[5/1, 10:07 AM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK KISWAH (Linked through surrogacy). Na CHUCHUJAY ✍️ Book 1⃣ Episode 1⃣ ◼ A/N Assalamu Alaikum masoyana abun alfahari na,Fatan na sameku cikin koshin lafiya , Ina kaunarku a koda yaushe kuma bazan daina ba domin kuwa Allah ne ya haɗa ni daku wanda ba yine 'na mutum ba, Ina rubutu kuna kaunarsa sannan kuna bani kwarin gwiwa wajen so da yaba abunda 'na rubuta,😪ni ba kowa bace idan Babu ku ❤. So yarda Allah ya bani ikon haɗa Littafin AURE UKU da AHALINA ina Addu'ar 'ya ara mana rayuwa da lafiya domin kawo muku wannan littafi nawa Na KISWAH(Surrogacy was the cause ) amma a wannan zagayyen tafiyar ta dabance domin kuwa littafin 'ya kasu kashi biyu ma'ana book 1&2 ,book 1 zai zo maku kyauta ne book two kuma na kuɗi,kamar yarda na nishaɗantar daku a series biyu da 'ya gabata ina fatan nima zaku nishaɗantar dani da beautiful sales na wannan littafin Na KISWA,kilan kin taba ko ka taba jin story line ɗin kilan kuma wannan ne na farkon ka,abu guda ɗaya na sani wanda shine ,insha Allahu zai ilimantar,zai nishaɗantar . Na sake faɗa Book two 'na kuɗi ne kar ki fara karantashi ya katse kiji haushina akan bance 'na kuɗi bane saida mutum ya fara' thats what happpend a Abla Adnan amma insha Allahu zaizo muku akan farashi mai sauki cos biyan zai zo da tsari,iya kudinka iya shagalinka❤ TSOKACI. ◽Surrogacy Wani method ne da turawa suka kirkira wanda idan ma'aurata biyu na san haihuwa misali idan ɗaya daga cikin ma'auratan bazai iya haihuwa ba ko kuma matar bata san ta haihu ɗin sai su samo wadda za'a sakawa Maniyi na mauratan biyu,da taimakon technology zasuyi developing ciki jikin Matar da wannan halittar samun ciki na Ma'aurata biyu, Surrogate mother ɗin zata masu rainan cikin ta haife ta basu abunsu wanda shi yasa a kasashen yahudu surrogate mothers suna nan aikinsu ne iyakacin su haifa maka su baka abunka aikinsu 'ya gama kenan,wannan kana ji aikine na nasara domin kuwa Musulunci yayi Allah wadai da wannan tsari,sannan baya da gurbi ko waje ko wata ɗauraya a addinin Islama. Wannan kenan. DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI. Ko wanne ɗan Adam dake numfashi a rayuwa An haliccesa ne sannan aka rubuta masu ƙaddararsa sai dai yiyuwarta da wanzuwarta a lokacin rayuwa domin kuwa sai tazo kuma sai ta faru jira ne kawai bawa ke yi, A haka rayuwa da ƙaddarar KISWAH UBAID ke tafiya a rubuce cikin tsari da godiyar Allah domin kuwa duk wani musulmi na ƙawarai yana daga cikin Imaninsa 'ya yarda da ƙaddara wala mai kyau ko kuwa akasinta , Iyayen KISWA biyu Malam UBAID da Zubaida ,Mutane yan asalin jihar Bauchi,a rayuwar Aurensu sun jima basu samu rabo ba domin rabon nasu na chan nesa,Zubaida bata samu ciki da mijinta ba har sai da suka shekara huɗu da Aure ,a lokacin kuwa da sanin cikin ya ziyarci Malam UBAID ba ƙaramun mirna yayi ba da farin ciki domin kuwa yana mutuƙar kaunar Ace yau zubaidarsa ta basa Farin cikinsa wanda shine ganin yaronsa ko yarinyarsa a hannunta. A lokacin da Ya samu labarin cikin kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha dan murna,idan kuwa ka haɗu dashi a wannan rana To tabbas sai yayi maka ihsani saboda wanda ubangiji yayi masa. Mutane da dama kan faɗi masa maganganu iri iri akan rashin samun cikin Zubaida dan harda masu ce masa rashin haihuwa Ya saka mijinta na farko sakinta domin bashine Ya fara Aurenta ba a bazawara Ya Aurenta, Dukkan wata magana Da wani zai faɗa masa zata shiga ta kunne guda ne ta fita ta guda dan Babu wadda ke tasiri akansa,abu guda ɗaya ya sani wanda shine yana san matarsa sannan itama tana sansa sannan mahaifansa basu taba masa ƙorafi akan rashin haihuwar matarsa ba sannan ya sani da samu da rashi duk na ubangijine wanda a lokaci guda ya azurtasa a lokacin da bai tsammani ba, Lokacin da Matarsa ta isa haihuwa ta zanƙado masa yarinya mace mai kyau wadda yana kallanta yace Allah ya basa KISWAH (Madubi,Rufi na Ka'aba)ya bata sunanne saboda Itace madubinsa na farko gurin sanin menene jininka,yana kuma fatan ta kasance mai tsarki da purity kamar irin na gold and Black lullubi na Ka'aba domin kuwa yan representing unity irin na islama. Ranar sunan KISWAH kuwa ba ƙaramun bajinta yayi ba dan idan ka gani zakayi tunanin dukkan wata dukiyarsa yake ƙoƙarin ƙararwa a wannan rana, Yana samu domin ɗan kasuwa ne wanda Allah ya bawa nasibi a kasuwancin nasa, A lokacin da Zubaida tayi Arbain ya biya masu saudiyya domin kai KISWAH ya shafa hannunta akan KISWAH. Lokacin da KISWAH ta shiga shekaru huɗu a Duniya Allah ya jarabci Malam UBAID da larura wadda tazo da ajali,bayan Kiswa basu sake samun wani rabon ba ashe ita ɗin ita kaɗaice rabo tsakaninsu. Sosai Lalurar ta far masa wadda likitoci suka kasa gano bakin zarenta yayin da a bangare guda kuma ciwan ya ringa tafiya da dukkan arziƙinsa da tanadinsa wajen nema masa lafiya inda daga bisani Allah yayi masa cikawa , Bayan rasuwarsa a hankali Zubaida ta fara shiga chakwakiya ta rayuwa domin kuwa komai nasa ya kare sai gida wanda suke ciki inda shima ya shiga cikin gado,iyayensa da basu nuna masa san zuciya a fili ba lokacin rayuwarsa sai suka Nunawa Zubaida da ɗiyarsa KISWA domin kuwa ana saida gida suka karbi gadonsu suka sallama mata KISWA,itama iyayenta ba masu ƙarfi ba amma a haka ta cigaba da rayuwa da daɗi ba daɗi karkashinsu inda daga bisani lokacin da KISWA ta isa shiga makaranta Yayan zubaida ,Aliyu dake da Hali ya ɗauketa ya kaita gidansa domin sakata makaranta wanda ya shaida mata shine kawai abunda zai iya mata domin ba wani shiri suke ba amma sai Allah ya ɗora masa san Kiswa ,daga bisani kuma miji ya fito mata mai mace biyu ta Aura a nan cikin bauchin inda a gefe guda ta kama sana'ar abinci. *** 24 YEARS LATER ABUJA NIGERIA! Zaune ƙyakƙyawar budurwa take kan gado a wani ɗaki dake ihun Naira,komai na cikinsa princess like ne cikin color na pink and white,ɗakin na ɗauke da gado guda biyu wanda zai ɗauki mutum biyu each,a hankali take taba tab ɗin dake hannunta cike da siga ta mayar da hankali,ba fara bace irin matan nan ne da ake ma ikirari da black beauty wadda a kalo ɗaya idan kayiwa fatarta tabbas kasan ta samu kulawa,tana wannan zaman aka turo kofar ɗakin ,wata budurwarce da bazata wuce tsarar ta ba,Babu sallama a bakinta ta shigo ta na mai jefar da jakar hannunta kan gado na biyun a yayin da ta zauna tana mai cire takalminta wanda Ya gaji da tsini, Kallo ɗaya budurwa farkon tayi mata ta dauke kanta,ƙaramun tsaki ta biyun tayi tace"Wallahi KISWA kina da matsala ba kaɗan ba ,kina jina na shigo Ai ko sannu ne kya faɗa mun amma dan tsabar bakin nukuburci kinyi kamar bama kisan na shigo ba,tsaki ta kumayi tace "today was beyond stressful ". Murmushi kawai KISWA tayi sanin halin mai magana,tana so a koda yaushe kasan da ita ka bata attention, FARIDHA ALIYU kenan wadda ake wa laƙani da FARRY ɗiya mace tilo a gurin ALHAJI ALIYU yayan zubaida mahafiyyar KISWA da Matarsa Barrister JUWAIRIYYAH ,yarinya wadda a kayiwa rainon gata da sangarta,yarinya wadda aka raina kamar ɗiyar sarki,Yarinya mai taƙama da ita ɗin yar gatace gurin Yayyunta guda biyu maza SAMEER da SAGIR wadanda basu san laifinta, Bata da kara bata kuma gudun nuna maka kaiɗin ba komai Bane,duk da Halinta a bangare guda tana mutuwar san Kiswa duk da kuwa yarda mahaifiyarta ke mutukar nuna tsanar Kiswa ɗin tsantsa 'dan a cewarta tana neman kwacewa yayanta gida ne duba da yarda mai gidanta ke nuna kulawa ga Kiswa ɗin bugu da kari kuma yaranta maza dake faman mata shishshigi ,tsoranta guda kar wani cikinsu yace yana so, Sau da dama Kiswa ke bin mess ɗin Farry tana gyarawa 'dan ita ɗin bata ji a yayin da gefe guda kuma Kiswa tasan ta duk wata hanya da zata bi ta kare Farry ɗiin. Aje tab din nata tayi ta kalli Farry wadda ke ƙokarin Ɗaura towel tace "last da na tuna lokacin da zaki shigo bakinki babu sallama so mene zai dameni akan kulaki,and Yes maganar guy ɗin chan dake stalking ɗinki is all done and Abeg Farry ki barni haka nan na huta i have a life too" Da sauri Farry ta dawo inda Kiswa ke zaune ta kama hannunta tace"God ina mutuwar sanki yar uwata ,na gode and anjima kaɗa zakiji alert na 500k " Kallanta da kyau Kiswa tayi tace "you must be Nuts,wai sau nawa zance miki idan abu haka ya faru tsakanina dake ki daina ƙokarin biyana bana so abeg ,idan kina san ana miki aiki ne kina biya ki samu masu aikin a waje wanda irin aikinsu kenan mana." Saurin kama hannunta Farry tayi tace"Chill girl calm down ba ina nufin wani abu haka ba wallahi,kawai ihsani ne and Yes nasan you're doing Okay financially amma aibu ne dan na maki kyauta?" Kinsan im off better financially ki kalla fa ina hawa Landcruiser kina hawa 306 so girl i mean no harm,Tashi tayi tana mai gyara towel ɗinta ta nufi bathroom ɗinsu,har zata shiga ta juyo ta kalli Kiswa dake kallanta tace "500k im sending it idan kinga dama ki kyautar"Tana kai aya ta faɗa. 'dan murmushi Kiswa tayi a fili tace "im also doing well cos ina da savings na wajen 5 million and ban raina ba cos i earned it and motana i bought it my self" Daga cikin bayin Farry tace "'dan kina da 5 million doesn't mean zaki saka kanki cikin millionaires ,you have alot way To go,so idan zakiyi quiting wannan kamfinin da kike ma aiki ki dawo na Daddy kiyi cos chan zaki samu kuɗi ba inda wani zai biyaki ba trust Me zan biyaki da kyau,yes im enjoying daddys money wanda kema ke kika hana kanki,cos motar nan Ya siyan miki kika ƙi karba. Tashi Kiswa tayi tana mai sake gyara gadonta tace "nasan dai kinyi karatun addini sannan a cikinsa kinsan surutu a bayi haramun ne ,so ki bari idan kin fito sai ki bani wannan lecture ɗin." Haka nan Farry take,idan magana tazo bakinta bata tunanin saka mata filter idan zata faɗe ta sannan duk abunda tayi niyyar faɗa shi take faɗa bata damuwa da abunda kai zakaji as far as ita ta futar da ta cikinta,haka nan take koda kuwa da Kiswa ne amma idan abu ta bangaren Kiswa ne bata wasa dashi komai ƙanƙantarsa,koda zuwan Kiswa gidan afafur ta ki yarda da a raba masu ɗaki duk da wadatar hakan ,duk nacin mahaifiyarta dole ta barsu. Dauke takalman da ta watsar Kiswa tayi tana mai jadadda mitar ta daina aje masu takalmii a ko ina, Kafun Farry ta fito ta gama gyara ko ina tana mai haɗama kanta cornflakes ɗin da tasa akawo mata,tana cikin ci Farry ta fito Babu wani tambaya ta kwace cup ɗin Ta fara ci tana mai cewa"ki haɗa wani" Tsaki Kiswa tasa tace "wata rana sai kinci abu mai guba". Zama gefenta tayi tace"indai a gurinki ne sis nasan bazan taba cin guba ba,kinsan dai kin bani wata ɗaya dole ne kina Cin girman,yauwa ina ma san tambayarki Ina Haidar ɗinki, Ɗan ƙaramun tsaki Kiswa tayi tace "rabu da wannan yana tunanin bazan iya rayuwa babu shi ba shine yake faman shan ƙamshi a faɗan da ba laifina ba,well muje zuwa wanda Ya fasa gajiya." Yar dariya Farry tayi tace "ke dai faɗanki da Haidar ɗinkin nan bamu shiga muji kunya,ina,ni 'fa shi yasa da kika ganni Babu ruwan da wani relationship' kuɗin dai da power ɗin tukunna . A tare suka saka dariya 'dan a kullum furucin ta kenan a yayin da Kiswa kan faɗa mata bai zo Bane shi yasa. Share fisabililahi https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK CHUCHUJAY ✍️ https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05 Join my Whatsapp channel [5/1, 7:01 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK KISWAH (Linked through surrogacy) By CHUCHUJAY Book1⃣ Page 2⃣ ◼ MONDAY MORNING. Cikin gidan Na Alhaji Aliyu kowa ka gani yana sauri ne da kimtsawa domin tafiya aiki ,Kiswa wadda idan tayi sallar asuba bata iya komawa ce ta kamawa Baraka mai girkin gidan duk da kuwa yarda bata san Kiswa din na zuwa taya ta aiki amma nacin Kiswa ya saka ta barta dan Babu yarda zatayi da ita tun kafun ta kai haka. Zazzaune suke baki ɗaya kan teburin cin Abinci suna jiran Kiswa wadda bata kai ga ƙarasowa ba ,rules na gidan bai barka kaci abinci ba tare da kowa ya hallarci gurin ba ,idan kana saurine to ranar sai dai kaci abincinka daban,wani irin tsaki Barrister JUWAIRIYYAH taja tana mai kallan mijinta tace"wai kai Alhaji mene damuwarka da sai anjira kowa za'a karyane?wannan yarinyar sanin haka ya saka take miƙe kafafu a ɗaki sai lokacin da taga dama zata fito ,gaskiya abinci zanci dan ina da abunyi a court haba." Cup din dake gabanta ta ɗaga dan haɗa tea,Alhaji Aliyu bai tankata ba har ta fara haɗa tea ɗinta sanin koda yace ta yi hakuri bayi ɗin zatayi ba,sameer da maganar mahaifiyar tasu bata gamshe sa Bane yace "Amma Mother jiya Sageer yafi kowa fitowa latti and we waited Babu wanda yayi complain,after all Babu mai latti tunda baifi mu ɗauki minti talatin ba wajen karyawa kowa ya kama gabansa,its 6:30 am saboda Allah. Cike da masifa ta kalli Sameer tace"zaneni mana Sameer sai nasan kana shigar wa uwarka juwairiyyah faɗa,bana san iskanci fa Zan bata maka fiye da yarda baka zato,"kafin wani yayi wata magana Kiswa y Ta fito cikin shirinta Na zuwa aiki tana mai faɗin"kuyi hakuri na saka ku jira ,Im sorry da kun fara without me" Tsaki Mother tayi tace"su da zasu iya jiranki ai gashi nan suna jiranki tunda basu da abunyi ,Ina ga zubaida ta sassaƙasu" Da ƙarfi Alhaji Aliyu ya daki table din wanda da bashi da girma da yayi Bari,cikin yanayi na karsashi yace"sau nawa zanna faɗa miki ki cire zubaida daga fitinarki Barrister,ya isheni fa bana san kina saka ƙanwata a al'amarinki na rashin kirki na faɗa miki ba yau ba ba jiya ba " Kallansa tayi narainarai da ido ganin yarda yake mata tsawa gaban yaranta which is not like Him,aje spoon ɗin ta tayi tace"Its okay ka cigaba da mun tsawa gaban yara amma hakan bashine zai boye gaskiyar cewa ƙanwaka Zubaida is a disappointment ba,sannan hakan bazai taba chanzawa ba so kama daina pretending caring brother cos kasani na sani its a pretence ,quit it already,excuse me"tashi tayi tana gama maganarta ta ɗauki jakarta ba tare da ta tsaya kula Sageer dake faman kiran sunan ta ba ta fice ,a hankali Kiswa taja kujerar kusa da Farry ta zauna tana mai faɗin"Im sorry about that,ba niyana nayi causing matsala ba ,na cire kayan da zan saka ne tun jiya so dana saka yau da safe yaki shigana since dama na daɗe ban saka ba so dole na sake neman wasu and i had to look responsible cause yau muna da baƙi masu muhimmanci and nice host dinsu sannan..." Dariyar da suka saka ne a tare ya katse ta,dan taune lebenta tayi tace"well i didn't think i sounded funny,"Sageer dake gefenta ne yace"Aikin jarida ne kawai ya dace dake mai ya kaiki karanta Public relation?,". Ɗan murmushi tayi tace "dalilin da yasa Appa karantar Kasuwanci sannan abunda yasa Farry karantar kasuwanci,abunda ya saka Mother karantar Law,abunda ya saka Ya Sameer shiga Immigration da abunda ya kai ka Ya Sageer karantar Accountancy which is Passion " "Case closed"Alhaji Aliyu wanda suke kira da Appa ya kara yana mai jin Kiswa har ransa,She's smart beyond expectation,yaso tayi aiki karkashin kamfaninsa amma taƙi wanda take ganin kamar alfarmace inda shi kuma ya rabu da ita dan baya san takurata amma ko yaushe idan ta shirya dawowa Akwai gurbinta. A Haka suka fara cin abinci har suka gama Babu wanda yayi maganar Mother domin abune wanda aka saba duk da kuwa tsawar Appa gareta shine abu na farko a gurinsu,amma ina zasu shiga gurin da bana su ba,duk da kuwa rayuwar gidan free rayuwace ta yan boko amma ko wanne yaro yasan limit ɗinsa da iyayensa. Ko wannensu ya shige arniyar motarsa a yayin da Kiswa ta shiga cikin 306 ɗinta wadda take alfahari da ita ba tare da tana jin wai ita ɗin bata kai ba. A parking space wanda aka tanada domin ma'aikata ta faka motarta a katafaren Building na Ma'aikatar ta AYZEL FOUNDATION,kamfanine wanda ke harƙalla da abubuwa daban daban wanda ya danganci kayan zaƙi,kamar su sweets,chocolates,ruwa,drinks,food stuffs ,sutura da sauransu wanda yake karkashin jagorancin Founder kuma chairperson na Group ɗin wato Alhaji Basil Madugu Dattijo mai fitarwa da ma'aikatan sa hakkinsu sannan mutum mai kirki na gaske,idan kana san shiryawa dashi to tabbas ya zamana kana san aikinka sannan kana cikin masu maida hankali akan aikinsu,wannan dalili ya saka yake mutuƙar ƙaunar Kiswa matsayin PR officer ɗin sa domin kuwa tasan aikinta yarda ya kamata. Tunda ta shiga cikin ma'aikatar Take gaisawa da abokanan aikinta cikin mutunta juna domin kuwa ita d'in She's frndly ƙaryarka kace yau kuna zaune ga matsalarta, Kai tsaye ofishin chairman d'in ta nufa domin shaida masa shigowata dan koda bata je ba zai nemeta ,gaisawa tayi da sakatariyarsa wadda ke faman yamutsa fuska dan bata ƙaunar Kiswa ko kaɗan Ganin Yarda chairman ke ji da ita kamar ya maida ta ciki dan haka duk wani chance da zata samu wurin bata Kiswa a ma'aikatar bata rainasa dan har rumours ɗin cewa Kiswa mistress ɗinsa ce ta assasa a kamfanin ,amma mey babu wanda ya isa 'ya tunkari Kiswa da maganar ko ya yaba mata Ya jawa aikinsa. Cike da mutunci da girmamawa Kiswa ta Gaida Alhaji Basil wanda yana ganinta ya washe baki yana mai faɗin"yarinyar Albarka yanzu nagama maganarki da manager akan meetinq ɗin chan amma sanin baki latti yasa na kwantar da hankalina dan kamfanina kansa idan yana hannunki bana da damuwa" Faɗaɗa murmushinta tayi tace"Nagode sir and na ɗauki Aikina kamar rayuwata Babu yarda za'ayi nayi Wasa dashi and meeting ɗin nan munyi hosting ɗinsa yarda ya kamata ,insha Allahu Babu complain." Murmushi yayi yace"I trust you,and yes karna manta ban faɗa miki ba SALIK na nan dawowa daga Australia And inaso kafun na bashi kamfanin nan ya zamana hes responsible dan haka nake san fixing masa Business' marriage wanda zai benefiting ɗinsa," Kaɗa kai Kiswa tayi tana mai faɗin"hakan dabara ce mai kyau sir"Dan tasan Babu abunda zata fada ta goge wannan mindset ɗin nasu na masu kasuwancin dake san hannun jari sannan tabbas idan ya Aurawa yaransa ɗiyar wani babban Business' tycoon ɗin kamarsa ba karamun advantage Bane ,amma anata tunanin bata ɗauki irin wannan Auren abunda ya kamata ba. Sake Faɗaɗa murmushi yayi yace "So i will be expecting meeting din yau" Murmushin itama tayi masa Kana Tayi masa sallama. Kamar yarda Alhaji Basil yayi expecting gurin Kiswa haka ya faru domin kuwa kafun client din su tafi sai da sukayi signing contract ɗin da suke ta hange,Kiswa kenan She's very intelligent And Smart,as a PR officer tasan ways ɗinta da clients sannan She's patient And humble kamar yarda ake expecting duk wani PR officer ya kasance, Bayan komawatta office ɗinta tayi ma Assistant ɗinta umarni da taje ta kawo mata documentaries ɗin da zata fara scheduling ma SALIK bisa umarnin chairman Basil, Tana kanyi taji wayarta ta dauki ruri ,kallan screen ɗin tayi taga "Quratul ayn❤" na yawo akan screen ɗin,rejecting tayi yayin da shi kuma ya cigaba da nacin kira tana kashewa karshe dai har ya hakura da kiran nata ganin bata da niyyan ɗagawa. Assistant ɗinta tasaka akan ta kawo mata Take away na lunch cos aikin gabanta bata tunanin zai barta taje cin abincin a wani gurin, Tana cikin aiki taji an buɗe kofar office dinta,ba tare da ta ɗaga kanta ba tace"Yauwa Ameera thank you kamar kin san..."bata ƙarasa ba sakamakon Kamshin HAIDAR dinta da ya ziyarceta wanda yake ɗaya daga cikin abinda ke burgeta dashi baya rabo da kamshi ,sannan wannan kamshin guda ,a hankali ta daga kanta dan tabbatarwa da zuciyarta tunanin da Take na ko shine,suna haɗa ido tayi saurin dake nata tasha kunu,murmushinsa mai kyau ya Faɗaɗa yana mai Takowa gareta hannunsa dauke da bunch na red roses ,zagayawa yayi ta inda Take zaune ya duƙa cikin sassanyar muryarsa yace"Haba Love kinsan dai fushinki baya barina na samu sukuni daidai da na minti ɗaya ,mai yasa zakiyi kwana uku kina fushi dani bayan kinsan kece rayuwata?" Wani irin kallo ta bashi cike da haushin da Take ji na Abunda ya faru tace"Haidar ka rabu dani tun muna shaida juna cos banga amfaniin da zai saka na cigaba da kula ka ba bayan gidanku an maka mata so gwanda ka tashi ka tafi gurin tasleem da zaka Aura nan da wata biyu ka rabu dani. "Shafa sumar kansa dake sheki yayii yace "ya Allah,so tasleem ta fada miki ni da ita zamuyi Aure nan da month shine kike ta wannan fushin?zata ci ƙaniyarta kuwa ,tashi tsaye yayi ya ciro wayansa Ya danna kiran wayan Tasleem yasa a speaker wadda a kira ɗaya ta dauka tana mai fadin"hello favourite brother"katse ta yayi ta hanyar faɗin"a gidan uban wanene zamuyi Aure ni dake nan da wata biyu?" She was dumbfounded for a Moment kafun realisation yayi hitting dinta na haduwa da tayi da Kiswa a shopping mall tayi franking ɗinka akan ita fiancee ɗin Haidar ce sannan Aurensu nan da two months,she was only joking tunda daga bisani tayi introducing kanta ma Kiswa a matsayin sister ɗin Haidar batayi tunanin ta dauki maganar da zafi ba . Dariya ta saka tana mai faɗin"Yaya i was only joking fa and after all na faɗa mata kai yaya nane and nothing more Bansan She's This possessive ba im sorry. Ƙaramun tsaki yayi yace "possessive or not ni nata ne insha Allahu na har abada ki kiyaye ni"yana jin dariyarta Ya kashe wayansa cos Tasleem yar banzan yarinya ce idan Ya biyeta hurasa kawai zata cigaba dayi. Kujera Ya jawo Ya zauna yana facing ɗin Kiswa wadda borin kunya Ya saka Ya haɗe rai,kafun yayi wata magana tace"okay naji i was only mad which is justify dont say a word im embarrassed right now".dariya Ya saka yana mai jin santa yana ɗibarsa,yana mutukar san Kiswa ba kaɗan ba sannan shima Ya yarda da soyayyar da Take masa cos bata iya boye masa sannan ita macece mai kishinsa Ya sani tabbas yau idan akace bashine Ya Auri Kiswa ba zai shiga mawuyacin hali dan tabbas badan shi musulmi bane Ya kuma san hukuncin musulmi yakashe kansa da yace zai kashe kansa Ya huta da rayuwa baki daya , flower din hannunsa ya kalla yace"so ya zanyi da roses ɗin nan?" Hannunta ta saka ta kwace tana mai faɗin "rose is a symbol of love and im your love and life kaga kuwa rose ɗinka a hannuna zai kasance." Cike da kaunar juna ta ringa guiding ɗinta yana tayata paper work kana suka fita cin abinci tare. Shin wanene wannan HAIDAR ɗin? TBC CHUCHUJAY ✍️ 08130229878 [5/2, 4:16 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK KISWA (Linked through Surrogacy) Na CHUCHUJAY ✍️ Book1⃣ Page3⃣. ALIYU'HAIDAR TUKUR BULA shine asalin sunan sa matashin saurayi mai shekara ashirin da tara ,haifafen cikin garin Abuja ne amma asalin su mutanen dutse ne dake cikin garin jigawa amma a tashin Haidar Abuja Ya sani gidan dan tunda yake da iyayansa biyu basu taba cewa yau Haidar shirya muje usulin Garin ka ba a yayin da shi ma bai damu ba ganin yan uwan nasu na chan garin suna zuwa inda suke. Haidar ɗa guda ne tilo wurin iyayen sa Alhaji Tukur Bula da Matarsa Hajiya zainaba Bula dan haka suka dauki soyayya ta duniya suka ɗora masa ,Babu wani abu da Haidar yake nema a rayuwar sa ya rasa tun yarinta indai kuɗi ne zai bada su ,irin girman sangarta da akayi masa kawai ya ishe sa lalacewa a yayin girmansa Amma sai Allah ya rainesa cikin sahun mutane masu nutsuwa da sanin ya kamata,sau da dama mahaifiyar sa kan ɗorasa a abu mara kyau wanda zahiri tasan mara kyau dinne amma saboda dabia ta nasara sai ta danne inda shi kuma idan ya hanga rashin dacewar wannan abun sai yayi kokarin wajen ganin ya dorata a hanya. Iyayen sa shahararrun masu kuɗi ne domin mahaifiyar sa babbar sananniyar yar kasuwace a garin wadda keda boutiques ɗin da zaka gaji da irgawa a yayin da mahaifinsa yake babban custom,magana ta rashi a gidansu Haidar fa babu ita domin kuwa Allah ya azurta iyayensa wanda dalilin hakan yasaka basu damu da subi danginsu inda suke ba sai dai su su biyosu inda suke su dan lasa., Rashin samun wani haihuwar bayan haidar baya damun iyayensa illa shi din da suka samu suka duƙu fa wajen tara masa abunda yake nasu ne ma'ana dukiyarsu, Sanin iyayen Haidar Nada kudi bai taba kashe masa zuciya ba wajen neman na kansa duk da kuwa yarda mahaifiyarsa ke nacin yaji dadin rayuwarsa kawai domin kudi sun tara masa ba sai ya wahalar da kansa wajen nema ba amma yayi fafur akan cewa su barshi yayi aiki domin career ɗin abunda yake mafarkinsa ne kuma abune wanda yake da sha'awa tun yarinta wato aikin Likitanci,ganin ga abunda yaran nasu yake So shi yasa suka bude bakin jaka wajen ganin sun bashi ilimi isashe wanda ya samu ƙwarewa a harkar inda daga bisani suka tamfatsa masa Asibiti wanda yaci sunasa "AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL "Haidar kwararren likitane wanda ya taba fannika daban daban ,sabida san zaman komai dai dai a asibitin Nasa yasaka yake daukar likitoci wadanda suka san mai suke ,a kalma guda Asibitin Al'Haidar asibitine wanda baza kace likita daya ke duba zuciya ba sannan ya duba hakori ya duba kunne ,ya duba ƙashi da dai sauransu,asibitine da ke dauke da zuga na komai da ruwanka. Da kansa ya samawa kansa ilimin addini duba da iyayensa sunfi bada muhimmanci akan bokonsa cos bai taba zama ajin islamiyya ba sai dai malami yazo gida yayi masa wanda shima bayan fara tasawarsa aka sallamesa acewar Hajiya zainaba 'ya samu 'na sallah ,sanin yana bukatar bunkasa saninsa akan addininsa 'ya saka ya dage wajen sanin littattafai domin duk yarda yake san iyayensa yayi alwashin idan ya haihu bazai taba Bawa yaran sa tarbiyya irin wadda 'ya samu ba,mutum ne shi mai nutsuwa kamili wanda bai damu da sabgar yan mata ba duk da harin da suke kawo masa domin shi din mai kyaune da kyawun kira irin wadda duk wani namiji ke fata,sau da dama idan aka tada ma mahaiffiyasa maganar 'ya kamata yayi Aure sai tace "duka nawa Haidar din yake,abarsa yayi rayuwarsa cos life is too short duk lokacin da ya gama gwara kan yan mata ya samu ta Aure"jin Wannan furucin yasa ƙanwarta mahaifiyar Tasleem ta kawo tasleem gidan da zummar tana daukewa haidar din kewar rashin dan uwa amma a kasan zuciyarta ta kawo tasleem ne domin ta Auri Haidar nan gaba. Kowa yana saka da warwararsa a yayin da Haidar yayi gamo da tauraruwar da ta sace masa dukkan nutsuwarsa da tunaninsa a lokaci guda wata rana da tazo asibitinsa,yana kokarin fita daga Asibitin tana shiga a motarta wanda ta shige da zuciyarsa at first sight,bai wata wata ba 'ya koma Asibitin 'ya jirata har ta fito 'ya bita, babu kasa a gwiwa 'ya fallasa mata asirin zuciyarsa,ya dan sha wahala kafun 'ya samu hadin kanta cos a ranar bata kulasa ba sai da yayi ta bincike 'ya gano inda take aiki ya sarrafi addabarta wanda a hankali ta bude masa tata kofa zuciyar da ta gama karantarsa,yarda bai taba budurwa in a Serious way ba Haka nan Kiswa dan haka suke ma juna mayyar soyayya cos akan juna suka san daɗin ta. ****** Duk weekend rana ne da Kiswa da Haidar suka ware domin kasance da juna ta hanyar zaga duk wani gurin shaƙatawa domin ranar ne suke free baki ɗayansu,yau ma kamar kullum 'ya sameta gurin Spa 'dan su wuce classic restaurant ɗin da aka buɗe sabo aka bashi gayyata,chan 'ya tsaya bakin motanta yana jiran fitowarta inda bata wani bata masa lokaci ba ta fito garesa,tun daga nesa take kallansa tana yaban kyan da yayi mata a zuciya cos a ko wanne sutura takan tsinci Haidar dinta cikin kyawawan maza da komai ke fitting,sanye yake cikin royal blue button up riga mai sleeves gajere da dark Pants,sosai yayi mata kyau,cikin takunta mai daukar hankali ta ƙaraso garesa ,snapping 'yatsunta tayi a fuskarsa ganin yarda ya zama lost a kallonta,murmushi yayi lokacin da ta jingina da motan kamar yarda yayi tace"'na sake kama hala?" Juyowa yayi yana kallanta yace"dan Allah kiyi wuff dani Girlfriend ,husband me cos kina kasheni da yawa ,i just cant wait naga kin zama mallakina,What are we waiting for? Licking life dinta 'na ƙasa tayi tana mai tambayar kanta a zuciya "What is she waiting for?"'ya kamata ace yarda ta yarda da Haidar zuciyarta kuma ta gamsu dashi magana ɗaya 'ya kamata ace a yanzu anayi tsakaninsu which is maganar Aure,shekarar su guda kenan tare da juna amma bayan Farry Babu wanda yasan labarinsa a gidansu,itama Farry din kamata tayi suna waya ta dinga bin kwakwafi sai da ta gano wanene shi,lokacin da tasan kuwa Mai Al'Haidar hospital ne kamar tayi hauka tana mai ingiza Kiswa akan kar ta sakesa cos shi ɗin catch ne babba. Tana san maganar Haidar ga Appa amma tana tsoran Outcome 'na Mother wanda tasan Babu daɗi domin duk cigabanta idan mother zata sanshi to zatayi yarda zatayi ta koresa 'dan haka ta sama ranta maganar Haidar sai ta shirya,kamar yarda take faɗa masa a kullum yauma shine dai wato"Babe ka bani time kaɗan na dan Sake gina career ta kaɗan ,i assure you indai ina rayuwa kaima kanayi to da yarda Allaah da ikonsa nida kai mallakin juna ne". Daɗi maganar tata tayi masa 'dan haka ya tsincii kansa da washe mata baki,ganin yarda ya washe hakoransa 'ya sakata darawa tace"baka da dama baby baki ɗayanka,"tana ƙokarin buɗe motarta 'ya wani marairaice yace "baby muje motana mana"daga gira guda daya tayi tace "Aw kaima ka fara looking down on my car kamar kowa ko, kana jin kunya muje high class restaurant na aje motana ace ga motan budurwar Mai Al'Haidar ko? " Okay good ka wuce nima bari na tafi gida kar na kunyata ka. Saurin rike bakinsa yayi yace "Auzubillah Girlfriend mene hakan kuma,kisan dai i would never look down on you,beside motanki yafi Rolls royce Phantom ɗina cos ni Daddy ya siya mun ke kuma you bought This with your hard earn,im sorry idan na baki wrong impression" Ganin yarda ya wani marairaice ya sakata saka dariya sosai tana mai kallansa kafun tace"oga park well i was joking ka wani saka Serious face kana bani jamb answer go hop in your car ina bayanka," Shafa kansa yayi yana mai kallanta kana yace "kinsan wani Abu?" Kaɗa kai tayi 'a'a ganin yarda ya saka Serious face tana tunanin wani Abu ne , "I LOVE YOU" Shine abunda ya faɗa 'ya shiga motan nata yana mai faɗin a motanki zani nima, Haka nan ta jasu duk yarda tayi dashi akan yaje 'ya shiga motansa amma Yaki dole ta. Jasu suka tafi,she love teasing Him alot. After long day na soyyayya da suka sha Tayi dropping ɗinsa 'ya dauki motansa kana ya rakata gida,sun jima nan ɗin ma kafun su rabu kana daga bisani sukayi sallama shima calls din Mother da ta ringa gani yana shigowa wayanta ne wanda bazata ce Ga dalili ba 'dan sabon abu ne,ile kuwa tana shiga gidan suka ci karo da mother wadda ke faman safa da marwa a falon cike da damuwa,cikin kulawa Kiswa ta ƙarasa bakinta dauke da sallama tace "Mother naga kiranki ina hanyar shigowa shine yasa ban dauka ba hope lafiya"? Marin da Mother ta dauke ta dashine yafi komai daure mata kai,da mamaki take bin mothern da kallo wadda ke faman kumbura kamar wata mesa kana ta nunata da ɗan yatsa tace"duk wani abu mai kyau bai dace dake ba,baki chan chanci duk wani abu da yake da kyau a rayuwa ba sannan kisan da sanin cewa i cursed you,bazaki taba samun cigaba a rayuwarki ba 'dan Haka tun muna mu biyu kuma mu biyu muka san maganar nan kiyi saurin rabuwa da Al'Haidar domin jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa,ba sa'anki bane ba tsaranki bane,Haidar irin mazan daya kamata suyima Farry rububine bake ba stinky orphan ,saboda Kin tsotsi munafurcin Kin iya boye relation ɗinki har na shekara babu wanda ya sani,yanzu ba dan an ganku tare an faɗa mun ba Haka zaki maida kowa dan iska,to Allah ya tona miki asiri." Tana kai aya ta juya 'dan barin falon,cikin karfin hali Kiswa tace"kiyi hakuri Mother amma bazan iya rabuwa da Haidar ba,abu guda daya ne zai raba mu wanda shine mutuwa ,sannan ba dan na bata miki ba ko na miki rashin kunya ba amma kowa da kika gani yana rayuwa marayane a tafe ,maganar kuma bazan nasara a rayuwa ba wannan ba sani na ban ba naki bane ba,na Ubangiji ne". Kafun Mother ta furta wani abu Kiswa tabar gurin dan nufa dakinta,Sameer dake sama yana kallan komai ne 'ya sakko 'dan fita ya kalli Mother yace "Thats embarrassing Mother stop it already mana ,ni banga mai yarinyar nan ta tsare miki ba duk kinbi Kin saka ta a gaba ,'dan Allah Mother ki daina mana kar ta rainaki" Cike da bala'in da bata saukewa Kiswa ba tace"to 'dan ubanka sameer ka hanani magana sannan tunda Zubaida tace bazan rintsa ba wallahi ko gyangyadi baza tayi ba,idan ba balaii ba an kawo yarinya an aje mun Ban haifa ba na raina ,to ta Auri mai kuɗin na gani ,wannan toilet din data fito nan zata koma ta Auro amma ba'a abuja ba"wani dogon tsaki taja ta haura sama zuciyarta na mata wani irin zafi 'dan har ga Allah bata san dangin Mijinta karma ace Kiswa data rabe su. Kaɗa kai sameer yayi ya nufi ɗakinsu Kiswa,sau biyu yana kwankwasa kafun ta bashi izinin shiga bayan ta gama dai daita kanta,yana shigowa ta washe masa haƙoranta tace "Yaya Sameer?" Murmushi Yayi yace "yes"yana mai jan stool 'ya zauna kana yace "dont fake it i saw everything"murmushin yake tayi tace"Kayi hakuri Ya Sameer Nasan nayiwa Mother magana out of tone,na kasa rike kaina ne". Hannunsa 'ya saka ya kama nata 'yace"ki daina yawan bada hakurin nan Kiswa akan abunda baki da laifi bana san shi,trust me idan da Nine a maimakonki i would have acted worst,kiyi hakuri nasan babu abbunda zan fada yayi justifying hallayyar mother gareki ,ki kara hakuri wata ranaa sai labari,ehn kafun na manta wanene Al'_Haidar" Dan kasa tayi da Kai tace "He's your in law to be"Rike baki yayi yace"kaji yarinya babu ko kunyaa"Dariya tasa tana mai yin kasa da kanta inda shima ya tayata yana mai fadin "kima daina jin kunya aii" a haka cikin hirarsu ya kawar mata da dakuwar Mother inda suka kafa hirar Haidar. TBC CHUCHUJAY✍️ 08130229878 Wattpad:Chuchujay [5/3, 5:43 PM] Chuchujay✍️: KISWAH (Linked through surrogacy) By CHUCHUJAY ✍️ Book1⃣ Page 4⃣ "Uhum Hajiya Farry ina jinki kince kina da magana dani"Kiswa ta faɗa tana mai taje sumar kanta mai madaidaicin yalwa, Tasowa Farry tayi tazo inda Kiswa take ta zaunar da ita kan stool sannan ta karbi comb ɗin hannunta ta cigaba da taje mata kan tana shafa mai a hankali,daga kai tayi ta kalli mudubi wanda ta tarar da idanun Kiswa a ciki suna kallonta irin kallan nan na "nasan wani abu kike so" Aje comb ɗin tayi tace "Fine i want you to do me a favour dan Allah Kiswa,"zagayowa tayi ta durkusa gaba Kiswa ta kama hannunta tace "Dan Allah Masoyiya taimako na zakiyi dan nasani kina mun soyayyar da bazaki So na faɗa halaka ba,a wannan karan kuma halakar ke kirana,Appa da mother ne ya suka haɗa mun blind date da wani yaran abokinsa wai muje mu sasanta kan mu,kin dai san abunda ya saba mun and i hate it sosai "shiru tayi tana kallan Kiswa wadda tayi mata alamu da hannu tace "uhum So?"dan tasan maganar Farry ɗin bata ƙare ba. Cije lebe tayi tace"nayi bincike akan sa and bincike na 'ya nuna mun he's not the guy at all dan ba mutumin kirki bane,dan shaye shaye ne sannan clubber dan ance mun har giya yana sha ga neman mata na bala'i"cije lebe farry tayi tana tunanin Ta ina zata fara roƙon Kiswa ,rufe idanunta tayi gam tace"ina son kije a maimakona nasan you can handle Him ta yarda bazai yarda da Alliance din nan ba" Mikewa zumbur Kiswa tayi tace"na miki sau ɗaya sannan idan na tuna na faɗa miki shine na farko shine na karshe ,solution ɗin is simple,muje mu samu Appa mu faɗa masa dukkan ill halayyarsa da kika lissafo mun in yaso ya sake bincike ,nasan dai babu yarda Appa zaiyyi ya Aura miki miji irinsa" Ganin fa da gaske yanayin Kiswa yake ya saka farry fashewa da kuka tace"kina tunanin Appa Zai saurareni? Zaice