[7/16, 3:53 PM] S Reza: *_TSINUWAR UWA_* _By S Reza ✍️_ *First class writer's asos...* *_GARGAƊI⚠️_* _Kuskure ne yin amfani da wani bangare daga cikin wannan littafin ba tare da izini ba. Ban yarda wani ya sauya ko abu ɗaya daga cikin saba. Haka zaluka idan na kama wani/wata ya ɗora min littafi a YouTube channel ba tare da izini ba zan ɗauki mummunan mataki a kansa wanda ba zai masa daɗi ba🙏_ *My Whatsapp chanel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *_TAMBAYA DAGA MAI RUBUTU ⁉️_* Shin wai me yake kawo yin tsinuwa? Yaya ma ake yin tsinuwar? Laifin ƴaƴa ne ko laifin iyaye ne? Shin ma wai da gaske ne ana yin tsinuwar? To idan anyi me ke biyo bayan yin tsinuwar? Shin da gaske tsinuwa na kama wanda akaiwa tun anan gidan duniya ko sai an je lahira? To shi wanda yayi tsinuwar yana wanyewa lafiya ko dai shi ba shi da laifin komai? Shin kun taɓa ganin rayuwar wanda iyayen sa suka tsine masa? Idan kun taɓa gani to yaya rayuwar take? Yana yin nasara a rayuwarsa ko dai taɓewa yake yi? Mu buɗe kunuwa mu ɗauki darasi mai muhimmanci a wannan tafiyar, Kuzo mu shiga cikin wannan littafin na TSINUWAR UWA wanda nai masa taken DAMA TA UKU, domin jin amsoshin duk waɗannan tambayoyin. Bada ɓata lokaci ba duk kanku zai buɗe in sha Allah. *Page one* 1️⃣ ***** _MABUƊI_ Gawa ce kwance a tsakiyar gidan wanda mutanen dake kan gawar basu fi mutane hudu ba, tsaye suke kowa fuskarsa babu alamun wannan damuwar da fuskar wanda ya rasa wani nasa ke nunawa na Alihini sai mutum ɗaya da kallo ɗaya zakai masa ka gane yana cikin damuwa. Namijin ne ya ƙara faɗin "Aje a kira maza su zo su fita da gawar nan domin wallhi babu wanda zai mata wanka bare ma wai aje ga yin Salla, idan kuwa ba'a samo masu kaita ba to wallhi tona rami zamuyi a ƙofar gida mu turata ko kuma muje mu jefar da ita a shara, ku mubar mutanen ƙofar gida su shigo susan yadda zasu yi da ita. Ya faɗa yana nuna gawar da kuma hanyar waje da kana iya jin ihun mutane daga waje alamar ana son shigowa cikin gidan. Ɗaya Namijin dake kusa da shi wadda shine mai ɗan nuna damuwa ya ce "Dan Allah ranka shi daɗe mu taimaka ko wanka ai mata kuma mu sallaceta domin nema mata rahamar Ubangiji domin shi mai yafiya ne, dan Allah ranka shi daɗe ka daure? Mutumin da kana gani kasan bashi da alaƙa da gawar ya faɗa yana kallon wanda yayi magana da farkon. Kafin wanda aka kira da ranka shi daɗe yayi magana matar dake tsaye tana wani irin kuka wanda ba zaka gane kukan me take ba, domin babu alamar wannan kukan na alhinin rabuwa da wannan gawar ne. Ta ce "Duk wanda ya sallaci gawar nan Allah ya isa ban yafe masa ba a cikin ku,kai kuma bako, ta nuna mutum da ya gama magana yanzu, idan baka fita kabar gidan nan ba zansa samari suyi maka dukan tsiya, taimako ne na kawota gida kuma ka kawo angode, dan haka ga hanya. Kuma kafin minti biyar wannan gawar ta bar min cikin gida. Matar da kana gani kasan mahaifiyarsu ce ta faɗa idanuwanta duk sunyi jaa, ga wani irin kuka da take yi mai tafiya da imanin mai kallo da sauraronta. Tana faɗa ta shige cikin gidan ba tare da ta ƙara bi ta kan su ba. Ganin da gaske fa mutumin na bazasu suturce wannan gawar bane yasa mutumin ya fita waje ya tarar da mutane ƴan anguwa duk sun tsaya sai kananan maganganu suke yi, wasu na zage-zage akan sai afitar da gawar daga cikin unguwar, kai ka rantse ba gidan mutuwa suka zo ba. Wasu ma har dariya suke suna kallon waya da alamar dai wani abun da ya sha fi mutuwar suke kallo. Da ƙyar yayi ƙarfin halin kiran wasu samari dake gefe akan su zo a ɗauko gawar a kaita. Samarin da suka zo gurin ba da niyyar kaiwa gawa ba sai domin muna furci da ganin yaya za'ayi da gawar wannan. Cikin iskanci da isgilanci samarin suka fara faɗin "Kai wallhi babu shegen da zai kai gawar nan cikin maƙabartarmu, wallhi ba'a isa ba, dama abun da muke jira kenan mu gani, kawai a bamu ita muje mu yasar da gawar ashara kawai. Ganin yanda suka hayayyaƙo masa ne yasa ya koma ciki da sauri yana zubar da hawayen takaici yana kai co da wannan rayuwar ta wannan yarinya. Sosai mutane ke dukan ƙofar gidan a kan a basu gawar ko su ƙona ko suje su yasar da ita. Yana shiga gidan ya kalli wannan na ɗazun da yace baza'a mata wanka ba ya ce "Yallaɓai dan Allah dan soyayyar ka da Manzon Rahman kuzo mu kamata mu binne ta haka koda babu wankan dan Allah? Mutumin mai suna Bala ya kalleshi ya ja tsaki ya ce "Ai kaji abun da mahaifiyarmu ta ce, kuma ma koda bata ce ba to wallhi babu ni babu wannan gawar da Allah ya tsinewa. Yana faɗa ya juya shima ya bar gurin. Gurin ya rage mutum biyu wato Nasiru wanda ya ke ƙani a gurin Bala sai shi wannan mutumin da ko sunansa basu sani ba. Mutumin mai suna Sani ya kalli Nasiru ya ce "Mu kama ta koda mu biyu ne mu kaita maƙabartan nan please dan Allah. Da ƙyar dai Nasiru ya taimaka suka yi kama-kama su biyu suka ɗauki gawar da babu wanka babu salla, ko makara bata samu damar shiga ciki ba, daga ita sai tsinma da aka naɗe ta a ciki, daga inda kake kana iya hango fuskar gawar wance tayi fari kamar ka kira sunanta ta amsa, sai gefen fuskarta ta ke fitar da jini ƙan-ƙadan. Haka suka fita da ita waje ai kuwa suna fita samarin nan kowa ya tashi ya fara tofa albarkacin bakinsa. Take gurin ya rikice da hayaniya suna tare hanyar da za'a fita da gawar. Kowa na ƙoƙarin kai hanu domin yakico gawar har dai suka fi karfin su Nasiru take sai ga gawar ta faɗi tim a ƙasa. Nan ma basu tsaya ba suka ci gaba da fincike ɗan suturar da ta samu na tsinma har sai da suka yage shi, ya rage da ga ita sai kayan jikin ta, shima dai wasu daga ciki ne suke ƙoƙarin rabata da su. "Inna'ilaihi wa inna'ilaihi raju'un, wannan wacce irin mutuwa ce haka wacce tun a duniya babu sauƙi, wannan wani irin tonon asiri ne haka, haba al'umma ba kwa tsoron Allah ne? Shin meye hakan kuke yi, idan ma laifi tayi ai tsakanin ta da Ubangijin tane ba kuba, dan Allah ku dai na wannan abun da kuke yi sam bai dace ba kunji? Cewar wani da ya kutso kai yaga abun dake faru wanda daga gani kasan shima baƙone a cikin unguwar. Ɗaya daga cikin samarin ya ce "Wallhi malam idan ka ƙara magana akan wannan gawar kaima zamu haɗa da kai, baka san komai game da ita ba kawai kaja baki kayi shiru. Haka mutumin yaja bakinsa yayi shiru ganin yadda suka hayayyeƙomasa kamar zasu cinyesa ɗanye ba gashi. Haka dai Sani da Nasiru suka shiga ɗauƙar gawar suna tafiya samarin na ƙoƙarin rabata da kayan jikinta, tana faɗuwa suna ɗauka har suka kusa isa maƙabar tar, daidai anzu kan babban titin wanda sai an tsallaka kafin akai ga maƙabartar ne samarin sukayi nasarar yake mata gefe ɗaya daga rigar jikinta wanda hakan yasa su Nasiru sakin gawar a ƙasa ta ƙara faduwa a kan titin, nan take aka fara dambe da zage-zage a gurin wasu na ganin hakan bai dace ba, wasu kuma na cewar wallhi sai sun wulakanta wannan gawar tun a gidan duniya. Sosai ake kutuntumo ashariya irin ta ƴan iskan anguwa, Sani dai sai kuka yake yana tare duk wanda ke son zuwa ya taɓa gawar. Nan dai al'umma suka ƙara taruwa sosai kasan cewar an zo kan titi, motoci kuwa dole suka faka kowa yana zuwa kallo, duk wanda yazo yaga wannan abun mai kama da almara sai ya yi salati. An kwashe a ƙalla mintoci talatin ana abu ɗaya, akan titunan, ga bayin Allah a mota da mashin an hana su wucewa. Haka dai har suka zo bakin makabartar nan ma dai aka ƙara tsayawa aka yi rikici sosai kafin suka samu damar shiga da ita, kasancewar yanzu masu taimakon ganin an binne gawar sun ƙara yawa, ai kuwa zo kaga al'umma iya kallonka, amma babu abun dake fita daga bakukan wasunsu sai zagi da aibata wannan gawar. Ana zuwa nan ma dai jefar da ita a kayi a gefen ramin da dama a haƙe yake. Ga shi dai a cikin maƙabarta ake amma anki ayi shiru sai surutu kowa ke yi, su wai a dole baza'a binneta a maƙabartarsu ba, ganin dai bazasu bari a binne ta bane yasa Sani kamo ƙafafuwan gawar ya turata cikin ramin babu ko tsayawa bin ƙaidar yanda ake saka gawa, wani yayi saurin riƙota yana faɗin "Wallahi baza'a binneta a wannan makaranta ba. Ganin haka yasa Sani saurin turata gaba ɗaya domin a rufe kowa ya huta, ko ina ya shiga sai ya rage gefen kanta da ya tsaya bai ƙarasa shiga wannan tsakiyar ramin ba hakan yasa ya kamo kan kenan sai yaga kamar tana motsi, tsayawa yayi yana bin fuskarta da kallo sai yaga ta sauke wani dogon ajiyar numfashi tana ƙoƙarin buɗe ido. Ai kuwa da sauri cikin tsoro ya sake ta ta faɗa a cikin ramin, kafin ka ce me sai kawai aka fara turo ƙasa wasu harda duwatsu da ganye ana so a rufe ta a haka ba tare da an saka itace ko tukunya ba, shi dai Sani ya rikice domin shi kadai ya lura da abun da ya gani ɗin. Ana ihu na turo ƙasa har an daina ganin ta sai kawai gani a kayi ta ɗago daga cikin ramin ta saki wani ihun da yasa kowa dake gurin rikicewa kowa ya ɗau na kare, wani tsabar rudewa ma cikin ramin ya faɗo yana ihu! Ai kuwa ita da take neman mafita cikin rashin sanin komai ta kamosa, yana ihu tana ihu gashi taƙi sakar masa riga sai ma ƙara chakumeshi da take yi. Sosai maƙabarta ta rikice da ihun al'umma shi kuwa Sani sai da ya ɗan ja baya sannan ya tsaya ya fara karanto addu'o'i yana kallon ta, ita kuwa gawar da kyar ta iya ɗagawa daga cikin ramin ta saki wannan mutumin ai kuwa ya arce a guje itama ta fito bakin ramin ta kwanta ta fashe da wani irin kuka ta sunkuyar da kanta gashi jikinta duk ƙasa, ga gefen kayanta a fashe, sosai take kuka ko tsagaitawa ma bata yi, haka makabarta ta watse sai Sani dake gefe ɗaya yana ta kallon ta cike da tsoron Allah a ransa ganin ashe dai bata mutu ba har zasu binneta a haka, a fili ya ce "Tabbas Allah na son wannan baiwar tasa tabbas wannan wata aya ce ga al'umma, sannan wata dama ce gare ta ita wannan baiwar Allah, take ya tuno yadda kowa yake gudun ta, yadda kowa keson ganin a wulaƙantata amma gashi daga tashin ta kowa ya gudu, kamar ba ɗazu maƙabartan nan ke cike da mutane ba amma yanzu babu kowa da ga shi sai ita, shima Nasiru ya gudu yanzu haka labari ya ƙarade cewar gawa ta tashi. A hankali ya tashi ya nufo gurin ta ganin har yanzu bata ko daina kukan ba. Yazo ɗan nesa da ita ya tsaya ya ce "Assalamu'alaikum baiwar Allah? Ba ta ko ɗago ba, kuma bata dai na kukan ba. Ya sake cewa "Ki taso mu tafi ni ɗan uwanki ne". Nan ma dai bata ɗago ta kallesa ba. Ya ce "Farko munyi tunanin kin mutu ne, har munzo binneki amma Allah yayi ikon sa kafin hakan ta faru ashe baki mutu ba. Sai a lokacin ta tsayar da kukan da take yi, sannan ta bi jikinta da kallo, sai kuma ta ɗago da sauri ta kalli mai yin maganar, sannan ta fara bin faɗin gurin da take da kallo, lokaci ɗaya ta fara kakkare jikinta tana kallon ko ina dake gurin da take, ai kuwa take ta ƙara sakin wani ihu mai karfi ganinta babu maraba da tsirara kuma a cikin maƙabarta bakin rami, nan take ta zube a gurin sumammiya. *** LABARI Abuja New Aria. Da sallama ya shigo cikin gidan wanda yana shiga ya tarar da duk mutanen gidan zaune a Palo suna ta hira cikin raha da farin ciki. Suna ganin sa fara'ar dake kan fuskokinsu ta ƙaru da lilin ganin babban jigon nasu wanda yanzu shine matsayin uba a gare su, shi ne ke faɗi tashi da su duk rintsi duk wahala. Su shida ne a ɗan ƙaramin familys ɗin nasu, shi kansa Yaya Bala sai matarsa Anty Zainab sai ƙaninsa Nasiru wanda ke binsa, amma akwai tazarar shekaru tsakanin su sosai, sai ƙanwar Nasiru ɗin mai suna Siyama sai ƙanwar siya ma ɗin wacce itace auta a gidan nasu mai suna Fatima suna ce mata fati. Sai kuma mahaifiyar su wacce itama ke zaune tare da su domin Yaya Bala ya ce baya so yayi nesa da ita, hakan yasa suka saka haya a gidan da suke da wato a salin gidan mahaifinsu sukuma suka tare a nan. A kwai kyakkyawar fahimta a tsakanin wannan family ɗin sosai domin kuwa kansu a haɗe yake, mahaifinsu duk da ba mai arziki bane amma sosai ya jajirce a kan family's ɗin nasa shi da matar sa har Allah ya dafa musu kan su ya hadu. Idan kaga yanda suke zama ayi hiri abun gwanin ban sha'awa, har da Ita ma Anty Zainab haka suke janta a jiki babu wannan abun na sirikanci, har ma da ita Umma bata nuna mata komai na uwar miji. A gidan Yaya Bala ne ya gama karatu har ma yanzu haka yana aiki a wani kamfani na abokin mahaifinsu, to babu laifi dai baza'a kirasu da masu kudi ba, haka zalika baza'a ce musu talakawa ba, a baya dai kam suna daga cikin talakawan da kallo ɗaya za kai musu ka tabbatar da haka, amma bayan samun aikin Yaya Bala abun yayi sauƙi harma ya mallaki gida wanda ba wani babba bane, dukda aikin nasu sai ya samu ake yi. Shi kuma Nasiru yanzu haka wannan shekarar zai kammala karatun digiri dinsa ya fara bautar ƙasa. Sai itta kuma Siyama da take matakin difiloma shekarar ta farko kenan. Sai auta Fati da take secondary school aji biyu wato kusa da ta karshe kenan. Da sauri Fati ta ƙaraso gurin Yaya Bala tana faɗawa jikin sa tana masa Barka da dawowa sannan ta amshi jakar hannunsa tayi hanyar ɗakinsa da gudun ta, itama Siyama tasowa tayi ta rungume shi, shima Nasiru yayi kamar yadda tayi, itama Anty Zaibab haka tazo tayi masa kamar dai yadda suka saba. Bayan sun gama al'adar tasu ya samu guri ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Anty Zainab ce ta fara masa magana da faɗin. Yaya Bala yau kun daɗe fa tun ɗazu muke tsammanin ganin ka amma shiru, Allah dai yasa lafiya? Yaya Bala ya ce "Hanm lafiyar kenan, kin san gobe za'ayi wannan gasar da ake yi duk shekara a nan Abuja to kamfanin mu ne zai yi komai na shirye-shiryen abun da za'ayi, to shine fa muka daɗe a gurin ana ta shirye-shiryen tsara komai. Aunty Zainab ta ƙara cewa "Ikon Allah wato dai wannan abun shima har wani muhimmanci ake basa a wannan ƙasar tamu duk da irin halin rayuwar da muke ciki? Yaya Bala ya sake cewa "Wannan karan duk zan kwashe ku domin ku ga irin yadda wannan abun keda muhimmanci a wannan ƙasar, Nasiru dake danna waya shima ya ce "Ni abun da yake ban takaici ma shine ... Sai an gama zaɓar ita mai kyau ɗin amma idan ka kalli wacce aka zaɓa ɗin kamar ka yi amai, sai kace makafi ne masu zaɓar wallahi wata kamar jikar aljannu wai a hakan ita mai kyau. Duk suka kwashe da dariya daidai lokacin Fati ta dawo itama ta samu guri ta zauna. Siyama ta tsayar da dariyar maganar Nasiru ta ce "Haka fa yarinyar da aka zaɓa waccer shekara ga ƙaton goshi kamar gaban mota, ga hanci a shafe ga wani ƙaton baki, kai ni wallhi dariya ma yarinyar take bani har yanzu idan naci karo da hoton ta a social media. Nasiru ya ce "To zaki fara ko? Aunty Zainab da fara dariya ta ce "To ai gaskiya ne waye bai san haka ba, yarinya da ƙaton goshi wai ita sarauniyar kayu. Yaya Bala ya tsayar da hirar da faɗin "To ya isa haka koma dai yaya take Allah ne ya halicce ta, kuma shi ne ya bata nasarar, kuma ai duk kanku dai tafiku kyau. Yana faɗa ya ce "A kawo min abinci na ci tunda gulma ya hana a min tayi, kuma nasan duk kunci naku. Ya faɗa domin kawar da martanin da zasu bashi akan maganar da yayi domin kuwa yasan yanzu za'a fara. Anty Zainab ta amsa da cewar "Dama dai wanka ka fara yi tukun sai a Kawo abincin ko? Ya ce "To duk yanda kika ce Madam" Haka ta miƙe ta nufi ɗakin sa ta haɗa masa ruwan wanka kafin ta kirasa ya mike ya bar Nasiru da su Siyama a palon. Itama Siyama tashi tayi ta nufi ɗakin su wanda yake mallakinsu su biyu ita da Fati, ta na shiga ta tsaya tana kallon fuskantar a jikin madubin dake cikin dakin. A ranta tana jin cewar wallhi idan ta shiga wannan ƙasar kyawun da keyi Allah ko babu kwalliya sai tazo ta ɗaya, barin idan ta tuno da wacce tazo ta ɗaya a waccer shekarar. Sosai take cigaba da yin yanda taga ƴan matan na tafiya idan zasu fito gurin, yanda suke jijjuya mazaunansu da ma jikin su. Tana cikin haka Fati ta shigo, ai kuwa tana ganin ta ta ce "To sarauniyar kyau ta gidan Yaya Bala an fara ko? Ta faɗa tana ƙara shigowa cikin ɗakin tana ci gaba da kallon yadda yayar tata ke ta karkarya jiki kai ka rantse da Allah cewar gobe da ita za'ayi wannan gasar tana yin bita ne. Fati ta ce "To Anty Siyama mai zai hana kawai shekara mai zuwa ki shiga wannan gasar ko ke ma za..." Da sauri Siyama ta toshe mata baki domin kar ma wani a gidan yaji. Wannan shine burin ta, wannan shine mafarkin ta, taso ace yau duniya tasan da irin kyawun da Allah yayi mata, ita burin ta tayi zarra da kyawunta, wannan burin ya daɗe a ranta bata so kowa ya sanda shi hakan yasa ta shirya komai ba tare da kowa ya sani ba, tasan za'a sha mamaki idan akaji abun da tayi, tafi so kowa yaga komai a aikace wato gani da ido. Ta sha wahala sosai kafin azo wannan matakin saboda haka dole ta ƙara kiyayewa kar komai ya kwafce mata. Tasan ko a mafarki ƴan gidansu suka ji abun da tayi bazasu yarda ba domin tayi komai ne cikin iya taku da taimakon babbar ƙawa Aida. Sosai ita kanta take mamakin faruwar abun dukda cewar tasan bata bada wata hanya guda ɗaya da wani zai zargeta ko ya gane ta ba, to amma mai zai faru idan aka gano gaskiyar abun da tayi. A zuciyarta ta ce "Babu abun da zai faru a lokacin domin na cika buri na...✍️ Farko kenan kuma ɗan ɗano daga littafin tsinuwar uwa. Shering Please my fan's Duk mai son a tallata masa hajarsa zai iya tuntubar mu ta wannan number 08100785177 Love all Shering One love Comment's Shering Please By S Reza writer ✍️ [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA* *_By S-* Reza✍️_ *My Whatsapp chanel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a _First class writer's asos..._ *Page* 2️⃣ Siyama ta ce "Ke rufa min asiri so kike Yaya Bala ya karkaryani a gidan nan ne ko? Ta faɗa tana sakar mata bakin da ta toshe mata ta na ɗan sakin Itama Fati dariyar tayi ta na faɗin "To ai naga yanda kika ƙwallafa ranki a kan wannan gasar ne, tun fa lokacin da aka gama na waccer shekarar kike lissafin na wannan shekarar, sannan kuma kullum kece ke kushe wacce tazo ta ɗaya last time, to shine nake tunanin ko kina shirin shiga ne kema sai musani ai.Siyama tayi shiru tana tunanin garin yaya har Fati ta gano duk wannan! Dama ta baiyana komai ne! Siyama ta matso kusa da Fati ta kamo hannunta ta ce "Yauwa Fati na tambayeki mana dan Allah? Ta ce "Ina jin ki" Siyama ta yi murmushin da ke ƙara lotsa gefe da gefen kumatunta sannan ta ce "Tsakanin ki da Allah dani da wannan rayinyar da tazo ta ɗaya last time wacece tafi wata kyau? Tayi tambayar har tana wani juya idanuwa kamar mai jin bacci. Fati tayi dariya har tana tashi tsaye ta ce "Gaskiya kike so na faɗa ko karya? "Ai gaskiya na tambayeki ba ƙarya ba" Siyama ta faɗa da ɗan ɓacin rai. Sai Fati ta ce "To idan gaskiya ne tafiki kyau wallhi, idan kuma ƙarya ne kin fita kyau tallahi kawai dai ita goshi ne yayi mata yawa amma badan haka ba ai da ko gefen takalmin ta ma ba zaki gani ba. Tana faɗa ta yi hanyar waje da sauri domin kuwa tabbas tasan abun da zai biyo bayan hakan. Tana fita Siyama da ta gama cika tabi bayanta da kallo tana cije baki. Tana barin ɗakin Siyama ta ɗauko wayarta tana sauri ta danna kira, jin ta shiga ne yasa ta nufi ƙofar ɗakin ta tura ta tabbatar ta rufe sannan ta dawo kan gadon ta zauna, tana zama aka ɗaga wayar cikin masifa ta cikin wayar ake faɗin. "Ke dai wallhi baki da mutunci to ko kizo yanzu ko kuma nima na zare hannuna, haka mukayi da ke, to wallhi bazan ƙara tambayar sa ba. Siyama ta ce "Please mana Aida yayanmu ya dawo gida bazan iya fita ba, kuma ai mun gama komai ɗazu ku da kanku kuka ce sai gobe zamu haɗu ko? Cikin bala'i ta sake cewa "To ni na gaji da riƙon sa, ko kizo ko ya jiƙa miki aiki. Tana faɗa ta kashe wayar. Siyama ta dafe ƙirji tana jin wani sabon lukutin tashin hankali, to tayaya zata iya fita yanzu. Tabbas tasan idan Yaya Bala ya kamata babu wata-wata sai ya karya ta kamar yadda yake faɗa. Shiru tayi tana tunani sai kuma ta mike ta shiga toilet. Zaune suke dukkansu a gurin cin abinci suna ci suna hira gwanin ban sha'awa kowa sai murmushi yake, kana kallon su zaka ga haɗin kai da ƙaunar juna a tsakaninsu. Yaya Bala ya ce "Siyama gobe zaki zauna a gida tare da Umma ba zai yiwu a barta ita kaɗai a cikin gida ba kin san halin ta. Ya faɗa babu alamar wasa a fuskar sa wanda daga ji kasan umarni yake bata. Da sauri Siyama ta dawo da ruwan da ta ƙurɓa yanzu tsabar wani irin shok da ta shiga har tana kwarewa. Kallonsa tayi ganin yana ci gaba da cikin abincin sa alamar dai ya gama magana, ta mai da kallonta izuwa ga Anty Zainab sai suka haɗa ido. Take tayi ƙarfin halin cewa "Yaya dan Allah ga Fati ita sai ta zauna da Umma saboda..."Saboda ke ban isa da ke ba ko? Saboda ke kin fi ƙarfina ban isa na sa ki ba ko?. Yaya Bala ya katse ta yana kafe ta da ido. Ya ce "Siyama wallhi ina tausaya miki, ke a tunaninki bana kula da duk take taken ki ko? Allah kadai yasan abun da kike shirya wa idan kin je gurin wannan taron gobe, tsrona ɗaya kar kije kice zaki haɗu da wata daga cikin masu wannan gasar ganin yadda kike ta zubuɗi a kai, ɗazu haka naga lokacin da kika fita ban san ina kika ji ba, ke a tunaninki ban ganki ba ko, wallhi Siyama idan na kamaki da wata rawar ƙafa wallhi kin san halina, kuma zuwa ne bazaki yi ba, na gama magana. Yana faɗa ya tashi ya bar palon ran sa a mugun ɓace. Aunty Zainab ta ce "Ni narasa irin wannan zumudin naki wallhi, kullum sai kin yi maganar wannan gasar ai dole Yaya Bala ya tsargu, ko jiya sai da yamin magana nace kar ya ji komai ai ke kina da tunani, to kuma sai jiya ya ƙara kama ki kin fita, kawai ki haƙura ku kalla a gida ke da Umma. Nasiru da tun ɗazu yake ta faman surfa lauma yana dariya a ciki-ciki ya ce "Sis na miki alƙawarin ɗaukar komai a waya na nuna miki in sha Allah" Yana faɗa ya tashi ya nufi ɗakin sa yana mata dariya mugunta. Fati kuwa da dariya ta gama cika mata ciki amma tsoro ya hana ta sake su, amma jin abun da Nasiru ya faɗa yasa ta saki a barta tana toshe baki. Siyama ta tsaya shiru kamar wacce tayi suman tsaye. Ta kai minti biyu a haka kafin ta yi murmushi ta ci gaba da cikin abin cin ta bata ko bi ta kan Fati da Nasiru ba. Aunty Zainab dai sai kallonta take yi ganin bata sake cewa komai ba. Haka dai har suka gama cin abincin kowa ya shiga ɗakin sa. Ta na shiga ɗaki ta tarar da Fati ta kwaso takardun makarantar ta tana ta fama da karatu. Sosai Fati take a tsorace amma taga ko ta kanta bata bi ba, sai ma waya da ta ɗauka ta fara chatting. Tana cikin chatting ɗin kira ya shigo wayar ta, da sauri ta ɗaga ta ce "Ka ƙaraso ne? Tana faɗa ta kashe kiran ta ci gaba da chatting ɗin ta, sai da tayi a ƙalla minti biyar kafin ta tashi ta ɗora wata doguwar riga tayi hanyar waje. Tun daga nesa ya hango ta fuskar nan a haɗe sai wani cin magani take yi, sannan kaman dai yadda ta saba ko ɗankwali babu a kan ta, daga ita sai doguwar riga, kuma zai iya rantse wa da Allah iya wannan doguwar riga ce a jikin ta. Sosai shima yake mamakin kasan a kan ta. Na farko kamar yadda kowa ke faɗa a anguwar cewar ita ɗin ba sa'ar sa bace, kuma wallhi ba dan Allah take son sa ba, shi ma yasan da gaske Siyama ba ajin sa ba ce, domin ita ɗin irin matan nannane da ake kiran su da wanke hannu ka taɓa. Sannan ita ɗin ta kasance mai yin duk abun da ya raya mata, sannan bata kunyar yin abu idan tasan ya sha feta, amma yadda take nuna masa soyayya yasa ya ƙaryata cewar bata son sa, duk da cewa shi ɗin baƙi ne, kuma talaka ɗan talakawa kamar Ita dai Siyamar. Shi dai yasan idan yasaka ta yin abu tana bari kuma tana bashi lokacin ta da kulawa daidai gwargwado, to meye soyayyar, duk wanda ya samu wannan ai a tunaninsa ya gama samun soyayya amma mutane sunce ba sonsa take, to amma mai yasa mutane suke tunanin bata son sa ne. Shi dai yasan bayan yayanta Bala da mahaifiyarsu da suke tsoro kamar mutuwa, yasan babu wani mutum da Siyama ke jin maganar sa sai shi. Abun da mutane basu gane game da ita ba shi ne, ita tana da wasu irin ɗabi'u ne da ba zaka taɓa fahimtar ta ba har sai ka zauna da ita, shi dai yasan tana son sa kamar yadda take faɗa kuma yake gani a aikace, dukda cewar mutane suna ce masa dole ne shi mara wayo ba zai gane ba, amma shi ya yarda da haka. Tana isowa gurin da yake ta ce "Tun ɗazu kace zaka zo yanzu gashi har na fara jin barci". Ta faɗa fuskar nan a haɗe kuma da alamar shagwaɓa a muryarta dukda cewar kusan haka maganar tata take a koda yaushe. Ibrahim ya ce "Yau aikin wata mota muka samu shine ma ya kaimu har bayan sallar isha, yanzu ma fa ko gida ban shiga ba na ce bari nazo na duba ki karki jini shiru. Ya faɗa yana nuna mata jikin sa da yake kamar an fito da shi daga cikin kwalta. Sai a lokacin ta kalleshi taga da gaske ko wanka bayi ba. Ta ce "Ni dai wannan aikin naka wallhi matsala ta ɗaya da shi kawai ƙazanta, kalleka fa dan Allah kamar wani mahaukaci, ni dai kawai ka je gida zamu haɗu gobe kawai, na sha faɗa maka ka daina zuwa idan baka yi wanka ba, dan Allah tayaya zamu sake a haka kana warin baƙin mai. Ya ce "To ai sabo da alƙawarin da yi ne yasa nace bari nazo karki jini shiru kuma kiyi fushi. Te ce "To naji ya aikin? "Aiki fa babu daɗi Siyama ta sai dai muce Alhamdu lilliha! Daga haka tayi shiru shima yayi shiru. Ya ce "Wai me ke damun ki ne yau Siyamata? Yayi tambayar ganin yau gaba ɗaya taƙi sakewa Ta ce "Babu komai kawai bacci nake ji. Ya ce "No kina da damuwa please sanar dani dan Allah Siyamata, kin san bana son ganin damuwar ki" Ta kalleshi sosai irin kallon da ke sa mutum ya ji ya tsargu irin kallon da idan a kai maka dole kaji kamar an raina ka ne ko ana so a gano wata gaskiya a gare ka. Ta ce "Babu komai fa kawai barci ne ke damuna. Ya ce "To ai gobe Lahadi zan zo da rana sai muyi magana ko? Ta ce "Kamanta gobe...Kamin ta ƙarasa ya ce "Ranar zaɓen sarauniyar kyau ta ƙasa a nan Abuja ko? Tayi dariya ta ce "Ashe dai baka manta ba? Ya ce "Ya za'ayi na manta da abun da kullum sai an min zancen sa, nifa sai nake ganin ko waɗanda zasu yi wannan gasar basu kaiki zumudi ba. Ta ce "Ina son naga mata masu amsa sunan mata ne, da kuma kwalliya da tsan-tsar kyau. Ibrahim ya ce "Ni dai ba zan samu damar zuwa ba, da naje nima, amma zamu kalla a tibi ai ko waya. Ya na faɗa ya miƙa mata ledar da yazo da ita ya ce sai gobe idan kun dawo zan kiraki da safe. Ta ƙarɓa tana godiya ta shige gida ta barsa a tsaye yana bin ta da kallo, shi kansa wata zuciyar na sanar masa da cewar wannan yarinyar tafi ƙarfin sa, domin shi kansa yasan Siyama tana da buri sosai da son wadata, amma idan ya tuno da irin son da take masa sai ya ji cewar tabbas zai iya. Lokaci da ta isa ɗakin har Fati tayi barci, sai kawai ta fito Palo ta saka ledar da ya bata a cikin friza ba tare da ta bude ba, domin tasan ba zai wuce nana bane, kuma ita yanzu bata son cin komai. Ta na ajiyewa ta juya ɗaki tana shiga ta kunna wayarta ta shiga chatting. Washe gari tun da wuri Yaya Bala da anty Zainab da Fati da Nasiru suka shirya kasancewar da wuri