💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍 {The famous Arabic poetess} Na Babylorh♥️🌹 Alhamdulillah! All praises to Allah (SWT)... Godia ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki! Kamar yadda na fara rubuta littafina lafiya Allah nake roƙo ya bani ikon gamawa lafiya... Babylor ce😍 na dawo muku ɗauke da wani sabon gajeren labari mai tsantsagwaron daɗi. Labari na ƘIRƘIRARRE ne, banyi da niyyar cin zarafin wata ko wani ba, idan har yayi kama da naki/naka, so sorry, bada sani nayi ba. GARGAƊI: ban yadda wani ko wata ya chanzamin koda harafi ɗaya na littafi ba, dan haka a kikaye. SADAUKARWA: wannan littafi kochokam sadaukarwa ne gareki Aminiyar ƙwarai mai farar zuciya *Khansa'u*, my love fr u is extraordinary😫🌹💞 Bismillahir-rahmanir-raheem.... Marubuciyar: *Rushdah* *Maraici Na* and now; *Khansa'u* {The famous Arabic poetess} 1 & 2.... Jihar Kano tana ɗaya daga cikin manyan jihohin Nigeria, Jiha ce mai ɗauke da ɗumbin al'umma sama da miliyan 9, a fannin ƙananan hukumomi ma ba'a barta a baya ba, inda take ɗauke da local government guda arba'in da huɗu (44). *NASARAWA GRA* Fara ce doguwa, kyakkyawa ba mai muni ba mai dogon hanci. Bata da jiki, amma baza'a kirata siririya ba kuma ba mai ƙiba ba, ƴar daidai, sanye take cikin Swiss atampa baƙa mai touch ɗin blue da ratsin pink ɗinkin fitted gown, wanda ya bayyana ilahirin surar jikin ta. Ɗaurin dake kanta Zahra Buhari ne, sai medium ɗin pink veil ƙirar Kashka data rufe bayan ta zuwa waist ɗin ta, yayin da gaban ke a buɗe. Chain bag ne maƙale a kafaɗar ta, inda ƙafar ta ke sanye da pink high heel mai tsayin dunduniya da igiya. A natse take takowa harta iso farfajiyar gidan, gyatsine ta ɗanyi gami da tsaki kana tasa tafin hannun ta ta kare fuskar ta tana mai faɗin ''the weather's so hot'' Cigaba tayi da nufar makeken gate ɗin gidan ƙirar Tanzania harta iso gareshi, tun daga nesa mai gadin gidan (mal. Garba) keta kwarara mata kirari kamar ƴar sarki, murmushi kawai budurwar tayi, dan idan da sabo ta saba da hali irin nashi na ban dariya. Allah ya ƙara nisan kwana matar manya, ganin ki alkhairi ne gaba salamun baya salamun, kariyar Ubangiji ta cigaba da yalwatuwa a duniyar ki shalelen Alhaji Babba! Haka mal. Garba ya ringa kirari kamar Allah ya aiko shi, 2k ta zaro a jakar ta miƙa masa kana ta fice. Karɓa yayi yana mai washe baki tare da dunƙule hannun hagun sa yana faɗin ''Allah ya ƙarama rayuwa albarka Hajiya Khansa'u, ya kuma ƙara nisan kwana'' Ko ta kanshi bata bi ba tayi gaba abinta, waige-waige ta somayi kafin ta hango wata Maroon ɗin mota ƙira Accord tana sheƙi fake aɗan nesa da gidan nasu, glass ɗin yaji dare (tinted). Tsaki taja tana mai kauda kanta gefe. Ganin bata da niyyar ƙarasowa yasa mai motar ƙarasawa gareta tare da sauke glass din motar. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!! Allah yayi halitta anan, kyakkyawan matashi ne wanda ganin sa saida yasa alƙalami na faɗuwa, bazai gaza shekara 30 ba, duk da cewa ba fari bane amma tabbas yana da kyau, kwantacciyar baƙar suma ce kwance ta kanshi data haɗa da sajen gami da gyararriyar ƙasumbar dake fuskar sa, inda ya zuba mata manyan fararen oily eyes ɗin shi mai cike da kwarjini, inda fuskar sa ta ƙara yalwatuwa da siririn dogon hanci da madaidaicin baki. Saida yaja iska ya fesar kafin ya fita, dan yasan halin kayar tashi sarai, tunda ta juya masa ƙeya fa bazata shiga ba. Haba my love, fushin ya isa haka, ya kikeso nayi? Nayi iya bakin ƙoƙari na na fahimtar dake babu abinda ke tsakani na da Amreesh wlh, yarinyar yayan Mummy (mahaifiyar shi) ne kinji na rantse miki. Hutu tazo gidan mu, shine tace jiya na ɗan fita da ita taga gari, wannan shine dalili. Uhm! Naji, sai kuma me? Khansa'u ta faɗa cikin ƙunar zuciya kamar ta fashe da kuka. Ajiyar zuciya matashin ya sauke yace ''Khansa'u''! Cike da mamaki ta kalleshi, dan bai taɓa kiran sunan ta haka ba cikin kakkausar murya. Baki yarda da Zayd ɗinki bane? Juyawa tayi ta kuma cewa ''uhm''. Murmushi yayi dan idan da sabo ya saba da shan wahala wajen rarrashin masoyiyar tashi, yanzun ma hakan ne ta kasance saida suka share kusan 40mins suna abu ɗaya, kafin ya samu ya shawo kanta. Ɗaukar ta yayi suka fita, basu tsaya ko ina ba sai munjibir park, dan ya santa da ƙaunar park, sosai taji daɗi kuwa yana ta yi mata hotuna tana dariya wanda ke ƙara bayyana kyawun fuskar tata. Saida suka biya ta gidan sister ɗinshi dake zoo road kafin suka kamo hanyar gida, akan hanyar su ne aka soma wani faɗa tsakanin wasu samari dake unguwa daban-daban, sosai ake faɗa ana zubda jini ana kisa tamkar rai ba'a hannun kowa yake ba, ganin haka yasa Zayd ƙoƙarin yin reverse saidai kafin yakai gayi sun far musu. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa ita kuma tana kuka tana ƙoƙarin kiran Abban ta.... Ji kake tassssss ƙarar fashewar glass, glass ɗin dake gefen driver aka fasa inda yayi tsalle ya caki goshin Zayd ya shige ciki, ko shurawa baiyi ba, su kuma suka ci gaba da tarwatsa mota tare da tsiyaya mata fetur, saidai ashanar su taƙi kamawa hakan yasa sukayi gama abinsu... Faɗi kawai suke ''sai mun rama, baza'a dakemu da daki banza ba, sai mun ɗau fansa akan al'umma''. Inda a ɓangaren Khansa'u kuwa girgiza Zayd kawai takeyi tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraron ta, sosai take kuka ta ɗauki kusan awa ɗaya tana abu ɗaya kafin ta fito daga motar zuwa lokacin abubuwan sun lafa, dan har al'ummar Annabi sun ɗan soma fitowa. Kallon motar kawai tayi ta kuma rushewa da kuka ganin yadda ta tarwatse, wayar ta ta fiddo ta kira Abban ta har kira uku bai ɗagaba, nan ta maida akalar wayar kan lambar Mummy itama bata ɗaga ba, hakan yasa ta kira Aliyu ƙanin Zayd ta sanar masa halin da ake ciki tare da faɗa masa inda suke. Hankali tashe ta tabbatar mata da gashi nan kuma kada subar wajen. Ba ɓata lokaci kuwa ya iso, kallo ɗaya zaka masa ka hango tsantsagwaron tashin hankali a fuskar sa, da ƙyar suka iya buɗe ƙofar mazaunin direban shida wasu matasa biyu. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu ya furta har sau uku, kafin wani zazzafan hawaye ya biyo kuncin sa, ya ƙurawa Zayd da fuskar sa ke ɗauke da murmushi ido, kamar ka kirasa ya amsa. Lee (daman haka take kiran shi) mu kaishi asibiti mana.. ta faɗa cike da tashin hankali. Girgiza kai kawai Aliyu yayi, dan kallo ɗaya yayiwa ɗan uwan nashi ya gano babu sauran numfashi a tare dashi.... Lee dan Allah ka ɗauko shi mu tafi, ta ƙara faɗa a karo na biyu cikin kuka mai ban tausayi. Shi da ƴan samarin ne suka cicciɓeshi tare zuwa motar Aliyu, kowa na wajen fuskar shi cike da alhini, yayin da ƙwalla ta gangaro kan fuskar Aliyu, tunanin sa ɗaya idan har Zayd ya rasu tayaya zasu fara gayawa Daddy, daddy nada hawan jini faɗa mai irin wannan tashin hankalin akwai matsala, daidai sun ƙaraso hospital ɗin... Nurses ne suka fito da gadon da za'a ɗaurashi a gurguje, cikin ƙanƙanin lokaci aka shiga dashi Emergency room.... _____________________________________✍️ Babylor ce😘 More comments,,, more typing..... Sai najiku a jam'iyar comments, dan shi kaɗai zai ƙaramin ƙarfin gwiwar sakin muku sabon update😇 [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍 *(The famous Arabic Poetess)* By Babylorh❤️🌹 Marubuciyar; *Rushdah* *Maraici Na* nd now: *KHANSA'U* (The famous Arabic Poetess) 3 & 4... ______Safa da marwa kawai Khansa'u keyi, tama rasa ina zata sa kanta, duk addu'ar da tazo mata yi kawai takeyi, zattauyi. Aliyu ma da kallon tausayi kawai ya bisa kafin ya fito da wayar shi ya danna kiran Mummy, kamar kuwa jira take, bugu ɗaya ta amsa. Aliyu wai ina Zayd ya shiga ne, ko kuma tare? Amm Mummy Zayd ya samu accident ne, yanzu haka muna hospital an shiga dashi Emergency room. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, gani nan zuwa yanzu insha Allah. Mum..., bai kai ga ƙarasawa ba ta katse wayar. Zama kawai yayi yana cigaba da addu'a Allah yaba Zayd lafiya. Babu daɗewa mom ta ƙaraso tun kafin driver ya daidaita parking ma ta fito. Mata ce wadda aƙalla zatakai 47yrs, farace mai ɗan jiki mai matsakaicin tsayi, dan Aliyu ma ya fita, sanye take cikin Swiss Lace blue sai sky blue din flowers, kana ya yafa sky blue din mayafi babba. Direct inda Emergency room yake ta nufa, nan taga halin dasu Aliyun ke ciki. Dagudu Khansa'u tayi kanta tana rusar kuka marar ƙaran sauti, bubbuga bayan ta kawai Mummy takeyi alamar rarrashi har suka zauna. Sannu da zuwa yayi mata kafin ta soma tanbayar shi har yanzu likitan bai fito ba? Gyaɗa mata kai kawai yayi ba tare da ya iya cewa komai ba. Suna hakane likitoci biyu suka fito daga ɗakin, ɗaya yana zare facemask ɗin fuskar sa ɗaya kuma yana sharce zufa, ɗaya daga cikin su Aliyu ya nufa yana mai tanbayar ya yaya jikin ɗan uwan nasa. Girgiza kai kawai yayi tare da yi masa alama daya bishi office, gaba ɗaya suka tashi dan bin likitan amma ya takatar dasu, hakan yasa suka koma suka zauna Aliyu ya tafi. Saida likitan yasha ruwa mai ɗan sanyi kafin ya fuskanci Aliyu.. Kayi haƙuri da abinda zan faɗa maka yanzu...tin kafin ya ƙarasa Aliyu yace ya mutu zakace koh? Ɗan murmushin gefen baki yayi kafin yace ''a'a, yana da sauran rai, kuma munyi nasarar tsaida jinin dakeson haura masa ƙwaƙwalwa, and muna saka ran farkawar sa nan da awa huɗu, duk da bamu da tabbacin tashin sa, amma muna fatan ya tashi ɗin''. Hawaye ne ya ziraro ma Aliyu na tausayin halin da Daddy zai shiga idan aka faɗa masa wannan labari. Zagayowa likitan yayi tare da dafa kafaɗar sa yaɗan bubbuga kana yace ''so sorry pls, take heart kudai kawai kuci gaba da yi masa addu'a, Ubangiji Allah ya tashi kafaɗun sa ya bashi lfy mai ɗorewa''. Ameen Aliyu ya amsa kana yayiwa doctor ɗin godia ya fita. A hankali yake takawa ba tare da yasan inda yake sanya ƙafarshi ba, harya iso