kawai ina san kaucewa Aure ne amma ni ba Haka bane,and worst thing din im not even lying,na kasa zama na fadawa kowa sai ke amma kema da nake tunanin zaki tsamoni daga faɗawa halaka kince a'a ."kuka sosai Ta cigaba dayi wanda yazo ma Kiswa cikin rashin zato da tsammani,da saurinta ta koma ta kamo Farry tace "haba Farry mene hakan?Ban dauka wani abun ba sannan nayi zatan hakan zai zama best solution ne im sorry,when are you guys meeting sannan a ina ne"?. Da sauri Farry ta ɗago tace "kina nufin zaki je?" Kada mata kai Kiswa tayi tace "Amma wannan kawai Babu next time dole ne kisan ya zakiyi da rayuwarki sabida you're not getting any younger,dole kiyi Aure kije gida wani no matter abunki,sannan wannan zanje ne saboda na san koda nice a situation ɗinki zakiyi mun Haka,but This should be the last time,no it has To be the last time". Da sauri Farry ta share hawayen ta tace "thank you sister ina mutuwar sanki,lunch time zamu haɗu a "meet up restaurant. " And ai kema Haidar bai motsa ba and ke ya kamata ma ayi maganar Auranki bani ba.,kallanta Kiswa tayi tana san kauda duk wani tunani kafun ttace"well gwanda Ni tunda ina ma da wanda nake kulawa sannan kinsan Auren nan is for your own benefit tunda kina san business dinki as a CEO ALIJUA company dole kiyi Aure kinsan dokan Appa and i work under wasu so stop compering ". ******** 1:30 MEET UP RESTAURANT ABUJA. Cikin shiga wadda Kiswa batayi ta ke takawa dan shiga meet up,sanye take cikin body con mai dogon hannu mai kauri wadda ta fitar Da shape ɗin jikinta madaidaici mai kyan gani,boyfriend jacket ta saka a sama sai dan gyalen da kanta kawai ya rufe,fuskarta dauke take da hard Bitch make up wanda kana kallan ta sau ɗaya zakace wannan tab'ata kaji fitsarace yayin da bakin ta ke dauke da chew gum ɗin da take taunawa a hankali,inda Black lips ɗin da ta saka a lebenta dan charas ras yake motsawa cikin wani yanayi mai kyau, Daga kanta tayi dan ganin table ɗin da Farry ta faɗa mata wanda ke occupied da saurayi wanda ya saka dukkan nutsuwarsa cikin wayarsa da yake faman dannawa ,ta san shine amma dan san clearing doubts ɗinta ya saka tayi dialing numbern sa da Farry ta bata ,tana shiga kuwa wayarsa ta dauki ruri,cikin takun heels ɗinta ta karasa garesa tana making bubbles da cingam din bakin ta,Babu ko sallama a bakita taja kujerar dake kallan tasa ta zauna tana mai yin wani irin ƙas , Dago kai saurayin mai daukar hankali yayi ya kalli Kiswa da wani irin yanayi,itama kallan nasa tayi tana mai ƙare masa kallo,haɗadden saurayine wanda ba domin bad halayyarsa Da Farry ta lissafa mata ba Da ta tayata murnar samun hot smokey handsome guy,ya haɗu iya haɗu,farine amma bai kai Haidar ɗinta fari ba,farinsa irin creamy dark ɗin nan ne mai kyau bugu da ƙari ga hutu,yana da idanu masu brown eyeballs Masha Allah waɗanda kallo ɗaya zai maka dasu kayi shakarsu,bazata iya misalta yanayin kyansa ba mai wani irin sirri wanda Ko wacce irin mace idan ya ɗana mata tarkon sa ta kamu,amma banda ita Kiswa Ubaid domin kuwa Babu wani kyau na ɗa namiji da zai ruɗeta bayan na Haidar. Sanye yake cikin loose baggy riga white da wandonsu shima fari,kansa nada yalwar gashi wanda ke sheƙi Brown wanda ba sai ya faɗa mata ba tasan yayi dying kansa duk da ya fara fading,murmushinn gefen baki tayi tace "exactly like a typical play boy". Cikin wani irin yanayi ya kalleta yace "excuse me?" Bell ɗin dake kan table ɗin ta danna wanda yayi mata kira ga waiter wanda babu bata lokaci yazo,kallansa tayi tace "Wine and two plate of steak please". Kaɗa kai waiter din yayi 'ya juya dan kawo mata abunda tayi order,da kyau saurayin yake kallanta kana yayi wani irin murmushi yace"and what the hell do you think you're doing"? Ƙafarta tayi crossing kana ta miƙa masa hannunta tace "im sorry ban introducing kaina ba,Sunana Fareedha Aliyu ,ka kirani da Farry i bet We are suppose to be here for blind date ,SB Madugu right?" Licking lebensa na ƙasa yayi 'ya Faɗaɗa murmushinsa lokacin da 'ya kula da yarda ƙafar Kiswa take rawa out of nervousness , mutum ne Shi mai sharp kai,kallo ɗaya zai maka yasan inda ka dosa, a fannin KIswa ma ya gane cewa tana san ruining date ɗin nasu ne ta bashi wrong impression akanta,abu guda ɗaya ne bata sani ba shima dole mahaifinsa yayi masa yazo yana bata lokacinsa da sunan jiran mace which is not like Him,ganin yana mata wani irin kallo ne yasa ta janye hannunta ta buɗe jakartta ta ciro cigarette ɗin da ta saka Farry siyo mata,guɗa daya ta ciro ta bubbugata kan finger ɗinta yarda taga yan sigari nayi kana ta kalle shi tace "kana da lighter na manta nawa a gida saboda sauri and nasan baza ka rasa ba Cos i know Babu yarda za'ayi ace you don't smoke". Sake gyara zamansa yayi yana mai murmusawa Cos yana finding Abunda Ke faruwa gabansa interesting,folding hannunsa yayi 'ya kafeta da idanunsa da suke bata shakka yace"a matsayinki Na Yar sigari wadda bata manta sigari bai kamata ace Kin manta lighter ba,'ya kamata ace itace first priority din ki indai da gaske sigariin zakiyi". Rolling idanunta tayi ma maganarsa kana tace"ji yarda kake magana kamar you're saint,shan sigari aii ba aibu bane 'dan nasan kaima bazaka rasa sha ba abeg ni da kai kowa yasan harka kar ka fara mun wasu maganganu". Kafun ya furta wani abu waiter 'ya kawo masu order ɗinsu inda yana kallan sigarin hannun Kiswa yace "im sorry ma''am smoking is not allow here"Dan Murmshi tayima waiter din tace"sadly i left my lighter at home So you see ain't even gonna smoke here ,"murmushi waiter ɗin yayi mata 'ya saka hannu 'ya ciro lighter a aljihunsa 'ya aje mata kan table yace"consider it a gift from me"Murmushi tayi masa kana tace "awwn thank you love". Yana barin gurin ta Maida hankalinta Kan SB madugu tace"well i got a lighter amma kaji sai Na fita,i would manage amma yanzu ga Alcoholic wine how about We party on it then idan mun gama i will booked a nice hotel i love it on a first date? Hannunsa 'ya shafa a kansa kana ya tashi ya kama hannunta ya tasar da ita daga kujerar data ke ,take ya fara janta,ganin idanu sun dawo kansu ya saka ta fara ƙokarin kwace hannunta amma yaki sakinta har saida ya gama biyan kuɗin abunda tayi ordering kana ya cigaba da fincikarta,bai sake ta ba har saida suka bar harabar gurin sannan ya kalleta da wani irin kallo wanda ta kasa fassara na menene yace"mai kike So ki nuna mun ,ko kuma mai kike san achieving ". Mugurɗa baki tayi tace"well abu guda daya nake san nuna maka wanda shine wacece ni,nasan cewa you're not any way better and ni da kai Babu wanda zaiso ya Auri wani Cos dukkan mu muna abunda ɗaya bazai alfahari ace yau ya uwa ko uban yaran sa ba,So Its better muje mu samu masu ɗa'a ba irin mu ba." Dariya ya saka sosai yana mai nunata da yatsa sannan yace"So ni dake bamu da ɗa'a,?"dariya ya kuma sakawa sannan yace "Kin sanni?tayaya kika san Ban da ɗa'a?" Haɗe rai tayi ganin yana neman raina mata wayau sannan tace"a kallonka ɗaya ma ai ba sai ka faɗawa mutum kai play boy bane,you look typically like one,nima kuma idan ka kalleni im not anyway better,kai bari 'na fito maka a mutum ,nasan you're a womanizer,clubber,drunkard ,druggie and a smoker So kar kazo nan kana mun acting saint fuck It up, bana san Aurenka sannan kaima na tabbatar ba san Auren kake ba dan haka ka san mai zaka faɗa a gida". Gefensa ta rabe 'dan ta wuce amma ga mamakinta sai gani tayi 'ya saka hannu 'ya fincikota baya,motar dake bayanta yayi pinning ɗinta da ita sannan yayi mata rumfa da jikinsa,kafun 'ya kai ga furta wani abu ta daukesa da mari wanda yayi mutuƙar shigarsa,hannu tasa ta turesa Tana mai nuna sa da yatsa tace"hungry horny bastard".wucewa tayi har tana mai gurɗewa da takalminta saboda sauri yayin da lokaci guda kuma kirjinta ke dukan uku uku. Tsaye yayi yana binta da kallo inda hannunsa guda ke kuncinsa,he cant blv what happend abunda bai taba faruwa dashi ba yau 'ya sameshi,shi SALEEK mace zata ɗaga hannu ta wankawa mari ba ma wannan kadai ba har da masa ƙazaman ƙazafi,yana tsaye yana wannan jimamin PA ɗinsa Khalifa Adnan wanda ke matsayin abokinsa ,amininsa yazo gurin yana mai faɗin akaramakallu Sir SALEEK 'ya date ɗin and how About Babe ɗin tayi? Tsintar kansa yayi da murmusawa sannan yace" kai 'dan baka da mutunci kasan ni"womanizer ne,drunkard,smoker, druggie,clubber amma Shine ko da wasa baka taba faɗa mun ba" Kallansa Khaleefa yayi da mamaki kafun 'ya kwashe da dariya yace"To ni basan kanayi ba amma Ban sani ba ko bayan barina Australia ka faɗa harka tunda dai ni na rigaka tahowa,"Duka SALEEK 'ya kaimasa yace "dan iska ba abun nayi firing ɗinka nasha wahala ba "a tare suka saka dariya Kana suka taka zuwa ga rantsatsiyar Rolls Royce ɗinsu inda SALEEK ke cewa"mutumina kamun bincike kan yarinyarnan ,ina san nasan wacece ita 'dan im sure ta yau ba version ɗin rayuwarta bane"murmushi Khaleefa yayi yace ka shiga ciki kenan?sosa ƙeyarsa yayi yace "Abeg wane ciki ,i Just find her intresting,ina san nasan wacece ita sannan wanene 'ya jera mata wanchan Ƙazamun ɗabiun a matsayin nawa,i have to punish her for that kaga to do that kuma sai na san more about her".a Haka suka garzaya Khalifa nata mai shaƙiyanci. Koda Kiswa ta isa gida kai tsaye ɗaki ta shiga 'dan tasan a wannan lokaci kowa na ɗakinsa yana hutawa,ille kuwa tana shiga ta tarar da Farry kwance tana bacci,kallanta tayi ganin yarda take bacci peacefully wanda yau da ace ta Auri SALEEK da wannan baccin ma bazata samu damar yinsa ba saboda rashin samun nutsuwa da zatayi da saleek Cos kallo ɗaya zakayi masa kasan ina 'ya dosa,a nata tunanin. Make up ɗin fuskarta ta cire kafun ta shiga bayi 'danyin wanka ,tunanin kala kala sukayi ta mata zarya a kwanyar kai 'dan ta sani muddin Mother tasan da maganar abunda ya faru yau to ta kaɗe ta lalace har ganyenta,bayan ta fito tana saka kaya Farry ta farka tana mai hamma tace "best sis Kin dawo kenan," Wani irin kallo Kiswa ta bata kana tace "Dole kice mun best sis mana ,naje 'na samesa apart from halayyan sa 'na banza da kika lissafa he is a go with Handsome dude i hope Kin samu information a kansa from a good source kar kije ki jamun wahala dan kinsan Mother 'na jin maganar nan sai ta kusa kasheni in bata kashe ni bama kenan" Dariya farry tasa sosai cikin Dariyar tace "calm down babe Babu mai kashe wani after all gobe ma idan 'ya ganki ba lallai ya tuna ki ba,after all the make up was something And maganar Mother kuwa ko da ta baci ina da plan B And na ma san you can never do something like This wrong Yea And lastly Haidar yazo And We went out together . " Kallanta Kiswa tayi tace "haidar yazo and bai kira ni ba? "Uhum,yazo nace masa Kin fita date but ban faɗa masa dawa kika fita ba i was bored and i took that opportunity ta clear up my boredom and i most say he's a nice catch . Bata kuma cewa komai ba tayi bathroom dan daura Alwala tayi Sallah,bin bayin Kiswa tayi da kallo kafun ta ciro wayarta dan kiran Haidar,kamar zata Kirasa amma sai ta fasa ta aje wayan ta cigaba da abunda yake gabanta. Share,react and comment. CHUCHUJAY 08130229878 Follow me on wattpad @chuchujay. [5/4, 3:08 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK KISWAH (Linked By surrogacy ) Na CHUCHUJAY ✍️ Book 1⃣ Page5⃣ Monday Morning. Safiyar litinin ya kasance Kiswa bazata fita aiki da wuri ba sai 10 da rabi dan haka bata fito breakfast ba lokacin da dukkan su sunayi sai wurin Tara wanda lokacin kowa na gidan ya fita har da Baraka mai Aiki wadda ta tafi kasuwa domin siyan kayayyakin da Babu 'na amfani. Fridge ta buɗe domin dauko fresh milk dan ita kawai zata iya sha tunda bata craving wani abinci mai nauyi Cos yau suna da lunch Da chairman Basil ya shirya a kamfanin ta tarbar ɗansa da zai fara zuwa office din yau.,tana kan danna wayarta a yayin da take shan fresh milk din taji kamar ana kallanta,daga kai tayi sabida yarda jikinta ya cigaba da bata Eh tabbas ana kallanta ɗin,kan ya Sageer ta sauke su wanda ke tsaye in a mess Cos daga ganinsa ba sai ya faɗa maka ko wanka baiyyi ba,singlet ce baka a jikinsa sai boxer wanda ke nuna mazantakarsa ta ɗa namiji wadda turawa kewa laƙabi da" morning bone"saurin dauke idanunta tayi cause This is not like Him. Ganin abunda tayi ne ya sakashi yin karamun murmushi kafun ya tako yana mai dauko Cup ya karbi kwallin fresh milk ɗin gefenta ya zuba 'ya fara sha yana maiyyi mata wani irin kallo kafun yace"Kiswa baki ganni bane babu ko gaisuwa"? cup dinta ta kai cikin sink tana mai kunna tap dan wankewa kafun tace"ina Kwana 'ya Sageer baka fita ba ashe ,And Yes you need to get dressed dan you're semi naked,Nasan nima dan baka expecting dina a nan ne ka shigo hakan ,nima yanzu nake san wucewa gurin aiki ,hope you're okay "Murmushi yayi kafun ya tako inda take shedan yana hura masa wata irin sha'awarta wadda ya jima yana faman dannewa,aje nasa cup din yayi cikin sink din sannan ya zauna a gefe yana mai kallanta tana ɗauraye nasa cup din,hannunsa yasa a hankali ya shaafa nata wanda taji zuwan a bazata ,ɗago kai tayi ta kallesa ta ɗaga masa gira ɗaya tace"lafiya dai ya Sageer"? Cije lebensa guda ɗaya yayi yace "lafiya ba lafiya ba,taimako ne nake san kiyi mun wanda ke kadaice zaki iya yinsa a duk duniyar nan". Da mamaki ta kallesa sannan ta taka Dan zuwa aje cup din a ma'adanarsu tana mai cewa"Nikam 'ya sageer wanne irin taimako ne da ni Kaɗai zan iya yinsa duk duniyar nan?Just shot it Allah yasa wanda zan iya ne dan bana fatan wani dan uwa na ya nemi abu gurina na kasa masa kar ma ace 'Kai,'ya sameer ko Farry ,sai dai idan yafi karfina ko kuma ya sabawa mahaliccina". Taune lebensa na ƙasa yayi kafun ya sa hannunsa yana mai rufe gabansa da ke neman fita masa,yana ƙokarin magana muryar Baraka ta katsesa wadda ta shigo kitchen din kai tsaye saboda mantuwan pack ɗin da tayi,a tare suka daga Kai suka kalleta, sallama tayi Kiswa ta amsa tana Mai fadin"baki wuce ba ashe baba baraka" Kallan Sageer tayi kafun tace"wallahi har naje titi nayi mantuwa na dawo,ashe Alhaji karami ma bai fita ba"wani banzan kallo Sageer ya bata ba tare Da ya tanka ta ba ya sauko yana Mai kakare gabansa ya rabe ta gefenta yana Mai cewa Kiswa"sis chat you up later" Okay kawai tace masa tana Mai binsa da kallo saboda ba Haka ta san ya SAGIR ba,tabbas wani abun ba dai dai bane ba,shigowa Baraka tayi itama tana Mai binsa da kallo kafun ta dawo da kallanta kan Kiswa tace "kiswatu Anya sagiru kalau yake"?'dan tabe baki Kiswa tayi tace nima dai Bansan Mai ke damun sa ba Cos ko niyar fita aiki banga yana da ita ba kilan dai yana da uzuri ne,dauko pack din nan rage miki hanya Cos nima yanzu zan fita, "To" kawai baba Baraka tace amma yanayin sagir da yarda ta shigo taga yaana kallan Kiswa abu ne da a matsayinta na babba tasan akwai wani abu a ƙasa,har suka bar gidan ita da Kiswa abun yana ranta tana tunanin ta yarda zata fara fadarsa,kasa hakuri tayi domin tana ganin Kiswa ne matsayin diya a gurinta 'dan haka bazata iya ganin abu zai cutar da ita ba ko ba dai dai ba tayi shiru dan Haka cikin hikima irin ta babba tace"Nikam kiswatu ina san faɗar wani abu ina tsoro Ban san ya zaki dauki magana ta ba" Kallanta Kiswa tayi kafun ta mayar da hankalinta kan tukin da take ta 'dan murmusa tace "Baba Baraka ai ke uwace ko me zaki faɗa mun bazan taba jin haushi ba dan Nasan duk abunda zaki fada gyara ne".'dan gyara zama Baba Baraka tayi tace"nasan ke da yaran Alhaji babu bambanci sannan ku din yan uwan juna ne wanda nake fatan kar wani ya cutar da wani,a gaskiya yau yanayin da naje na riskeki da sagir da yanayin da yake da kuma kallan da yake miki bai gamsar dani ba,bakiga yarda mazantakarsa ke neman fasa wando ba dan banza suyi Aure sun Kai munzali sunƙiyi,ba wai ina san hadaki dashi bane saboda nasan shakuwar ku ta yaran gidan nan amma ina So a kullum ki ringa sakawa a ranki ke dasu ba muharramai bane tunda zasu Aureki basu Auri Farida ba,idan magana ta bata miki dadi ba kiyi hakuri amma wai dama nayi gyarane". Murmushi Kiswa tayi tana Mai packing bakin super market ɗin da Baba Baraka zataje Kafun tace"Baba Baraka ki daina bani hakuri sannan ai maganarki gaskiya ce ba ƙarya ba nasan cewa ba muharramai na bane ,amma abu guda daya wanda na yarda dashi shine na yarda dasu da rayuwata,irin yardar da nayi musu yarda nasan Babu wanda zai kalleni da wani tunani mara kyau a zuciyarsa insha Allah,yarda kuma kika tunatar dani ,insha Allahu zanyi ƙokari wajen ganin na kula" "Allah ya duba yardarki dasu Ƴar nan"shine abunda Baba baraka tace kafun ta fita tayi wa Kiswa sallama ta wuce,bin ta Kiswa tayi da kallo tana nazari a yayin da guri guda kuma take ƙaryata duk wata wasiwasi da ke ɗarsuwa a zuciyarta,take kuma maganar Ya Sageer na taimakon da zatayi masa ya fara mata yawo a ƙwanyar ki,"shin wanne irin taimako yake bukata gareta har yake ikirarin ita kaɗai zata iya yi masa shi?"sanin baya nan da zai bata amsa 'ya saka ta ja motarta dan tafiya Aiki Cos tasan koma menene zai nemeta . ** Kamar kullum yarda ta saba gaisawa da abokan aikinta yau ma hakan ta shiga Building ɗin cike da fara'a yayin da take gaisawa da duk wanda taci Arba dashi a hanyarta ,tana ƙokarin shiga office dinta sakatriyarta Amira ta tareta tana mai faɗin "Ina kwana ma ,barka da shigowa yanzu chairman ke nemanki na faɗa masa baki shigo ba da wuri cos yau 10 zaki zo",cike da girmama Amira ɗin tace"hope im safe ,sannan kinyi forwarding documents ɗin nan zuwa ga office ɗin chairman."? Ƙaɗa kai Amira tayi tace"Nayi Ma'am and as the gossip is going on and on kamar yaran chairman yazo office yau zai fara aiki kafun chairman yayi masa handing over,"ƙarasa maganar tayi cikin ƙasa ƙasa da murya tana mai faɗin"And guess what rumours said he's dead Handsome". Dariya Kiswa tasa tace "kai jama'a Amira,hala yan department ɗin ƙasa suna sa bata mun ke da gulma"dariya itama Amira ɗin ta saka tana mai faɗin"kinsan halin ma'aikata ta gaji Haka 'this,them and that". Kaɗa kai Kiswa tayi tace "And las las na work We go do,bari na aje jakana naje gurin chairman din cos nasan yanzu yana sanin zuwana zai fara nema na." Bayan fitowarta kai tsaye office ɗin chairman ta nufa tana tunanin New headache ɗinta da zai fara kawo mata ziyara 'dan koda ba'a faɗa mata ba tasan yaran chairman Saleek zai bata wahala adduarta kawai Allah yasa wanda baya wasa da Aiki ne,bayan kallo na banza da PA ɗin chairman da fake gaisuwa da ta karba ta nufi office din bisa jagorancin Pa ɗin wadda ta sanar dashi zuwanta, Bakin ta dauke da sallama ta shiga office ɗin yayin da take Faɗaɗa fara'arta,lokaci guda kuma chak sai fara'ar ta tsaya a yayin da idanunta suka dira kan SALEEK wanda ke zaune calmly cikin ash Sweatpants da black polo shirt ,wani irin ras gabanta ya bata inda lokaci ɗaya nutsuwarta ke neman daukewa domin kuwa fuskarsa ba fuska bace da zata manta a dare ɗaya. KISWAH?? Muryar chairman ta fito da ita daga trance ɗinta ,cikin yanayin in ina tace,yeesss.sir Good morning,cike da kulawa 'ya kalleta yace"Good morning but bana tunanin taki safiyar mai kyauce hope lafiya dai" Saurin taresa tayi tace "Lafiya lau sir something skipped my mind ne ,im sorry" Murmuushi yayi yace 'bismillah zauna,And proudly zanyi introducing ɗinki ga SALEEK babban yarona wanda zai gaji kujerata, Kallan SALEEK yayi wanda ya kafe Kiswah da ido yace "my boy meet my lovely beautiful And smart PR officer ,KISWAH UBAID" Murmushin gefen baki SALEEK yayi yace "KISWA UBAID,ga sunanta ma mai daɗi 'dan yarda kaketa koɗata ma Abba ai tafi Haka,bai daina kallanta ba wanda kallan ke watsa mata Chill ta ko wanne sashe na jikinta,"wani irin smirk Saleek yayi da 'ya fahimci halin da ya jefata Kana yace "Anya bamu taba haɗuwa ba"? Cikin dakiya tace"gaskiya ba dai dani ba 'dan Ban taba zuwa Australia ba kaga kai kuma chan kai rabin rayuwarka,maybe dai wata mai kama dani ce"murmushi SALEEK ya kumayi yace"gaskiya to wannan kama ta baci" Baki chairman ya saka masu cikin maganar taso inda yake fadin"kasan Allah yana Haka ,sai kaga wani kuna mugun kama kuma baku ma sa juna ba,And kamar yarda ta faɗa maka bata taba zuwa Australia ba So ba ita ka sani ba amma soon ina sa ran zuwanku tare saboda akwai wani business opportunity da nake So kayi mana grabbing sannan my dear Pr would be of help that i can promise". Gyara zama SALEEK yayi yace "zanji daɗin Haka Abba dan nima ina so ace naje na karbo maka business' ɗin nan yarda bazakace mai yasa ka bani Matsayin nan ba ,and nima ina so ace kana praising ɗina kamar yarda kake praising dear Kiswah ". Dariya chairman yasa yana mai faɗi"i smell jealousy,to naji make me proud my boy"Kallansa ya maida kan Kiswa yace So my dear ga SALEEK nan ƙarkashin kulawarki,guide Him da abubuwan da bai sani ba na cikin company ɗin mu,but mind you he knows business Cos masters ɗinsa gareshi at 29. Faɗaɗa murmushinta tayi nervously tace "insha Allahu sir and nasan dama yaranka koda bai kwaso komai naka ba zai kwaso kwakwalwarka da smartness ɗinka that im sure of.wani irin murmushi SALEEK yayi yana hango girman gut ɗinta domin kowa idan duka makeup ɗin duniya zata saka Babu yarda za'ayi ya manta macen da ta ɗaga masa hannu ta sauke a fuskarsa ,abu guda kuma dake masa zarya yake neman tarwatsa masa tunaninsa shine rashin sanin wacece ita ,Yasan dai da ita Abban sa ya haɗa masu blind tare zai faɗa masa sannan bazai bashi wrong suna ba which he is Sure ba Fareedha sunanta ba Kiswa ne dai dai,to amma wacece wannan Fareedha ɗin and how are they related ? Cos babu yarda za'ayi ace basu da kusanci , Bayan komawarsa gurin mahaifinsa da ya tambayesa blind date ɗinsa Haka nan yace masa yana san ya sake saninta more sannan ya duba yanayi na samuwa da Auren nata zai bashi da amfana inda mahaifin nasa bai masa jayayya ba ya amince masa,dama yaso ace ne daga baya ya kawo masa wasu excuses masu karfi wanda yasan dole ya rabu dashi da labarinta amma a yanzu kuwa wani tunani daban yake domin labarin yazo masa da wani twist da ya ɗauki hankalinsa wanda bazai iya bari ya wuce haka nan ba. Har lokacin da tawa mahaifinsa sallama ta fita yana binta da kallo sannan bai masa doguwar tambaya ba dan ya lura Abban sa naji da ita bangare guda kuma bai san wace ita ba,wannan Aikin nasa ne kuma zaiyyisa da kansa. Wata irin Ajiyar zuciya Kiswa ta sauke lokacin da ta fita daga cikin office ɗin yayin da zuciyarta ke wani irin lugude domin kuwa bata taba tunanin date ɗin Farry heir ɗin Chairman Basil bane which makes him her Boss,da ace ta sani babu ma yarda za'ayi taje date ɗin nan har tayi tarnishing ma kanta image,Babu ma yarda za'ayi hakan ya faru,nervously take cinye farcenta har ta isa office ɗinta inda lokaci guda kuma take dialling number ɗin Farry wadda Batayi picking ba,aje wayar tata tayi kan desk ɗinta tana mai kwantarwa da kanta hankali akan Babu yarda za'ayi ace 'ya ganeta Cos the make up was hard and da ace ya ganota to tabbas zai iya maganarta gaban chairman,sannan a yarda bata disclosing identity ɗinta ko chairman bai san tana da dangantaka da ALIJUA company ba yana ganinta ne kawai as a girl wadda kesan aikinta and take ƙokarin kaiwa wani mataki na nasara a rayuwa inda yake bata goyan baya,abu guda ɗayane bazata dauka ba wanda shine Saleek ya shiga rayuwar aikinta ya lalata mata,dole tayi wani abu. To amma mai zatayi? Tana wannan zagaye da saƙe saƙen taji an buɗe kofar office ɗinta anshigo babu neman izini kai tsaye. CHUCHUJAY ✍️ 08130229878. [5/5, 8:02 PM] Chuchujay✍️: KISWAH (Surrogacy was the cause) Na CHUCHUJAY ✍️ Book 1⃣ Page6⃣ Daga kai Kiswa tayi dan ganin wanda ya shigo,ras gabanta ya fadi lokacin da idanunsu ya sarke cikin na juna, Nemo murmushi tayi gudun kar ta bada kanta tace "Sir barka come in ,feel free,have a sit" Wani irin murmushi yayi wanda baya rabo dashi ganin yarda take raina masa hankali,Takowa yayi ya zauna kan kujerar da ya tabbatar tata ce ya wani juya kafun ya dawo direction dinta yana kallanta,Name plate dinta ya ɗaga wanda ke rubuce da KISWAH UBAID a ƙasan sunan kuma an saka Public relation officer 1,shafawa yayi a hankali kafun ya kalle ta yace"idan da za'ace maimakon karatun da kakayi wasan kwaikwayo kika karanta na tabbata zaki ci abinci mai kyau a gurin,im impressed i must say,Kin iya wasa sannan wasan naki ya burgeni,abu guda ɗayane kika yi a cikinsa wanda nake kira ganganci wato wasa dani da shiga hurumin da ba naki ba,ni ba mutum bane mai boye boye ko kwana kwana dan haka zan tambayeki sau ɗaya ki bani amsa ,wacece ke sannan mai kikeyi a Blind date ɗina maimakon wadda ya kamata ace taje?" Ki fara bani amsa wadda babu karya cikinta domin kuwa idan na kwace bazaki gane ni ba,behind murmushin dake fuska ta akwai wani abun. Kafafunta taji sun fara rawa gudun faɗuwa ya sakata zaunawa kujerar da tayi masa tayi ta nemo dukkan wani yanayi wanda zai saka ta karyatashi ya yarda tace"Naji daɗin haduwa da kai mutuƙa amma inaso na sanar da kai ,na gamsar da kai akan cewa Bansan maganar da kake yi ba ,blind date or what kake magana bansan anything about it ba ranar ma ina gwagwalada"Haɗe rai tayi lokacin da ta kai karshen maganar ta. Dariya yasa sosai wadda ta saka ta maida kalllan ta gareshi,sake hade ranta tayi tace"bansan wanne ne abun dariya ba a cikin maganata with all due respect sir," Nunata yayi da ɗan yatsa yace"exactly with all due respect my dear,bani da isashen lokacin da zaki zaunar dani anan kina mun karya Cos dana zauna a nan bance miki ga ranar da nake magana akai ba So ya akayi kika san ranar da blind date ɗina yayi taking place?" Haɗe rai tayi ta saka serious face tace"well abunda baka sani ba you're the talk of the company So bana tunanin da wanda bai san ka dawo an hada maka blind date ba ranar Sunday,any ways you're highly welcome sannan ina fatan bazan baka wani reason da zakayi complaining dani ba a iya kacin aikin da zanyi da kai,its your welcome lunch today if you will excuse me dan ina san zuwa gurin da mukayi reserving dan duba abunda ba'ayi ba domin faranta maka shine first priority ɗin mu a yau" Tashi tsaye yayi ya kalleta da kyau ya sake darawa Kana ya tako inda take yace"deny it duk yarda kike So amma ina san kisan abu guda daya zan kamaki kuma zan hukuntaki fiye da yarda baki zato,Its a pleasure meeting you Dear KISWAH UBAID" Yana kai ayar maganarsa ya fita inda ya bar KIswa da wata irin faduwar gaba,wayarta ta jawo ta cigaba da dialing numbern Farry amma still bata dauka ba,cikin gaggawa ta tura mata saƙon "Call Me back Asap". Jakarta ta dauka ta fita a office din 'dan zuwa duba gurin da aka tanada domin taron,tana fita ta tarar da Saleek 'na magana da wani saurayi wanda bazai wuce shekarunsa ba,ganinsa kawai sai da ya haifar mata da faduwar gaba,tabbas Farry ta saka ta a chakwakiyar da bata san ta inda zata fara tunkarar ta ba,amma abu daya ta sani wanda shine dole tasan yarda zatana avoidinq SALEEK ko yaya ne,saita kanta tayi ta cigaba da takunta 'dan wuce su amma kafun ta ƙara taku ɗaya daga bayan su Saleek ya kira sunanta yana mai cewa "yauwa Kiswah meet Khalifa my best man And PA,Khalifa meet Kiswah pride ɗin Abba cikin company ɗin nan,"cije lebenta na ƙasa tayi tana mai jin kamar ta ruga da gudu,ajiyar zuciya tayi ta juyo tana mai saka fake smile ta kalle su tace"Good morning Its nice meeting you". Murmushi Khalifa yayi ya miƙa mata hannunsa yace"the pleasure is mine angel". Kallan hannun nasa tayi sannan ta kalli fuskar SALEEK wanda ke faman wani irin smirking wanda bata san mai ya kunsa ba,dawo da kallanta tayi kan Khalifa tace"im sorry but i dont do hand shakes" Wata irin dariyace ta kwacewa SALEEK wadda sai da yasaka hannunsa ya rufe bakinsa kafun yace "says a girl who smoke". Wani irin kallo ta bashi na takaici kafun tace "excuse me"bata jira mai zaice ba ta wuce su tana mai runtse idanunta ,ta sani ba sai an faɗa mata ba she don fuck up. Bayan wucewarta Khalifa ya Kalli SALEEK yace "Man that was rude mene nayiwa innocent statement dinta dariya,ni ta burgeni Cos she values abunda addininta ya hana so Ban dauke sa big deal ba 'dan tayi rejecting handshake". Wata Dariyar Saleek ya saka kafun ya dafa kafaɗarsa yace "calm down man kar kyanta ya ruɗeka ka fara tunanin zura jiki dan nasan halinka da mata wannan yarinyar kuma da kake gani She's not who she seems to be akwai wani abu behind her wanda tabbas zan gano menene shi". Wucewa yayi shima ya bar Khalifa da sake saken abunda yake nufi. ***** Kamar yarda chairman baiyi expecting flows ba Haka nan taron da aka ƙirkira domin Saleek ya tafi perfectly kowa yaci to his own satisfaction sannan chairman yayi speech mai karyar da jikin mai sauraro inda yake sake shaidawa kowa a gurin Shi talakane a da wanda abincin da zai saka ma a baki yake wahala ,yarda 'ya gina FOUNDATION ɗinsa from Scratch ,using tears,sweats and blood sannan yake farin ciki Na zuwa ya huta domin bawa magajinsa guda wannan gurin dan tayashi gina legacy ɗinsa, Tafi gurin ya dauka Kana Saleek yayi nasa speech ɗin inda yake assuring zai bada gudunmawar da mahaifinsa zai alfahari dashi,fatansa guda ɗayane shine hadin kan ma'aikatan domin kuwa sai dasu komai zai zama masa dai dai, Haka nan welcoming lunch ɗin Saleek ya kasance cikin jin daɗi yayin da yan matan kamfanin ke ta koɗa haduwarsa da humbleness ɗin sa,not like a regular young arrogant And snobbish billionaire. Bangaren Kiswah kuwa hankalinta ta maida kan abunda ya dameta dan idan zata ɗaga kai sau dubu sai idanunta sunyi arba da Na Saleek ,wayarta ce da tayi ƙara ta bata damar tashi a gurin dan zuwa amsa kiran wanda baki daya yau bataji muryar sa ba,bayan zuwanta inda babu hayaniya ta ɗaga wayar tana mai fadin"ran abun alfaharina ya dade" Murmushi yayi daga ɗayan bangaren yace"come down stairs "sake maƙala wayar tayi a kunneta ta lumshe idanunta tace"kazo company ɗin mu hala,And muna throwing ma yaran chairman ɗin mu welcoming lunch but give Me a Moment yanzu Zanzo ina sameka don a gaba kake da abunda nake yanzu a rayuwana". Wata irin ajiyar zuciyar jin daɗi Haidar yayi saki kafun yace"babyyy kina tunanin zan taba mistaking inda kike bayan kina tafiyane da akalar tunanina da alamurana,so get down And see your man" Kamar yana kallanta ta saki wani irin murmushi mai sanyi kafun ta fara takawa domin sauka ƙasan da ya bata umarni tazo, Tana barin gurin Saleek dake boye yana sauraran wayar da take ya fito daga gurin boyansa yace "so she even have a man,well muje zuwa a yau sai na san wacece ke And menene dalili ki da hujjarki na aran identity' ɗin wani,Cos dole yasan Kiswah version is her identity not Faridha". Tana sauka ta fara ɗaga ido tana neman inda zata hango Haidar,har lokacin wayarta na kunneta bata cire ba,taune lebenta na ƙasa tayi tace "Baby just show your self mana ,"murmushi yayi yace kizo inda kikayi parking motan ki,Babu musu ta taka inda ta aje motan ta tana cewa "i hope you're not playing any frank"tana isa figure din sa yayi mata sallama jingine jikin mota irin tata sak komai da komai,maida hankalinta tayi kan tata motan Wadda ke aje inda ta aje ta Kafun ta sake maida kallanta kan HAIDAR wanda ke faman kada key a hannunsa yana mai bata expensive smile ɗinsa mai kasheta, Cire wayarta tayi a kunnenta tana mai kallansa cikin ido tace"okay now tell Me motan wanene wannan kuma"? Murmusawa yayi har haƙoransa na fitowa kafun yace "tawa of course,na siya mota ne irin taki dan na nuna miki zan iya zuwa ko wanne level akan ki muddin nan kike san muje,i dont mind na ringa hawa okada indai kema Shi zaki hau ,so daga yau bazan sake hawa wani luxurious car ba sai wadda kika hau ,so daga yau ga motan Haidar nan masoyin Kiswa". Cike da kulawa ta matsa kusa dashi tace"habibi this is not necessary and i told you wasa kawai nake maka ,you dont have to stood to this so abunda ya hanaka nemana koda jiya kenan ka fita da Farry". Kashe mata ido guda ɗaya yayi yace"Well ina san baki surprise ne so Farry ta rakani siyan mota irin naki And We went for lunch after that,she was teasing Me wai na fara tunani irin naki ,kinsan Shi soyayya babu abunda bata sakawa,a nawa bangaren kuma soyayyata takice komai kuma zan iya domin zama dai dai dake so tell Me Farry tace mun you went on a date ,who was it with,it doesn't matter idan ex boyfriend ne,stalker Ko crusher cos duk zanji dasu dan yanzu you're mine i just cant wait to mark you kowa ya gani ya fahimta" Dariya ta saka ganin yarda ya kare maganar tasa Kafun ta jiingina ita ma da mota tace"business date ne naje so calm down kar ka fasa ma mutum baki cos Ba sai kayi marking dina ba duniya zata san ni takace And only yours,juyo da fuskarta tayi tana kallansa tace'i really do love you habibi ,bana ganin Ko wanne namiji a matsayin kallan da nake maka,i can give up my everything for you idan da bukatar hakan,my identity,my work ,my life and everything indai iyuwar hakan ta kama,but kamar yarda kasan sirrin zuciyata da irin raunin da take akan ka ina roƙonka kar ka karya ta,Ban san soyayyar wani da namiji ba bayan kai bama mahaifina ba cos ban ma rayu dashi ba ballantana Nasan dadin soyyyarsa". Dan shiru Haidar yayi yana kallanta,da ace tasan yarda zuciyarsa ke fitinar santa da bazata taba kawowa zai karya tata zuciyar ba wata rana,kallan sa itama take inda ta hango moist na ƙwalla a gefen idanun sa, nuna sa tayi da ɗan yatsa tace"habibi mene a idanunka kamar hawaye?" Saurin gogewa yayi yana mai cewa"Na sanki ne kafun ya saka dariya yace"how wish nayi recording confession ɗin nan na bazaki iya rayuwa Babu ni ba for future use. Dariya suka saka a tare Cos sai a karshe dukkan su suka bama juna dariya,juyawa yayi ya buɗe motan yana mai fadin"kar na manta da kyautar ki," Dan shagwabe fuska tayi tace "kai kam baka gajiya da batani da kyauta kullum idan zaka zo gurina" Ciro dan box yayi daga motan yana mai cewa"well ba hakarum bane idan nayi spending ma matata kuɗi after all ina dasu kuma dan na kashe miki nake nema,"miƙa mata box ɗin yayi da ƙaramar package bag ɗin da yake ciki yace ba yawa. Ƙarba tayi tana cewa"awnn you're such a durlyn,tana buɗe wa idanunta suka ci mata karo da diamond necklace dake ta faman sheƙi"saurin kulle box ɗin tayi tana mai kallansa tace "no no Baby i cant take this" Motansa ya buɗe ya shiga ya mata key kafun ya kalleta ya kashe mata ido daya yace"you're welcome and i love you to the Moon and back,kiss yayi blowing mata da hannu kafun yace "na samu charge dina ta hanyar ganinki ,kinga yanzu Zan iya aiki cikin walwala Babu kasala, Ɗaga mata hannu yayi ya kunna motan yana mai bata murmushin nan nasa mai kyau,itama murmusawar tayi tana mai ɗaga masa hannu kafun ta ciro wayarta ta tura masa saƙon"lets have dinner ,Its on me".kallanta yayi yayi saluting dinta bayan ya kashe mata ido daya kafun yaja motarsa ya bar harabar gurin. Tsaye tayi tana sake duba sarkar da ya bata tana murmusawa cike da shaukina inda a zuciyarta take addu'ar Allah ya sa hutunta yazo mata da wuri shekararnan taje Bauchi ta fara bawa Mamanta labarin Haidar ,ya kamata tasan da labarin wanda ke kaunar ƴarta fiye da yarda yake san kansa its high time,tafin da taji anayi a bayanta shine abunda ya katse mata hazari ta juya... TBC CHUCHUJAY ✍️ 08130229878. [5/6, 8:16 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na CHUCHUJAY ✍️ Book1⃣ Page7⃣ Da mamaki Kiswah ke kallan Saleek wanda ya bayyana gaban