zasu je gurin kafin a fara saboda Yaya Bala ne zai kara kula da gyaran gurin. Umma ce ta nufo gurin da suke tana kiran sunan Yaya Bala "Bala.. Bala.. "Da sauri ya amsa yana faɗin "Na'am Umma lafiya irin wannan kira kamar nayi laifi, dama yanzu nake shirin shigowa gurin ki kamun mutafi . Ya faɗa a ɗan tsorace har yana saurin baki, domin tabbas suna tsoron ta sosai. Ta ce "Bance karka ƙara zuwa da kowa gurin wannan shegen takar ba? Yanzu gurin da ake zuwa ana tallan tsaraicin shine zaka kwashi iyalinka ka kai su gurin fatan suma su ɗauko ɗabi'un ko? Yanzu tun da ka fara zuwa da su waccer shekarar shikenan kullum sai wannan yarinyar Siyama ta dame mu da zancen, ga shi daga shigar da take yi ya sauya, shine yanzu zaka kwashe su ku tafi saboda kaima ka zama lalacecce ko, to ban yarda ba. Yaya Bala ya ce "Haba Umma tallan tsaraici kuma, wallhi ba haka bane, kuma ba iya arna ne kawai ke shiga ba har musulmai suna shiga, dan Allah ki yi hakuri mu huɗu kawai zamu je banda ita Siyama ɗin domin nima ina tsoron zuwanta gurin. Cikin Masifa Umma ta sake faɗin "To idan ba tallan tsaraici ba ne me nene duk surar ji a waje, to Gara dai kai da Nasiru ɗin amma ko ita Fatima da matar taka ban yarda aje da suba, suma a bar min su a gida, kuje daga kai sai Nasiru.Da gyar dai Umma ta yarda aka haɗa da anty Zainab. Ai kuwa take Fati ta fashe da kuka tana faɗin dan Allah Umma. Amma Umma ta ce "Iana taron Allah ina taron mutanen nan kar su ɓatawa yarana tarbiyya. Haka kuwa a kayi su uku suka tafi aka bar Siyama da Fati a cikin gidan fati sai kuka take yi kamar ranta zai fita. Ita kuwa Siyama wanka tayi ta shirya sannan ta saci hanya ta fita ba tare da kowa ya lura da fitar ta ba a gidan. Sosai gurin taron ya cika sai waƙoƙin da aka tanada domin gasar ne kawai ke tashi a gurin da harshen turanci. Sosai holl ɗin ya cika manyan mutane ne zaune kowa ya buɗe idon sa domin basu abinci da kallon kyawawan matayen da zasu baiyana a gurin. Gefe guda kuma ga alƙalai masu tantancewa a gefe sun sha bakaken kaya, ga wasu na'urori a gaban su sai danne-danne suke yi. Ɗaya gifen kuma ga Iyalan gidan Yaya Bala zaune a gefe ma'aikatan gurin kowa shida iyalan sa. Haka dai aka fara kiran sunan jaruman da suka samu damar zuwa wannan zangon na jaha-jaha. Nan aka fara kiran ƴar jihar Borno. Ta fito tana tafiya kamar ɗawisu, ga ɗinkin dai sai subahanllah! Rabin ƙirji a waje, ga kai babu ɗan kwali, ga shi dinkin doguwar rigar gefen ta a yage har zuwa cinya, tana sanye da wani kyalle mai kamar igiya a kafaɗar ta mai ɗauke da sunan jaharta ta Barno. Bayan ta gama duk wata girgiza da rausaya tayi ɗan jawabi a taƙaice sai aka kira ƴar Bauchi, itama sanye da irin shigar waccer. Haka dai aka dinga kira har aka zo kan ƴar Jigawa. Itama ta gana sannan aka zo ƴar Nassarawa , itama dai haka tayi nata, ai kuwa ana kiran sunan ƴar Lagos guri ya kaure domin kowa na mata zaton itace zata ci, babu laifi tasha kyau sosai, haka itama ta gama aka kira ƴar Abuja mai kiran suna ya ce "Siyam Olosha from FCT Abuja. Nan take kuwa ya zuba ido domin ganin wacce halitta ce zata wakilci garin Abuja, domin tabbas wannan shine karo na farko da wata musulma ta wakilci garin Abuja a tarihin gasar. Nan take Siyam Olosha ta fara fitowa cikin takun ta da ta koya tun kafin zuwan wannan ranar, sosai akai mata kwalliya wacce sai ka mata farin sani kafin ka gane ta. Lokaci ɗaya filin taron ya cika da tafi da shewa ganin wata irin halitta mai tafiya kamar shanshani ta baiyana a gurin, sosai kowa ke kallonta ganin ta ƙaramar yarinya. Haka ta iso filin gurin ta fara girgiza ko ina nata tana rausaya haɗi da murmushi, babu alamar tsoro ko kunya a tare da fuskar tata, kallo ɗaya kawai zakai mata kasan tayi kyau bana wasa ba. Ɓagaren Yaya Bala kuwa da Anty Zainab da Nasiru kallo ɗaya dukkanninsu sukai wa Siyama Alhasan su suka gane ta. Dukda kuwa sunji an kirata da wani sunan daban ba wannan ba. Cikin wani irin tashin hankali yaya Bala ke kallon gurin da Siyama ke karkaɗa mazaune, sannan ga duk wani sirrin da Allah yayi mata na ƴa mace nan sun gama fallasa kansu a waje. Bai tashi rudewa ba sai da yaji yadda Siyama ke zubo turanci tana magana tana gaisuwa ga shuwagabannin gasar da manyan mutanen da suka halarta da gwamnonin dake gurin. Shi kansa Nasiru abun neman hana shi nutsuwa yake yi, anty Zainab kuwa ta gama cika da mamaki, badan muryarta da taji da bazata yarda cewar wannan Siyama ce ba. Siyama Alhasan ce ta koma Siyam Olosha! Ta yaya? Anya ma kuwa ita ce, ko dai mai kama da ita ne? To waye kuma Olosha? Haka dai take ta zancen zuci, jin tana neman zaucewa da mamaki yasa ta ce "Yaya Bala wannan ba Siyamar mu ba ce? inaga mai kama da ita ce dai, domin Siyamar mu wallahi ba zata iya haka ba, kuma ai mun barota a gida ita, dan Allah kira mana Umma ko ita Siyama ɗin domin tabbatarwa. Cikin ihu da wani irin tsawa ya ce "Ya isa haka! Wacce idan ba ita ba, ke a tunanin ki a kwai abun da Siyama zata yi ne na kasa gane ta. Ya faɗa idanunsa na cikowa da ruwa na takaici da ganin irin tozarcin da wannan yarinyar ta jawo musu. Lokaci ɗaya Anty Zainab ta kafe Siyama dake ta murmushi ana daukar ta hoto da kallo, sosai ta kafe ta da ido tana son gano gaskiya. Tabbas ita ce ga yanayin dariyar ta, ga yanayin tsayuwar ta da ɗan dogon hancinta. Lokaci ɗaya itama ta fashewa da kuka. Shi dai Nasiru sai kallon ta yake yana ta tunani, ta yaya haka ta faru a garin yaya. Sosai a kayi taro na ban mamaki a cikin garin Abuja, wanda yanzu an gama komai sai faɗin sakamako, daga na ɗaya zuwa na uku sune keda kyauta, ta karramawa, sai kuma daga na huɗu zuwa na goma suma za'a basu tasu kyautar wacce bata kai ta ƴan farko ba. Daga na goma aka fara kira zuwa na huɗu. Siyama jin bata ji sunanta a cikin na goma zuwa na huɗu ba yasa ta haƙura domin tasan ta faɗi. Hakan yasa ta ɗaga kai ta kalli ƴan team members ɗin ta da jagororin su sai taga suma duk jikinsu ya mutu. Amma ƙawarta mai ƙara mata kwarin gwiwa tana daga mata hannu alamar in sha Allah bata fadi ba. Nan dai aka kira sunan wacce tazo ta uku wata Kirista daga garin Benue mokordi. Ana kira aka fara karanto tarishin matar da matakin karatun ta, da irin ƙoƙarin ta. Ana gamawa aka kira sunan ta biyu wato Siyam Olosha. Zo kaga ihu daga gurin ƴan team members ɗin ta harda masoyan da ta samu a gurin. Sosai itama ta fara kukan farinciki da murna. Hakan yasa ta fara ɗaga kai ko zata hango family's ɗin ta, amma ina duk inda ta duba bata hango kowa ba. Nan aka fara karanto tarishin ta itama da matakin karatun ta da inda take zaune. Ana gamawa aka kira ta ɗaya, wannan ƴar Lagos ɗin. Nan take aka basu takardar yabo da lambobin yabo da zunzurutun kuɗaɗe banda kyaututtukan da ta dinga samu a gurin, daga mota sai kuɗaɗe. Sosai Siyam Olosha ta bada mamaki domin wannan shine karon farko da ƙaramar yarinya kamarta ta shiga gasar, sannan kuma musulma kuma ta wakilci Abuja, sai hakan ya zama kamar ma itace tazo ta ɗayar domin tafi bada mamaki. Haka manyan mutane kowa sai hoto yake son ɗauka da ita ko ina sai kiran sunan Siyam Siyam Siyam ake yi...📝 (Muje zuwa masoya) Bana yin posting ranar juma'a da Lahadi kamar yadda kuka sani. Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza writer ✍️ [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* 3 _By S-Reza_ ✍️ *FCW* *My WhatsApp channel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Page 3️⃣* Sosai Siyama ta samu alheri ga kuma mutane masu neman lambar ta, wasu kuma burinsu suyi hoto da ita, haka dai al'umma suka hanata samun lokacin da zata zanta da ƴan team ɗin ta har sai da komai ya lafa. Shugaban team ɗin nasu mai suna Oga Fita shine ya fara zuwa gurin ta, yana zuwa kuwa ya ware hannuwa cikin farinciki itama baki har kunne ta shige jikin sa har yana ɗaga ta yana yawo da ita a sama kamar ƴar Baby, ya ce " You are the best Siyam! I no you can do it thank you Siyam! Ya faɗa yana ƙara ɗagata. Itama sai dariya take tana jin daɗin yabon da kowa yake mata. Bayan ya gama ne sauran ma suka zo suka fara nasu suna ta murna ana rungume ta. Ita dai tasan masu taya ta murna har zuciya, kuma tasan munafukai karmar dai wannan ta gaban nata mai suna Adawiya da ɗaya ƙawar tata mai suna Badawiya, tasan yarinyar bata sonta tun lokacin da Oga Fita ya fitar da ita akan ita zata wakilci team ɗin su, tun daga lokacin yarinyar ta fara gaba da ita, kuma ta hana sauran members ɗin ma, yanzu ma ta tabbatar da cewar basu ji dadin wannan nasarar ba, kawai dai babu yadda za suyi ne. Wani irin kallo Adawiyar tabi Siyama da shi, har tana cije baki, ita dai bata ko ce mata komai ba, domin yau ranar farinciki ce.Aida ce ta ce "Ke manta da ita aniyar ta ta bita, duk zakaran da Allah ya nufa da chara, to wallhi ko ana ruwan muzuru da shirwa sai yayi". Aida ita ce babbar ƙawar Siyama, kuma a bokiyar shawarar ta, sannan tafi kowa bada gudunmawa a wannan nasarar ta Siyama domin kuwa ita ke tsaya mata a komai duk da cewa itama taso ta wakilci team ɗin nasu amma Allah bai yi ba. Siyama tayi dariya suna ci gaba da hotuna. ****** *YAYA BALA* Ana gama komai ya samu ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin nasu ya sanar da shi zai tafi gida yanzu idan an gama komai sai yasa a gyara gurin, mutumin ya amsa da to in sha Allah. Haka Yaya Bala ya tattara iyalan sa suka bar gurin duk ransa a ɓace. Ita dai Anty Zainab jikinta ne yayi sanyi sosai tana so ta sake yiwa Yaya Bala magana amma tana tsoro, ko da suka zo zasu shiga motar sai da tace karyayi tuƙi a haka ya bata ko ya bama Nasiru amma Yaya Bala ya daka musu tsawa. Haka dai suka ja baki suka fara tafiya duk a tsorace. ****** *SIYAMA* Siyama kuwa basu bar gurin ba sai bayan sallar magriba, bayan sun gama amsar duk kyaututtukan su. Lokacin da suka isa office ɗinsu ko nace gidan su da suka saya na team ɗin su, sai Oga Fita ya nemi da Siyama ta kwana a nan zuwa gobe sai ta tafi, saboda yanzu dare yayi kuma wasu zasu iya bibiyar ta, duk da kuwa yasan bata kwana a gurin, kuma yasan duk wannan abun da take yi babu sanin iyayenta. Siyama ta ce ita ba zata kwana a gurin ba, gida zata tafi yanzu ma haka tsoro take ji. Haka dai Oga Fita ya sako ta a mota ita da Aida, bayan ya sauke Aida ne ya faka a gefen titi ya juyo ya kalli Siyama wacce ta yi nisa a tunanin halin da zata shiga idan taje gida. Cikin harshen turanci ya fara mata magana kamar dai yadda tun tuni ya saba akan ta bar gidan iyayen ta dawo nan da zama tana da kyau zata iya zama komai da ta ke son zama a duniya, kamar yadda tun farkon haduwarsu ta sanar masa da ƙudurinta, amma yanzu iyayen ta sun hana ta sakewa, bata ganin sauran ƴan matan da suke tare da shi ne. To duk idan yayi mata irin wannan maganar bata yarda domin ita batayi wannan ƙwarin kan da zata ma iya mayarwa da yaya Bala magana ba bare kuma ma Umma. Lokacin da ta tuno da Umma sai da gabanta ya faɗi domin ba karamin shakkar ta suke yi ba. Ya ce "Siyam yanzu ke ba kamar yarinya bace, ki sani yanzu sunanki da fuskar ki sun zagaya duniya, saboda haka yanzu kin fara zama salebiriti, babu inda zaki shiga a duniya da za'a wulaƙanta ki, kuma babu abun da zai iya gagaranki yanzu a gidan duniya. Kin ga yanzu kina da motoci sun kai goma, ga zunzurutun kuɗaɗe wanda har yanzu babu wanda yasan lokacin da zasu daina zuwar miki, saboda haka, ina so kiyi amfani da kuɗin ki ki jawo hankalin iyayenki, idan kuma basu yarda ba, to yanzu ba da bace, kizo duk irin gidan da kike so a garin Abuja zaki saya. Siyama dai sai jin sa take yi, tana sauraron shirmen sa, domin kuwa ita tasan ko giyar wake tashs ba zata iya duk wadannan abubuwan ba. Ita yanzu Babbar damuwar ta ma ta ƙarass gidan ko yankanta ne Yaya Bala yayi kowa ya huta. A haka Oga Fita ya kaita har ƙofar anguwarsu domin bata yadda yaga gidan su ba, Kallonta yayi ya sake cewa "Dubi unguwar da kike dan Allah Siyama, ki tsaya dai kiyi tunani. Yana faɗa ya mika mata wayar ta da take a kashe tun lokacin da ta isa gurin taron. A hankali ta tura ɗan ƙaramin ƙofar gin nasu mai ɗauke da wani tsohon get ɗan ƙarami ta shiga, ta kalli gurin da yake ajiye tsohuwar Motar sa amma bata ganta a gurin ba, lokaci ɗaya gabanta ya fadi, basu dawo ba kenan, ta ci gaba da tafiya tana jin gabanta na ƙara faɗuwa. Kafin ta ƙarasa cikin gidan taji ana kiran sunanta. A ɗan tsorace ta juyo jin muryar Ibrahim, ai kuwa dai shine, yau ma dai kamar jiya ko wanka bai yi ba, waɗannan kayan ne dai na aikin sa, dukda kuwa yace yau basu da aiki domin yau Lahadi ranar hutu ce, amma gashi da kayan aiki, take ranta ya ɓaci. Ya ce "Zuwa na kenan sai kuma na hango ki zaki shiga gida shine na kira ki". Ya faɗa yana murmushi yana binta da kallo ganin yanda yau ta rufe gashin kanta, ga kuma wani irin kyau da tai masa, ga doguwar rigar ta tasa bai taba ganin ta da ita ba. Sosai asalin kyawun Siyama ya baiyana wanda shi kansa sai da ya ƙara tabbatar da cewar gaskiya Siyama matar manya ce, domin shi wallhi sai yaga yau ma kamar ba zai ma iya kallon cikin idon ta ba tsabar kwarjini. Sai kawai ya tafi tunanin shin me Siyama ta gani a tare da shi tace tana sonsa, gashi baƙi, talaka ƙazami,mara wayo kamar yadda ake cewa, anya kuwa bai yaudari kansa ba, to dama yana da kuɗi ne sai yace sabo da kuɗin sa ta ke sonsa. Ta ce "I B (Kasancewar wani lokaci bata ce masa Ibrahim sai tace IB)jiya fa na ƙara tabbatar maka da cewar ka daina zuwa idan baka yi wanka ba, kuma gashi ka ƙara zuwa haka" Ta faɗa da ɗan damuwa a muryarta. Wani suna da ita ta saka masa wanda yanzu kusan duk unguwar haka suke kiran sa da shi, duk lokacin da ta kira sa da I B wani irin farin ciki yake ji. Ya ce "Wallhi aikin motar jiya ne, sai yau muka ƙara sa ta, ina gida oga ya kirani wai dan Allah muzo mu ƙarasa masa yau zai tafi da ita ne, to shine fa naga yauma dare yayi, kin ga kuma idan takwas ta wuce bazan samu damar ganin ki ba shine yasa na ce ko ganin ki nayi. Ya ƙarasa yana ƙoƙarin ganin ta ina suka dace da Siyama. Ta ce "To sannu da aiki, yau dai an gama da wannan motar kowa sai ya huta ko? "Hamm sosai fa, ai gobe idan na fara hutu sai rana ta fito. Ya faɗa yana dariya. Kafin tayi magana wayarsa ta fara ƙara. Yana dagawa ya ce "Ina zuwa gani nan. Siyama ta kalli wayar hannunsa, a fili ta ce "Wannan wayar dai kai jin daɗin ta kake yi ko? Ibrahim ya ce "To yaya zan yi ko bana jin daɗin ta, bari dai kuɗi su shigo in sha Allah zan samu ƴar babba nima na siya ko fecbook da TikTok ɗin nan da ake faɗa nima na fara. Ya na faɗa ya miƙa mata ledar hannunsa yana fadin sai da safe. Karmar ta ce a'a, amma ta amsa tana masa sai da safe ganin yana ta sauri. Ya juya yana ɗaga mata hannu itama haka har ya tafi. Sai da taga ya fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta nufi ciki. Da sallama ta shiga cikin falon, sai dai bata ga kowa ba, hakan yasa ta fara sanɗawa tana yin hanyar shiga ɗakin su. Har ta shiga babu wanda ya ganta. Tana juyawa ta ga Fati a gefen gado tayi kuka har idanuwanta sun yi jaa! Tana shiga itama Fati ta ɗago ai kuwa suna haɗa ido Fati ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana faɗin Aunty Zainab ta ta ta rasu! Cikin wani irin shok da faɗuwar gaba Siyama ta saki ledar hannunta tana tambayar ta wacce anty Zainab ɗin, mutuwa kamar yaya me take nufi? Fati ta ce "A hanyar dawowarsu daga gurin gasar ne sukayi hatsari shine wai ita ta mutu, yaya Bala kuma yana kwance rai a hanun Allah ga Nasiru shima ya samu karaya a kafaɗa da hannun". Siyama ta kurma wani uban ihu tana kiran sunan Yaya Bala da anty Zainab. Tashi tayi ta nufi sashen Umma tana tafiya tana kuka koda taje sai ta tarar da ƙofar Umma ɗin a rufe alamar bata gidan. Da sauri ta koma ɗaki tana tambayar fati wani asibiti suka tafi. Nan ta sanar mata da yadda itama taji wai kusa da gurin da aka yi taron ne domin waɗan da suka kira number Umma sune suka fadi sunan asibitin. Haka ta shirya ta saka hijjab ɗin ta ta fita, bayan ta sanar da Fati cewar ta rufe gidan. Ko da ta fita wani asibiti da ke kusa da gurin da a kayi taron ta fara zuwa, ai kuwa tana ta tambaya aka tabbatar mata da cewar gurin ne. Koda taje asibitin ta tarar da Umma nata kuka domin da gaske anty Zainab ta rasu, sai yaya Bala da har zuwa yanzu bai farka ba. Umma tana ganin Siyama ta ƙara fashewa da kuka. Haka Siyama tazo suka zauna sai sharar kuka suke yi A nan asibitin suka kwana sai washegari Umma ta tafi gida ta bar Siyama a gurin, kuma har lokacin babu wanda ya farka. Tana zaune a gurin kafin Umma ta dawo ita kuma ta ciro wayar ta. Ganin babu abun da take yi ne yasa ta kunna Data. Lokaci ɗaya ta dinga ganin saƙonni suna shigowa tako ta ina fecbook da TikTok da Whasopp. Sosai hankalin ta ya tafi kan wayar har bata san lokacin da likitan ya shigo ba. Har sallama yayi amma bata ko sani ba.tana kallon daga iya jiya zuwa yau ta samu mabiya a TikTok da fecbook na ban mamaki har yanzu ma ƙaruwa suke yi. Tana shiga Whasopp taga group ɗin su na ƴan team ɗin su, sai posting hoton ta na jiya a keyi, ga sitatus ɗin mutane ma, nan take taga message ɗin Oga Fita tana shiga tagan su da yawa, ta fara buɗe na farko taga saƙon magana ne yana cewa ta ɗora wannan bidiyo ɗin da hotuna a shafin ta na TikTok da fecbook tayi jawabi domin har mutane sun fara buɗe account da sunanta, duk da cewar dama tana da nata mai suna Siyam Olosha wanda babu wanda yasan ta da shi a gidan su. Ai kuwa nan take ta fara posting, kafin ta yi na biyu ta fara samun like da comments, bata da lokacin dubawa hakan yasa tana gamawa da fecbook ta koma TikTok, shima bayan ta gama sai ta fara shiga comments tana kallon masu yabo da zagi. Likitan ne ya ƙara faɗin "Madam kina tare da ni kuwa?" Sai a lokacin ta jisa. Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace ta ce "Yes ina tare da kai". Ya ce "Ina ta magana kin mai da hankalin ki izuwa waya, alhalin zaman jinya kike yi. Kafin tayi magana taji kira na shigowa wayar ta amma ta share ta ce "Eh ina yin wani abu ne" Sosai likitan ya kafe ta da ido kamar dai itace yarinyar da tazo ta biyu a gasar jiya, kamar kuma ba ita ba, domin daga jiya zuwa yau indai kana yin media to zaka ci karo da hotunan ta. Siyama da ta lura da irin kallon da yake mata sai ta ce "Yanzu me ake buƙata?" Cikin diriricewa ya ce "Amm umm dama ɗaya ne ya farka daga cikinsu, kuma yana buƙatar abinci mai ruwa-ruwa kafin mu ƙara masa allura. Siyama ta kai kallonta izuwa gurin ai kuwa suka haɗa ido da Nasiru da ya buɗe ido yana kallon ta tun ɗazu ita bata sani ba. Ta ce "Sannu yaya Nass ya jikin? Me zaka ci? Ina yake maka ciwo? Nasiru ya lumshi ido ya buɗe yana jin jikinsa ya masa nauyi. Sallama suka ji anyi Umma da wasu daga cikin kawunansu suna biye da ita, sai Fati da ta ɗauko kwanukan abinci. Ganin haka likitan fita yana satar kallon Siyama. Daidai lokacin shima yaya Bala ya buɗe ido yana bin ɗakin da kallo. A hankali ya ce "Ina Zainab?" Kawunsu ƙanin mahaifinsu mai suna Kawu Inuwa ɗan bala'i ne na gaske, yana da faɗa sosai domin duk faɗan Umma tana tsoran sa, shine ke bin Gambon Hassan da Hussaini duk da ita Gambon Allah yayi mata rasuwa, shima Al-Hasan ɗin wato mahaifin su Siyama shima ya rasu, yanzu daga Kawu Inuwa ɗin sai Baba Husaini ɗin. ya ce "Ka natsu tukunna Bala yanzu ta lafiyar ka ake yi". Ganin Bala yaƙi tsayawa ne yasa suka kira likita, nan ya sanar musu cewar babu abun da ke damun sa, kawai karya ce a hannun kawai, kuma an ɗaure. Shima ɗayan karaya ce hannu da ƙafaɗa shima an ɗaure. Sai da aka zuba musu abinci sukaci ƙadan kafin aka ƙara musu allura likitan yace zuwa gobe in sha Allah za'a sallamesu, sai suje su cigaba da jinyar hannunsu a gida. Sai da barci ya ɗauke su kafin kawu Inuwa da sauran suka koma gida aka bar Umma da Siyama da Fati. Umma ta kalli Siyama ta ce "Jiya bayan fitar su Yayanki ina kika je? Umma tayi tambayar ne badan tasan komai ba, domin ita bata ko kalli shirin ba kasancewar babu wuta. Siyama ta ɗago daga chatting ɗin da take yi da Aida ta kalli Umma. Umma cikin faɗa ta ce "Ina miki magana kina danna waya tsabar raini ko Siyama" Ai da sauri ta kashe wayar tana dawo da hankalin ta ga Umma. Umma ta sake faɗin "Ina kika je baki dawo bar har wannan abun ya faru tun safe? Siyama ta kalli Fati taga itama ita take kallo sai kawai ta ce "Gurin taron nima naje". Umma da dama tasan dole gurin taje, domin yadda Siyama ta ƙwallafa wannan gasar a ranta tasan ko masu shiga gasar ƙare kenan. Umma ta ce "Amma ai Yayanki ya hana ki ko, kuma nima na hana ki, amma kin nuna mana cewar bamu isa ba ko? Siyama kibi duniya a hankali, yanzu gashi kina kallo yadda ake mutuwa cikin rashin shiri, yanzu da nice na mutu ina fishi da ke Siyama yaya zaki ji! Lokaci ɗaya gaban siyama ya faɗi jin kalmar mutuwa, ga kuma tunowa da yanzu fa da gaske Anty Zainab ta rasu ko. Umma ta ci gaba da cewa "Ki duba yadda yake fadi tashi akan mu, shi kansa ba wani samun kirki yake yi ba, amma haka yake kokari damu, yanzu ko wannan ba zaki duba ba ki riƙe maraicin kiba Siyama, yanzu ba kya tsoron wani abu ya dameki a hanya da kika tafi har gurin ke ɗaya bayan Uwar da ta haife ki tace karki je?. Daidai lokacin Siyama taji ƙarar shigowar message a wayarta hakan yasa ta kalli wayar ba tare da Umma ta kula ba, shigar kuɗi ne cikin account ɗin ta wanda tun ɗazu take jin shigar su. Haka dai Umma tai mata faɗa sosai wanda Fati dake kusa da ita tasha kuka ita kuwa rabin hankalin ta naga wayar ta ne. Haka dai Bayan farkawar su Nasiru Umma da Fati suka tafi gida. Har lokacin yaya Bala bai ko yi wa Siyama magana ba, yakan dai saci kallonta lokacin da take chatting yana ganin irin dariyar da take yi ko tayi murmushi. Sosai ya shiga tunanin meye laifin sa a riƙon da yayiwa Siyama, sannan tayaya har ta shiga team har ta samu damar halartar gasar batare da ta bar wata alama ko ɗaya da zai gane ba, ta yaya duk irin tsaron da ya saka mata, sosai wannan tunanin ke masa yawo akai. Chatting suke yi a group ɗin su wanda ake sanar da ita dole sai tazo gurin aikin su wato shagonsu damin sa hannun akan komai nata, kuma ta warewa team nasu, kuma ga wasu manyan mutane dake son ganin ta. Ta ce duk Aida ta wakilceta amma Oga Fita yace, awa ɗaya aka bata ta shirya tazo, kuma ta tabbatar ta sha wanka domin ba ƙananan mutane bane zasu zanta da ita. Haka tace to zata zo.tana ɗago kai taga Yaya Bala yana kallon ta hawaye na zubo masa ta kumatu, ta kashe datar tana kallon sa, taje kusa da shi tana share hawayen ta kamo hannunsa, lokaci ɗaya ya dawo daga tunanin da yake ya riƙe mata hannun yana faɗin "Zainab baki mutu ba ko, kin dawo gare ni ko. Yana faɗa ya haɗa ido da Siyama ya sakar mata hannu ya juya kai gefe. Sai a lokacin Siyama ta ce "Dan Allah yaya kayi haƙu" Da sauri ya daga mata hannunsa mara ciwon ya juya baya. Siyama ta fashe da kuka tana toshe baki. Ta kalli Nasiru ta ce "Dan Allah yaya Nasiru" shima ya dakatar da ita. Ta juya ta fita daga ɗakin ta shiga Gurin likitan ta ce "Yanzu babu wani abu da ake binmu ko? likitan ya ce ba komai, sai maganin da zaki siya idan sun koma gida su dinga sha, amma sai zaku tafi za'a rubuta muku. Ta ce "Suma rubuta tun yanzu. Ai kuwa take ta fidda kuɗin maganin dama ita ce ta biya na komai, sannan ta kama hanyar gida. Ganin tana tafiya ana kallonta ne yasa ta samu wani guri a gefen asibitin ta tsaya ta kira Aida ta ce tazo da Mota yanzu ta dauke ta, bayan tai mata kwatancen gurin da take. Ai kuwa bata daɗe sosai ba sai ga ta nan da Mota, tana zuwa ta buɗe mata gidan gaba ta shiga. Aida ta kalleta ta ce "Ina muka nufa? Siyama ta kwantar da kanta a kujerar matotar tana tuna faɗan da Umma tai mata, ta ce "Muje gidan ki" Aida ta juyo ta kalleta bata ce komai ba har suka isa gidan Aida ɗin da ta kama take zaune ita da ƙanwarta da ƙanin ta Jamila da jamilu. Kana shiga gidan Aida kasan ka shigo gidan Model, hotunan ta ne ta ko'ina a cikin palon, haka cikin ɗakinta, hotuna dai irin na Model wasu doguwar riga wasu iya kayan barci. Ganin Siyamar ta kwanta a kan gado ne yasa Aida faɗin "Amma kinsan awa ɗaya Oga Fita ya baki ko? Siyama ta ce "Ban san kayan da zan sa ba, kuma ni barci naje ji wallahi na gaji tun jiya ban huta ba, kawai kije a maimako na please. Siyama ta faɗa Domin tasan tabbas Aida ita ce komai nata, zata iya rantse wa da Allah akan cewar duk wani abu nata Aida ta fita sanin sa, haka zaluka wasu abubuwan ma duk Aida ɗin ce ke mata su, haka ko a team ɗin su idan kaji Aida na faɗa to an taɓa Siyam ne. Aida ta ce "To dama waye zai tsaya jiran ki yaji kunya, ai daga yau zuwa sati daya duk na tana di kayan da zaki dinga sakawa, ai ke sai dai a barki da halinki, Malama ki tashi ki shiga wanka ko wankan ma sai na miki ne? Ta faɗa tana sauko da wata akwati mai kama da Zakara. Take ta buɗe shi ta ɗauko wata doguwar riga jaa, mai adon duwatsu sai ɗaukar ido take yi, gefe ɗaya kuma ga taƙalmi da jaka duk irin ruwan riga, ga wata sarƙa mai tafiya da imanin wanda yasan darajar sa, kana ganin kayan kasan a haka suke zuwa a cikin wannan akwatin. Siyam na ganin haka ta shige toilet ta faɗa wanka tana tuno yadda suka yi da yaya Bala ɗazu. Koda ta fito ta tarar da matar da take musu kwalliya tana jiranta, ai kuwa nan aka fara mata, tana gamawa ta saka kayan sannan Aida tai musu hotuna, nan take suka dora a Fage ɗin su. Sai da suka gama sannan suka fita izuwa gurin aikin su. Ita dai Siyama duk rabin hankalin ta na ga asibiti, ga shi bata sani ba ko anyi jana izar anty Zainab ko sai yaya Bala ya tashi, ko dai ɗazu da ƙanin babansu ya tafi aka je akayi, sai take ganin kamar bai dace ta bar gida yanzu ba, amma wata zuciyar take sanar da ita cewar ai yanzu zata dawo. A haka suka ƙaraso Team ɗin nasu....