corridor ɗin dazai sada shi da Emergency section ɗin, tunda Khansa'u ta hango shi ta nufeshi da sassarfa harta isa gareshi tace ''Lee me likitan yace, ina ya Zayd ɗin, sunce mu shiga mu ganshi''? Ta jero masa tanbayoyin duk a lokaci ɗaya. Hannun ta kawai ya kama zuwa inda Mummy ke zaune tare da sanar mata abinda likitan yace, amma bai faɗa mata basa da tabbacin tashin sa ba. Har awanni huɗun nan suka cika babu wanda ya tashi a wajen sai Aliyu da yaje sallah, zuwa lokacin kuwa Hajia Mariya (mahaifiyar Khansa'u), da ƙannen ta biyu Haseena da Ayeesh, sai yayyin ta Zayyad (abokin Zayd ɗin) da Kuma Mahfouz (abokin Aliyu kenan) duk sun zo asibitin, harda ƙanwar su Zayd ɗin Ma'eesha. A daidai lokacin ne wani likita ya fito tare da tanbayar mummyn patient ɗin, matsawa kusa Mummy tayi, likitan yace tabi bayan sa. Ƙwance yake saman gadon marasa lafiya, ɗaure da wani abu a yatsan shi wadda batasan meye ba, sai hancin sa dake ɗauke da Oxygen, ga kuma kanshi dake ɗaure da bandage, hawaye ne kawai ya biyo fuskar Mummy (Allah sarki uwa😭). Tana isa gareshi ya sauke Oxygen ɗin tare da furta kalmar 'Mummy' cikin murmushi. Murmushin itama ta masa dukda fuskar ta akwai hawaye ta rungume ɗan nata, kusan 2mins kafin ta sake shi, likitan yana ta kallon su cike da sha'awa da tausaya wa. Ina sonki Mummy, shine abinda ya ƙara fitowa daga bakin shi har lokacin kuma Mummy yake kallo. Nima Ina sonka son, Allah ya baka lfy. Hmm kawai yace tare da kauda kansa gefe. Shigowar Khansa'u ne yasa Zayd juyowa ta kalleta, gaba ɗaya fuskar tayi fiyau ga kuma hawaye da yaƙi tsayawa. Shine ni bakace a kirani ba ko ya Zayd, yanzu ma ture likitan nayi na shigo. Gaba ɗayan su suka saka dariya harta isa inda suke, ya Zayd ya jikin naka? Da sauki Baby, ya bata amsa cike da ƙauna. A hankali a hankali kowa ya hallara a ɗakin duk suka zazzauna suna jimami, ƙarewa kowa na ɗakin kallo Zayd yayi kafin yace ''Mummy ina Daddy fah''? Bai dawo ba Zayd, amma ya kirani zuwa anjima zai sauka insha Allah. Saida suka kwashi kusan 2hrs a haka, akan ɗanyi nishaɗi da wasa da dariya har zuwa lokacin da Daddy ya iso. Ba ƙaramin tashi hankalin Daddy yayi ba, ganin beloved son ɗinshi cikin wannan halin, amma saiya ɗau ƙaddara yayi masa addu'a kafin suka tafi masallaci shida sauran mazan. Itama Mummy da Mummyn Khansa'u tashi sukayi suka nufi wajen Sallah, Haseena ma (mai bin Khansa'u) itama tashin tayi, ya rage daga Zayd, Khans, sai Ayeesh da Ma'eesha a ɗakin. Khansa'u tana zaune gefen gadon riƙe da hannun Zayd tana matsa masa har zuwa wani ɗan lokaci. Wata irin jijjiga yakeyi, gadon ma kaman zai ɓalle, ƙara damƙe hannun ta yayi ya mata wani irin riƙo mai azaba, Ayeesh da Ma'eesha ne suka fita kiran likita, ba daɗewa suka dawo da likitoci guda uku, da ƙyar da wuya suka raba hannun Zayd da Khansa'u, aka fita dashi daga ɗakin zuwa ICU (Intensive Care Unit). Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Sosai hankulan jama'a ya ƙara tashi, wa'inda suka dawo masallaci. Sun ɗauki kusan awa ɗaya kafin suka fito gaba ɗayan su jiki a mace. Kafin akai ga yi musu magana sukayi saurin barin wajen tare da nufar office, da hanzari Daddy da ƴan sauran mazan sukabi bayan su har zuwa office. Sosai likitan ke fargabar sanarwa Daddy dan yasan halin da yake ciki, shine likitan shi ma. Amma Daddy sai ƙwarin gwiwa yake bashi na yin magana, hardai yayi jahadin faɗa musu cewa jijiyar ƙanshi ta tsinke kuma jini yayi nasarar taɓa ƙwaƙwalwar, wannan yana da nasaba da yawan magana da yayi da kuma rashin hutawa bayan farfaɗowar sa.. kuyi haƙuri Alhaji, every soul shall taste death, Allah Ubangiji yaji ƙansa da Rahma. Tunda likitan ya soma magana Aliyu ya koma bayan Daddy ya tsaya, dan yasan wajibi ne wani abu ya faru, amma ga mamakin su ko gezau Daddy baiyi ba, saima hakuri da yake basu na rashin ɗan uwa da sukayi, sun yanke shawarar ƙin sanarwa matan har sai anje gida kada su cika asibitin... Da ban baki da nasiha Daddy ya ɗauke su a motar shi zuwa gida, saida ya fara sauke su Mummyn Khansa'u da ƙannen ta amma furrrrr Khans tace saita ƙara haɗuwa da Zayd zata kwanta, babu yadda suka iya haka aka rabu da ita, suka tafi duka zuwa gidan su Zayd. Ba daɗewa shima Aliyu suka dawo da gawar a motar sa, cikin ƙanƙanin lokaci labari ya karaɗe ko'ina, amma har zuwa lokacin babu wanda ya sani tsakanin Mummy da Khansa'u, gwara ma chan gidan su Khansa'u sunji labari wajen Zayyad. Saida akayi masa sutura da komai amma an bari sai gobe a kaishi, kasancewar duhu daya fara wanzuwa. Kiran da Mummy ta samu da gaisuwa da aka matane ya sanya ta a ruɗani, a sittin ta nufi ɗakin Daddy danjin ƙarin bayani... _____________________________________✍️ Babylorh🌹❤️ 07069929131 [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍 {The famous Arabic poetess} Na Babylorh♥️🌹 Alhamdulillah! All praises to Allah (SWT)... Godia ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki! Kamar yadda na fara rubuta littafina lafiya Allah nake roƙo ya bani ikon gamawa lafiya... Babylor ce😍 na dawo muku ɗauke da wani sabon gajeren labari mai tsantsagwaron daɗi. Labari na ƘIRƘIRARRE ne, banyi da niyyar cin zarafin wata ko wani ba, idan har yayi kama da naki/naka, so sorry, bada sani nayi ba. GARGAƊI: ban yadda wani ko wata ya chanzamin koda harafi ɗaya na littafi ba, dan haka a kikaye. SADAUKARWA: wannan littafi kochokam sadaukarwa ne gareki Aminiyar ƙwarai mai farar zuciya *Khansa'u*, my love fr u is extraordinary😫🌹💞 Bismillahir-rahmanir-raheem.... Marubuciyar: *Rushdah* *Maraici Na* and now; *Khansa'u* {The famous Arabic poetess} 1 & 2.... Jihar Kano tana ɗaya daga cikin manyan jihohin Nigeria, Jiha ce mai ɗauke da ɗumbin al'umma sama da miliyan 9, a fannin ƙananan hukumomi ma ba'a barta a baya ba, inda take ɗauke da local government guda arba'in da huɗu (44). *NASARAWA GRA* Fara ce doguwa, kyakkyawa ba mai muni ba mai dogon hanci. Bata da jiki, amma baza'a kirata siririya ba kuma ba mai ƙiba ba, ƴar daidai, sanye take cikin Swiss atampa baƙa mai touch ɗin blue da ratsin pink ɗinkin fitted gown, wanda ya bayyana ilahirin surar jikin ta. Ɗaurin dake kanta Zahra Buhari ne, sai medium ɗin pink veil ƙirar Kashka data rufe bayan ta zuwa waist ɗin ta, yayin da gaban ke a buɗe. Chain bag ne maƙale a kafaɗar ta, inda ƙafar ta ke sanye da pink high heel mai tsayin dunduniya da igiya. A natse take takowa harta iso farfajiyar gidan, gyatsine ta ɗanyi gami da tsaki kana tasa tafin hannun ta ta kare fuskar ta tana mai faɗin ''the weather's so hot'' Cigaba tayi da nufar makeken gate ɗin gidan ƙirar Tanzania harta iso gareshi, tun daga nesa mai gadin gidan (mal. Garba) keta kwarara mata kirari kamar ƴar sarki, murmushi kawai budurwar tayi, dan idan da sabo ta saba da hali irin nashi na ban dariya. Allah ya ƙara nisan kwana matar manya, ganin ki alkhairi ne gaba salamun baya salamun, kariyar Ubangiji ta cigaba da yalwatuwa a duniyar ki shalelen Alhaji Babba! Haka mal. Garba ya ringa kirari kamar Allah ya aiko shi, 2k ta zaro a jakar ta miƙa masa kana ta fice. Karɓa yayi yana mai washe baki tare da dunƙule hannun hagun sa yana faɗin ''Allah ya ƙarama rayuwa albarka Hajiya Khansa'u, ya kuma ƙara nisan kwana'' Ko ta kanshi bata bi ba tayi gaba abinta, waige-waige ta somayi kafin ta hango wata Maroon ɗin mota ƙira Accord tana sheƙi fake aɗan nesa da gidan nasu, glass ɗin yaji dare (tinted). Tsaki taja tana mai kauda kanta gefe. Ganin bata da niyyar ƙarasowa yasa mai motar ƙarasawa gareta tare da sauke glass din motar. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!! Allah yayi halitta anan, kyakkyawan matashi ne wanda ganin sa saida yasa alƙalami na faɗuwa, bazai gaza shekara 30 ba, duk da cewa ba fari bane amma tabbas yana da kyau, kwantacciyar baƙar suma ce kwance ta kanshi data haɗa da sajen gami da gyararriyar ƙasumbar dake fuskar sa, inda ya zuba mata manyan fararen oily eyes ɗin shi mai cike da kwarjini, inda fuskar sa ta ƙara yalwatuwa da siririn dogon hanci da madaidaicin baki. Saida yaja iska ya fesar kafin ya fita, dan yasan halin kayar tashi sarai, tunda ta juya masa ƙeya fa bazata shiga ba. Haba my love, fushin ya isa haka, ya kikeso nayi? Nayi iya bakin ƙoƙari na na fahimtar dake babu abinda ke tsakani na da Amreesh wlh, yarinyar yayan Mummy (mahaifiyar shi) ne kinji na rantse miki. Hutu tazo gidan mu, shine tace jiya na ɗan fita da ita taga gari, wannan shine dalili. Uhm! Naji, sai kuma me? Khansa'u ta faɗa cikin ƙunar zuciya kamar ta fashe da kuka. Ajiyar zuciya matashin ya sauke yace ''Khansa'u''! Cike da mamaki ta kalleshi, dan bai taɓa kiran sunan ta haka ba cikin kakkausar murya. Baki yarda da Zayd ɗinki bane? Juyawa tayi ta kuma cewa ''uhm''. Murmushi yayi dan idan da sabo ya saba da shan wahala wajen rarrashin masoyiyar tashi, yanzun ma hakan ne ta kasance saida suka share kusan 40mins suna abu ɗaya, kafin ya samu ya shawo kanta. Ɗaukar ta yayi suka fita, basu tsaya ko ina ba sai munjibir park, dan ya santa da ƙaunar park, sosai taji daɗi kuwa yana ta yi mata hotuna tana dariya wanda ke ƙara bayyana kyawun fuskar tata. Saida suka biya ta gidan sister ɗinshi dake zoo road kafin suka kamo hanyar gida, akan hanyar su ne aka soma wani faɗa tsakanin wasu samari dake unguwa daban-daban, sosai ake faɗa ana zubda jini ana kisa tamkar rai ba'a hannun kowa yake ba, ganin haka yasa Zayd ƙoƙarin yin reverse saidai kafin yakai gayi sun far musu. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa ita kuma tana kuka tana ƙoƙarin kiran Abban ta.... Ji kake tassssss ƙarar fashewar glass, glass ɗin dake gefen driver aka fasa inda yayi tsalle ya caki goshin Zayd ya shige ciki, ko shurawa baiyi ba, su kuma suka ci gaba da tarwatsa mota tare da tsiyaya mata fetur, saidai ashanar su taƙi kamawa hakan yasa sukayi gama abinsu... Faɗi kawai suke ''sai mun rama, baza'a dakemu da daki banza ba, sai mun ɗau fansa akan al'umma''. Inda a ɓangaren Khansa'u kuwa girgiza Zayd kawai takeyi tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraron ta, sosai take kuka ta ɗauki kusan awa ɗaya tana abu ɗaya kafin ta fito daga motar zuwa lokacin abubuwan sun lafa, dan har al'ummar Annabi sun ɗan soma fitowa. Kallon motar kawai tayi ta kuma rushewa da kuka ganin yadda ta tarwatse, wayar ta ta fiddo ta kira Abban ta har kira uku bai ɗagaba, nan ta maida akalar wayar kan lambar Mummy itama bata ɗaga ba, hakan yasa ta kira Aliyu ƙanin Zayd ta sanar masa halin da ake ciki tare da faɗa masa inda suke. Hankali tashe ta tabbatar mata da gashi nan kuma kada subar wajen. Ba ɓata lokaci kuwa ya iso, kallo ɗaya zaka masa ka hango tsantsagwaron tashin hankali a fuskar sa, da ƙyar suka iya buɗe ƙofar mazaunin direban shida wasu matasa biyu. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu ya furta har sau uku, kafin wani zazzafan hawaye ya biyo kuncin sa, ya ƙurawa Zayd da fuskar sa ke ɗauke da murmushi ido, kamar ka kirasa ya amsa. Lee (daman haka take kiran shi) mu kaishi asibiti mana.. ta faɗa cike da tashin hankali. Girgiza kai kawai Aliyu yayi, dan kallo ɗaya yayiwa ɗan uwan nashi ya gano babu sauran numfashi a tare dashi.... Lee dan Allah ka ɗauko shi mu tafi, ta ƙara faɗa a karo na biyu cikin kuka mai ban tausayi. Shi da ƴan samarin ne suka cicciɓeshi tare zuwa motar Aliyu, kowa na wajen fuskar shi cike da alhini, yayin da ƙwalla ta gangaro kan fuskar Aliyu, tunanin sa ɗaya idan har Zayd ya rasu tayaya zasu fara gayawa Daddy, daddy nada hawan jini faɗa mai irin wannan tashin hankalin akwai matsala, daidai sun ƙaraso hospital ɗin... Nurses ne suka fito da gadon da za'a ɗaurashi a gurguje, cikin ƙanƙanin lokaci aka shiga dashi Emergency room.... _____________________________________✍️ Babylor ce😘 More comments,,, more typing..... Sai najiku a jam'iyar comments, dan shi kaɗai zai ƙaramin ƙarfin gwiwar sakin muku sabon update😇 [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍 *{The famous arabic poetess}* By Babylorh Marubuciyar; *Rushdah* *Maraici Na* and now.... *KHANSA'U* _(The famous arabic poetess)_ 5 & 6..... ________Kiciɓis sukayi da Daddy daidai ƙofar ɗakin shi shima yana shirin fitowa. Alhaji, dama wajen ka zanzo, meya faru da Zayd ne, yanzu aka kirani anayimin ya haƙuri, dan Allah idan wani abu ya faru ne ka sanar dani dan Allah Alhaji, sosai ta bashi tausayi yadda tayi maganar, daya rasa yadda zaiyi kawai saiya kama hannun ta yaja ta suka bar part din. Khansa'u da fitowar ta kenan taga sun fita itama ta mara musu gaba gaban ta na tsananta faɗuwa. Daddy bai tsaya ko ina ba sai sashin su Zayd, har ɗakin sa ya kaita sannan ya saki hannun ta ya tsaya daga bakin ƙofar, a hankali Mummy ke takawa harta isa bakin gadon, hannun ta har rawa yakeyi wajen ƙoƙarin buɗe mayafin da aka rufe Zayd dashi. Da sauri tayi baya jikin ta na ƙara tsananta wajen karkarwa, wata ƙara mai sauti aka saki daga bayan su koda suka juya wa zasu gani? Khansa'u ce kwance a ƙasa sumammiya, hawaye ne suka zubowa Mummy kana ta ɗaga hannu sama tana yiwa ɗan nata, tanayi tana kuka har takai inda kukan ya ƙwace mata, daidai su Aliyu da Ma'eesha da sukaji ihu sun shigo a sittin, girgiza ta Aliyu ya somayi amma ko alamar motsi ba tayi, nan ya ɗauke ta suka nufi part ɗin su Mum bayan yayi kiran Zayyad ya tabbatar masa da gashi nan zuwa. Sai kusan bayan 20mins sannan Zayyad ya shigo, dubata ya somayi tare da bata taimako amma abin yaci tura, ganin abin bana gida bane yasa ya ɗauke ta zuwa mota, Mummy da Daddy sunso su bisu amma Zayyad yace suyi zaman su, da Ma'eesha kawai suka tafi incase Khansa'u ta farka ya zamana akwai wani kusa da ita, cikin daƙiƙu goma suka isa asibitin Zayyad take Sharaɗa phase 1, cikin ƙanƙanin lokaci aka kawo gadon suka shiga da ita emerge, har kusan awanni biyu amma shiru kakeji, wai malam yaci shurwa, sai kusan awa biyu da rabi sannan Zayyad ya fito yana sharce zufa kana yayi wa Aliyu alama daya biyo sa office. Ba musu yabi bayan shi zuwa office, zama sukayi kafin Zayyad ya yace masa ''ammm Aliyu ina ganin ku tafi gida kawai dan a gaskiya bana saka ran farfaɗowar yanzu, zuciyar ta ta harba da alama taga wani abin daya mugun firgita ta, so a lokacin da mukazo ko numfashi ma batayi, sai yanzu mukayi nasarar daidaita numfashin ta, so yanzu ka ɗauka motana kuje gida, amma karka sanarwa kowa halin da ake ciki plss'', ya ƙarasa tare da miƙa masa key ɗin motar tasa. Amsa Aliyu yayi cike da tausayin Khansa'un, kallon Zayyad yayi da niyyar aika masa tambaya, amma inaa tuni ya faɗa toilet ɗin office din nasa, gudun tambayar. A ɓangaren su Mummy kuwa kuka kawai takeyi kamar yarinya, zuciyar ta cike da tunani da jimamin rasuwar ɗan nata, babu abinda take tunawa illa yadda Zayd ke kula da ita, ta yadda yake nuna tsantsar biyayyar sa gare su, domin kuwa Zayd namiji ne mai tarbiyya da daraja na gaba dashi, bashi da ɗagawa sannan bashi da nuna yana dashi balle kuma girman kai, ga haƙuri ya kauda kai akan abu, dan kafin kaga fushin sa abune mai matuƙar wuya, da ire-iren tunanin nan har su Aliyu suka shigo. Ganin jikin sa a mace yasa hankalin ta ƙara tashi, dan Aliyu mutum ne dake kasa ɓoye damuwar sa. Son, lafiya yana ganka haka, Ina Khansa'un da Zayyad? Murmushi Aliyu ya ƙaƙalo sannan yace ''relax Mummy na, mun barsu chan asibitin, so bazasu iya sallamar ta yanzu ba, shiyasa muka taho, amma Bro yace duk yadda ake ciki zai kirani''. Wata ajiyar zuciya Mummy ta sauke kana ta zabga uban tagumi ta cigaba da aikin tunanin ta, duk yadda akayi da ita da taje ta kwanta taƙi, saida Daddy yayi da gaske sannan ta tashi ta shiga ɗaki ita da Ma'eesha bawai dan zasuyi bacci ba, ganin zaman bazai ƙaresu da komai ba yasa Mummy ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta soma gabatar da nafila, yayin da Ma'eesha ke zaune tana karatun Alkur'ani a haka har aka yi kiran assalatu, saida suka gabatar da Sallah sannan suka fito, zuwa lokacin gari harya fara haske daidai lokacin Daddy da Aliyu sun shigo suma. Nan fa aka fara shirye-shiryen tafiya da gawar Zayd gidan ta gaskiya har kusan ƙarfe 7:30, daidai sistern su (Jumayna/anty Jumayna) ta iso itama cikin kuka da tashin hankali, jikin Mummy ta faɗa ba tare da la'akari da abinda zai samu cikin dake jikin taba, da sauri Mummy ta gyara ta tare da daidaita ta ganin bata ma damu da cikin nata ba. Sosai take kuka Mummy kam tana da rarrashi, dan zuwa lokacin damuwar ta sun ragu cikin 100 kusan 75 sun ragu sakamakon kukan ta da takai wajen mahalicci, ganin Jumaynan bata da niyyar tsayawa yasa ta ɗago ta ta soma magana cikin faɗa tana mai faɗin ''haba Jumayna meye haka ne wai? Kinzo kin tasa ni a gaba sai kuka kike kamar wadda iyayen ta suka rasu, haba sai kace baki san ƙaddara ko jarabawa ba, yadda na rungumi ƙaddarar rashin Zayd da dukkan ku kunsan nayi rashi ba kaɗan ba, kuma haka zaku rungumi taku ƙaddarar, Allah ya bamu ikon cin jarabawar mu kawai, amma a halin yanzu ba kuka Zayd ke buƙata ba, dan ina masa kyakkyawan zato da kuma addu'ar Allah ya dube shi da idon rahma sannan kuma halayen sa na gari su bishi''. Daga Ma'eesha har Jumaynan saida jikin su yayi sanyi matuƙa, wani mummunan faɗuwa gaban Jumayna yayi tunawa da hawan jinin Daddy da tayi, wanda idan ya tashi Allah kaɗai yasan mai zai faru, nan hawayen ta suka cigaba da ambaliya aranta kuma ta kwararawa Zayd da Daddy addu'a. Mummy ko sai faman faɗa take mata dan a zaton ta mutuwar takeyi wa kuka, daidai lokacin an fito da gawar Zayd za'a kaishi gidan shi na gaskiya, daidai gaban Mummy suka ijiye gawar kana suka ce mata ta masa addu'a. Jiki a sanyaye Mummy ta matsa kusa dashi ta soma yi masa addu'a harta gama, sannan suka daukeshi suka fita dashi, hawayen da Mummy keta riƙe wa be suka zubo ganin wai yau Zayd ne aka ɗauke shi aka fita dashi a kafaɗa da sunan ya rasu, Allah sarki rayuwa kenan, yau kaine gobe wanin ka, mutuwa mai yanke ƙauna, toh mukam saidai muce Zayd Allah yaji ƙanka, Ameen. Sosai nayi mamakin dubban jama'an da Zayd ya tara kamar babban mutum, gaba ɗaya tun daga farko har ƙarshen layin nasu baya biyuwa, a haka aka yi mota mota manya-manya sama da guda talatin, banda masu mashina da sauran su, aka ɗunguma zuwa maƙabarta, cikin lokaci ƙalilan aka gama haƙa kabarin sa, da Daddy da Abba (Daddyn Khansa'u) da Aliyu da Mahfouz da kuma Zayyad ɗin aka kama Zayd wajen saka shi a gidan nasa, sun gama saitawa kenan zasu sakashi aciki..... _____________________________________✍️ Babylorh❤‍🔥💞 07069929131 [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍 *{The famous Arabic Poetess}* By Babylorh🌹💞 Marubuciyar; *Rushdah* *Maraici na* loading......... *KHANSA'U* _(The famous arabic poetess)_ 9 & 10..... _________Washegari da misalin ƙarfe 8 su Mummy dasu Ummi harda anty Jumayna duk suka ɗunguma zuwa asibitin, inda suka saba zama nan suka nufa, wato corridor ɗin ɗakin da Khans ke ciki, yadda dai suka barta jiya haka suka tadda ta yanzu ma, zama Jumayna da Mummy da Ummi da duk damuwa sun bayyana ƙarara kan fuskar ta sukayi, yayin da Ayeesh da Ma'eesha ke tsaye jikin window ɗin glass ɗin da suke iya hango Khansa'un kwance. Wata iriyar zabura Ayeesh tayi tare da damƙe hannun Ma'eesha tare da murmushi kan fuskar ta da tayi jagab da hawaye, faɗi take ''sis Ma'eesha kinga hannun ta na motsi ko, wallahi ta motsa, bari inje in kira ya Zayyad'', tayi hanyar barin wajen da gudu. Da sauri su Mummy suma suka miƙe dan ganewa idanun su, daidai lokacin ta ƙara motsa hannun ta, nan Ummi ta ɗaga hannayen ta ta soma godiya ga Allah tana mai hawaye. Suna cikin hakane saiga Zayyad da Ayeesh da kuma wasu likitoci guda uku cikin