ta yana tafa hannunsa yayin da fuskarsa ke dauke da wani irin murmushin da take ji kamar ta cire masa Shi da tafin hannunta domin ba sai ya faɗa mata ba labe yayi mata, Cike haɗe rai tace"na haɗu da maza kala kala amma Ban taba haɗuwa da ill mannared irin ka ba,bana tunanin ka samu tarbiyya sanin menene labe akan maganar wasu take nufi,idan kuma ka samu to a wannan gibar bakayi amfani da ita ba. Wani irin haɗe rai Saleek yayi domin maganar ta tayi masa zafin da bai tunanin zatayi masa ba,cikin mutuƙar bacin rai yace"Ko Me zaki ce kar ki fara jimamin yama tarbiyya ta take Cos bana tunani Kin fitini ta wani guri Cos Your personality is a mess,kinsan bake nake tausayi ba shi wanchan guy din da ya wuce shine yake mugun bani tausayi saboda he's in a deep shit da yayi getting involved da Gold digging bitch kamar ki,Just imagine baki Ko jin nauyi da tsoran Allah,mata irinki mayaudara maha'inta babu waɗanda Ban gani ba,running from one man's pants to another..... Marin da ta dauke sa dashi cikin hawaye shine abunda ya katse masa hanzari ,hannun sa ya ɗaga cikin fushi ya daki gefen motarta yana mai faman huci kan ya kama hannunta da karfi yace"This should be the last time da zaki kuma daukan wannan hannun naki mai kama da bulaliyar kara ki taba fuskanta,sannan ki gode ma Allah bana dukan mata da yau sai na fasa miki baki,and for Your information i heard it jiya kece kika je date dina wanda dama na sani i would never be wrong ,ki shirya saboda i will sue you for slender idan ba haka ba ba sunana Saleek ba " Sakin hannun ta da ya damƙe da karfi yayi ya juya a fusace yana mai fadin"useless girl". Kuka ta rushe dashi tace"you're the must useless stupid jerk I've ever meet sannan idan ka sake shiga hurumina Zan ci maka mutunci fiye da tunanin ka,wawa kawai" Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da tafiya zuciyarsa kuma na masa wata irin zafi da ƙuna na tabbatarwa da yayi cewa Kiswa itace taje gurin sa jiya abunda kuma ke sake soya masa zuciya shine rashin sanin dalilin yin hakan,tunanin sa ya fara bashi kilan dan kuɗi tayi,maimakon ya koma ciki sai ya shiga motan sa ya bar harbar gurin zuciyarsa nayi masa wani irin tuya da ba zai iya fasaltawa ba. ****** SALEEK BASIL MADUGU babban ɗa a gurin Chairman Basil Madugu da matarsa Hajiya Asiya,asalinsu mutanen cikin Kauyen Gwagwalada ne dake cikin garin Abuja,mahaifinsa Chairman Basil ada talaka ne wanda idan ka kallesa a yanzu da da zaka daɗe kana karyatawa akan bashi bane waninsa ne,rayuwa yayi shida matarsa da yaransu guda ɗaya Habib cikin yan uba wanda suka sakashi gaba cike da tsangwama da takura musamman da 'ya kasance shine bashi da komai ,rashin jituwa da kuma rashin daɗin zama shine ya fito da Chairman Basil daga cikin Gwagwalada inda 'ya tarar da Alherin sa cikin garin na Abuja,Rayuwa da daɗi babu daɗi haka ya dage wajen ganin ya gina rayuwar yaran sa Habib da matarsa Asiya mai hakuri da juriya,lokaci ɗaya ciwan cancer ya kama Habib ta kwakwalwa wadda ke neman maƙuda kuɗin da za'a shawo kanta amma duk yarda ya buga ya buga a kulle ga dukkan wasu samuwarsa ta ta'allake kan ciwan na Habib,ganin abun yaci tura ga habib na buƙatar a fitar dashi kasar yasa ya koma gida domin a siyar da gadonsa a raba a bashi amma abunda ya tarar yafi na da domin kuwa karyata kasan cewarsa jinin mahaifinsa sukayi sannan suka masa korar kare,baƙin ciki goma da ishirin komawarsa gida ya tarar da gawar Habib,yaci kuka iya kuka domin shi daya Allah ya basa ga kuma bakin ciki Na karyata identity ɗin sa da yan uwansa sukayi bugu da ƙari har da manyan garin waɗada suka san tabbas Shi ɗin jin mahaifnsa ne amma suka juya masa baya saboda abun duniya,yayi fushi mutuƙa wanda ya sakashi rantsuwar babu shi babu danginsa har abada,a haka ya rungumi matar sa suka cigaba da rayuwa inda 'ya samu wani uban gidan da yake aiki karkashinsa cikin aminci da amana,a hankali arziƙi ya fara zuwar masa kasancewar 'ya samu uban gida na gari mara mugunta ,yana da nasibi na kasuwanci dan a kome 'ya taba sai albarka ta sauka cikinsa,lokacin da ya samu shago na kansa Asiya ta samu cikin Saleek wanda Chairman Basil ya kwallafa rai akansa ,kulawa ga Asiya kuwa sai tafi ta da a haka har ta sauke cikin Saleek wanda suka dauki san duniya suka ɗora masa,haihuwar Saleek kuwa kamar an ƙara masa arziƙi haka arziƙinsa ya cigaba da habaka,kafun kace mene abun yasha banban Dan shi mutum ne maiyi da gaske,Ko ta ina kasuwanci zuwa masa yake ana damawa dashi, Lokacin da Saleek ya shiga shekara goma Asiya ta samu ciki lokacin kuwa arziƙi yafi na da Dan Mijinta mutum ne mara mugunta,cikinta na shiga wata tara ta haifi tsankaɗeɗiya yarinyarta mace wadda taci suna Amatul'islam ,baya ga nan likitoci suka tabbatar wa da chairman Basil haɗarin dake ga sake daukar cikinta saboda wahalar da tasha ga girma Dan haka ya hakura da haihuwa suka rungumi yaransu biyu cikin kauna da tarbiyya dai dai gwargwadon da baza'ayi Allah wadai da iyayensu ba, haka nan suke rayuwa mai inganci inda Suke bawa yaransu kuma karatu mai kyau kar ma ace Saleek dake kan gaba a karatun,cikin kiftawar ido Chairman Basil ya fara planning company dinsa wanda cikin aminci abun 'ya bawa kowa mamaki,a haka ya fara gina kasuwancinsa da haɗaka ta mutanen da baya tsammani,lokacin da Saleek ya isa shiga secondary school mahaifinsa 'ya juya akalar karatunsa ƙasar Australia inda yayi baki ɗayan rayuwar karatunsa har masters,wanda lokacin da ya kammalata ya dawo da akalar rayuwarsa ƙasa Nigeria domin taya mahaifinsa gina legacy ɗinsa, Saleek irin mazan nanne haɗaɗu masu san gayu waɗanda Kana kallansu sun san kan gayun,haduwarsa ta saka yake sace zuciyar yan mata wadda Babu inda yake kaisu saboda a nashi yarda da kan"he's not ready for commitment of any sort,ya dauki relationship bata lokaci musamman idan ya kula da san kuɗi irin na matan yanzu,maganar kuwa wani true love or shit bai daukesa da gaske ba,he Just dated have fun in the Name of dating Then ya Kana gabansa ,although dating ɗin da yake is platonic amma 'fa ba Shi yake nufin he's Serious about you ba,lokaci kaɗan zai rabu dake ki ya kama gaban sa,shiyasa lokaci da dama yake daukan hakan bata lokaci ya share yan matan," Duk wani kuɗi da suke dashi baya taba mantawa da asalinsa Shi yasa baya daga cikin masu fariya da almubazuranci dan kawai yana dashi,a kallo daya zaka masa kallan marasa ji amma a zahiri kuwa mutum ne Shi mai sanin ya kamata wanda baya wasa da addinin sa,he's a very religious man abunsa guda ɗaya wanda yake fama dashi shine fushi,yanzu zaiyyi losing temper ɗinsa musamman idan abun yazo da an raina masa hankali Ko anyi wasa da tunaninsa kamar dai yarda ta kasance bangarensa da KISWAH. Dama dai ɗan Adam baya taba cika goma taran nan dai haka yake dole ka sameshi da flows. *********** Kiswah bata bari abunda ya shiga tsakaninta da Saleek ya hanata zuwa gama Abunda yake a wuyanta ba,bayan gamawarta kai tsaye reserving inda zatayi having dinner da Haidar tayi saboda she needs to clear up her head ,gidan ta wuce domin freshing up kafun ta je gurin cin abincin, Tana shiga falo ta tarar da Mother da Appa suna zaune suna hira gwanin Ban sha'awa,duk da girmansu amma akwai wannan shaƙuwar tsakanin su,da far'arta tayi musu sallama inda Suka amsa a tare harda Mother wadda abun yazo ma Kiswa a bazata, Gaidasu tayi kana tace "sannunku da gida"alamu Appa yayi mata da hannu yace "yauwa Kiswah zo zauna abun kirki ne da Mother take san yi wanda ya sa ni jin daɗi har raina,zo kiga picture ɗin nan " Babu musu ta taka dan zuwa ganin hoton dake tab ɗin hannun Appa ,namijine wanda kana kallansa kasan yaje ma 40s ɗinsa,kallan Appa da Mother tayi kafun tace "Wane wannan ɗin Appa im i suppose to know Him?"dafata Mother tayi tace"of course hayatee dan hes Your husband to be sannan Ban zaba miki shi ba sai da na tabbatar da cewa na gamsu dashi da halayyarsa"hes from our firm,sunan sa Barrister Aliyu maitama,very calm young and collected man,recently matarsa ta rasu ,suna da yara biyu so he talked to Me about you nace masa ya bari naji naki dan bazan mikii dole ba duk da Nasan baza ki taba ƙin decision ɗina ba ,trust Me Aliyu is a very nice man,kinga idan waccan yar uwar taki taga Kin motsa she have no option da ya wuce ta motsa itama you guys are hitting 25 and yet still Single. "But im not single mother"Kiswa ta tsinci kanta da faɗa"gyara zama Appa yayi yace "okay this is getting more interesting,so dotana is not single yet bani da koda slightest information akai?" Saurin tare ta Mother tayi tace"so dama kana rasa su da samari masu hure musu kunne ne my dear?"Ai dama akwaisu amma Na Auren ne babu Wannan kana ganinsa ba sai an fada maka ba wasa yazo ba and na tabbata zai riƙe Kiswa cikin Aminci. Sake kallan Appa Kiswa tayi a karo na biyu tace "Appa ina da wanda nake tare dashi sannan Ko yau akace ya fito zai fito,nice dai Ban basa dama ba...dukan cinya Mother tayi ganin Kiswa zata baro mata ruwa tace"Its okay take Your time ,and Kije ki sake tunani akai and bazan so ace Appa ya fara jin wanene lucky guy ɗin nan ba,zamuyi magana Then zanwa Appa ɗinki magana"wani irin kallo Kiswa ta bata tana hango tsanarta kiri kiri a cikin idanunta,tashi tayi tace to Mother bari naje na watsa ruwa,jikinta a sabule tabar gurin tana mai jiyo Mother na janye hankalin APpa daga maganar da ta fara,abu guda ɗayane bata sani ba,akan Haidar ta shiya fito na fito,dan bazata bari a tauyeta ba akan rayuwar da zatayi da namiji a matsayin matarsa, Tana shiga ɗaki ta tarar da wayar Farry na disco daga bathroom kuma tana wanka tana bin waƙar,"ƙaramun tsaki tayi ta shiga walk in closet ɗinsu domin cire kayan jikinta"bayan ta fito ta tarar da Farry tana drying jikinta,kallanta tayi zuciyarta na mata wani irin zafi tace"Amma Farry kinga kiran da na ringa miki earlier amma baki damu da ki biyo ni ba kiji menene ,ba kuma daukar wayarkine bakiyi ba cos yanzu ma waƙar banza kikeyi kina bi kina cikin banɗaki". Kallanta Farry tayi tace"Kiswah free me abeg,kinsan irin abunda 'ya sha kaina kuwa yau gurin aiki,and i saw kiranki daga baya ban kiraki ba saboda Nasan dole guri ɗaya zamu Ƙwana. Tsaki Kiswa tayi tace "dont give Me that attitude,kinsan ai ba duniya zaki bani ba dazan ta kiranki adadin wanda na miki tunda ba mahaukaciya bace ni dole akwai dalili,wani kallo Farry ta bata kafun tace"Abeg Kiswa kar mu fara ni da ke kowa yana buƙatar hutu to mu huta mana ". Kiswa bata kuma cewa komai ba ta shiga bathroom domin yin wanka,bayan ta fito Ko kallan Farry Batayi ba ta shiga closet ta dauko riganta dinkin Bubu ta saka ,tana kan saka pin barimar da ta dauko Farry ta taso tazo inda take lokacin da idanunta suka sauka kan Diamond necklace ɗin da Haidar ya siya mata ,saurin saka hannu Farry tayi tana mai cewa"girl who gave you this"? Hannunta Kiswa ta buge tace"don't touch my stuffs cos wallahi zan bata miki,tunda ke baki da kirki,kanki kawai kika sani,Kin saka ni a mess wanda danke na shiga amma saboda san kai bazaki ma saurareni ba wato naje nasan abunda zanyi, to ki sani Saleek yaron da Appa yayi fixing miki date dashi naje maimakonki Boss ɗina ne a gurin aiki,sannan he knows cewa bani ya kamata ace naje ba,'ya ganeni so ki shirya yiwa Appa bayani dan zan faɗa masa komai na ɗauki duk wani hukunci da zaimun it doesn't matter any more" Juyawa tayi ta dauki jakarta tana Mai sake duba wayarta dan bata san tayi dare a waje Shi yasa ma tayi fixing dinner ɗin seven dan ita ke nunawa kanta ba dai dai ba amma indai ta Mother ne to ta kwana waje,bata waiwayi Farry dake tsaye cikin rashin sanin Mai zatace ba ta nufi sashen Baba baraka domin yin sallarn Magreeb Kafun ta fita. Bayan ta idar ta nufi sashen Mother domin sanar mata da zata fita duk da tasan Ko a jikinta,ille kuwa da ta sanar mata din cewa tayi"ba damuwa ta bace kawai dai ina sake baki shawarar using protection sabida komene kikayi a gari mu za'a zaga,so enjoy it while It last" Irin maganganun nan na Mother suna shigar mata Zuciya amma ta zabi datayi ignoring domin tasan abu ɗaya da Mother ke so shine lalacewart da yin Abunda Appa zai Allah wadaran da ita wanda tayi ma kanta Alkwarin bazata taba bari ba insha Allahu. CHUCHUJAY ✍️ 08130229878 [5/7, 8:23 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na CHUCHUJAY ✍️ Book1⃣ Page8⃣ Tun fitar Kiswa daga gida taga kamar ana binta a baya ,juyowa tayi dan ganin wanene dan for sure bin nata ake,"'ya Sageer ?"ta furta tana Mai kalllan sa ,Takowa yayi inda take yana Mai sosa ƙeyarsa yace "sai ina"? Faɗaɗa murmushin ta tayi tace "wallahi im going out for a dinner date ne so bana san nayi dare nake san nayi making ɗinsa fast,". Kallan agogon hannunsa yayi kafun 'ya maida kallan fuskarta yace"so my Baby sis have a man amma baki taba faɗa mun ba har ma kinyi girman zuwa dinner date da namiji" Dan ƙaramun murmushi tayi tace "'ya Sageer mana,ina jiran lokaci ne nayi introducing ɗinsa gida wanda ina Ganin lokaci yayi cause i don cast,"maganarta ta ƙarasa tana mai ƙokarin saka humour a ciki amma ga mamakinta ya Sageer bai responding ba illa ma haɗe rai da yayi kafun yace"what if idan nace baza kije ba". Ganin yarda yayi magana in a Serious tone ne ya saka Kiswa cewa"Dan Allah ya Sageer kar ma ka faɗa saboda bana san a tashi yau ina daga cikin masu yiwa yayyuna rashin biyayya,and idan kace kar naje inda haidar yake a yanzu bansan ya zan hana kaina ba saboda na saka masa rai tun dazu yake kira na,idan kuma banje ba i swear bazai ci abincin dare ba ni kuma i cant sleep with that fact!" "Inyeeeeh"muryar ya Sameer ta bayyana bayanta"wani irin kunya ce ta lullube ta dan da saurinta ta juya ta bar gurin dan bata san mai zata kuma cewa ba domin sai da ta gama maganar kunya ta kamata ,She's so much in love da take mantawa da kawaicii akan Haidar domin kuwa taga idan ta biyewa kawaici za'ayi mata sakiyar da ba ruwa . Kallan Sageer sameer yayi yace "mai yasa zakace zaka hanata fita ,shes matured enough' sannan i trust Kiswa bazatayi abunda zamuyi Allah wadaran da ita ba,nasan abunda kake ma tarewa kenan,Chill and calm down dole wataran gidan wani zasuje and idan ba yanzu ba sai yaushe". Dan murmushi sageer yayi yace "bro kasan mazan yanzu ne burin su su dauki advantage na mace ,ni kuma bana san wani abu makamancin haka yake samu sisters' ɗina ".dafasa Sameer yayi yace "insha Allahu sai dai Alheri bari na shiga ciki naga kamar zaka fita ne". Wucewa Sameer yayi yayin da Sageer ya bi bayan motar Kiswa data fita da kallo yana Mai jin wata irin fitina na dukan Ko wanne sashe na zuciyarsa dangane da ita. ******** Tsaye black BMW din mother take a bakin katafaren Boutique ɗin dake dauke da suna ZEE BULA Fashion House tana mai duba wayanta dan kar taran da take hari ta wuce bata gana da hajiya Zainaba Bula ba ,yau zata nunawa Kiswa mene ake kira da kuɗi da isa da kuma karfin burin Uwa, Tana wannan tsayuwa kuwa motar Hajiya zainaba ta faka inda Bodyguards ɗinta suka fito su biyu suka buɗe mata ƙofar mota ta fito cikin shiga ta alfarma,yar gayuce mai harka da abunda ya shafi gayu shiyasa Mother ma ta kashe nata gayun dan zuwa ganawa da ita,sai da ta Bari Tayi wurin minti ishirin da shigaa ciki Kafun itama ta fito ta kulle tata motan ta nufi ciki ,bayan dan zagaye da tayi a ciki ta haura sama da taimakon ma'aikaciyar gurin domin ganawa da Md wato hajiya Zainaba,da fari basu bata dama ba amma da sales manager ɗin taga irin shigar jikin Mother sai jikinta ya bata ƙawar Hajiya BULA ce dan sukan yawan kawo mata ziyara shiyasa Mother na mata ihsani ta mata iso zuwa sama,bayan zuwan su PA dinta ta kira waya akan tayi baƙuwa,bata expecting kowa dan haka tace Ko ma Wane yayi booking appointment tukunna. Nacin Mother da persistence ya saka Daga karshe Hajiya Bula tace a mata iso ta shigo ,kallan katafaren ofishin Hajiya Bula Mother ta fara Kafun ta fito daga wani daki da yake na hutawanta fuskarta Babu yabo Babu fallasa,zama tayi tana mai kallan Mother cikin kallan Ban sanki ba Kafun tace"barka Ina fatan dai wannan zuwan naki mai amfani ne a yarda na karbeki babu Appointment sai gashi kuma yazo da ban ma san fuskarki ba,hope im safe." Murmushi Mother tayi Ta saka hannunta cikin jakarta ta ciro office card ɗinta tace"sunana Barrister Juwairiyyah ALIJUA,mijina shine Founder kuma babban shareholder na ALIJUA inda ni kuma nake babbar Barrister wadda ake damawa dani shekara talatin da uku kenan,bazan bata miki lokaci ba sannan bazan beating around the bush ba,wayarta ta kunna a dauko hotan Farry wanda ta gaji da haduwa ta miƙa mata tace"take a look wannan yarinya tace sunanta Fareedha ALIJUA sannan youngest CEo dake ruling babban FOUNDATION na ALIJUA da confidence' ,Nasan kina da yaro Haidar i mean Wane bai sani ba,sannan duk wanda ya sani yasan shine sanyin idaniyarki ,a matsayina na uwa na zauna nayi tunani a cikin society dinmu da status ɗinmu abune na kwarya tabi ƙwarya sannan na dauki step ɗin nan ne domin Farry dake crushing kan HAIDAR and matsayina na uwa kinga i can stoop to kowane level domin farantawa yarinyata inda nasan kema a gurinki haka yake, Ina san mu kulla alaƙa ta hanyar Auratayya tsakanin yaranmu,ki daukesa proposal na ƙaruwa domin Farry bazata taba zama liability ba ga Haidar tunda itama ta da akwai,im Just looking out for us tunda koda Ban faɗa miki ba kinsan duk macen da zata bi Haidar kudinsa da kyansa ne,shine reality' ɗin mu a yanzu,shine dama abunda ya kawo ni har na zo Babu appointment ina fatan dacewa". Shiru Hajiya Bula tayi tana kallan Mother tana jinjina guts ɗinta,wani dan madanni ta danna kan desk dinta wanda cikin minti ƙalililan PA ɗinta ta shigo tace"Yes ma" Kallan PA ɗin hajiya Bula tayi kana tace ma Mother tea or coffee? Murmushi Mother tayi tace"coffee ,"Kaɗa Kai Hajiya Bula taya tace"two cups please," Bayan fitar PA din Hajiya Bula ta kalli Mother tace"kinzo mun da magana mai kyau i must say sannan kina da yarinya mai kyau,ta shiga raina sannan straight forward halayyarki ta burgeni itama ,bazan watsi da tayinki ba amma ina so ki sani ,Haidar shine abu mafi soyuwa a gareni dan haka idan yacee yarki batayi masa ba babu abunda zan iya miki illa nace kiyi hakuri but kamar yarda na faɗa miki yarinyarki tayi mun zan gani"murmushi Mother tayi dan tasan Babu namijin da zaiƙi Farry ɗinta saboda tata ƴar farace tas ita kuma Kiswa baƙa sannan koda ace Haidar yasan Farry tasan bai taba kawo maganar nan a zuciyarsa ba and bata tunanin yasan cewa Kiswa yar riƙoce ba yar gida ba,tasha Alwashin Kiswa bazata Auri Haidar ba Shi ɗin tanadin Farry ne. Bayan sipping coffee ɗin da Mother tayi tana mai sake shigewa Hajiya BULA sosai dan bazatayi ƙasa a gwiwa ba,sallama Mother tayi mata yayin da Hajiya Bula ke kan juya office card din Mother tana mai yin nazari akanta ,wani bangare na zuciyarta yana san gamsuwa da tayin Mother inda dayan ke mata wasiwasi,duk da haidar bai taba zama yace mata yana da budurwa da yake gani ba amma jikinta da abunda ta fuskanta akwai mace a rayuwarsa amma koma mene zata sani. Da wuri hajia Zainaba ta tashi yau cos dama daɗewarta idan tayi sosai bayan sallar isha'i ne,Tana shiga shahararen falonsu ta tarar da Tasleem wadda ke aikin danna waya,Jakarta ta cilla mata tana mai fadin"aikin ki kenan danna waya kamar mai wani muhimmin kasuwanci a cikin"tashi Tasleem tayi tana mai Faɗaɗa murmushin ta tace"Ummi sannu da dawowa ,takowa tayi tana mai kama hannun Ummin tana matsawa Kaɗan tace"and Ummi nasan so kike na faɗa miki Me nake a waya to i will tell you,brother Haidar ya bani 1 million na fara business ɗin snacks ɗin da nace miki ina so na fara and i didn't even ask him," Takawa Ummi take Tasleem na binta gefe da gefe,kallanta Ummi tayi lokacin da suka iso Door step ɗin ɗakinta ta kalli Tasleem tace"i hope ba soyayya kuke ba?" Dan turus Tasleem tayi jin yarda maganar Ummin ta fito da wani irin yanayi ,murmuswa tayi tace"ina ni ina soyayya da Brother ina sane Ummi da maganarki da kikace Brother Haidar sai Babbar mace ,nikam kuwa ai ina kan hanya ne wadda zaki mayar dani" Dan kallanta Ummi tayi Kafun tace "better cos ke da Haidar yan uwa ne "Kafin Tasleem tace wani Abu Ummi ta shige ɗakinta,wata ajiye zuciya Tasleem ta Sauke,Allah ya sani tana mutuwar san Haidar amma yanayi na Ummi yasa take kama kanta gudun karta saita mata hanya tace ta tafi gida ,sau da dama idan ta zauna da Mamanta maganarta guda ɗaya ce"ki shawo kan Haidar"amma ita ta sakawa ranta bazata taba furta masa soyayya ba muddin bashi ne ya nuna mata ya furta mata yana santa ba ,ta sani a wannan geji kuwa Haidar baya ganin kowa bayan Budurwarsa Kiswa. Tunda Ummi ta kankarawa Tasleem basu haɗu ba sai lokacin Dinner wanda dukkan su suka Halarta dan sau da dama tare suke Dinner dan ita kaɗai ce suke da lokaci,akai akai Ummi kan Kalli Haidar wanda ke ta santin Abincin musamman da ya zamana Tasleem tace masa ita ta girka ba cook ba,aje spoon Ummi tayi tace"Haidar what's so Good about abincin nan da zaka ishe mu ka hanamu ci cikin kwanciyar hankali ?" Kallanta mijinta Tukur Bula yayi yace"sweet heart ya dai?mene aibu dan ya yabi abincin Tasleem When Its not a lie She's a Good cook"Kaɗa kai Haidar yayi yace "oho Baba tell her ,idan Ban yabi girkin ƙanwata ba Wane zai yaba?"kallan Tasleem wadda ke ɗan yaƙe yayi yace"girl you can cook for Africa Abincinki da daɗi amma kina da masu jealousing Ummi kuma tana ciki amma ni da Baba we have Your back".one spoon Baba Ya sake yace "For real Boy" Ƙaramun tsaki Ummi tayi ta cigaba da cin abincinta ,bayan sun gama Ummi ta fara tashi tana mai cewa"Haidar ka sameni a falona zamuyi magana, bata jira mai zai ce ba tabar gurin yayin da suka cigaba da cin abincin su ba tare da kowa ya damu da sudden Halayyar Ummi ba idan aka cire Tasleem ". Bayan gama cin abincin sa Ya nufi sashen Ummi dan jin kiran da take masa,zaune Ya tarar da ita tana Kaɗa kafa ɗaya,zama yayi gefenta yana mai kama hannunta yace"Ummi na wanene Ya taba mun ke aji kan mu a garin nan na Abuja"ƙaramun murmushi tayi ta kallesa tace"ai ka iya wannan dama and Wane kake gani zai tab'ani garin Abuja Ya kwana lafiya dama,"yar dariya Haidar yayi yace "Allah Ya jada ran Ummon Haidar "serious face ta saka tace "mene tsakaninka da Tasleem"? Da mamaki yace"Tsakanin mu kuma Ummi ,ƙanwatace da nake Alfahari da ,kema Kin sani ina jin Tasleem kamar ke kika haifeta ba Aunty Maryama ba" Da kyau Ummi ta kallesa tace "ka tabbata baka kallanta romantically cos bazan so hakan ba Ko kaɗan". Dariya Ya saka lokacin da ta kai karshen maganarta yace "Ummi Tasleem fa?tayaya zan kalleta romantically?dariya Ya sake fashewa da yace"Allah yasa daga ni sai ke Ummi babu wanda yaji wannan maganar taki". Yar Dariyar itama tayi tana mai jin daɗin yarda Haidar ya dauki Tasleem ,wayarta ta dauka ta shiga images ɗinta kana ta miƙa masa tace "oya kalli ka faɗamun ya ta jikin hoton nan take".hannunsa ya saka ya karbi wayan yana mai fadin "hope ba matchmaking zaki mun ba Dan im taking,"idanun sa ya ɗora kan hoton da mamaki yace"Farry"?Dago idanunsa yayi ya kalleta yace "Ina kika san Farry Ummi and mai kike da hotonta"? Kallansa Ummi tayi da Mamakin jin ya ambaci sunan Farry wadda ga dukkan Alamu ya santa,cikin ƙaguwa tace"kasan ta ne?abun ma yazo da sauki kenan cos wannan yarinyar ina san nayi bincike mai kyau akanta kaje ku sasanta Dan a yarda na gana da mahaifiyarta na gamsu ." Gyara Zama Haidar yayi yace"wait Ummi let me understand,Wane ya gana da Wane sannan Wane zai sasanta Dan Wane im lost".murmushi Ummi tayi tace"mahaifiyarta ta sameni yau a office ta kawo mun tayin Aurenta gareka so na zauna nayi tunani naga offer ɗinta is not bad cos yanzu duk macen da zatazo tana sanka dole She's after money and Your look amma wannan yarinyar atleast koda iyayenta basu kaimu kuɗi ba bazatayi ƙwaɗayi ba since itama shes loaded so na faɗawa mahaifiyar ta zan nemeta idan na gana da kai and of course Babu dole amma inasan ka bawa abun nutsuwa da tunani mai kyau sannan ka samu kaga ita Farry ɗin". Wata irin gajeriyar dariya yayi yace "Ummi you cant choose yarinya for me Just Dan mahaifiyarta tazo ta sameki akan tana san ɗanki ya Auri ƴarta,bamafa ki sansu bafa Ummi,and Wane yace wai duk macen dake sona dan kuɗine,? Gyara zaman sa yayi yana mai cewa"Ummi Wannan yarinyar da kike gani sister ɗin yarinyar da nake soyayya da ita ne for year and counting now "Da mamaki Ummi tace "ta yaya and how comes ita maman nasu bata sani ba take san ka Auri ɗayar?" Tabe baki yayi yace "ga dukkan alama dai but Ummi Haidar dai Kiswa yake so sannan inata san na faɗa miki amma na shirya baki surprise ne amma abun yazo a haka,"wayarsa ya ciro ya shiga hoton Kiswa yace "kalleta nan Ummi wadda tayi gaba da zuciyar ɗanki". Karban wayar Ummi tayi tana mai ɗora idanunta kan beautiful Black Queen ɗin Haidar ,Dan washe baki tayi tana mai fadin"kuma gata mai kyau da ita,to ai ba abun tada hankali bane,im sure maman bata sani ba but na tabbata zatayi farin ciki idan taji already ma kana tare da ƴarta,i will talk to her sannan yaushe zaka kawo mun ita na ganta cos na ƙosa naga wannan Yarinya da Haidar ɗin Ummi yake ikirarin ta tafi dashi" Sosa kansa yayi yana mai murmusawa kafin yace "Soon ummi i will talk to her duk lokacin da take da free time zan kawota ku gaisa and im sure Ummi zaki sota cos Kiswa is a very lovely girl,cute and stunning".Kalllansa Ummi take ganin yarda yake faman koɗa Kiswa ba sai an faɗa mata ba yana santa and hes happy about that and farin cikinsa shine gaba cikin abinda ke sakata farin ciki,haka nan take jin kamar taje ta dauko Kiswa ta kawo ta gidan ta,shafa gashin kansa tayi tace"badan dare yayi ba ai yanzu zan kira Barrister Juwarriyah amma da yau da goben duk Na Allah ne tunda dare yayi bazan dameta ba,nasan itama zatayi farin ciki sosai idan taji maganar nan".washe baki Haidar yayi ya cigaba dawa mami waƙar yaban Kiswa. TBC CHUCHUJAY✍️ (Amina jamil Adam) 08130229878 [5/8, 12:13 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na CHUCHUJAY ✍️ Book1⃣ Page 9⃣ AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL. Cikin Yanayi na nutsuwa Haidar ke takawa domin isa office ɗin sa inda yake mai karban gaisuwar ma'aikatan sa yana miƙa musu cikin girmamawa , yana isa bakin office din sa Ya saka key domin buɗewa amma ga mamakin sa yaji kofar a bude ,turawa yayi yana mai tunanin Ko jiya bai kulle ba Ya wuce,turus yayi lokacin da Ya shiga office ɗin ,roses ya ganin an cicire su an rubuta Good Morning love da kuma tambari na heart,kan desk kuma dauke da food pack wanda ba a bude ba ,dan kalle kalle Ya fara dan ganin Ko zaiga giftawar wani ,a hankali Ya taka dan sake dubawa,kofar shigowa da yaji an buɗe ne Ya sakashi waigawa,Kiswa ce tsaye bakin kofar hannun ta dauke da leda yayin da fuskar ta ke dauke da babban murmushi,dafe fuska Haidar yayi yana mai sauke ajiyaar zuciyar ganinta Kafun Ya ƙarasa gareta hakoran sa washe kamar anma yaro kyautar candy. Ledan hannunta Ya karba yana mai fadin"Good morning my romantic heartrob to what did i owe this?" Faɗaɗa murmushinta tayi ta shigo ciki tana mai cewa"to love masoyi,i woke up naji yau ina san ka fara sakani a idanun ka idan kazo office ɗin nan and of course i made you breakfast dan na sanka da rashin san karyawa idan zaka fita office which you will have to work on dan idan mukayi Aure bazan dauka ba,yanzu abunda za'ayi ka zauna nayi serving maka breakfast Then na wuce aiki cos kar ka manta i work for someone and i cant afford being sacked". Cike da wani irin santa dake faman fuzgarsa ya zauna inda ta masa nuni yana mai binta da ido fuskarsa dauke da wani irin murmushi na farin ciki da ya kasa cirewa ,. Buɗe food pack din tayi ta ciro Kulan dake dauke da plantain mossa,sannan ta dauko plate ta saka masa guda uku manya a kai Then cutleries Kafun ta aje a kan cinyansa then ta ciro Cup ta buɗe karamun flask ɗin dake dauke da kunun gyaɗa a ciki ta zuba sannan ta dawo Gefensa ta zauna tace "bismillah hero and mind you sai ka cinye mossa ɗinn nan da kunun gyaɗan nan,"rufe idanunsa yayi ya buɗe yana mai shaƙar kamshin abincin dake gaban sa Kafun yace "my favourite,ya akayi kika sani ban taba faɗa miki ba idan Zan tuna" Haɗa hannayenta tayi guri ɗaya tace "well idan ban san favourite abunda mijin da zan Aura nayi rayuwa ta har abada dashi ba mai ya kamata na sani?,well just eat already" "What about you?"ya tambaya yana mai zuba mata ido. Wani fari da ido tayi Kafun tace "well ni a ƙoshe nake burina kawai kai ka ƙoshi,"murmshi yayi yayi bismillah ya fara cin abincin Cikin nashaɗi, bayan ya gama Ya kalleta da soyayya yace"Allah yayi miki albarka Kiswa,Allah ya mallaka mun ke a matsayin matata uwar ƴaƴana wallahi ina sanki da yawa sannan a kullum sake sanki nake sosai ba wai so na wasa ba,dan Allah ki dage da yin Addu'a kema Allah yasa mu mallaki juna kafun mu koma ga mahaliccin mu". Tashi tayi ta fara haɗa kwanikan kafun tace"na faɗawa Mama maganar ka jiya da mukayi waya and ta ƙosa na kawo ka Bauchi ta ganka,i can tell tun Kafun ta ganka kayi mata already" Cike da zumuɗi yace"OmG Baby i love you ,dan Allah ki samu free time muje cos ni kaina yakamata na ga macen da ta haifa mun macen da bana da nutsuwa idan akanta ne"dan shiru yayi kafun yace"Yea kafun na manta ina ganin ya kamata ace by this time Mother ta san dani a rayuwarki sabida rashin sanin yasa ta samu Ummi jiya a office tana san haɗani da Farry na Aura and im sure dan bata san muna tare bane ,but i told Ummi jiya about us and tayi farin ciki sosai dan idan da dan ranta ne yanzu ma na kaimata ke ta ganki,ba kiga yarda take murna ba". Jin maganar mother ta je gurin mahaifiyar Haidar tayi kamar almara,bata taba sunanin san zuciyar Mother ya kai har inda bata zato ba,kallan Haidar tayi da kyau cikin sigar boye abunda ke ranta ta saka wata dariya tace "so mother did that,gaskiya ya kamata yau na shigar da kai gida a samana rana dan yanzu mother taje cikin rashin sani gobe wanine zai je ." Dariya ya saka sosai yace "ke yarrinyar nan mai kika maida ni,sai kace wani kaya a cikin Boutique din Ummi,well kima saka aranki babu wannan maganar tunda dai duk tallan yan matan da za'a kawowa mother sai na amince zata amince ,and you know my heart beats for only you,zuciyata idan tana bugawa babu abunda take ambato face Kiswy babbyyy". Dariya ta saka sosai Ganin yarda yayi da fuska kana tace"idan na biye ka anan anjima zan baka labarin An koreni gurin Aiki bari kaga nayi harama. Dafe saitin zuciyarsa yayi yace "ouch kinga kuwa ni Ai gaba ta kaini sai na daukeki a asibiti na na baki post ɗin Energy plug ɗina ,kawai nayi ta kallanki kullum kina banii Energy".pack ɗinta ta dauka ta kalleshi da kyau tace"get well soon Hayati ni nayi gaba and i love you".dariya yayi ya mara mata baya dan rakata inda ta aje motanta wanda ya jawo manyan Gulma, da yawan ma'aikatansa sunan ta suka sani basu san fuskarta ba,wasu su yabi kyawuntaa wasu su kusheta dama haka rayuwar dan Adam take. Tunda Kiswa ta baro Asibitin Haidar take tunanin maganar Haidar na zuwan Mother gurin Umminsa dan talata masu Farry bayan ta sani cewa ita ɗin budurwarsa ce,da tunani kala kala ta nufi office inda tasan zata haɗu da sabuwar matsalarta Saleek dan jiya baki ɗaya bai shigo aiki ba Wanda hakan yayi mata daɗi sosai domin kuwa bata san fuskar da zata fara kallansa ita ba dan tagama making up zuciyarta akan faɗa masa gaskiya kafun ya riga nufan Appa ,tun shekaran jiya tsakaninta da Farry kuwa babu wanda yace da kowa komai , Tana isa kai tsaye office dinta ta wuce dan bata cikin mood ma na tsayawa doguwar gaisuwa da kowa ,shes so pissed to Spare a kind heart,zama tayi kan kujerarta tana inhaling deep breath a hankali tana san calming kanta,zuuciyarta wani irin zafi take mussamman idan ta duba iya tsawan rayuwar ta taga Babu abunda ta taba yiwa Mother da take kasa boye mata irin adadin tsanar da take mata ,this madness need to stop,din yarda ta kai da kawaici da girmama Mother akan Abunda take so bazatayi shiru ba,lokaci yayi da ya kamata ace ta yiwa Appa magana akan Haidar ya tura iyayansa ayi maganar Aurensu.,tana tsaka da tunani da zuciyarta taji An banko kofar office ɗinta babu excuse, a hankali ta daga idanun ta dan ganin wanene duk da kuwa tasan duk fadin ma'aikatar Babu maiyyi mata haka bayan SALEEK,ille kuwa shike Takowa hannayensa cikin Aljihun wandonsa,binsa tayi da kallo ,sanye yake cikin Suit grey wanda ya cire rigar suit din ya bar long sleeve din dake ciki fara tas,gashin kansa wanda dye ɗinsa brown Ya rage sosai a kwance gwanin burgewa,Takowa yayi ya Zauna kan kujerarta dake facing ɗinta Ya zauna yana Mai faɗin"KISWA UBAID,Niece ɗin Alhaji Aliyu Alijua,Yar asalin garin bauchi 24 years old turning 25 next month,cousin sister din sameer,Sageer da Faridha Aliyu Alijua,Kin karanci Public relationship a Nile university,Kin fara karatu da wuri Kin gama da shekarun haihuwa marasa yawa wanda ya baki damar achieving career ɗinki na yanzu,Kin samu aiki a AYZEL FOUNDATION exactly after service,Kina saurin fahimta da sharp brain a wurin waɗanda suka daukeki mutum,you're in a Serious damn relationship with Haidar Tukur Bula yaro ɗaya tilo gurin Costum Tukur Bula da matarsa Hajiya zainaba Bula a very rich business' woman,a gidansu suna tare da cousin sister ɗinsa Tasleem Haroon ,poor guy bai san macen da ya dauka rayuwa ba miciijiyace mai dafin tsiyarda idan ta kafa maka sai ka mutu. " Ajiyar zuciya Kiswa Tayi tace"Saleek menene point ɗinka anan,baka tunanin bincike da kayi haka akaina ya shiga personal privacy ɗina,i mean you have no damn right"murmushi yayi yace "calm down baby girl kar kizo nan kice zaki ɗaga mun jijiyoyin wuya When you wronged me sannann shine worst abunda kikayi a rayuwarki da zai barki da dana sani". Wani irin kallo tamasa Kafun tace "na dauki wannan threat Ko mene cos it sounds like one,"Kaɗa kansa yayi yace well bani da ikon hana ƙaramar ƙwaƙwalwarki yin tunanin da taga dama ,imma ki daukesa threat' Ko warning na abunda kika saka kanki Ko akasin haka matsalar kice Abu guda ɗaya na sani wanda shine Kin debo ruwan dafa kanki da kanki "kafun Kiswa tace wani abu an turo kofarta a hankali,kallan kofar tayi dan ganin mai shigowa yayin da Saleek Ko alamar kallan kofar ma baiyyi ba,cikin sanyin murya Kiswa ta furta "Farry?" Takowa ciki Farry tayi tana mai cewa "look here babe banzo nan muyi faɗa ba,i came to apologise and..."kasa karasawa tayi lokacin da ta sauke idanunta Kan Saleek wanda shima ita ɗin yake kallo wadda a kallo ɗaya ya gane ta,haɗe rai yayi yace "im very pleased and glad you came here kinga sai ayi a gabanki afer all you're the mastermind "dan kallan Kiswa Farry tayi Kafun ta zauna kujerar dake facing ɗinsa Ta danyi murmushi tace "you must be Saleek right"haɗe rai yayi sosai yace"bai kama ta ace kina tamabaaya ta ba " Cikin rashin nutsuwar ganin haɗuwarsa Farry tace"Nasan definitely abunda nayi bai kyautu ba sannan bazan boye maka ba nayi dana sanin abunda ya faru musamman da ya zama nayi involving innocent sister na ,i was not fair sannan banyi tunanin abunda zai faru ba,i was wrong so ina mai neman afuwarka da yafiyarka and domin gyarawa zamu iya magana da iyayenmu mu sasanta kan mu a shirye nake domin zama matar ka,a shirye nake domin gyara abunda na