📝 (Muna tare daku kuwa masoya? Kuzo mubi Siyama a hankali muga ina take son zuwa) Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza write ✍️ [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza ✍️_ *FCW* *My WhatsApp channel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *PAGE 4️⃣* Shiru Siyama tayi a cikin motar tana kallon shigar da tayi. A hankali Aida ta ce "Lafiya dai ko?" Siyama ta sauke ajiyar zuciya ta kawar da kai gefe, ita da kanta tasan shigar da tayi sam bai dace da itaba. Ta ce "Lafiya ina ɗan wani tunani ne" Ka she motar Aida tayi ta juyo ta kalleta da kyau kafin ta fara bata baki har dai Siyama ta sauƙo. Duk da hakan wata zuciyar na sanar da ita bata kyauta ba, amma ta danne suka shiga cikin group din da tun daga bakin get zaka fara cikin karo da manyan motoci na Medels ɗin dake gurin da kuma mutanen da aka ce suna san ganin ta. *** *Yaya Bala* Cikin tsananin ɓacin ran da ya sarƙe masa zuciya yake tuƙa motar kamar zai tashi sama, Anty Zainab kuwa sai kuka take duk ta rikice da ganin wannan sabon al'amarin. Sosai wata zuciyar tata ke ƙoƙarin ƙin yarda da cewar Siyamarsu ce haka. Shi kuwa Nasiru gaba ɗaya ma shi halin da Yaya Bala ɗin ya shiga ne yafi tashar masa da hankali gashi sai gudu yake yaƙi yayi magana da kowa. Daidai lokacin aka kirasa a waya ai kuwa take ya kai hannu da niyyar ɗauka kuma gashi sun iso kan jakshon, bai ma san sun iso ba hakan yaba wata babbar motar damar hawa kansu, lokaci ɗaya motar ta komatse ta baya, yayin da itama babbar motar ta dungura gefe ɗaya. Lokacin da mutane suka iso gurin Nasiru ne kawai ke motsi, kafin minti biyar har motar agaji ta iso aka kaisu asibiti mafi kusa da gurin. Take likitoci suka tabbatar da mutuwar macen cikin su, sannan suka naimi da a sanar da wani nasu. Cikin ikon Allah kuma waya biyu aka samu ta Yaya Bala da Nasiru, sai dai wayar Nasiru ta fashe hakan yasa aka duba number da ya kira karshe. Number yaran wajan aikin su ne wanda ya kira lokacin da suke tafiyar, koda aka kira aka sanar dasu shine suka zo gurin. Shine suma suka kira number mamar su suka sanar da ita. Koda Umma ta ƙaraso sai ta cika asibitin da kuka, tana kiran sunan yaran nata, sosai ta fita a haiyacinta sai faɗin dama ta hana su zuwa wannan gurin amma suka ce sai sunje yanzu ga abun da ya sake su, sosai take ta zaro magana harma bata san tana yi ba. Sai da likitoci suka tabbatar mata da cewar suna lafiya kafin ta ɗan rage kukan, amma duk da haka bata daina faɗa ba. Ganin halin da take ciki ne yasa likitan bai mata maganar macen da ta mutu ba, sai ma tabbayarta ko zata kira mahaifinsu ko kuma wani Namijin. Jin haka yasa ta bada number Kawu Inuwa wanda aka kirasa shima yazo cikin daren. Nan likitan ya sanar da shi cewar a kwai mace ɗaya a cikin su kuma Allah yayi mata rasuwa. Haka suka je ya ganta sannan ya dawo ya sanarwa da Umma wacce jin haka yasa ta ƙara dawowa da sabon faɗa. "Sai da nace masa kar ya je da ita amma yace yaji ya gani, yanzu dan Allah mai zai cewa iyayenta, wannan wacce irin masifa ce, wannan abun na arna da gaba ɗaya ma saɓon Allah ne, abun da babu wani ɗan musulmi kuma ɗan kirki da ya fito daga gidan mutunci zai bar ƴarsa tayi, shine har kuke ɗaukar iyalai kuje kallo to ga abun da ya jawo muku, ni dai sam ban ji daɗin wannan abun ba, Allah ma dai ya tarwatsa taron mutanen da suka ƙirƙiro wannan kafurcin Allah ya isa ban yafe ba. Sosai Umma take kuka tana face majina, sosai mutuwar Anty Zainab ya taɓa ta, samun sirika irin Zainab a wannan lokacin sai an tona, yarin ya ce mai kawai ci ga na tsuwa, duk da irin faɗan da Umma keda ita amma hakan baisa kana yawan jin kansu ba, gasu a gida ɗaya. Haka ƙanin Kawu Inuwa ya fita da gawar Anty zaibab ɗin, basu Kaita gida ba sai suka wuce da ita babban masallacin domin tayi kwanan kaso a gurin. Acikin daren aka fara sanar da dangin ta da sauran abokon zama. Tun a daren likitan ya tabbatar da cewar karaya kawai suka samu ɗaya guri biyu ɗaya kuma guri ɗaya, sai kuma ɗan buguwa da suka samu amma ina sha Allah zuwa safiya zasu farka. Yana cikin barci yake mafarkin matarsa na cikin matsanancin hali, lokaci ɗaya ya buɗe ido da sauri yana bin gurin da aka kwantar da shi da kallo, ganin Umma da Kawu Inuwa ne yasa shi tambayar ina matarsa. Tun da yaga sun fara ce masa ya kwantar da hankalin da ya tabbatar da cewar ba lafiya ba, yana ƙoƙarin rufe ido ya haɗa ido da Siyama, wacce take zaune ta kusa da hannun sa mai karayar. Kallon ta yayi yaga komai na dawo masa. Haka dai bai ƙara cewa komai ba har suka ci abincin da aka kawo musu, sannan barci ya ƙara ɗauke sa bayan an masa allura. Lokacin da ya ƙara buɗe ido sai ya sauƙe a kanta ita kaɗai zaune a ɗakin tana kallon waya tana dariya. Sosai ya dade yana kallonta yana ƙoƙarin haɗa fuskar wannan ta gaban nasa da kuma wacce yaji jiya ana kira da Siyam Olosha. Sosai ya tabbatar da basu da wani banbanci sai dai wannan da take zaune a gaban sa yanzu hijabi ne a jikin ta waccer kuwa marabanta da tsirara babu nisa. A hankali yake lumshe ido yana budewa yana tunanin Allah yasa matarsa lafiya take. Yana cikin haka likitan ya shigo hakan yasa ya lumshe ido kamar mai barci. Yana ji likitan yana mata magana amma bata ji ba. Har sai da ya sanar da ita Nasiru ya tashi kuma abinci zasu ci kafin anjima. Likitan na fita ta shima ya sake buɗe ido.Yana farkawa itama tana satar kallonsa, ganin yana kallonta ne yasa ta fara masa sannu tana tambayar ina ke masa ciwo. Shi kuwa wani irin haushin ta da yake jine yasa ya juya mata baya yana ɗaga mata hannu yana kawar da kai gefe, sai yaga ta fashe da kuka tana wa Nasiru magana sai kuma yaji tabar dakin da gudu. Bangaren su kawo Inuwa kuwa washegari aka shirya gawar Anty Zainab ƴan uwanta sukai mata addu'a harda Umma da itama ta zauna a gurin, nan dai ƴan uwanta su kai mata rakiya izuwa gidan ta na gaskiya. Lokacin da Kawu Inuwa ke sanar masa da rasuwar matar tasa sai kawai ya saki murmushi haɗi da hawaye duk lokaci ɗaya, dama ya ji a jikinsa hakan yasa ya kasa yin wani yunguri, amma zuciyarsa wani irin zafi take masa ga shi abun takaici har yanzu babu wanda ya gano cewar Siyama tun da ta fita bata dawo ba. Shi yanzu abun da yafi basa tsoro ma itace Umma, yanzu tana sanin wannan abun shi zata baiwa laifi. Lokaci ɗaya Yaya Bala ya fashe da wani irin kuka wanda yasa Nasiru ma da ke kusa da shi fashewa da kuka. Sosai yaya Bala ke kukan rashin matarsa abar son sa wacce take zaɓar farin cikin sa fiye da nata. Wata zuciyar kuma na nuno masa Siyam a filin taron sarauniyar kyau ta ƙasa! Sosai yake jin ya muzan ta, ya gama zama babban banza kuma ƙaton daƙiƙen da ƙaramar yarinya ta mayar kwandon shara, hannunsa ya kalla ya gani a ɗaure ya cici yatsa. Sosai su kawo Inuwa suke bashi haƙuri har dai ya samu ya ɗan daina kukan. Likita na shigowa Yaya Bala ya ce a sallame shi ya warke, likitan yace yayi hakuri zuwa gobe, amma yaya Bala ya daka masa wata tsawar da tasa likitan rikicewa. Ya ce "Ok ok ok kwantar da hankalinka bari yanzu nasa a rubuta maku takardar sallama. Suna zaune Yaya Bala ya dafe kai, Nasiru kuma ya shiga Toilet yana uzuri sai ga likitan tare da wata noss a bayan sa. Yana zuwa ya miƙawa kawo Inuwa takardar shedar biyan kuɗin su da kuma magunguna da aka sayo musu sai kuma ta sallama. Kawu Inuwa ya amsa yana tambayar na maye? Likitan ya masa ƙarin bayani. Haka dai ba tare da sun fahimci komai ba suka tattara izuwa gida bayan kawo Inuwa ya tare musu mai ɗan sahu. Yaya Bala yace a saukesa a ƙofar gidan su Zainab kasancewar babu nisa da gidansu. Babu yadda kawo Inuwa bai yi da shi ba amma ina haka ya sauƙa hannu a saƙale bai ko bi ta kan mutanen da ke ƙofar gidan ba ya shige cikin gidan. Koda ya shiga ya tarar da mutane da yawa a ciki hakan yasa ya fara gaisuwa yana hawaye, yana zuwa gurin mahaifiyar Zainab kuwa ya fashe da kuka kamar mace, sosai yake kuka har ya dawo da sabon kuka a gidan. Ƙanwar ta mai suna Zilai da dama tun tuni basa shiri da Yaya Bala domin yarinyar irin marasa kunyar nan ce, shi kuma yaya Bala baya son raini gashi da saurin kai hannu yasa basa shiri da ita, domin kuwa ya sha kwaɗe ta idan tayi rashin kunya a gaban sa. Zilai ta fashe da kuka tana faɗin "Wayyoo Anty Zainab ta tafi ta barmu kun kashe mana ita, to wallahi ba zamu yarda ba, ai ance ba ita kaɗai ce a motar ba amma ita ka dai zata mutu... "Wata ƴar uwarsu ce ta buge mata baki tana harararta. Ohoo shi baima san tana yi ba. jin abun yaƙi ƙarewa ne yasa baban su Zainab ɗin shigowa cikin gidan ya fita da Yaya Bala. Ganin halin da Bala ɗin ke ciki ne yasa Alhaji Sani wato baban su Zainab fara basa baki hardar yaci nasarar shigar da shi ɗan sahun suka tafi. Koda suka isa gida Umma ce sai matar kawo Inuwa suna kiranta da Mama da matar Husaini suna ce mata Momy, sai wasu daga cikin ƴan uwa. Koda Umma ta gansu tayi mamaki domin ta yi zaton sai gobe ko jibi zasu dawo. Basu jima da dawowa ba sai mutanen gurin aikin su yaya Bala ɗin nan sun yo Mota guda sun zo gidan. Yana aiki da wani karamin kamfani ne irin masu shirya guraren taro ko wani gida idan anyi ko dai filen gabatar da wani taron a nan cikin garin Abuja. Kasancewar aikin ba kullum ake samu bane yasa wani lokaci sukan shiga halin babu, godiyar Allah ma da yasa gidan da suke ciki nasa ne ba na haya ba, domin aikin nasu babu laifi idan aiki ya samu ana samu hakan yasa lokacin da yaji kuɗi a hannunsa sai ya sayi wannan suka dawo wanda suke ciki muka ya saka ƴan haya. Duk da gidan ƙarami ne amma Alhamdu lillah ya ishe su bata tare da takura ba. Bangare biyu ne gidan daya wanda Umma ke ciki, ɗakuna biyu ne sai Toilet daya a gefen ɗakunan babu kicin agurin. Bangaren da suke ciki kuma a kwai ɗakuna hudu da kicin sai kuma kowani ɗakuna guda uku a kwai Toilet a ciki. Ɗaki daya na Nasiru sai ɗaya na Siyama da Fati, biyun kuma shida matarsa, sai kicin guda ɗaya. Idan sun yi baƙi sai su turasu bangaren Umma, haka suke rayuwarsu babu hangen Dala. Ganin haka yasa Umma sa Fati ta shiga kicin tayi girki sabo da baƙin, hakan yasa ƴar gidan matar kawo Hassan mai suna Binta tashi ta raka ta suka fara girkin.Baƙin basu jima ba suka tashi suka tafi bayan sun bar masa abu dubiya da suka ruƙo masa. Bayan sauran sun fita ne ɗaya daga ciki ya dawo da alamar dai a bokiksa ne yazo ya fara masa tambayar da yasan sai ya gaji da amsawa. "Wai da gaske ne yarinyar da tazo ta biyu a gasar jiya ƙanwar ka ce? Yaya Bala ya ce "Eh" mutumin yace "Sunanta fa wai Siyam Olosha? Yaya Bala da ya gama kaiwa iya wuya ya ce "Eh itace " ya faɗa da ƙarfi har sai da hankalin su Umma ya dawo gare su. Shi kuwa mutumin yayi sum-sum ya bar palon. Umma kuwa da tun da suka shigo take son taji ko dai Siyama taje gidan su Anty zaibab ɗin ne ganin bata gansu tare ba ta ce "Lafiya dai kake ihu ga mutumin da yazo duba ka? Yaya Bala ya tashi ya shige cikin ɗakin yana jin hawaye na son zubo masa. Umma ta dawo da kallonta ga Nasiru da shima hannunsa ke maƙale da ƙafaɗa ta ce "Wai ina kuka baro Siyama ɗin ne, ko dai ta tsaya gidan su Zainab ne? Nasiru ya kalli Umma da yasan wallahi babu ruwan ta da wannan ciwon tana jin abun da ya faru shi kenan hankalin kowa ya tashi kenan. Ya ce "Eh tana gidan sai an jima zata dawo koma ta kwana a gurin" Umma ta ce "To ai ta kyauta dama haka ya kamata ace wani yaje gidan nasu. Nasiru ganin haka shima ya miƙe da gyar ya shige ɗaki ya bar palon. Suna cikin Girkin Binta ta ce da Fati "Wai ina Anty Siyama ne naga ban ganta a gida ba? Fati ta ce "To mun barta a asibiti dai ban sani ba ko kayan ta tsaya kwasuwa. Binta ta ce "Alasarki Anty Zainab wallahi ko ni da ba gidan nan a zaune ba nayi kewar matar tana da kirki sosai ga son mutane. Fati da har ruwan hawaye ya fara taruwa mata ta ce "Da yanzu da ni za'a tafi, Umma tazo tayi faɗa akan baza'a je dani ba, har fa na ke ta kuka ashe dai Allah ya tsara komai ne. Binta ta ce "Alasarki Kinga amfanin bin maganar iyaye ko, yanzu da kin ƙi yarda kin bisu, Kinga ko baki mutu ba ai zaki sha wahala" Fati ta share hawaye ta ce "Ana ganin kamar Umma tana da faɗa har ake ganin hakan yasa bata sakewa sosai da yaran ta, kuma abun da take yi ɗin shine daidai, ni kam daga yanzu duk abinda Umma ta hana ni wallahi ba zan ƙara yi ba. Suna cikin haka wayar Binta ta hau ƙara tana dagawa ba tare da sallama ba wata ƙawarta ta ce "Ke shegiya shiga Whatsapp ki raba mana wannan gardamar ni nace wannan wannan kozin ɗin taki ce Siyama amma su Laila sun ce ƙarya ne. Binta da bata fahimta ba ta ce "Ban gane ba? Ta ce "ki shiga zaki gani ai muna jiran ki" Ana faɗa aka kashe wayar. Fati ta ce "Wannan Farida ce ko? Binta ta amsa da "Yaya kika gane" t Ta faɗa tana buɗe datar ta. Fati ta ce "Wannan saurin zagin nata mana, wallahi bana son mutum mai saurin zagi, yanzu fa ji wannan wayar da kukayi ta zage ki har sau biyu kamar wata kafura. Binta ta ɗan yi murmushi ta na faɗin ai Farida da zagi kamar jikar maguzawa. Daidai lokacin Binta ta fara kallon video ɗin da ya gama budewa. Ganin wata kamar Siyama yayarta yasa ta jawo Fati tana faɗin ke duba min nan dan Allah kamar fa Anty Siyama ko? Fati ta amsa tana kallo. Lokaci ɗaya Fati ta ce "Wannan ai ba Siyama ba ce" ai kuwa Binta da farin ciki ya gama kamata tayi hanyar waje da gudu da niyyar nuna wa mahaifiyarta, har tana dariya ta ma manta da cewar zaman makoki suke yi. Ai kuwa suna zaune a gurin gaba ɗaya Binta ta shiga palon tana dariya tana cewa "Umma Mommy Mama kuzo kuga Anty Siyamar mu ta zama tauraruwa. Ta faɗa tana dawo musu da kallon baya. Umma da ta ƙaraso gurin tana cewa wacce Siyama kuma. Nan dai suka fara kallo. Tabbas Siyama ce ga rabin nonuwa a waje, ga kai a bude ga wani irin ɗan banzan ɗinkin da ya gama fitar da mazaunan ta. Sosai Umma tayi sumam tsaye daidai lokacin da Farida ta ƙara kiran Binta... 📝 Muje zuwa masoya, kubi komai a hankali har mukai gurin da kowa zai fuskancin hanya. Yanzu dai kowa yasan abun da ya faru, dama Umma ka dai ta rage... Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza....✍️ [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ *FCWS* _Duk mai son samun cigaban wannan labarin to ya shiga wannan WhatsApp channel ɗin_👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Page 5️⃣* Nan take Binta ta ɗaga kiran tana sanar musu cewar Siyama ce acikin vedio ɗin, ai kuwa tana jin Farida ta ƙundumawa Lailai wani ƙatoton zagi jin tayi nasara. Jin haka yasa Binta kashe wayar tana ƙara yiwa su Umm ƙarin bayani ganin sun kasa magana. Ta ce "Wai baku gane ta bane? Ina wannan taron da akayi jiya na sarauniyar kyau, to shine fa Anty Siyama ta shiga kuma tazo ta biyu kun gani?" Ta faɗa tana nuna musu takardar shedar zuwa ta biyun da Siyama ta riƙe ana ɗaukarta hoto. Taci gaba da faɗin "kuma Mommy wallahi shi kenan Siyama ta zama.." Wani tsawa Mommy ta daga mata yasa tayi shiru tana bin fuskokinsu da kallon mamakin irin wannan abun farin cikin sukuma duk sun ɓata rai. ****** *SIYAMA* Lokacin da suka shiga cikin shagon nasu duk wata ƴar team members ɗin su maza da mata duk sun hallara, dama daga ita sai Aida suka rage. Ai kuwa suna shiga gurin ya ruɗe da ihu barin ma ganin irin shigar da tayi. Sosai members ɗin su ke ƙoƙarin nuna mata farin cikin su, amma duk karr take kallon kowa. Haka ta dinga binsu mazan da matan tana runguma suna wa junansu kiss a gefen kumatunsu. Bayan sun zauna Oga Fita ya fara magana cikin harshen Ingilishi. "Muna sake godiya ga Allah da ya ƙara bamu nasara tun bayan shekara shida da muka taɓa zuwa na uku sai yau gashi mun samu ta biyu a cikin mu, kuma nuna san rai shekara mai zuwa mu samu ta ɗaya. Duk suka yi tafi suna amsawa da amen in sha Allah. Ya cigaba da faɗin "Wannan nasarar ba iya ta Siyam Olosha ba ce, nasara ce ta duk wani members da ke cikin wannan group ɗin mai suna wait house (Farin gida). Kuma ina so na sanar daku cewar yanzu haka sabo da wannan nasar da muka samu mun ƙara samu karrama wa ta musamman, sannan mun samu dama guda uku daga kamfanin Baby and me na yin aki damu a matsayin sabbin Models ɗin su na wannan shekara, kuma sun tabbatar da cewar Siyam itace zata gudanar musu da duk wasu tallukansu na kamfanin su muddin ta yarda, yanzu haka sune ke jiran ta a ofec ɗin tan ɗazu". Ai yana ƙarasa wa suka fara ihu da farin ciki jin abun da suke buri zai tabbata. Aida kuwa kamar ta tashi ta taka rawa tsabar farin ciki, tana son zama Model amma ba irin wannan na ƙaramin kamfani ba, tana so ace irin manyan kasashen duniya su gaiyaceta domin yi musu talla, amma babu laifi idan ta samu wannan ɗin ma Alhamdu Lillah, a hankali watarana zata kai har gurin da take so. Ita kuwa Siyam Olosha farin ciki baki har kunne, dama Oga Fita ya sanar da ita cewar muddin tana son zama Model to wannan hanyar ita ce mafi sauƙi gashi ta yarda tun ba'a je ko ina ba har ta fara zama Model. Adawiya da Badawiya sune suka fara faɗin "Oga Fita amma masu kamfanin babby and me ba wai Siyam Olosha suke so ba, sunce a basu mutum uku ne kawai a cikin members domin ba irin ta suke so a talansu ba. Adawiya da Badawiya sune manya a cikin wannan group ɗin hakan ya Oga Fita baya son rabuwa dasu, domin suɗin sune fitilar wannan taem ɗin, yasan yadda suke nuna ƙiyayyar su akan Siyam, saboda Badawiya ce zata jagoranci team ɗin amma zuwan Siyam da kuma yadda shi Fita ɗin yake ganin zata fi bada abun da ake so ba wai sabo da tafi Badawiya kyau ba, a'a saboda da irin zubin halittar tane yasa ya yarda da ita. Fita ya ce "No ba haka bane, sunce bayan ita a samu mutane uku kuma ke Adawiya ai kina da Contract akan ki, ita kuma Badawiya tace bazata yi aikin Model a ƙananan kamfani ba hakan yasa ban saka sunan ku ba. Na saka Siyama da Nusee sai Sarah da Hafness. Da sauri Siyam ta miƙe jin babu sunan Aida ta ce "Oga Fita banji sunan Aida ba? Oga Fita ya ce "Kamfanin Baby and me kin san basa aiki da baƙin mutum, sunce farare suke so kin ga kuma ita Aida ai bleak biyuti ce, shi ne yasa ban saka da ita ba. Lokaci ɗaya Siyam taji kamar cin fuska ne a kaiwa Aida domin kuwa Aida ai ba baka bace, kuma ma ko bakar ce ai bai dace yace haka ba. Nan take su Adawiya suka fara dariya jin cewar Babu Aida domin sun san abu sai yafi ɓatawa Siyam rai, domin kowa yasan burin Aida kenan zama Model. Haka aka gama taro duk ran Siyam da Aida a ɓace. Sai da tafi komai da ta samu ta saka hannu kafin ta warewa team nasu ita kuma ta tafi gidan Aida da sauran. Kyautar motoci uku, sai kuɗaɗe masu yawa. Sun yi magana da masu kamfanin Baby and me Kuma ta yarda zatai musu aiki amma sai ta shirya tukunna kafin ta saka hannu, domin tana so taje tayi bincike akan irin aikin nasu. Haka suka bar maganar akan zata ne mesu. Koda suka isa gidan Aida sun tara Jamila da jamilu har sun gama abinci sun ci nasu suna kallo. Sannu da dawowa su kai musu suka ci gaba da kallonsu. Ganin Aida bata tada maganar ɗazu bane yasa Siyama faɗin "Ɗazu munyi magana da Fita akan ina so na sanar da iyayena gaskiya dukda cewar lokaci ya ƙure amma ya kamata na nemi yardar su, domin yanzu Kinga zan fara taka wani matsayi da dole ina buƙatar addu'ar iyayena da ƴan uwana, nasan abu ne mai wahala Umma ta yarda nayi sana'ar Model amma idan aka fahimtar da ita zata yarda domin kisan mu Hausawa duk wani abu da bai shafi addini ba gani ake duk mai yin sa ɗan iska ne, so yanzu ina so naji shawarki yanzu na samu damar zama Model, idan sun ce sai na gama karatu ne shima mai sauki ne shekara biyu ya rage min, amma dai na gaji da yin amfani da sunan wani wai Olosha. Aida taja dogon numfashi, tana haɗeye wani ƙatoton abu a ranta na irin cin mutuncin da a kai mata, wai itace baƙa, sosai ta danne komai kafin ta ce "Kin yi shawara mai kyau, amma gaskiya ina tabbatar miki da cewar babu yadda za'ayi Umma ta yarda kiyi Model, domin yadda suka ɗauki abun ba haka yake ba. Yanzu shawarar da zan baki itace kije gida ki fuskanci komai in sha Allah zasu yarda ni na faɗa miki. Siyama ta ce "Ta sanadiya ta Yaya Bala wanda ya zama kaman Uba a garemu ya rasa matarsa, ya karye a hannu, ga Nasiru ya karya a hannu da ƙafaɗa kuma yana karshen shekara kenan a karatun sa, anny kuwa na kyautawa dangi na. Sosai take kuka tana cigaba da faɗin "Wallahi badan kaina nake wannan abun ba, ina yi ne domin na taimaki su, wannan dama na samu kuma in sha Allah sai nayi amfani da ita. Aida ta ce "Yanzu ni dubeni, badan ina yin wannan sana'ar ba ina zan sa kaina da ƙanne na, da yanzu muna bin gidan ƴan uwa ana cimmana mutunci, a matsayin ki na mace yana da kyau ki kare mutuncin ki, kuma ki tsaya da ƙafafunki babu Maraya sai raggo". Sosai Aida ta danne nata abun ta bawa Siyama goyon baya da kwarin gwiwa. Haka Siyama ta bar komai a gidan Aida sannan ta shirya da niyyar tafiya sai ga kira ya shigo wayar ta. Ganin sunan Ibrahim ne yasa gaban ta faduwa domin har ga Allah ta manta da shi a gaba ɗaya. Nunawa Aida fuskar wayar tayi suka yi dariya kafin ta ɗaga Aida na cigaba da dariya. "Siyama da gaske wai kece ake cewa kin shiga gasar kyau jiya? Ibrahim ya tambaya a dan rikice. Dariya ta ɗanyi ta ce "Baka taya ni murna bane?" Ibrahim da ransa ya gama ɓaci da kishin ganin video ɗin ta da irin wannan kyawun da tayi yasa yake jin kamar zuciyarsa zata soye, yana kishin abun da yake so hakan yasa yaƙi yadda lokacin da aka nuna masa sai yanzu kuma tazo tana masa dariya. Cikin wata iriyar muryar da baisan yana da itaba ita kanta Siyama ɗin a karo na farko kenan da taji shakkar sa ya ce "Siyama bana son hauka ba wasa nake ba, da gaske kece? Siyama da sai da ta ɗauke wayar daga kunnenta tsabar tsoro tana haɗeye yawu, ta kalli Aida da itama ta tsayar da dariyar. Cikin rikicewa ta ce "Kazo gida muyi magana" tana faɗa ta kashe wayar, ai kuwa sai ga wani kira, take ta kashe wayar tana faɗin "Na shiga uku ni Siyama! Aida karfa wannan mutumin ya zama min masifa fa, naga har na fara tsoronsa. Aida ta ce "Ai ni dama na faɗa miki wannan shirin naki daga baya ke zai dama, kika ce wai babu komai shima ai ba zai gane ba, harda cewa wai wawa ne, bashi da wayo, yanzu dai ga shi kina gani tun bai gano komai ba zai fara kawo mana matsala. Siyama ta ce "Karki damu a kwai kudi idan ya gansu ko da yaji dalilin na a kan sa ba zai yi komai ba idan yaji kuɗaɗe. Aida ta ce "Hamm ayi dai mugani idan tusa zata hura huta" Siyama ta amsa da cewar irin tusar ki kam sai dai ta kashe wutar ma". Haka Siyama ta fita ta tare mai ɗan sahu ta shiga izuwa anguwarsu, tayi niyyar zuwa asibiti amma tana so ta sauya kayan jikinta, sai ta biya ta gidan su Anty Zainab da ake makoki. Tana sauƙa taga mutanen unguwa kowa na kallonta, hakan sai yanzu ta kalli jikinta taga babu hijjab, da sauri ta shige cikin gida, tana shiga ta tarar da Ibrahim zaune ya dafe haɓa alamar tagumi yana kallon waje. Ai kuwa yana ganinta ya taso yayo kanta kamar wani zaki, sosai Siyama ta tsorata har ga Allah Ibrahim ya sauya sosai. Yana zuwa kusa da ita kallo ɗaya taiwa idanunsa taga sun yi jaa, ai kuwa ta kawar da kai gefe tana jin kamar ya cika gidan nasu. Ya ce "Da gaske kece wannan Siyama? Ya faɗa yana kallon kayan jikinta. Takurewa tayi a guri ɗaya tsabar wani irin tsoro da ya shigeta, sosai ta matse a guri guda tana jiran sauƙar mari ko kuma taji anyi kutuball da ita, jin shiru ne yasa ta ɗaga kai ta kallesa ya tsaya a gaban ta sai sakin huci yake yi. Lokaci ɗaya ta tuna da cewar Ibrahim ne fa, wanda ta mayar kwandon shara, wannan talakan da ta fake da shi take cika muradanta, sannan yanzu fa ita Siyam ce ba Siyama, zata iya sa a kulle duk danginsa ma ba shi ba, kuma ai yanzu ya gama mata duk wani amfani, lokaci ɗaya taji wani ƙwarin gwuiwa yazo mata, hakan yasa ta sake daga takurewar da tayi ta kallesa cikin ido ta ce "Eh nice wannan da kake kallo yanzu, kuma in sha Allah na fara kenan har zuwa na ciga dukkan burikana na rayuwa, ina son zama Model bama a iya nan ƙasa Nigeria ba har kasashen Turai in sha Allah. Tana faɗa ta kama hanyar gida tana jin mai ma yasa da take neman kada kanta a gaban wannan talakan. Sai dai ko taku uku mai kyau bata yi ba, Ibrahim ya dawo da ita baya, ya kalleta cikin ido, babu wannan tsoron nata yau a cikin idanunsa da ta saba gani kullum, zata iya rantsewa ma kamar ba fuskarsa ba ce."Mai kike nufi da wannan maganar taki? kina nufin dama ba sona kike ba kawai kina amfani da nine ko yaya? Siyama ta ce "Na godewa Allah da yasa har kayi saurin ganowa da kanka. Sai da ta dawo kusa da shi kafin ta fara faɗin... "Dubeka dubi zubin tsarin halintarka sannan ka kalleni, kai ko giyar wake kake sha har zaka yi tunanin ni Siyama zan iya yin soyayya ta gaskiya da gaskiya da kai, to wallahi bari kaji na faɗa maka, tun da nake tare da kai Ibrahim ban taɓa sonka ba, ban taɓa jin zan iya son ka ba, ina yin amfani da kai ne domin yaya na da kuma mahaifiyata, sannan daga yau ina so na sanar maka da cewar babu ni babu kai, karka ƙara nuna kasanni, kaje kayi lissafin abun da ka kashe min tun daga haɗuwarmu ni kuma zan ninninka maka su, amma dan Allah daga yau karka ƙara nuna ka sanni please, sama tayiwa yaro nisa. Tana faɗa tai masa wani irin kallon sama da ƙasa kafin ta saki wani wawan tsaki ta shiga cikin gidan ta barsa a gurin tsaye yana kallonta, a lamar abun yazo masa a bazata. ****** *IBRAHIM* Duk yadda ya kai da zafin zuciya da zafin rai amma lokaci ɗaya yaji duk sun zube, take yaji jikinsa kamar an zare masa dukkanin lakar sa, babu abun da ya fi taɓa masa rai kamar da tace tun da take bata taɓa jin sonsa ba, kuma bata taɓa masa kallon wanda zata iya so ba. Tabbas jin wannan kalmar daga bakin wanda ka gama yarda dashi ka gama basa amanarka a kwai ciwo. Shi kansa ya sha yiwa kansa tambayar dalilin da zai sa Siyama ta ce tana sonsa, amma idan ya duba yadda take kula sa, kuma take jin maganar sa take basa mutuncinsa sai ya bari akan kawai haduwar jinine, amma ashe ba haka bane. Shiru yayi yana tuna abun da tace wai dama tayi amfani da shine domin cika burinta na zama Model, kuma gashi ta zama, tayi amfani da shi ne domin Yayanta da Mahaifiyar ta. A fili yace "Menene Model! Shiru yayi ya kai minti goma a gurin kafin ya bar unguwar zuciyarsa nata saka masa abubuwa. Har sai da ya wuce ƙofar gidan su kafin wani yaro ya ankarar da shi, haka ya dawo da baya ya shiga zauran gidan su kafin ya sunkuyar da kansa yana tunani. Bai san adadin mintinan da ya kwashe a gurin ba sai ji yayi ana kiran sunansa. Da mamaki yake kallon zauren ganin duhu alamar dai dare ne yayi sosai, fuskarsa yaji danshin lema, koda ya kai hannu ya shafi sai yaji hawaye ne. Cikin mamaki Hajja ta ke faɗin "Kai Ibrahim meneke gani haka, wai dama kana nan ne ko dai yanzu kazo, tun ɗazu muna ta jiran dawowarka ashe ma kana gidan, me ke faru da kaine?" Hajja kenan kaka ce a gurin Ibrahim wacce ta haifi Babansa yanzu haka tare suke zaune shida ƙanwarsa da ita Hajja ɗin kasancewar iyayensa duk sun rasu, yanzu shi da ƙanwarsa Nana da Hajja suke rayuwa a gidan. Ya ce "Hajja Siyama ce" Cike da mamaki ta ce "Me ya sami Siyamar? ina ance matar Yayan nasu ce ta rasu, ko itama wani abu ya sameta ne? Lokaci ɗaya Ibrahim ya fashe da wani irin kuka wanda yasa Hajja kwaɗa wani irin salati haɗi da kiran sunan Nana wacce har barci ya fara ɗaukarta. Da sauri ta fito tana tambayar lafiya, haka suka kama shi har cikin ɗakinsa suka kwantar da shi kafin suka fara tambayarsa abun da ya sami Siyama ɗin, domin kuwa babu wanda bai san shi da Siyama ba, daga gidan su Siyama ɗin har gidan su da kuma mutanen unguwa. Ita kanta Hajja farko bata yarda da cewar Siyama tana son Ibrahim ba, domin babu yadda bata yi ba ganin ta raba su, amma ganin yadda ya dage, itama kuma Siyamar har gida take zuwa ta gaidata yasa ta hakura. Ita kuwa Nana dama basa shiri da Siyama kasancewar tana da girman kai ga