shigar likitanci cikin sassarfa, da sauri suka buɗe ɗakin tare da faɗawa ciki kana suka rufo ƙofar. Wajen da suke iya hangota Ayeesh ta nufa tana mai share hawayen daya ɓata mata fuska bawai dan sun dena zubowa ba. Zayyad ganin motsin takeyi da gaske yasa yazo ya sauke curtain ɗin wajen da ake hangowa tare da komawa suka soma gudanar da aikin su cikin ƙwarewa. A hankali ta soma buɗe idanun ta da sukayi nauyi da duhu, tana buɗewa tana lumshe wa harta daidaita tare da sauke su kan yayan nata dake tsaye, a hankali a hankali abubuwan da suka faru suke dawo mata kamar sabo, wani zabura tayi tunawa da cewa ta rasa Zayd ɗin ta, nan su Zayyad suka rirriƙe ta tana cigaba da ƙwace wa kamar sabuwar kamu. ''Ku sake ni, ni ku sakeni, ya Zayyad ka sakeni nace, ina Zayd ɗina yake? Ni nasan bai mutu ba, kuma bazai taɓa tafiya ya barni ba....'' haka dai ta ringa sambatu tana ƙwace kanta ita ƙarfin nan, ganin haka yasa Zayyad sakin ta tare da nufar inda ya ajiye allurar daya shigo da ita, da sauri-sauri yake haɗawa harya gama yazo yayi mata, cikin minti ɗaya jikin ta ya saki gaba ɗaya kamar lagwani ta tafi luuuuu, maidata kan gadon sukayi sannan sukayi abubuwan da zasuyi suka fito bayan sun bar nurses guda a wajen koda ta farka. Koda suka fito saurin barin wajen Zayyad yayi gudun kada suyi ta tambayar sa dan yasan sunji ihun data rinƙayi, suma basuyi yunƙurin dawo dashi ba dan sunsan babu labari mai daɗi, Ummi kam tunda ta fara jin ihun Khansa'u hawaye ke zirya a fuskar ta, dukda tasan manta Zayd a tarihin Khansa'u abu ne mai matuƙar wuya, amma basu taɓa tunanin abun yakai haka ba. Toh a ɓangaren daddy kuwa abin sai godiya, dan basu Aliyu kaɗai ba, hatta likitocin sunyi matuƙar mamakin yadda Daddy ya farka kamar bashi ne yake cikin wannan yanayin ba, nan kuwa akayi discharging ɗinsu bayan magungunan da aka basa wanda aka chanza masa, saida yaci abinci yasha maganin sa sannan suka nufi gida shida Aliyu suka bar Abba da Mahfouz. Wanka kawai Daddy yayi suka dawo asibitin, sai a lokacin sukejin labarin abinda ya faru, sosai hankalin Abba ya tashi amma yayita ƙoƙarin danne damuwar shi gudun kada a gane, Daddy ma addu'a kawai yakeyi ɗiyar aboki kuma ɗan uwan nashi. Suna nan zaune har kusan ƙarfe 3 sannan Khansa'u ta farka, ɗaya daga cikin nurses ɗin da aka bari ne suka ta fito tana mai nufar office ɗin Dr. Zayyad, nan ta sanar masa data farka, da sauri ya miƙe ya fita office ɗin nurse ɗin ta mara masa baya, bai tsaya ko ina ba sai ICU room 2 inda Khansa'u take, kwance ya sameta idanuwan ta na kallon sama suna tsiyayar iska wanda a baɗini ba saman take ba. Da gudu ta miƙe ta nufeshi tare da faɗawa jikin sa ta saki wani marayan kuka kamar zata sheƙe, da kallon tausayi kawai nurses ɗin suka bita suna masu tausayi ga halin data shiga. Da ƙyar Zayyad ya iya raba ta da jikin sa kana ya zaunar da ita kan gadon shima ya zauna, hawayen ta ya fara sharewa kafin ya sakar mata murmushi tare da tanbayar ta ya jikin nata, ko akwai inda ke mata ciwo? Kanta kawai ta girgiza masa tana cigaba da hawaye kamar famfo. Ɗagowa tayi ta kalle sa tana faɗin ''yaya ina Zayd ɗin?''. Sunkuyar da kansa yayi ƙasa yana mai girgiza kan kafin kuma yace ''Khans ɗina kiyi haƙuri, Zayd ya amsa kiran da bazai taɓa dawowa ba''. Wani kukan ta kuma saki daidai lokacin dasu Mummy suke shigowa, da sauri Mummy ta ƙarasa inda take zaune shi kuma Zayyad ya miƙe tare da ficewa. Kuka sosai Khansa'u takeyi tana kwance jikin Mummy, rarrashin duniyar nan anyi amma Khansa'u taƙi shiru har sun gaji, kuka kawai take tana faɗin ''Mai yasa Zayd zai tafi ya barni Mummy, Maiyasa sai a lokacin da rayuwa ta zata shiga gagari a dalilin rashin sa zai tafi ya barni, mai yasa zai barni in this horrible life Mummy, na tabbata nima bazanyi lasting ba, dan banga amfanin zamana da duniyar nan..... Da saurin Mummy ta toshe mata baki tana mai girgiza mata kai, Ummi dake zaune kan kujera kuwa kasa cewa komai tayi banda hawayen dake ambaliya kan fuskar ta, Mummy ne kawai tayi ƙarfin halin faɗin ''ki dena faɗar haka Khans, a duniya ko wani bawa yana da tasa ƙaddarar, toh ke irin taki ƙaddarar kenan ko ince irin tamu ƙaddarar kenan, mai yasa baza kiyi imani da ƙaddara ki kuma roƙi Allah ya baki ikon cinye jarabawar ki ba? Allah ne ya baki yanzu kuma ya amsa abinsa, duk son da kike masa yakai kwatankwacin wanda Allah ke masa ne? Dan kawai ya karba abinsa shine zakiyi masa butulci Khansa'u? Har kina iƙirarin kema kin kusa mutuwa, kashe kanki zakayi ko me? Kada in ƙarajin makamanciyar irin wannan maganar a bakin ki, ki zama mai godiya ga Allah aduk halin da kika samu kanki Khans, kinji''. Ba Khansa'u kaɗai ba duk wanda ke wajen saida jikin sa yayi sanyi, babu abinda kakeji sai shessheƙar kukan Khansa'u, can kuma sai idanuwan ta suka ƙafe duk jikin ta ya rirriƙe, dukkan su sunji tsoron ganin ta haka, Jumayna data tashi domin kiran likita ne sukayi kiciɓis da Zayyad a bakin ƙofa, da sauri shima ya ƙaraso dan duba maike faruwa. Nan yaba su Mummy umarnin su fita, basuyi gardama ba suka miƙe suka fita, sai da yayi kusan 30mins sannan ya fito. Office ya koma ya zauna tare da dafe kansa yana mai mamakin wani irin so ne yayi wa Khansa'u mummunan kamu haka har yayi causing mata ```Heart Attack```. Yana wannan tunanin ne su Abba suka shigo, dukan su zama sukayi tare da ƙurawa Zayyad ɗin ido cikin son ƙarin bayani game da Khansa'u. Saida ya fuzgi iska ya fesar sannan ya soma magana kamar haka ''amm Abba bisa yadda bincike ya nuna min, ta kamu da heart attack, wanda in har ba'ayi takatsantsan wajen ɓacin ranta da damuwar taba, it can lead to her death. Moreover, brain ɗin ta yayi sanyi shima, so dole za'a chanza mata asibiti, coz ba fanni na bane, ni a nawa shawaran ina ganin a fitar da ita outside kawai, su zasu fi bata irin kulawar data dace'', ya ƙarasa maganar yana mai kallon Daddy. Sunkuyar da kansa Abba yayi da yakejin wani hawaye na ƙoƙarin zubo masa, yana matuƙar ƙaunar ɗiyar sa, addu'ar sa ɗaya Allah ya raya masa ita cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali. Daddy ne yayi ta maza yace ''yanzu wani asibiti ne kake ganin suna da kula sosai ta wannan fannin''? Eh toh, kamar London, ko Dubai ina ganin zaifi gaskiya, ko India ma, cewar Zayyad. Daga haka Daddy bai ƙara cewa komai ba illa kama Abba da yayi suka fita...... __________________________________✍️ Babylorh ce💖❤‍🔥 07069929131 [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍 *(The famous arabic poetess)* By Babylorh🌹 Marubuciyar; *RUSHDAH* *MARAICI NA* loading...... *_KHANSA'U_* {The famous Arabic Poetess} Wannan page sadaukarwa ne kacokam gareku masoya littafin Khansa'u, ina alfahari daku😍🌹💝❣️ Page 7 & 8..... ___________sun gama daidaita shi zasu sakashi ciki kenan jikin Daddy ya soma wata irin rawa yana karkarwa, da sauri Aliyu da Mahfouz suka nufesa suka riƙe shi tare da barin wajen dashi. Mota suka koma suka sanya shi ciki suna masu tashefa da addu'a, ganin kamar zai shiɗe yasa Aliyu komawa mazaunin driver suka yaja motar, yayin da Mahfooz ke ci gaba dayi masa addu'o'i har suka isa asibitin Zayyad, cikin gaggawa aka karɓe sa akayi ciki dashi, basu tsaya dashi ko ina ba sai Emergency room, abinka da asibitin kuɗi da nuna kulawa wa patients, nan doctors suka rufu akan sa, moreover kuma sunsan Family ɗin su Daddy da nasu Khansa'u, sai zuwa kusan 45mins sannan likitocin suka fito, ɗayan cikin su yayiwa su Aliyu alamar su biyo sa office. Ba musu sukabi bayan shi zuwa ofishin nasa suka zauna, likitan ne ya soma magana kamar haka ''a gaskiya a halin da ake ciki akwai matsala, is like Alhaji ya sanyawa kanshi damuwa ne zance ko tunani, har takai ga jinin sa ya hau sosai, yanzu akwai buƙatar sauyin magunguna da za'ayi masa, kuma insha Allah zai samu lafiya''. Rinannun idanun sa Aliyu ya ɗago tare da sauke su kan doctor ɗin na ɗan wani lokaci kafin ya maida su kan Mahfouz dake faɗin ''toh shikenan doctor, mun gode sosai, amma yanzu zamu iya ganin shi?'' Nope, sabida har yanzu yana emerg sannan mun masa allurar bacci dan yasamu ya rage tunanin nan, cewar doctor. Nan Mahfooz ya ƙara da ''okay doctor toh sistern mu fa, ita zamu samu damar ganin ta?'', ya faɗa cike da damuwa shimfiɗe kan fuskar sa. Murmushi likitan ya masa kana ya zagayo tare da dafa kafaɗun sa yace ''calm down my bros, suna cikin ƙoshin lafiya insha Allah, bt file ɗin kula da ita baya waje na, yana tare da Zayyad, so idan yazo zakuji komai daga gareshi''. Godiya Mahfouz ya masa kana yaja hannu abokin nasa dake zaune kamar an dasa shi suka fita, ganin suna nufi parking lot yana Aliyu cewa ''Malam wai ina zaka kaini sai wani jana kakeyi''? ya faɗa tare da fizge hannun sa. Mahfouz dake jingine jikin mota ne yayi folding hannaye sa yana mai faɗin ''Aliyu zuwa yanzu nasan su Abba (baban shi) sun dawo daga maƙabarta, ya kamata kazo mu koma mu sanar dasu halin da ake ciki, kada hankalin su ya tashi''. Babu inda zanje Mahfouz, kaidai kawai ka tafi kaje duk yadda ake ciki na kira ka, idan na tafi waye zai kula da Daddy in ya farka? Ina tare dashi har inga yadda ta Allah zata kasance, Aliyu ya faɗa cikin tsantsar damuwa. Aliyu, Daddy yana ƙarƙashin kulawar Ubangiji dana doctors, nothing will happen insha Allah kuma zai farka very soon, kazo muje gida dan Allah. Wallahi Mahfouz babu inda zanje, kaji na rantse, ya ƙarasa tare da komawa cikin asibitin ba tare daya jira cewar Mahfouz ba. Da kallo kawai Mahfooz ya rakasa harya ɓacewa ganin sa, sannan ya shiga mota yayi mata key ya fice, kusan tare ya dawo da ƴan maƙabarta dan a lokaci ɗaya suka isa. Jira yayi har su Abba suka ƙaraso, Abbane ya soma tanbayar sa ina suka kai Alhajin? Yana asibiti Abba, wai hawan jinin sa ya tashi sosai, shine nace bari in dawo in sanar daku halin da ake ciki. Toh yanzu