bata but please ina sake roƙonka da ka yafewa Kiswa We are Adults zamu iya gyara abunnan ba tare da kowa yaji ba. Kafe Farry Kawai yayi da ido yana mai observing ɗinta da wani kanannaɗa da take kamar wata crayfish ajiyar zuciya yayi yace "kinsan wani abu,koda ace ke kikaje gurina ba ita ba bazan taba approving ɗinki ba domin you're not my spec ,You are not in my lane,you're not my type i mean ki kalli kanki a mudubi mana ,so Just shut the fuck up and get out of my issue, ita kuma sister ɗin naki da taje ta raina mun wayau zata biya da kanta dan haka idan kinsan abunda yake damunki ki cire kanki daga shirgina cos next time abunda zan miki bazaki so shi ba kar kice Ban faɗa miki ba and mark it bazan taba sanki ba ballanta na Aureki ,bana san mata masu tura kansu shamelessly ga namiji"kallansa Ya mayar kan Kiswa wadda take binsa da idanun takaici yace "ke kuma punishment dinki guda ɗayane ,zaki rabu da wancan likitan da kike faman yaudara sannan zakiyi dating ɗina har sai lokacin da domin kaina na koreki daga rayuwata ,zan bawa PA ɗinki ta kawo miki contract paper kiyi signing wannan shine hukuncinki nayi mun katsalandan a rayuwa idan kuma ba haka ba da kaina zan kai ƙararku gurin mahaifinku kunsan kuma mai zai biyo baya" Yana kai ayar maganarsa ya tashi a kujerar da yake zaune yana mai bin Farry da wani irin disgusting kallo kafun ya saka kai ya fice. System Kiswa ta jawo ta cigaba da aikin da take ba tare da tace Ko uffan ba,juyi Farry Tayi akan kujerar da take tana nazarin Saleek Kafun ta kalli Kiswa wadda tayi kamar ma ba mutum a office ɗin tace"Kiswah naga kamar maganar Saleek bata dameki ba ,yana san kiyi breaking up da Haidar ne fa,and to date Him is one stupid method of thinking a bangare guda,and God kinji abunda ya faɗa mun he is so mean and full of him self,to hell with him after all baya da abun bani he is Just a rat and chewgum sticking beside his father sakarai kawai,in kyau yake taƙama dashi nima ina dashi sannan yaje Ya tambaya irin mazan dake bina basa samu"A hasale ta kai karsheen maganar ta tana Kaɗa kafa guda. Kallan ta Kiswa tayi kamar bazata ce komai ba da farko amma sai taga rashin amfanin yi mata shirun dan haka tace"i thought Kin tsani relationships sannan baki shirya sadaukarwa dake cikin sa ba,bai kamata ki cusa masa kanki ba daga ganin ya haɗu baki san halin mutum ba,to wannan baya da mutunci ba sai na faɗa miki ba saboda kunnuwanki Ai sunji irin cin mutuncin da yayi miki anan,had It been kinsan zakiji ya kwanta miki ai bai kamata ki tura ni ba in the first place wanda a yanzu nake mutuƙar dana sanin biye ki,and maganar na rabu da Haidar kuwa Allah ne yake da wannan ikon ba mutum ba duk girmansa duk surkullensa,idan kika ga kuwa mutum yayi sanadin rabuwata da Haidar to Allah ya basa wannan karfin amma ba yin kansa ba". Cike da jin zafin maganarta Farry tace"kinga Kiswah bafa daureki nayi Ko na zare miki ido Ko na miki dole ba akan zuwa gurin Saleek ,i Just asked for a favor duk nacina idan baki je ba Ai bazan kashe ki ba,so kema kina da equal laifi da kin ƙi da dole zanje and im sure da wata maganar ake yanzu ba wannan ba". Da mutuƙar mamaki Kiswah ke bin Farry da kallo tana san gasgata maganar daga bakinta take fitowa,ƙaramun murmushi Kiswah tayi tace "ba laifin ki bane Faridha laifi nane,da ace nayi refusing dinki da hakan bazai faru ba har ki zauna a gabana kina kallan tsabar idona saboda baki da kunya kina faɗin wai ina da laifi,Its okay ina da laifi da banje na kai ƙararki gurin Appa ba lokacin da kika nemi na taimake ki,laifi nane da banyi hangen nesa ba saboda rauni na akanki naje na miki abunda kike so dan haka kar ki damu zan gyara abunda na bata ,now get out of my office kafun nayi losing cool ɗina akanki". Wani irin dogon tsaki Farry tayi tana mai karewa office ɗin kallo kafun tace "wannan abun kike kira office har kike wani faɗa mun na tashi na fita?ba sai kin koreni ba cos kinsan na wuce nan dama this place is suffocating me already and yes na me fuck up".tana kai karshen maganarta ta dauki Jakarta ta fita a office ɗin yayin da ta bar Kiswah da bin kofar da kallo cos jin abunda ya faru yanzu tsakaninta da Farry tayi kamar almara Ko mafarki mara daɗi. TBC CHUCHUJAY ✍️ 08130229878 [5/9, 9:48 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) By Chuchujay Book1⃣ Page 1⃣0⃣ Baki ɗayan ranar haka Kiswa Tayi shi sukuku,tunda Amira ta kawo mata file ɗin da Saleek ya Bata ta sakashi gefe guda ba tare da ta Ko buɗe ba,idan yana tunanin shi baya da hankali to zata nuna masa bai isa ba,bai kai matsayin da zai juyata tayi abunda Batayi niyya ba Just because taje date dashi,da wuri ta wuce saboda yanayin yarda take jinta tana buƙata ta huta domin kuwa yau tana da abunyi a gida wanda tasan ranta zai bacci sosai cos Mother bazata barta haka nan ba amma still yau tayi alkawari ma kanta bazatayi shiru ba ,shirun ya isa haka nan . Koda ta isa gida babu wanda ya dawo dan haka ta wuce ɗaki kai tsaye ta watsa ruwa Kafun ta fita kitchen dan kamawa Baba baraka aiki,a haka suna hira suka gama dinner ,ɗaki ta koma ta kira Maman ta dan yi mata tambayar da ta daɗe tana so tayi mata,kira ɗaya ta dauka tace"Hello Kiswan Mama"murmusawa tayi kamar tana gabanta tace"Maman Kiswah ina wuni Ya gida ya Khalil da Rabiatu ?" "Suna nan lafiya ,Khalil yaje makaranta bai kai Ga dawowa ba Rabiatu kuma na aiketa,ya gidan yasu Faridha yarinyar kirki"? Dan tabe baki Kiswa tayi jin Mama na kiran Farida yarinyar kirki ,gudun kar ta gane sun samu sabani tayi mata faɗa ya saka tace" tana nan lafiya bata kai Ga dawowa aiki bane bama ,yauwa Mama wata tambaya nake san nayi miki amma ina tsoro Ban san ya zaki dauke ta ba,amma kiyi hakuri bana san na bata miki saboda tambayar ". Mama dake Kwance ta tashi ta zauna tana mai faɗin"ina jinki Kiswa Allah yasa lafiya". Ajiyar zuciya Kiswa ta sauke Kafun tace "Mama mai kika taba yiwa mother da bata kasa boye tsanarki karara wadda har ta kai Ga ta shafeni ,Babu damar nayi wani abu domin burgeta Ya burgeta ,kullum cikin nuna mun tsana take tana zaginki Nasan dole akwai wani abu da zai saka mutum ya saka gaba,ni dai na duba ,nayi tunani nayi nazari naga Babu Abunda Na taba mata a rayuwa da zai saka tayi ta tsangwamata kamar na kashe mata wani". Wani irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Mama,cike da kulawa tace "Babu abunda 'na tabawa juwariyyah a rayuwa kawai sai ita halayyar ta kenan sau da dama kalaman bakin ta basu da daɗi,a kullum ita haka take bata so wani na Ya Aliyu Yar rabe ta gani take kamar duk wani abu da Ya tanada zai ƙare kan danginsa ,baki gani ba daga shi sai ita sai yaransu,cikin danginsa babu Wanda yake cin arziƙinsa kamar ke saboda yi na Allah da Ya ɗora masa kaunar ki dan haka wannan Kaɗai 'ya isa Ya zama babba dalilin da zai saka ki shiga idanun juwairiyyah ki zamar mata matsala,roƙona gareki guda ɗaya ne ,kin daɗe dasu ki rabu dasu lafiya kar ki bari a wannan gejin na rayuwarki Juwairiyyah tazamar miki damuwa,Eh tsakanina da Ya Aliyu Babu jituwa shi yasa kika ga Ban taba zuwa ba tunda Ya daukeki,amma tsakanin sa dake da soyayyar da yake miki kuwa fisabilillahi ce daga ubangiji kijini Ko,'dan Allah kada ki bari ta zama sanadin da zaki Bata dukkan wannan abun ". Dan shiru Kiswa tayi Kafun ta goge yar ƙwallarta tace "Nagode mama sannan matsala indai daga gareni ne bazata taba fitowa ba insha Allah"bayan sun gama waya ta koma ta kwanta tana mai dogon nazari akan tsanar da Mother tayi mata wadda Babu abunda zata iya akai,amma dangane da Haidar akwai abunda zata iya bazata zauna ta nannaɗe hannunta ba. Lokacin dinner haka dukkan su suka halarci cin abincin Appa na gamawa yana ƙokarin tashi Kiswa ta aje spoon ɗinta tace "Appa ina san magana idan ba damuwa"dan kallanta yayi Ya zauna yana mai goge bakinsa da Napkin yace"Uhum my dota hope ba damuwa,kallan family ɗinsa dake zaune yayi yace"ko muje ciki ne ".? Cikin haɗe baki Mother da Farry suka furta a'a,a tare dukka suka kallesu,Ita Farry na tunanin Maganar Saleek zata tona Mother kuma nasan dole taji menene,kallansu Appa yayi a tare yace"so ina tunanin babbar magana ce da kuka sani yarda kuka haɗa bakin nan wajen faɗin A'a.haɗe rai Mother tayi tace "ba wani babbar magana Amma ai we are family Babu wata magana da zamu boyewa juna" Dan murmushi Appa yayi yace "my Barrister akwai maganar da take bukatar privacy tsakanina da dota na,so please calm down idan ta sani ce zaku sani"aje cukali Kiswa tayi tana mai Kallan Appa tace "Appa ba magana ce ta boyewa ba ina ɗan jin kunya ne amma tunda Mother na san sani its okay nasan ita ma zatayi farin ciki da maganar da zan faɗa,dan cije lebenta na kasa tayi tana debating da zuciyarta kafun tayi mustering courage tace "Appa ina tare da wani in a relationship na almost shekara ɗaya da rabi and Appa yana so ne Ya saka iyayensa a maganar ayi magana dasu,Shine nace bari na faɗa maka" Cikin rashin tsammanin maganar Mother ta ɗago da sauri tace "Wane irin shashanci ne wannan sannan mai kuke san zama yan matan yanzu,tsabar baki da kunya kike zaune nan kike faɗan saurayinki zai turo" Kallan Mother Sameer yayi yace"Ah ah,Mother mene abun kunya a ciki ?"cike da masifa tace "idan baka mun shiru ba sai na watsa maka plate ɗin nan tunda kai wannan yarinyar bata isa tayi ba dai dai ba a nuna mata kayi shiru"kallan Kiswah wadda ta mayar da kai cikin Plate ɗinta Appa yayi yace"yar Albarka who is the guy,a ina yake sannan ɗan wanene kinsan dole nayi bincike Akansa ". Cike da wutar balai Mother ta sake cewa"au mahaukaciya ka mayar dani ko,?dama wa kake tunanin zata kula idan ba yan iska ba abunda yar Zubaida zata iya kenan"wata irin tsawa Appa ya buga mata yace "keep quit you damn woman,mene yake damunki,sau dubu nawa zance ki cire zubaida a bakinki amma baki ji,bari fa kiji na faɗa miki duk wani maltreatment da kike yiwa Kiswah ina sane,Nasan you never wish good on her amma ina dauke miki kaina,idan Batayi Aure ba mai kike so tayi,kina so tayi ta zama kamar wannan Silly yarinyar taki da bata san Aure,nan blind date na haɗa mata da yaran kirki amma me tayi sai da taje tayi abunda yasa yaran yaje ya faɗawa mahaifinsa Batayi masa ba,gata nan ki tambeyata ita Kaɗai tasan abunda tayi" Wani irin faɗuwa gaba ne ya riski Farry lokacin da ya sako wannan maganar,Kallan bakin Kiswa ta fara tana adduar Allah yasa kar ta tona mata asiri.cikin fushi da saurin tare Kiswa Mother tace "bata sanshi ne amma yanzu da take san Haidar Mai asibitin Al'Haidar ai gashi tana kokarin settling down faɗa maka ne Ban ba" Da mamaki dukka yaran suka kalli Mother 'dan basuyi tsamanni ba karma sameer yaji labari Wanda takaicin zubar da girmanta yake ƙona masa rai fiye da tunani,ƙaramun murmushi Kiswa tayi Kafun Appa yace wani abu tace"but Mother kisan Its not true Babu komai tsakanin Farry da Haidar Ban san mai yasa kike san kwace mun farin ciki na ba ,"da wani zafin Nama Mother ta taso tana mai cewa "naci ubanki dan uwarki,kike ƙokarin kwace mata saurayi dai shegiya mai gadon witchcraft to Aureshi mugani yar dangin kwaɗayayyu".plate ɗin da Appa yayi jifa dashine ya saka kowa maida hankalinsa a razane,cikin wani irin fushi da yake san daidaitawa gaban yaransa yace "Juwairiyyah rashin mutuncinki yana nema ya wuce gona da iri Wanda bazan dauka ba,wallahi idan bakiyi wasa ba gaban yaran nan zan baki mamaki".cike da rashin kunya tace "to dake ni mana Aliyu Shine kaɗai mamakin da zaka bani,kar ka manta im a lawyer that knows her right wallahi duk ranar da ka saka hannunka jikina sai na baka mamaki mara misaltuwa,nuna Kiswa tayi da hannu tace"akan wanna ɗiyar karuwar zaka nemi ka raina mun wayau"Kafun yace wani abu ta bar gurin Farry ma ta tashi tana kuka ta mara mata baya,aje spoon Sageer yayi yace "Allah ya kyauta "yayin da Kiswa ta fashe da wani iri kuka mai cin rai,lallashinta Sameer ya fara yayin da Appa ya zauna ya ɗora hannunsa a fuskarsa yana mai jin wani irin yanayi na baccin rai a tattare dashi,tashi yayi bai ce musu komai ba ya bar gurin,kuka sosai Kiswa ta cigaba da yi tana mai jin kirjinta kamar zai faɗi Yayin da sameer ya cigaba da lallashinta yana mai bata hakuri har sai da tayi shiru kafun yayi mata magana masu kwatar da hankali Kafun ya rakata ɗakinsu. Bangaren Mother kuwa tana shiga ɗaki kiran Mahaifiyar Haidar ya shigo mata,cikin zumuɗi kuwa ta dauka ta samu guri ta zauna tana mai saita kanta tace"Assalamu alaikum future sirikata barka da warhaka,daga ɗayan bangaren Ummi tace"barka dai dama ina ta san na kira ki amma Ban samu dama ba saboda jiya naga dare yayi,na kiraki ne da albishir mai daɗi,jiya na zauna da Haidar nayi masa magana kan diƴarki Faridha,so ya faɗa mun yana dating ,amma abunda yayi mun daɗi sosai yar uwar Faridha ɗin yake so daya yarinyar ki Kiswa,im Just happy da ya zamana either way zamu zama sirikai na bada dukkan goyan bayana musamman da ya zamana Haidar na mutuƙar san ita Kiswa ɗin Ko ya kikace? Ajiyar zuciya Mother ta sauke Kafun tayi wata ƴar dariya tace"Hajiya kenan,kicce sharriin Kiswa ya ziyarci Haidar kenan,kyau Babu kyan hali ake faɗa miki,to ni Kiswa ba yarinyata bace domin kuwa ina Allah wadai ace na dauki ciki kamar na Kiswa a jikina ban zubar ba wada da haihuwarta gwanda barinta,koda yake ai ba abun mamaki bane idan tazo duniya Ta hanyar uwarta domin kowa ita kanta uwar tata karuwace wadda ta samu cikinta ba da Aure ba kasancewar Mahafiyarta kanwar mijina ce ta saka ya daukota domin bata rayuwa mai kyau amma duk da haka bata bar komai ba a halayyar uwarta,kinga hajiya ba wai san zuciya ba Ko wani abun ba amma Kiswa bata dace da shiga zuriar ku ba domin kuwa Kiswa Wake ɗaya ce mai bata miya. Shiru Ummi tayi tana mai jin maganar kamar dukan guduma,sai da Mother ta sake cewa "Hello Hajiya"Kafun Ummi ta dawo daga shock ɗin da ta shiga,ajiyar zuuciya tayi tace"zan nemeki Hajiya i need to digest this".tana kashe waya Mother ta saka dariya tana mai faɗin"indai nice wallahi muzuba mu gani domin kuwa nafi karfin bataliya guda",zama Farry da mamaki Ya kusa kashewa tayi tace "mother mai yasa kike yin haka wai don't you think Bai kamata ba sannan ni dake munsan Kiswa is decent kuma da Aure aka sameta mai yasa zakice yar karuwa ce,beside ni mai yasa kike san haɗa ni da Haidar?. Wani irin Kallo mother ta bita dashi kafun ta kamo hannun Farry tace "kalli Nan Faridha,kowa da kike gani kansa ya sani sannan a maganar da na faɗa ai ba duka ne karya ba cos Zubaida Na da reputation ,but ba wannan ba ,ki saurareni da kyau,duk duniya babu mai sanku sama dani ,ina san ki sani Kiswah ba sanki take ba,da zataga abunda zai cutar dake bazata taba faɗa miki ba ,iyakaci ma ta tura ki,ni Na tabbata idan kika kuskura kina gidan nan ta Auri mai kuɗi kamar Haidar to kisa a ranki wulakanci da sharri a gurinta sai ya baki mutukar mamaki,She's Just using you a gidannan domin zuwa wani matsayi mai girma,and gradually zata kai dan tunda Appanku ya fara wannan Abun wata rana zakiji ya tsigeki daga Kujerar ki ya bata. da sauri Farry tace"God forbid Mother kar ki mun baki mana"ajiyar zuciya mother tayi tace "abunda nake nufi kenan kuma zai faru idan baki bani Haɗin kai ba zaki sha mamaki dan haka dole ki kwace Haidar a hannunta,a hankali cikin karfin Zancen uwa ga ɗanta Mother ta wankewa Farry kwakwalwarta tass inda ta fara disgusting tunanin marasa kyau kan Kiswa , Kai tsaye bayan ta gama da Mother ta nufi ɗakinsu da zummar korar Kiswa daga dakin ,tana shiga ta tarar da Kiswa kwance ta rumtse idanunta Ta lullube da bargo, kanta tayi kai tsaye ta yaye bargon wanda yasa Kiswa buɗe idanunta amma bata tashi ba,fahimtar idanunta biyu ya saka Farry cewa"bai dameni ba ki tashi Ko kar ki tashi amma Nasan kunnuwanki suna saurarena,to kiji nan you're selfish,san kanki yayi miki yawa ,idan ba haka ba mai zakiyi da maza biyu indai ba zalama ba tunda kinsan mutum ɗaya zaki Aura and maganar Saleek kuma ai kinsan i appreciate Handsome guys idan da na ganshi bazan taba cewa bana sanshi ba sannan bazan taba kirkirar masa halayyar banza da na lissafa ba,da Kin bani hint bayan dawowarki yarda yake da yanzu komai ya dai dai ta tsakanin mu" Tashi zaune Kiswa tayi tace "madam Hold on ,kina nufin duk abunda kika faɗa mun kan Saleek karya kike?"murguɗa baki Farry tayi tace and so?after all kuɗi kike yiwa cos ina baki baki taba so mun abu mai kyau ba a rayuwa,you're always this greedy ga san nuna ke mai gaskiya ce bayan cewa mamanki ma dake bauchi reputation gareta...wani irin tashi Kiswa tayi inda Kafun Farry ta ankara a dauke mata fuska da mari mai kyau Kafun tace"wallahi tallahi idan kina haukanki da aka doraki akai kika zo inda nake kina ƙokarin faɗan abu mara kyau kan mamana to baki ɗaya garin nan yamana kaɗan,sannan magana da kike akn kuɗi ko mene ke kinsani abunda nake dashi baya mun kaɗan sannan a kullum ina godewa Allah da abunda ya bani and kuɗinki idan har ba daƙiƙiyace ke ba kinsan ban taba roƙonki ba sannan in faɗa miki idan baki sani ba duk da ban taba kawowa zaki mun gori ba amma ban taba kashe su ba suna nan a account and i will send Your fucking shit back,sannan maganar Saleek da kika hada kika saka nayi making fool of myself shima zan baki mamaki ,sha sha sha kawai wadda bata san inda yake mata ciwo ba". Cike da fitina Farry ke riƙe da kuncinta hawaye na mata reto a fuska,cije lebe tayi tace "ni kika mara Kiswah?"kaɗa kai Kiswah tayi tace ki rama mana sai naga adadin haukanki,ai Kafun kace ƙwabo faɗa ya kece a tsakaninsu ,hayaniyarsu Mother ta fara ji,dakin tayi kai tsaye dan ganin maike faruwa,ganin yarda suka chakume gashin Juna ya saka Mother shiga da gudu tana fadin"wanne irin hauka kenan"ganin yarda Kiswa ke neman fin karfin Farry yasa Mother shiga ta kama Kiswa a rike kam tace ma Farry "oya zo ki yamutsa mun fuskarta da mari,aikuwa kamar Farry na jira ta fara haɗawa fuskar Kiswa mari,tana ƙokarin yin na huɗu Appa ya Sameer da sagir suka shigo,cikin zafin Nama samer ya shiga ya dauke Farry da wani irin mari da saida ta tuntsura,kafin ya farga Mother ta rama mata tana mai faɗin"'dan baka da hankali kasan mai tayi mata da zaka rama mata."wani irin fushi ke daukar Appa dangane da Mother wadda idan ya biye ta yau bazata kwana gidan sa ba ,a hankali ya saita kansa yace kai Sageer je ka riƙeta kamar yarda Mother ta riƙe Kiswa,Babu musu sageer ya riƙeta ba tare da ya saurari mai Mother ke faɗi ba,kallan Kiswa da fuskarta ya tashi yayi yace"idan har na isa dake ina so yanzu ki rama adadin Marin da tayi miki "aikuwa ba abune mai sabuwa ba"mother ta faɗa hannunta a kugu". "Idan kuwa kika kuskura kika matsa daga inda kike da zummar hanata to a bakin Aurenki,na miki alƙawari". TBC Chuchujay 08130229878 [5/13, 9:28 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na Chuchujay ✍️ Book1⃣ Page1⃣1⃣ Da mutuƙar mamaki Mother ta juyo tana kallan Appa Wanda ya haɗe rai iya mutuƙar haɗewa,kanta ta nuna da yatsa idanunta sun kawo ruwa tace"ni zaka faɗawa abakin Aurena akan yarinyar da zubaida ta haifa ?" Cikin nuna mata rashin wasa a maganarsa yace "ƙwarai kuwa idan kuma kina ganin bazan iya ba dan Allah ki ƙara taku daya daga inda kike kiga cikakken mamaki,magana da kika akan yarinyar da zubaida ta haifa Eh ita ɗin sannan ina so ki sani zan iya chanza ki amma bazan taba chanza Zubaida da Kiswa ba"maida hankalinsa yayi ga Kiswa yace"oya fara rama marukanki"Babu musu Kiswa ta matsa ga Farry wadda ke fuzgewa ta fara shatata mata mari har saida tayi mata huɗu masu kyau Kafun ta saka kuka jin yarda Farry ke kuka,har ga Allah rana ta yau ba ƙaramun muni gareta ba a gurinta dan ita mutum ce mai bawa family ɗinta muhimmanci ,bata san abunda zai taba mata su ,yau sai gashi irin sabanin da suka samu bashi da daɗin ji,kallan Farry dake faɗin wallahi bazata yarda ba Appa yayi yace "to dan Allah Faridha ki dauki mataki ni kuma zan baki mamakin da tunda nake matsayin Mahaifinki ban taba baki ba." Sanin Halin sa idan yayi fushi yasa Mother da tayi tsit cewa"kija bakinki ki yi mana shiru anan Farry"wani irin kallo Appa ya bata yace "better da kina faɗa mata tuntuni da rana irin wannan bata zo ba"'dan shiru yayi yana nazari Kafun yace"Its better ku raba ɗaki, dama ai Faridha ɗin ta nace tun yarinta a haɗa su ,so dole yanzu tunda shashanci ya fara shiga tsakani kowa ya zauna ɗakin sa" Yana kai karshen maganarsa ya bar ɗakin,kwafa Mother tayi itama ta fita,faɗa sosai Sameer ya fara yi musu inda Sagir yace "Just kallesu akan namiji wanda kilan ma yaudarace a zuciyar sa suke wannan faɗan kamar zasu kashe kan su"tsaki yayi ya fita a ɗakin yayin da Sameer ya yi musu Nasiha wadda Kiswa kawai ke gamsuwa dashi Amma banda Farry.daren Ranar Kiswa guest room ta kwana kafun washe gari tayi aikin parking to koma ɗakinta wanda yake da komai gyarawa kawai zatayi saboda Babu mai kwana cikin sa,washe gari bata iya fita aiki ba saboda ciwan kai dake damunta amma Farry kam karfin hali tayi ta fita dan da zaman gidan gwara ta fita ɗin koda ba office zata ba kuwa,Babu wani breakfast kowa ya kama gaban sa ban da Sameer wanda ya tsaya dan ganin mai Kiswa ke buƙata a saban ɗakinta ya taimaka mata. •••••••••• •••••••••• •••••••••• TUKUR BULA'S MANSION "Son wait we need to talk like right now"mahaifiyar haidar ta shigo ɗakinsa tana mai zama kan couch kamar an koro ta, Haidar dake tsaye yana gyara tie ɗin sa ne ya juyo yana mai cewa"Ummi hope im safe dai"kafarta ta ɗora kan ɗaya tace"trust me muddin kana tare da yarinyar nan Kiswa to bazaka taba zama lafiya ba,Ko kasan cewa ba yar ALIJUA bace sannan ɗiyar karuwa ce and bada Aure aka sameta ba,no bazan taba yarda da mace irin wannan ba cikin zuri'a ta". Cike da confusion ya zauna yace"well rashin zama ƴar sa abune da na sani niece ɗin sa ce da Maman ta dashi uwa ɗaya uba ɗaya and ya ɗauko ta ne daga garin su bauchi bayan rasuwar mahaifinta ,a zallar sanina da kuma gaskiyar magana ita ba wadda aka haifa bace wajen Aure, da mahaifinta dangin sa kuma suna cikin garin Bauchi though sunyi abandoning ɗinsu,yanzu haka mahaifiyarta tana cikin garin Bauchi tayi Aure da yaranta biyu Khalel da Ra'abiatu ,Bansan Wake feeding ɗinki waccan maganar ba amma Ko wanne maƙiyin Kiswa ne and dole zan suing ɗinsa for defamation of character ki bani suna kawai Ummi. Shiru ummi tayi tana nazari yayin da Abubuwa suka fara dawo mata daga zuwan Mother office ɗinta tayi mata tallan Farry har izuwa kiran da tayi mata jiya da daddare .kallansa Ummi tayi tace "ya zaman takewarta da Barrister juwairiyyah?" 'dan shiru Haidar yayi yana san ya fahimta dan a iya zamansa da Kiswa bata taba nuna masa koda da wasa ba tana fuskantar matsala a gidansu ba ,sannan a iya saninsa tsakaninta da yan gidan Babu wani matsala tana san su suna santa ,dan haka yace"Gaskiya Ummi i dont know about Mother tunda ba hirarta ta cika yi mun ba amma ga dukkan alama tsakaninsu ba matsala duba da yanayi na yarda mu'amalar Kiswa take da yaran gidan".shiru Ummi tayi tana kallan fuskarsa da yarda baya so ace akwai Matsala a rayuwar Kiswan sa,ajiyar zuciya tayi tace"i need to see that girl cos na tabbata akwai wani abu a rayuwarta wanda take boyewa,sannan a wannan gidan na Alijua na tabbata akwai bangaren da bata jin daɗi saboda Barrister juwairiyyah jiya take fada mun maganganun nan da daddare bayan na kirata,but my instinct is telling me otherwise duk da Kafun naji ta bakin ka hankalina ya yarda da maganarta amma da nayi magana da kai yanzu hankali na ya kwanta akan cewa ta haɗa labari ne saboda tana san ƴarta ta Auren ka ba Kiswa ba,koma dai yaya ne zamu san gaskiya Just bring the girl to my Boutique. Tashi tayi ta fita tabar Haidar da jimami yana san sanin mai yasa tayi ma Ummi ƙarya sannan wacce irin rayuwa ma Kiswa ke yi a gidan ,yakamata yaje ya sameta,wayarsa ya ciro ya fara kiran layinta akashe dan haka kai tsaye da ya fita ya nufi office ɗinta, yana ƙokarin shiga Elevator ɗin da zai sadashi da floor ɗin office ɗinta Saleek ya na ƙokarin shiga,dakata masa Haidar yayi ya shiga kafin yabi bayan sa,kallo ɗaya Saleek yayi masa ya gane sa yayin da Haidar bai ma sanshi ba ,ba tare da Saleek ya kallesa ba yace "You're a doctor right"? Kallansa Haidar yayi yana mai tabbatar dashi yake magana Ko a'a,murmushi Saleek yayi yace"i hope you made it out of Your relationship Alivee"kafun Haidar yace wani abu lifter ɗin ya tsaya a Floor ɗin da zasu sauka,Saleek ya Fara fita kafun Haidar yabi bayan sa yana mai Juya maganar da ya faɗa masa Na Allah yasa ya fita a relationship dinsa a raye wanda baya ce ga mai yake nufi ba,jan kunne ne Ko barazana,ƙaramun tsaki yayi ya nufi hanyar da zata sadaka da ofishin Kiswa , yana isa Amira ta taresa tana mai faɗin "barka da zuwa yallabai ,unfortunately yau Madam Kiswa bata shigo ba and Batayi reporting ba ina ta ƙoƙarin kiranta amma akashe,"dauko wayarsa yayi yana mai sake dialing ɗin wayarsa Kafun ya ɗagawa Amira Hannu ya fita a gurin dan zuwa gidan su Kiswa ,gudu kawai yake a titi dan a yanzu He's worried beyond expectation,koda yaje bakin gidan su cigaba da kiran wayarta yayi amma a kashe ,fitowa yayi a motarsa ya taka zuwa bakin gate ɗin gida ya Fara knocking cikin nutsuwa,yayi wajen knocking uku zaiyi na huɗun Aka buɗe ƙofar gate ɗin,sauke hannunsa da yayi ƙokarin knocking yayi yana kallan wanda 'ya fito,'ya sameer ne tsaye,Takowa yayi fuskarsa babu yabo Babu fallasa ya miƙa masa hannu yana mai faɗin "Assalamu alaikum" Karba Haidar yayi yana mai amsa masa sallamarsa Kafun kuma yayi shiru bayan sun raba hannun su ,kallan sa ya sameer yayi da Kyau kafun yace "wa kake nema naga kana knocking hala kazo gurin Sageer ne"murmushi Haidar yayi yace "yaya Sameer right"? Kallansa sameer yayi musamman da yaga yarda yake sinnewa ga kuma kiransa da yayi yaya wanda a ƙalla zasu iya yin sa'ani,ganin kallan da yake masane ya saka Haidar cewa"sunana Haidar and nazo gurin Kiswa ne dan ina ta kiran wayarta a kashe sannan naje gurin Aikinta an tabbatar mun bata zo ba shine nace bari nazo gida naga Ko lafiya". Cike da Fara'a Sameer yace "kace mun wanda yayi wuff da zuciyar ƙanwata ya hanata sukuni"ƙasa Haidar yayi da kansa yana mai murmusawa kafun Sameer yayi masa jagora suka shiga yana mai dan jan sa da hira mai kama da tambayoyi har ya ajjesa falon da aka tanada domin baƙi Kafun ya shiga ciki domin yiwa Kiswa magana,ya jima yana ƙwanƙwasa mata ƙofa Kafun ta bashi izini ya shigo,da mamaki ya kalleta yace"har kin bani tsoro danaji baki amsani,ya jikin naki"? Murmushi tayi tace"jiki da sauki yaya Sameer but my heart is still bleeding na rasa abunda yake Mun daɗi baki ɗaya na". Murmushi yayi yace"well ina tunanin maganin matsalarki yazo ,kinyi baƙo a kasa,bazan kuma tsaya ja miki rai ba mai kiranki ba kowa bane face Haidar ɗinki,"wani irin daɗi taji ya ziyarce inda lokaci guda ta nemi damuwarta ta rasa, hijab ɗinta da tayi sallah dashi ta ɗauko ta saka taɗan gyara fuskarta kaɗan Kafun ta fita dan zuwa gurinsa ranta fari tas,da sallama a bakinta ta shiga falon tana mai faɗaɗa fara'arta ,tasowa yayi cike da damuwa da kulawa yace"Baby mai ya faru,mai ya same ki?are you sick?mai yasa kika kashe wayarki sannan mai yasa bakije aiki ba?you got me worried". Ajiyar zuciya ta sauke tana mai sauke idanunta akansa ganin yarda ya wani ruɗe ,murmushi tayi tace "calm down masoyina wannan tambayoyin naka wanne kake so na Amsa,?Nasan duka ne dan haka bari na amsa maka su duka,Bana jin daɗi ne shi yasa ban bar wayata a kunne ba cos i was very sick to talk and bana yanayin da zan iya waya kuma shine dalilin da banje office ba,kaga na amsa tambayoyin ka baki daya. Cike da damuwar da tafi ta farko yace"baki da lafiya shine baki karani ba ,mene amfanin zamana Likita rayuwata bata da lafiya "? Takawa tayi dan zuwa ta zauna kafun tace"calm down nawan baka ga na fito gareka ba kasan idan na saka ka cikin idona Ko wacce irin damuwata da ciwo na daukewa suke ,ka kwantar da hankalin ka ciwan Kai ne kuma na warke Alhamdulillah . Zuwa yayi ya zauna inda take yace"ina fatan ba faɗa kike ba kawai dan naji daɗi,kinsan lafiyarki tafi mun komai a rayuwa"murmushi tayi tace "hayatee calm down im okay wallahi,and maimakon kabari sai ka tashi a aiki kazo amma kabar aikin ka Just to see me". Kaɗa kan sa yayi yace "yarinya kenan baki san bana tunanin komai ba muddin wani abu akace ya sameki"Serious face yasa yace "yauwa Girl we need to talk idan zaki iya idan kuma You cant talk much just tell me na bari other time. Kallan sa take cikin ido tana mai san gano maganar da yake san mata amma ta kasa gano komai,murmushinta ta Faɗaɗa tace "na warke fa na faɗa maka Ina sauraran ka. "lasar leben sa na ƙasa yayi Kafun yace "ban san ta ina zan fara ba and i wish baza kiyi fushi dani ba,im Just curious ina san nasan ya yanayin zaman ki yake da Mother cos im not understanding it ,bana san na boye miki saboda tsakanina dake bana fatan boye boye ya shiga tsakanina dake ,ummina ta kira Mother akan maganar mu so Mother take faɗa mata cewa ke ɗin ba da Aure aka sameki ba sannan mama zaman kanta take which im sure ba haka bane ,na kasa haɗa maganar guri ɗaya sannan im confuse akan mai yasa Mother zatayi hakan ,hope banyi mata ko Kin mata wani laifi ba cos im sure akwai wani abun a ƙasa." Cikin wani irin siga da yanayi Kiswa ta tsinci maganar wadda tayi mutuƙar bata mamaki ,yar dariya Tayi tace "for real ?Mother tace ni bada Aure aka haifeni ba sannan idan na fahimta tana nufin mama ma karuwa ce,wata Dariyar ta kuma sakawa Kafun kuka ya kwace mata,bata san lokacin da ta kama hanunsa ba ta saka kuka sosai tana mai faɗin"Baby i swear To God wallahi Mama ba karuwa bace koda kuwa a baya bata taba karuwanci ba sannan ni ba yar zina bace idan Ummi bata yarda ba kuma ta saka ayi mata bincike,mahaifiyata da Aure ta Haifeni sannan bayan rasuwar Mahaifina bata zauna haka nan ba sai da ta sake wani Auren inda ta haifi Khalel da Rabiatu wallahi ba ƙarya nake maka ba ,idan ma baka yarda ba bari na kira maka yaya sameer kaji a abakinsa ,zumbur ta tashi dan zuwa kiran Yaya sameer,da hanzari ya saka hannunsa ya jawota ta zauna,tana zama ta fashe da wani irin Kuka mai ban tausayi tana mai faɗin"ban san mai na tabawa Mother a rayuwa ba da take san kushe Asalina ta lalata mun soyayya,idan ban Aure ka ba zan iya mutuwa saboda dukkan wata soyayyata na dauka na baka,bazan boye maka ba ,a soyayyarka baki ɗaya na zira jikina saboda na gama yarda da cewa naje destination ɗin karshe ,Babu wani gurbi dana ajewa wani ɗa namiji a wannan rayuwar,dan Allah Haidar kar ka rabu dani duk runtsi duk wahala". A wannan gejin ji yake kamar ya jawota 'ya rungumeta jikinsa har sai hawayen dake zuba a idanunta sun daina zuba ,jin dumi a kuncinsa ya saka shi ɗora hannunsa inda ya tabo hawaye,kokarin gogewa yayi domin kuwa baya san ya zama mai rauni a lokacin da Abar kaunarsa ta kasance a raunace,dolene ya nemo dukkan wani ƙwarin gwiwarsa ya bata karfin gwiwa,saita kansa yayi yace "Baby its okay ki daina wannan kukan cos idan kina yinsa jina nake kamar zuciyata zatayi bindiga ta fashe ,Bansan mai nan gaba zai haifa mana a rayuwa ba saboda ban san abunda Zai faru gaba ba sanin wannan sai Allah amma koma mene ina san ki sani,Ina miki san da bana kallan komai da kowa face ke,ina maki soyyayar da bana iya gane dai dai da kuma abunda ba dai dai ba,ina sanki to the extent that zan iya sadaukar da dukkan wani abu da na mallaka domin na mallakeki,Baby i love you to the very last extent that i don't give a shaking damn about how you were born,abu guda ɗaya na sani an halliceki an Haifekii sannan Allah ya haɗani dake,nasan waccan maganar ba gaskiya bace cos bayan kowa maganarki ce gaskiya,a rayuwata Babu wanda zai faɗa mun abu mara kyau akanki na dauka,koda ace maganar ma gaskiya ce Babu abunda zai sauya yarda kike a zuciyata so calm down ki kwantar da hankali Haidar naki ne da yardar Allah koma mene ke faruwa it will get over saboda insha Allah cikin satin nan Baba zai zo suyi magana da Appa ,magana ce ta bincike ko wanne side yayi then bayan nan cikin wata jikina ya ma gama bani Zanzo na daukeki na maidake gidana karkashin kulawata ,'dan haka ki goge wannan hawayen naki mai tsada kinji yar tsana ta" Tsintar kanta tayi da yin dariya tana mai faɗin Wane ƴar tsana,murmushinsa mai kyau yayi yace "ke mana abar kauna,you look like a barbie doll bakiga ba da kikayi Dariyar nan kamar na saceki mu gudu," Hannu ta saka ta rufe idanunta,tabe baki yayi yace "aw kunya come on jo yanzun nan ko tashi ba'ayi ba kika gama fallasamun sirrin zuciyarki Shine kike mun wani kunya yanzu ,im very sure baki ci komai ba so yanzu ki tashi na kaiki wani sabon gurin cin abinci mai kyau " Binsa tayi da kallo tana mai jin daɗin idea ɗin Kafun daga bisani tace"Aikin naka fa i mean bana san kayi late"ɗaga gira yayi yace "well im the Ceo ,d king and the founder Babu mai bani query,shall we?" Tashi tayi tana mai nuna masa farin cikinta tsantsa tace "bari naje na chanza kaya" Kafun ta kai ga takawa yace "Why?,kinyi mun kyau a haka so muje kawai sai dai in zaki dauki wani abu ne kuma". Kallan kanta tayi Kafun tayi murmushi tace "okay bari na ɗauko wayata Just a moment"bayan mintina Kaɗan ta fito bayan ta sanarwa da baba Baraka cos yaya sameer ma ya fita. ******* ________________"Sageer magana mai muhimmanci nake san nayi da kai matsayina na mahaifiyar ka "Mother ta faɗa tana mai bin Sagir da kallo wanda ke zaune kan stool a bedroom ɗinta. Nutsuwar sa ya bata yana mai faɗin"Ina sauraran ki Mother" Gyara zamanta tayi tace"well a matsayina na mahaifiyar ka kasan cewa Babu wani abu da zakayi yayi skipping ɗina sannan babu wani abu da zaka so na gagara ganewa ,after all i gave birth to You,lokuta da dama idan iyaye suka fuskanci abunda ɗan su yake so sai su zauna su duba suga yanayin kyan sa da rashin kyan sa,a wannan zagayen ni dana duba kyansa na gani sabida zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya,ni mahaifyarka ce dan haka ba sai wai an faɗa mun kana sha'awar Kiswa ba".. Da saurin sa ya zabura yace "Mother ni kuma,wallahi..