raini, ko a hanya suka haɗu sai dai ta wuce ta wuce. Ganin yadda suka shiga damuwa ne yasa Ibrahim daurawa ya miƙe yace Nana ta dafa masa ruwan zafi zai yi wanka. Kasancewar akwai wutan nefa yasa ta miƙe domin jona masa. Babu yadda Hajja bata yi da shi ba amma bai ce mata komai ba hakan yasa ta hakura tana ce masa karya sa damuwar mace a kansa fa, ya rufa musu asiri dan Allah shi kaɗai ga resu. Hajja na fita ya ɗauko wayarsa ya danna kiran number Siyama, amma ya jita a kashe ya ƙara kira nan ma a kashe, take ya sauke ajiyar zuciya yana ɗauke babbar wayar abokinsa da ya nuna masa wannan video ɗin. Kunna wayar yayi yaga ta shiga ki, ya cire kin kasancewar yasan ki ɗin wayar, Yana budewa vedio ɗin ya shiga aki kasancewar dama a kai yake, sosai yake ta bin ta da kallo yana so ya gano tayaya haka ta faru, mai yasa bai taɓa lura da cewar Siyama tayi amfani da shi ne domin cika muradanta ba. Yana cikin haka Nana ta shigo ta sheda masa cewar ta shigar masa da ruwan. ****** *ADAWIYA* Kallon Badawiya tayi ta ce "Ni matsala ta dake kenan wallahi shegen jiji da kai, yanzu dan Allah meye laifin kamfanin Baby and me da zaki ce bazayi aiki da su ba, ai ko domin mu wulakanta wannan yarinyar ai kya karɓa. Badawiya ta ce "Ni kaina sai yanzu nake da na sani, domin na bibiyi aikin naga a kwai tsoka, kuma ba wai aikin Contract za'ayi ba, zaka iya haɗa aikin su da na wani ba kamar na Magazing bane da babu dama kayi aiki da wasu har sai lokacin da ka basu ya cika. Adawiya ta ce "You see ni wallahi lokacin da naji Fita na faɗin wai ke kince bazakiyi aiki da ƙaramin kamfani ba abun ya bani manaki domin Baby and me suna biya sosai kuma suna da costoma a ko'ina. "To yanzu yaya kike so ayi domin gaskiya ina son wannan aiki? Badawiya ta faɗa tana kallon Adawiya da ta cika tayi famm. Ta ce "Ai kin gama zubar da damar ki wallahi, amma bari zan samu Fita idan yaso sai a cire wannan Nusee ɗin dan nasan babu yadda za'ayi da zai sa Shara ta fita. Sai a lokacin Badawiya ta ce "To ko dai musan yadda za'ayi a cire ita Munafukar Siyama ɗin sai kawai a saka ni. Adawiya ta ce "Ta yaya? Tayi dariya ta ce "Olusha" Adawiya ta riƙe baki tana dube-dube ko wani ya jisu. Take suka tafa suna ganin ashe ma ga hanya mai kyau da zasu bi su rusa wannan banzar. ****** *SIYAMA* Duk da irin faɗuwar da gabanta keyi bai hana taji tsoron kar Ibrahim ya shaƙota ta baya ya fara dalla mata mari ba, sosai take tafiya ta ankare da shi, har sai da taga ta shiga cikin palon gidan nasu kafin ta sauke ajiyar zuciya tana jin in sha Allah ta rabu da ƙaya. A fili ta furta "Na tsallake ƙofa ta farko a cikin ƙofofin matsalolin da zan fuskanta. Tana ɗaga kai taci karo da matar kawu Inuwa wato mahaifiya Binta wacce suke kira da Momy. Kallo ɗaya tai mata ta kawar da kai gefe tana ƙoƙarin wucewa domin kuwa basa shiri da matar. Ganin tana ƙoƙarin yin hanyar ɗakinsu ne yasa ta faɗin "Ke Siyama dan ubanki bakya ganina ne da har zaki kama hanya ki wuce ni ko gaisuwa babu? To ke nake jira dama tun ɗazu nake zaune anan an kira number ki bata tafiya, idan har kina son kanki da arziki ki juya mu tafi gidana idan kuwa ba haka ba wallahi sai Ummar ku ta kusan hallaka ki, gata cen babu yadda ba'ayi da ita ba amma taƙi hakura, shi kan sa Bala da baida lafiya bata kyale sa ba, to sabo da haka ki juya yanzu mu tafi. Momy ta faɗa tana ƙarasowa gurin da Siyama take. Siyama da gabanta ya fara dukan goma sha tara-tara jin cewar yanzu kowa na gidan su yaji kuma ya gani kenan. Duk da cewa tana tsoron Umma sosai amma bata jin zata bar gidan nan ba tare da ta nemi amincewar ta akan fara aikin Model ba, ko da kuwa tsriranta zata yi ta cinye to wallahi sai ta tsaya ta ƙwaci yancin kanta. Momy ta ce "Wuce mutafi" Siyama ta ce "Babu inda zan je, yau ko soyani Umma zata yi sai dai tayi, aikin gama ne ya riga ya gama, kawai ki barni" Cikin tsawa da masifa Momy ta ce "Dan ubanki kin san halin da kika jefa ahalinki kuwa? Ina so na tafi dake domin zuciyarta tayi sanyi karta aikata miki abun da zai dameki keda ita amma kina cewa babu inda zaki, Siyama mai kike so ki zama ne, kije kina baiyana kanki a duniya akan kuɗi, to wallahi ina baki shawara akan karki yarda ki shiga cikin gidan nan har ki haɗu da Umma na faɗa miki. Momy na faɗa ta koma ciki ta bar Siyama tsaye idanunta na ta kallon mashiga sashen Umma ɗin...📝 Yanzu aka fara shiga labari, kudai kuci gaba da nuna goyon baya masoya. Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza writer ✍️ [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FCWS_ *My WhatsApp channel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *PAGE 6️⃣* A hankali ta fara nufar ɗakinsu tana tafiya kamar mai ciwon ƙafa, tana tura ƙofar ɗakin nasu sukayi ido biyu da Binta da take ta chatting abun ta, domin ita abun ma wani abun alfahari ya zama mata, sai posting hotonta da suka taɓa ɗauka da Siyama ɗin take yi tana faɗin ai ita ɗin ƙanwar Siyam Olusha ce. Tana ganin Siyama ta miƙe ta nufo gurinta tana kallonta itama sai binta da kallo take. Kafin tayi magana ta ce "Ina Fati?" Binta ta ce "Tana sashen Umma tun ɗazu" Tana jin haka ta sauke ajiyar zuciya ta zauna a gefen gadon ta sauƙe jakar dake jikinta sannan ta kwanta a kan gadon tana mai kallon saman rufin ɗakin. Ita dai Binta sai binta da kallo take amma ta kasa ce mata komai, ganin shirun yayi yawa yasa Binta faɗin "Anty Siyama ko zamu ɗanyi salfi guda biyu ne? Ta faɗa domin tambayar da ake mata na cewar tayi hoto da ita yanzu idan har da gaske ne ita ɗin ƙanwarta ce. Kafin Siyama ta bata amsa sai ji sukai an turo ƙofar an shigo da sauri. Da sauri Siyama ta miƙe zaune tana kallon Fati da take ƙoƙarin saka saƙata sama da ƙasa a ƙofar ɗakin. Siyama dai sai binta da kallo take. Itama dai Binta a tsorace take sosai ganin yanayin Fati ɗin. Fati cikin rawar murya ta ce "Anty Siyama Umma ce wallahi tace sai ta yanka ki, wai sai kin bar mata gida, ga cen Momy da Mama suna bata hakuri amma sai kuka take yi, shima Yaya Bala bata gyalesa ba, duk da ciwon hannunsa amma haka take ta dukan sa, shima Nasiru sai kulle shi akayi a ɗaki. Siyama ta ce "Buɗe ƙofar" Fati ta kalleta ceke da madarar mamaki ta ce "Baki da hankali ne, bakiji me nace ba?" Cikin zafin hannu Siyama ta miƙe ta shiga ƙoƙarin cire saƙatan da Fati ta sa, amma Fati ɗin tana hanata domin ita tasan abun da ta gani daga Umma. Kasancewar ƙarfin su ba ɗaya ba yasa Siyama ta tureta gefe ta cire saƙatan. Daidai lokacin kuwa Umma ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Turus suka yi kowa na kallon kowa, lokaci ɗaya Umma ta tsaya da kukan da take yi tana ƙarewa Siyama kallo, ganin irin kayan dake jikinta. Itama Siyama kallo Umma ɗin take yi, tana ganin yadda ta rame lokaci ɗaya a cikin kwana ɗaya kawai, ga wannan kwarjinin da take mata yauma dai an ninninka shi, sosai take tsoron Umma domin mace ce mai zafin gaske, bama ita ba, dukkanin su suna taron ta sosai. Lokaci ɗaya Umma ta ɗauke fuskar Siyama da mari sannan ta kamo ta ta turo ta baya ta fara faɗin..."Siyama mai muka rage ki da shi? So kike Allah yayi fushi dani yace ban kula da tarbiyyar Kuba, duk irin ƙoƙarin da nake yi a kan ku amma Siyama sai kin wulaƙanta ni, Siyama ki fito bainar duniya tsirara Siyama, kina ƴar musulmai akan kuɗi, ko mun faɗa miki bamu gode a yadda Allah ya yimu bane? Sosai Umma ke kuka tana dukan Siyama wacce itama kukan take yi. Itama Fati kuka take yi kaman ranta zai fita. Umma ta ce "Faɗa min waye ya baki wannan shawarar kuma mai ya kaiki aikata wannan abun? Ganin taƙi yin magana yasa Umma ɗin ƙara mata mari ta na faɗin "Na rantse da Allah idan baki min bayani ba sai na yankaki kowa ya huta, ina miki magana kina kallona tsabar raini. Ana cikin Haka Kawu Inuwa ya shigo dalilin kiransa da Nasiru yayi. Ai kuwa yana zuwa ya hau Umma da faɗa kamar zai mareta, sosai yayi mata kace-kace ganin yadda duk ta bi ta ɗaga hankalin gidan. Sosai Siyama ke kuka Kawu Inuwa nata rarrashin ta. Haka dai Umma ta koma sashen ta Momy nata bata hakuri amma ina idan Umma ta tuno da yadda taga Siyama sai hankalinta ya ƙara tashi. Sosai Kawu Inuwa ya shiga lamarin har dai komai yayi sauki har akayi sadaƙar bakwai, har lokacin kuwa Umma bata ƙara bi ta kan Siyama ba, itama Siyama ɗin bata ko ƙara fita waje ba, haka zalika tun lokacin da ta kashe wayar ta a gidan Aida bata ƙara ko bi ta kan wayar ba, domin wani irin zazzaɓi ne mai zafi ya kamata tun lokacin da Umma ta jibgeta. Sosai Fati ke ta ɗawainiya da ita, shima Nasiru ya yi fushin ya haƙura yanzu har ɗakinta yake shigowa suyi hira, amma har yanzu basu magana akan abun da ya shafi matsalar ba, shi kansa yanzu Yaya Bala abun ya haɗar masa goma, ga rashin matarsa ga ciwon jikinsa ga wannan abun da Siyama tayi, yasa kowa sai kiransa yake yana tambayar sa, ga kuma fushin da Umma take yi da shi yanzu, ko yaje gaidata bata amsa wa babu yadda bai yi da ita ba amma taƙi sakar masa fuska. Washegarin ranar da akayi sadaƙar bakwai ne Fati da Siyama da Binta na cikin daki suna hira sama-sama sai ga Nasiru ya shigo ya kalli Siyama ya ce "Ina wayarki?" Siyama da har yanzu jikin nata baiyi daidai ba tace "Tana cikin jaka" Nasiru ya ce "Ibrahim ne ke ta kiranki yanzu haka yana waje, ya dade ki tashi kije. Yana faɗa ya juya bai ko bi ta kan maganar da take na cewar yace masa bata da lafiya ba. Fati ta ce "Ki tashi kije kice masa bakya da lafiya ne. Siyama ta kalli Binta ta ce "Binta fita kice masa bana da lafiya" Har Binta ta tashi Fati ta ce "A'a anty Siyama dan Allah kije da kanki please. Siyama ta miƙe zaune tana jin ai wallahi ba zata taɓa ƴarda ta ƙara haduwa da shi ba, ai tunda Allah ya taimake ta ya rabata da shi cikin ruwan sanyi to wallahi ta gode. Siyama ta ce "Ke wallahi ba zan iya fita a haka ba" Fati da ta cika da mamaki ta ce "Ibrahim ɗinki ne fa IB dai naki makaniki? Siyama ta ja tsaki ta koma kwanciyarta. Fati da ta buɗe baki da mamaki ta rufe ta ce "Ai wallahi anty Siyama bana tare da ke wajen yaudarar wannan bawan Allah ɗin, ai wallahi zunubin ki sai ya shafi mu muda muke kusa da ke, ki hana mutun kula kowa tsawon shekaru amma yanzu lokaci ɗaya kice zaki guje masa, dan Allah Karki fara. Siyama ta ce "To bari kiji wallahi ban taɓa son Ibrahim ba ko na minti rabi, dama nayi haka ne domin kar kowa ya gano shiri na, yanzu kuma na gama, abu ɗaya zan iya masa yanzu shine zan basa kuɗi masu yawa da zai ja jari idan kuma yaƙi ya fita a sabgata to Allah zan sa a ɓatar da shi. Yanzu haka saboda bani da lafiya ne yasa kika ga nayi shiru amma zuwa na warke komai zai cigaba, itama kanta Umma idan taji kuɗi duk wannan abun mantawa da shi zata yi, yanzu haka ina da Contract ɗin aikin Model da zan fara in sha Allah. Lokaci ɗaya Fati da Binta suka haɗa baki gurin cewa "Model" Siyama ta ja tsaki ta juya musu baya. Suka kalli juna suna mamakin Siyama. *IBRAHIM* Haka ya kwanta a wannan daren yayi barci rabi da rabi, ko da ya tashi da safe number ta ya fara kira amma dai har lokacin a ka she. Kamar da wasa ya tashi da ciwon kai mai zafi har baya ko iya magana sosai. Hajja dai gaba ɗaya ta rikice gashi ya ƙi sanar da su abun da ya faru. Haka tasa Nana ta je ta sayo musu maganin ciwon kai, bayan ya karya ta basa maganin ya sha, Ko da ya sha shine ya ɗan samu sauƙi, ganin barci ya ɗauke sa ne yasa ta fita ta bar masa dakin. Ita kuma Nana ta fara aikin gida. Hajja tana zaune Nana na kama mata kai shi kuma Ibrahim ya shiga wanka sai ga wata ƴar makwabtansu ta shigo da gudunta tana kiran sunan Nana. Har sai da suka tsorata bata ko tsaya wata-wata ba ta fara faɗin "Nana zo kika sirikarku ta zama tauraruwa. Tana faɗa tana turawa Nana wayar da har ta miƙe tsaye zata gudu, Hajja da kuwa tuni itama ta miƙe kasancewar har yanzu tana da ɗan kuzarin ta bata sakwarkwace sosai ba. Har Hajja zata fara masifa amma idanunta ya sauƙa a kan wata mai kamar Siyamar Ibrahim dinta sanye da wasu kaya komai nata a waje. Da dan mamaki Hajja ta ce "Me zan gani haka, wacce wannan ɗin jiki duk a waje? Yarinyar mai suna Fatima ta ce "Hajja ai Siyamar Ibrahim ce, ina wannan taron da a keyi na sarauniyar kyau, to shine fa ta shiga kuma gashi Alhamdu Lillah ta zo ta biyu. Fatima ta ƙarasa tana sakin murmushi. Hajja ta saki dogon salati har zuwa ƙarshe kafin ta amshi wayar daga hannun Nana da tayi shiru tana mamaki. Hajja ta ƙara kafawa wayar ido kamar zata shige ciki. Ta kai minti biyu kafin ta ce "Lala-lala wannan ba Siyama ba ce, Nana gane min wannan yarinyar da idanunta babu ko a lamar kunya, kalli yanda take abun fa da gani kasan ta saba, wannan ba Siyama bace. Ganin dai Hajja taki yarda yasa Nana faɗin. "Hajja ita ce mana ai shine dalilin da yasa Yaya wannan ciwon. Daidai lokacin kuwa sai ga Ibrahim ya fito daga wanka ai kuwa Hajja ta miƙe ta samesa ta na nuna masa wai da gaske Siyama ce wannan? Ibrahim ya kalli Fatima da ta sunkuyar da kai ganin sa ya fito, ya ce "Karɓi wayarki ki bar gidan nan" Hajja ta ce "Taje ina baka sanar da ni gaskiya ba? Ganin Ibrahim yana ƙoƙarin ajiye bokitin hannunsa ne yasa ta amshi wayar ta ta bar gidan da sauri. Hajja kuwa gaba ɗaya ta shiga ruɗani ita dai har yanzu bata yarda Siyama ce wannan ƴar duniyar da ta gani ba. Nana ma dai abun yazo mata a bazata, domin dai Siyama barta da iyayi da girman kai, amma sam halinta bana kwaɗayi bane, sannan a ɗan sanin da tai mata tun da suka dawo wannan unguwar zata iya tabbatar da cewar yarinya ce ba mai hangen nesa ba, to ko dai ɗan wannan kyawun da take da shi ne ya ruɗeta har ta shiga wannan harkar. Haka kawai taji ta fara tausayin Yayanta domin kuwa tabbas tasan ya rasa Siyama kenan kuma tasan irin son da yake mata. Ibrahim kuwa haka ya shiga ya shirya sannan ya fito da kayan aikin sa na zuwa gareji, kallo ɗaya Hajja tai masa ta tsorata domin kuwa tabbas ya rame sosai. Hajja ta ce "Ina kuma zaka je bayan baka da lafiya? "Hajja kirana a kayi wani aiki zamu karasa yanzu zan dawo " Ya faɗa yana ƙoƙarin fita. Hajja ta ce "To dan Allah dai karka dade idan kasan ba zaka iya ba ka dawo gida kaji?" Ibrahim ya amsa da tom kafin ya sa kai ya fita. Koda ya fita ya fara takawa a ƙafa har gurin aikin nasu. Yana zuwa ogan nasu ya fara tambayarsa lafiya yau ya makara Ibrahim ya sanar masa cewar baya jin dad'i ne shi yasa. Haka suka fara aiki amma ina wani irin sabon zazzaɓi ne ya rufe sa, ogan nasa da kansa ya tare masa mai mashin ya dawo da shi gida. Ko lokacin da ya dawo gida labarin Siyama ya gama yaɗuwa, izuwa yanzu Hajja ta yarda da cewa Siyama ce domin kuwa yadda mutane suka dinga kawo mata tsegumi kamar ba gobe. Nan dai Hajja ta shiga basa baki akan yayi hakuri ai tana sonsa wannan ma kuskure ne idan yayi mata faɗa zata bari. Shi dai Ibrahim babu abun da yake masa zafi sai idan ya tuno da cewar Siyama fa bata taɓa son sa ba, tayi amfani da shi ne kawai, a takaice dai yaudarar sa tayi. Idan ya tuna wannan shine ciwon ke ƙaruwa ga kuma wani irin sonta da yake ɗawainiya da shi, ji yake kawai ita yake son gani ko da kuwa zaginsa ne zata yi, gashi har yanzu bata kunna wayar tata ba. Wani abokinsa ne ya shigo gidan mai suna Haladu wanda ya bashi aron wayar da yaga video ɗin a ciki. Ya ce "Daga garejin ku nake aka ce ka dawo gida yanzu? Ibrahim ya meƙe zauna ya ce "Eh yanzu na shigo zazzaɓi ke damu na" Haladu ya ce "Ka dai saka damuwar wannan yarinyar kawai, ai dama kaga abun da nake faɗa maka, wallahi yarinyar nan ba dan Allah take sonka ba, amma kai kace ƙarya ne, to yanzu ka gani abun da nake so da kai shine wallahi tun wuri kayiwa kanka karatun ka natsu ka manta da wanzuwarta ka kama gaban ka, ka dai ga inda ta dosa harkar zubar da mutunci da wulaƙanta. Ibrahim da ya kafe Haladu da kallo har sai da ya gama kafin cikin ƙarfin hali ya ce "Haladu wallahi daga ranar da abun ya faru zuwa yau wani irin sonta ne ya ƙara ƙaruwa a zuciyta, wallahi ina son Siyama sosai, domin ina ji kamar zan yi hauka idan na rasa ta, please dan Allah ka bani shawarar da zata kaini ga samun Siyama please? Haladu ya ɗanyi dariya kaɗan kafin ya ce "Kaga IB karka ɗorawa kanka abun da Allah bai ɗora maka ba, tun wuri ka fita batun wannan yarinyar, ni dai ita ce shawarar da zan iya baka. Ibrahim ya ce "Wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba, domin ni sabo da Allah nake sonta, kuma itama tana sona inaga wani ne yayi wasa da tunaninta kasan mace kuma yarinya ce. Haladu ya ce "Ina waya ta? Ibrahim ya ce "Kasan me ya faru jiya tsakanin mu da ita? Haladu dai ya ce "Dan Allah ka bani wayata ana jirana. Ba tare da ya ɗauko masa wayar ba ya ce "Dan Allah ka kira min ita da wayar ka ni inaga tayi blocking dina ne. Cike da mamaki Haladu ya ce "Sabo da me? Domin kuwa shi kansa Haladu ya san da cewar Siyama tana nunawa IB so amma shi dai yasan ƙarya ne, babu yadda za'ayi mace irin wannan ta kamu da son mutum kamar IB wanda ko a cikin abokansu yafi kowa ƙazanta ga shi dai wani lokaci yana abu kamar mara wayo ko dolo. Amma kam tabbas idan baka san wacece mace ba tsaf zaka yarda cewar Siyama son sa take. "Ta ce wai daga yau babu ni babu ita wai tayi amfani dani ne domin cika burin ta kuma ta cika saboda haka karna ƙara nuna nasanta, Kuma tun juya ina kiran number ta bata shiga. Ibrahim ya faɗa hawaye na zubo masa. Haladu ya saki baki yana kallon ikon Allah. Ya ce "Ita ce ta kalleka ta ce karka ƙara nuna kasanta? IB ya gyaɗa kai. Haladu ya ce "Babbar magana wai kare da kiwon kura. Ya ce "Amma yarinyar nan ba ƙaramar jar wuya bace, wato anci moriyar ganga ko? To wallahi bata isa ba, ai yanzu ta zama sele kuma tayi kuɗi sabo da haka dole ta biyaka duk abun da ka kashe mata harda ƙari, kai nifa wallahi idan nine kai sai ta siya min gida da mota da kuma jari mai gwaɓi harda raran kudade a account, yo kai ai dama ce tazo maka mai kyau, kawai ka manta da ita. Ibrahim da ya gama zuwa ƙarshe ya ce "Haladu bana son zancen banza, wallahi ko kaɗan kudinta bai dame ni ba, ni ita nake so kuma wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba. Haladu ya katse shi da faɗin Ita dai sarauniyar kyau ɗin ko?. Sosai ran sa ya ɓaci har ya fito ya nunawa Haladu ɗin a fili kar she dai haka suka rabu. Da yamma ya tashi ya nufi gidan su Siyama ɗin amma haka ya ƙaraci zama bata ko fito ba, haka ya hakura zuwa gobe domin gobe ne za'ayi sadaƙar uku na Zainab, haka nan ma yanzu amma bai samu ya ganta ba. Sosai Ibrahim ya shiga damuwa babu yadda Hajja bata yi da shi ba akan ya hakura da ita amma ya kasa. Yau kwana takwas da faruwar komai kuma izuwa yanzu bai daina ziryar zuwa gidan su Siyama ɗin ba, hardai yaci karo jiya a gurin sadaƙar bakwai suka haɗu da Nasiru yake sanar da shi baya samun wayar Siyama. A nan dai Nasiru yake sanar masa cewar ai bata da lafiya ne, haka Ibrahim ya ƙarbi number sa akan idan yazo gobe zai kirasa sai ya turo masa ita. Haka washegari da kyar ya samu Haladu ya rakoshi akan zasu duba jikin Yaya Bala ne da Nasiru. Koda yazo ya kira Nasiru yazo ya shigar dasu har cikin gidan suka duba Yaya Bala sannan suka gai da Umma sannan suka sake yi musu ta'aziyar rashin Anty Zainab. Bayan sun fito ne Nasiru yaje ya kira musu Siyama akan Ibrahim na waje yana jiran ta. A lokacin zuciyar Ibrahim kamar ta fita tazo gareta jin ance bata da lafiya sai yake tunanin kamar abun da tai masa ne yasa, yasan itama tana sonsa ba zata iya rayuwa ba tare da shi ba. Haka suka dinga tsayuwa zaman jira har dai Haladu ya fara magana, wasa-wasa sun kwashe kusan awa da rabi amma shiru. Hakan yasa Ibrahim sake kiran Nasiru yana ɗagawa ya ce "Har yanzu fa bata zo ba. Cike da mamaki ya ce "Wace ɗin?" Yayi tambayar da mamaki ganin kusan awa biyu da kiranta. *SIYAMA* Wayarta ta ɗauko ta jona a chaji tana jin yau dai ya kamata ta ɗan matsa ko Aida ta samu ta kira taji yaya a ke ciki a Team. Ita har ta manta da batun wani Ibrahim a waje, suma su Fati sun ma manta har sun bar maganar. Tana ƙoƙarin saka wayar a chaji sai ga Nasiru ya shigo hannu a saƙale ya na faɗin "Siyama wannan wani irin rashin hankali ne zaki bar mutum sama da awa a waje yana jiran ki, baki da hankali ne? Siyama ta ja tsaki a fili ta ce "Amma ai nace maka kace masa bana da lafiya ne ko? Kuma ai na sanar da shi babu ni babu shi to mai kuma yazo yi mini" Fati da Binta suka cika da mamakin jin cewar har yanzu Ibrahim na tsaye. Nasiru da ransa ya gama ɓaci, gashi dama cike yake da ita, jira yake kawai ya warke sai ya saita mata zama. Ya ce "Na tsare da Allah idan baki tashi kin fita ba sai na ɓata miki fuska da mari, dan ubanki waye ya kawo shi a matsayin wanda take so, na rantse kika ƙara magana a gurin nan sai na tar watsa miki baki wawiya kawai mara hankali. Jin haka yasa ta tashi ko hijjab bata tsaya ɗauka ba, kanta babu ko hula ta nufi hanyar fita. Sai dai ganin Umma zaune a palon ita da Kawu Inuwa suna tattaunawa ne yasa ta juya da sauri ta saka hijjab ta fito fuska a haɗe, babu wanda taiwa magana Palon ta sakai ta fita. A nesa ta hango su, hakan yasa ta nufe su da sauri tana aiyana irin cin mutuncin da zatai musu. Kallo ɗaya tai masa taga ramar da yayi harda wani dogon wuya kamar yaron raƙumi. Tana zuwa babu ko sallama ta ce...📝 Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza writer [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ *FCWA* *My WhatsApp channel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Page 7️⃣* "Uban me ya kawoka ƙofar gidan mu bayan na maka iyaka da ni, na faɗa maka babu ni babu kai, abun da ya rage tsakanina da kai shine ka lissafo duk abun da kasan ka taɓa kashe mini zan ninka maka kayan ka, bayan haka karka ƙara nuna ka sanni idan kuma ba haka ba, wallahi Ibrahim sai kayi da ka sanin sanin Siyama da kayi a rayuwar ka, zan sa a ƙulleka har karshen rayuwarka. Siyama ta faɗa ranta a mugun-mugun ɓace, domin har ga Allah ya kaita bango, gara tai masa barazana ko zaiji tsoro ya rabu da ita ta sakata ta wala arayuwarta. Cikin karyewar murya Ibrahim ya fara faɗin "Siyamata karki min haka wallahi na yarda zan barki ki ci gaba da yin wannan aikin naki amma ba zan iya rabuwa da ke ba, wallahi da gaske ne ina sonki kuma na hakura da komai dan Allah karki min haka zan iya mutuwa wallahi" Ya karasa yana sunkuyawa har ƙasa. Wani irin banzan kallo tai masa kafin ta ce "Innalillahi wai nima mai ya kaini ai ga shi zan jawa kaina annoba. To bari kaji, na rantse da girman Allah ko mutawa zaka yi ka dawo duniya ka ƙara mutuwa ba zan ƙara bari ka ganni ba, na baka nan da kwana uku ka kawo min lissafin ka zan biya komai idan kuma muka wuce kwana uku to duk abun da ya same ka kai ka jawa kanka. Ta kalli Haladu da ya rakuɓe gefe ta ce "Idan shi wawa ne kuma dolo bai san abun da yake yiba, to kai ka sanar da shi, babu ni babu shi, idan kuma yaƙi ji ba zai ƙi gani ba, soyayya ce munyi a baya yanzu kuma nace na gama ba zanyi ba, kana dai ji ko?" Haladu ya ɗaga kai da sauri ita kuma ta juya zata shige gida. Da sauri Ibrahim ya kamo gefen hijjabin ta yana faɗin dan soyayarki da Annabi Muhammad s a w Siyama karki azabtar da zuciya da sanki, wallahi Siyama babu wasa a magana ta, zan barki kiyi komai ni Ina son ki a haka please. Siyama ta juyo a zuciye ta ce "Sakar min hijabi kafin na wanke maka fuska da mari, wai kai wani irin maye ne mara zuciya, ana soyayya dole ne. Ibrahim ya miƙe tsaye yana kallonta ganin yanda ta ɗanyi fari alamar rama sai hakan ya kara fito da hasken ta, ga wani kyau da tai masa fiye da kullum, jin sonta yake har wani fusgarsa yake kamar magineto ya ce "Siyama ke da kanki kika min alkawarin bazaki barni ba, kuma kince..."Kafin ya ƙara cewa komai ta fusge hijjabin ta ta juya zata shiga gida amma bata an kara ba sai jin ta tayi a cikin jikin Ibrahim kwance kamar ta samu gadon baccin ta. Sosai ya haɗe jikinsu a karo na farko yana sauke ajiyar zuciya har wani lumshe ido yake, yana jin ina ma zasu dauwama ahaka shi da Siyamar sa. Shi kansa Haladu ba karamin shok ya shiga ba ganin abun da Ibrahim ɗin yayi, sosai ya tabbatar da cewar Ibrahim baya cikin hankalin sa, idan kuwa ba haka ba tayaya zai rungumeta bayan nuna masa tsana da take yi har tana faɗin ko mutuwa ma zai yi sai dai yayi. Ita kuwa Siyama tsabar mamaki yasa bata fahimci komai ba, sai da taji yana ƙara kwantar da kansa a wuyan ta, har wani sauke ajiyar zuciya yake, idan bata yi ƙarya ba har wani wari yake yi na ƙazanta. Sosai ta dawo cikin hankalinta, ai kuwa da wani irin ƙarfi ta shiga raba jikinsu amma Ibrahim yaki bata damar hakan, tayi iya yinta amma ya manne ta sosai har neman ƙaryata yake yi. Ita kuwa ganin ta kasa kwacewa ga azabar ruƙo yasa ta fashe da kuka, amma ina Ibrahim bai san tana yi ba, sosai take kuka tana dukan sa ta ko inna amma shi sai lumshe ido yake ya faɗa duniyar tunani. Ganin dai kamar baya cikin hankalinsa ne yasa Haladu zuwa ya shiga ƙwatarta da ƙarfi, da kyar ya yageta daga jikin sa yana jan sa baya. Ita kuwa Siyama ganin haka yasa ta kwasa da gudu tayi cikin gida. Daidai zata shiga Palo shi kuma Kawu Inuwa zai fito suka haɗu. Ya ce "Lafiya ke kuma keda waye haka?" Siyama ta fashe da kuka mai ƙarfi tana nuna waje. Kawu Inuwa ya leƙa sai dai bai hango kowa ba, ganin ta shige ciki ne yasa ya girgiza kai ya bar gidan yana mamakin Siyama. Ko da ta shiga ɗakin su ta tarar da Fati da Binta kowacce na danna waya, bata ko bi ta kansu ba ta shiga rusar kuka kamar wacce aka yankewa ƙafa. Miƙewa tayi ta shiga toilel ta sakarwa kanta ruwa ba tare da ta cire kayan jikin ta ba, sosai Fati suka bita da kallo jin irin kukan da take, har Fati zata tambaye ta amma taga ta shige toilel hakan yasa ta fita izuwa dakin Nasiru. Sosai ta shiga wanke jikinta har lokacin tana jinsa a manne a jikinta, tana kuka tana tsine masa. Koda da fito Binta kawai ta gani a dakin bata ce mata komai ba ta kwashi kayan da zata sake ta komai toilel ɗin. Tana gama shirya wa ta fito Palo domin ɗaukar a binci, amma tana zuwa taga Umma da Nasiru da yaya Bala da Kawu Inuwa Harda Fati duk sun saka waya gaba suna kallo. Gabanta ne ya bada wani rass domin jin ana kiran sunanta a cikin maganar da a keyi ta cikin wayar duk da cewar kuwa da turanci ake maganar. Kallon Umma tayi taga wani irin kallo da take mata, haka yaya Bala shima. Ƙamewa tayi a gurin ta kasa gaba ta kasa baya domin bata san kuma me ta ƙara yi ba. Umma ce ta ce "Haƙika samuwarki a cikinmu bai amfana mana komai sai masifa da tashin hankali, wato mu iyayenki mune abun cin mutumci har kina faɗa wa duniya cewar bamu da mutunci ko, yanzu Siyama mai muka miki a duniya da muka cancanci wannan abun, bayan zubewar mutuncin da kika jawo mana shine sai kin ƙara tozarta mu a cikin idon duniya. Yaya Bala ya ce "Umma kiyi hakuri duniya ce, wanda mai zo bama tana jiransa bare kuma wanda ke cikin