wa kuka bari a wajen sa? Cewar Abba. Eh Aliyu na can, Ni kaɗai nazo dama. Muje ka kaini asibitin, daddy ya faɗa tare da shiga motar Aliyu da Mahfouz ya taho da ita. Zayyad kam bai bisu ba, illa ma shiga cikin gidan da yayi wajen Mummy. Zakuyi mamakin yadda ya shiga cikin gida wasu zasuce cikin mata, so a ƙa'idar al'adar su basa zaman makoki zaman gulma, a cewar su babu abinda akeyi sai gulma da munafinci uwa uba gutsiri tsoma, hakan yasa saidai kawai azo ayi musu gaisuwa a wuce. Zayyad bai daɗe ba ya fito shima ya shiga tashi motar zuwa asibiti, yana isa bai wani ɗauki lokaci ba yaje ya shirya cikin kayan likitoci sannan ya fito tare da bada umarnin a chanzawa Daddy ɗaki zuwa special emerg, hakan kuwa akayi cikin lokaci ƙalilan aka fito dashi akan gadon su na turawa, da sauri Aliyu ya miƙe cikin tashin hankali ganin yadda Daddyn nashi yake, sanye yake cikin rigar asibiti blue ɗinnan ta patients da hula, sai hancin sa dake ɗauke da Oxygen yana fuzgar numfashi, da sauri Aliyu ya taka zaije wajen, Mahfouz yayi saurin riƙe shi tare da girgiza mai kai alamar yayi haƙuri mana, baiyi musu ba ya koma ya zauna wasu hawaye na bin fuskar sa, tsoro yakeyi kada ya rasa Daddyn sa da yayi masa saura, addu'a ma ƙauracewa bakin sa tayi sai daga baya ya samu ya iya aikawa mahaifin nasa addu'a. Sosai kuwa Daddy ya samu sauyin kulawa a special emerg, dan harsun samu nasarar ƙara daidaita numfashin sa a karo na biyu, wanda suke tsoron zuwan karo na uku dan komai zai iya faruwa. Yana zaune cikin wannan halin na mutuwar ɗan uwan sa da kuma rashin lafiyar mahaifin sane wayar sa ta hau kuka tana neman ɗauki, koda ya duba 'Role model' ya gani yana yawo kan screen ɗin wayar, da sauri ya ɗaga tare da karawa a kunnen sa yana mai furta ''Mummy''. _Hello Son wai Ina kuka shiga ne kaida Alhaji? Koda kuka dawo maƙabarta Zayyad ne kawai ya shigo._ Amm Mummy muna asibiti, daddy ne ya faɗi a maƙabarta, sunce hawan jinin sane ya tashi shiyasa, bakiga yanda aka fito dashi ba Mummy zattausayi, Ina tsoron...... A fusace Mahfouz ya kwace wayar daga hannun sa yana mai auna masa harara kana ya kara wayar a kunnen ya soma magana ''Mummy kinaji, ba wani abu bane kawai hawan jinin sane ya tashi, so yanzu an fito dashi zuwa inda za'a chanza masa magunguna ne ba wani abu ba, karki damu, ai bazai wuce 30mins ba zai farka insha Allah''. Ajiyar zuciya Mummy ta sauke kana tace _shikenan son duk yadda ake ciki ka kirani dan Allah. Ya batun Khans kuma?_ Eh muna jiran fitowar Zayyad ne tukun, tunda sunce file ɗin ta na wajen shi. _Okay Allah ya basu lafiya, sai naji ka_ Ameen Mummy sai anjima, ya katse wayar tare da fuskantar Aliyu ya soma magana cikin faɗa kamar haka ''wani irin raunin zuciya gareka ne wai Aliyu, sai kace mace, gaba ɗaya ka kasa sawa kanka natsuwa duk kabi ka tada hankalin ka kuma kana ƙoƙarin tadawa Mummy nata, dame zataji ? Mutuwar Zayd ko halin da Daddy ke ciki, instead ka kwantar mata da hankali amma kanata wani ƙoƙarin sanya ta cikin ruɗani, ya ƙara sa tare da jan tsaki. Aliyu dai baice komai ba, dan ba ƙaramin ɓata masa rai Mahfouz yayi ba, idan yace zaiyi magana zasu iya samun matsala, danshi mutum ne mai shegiyar zuciya hakan yasa kawai yayi shiru ya ƙyale shi. A ɓangaren Khansa'u kuwa abin saidai godiyar rabbi kawai, dan yadda aka kawo ta haka take, wataran numfashin ta ya tsaya cak, wataran kuma yayi daidai, hakan yasa Zayyad yanke shawarar shiga da ita Intensive Care Unit (ICU) Wanda kanawa suke masa laƙabi da (ɗakin duhu)😜. Hakan kuwa akayi washe gari da safe around 8am aka shiga da ita ICU, gaba ɗaya ahalin biyu sun hallara a asibiti gashi sun gaza samun sukuni daga masu hawaye sai masu kukan zuci, dan kowa ya shaida daga ICU babu kuma wani ɗakin gaba, ko rai ko mutuwa. Sosai Zayyad yake nuna bajintar sa wajen ganin ya ceto ran ƴar uwar tasa kuma mafi soyuwa a gare sa, dan yadda yakeji da ita daban ne. Akai-akai Ummi (mummyn Khans) takan duba agogo sannan ta kalli ƙofar ɗakin ko zataga sun fito amma shiru kakeji har kusan 1hr, hakanan suka cigaba da haƙuri har suga abinda Allah zaiyi. Fitowar Zayyad yasa dukkanin su miƙewa suka nufe sa tare da tanbayar sa an samu nasara, share zufar sa yayi yace ''calm down all of u, har yanzu dai bata farka ba, amma zamu jira zuwa gobe mu gani idan har bata farka ba dole saidai a fita da ita outside''. Abba ne yaja wani dogon numfashi, dan shi inda za'abi ta shawarar shima yanzu bai ƙi su fitar da ita ba, amma zaiyi haƙurin su jira zuwan goben. Kamar yadda Zayd yake shalelen parents ɗinsa, haka itama Khansa'u, Zayyad da Mahfouz ba ƙaramin ji suke da ita ba balle kuma uwa uba Ummi da Abba, kowa ya shaida yanda Khansa'u keda babban matsayi a zuƙatan su, domin kyawawan ɗabi'un ta kaɗai sun isa susa mutum ya sota saidai kuma in kana hassada, hakan yasa duk hankalin su ya gaza kwanciya, babban burin su bai wuce ace musu ta farka ba, amma abu yaci tura......... ```Toh wai waɗannan ahalin biyu meye alaƙar su ne? Ƴan uwan juna ne ko kuwa maƙwafta ne ko abokai?``` Nasan readers kuna ta wannan tunanin, toh karku damu, kasance tare da Babylorh danjin jikakkun tarihin wannan family ____________________________________✍️ Bebilo ce❤‍🔥💝 07069929131 [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍 *{The famous arabic poetess}* __________________________________ By Babylorh♥️❤‍🔥 Marubuciyar; *Rushdah* *Maraici na* loading.......... *KHANSA'U* _(The famous arabic poetess)_ *WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚 _(Domin Marubuta Mata)_ ✨(W.W.A)✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ ___________________________________ 11 & 12...... *INDIA* Hakan kuwa akayi, washegari da safe jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasar India, inda suka tafi da Daddy, Abba, Ummi, Aliyu sai kuma Mahfouz, a wani *City Psychiatric Hospital* dake babban birnin Mumbai akayi admitting ɗin ta, tare da fara aiki kan matsalar ta. Abinka da ƙasar waje, basu da matsala fannin kayan aiki nan danan kuwa suka gano matsalar tata tare da yi mata dukkan abinda ya dace. Doctor Karan wanda ke kula da sashin Khans ne ya fito tare da cewa su Daddy su sameshi a office. Office ɗin nashi suka shiga tare da zama inda aka tanadar musu, doctor ɗinne ya soma magana kamar haka ''Sir, yarinyar ku ta kamu da matsalar zuciya da ƙwaƙwalwa, duk da ƙwaƙwalwar tara bawai ta samu matsala bane, saidai koda ta farka she would become a psychiatrist, a yanayin binciken mu hakan ta faru ne due to heart attack data samu shiyasa ya taɓa ƙwaƙwalwar ta, amma karku damu, she would be fine and become healthy as before, saidai zuciyar ta ba zata dawo daidai ba, saidai kuma wani iko na ubangiji'', duk cikin harshen turanci yake maganar harya gama. Ajiyar zuciya Abba ya sauke yanajin wani irin yanayi na ziyartar shi, ganin haka yasa Daddy tanbayar ''shin zata ɗauki tsawon wani lokaci a haka''? Zatakai kamar 6 months with us here, shima dan kun kawo ta da wuri ne kafin abin yayi worst, so we would try our best akan ta muga ta samu lafiya, kada ku damu ku cigaba dayi mata addu'a, she will soon recovered by the grace of Almighty, daga haka bai ƙara cewa komai ba, nan suma su Abba suka bar ofishin. Kwanan su Mahfouz uku suka dawo 9ja inda aka bar Ummi da Abba suna jinyar ta, badan Mahfouz yaso ba haka ya dawo saidan kawai aikin shi, amma yakan je ya duba ta musamman weekend. Shima Zayyad ba'a barshi a baya ba, dukkanin su sukan zo su duba ta a haka har suka kwashi watanni uku, amma babu abinda ya canza, ba Ummi ba hatta Abba kanshi ya riga ya sallama Khans bazata rayu ba, duba da yadda ta lalace ta rame tayi baƙi bata Um bare um um, in kaga tayi magana toh abu yakai ya kawo, amma komai ta gwammaci tayi shi da gaɓoɓin ta. Yauma zaune suke ita da Ummi da kuma su Haseena da Ayeesh da Mahfouz da suka zo, a wanan karon ma harda Zayyad, sosai tayi farin cikin ganin su saidai ta kasa nuna hakan, sosai sukejan ta ta hira amma ba wani fiye amsa su takeyi ba, amma babu yadda suka iya, ko hakan da suka samu ma sunji daɗi. Washegari da safe bayan Dr. Karan ya shigo sashin su Abba ya bishi Office, da gaisuwa suka fara kafin Abba ya nemi sallama daga asibitin a cewar sa gara ya koma suyi mata da Islamic. Duk yadda Dr. Karan yaso ga tausasa Abba kan a bari zuwa ko nan da wata ɗaya amma Abba yaƙi sam, tunda ta samu lafiya me zai zauna kuma yayi? Abin daya rage kaɗan ne dan haka tafiya kawai zaiyi. Badan yaso ba haka yayi discharging nasu tare da musayar number da sukayi dan wata matsalar. A ranar Abba yayi musu booking jirgin dazai tashi washe gari, cikin sa'a kuwa ya samu wanda zai tashi da ƙarfe 7 na safe. Ba Ummi kaɗai ba hatta ita Khansa'un ba ƙaramin daɗi taji ba na komawar su 9ja, dan dama ta gaji da zaman asibitin ainun, a daren ranar duk suka wuce *Jalwa Guest Palace* da suka kama da zunmar shirya kayan su, babu wanda yayi bacci saida suka tabbatar da duk sun kimtsa. Washegari da misalin ƙarfe 7 daidai jirgin su ya ɗaga zuwa Nigeria.... *NIGERIA* _____Alhmdlh sun isa lafiya kuma cikin ƙoshin lafiya, manyan motoci na alfarma ne har guda uku suka zo ɗaukar su, da Abba, Mahfouz da Zayyad motar su ɗaya, Haseena da Ayeesh suma motar su ɗaya, sai Ummi da Khansa'u suma mota ɗaya, tafiyar sa'a guda ta kaisu gida. Nan fa al'ummar annabi suka soma shigowa jajanta musu da kuma gaida maras lafiya, ranar gidan gaba ɗaya hargitsewa yayi kamar ana sha'ani, hatta Mummy da tawagar ta duk saida suka hallara a gidan, basubar gidan ba sai misalin ƙarfe 11 na dare....... *Masu iya magana kan ce _WAIWAYE ADON TAFIYA_, toh! A wannan gaɓar nake mai muku albishir da muma zamu waiwaya danjin cikakken tarihin wannan Family.