…"saurin katse tayi da hannu tace "uhm uhm kar Kafara mun rantse rantse Ina sane da irin yarda kake kallan waɗan nan manyan mazaunan nata da kallo, so cut it ni ba wani abu zanyi maka ba ,im fighting for Your sister sannan nasan ko wanne abune zaka iya yi Muddin Faridha zata samu fari ciki dan haka wannan karan zumuntar ka da tausayin ka zaka bada 'na ɗa wani lokaci,so nake kayi wa Kiswa fyaɗe sannan Ina san ka ɗauko mun ita wasu hotuna na Nudes ɗinta,zan baka dukan goyan baya daga baya Babu wani abu da zai faru " Wani iri sagir ya tsinci maganar musammman da ya kasance da mahaifiyarsa yake wannan maganar,sosa keyar sa yayi yace"Mother kin san Idan Appa ya kamani na mutu sannan this is a sin in the other hand" Tsaki ta buga tace"amma lokacin da gabanka ke tashi idan ka ganta baka taba tunani sin ne ba ko,kalli nan Sagir Allah gafurur rahim ne Mai yafiya ne zamu nemi gafara daga baya"shiru yayi yana nazari yayin da a lokaci guda shedan ya cigaba da assasa mishi sha'awar Kiswa wanda a lokaci guda ya amince,daɗi kuwa a gurin Mother ba'a cewa komai domin kuwa ta kai wani guri da ake cewa ba gudu ba ja da baya musamman da ya zamana a ranar farko saboda Kiswa mijin ta mai kaunar ta yayi mata barazanar saki gaban yaranta,wannan abune wanda bazata taba yafewa ba har sai taga ta lalata wa Kiswa rayuwa ta yarda Appa zai ƙwashe ta ya mayar da ita inda ya ɗaukota. TBC I miss you guys, Do you miss me? Chuchujay ✍️ 08130229878 [5/14, 10:34 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na CHUCHUJAY ✍️ Book1⃣ Page 1⃣2⃣ __________Washe gari cikin wata irin walwala Kiswa ta tashi,dan haka tayi shirin office ,bata da Niyyar yin wani breakfast dan haka tacewa Baba Baraka idan an tambaye ta inda take tace tana azumi ,ille kuwa Appa ya tambayi Baba Baraka ganin kowa yazo banda ita,Kafun ya rufe baki daga tambayar da yayi Farry ta cabe inda take cewa"Appa we are complete here tunda dai dama ai ba ƴarka bace Ko Mother Why bother?" Wani irin kallo Appa ya bata Kafun yace"sai dai in ba ƴar maman ki ba amma ni Kiswa tawace domin kuwa yarda nake jinta a raina ma bana jinki sannan idan na sake jin wata maganar banza a bakin ki zaki zauna a gida ki bani kujerar office ɗina dan bana tunanin zaki iya girmama ma'aikatana yarda ya kamata duba da yarda respect ɗinki yake neman ƙarewa ". Dif kake jin Farry kamar anyi Ruwa an ɗauke,duk da yarda bakin ta ke ƙyaiƙayi akan tayi magana ta ƙwabesa dan tasan halin Appa. Fitowa Kiswa tayi cikin shirinta tsaf tare da wani vibe Energy da ta samarwa kanta dan tayi Alƙwarin sauke nauyin Saleek dake kanta a yau wanda take ganin Shine best solution,at least bazai kashe ta ba haka zalika bazai daketa ba,ganin yarda suka zauna suna cin abinci zuciyarta taji tana mai bata taje ta zauna musamman yarda taga seat ɗinta empty ,Allah ya sani tana san su tana ƙaunar su saboda sune family ɗin da ta sani sannan ta shaƙu dasu tun yarinta bata fatan ace yau sabani mai girma yana shiga tsakanin su amma Mother is hellbent taga ta b'ata mata abunda take so da sunanta dana mahaifiyarta ,dan haka itama ta ɗaura ɗamarar kare duk wani bullet da zata jefeta da shi,Takawa tayi dan zuwa gaisawa dasu Kafun ta wuce,tana isa gurin Appa ya Faɗaɗa fara'arsa yace "har na fara tunanin fushi Kike damu da yasa ba zakici abinci da mu ba "cike da ƙaunarsa tace "Appa ni ina zan fushi da family na mai kyau,na tashine da azumi ,ina ƙwana"ta faɗa gudun zama taci abincin dasu duk da ba azumin take ba. Cike da jin dadi ya amsa mata gaisuwarta yayin da ta gaida mother da yayyinta amma su kadai suka amsa banda mother,ba tare da ta damu ba ta tashi tayi musu sallama ta fita.. ********** Ta daɗe cikin motar ta tana tunanin yarda zata fuskanci Saleek kasancewar sa mutum mai murɗaɗen hali,ta iya iyuwa jira yake tazo tayi confessing ya ɗauki wani matakin akanta amma hakan bai dameta ba domin kuwa ta shirya daukar consequences na abunda ta aikata at least ta fito masa da gaskiya kuma zata basa hakuri hukuncin da zai ɗauka ya rage nasa ,wata irin kunyarsa take ji musamman da ya kasance irin sunayen da ta kirasa dasu waɗanda ba hallayarsa bace sharrin Farry ne ,ajiyar zuciya tayi ta dauko Jakarta ta fito a motan ta kulle ta nufi cikin company ɗin,straight office ɗin Saleek ta nufa Kafun kwarin gwiwarta ya ƙare dan a yanzu ta shirya fuskantar sa da karfinta ,koda ta isa bakin ƙofar sa tsaye tayi tana cije baki Kafun tayi karfin hali wajen ƙwanƙwasa masa ,knocking ɗaya tayi ya bata izini da ta shigo kamar barauniya haka ta shiga bakinta ɗauke da sallama,kamar an mitsinesa haka ya ɗago ya kalleta dan baya expecting ɗinta ,jingina bayansa yayi da kujerarsa yana kallanta Kafun ya Amsa mata sallamar ta ya ƙara da cewa"lafiya dai Ko? dan duk wani document, da nake bukata yana kan desk dina sannan duk wani meeting schedule ɗina Khaleefa yayi arranging mini so a yarda nake tunani abu daya ne zai kawoki inda nake wanda Shine ƙarya da rashin kunya domin kuwa idan akwai abunda kika ƙware akai Shine wannan abu guda biyun bayan aikin ki dan haka bismillah nasan duk wata hanya da zanbi dake in dai Nine have a seat ". Zama tayi tana mai saukar da kanta ƙasaa cike da jin kunyarsa sosai,kula da yayi da kunyarsa da take jine yasaka shi kwashe wa da wata irin dariya har yana mai fito da ƙwalla yace"kaji mun yarinyar nan fa,nine kike jin kunya Ko kuma wani sabon salan munafurcinne kika shiryo da safiyar Allahn nan kika zo ki sauke mun ita dan bana tunanin Ko office ɗinki Kin shiga,Allah yasa ba wani bacin ran kika kullo mun ba domin kuwa Dariyar nan da kikaga inayi akwai wani abu a bayanta idan aka tunzura ni dan haka karki fara. Ajiyar zuciya tayi ta ɗora hannayen ta dukka kan desk ɗinsa tace "Sir bana zo bane nan domin aiki ba, nazo ne domin confession wanda nake fatan zaka karbi ban haƙurina in the process ,ni mutum ce mai rauni idan abu ta shafi Family na wanda wani lokacin bana tunanin menene zai fito sakamako saboda wannan mistake din nawa,haka akan ka i made a huge mistake wanda ya sakani nake jin mutuƙar kunyar ka a yanzu haka ,kayi hakuri dangane da hallayyata dana nuna maka mara daɗi sannan da ɗabi'un dana danganaka dasu waɗanda ba naka ba,it was all my idea bana Farry ba kar kace zaka ɗauki wani mataki akanta ,ta nuna mun bata san Alliance da iyayen mu ke san haɗawa tsakanin ku ,a yanayin yarda ta nuna mun rashin san abun yasa na kawo idea ɗin wanda na tabbata Babu wadda zai so ya Auri mace kamar wadda na nuna maka a ranar ,nasan ban kyauta ba and it was very stupid of me ,dan Allah dan Annabi ka samu wani guri da gurbi a cikin zuciyarka ka yafe mun ,idan kuma kace zaka dauki wani hukunci ne bazan yi ƙorafi ba ,hakkin kane kuma a shirye nake domin na ɗauki wani hukunci da zaka mun amma ina neman alfarmarka da kayi hakuri kar ka saka Farry Ko mahaifan mu a ciki dan idan Appa yaji maganar nan wallahi bazamuji daɗi ba shi yasa nazo na sameka.. _Ya ɗauki lokaci kaɗan yana kallanta tare da hango tsantsar nadamar abun a tattare da ita sannan a ɗayan bangaren abunda yake hangowa a idanun Kiswa baya tunanin haka yake a bangaren Farry domin shi mutum ne mai gane mutane cikin lokaci mara tsayi sannan selfishness da ya hango tattare da Farry ba wai gizo ne yake masa ba gaskiyar al'amari ne.shafa sumar kansa yayi yace"so idan Babu hannun ita waccan sister taki a wannan babban plan naku mai yasa a office ɗinki ta nemi da nazo mu sasanta bayan ga dama tana da ita tun farko taƙi amfani da ita ,Ko hakan yana nufin ke kina sona ne kuma kina san ki mallakeni a maimakon ta dan haka kika kawo waccan shawarar after all nasan wancan likitan ba fina komai yayi ba and ke kuma you're not bad zan iya maneji dake duk da kuwa you're not my type. Tsintar kanta tayi da murmusawa kafun tace "Sir with all due respect relationship ɗina bai shafi laifin da nayi maka ba sannan idan zaka mun alfarma bana san ka sakashi cikin maganar da muke yanzu domin kuwa Haidar rayuwa ta ne bana jin kuma a rayuwa zan iya bawa wani ɗa namiji gurbinsa koda da wasa ne shi yasa ban saka hannu akan waccan takardun da ka bani ba na zabi da nazo na faɗa maka gaskiya domin kuwa soyayyata ita ce rayuwa ta babu kuma abunda zan iya trading ɗinta akai,haka ƙarfin ta yake gareni,Farry kuwa akan maganar da tayi maka ta iyu kayi mata ne a yanzu wanda da nasan zaka mata wanchan act ɗin ma bazai samu gurbi ba,and ka yarda dani When i said this Sir Farry yarinyar Kirki ce duk da kuwa ɗan Adam yana da wani guri a gefe guda na rayuwarsa wanda bai cika ba, amma idan kaga Its okay zaku iya sasantawa kamar yarda nace dama abunda iyayenmu ke so kenan,bazan dai daina baka hakuri ba dan Allah kamun afuwa. Murmushi ne kwance a fuskarsa yana mai yaba wautarta a soyayya Kafun yace"hala wannan soyayyar first love ce,kinsan akanta Babu gangacin da mutum baya aikatawa ,akan maganar ƴar uwarki kuma She's definitely not my type ,sannan ki ƙwantar da hankalin ki kamar yarda kika buƙata bazan saka sister ɗinki a ciki ba sannan maganar nan zata shafe kamar ma ba'a taba yinta ba,kinsa ni family man ne ina mutuƙar san naga mutum na da dedication akan danginsa dan haka zan yafe miki komai ya wuce amma fa cikin sharaɗi guda ɗaya. Saurin gyara zamanta tayi tana mai san jin menene wannan sharaɗin,ganin yarda ta zama restless tana san jin mai zai faɗa ya saka yayi waving hannun sa yace "calm down ba wani abun tashin hankali bane kike wani zazzare mun ido ,im not a bad person,ba komai kuma ne zai zama hukuncin ki ba face zama abokiya ta sannan mai tayani office work ɗin daya kakare mun ,.wayar sa ya cire a key ya tura mata gaban ta yace idan muna da deal ki saka mun numbern ki cikin wayana daga yanzu kuma Kin zama friend ɗina. Jin maganar tayi kamar wasa dan ba abunda take tsammani daga tare shi ba kenan,haɗe hannayen ta tayi guri biyu tace "Sir im sorry ban gane ba". Ƴar dariya yayi yace "na faɗa miki ni ba mutumin banza bane sannan bana nufinki da cutarwa ina sone kawai mu ƙulla abota wanda Shine hukuncin ki so zabi ya rage naki sannan na baki assurance bazaki samu aboki kamar Saleek ba and yauwa bana san Kina kirana Sir ɗin nan sunana Saleek kuma dashi nake san ki kirani ba wani Sir ba" Kallan sa take cike da mamakin juyin halayyar sa inda shi kuma yayi mata alamu da ido akan ta ɗauki wayar ta saka number ta.cikin nutsuwa ta ɗauki wayar tasa ta rubuta number ta ta miƙa masa,faɗaɗa fara'arsa yayi sannan yayi dialing ,ringing wayar ta tafara cikin Jakar ta ,daukowa tayi ta kalle shi,shima ɗin ita yake kallo Kafun yace"oya save my number sannan ina mai tayaki murnar zama abokiyar Saleek ina kuma san na tabbatar miki kamar yarda kike loyal a soyayyar ki,haka nake a abotata so lunch during lunch time and Its on me". Murmushi kawai tayi tace "thank you"still awkwardly domin kuwa abun baki ɗaya sabo ta tsincesa,ta kasa yarda wannan arrogant man ɗin ne a gabanta haka,koma dai mene tasan she will need to be very careful,sallama tayi masa ta tashi dan fita,tana ƙoƙarin fita Khalipha yana shigowa,matsa mata yayi ta wuce tana mai gaida sa inda ya amsa cike da fara'a da sakin fuska,binta yayi da ido har saida ta b'ace Kafun ya kulle ƙofar ya shigo ciki yana mai faɗin"mutumina ka ƙyaleni na gwada sa'ata kan Kiswa dan Allah alaji,babyn nan ta kashe ni so nake koda ba Serious abu ba a ɗan wana". Haɗe rai sosai Saleek yayi yace "a wana mene?bana san iskanci fa Khalipha,ba tun yau ba nake faɗa maka Kiswa ba Ko wacce irin mace bace kaje dai Chan ka nemo yan matan ka marasa nutsuwa amma banda wannan sannan idan baka sani ba na sanar da kai cewa She's in a Serious relationship sannan She's so loyal about it dan Ko kaje kace kana santa a banza dan haka ka riƙe sauran mutuncinka da take gani mu zauna lafiya. Zama khalipa yayi kan desk ɗin sa yace "ita da take Serious relationship sai kayi yaya?" "Nayi yaya kuwa?dame fa?"dariya Khaleepa ya saka sosai yace "mutumina kenan nasan dai akwai wata a ƙasa kuma idan tayi tsami zamuji "ƴar waƙa ya fara masa ta zolaya,jifan sa Saleek ya fara da files ɗin sa yana mai faɗa masa he's fired! Dariya khalipa ya fita yanayi yana mai faɗin"mutu ka raba ɗan nan Koma bazan daina faɗa maka you're in love ba" Hannu Saleek ya saka a baki yayi ƴar dariya yana mai shafa kansa yana maida maganar Khalipha a kansa,Kaɗa kai yayi a fili yace "No Babu ma yarda za'ayi haka ya faru no",files ɗin da ya jefi khalipa da ya kwashe ya fara duba su da kawar da tunaninsa. Kamar yarda ya nemi suje lunch hakan ya faru inda baki ɗaya cikin rashin sabo dashi taci abincin yayin da shi kuma yake mata hira cikin san ta saki Jiki dashi,wayarta da tayi ringing ne ta saka ta dakatawa tana mai faɗin "excuse me "kafun ta kara wayar a kunne tace"Assalamu alaikum hayatee" Take bite ɗin da Saleek ya saka a bakin sa yana tauna ya dakata,wata irin shagwababiyar murya da tayi magana da ita ce ta dake shi,he Just cant blv a gaban sa dan yarda ta cigaba da wayar kamar ma baya gabanta,cigaba yayi da cin abincinsa a hankali yana sauraran yarda take jefawa Haidar kalaman soyayya,ya kasa yarda wai Kiswa ce. Sai bayan ta gama wayar ne tayi realizing wai a gaban Saleek take,take wata kunya ta lullube ta ta fara kame kame,murmushi yayi yace"yanzu ne kike jin kunya ta bayan Kin gama narkewa a waya,dole nayi jotting down friend ɗina idan babe ɗinta ya kira ta mantawa take da kowa a gabanta" Sosai taji kunyarsa ta kamata dan kamar yarda ya faɗa indai akan Haidar ne ta wuce nan,haka suka gama cin abinci suka koma office a tare yana ta janta da hira wanda bata taba expecting yama iya ba. Chuchujay 08130229878 [5/16, 10:55 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na Chuchujay Book1⃣ Page1⃣3⃣ ___________karfe biyar na yamma Haidar yazo suka wuce da Kiswa gida bisa umarnin Ummi tunda basu samu zuwa Boutique ɗin ba da rana,da fari taso tayi masa gardama akan zuwan amma da ya fita da baki ya lallabata ya kuma sake tabbatar mata da bazata samu matsala ba indai daga gurin Ummi ne,da haka ta yarda tabi bayan sa a motar ta suka tafi tare . Koda suka isa gidan su Haidar Babu abunda gaban ta yake sai faɗuwa cos magane ne na zata ga sirikarta for the first time wanda abune take jinta very weird amma kasancewar Ummi ta saka tazo ya zama dole ta zo ɗin domin nuna girmamawar ta a gareta,rawar kan da Haidar yake Kiswan sa ta amsa kiran Ummi kuwa ba karami bane cos koda suka shiga Ummi bata falon ɗakin ta yayi Kai tsaye dan kiranta domin yasan tana ciki,ita dai Kiswa zaune tayi hannayen ta nata zufa yayin da a bangare guda kuwa kafun kace ƙwabo gabanta ya shiryu da kayan tabawa ,tana wannan zaman Tasleem ta shigo bakinta da sallama,da mamaki ta kalli Kiswa dan bata tsammanin ta sannan ba sai an faɗa mata ita bace duk da kuwa sau ɗaya suka taba haɗuwa,da fara'arta ta ƙaraso ciki tana cewa"wa nake gani kamar Auntyn mu" Kallan ta Kiswa tayi inda itama kallo ɗaya ta gane ta,wata irin kunya ce ta kamata dan tun abunda ya faru tsakanin su basu sake haɗuwa ba,murmushin dole tayi tace "ina wuni"dariya Tasleem tasa tace "ina wuni ?"Kina matar yayan nawa to be kike faɗawa ƙanwarki ina wuni,apart from that nasan kilan ma kin girme ni!.ƙare maganar Tasleem tayi tana mai zama kusa da Kiswa. Cike da fara'a Kiswa tace "well age never matters sannan bana tunanin gaisuwa tsakanin ƙarami ne zuwa babba,Babu laifi idan shima babban ya gaida ƙarami,thats exactly what respect mean" "Exactly my dear"muryar Ummi dake fitowa daga ɗakinta ya karaɗe gurin,saurin saukowa Kiswa tayi daga kan kujera ta zauna a ƙasa ,da sauri Haidar ya zo gurin ta yana cewa"babe mene Hakan"? Takowa Ummi tayi tana mai cewa "part of respect my dear"gaban Kiswa da ta kasa dagowa da idanta ta ƙaraso ta kama hannunta ta zaunar kan kujera tace "im not complaining Kiswa ki zauna kan kujera" Murmushi Kiswa tayi tace"nagode ummi ,ina wuni".ɗaya gefenta Ummi ta samu ta zauna kafun ta kama hannunta tana mai cewa "ina wuni yarinyata ,ya aiki ya kuma fama da Handsome yarona dan Nasan anayi". Murmushi kawai kiswa tayi ta kasa cewa komai saboda wani irin nauyin Ummi da take ji,itama Ummi ɗin ta fuskanci haka, haka nan taji Kiswa ta shiga ranta sosai dan ganinta ma yafi jinta ,kallan Tasleem da Haidar tayi tace "ku ɗan bamu guri mu gana da ƴarinyata,we need privacy" Ɗaga hannu Haidar yayi yace"of course bari nayi using damar naje na ɗan watsa ruwa,Ummi ga amanar Kiswa nan na baki"dariya Tasleem dake ƙokarin boye kishinta tayi tana mai cewa"Brother yarda ka barwa Ummi ita ni dai nasan haka zaka sameta".dariya ya saka kafun ya nufi hanyar fita a falan Ummi domin zuwa ya watsa ruwa yayin da Tasleem ma ta wuce tana mai jaddadawa Kiswa kan idan tana bukatar wani abu tayi mata maganaa zata zo Babu bata lokaci,da ƙwarin Gwiwa Tasleem ta fita tana tsoran kar zuciyar ta ta karaya ta fashe da kuka a gurin ,kamar jira take kuwa tana shiga ɗakinta ta fashe da wani irin kuka Mai cin rai tana mai jin zuciyarta kamar zata fita a kirjinta ,a hankali ta fara shafa saitin zuciyar ta tana mai Addua a hankali tana mai cewa"'ya Allah help me ,ka taimaka mun ka cire mun san yaya Haidar indai babu alheri a cikinta,Allah 'ya sani ina san shi ba domin kuɗirin mahaifiyata ba sai domin Allah amma nasan jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa Allah ka kawo mun ɗauki "a haka ta ringa lallashin kanta kafun ta gangara kan gadonta ta ƙwanta ta rumtse idanunta tana mai ambatan Allah,ba sai wani ya faɗa mata ba,Kiswa ta haɗu ta Ko ina ta yarda babu ma yarda za'ayi ta haɗa kanta da ita,She's not in her lane a kyau ,class da komai ma kuma tasan idan aka ajeta aka aje Kiswa to Kiswa zai zaba sau dubu,haka nan ta ringa bawa zuciyarta hakuri da addu'ar fin ƙarfinta. ** __Bayan tafiyar Haidar da Tasleem sai ya zamana daga Kiswa Sai ummi,shiru Ummi na karantar ta yayin da ita kuma ta kasa haɗa ido da ita,murmushi ummi tayi da ta fahimci hakan,gyaran murya tayi tace "ni uwace mai san kanta muddin abu ya haɗa da Haidar,zan zab'esa fiye da komai a rayuwa sannan zanyi hakan over and over again koda kuwa abun zai zammar mun matsala,shi Kaɗai Allah ya malaka mun sannan wahalar da aka sha kafun samun sa abune wanda bana san maganar sa a yanzu ya zama labari,ina da san Kai yarda baki tunani akan haidar domin kuwa shi yasa na zabeki kan Faridha domin kuwa ke ya zab'a ba ita ba sannan ni abunda yake so shi nake sannan sai gashi nima kin shiga raina duk da ba wai muna status ɗaya bane,magana ɗaya cikin biyu nake san yi dake,ga Haidar nan please dont hurt or break his heart domin kuwa ya dauki soyayyar duniya ya ɗora miki,sannan abu na biyu indai pure kike ban damu da maganar wani ba a kanki musamman ita Aunt ɗinki da kike gurinta wannan matar mean no Good,bazan ce dole sai naji ya zamantakewar ku take ba dan nima ba mutum bace mai yaɗa sirrin gidana ga wani ba dan haka na wani bai dameni dole sai naji ba,but please be careful a duk inda kike domin kuwa in wani abu ya sameki zamu shiga matsala domin idan Haidar ya shiga daga ni har Baban sa mun shiga idan kuma kika shiga kinga dole shi ma ya shiga ,sauran magana kuma ta maza ce ,Baban Haidar zaije ya samu shi kawunki idan yaso duk abunda za'ayi sai ayi, but definitely zanyi binciken background ɗinki duk da nasa ko da negative abu aka samu kanki babu mai sakewa Haidar ra'ayi akan ki ,but still ina san nasan wacece ke its My right"gyara zama tayi tana mai mayar da hankalinta kan wayarta kafun tace "so wacce kala kika fi so" Cike da confusion na rashin gane tambayar Kiswa tace "Na'am?"ɗaga gira guda mami tayi tace"Uhum ya kamata nasan likes ɗinki da dislikes ɗinki saboda idan ƙawayena na hirar taste ɗin sirikansu da siyan musu abunda suke so nima nayi bragging and hope kina da classy taste sannan bazan boye miki ba i dont like it yarda kike wannan sunkuyar da kan ni ba surukar da bace ta yanzu ce dan ni so nake matar Haidar ta zama kamar ƙawata dan haka already na siya miki VIP membership a Spa ɗin danake zuwa and nayi mana booking saturday make sure kinyi squeezing idan ma Kina da abunyi cos na riga nafara anticipating ma frnds ɗina zan kawo musu in Law na 9 sharp,wanne car kike driving By the way? Cikin rashin sakewa da abunda Ummi ta faɗa na Tayi mata Register na membership tace "im driving 306 and Ummi please ba sai Kin mun reg na membership ba yayi yawa" kallanta Ummi tayi tana san maganar 306 ɗin da tace tana ja ya gama blending a kanta kafun tace"306? Kice mun ke Haidar ya gani da ita ya siya,Babu irin fadan da banyi ba akan ya daina embarrassing kansa da motar nan ,ga nan motocinsa worthing many millions amma ya aje su gida,but yea im not complaining dole idan kika shigo ki daina jan 306 dole kinga shima ya hakura amma yanzu bazan maku dole ba,zan aiko driver yazo ya daukeki ranar saturday wanda kinga yana nufin bana san gardama akan maganar ," Dole Kiswa ta bar mata ta cigaba da yi mata godiya yayin da ta dan saki jikinta da ita tana faɗa mata likes and dislikes ɗinta kamar yarda ta buƙata,suna cikin hakan Haidar ya fito cikin jallabiya Navy blue yana ta zuba kamshi,zama yayi yace "yauwa menene kyawawan yan matan da nake bala'in so guda biyu a rayuwata suke tattaunawa cikin nishaɗi Haka"? Yar dariya suka saka a tare inda Ummi ta bashi amsa da"magance ta mata biyu dan haka baza kaji ba"murmushi yayi yana mai jin daɗi a zuciyar sa Ummi ta karb'i Kiswa hannu biyu biyu sannan Kiswa ɗin Ma ta fara sakin jiki da ita ,abu guda ɗayane zatayi fama dashi wanda Shine rich life style ɗin Ummi da yanayin yarda suke da rich ƙawayen ta kowa yana san yace shine na gaba.a haka ranar Kiswa ta shashance gidan ko tace Ummi ta riƙe ta har sai da taci dinner duk da kuwa hankalinta yayi gida although tasan ba wanda zai ce mata dan me ko daga ina take amma a hankalinta tasan tabbas bai kamata tana gidan ba har dinner amma ta kula Ummi mutum ce wadda bata san kace mata a'a dan haka ta yi hakuri har after Dinner ɗin wadda Baba ya hallarta yayin da Shima ya ringa yaban ta ta ko ina . Lokacin da tazo tafiya baki ɗayan su suka rakota har compound inda Ummi ke sake jaddada mata fitar su nan da Ƙwana huɗu, Fafur Haidar yaƙi barin ta ta tafi ita Kaɗai duk da kuwa ba a mota ɗaya zasu tafi ba,Baba ma ya saka baki akan lallai Haidar ɗin ya bita a baya,murmushi kawai kiswa take domin kuwa wannan soyayyar da suke nuna mata cikin ɗan ƙanƙanin lokacin nan bama tasan inda zata kaita ba,godewa Allah tayi a zuciyarta tana"Addu'ar kawar da fitina a cikin ta"har gida ya raka ta sannan bai wuce ba sai da yaga ta shiga gida tukkun ya juya motar sa ya nufi gida. Tana shiga ta faka motarta ta shiga ta ɗauki system ɗin ta ta shiga gida tana mai jin duk wata damuwa tata ta yaye mata,Babu wata fargabar za'ace ina kikaje kika kai haka tunda normally bata Kai bayan sallar isha'i a waje sannan da Mama ke gidan dole zata yi mata faɗa akan taje gidan surukai ta zauna Babu kunya amma Mother kuwa koda ɗakin saurayi zataje ta kwana Babu Abunda zai dameta iya kace ma ta zama mutum ta farko da zata fara yayatata,tana shiga Falon dake na kowa wanda yake farkon sashen gidan tayi turus ganin Mother zaune a kan kujera ta kunna Tv tana kallo,sallama tayi tace "sannu da gida Mother ina wuni" ? Wani irin banzan Kallo Mother tayi mata kafun tace"daga gidan uban wa kike karfe takwas na dare sannan zaki shigo gida Kina daga hanci kamar na ubanki,Kina san ki nuna ke kinfi uwarki ko"? Da fari kamar ta wuce ta bata ce mata komai ba sai kuma taga Babu amfanin ta wuce ta ɗin gwanda ta bata amsa dai dai tata ,dan haka ta samu guri ta zauna tace "daga gurin Aiki Haidar yazo ya ɗaukeni akan Ummin sa na san ganina ,wurin yamma dai haka mukaje gidan ,baki ga irin soyayyar da suka nuna mun ba dan Ummi har Membership ta siya mun a inda take Spa ranar saturday za muje tare na tabbatar kuma gurine na mata masu aji da ji da kansu,sannan Ummi ta karbe ni hannu biyu yanzu haka tace magana ba za'a barwa mata ba ta maza ce,and Yes kafun na manta hakan yana nufin tayi rejecting offer ɗin ki ne ta zab'eni zabin ɗanta ,dan Allah Mother ba sai Kin kirata ba ta daina ganin sauran mutuncin mu ba,sannan kiyi hakuri nayi dare bazan Sake ba banyi tunanin zan saki rashin bacci ba saboda ban dawo ba,bari naje na watsa ruwa ,"tashi tayi dan barin gurin taji an kamo mata hannu,juyowa tayi taga Farry tana faman huci kamar wata zakanya kafun tace"how dare you kike faɗawa Mother magana haka". Wani irin kallo Kiswa ta bata kafun ta kwace hannunta cikin muryarta Babu zafi tace"how dare you Ask me that stupid ,lame,idiotic ,useless question?" Kama ƙugu Farry tayi tace"na tambaye ki ɗin sannan ki bata hakuri idan kuma ba haka ba wallahi ki gane kuɗar ki" Kallanta Kiswa tayi tana san karyata Wai tare sukayi yarinta mai daɗi,ta rasa ina aka kai mata Farry mai nuna tana ƙaunarta sannan mai shigar mata faɗa muddin Mother nayi mata akan rashin Gaskia sai gashi a yau wai tare suka haɗe Kai ake mata cin kashi wanda bata shirya bar musu ba dolene ta ƙwatarwa kanta yanci kafun su ƙwace mata.bata Sake ce musu komai ba ta bar gurin tana mai jiyo Farry na fada mata maganganu mara sa daɗi,.kamo Farry Mother tayi tace "ki ƙwantar da hankalin ki Farry mana dani take maganar wallahi,na fita iya Shege sannan duk abunda take ji dashi nawa ya ninka" Tashi sukayi kowa yayi ɗanƙin sa dan kimtsawa . Kai tsaye Kiswa na shiga ɗakinta ta cire kayanta ta faɗa bathroom dan yin wanka,tana jin alamun mutum a ɗakin ta tunanin kila Farry ce tazo neman wani balain ya saka ta cigaba da wankanta,bayan ta gama ta sako bathrobe dinta fara ta fito tana tunanin da wadda Farry ta shigo amma ga mamakinta sai ganin 'Yaya Sageer tayi kwance kan gadonta daga shi sai boxers da singlet,wani irin faɗuwa gabanta yayi, mazewa tayi tana daga bakin kofar bathroom ɗin tace"yaya Sagir lafiya?,ko kayi batan hanya ne ka shigo nan i mean a kallan gadan ma zaka gane ba naka bane". Tasowa yayi ya zauna yana binta da wani mayen kallo yayin da ita kuma ta Sake tamke igiyar bathrobe ɗinta ganin kallan da yake mata. Duba agogon bangon ta yayi yace"well lafiya Baby sannan ba batan hanya nayi ba inda nake san zuwa hanya ta kawoni kuma ina fatan a bani hanyar da nake san bi nabi domin kuwa dole ne na samu,".ƙaramar dariya tayi tana san gane inda ya dosa wanda idan hasashenta yana kai mata dai dai lalata yake san yayi da ita ,waiyazubillah.riƙe handle ɗin bayin tayi gam tace"Yaya Sagir ban fahimci abunda kake cewa ba sannan bana fatan na fahimta,zanyi shiru Babu wanda zaiji zuwan nan naka amma fa sai dai in idan kaso haka ka fitar mun a ɗaki tun ina da sauran girma a gareka". Dariya yayi yar ƙarama yace"Kiswa kenan,kinsan irin wahalar dana sha wajen danne duk wata sha'awa taki da nake ji? ,kinsa ya na danne na daure nake kiranki ƙanwata duk da yarda nake ji akanki,?kinsan ya nake ji idan naji Kina ambaton wani banza Chan har Kina wani faɗa akansa?duk baki da idea dan haka kar ki fara mun wasu maganganu yanzun nan,i will have sex with you idan kina so ko ba kya so,dole ne na sauke craves ɗina akanki yau ko me za'ayi ,and trust me Babu mai ji after all ni zan Aureki domin dare ɗaya bazai ɗauke mun buƙatata akan ki ba". TBC Chuchujay ✍️ 08130229878 Kuyi hakuri kunjini sai a hankali makaranta ta buɗen wuta,kun dai san watan karshe kafun grad akwai wuta. Xx❤ [5/19, 11:45 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na Chuchujay ✍️ Book1⃣ Episode1⃣4⃣. _________Takowa Yaya Sagir ya farayi zuwa gurin ta yayin da take jikinta ya fara rawa,ganin da gaske gurin nata yake nufowa ya saka ta buɗe ƙofar bayi ta faɗa da wani irin zafin Nama ta kullo tana ambatan Allah wanda tasan shine zai kawo mata ɗauki ba mutum ba,Takowa yayi bakin kofar bathroom ɗin ya murɗa handle ɗin cike da baccin rai yace"ki buɗe kofar nan Kiswa domin kuwa idan kika kuskura na b'allata baza kiji daɗin ba wallahi dan haka tun muna mu biyu ina lallab'aki ki fito muyi abunda zamuyi na wuce ,ina da aiki kema Kina dashi da safe" Ƙaramar dariya tasa cikin kuka tace"you're far beyond a devil yaya Sagir,you're evil sannan Allah ba zai tab'a baka dama akaina ba wallahi domin ni na rigaka nace Allah,duk wani mugun nufin ka da kake dashi akai na wallahi sai dai kayi ka gama Allah bazai tab'a baka dama ba,im disappointed in You sannan yau ka tabbatar mun ni ba taku bace tunda nayi imani da Allah bazaka tab'a neman Farry ba,sai ni zaka wulaƙanta?" Cije leben sa yayi yana mai shafa ƙansa cike da takaici kafun yace"Kiswa idan kin ɗauki wannan mugunta so be it amma ni nasan ba mugunta bace ,We are two adults for God sake,muna da buƙata kin fi sone naje waje na biya buƙata ta da ƙazaman mata na samo wa kaina wani ciwo bayan gaki wadda nake so a gida clean and pure haba mana Kiswa ki tausaya wa yayanki." Sanin bashi amsa bata da amfani duba da yarda yayi wannan maganar ya saka ta furta "mahaukaci,daƙiƙi,jahili".cike da wani irin fushi da ya taso masa jin kalmomin da ta kira shi dashi ya daki kofar bayin yace"ni kike zagi?" "An zage ka ɗin, kayi abun zagin wanda da akwai dama jefe ka ya kamata ayi "useless dog sannan kayi mun alfarma ka cigaba da dukan ƙofar bayin nan yarda mutanen gida zasu gane kana nan su zo"sanin abunda ta faɗa gaskiya ne ya saka shi cije lebensa yana mai nuna ƙofar da yatsa yace"zamu haɗu Kiswa sannan idan na tashi dawowa baza kiji daɗi ba dan ashirye zan zo and na maki rantsuwa sai na sameki" Yar dariya tayi daga ciki tace"yayi,sannan nagode da kayi pointing mun kanka kaga kuwa yanzu na gane ɗan akuyan da ke zaune gidan nan sannan ranar da zaka dawo nima ashirye zaka sameni wallahi concerning my dignity i can hospitalize you Just dare me and See kuma ,Try me you dog".ƙwafa yayi ya juya ya fita da ƙudirirka masu yawa akan ta,sai da ta tabbatar ya fita tukunna ta buɗe a hankali ta fito ,zazzare idanu ta fara tana mai san tabbatarwa bai boye a wani gurin ba,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fito ,direct ƙofarta ta nufa ta sakawa key sannan ta dawo ta zauna kan gadonta ta rushe da wani irin kuka tana addu'ar dama ace mumunan mafarki ne wannan tasan dole wani zai tashe ta ,amma kash gaskiya ce mai ɗaci da rashin daɗin saurare ,babu abun da yake damunta kamar irin yardar da ta basu,shin wane kuma zata yarda dashi gidan nan bayan hell ɗin da tayi facing cikin satin baki ɗaya,tana wannan zaman Haidar ya ƙirata cos yana jiran kiranta dama amma ganin bata kirasa ba ya sakashi gazawa da jiran kira nata shi ya kira ,Kamar zata ɗauka Amma sanin shi mutum ne mai saurin gano damuwa a muryarta ya saka Bata ɗauki wayar ta ta saka ta a silent,ganin kukan bazai mata ba ya saka ta tashi ta shiga closet ɗinta domin saka kayan bacci,dama already ta yi sallah gidan su Haidar dan haka kawanciya kawai tayi tana saƙa da warwarar yarda zata kawo karshen wannan sabuwar ƙaddarar da ke tun kararta kamar guguwa,ita dai bata da wata hujja sannan babu wata mace da zata goya mata baya gidan ,Appa kuma ba magana ce wannan wadda zata iya yi mata ba ,Amma Ya sameer fa ,shin shima yana mata irin kallan da ya Sagir yake mata ko A'a domin yanzu bata san inda zata kama ba bata san wa zata tunkara ba saboda shima yaya Sagir ɗin bata tab'a tsammanin zai bijiro mata da wannan badaƙalar ba ,a haka tana waɗanan tunanuka bacci ya ɗauke ta wanda zata kira da barawo domin kuwa baki ɗayanta a tsorace take. **** Washe gari koda ta tashi tayi sallah da asuba kasa komawa bacci tayi,Qur'ani ta ɗauko tayi ta muraja'a har sai da gari ya fara haske,wanka ta shiga ta yi kafun tazo tayi shirin tafiya office ,tsaye tayi bakin mudubi lokacin da ta gama tana mai duba kanta a mudubi,ita dai mutum ce wadda bata tab'a mantawa da ita ba muharrramar mazan gidan bace wanda hakan ya saka duk lokacin da ta saka kaya zata duba ta kalli kanta da kyau ta tabbatar da cewa Batayi shigar da bata dace ba,amma duk da haka sai da ya zamana Ya Sagir ya ɗauke ta ta hanyar banza wanda tunanin abunda ya faru kawai zuciyarta kan mata ɗaci taji baki ɗaya bazata iya yafe abunda ya faru ba,haka nan take ji kamar idan ta fita wani zai gano wani abu wanda bata fatan kowa ya gane hakan, tana so ya zamana ita zata yiwa tufkar hanci,ta shirya kanta ,ta shirya zama Mai dauriya juriyar da zata yiwa kanta faɗa,gyara tsayuwarta tayi tana mai Sake kallan kanta da kyau kafun ta ɗauki hand bag ɗinta ta fita dan bazata dawo ɗakin ba after breakfast wucewa kawai zatayi,a da tace bazata tsaya breakfast ba gudun haɗuwa da yaya sagir amma tunawa da tayi kunyar mara kunya asara ya saka zata tsaya,sannan tana san ta kalli fuskar sa ta tabbatar da cewa shi ɗinne yazo keta mata haddi,?shi ɗinne ya faɗa mata maganganun jiya?shin zai iya haɗa ido da ita?koda ta isa table shi Kaɗai ke Kai wanda ya tabbatar mata cewa ya fito da wuri ne yana jiranta ba sai an faɗa mata ba,ajiyar zuciya tayi ta taka zuwa dining table ɗin ta zauna hannunta ɗauke da wayarta ,kujerarta ta jawo ta zauna ta cigaba da danna wayarta ,tunda tazo gurin yake kallan ta, sanin yana Kallanta ya saka ta haɗe ranta sosai ,yar dariya yayi yace "Kiswa kenan,babu sallama Babu gaisuwa?mene yayi zafi?" Yi tayi kamar bata ji sa ba dan kula sa ma bata tunanin yana da amfani tunda ita dai a gurinta yanzu baya da wani mutunci ƙwataƙwata ,dariya ya kuma yi kafun yace"ina fatan baki shirya faɗawa wani little encounter ɗin mu ba domin kuwa babu mai yarda dake,kowa zai ɗauka sharri kike mun musamman yarda dukkansu suka yarda im decent ,and abunda baki sani ba my mom will die backing me up so ki rike sirrin ki a bakin ki kar ya kaiki ga tushen dana sani dan Wallahi idan kika zabi buɗe wannan bakin wahala ta ganki". Ɗauke idanunta tayi daga kan wayar tana mai kalllansa a karo na farko kafun tayi wata irin dariya kafun a cigaba da danna wayarta Kamar bata ji abunda yace ba wanda yin hakan ya Sake tunzursa ainun.tana Danna waya ne amma a bangare guda tana tunanin maganar da yayi na Mother zata goya masa baya,a nata tunanin da yarda duk tsanar da Mother tayi mata baza ta taba bada goyan baya a keta mata haddiinta ba tunda ita uwa ce mai ɗiya mace wadda bazata so hakan yafaru da tata ƴar da ta haifa ba,it would be ridiculous ,tasan duk tsanar da tayi mata idan taji maganar nan bazata taba ragawa sagir ba ,haka nata tunanin yake bata,amma koma dai menene magana ce ake ta bai samu nasara akanta ba a tayin farko sannan ya bata hint na sharrin da yake binta dashi so next time he wont like her ,sai a yanzu maganar Baba Baraka ta fara dawo mata da kuma nacin maganar da yake mata na tayi masa wani taimako,a haka suna wannan zaman sauran mutanen gidan suka hallarta inda kowa ya gaida da kowa wanda yin hakan ta b'angaren Mother ya mutuƙar bawa Kiswa mamaki ganin yarda Mother ke amsata faran faran,Kai bama ita ba kowa abun ya bashi mamaki ,hakan yasa Kiswa ta fara zargin wani abu ba dai dai yake ba a wannan fara'ar ta Mother. Kiswa na ƙokarin aje Cup ɗinta da ta shanye tea ɗinta Appa ya jefeta da maganar da ta daɗe bata ji mai daɗin ta ba inda yake cewa"nayi waya da Costum Bula, and labari mai daɗi,ranar sunday zasu zo tambayawa Haidar Auren Kiswa kuma ina san Auren kar ya ɗauki lokaci,ba kuma shawarar wani anan nake nema ba,naga ya kamata ku sani ne duk da wasu cikin ku ba san Auren suke ba"hankalin sa ya mayar ga Kiswa wadda take ƙokarin boye ihun murnar dake neman san ya ƙwace mata yace"dota what are Your prayers?". Kasa rufe bakinta tayi ,gyara zaman ta tayi tana mai kallan Appa tace "Appa burina guda ɗaya ne wanda bai wuce ina san a saka dangin Abbana ko guda ɗaya ne a cikin maganar Aurena after all nasan ba dukkan su ne na banza ba ,ga kawu Halilu kawun Abbana he is very kind to me and a sau da dama yana yawan kirana yaji lafiya na,and yace mun idan har na tashi Aure kar a cire sa,and Appa nima ina san haka musamman da ya zamana akwai masu tantamar ko ina ma da uban nan ina ganin hakan zai wanke zarginsu ,sannan nasan Kai Kaɗai zaka iya yiwa Mama magana yarda ta ɗauki zafin nan da su. " Cike da yaba hankalin Kiswa sameer yace "nima dai Appa ina tunanin maganar nan ta Kiswa abun a duba ce at least Sun chanchanta"ajiyar zuciya Appa yayi yace"well banyi Alkwarin zama da Zubaida akan yi mata wannan maganar ba domin bana fatan zama ni da Zubaida dan na faɗa mata wani abu da zummar ta jini domin da Zataji maganata shekaru da yawa da taji amma zanyi wa Dada da baffan mu magana tunda dai ni da Zubaida sune iyayenmu,Dole zata ji maganarsu, sannan da yardar Zubaida da rashin yardarta babu abunda zai sake na cewa Dangin mahaifin Kiswa sun fimu karfi a abunda ya shafi Aurenta duk da muma zamu iya Aurar da ita basu amma hakkin su ne sannan suma masu