ta, mu dai Allah ya gani wannan abun da ta faɗa idan Sherri tai mana Allah na gani, idan kuma gaskiya ne shima Allah zai saka mata. Umma ta fashe da kuka tana face hanci, gaba ɗaya lamarin Siyama yafi ƙarfin ta, bayan wannan abun da tayi shine bai ishe ta ba, har sai ta tabbatar wa da duniya cewar iyayenta mutanen baza ne. Kawu Inuwa ne ya iya faɗin "Haba Siyama Meya hakan kikayi, me iyayenki su kai miki mai suka rageki da shi a gidan duniya da zaki wulaƙantamu har haka, Siyama me duniya zata baki wacce baki samu tare da mu iyayenki ba. Yanzu wannan abun da kika fadawa duniya Kinsan iya lokacin da abun zai kai yana yaɗuwa. Siyama dai gaba ɗaya kanta ya ƙulle, to ita me tayi me tace! Ganin bata gane bane yasa ta juya da sauri ta ɗauko wayarta ai kuwa daga ɗazu da ta kunna wayar zuwa yanzu har ta samu kira sama da guda hamsin, Fita Aida ga kuma number Ibrahim ga Nusee. Sosai ta rikice har ma bata san wa zata fara kira ba. Kafin ta danna kira sai ga kiran oga Fita. Amma taji ba zata iya ɗaga kiran kowa ba a halin yanzu sai na Aida, ita ce kaɗai zata iya rarrashin ta har tayi shiru. Kira ɗaya Aida ta ɗaga a ɗan rikice ta ce "Siyama kina ina ne kinga abun da ke faruwa kuwa?" Siyama ta ce "Please Aida wai menene, na kasa fahimta meke faruwa ne?" Aida tace "Karki damu nasan aikin waye, yanzu dai ki tabbatar kina gida, kuma idan Oga fita ya kiraki Karki ɗaga har sai na ce miki ki ɗaga, yanzu shiga WhatsApp zan turo miki da video ɗin. A kwai waɗanda nake zargi bari na tabbatar". Ita dai Siyama sai gyaɗa kai take tana sauraron ta. Dama tasan Aida itace komai nata, wallahi da babu Aida a rayuwarta da yanzu ta gama lalacewa. Suna gama wayar ta kunna data, kasancewar ta daɗe bata shiga WhatsApp ba, sai da ta tsaya sakonni suka gama shigowa kafin ta shiga sakon Aida. Kafin ta buɗe taga anyi rubuta a ƙasa sai ta karanta rubutan kafin ta shiga playing video ɗin. Cikekken labari akan Siyama Olusha tare da kafar yaɗa labarai na BBC. Sosai gabanta ya faɗi da sauri ta danna kan video ɗin kasancewar dama ya gama budewa. Wannan mutumin da Oga Fita ya haɗa su da shi a matsayin ubanta na karya ne zaune a cikin gidan jaridar BBC yana basu labarin da bata san a ina aka kirkirosa ba. Sosai zufa ke karyo mata jin irin ƙaryar da mutumin ke shiryowa, harda faɗin wai iyayen siyama ɗin ne basa ko iya ciyar da ita, haka makaranta ma shine ya ɗauki nauyin biya mata, domin iyayenta sun ce bazasu iya ba. BBC su kai masa wata tambaya da tasa Siyama sakin fitsari a gurin domin jin amsar da Olusha ya bayar. Aka ce masa "Har yanzu kuma iyayenta basu nemeka ba ko dan ganin yanzu ƴar su ta samu abun duniya?" Olusha ya ɗan yi dariya ya ce "Yanzu haka halin da ake ciki kenan, ganin Allah ya ɗaukakata shine suka zagaya gefe suka lalaɓeta har yanzu tana nuna min cewar zata daina amfani da suna ta koma yi da na ubanta, sannan yanzu haka tun bayan faruwar abun tana gidan iyayenta ne, har yanzu bata ko zo gurin da nake ba, gaskiya nayi mamakin irin wannan butulcin da Siyam Olusha take son min. Sosai Siyama ta shiga tashin hankali mara misaltawa, domin kuwa Olusha cigaba yayi da bankaɗo abubuwa masu yawa, domin har mahaifin ta da ke ƙabari Olusha bai bari ba sai da yayi masa sharri. Daga karshe ya karasa da faɗin cewar, a lokacin da take hannunsa ta bar addinin Musulunci amma bai san yanzu ba ko iyayenta sun mayar da ita. "Innalillahi wa innalillahi raji'un! Shine abun da Siyama ke faɗa ta na zama daɓas agurin. Tana jin wayarta na ƙara amma ko ta kanta bata bi ba, ita tama rasa wani irin tunani zata yi. Ganin ana ta kira ne yasa ta duba wayar ganin Aida ce yasa ta daga ta kai kunne. Aida ta ce "Kinga ki natsu kiji abun da zance miki... Kinsan su waye su kai wannan aikin? Siyama ta girgiza kai Aida ta ce "Adawiya da Badawiya ne, amma abun da nake so da ke Karki amsa kiran kowa, kuma ki zauna a gida yanzu haka Oga Fita yayi kiran gaggawa domin shima har yanzu bai gano gaskiya ba, nima bincike nayi, duk da har yanzu ban tabbatar ba, amma dai ina da tabbacin sune, yanzu dai idan na dawo zan kiraki, Karki amsa kiran kowa kinji? Batare da tace komai ba ta kashe wayar tana bin wayar da kallo. Daidai lokacin Nasiru ya shigo ɗakin ya bita da wani irin kallon tsana ya ce "Wallahi Siyama kinyi a sarar rayuwarki, da har ina tunanin butulcin da kikaiwa Ibrahim ashe harda iyayenki ma zaki sauya, wato kin ɗaukaka, kin samu abun duniya bari ki sauya kowa domin kar a dame ki ko? To gaki ga duniya da kuma Olusha, o! Sorry ashe fa kin koma Siyam Olusha Christa ko? Kallonsa take yi tana son ta ce masa wallahi ƙarya ne ake mata amma harshen ta yaƙi bata damar yin hakan. Nasiru ya ce "Kafin Umma tazo Gara ma ki tattara kayan ki ki tafi zuwa gurin ubanki da ya wadata ki da komai da mu muka kasa baki. Nasiru ya fita yana jin badan ciwon da hannunsa ke masa ba Allah da sai ya kusa ɓalla wannan yarinyar. Kuka take yi sosai tana tunano babban abun da zai sa Su Adawiya suyi mata haka. Dama har ƙiyayar da suke mata ya kai har haka. ****** *YAYA BALA* Du ƙyar yayi sa'a Umma ta sakko daga fushin da take yi da shi, amma har yanzu taƙi yarda suya maganar Siyama. Shi kansa damuwar da yake ciki ce tasa bai ko zauna da ita ba, farko ya ɗauki abun da zafi, amma rasuwar matarsa yasa ya tattara komai yasa a gefe, yana so ya nusar da Umma cewar abun da Siyama tayi laifi ne amma yanzu tunda ya faru a jawota jiki domin kar ganin haka yasa ta fara tunanin yin abun da yafi haka. Amma ganin yadda Umma ɗin tayi ne yasa bai tare ta da maganar ba. Sai da a kayi sadaƙar bakwai kafin ya samu damar tunkarar Kawu Inuwa da maganar akan ya sanar da Umma ko zata hakura. Ai kuwa Kawu Inuwa ma ya fahimci sa hakan yasa ya samu Umma da maganar, sosai Umma ta shiga masifa akan sabo da me za'a jawota jiki bayan ta gama zubar musu da mutumci. Sai da akayi da gaske kafin Umma ta haƙura akan za'a raba Siyama da zuwa ko ina, sannan makarantar ta ma ta gama kenan, kuma ta sanar da Ibrahim ya turo ko baida komai a ɗaura auran domin dai shine kaɗai wanda ta bari yake zuwa gurin ta, har kuma ta tabbatar wa da iyayenta shi take so. Haka dai aka bar maganar akan gobe za'a zauna da ita aji yadda abun ya faru sannan a yiwa tufkar hanci. Washegari kuwa tun misalin takwas na safe Yaya Bala yaci karo da wannan sabon Video ɗin a Fecbok, ga kuma turo masa da shi da mutane ke tayi ta WhatsApp. Sosai ya shiga cikin tashin hankali ganin wata sabuwa. Farko yaso yaƙi yarda da abun amma idan yaga yadda mutumin ke magana kuma gashi tsoho, sannan kuma ai gaskiya ne, yanzu ta mayar da sunanta Siyam Olusha ba Siyama Al-Hasan ba. Daidai lokacin Nasiru ma ya shigo ɗakin nasa yana nuna masa. An taru akan a samo mafita sai taro ya dawo sabon tashin hankali, domin kuwa lokacin da Umma taga video ɗin kasa magana tayi, ai kuwa ana cikin haka sai ga Siyama ɗin ta fito. Sosai Umma ta shiga faɗin abun dake ranta, shima Kawu Inuwa zuwa yanzu yayi laushi da lamarin ta. Sosai yaya Bala ya shiga bawa Umma hakuri tana faɗin "Wallahi Siyama ba ƴar rufin asiri bace, mai muka mata a duniya da muka cancanci haka, aihuwarta da mukayi ne laifin ko rainonta da shayarwar da mu kai mata, rashin lafiyar ta da makarantar da ne ko dai menene. Sosai Umma ta basu tausayi har dai yaya Bala ya kaita sashen ta. Shiru yayi yana tunanin abun yi, anya kuwa wannan shirun da yayi ba matsala bane, to me zai yi shida baida lafiya, wata zuciyar ta ce "Kaje ka sami ita Siyama ɗin kuyi magana domin har yanzu baka san komai akan abun ba. Haka ya tashi ya nufi sashen su Siyama ɗin. ***** *ADAWIYA DA BADAWIYA* Adawiya ta ce "Ba wai shawo kan wannan tsohon ne matsalar ba, yadda zamu shirya zama da gidajen talabijin din shine matsalar. Shiru Badawiya tayi tana tuna cewar ai tana da wani saurayi mai aiki a BBC sannan kuma shi babba ne a gurin Badawiya ta ce "Wannan mai sauki ne, kawai dai amincewar shi mutumin ne matsalar. Adawiya da bata yarda ba ta saki tsaki tace "Wallahi duk kece kika ja mana wannan abun da yanzu ba wannan maganar ake ba. Ita Badau (Wani lokaci ana kiran ta Badau ne saboda a yanke sunan wato Badawiya ( tayi shiru domin kuwa tabbas tasan ita ce ta ja. Badau ta ce "Yanzu ke kiji da shawo kan sa, ni kuma zan haɗa musu zama koda da gidan radiyo guda uku ne ko biyu. Haka suka shirya kowacce ta fara gabatar da nata aikin. Lokaci da Adawiya ta fara samun Olusha da maganar bai yarda ba, domin ba karamin jan kunne Oga Fita da Siyama ɗin sukai masa ba, musamman ma bayan samun wannan nasarar tasu, domin kuwa har kuɗi suka ƙara masa. Babu yadda Adawiya bata yi ba, amma yaƙi yarda hakan yasa ta barsa harna tsahon kwana uku. Nan ma babu yadda bata yi ba yaƙi, sai da suka mallaka masa gida harda mota kafin ya yarda zai yi hira da gidan radiyo, farko yace sai dai ayi audio amma suka ce kar ya damu babu abun da zai faru, idan ma Oga Fita yace a biya sa komai da ya basa su zasu biya. Hakan yasa ya yarda, suka zauna suka shirya komai yadda abun zai tafi. Bangaren Badawiya Badau kuwa, dama suma BBC suna so zasu yi hira da ita Siyama ɗin, domin magana nata yawo akan ta, wasu suce musulma ce wasu kuma suce Christa ce, hakan yasa babu wata-wata suka saka musu rana. Bayan fitar video ɗin kuwa sai ga abun da suke so ya samu, domin kamar dama abun da ake jira kenan labari ya yaɗu ta ko ina. Sosai abun yayi musu daɗi suna jira kawai suji labarin kwace aikin Baby and me da za'ayi da kuma rikici tsakanin iyayen Siyama da Siyama ɗin da kuma Fita da Olusha. Badau ce ta tura video ɗin cikin group ɗin su, duk da cewar kuwa wasu da yawa sun gani. Hakan yasa Oga Fita ya tara taron gaggawa. Adawiya da Badawiya ne suka fara isa gurin, kafin kace me kowa ya hallara amma babu Siyama. Cikin tsananin tashin hankali Oga Fita yake Tambayar Aida ina Siyama ɗin. Itama Aida ta ce bata san inda take ba. Nan fa Fita ya shiga faɗa yana zage-zage wai ita mai ya hana bata zoba. Adawiya ta ce "To tana ganin ita yanzu ta zama sele to mai zai kawo ta, yanzu ga shi irin abun da ubanta ya jawa mutane, kuma anyi taro domin a shawo kan abun ita da ya kamata ace tana gurin amma bata zo ba, to muma Meya amfanin zuwan mu, wa abun zai shafa idan ba ita ba. Aida ta kafe Adawiya da ido tana mamakin ƙarfin halin ta. Oga Fita ya daka mata tsawa yana faɗin "Kirufe mana baki a gurin malama" sosai kowa ya tsorata da tsawar da yayi. Shi Fita tunaninsa damar da suka samu karta kufce musu, sannan gashi yasan yadda Siyama take son iyayenta da tsoron su, tabbas idan har wannan abun ya baiyana zai iya rasa Siyama, domin yasan iyayenta zasu hanata kuma dole ta hanu. Tun ɗazu yake shiga da fita domin neman mafita, amma ya rasa. Ya taro wannan taron ne domin zai samu wata mafita guda ɗaya, shi har ga Allah baiyi zaton ko wasu daga cikinsu ne suka shirya ba, shi dai ya bari akan Olusha yayi halin su na ƴaƴan Adamu, kuma dole sai ya kai maganar gaba, dole sai ya sanar da shi waye ya saka shi wannan aikin bayan sun gama biyan sa. Oga Fita ya ce "Kaman yadda kuka ji wannan mutumin ya faɗa cewar Siyama ba ƴarsa bace to tabbas haka ne, amma komai da ya faɗa bayan haka duk ƙarya ne, kuma koda za'a gaiyaci ɗaya daga cikin ku zuwa hira wani gidan radiyo ɗin to ta ƙaryata komai da yace. Badau ta ce "Yaya za'ayi mu ƙaryata bayan ita da kanta bata zo ta ƙaryata ba, Adawiya ma ta ce "Ai tun da kaji ya faɗa to gaskiya ne, dama haka halin matsiyata yake, daga lokacin da suka samu ɗaukaka babu wanda zasu fara wulakantawa sai wanda ya taimakesu, yanzu dai gashi, anyi mata abu har yanzu bata ce komai akai ba, yanzu kuma munyi taro amma bata halarci gurin ba. Sai a lokacin Aida ta ce "Duk abun da wannan tsohon ya faɗa ƙarya yake, kuma ko shakka babu saka shi akayi, ita kuma Siyama tana gida bata da lafiya yau sati ɗaya kenan, ko ƙofar gida bata fita, kuma wayarta a kashe sai ɗazu ta kunna, yanzu abun da ya dace ayi yanzu Oga Fita shine mu nemo su waye suka haɗa wannan munafuncin, kuma ko shakka babu suna cikin wannan team. Aida na faɗa gurin ya kaure da surutai, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Shi kuwa Oga Fita kansa ya dafe yana tunani. Adawiya ce ta mayar mata da amsa "Sai dai ko idan kece kika haɗa komai domin kuwa kece kika san duk wani sirrin ta a wannan team ɗin, domin mu sai yauma muka san ita ba ƴar gidan Olusha bace. Aida ta ce "Ko kuma kuda kuke bakin ciki da ɗaukakar da Allah yayi mata ba" Lokaci ɗaya Adawiya ta ɗauke wuta, tana kallon Aida. Oga Fita ya ɗago yana kallon su. Lokaci ɗaya ya ce "Kowa yayi shiru. Kuma kowa ya tashi ya tafi an fasa yin taron. Haka kowa ya tashi sai kallon-kallo ake kowa na jin kamar ya kaiwa ɗan uwansa duka. Sosai video ɗin ya ɗauki hankulan mutane ga shi har yanzu babu wanda ya fito yace wani abu akan maganar, sai yan Socal media da aka bari da aikin yaɗa karya da gaskiya. Ana cikin wannan halin kamfanin Magazing wanda Adawiya take musu aiki suka sanar da ita cewar zasu yi aiki da ita na tsahon wata uku a Ingila zata je ta haɗu da sauran Models na kasashe daban-daban domin suyi aiki tare. Sosai murna ta samu team ɗin nasu Oga Fita duk da cewar yana cikin damuwa amma bai hana jin dadin abun ba. Washegari Adawiya suka tashi izuwa Ingila bayan ta gama shiryawa Badawiya komai. ****** *IBRAHIM* Haladu na jansa yana tirjewa kamar sabon mahaukaci, sosai yake tirjewa yana kiran sunan Siyama, shi dai Haladu abun da ya gani kuma yaji yafi karfin hankalin sa, sosai ya ƙara tabbatar da cewar tabbas Ibrahim yana son Siyama so ba na wasa ba, duk inda suka wuce sai an bisu da kallo domin kuwa Ibrahim buɗe baki yayi yake kiran sunan Siyama, duk wanda kuwa ya sanshi da Siyama dariya yake masa. A haka ya kawo shi har cikin gidan su kafin ya sanarwa da Hajja komai da ya faru tsakanin sa da Siyama. Ai kuwa Hajja ta fashe da kuka ganin yadda ɗan jikan nata ya koma kamar sabon mahaukaci a kan Mace. Sosai take kuka tana basa baki akan ya rufa musu asiri karya kashe kansa akan Mace, amma ina Ibrahim sunan Siyama kawai yake ambato. Ta shi yayi ya ɗauko wayarsa ya shiga gurin number ya latsa kira, amma bata shiga ba ita dai Hajja tana ta kallonsa. Ta ce "Ibrahim yanzu a kan Mace ka mayar da kanka haka, macen ma irin wannan mara tarbiyya da tunani, dan Allah ka yi hakuri ka samo wata ka cire tunaninta domin kaji tace bata sonka, dan Allah kaima kayi zuciya kaji ɗan ƙalilan?". Ibrahim ya ɗaga kai ya kalli Hajja sai kawai ya sunkuyar da kai ya fara ƙoƙarin tashi zai fita. Da sauri Haladu ya tare shi yana faɗin. "Wallahi Hajja a shiga tsakaninsa da wannan yarinyar domin tsaf zata iya aikata abun da tace, kin ga yadda take magana, harda cewa fa tayi zata sa a ɓatar da shi idan ya ƙara nuna ya santa. Ni Hajja shawarar da na basa ita ce, tunda har tace yaje yayi lissafin komai da ya kashe mata zata biya to kawai ya kai mata in yaso sai yayi amfani da kuɗin yayi wani auran". Hajja ta ce "Na yarda da maganar ka Haladu, kawai ta biya sa komai nasa. Haladu ya ce "Nifa na fara tunanin ma yarinyar bata da cikakkun hankula a kanta, domin irin abun da take yi kamar mara hankali. Ibrahim dai yana jinsu bai ce komai ba har suka gama Haladu ya bar gidan. ****** *SIYAMA* A hankali take tafiya domin bata bukatar kowa yasan da fitar ta. Ai kuwa cikin ikon Allah babu wanda ya ganta har ta bar cikin gidan. Tana tafiya kamar mara gaskiya sai juye-juye take tana kallon baya, gashi hijabi da tasa ya mata ƙadan, duk wanda ta wuce ta kusa da shi sai ya ƙara kallonta, wanda ya gane ta ya cigaba da kallo wanda kuwa bai gane ta ba ya girgiza kai ya ƙara gaba. Sai da tazo bakin titi kafin ta samu mai mashin tai masa kwatancen gidan Aida ta hau suka tafi. Suna zuwa ta sauƙa ta shiga cikin gidan domin karɓo masa kuɗin sa. Amma tana shiga gidan taga alamar babu kowa, sosai take mamaki domin kuwa tasan idan Aida bata nan to Jamila da jamilu koda yaushe suna cikin gidan a zaune. Dama ita har mamakin yaran take, domin zai yi wahala ka gansu a waje, kullum suna cikin gida kamar wasu amare, gasu da tarbiyya da ladabi, sosai take jinjinawa Aida akan tarbiyyar yaran duk da cewar yara ne amma dai tayi ƙoƙari, ƙarya ne tazo gidan basu gaida ta ba, gashi kullum kansu a ƙasa kamar wasu makafi, gashi basa da magana kwata-kwata ita dai yaran na burgeta. Haka ta shiga kiran sunan Jamila amma shiru sai kawai ta shiga ɗakin Aida ta kwanta domin kuwa wallahi bazata iya fita waje tace masa bata da kuɗi ba, sai dai ya tsaya har Aida ko Jamila da jamilu su dawo. Ta kai minti biyar a kwance sai taji kamar motsi a ɗaya ɗakin da yake jikin na Aida, hakan yasa ta sake saurara da kyau ai kuwa motsi ne harda ɗan ihu kaɗan. Hakan yasa ta tashi da sauri ta fita ta nufi ɗakin, a hankali ta tura tana raba idonta cikin ɗaki a ɗan tsorace. Gabanta ne ya fadi taji wani irin shok ya daketa lokaci ɗaya taji tana neman rasa tunaninta ganin Jamila da jamilu tsirara aihuwar uwarsu suna yin Seex. Innalillahi wa innalillahi raji'un! Take furtawa a ranta...📝 Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza writer [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FCWA_ _My WhatsApp channel_ https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Page 8️⃣* Sosai gabanta ke faɗuwa kana ƙara kallon ikon Allah, azuciyarta tana cika da mamakin wai Jamila da jamilu ne ke aikata wannan ɗan yen aikin, ganin basu ganta bane yasa ta sake leƙawa, ta ja musu kofar ta koma da baya har zuwa cikin ɗakin Aida tana jin wani irin tsoro a ranta. Waya ta ɗauko ta kira number Aida tana ɗagawa Aida ta ce "Yauwa yanzu nake son na kira ki, ki duba Email ɗinki zakiga sako, sannan maganar aikin Baby and me ya taso, yanzu haka maganar muka gama yi da Oga Fita, kuma an yanke shawarar Fita zai zo gidanku domin yayi magana da iyayenki, ya sanar da su gaskiyar magana, domin sanadin abun da ya faru yana son kawo matsala a aikin da za'ayi, yanzu haka mutane sai ƙara rura wutar abun suke yi. Cikin wata irin murya ta ce "Aida ina cikin gidan ki kizo yanzu". Aida cike da mamaki ta ce "Wani gida kuma ba nace miki karki fito yanzu ba, Kinsan ilar take tattare da fitowar taki kuwa, mai yasa ba kya da tunani ne wani lokaci, sosai Aida ta rikice har tana masifa, ita dai Siyama tasan za'ayi haka. Siyama ta katse ta da faɗin "Na riga na fito kawai kizo. Cikin mamaki Aida ke tambayarta lafiya kuwa take ya taji muryarta haka. Siyama dai ta katse wayar tana tunanin abun yi, shin ta sanar wa da Aida ne ko dai ta bari babu ruwanta, ko kuma ta samu Jamila da jamilu ɗin tayi musu faɗa da nasiha, sosai take ta sake-saƙe har taji ana sallama. Amsawa tayi tana bada izinin a shigo. Jamila ce ta shigo tana ganin Siyama ta tsuguna har ƙasa tana gai da ta. Siyama ta amsa tana binta da kallo. Ta ce "Na shigo gidan ban ga kowa ba, kuma ga gidan a buɗe, shine nace bari nazo na huta kafin ku dawo. Jamila tace "Eh anty Aida bata dade da fita ba, shi kuma Jamilu baya jin dad'i ne, yana kwance shine naje kula da shi har barci ya ɗauke ne. Tun da ta fara magana Siyama ke ta kallon bakin ta, tana jin abun da take faɗa, a zuciyarta tana mamakin ashe dai yarinyar ta iya magana har haka. A fili kuwa ta ɗanyi alamar tausayi ta ce "Aiya to Allah ya bashi lafiya amma ai asibiti ya kamata kuje ko? Ta ce "Kawai fa ciwon ne kuma na ɗan lokaci ne, wani lokaci yana masa haka dama. Siyama dai ta amsa da to Allah ya sawaƙe. Haka Ta bar ɗakin bata jima ba sai gata da abun sha harda soyayyen nama da cincin. Siyama ta ce "Nagode. Har Jamila ta juya zata fita Siyama ta ce "Am Jamila minti ɗaya mana please? Jamila ta dawo ta zauna ba tare da tayi magana ba. Siyama ta kalleta sosai ganin ko Fati bata kai ba, sosai take tunanin anya kuwa wannan uwa ɗaya uba ɗaya suke da Jamilu da kuma Aida ɗin kuwa! Ita sai yanzu ma ta tsaya ta ƙarewa yarinyar kallo, gata dai masha Allah amma ta ɓata rayuwar ta. Siyama ta ce "Idan akwai kuɗi a gurin ki, please kije waje a kwai mai mashin da ya kawo ni, to ban fito da kuɗi ba kuma yana jira na. Da sauri ta miƙe tayi waje Siyama tabi bayan ta da kallo. Gashi dai bayan nata ma ba wani girma suka yi ba, domin irin dogwayen yaran nan ne, marasa jiki. Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗauki nama ɗaya ta kai bakin ta. Lokaci ɗaya kuma abun da tazo yi ya dawo mata. Waya ta ɗauko ta buɗe data, sai ga sako daga email. Tana budewa taga daga campanin Baby and me ne, nan take ta shiga karantawa. Bayani ne akan sun shirya zasu fara aiki da ita, kuma ranar Laraba mai zuwa, kuma aikin na kwana uku ne, kwana ɗaya a kamfanin su dake Lagos, kwana biyun kuma duk a Maroco zasu yi, sosai take mamaki. A fili tace "Lallai baku da hankali wacce Siyama ce zata tafi har wani guri har kwana uku. Take taja wani gajeren tsaki tana ci gaba da kallon dokokin aikin nasu da suka turo mata, ita sosai take mamaki wai dama haka aikin Model ɗin yake ne. Ita fa a tunaninta kawai zaka je kamfane kayi musu hoton kayan da suke sai dawa sai kawai a sallame kane, amma shine harda kwana. Tana cikin haka taji sallamar Jamila ta ce mata "Anty yana ta zagi da kyar ya karɓi kuɗin ma fa" Siyama ta ce "Ai dole yayi faɗa yafa dade a gurin. Jamila dai bata ƙara cewa komai ba. Ganin haka yasa Siyama cewa "Dama kin ƙara masa kuɗi akan wanda yace ko? Ta girgiza kai! Siyama tace tom nawa kika basa tace "Yace wai ɗari huɗu shine na basa dubu daya ya bani ɗari biyar wai ɗari ladan jira. Ta faɗa tana miƙa mata canjin ɗari biyar ɗin. Siyama tace "Ai da kin bar masa gaba ɗaya kawai, to yanzu ai wannan naki ne ba nawa ba, sannan kina da account? Ta ɗaga kai. Siyama tace to bani sai na dawo miki da kuɗin ki harda kyautar da nayi niyar yi miki ko? Jamila ta girgiza kai ta ce "Wannan ma ai kuɗin ki ne, Anty Aida tace naki ne, shine yasa na baki chanji ɗin. Siyama da ta gano nufinta sai tayi murmushi tace "To kije na bar miki, kuma ki bani account ɗin naki kinji. Haka Jamila ta bata account ta tura mata dubu hamsin, tayi godiya ta bar cikin ɗakin. Sai a lokacin Siyama ta kalli uban kukadeden dake cikin account ɗinta. Ita fa sai ma yanzu ta tuna da cewar tun da aka fara wannan abun babu wanda ta bawa ko sisi, ita kanta bata samu natsuwar ci ba, kamata yayi ta fara siye bakin mutane da kuɗi, domin dai a kwai su, kuma sun fara zuwa ma kenan, domin ko ɗazu kuɗin da Baby and me suka rubuta na fement ɗin ranar ma kawai masu yawa ne. Da sallama Aida ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta rike da leda fara mai dan girma, sai Jamila da jamilu biye a bayanta kowa da reƙe da leda. Jamilu ya gaida Siyama sannan suka ajiye kayan suka fita. Aida cikin kulawa ta ce "Me ya faru naji muryarki alamar damuwa? Siyama dai sai bin Aida da kallo take bata ce komai ba har ta fara tsarguwa. Ta ce "Wai lafiya kuwa meye a jikin nawa? Ta faɗa tana bin jikinta da kallo. Siyama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Babu komai, ina so ne kawai na haɗu da wannan tsohon banzan Olusha, wallahi sai ya faɗa min a gidan oban waye mukayi haka da shi. Aida ta ce "Matsala ta dake kenan wallahi rashin nazari, ke yanzu idan aka ganki a gurin wannan mutumin me kike tunani zai faru, za'a ce kinje neman yafiya ko kinje ki masa wani abun. Kinga dan Allah bama wannan ba, yanzu wani kokari kikayi ta bangaren ki, yanzu fa kusan kwana goma fa. Bama wannan ba, kin duba sakon aikin naku ko? Kuma kinga lokaci kaɗan suka bayar hakan yasa Oga Fita ya yanke shawarar zuwa ya samu iyayanki da Umma. Domin nasan dai ke babu abun da kikayi. Siyama ta ce "Karki damu babu wanda zai zo gidanmu, nasan abun yi. Amma kuma Aida wannan aikin nasu kinji fa wai harda kwana, kuma harda barin ƙasa fa? Aida tayi dariya ta ce "To ke da meyi nufin ki, to ai ke dan ma a iya Afirka kika tsaya ne, bari ki fara aga aikin ki yayi kyau kigani har Jamani da Chaina da Faransa da Ingila za'a kiraki, yanzu Kinsan Adawiya ma tana Ingila kuwa? Siyama ta waro ido ta ce "Ingila dai? Aida tayi dariya tace "In sha Allah Siyama sai kin zama Model ɗin duniya ba iya Afirka ba. Siyama dai tayi shiru tana hango kanta tare da manyan Model irin su Razina da Alexander da Laila da kuma Oluwalu da kuma wanda take gani a matsayin madubi ko kuma tace yawan kallon aikinsa yasa ta fara sha'awar aikin Model, wanda take bin sa a duk wani kafa sadarwa da take yi Wato Adam Rezor. Sosai ta shiga tunanin Allah yasa watarana aiki ya haɗa ta da shi domin kuwa ita fan ɗin sa ce. Aida ta ce "Yanzu ga shawara? Kibi duk wani dankinki mai faɗa aji ki musu kyautar yanke talauci akan su zo su samu Umma su sanar da ita cewar Sana'ar Model sana'a ce kamar kowacce, kuma musulmai da Yahudawa da Kirista duk suna yi, kice su shawo kanta har ta yarda. Sosai Siyama tayi na'am da wannan shawarar haka ta kama hanyar gida tana tunanin rashin fadawa Aida halinda taga Jamila da jamilu a ciki, wata zuciyar kuma ta ce "To idan kuma ta sani fa! Daidai ta kusa fita Aida ta tsayar da ita tana zuwa ta ce "Kinga dan Allah maganar tafiya a ƙafa da wani boye-ɓoye duk ya ƙare yanzu. Acikin mutocinki wallahi sai kin ɗauki ɗaya kinje da ita gida. Wai ke an faɗa miki matsoraci na zama gwani ne, wa ya ce miki a haka zaki zama wata aba, kamata yayi ace izuwa yanzu sai abun da kika faɗa a gidan ku, amma kin tsaya kina tsoro. Siyama tayi murmushi tana jin wani ƙwarin gwuiwa amma gefe ɗaya tana cewa Aida baki san wacce Umma bane wallahi. Suna tsaye sai ga Jamila da jamilu sun fito da ledojin ɗazu sun bode wata arniyar mota sun zuba kayan a ciki. Aida ta ce "Waccer zaki ɗauka itace daidai ke. Siyama dai sai taji anya zata iya kuwa. Haka Aida tai mata dole har ta dauki motar ta fita da ita. Haka tana tafiya tana ƙara sakawa kanta ƙwarin gwuiwa, lokacin da ta shigo unguwar su ta New ariya dake Abuja, kasancewar unguwar dama ta yaku bayi ce, yasa duk inda ta wuce sai an ƙara kallonta, sosai ta dake tana kallon gabanta. Daidai tazo ta saitin gidan su Ibrahim zata wuce shi kuma ya fito, kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kai, shi kuma ya kafe ta da ido ganin ita ne yasa ya biyo bayanta da gudu. Ganin yana Binta yasa ta ƙara gudu hakan yasa mutane keta kauce mata, wasu na zagi wasu na Allah ya sawaƙe. Tana zuwa kofar gidan su ta sauƙa da kanta ta buɗe gidan kasancewar akwai gurin ajiye mota zai iya ɗaukar motoci uku, yasa ta shiga da motar, tana fitowa da niyar shiga gida sai taga Ibrahim yana haki na gudun da yayi. "Bani hanya na wuce? Ta faɗa tana harararsa. Ya ce "Siyama kashe ni kike son yi ne? Tsaya kiji abun da zance miki please? Lokaci ɗaya Siyama ta saki murmushi tunowa da tayi da shawarar ta ta ɗazu. Ta ce "Ina jinka" ya ce "Siyama dan Allah idan wasa kike min wallahi na horu haka, mutuwa kawai ya rage ban yi ba, wallahi ban san cewar san da nake miki har ya kai haka ba sai da kika fara min wannan wasan, dan Allah a tsayar da wasan haka, wallahi nayi alƙawarin idan har muka dawo kamar da zan zama miki duk abun da kike so. Kallonsa kawai take tana tunanin wai ita maima ya kaita fara wannan abun da wannan wawan ne. Ta ce "Yanzu da na baka miliyan biyar da mota da kuma na yarda na dawo soyayya da kai wanne ka tsaɓa? Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye ya ce "Wallahi Siyama ke nake so ba kuɗin kiba, na zaɓeki, bana son komai naki sai ke ɗin. Lokaci ɗaya Siyama ta waro ido waje tace "Kai lallai na yarda kai wawa ne kuma dolo kamar yadda ake faɗa. To ni wallahi ko dubu biyar nafi so a kanka kaji ma da kyau kenan. Ta ce "Zan baka miliyan goma da mota kaima kaje ka gina kanka amma dan Allah ka barni nayi rayuwata please. Ibrahim ya ce "Wallahi Siyama ko duk abun da kika mallaka zaki bani akan na daina sonki ba zan iya ba, ni Ke ɗin nake so, kuma domin Allah nake sonki. Lokaci ɗaya Siyama ta zuba masa ido, sai kuma wani tunani ya ɗauketa na minti biyu, ta shiga tunanin ko dai wannan shine soyayyar gaskiya da ake cewa, ko dai ta yarda da shine in yaso ta gina shi sai kawai ta auresa ta dinga juyashi kamar ita ce matar, to ai kuma bata son sa, ina zata kai son mutumin da ta gama narkewa a cikin sa, duk da bai san tana yi ba, to amma idan ta yarda ta auri Ibrahim bata muzanta ba. Kuwa, kaman ita ta auri wawa. Lokaci ɗaya ta dawo tunaninta ta ce "Kai wawa ne, kaje gida ko ka samu abokinka kayi shawara da shi, ko kaje ka samu wannan tsohuwar kakar taka kayi shawara da ita, idan ka gama ina jiranka, domin dai na fahimci kai baka san me kake yi ba har yanzu. Tana faɗa ta kama hanyar gida ta barsa tsaye yana kallonta. Tana shiga cikin palon taga Umma da da Nasiru da Yaya Bala suna zaune sai Fati da take cin abinci. ****** *YAYA BALA* Lokaci da suka je ɗakin Siyama sai suka tarar bata nan hakan ya ƙara ɓata ran Umma sosai, ta shiga faɗin "Yanzu shi kenan Siyama tafi ƙarfinmu ko Bala, muna gidan nan da ita sai ta saka ƙafa ta fita nata gurin babu wanda ya sani ko, to wallahi na gaji ba zan iya ba, ka kira min ita yanzu duk inda take tazo gida ina son ganin ta. Sosai Umma tayi faɗa Yaya Bala dai sukai mata shiru domin shima harda shi take haɗawa. Haka Umma ta dawo Palo tana jiran a kira mata Siyama. Yaya Bala ya kalli Nasiru ya ce "Ɗauko wayarka ka kira ta" Nasiru ya shiga ɗaki da niyyar ɗaukar wayar, koda ya ɗauko baida kati a ciki, hakan yasa Yaya Bala yace a barta ai zata dawo duk ma inda taje. Yaya Bala ya kalli Umma cikin kwantar da murya ya ce "Umma magana nake so muyi akan karatun Nasiru da Siyama. Umma ta juyo ta kallesa har yanzu ranta a ɓace yake. Ta ce "Ita Siyama yanzu wani karatu kuma ya rage mata, yarinyar da tafi ƙarfin iyayenta, yarinyar da take da gaban kanta, kuma yanzu maganar aure zaka yi kawai ba karatu ba, ina so ka samu shi yaron da take tsayuwa da shi ya ruro idan da gaske yake kawai ayi mata aure mu huta, domin ni na gaji da wannan halin nata. Yaya Bala ya sauke ajiyar zuciya ya ce "To Umma shi kuma Nasiru fa, kinga yanzu suna shekarar karshe ne, kuma har yanzu hannunsa bai warke ba, gashi yanzu maganar kuɗi ne, bamu biya kudin jarabawar ba har yanzu kuma gashi ciwon nasa sai an ƙara komawa asibiti, ni dai nawa Alhamdu Lillah, shima sabo da yana da ƙanjiki ne ciwo ko yaya yake a jiki sai yaƙi warkewa. Umma tayi shiru tana tunanin lokacin da mahaifin su wato Al-Hasan shima haka yake da ƙanjiki koyaya yaji ciwo to ya fara ƙaruwa kenan ko yaƙi warkewa, sai sun sha fama sosai. Tabbas shi Nasiru da Siyama suka gado, itama haka ciwo yake mata ya bata wahala sosai. Umma ta kalli Yaya Bala ta ce "To ko shi Nasiru zai bar karatun ne har bayan shekara idan ya warke, kaga sai muji da kuɗin maganin ko? Domin kaga yanzu idan ba hakan a kayi ba zamu shiga cikin matsala. Yaya Bala ya ce "A'a fa Umma yanzu maganar barin karatu har sai wata shekarar ba dabara bace, domin idan shekarar ta dawo sai mun biya komai da muka biya a baya, kuma shi kansa ba zai ji daɗin karatun ba. Umma tayi shiru cen ta ce "To ko zaka je gurin masu gidan naku su bada kuɗin hayar wannan shekarar ne idan yaso kaga ko shekarar ta ƙare sun biya kenan ko? Yaya Bala yayi murmushi ya ce "Umma ko wata biyar bai yi bafa da suka bamu na waccer shekarar, kuma shima da yaya suka haɗa mana, yanzu kuwa muna zuwa zasu ce ai shekarar bata yi ba, kawai dai Umma bari na kira shi Nasiru ɗin muji ta bakin sa. Daga nan yaya Bala ya shiga kiran Nasiru sai gashi ya fito rike da waya a hannu, hannun ciwon nasa ya kumbura sosai babu ko kyawun gani. Bayan ya zauna Umma tace ya tashi ya kira mata Fati. Bayan sun zauna ta mayar musu da duk yanda sukayi, Nasiru ya ɗago da sauri jin abun da ake ciki. Ya ce "Yaya shekara mai zuwa fa cikin jiniyoyina fa zan shiga duk abokaina lokacin sun tafi sun barni, gaskiya Yaya a'a ba zan iya jira har wata shekara ba. Umma ta ce "To da wani hannun zaka yi karatun da rubutun ana magana kana faɗin ba zaka iya ba kamar wani karamin yaro, ko baka fahimci matsalar da ake ciki bane, duk akan maganar kuɗi ne, yanzu ma asibiti za'a koma a kan wannan hannun naka amma kazo kana abu kamar karamin yaro. Nasiru dai ya cuno baki ya shiga haɗa rai. Fati dai tayi shiru tana sauraronsu. Bayan kamar minti biyu Umma ta ce "To ko za'a saka wancen gidan a kasuwa ne, idan yaso sauran kudin sai ka fara wani kasuwancin da shi, tunda kaga aikinku ba kullum ake samu ba ko? Da sauri Yaya Bala ya ce "No a'a Umma ba zamu sayar da abun da muka mallaka na gado ba. Ya ce "Umma idan muka sayar da gidan zamu zo muyi da na sani, domin gidan Nasiru nake so idan Allah ya kai mu lokacin auransa sai kawai a gyara ya shiga. Cikin faɗa Umma ta ce "To Allah zai hore muku in sha Allah kafin lokacin ku siya wani, yanzu yaya kake so ayi, wannan dai gida naku ne, bayan shi baku da wani abu da za'a sayar asamu lafiya da kuma ci gaban karatun ku, to yanzu ni dai na gama magana aje a sayar Allah zai hore, lokacin da ka sayi wannan gidan kasan zaka samu kuɗin ne, Allah ne yaso kuma ya nufa har ka siya, sabo da haka ku dinga kyautata zato mai kyau ga ubangijinku shine ke yi a lokacin da babu mai baka. Sosai Umma ta shiga faɗa cikin na nasiha hardai suka yarda akan za'a sayar. Bayan an amince ne yaya Bala ya ce "To Umma yanzu mu sanarwa da Kawu Inuwa da Baba (wato Husaini ƙanin mahaifinsu shi suke cewa Baba) Umma ta ce "Eh ai dole zasu sani. Fati dai tuni ta tashi ta shiga cikin gurin Binta da ta bari tana ƙarasa abincin nasu, ganin bata gama bane yasa ta ɗauki kwano ta ɗebo kaɗan domin yunwa take ji. Haka ta fito palon ta zauna Umma ta bita da kallo domin kuwa tasan ba'a gama ba ta ɗebo. Umma ta sake cewa da Yaya Bala "Yanzu wacce sana'ar kake ganin zaka fara ? Kafin yayi magana suka ga an turo ƙofar an shigo, gaba ɗaya suka mai da kallonsu ga ƙofar. Siyama ce riƙe da kin mota a hannu. Itama kallonsu take, ganin yadda suka haɗu family amma babu ita a ciki sannan babu Anty Zainab. Sallama tayi tana kallon hannun yaya Nasiru da yayi wani irin kumburi wanda bata taɓa kula ba. Kusa da shi taje ta zauna tana ta kallon hannun. Umma dai tun kallo ɗaya bata ƙara bi ta kanta ba. Yaya Bala a karon farko da zai yi magana da ita kenan tun da abun ya faru. Ya ce "Daga ina kike? Wa kika fadawa zaki fita? Kamar daga sama taji tambayoyin nasa domin sai yanzu ya shiga sha'anin ta tun da komai ya baiyana. Sai da ta tabbatar da ta haɗa maganar a bakin ta tsabar rudewa kafin ta iya cewa "Dama da dama dama naje gurin mutumin da yayi min Sherri ne ku... "Wani tsawa da Umma ta daka mata ne yasa ta bata san lokacin da ta zamo ƙasa ba. Sosai ran Umma ya ɓaci jin tana neman raina musu wayo wai yayi mata Sherri. Ta ce "Da baki je kin sanar da shi komai ba yaya za'ayi ya sani, idan baki fito kin faɗi gaskiyar inda kika je ba, Allah zan shayar dake ruwan mamaki, kuma daga nan zaki haɗa kayan ki ki koma gurin shi arnen uban naki. Umma ta faɗa tana miƙewa tsaye domin Umma nada zafi sosai, abu kaɗan ke ɓata mata rai. Yaya Bala da shima saida ya tsorata da irin wannan tsawar da Umma tayi ya ce "Wannan makullin motar ta waye? Siyama da ta gama tsorata ta ce "Mota ta ce" kallon-kallo aka fara yi a palon. Ya ce "Waye ya baki? Sai a lokacin Siyama ta ɗago ta kalli Umma ganin ita take kallo sai tayi saurin yin ƙasa da kai, sosai take son aro jarunta tasa a kanta amma da ta haɗa ido da Umma sai ta kasa, tabbas tsoron da Umma ta saka musu nata tun suna yara yayi tasiri akan Siyama, domin duk yadda takai da son yin magana mai ma'ana da ta kalli Umma sai komai ya kwance mata. Sosai Umma ta daure bata sharara mata mari ba jin ana tambayarta ta yi shiru. Yaya Bala ya ƙara maimaita tambayar ta ce "Tawa ce da na samu bayan nazo ta biyu" Sosai yanzu harda Yaya Bala ɗin suke mamaki. Ita dai Umma bata fahimta ba, haka kawai sai a bata mota dan tazo ta biyu dole akwai dai wani bayanin. A lokacin wayar Siyama ta shiga ƙara ta duba taga Aida sai ta kalli Umma da Itama ita take kallo suna haɗa ido ta kawar da nata. Yaya Bala yace ki ɗaga mana. Kafin ta ɗaga kiran ya katse. Nan sai ga wani kiran. Tana ɗagawa Aida ta ce "Ke a kwai matsala fa, babu yadda banyi da Oga Fita ba amma yace Wallahi sai na kawo su gidan ku, wai masu aikin ne suka matsa sosai, shi kuma baya so ki rasa aikin yanzu haka gamu a hanya, domin kina fita yazo Allah ne ma yayi ba zaku haɗu ba. Siyama ta gama shiga ruɗu ta ce "No dan Allah karki kawo shi please " Aida kuwa ta miƙawa Oga Fita waya shi kuwa ya ce "Naga ke ɗin ce har yanzu baki yi serus bane, kawai yau ayi komai. Yana faɗa ya ka she wayar. Lokaci ɗaya hawaye suka zubowa Siyama. Yaya Bala ya riga Umma yin magana ya ce "Su waye zasu zo?" Ba tare da ta kalli kowa ba ta ce "Oganmu ne zaizo yayi muku bayani domin ni bazaku yarda da niba. Umma dai sai kawai taji Siyama ɗin ta bata tausayi ganin tana hawaye. Binta ce ta fito daga kicin tana faɗin an gama abinci a kawo yanzu ne? Yaya Bala ya ce "Bari tukunna baƙi zasu zo yanzu sai kawai a kawo idan sun zo. Yaya Bala ya dawo da kallon sa izuwa ga Siyama ya ce "Kenan shine yasaka ki a wannan abun shi ogan naki?* Lokaci ɗaya Siyama ta tuno da wanda yasa mata kwadayin abun, sai kawai taji wani irin ƙwarin gwuiwa yazo mata ta ce "Babu wanda ya saka ni, kawai ina son abun ne tun ba yanzu ba. Ta faɗa a dake. Binta dai sai bin Siyama da kallo take, sannan a karo na farko da take wa Yaya Bala kallon ƙurulla tun bayan da Momy (wato mahaifiyarta) ta ɗarsa mata a kan cewar ta dinga manne masa komai tai masa ko Allah zai sa ta maye gurbin matarsa Zainab. Farko Binta taji tsaro domin bata taba harsaso haka a ranta ba, kuma tana ganin yayi mata girma, mai zai hana ace Nasiru amma Yaya Bala ina zata kai shi. Sai da Momy tai mata dogon bayani sosai kamar yadda itama akai mata akan cewar ai yanzu Siyama zata fara samun kuɗi na bam mamaki domin yanzu ta zama salebiriti. Hakan yasa take so aci kuɗin da ƴarta. Sosai Binta ta yarda Duk da bata jin sonsa ko na ɗugo ɗaya. Yaya Bala ya ce "Siyama shekarar ki nawa? Kin gama karatu? Mai muka rageki dashi da har kika zaɓi wannan aikin na zubar da mutunci? Siyama ta ce "Yaya wallahi babu abun da kuka rageni da shi, kuma banyi komai ba sai sabo da ku, duk abun da nake yi sabo da kune wallahi yaya. Yanzu haka na mallaki abubuwa da dama harda motoci da kuɗaɗen da ban san a dadin su ba, kuma yanzu haka na samu wani aiki shine nake tsoron tambayar ku, dan Allah karku hana ni, wallahi zan kula da kaina nasan me nake yi, please dan Allah yaya, kuma wannan maganar da tsohon nan yayi duk ƙaryace wasu maƙiyan nawa ne suka haɗa baki dashi domin aci mani mutunci amma zan gano koma su waye, kuma zaku gani please Umma. Ba Nasiru da Fati da Binta ba, har Umma da Yaya Bala saida suka shiga mamaki. Lokaci ɗaya Nasiru ya tashi daga ƙasa ya zauna a ransa yana jin ya samu mota. Ita kuwa Binta gaba ɗaya ma ruɗewa taso yi, domin kaɗan ya rage ta nuna kanta a gurin. Yaya Bala ma dai jin abun da take cewa yasa ya kalli Umma. Umma ce ta fara buɗe baki zata yi magana suka ji anyi sallama. Amsawa akayi kafin Aida ta shigo, sai Oga Fita sai wani mutumi sanye da bakaken kaya. Guri aka basu suka zauna aka shiga gaisawa. Fita baya jin Hausa shida baƙon nasu. Umma kuma bata jin turanci. Hakan yasa lokacin da suka gai data sai kawai ta ɗaga musu hannu. Yaya Bala yasa Binta da Fati suje su fito musu da abinci. Lokaci ɗaya Siyama ta tuno da Jamil da jamilu yanzu haka suna cen suna aikata iskancin su, kallon Aida tayi ganin tana ta sunne kai, lokaci ɗaya suka haɗa ido kowa na tausayin junan su da irin nufinsa. Yaya Bala yayi wa su fita tayin abinci. Suka sha abun sha suka ce a ƙoshe suke. Yaya Bala dai sai kallon Siyama yake akan tayi musu bayanin mutanen, kaman kuwa tasan abun da yake nufi ta fara jawabi. Ta nuna Oga Fita tace "Wannan shine Oga Fita ogan mu. Ta nuna Aida ta ce "Wannan sunanta Aida abokiyar aiki nace, kuma ƙawata. Waccen kuma ban san sa ba. Ta nuna gurin da wannan mai baƙaƙen kayan yake. Umma sai kallo Aida take ganinta kyakkyawa da ita, a ranta tana faɗin Sai dai babu kyawun zuciya. Oga Fita ya fara maganar abun da ya kawo su. Ya fara basu labarin yadda akayi yasan Siyama da kuma lokacin da suka fara aiki tare, har dalilin da yasa suka ƙirƙiri iyayen ƙarya akan tana tsoron a gano cewar itace a gidan su domin tana tsoro sosai. Har dai lokacin da ta samu nasarar zuwa ta biyu da irin kyautar da ta samu da kuma aikin da ta samu na Model. Sannan ya warware musu gaskiyar magana akan abun da Olusha yayi cewar ƙarya ne. Yana yi Nasiru na fassarawa Umma. Bayan ya gama jawabin ne ya ɗora da faɗin abun da ya sani iya gaskiyar sa akan aikin Model..."Aikin Modelling aiki ne mai kyau wanda mutum zai tara kuɗi sosai, kuma mutum zai zama salebiriti a duniya, duk inda ka shiga za'a san ka. Kuma aikin kowa nayi muddin kana da jiki mai kyau. Saboda haka ina baku shawarar da kuyi hakuri kubar Siyama ta fara wannan aikin zakuyi alfahari da ita kuma zaku samu kuɗi. Fita ya nuna wannan mutumin ya ce "Wannan ɗaya daga cikin mutanen da zata yi aiki a campanin su ne, to suna ta damu na akan sai tazo an fara ni kuma na sanar da shi cewar ai tana da ɗan matsala da iyayenta ne, shine ya ce azo tare da shi yaji meye matsalar ku. Ya ƙarasa yana bawa mutumin damar yin magana. Mutun ya ɗaga musu hannu ya fara da faɗin "My name is Dele Ali I'm from England London, I'm the manager of the Baby and me Company for Nigeria and Marocco. Yaci gaba da faɗin...mun ga Siyama a taron kyau na nan ƙasa Nigeria kuma tayi kyau da irin kalar da muke so mu dora a fuskar tallan kayan mu, shine muka zo neman yarda ta da ta iyayen ta, zamu yi aiki da ita a duk inda muke da gurbin kamfani. Kuma mun dauki nauyin baku jari daga garemu, harda gida kyauta anan garin Abuja duk daga garemu. Sosai Nasiru yake aikin fassara, ita dai Umma sai saurara take har aka zo karshe. Binta kuma ta gama cika da mamakin jin irin abun Alkairin dake tunkaro wannan ahalin. Kafin kowa yayi magana Oga Fita ya ɗora da faɗin... "Yarinyar ku tana da hankali domin tasan me take yi, kar kuji komai a kanta ko ni na yarda da ita...📝 Love all One love Comments Ana shering Love my fan's By S-Reza writer [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FCWA_ *TA'AZIYA!* _Ina miƙa saƙon ta'aziya ga ƴan uwan Marubuciya *Rahama na lale* da masoyanta da ma ƴan uwa marubuta na wannan rashin da mukayi. Allah yaji ƙanta da rahamarsa ya gafarta mata, Allah ya kyautata makwancinta, Allah ya sadata da Annabin rahama, Allah ya amshi baƙuncin ta. Muma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani, Allah yasa muyi kyakkyawan ƙarshe. Ilahiran mamba na kungiyar first class suna ƙara bayar da saƙon addu'ar rahama da jin ƙai cikin ga Rahama na lale, Allah yasa ta hutu. Amin ya Allah rabil alamin._ *Page 9️⃣* Yaya Bala ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Nasiru da yake ta murmushi yana karasa fassarawa Umma maganar Oga Fita. Siyama dai kanta na ƙasa tana addu'ar Allah yasa Umma ta yarda da wannan aikin. Yaya Bala ya ce "Umma me kika ce? Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ka sanar dasu cewar bazata yi ba, kuma Aure zamu yi mata, sannan karsu ƙara zuwa gidan nan daga yau. Tana faɗa ta miƙe tsaye tabar palon tana jin ta kaicin rashin jin yaran nasara da ba tayi, wallahi yau da sai taci uban mutanen nan mai baƙaƙen kayan nan, wato su ga mayun kuɗi talakawa sai su salwantar da rayuwar ƴarsu akan wasu kuɗi, har suna kallon idonta a matsayin ta na uwar yarinya wai jikinta yayi kala da irin jikin da suke so, ita tun kafin ma ayi nisa taso ta tsayar dasu amma bata san me zata ce ba. Sosai Umma ta shiga damuwa jin yadda abun yake, tunda har ake kashe kuɗi har haka to tabbas wannan sana'ar bata kirki bace, kuma ma dole sai yara mata kuma suma dole ne sai yara ƙanana mai zai hana su nemo manya idan ma dole sai mata ne ai sai a nemo masu hankali ba irin su Siyama ba. Yaya Bala ya dawo da kallon sa izuwa ga su Fita cikin harshen nasara ya ce "Mahaifiyarta bata yarda ba, wai karatu take yi yanzu, saboda haka kuje duk yadda ake ciki ita Siyama ɗin zatayi muku ƙarin bayani. Oga Fita yace "Kafin ranar Alhamis ake so a fara aikin fa, yau kuma kaga muna Litinin ne? Yaya Bala yace babu damuwa. Haka suka fita harda Aida da ta mugun tausayawa Siyama, domin zai yi wahala Umma ta yarda. Suna fita Nasiru ya ce "Kai wallahi wannan karan harda ni za'a shawo kan Umma, irin wannan abun Alkairin haka, ke kuma dan ƙaniyarki tun tuni dama kina da kuɗi shine kika barmu kina gani bama da lafiya ko ki ɗan sayo mana kaji muci, amma dai ke anyi ƴar ɓakin ciki. Yanzu dai bani makullin motar naje na gani, kinga da lafiya nake ai ko ɗani sai na tafi. Yana faɗa ya amshi makullin motar ya fita. Yana fita yaya Bala ya miƙe yayi hanyar ɗakinsa ba tare da yace wa kowa komai ba. Binta kuwa gyara zama tayi ta fara cin abincin ta. Ita kuma Aida taso tayi magana da Siyama ganin ko motsi batayi ba amma har suka bar gidan bata samu damar yin hakan ba. ****** *SIYAMA* Sosai take addu'ar Allah yasa Umma ta yarda da wannan abun, jin yadda fita yake faɗar maganar sam babu karsashi, sai ambaton za'a samu kudi yake ta yi. Da mamaki taji Umma tayi wannan furricin, hakan yasa ta ɗago tana kallon Umma karo na farko da ta iya kallonta cikin ido tana jin zata iya cewa komai yanzu. Bata ƙara shiga rikici ba sai da taji cewar wai aure za'ayi mata, sosai tayi suman zaune tana aiyana abun da zai faru idan suka ce aure zasu yi mata. Ita fa sabo da irin haka ne fa yasa bata bawa kowani Namiji damar shiga rayuwarta ba bayan wannan ƙazamin, shima tayi haka ne domin tasan babu yadda za'ayi ya iya mata komai koda ta nuna masa bata son sa, domin kuwa shi ɗin dole ne kaman yadda ake faɗa, sosai ta shiga tunani har bata san lokacin da su Fita suka bar gidan ba, haka bata san lokacin da yaya Nasiru ya ƙarbi makullin motar ba, haka bata san lokacin da yaya Bala ma ya shiga ɗaki ba, sai ji tayi ana ɗaga ta. Tana ganin Fati sai ta miƙe suka shiga ɗaki. Fati ta fito ta ɗibar musu abinci, ta juya ɗaki, itama Binta ganin an barta ita kadai sai ta tashi ta ƙara abincin harda nama da yawa kafin itama ta koma cikin ɗakin. Zata shiga suka ci karo da Fati zata fito, wucewa tayi tana kallon cikin kwanon nata. Fati abincin ta zuba ta ɗauki ruwan sha da abun sha ta nufi sashen Umma. Bayan ta dawo ta sake ɗiba da nufin kawai Yaya Bala duk da kuwa taga abincin kafin ta dawo daga kaiwa Umma kamar an diba. Zata tafi kenan taga Binta ta fito daga sashen Yaya Bala ɗin tana sakin murmushi! Kallonta tayi ta ce "Abinci kika kai masa? "Ta amsa da eh" Fati tayi murmushi ta ce "Kin kyauta ƴan Mata" Binta ta ce "Nabi ƴan mata da gudu ba takƙalmi. Aranta tana jin ko dai Fati ta ganota ne. Haka suka koma ɗakin suka tarar da Siyama na waya. ****** *IBRAHIM* Bai taɓa zaton Siyama da gaske take masa ba, shi duk a tunaninsa wasa ne, sosai ya maƙale a gurin har ta shiga cikin gida, dawo da kallonsa yayi izuwa ga motar da ta fito a ciki. Kallon motar yayi yana girgiza kai. Kusa da motar yaje ya shafa ta, yana jin son motar a ransa kawai sabo da motar siyamarsa ce. Sosai ya shagala da kallon motar har bai san ya dade a gurin ba. Haka ya fita yana tafiya yana tunanin tayaya zai yi rayuwa babu Siyama. Yana tafiya mutane suna ta kallonsa domin kuwa kowa yaga lokacin da yake bin motar da gudu. Haka har yazo gida yana tunani. Yana shiga ya tarar da Hajja da Nana sunyi tagumi na rashin madafa, domin tun da wannan abun ya faru Ibrahim yaƙi zuwa aiki, abun da zasu ci kullum a kame-kame ake, yau ma da kyar dai tayi sa'a ta rarra shesa akan zai je, duk da ya makara shine yana fita yaga motar Siyama shine ya bita a guje kamar yadda aka zo aka sanar mata. Ita izuwa yanzu bata san yadda zatayi da shi ba, babu wanda zata kaiwa ƙararsa, dama a kwai ƙanin mahaifinsu wanda suke ƴan kishiya da kuma ƙanwar su autarsu. To tun a gurin rabon gado akayi bata kashi har takai da anyi doke-doke tsakanin su da su, hakan yasa suka fita samgar juna. Matar mai suna Maryam suna ce mata Inna. Itace kishiyar Hajja. Yayin da Hajja ta haifi iya mahaifin su Ibrahim wato Nasiru. Ita kuma Inna ta haifi Shuaibu da Sadiya. Bayan mahaifinsu ya rasu ne aka zo rabon gado wanda dama babu jituwa tsakanin su tun abaya. Hakan yasa aka sha fama sosai, mahaifin su Ibrahim ya tsira da wannan gidan sai kuɗi da kuma abun hawa guda ɗaya. Su kuma su Shuaibu da Sadiya suka mallaki asalin gidan da suke ciki da abun hawa biyu da kuɗaɗe masu yawa. Suma matan nasu aka ware musu nasu. Daga nan kowacce taja yaranta suka ware. Ahaka dai har mahaifin su Ibrahim ɗin yayi aure yana buga-buga. Bayan ya haifi Ibrahim ne ya samu aiki da yake yayi kasancewar duk sunyi karatu. Sai dai kuma aikin da ya samu sai ya bada cin abinci kafin a ɗauke sa. Hakan yasa ya sayar da motar da ya bayar ake masa haya da ita kasancewar Motar Boss ce. Cikin ikon Allah kuwa ranar da ya fara aikin a ranar aka haifi Aisha wato Nana. Sosai ya fara aiki kuma babu laifi ana biyan sa da tsoka. Shekarar Nana huɗu mahaifiyarsu ta ƙara samun juna biyu, a wajen aihuwa ta rasu bayan ta haifi jaririyar, ita jaririyar a ranar ta koma. Sosai suka shiga cikin damuwa da rashin ta acikin su ,mata mai mutunci da taya muji rufawa juna asiri. Bayan rasuwar Mufida shima bai jima ba yana dawowa daga gurin aiki suka yi hatsari a mota haya yaji ciwo sosai, bai mutu ba har sai da yayi kwana uku a asibiti. Tun daga nan Hajja ta shiga ɗawai niya da jikokinta har ta samu ta saka Ibrahim a gurin aikin mota, Sukuma gurin aikin da mahaifin nasu yake aiki suma suka taimaka musu da kuɗi masu ɗan kauri dashi tajari a cikin gida har ta saka Nana a makaranta da yake lokacin Ibrahim yana secondary. Cikin ikon Allah har ya fara iya aiki ana biyan sa, harma takai ana iya turasa aiki shi ɗaya, ga mota da ya iyaja, zai iya jan mota daga nan har gurin da motar zata iya zuwa, hakan yasa komai ya dawo kansa itama ta huta, har zuwa yanzu da wannan ƙaddarar ta soyayyar ƴar iska da ta same shi cewar Hajja. Bangaren su Shuaibu da Sadiya ƙannen mahaifinsu kuwa suma duk suna raye. Ita Sadiya tayi aure a Kano yanzu haka tana da yara uku biyu mata ɗaya Namiji. Shi kuma Shuaibu yana garin Abuja amma cikin gari da matansa biyu yara huɗu uku na uwar gida daya na amarya, sai agola guda ɗaya da amaryar tazo da shi duk da cewar ya girma. Sai kuma Inna da suke tare a gida ɗaya da matan ɗan nata. Yanzu Shuaibu yayi kuɗi sosai domin ya dilmiya a cikin siyasa bayan kasuwancin da yake yi, kuma sosai yake da matsayi a cikin jam'iyyar tasu. A kwai rashin jituwa sosai tsakanin matansa da mahaifiyarsa domin Inna tana da faɗa sosai da shiga abun da babu ruwanta, hakan yasa matan suka hade mata kai duk da cewar suma ba ƙaunar juna suke ba. Uwar gidan mai suna Zainab mai yara uku Sani salis Sadiq. Sai amaryar mai suna Blesin mai yarinya ɗaya Latifa. Christa ce ita, kuma haka ya yarda ya aureta amma kowa zai yi addininsa, yara kuma gaba ɗaya shi zasu bi. Haka ta yarda shima ya yarda. Tace yaronta guda ɗaya da take da shi a gurin tsohon mijinta ya ishe ta.(Wannan kenan) Kallonsa Hajja tayi ganin ya wuce su zai shiga ɗakin sa. Ta ce "Ibrahim yanzu haka zamu cigaba da rayuwa a gidan nan, duk ka sauya rayuwarmu? Ta faɗa muryarta na fita da kyar tsabar yunwa. Ya dawo da baya ya ce "Hajja wai da gaske take bata sona dan Allah kije gidan su ko zata faɗa miki cewar wasa take min, dan Allah Hajja ki taimaka mani. Hajja ta sauke tagumin da tayi ta ce "Kalil wallahi yarinyar nan ba matar auran kabace, dan Allah ka rufa mana asiri ka hakura da ita Allah zai saka maka akan abun da tai maka, yanzu wannan abun da kake yi mu yake shafa da muke tare dakai, ko badan kowa ba ko sabo da wannan ƙanwar taka dan Allah ka dawo tunaninka Ibrahim, yanzu kallemu babu abun da muka saka a bakunan mu tun safe, da Allah muka dogara sai kuma kai mai bamu, yanzu idan ka ɓata rayuwar ka ina zamu saka kanmu. Ibrahim ya ce "Hajja babu abun da zai same ku in sha Allah, damuwata ku tausaya min halin da nake ciki, zan iya shiga wani hali idan na rasa Siyama, ba zan iya yin komai ba dan Allah Hajja kije gidan nasu kiji ko Allah zai sa ta faɗa miki gaskiya. Ibrahim ya ƙarasa yana faɗawa jikin ta yana ƙoƙarin mayar da kukan dake son zuwar masa. Hajja ta ce "Tom naji zanje amma sai ka tashi ka tafi gurin aiki yanzu domin zaka samo mana abun da zamu ci kaji? Ya ce "Da gaske kike zaki je gidan su Siyama ɗin? Ta gyaɗa masa kai hawaye na zubo mata, tana tausayin sa, duk wannan halin dolancin nasa ne yasa har tayi wasa da tunaninsa har haka. Tsoron ta ɗaya karfa ya ƙara zama wani sauna akan wannan abun. Haka Ibrahim ya tashi ya nufi gurin aiki yana tafiya yana zancen zuci a cewarsa amma idan kana kusa da shi zaka dinga jin abun da yake cewa. Yana fita Hajja ta ce da Nana "Je gidan su Hajara kice ta baki shinkafa kwano ɗaya da gawayi da mai kafin Ibrahim ya dawo? Kasancewar dama wani lokaci haka sukayi kuma matar tana basu, idan kuma Ibrahim ɗin ya dawo ya bayar a kai mata. Ibrahim bai dade da fita ba sai ga Abokinsa Haladu ya shigo gidan da sallama. Bayan hajja ta amsa ne ya samu guri ya zauna a kan shinfiɗar da take. Nan suka shiga sabuwar gaisuwa. Haladu ya dubi Hajja ya ce "Dama ina waje naga fitar Ibrahim shine nace bari na zo na sameki muyi magana akan halin da yake ciki. Hajja ta gyara zama da kyau ta dubi Haladu ta ce "To ka ga dai halin da ake ciki dama yaya Ibrahim yake bare yanzu da wannan yarinya ta ƙara susutar da shi... Dama yanzu nake tunanin ko zan je chan gurin ƙanin mahaifinsu ne na sanar dashi halin da ake ciki koda ɗaukesa ne yayi daga nan ko Allah zai sa a dace ya manta da ita, to amma shi din ma ina taron abun da zai biyo baya domin babu shiri tsakanin mu da su tun ba yanzu ba, kuma na rasa ma wa zamu sanarwa da wannan abun. Hajja ta karasa tana tagumi duk tayi kalar tausayi sosai. Haladu ya ce "Alasarki ai Hajja ba ma sai kun je gurin sa ba, dama ranar da muka je gurin ita Siyama ɗin tare da shi, to a ranar tayi maganganu marasa daɗi akan sa, dan tayi alkawarin ɓatar da shi idan bai daina shiga sabgarta ba..."