* _Alh. Muhammad Shehu wato (Abba) da kuma Alh. Safwan Shehu wato Daddy sun taso tare inda sukayi komai tare, suka zauna tare kana sukayi aure tare a rana ɗaya._ _Alh. Muhammad (Abba) ya kasance ɗan riƙo ne a gidan su Alh. Safwan (Daddy), ya kasance maraya wanda tun tasowar sa bai taɓa tozali da iyayen sa ba. Ya kasance tsintacce ne wanda ba'a san iyayen sa ba, Mahaifin Daddy (Malam. Shehu, Allah ya masa rahma🙏) ya tsincesa ne a wani hatsari daya faru a KOFA dake ƙaramar hukumar BEBEJI dake garin Kano, hatsarin ya auku ne daidai express ɗin shiga KOFA, da misalin ƙarfe 6:30 na yanma inda burki ya ƙwacewa motar dake bayan su harta cin masu, da musu wani irin duka da bazaka so ka ƙara ƙallo ba, yadda motar ta tarwatse kaɗai ya isa ya tabbatar maka da bbu mai rai. ba'a iya ganin wanda ke tuƙin bama balle wa'inda ke ciki, unfortunately aka jiyo kukan jariri na tashi, daƙyar da wuya aka iya ɓamɓare ƙarafunan jikin motar aka binciko inda jaririn yake, zattausayi ganin a lokacin yazo duniya dan gaba ɗaya jikin sa jinin haihuwa ne, rasa wanda zai ɗauki jaririn da akayi yasa malam Shehu yin jahadi da ƙarfin halin ɗauka tare da tunanin rayuwar da jaririn zai shiga na halin rashi domin shi ɗin ya kasance talaka ne iyayen sa talakawa, wanda bai ajiye ba kuma bai bada ajiya ba, mutum na shi mai zuciyar nema kuma bashi da son abin duniya, wannan yasa Allah ke basa damar samun abu aduk lokacin da yayi ƙoƙarin nema. A lokacin daya dawo gida da wannan jariri ya fuskanci tashin hankali da barazana iri-iri wajen matar sa Sa'ade (kishiyar mamar Daddy), daga baya ma cewa tayi ya fitar mata da ɗan shege daga gida, wai yaje yayi cikin shege an haife masa. Kasancewar malam Shehu mutum mai haƙuri yasa ya tafi gidan ɗaya matar sa Habiba, saida ta fara tambayar sa inda ya samo shi dan kada zargin ta ya tabbata, bai ɓoye mata komai ba ya sanar da ita, sosai ta tausaya masa matuƙa gaya kana ta amsheshi ta cigaba da shayar dashi, dan dama batayi arba'in da haihuwa bama_........... ___________________________________✍️ Daga alƙamin babylor💓🌹 07069929131 [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 (The famous arabic poetess By Babylorh🌹❤️ *(Shalelen Women Writers)*😎 Marubuciyar; 1. *Rushdah* 2. *Maraici na* Loading....... 3. *KHANSA'U* _(The famous arabic poetess)_ 13 & 14..... __________ _Bayan faruwar al'amarin kam sosai harkar kasuwancin mal.Shehu ya ƙara haɓaka, sosai yake ganin haske cikin al'amuran sa ga kuma ƴan yaransa maza suna ta wayau abin su abin sai godiya. A ɓangaren Sa'ade kuwa ta uzirawa malam ta hanasa rawar gaban hantsi, ganin bazai iya ba yasa ya sauwaƙe mata, murna wajen ta kam ba'a magana._ _Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu har girman su, su Daddy nada shekara 18 Malam Shehu ya soma wata cuta wadda aka rasa gane kanta, yayi jinya ba kaɗan ba kafin Allah ya karɓi rayuwar sa a safiyar juma'a. Nan sabon babin rayuwa ya buɗe musu, kasancewar dukkanin su dashi suka dogara, dan a lokacin yaran duk sun kammala secondary amma babu halin cigab. Da wuya da zufa suke iya buga-buga su nemo abinda za'a saka a bakin salati, haka rayuwar su tayi ta tafiya, Abba bai taɓa sanin su mal Shehu ba sune iyayen sa ba sai lokacin da inna ta tashi rasuwa bayan shekara 1 da mutuwar mal. Shehu, daren ranar da zata rasu ne duk ta sanar dasu labarin Abba, tana gama faɗa kuwa ta cika da kalmar shahada, sosai Abba yayi kuka ba kaɗan ba, kuka masu tarin dalilai ciki har da rashin sanin iyayen sa da baiyi ba haɗi da rasuwar wa'innan bayin Allah da suka riƙe shi da zuciya ɗaya._ _Sosai suke fuskantar rayuwa da halin rashi da suke fama har suka soma ƴar sana'ar su, su nami na yau su samu na gobe, Allah cikin ikon sa kuwa ya cigaba da buɗa musu har shekaru yaja musu, cikin ƙanƙanin lokaci sukayi suna suka zaga arewacin Najeriya, a lokacin suka soma tunanin aure. Nan Abba da Daddy suka firgita da mata har aka sanya ranar aure, a ranar ashirin da biyu ga watan Agusta shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar 2015 da misalin ƙarfe ɗaya na rana aka ɗaura auren *Daddy da matar sa Rabi'atu* sai kuma *Abba da matar sa Maria*_. _Bayan zuri'a da kowannen su ya tara ne babban ɗan Daddy wato Zayd da ɗiyar Abba Khansa'u suka jone, a lokacin Khansa'u na aji biyu a Babban sakandare wato SS 2, yayin da Zayd ke ajin ƙarshe a jami'a, babu wanda baiyi na'am da wagga lamari ba, tun suna jin kunyar bayyana soyayyar su har suka daina. Khansa'u ta kasance mace mai kishi ta yadda ko yaya taga Zayd da wata mace da bata santa ba ta ringa kishi tana kumbure-kumbure, wannan yasa Zayd kiyaye duk wani abu dazai ɓata mata rai, domin sonta a halittar sa yake, bai taɓa ganin ko wacce mace yadda yake ganin Khansa'u ba. Wannan dalili ne yasa Khansa'u kasa ɗaukar mutuwar Zayd a zahiri, duk duniya bayan iyayen ta babu wanda ke nuna mata ƙauna da gudun ɓacin ranta sama da Zayd, duk da kuwa suma su Zayyad ba daga baya ba wajen bata kulawa, sabida yarinya ce ita mai shiga rai lokaci ƙalilan._ _~WANNAN KENAN~_ *BACK TO STORY* Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakanin ahalin biyu, burin ko wannen su ya farantawa Khans, burin ko wanne ya kiyaye wajen ɓata mata rai, ita kanta tasan duk inda wani maiji da dangi maiji da kanshi cikin shalelen dangi ta wuce nan, a ko da yaushe takan yi iya bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta cire abin a ranta amma ta kasa, bata taɓa zaton haka takeson Zayd ba, tayi danasani iya danasani na fitar da sukayi a ranar, amma har yanzu bata daina addu'a ba kullum tanayi, sannan iyayen tama na taya ta. Kamar yadda ta saba ƙulewa cikin ɗaki ta zauna tasha kukan ta sa'ilin data tuna da Zayd, yau ɗin ma hakan ne ya kasance, zaune take bisa lallausan katifar data mamaye ƙaton gadon ta hannun ta riƙe da album na zallar hoton Zayd tana kallo, sautin kukan tane naga ya ƙari yayin da tazo kan wani hoto da suke tare, tana sanye da baƙar Abaya shi kuma ya sanya farar jallabiya da baƙin takalmi sau ciki haɗi da rawani, sakk suka fito larabawa, musamman data ƙawata fuskar ta da murmushi suna kallon junan su, ban ankara ba naga ɗiyar ruwa akan hoton, koda na duba sai naga hawayen Khans ne ya zuba akai, a hankali tasa hannu ta share ta cigaba da buɗe album ɗin. Zaman da taji anyi kusa da ita ne yasa tayi saurin ɗagowa, Ummi ce ke zaune fuskar ta cike da tausayin ɗiyar tata, "haba Khans, meya sanya kike son shiga damuwa ne? Which is very very risk to ur life, shin mune bama faranta miki? Ko kuwa salon kula dake da mukeyi ne bakyajin daɗi?" Kukan daya ƙwace mata ne ya hanata magana yayin da take girgiza wa Ummi kai alamar a'a kafin tace "Ummi na duk ta dalilina wannan abin ya faru da ya Zayd, da ban biye masa mun fita ba da duk haka ta faru ba, naso ace ni suka kashe suka barshi a raye, nasan zai fini jure rayuwa babu ni." Ta ƙarasa tana faɗawa jikin Ummi tare da sakin wani kukan. A hankali Umma ke bubbuga bayanta haɗi da rarrashin ta har kukan ya lafa, cikin dibara Ummi ta zameta a jikin ta ta shiga bathroom, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta fito, badan Khans taso ba haka ta tashi ta shiga, dan a halin da take ciki ma wanka ba ƙaramin wuya yake mata ba. Aikam bata wani daɗe ba ta fito, Ummi taso ta mata magana, amma gudun matsala yasa ta ƙyale ta tare da bata wuri ta shirya. Cikin combination na paper lace pink da purple ɗin atamta ɗinkin doguwar riga ta shirya, ba tare data shafa koda mai ba ta fito, dan hatta gashin kanta ma bata gyara ba, tamkar dai wacce ta tashi daga bacci. Parlor taje inda su Haseena ke zaune itama ta zauna, nan suka soma sakata cikin hirar su kuma ba laifi ta sake anyi hirar da ita, dan su har sunyi mamaki ma matuƙa. *********** Yammaci ne mai ɗauke da sassanyar iska inda bishiyo ke kaɗawa suna bada ni'imtacciyar iska mai ratsa jiki, tsaye take a garden ta harɗe hannayen ta ta ƙurawa ɗan matsakaicin pool ɗin dake gefe ido kamar mai nazari, ta ɗauki lokaci sosai kamin fuskar ta ta fidda wani ƙayataccen murmushi da rabon da tayi irin shi tun kafin rasuwar Zaid. Mahfouz dake tahowa a hankali cikin sanɗa hannun sa riƙe da feather 🪶 ya goga mata a wuya, da wata razananniyar ƙara ta juyo dan ganin meye, lokaci guda kuwa ta tamke fuska tace "ya Mahfouz ba kyau firgita mutum." Ƴar dariya yayi yace yace "Congratulations sis." Da mamaki ta kalle sa kafin cikin rashin sani ta furta "for?" "Ohh, baki ma sani ba kenan?," ya faɗa yana zaro wayar sa ƙirar iPhone daga aljihu, ƴan latse-latse yayi kafin ya ya miƙa mata wayar. Amsa tayi ta soma dubawa, 'Admission later' ne dake nuna ta samu admission kuma akan course ɗin da duk duniya take muraɗi wato (Lawyer). Wani tsalle ta buga tare da rungume yayan nata tsabar murna, da sauri ya ture ta yana ɓata rai kamin yace "ke bakisan kin girma bane, meye kuma na wani faɗomin kamar sa'anki." Ɗan ɓata rai tayi tana turo baki tace "toh kai ɗin ba yayana bane." "Uhm bani waya ta nidai, saiki fara shiri," ya faɗa yana miƙa mata hannu. Itama miƙa masa tayi tana murmushi sannan tayi cikin gida da ƴar murnar ta harda tsalle, sosai Mahfouz yaji daɗi ganin ƴar ƙanwar tasa cikin farin ciki, shima juyawa yayi tare da nufar sashin su... _______________________________________✍️ *BABYLORH*🤞❣️ ~*(Shalelen Women Writers)*~ 07069929131✍️ Next page loading........ [9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(Shalelen Women Writers)*🌹💓 Marubuciyar: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading....... 