tantamar mahaifin Kiswa a wanke musu doubts ,shi yasa na tambayeki ,what are your prayers domin kuwa abunda kike so shi za'ayi " Godiya tayi ma Appa kana ta tashi tana Mai satar kallan Mother wadda tunda Aka fara maganar bata saka baki ba hankalinta na kan arish ɗin da take ci,fita Kiswa tayi tana Mai yi masu sallama wanda tana tashi Farry ma ta tashi ta musu sallama,Kiswa na ƙokarin buɗe motarta taji an riƙe mata hannu,juyowa tayi cos already tasan Wane,haɗe ranta tayi tamau tace"yanzu kuma Waccece matsalar ki Farry?" Haɗe rai itama Farry ɗin tayi ta saka hannunta cikin jakarta ta ciro check book ta cike komai banda amount ɗin kudi ta mika mata ta tace"ga blank check nan ki saka duk wani amount da kike tunanin zai miki zan biya In dai zaki bar mun Haidar ." Kallan check ɗin Kiswa tayi sannan ta kalleta tayi ƴar ƙaramar dariya tace"so yaushe wannan dramar karyar san na bar miki Haidar ta fara?i mean are you Nuts or you're just trying to deny the fact that you have lost it?kina hauka ko?bari kiji na faɗa miki wani abu,A gurina Haidar ya wuce duniya da abunda ke cikinta har su ƙudi da kike ɗaga kafaɗu dasu kina thinking Kin wuce kowa a rayuwa,when wanda ya tarasu from scratch bai ɗaga kafaɗa ba,See Farry ki shiga hankalinki tun wuri ki rabu dani da wannan shashancin 'dan wallahi idan kika sake mun wannan iskanci i wont mind beating you blue black"tsaki taja tana Mai tureta gefe ta shiga motanta ta tada. Bin ta Farry tayi da kallo har ta figi motar,kwafa tayi tace "wallahi idan ban samu Haidar ba bazaki sameshi ba,im tired na gaji da nuna mun da Appa yake Kin fini,abunda yake taƙama dashi wanda yake sakawa yake maganar gwara ke akaina zan ƙwacesa sai naga kuma sai mene,Haidar dole ya zama nawa kuma ni zan Mai dashi nawa ko Kin so ko kinƙi,that i promise."motarta ta nufa tana Mai yiwa gate man jaraba akan ya buɗe Mata gate. Bayan kowa ya fita Ya rage daga mother sai sagir wanda dama space suke jira,washe baki mother tayi tace"uhumm Sagir ka bani labari mai daɗi na tabbatar duk strong shit ɗin nan da take forming pretending ne,Mai yasa kaga tunda Aka fara maganar Auren ban saka baki ba?saboda nasan na saka hannuna a kan abunda bazai taba barin wannan Aure ya wakana ba so ina abunda na saka ka?". Shafa kansa yayi yace "akwai matsala fa dan abun bai iyu ba cos she was fast ta shige banɗaki sannan tayi warning ɗina akan zata yi ihu kuma kinga tana Yimun ihu game over ,na mutu shi yasa na fita a ɗakin,worst abun kuma yanzu tasan mai nake so akanta" Shiru Mother tayi tana Mai jin wani irin baƙin ciki kafun ta kallesa tace"its okay kar dan wai ba'aci nasara ba yanzu abun ya karyar da kai,next time zamu gwaɗa amma muje a shirye dan na fahimci wannan yarinya tayi fukafukai waɗanda idan ban balle mata su ba zata fara tashi sama,and trust me wannan yaran Haidar mijin faridha ne,yanzu ka tashi ka wuce gurin aiki zamu san abun yi,nima ina da appointment da client bari na wuce kar nayi latti". Haka nan Mother ta fita zuciyarta baka wuluk ,koda ta isa firm ɗin su client ɗinta ma haka nan ta gana dashi sama sama kafun ta ɗaga haɗuwar su domin bata da nutsuwar ganawa da shi ta fahimci case ɗinsa yarda ya kamata ,aminiyar ta Brrst Salamatu ce ta matso inda take tace "ƙawata wai menene damuwar ne ,kar dai akan wannan yar riƙon ne kike nema ki sakawa kanki hawan jini." Ajiya zuciya Mother ta sauke ta kalleta tace "ki barni kawai ƙawata wallahi al'amarin Kiswa yana nema ya saka zuciyata ta buga,baki ɗaya yarinyar nan na nema ta zamar mun karfen ƙafa,na rasa yarda zanyi na cire ta,yau kina ji maigidana maganar Aurenta da Haidar yake,na rasa abunda zanyi gashi duk abunda na shirya sai kiga ya lalalce".dafata Barr Salamatu tayi tace"yo Allah na tuba idan duk wani makirci yaƙiyi menene amfanin Malaman garin nan,kinga akwai wani malami na babu bata lokaci idan yayi aiki,abu guda ɗaya zamuyi wanda Shine sakawa ya farraƙa su wallahi idan yayi miki aikin nan ba wasa,dan aikinsa yafi na wannan malamin da ya baki mallakar Appan su sameer. Shiru Mother tayi tana nazari kafun tace"ke ni rabani da wannan harkar tukunna shi kanshi Appan nasu kaɗan ya rage wanda Shine na rashin kashewa iyayensa unnecessary kuɗi amma tsakanin sa da wannan yarinyar yaƙi kamuwa ,nima nan kina ji ranar abunda yayi mun i told you ai ,dan haka ni kawai ki barni na buga tugguna dan yanzu card d'in da nake bugawa zai baki mamaki sannan jikina yana bani zanyi nasara ". Kaɗa Kai Brr Salama tayi tace "ai shikenan idan uwar bari ta kamaki zakizo ai ni dai a ko yaushe ƙofata ta taimaka miki a buɗe take" "Ƙofar ki ta kaita wuta dai"Brrs Hafsat wadda take itama ƙawarsu dan duk tare suka shigo firm ɗin ta faɗa tana Mai sake maida hankalinta kan system ɗinta,bayan ta gama ta ɗago ta kallesu tace"wallahi juwairiyyah ki guji biyewa Salamatu Kin san dai Halin ta,idan kuma kika ce ke Abunda Allah ya tsara bai miki ba to Kina daf da kalmashe dana sani babu wanda ya sani,and after all yarinyar nan fa babu abunda ta tsare miki,kamfaninku kanshi taƙi karban aiki a gurin,koda kuwa mijinki ne 'ya mutu Bata da gado so mene na cutarawar har tana alfaharin tuna miki ta kaiki gun malami 'ya raba mijinki da danginsa yo boka dai sannan abunda kashuka shi zaka girba dan Allah mu gujewa yin abunda zai faɗa kan yaran mu da basu ji basu gani ba". Tsaki Brr salamatu tayi tace"says someone who had an abortion When she was 16 ,abeg my frnd idan zaki saurara ki saurara idan kuma bazaki iya ba kar ki damemu da wani kinibibinki after all we are all sinners". Murmushi Brr Hafsat tayyi tace"well naji i had an abortion da shekara sha shida ,kuskure nane wanda ɗan adam baya wuce sa amma kar ki manta at that sixteen i was raped ba karuwanci nayi ba sannan Alhamdulillah ban taba siyar da imanina ba dan zuwa gurin wani mushiriki 'ya biya mun buƙatar duniya ba kinga kuwa shima abun buga ƙirji ne,duk kuma abunda kuka ga dai dai ne kuyi dan Allah wanda baiji bari ba...... "Ita dai Mother bata ce komai ba dan bata san musu da Hafsa ta nemi ta chanza mata kuɗirinta Akan Kiswa wanda bata nemi ta sauke makamai ba sai taga ƙarshen yaƙi ,amma magana kuwa ta malam dama bata ma sakashi a ranta ba. ********** Delay a update bashi na shirya muku ba a littafin Kiswa,but ina da alot a plate ɗina wanda nake dealing da within lokutan nan,but i will be trying my best naga koda book one ne na gama muku update da wuri tunda wancan book two dama kuɗinka karatun ka and like i said its affordable,ku dai ku cigaba da kasancewa dani a tafiyar labarin Kiswa ❤❤ Xx Chuchujay ✍️ 08130229878 Yar arewa 1&2 N500 Abla adnan N500 They are still on my paid book shelf Come and purchase 🥰❤ [5/22, 10:10 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWA💥 (Surrogacy was the cause) Na CHUCHUJAY ✍️ Ku bi whatsapp channel ɗina domin karatu cikin nutsuwa. https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05 Book1⃣ Page1⃣5⃣ ________Murmushi Shine kawai abunda ke kwance akan fuskar kiswa yayin da a lokaci guda idan ka kalleta zaka gane tana cikin farin ciki ne , hannun ta guda ɗaya riƙe yake da wayarta manne a kunnen ta tana Mai sauraran Haidar yana rera mata waƙar yabonta tare da zayyana mata irin adadin farin cikin da yake ciki,knocking ɗin da ake a ƙofarta ne ya saka tayi excusing kanta da tabbatar masa zasuyi waya anjima kafun sukayi hanging up ta bawa Mai ƙwanƙwasawar izinin shigowa. Saleek ne hannun sa ɗauke da bunch na flower ,da mamaki ta kallesa tana Mai cewa"Kai ne dama kake knocking?it doesn't sounds like you " Murmushi Yayi ya samu guri ya zauna yana Mai aje flower ɗin kan table ɗinta yace"Good morning beautiful,ga flower nan Mai kyau na gani a hanya ta 'na siya cos kyawunta a kyakkyawan hannu kamar naki hope you love flowers,and knocking kuma ai abune na wajibi,forget wancan lokacin danake behaving gareki as a jerk ,trust me im one sweet guy that respect women,so tell me naga kamar kina cikin farin ciki share with me". Ɗaukar flowers ɗin tayi tana Mai kaiwa saitin hancin ta kafun tayi sniffing tace "i love flowers ,and thank you for trying to be a Good guy"aje flowers ɗin tayi tace"dama Ina da empty Vase ina zuwa"tashi tayi ta shiga cikin store room ɗin dake cikin office ɗin ta ɗauko Ƙaramun Vase ɗin ta ɗora masa kan desk a gaban sa tace "oya get to work".ƴar ƙaramar dariya yayi yace "ke bama kya tsoran wani ya shigo yaga kina saka acting chairman aiki ko,i mean the guts for me". Ƴar karamar dariya tayi kafun tace"well a gaban kowa you're an acting chairman wanda zai zama chairman In two weeks time amma a gabana idan ina tare da kai i only See my friend and i cant help it kai ka bani wannan damar and abun mamakin Shine i like it and Guess what,farin cikin da kaga inayi ba komai yake sani ba face yau Appa yace iyayen Babe su tura a tambaya masa Aure na ,i Just can't help it na kasa boye farin cikina ,i mean it was a rough road ɗin da yanzu nake jin kamar anzo ƙarshe."ƙarshe maganar tayi tana Mai saka fuskar damuwa kaɗan. Wani irin yanayin Saleek ya tsinci kansa jin wai za'a zo tambayar Auren ta wanda take cikin mutukar farin cikin da ba sai an faɗa maka ba ,Ganin kuma yanayin da ta saka a fuskarta lokacin da takai ƙarshen maganar ya danne san ran sa yace "Wow im very Happy for you,i mean abu ne na ayi murna cos finally Mai sakaki mantawa gaban wani kike zai kaiki gidan sa las las,but What's with the sad face ?hope ba wani matsala ". Ɗan shiru tayi tana kallan sa tana Mai nazari a akan sa ganin yarda ya nuna mutuƙar damuwarsa ,murmushi tayi tana mai wasa da hannunta tace"kasan its funny yarda wai ni dakai ne muke zaune muke magana a matsayin abokai like har kana nuna damuwarka a kaina,i just hope ba wani fansa kake san ɗauka akai na ba,idan fansa ne just tell me already domin kuwa im getting comfortable around you musamman da yarda kake nuna kulawarka akaina,kaga ni bana da wata ƙawa mace wadda zance maka mun shaƙu sosai,they are all schoolmates waɗanda they are after Farry not me dan yanzu ma duk sune ƙawayenta and idan kaga yarda suke ignoring ɗina sai ka ƙaryata kace ba tare mukayi karatu ba,and ni i dont care cos ni Abunda nake chasing daban yake da wanda suke chasing ,i want to build my self dan ni in ten years ina hangoni da company wanda nice na ƙirƙiresa,Thats how ambitious i am. Licking leben sa yayi yace "that sounds interesting ,well wani lokacin aje abokai barkatai ma matsala ne domin sai kiga wanda ka ɗauka naka na jikin ka Shine zai bada babbar gudunmawa wajen ganin ya lalata ka,amma a nawa bangaren what i have towards you is pure ,babu cuta babu cutarwa cos attimes idan na kalleki over hills kan Haidar sai naji a raina mai yasa bani na fara haɗuwa dake ba,cos i mean a fahimtar ki da nayi cikin ƙankanin lokaci na san you're a Good person,tsakanina dake was a bad encounter wadda ta b'ata mun rai sosai bazan boye miki ba,amma daga baya na fahimta you did it for Your sister no matter yarda zakiyi denying nasan you're a family person kuma baki da san kanki wanda yana ɗaya daga cikin abunda yasa naji bai kamata na zama bad guy ba akan ki,i wont lie na fara jin ki a raina ina mai ji dama Nine Haidar ,but idan na kalli yanayin ta wani bangaren sai na bawa kaina haƙuri cos idan ina san na zama right hand buddy ɗinki i have to be like a brother figure,yarda zan so wa Amatul'islam abu mai kyau haka zan so miki and Haidar mutumin kirki ne wanda nasan zai riƙeki da amana fiye da ko wanne ɗa namiji a duniya so Chill girl,komene Kike so a rayuwa Ina san ki sani ina gefenki,Just talk ni kuma zan supporting ɗinki da dukkan karfina i promise,duk damuwar ki zan ɗauke ta tawa,i will be a Good listener indai zaki faɗa mun damuwar ki. Bata san tana hawaye ba sai da ya ɗiga kan hannun ta,saurin goge wa tayi tana mai yin ƴar dariya kafun tace"you're getting me emotional,nagode sosai,naji daɗi da baka yi complicating abu tsakanina da Kai ba,and naji daɗi da kamun alkwarin Kasancewa a gefena duk lokacin da na buƙace hakan,naji daɗin babu abunda zance maka sai dai nace Allah ya saka maka da Aljanna ya baka mace ta gari and By the way wace Amatul'islam?" Shafa kansa yayi yace "nasan yanzu nan kina tunanin girlfriend or something ,well im sorry to disappoint you,Amatul'islam sister na ce,shes 19 and yanzu haka tana cyprus' university final year and shes kind of Tough But nice She's low key dan bana tunanin akwai wanda ya taba ganin ta face to face a company ɗin nan sha tana nan dawowa soon " Ɗan murmushi Tayi tace "and abun mamaki chairman bai taba mun maganar ta ba,bazan manta mata wannan side ɗin labarin ba cos duk labarin sa akan Saleek ɗin sa ne,tho nasan yana da daughter But ban san sunanta ba,sunanta mai daɗi"kallan time tayi tace"well oga Sir aiki muka zo kar anjima kagama hirar nan dani ka aiko mun da sacking letter"murmushi yayi yace "well idan zan sacking ɗinki to tare zamu tafi,mu haɗu lunch time and bills on you". Dariya kawai tayi masa tana mai kaɗa kai har ya fita yana maimaita mata,bills on you 'fa.koda ya Fita Kai tsaye office ɗinsa ya nufa yana mai jin wani irin nauyi a ƙirjinsa musamman da maganar Auren Kiswa ta ringa dawo masa kamar fitina,zama yayi ya dafe kansa yana mai ambaton Allah,yana wannan yanayin Khalipha ya shigo,ƙokarin saita kansa yayi amma Khalipha ya riga ya gano ,zama Khalipa yayi yace "mutumina menene damuwar ni Nasan Ƙwana biyun nan akwai abunda yake damun ka man talk to me kasan ni da Kai muke sharing damuwar mu kuma kaga mun samawar wa kan mu masalaha,kamun magana mene ke damun ka. Ajiyar zuciya Ya sauke yace"Khalipa na gaji da boye maka saboda bazan iya cigaba da boyewa ba,ban san yaushe ya fara ba ban kuma san ya akayi haka ya faru ba,abu guda ɗaya na sani wanda Shine "im madly In love with Kiswa and i cant help it". Cike da confusion Khalipa yace"wace Kiswa ɗin ?kar dai kace mun babe ɗina?" Tsaki Saleek yayi yace"abunda yafi babe ɗinka bana san iskanci ina maka maganar da bata wasa ba kana mai da ta wasa,kana tunanin nasan wata Kiswa ne bayan ita?".ɗaga hannu Khalipa yayi yace "naji my buddy is In love,so mene kake jira,Fine boy like you wanda yan mata kewa zarya,ka faɗa mata mana nasan dai bazata rasa sanka ba cos i mean ka kalleka mana". "Nan matsalar take my guy,ina mutuƙar san Babe ɗin nan amma ina yi mata san da bazan so kaina ba domin shi ba domin maganar da nake maka yanzu haka maganar Aurenta ake sannan yaran da zata Aura mutuwar sanshi take ,babu abunda wani Zaice ta rabu dashi,and i respect that saboda bangaren sa ma haka take,ni dai Just pray for me Allah ya yaye mun cos bazan so ace nan gaba ina san matar Aure ba ,domin kuwa ina san na zama kamar ɗan uwa a gareka domin idan na kalli cikin idon ta yana faɗa mun wani saƙo daban bayan wanda take nunawa a zahiri,i can feel it that tana zagaye da maƙiyanta kawai bata san magana akai ne".Saleek ya faɗa yana mai jin wani irin nauyi a ƙirjinsa. Tasowa Khalipa yayi ya dawo inda yake ya zauna kan desk ɗinsa ya dafasa yace"mutumina this is deep amma kasan shawarar da zan baka cikin wannan tafiyar? Ba komai bace face ka fara dating,Just Try Elham yarinyar nan tana sanka tana binka ,tana da kyau ga kuɗi ga aji malam,ni zan iya cewa tafi Kiswa ma. Wani wawan tsaki Saleek yaja yace"wannan fiƙaƙƙiyar yarinyar ce tafi Kiswa?"you're mad,ka kalli Kiswa da kyau ,black beauty ga aji ga nutsuwa ga sanin ya kamata,amma Elham 'fa kasan idan magana ake ta tarbiyya bata da ita ko kaɗan,tayi ta wani tab'a mutum da sunan relationship abeg Who does that,yarinya mai nutsuwa da kamun Kai bazatayi abunda Elham take yi ba. "Naji naji SBM amma ka sani Elham na maka soyayyar da zaka iya juyata zuwa yarda kake so,amma kaje kayi tunani,yanzu dai bari naje nayi aikin gabana kafun ka fara maganar kora ta". Dariya Saleek ya saka yana mai bin Khalipa da kallo yana wata tafiya da rangwaɗa,juya maganar Khalipa ya ringa yi akan sa yana tunanin iyuwar hakan dan Elham bad news ce . *********** Zaune Farry take a office ɗin Haidar tana sipping coffee tana jiran ya gama ganin patient tukunna,wurin awarta guda a zaune tana jiran sa dan coffee ɗin da take sha Cup na biyu kenan,ta riga ta saka a ranta bazata bar office ɗin sa ba yau sai ta gansa,tana wannan zaman Ya shigo fuskarsa cike da kulawa yace"im sorry Farry na barki ke ɗaya anan wallahi patients ne sai godiyar Allah yau ɗin,and its Like a charity thing muke yi yau dole ni zan duba su a basu magani,But i will make it up for you". Murmushi tayi tace"how will you make it up for me?ko ni zan zab'a cos ina buƙatar abu a gurinka".zama yayi yace "Uhum ina saurarenkii,ki faɗa ko mene zan miki indai zan iya"gyara zaman ta tayi tace"zaka iya ma dan ba abune wanda yafi ƙarfin ka ba,nasan kasan maganar da Mother sukayi da ummi akan mu Sannan Nasan dan bakaji ta bakina bane amma Haidar ina san ka sani nice na dace da Kai ba Kiswa ba,zan so ka fiye da Yarda Kiswa zata so ka,aso mene ma take maka bayan kuna tare ma tayi samari biyar,yanzu ma ana maganar Auren ku soyayya take da Saleek yaran chairman ɗin company ɗinsu, kalleni da kyau Haidar ni ce na dace da Kai ba Kiswa ba,kasan dai nice nake zaune da ita gida ɗaya, i know her best ,babu wani abu da zata ƙareka dashi amma ni fa?nike kula da dukkan wani aiki a kamfanin Alijua,karfin signature yana hannuna,bazan maka bani bani ba saboda im loaded amma Kiswa fa?shes Just a rat hiding behind Ayzel foundation nothing more,babu wani abu da Kiswa zata tsinana maka dashi sai dai ta zamar maka liability,please Haidar marry me. " Idan da wani zai zaunar da Haidar ya faɗa masa wai Farry ke zaune gaban sa tana faɗa masa waɗannan maganganun sai ya ƙaryata,Kallanta yayi still mamaki yaƙi sakin sa yace"da ace mafarki nake na wannan scenario ɗin tsakanina dake zan ta addua ne na farka nayi Kuma fatan ban maimaita ba,wallahi Faridha im very disappointment In you,Kin bani kunya fiye da yarda bana tunani,wallahi Faridha ke ba yar uwa bace ta gari domin da ace ke yar uwace ta arziki bazaki taba zuwa mun da wannan maganar ba bayan kinsan da ace Kiswa ce a matsayin ki bazata tab'a yi miki abunda kike ƙoƙarin yi mata ba amma ina san ki san wani abu,Kiswa bazataji wannan maganar ba saboda ban san yardarta ta ƙare,abu guda ɗaya kuma da nake so ki sani Shine Allah kaɗai zai iya raba tsakanin da Kiswa ba mutum ba,ina kuma so ki sani idan ni dake muka kasance a duniya bazan taba Aurenki ba na miki alkwari,abu guda ɗaya yasa bazan faɗa miki magana mara daɗi ba wanda Shine Kiswa,bazan so a ce wanda suka haɗa jini dashi ba ya ji maganaa mara daɗi daga bakina ,hakan kamar na zagi soyayyata ne ,ki tashi ki fita mun a office kuma kar na sake ganin ƙafarki a inda nake . " Sosai zuciyar Faridha take mata tafasa kamar zata ƙone,tashi tayi ta ɗauki hand bag ɗinta da wayarta ta nuna sa da hannu tace"Kai nawa ne Haidar ,tunda na saka idona da zuciyata kuwa akanka babu abunda zai hanani samun ka musmman da kowa ke nuna mun bazan samu ba,kajira zuwana"binta yayi da kallo har ta fice a office ɗin tana maiyyin wata irin tafiya kamar zata karye,tausayin Halin da Kiswa zata tsinci kanta muddin ta samu wannan labarin yaji,he cant blv tana undergoing irin wannan trial ɗin, dan koda bata faɗa masa ba yasan tunda aka fara maganar su tana fuskantar ƙalubale wanda yake sakashi jin dama a dai dai lokacin ta zama matar sa ya ɗauketa daga dukkan wani yanayi mara daɗi na rayuwa ,wayar sa ya ciro sanin a dai dai lokacin tana aiki ya tura mata text na"i love you and i will forever do". Murmushi yayi lokacin da yaga ta maido masa babu bata lokaci da"i love you back Baby,no one But you".idan yace bai san Kiswa fiye da kansa to tabbas babbar Ƙarya yayi,domin kuwa yarda yake jinta a zuciyarsa abune da idan yafara faɗa za'ace yayi shiru haka nan,fatansa guda ɗayane wanda Shine kar ya mutu bai mayar da ita matar sa ba ,koda kuwa ana ɗaura musu Aure Allah ya ɗauki ransa ya gode masa domin kuwa ya biya masa buƙatarsa na mayar da ita matarsa and babu wani mahaluƙi da ya isa ya chanza iyuwar hakan. ________kamar yarda Appa Ya bukaci ganawa da Mahaifin Haidar hakkan ne ya kasance domin kuwa washe garin ranar suka zo dan ayi maganar ,kawun ta Halilu da taso a saka a ciki surprise Appa ya bata dan kuwa jirgi ya biya masa yazo Abuja,zama ɗaya sukayi Aka saka Aure watan da zai kama,Kawu Halilu yaso a ɗaura a ranar dan acewarsa mene amfanin jinkinrin tunda sun riga sun fuskanci junansu,Appa ne ya bada shawara akan a bari zuwa watan dai a ganinsa zaifi dan haka suka samu masalaha da juna aka tsayar da magana guda,a ranar idan ka kalli Haidar da Kiswa abun ba'a magana dan sun taka wani mataki ne na zama tare wanda lokaci ƙalilan ne ya rage su Kai matakin da suke mafarkin kaiwa a rayuwa. Tunda akayi maganar tsayar da ranar Kiswa da Haidar mutane uku suka shiga cikin mutuƙar tashin hankali,meeting suka zauna na musamman Farry na ta cin uban kuka,lallashinta kawai Mother take ita kanta ta rasa abunda yake mata daɗi,cikin kuka Farry tace"Mother ya ake so nayi?lokaci guda na nuna ga abunda nake so Amma Appa ya kulle ido zai bawa Kiswa bayan kuma Shine mutum na farko da yake fara faɗa mun na kasa samo miji nayi Aure ,yanzu kuma ga wanda nake so kuma. Idan da ace za'ayi adalci dani ya dace bada Kiswa ba,ba wai maganar san Kai ba,itace ta lalata blind date ɗin da Appa ya haɗa mun da Saleek and yanzu gashi tana tare da Saleek ɗin to tabar mun Haidar mana indai ba san Kai ba. Cike da wani irin yanayi Mother tace"kika ce mene?Kina nufin ita ta b'ata miki blind date Shine kikayi shiru baki faɗa mun ba?"cikin kuka Farry tace"wallahi Mother baki ga yarda ta b'atani agurin sa ba,a irin shigar da tayi kanta In dai namijin kirikine yana ganinka zai fasa Auren ka sannan maganganun da ta faɗa masa kansu bazan iya maimaitawa ba". Tashi Mother tayi tana mai cewa"jar bura ubancan,ai kuwa wallahi bazata sab'u ba,taci ƙarya ta tarwatsa miki farin cikin ki ita ta samu,wallahi idan a tafe take ni Chan na ƙwana bari naje na samu Appan naku". Cike da fitina Mother ta nufi ɗakin Appa,Kai tsaye ta faɗa tana mai cewa"wallahi an daɗe ana ruwa ƙasa na shanye wa,wannan karan kuma ta gaji,billahillazi idan baka ɗauki mataki ba ni zan ɗauka da kaina". Appa dake zaune yana danna wayarsa ne ya ɗago ya kalleta yace"wai ke a rayuwar ki ba ki san a zauna lafiya ne?tunda aka fara maganar Auren Kiswa kullum Kina da damuwa ,a yanzu mene damuwarki mata?" "Nice nake da damuwa ma kuwa,ai a idanunka Kiswa bata laifi to a yanzu bazan taba yarda ba sai an Ƙwatarwa Faridha yancinta ,wannan yarinyar Kiswa da kake gani muguwa ce wadda bata san cigaban wani,to date ɗin da Ka haɗawa Farry da yaron mai AYZEL FOUNDATION itace ta lalata domin ita taje maimakon Farry sannan bata tsaya nan ba sai da ta b'atawa Farry suna a gurin sa ,dama ni dai ince ta yaya namiji zai ƙi yarinya kamar Farry? " Aje wayar Appa yayi yana mai kallan Mother yace"daga ina kika samo wannan maganar kuma?" "Ka fito kaji ai Kiswa ɗin na gida itama haka Faridha ɗin babu wanda ya isa yayi ma wani ƙarya"fita tayi inda Appa baya da wani zab'i da ya wuce ya bita. Koda Mother ta fita Kai tsaye ɗakin Kiswa ta nufa wadda already ta kulle ta kwanta dan bata barin ɗakinta a buɗe tun haɗuwarta da Sagir,irin ƙwanƙwasawar da Mother take kamar tashin hankali Shine ya tashi kiswa daga ɗan baccin da ta fara,cikin muryar bacci tace "Wane?" "Uwarkii ce Zubaida "Mother ta bata amsa,hijab ɗin da tayi sallah dashi ta dauko ta saka kafun ta buɗe ƙofar,kamar tashin hankali haka Mother ta Jawo ta waje ta ɗauke ta da mari. Gafe guda Farry ce wadda taƙi daina kuka inda sagir ke gefenta yana bata haƙuri Appa kuma yana mai kamo Mother dake shirin yiwa Kiswa luguden masu,ihun da Mother take ne ya jawo hankali Sameer wanda already shima ya kwanta dan a lokacin ƙarfe Goma na dare.cike da mamakin halin da ya same su yace "lafiya ??" Cike da bala'i Mother tace" inafa lafiya,gata nan ka tambayeta mene tayiwa Farry,.ganin abun na neman wuce gona da irin ne ya saka Appa cewa "kowa ya sameni a falo na." Zaune baki ɗayan su suke Falon Appa inda Farry taƙi daina kuka,sameer ne kalleta yace"to ke idan baki daina kuka ba tayaya za asan mene matsalar har ayii maganinta,dama ai kuka alamune na mara gaskiya". Cikin bacin rai mother tace"ka kuma faɗa mata mara gaskiya kaga abunda zai faru sakarai mara kishin yan uwansa"saka bakin da Appa yayi ne ya saka kowa ya nutsu kafun ya saka Faridha ta fara bayanin abunda ya faru. *su hajiya Farry kuma da karyaa ake tunanin za'aci yaƙi,Allah ya kyauta, Shin zata ci wannan yaƙin ko kuwa A'a? Ko kun san mai yasa ake wa wannan littafin laƙani da Surrogacy was the cause? Ku cigaba da bibiyar littafin Kiswa domin jin yaya zata kasance. Mu haɗu a update na gama. TBC CHUCHUJAY ✍️ 08130229878 [5/27, 12:16 AM] Chuchujay✍️: 💥KISWA💥 (Surrogacy was the cause) Na Chuchujay Follow my whatsapp channel https://whatsapp.com/channel/0029VaRpQeUHwXb52H0abb05 Book1⃣ Page 1⃣6⃣ ____________Cike da mamaki Kiswa ke kallan yarda Farry ta gyara zama tana ƙwararo ƙarya harda faɗin ita ke korar mata duk wani saurayi da ke zuwa gurin ta ,bayan ta gama narrating labarin ta bangaren ta Appa ya kalli Kiswa yace"ina san naji daga naki bangaren Kiswa,shin da gaske ne ke kike korar mata samari ko a'a ,sannan wannan magana ta Saleek menene gaskiyar ta domin idan na kama ɗaya daga cikin ku da ƙarya tabbas zan sab'a masa fiye da tunani domin kuwa ba sunanku kaɗai kuka b'ata ba,kun haɗa baki ɗaya da nawa kun lalata wanda bazan lamunta ba". Goge hawayen dake fuskarta tayi ta mayar da Kallanta ga Appa tace"Appa magana da Farry tayi na ina korar mata samari ƙaryane domin ni banga menene ribata na son cutar da ita ba ko ganin taci baya,Allah shaida tane,sannan magana da take 'na Saleek bani da shaidar lokacin da abun ya faru tsakanina da ita amma abu guda ɗaya 'na sani wanda Shine Allah na tsakanin mu a lokacin,and ni abunda nayi was out of kindness for my sister domin Farry ta sameni a ranar ta kawo mun maganar date ɗin dan ban ma san da Saleek madugu bane domin bani da masaniyar a lokacin ma yaran ogan mu ne,tace naje a maimakonta saboda bazata iya handling abun da kanta ba ni zan iya saboda na taimaka mata lokacin da wani saurayinta na harrassing ɗin ta,koda ta mun maganar gata nan a zaune sai In taƙi Allah taƙi faɗar gaskiya da ƙyar na yarda dan sai da ta lissafa mun cewa yana shan giya,yana shan sigari,mazinaci ne,wanda babu wahala ya b'ata ka,sai da nace mata zan sameka da maganar But tayi blackmailing ɗina emotionally wanda dole babu yarda na iya haka nan na biye mata wanda na yarda Shine kuskure na,amma a nawa lissafin idan zata fita cikin haɗari hukuncin kuskuren bazai dameni ba alfahari na ɗaya na fitar da ƴar uwata daga mugun hali,sannan duk wani taimako da zanyiwa Faridha bata ƙasa a gwiwa wajen tura mun kuɗi ,cikin wannan satukan da muka fara samun matsala har maganar Saleek ta shiga ciki dan har ta sameshi a office ɗina su sasanta Amma yaƙi,ta faɗa mun akan duk abunda nayi mata a rayuwa ai tana biyana ne ni kuma na maayar mata da duk wani kudi da ta bani akan abun Alheri da nayi mata kimanin Naira miliyan biyu da rabi,ina da alert and im sure itama tana dashi,ban yarda naci kudin nan ba dan gani nake kamar zan cinye zumunci nane,Mother nasan baki sona sannan a yanayi na aikinki kinsan ba karya nake ba ,kiyi mun alƙalanci a matsayina na ƴar Adam ba matsayin Ƴar ƙanwar mijinki da kike ji kamar ki kashe ba. Tafi Mother ta saka tace"tabbas Kin girma Kiswa,''na yarda kinyi girman da zaki zauna ki tsara sharri har kike ƙoƙarin faɗa mun maganar banza,to bari kiji wallahi babu wani sharri da ban gani ba kuma ban sani ba"kallanta ta mayar ga Appa tace "kanaji ai ko?kanaji da kunenka ba sai na zauna na faɗa maka wacece kiswa ba,irin ƙaryar dake fita a bakinta kawai kasan zata kashe mutum,yanzu Kai Ina Farry yarinyar da Aka haifa jiya jiya zata aikata hakan?"kana kallo saboda tsabar kuka idanunta har sunyi jawur . Cike da rashin tsoro Kiswa tace"Mother nima na iya kuka fa dan zan zauna na rerashi koda kuwa banaji amma sanin ina da gaskiya ya saka ban zauna nayi ba sannan maganar nan da nake ba dan dare yayi ba da da na kira Shi Saleek d'in ya faɗa da bakinsa kamar yarda na faɗa muku,shima ai ya san komai kuma nayi imani da Allah itama tasan idan yazo itace zata ji kunya." "To yazo mana muga ƙarshen gaskiyar ki fitsarariya mara kunya,"Mother ta faɗa tana mai haƙiƙancewa . tashi Farry tayi tana mai rushewa da kuka ta ruga da gudu,Kaɗa Kai sameer yayi yace "kingani ko?"Kina gani kinsan bata da gaskiya,maganace ta fatar baki sai a zauna ayi menene na tashi tana kuka. Hayyayaƙo masa Mother tayi tana mai faɗin"wallahi akan wannan yarinyar Sai na baka mamakin da baza kayi zato ba,dan me kuma bazata tashi ba ta zauna tana gillo ƙarya kuna saurarenta shi shugaban baice komai ba." Murmushi Appa ya tsinci kansa da yi yace "juwairiyyah kenan,ke kikayi rainon cikin Faridha kika haifeta kike rainta ta girma a gabanki amman ni nafiki sanin abunda zatayi da wanda bazatayi ba,sannan magana da kike Kina wai yiwa sameer hargagi ai gaskiya ce ya faɗa sannan kamar yarda kiswa ta faɗa miki kiyi mata alƙalanci a matsayinki na wadda tasan shari'a ba wadda ta tsaneta to the core ba,wallahi shame on you Juwairiyyah ,shame on you,kunya kike bani sosai idan ina kallan irin wannan halayyar taki mara amfani wadda babu inda zata kaiki sai zauren dana sani,wallahi kisan abunda ke gabanki ki kiyayi kan ki,sannan ke kuma kiswa ba abunda nayi tsammani daga gareki ba Kenan,lokaci da ta nema kiyi mata wannan shashancin da Kin sameni Kai tsaye duk yarda zata biki tana miki daɗin baki,ban ji daɗin abunda kuka yi ba ". Ƙasa tayi da kanta cike da dana sani tace"nasan nayi kuskure Appa kayi hakuri insha Allahu hakan ba zai kuma faruwa ba". Murmushi Appa yayi yace"Allah yayi muku albarka "kafun ya tashi ya Shige ɗakin sa bai kuma cewa komai ba. Wata uwar ashar da Mother ta durguzo sai da ta bawa kowa tsoro ,tashi Kiswa tayi da sauri ta bar gurin yayin da sameer ya tashi shima yana mai faɗin "Allah ya kyauuta" Kallan Mother sagir yayi yace "mother kar ki damu ni nan zan miki maganin komai dake neman baki da Faridha Matsala ,ki tashi kije ki ƙwanta".tashi tayi tana mai jin zuciyar ta na yi mata zuga kala kala akan Kiswa . _____________Washe gari ya kama asabar,duk da yayin da Kiswa ta Ƙwana na rashin jin daɗi bata manta fitar da zatayi da Ummi ba ,bayan gama duk wani abu da zatayi tana ƙwance tana jiran kira Ummi kiran Haidar ya shigo mata,tana ɗagawa yace"Baby na zo ɗaukowa Ummi ke ,im outside". Gyalenta da jakarta da wayan ta kawai ta ɗauka ta fita dan zuwa gareshi,har ta ɗauki hanya zata fita ta juya ta nufi sashen mother dan sanar mata zata fita,a falo ta tarar da ita,sallama tayi ba tare da ta damu da rashin Amsawarta ba tace"mother dama zan wuce ne fitar da nace miki zamuyi da Ummi, to ta aiko a ɗaukeni shine nace bari nazo na faɗa miki kar ki jini shiru. Wani irin tsaki mother ta ja ta juyar da kanta ba tare da tace komai ba amma ji take kamar ta tashi tayi mata shegen duka Ko ta saka hannu ta shaƙeta Haka take ji ,amma tuggun da suka haɗa mata daren yau kawai ya isheta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Ganin mother ta cigaba da abunda take ya sakata juyawa dan fita tunda ai ta sauke nata nauyin na sanar mata zata fita ,tana ƙoƙarin fita taci karo da Farry wadda taja wani dogon tsaki ta bangaje ta ta shiga ciki tana mai faɗin"uwata abun alfaharina barka da hutawa ".juyawa Kiswa Batayi ba ta fita a ɗakin. Zama Farry tayi kan kujerar da mother take tace"mother kince na kwantar da hankalina zakiyi maganin kiswa yau mene akwai a ƙasa?murmushi mother tayi tace "Abun bana faɗa bane yanzu amma ki ƙwantar da hankalinki gobe da safe idan Allah ya kaimu zaki karya da labari mai daɗi domin kuwa za'a fasa Auren Haidar da Kiswa." Ajiyar zuciya Farry tayi tana mai jin kamar ta zuƙo gobe duk da kuwa mother bata faɗa mata ga plan ɗin da ta shirya ba amma tasan koma mene farin cikinta zai fara kaɗawa gobe. Koda Kiswa ta fita Landcruiser prado ce ta fara yi mata sallama cikin compound ɗin gidansu wadda tasan ba ta gidan bace sannan bata san haidar da ita ba,sanin Shine ciki ya saka ta taka cike da tafiyarta da ke mutuƙar burge Haidar wanda yake daga cikin tinted motor ɗin sa yana kallo,kafun ta ƙaraso ya fito ya buɗe mata motan fuskarsa cike da fara'a,murmushi tayi masa kafun ta shiga tana mai cewa "thank you"bayan ta shiga shima ya zagaya ya shiga nashi seat ɗin yana mai faɗin"you're welcome abar ƙauna,sannan kinyi mun kyawun da nake ji kamar kar kifita da Ummi instead ni na ɗaukeki mu tafi on a date kwana biyu bamu fita ba". Gyara zaman ta tayi ta juyo tana mai facing ɗin sa kafun tace "nima ina jin hakan a raina amma duk yarda nake san yin hakan Ummi first dan kasan yau idan nayi disappointing Ummi mun bani" Dariya yayi yana mai tashin motan yace "duk abunda kika ce haka za'ayi"Kashe mata ido guda yayi yana mai tashin motan ,hira suka ringa yi ta soyayya har suka isa "QUEENS PARLOUR "guri mai kyau ya samu ya faka motarsa ya maido da kallansa gareta yace"ko dai nazo na rakaki ciki?"tana ƙokarin bashi Amsa wayarta ta hau ruri ɗauke da sunan Saleek a jiki,idanun Haidar akan wayar tata kafun ya mayar kanta yana mai Kallanta,ita ma ɗin shi take kallo kafun ta mayar da idanunta kan wayar Har ta yanke bata ɗauka ba sai da ya sake kira ya kalleta yace "ki ɗauka mana"murmushi tayi masa kafun ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta tana mai faɗin"Hello sir" Daga ɗayan bangaren Saleek dake ƙwance kan makeken gadon sa yace "Sir ?,girl kar ki manta its weekend a wajen office muke and da friend ɗinki Saleek kike magana ba Sir ba,so are you free,i want to take you out for a frndly date".kallan Haidar tayi wanda Shima ita yake kallo,murmushi tayi tace "well zanyi disappointing ɗinka domin yanzu haka ina tare da Haidar ya kawo ni gurin Ummi cos muna da appointment " Sauke ajiyar zuciya na disappointment yayi yace "well have a nice day sai munyi magana ,and send my regards". Bayan ta kashe wayar ta kalli Haidar wanda ya ɗauke kansa yana mai kallan gefe,"babe shall we"?ba tare da ya juyo ba yace "you shall"a yanayin da yayi maganar ya tabbatar mata da cewa wani abun ba dai dai ba,gabanta taji ya faɗi cos tabbas fushi yayi da ita wanda bata san akan mene ba, Babe?ta faɗa tana mai saka fuskar damuwa,juyowa yayi yace"Haidar ,Just call me Haidar tunda Yanzu ai abunda kika kirani kenan tunda baki san asan wanene ni a gurin ki,and this Saleek of a guy dama ni already i hate his guts"he is asking you out ko?zaki iya cancelling appointment ɗin Ummi kije ai,dama ai i was warned akan sa ,i was told kuna soyayya. Shiru tayi tana kallansa domin abunda take gani na kishi a idanunsa bata taba gani ba,bangare guda kuwa maganarshi ta karshe ce ta dake ta na cewa wai dama an gargaɗesa sannan he was told suna soyayya,bata ce masa komai ba ta buɗe motar ta fita,kai tsaye ta shiga QUEENS PARLOUR ɗin bayan ta nuna ID ɗin da Ummi ta tura mata ranta yana mata babu daɗi sosai . Koda Kiswa ta fita a motar dafe fuskarsa yayi yana mai dana sanin abunda ya furta,bai so ya dawo da maganar Farry ba amma tunani da yake Shine guy ɗin da suka haɗu dashi a company ɗin su ya saka zuciya ta jashi ya faɗin