Ɓatarwa fa kace ɗan nan? Ɗan mutum din guda za'a ɓatar kamar ɗan kaza, kuma ita Siyama ɗin ce da kanta tace zata ɓatar da Ibrahim? Hajja ta katse Haladu cikin tsoro da jin wai zata ɓatar da Ibrahim. Haladu ya amsa da "Ai Hajja wannan ƙaramin aiki ne idan mutum yana da kuɗi, amma kuma ba wannan ne ya kawo ni ba. Hajja dai jikinta yayi sanyi tana kallon sa. Kafin yayi magana sai ga Nana ta shigo gidan da sallama. Suka amsa suna kallon fuskar nan tata a murtuƙe kamar kuturon da a kaiwa gorin hannu. Kallonta Hajja tayi bata bukatar ƙarin bayani domin babu komai a hannunta. Ganin Nana ɗin ta shige ɗaki yasa ta sauke ajiyar zuciya ta dawo da kallonta ga Haladu shima da yabi Nana ɗin da kallo ganin ko gaishesa bata yi. Ya ce "Hajja Siyama da kanta tace "Yaje ya rubuto duk wani abu da ya taɓa kashe mata zata ninninka masa ta biya sa. Kuma Hajja wallahi ko nawa yace zata ba sa, shine fa tun lokacin nake masa magana amma shi yaƙi ma ya saurareni, nace masa ko jari ai sai ya samu amma yaƙi. Shine nace bari nazo na sanar miki domin naga ai hakkinsa ne ba roka yayi ba. Hajja ta ce "To ai Ibrahim ɗin ne shifa yanzu damuwarsa yarinyar, kuma ai kaine zaka taimaka ka shawo kansa domin zaifi jin maganar ka. Ko kuma kawai kai ka zauna ka rubutu komai sai kuje da shi kasa ya bata. Haladu yayi shiru sai chan ya ce "To shi kenan Hajja in sha Allah zan masa hakan. Ya tashi zai fita sai kuma ya sa hannu a aljihu ya ɗauko dubu biyu ƴan ɗari biyar guda huɗu ya ajiye wa Hajja ba tare da yace komai ba. Hajja ta bisa da addu'a domin dama ya saba yi mata kyauta har fiye da haka ma, kasancewar shi Haladu shago garesa kuma babu laifi ana ciniki sosai. Yana fita Nana ta fito daga ɗakin. Kafin tayi magana Hajja ta ce "Ga kuɗi nan yayanki ya bani ɗauka kije kisan abun da zaki samo mana, kiyi sauri kuma tunda ga wuta sun kawo. Haka ta kwashi kuɗin ta fita Hajja ta bita da kallo. ****** *ADAWIYA* Wannan ba shine karon ta na farko da tazo ƙasar Ingila ba, amma wannan shine karo na farko da tazo a sa'a. Sosai komai yake tafiya mata kaman yadda take so, babban abun da yafi burgeta ma shine ganin manya-manyan salebiritis da kuma manyan Model's da bata taɓa tunanin zata haɗu dasu ba ta haɗu da su yau. Bata ƙara cika da mamaki ba sai da wani kamfani dage Ingila suka zo har Hotel ɗin da ta sauƙa suka kawo mata tayin yarjewa ta zama Models ɗinsu ta shekara ɗaya. Bata amince ba tace subata lokaci zata yi shawarwari. Bayan fitar su, ta kira Manager dinta yazo har ɗakin ya sameta, kasancewar tare suke tafiye-tafiye ko ina. Ta sanar da shi komai akan sun nemi da ta zauna tayi aiki dasu. Jin sunan Kamfanin yasa Manajan saurin kallon Adawiya ya ce "Madam Baki San wani kamfani bane? Ta ce "No ban san su ba, amma ina jin sunan su But ban taɓa bin aikin su ba, amma ina kallon fina-finansu ai. Manajan ya ce "Suna yin Really Video's ne na sex babu inda video ɗin su baya zagawa, kuma basa yi da kowa sai Model's, kuma kema ba wani aiki zaki musu ba sai shi wannan aikin. Adawiya ta dafe ƙirji tace kenan rom service and romantics Seex videos kenan fa? Ya ɗaga mata kai. Take ta sallamesa yana fita ta kira Badawiya Badau. Tana ɗagawa ta kwashe mata komai ta faɗa mata. Ai kuwa da sauri Badau ta ce "Ke ƴar sa'a da gaske? "Adawiya ta ce "Ban gane ƴar sa'a ba kin san wani kamfani nake magana ne? Badau ta ce "Yes ba VIP London ba ne? Cike da mamaki Adawiya ta ce "Wai dama sune? Badau tayi dariya ta ce "Shegiya ai dama nasan baki ma san suwaye suka zo gurin ki bane shi yasa kika tsaya wasa. Adawiya ta ce "Nashiga aljanna daɗi zai kashe Adawiya, VIP London ne wai dan Allah? Badau tace "Ke dalla tsaya, wai yaya ma akayi har suka ganki? Ta ce "Yau minyi aiki ne na taron salebiritis mawaƙa Model's ƴan Film da ƴan ƙwallo, ke duk dai wasu salebiritis, kuma nima na shiga inaga anan suka ganni. Badau tace "To zuwa gobe ki tabbatar kin kirasu kin yarda zakuyi aiki tare. Adawiya da har yanzu mamaki take ta ce "Yanzu zan ƙara duba shafinsu na gani. Badau tace "To sai kuma kiyi, mutanen da kullum sai na kallesu, ke zan iya lissafa miki ƴan team ɗin nasu gaba ɗaya musamman ma mazan, ke suna da wasu irin maza masu ƙirar jayent, Maza iya maza ga kyau ga lafiya ga iya aiki, nasha yin mafarkin su bayan na gama kallonsu, kema yanzu haka zamu fara kallonki a gurin fa. Adawiya tayi dariya tace "Wallahi har na fara tsoron wadannan mazan mazu ƙirar dakunan yaƙi, sai nake ganin kamar ban kai na shiga Team ɗin ba. Badau ta ce "Ai kuwa kece kika isa ki shiga VIP wallahi, to sauran matan finki sukayi ne, wai ke kamar ba ke ba, Please karki ba dani. Sai a lokacin ta ce "Yanzu to idan na yarda yaya batun kamfanin Magazin? Da sauri tace "Ke amma baki da hankali, ana maganar VIP kina zancen wasu talakawa, to bari kiji alawus ɗin VIP kaɗai ya kai fement ɗin Magazin na wata biyar wallahi. Ke ai idan kika shiga wannan team ɗin kinyi ban kwana da taulauci daga ke har zuri'arki. Adawiya dai ta saki baki tana mamakin a ina duk Badau tasan duk waɗannan. Haka suka yi sallama akan idan ta yarda da VIP ɗin zata juya conturak ɗin ta ya koma kan Badau na Magazing da take yi yanzu. Washegari kuwa shine zasu je su ƙarasa aikin da sukayi. Hakan yasa ta shirya da wuri cikin shigar wasu arnan kaya wanda kallo ɗaya zakaiwa kayan kasan dole sai dai Model's irin su. Doguwar riga ce mai adon duwatsu daga sama har ƙasa, kasancewar ita ɗin siririya ce yasa kayan suka fito da dirin ta, ga kuma gefe da gefen rigar a yage har cinyarta. Ta saka wani taƙami da tsininsa zai kai tsayin tsinken tsire, amma tsabar sabo da iya tafiya da shi ko alamar faɗuwa bata yi, hannun ta na riƙe da wata ƙaramar jaka kalar kayan wacce bata fi a saka waya kawai a ciki ba. Tana ƙarasowa aka buɗe mata motar mai buɗandan sama. Ta shiga ta zauna sannan aka ƙara gaba da ita. Suna tafiya Manager ɗinta yana mamakin yadda da akayi zata yi aiki da VIP domin tun da safe ta sanar da shi zasu je susa hannu, domin daran jiya ta gama shiga komai ta gani. Sai da ta shiga Magazin ta karasa aikin ta na ranar wanda hoto kawai ta ɗauka na wasu sabbin fantis da bra da aka kawo Magazin kuma ita aka zaɓa a matsayin wacce zata fara sakawa ayi tallan kayan. Sosai kayan suka mata kyau haka ta shiga saka su ɗaya bayan ɗaya duk wani color dake gurin sai da ta saka ana ɗau karta hoto dasu, duk wanda tasa zata tsaya ne tayi wani irin tsayiwa ta karkace gefe ko ta ɗan juya cinyarta ta baya, style dai kala da ban da ban har ta gama kafin ta mayar da kayan ta da tazo dasu, sannan ta ɗiɓi kayan da tayi talansu guda biyar domin sun mata kyau. Tazo zata fita wani daga cikin masu ɗaukar hoton ya sanar da ita Manaja na nemanta a ofishin sa. Haka ta tafi tana kwarkwasa kaman yadda ta saba. Tana shiga ta tarar da wasu matan a ciki suma a zaune suma duk Model's ɗin ne su Uku. Tana shiga tai musu Hai suka amsa kasancewar sun san juna. Bayan sun zaune manajan mai suna Alesx ya ce "Ku huɗu muka zaɓa zamu yi aiki daku karshen shekara, kafin lokacin zamu baku hutu na tsawon wata ɗaya, amma a cikin wannan watan babu sex koda kuwa da miji ne (Ma'ana ko kina da aure ne), ko da kuwa da Mace ƴar uwarki ce. Lokaci ɗaya matan suka kalli juna jin wani sabon iskanci. Duk da kuwa sun san haka aikin yake, amma mai ya kawo na cewa koda kuwa da Mace ƴar uwarki ne, ya ma raina musu wayo. Adawiya tace "Sabo da me? Ya ce "Saboda aikin da za'ayi yana buƙatar natsuwa da tabbatar da lafiyar Model's ɗin mu. Muddin wani abun ya shiga tsakaninsu da Maza to za'a gane kuma matsala ne, abun tsoron ma shine shigar ciki shine babbar matsalar, shine ma yasa ake kiyayewa. Adawiya da take jin ita da ta riga da ta gama aiki dasu muddin VIP London suka amshi komai nata, ta ce "Zanyi tunani akai" Alesx ya kalleta da mamaki ya ce "Ban gane zaki yi tunani ba kamar wacce aka bata shawara? Yaci gaba da faɗin Wannan dokar aiki ne ba wai shawara ake nema daga gareku ba, duk wacce taga bazata iya ba babu dole ta sanar tun da wuri mu nemo wata. Yayi maganar da ɗan ɓacin rai a muryarsa, kasancewar wannan dama ce da duk wata Model's ke fatan samu shiga a cikin wannan aikin na karshen shekara. Kafin kowa yayi magana wata daga cikin matan kai da gani kasan baturiya ce ƴar ƙasa ta ce "Yes mun yarda zamu iya, idan lokacin yayi sai a sanar mana sai mu kiyaye. Adawiya kuwa babu wani tunani tace bazata iya ba. She kansa Alesx ta bashi mamaki, amma bai ce mata komai ba har ta bar gurin suka bita da kallo. Wata daga cikin Model's ɗin ta ce Afirkan Model's. ta faɗa tana jan tsaki, sauran kuma suka kwashe da dariya...📝 Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza write [7/16, 3:54 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FCWA_ *My WhatsApp channel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Page 1️⃣0️⃣* Duk da Alesx yaji zafin rashin shigar Adawiya cikin tawagar aikin nasu amma haka ya haƙura suka fara neman cikon ta huɗun ƴar Afrika wacce zata wakilceta. Dama shi yarinyar na basa mamaki tun ba yanzu ba, tana yin wasu abubuwa kamar bata tsoro, amma a ransa ya yanke shawarar wannan karan zai koya mata hankali, sai tayi nadamar ɓata musu lokaci da tayi. Bayan ta fita ne ya sallami sauran ƴan matan shima ya tashi. Daga nan VIP ta nufa ranta fess tana jin ai ita dama ce mai kyau tazo mata kuma tabbas zata dama harda sikari tasha kayanta. Lokacin da taje get ɗin shiga VIP kuwa duk da cewar an ganta Model domin kallo ɗaya take buƙata duba da irin shigarta zaka gane ita ɗin Model ce. Amma hakan bai sa an barta ta shiga ba sai da ta nuna shaidar da aka bata lokacin da suka zo gurin nata. Lokacin da ta ƙarasa ciki sai aka tsayar da escort ɗinta (Mai tsaron ta) aka nuna musu hanya ita da manager dinta suka shiga ciki, shi kuma ya tsaya waje. ****** *SIYAMA* Yau kwana biyu da zuwan su Oga Fita gidan su, kuma har yanzu babu wani cigaba daga gurin Umma na amincewarta, hakan yasa tun jiya Siyama ta je gidan Kawu Inuwa da kuma Baba Hassan mahaifin Binta. Sosai tai musu ruwan ihisani da yasa kowa a cikin su sai da ya rikice. Shi Kawu Inuwa farko da taje kamar zai dake ta, domin haushi ta basa, amma lokacin da ta faɗa masa irin samun da ake yi, sai ya fara sakkowa. Bai sakƙo daga kan bishiyar kwakwan bama sai da yaga ta sauke masa rafar yan dubu-dubu guda biyar wato dubu ɗari biyar lokaci ɗaya ya duro daka saman, ya rikice har bai san lokacin da yake ce mata "To ai dama wannan aikin da moda shi ya dace da ke, yarinya fara kyakkyawar gaske, ai itama Umman taku wasa take, to wa zai ƙi nasa da abun arziki. Bari na shigar da su sai mu tafi gidan yanzu, to ai wannan sana'a ce ta rufin asiri, shekara ta nawa ban taɓa riƙe irin wannan kuɗin ba, amma ke daga rana ɗaya kawai kin riƙe, dama ana cewa wani lokaci idan kaga kana addu'a akan kayi arziki to kuma baka yi ba, to malamai sun ce tana komawa kan ƴaƴa ne, to babu shakka nawa kanki ya faɗa wallahi. Sosai ya shiga zaro zance ita dai Siyama tana sunkuye a ƙasa tana mamakin mai ya hana ta tun farko bata fara aiki da kuɗin ba, ai da tuni ba wannan maganar ake ba. Daga nan gidan Baba Hassan ɗan biyun mahaifinsu taje. Lokacin da ta isa gidan kasancewar shi yana da ɗan hali domin harda mota garesa dukda cewar tsohuwa ce amma dai yana da ita. Shima ganin ta a cikin wannan Motar sai da ya shiga boɗe baki. Bayan ta gama zaiyana masa komai ne ya shiga girgiza kai alamar tunani. Ganin kamar bai yarda bane yasa kafin yace komai ta sanar da shi irin alkarin dake cikin aikin nata, ta fara faɗa masa irin kuɗaɗen da zata samu, tana gamawa shima ta zaro guda shida ta ajiye masa, ta sanar da shi abun da take so yayi mata. Baba Hassan ya kalleta ya kalli kuɗin ya ce "Yanzu iya wannan abun da kika yi ne har kika samu wannan kuɗaɗen?" Siyama ta ce "Eh ai Baba wannan ma iya kyautar da na samu a gurin ne ba ma wanda aka bani na gasar bane". Jin haka sai yace "to shi kenan zuwa gobe zan je na sameta". Sai da ta shiga suka gaisa da Mommy itama ta bata rafa ɗaya kafin ta bar gidan. Tana fita Mommy ta dau waya ta kira Binta. Taso shiga gidan su Ibrahim lokacin da tazo wucewa, domin so take ta jawa tsohuwar sa kunne ganin shi baya jin magana. Amma ta bari har sai ta samu Umma ta yarda. Shi kuwa Nasiru babu wata-wata kuɗaɗe ya amsa daga gurin ta ya fara hutawa abun sa, har Allah-Allah yake ya warke ya ƙwace wannan motar ta zama tasa. Zaune suke a sashen Umma Kawu Inuwa da Baba Hassan sai wani abokin Kawu Inuwa da ya gayyato acewarsa wai Malami ne, zaiwa Umma bayani yadda zata fahimta. Sai yaya Bala da shima har yanzu yaƙi amincewa da wannan aikin a ransa. Bayan an gama gaisawa ne Kawu Inuwa ya fara da faɗin "Uwar yara gurinki muka zo akan yarinyar mu, izuwa yanzu dai kowa yaji abubuwan da suka faru da ita, to mun zauna munyi shawari nida babanta gashi. Ya faɗa yana nuna Baba Hassan. Yaci gaba da faɗin "To shine yasa nace a matsayin ki ta uwa shine muka ga ya dace musanar dake karmuyi gaban kanmu dukda cewar mun isa da yarinya, koba haka bane Malam Hassan? Ya karasa yana tambayar Baba Hassan da gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi ganin yanayin Umma da Yaya Bala. Baba Hassan ya ce "To dama ba komai bane sai kawai abar yarinyar nan tayi sana'ar ta, tunda dai ba zai hanata karatu ba, kuma wannan sana'ar sana'a ce ba mai muni ba. Umma ta ɗaga kai ta kallesa sai ta kawar da kai ganin sun haɗa ido. Ai kuwa shi kaɗai ya duburburce ya kasa ci gaba da jawabin. Sai Kawu Inuwa ya ɗora da "Yanzu muna so a matsayin ki ta uwa maba da mama, mai son cigaban ƴaƴanta kiyi hakuri kibi Siyama da addu'a akan aikin ta, kinga kema sai ku huta, nasan har gida sai ta sauya muku, dama gata yarinya ce mai kyauta da sanin yakamata, sam abun hannunta baya rufe mata ido. Umma ta ce "Yanzu tsakanin ku da Allah idan Siyama ƴarku ce ta cikinku zaku yarda tayi wannan sana'ar ta ƴan isa ta tallan jiki, ai duk kuna da yara mai yasa ba zaku tura su suma suje su samo abun arzikin ba kamar yadda kuka ce, to ni dai ban yarda Siyama ta ƙara aiki da wadannan mutanen ba, wanda tayi a baya ma kuskure ne kuma yarinta ne, amma in sha Allah ba zata ƙara ba. Ku kuma wallahi kun bani mamaki akan abun duniya zaku salwantar min da rayuwar yarinya har kuna iya kallon idona kuce wai na bar ta tayi talan tsaraici, A'uzubillahi-mina-shaiɗanunrajin, tuf da wannan tunanin naku. Kawu Inuwa ya ce "Yanzu mune shai ɗanunn kenan Aisha? Kuma mune kike wa gorin yarinya, shi kenan babu komai ba laifinki bane, ai mu ne marasa mutuncin da muka tako har cikin gidan ki, dole ki zagemu san ranki. Umma ta ce "Ni ban zageku ba, kuma babu yadda za'ayi nayi muku gurin aihuwa domin duk kun haifa. kuma Siyama ƴar kuce ban isa na shiga tsakaninku ba. Kawai dai abun da kuke nufi ne ba zan taɓa yarda ba."To me kike nufi da a'uziya da kika jawo mana yanzu na neman tsari da sheɗanu, ko ake ce miki bamu je islamiyya bane, to bari kiji babu wata addu'a da zaki yi wacce ban san ina ta dosa ba, dan haka karki ƙara mana addu'ar shaɗanu tun girma da arziki domin mu ba su bane, ya daga abun kirki a fara danganaka da jinsin tsinannu. Sosai wannan addu'ar ta ɓatawa Kawu Inuwa rai domin ji yake kamar shi ta kira da shaɗanin. Umma ta ce "Kayi hakuri ni ba nufi na kenan ba. Ta faɗa tana jin nauyin sa da take ji yana raguwa. Sosai take kunyarsu su duka su biyun amma wannan abun yasa take jin nauyin nasu na raguwa a ranta, dama shi Kawu Inuwa ya iya daukar abu da zafi kamar dai ita, shi dai Baba Hassan bai ma cika tsoma baki a lamarin gidan ba sai dole. Kawu Inuwa ya kalli Yaya Bala da yayi shiru yana ta tunani ya ce "Yanzu Bala a gabanka ina matsayin ƙanin ubanka kana ji uwarka na kirana da shaɗani amma kayi shiru ko? Kai Bala kana so ka gama da duniya lafiya kuwa. Sosai yaya Bala ya danne abun dake taso masa ya shiga basa hakuri har dai akayi sa'a ya tsaya da mitar kamar mace. Mutumin da suka zo da shi ne ya fara magana cikin natsuwa da dole kai mai sauraron sa ka tsaya ka ji abun da yake cewa domin ya iya magana. Ya ce "Duk na fahimce ku, kuma na gane inda zancen naku ya dosa. Yanzu ina so ku ɗan bani dama nace wani abu? Duk suka basa dama ya buɗe baki zai yi magana suka ji anyi sallama. Amsawa sukayi sai ga Hajja ta shigo ɗakin cikin sauri idanunta duk sun yi jaa, sai kuka take. Gata dai tsohuwa amma jikinta bai tsofe sosai ba, amma kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar da tana cikin wahala. Ganin mutane da yawa a palon yasa ta cire taƙalmi ta shiga gaisuwa da sauri-sauri. Kawu Inuwa ne ya fara faɗin "Baiwar Allah lafiya kuwa me kike buƙata gurin wa kika zo da zaki shigowa mutane cikin gida haka kamar sauƙar aradu babu neman izini?. Kallo ɗaya Umma tayi mata ta gane ta, ta ce "Sirikarku ce kakar yaron da yake zuwa gurin ita ƴar taku da kuka zo karewa" Da ƙarfi ya ce "Ita dai wannan ɗin, to wallahi wuce nan, ina dangin wannan matar ina Siyama da take shirin zama tauraruwa sha kallo. Hajja ta ce "Hajiya Aisha Ibrahim ne ba shi da lafiya kamar zai mutu sai sunan Siyama yake kira, dan Allah ki taimakeni Siyama tazo muje ko ganinta yayi dan Allah a taimaka. Da ƙarfi Umma take furta innalillahi tana faɗin "Mutuwa fa kike cewa Hajja? To meye ya sameshi haka? Umma tayi tambayar tana ƙarasowa gurin Hajja. Hajja tayi ƙarfin halin faɗin "Wallahi shida ita Siyama ɗin ce, wai inaga yanzu ta daina sonsa ne, shine ya shiga wani hali, yau kusan kwana biyar kenan mun kasa gane masa, dan Allah ku taimaka ko ganinsa tazo tayi zai samu sauki domin sunanta kawai yake kira. Umma ta kalli Yaya Bala da bai iya cewa komai ba ta ce "Kaji zancen da Nasiru ya gama faɗa jiya ko, dama nasan wannan yarinyar wallahi ba dan Allah take son wannan yaron ba, kawai tana so ta yaudaresa ne, kuma wallhi bata isa ba, muddin nine na haife ta to wallhi sai ta auri wannan yaron ai ita ta kawo mana shi akan shi take so, to dole ne sai ta aure sa. tace "Je ka kira min ita. Dama tana jin duk abun dake faruwa domin tun shigowar su Kawu Inuwa ta laɓe tana sauraron su. Umma ta ce "To ga kakar yaro ga ni uwar yarinya ga kuma iyayenta maza, sabo da haka a tsayar da magana yanzu, ni na yanke shawarar aurar da Siyama idan yaso ta ƙarasa karatun nata a gidan shi yaron, domin na gaji da wannan masifar da take ƙoƙarin tun karomu. Idan yaso ko bayan auran ne mijin nata ya barta sai tayi duk abun da zata yi, amma tana gabana dai ba zan yarda ba, Umma ta ce "Kuyi shaida ni Aisha na bawa Ibrahim auran Siyama ko bana raye. Da sauri Kawu Inuwa ya miƙe tsaye shima cikin masifa ya ce "Wannan wani irin rashin hankali ne haka Aisha? Haka ake aurar da yarinya dama, ko kin taɓa ganin inda mace ta bada aure ne? Cikin masifa da haushin da Siyama ta gama bata domin ta lura kamar kuɗi ta basu domin su zo su shawo kanta ta ce "To yaya zanyi da Siyama, so take sai ta kashe ni kuma in sha Allah bazata iya ba har sai lokaci na yayi, yaro kuma ita ce ta kawo shi ba dole za'ayi mata ba, kuma gata nan ku tambaye ta, har gida ta kawo shi a matsayin shi ne zabin ta. Lokaci ɗaya kowa ya kalli Siyama da ta sunkuyar da kai. Ita dai Hajja sai kuka take burinta kawai Siyama tazo suje tayiwa Ibrahim magana ko zai tashi ya samu ko abinci yaci. Cikin fushi Kawu Inuwa ya ce "Siyama wai da gaske ne kece kika kawo yaron matsayin wanda zaki aura? Kowa ya zuba mata ido, domin jin abun da zata ce. sai da tayi kamar baza ce komai ba sai cen ta ce "A'a ni ban turo kowa ba, kuma ai dama ba soyayyar gaskiya muke yi da shi ba ta wasa ce domin ai shima ya sa..."Bata ƙarasa ba taji sauƙar mari a kumatunta wanda yasa ta tsayar da maganar. Kawu Inuwa yace "Wallahi idan ka ƙara taɓata sai na rama mata babu ruwana da ciwon hannunka, yaya yarinya ba ƙarama ba da wayonta kuna so kuyi mata ƙarya a gaban ta. "Umma cike da mamaki kamar zata yi kuka ta ce "Siyama karya nayi miki kenan ko? Siyama ni kike ƙaryatawa? Siyama dai sai kuka take tana jin tsanar Yaya Bala a ranta na marin da yayi mata domin kuwa ya shige ta da kyau. Yaya Bala yaci gaba da faɗin "Ƙarya kike dan ubanki wallahi kinyi ƙadan Siyama yau she aka haife ki, kizo da yaro kice shi kike so yanzu sabo da wani dalilinki kece karya akai miki, to bari kiji wallahi Ibrahim shine mijin ki sai dai idan gidan nan zaki bari kije ki nemi wasu iyayen amma dai idai mune iyayenki Ibrahim zaki aura, wawiya sokuwa mai baƙin hali kawai. Ita dai Hajja tana tunanin waye zai yarda ya zama sirikar wannan mara kunyar da bata bar iyayenta bama bare na wasu, ita dai badan halin da jikanta ke cikiba wallhi ba zata yarda Ibrahim ya auri wannan mai ido a tsakiyar kai ɗin ba. Babu kunya ko tsoro Siyama ta ce "Ni dai wallahi ba aure zanyi yanzu ba, kuma babu wani zancen soyayya tsakanina da shi Ibrahim ɗin, kuma ko aure zanyi na rasa wa zan aura sai wannan dolo wawa ƙazami ɗin, wallahi ba wanda zai aura min shi, kuma ni ba aure zanyi ba yanzu. Tana faɗa ta miƙe zata fita amma Umma tayi saurin jawota ta sauke mata mari tana faɗin "Wallahi baki isa ba Siyama kinyi kaɗan ki raina ni har haka, nice nan na haifeki ba ke kika haifeni ba, kuma ban haifi wata ƴar da zan faɗa tana faɗa ba, kinyi ƙadan idan kuma kina ganin karfin ki ya kai to Siyama tashi ki dake ni, nace tashi Siyama. Umma na faɗa tana kuka tana kuma naushin Siyama ta ko ta ita ga wani irin kunya da ta tsinci kanta a ciki, dukanta take yi tana faɗin ta rama. Siyama na kuka tana kare kanta kuma taƙi guduwa har Nasiru da su Fati da Binta dake cikin ɗaki suka fito. Da ƙarfi su Kawu Inuwa suka shiga tsakaninsu domin Yaya Bala ba zai iya ba saboda ciwon hannunsa. Su kansu su Kawu Inuwa da Baba Hassan jikinsu ya mutu ganin abun da ke faruwa. Ganin haka Umma ta ce "Ki fito ki bisu kije chan gidan su kiyi abun da kika ga dama amma ba a nan gidan ba. Siyama da bakinta yaƙi mutuwa tace "Babu inda zance kuma ni ba aure zanyi ba. Wani irin tsawa da zagi Yaya Bala ya kutuntuma mata yana jin yau da babu ciwo a jikinsa wallahi sai ya kusa karya wannan yarinyar. Shi kansa Nasiru abun ya basa mamaki gashi duk hannunsu na ciwo. Kawu Inuwa da ya shiga tunanin to ko dai ya lallaɓa Siyama ɗin ta auri Ibrahim ɗin ne, idan yaso sai shi Ibrahim ɗin ya barta ta yi sana'ar tata. Nasiru ne ya kama hannunta suka shige ɗakinta tana kuka kamar ranta zai fita. Umma ta ce "Ki fito ki bar min gida ai ba gidan ubanki bane, kije gurin masu zuga ki ɗin ko kuma ki tafi gurin su iyayen da kika sake su arnan da kika nunawa duniya cewar sun fimu daraja a gurin ki" Yaya Bala dai sai bata hakuri yake, dama Umma akwai faɗa idan ranta ya ɓaci bata jin rarrashi. Kawu Inuwa ya bita ɗakin bai lura da irin kukan da take yi ba ya ce "Siyama mai zai hana ki yarda da shi Ibrahim ɗin tunda ba auran za'ayi yanzu ba, daga baya sai ki saye shi da kuɗi shi da kansa yace ya fasa. Cikin masifa da rufewar ido ta ce "Sai naga uban da zai sa na aure sa ɗin, kafita min daga daki ai dukkanin ku muna fukai ne, ai ba haka muka yi daku ba. Kawu Inuwa da ya cika da mamaki ya ce "Siyama nine munafikin? Ai kuwa ta hayayyaƙo masa ta ce "Eh kaine ai ba haka muka yi ba, kai kazo kana ta nuna mata ƙwadayin ka a kan kuɗi duk ka ɓata komai ni ka bar min ɗaki. A zuciya Kawu Inuwa ya ce "Shi kenan girma ya fadi akan kuɗi! Afili kuma ya ce "Shi kenan Siyama na tafi Nagode" Ko kallonsa bata yi ba har ya bar ɗakin. Ganin ya fita yasa Nasiru dawowa ɗakin domin lokacin da ya shigo shi kuma fita yayi. Lokaci ɗaya taji wani irin tsanar Yaya Bala da kuma tsoron Umma da taji yana fita a ranta, barin ma idan ta tuna da cewar tana da kuɗi. Sai kuma shi waccan yaron dolon da take jin wallahi zata iya kashe shi idan suka haɗu. Sosai take yin da ta sanin shiga da Ibrahim cikin rayuwarta ganin duk sabo da shi burin ta ke neman tarwatsewa. Kai dole nema taje gidan nasu taci kutumar ubansa shida kakar tasa, to ana so dole ne, su basu ga yanayin yaron nasu ba mai zubin doleye sakalai wai shi zata sura to ta kai ina tayi yaya da shi. Haka ta sha kukanta kafin ta miƙe ko wanka bata yi ba, ta ɗauki mayafi da niyyar zuwa gidan su Ibrahim. Binta da Fati ne suka kai Umma sashen ta, wanda har kanta ya fara mata ciwo, magani suka ɓallo mata tasha sannan ta kwanta tana tunanin abun da ya faru, ko tace yake faruwa. Sosai ta ɗorawa Yaya Bala laifin komai da kuma aikin sa, anan take ta yanke shawarar wallahi dole sai Siyama ta auri Ibrahim sai dai idan ita ba uwarta bace, sannan dole Bala yabar wannan aikin nasa, kawai gidan su nada za'a saka a kasuwa sai ya ja jari da kuɗin, sannan a biyawa Nasiru kudin makaranta sannan a koma asibiti da shi. Haka dai Umma ta gama sake-saken ta har tayi Sa'a barci yayi gaba da ita. Sunzo sai tin ɗakin yaya Bala Binta ta tsaya ta ce da Fati "Bari na duba Yaya ko lafiya" kafin ta bata amsa ta tura ƙofar ta shiga tana sanɗa. Ganin haka yasa Fati tafiya ta barta domin ta gano takun Binta ɗin, ita dai tace ga fili ga mai doki indai Yaya Bala ne. ****** *YAYA BALA* Sosai ya shiga ruɗu jin irin rashin Kunyar da Siyama ke yi, bai san lokacin da ya ɗauketa da mari ba, har sai da hannunsa mai ciwon yayi kara wanda hakan yasa ya ƙara fama ciwon nasa, sosai yake masa zafi dan kamar ruwa ne yaji yana ɗan fita ta cikin ɗaurin da a kai masa. Haka ya ɗaure ba tare da kowa ya lura ba har dai ya dinga bawa Umma hakuri yasa su Fati suka tafi da ita bangaren ta, bayan Baba Hassan da wannan tsohuwar sun tafi ne shima ya tashi da ƙyar ya nufi ɗakinsa yana ji kamar hannun nasa baya jikin sa. Sosai yake shan a zaba haka yasa ya shiga warware nadin da a kai masa. Ganin jini ya fara nuna a lama ne yasa ya fara cire kayan jikinsa kasancewar farare ne. Sosai yayi da ya sanin dukan ta gashi ya dawo da ciwon sa sabo, tsabar azaba ji yake kamar ya fashe da kuka, dan har wani hawayen azaba ke fitowa daga idonsa. Sai da ya rage daga shi sai gajeren wando ɗan ciki, kafin ya shiga warware ciwon yana tunanin ƙara dai ya samo mai ɗaurin gargajiya ya ɗaura shi zai fi. Sosai ya warware naɗin ai kuwa ga jini ya ɗan fito alamar dai ya fame sosai. Yana son ya tashi ya shiga Toilet ya ɗebo ruwa amma ya kasa sai sauƙe ajiyar zuciya yake yi. Haka dai ya miƙe tsaye kenan yaji an turo ƙofar dakin an shigo ba tare da sallama ba. Kallonta yayi cike da mamaki yake binta da kallo ganin ta shigo masa ɗaki babu sallama ga shi ta doso gurinsa a rikice tana neman kamo masa hannu. Wata tsawa ya daka mata wacce yaji ta har cikin ciwon nasa, wanda yasa sai da ya koma zaunen da yake da. Binta kuwa ta tsorata da tsawar amma hakan bai hanata ƙarasawa gurin tana kamo hannunsa ba ta ce...