3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_ 15 & 16.... _________Nan fa su Khans aka soma shirye-shiryen shiga jami'a, domin nan da wata ɗaya zasu soma karatu. Saida suka kammala komai daya ƙunshi makarantar da kuma tabbatar data mallaki dukkanin abin buƙata kafin ranar karatu. Yau take Monday, wato ranar dasu Khansa'u zasu fara karatu, Zayyad shine ya ɗauke ta zuwa makaranta ya kuma nuna mata department ɗin su, saida ya tabbatar da bata buƙatar komai sannan ya tafi. *1st day at school* Duk wata murna dajin daɗin da take tayi suna zuwa taji sun tafi, tunanin ta ɗaya yadda zata fara rayuwa cikin makarantar da babu wanda ta sani balle kuma a santa, waje ta nema ta zauna a kujerar dake ɗan nesa da department ɗin nasu ta cigaba da kallon yadda al'umma ke kai komo. "Assalamu alaikum baiwar Allah," wata kyakkyawar budurwa ta faɗa wadda alamu suka nuna itama sabuwar zuwa ce. "Wa'alaikis Salam," Khans ta amsa mata cikin sakewar fuska. "Sannu baiwar Allah, dan Allah department of law nake nema." "Ga shi can," Khans ta faɗa tana nuna mata da yatsa. "Okay na gode sosai, sunana Nasreen Ahmad Sulaiman, kefa?" "Khansa'u Muhammad," ta furta a taƙaice. "Wow, nice name. Da alama kema sabuwar zuwa ce koh?" "Eh," khans ta bata amsa cike da ciƙe da ƙosawa da shegen tambayoyi da surutun Nasreen din. "Wow, amma ko wuri baki bani ba, kuma kinsan ance baƙon ka annabin ka." Cikin murmushin yaƙe Khans tace "bismillah zauna mana." Zama Nasreen ɗin tayi ta cigaba da jan Khans da surutu, duk da sai tayi magana kusan biyar kafin Khans ta bata amsar biyu, tun dai bata sake ba har ta saki jiki suka ɗan taɓa hira, duk da kusan gaba ɗaya hirar akan karatu ne. Basu wani jima a wajen ba suka shiga class aka soma lectures, sai kusan 2 suka fito, a gajiye Khans ta fito ga kuma yunwa da takeji, wayar ta ta ɗaga ta daddanna kamin ta kara a kunnen ta na ɗan wasu lokuta sannan tace "Hello ya Mahfouz, dan Allah kazo ka ɗauke ni kaji?" Banji me akacedai ba daga ɗaya ɓangaren, naji ta amsa da zan jira ka kusa da department ɗinmu toh. Inda ta zauna ɗazun nan ta koma ta zauna ta soma game da wayar ta, kwatsam saiga Nasreen, ita harga Allah tama manta da wata Nasreen wallahi, nan dai ta murmusa mata kana tace "sai yanzu kika fito?" Wallahi kuwa Khans, ki taso muke muci abinci mana, yunwa nakeji sosai. Laaaa, nikam har na kira yaya nama, yanzu zaizo ya ɗauke ni. Okay, nima bari insa azo a ɗauke ni kawai, ta faɗa tana fiddo wayar ta, kira tayi itama kan azo a ɗauke ta, kamin suka cigaba da hira. A wannan karon kam babu laifi Khans ta saki jiki da Nasreen, sunyi hira sosai kamin Mahfouz yazo. Nan sukayi sallama cike da kewa, musamman ma Nasreen da lokaci ɗaya taji son Khans da ƙawa. Da sallama ta shiga ɗauke a bakin ta, Mahfouz dake motar ya amsa mata. Washh, ta furta yayin da take zama. Dariya Mahfouz yayi sosai sannan yace "yau fa manya an banbance secondary school da jami'a." Baki ta turo tana ɓata rai yayin da take faɗin "kaiii yaya bazaka gane bane wallahi, akwai gajiya sosai." Haha, lallai fa bazan gane ba, tunda ni banje jami'a ba. Dariya duk suka sa kamin ta soma duba jakar ta, ganin bataga abinda take nema ba yasa ta ɗaga wayar ta tayi dialing number Nasreen. Bugu biyu kuwa ta ɗaga tana faɗin "ba sai kin tambaye ni ba, yana waje na, saida kika tafi nima na gani." Dariya duk sukayi kana sukayi sallama ta cigaba da sauraron ƙira'ar *Al'afasy* da Mahfouz ɗin ya kunna, har suka ƙarasa gida. Cikin tangaɗi ta shiga parlor tamkar wacce bata taɓa zuwa makaranta ba, kan kace me dukkan wajen ya kaure da dariya, harda autar su Ayeesh ta dake cire socks ɗin ƙafar ta, wanda k nuni da itama yanzu ta dawo gidan. Sosai ta ɓata rai ta nufi inda Ummi ke zaune itama ta zauna yayin da take faɗin "kinga Ummi wallahi ki jawa yaran ki kunne, musamman waccan mai ƙaramin hancin su fita a idona," ta ƙarasa tana nuna Ayeesh. Nan ma dariyar aka ƙarayi kamin Ummi tace "toh ɗiyar albarka za'a ja musu kunne, maza tashi kije kiyi wanka kizo muci abinci." "Tabdi, ƙyale wankan nan Ummi, bari in fara cika tumbin na tukun, kinji yadda kayan cikina ke kuka kamar zasu faɗo kasa," ta faɗa tana miƙewa tare da nufar dinning. Da dariya ƴan uwan nata suka bita, yayin da Ummi ta raka ta da murmushi haɗi da kallon ƙaunar ƴar tata, tare da fatan Allah yasa farin ciki ya ɗore har ƙarshen rayuwar ta. Washegari ma haka Zayyad ne ya sauke ta a makaranta shi kuma ya wuce, nan suka ƙara jonewa da Nasreen, yau kam sosai Khans ta sake sukayi hira, cikik ƙanƙanin lokaci kuwa sabo mai tsanani ya shiga tsakanin su kasancewar tasu tazo ɗaya, abu ɗaya ke ɓatawa Khans rai da Nasreen shine yawan surutun ta, amma da sauƙi abun tunda bata sakin baki, surutun ta mai ma'ana ne. A haka har suka kammala level 1 suka shiga 2, ba ƙaramin ƙara maida hankali suka yi ba, duk da cewar ƴan matan biyu ba daga nan ba.... Kamar yadda suka tsarawa kansu shiga library bayan kammala lecture ta ƙarshe, yauma hakan ce ta kasance, basa bari wani uziri ya shigo musu a lokacin, a ƙalla kusanyi karatun 40mins kafin ko wacce ta kira azo a ɗauke su. Yauma tafe ƴan matan biyu suke suna labari har suka isa wajen wani cin abinci dake cikin makarantar, sosai Khans ke bin wajen da kallo, dan a iya shekara ɗaya da ƴan ɗoriya data ɗauka a makarantar bata taɓa shiga cafeteria ba. Nan dai suka ci abinci su suka fito, inda suka saba zama nan suka koma yayin da Khans ta kira Zayyad kan yazo ya ɗauke ta, itama Nasreen drivern su ta kira, hirar su suka cigaba dayi har akazo ɗaukar Nasreen ɗin, sallama sukayi sannan sannan ta wuce yayin da Khans ta cigaba da jiran Zayyad. Wayar ta ta fiddo waje ta soma game kwatsam ta jiyo sallama daga tsakiyar kanta. Da sauri ta ɗago dan ganin waye, wani matashi fari mai kyau ke tsaye gaban ta fuskar sa ta ƙawatu da sassanyan murmushi. A hankali ta amsa masa tana tanbayar lafiya? Zama yayi a kujerar dake gefen ta yace "lafiya lau ma kuwa, idan bazaki damu ba zanso ki bani aron lokacin ki domin in zayyane maki abin da ke tafe dani." "Saidai kayi sauri, domin kuwa dap nake da tafiya." "Babu komai na gode, ko zan iya sanin sunan ki?" "Magana kace zakayi koko sanin sunana ne ya kawo ka." "Afwan ranki ya daɗe, da farko ni sunana Zaid Ibrahim , ina ajin ƙarshe a ɓangaren karatun likitanci a wannan jami'a, ni ɗan asalin jihar Kaduna ne, karatu ne ya kawo ni garin Kano, dan Allah kema zanso insan sunan......." "Bai ankara ba ya lura da runtse idanun da tayi, domin tun a lokacin daya ambato sunan shi zuciyar ta tayi wata mugun bugawa. Zayyad da ƙarasowar shi kenan ya hangi Khans dafe da gefen zuciyar ta ya fito da sauri, cikin sassarfa ya ƙaraso gare ta tare da kama ta yana tanbayar Zaid (part 2) abinda ke faruwa. Iya abinda ya sani kawai ya faɗa, shi kanshi Zayyad saida ya ƙara ƙare masa kallo sannan ya jata suka wuce, baya kama da asalin Zayd ɗin Khansa'u ta fuska, amma yanayin sak iri ɗaya hatta da yanayin askin sumar kansu iri ɗaya ce, sai dai masu iya magana sunce *kama da wane bata wane*, Zaid ɗin daya riga ya daɗe da rasuwa. Gidan gaba ya sanya ta tare da sauke mata kujerar, shi kuma ya zagaya ya shiga mazaunin sa, a natse yake nuƙi yana kallon ƴar uwar tasa akai-akai, jin ta soma magana yasa shi tattara dukkan hankalin sa wajen ta "Yaya kace min abin daya faru mafarki ne, ni Zayd ɗina ba haka yake ba, ba kunce ya rasu ba yaya...?" Ta ƙarasa tana fashewa da kuka jin wata irin suka da zuciyar ta tayi, Zayyad dai baice da ita komai ba har suka ƙarasa asibitin nashi, dan dama shi ba ma'abocin magana bane, shi da kanshi ya shigar da ita tare dayi mata allurar da aka tadana na masu irin ciwon idan ya tashi. Ta samu bacci na kusan awa ɗaya da rabi sannan ta farka bakin ta ɗauke da addu'a, bin wajen tayi da kallo sosai sannan ta gano asibiti ne, sai a lokacin abin da ya faru ya dawo mata, bata wani tsaya dogon tunani ba ta miƙe ta shiga toilet, alwala tayi ta fito kana da tada sallah, tana tsaka da sallah ne Zayyad ya shigo, zama yayi a ɗaya daga kujerun room ɗin harya jira ta idar, "muje in maida ki gida." Ya faɗa a taƙaice. Da ido kawai ta bishi tana mai tausayawa ɗiyar da Zayyad ɗin zai auro, dan ba ƙaramin fama za'a sha ba musamman idan bata da haƙuri, ace mutum magana ma wuya take yi masa.... daidai ta gama ɗaukar kayan ta tayi waje, a parking lot ta taddashi da alama ita yake jira, yana ganin ta kam ya buɗe motar, itama zagayawa tayi ta shiga nata mazaunin suka fice..... ___________________________________________✍️🖊️ *BABYLORH*❤‍🔥 (Shalelen Women Writers)🤞 07069929131 [9/26, 8:14 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(Shalelen Women Writers)*🌹 Writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading...... 3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_ 17 & 18... _______Koda suka dawo gida babu wanda suka sanar mawa domin babu wata alama data nuna wani abu ya faru, harkokin ta kawai ta shiga yi shi kuma ya koma asibiti. Toh Khans ta cigaba da zuwa makaranta cikin jin daɗi, kuma sosai take karatu ita da kawar tata wato Nasreen, dan itama ba daga baya ba wajen son karatu. A ɓangare guda kuwa alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su da Zaid, duk sanda ya rigasu fita lecture yakan zo ya jira su su gama su fito, harya gama karatun nasa, lokacin daya labartawa Khans ba ƙaramin baƙin ciki da tashin hankali ta shiga ba, dan ta kasa tantance alaƙar ta da Zaid, sau tari Nasreen kan faɗi mata sun kamu da son juna amma taƙi yarda da hakan, a cewar ta mutunci ne kawai, kuma dan yana da sunan masoyin ta ne. Sai a ranar ƙarshen shi a makaranta ta soma gasgata zuciyar ta kan ta faɗa soyayyar Zaid, yayin da wata zuciyar ke raya mata shaƙuwar da sukayi ce kawai tasa hakan, ita kanta tafi gasgata shaƙuwa ce. Shi kanshi Zaid ji yake kamar karya tafi amma ya zamar masa dole, domin tun last week ya kamata ace ya tafi amma ya kasa, yana son Khans matuƙa, amma jin labarin ta yasa yake fargabar sanar da ita, sabida besan menene zai zama respond dinta ba, kuma bayason hakan ya taɓa alaƙar su da shaƙuwar su, shiyasa bai taɓa gigin sanar da ita ba. Tun bayan komawar Zaid gida kuwa makarantar ta zamo tamkar ƙabari wa Khansa'u, duk da kuwa