambayan kansa yake 'Waye a gidan nan?' Dan sam bai san da dawowar Basma ba. Zama yayi a falo yana jiran yaga wanda zai fito, baifi minti biyar da zamansa ba Basma ta fito cikin shiga na English Wears riga da sket, rigar iya cibiya ya tsaya mata, sket d'in kuma iya rabin cinya, gashin kanta ta d'aure shi da ribom ta saki jelan a bayanta, k'amshi take zubawa mai sanyin k'amshi, Baby Hydar ta sab'ashi a kafad'a, shima ta zuba masa nashi kwalliyar. Yaya Aryan sakin baki yayi yana kallonta harta k'arasa wurinsa, kwantar da Hydar tayi ta koma kusa da shi ta zauna tare da kallonsa tana murmushi ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, hura masa iskan bakinta tayi a idonsa, ya lumshi ya kuma bud'ewa, magana zai yi ta had'e bakinta da nashi suka lula duniyar masoya, sun d'auki kusan rabin awa suna faranta ran juna, daga bisani Basma ta jaye jikinta tace cikin kasala "Muje kaci abinci" Murmushi kawai yayi ya mik'e ya d'auki Baby Hydar tace "Ki sameni a d'aki" Bin bayansa tayi cike da farin ciki tace da k'arfi "I love u Yaya Aryan" Sai ya juwo cikin kulawa tare da d'age gira "Love u too My Queen" Ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta suka koma suka zauna yace "Basma kin zamo min haske a rayuwata, sonki halitta ne daga tsatson jikina, zan kasance dake har abada taurauwata, zan cigaba sa shayar dake da ruwan farin ciki wanda yake kwaranya daga koramar masoya" Ya sumbaci bayan hannunta. Tace "in sonka Mijina, Allah ya k'ara mana zaman lafiya da kwanciyar Hankali, ya kauda dukkan shairin Shaid'an, Mutum da Aljan, ya k'ara maka bud'i na Alkhairi ya kuma Albarkaci zuri'anmu" "Ameen ya Habibty" ya amsa tare da manta mata kiss a baki, daga bisani sai suka mik'e suka wuce d'akinsu, dan cigaba da shayar da juna Zumar Masoya. *Tammat Bi Hamdillah* *_Alhamdulillah Ala Kullu Halin_* Alhamdulillah, Yau Allah ya bani damar kammala wannan littafi mai suna *'YAR SHUGABA*, ina mai godiya ga Allah S.W.A daya bani ikon kammlashi cikin koshin lafiya. *_MASOYANA_* _*Bani da bakin gode muku masoyana masu bibiyar wannan labari, kunada yawa domin lissafaku wani sabon littafi zan cika, Allah ya saka muku da Alkhairi ya k'ara mana zumunci ya kuma had'a fuskokinmu a Gidan Aljanna. Ameen. Addu'o'inku yana isa gareni, Nagode sosai wallahi ina sonku sosai, so wanda baida algush😃, so irin da yawan d'in nan, irin totally d'in nan, ina yinku ba adadi Allah ya bar kauna. Ameen😍❤❤*_ *Wannan labari kamar yanda na fad'a a farko k'agaggen labarine, banyishi ko dan wata ko wani ba, hasalima idan muka fuskanci labarin yasha banban da yana yin mulkin k'asar mu da ma sarauta. Na yishi domin ilmantarwa da kuma fad'akarwa acikin siga na nishad'antarwa.* _Allah ya bamu ikwan Amfani da abinda ke cikin wannan labari, kuskuren dake ciki Allah ya nisantamu dashi ya yafe mana gaba d'aya. Ameen._ _Taku a kullun_ *RAHMA KABIR* sai kun jini a sabon littafina wanda zaizo nan bada dad'ewa ba *MAI HAK'URI (shi ke da riba)* *Rahmar Ku Ce*💃😍