📝 Wannan littafin na kuɗi ne duk mai son karantawa sai ta biya a sakata a group. Duk wacce take son karantawa zata iya fara biya tun yanzu naga kaman hakan zaifi. Complete ɗinsa ɗari biyar 500₦ a tura ta wannan lambar 8100785178 opay Adam Salisu. A turo da shedar biya ta wannan lambar 08100785178. Na kusa gama free page. Babu laillai babu dole, idan kinga zaki iya kizo ayi tafiyar dake, idan kuma kinga ba zaki iya ba ki bimu da addu'a, nasan ina tare da ƴan amanar S Reza masu bina duk rintsi. Daga page 11 za'a daina ganin posting har sai mutum ya biya zai samu. Love all One love Comments Ana shering Love my fan's By S-Reza write [7/16, 3:54 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FWAS_ *Page 1️⃣1️⃣* Binta ta ce "Yaya dama karaya kayi ne? Ai ina ce targaɗe ne, kawo na gyara maka na iya" ta faɗa tana ruƙo hannun nasa. Yaya Bala kuwa sai yanzu ya tuna da cewar Mommy fa ta iya gyaran karaya da targaɗe to amma bai san ita Binta yau she ta koya ba. Ya ce "Tashi ki fita daga ɗakin nan yanzu?" Ta ce "Yaya ɗaurin da a kai maka ɗin ne bai yi ba ina zuwa ka gani, karka tashi kaji yanzu zan dawo" Tana faɗa tana miƙe wa da sauri ta bar ɗakin ta nufi ɗakin su, shi dai ya bita da kallo bai ce komai ba. Bata yi sallama ba ta shiga duba jakarta ta kwaso wasu kwalabai gudu uku ita dai Fati tana ta raka ta da ido. Haka ta koma ta same sa a gurin da ta barshi. Toilet ta shiga ta fara dube-dube sai ta ɗauko wata singlet ɗin sa ta ce "Yaya kana son wannan rigar? Ya kalli rigar da kyau ya ce "Meye kike yi haka a ina kika koyo gyaran karaya?" Ta ce "Yaya kenan kai dai tsaya ka ganewa idon ka. Sai ta shiga duba inda zata ga tsunma, ganin bata samu bane ta cire hular kanta shi dai ya bita da kallo yana ta mamaki. Gashin ta yake kallo ganin sa baki ƙirin kuma a wanke gashi babu laifi yana da tsayi kasancewar babu kitso akan, har wani ƙamshi ke fita daga cikin gashin, lokaci ɗaya ya tuno da Anty Zainab itama haka take da gashi har ma yafi wannan tsayi, sannan takan buɗe gashin kan nata idan suna su biyu, domin yana son mace mai gashi sosai kuma bai cika son yaga mace na yin kitso ba, yafi son ganin gashi a haka. Kallonsa ya kai gurin da hoton ta yake ita kaɗai sanye da doguwar riga ta saka glas ta riƙe gife da gefen glas ɗin da hannu biyu tana murmushi. Kallon gurin da yake kallo tayi sai ta sauke ajiyar zuciya a zuciya ta ce "Lallai a kwai Binta kina da aiki". Yana ta kallon hoton har ta jona ruwa ya ɗan yi zafi ƙadan, kafin ta cire ganin har lokacin yana kallon hoton harda hawaye ne, yasa ta tsoma hular tata a cikin ruwan ta ɗan matse kafin ta danna masa da ɗan karfi wanda yasa da sauri ya dawo da kallonsa gareta. Tayi ɗan murmushi ta ce "Yaya bari kaga aikin ƴar gado". Haka ta wanke masa jinin ta ɗan danddana hannun da ruwan zafi kafin ta ja masa hannun, ganin yadda yake yi ne ta ke yi da gaiyya amma ya dake, haka ta shafa masa wannan mayukan da ta ɗebo, sannan ta yi amfani da igiyar da ya ware ɗazu ta wanke ta ɗaure masa. Tana gamawa ta ce "In sha Allah sati ɗaya za'a warware ɗaurin. Ya ce "Idan kuwa kaka ɓata min hannu zan koya miki hankali, je ki kawo min abinci".Tayi dariya ta ce "Yaya bani da hankali dama?" Ya ce "Nace ki kawo min abinci ko? Ta ce "Ni dai Allah yaya ka daina ce min bani da hankali, to me nake yi na rashin hankali?" Ta faɗa harda bubbuga ƙafa a ƙasa ita a dole zata yi shaƙwaɓa. Yaya Bala da mamaki yake kallonta har abun yaso basa dariya amma ya dake. A ransa yana mamakin Binta yana tunanin Allah yasa dai ba sonsa take ba, domin kwana biyu gaba daya ya lura da ita. Ya haɗe rai ya ce "Yau she na fara wasa da ke Binta? Kin raina ni ko? Ya faɗa yana tamke fuska. Ita kuwa Binta ta ƙara maraireciwa ta ce "To yaya haka kawai sai kace min mahaukaciya, yanzu fa na gama maka gyara ko na gode baka ce ba, kuma baka biya kuɗin gyara ba shine zaka ce min mahaukaciya. Yaya Bala tsabar mamaki bai san dariya ta kufce masa ba. Shi yaushe ya ce mata mahaukaciya. Ganin harda kukanta yasa ya ce "Ok tom naji ke ba mahaukaciya ba ce, kuma na gode sosai, sannan nawa ne kuɗin aikin. Jin haka yasa Binta sakin dariya da karfi harda riƙe ciki ta ce "Yaya kaga nasa kayi dariya, kuma kuɗin aiki na dubu goma ne amma ka ajiye min a gurinka ka tara min idan ciwon bai gyaru ba na sake gyarawa shima sai ka ajiye min har na tara da yawa. Tana faɗa ta bar ɗakin tana dariya. Waro ido yayi yana kallonta amma har ta bar ɗakin. Dariya yayi yana kallon hannunsa da har ya daina masa zugi sai wani sanyi yake masa da alamar man da ta shafa a gurin ne. Rabonsa da ya samu kansa a cikin farin ciki haka tun kafin rasuwar Anty Zainab. Kwantawa yayi yana jira ta kawo masa abincin. **** *IBRAHIM* Lokacin da ya dawo daga aikin Hajja ta tare shi da zancen da Haladu yayi mata na karbar kuɗin da Siyama ta ce ya rubuto zata basa tayi masa. Amma Ibrahim ya ce shi sam ba dan kuɗi yake sonta ba, kuma duk abun da ya taɓa bata ya bata domin Allah da kuma son da yake mata ne. Shima ya shiga tambayar Hajja ɗin akan taje gidan su Siyama ɗin. Tsabar haushi da takaici yasa Hajja faɗin. "To bari kaji wallahi babu inda zanje, idan kuma kana son naje to sai kaje ka ƙarbo mana wannan kuɗin, haba Ibrahim kai idan baka buƙata ai mu muna da buƙata, yarinyar nan tace bata sonka to dole ne kayi hakuri kowa yaje yayi rayuwarsa mana. Ibrahim da baya son jin kalmar wai Siyama bata son sa kuwa wani irin ɓacin rai ne ke taso masa yana jin zai iya cewa komai ga Hajja idan ya tsaya sauraronta, hakan yasa ya barta a gurin tana cigaba da faɗa. Washegari kuwa sai ga Haladu yazo da takarda ya rubuto abubuwan da yaga sun dace, aka duba kuɗi totall nera dubu talatin da biyu harda ɗari biyu da ashirin. Hajja da kuwa bayan Nana ta sanar da ita yawan kuɗin ne yasa ta riƙe baki tana faɗin "Kuma gaba ɗaya zata bayar? Haladu ya ce "Ai Hajja wannan ma iya wanda na sani ne, ina so shima ya fadi sauran kinga ko dubu hamsin da wani abu aka kai ya ya isa yaja jari ya manta da ita. Haka suka runtuma zuwa ɗakin Ibrahim da yau yace bashi da lafiya ba zai je aiki ba. Kwance suka samesa yana kallon sama duk ya rame, domin tun da abun ya faru baya wani cin abinci da yawa. Zama Haladu yayi ya ce "Ta shi malam duba ka gani meye ban saka ba, harda tsiren da kake sintirin saya mata duk ran juma'a na ɗari uku-uku na saka kuma shima iya wanda na gani ne, ai kwara a ramawa kura aniyar ta, kai da nine kai wallahi har wanda ban bata Bama sai na saka. Haladu ya faɗa yana miƙa masa takardar. Ibrahim ya ce "Wai meye ne duk kunzo zaku dame ni, ni barci nake ji dan Allah ku fita min" Haladu ya tura masa takardar gabansa yana faɗin, kai ɗin banza nasha wahalar rubutun kace na fita. Dole ya mike ya amshi takardar yana dubawa. Ibrahim na gama kalla ya yaga ta yana sakin tsaki. Ya ce "Ni wallahi matsala ta dai kai Haladu kwaɗayi da shegen son kuɗi, kai a tunaninka kuɗi ko wani abu zai sa na rabu da Siyama ne, nifa wallahi sai dai ko mutuwa nayi, amma muddin an barni a raye to babu mai iya rabani da siyamata, kuma maganar kuɗi ni ba domin ta biyani nayi ba, siyama ba zata iya biyena abun da nayi mata ba har sai ta yarda zata aure ni. Hajja da ta gama ƙuluwa tace "Haladu ku rabu dashi ai bari ba shegiya bace da ubanta, yunwa da damuwa ba ƙannen ubansa babe, ta shi ka tafi sannunka da ƙoƙari kaji mun gode. Haka Haladu ya tafi yana mamakin anya kuwa abakinsa bai samu tabin hankali ba, duk da cewar dama kamar dai yana da ɗan matsala. Haka suka manta da shi har dare, ganin bai fito bane yasa Hajja ƙara leƙasa, ta ganshi zaune ya dafe kai. Ta karasa ciki taga yana kuka yasa waya a gaba alamar dai Siyama yake kira. Lokaci ɗaya Hajja ta tausaya masa, ta zauna tana lallashin sa, tasa Nana ta kawo masa abinci amma sam yaki ci, sai sunan Siyama yake kira, sosai fa Hajja da Nana suka tsorata, har dare yaki cin abinci, karshe ma ya fara amai yana tari. Da safe ta kira masa mai dan shagon gurin magani yayi masa allura bayan an bashi baƙin shayi ya sha. Shima a shagon Haladu aka karbo, ko kuɗin maganin ma shine ya dauki nauyin biya. Haka jikin nasa ya ƙara sauki har washe gari da ya tashi da wani irin ciwon zuciya wai shi dole sai yaga Siyama, gashi baya iya tafiya, kuma sai riƙe zuciya yake yi, hakan yasa Hajja ta zari hijjabi sai gidan su. Lokacin da ta dawo daga gidan su Siyama da kuka ta shigo domin kuwa taga duk abun da yake faruwa a gaban ta. Yanzu kam ta tabbatar sai dai Ibrahim ya mutu idan a kan Siyama ɗin ne. Lokacin da ya ga Hajja na kuka sai ya ƙara ruɗewa yana tambayar meye ya samu Siyama ɗin, Bama meye ya samu Ita Hajja ɗin da taje gidan ba a'a shi dai siyamarsa. Sosai Hajja ke kuka tama rasa ta ina zata fara yi musa bayani. Nana ta ce "Hajja ko Siyama ɗin ta mutu ne?" Lokaci ɗaya Ibrahim ya miƙe zaune yana sakarwa Nana mari tass a bakinta! Ta riƙe bakin tana kallonsa shima ya na kallonta kowa yaƙi yin magana sai hannu ɗaya da ya riƙe zuciyar sa. Nana ta ja dogon tsaki ta tashi ta bar ɗakin tana faɗin "Allah yasa ma ta mutu mota ta take tsinanniyar kowa ya huta, ƴar banza mai girman kai" Ibrahim ya bita da kallo yana ƙara cigaba da tari yana kallon Hajja da take ta kuka, a ransa yana jin zai iya ɓalla Nana a gidan tabbas kuwa. Ya ce "Wai Hajja ba zaki min magana bane, kinzo kin sani a gaba sai kuka kike baki ce min komai ba, kina so sai zuciyata ta fashe ne kafin ki sanar dani. Itama cikin Irin ihun da yayi ta ce "Dan ubanka zuciyar taka ta fashe ko yanzu wawa mara hankali kawai kaje kana hauka akan yarinyar da bata ragawa kowa ba har iyayenta, wacce babu wanda ya isa da ita, to ni wallahi ma ko tace zata aure ka ba zan yarda ba, me za'ayi da irin marasa tarbiyya da rashin ganin girman iyayensa, yarinyar da a gabana uwarta na faɗa tana faɗa, to wallahi kamaji bada niba. Tana rufe baki Siyama ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin "Eh fadi ki ƙara tsohuwar muna fuka ashe gulma ya kai ki gidan namu. Kwallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin Siyama da Hajja da IB. Da sauri ya miƙe tsaye yana kallonta kamar dai gizo take masa. Ganin kowa yayi shiru ne yasa Ibrahim ɗin faɗin "Siyamata kece da gaske ko dai gizo ne?" Ya faɗa yana ƙoƙarin kamo hannunta. Ita dai Hajja tayi mutuwar tsaye domin tsoro take ji, yanzu-yanzu ta gama da iyayenta ma bare ita, hakan yasa ta takure agefe ta kasa cewa komai. "Da sauri ta ture hannunsa tana faɗin "Kai wawa soko ɗan dolo-dolo, saurareni kaji, gargaɗi nazo nayi muku kai da wannan tsohon magulmaciyar taka. Ta faɗa tana nuna Hajja da hannu kamar zata tsokale mata ido. Taci gaba da faɗin... Na rantse da girman Allah idan baku fita daga sabgata ba zan sa a kulle wannan soloɓiyon jikan naki, kuma ƙullewar da bazaki sake ganinsa ba. Kai kuma ɗan dolo, ba kana yin abu kamar wawa ba, kana yi kamar baka da zuciya ba, to wallahi muddin ka ƙara nuna ka sanni na rantse sai na aikata abun da na faɗa maka. Daga yau ko nace daga yanzu idan na fita daga gidan nan to babu ni babu ku, karku ƙara nuna kun taɓa ganina, idan ma wani ya kiraku daga gidan mu kace kai yanzu ka daina sona, koma waye kana dai jina ko? Ta karasa tana daka masa tsawa kuma tana kama kunne alamar gargaɗi. Ibrahim da yaji ciwon zuciyar da ke damunsa ya tafi dalilin ganin Siyama ya ce "Siyama kome zaki min sai dai kiyi amma wallahi ba zan daina sonki ba, nima ba yin kaina bane laifin zuciyata ne, kuma zan cigaba da faɗa miki cewar ina sonki, kuma ba zan daina ba har sai kin aureni kamar yadda kika min alƙawari, dan Allah Siyamata abar wannan wasan na horu haka, baki san abun da nake ji bane, ni kaina wani lokaci sai nake jin inama zuciyata tamin adalci ta manta da ke, amma kullum sai ƙara sonki take yi. Siyama da ta gama zuwa ƙarshe da ɓacin rai ta ce "Kai dai anyi ɗan marasa zuciya wawa kawai, kai ni duk duniya a kwai wata halittar da zai ce baya sona amma na dage har haka ne dan uban mutum ko waye shi. Ibrahim ya ce "Nima ke ɗaya ce duk duniyar nan wallahi wacce zan iya mutuwa a kanta". Ya faɗa yana ƙara matsowa kusa da ita. Ita dai Hajja gaba ɗaya sai sauraronsu take, kamar tace da Ibrahim yayi shiru karta kashe su a cikin ɗakin domin taga a lamar zata iya. Siyama ta ce "Ni ɗin ƙanwar uwarka ce da bazaka iya rabuwa da Ni ba? Ibrahim da yake jin daɗin hirar da suke yi ya ce "Kinfi nan Siyama, wallahi kin wuce ƙanwar uwata a zuciyata, ni yanzu ki faɗa min abun da zan miki domin ki tabbatar da irin son da nake miki wallahi ko me kike so zanyi in dai akan ki ne. Ta ce "Wai kai mutum ne kuwa?" Ya ce "Mutum ne mana kamar ke Siyamata. Siyama kamar tayi kuka ta ce "So nake ka rabu dani, ka faɗa daga kan miliyan ashirin zuwa ƙasa fadi yadda kake so yanzu na baka ka manta da ni, domin naga kamar talauci ne duk ya cika maka ƙwaƙwalwa da baka san daidai da rashin ba. Ta faɗa tana bin dakin da wani irin kallon raini harda toshe hanci. Sai a lokacin Hajja tayi magana ta ce "kinga ajiye mana duk abun da kika yi niyya, na miki alƙawarin ba zai ƙara ko kallon hanyar da kike ba" Hajja ta faɗa a tsorace. Ko kallonta Siyama bata yi ba. Siyama ta kalli Ibrahim tana jira yace wani abu. Sai ya ce "Ni Siyamata tafi ƙarfin kuɗi a gurina, idan har zan amshi kuɗi akan son da nake mata to na ci amanar so, kuma shugaban masoya zai yi fushi da ni" Cikin zafin zuciya ta ce "Da kai da shugaban masoyan duk kunci kutumar ubanku, banza sakali, dolo ƙazami wawa mahaukaci" Ya ce "Siyama karfa ki manta ke kika koya min sonki, ke kika nemi da mu fara soyayya, to bayan na yarda da ke na gama zurmawa a sonki shine yanzu zaki nuna wai wasa kike min, to ni dai da gaske nake ina sonki. Siyama da ta rasa me zata ƙara cewa ta buɗe jakarta ta kwaso kuɗi rafar biyar dubu ɗari biyar kenan ta watsa masa ta ce "Ibrahim wannan shine gargadin karshe tsakaninmu, idan kaji to shi kenan, tana faɗa ta miƙe zata fita amma Ibrahim ya jawo ta jikinsa, ai kuwa ta faɗo kan gadon sa, ta hau kansa. Ganin haka yasa Hajja fita da gudu tana ihun kiran Nana. Sosai ya manneta a jikinsa yana shaƙar sassanyan ƙamshin turatenta da ya kama ɗakin tun ɗazu da ta shigo. Sosai ta shiga ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa hakan yasa ta sakar masa cizo amma ko a jikinsa, sai ma ƙara matseta da yake yi yana ƙara tabbatar mata da cewar yana sonta. A haka Haladu da Nana da Hajja suka zo suka samesu, Siyama tayi-tayi har ta haƙura ta fara kuka domin ta matsu sosai. Shi kuwa wani irin sanyi da natsuwar zuciya ya samu kansa a ciki har yake nema ya shagala barci ya ɗauke sa. Yana jin an shigo ya saketa yana miƙewa. Ita kuwa da kuka ya cika mata baki ta fashe da shi tana gyara rigar ta da ta tattare. Hajja ta ce "Ibrahim ka fara hauka ne, meye wannan ɗin kayi, ko ka zama mahaukaci ne. Ta faɗa tana kallon Siyama da ta miƙe tsaye tana gyare-gyare. Ta juyo ta kalli Ibrahim ya sakar mata murmushi ta ce "Zaka san ka haɗa jiki dani, ba dai kai wawa ɗan iska dole shege ba ka jira dawowa ta" ya ce "Dan Allah ki dawo da wuri please Siyamata" ya faɗa da dan ƙarfi domin har ta bar gidan. Suna fita Hajja ta ɗauke shi da mari ta ƙara masa tana faɗin "Yanzu kasan me zata aikata mana ne, me yasa baka da tunanine Ibrahim yaushe ka zama ɗan iska a cikin gida zaka kama musu yarinya haka ake so ɗin" sosai Hajja tai masa kace-kace, kuma tace karya kuskura ya leƙa ko waje. Tana gamawa ta kwashe kuɗin tana nunawa Haladu da yake ta kallonsu tun da yazo. Hajja ta ce "Haladu yanzu nawa kenan wannan kuɗin. Ya ce "Hajja guda biyar ne sun kama dubu ɗari biyar kenan" Hajja ta waro ido tana kama baki ta ce "Ɗari biyar dai Haladu? Haladu yayi dariya ya ce "Allah ne ya baku" "Yanzu zamu iya taɓawa nifa ina tsoro karta dawo tace a bata kayanta? Kafin Haladu yayi magana Ibrahim ya wafce kuɗin ya saka a ƙarƙashin katifarsa ya ce "Babu wanda zai taɓa mata kuɗi mayar mata da shi za'ayi. Haladu ya ce "To wallahi baka isa ba, ina ruwanka kai ne ka bayar, kai dai kaje da rashin zuciyarka yarinya ta zageka ta zagi uwarka a gaban ka, ai ni wallahi ka bagama bani mamaki. Ibrahim ya ce "To ko kaima zaka zaga ne ka gani? Haladu ya ce "Ba zan zaga ba domin nasan illar hakan amma kuɗi ne dai sai ka bayar anbawa masu hankali su hajja. Ibrahim yace "To zoka ƙwata. Haladu ya ce "Yanzu kuwa" Haka suka shiga dambe har sai da Haladu ya ciro kuɗin ya mikawa su hajja raba ɗaya ya ce zai ajiye musu sauran sabo da kar ya zo ya kwashe. Hajja dai sai godiya take duk da har yanzu tana tsoro, ita dai Nana har ta fara lissafin abubuwan siya. ****** *AIDA" Sai da ta tabbatar da duk wata shedar ta da yake nuna cewar Adawiya da Badawiya ne suka saka wannan tsohon banzan Olusha yayi wannan aikin hakan yasa ta samu Oga Fita ta sanar masa, shima yayi mamaki ai kuwa nan take ya haɗa mintin aka taru ya tambayi Badau kasancewar ita Adawiya bata nan. Farko tayi musu amma ganin shedar da Aida ta kawo yasa ta tabbatar. Nan take Oga Fita ya wanketa tass akan yanzu gashi sun jawo mata zagi agurin iyayenta da jama'ar gari. Sannan yace "Zasu yi vedio su ƙaryata kansu. Nan fa Badawiya tace ba zata iya ba. Haka zaman ya watse akan ita dai wallahi ba zata yi video ba. Ai lukacin da Adawiya ta samu labari daga gurin Badawiya, lokacin har ta sa hannu a VIP London, dama tana neman yadda za'ayi ta bar team ɗin su na Farin gida, kuma dama sunyi magana da shugaban Magazing akan zata mayar da Badau taci gaba da aiki a tare da su a matsayin ta, ita ta samu wani aikin. Alesx da haushin ta yake ji tun lokacin da yayi mata maganar Aikin karshen shekara tace ba zata yi ba. Bai nuna mata komai ba yace ta kawo hotunan ƴar uwar tata. Sosai Adawiya ta kira Oga Fita suka yi kace-kace har tana ƙara sanar da shi cewar zata ƙara yin wani sabon Video ɗin akan shi Oga Fita ɗin yana kwanciya ne da duk members ɗin team ɗin su kafin ya ɗauke su harda ita Siyama ɗin, kuma harda ita kanta Adawiya ɗin. Sosai Oga Fita ya shiga tashin hankali domin shi ba rabuwar da sukayi da su bane matsalar ko faɗin cewar zata ce yana kwanciya da su ba, a'a shi abu biyu yake tsoro, na ɗaya Siyama da iyayenta, domin ya tsorata da Umma da ya ganta. Na biyu kuma jin cewar Adawiya ta shiga VIP London, sosai yake mamaki da tsoro. Haka dai a ka rabu tsakanin team da Adawiya da Badawiya. Haka kuwa ta tattara komai nasu sai England London tarar da ita a cen. Hakan yasa sunan Aida ya shiga cikin waɗanda zasu yi tala ga Baby and me. Yanzu haka ita da Nusee da Sarah ne zasu fara zuwa gurin domin saka hannu kuma a ƙara koya musu duk wasu abubuwan da zasu yi. Ganin har lokacin da aka bawa Siyama ya wuce ne yasa suka ce kawai a fara aikin da sauran Medels ɗin, idan yaso duk lokacin da ita Siyama ɗin ta shirya zasu yi aiki da ita. Akan haka aka tsaya, Aida tana ta kiran Siyama domin ta sanar da ita amma bata amsawa, sai kawai ta tura mata message. Da sauri ta fito Palo tana kallon Jamila da ta fito daga kicin riƙe da kofin shayi tana sha. "Kar dai kice min baki gama girkin ba? Jamila tayi dariya ta ce "Harma munci namu ke kawai ya rage" Ta ce "Ina Jamilu? "Ya shiga wanka tun ɗazu nima shi nake jira" Da mamaki Aida ta ce "Ina zaku je da kike jiransa? Jamila ta buɗe mata kanta ba tare da tace komai ba. Sai Aida ta ce "Auf sorry ni bama Na manta munyi maganar wankin kai daku ba. Ta ce "Yauwa zan bar muku wannan farar motar, kuma karku tsaya a ko'ina, kuna gamawa ku dawo gida, zan kara muku kuɗi yanzu, karfa ku tsaya a ko'ina" Jamila ta amsa da tom. Haka ta shiga cin abincin tana sauri, kafin ta gama Jamilu ya fito cikin shirin sa na kayan ƴan kwallo yana kallon Aida ya ce "Anty baki tafi ba har yanzu ƙarfe tara saura fa?" Haka ta gama kafin ta wanke hannu ta ƙara jaddada musu cewar karsu tsaya a ko'ina ana gama gyara mata kan shima yayi askin su dawo gida, suka amsa da to kafin ta rungume su ɗaya bayan ɗaya suka rakata har gurin motarta ta shiga ta nufi team ɗin su. Tana barin gidan Jamila da jamilu suka koma ciki. Bata fi minti biyar da fita ba motar Siyama ta shigo gidan. Bata tsaya komai ba ta shige cikin ta nufi ɗakin Aida duk ranta a ɓace. Tun daga palon take jiyo Nishi a ɗakin Jamila, hakan yasa abun da ta gani ranar ya fado mata, take ta nufi ɗakin tana tunanin wai kullum haka suke yi ne, anya kuwa Aida bata sani ba, da mamaki taga ɗakin a buɗe, ta leka ta samesu kamar ranar yau ma dai sex suke yi, sosai wannan karan ta tsaya tana ta kallonsu har ta manta da abun da ya kawota, sosai taji tana neman rasa control ɗin ta, hakan yasa ta ciro wayarta ta shiga camera ta fara ɗaukarsu vedio. Haka ta juya ta fita ganin haka tasan Aida bata gida, hakan yasa ta bar gidan itama. Aida kuwa tare suka tafi su uku kowacce da motarta. Bayan sun isa gurin ne, aka tabbatar da cewar zasu iya, nan suka saka hannu, kafin aka shigar dasu wani ƙaton abu mai kamar irin abun gurin wanka, amma wannan a zagaye yake kamar saiko. Da mamaki sukaga ruwan zafi ne a ciki sai tururi yake yi, gashi ruwan kamar yalo kamar kore. Haka dai Nusee ta fara shiga sai Sarah sai ita Aida ɗin. Jin ruwan ba zafi sosai ne yasa suka sake. Sunyi a ƙalla minti talatin kafin aka ce su fito. Nan ma aka basu wani ruwa mai kaman mai aka ce su shafe jikinsu, su dai komai aka ce sai yi suke, suna sanye da bra da banti kawai a jikinsu. Lokacin da suka kalli jikinsu suka ga sun kara wani haske da kyau. Bayan sun gama shafe jikinsu aka basu wani ruwa irin na da suka shiga ciki amma wannan normal ruwane su shiga ciki irin dai na ɗaxu. Bayan sun fito aka basu wasu kayan suka saka, aka fara yin hotuna. Ita Sarah tallan fauda suka ɗauketa wanda uwa da ƴarta zasu iya yin amfani da shi a lokaci guda, za'a dinga ɗora hotonta a jikin fauda ɗin. Ita kuma Nusee tallan man shafawa ne nata itace za'a dinga ɗora hotonta a jikin man ita da yarinyar da aka bata mai kyau da ita suka yi hoton yarinyar sai dariya take yi. Ita kuma Aida turare ne shima duk na kampanin Baby and me ne, wannan shine karo na farko da suka fito da turare na Baby and me hakan yasa suka zaɓi ita Aida ɗin ganin ita ba fara mace. Nan aka shiga nuna musu yadda kowacce zata tsaya a dauki hoto, sannan sati mai zuwa kuma za'ayi vedio domin fara haɗawa, kasancewar tallan nasu yana shiga gidajen talabijin da na rediyo harma online da dai sauransu. Haka dai kowacce ta dawo gida cike da farin ciki. ****** ADAWIYA Duk da yadda take kallon haɗuwar gurin amma hakan bai sa ta shagala da kallo ba saboda karma a raina ta. Sunyi tafiya mai tsayi a linta kafin suka isa wani ɗaki, suna shiga ta ga ɗaya daga cikin mutanen da suka zo gurin ta. Tana shiga ya miƙe tsaye suka yi hannu da manager ita kuma ya ɗaga mata hannu. Kallon ɗakin take ko tace ofishin da ya cika da hutunan fina-finai na batsa wanda wasu daga ciki ma duk ta kalla. Sosai sunan wani fim ya ɗauki hankalin ta ganin hoton wani saurayi Model ɗan ƙasar Faransa. Tasan yaron sun taɓa yin aiki da shi a nan Ingila a Magazing, amma bata san ya shiga VIP London ba, kallon hoton tayi taga a she ma film ɗin sabo ne, domin ba'a sake shi ba. Maganar da mutumin yayi ce ta dawo da Adawiya cikin tunaninta ya ce "Ga dokokin aikin VIP" Ya faɗa yana turawa manager ɗin wata zungureriyar takarda. Manager ya shiga karantawa yana yi yana kallon Adawiya da mutumin cike da mamaki. Sai da ya gama kafin ya share zufar da yayi ya ce "Zamu iya yin magana da ita mu biyu? Mutumin ya ce *Yes don't worry" Yana faɗa ya nuna musu wani ɗan Ƙaramin daki gefe da su. Adawiya ta ce "No ba sai munje ko ina ba, nasan komai game da aikin kawai asa hannu" manager ya kalleta da kyau ya ce "No Madam ki dai ƙara ki sake dubawa yanzu da kanki. Haka ta ƙarɓa ta shiga dubawa sama-sama ta karanta abun da idonta ya kai wanda bata kalla ba kuma ya wuce. Nan take ta saka hannu shima manager babu yadda ya iya ya saka hannu. Take aka bata wasu takardu akan taje ta ƙara cike su. Bayan sun gama mutumin ya ce ta biyo shi ita kaɗai. Nan suka shiga tafiya saida suka yi nisa kafin suka iso gurin ɗaya mutumin. Ya bata wasu kaya ta saka. Nan ta saka kayan wanda basu da maraba da tsirara. Wani dakin hoto ta shiga, ai kuwa tana shiga ta tarar da mata da maza sun kai goma ana ta hoto, yanayin shigar dai ba'a cewa komai. Domin dama haka shigar Medels yake musamman ma yan VIP. Ba'a tsaya da ita a nan ba suka shiga wani ɗaki bayan mata da mazan sun gama mata barka da zuwa. Suna shiga wani na miji yabi bayan su da abun ɗaukar video. Suna shiga taga ɗaki ne harda gano da komai. Kwanciya ya ce tayi, ta kwanta tana kallon namijin da shima ya zagayo kusa da ita babu komai a jikinsa sai ƙaramin wandon maza. Mutumin da suka shigo tare ya ce "Sau nawa kika taɓa yin sex? Ta haɗiye yawon tsoro tana tunanin to ina ruwansu da sanin wannan tace "Bata sani ba" Kallon Namijin yayi ya ce "Zata iya yi kuwa? Ya ce "Eh zata iya. Ya kalli mai ɗaukar video ɗin ya ce muje zuwa. Ya fara ƙoƙarin cire mata ɗan fanti dake jikinta sai ta riƙe, domin har ga Allah ta tsorata da namijin ganin sai jiki duk a murɗe kamar ɗan dambe.Wata tsawa mutumin ya daga mata yana cewa zata ɓata musu aiki gwaji za'a kawai idan har ta iya cin gwajin to za'a fara aiki da ita kwanan nan, idan kuma bata ci gwajin ba za'a ci gaba da bin ta a hankali har ta saba. Sosai ta tsorata a fili ta ce "Sex ne gwajin?" Ya ce "Yes baki gani a jikin takardar da kika sa hannu bane? Gabanta ya ba da wani rass...📝 _To masoya S Reza, wannan shine karshen free page Kaman yadda nayi alƙawari. Nera ɗari biyar kawai zaki biya a saka ki a cikin group aci gaba da posting. Kuma yanzu haka ba tsayawa zan yi da posting ba, domin wasu sun fara biyan nasu, idan kin biya sai na tura miki wanda akayi ba kyanan sai kuma a ci gaba da ga inda aka tsaya. Ba sai na ce muku komai akan wannan labarin ba kunsan za'a samu darasi mai muhimmanci, sanna akwai aikin da na sani a ɓangarorin cikin labarin kaman yadda kuka gani, Jamil da jamilu abun da suke yi Aida ta sani, Adawiya da Badawiya sun samu madafa, Siyama da Ibrahim me zai faru, Hamm ba sai na cika ku da surutu ba mu haɗu a VIP. Ga account number da za'a biya ɗari biyar 8100785178 Opay Adam Salisu. Sai a tura da shedar biya ta wannan lambar 08100785178. Idan ma katin waya zaki turo shima kiyi magana wa wannan number. Idan kika biya kudi akan wannan littafin wallahi ina sheda miki cewar baki faɗi ba domin zaki kwashi ruwan darasin rayuwa. Sai na ganku ƴan amanar S Reza_ 🥰 Love all One love Comments Ana shering Love my fan's By S-Reza write