abunda ya faɗa,sanin bazata tsaya ba ya saka baiyi yunƙarin binta ba amma shi kansa yasan ya taro match ɗin da baida players'. Koda Kiswa ta shiga a VIP tayi locating mother da ƙawayenta yan trillion dollars club ko waccensu ta manyanta amma sun gagara yarda da hakan,koda ta isa gurin Ummi kamar ta mayar da ita ciki,kamar yarda ko wannensu ke ɗauke da bathrobe hakan nan Itama taje ta chanza bisa umarnin Ummi,haka nan take finding abun weird ita kaɗai cikin iyayenta da sunan sunzo beauty parlour ,kafun kace mene ya faru Ummi ta fara bragging da Kiswa,mutum ɗaya da Kiswa ta kula ba wani shiri suke da Ummi bace tace"nayi zatan zanganta kamar tsada saboda haske"ƙarasa maganar tayi tana mai tab'e baki yayin da Ummi tayi ƙaramun murmushi tace"well idan kika kalleta da kyau ba sai an faɗa miki tafi sirikanki ɗin nan guda uku ba kar ma ace matar babban yaranki abun sai godiyar Allah,kamar da daddare suka haɗu amma kinga Kiswa kuwa,She's a spec ,real definition of melanin,Black beauty,hanci har baka,ga class,Ga hutu sannan gata san kowa ƙin wanda ya rasa"kamar jira yan koran bayanta suka cigaba da ƙoda Kiswa wadda take jin kamar ta tashi ta gudu,haka nan Aka masu massage sannan ,then gyaran da yake necessary,a wannan zaman Kiswa ta fahimci Ummi ce biggest influencer a gurin,idan da za'a tambayeta zata ce wannan Group ɗin is not healthy,dan toxicity ɗin dake cikin sa is In another level,kasan cewar Ummi mai kuɗin ciki sai abunda tace koda baiyyi sitting da sauran ba,saboda wani ƙwaɗayi sai kaga sun mata mubaya'a a bayan idanunta kuma su zageta. haka nan bayan sun gama Ummi ta dauke ta zuwa ɗaya daga cikin Boutique ɗinta tayi maa shopping na gani na faɗa duk kuwa yarda Kiswa ke nuna ta bari hakan amma kamar tana sake zugata dan a cewarta wadda haidar yake so ta wuce hakan a gurin ta. Har ƙofar gida Aka mayar da ita bayan dinner cos yawo sosai Ummi tayi da ita kafun sukaje 5star sukaci abinci,it was kind of hella girls out ,kamar yarda Ummi take faɗa girls out amma a gurin Kiswa it was hell,koda ta shiga gida ya sameer ta tarar a Falon farko yana sintiri,tana shiga da ledoji niƙi niƙi ya kafe ta da ido yace"daga ina kike Kiswa karfe takwas na dare?" Ɗan murmushi Tayi tace "yaya ina tare da Ummin Haidar ne"ɗaga Kai yayi ya kalli agogon dake Falon yace"amma dai sense is common mene ya saka baza ki faɗa mata dare yayi ki dawo gida haka nan ba,Eh iyayen wanda zaki Aura ne amma a matsayin tarbiyya bai kamata ki bisu kuyi wannan daren da kikaje kikayi ba,you got me worried musamman da na tambayi Mother tace mun bata san ina kikaje ba,koda mene ke tsakaninku Atleast idan zaki fita ki sanar mata ko kuma ni ki sanar dani." Batayi mamakin cewa mother tace bata san inda taje ba,rashin san ta ƙaryata mahaifiyarsa a gaban sa ya saka ta kama kunnuwanta guda biyu tayi narai narai da ido tace"kayi haƙuri yaya samir insha Allahu bazaka kuma samuna da laifi kamar wannan ba,kayi kun hakuri nayi kuskure ". Ganin yarda ta marairaice kamar zatayi kuka ne ya saka shi ɗan ƙaramun murmushi yace"ya isa ni kar kiyi mun kuka amma ina so wannan ya zama na karshe,sannan ba domin na takura miki bane ina dubawa ne saboda ke,"kallan ledojin hannun yayi yace "kawo nan na taimaka miki dasu"babu musu ta bashi tana mai binsa a baya tanaji a ranta kamar shine ya rage mata bayan Appa a gidan sannan tana fatan hakan kar ya zama hasashe. Koda ya aje mata sallama yayi mata yana mai sake sanar da ita ta kiyaye. Bayan ya wuce ta fara duba kayan tana ji a ranta sunyi tsada da yawa sannan sunyi yawa ,amma hannayenta a ɗaure suke dan muddin tana san zama da Ummi lafiya wajibine tayi shiru,zubasu tayi kan couch da zummar idan ta kintsa ta kaisu closet,key ta sakawa ɗakinta kafun ta rage kayan jikinta ta ɗauko bathrobe ɗinta daga Cikin kayan wankin ta da aka kawo ta saka, Kai tsaye bayi ta nufa dan wankan take so kawai taji tayi ,tana ƙokarin buɗe kofar taga ta buɗe kamar tsafi,Yaya sagir ne ya bayyana daga cikin bathroom ɗin yana mai faɗin"tadaaa,Good evening delicious". Topa. Bakina da goro. TBC Muhaɗu gobe idan Allah ya kaimu dan jin ya zata kaya. Nice taku CHUCHUJAY🥱 08130229878 Message me kofar amsar ƙorafi a buɗe takee❤ [5/29, 10:04 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Chuchujay ✍️ Book1⃣ Page1⃣7⃣ _________Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyar ce ta musamman da ta kulla da yarda yake babu kaya jikin sa a yayin da down there gabansa was hard,ja da baya ta farayi yayin da yake Takowa hannun sa da ɗan karamin towel ɗinta yana goge kansa . Wani irin murmushin mugunta ke ɗauke a fuskar sa cigaba da Takowa yayi yana mai faɗin"im glad Kin kulle mana ɗakin,and na dawo ne daga aiki so i kinda stink and ina san yau mu biya bashin dake kan mu ,shi yasa ban wani b'ata lokaci ba na shigo nan straight nayi wanka kinga kin shigo a dai dai ina gamawa dan haka ya kamata mu tafi kan business direct dan Wallahi yau Kiswa sai na samu abunda nake so a gurinki koda kuwa da ƙarfine,domin masu cetan naki basa nan,Appa yayi tafiya,shi kuma wanca mai kankanbar shi yayanki ne nasan yanzu haka yana Chan ya baje kan gado dan maganin baccin da yaci a abinci nasan ya Fara aiki" Babu abunda take karantowa a zuciyarta sai"lailah'ailla anta subhanaka inni kuntu minza'zzalimin"tayi yafi ba adadi dan tasan Allah kaɗai zai ƙwaceta hannunsa musamman da hasashenta ya bata cewa haɗakar ba tashi bace shi kaɗai har da Mother da Farry,baya ta cigaba da ja har sai da takai ƙarshen bangon kusa da bed side drawer ɗinta yayin da ya mara mata baya yayi mata cage da jikinsa,rufe idanunta tayi tsam lokaci da taji hannu sa a wuyanta yana shafawa ,rumtse idanunta tayi sosai hawaye na fitowa ta cikinsu kafun tace"Yaya sagir kaji tsoran Allah,duk wani abu da kake tunanin zakayi mun yanzu Allah yana kallanka kuma bazai barka ba domin zalunci ne ,ba zai tashi tambayar ka ba sai lokacin da ka manta ka sakankance , ka tausaya mun ko dan maraicina,babu abunda nake binka dashi a rayuwa sai alheri,dan Allah kada ka bini da sharri". Dukan ginin gefenta yayi ya damƙe hannunsa cike da bacin rai yace"kar ki Fara faɗa mun wannan a wannan gejin da nake wanda bazan iya huƙuri dake ba,please Kiswa na roƙeki,kar ki bani wahala,kiyi mun wannan alfarmar ko dan yan uwantakar dake tsakanin mu,wallahi na miki alkwarin cikin satin nan zan Aureki, kinga babu wani tunani na zaki fuskanci wulaƙancin Namiji,after all Nine na sanki ƴa mace kuma zan riƙe miki sirrinki. Abubuwan da suka haɗar mata sun haɗo ne da ƙyama,takaici da baƙin ciki,yawun da ke mata ɗaci a bakinta ta tattaro ta watsa masa a fuska tana mai faɗin"Allah ya tsinewa Aurenka da rufun asirinka ,To hell with you ."da wani irin zafin yanayi ya ɗauketa da mari ya Fara ƙokarin cire bathrobe ɗin dake jikin ta,kuka take sosai tana ihu wanda yaci ace wani a gidan ya farka ya kawo mata ɗauki,kokawa suka fara inda take mayar masa da iyakacin ƙarfin ta,kamar ance ta kalli Kan bedside ɗinta lokacin da yake faman sunsuna mata wuyanta,fitilar kan bedside din ta ƙarfe idanunta suka sauka akai inda take wata idea ta faɗo mata,cikin zafin nama ta saka hannunta ta ɗauko ta buga masa akai,wata wahalaliyar ƙara ya saki ya ja baya dafe gurin yayi yaga jini,gadan gadan yayi kanta yana mai fadin"wallahi sai kinci ubanki,kafun ya ƙaraso ta sake ɗaga lantern ta saita gaban shi da ke jansa yayi iskanci da ita ta buga masa iya ƙarfinta,wata iriyar azababbar ihu ya saki wanda ya dau ƙuwa a gidan,gefe Kiswa ta tsaya tana kallan yarda ya riƙe gabansa yana ihu ga jini da take gani yana fita,ko kaɗan bata ji tausayin sa ba,cike da ƙarfin hali ta ɗauki wayarta tana mai ƙokarin kiran layin Appa amma bata shiga,ƙarar ƙwankwasa ƙofarta ya saka ta rab'ewa ta buɗe jikinta na ƙyarma ƙaɗan kaɗan,mother ta shigo da saurin ta tana mai cewa "me kika yi masa ni juwairiyyah "kafun tace wani abu sai ga Farry ma tazo da gudun ta tana mai cewa "lafiya?"turus tayi lokacin da idanunta suka sauka kan sagir wanda ke faman ihu hannunsa bisa gabansa wanda ke faman jini,kafun kuma kace mene sai dif ya ɗauke a sume. Wani irin ihu Mother ta saka tana mai cewa ta kasheshi Faridha ta kashe mun ɗa maza ƙira sameer,cikin kuka Farry tace"mother Kin manta ɗazu ƙinyi drugging abincin sa ,babu abunda zamuyi ya farka a yanayin da yake bari na kira Mai gadi ya taimaka mu kaishi asibiti"fita Farry tayi da gudu yayin da mother ta taso kan Kiswa wadda babu dana sani ko tausayi a zuciyarta face mamaki tunda ai yaci ace ihunta ya kawo su amma basu zo ba sai da yayi nashi ,hakan ya tabbatar mata da cewa tare suke. Mari mother ta ɗauke ta dashi tana mai cewa"ke azzaluma ce,ke muguwa ce kiswa tuntuni na sani amma yau kika tabbatar mun,amma anzo ƙarshe ,kama hannunta tayi tace "zo ki bar gidan nan,wallahi sai Kin tafi,sannan idan Sagir ya mutu wallahi kema sai Kin mutu"hanunta ta fara ja zuwa hanyar waje ,tirjewa Kiswa ta fara ganin ko ɗan ƙwali babu akanta,cikin muryar rashin nadama tace "Mother ki bari na ɗauki mukullin motata sannan nasaka kaya mana,ki kalleni 'fa babu ko ɗan ƙwali kaina". "Wallahi tunda na jawoki ko babu kayane a jikinki sai kin bar gidan nan,sannan a duk inda kike ki shirya ƙarbar shammaci dan wallahi sai na kulleki"mother ta faɗa yayin da ta cigaba da jan Kiswa wadda a wannan gejin idanunta suka fara zubar hawaye sakamakon rashin imanin da Mother ke gwada mata. Koda suka isa bakin gate Mai gadi ma yana ƙokarin shiga ciki domin taimaka musu a fito da sagir a kaishi asibiti,buɗe ƙofar gate ɗin mother tayi ta watsa Kiswa wadda taji abun kamar a mafarki,kallan kanta tayi daga sama har ƙasa ,bathrobe ɗinta iya gwiwace sannan kanta Babu ɗan kwalli ,wanne hotel zata fara nufa a haka ?ita ba mai ƙawaye bace domin a rayuwarta Farry ta ɗauka ƙawarta yanzu kuma ga inda takaisu,Haidar ya faɗo mata,kallan kanta ta kumayi tayi saurin kaɗa kai,bazata taba bari ya ganta cikin yanayi irin wannan ba ,maƙiyinta ma bazata so taganshi haka ba,tana tsaye tana wannan jimamin ga waya dai a hannunta tarasa wanda zata kira,SALEEK?Shine mutum na farko da ya faɗo mata ,kira ɗaya tayi masa ya ɗaga,rasa abun cewa tayi kawai ta fashe masa da kuka,cike da tashin hankali yace"Kiswa lafiya?"cikin kuka tace "ina buƙatar taimakon ka idan zan samu please,zan kunna maka location kazo inda nake indai ban taƙura maka ba,and idan ba damuwa ka sama mun koda hijab ne. Cikin tashin hankali ya tashi daga kwancen da yake ya ɗauki mukullin motar sa yace"gani nan yanzun nan ,im coming."tana kashe wayan ta kunna masa location ta kuma gefe ta rab'e tana mai jin tsoro ganin yarda garin yayi shiru ga dare , dama koda rana unguwar na da ƙarancin Mutane,addu'a kawai take a zuciyarta Allah ya tsareta daga sharrin wajen da take,tana wannan tsayuwar Su mother suka fito inda Aka kulle gidan baki ɗaya gudun kar ta shiga,haka nan tana wannan tsayuwar Jiran Saleek motar sa ta danno gurin,wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana mai hamdala ,da mutuƙar damuwa ya fito a motansa hannunsa ɗauke da Hijab ɗin Maman shi cos Amatul'islam bata da hijab a gidan tunda bama ta gidan bai ɗaya,kafun ya fara tambayarta me ya faru hijab ɗin ya miƙa mata ya juya baya ,Bayan ta saka tace masa ta gama sai lokacinne ya juyo yana tambayar ta lafiya?mene yafaru? Mai kike yi a waje ?talk to me kiyi mun magana. Share hawayenta tayi tace"just take me out of here ,bana san na sake minti ɗaya anan i feel suffocated .bai sake cewa komai ba ya buɗe mata gaban motar sa ta shiga,key yayiwa motar bai tambayeta inda zai kaita ba ganin yarda take sheƙa kukan da sai a lokacin yadawo mata,tuƙi kawai yake bai san inda zashi ba,sai da tasha kukan ta mai isarta kafun tace"idan bazan takura maka ba ka kaini hotel mana zuwa safiya na saka a kawo mun jakana cos ina samun matsala da bank ɗina Ƙwana biyu gashi cards ɗina duka suna jakana." Bai ce mata komai ba ya ɗauki hanyar guest house ɗin su,tafiya ce mai ɗan tsayi dan har bacci ta samu ya fara ɗaukarta wanda tana farashi take farkawa,unguwace mara hayaniya kamar dai tasu wadda ke ɗauke da gidaje na gani na faɗa,horn yayi bakin gidan ,sai da yayi wajen sau huɗu kafun gate man ɗin ya fito dan ganin wanene domin baya tsammanin kowa ,ganin motar Saleek ya sakashi komawa da sauri dan buɗe masa gate. Yana shiga yayi fakin a gurin adana motoci kafun ya maida kalansa ga Kiswa wadda idanunta ke rufe,haka nan ya tsinci kansa da jin yana da gurbi mai muhimmaci a gare ta ,koda bata faɗa masa ba abun cikin gida ya fito da ita kuma ya tabbata abunnan ba mai daɗi bane,sannan kiran sa da tay ya nuna masa irin adadin yardar da ta bashi wadda ya ɗaukarwa kansa alƙawarin bazai bata damar yin dana sani na yardar da tayi masa ba. A hankali ta buɗe idanunta tana mai gyara zamanta da ta kula da ƙarfin halinta na baccin da tayi a motar sa,murmushi yayi ganin yarda take kallan window ɗinta dan tabbatar da inda take,cikin sigar kwantar mata da hankali yace"hajiya calm down ba sace ki nayi ba ,nan guest house ɗin Abba ne dake ALI AKILU estate,its safe sannan ki ƙwantar da hankalinki bazan taba cutar dake ba,naga da kije hotel gwanda ki zauna anan ɗin yafi,sannan ba ke kaɗaice cikin gidan ba akwai mai gadi da masu aiki mata uku,ɗaya na girki ɗaya na shara da wanke wanke,ɗaya kuma itace ogansu wadda ke kula da gidan baki ɗaya,suna gidanne kuma saboda yawan amfani da gida da nake domin Abba ma zan iya ce miki ya manta da gidan dan kulawarsa a hannuna take. Shiru tayi tana kallansa kafun ta buɗe bakinta tace"nagode Saleek bazan taba mantawa da abunda kayi mun ba yau ɗin nan".murmushi kawai yayi ya bude side ɗinsa ya fita kafun ya zagayo ya buɗe mata gefen ta. A baya take binsa suka shiga tamfatsetsan gidan yana maiyi mata jagora,duk da dare ne an rage haske gidan hakan bai hana kaga yanayin tsarin sa ba,staircase ɗin dake cikin falon suka haura inda ya buɗe wani ɗaki guda ya kalleta yace "bismillah". Babu musu tabi bayan sa bata jin wani ɗar zuciyarta domin kuwa tayiwa Saleek yardar da bai kamata ace tayi masa ba,amma a hakan nan zuciyarta bata dana sani da yardar da tayi masa ko kuma tunani na zai cutar da ita duk da kuwa hakan ta miƙawa ɗan uwanta Sagir amma ya nemi ya ƙeta mata haddi. Queen sized bed ne cikin ɗakin mai kyau wanda yasha farin bedding yayin da komai na ɗakin yake white and ash gwanin burgewa,juyowa yayi ya kalleta yace "kiyi amfani da ɗakin nan,Abba yayi sa domin Amatul'islam ne ,duk da kuwa bata ƙasa amma ya yarda yaran sa can be rebellious kinga kamar ni gidan nan Na mayar dashi gidan zuwa na dan nan na wuni dana kiraki ɗazu Kin fita ,so feel at home,kina jin yunwa ba? Bari naje na taso cook ta sama miki wani abun". Saurin taresa tayi ta hanyar cewa"im not hungry,bana jin yunwa ,sannan na gode sosai "shafa kansa yayi yace "godiyar nan ce bana so please ki daina yi mun,ina da damar nayi miki ne shiyasa nayi miki,ban san godiyar nan,ina ɗayan ɗakin dake jikin wannan Just Call me idan kina san wani abu". Kaɗa masa Kai tayi tana mai yi masa murmushi kafun ya juya ya fita shima yana maida mata fara'arta. Yana fita ta cire hijab ɗin jikinta ta cire ta ninke a gefe ta buɗe kofar da take tunanin bayi ne ta shiga domin watsa ruwa. *********** __B'angareen yaya sagir kuwa Kai tsaye suna zuwa asibitin da suke da insurance aka fara attempting masa ,babu abunda mother take sai kaiwa da komowa hankalinta a atashe musamman ganin yarda ɗanta ke bleeding sannan baya cikin hayyacin sa, Farry dake zaune itama cikin tashin hankalince ta kalli Mother tace "mother ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same shi amma Mother ni abunda nake san sani mai Yaya sagir yake a ɗakin Kiswa babu kaya? " Wani irin kallo Mother ta bata kafun tace"ke damuwar ki yana ɗakin Kiswa babu kaya ko?,kina tunanin a banza ne na miki alkwarin tashi da farin ciki yau?To ba komai yaje yi ɗakin ta ba,yana da buƙatar ta ni dake muna da buƙatar kaita ƙasa , wane opportunity' ne yafi wannan?amma da yake yarinyar nan sheɗaniyace shine ta nemi ta kasheshi" Shiru Farry tayi tana neman gasgata maganar Mother,ganin yanayin fuskarta ya saka Mother cewa"kada kice mun tausayinta kike?Bari kiji idan ma shi kike to ki daina,'dan wallahi idan baki kashe Kiswa ba zata kashe ki sannan duk abunda kika ga inayine domin farin cikin kine " Shiru Farry tayi tana sauraran mother yayin da wata zuciya ke faɗa mata hakan ba dai dai bane inda wata ke faɗa mata dai dai ne,ita a nata tunanin zasu koreta a gidan ne shiyasa koda tana jin ihun ta bata kawo komai ba,illa tunani Chan daban amma bata kawo fyaɗe ba tunda ba'a faɗa mata ba,shima wai yaya sagir. Suna wannan tsayuwar doctor ya fito yace ma mother ta sameshi a office, Koda taje bayani likitan ya fara mata kan ya zubar da jini da yawa ,ana buƙatar kara masa ,sannan yana buƙatar surgery saboda raunin da yaji a gabansa sosai ne ,amma a wannan lokacin su tsayar da jinin an saka masa ruwa da alluran da zasu taimaka masa wajen farfadowa ,sauran bayani kuma sai babban likita yazo da safe amma a yanzu dai babu wani abu da zasu iya cewa bayan he is out of danger. Hawaye kawai mother take tana Adduar kar abun ya haifa masa matsala,idan kuwa ya samu complications To tabbas ita zata zama ajalin Kiswa wannan alƙawari ne ta ɗaukawa kanta. 08130229878 CHUCHUJAY✍️ [5/31, 7:29 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) CHUCHUJAY✍️ Book1⃣ Page1⃣8⃣ __________Bayan rabuwar Haidar da Kiswa ba ƙaramun damuwa ya shiga ba domin maganar da yayi da yanayin da ta bar motarsa yasan cewa abun bata ɗaukesa ƙarami ba,bayan dawowar Ummi kamar yana jira ya tareta yana mai faɗin"Ummi Kiswa fa"? Kallan sa tayi tana mai murmushi tace "baka tunanin san Kiswa yayi yawa a gurinka wanda yake san zama ba lafiya ba,kasan dai ba zan siyar da ita ba dan haka na kai ta gida and fita da ita was fun dan tun yanzu na fara tunanin fixing mana wani date cos ina faɗa maka ina kallan idanun hajiya Aziza kishi na ne ƙarara a fuskarta". Yar dariya Haidar yayi yace "Ummi namu,well im glad kinji daɗin fita da ita and ina fatan itama bata damu ba" Takawa Ummi take dan shiga sashenta yana biye da ita a baya tace"idan ma da damuwa zata saba ne". Bayan ya raka mother ya koma ɗakin sa 'ya dauko wayarsa ya ƙurawa numbernta ido kamar ya kira amma yana tsoro,sanin sab'ani irin hakan bai saba faruwa tsakanin su ba ya saka ya yanke shawarar barinta ta huce zuwa safe yaje har gida ya sameta,a hakan nan yayi bacci duk da jikin sa yana basa wani irin yanayi dangane da ita amma sai ya bar hakan kan tana cikin damuwar maganar da ya faɗa mata ,haka nan ya lallashi zuciyarsa yayi bacci da niyyar washe gari da safe zaije ya sameta,ille kuwa tun asuba ya fara kiran layin ta amma baya samu,Har Allah Allah yake gari yayi haske ya tafi gidansu,duk yarda Ummi tayi dashi ya ƙarya ƙiyayi sai ce mata yayi yana da abu mai muhimmaci ne a asibiti amma zai ci abinci a waje. Koda ya isa gidan cigaba yayi da kiranta amma still a kashe,fitowa yayi a motan ya isa bakin gidan ya ƙwanƙwasa ƙofa,sai da ya buga sau uku kafun mai gadin gidan ya buɗe,yana ganin Haidar ya dashe baki dan yana yi masa alheri sosai,cike da girmamawa suka gaisa kafun haidar Ya nemi da yayi masa isoo gurin Kiswa,kamar kuwa yana jira ya tambayesa yace"aikuwa ranka shi daɗe hajiya Kiswa bata gida,dan In taƙaice maka jiya ba gidan nan ta Ƙwana ba. Cike da damuwa Haidar yace"To fatan lafiya dai ko,sannan ina taje dan bana samun wayarta". Ajiyar zuciya mai gadi yayi yace"bazan boye maka ba yallabai jiya dai gidan nan Babu daɗi domin kuwa hajiya Babba korar kare tayiwa hajiya kiswa dan isasshen kaya ma babu jikinta a lokaci ga dare,sannan a tawa fahimtar duba da yarda muka ɗauko yallabai Sagir tsindir babu kaya daga ɗakinta yana ta ambaliyar jini ina kyautata zatan yaje mata da lalatane ita kuma ta ƙwaci kanta ta hanyar yi masa rauni,yanzu haka ma yana asibiti ita kuma Hajiya Kiswa Allah kaɗai yasan inda take dan kaga Chan ga motarta cikin gida ko ita ba'a bari ta ɗauka ba dan rashin imani,Ga dare,ga Yallabai mai gida baya gari ,yallabai sameer kuma Bansan mai ya faru ba dan duk abunnan da ake bai fito ba har mukaje asibiti to sai da safen nan shima nake bashi labari da ya tambayi hajiya Kiswa". Wani irin yanayi na jirine ya ziyarci Haidar yayin da wani irin tsoro da fargaba da bai tab'a ji ba suka ziyarce sa,Hailala kawai yake iya furtawa ,juyawa yayi bai kuma cewa da Baba mai gadi komai ba ya shiga motarsa yayi mata key ,idan da zaka tambayeshi inda zaije shi kansa bai sani ba,dumin da yaji na bin hawayen sa shi ya tabbatar masa da hawaye yake ,shi mutum ne mai rauni indai akan abunda ya shafi Kiswa ne,magana ake fa ta fyaɗe sannan bama asan inda take ba duba da korar da akayi mata cikin dare ,tsoron sa kar ace tana hannun banza duba da yarda baya samun wayarta,Kai tsaye gida ya wuce bayan ya gama lalabansa cikin duhu,yana isa gida ya fara ƙwalawa Ummi kira wadda ta fito a kiɗime kanta ko ɗankwali babu,cikin tashin hankalin ganin sa yana kuka ya saka ta zuwa gareshi tana faɗin"Haidar lafiya?Wane ya mutu". Faɗawa yayi jikinta kamar ƙaramin yaro ya fashe da kuka yana cewa"Ummi gwanda ma ace mutuwa mutum yayi da abunda ke faruwa". "Mene kenan yake faruwa my Son,lafiya haka?"Alhaji Tukur Bula ya faɗa yana mai saukowa daga sama jin kukan ɗan nasa, Haka nan Tasleem ma wadda ganin yana kuka itama ta fashe da kukan domin sosai zuciyarta ta karaya ganin Haidar na kuka. Kamosa Ummi wadda itama idanunta ya ciko da ƙwalla tayi tace"oya zauna ka samu nutsuwa tukunna,Tasleem maza kawo masa ruwa". Zaunawa yayi Mahaifin sa ma ya zauna Gefen sa yana san yaji abunda ya saka jarumin ɗan sa kuka haka,Yasan abunda zai saka Haidar kuka ba ƙarami bane,.ruwan da Tasleem ta kawo ya ƙarb'a yayi sipping kaɗan kafun yace"Ummi,Baba Kiswa ta b'ata,babu wanda yasan inda take dan family ɗinta ma basu damu ba dan sune suka koreta cikin dare babu koda suturar kirki,gashi ina kiranta wayarta a kashe,I'm doom dan wallahi idan wani abu ya sameta ban san yaya zanyi surviving ba". Cike da mamaki Baba yace "Abunda ban gane ba,mai yasa zasu koreta cikin dare babu wani dalili?""Uhum nima abunda nake san sani kenan ,babu yarda za'ayi su koreta babu dalili".Ummi ta faɗa tana mai shafa kan Haidar. Kamar yarda mai gadi ya basa labari shima haka ya labartawa musu,salati Ummi ta saka yayin da Baba yayi shiru cike da mamakin inhumanity irin na Mother ,Kallan matar sa da tayi narai naraii da ido yayi yace"Madam ku ƙwantar da hankalin ku,za'a ganta,yanzu zanje na samu IG za'a ganta ne ,im sure tana guri mai kyau".cike da karaya tace"my dear ina zan kwantar da hankalina Na Haidar ba a kwance ba,ka kalli fa yarda yake kuka kamar ƙaramin yaro",dan Allah kayi wani abu a gano inda take i cant stand this,ana ganin ta kuma a ɗaura musu Aure gwara idan tana ƙarƙashin kulawarsa hankalin mu zai fi kwanciya. Haidar yaso yabi mahaifin nasa amma Ummi ta hana dan haka yayi mata karyar zaije ɗaki ya zaga da taimakon Tasleem ya fita dan bazai iya zama gida ya nannaɗe hannu ba baiyyi wani abu ba dole yaje nemanta shima. ************** _______yarda Mother ta cukumi wuyan Doctor Ben abune wanda kana kalla kasan magana ce ya faɗa mata mara daɗi musamman da ya kasance tana kuka tana mai ce masa ƙarya yake sakamakon da ya faɗa dangane da Sagir, Samir dake ta faman ƙokarin rabata da Doctor ɗin ne Yace"Mother mana please control Your self ,mu godewa Allah abun ma a haka ya tsaya bai yi gaba ba ,dan ai we learnt from our mistake,shi nashi ƙadarar kenan,gobe zai kiyaye". Kuka ta fashe dashi sosai tana mai cewa"yanzu sameer kana nufin ƙaddarar Sagir kenan bazai ga jinin sa ba,to mene yayi zafi haka,wallahi bazan yarda ba,sai na kashe Kiswa da hannuna zanji daɗi." Zage Zage take ɗugunzumawa Sameer na Kamota har suka fito daga ofishin likitaan,kukan suka tarar da Farry nayi gefen gadon Sagir wanda ya ɗan samu bacci,kamar wata kamun hauka Mother taje ta zauna gaban sa ta kama hannun sa tace"indai nice na haifeka Sagir ,yarda Kiswa ta ƙwace maka farin cikin ka na zama uba sai na ƙwace mata nata farin cikin na zama matar wani balantana ta zama uwa,sai na mayar mata da rayuwarta cikin rayuwa mafi muni da ƙasƙanci,wallahi sai taji dama baka kanta Tayi cikin ruwan sanyi babu gardama,abunda ta hanaka sai na saka maza goma sunyi amfani da ita a lokaci guda,bazan huta ba sai wannan alwashin nawa ya cika '". "Wow Mother wow,Wallahi kinsaka ina jin kunyar wani ya wuce nace masa ga mahafiya ta nan,ina jin kunya da ƙyamar abunda kuka aikawa Kiswa ,yarinyar nan cikin dare kika koreta babu koda suturar arziki,baki san Wane hali zata shiga ba ko wanne hannu zata faɗa,idan da ace Farida ce fa,koda baki tausaya mata dan komai ba zaki tausaya mata for the sake of humanity,amma abun kunya da takaici kece zaune kike alwashi munana akan yarinyar da ɗanki ya nemi ya ƙetawa haddi,ai koda kashe sa tayi Batayi laifi ba,ya godewa Allah a nan abun ya tsaya,Good for nothing bastard".yaya Sameer ya faɗa babu koda guntun tausayin Sagir a ransa. Tasowa mother tayi ta tako gaban sa ,sai da tazo daf dashi ta ɗauke sa da mari mai zafin gaske ta nuna sa da yatsa tace"kaine Good for nothing bastard ba yaran da ya nemi tsayar da hawayen dake bin kuncin mahaifiyar sa da ƙanwar sa ba,sannan kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa abunda nace sannan ka ƙara da cewa nice nan na bawa Sagir goyan bayan haike mata,duk inda kuma take idan ka nemota ka faɗa mata ta shirya tarbar fushin uwar da akayiwa ba dai dai ba,sannan kar tayi gangancin dawowa gidan mu ta cigaba da buya domin duk abun nan da kaji na furta sai ya faru da ita,wutar tsanarta tana yi mun rurin da babu mai iya kashewa sai biyan buƙatar fansa ta,bari kaji koda hakan yana nufin zan rasa aure nane,abu kuma na ƙarshe da nake san ka sani Shine ,idan ka sake goyan bayan Kiswa a gabana ban yafe maka nono na da Kasha ba." Wasu irin hawayene suka fara zarya akan kuncin samir yana mai jinjina tsantsar jahilcin dake cikin maganar Mahaifiyar sa ,bai ce komai ba ya juya ya fita a ɗakin,kai tsaye motar sa ya shige ,cikin rashin tsammani ya tsinci kansa da fashewa da wani irin kuka mai cin rai,tunanin sa halin da Kiswa take ciki da wanda Mother ke neman saka ta nan gaba,tun da ya tsinci labarin abunda ke faruwa yake gwada layinta amma baya samu,tunanin sa kuma da inda zai sameta baki ɗaya ya gushe,yasan a duk inda take tana buƙatar ɗan uwanta,numbern Appa ya sake nema a karo na babu adadi dan so yake ya zamana a bakin sa ya fara jin labarin nan,amma still a kashe bai sameshi ba,abokinsa masu binciken boye ya kira dan su fara cigiyar inda take,baya sun gama waya kai tsaye ya wuce gurin sa Ayi binciken dashi. Bangare Haidar kuwa babu inda bai duba ba akan neman Kiswa ,Baga asibitoci,Sashen aje gawa da duk wani guri da tunaninsa zai bashi amma bai ganta ba,abinci kuwa bama shi da lokacin tunawa da yanajin yunwa tun safe har dare baici ba,tracking layinta shima yaje a ayi a kashe wayanta amma suka tabbatar masa da zasu cigaba da gwadawa har Allah yasa ta kunna wayarta ,karshe dai da kyar ya iya komawa gida dan kanshi sakamakon zazzabi mai zafi da ya rufe shi. Shin ina labarin Kiswa kuwa? CHUCHUJAY ✍️ 08130229878 [5/31, 11:42 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na CHUCHU JAY ✍️ Book1⃣ Page1⃣9⃣ ________Da wani irin matsanancin ciwan kai Kiswa ta tashi washe gari sakamakon irin kuka data raba dare tana yi,babu abunda ke damun ta idan ta tuna yarda tsakaninta da Yaya Sagir yake,they were this close da take jin babu wani abu da zai kawo mata matsala muddin tana dasu,babu abunda yake da ciwo sama da buɗe ido ka wayi gari ace yau family ɗinka sunyi back stabbing ɗinka saboda kawai wani selfish abu nasu na san zuciya wanda bai chanchanci yaudara da lalata zumunci ba,Baccin da tayi baifi na Awa biyu ba wanda Shima tana farawa zata tashi a firgice wanda cikin deren anxiety ya ziyarce ta,yanayi na tsoro da kuma tunanin abunda yafaru zai sake maimaita kansa. Bayan tayi sallar asuba bata iya komawa ba,tana jin Saleek na mata knocking kan ta tashi lokacin sallah ta sanar dashi idanta biyu ta tashi,bayan nan bata iya komawa ba ta zauna tana neman Allah ya kawo mata ɗauki ya saka mata hannu a rayuwarta,gari na fara haske ta shiga wanka tana tunanin sake mayar da bathrobe ɗin dake jikinta dan da ita ta Ƙwana ,locker ɗin da aka tanada domin aje towels a bathroom ta buɗe ta gansu jere tsaf dasu ,guda ɗaya ta jawo ta ɗaura kafun ta fito ta zauna kan gado ta ɗauki wayar ta tana tunanin kunnawa ,tasan mutum uku sun nemeta basu sameta ba,Haidar ɗinta da yaya sameer sai Appa idan ya san labarin ko 'ya dawo,amma ta shirya saka idanunta cikin nasu?,bata san mai zata fara faɗa musu ba domin kuwa mayar da zancen kawai sakata yake ta jita cikin wata irin matsananciyar kunyar da ba'a saka mata rana,san kiran Mamanta ne ya faɗo mata amma bata shirya tada mata hankali ba domin tasan Mama najin maganar nan zata taho Abuja ne wanda tasan abun babu kyau,hakura tayi da kunna wayar ta koma ta kwanta tana mai jiran tashin Saleek ta ari wayarsa ta kira Baba Baraka ta kwaso mata wasu kayan ta a boye da jakar ta boye dan koda zata koma gida ba yanzu ba sai abun nan 'ya sake ta. Tunanin abun ya cigaba da dawo mata da yarda Baba baraka bata kwana gidan ba,ta yarda sun gama shirya abun su ne Allah ya nuna musu bai yarda abu ya samu bawan sa ba muddin ba Shine yaso ba. Ƙwanƙwasa mata ƙofa da ake ne ya fito da ita daga dogon tunanin da take,daga inda take tace "wanene"? Saleek dake tsaye bakin ƙofar ne yace "Nine,Saleek na kawo miki kaya ne and breakfast is ready".tashi tayi ta jawo Hijab ta saka kafun taje ta buɗe kofar ,da murmushi ɗauke a fuskarsa ya nuna mata ledar yana mai faɗin "Good morning" Murmushin itama ta mayar masa kafun ta karbi ledan hannun nasa tace "Good morning and thank you".ɗan sosa gefen safen fuskarsa yayi yace "well ban san 'ya zanyi dake da godiyar nan ba,imagine da sanyin safiyar nan,well get dressed ki fito mu karya,and i hope komai na ciki is to Your liking na saka An siyo ne anjima idan na fita zan shopping miki kaya da abunda zaki buƙata". Dan buɗe kayan tayi cikin ledan ta ɗan kalla kafun tace"Well wannan ma na gode anjima zan saka a kawo mun kaya na office ka taho min dashi ,but bari na shirya na fito".kaɗa mata kai yayi kafun ya Bar gurin yana faɗin yana jiran ta. Kulle ɗakin tayi ta juye kayan kan gado,doguwar rigace ta material ready made sai inners,wani irin kunyace ta kamata ,thank God bashine yaje ya siya ba,pant ɗin baiyyi mata kaɗan ba baiyyi yawa ba amma Bra ɗin ya ɗanyi mata kaɗan,haka na ta saka ta ɗauki JC veil ɗin dake ciki ta ɗaura,Room Slipper ɗinta wanda dama dashi ta fito ta saka ta fita .tana fitowa ta hango shi zaune kan dinning table gefe guda kuma mace wadda bazata wuce 35 years ba tana jera abinci kan table ɗin,karasa tayi nervously tayi sallama ,ɗagowa yayi ya sauke idanun sa akanta ,wani irin santa yaji yana yi masa yawo a cikin zuciyarsa musamman yarda ya ga tayi masa kyau ɗin nan,kome ta saka kyau yake mata, she's Just pure and natural,saurin saita kansa yayi tunawa da yayi akwai neman wani akanta sannan yayiwa kansa alƙawari zai tsarkake Alaƙar dake tsakanin su,zama tayi tana mai faɗin"barka ".murmushi yayi yace"barka and Guess What? you look Good"yauwa zarah je ki kira mun kowa ,"To yallabai" Bayan wucewar Zarah ta kallesa tace"hope bazan zamar maka damuwa ba dan ina so nayi koda sati biyu ne out of any matsala and ina san kamun alfarmar kar ka faɗawa wani inda nake,i need a break for this madness,and ina san kiran Mai aikin gidan mu zata kawo min wasu kayan ka taho mun dashi,and ina san ka ara mun wayan ka,sai na kira ta". Kaɗa kai yayi yace"baki tunanin ita bazata fitar da maganan ba,i mean do you trust her" 100%" ta bashi amsa tana mai yi masa murmushi da ƙara ganin girmansa musamman da bai tambayeta abunda ya faru ba,matar da ya aikace ta dawo tare da mata uku,ɗaya zatayi tsarar zarah ɗaya kuma dattijuwa ce sosai dan Aƙalla zata daki hamshin,cike da mutuntawa bayan isowarsu yace musu"Good morning and na saka kuzo ne dan na gabatar muku da baƙuwata Kiswa,she's a family and tazo ne zata ɗan zauna annan dan haka yarda zaku bani service haka zaku bata bana san naji complain,kallan babbar yayi yace "Mama asabe dan Allah a kula da ita idan bana nan".murmushi matar da ya kira dan Mama asabe tayi tace"Insha Allahu yallabai,sannu da zuwa Hajiya,sunana Asabe,nice kuma nake kula da gidan nan bisa umarnin Yallabai Babba da ƙarami,ga Zarah ita ke kula da kitchen ga kuma Jamila Ita ke kula da shareshare ".gaishe da Kiswa sukayi cike da girmamawa wadda ta tsinci hakan weird dan bata san taga babba yana nuna mata girma tana ƙasa dashi,bayan sun bar gurin Zarah tayi serving nasa kafun itama ta wuce. A hankali ta fara cin abincin tana mai kallan Saleek wanda shima abincin yake ci kafun tace"baka tsoran ko na kashe wani ne aka koreni daga gida ka bani masauki,what if ni wanted killer ce,atleast ka tambaye ni." Murmusawa yayi yace"nasan ko mene zaki aikata akwai dalili sannan idan baki faɗa mun ba akwai dalili,bazan tab'a miki dole ba ki faɗa mun abunda ke damunki,kilan ba abune wanda zaki iya faɗa ba and i understand,ina san kisan abu ɗaya ne,a kowanne hali ina tare dake kuma zan baki goyan bayana ɗari bisa ɗari,zan saurare ki zan taimaka miki idan iyuwar hakan ta tashi". Goge ƴar ƙwallar dake ƙokarin zubo mata tayi kafun tace "kamar yarda ka sani gidan su Farry gidan yayan Mama nane ,ya dawo dani gidan sa ne lokacin mahaifina ya rasu so nida Farry muka girma tare kamar yan biyu,duk da na girmeta amma ƙawa na ɗauketa kuma ƴar uwa,haka zalika yayyunta guda biyu,Sagir da Sameer ,they are my everything ,so jiya yaya Sagir yayi kokarin yi mun fyaɗe ,ni kuma a kan cetan kaina nayi masa rauni shine Mother ta koreni a gidan,she never likes me,and worst thing Shine da Haɗin bakin ta yaso yayi raping ɗina,she knows. Wani irin ɗaci ne ya tsayawa Saleek a maƙogaro,tunanin abun kawai ya sakashi jin baki ɗaya yayi losing apetite,tasowa yayi daga kujerar da yake ya dawo ta kusa da ita gannin tana hawaye,shafa kansa yayi cike da damuwa yace"look babu wanda ya ke da ikon nuna ki da ɗan yatsa,kilan ban san yarda zan comforting ɗin ki ba saboda ban ƙware a nan ba,amma ina so ki sani abunda kikayi dai dai ne,Idan nine a madadin ki ma zan iya abunda yafi haka,im so sorry to hear this sannan ina san ki sani ina bayanki ɗari bisa ,sannan kamar yarda kika yanke shawara hutawa daga madness ɗin nan is a Good thing amma baki tunanin ya kamata Haidar yasan inda kike?i mean man nasan a irin san da yake miki yanzu haka damuwar da yake ciki bazata misaltu ba." Ɗan Ajiyar zuciya tayi tace,well ina tunanin hakan amma ina san na ɗan huta kaɗan daga kowa ,hope zan iya Ɗaukar 1 to 2 weeks break daga aiki CEO Sir? Dariya yayi a karo na farko kafun yace"kar ki manta idan Kin dawo ki shirya amsa query amma for now zan kulle ido nayi kamar Bansan baki zuwa aiki ba,".a Haka ya ringa kwantar mata da hankali har taci abinci shima ya samu ya ɗanci,.kamar yarda tace zata kira Baba Baraka haka ne ya faru koda ta kirata kamar zatayi mene saboda murna tana tambayar ta inda take. Saƙo ta bata na duk abunda take so takawo mata office ɗinta sannan kar ta faɗawa kowa ta kirata.bayan sun gama waya Saleek ya wuce bayan ya tabbatar da babu abunda zata buƙata.. CHUCHUJAY ✍️ 08130229878 [6/2, 9:02 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) Na Chuchujay ✍️ Book1⃣ Page2⃣0⃣ _______Kiran Samer da Appa yayi ya saka shi ji kamar an tsundu ma shi Aljanna,cikin sauri ya shirya an zuwa Airport duk da Appa yace yazo wurin ɗaya na rana ne amma tun goma yaje yana jiran saukar sa domin he cant wait ya faɗa masa abunda yake faruwa da wanda yake Shirin faruwa,ya kamata wani ya tsaida Mother kuma yasan Appa ne kawai yake da wannan power ɗin.ille kuwa gaisuwa kawai ta haɗa Appa da sameer ya fara zayyana masa abunda ya faru ba tare da ya rage ko kaɗan ba. Yanayin da Appa ya shiga ba ƙarami bane musamman da yaji ko inda Kiswa take ba'a sani ba,yasan Mother zata iya komai wa ƙiyayyyarta amma bai san rashin imani yana ɗaya daga ciki ba,Asibitin ya nemi kai tsaye Samir ya kaishi domin ya kamata yayi wa tufkar hanci,yana isa kai tsaye ya shiga ɗakin bisa jagorancin Samir inda suka tarar da sagir yana faman wa Mother kuka tana taya sa Farry na gefe itama kuka take tana lallashin su,kuka sagir yake sosai yana cewa"yanzu Mother bazan ga yara na ba kenan fa,Mother please ki taimaka mun ,nasan akwai asibitocin da suke nan a ƙasashen turai da zasu iya mun aiki na iya haihuwa,this cant happen To me Mother ,no now,wallahi bazan taba barin Kiswa ba sai ta gane ni tayiwa haka". Kafun mother tace wani abu Appa ya sanar da zuwan sa ta hanyar faɗin"sai dai in kai ka gane ita kayi wa haka,sannan duk wani asibintin da zaka je ya kasance da sa hannun uwarka amma ba da nawa ba,ya kamata kuma ku sani ko Wane Aiki yana da kamashu naku sakamakon kuwa Shine bani babu ku,daga nan ki san inda zaki kaishi amma ba gidana ba,idan kuma kina san ganin tashin hankali ki dawo gida na juwairiyyah,sannan kafun nan ina san ki sani na datse igiyar Aurena guda Ɗaya daga kanki,kinga ina da babban dalilin da zai saka na hanaki shigar mun gida,shi kuma na yafe miki shi domin ni ban haifi ɗan da zai yiwa ƙanwarsa fyaɗe ba wallahi sai dai in kece kika haifa tunda gashi nan maganar ki yake ɗauka,sannan wallahi na rantse da Allah idan wani abu ya samu Kiswa Na rantse da Allah sai na ɗaure ku". Ya juya zai fita Mother tace"Amma dai idan baka manta ba kana da ƙanwa wadda ta haifi ɗa a waje,ita dame tafi Sagir". Sosai maganar ta daki Appa da mamaki ya juyo ya kalli Mother, ƙaramun murmushi yayi yace"Uhum ina da ita sannan ba sai na faɗa miki ba ta ko ina ta fiki ,tarbiyya da komai ta fiki,domin nayi imani da Allah bazata bada goyan ba ayiwa Faridha fyaɗe ba,haka tasan darajar ɗan Adam,tana da imani sannan tana da taƙawa da tsoran Allah,idan kuwa duk tana da wannan abun kinga kuwa tafi mace Jahila ,ɗakikiya ,mai halin dabbobi kamar ki,nayi dana sanin mayar dake matata juwairiyyah na cutar da yara na da ban nema musu uwa ta gari ba,nayi dana sani sosai".yana kai ƙarshen maganar sa ya fita yayin da Farry ta fashe da wani irin kuka,sameer ya juya zai bishi ta buga masa wata irin tsawa tace"zo nan dan ubanka". Rumtse idanunsa yayi kafun ya juya yana mai takawa gareta,nuna sa tayi da Ɗan yatsa tace "ni zaka yiwa munafurci,ni uwarka da na haife ka,To sai mene dan Aliyu ya sake ni ina ce na faɗa maka sai naga karshe Kiswa koda hakan zai sanadiyar mutuwar Aure na?bazan maka baki ba amma zaka ga muhimmancin uwa ga ɗanta ,kaje kamar yarda ya sallama mun Sagir nima na sallama masa kai kaje Chan ku ƙarata sannan ku fara irgen ƙwanakin da suka rage mata na jin daɗi a duniya,sai na ɗai ɗai ta ta ,sai na saka Kiswa abincin da zataci tayi barar sa ,sai na saka duniya ta tsaneta ,sai na saka duniya ta tsine mata,sai na tozartata,idan banyi haka ba darajar Aurena da narasa bata da amfani,ka fita ka vani guri bana san ganin ka ,kuma koda na mutu ne ban yarda kazo kan gawata ba". Durƙusawa Sameer yayi akan gwiwowin sa ya fashe da wani irin kuka mai cin rai,cikin kukan yace"Mother dan Allah dan darajar Annabi Kar ki lalata rayuwarki ki lalata mana tamu,Farry har yanzu bata yi Aure ba nima haka kina tunanin idan abun nan duniya taji mutane zasu so haɗa jini damu?all this bitterness and hatred is for what?yarinyar nan Kiswa babu abunda ta tab'a yi miki na sharri iyakaci ma a kullum burin ta taga ta saka ki jin daɗi,babu abunda ta tab'a yi miki na sharri wanda zai saka ki na nementa da wannan bala'in,zamu iya gyara komai Mother we can talk to Appa together muddin zaki yarda makaman yaƙinki ki tuba a kullum Mother zaki iya faɗuwa ki mutu mai zaki cewa ubangijin mu dangane da ba dai dai ɗin ki ba?dan Allah Mother ki duba magana ta. Wata irin dariya ta saka kafun tace"tashi ka bace mun da gani samir kafun raina ya b'acci na rasa gane abunda zanyi maka dan wallahi zan sab'a maka Sosai,get out babu kuma wani munafurci da zaka sake faɗa mun,banza mara kishin uwar sa da yan uwan sa".bai kuma cewa komai ba ya tashi ya fita a ɗakin,zama Mother tayi tace "sakaran banza,kai kuma Sagir ka ƙwantar a hankalinka koda komai nawa zai ƙare zan bayar dan ka warke"juyar da kansa yayi ya cigaba da kukan sa inda a bangare guda yake jin wata irin tsanar Kiswa sosai tana huda mada zuciya. Kallan Farry Mother tayi tace "nasan kina tare dani a duk abinda zanyi after all dama ai komai domin ke ne sannan ina mai tabbatar miki zaki Auri Haidar ko anƙi ko anso So ki ƙwantar da hankalin ki". Goge hawaye Farry tayi tace"amma Mother yaya sameer bai san dani a wannan abun ba after all dama Mother ai ba karya bane ban san dan cewa Yaya Sagir zaiyyi wa Kiswa fyaɗe ba "..wani irin kallo Mother ta bata kafun tace"ban fahimci inda kike Son dosa ba,Eh baki san zai mata fyaɗe ba amma dan ubanki dan Wane na bada goyan baya" Ganin kamar Mother na neman daukar zafi ya saka Farry saurin cewa"bafa wani Abu nake nufi ba Mother ,ina so ne na koma gida ,ba yarda za'ayi na biku keda yaya Sagir After all kina buƙatar mai kawo miki rahutan cikin gidan wanda kin san Yaya sameer bazai baki ba,sannan Mother bana san na rasa aiki na amma ba wai da wani Abu ba,kinsan Appa na sanin wani Abu koda babu saka hannuna zai kwace matsayina ne a company shi yasa yanzu nake san naje gida na nuna tare nake dasu amma kamar kina da spy ne a ciki,after all kina san ki san Kiswa ta dawo ko bata dawo ba."ƙarasa maganar Farry tayi tana Addu'ar Allah yasa kar Mother ta b'ata matsala. Shiru Mother tayi tana nazarin abun kafun tace"oya maza tashi kije gida ,ya kamata kiyi welcoming Appa ɗinki properly ."murmushi Farry tayi fahimtar abunda Mother ke nufi dan haka ta tashi ta ɗauki jakarta ta fita tana tunanin yarda zata gamsar da Appa da yaya sameer kan cewa ba'a bayan su Mother take ba..koda ta isa gida ganin motar Yaya sameer ta tabbatar mata sun dawo gida,tana shiga taci karo da Baba Baraka na arranging dining,kamar wadda tayiwa sarki ƙarya ta shiga tace "ina wuni"da mamaki Baba Baraka ta kalleta dan sabon abune wannan tsakaninta da Farry,amsawa tayi tana mai cewa sannu da zuwa,ɗan yaƙe Farry tayi kafun tace"yaya sameer fa?" "Yana sashen sa"ta bata amsa ta cigaba da abunda take yi ,kai tsaye Farry ta nufi gurin samir dan shi ya kamata ta kama tukunna, tana shiga Kamar munafuka tayi masa sallama,yana zaune ya rufe idanunsa abun duniya duk ya ishe ta,jin muryarta ya saka shi buɗe ido ya kalleta kafun yace"Na yi imani da Allah duk wani Abu da Mother zatayi da saka hannun ki,uban mene kuma ya kawo ki inda nake?wallahi Kin bani kunya da Mamaki Farry,akan duniya da abun duniya kike Name ki zama abun tsoro. Zubewa tayi kan gwiwowinta ta saka kuka tace"Wallahi yaya sameer ni ban da masaniya akan abun nan,na yarda muna da matsala tsakanina da Kiswa amma tunda aka saka bikinta na janye,ka tambayi Mother ɗin kaji,koda wasa basu sakani cIkin wannan abun ba dan da ace sun sakani baza'a zo nan ba,im also disappointed yaya sameer sannan na kiɗime da ban san cewa Mother ta kori Kiswa ba sai bayan na dawo nake nemanta ban ganta ba" Kallanta da kyau sameer yayi kafun yace"ki tabbatar wannan abun ba wani game ɗinne kuka haɗo ba,domin wallahi idan na kamaki da rashin Gaskiya Faridha kiyi kuka da kanki,'dan da kaina zan miki hukunci mumuna ba sai Appa ya saka baki ba.suna cikin haka Appa ya shigo yana mai cewa"Sameer zamu iya tafiya ."ganin Farry ya saka shi cewa "Allah ya saka tunani na n cewa dake ba gaskiya bane" Kuka ta sake rushewa dashi tana mai yi masa rantse rantse,haka nan dai shima yayi mata gargaɗi kafun suka wuce shi da samir domin sake saka cigiyar Kiswa. ********* ____________wasa wasa jikin Haidar yaso yaƙi hannu amma kasancewar sa likita ya saka bai bari sun gane ba domin kuwa shi yanzu zama bai ganshi ba,fitowar sa daga wanka kenan guy ɗin da yasaka yayi masa tracking wayar Kiswa ya kirasa ya shaida masa labari mai daɗi inda yake sanar masa da cewa sunyi tracking layin ta amma cikin minti talatin ta kashe wayarta amma kuma duk wani bayani na location ɗin ta da suke san sani sun samu. Jikinsa har rawa yake yana shiryawa domin sun tura masa address ɗin da zai ga Kiswa,bai fadawa kowa ba ya fita domin zuwa gare ta ,mamakin da yake kai Shine wanda ta sani a gurin domin gurine mai nisa kuma downtown ,dama 'ya sani jikinsa kuma ya bashi a duk inda take zai ganta duk kuwa nisan gurin da taje,a haka ya isa Unguwan cike da zumuɗi yana mai duba address ɗin da suka tura masa, he blv sun san abunda suke a aikinsu sannan shima ya ware bakin aljihu wajen neman ta ,baga gidaje radio da tv's ba baga trackers ba,he is just meant to find her. Yana cikin motar sa yana san gano gidan motar Saleek ta wuce sa and for real Saleek ya gani sannan ya tabbata hakan ba coincident bane,ganin yana horn bakin gate ya saka shi saurin fitowa a motarsa ya isa gurin motar tasa da gudu gudu sauri sauri,yana zuwa ya ƙwanƙwa sa masa glass,wani irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Saleek lokacin da idanun sa suka saka kan Haidar,tambayar da ya fara yiwa kansa ita ce"shin Haidar binsa yake?amma saboda mene?fitowa yayi domin yi masa wannan tambayar amma ga mamakinsa kafun yace wani abu Haidar ya kai masa naushi mai kyau a fuska yana faɗin"ina ka boye ta".yana ƙokarin sake kai masa wani ya riƙe hannunsa ƙam yace"kar ka kuskura,'dan mene daga ganina zaka fara kaimun duka,sannan lafiya Why are you stalking me? Cike da fushi Haidar yace"A for Audacity ,Just the temerity And the fucking guts,ni kake tambaya ko ina stalking ɗin ka ne,nasan kasan da b'atan Kiswa sannan nayi tracking ɗinta tana nan dan haka kada ka bani wani act din banza i know kayi kidnapping ɗinta ne and im calling the police yanzun nan ". Ɗaga kafaɗa Saleek yayi yace"suit Your Self amma kasani ni banyi kidnapping kowa ba had it been ka bini da sauki da na tausaya maka amma tunda ƙarfi zaka nuna mun ga fili ga mai doki saura sukuwa,motan sa ya buɗe zai shiga Haidar yayi saurin kama hannunsa desperately yace "kana nufin Kiswa na cikin gidan nan?"please kayi hakuri Just let me See her dan Girman ubangiji. Kallan sa Saleek yayi lokaci guda yana mai jin kishin sa inda bangare guda kuma yake mutuƙar tausayin sa ,ya tabbatar Haidar na mutuwar san Kiswa sannan ba ya so ya zama third wheel akan abunda bazai samu ba,kallan sa yayi a karo na biyu kafun yace"bismillah ". Buɗe motar Saleek yayi ya shiga inda ya sake horn aka buɗe masa tare suka shiga Saleek na mota Haidar wanda kejin kamar anyi masa babbar kyauta yana biye dashi a a baya yana Allah Allah yaga Kiswa ko zai ji daɗi a rayuwarsa. Chuchujay ✍️ 08130229878 [6/4, 11:01 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) By Chuchu jay Book1⃣ Page 2⃣1⃣ __________Koda suka shiga ma'aikatan gidan ne kawai a falo waɗan da suka gaida su cike da girmamawa,kallan Haidar dake raba ido yana neman inda kiswa zata fito Saleek yayi kafun yace masa"ka zauna bari nayi maka magana da ita ko zata gan ka cos kasan nayi gaban kai na ne babu yardar ta,idan kuma baza ta ganka ba babu abunda zan iya sai dai in na baka hakuri..murmushi Haidar yayi yace "i doubt if she will reject me".kallan sa kawai Saleek yayi ya juya dan zuwa yi mata magana duk da yasan yayi mata laifi tunda ta roƙe sa kar wanda yasan tana nan,but its not his fault Haidar yazo ne using his own method wanda koda Shine a stead ɗin sa shima haka zaiyyi ,Allah kaɗai yasan abunda guy ɗin yayi going through saboda soyayyar sa is Top notch..tsaye Saleek yayi a bakin ƙofarta yana debating da zuciyarsa kafun yayi ta maza ya ƙwanƙwasa mata,Knocking ɗaya yayi tace Wane,amsata yayi yace Shine,jin muryarsa ya saka ta kimtsa kanta tace"Bismillah". Kamar yayi wa sarki karya haka ya shiga ɗakin ,gaishe shi tayi ya amsa mata yana mai tunanin yarda zata dauki maganar kafun yace "na dawo kawo miki kayan ki ne da Baba Baraka ta kawo mun office so ina tunanin ko zaki buƙaci wani abu shi yasa nazo sannan in the process nayi miki laifi hope za'a yi mun afuwa,ina dawowa na tarar da Haidar bakin gidan nan and i swear bani na faɗa masa kina nan ba,nima i Just saw him ina shirin shigowa and he look Like a mess ,a yarda na ganshi kuma i had no option dole na bar shi ya shigo,but idan kince baza ki ganshi ba bani da matsala dama i told him idan baki yarda ba zai haƙuri ne".. Shiru tayi tana kallan sa kafun tace"yana ina yanzun?"."yana falo"ya bata amsa yana addu'ar Allah yasa kar tace bazata ganshi ba,it shouldn't be Like that,dan Shiru tayi kafin tace"its okay muje na ganshi". Koda ta fita ya juya baya yana Kallon ta inda zata fito,gyaran murya Saleek yayi yace"oga sir ga Madam ɗin ka fa"juyowa Haidar yayi da sauri take idanunsa suka cika da hawaye lokacin da ya sauke su akanta,bai san lokacin da ya ɗaga kafafun sa ba ya isa gareta kafun tayi Aune ya haɗe ta da jikin sa cikin runguma wadda yake ji kamar za'a ƙwace masa ita,ba tayi zato ba Batayi tsammani ba haka zalika Saleek wanda abun yazowa a bazata,tana ƙokarin kwacewa ya riƙeta yace"please Just a Moment ,"Ajiyar zuciya ya sauke kafun ya raba jikin sa da nata ya kalleta yace "mai yasa kika yi mun haka?,kinsan Wane irin hali na shiga da ban ganki ba,i know kina fushi dani Shine ya saka baki kirani ba,im sorry about abunda na faɗa miki ,sharrin shaiɗan ne and na miki alƙawari bazan ƙara miki zargi irin wannan ba so please kar ki bani wahala irin wannan.kallan sa take wani irin san sa na fizgar ta,ganin yarda baki ɗaya ya rame dare ɗaya kawai ya bata tsoro,ɗan murmushi tayi tace"ka zauna muyi magana"babu musu ya zauna,ganin cewa Haidar da Kiswa sun manta da Saleek ya na Falon ne ya saka shi jejely barin Falon wani Abu nayi masa yawo a ƙirji,sunnan Allah kawai yake kira domin wani irin kishin ta ya tsinci kansa ciki ,ji yake zuciyarsa nayi masa wani irin suka,amma sanin baya da hurumin da zaiyyi wannan kishin a kanta ya lallashi zuciyar sa ya roƙi Allah ya sassauta masa kishi akan abunda ba nasa ba. Zama Haidar yayi yana mai jin kamar zai buɗe ido yaga mafarki yake,zama itama tayi tana kallan yarda baki ɗayan sa ya kasa nutsuwa,Ajiyar zuciya tayi tace"yarda kazo and da yarda nake kallanka a yanzu nasan kasan komai da ya faru and im sorry ban kira ka ba domin bana fatan ka ganni cikin halin da nake ciki,and ban kira ka ba bayan nan saboda bana san na tada maka hankali"."ai rashin kiran Shine yafi komai tada min hankali baby cos gwanda nasan inda kike da ace Kin boye ban sani ba ,im sorry about komai sannan ina san a Rayuwar nan ace na zama a gefen ki a yanayi mai kyau ko mara kyau domin kuwa Alaƙa na dake is for better and worst ,don't do this to me ever please,nasan kuma abunda na faɗa miki kan Saleek ne yasaka, kar ki ga laifina kece burina ,duk wani ɗa namiji da zan gani a tare dake zuciyata sai tayi skipping beat musamman kuma namiji kamar Saleek,ta ko ina haɗaɗan gaye ne wanda mace zata ji a kallo ɗaya yayi mata Why wont i be scared.ɗan murmushi tayi tace"tsakanina da Saleek Pure relationship ne wanda babu wani tunani mara kyau a cikin sa,yana da kirki he is just very kind to me sannan mutum ne shi wanda na ɗauke sa kamar ɗan uwa haka zalika shima ya ɗauke ni haka,kai ma ka sani i will never be moved By any man When i have you,kai nake so kai na zaba idan kuma za'a sake dawo da hannun agogo baya i will still choose you,you're my muse in love and everything,i will never abandon Your love for another ya kamata ace tuntuni ka san wannan,so please ka daina sakawa kanka insecurity akan abunda ba haka yake ba,sannan da kake cewa kallo ɗaya mace zatayi wa Saleek ya tafi da ita kai kuma fa?ka dai san Saleek ba kyau ya fika ba iya kaci ace ya fika kama da play boys,you're so Handsome My Sugar"ƙarasa maganar tayi tana mai kashe masa ido guda ɗaya. Haɗe lebensa yayi guri ɗaya kafun ya sake su ya Faɗaɗa fara'arsa yace"dont do that gaban wasu cos you look cute,so yanzu dai kije ki ɗauko belongings ɗin ki mu tafi dan daga nan gidan mu zaki je,ba zaki koma gidan nan ba".ɗan shiru tayi kafun tace "bazan bika gidan ku ba gaskiya ,idan Mama taji ma raina zai b'aci i will be okay here"....kafun ya sake cewa wani abu sukaji ana buga ƙofar falo,tana ƙokarin tashi Saleek ya fito yana mai faɗin"i will get it". Koda yaje ya buɗe mai gadin gidan ne ya duƙa cike da girmamawa yace"Alhaji kayi baƙine nayi tunanin ma na Alhaji babban ne to amma sai suka ce kai suke nema".da mamaki Saleek yace ni kuma? "Eh kai kuwa muke nema"muryar Appa da ya kasa hakura ya tako ta karaɗe kunnuwan su,wani irln faɗuwar gaba ne ta ziyarci Kiswa ,tashi tayi daga zaunen da take tace "Appa?"jin tace Appa yasa Saleek cewa "bismillah ku shigo,"babu musu Appa ya shigo bakin sa ɗauke da sallama yayin da yaya sameer ke bayan sa shima yana mai yin sallama ɗin,muzurai Kiswa ta fara da ido tana mai cewa"sannu da zuwa Appa,durƙusa wa tayi domin gaida shi,saurin binta yayi ya ɗagota yana mai kaɗa mata kai yace"No my daughter ina mai mutuƙar jin kunyar abunda ya faru dake amma ina mai jin babu daɗi daya kasance bani kika fara kira kika sanar wa ba duk da ina matsayin mahaifinki".kallan Haidar yayi yace "tana gurin ka kenan,kaima baka kyauta ba domin ni ya kamata ka kira".duƙar da kai Haidar yayi yana mai gaidashi kafun yace"nima Appa zuwa na kenan dan sai da na saka ma a kayi mun tracking ɗin ta,amma wanda ya taimake ta gashi nan,Saleek ogan ta gurin aiki".Gaida Appa Saleek yayi inda Appa ɗin ya bisa da kallo domin yau ne ya fara ganin sa duk da kuwa mahaifinsa abokin sa ne,koda suka so haɗa alaƙa tsakanin yaran su shi baisan Saleek ba amma yana da yaƙi nin duk ɗan da za'ace daga Alhaji Basil yake to mai tarbiyya ne wanda dalilin da yasa yaso su haɗa Auratayya.cike da mutunci Appa ya amsa mishi kafun yace"nagode sosai da abunda kayi wa Kiswa im so glad hannunka ta faɗo thank you Allah yayi maka albarka,muma tracking ɗin nata mukayi,ina gayyatar ka gidan mu for saturday lunch ina fatan kuma baza kaƙi amsa gayyata ta ba".murmushi Saleek yayi yace"insha Allahu Appa ,"kafun ya juya suka gaisa da yaya sameer inda Haidar ma ya miƙa masa hannu suka gaisa. Duk yarda zuciyar Kiswa ke assasa mata ƙin komawa gida kasa nuna wa Appa tayi lokacin da ya mata izinin ta ƙwaso kayanta su wuce,kula da Appa yayi da rashin jin daɗin komawa gidan ya saka shi cewa"ki ƙwantar da hankali ki ,Mother da kika gani bata gida dan Aure na da ita ya ƙare,shima babban shaɗanin yaran na sallama mata shi dan haka ki saki jikin ki,gida na mahaifin ki ne kuma zanyi waje da duk wani wanda zai wasa da ƴata muddin ina raye.wata irin kwanciyar hankali ce ta ziyarci Kiswa domin dama tsoran ta su. Koda suka isa gidan kai tsaye ɗakinta ta nufa,tana shiga Baba Baraka tazo tana mai tambayarta abunda zata kawo mata.kallan ta Kiswa tayi kafun ta tashi ya rungume ta ta fashe da wani irin kuka,shafa bayanta Baba Baraka ta fara a hankali kafun tace"kiyi haƙuri Kiswatu,komai kika ga ya faru ga bawa ƙaddararsa ce,ke taki kenan,kuma Allah ya kawo miki da sauƙi,".cikin kukan Kiswa tace"banji daɗi ba Baba baraka da ya kasance hasashen ki ya zamo gaskiya,ji nake dama ace mafarki ne,nayi dana sani da ban bawa maganar ki muhimmanci ba inajin da ba'akai yanzu ba dan zanyi wa tufar hanci,gashi yau na zama silar da gidan nan yake neman tarwatsewa".cike da lallashi Baba Baraka tace"baki zama silar lalacewar komai ba cikin gidan nan kiswatu sai ma ke da akaso a lalata Allah ya tsaya miki dan haka ki daina wannan maganar,ba tun yau ba nasan Hajiya bata ƙaunarki ,dan haka hukuncin da Alhaji ya ɗauka akan ta yayi dai dai dan ni bana ko tausayin ta"haka nan tayi ta lallashin ta har ta ɗan samu nutsuwa. Bayan sati da faruwar al'amarin komai ya lafa domin bama sa jin Mother yayin da babu wata maganar arziƙi da ta shiga tsakanin Kiswa da Farry,Kamar yarda Kiswa ta nema kuwa hutun sati biyu Saleek ya bata na aiki,ranar Monday tana zaune tana aikin office ɗin ta a ta gida taji buruntun mutane a waje,rufe system ɗinta tayi ta tashi ta fita dan ganin meke faruwa,tana fita idanunta suka sauka kan na Maman ta ,gefe guda kuma kakar ta ,wani irin tsalle tayi ta rungume kakar tata tana mai faɗin"Dada"ɗan karamin ƙara Dada tayi tace"Ke kar ki karyawa mijina ni ki cucesa,jaira yaushe rabon da kije inda nake sai anyi magana kice aiki aiki"ƴar dariya Kiswa tayi tace"nima ina ƙewar ki abar ƙauna"Kallanta ta mayar kan Mama kafun itama ta rugumeta tana mai cewa "Mama na".kafun Mama tace wani abu Rabia Ta shigo tana mai faɗin"Didi"da gudu tayi kan Kiswa ta ɗane ta inda itama ta chab'eta tana mai jin wata irin murnar da ta rasa ina zata saka kanta,kallan ƙofa ta fara tayi tae"ina khaleel?"."yana boarding ai basuyi hutu ba".suna wannan ihun murnar yan uwansu Na bauchi suka fara shigowa ,mamaki ne sosai ya kama Kiswa wadda ta fara musu maraba tana gaidasu.tambayoyine fal zuciyar Kiswa tana san sanin abunda ya kawo su gidan wanda ita dai tasan ba taro ne ake yi ba,bayan kowa ya samu masaukin sa ne Kiswa ta nufi ɗakin Dada,chan ta tarar da Farry ,ƙin shiga tayi kawai ta koma gurin Mamanta,nan ne take ji wai Gobe za'a ɗaura Aurenta da Haidar. CHUCHUJAY ✍️ 08130229878 [6/8, 10:47 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥 (Surrogacy was the cause) By Chuchu jay ✍️ Book1⃣ ADVERT Assalamu alaikum Habibties Meet AISHA and AMINA , Kai biyu da suka kawo muku "CHAPTER GREEN",💚shin kun san mai chapter ɗin su ya ƙunsaa? Bari na faɗa muku,chapter ne dake ɗauke da Lover's Chapter ,ma'ana shafin masoya,inda tattaunawa kan abunda ya shafi soyayya zai wakana,akwai Family Chapter,ma'ana shafin iyali inda tattaunawa ta bangaren iyali zata gudana,akwai ISLAM Chapter,wannan sashen shi kuma shafi ne na tattaunawa kan abunda ya shige duhu a musulunci ,akwai Chapter na Rayuwar mu a yau,sannan akwai Matsala da maganinta,kamar yarda Bature yace "two heads are better than one"a wannan Chapter ɗin zaka kawo damuwarka a tattauna matsalar ka a baka solution ,sannan you can also shoot your shot. Wannan duk zai faru ne da yardar Allah a CHAPTER GREEN. Mai kuke jira baku kasance da su ba? Oya join them on Whatsapp via link below https://chat.whatsapp.com/JVI1jEszfJhHG1kri7xVAb Follow them on Instagram :Chapter_Green_ On X :Ameenatourh_jay Page 2⃣2⃣ Duk da cewa Kiswa na farin ciki da ko yaushe Auren Haidar zai zo mata amma taji abun wani iri,da mamaki ta kalli Mama tace "Mama Aure gobe babu shiri?ni kaina ban sani bafa".murmushi Mama tayi tace"Aure babu shiri?yaran yanzu kenan to mu a shirye muka zo,za'a ɗaura ne inna goggo zata gyara ki na sati biyu,bazaki tare da shi mijin naki ba sai sati biyun 'ya cika ,yarjejeniyar da yaya yayi dasu bisa umarnin Dada,dan haka ki kwantar da hankalin ki zamu haɗaki"wata irin kunyace ta ziyarci Kiswa,cikin san kare kanta tace"nifa Mama ba haka nake nufi ba Allah",shafa kuncin ta Mama tayi tace "koma ya kike nufi kinji tsarin dai, sannan koda baki faɗa mun abunda ya faru ba shima yayan yaƙi faɗa nasan akwai Matsala tunda nazo gidan nan banga juwariyyah ba sannan Yaya ke faɗin sun rabu yaƙi kuma faɗan dalili ga kuma maganar Auren ki nasan akan ki ne ,amma koma mene ki sani babu abunda ta isa tayi miki wanda Allah bai miki ba,sai wanda ya ga dama sannan ni nasan addu'ar uwa bata faɗuwa ƙasa banza ,kullum cikin yi miki nake,insha Allahu bazaki tab'e ba.murmushi Kiswa tayi ta rungume mahafiyarta ta tana kuma mai jin daɗi da ya zamana alfarmar data ruƙa gurin Appa na kar ya faɗa musu abunda ya faru yayi mata,yin hakan kuwa dalili Shine bata so hankalin su ya tashi ,bugu da ƙari kuma bata san mutuncin Sagir ya zube gurin dangin su,mussamman Mamanta dake mutuƙar san shi da girmama shi,haka ta ɗauki girman danginta koda kuwa za'a kirata sakariya,abu guda ɗayane ta sani wanda tsakaninta da sune inda bataji a zuciyarta zata iya yafe musu a yanzu kam ".kafun kace ƙwabo kuwa gidan Appa ya karaɗe da hidindimu,kamar wasa Haka abun ya fara,da yamma Haidar ya kirata a waya,tana ɗagawa yayi wani sassanyan murmushi yace "amarya ta ina ta san na kira ki Ummi ta sakani gaba Ina Boutique ɗinta tana zab'a miki kayan da zaki saka da taro,aƙwatin ki kuwa yana hanya daga Malaysia,Ummi da Draman ta,nace a Boutique ɗinta ma komai daga Chan ne amma taƙi wai ƴarta abu mai kyau ya dace da ita."ƙaramun murmushi Tayi tace "So kasan da maganar Aure baka faɗa mun ba ko?". "Nima Baba ya faɗa mun, amma labari ne da ban taba jin Mai daɗin irin sa ba,ina cikin wata irin murna da bazan iya misaltawa ba,nasan kema kina cikin farin ciki,,i mean mene yafi wannan farin ciki? "Murmushi tayi tace"babu fa,kawai dai an shammaceni ne ,but either ways Allah yasa haka shine mafi alheri." Ehen now you're talking"a haka suka cigaba da bawa junan su kalamai masu daɗi da sharing ma junan su irin burikansu na zama ma'aurata. ****** "Ban fahimci abunda kike faɗi ba Faridha,ki sake faɗa mun daga farko,kina nufin kice mun Aliyu Aure zai ɗaurawa Kiswa da Haidar gobe?"Mother da maganar ta daketa kamar saukar guduma ta faɗa zuciyarta nayi mata wani irin tafasa. Sagir dake zaune ne shima maganar ta shige sa yace"wallahi Mother bazai iyu ba,ai ko Kiswa zatayi Aure ni ɗin nan da ta nakasa ni zata Aura , kawai Mother kiyi wani abu".shiru Farry tayi kafun tace"ni dai a ganina Mother kinga dai inda abun nan ya kawo mu, akan ta Appa ya sake ki ya kore ki da Ya Sagir daga gida mai zai hanna mubar bala'in nan tayi bacci, yanzu yarda Dada tazo ɗin nan wallahi ƙiris Abu za'ayi ya zama babba,duk da na bigi cikinta kamar bata san mai ya haɗaki da Appa ba dan har tana tambayar inda Yaya Sagir yake nace mata baya ƙasar"."mitsiyaciya ,Algunguma kanwa uwar gami ai Dada tana ɗaya daga cikin masu zuga Appan ku,sannan idan bataji ba sai mene?idan yana ganin gwaninta ce yayi da zai boye abunda ya faru bai faɗa musu ba ,babban bala'in da zan jefesu dashi bazaiyyi tunani ba zai faɗa musu,na yarda a yanzu bana da wani abu da zanyi na katse Auren nan amma tabbas sai na lalatashi"Mother ta faɗa tana mai tashi ta ɗauki jakar ta da Car key ɗinta tana mai cewa"bari naje na samu Hajiya zee ɗin ma ku gani".tashi Farry ma tayi tace"nima dai bari na wuce gida dan nasan yanzu Dada zata fara nema na". Tare suka fita daga gidan wanda yake mallakin Mother ne ,Farry ta kama hanyar gida dan bata san matsala inda Mother kuma tayi hanyar kaiwa Ummi ziyara,kamar kuwa yarda ta ayyana tana Boutique ɗin ta,koda taje babu wata wahala ta samu ganin ummi ,tana shiga ta washe haƙora yayin da Ummi ta ɗaure fuska tace "fatan lafiya dai".kujera Mother taja zata zauna Ummi ta dakatar da ita hanyar faɗin"ban baki wanna izinin ba,sannan ina san ki faɗi kai tsaye abunda ya kawoki duk da nasan san zuciya ne amma still na baki damar ganina,i know how wicked and heartless you can be so dan Allah ki tafi mun kai tsaye ki kama gaban ki". Da mamaki Mother tace"ban san yaushe Alheri Ya zama sharri ba,mene laifina dan ina san cire ɗanki daga ƙangin fitina da yake neman zira kansa ?dan fa ina san taimakon ki bashine zai saka na zauna kina faɗa mun magana mara daɗi ba.".dariya Ummi tasa kafun tace"taimakona kikace ko?to Allah ya tsinewa halinki da taimakon ki,Kin bani mamaki sosai,ki kalleni nan da kyau,zan iya zuwa ko Wane extent domin na samu Farin Cikina dana iyalina ,amma Allah ya kiyaye naje level ɗin ki,sannan ina san ki sani zuwa gobe idan Allah ya kaimu,zamu bawa Kiswa legal right na zama dangin mu,wallahi ko ciwan kai tayi ta sanadin ki zaki sha mamaki,zan nuna miki baki da komai a bangaren power da kuɗi,get out now next kuma idan kika sake nuna minn ugly face ɗin ki ni kaina ban gama haddace abunda zan miki ba wallahi. "Da mamaki Mother ke Kallanta kafun tace"ba laifin ki bane"sannan ta juya ta fita a office ɗin gwiwarta a sage,tsaki Ummi tayi bayan fitar ta tana mai jin haushin Mother da rashin kame girmanta da darajarta ta uwa. Komai da Kiswa zata buƙata Ya hallarta ,kama da wadda zatayi mata gyaran jiki,kai,lalle da komai da amarya zata ɗauka wanda hakan nauyine da Ummi ta ɗora a wuyan ta domin kuwa irin mutuwar san da Ummi ke yi wa Kiswa abun ba'a cewa komai,gidan babu abunda kuwa ke tofawa sai irin sa'a da Kiswa tayi na samun mace ta gari a matsayin mahaifiyar miji dan soyayyar da Ummin ke nuna mata kana gani ba wai soyayya bace ta ƙarya musamman idan ka duba daga bangaren irin soyayyar da takewa Haidar wadda itace ta shafi Kiswa ɗin,kafun kace mene amarya ta fito ɗas kamar za ka saceta ka gudu,Fitowarta daga wanka turaren da Dada ta saka tayi taji wayarta na ƙasa,ɗauka tayi ganin sunan wanda ke jin wayar,da sallama a bakin ta tace"Boss Saleek good evening".karamin murmushi yayi kafun yace"kin san dai baki da kirki ko?,bai kamata ace bikinki a media zan gani ba,Kinsan koma mene im Your well wisher mai yasa zaki boye mun,abune na farin ciki fa".zama tayi kamar yana kallanta tace"im sorry, Like im very sorry kayi haƙuri nasan bazaka yarda ba idan nace maka nima yau nake sanin za'a ɗaura min Aure gobe iswear,kaima kasan kana na gaba cikin masu sanin Aure na bazan taba boye maka ba,abun kaji da yarda yazo"..ɗan shiru yayi kafun ya sauke ajiyan zuciya yace "its okay na yafe miki Just this one time nasa Abba ma ba mamaki ya rigani sani 'dan ina maganar Ɗazu ya katseni yana mai sabanta murnarsa ,but any ways im very happy for you naji miki daɗi sosai,sannan ina miki fatan shi ɗin abokin Alherin ki ne,and bazan boye miki ba,duk da yau ne last day amma ya kamata ki sani,'ina mutuƙar sanki Kiswa amma duk yarda naso da san kaina bai kai yarda nake sanki ba,dan haka ina miki fatan Alheri a sabuwar rayuwarki,sannan kamar yarda na faɗa ni dake mun zama family dan haka just a call idan kina da wani damuwan and i wil be right away,sannan kafun na manta,company ya baki month honey Moon leave,kiji daɗin ki"..tsintar kanta tayi da share ɗan hawayen da bata san taya ya fara fitowa ba,ta yarda tayi sa'ar samun mutum kamar Saleek a rayuwarta,goge hawayenta tayi tace"nagode Saleek im blessed to have you in my life ,sannan ina fatan Allah ubangiji ya baka mace wadda ta fini komai da komai ,inayi maka fatan Alheri,and im looking forward to meeting you as Mrs HAIDAR BULA."..bayan sunyi sallama ya kashe wayan Khalifa dake gefensa ya kallesa yace "mutumina kana da ƙarfin Hali da imani,wannan Babe ɗin fa you dey do her ne kana santa kaƙi kula kowa akanta amma gashi magana ake ta Aurenta fa Har kana da ƙarfin kiranta kayi mata fatan Alheri,omo nagode ƙanin Mother teressa.".Kallansa Saleek yayi kafun yace "abu guda ɗaya na yarda dashi wanda Shine babu wanda ya isa 'ya Auri matar wani sannan ga dukkan alamu ya bayyana cewa Kiswa ta Haidar ce so mene kake so nayi,kana san na halaka ne saboda ina santa?abeg idan zakayi mun Addua Allah ya kawo min sassauci kayi mun idan baza kamun ba ka zuba mun ido,kuma kar ka Sake kiranta babe".tabe baki Kalipha yayi yace"kaji dashi ni bari kaga tafiyata ma kafun yanzu saboda nasan akan Kiswa za ka nemi ka zageni."Bai ce masa komai ba har ya fita,komawa yayi ya ƙwanta ya rufe idanun sa abun duniya na mutuƙar damun sa ,ya kasa yarda da cewa wai Kiswa zata zama matar wani gobe da safe sannan yana addu'ar Allah ya bashi ikon Hallarta ,he Just can't bear it. 💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥 __Kamar yarda komai ake saka masa rana ya tabbata cikin yardar Allah haka nan ranar da aka saka domin Kiswa da Haidar tazo,Babban Masallacin na central mosque a cike yake da manya mutane domin amsa gayyata Ɗaurin Auren da yazo babu zato babu tsammani,bikine na kuɗi wanda cikin rana ɗaya suka tsinci Ɗaurin Auren amma kasancewar lahadi ne yasaka duk wanda ya samu gayya yayi ƙokari wajen ganin Ya amsa ta, taro yayi taro inda da albarkar jama'ar gurin Waliyin Haidar ya karba masa Auren Kiswa akan sadaki naira dubu ɗari biyar daga hannun Waliyinta,inda shi kuma waliyyin nata ya bada Aurenta bisa shedun mutanen da suka hallarci wannan Ɗaurin Aure mai Albarka,wani irin yanayi na farin ciki da Haidar ya tsinci kansa abun ba'a magana yayin da Saleek wanda yazo a daddafe yaji Abun ya saukar masa kamar Aradu,a haka dai ya ke ta faman washe baki gefen Abban sa wanda Shima nasa bakin ya kasa rufewa . Ana ɗaura Aure maganar ta isarwa mutanen gida inda take masu hancin guɗa suka kama,Kiswa dake zaune bakin gado cikin wani irin sassanyan ado kuwa ji tayi kirjinta yayi wani irin mugun bugawa,Kallan ta Dada tayi tana mai shafa mata baya tace"Alhamdulillah,maza kiyi sujjada ki godewa Allah da ya kaiki wannan matakin da kowacce mace take san ta ganta Akai."babu musu Kiswa tayi abunda Dada ta umarceta tana mai nunawa ubangiji godiyar ta da ya nuna mata wannan ranar da ta daɗe tana dako,guɗar da aka ɗauka sabuwa ce daga waje ta ja hankalin su,Baba Baraka ce ta shigo tana mai cewa "gafa mahaifiyar Haidar nan da tawagarta sun kawo akwatin Kiswa"Tashi Dada tayi tana mai cewa ,akaisu ɗakin masaukin baƙi za'a zo a tarbesu,hakan kuwa akayi inda sukayi musu tarb'a cikin mutunci da karramawa,kaya kuwa kamar za'a buɗe shago,Ummi ce ta nemi ganin Maman Kiswa domin gaisawa da ita sannan tayi mata godiya na haifan ɗiya kamar Kiswa wadda ta tafi da dukkan wata soyayyar Haidar,sanarwa da Mama akayi inda ta kimtsa tace a rakota dan itama tana san ganin Mahaifiyar Haidar domin tayi mata godiya da bata amanar ɗiyarta. Sallama Ummi tayi inda sallamarta ta katse sakamakon ganin Mama yayin da amsar Mama da farin cikinta ya katse ganin Wadda tayi sallamar a matsayin sirikarta . Tashi Mama tayi tace"wa nake gani kamar Hajiya zainab?"da mamaki Ummi tace nice Zubaida ba dai kece mahaifiyar Kiswa ba, Ƙaramun murmushi Mama tayi kafun tace"yanzu na fahimta sannan kema nasan Kin fahimta,wannan Auren dake tsakanin Kiswa da Haidar shi da zuba ruwa a rariya Ya tsiyaye haka yake ,dan Wallahi babu shi bama zai taba iyuwa ba".da sauri Ummi ta shigo ciki tana cewa"kar kice haka mana Zubaida,farin cikin ƴa ƴan mu ne kar mu bata da hannun mu"ƙarasawa tayi ta kama hannun Mama idanunta sun fara kawo ruwa..ƙwace hannu Mama tayi tace"tun ran gini tun ran zane wallahi indai nice na Haifi Kiswa wannan Auren babu shi ba zai taba zama da Akwai ba har abada". Dan dan dan dan dan dan Shin meke shirin faruwa ne? Muhaɗu a littafi na biyu domin jin Mai ke shirin faruwa mene zai faru,kamar kuma yarda na sanar a book 1 book 2 na kuɗi ne kan 300N kacal. 0264267657 Gt bank Amina jamil Adam Shaidar biya 08130229878. Ku zo maza ku biya kudin ku domin a cigaban da tafiyar daku❤ Nice Take a kullum CHUCHUJAY ✍️ (Amina jamil Adam) ❤