suna waya akai-akai da Zaid ɗin amma dukkanin su babu wanda ke gamsuwa da wayar, sun ɗauki lokaci mai tsawo kafin suka saba da hakan, zuwa lokacin har Zaid ya soma aiki a babban asibitin da mahaifinsa ya gina masa. ★★★★★ Kamar yadda suka saba gudanar da meeting duk bayan watanni uku tsakanin su, yau ma hakan ce ta kasance, amma abin mamaki a wannan karon harda yaran aka sanya cikin meeting ɗin. Su kansu Ummi da Mummy basu san meye dalilin su Abba nayin hakan ba, amma koma meye zasu ji. Bayan kammala tattaunawa kan abin da ya tarasu ne Abba yayi gyaran murya kana ya soma magana kamar haka "Ehmmm nasan dukkanin ku zakuyi mamakin wannan taro da aka haɗa domin ku, toh wannan ba abin mamaki bane a gare ku, domin kuwa mun zauna nida Daddyn ku munyi nazari sosai sannan mun yanke shawara a kanku, wanda muke fatan hakan ya yazo alkhairi a garemu baki ɗaya. Kada na cika ku da surutu, dalilin tara ku anan ba komai bane face magana akan kai Zayyad da ƴar uwar ka Khansa'u, ina son ku ɗauki furucin dazai fito daga baki na a matsayin ƙaddarar ku sannan zanso kuyi magana biyayya akan hakan," ya ƙarasa yana gyara zama sannan yace "na baiwa Zayyad auren ɗiya ta Khansa'u..." Ba Zayyad kaɗai ba, hatta Khansa'u da tunda Abba ya soma magana kanta ke ƙasa saida gaban ta yayi wani mummunan faɗuwa, Ummi da Mummy kam ƙasa sukayi da kansu, dan tunda wannan furucin ya fito daga bakin Abba tare da goyon bayan Daddy sunsan babu makawa saiya tabbata, saidai wani ikon Allahn. Bakin Khansa'u har karkarwa yake wajen furta "Abba ɗan uwa nane fah!" Gyaɗa mata kai kawai Abba yayi alamar tabbatarwa kuma yana cikin hayyacin sa... Zayyad dakejin sa kamar ya nutse cikin ƙasa ne ya saci kallon Khans a hankali a ranshi yana mai baƙin ciki da wannan hukuncin, bai taɓa kallon Khans a matsayin mata ba a rayuwar sa, baya banbance ta cikin ƙannan sa, bugu da ƙari shi bashi da ra'ayin aure yanzu ma, ko da yana da ra'ayi ma Khansa'u tayi masa ƙarama sosai, bai san me zaiyi da ita ba saidai ya raine ta. Amma alƙawarin ne ya ɗaukar wa kansa, bazai taɓa tozarta Abba ko Daddy da iyalan su ba, zaiyi iya bakin ƙoƙarin sa yayi biyayya ga wannan lamari. A ɓangaren Khansa'u kuwa tunani take anya Abba na cikin hayyacin sa kuwa, yo cikin hayyacin sa mana. Duk mutumin dake cikin hayyacin sa ai bazai haɗa ƴarsa da ɗansa daya haifa da cikin sa aure ba, idan kuwa hakane to hakan yana nufin akwai wani *ɓoyayyen al'amari* da aka ɓoye musu kenan, amma meyasa ba za'a barta ta fidda wanda take so ba, shin idan Zaid yaji wannan labarin me take tunanin zai faru..., Runtse idanun ta tayi tare da girgiza kanta dan tabbatar da abinda ke faruwa a zahiri ne kuwa, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta furta a ɗan bayyane kaɗan..,? maganar da Daddy ya somayi ne ya katse musu tunanin su yayin da yake faɗin "kuyi haƙuri yarana, nasan zakuji abin tamkar almara, kuma zakuyi zaton ko bamu cikin hayyacin mu, toh muna masu tabbatar muku da cikin hankalin mu muke, sannan kada ku sake naji wani abu mara dadi yaje ya dawo," ya ƙarasa tare da rufe taron da addu'a. Tun da suka tashi taro ta koma ɗaki sai faman saƙe-saƙe kawai take a ranta, ta rasa gane me su Abba suke nufi, ko a zamanin jahilai a ina ƙanwa ta taɓa auren wan ta, sosai abin yayi mata wani banbaraƙwai, sammm baza ayi wannan ta'asar da ita ba, bugu da ƙari bazata taɓa iya zama da Zayyad a matsayin miji ba, domin ko a gida ya zaman su ya ƙare balle zaman aure, dan kulawa kam tana samun ƙulawar da duk wata ƙanwa take samu daga wajen ɗan uwan ta, amma matsalar miskilancin shi baza ta iya tanƙwara shi ba, sosai magana ke yiwa zayyad wahala, a lokacin rashin lafiyar ta bayan ta farfaɗo nema taga ya ɗan yi magana, duk da tayi mamaki matuƙa dan bata taɓa tunanin akwai abinda zai sanya yayan nata magana ba...., tana tsaka da wannan tunanin Ayeesh ta shigo tare da sanar da ita Abba na kiran ta. Jiki a sanyaye ta miƙe tana mai fatan Allah yasa su janye maganar su, bata tadda Abba a parlorn sa ba hakan yasa ta shiga ɗakin nasa ɗauke da sallama, "Babban magana," ta furta cikin ranta yayin da taga Abba da Ummi zaune, sai Zayyad dake kan lallausan center carpet ɗin daya haska bedroom ɗin Abba ya sada kansa da ƙasa. Zama itama tayi kusa da Ummi tana opposite ɗin Zayyad ɗin. "Zayyad," Abba ya faɗa cikin muryar da take nuna babu wasa tattare dashi. Cikin sanyi Zayyad ya amsa da "na'am Abba." "Kunsan dalilin da yasa na kira ku?" Dukkanin su girgiza masa kai sukayi alamar a'a. "That's good, Zayyad me zakace game da wannan hukunci?" Ɗagowa yayi a hankali ya saci kallon Khans dake zaune ta tsare shi da idanu tana jiran taji me zaice, "Ahh--amm Abba ni babu abinda zance akai, duk abinda kuka yanke daidai ne Abba." "Ba haka nakeson kace ba Zayyad, kada ka damu da furuci na kona Daddyn ku na ɗazu na da mukace babu abinda zai hana hakan faruwa, ka faɗamin shin ka yarda da auren Khansa'u?" Wata irin bugawa zuciyar sa tayi kafin ya ƙara ɗagowa a karo na biyu ya saci kallon Khansa'u, har lokacin bata ɗauke idanun ta akan sa ba, jiran amsar da zata fito daga bakin sa kawai takeyi. "Na amince Abba." "Innalillahi wa inna ilaihi, ya Zayyad kaima haka zakace, a ina ƙanwa ta taɓa auren yayan ta da suke uwa ɗaya uba ɗaya, meya sanya kuke haka ne wai? Ummi kisa baki mana, wallahi.....! Saurin doshe mata baki Ummi tayi tana auna mata harara kafin tace "meke damunki ne, waye sa'an ki anan da kike mana magana haka? Ki shiga taitayin ki." Nan fa hawaye ya soma zarya a fuskar Khansa'u, kafin wani ya sauka wani ya fito, meke damun su Ummi ne wai, kodai mafarki takeyi ne? Idan mafarki ma nakeyi Allah kasa na farka kafin faruwar wannan lamari, ta faɗa a bayyane. Babu wanda yace da ita ƙala, illa gyara zama da Abba yayi yace "tashi kaje Zayyad, Allah yayi maka albarka." Jiki a mace Zayyad ya miƙe zuciyar sa na masa wani raɗaɗi jin irin kukan da Khansa'u keyi, duk dan an haɗa su aure. "Daughter, Inaso ki natsu ki saurareni, nasan abin zaizo maki wani iri ko? Kada ki damu, with time zaki fahimci komai, kada wata matsala da fito daga ɓangaren ki okay?" Bai jira amsar taba ya fice, sakamakon sallan da ake kira. Baki buɗe tabi bayan Abba da kallo harya fice kafin ta kifa kanta kan cinyar Ummi ta saki wani marayan kuka, "Ummi meyasa kika kasa yiwa Abba magana bayan kinsan abin da yake shirin yi ba daidai bane, ɗan uwa nafa Ummi! A ina aka taɓayin haka, taya zan kalli wanda muka fito ciki ɗaya dashi matsayin abokin rayuwa na dindindin, Ummi akwai sake a cikin al'amarin nan, kada ki bari son zuciya ya kaimu ga aikata abinda zai zamo dana sani a garemu Ummi dan Allah, banason ya Zayyad wallahi, har gobe kallon ɗan uwa nake masa, kwatsam kuma saina wayi gari dashi a matsayin miji? Na roƙe ki Ummi kada ki bar hakan ta faru, idan ba haka kuma saidai akai masa gawa t...." Da sauri Ummi ta toshe mata baki tana mai tausayawa ɗiyar tata, baza taso aurawa ɗaya daga cikin ƴaƴan ta wanda bayaso ba, balle kuma ɗiyar ta mafi soyuwa a gareta kuma mafi rauni cikin ƴaƴan nata, toh amma ya zatayi? Babu yadda za'ayi ta tunkari Abba akan ya janye maganar, domin Abba mutum ne mai kafiya akan abu. Rarrashin ƴar tata ta shiga yi tare dayi mata nasiha kan bin umarnin iyayi da kuma ribar dake tattare da hakan, da ƙyar Khansa'u tayi shiru tana cigaba da kukan zuci ganin daga Ummu har Abba sun kasa fahimtar ta. _Toh fans! Me tunanin ku ya kawo kan wannan hukuncin da Abba ya yanke mana, me zakuce game da hakan._ _Team Zayyad na tayaku murna, amma ya kamata Ku sanar damu hikimar yin hakan, domin auren wanda kuka fito ciki ɗaya haramun ne._ _Team Dr. Zaid ina tayaku jaje kan wannan lamari tare da fatan alkhairi akai._ _________________________________________✍️ Babylorh ce❤‍🔥💞 *(Shalelen Women Writers)*💋 07069929131 [9/29, 9:39 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* The writer of 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 19 & 20.... ________Koda Zayyad ya fita, direct sashin su ya koma tare da shiga ɗakin sa, kan bed kawai ya faɗa ya rasa meke masa daɗi, harga Allah baiso wannan haɗin da Abba yayi ba, amma bazai iya watsawa Abba ƙasa a ido ba, dan irin halacci da adalcin da Abba yayi masa ba kowa ne zai iya shi ba, duk da yasan Khansa'u daidai da minti ɗaya bazata so shi a matsayin miji ba, amma zai jure dukkan wani wulaƙanci daga gare ta, dan alƙawarin zuciyar sa ne baza'a taɓa tozarta ko wulaƙanta ɗaya daga cikin iyalan Abba a gaban sa ba, balle kuma shi ya wulaƙanta su. Ajiyar zuciya ya sauke yana mai ci gaba da tunani, ganin tunanin bazai fusshe shi ba yasa ya miƙe tare da nufar bathroom yayi wanka haɗi da alwala ya fito, sallah yayi gami da addu'o'in nasara da fatan alkhairi akan wannan al'amari dake shirin faruwa. Ya daɗe sosai kan sallaya yana nema masu zaɓin Allah kafin ya miƙe ya kwanta.. Washegari da wani matsanancin ciwon kai da ciki Khansa'u ta tashi wanda yayi sanadiyyar rashin zuwan ta makaranta, har su Haseena da Ayeesh suka wuce makaranta bata fito ba, dama Abba yana rigasu fita hakan yasa bai san da rashin fitowar taba. Sosai Zayyad yaji babu daɗi ganin irin halin da ƴar ƙanwar tashi keson jefa kanta akan shi, yanason faɗa mata gaskiyar shi ɗin ba yayan ta bane na jini amma yana tsoron faɗan Abba, dan Abba yace ko mutuwa tayi sai ankai gawar ta gidan Zayyad sannan za'a kaita makwancin ta. Mahfouz da yaji shurun yayi yawa ne yace "mom wai ina Khans ne?" "Tana ɗakin ta mana, ka ƙyale ta zata fito idan yunwar ta kusa kashe ta." Jikin Mahfouz ne ya basa ba lafiya ba hakan yasa ya miƙe yana faɗin "gaskiya Ummi ba lafiya ba, bari in duba ta." Ya faɗa tare da ficewa daga sashin dinning ɗin. Tun daga corridor yakejin shessheƙar kukan Khansa'u har ya isa ɗakin, knocking ya somayi amma shiru ba'a buɗe ba, ga kuma kukan ta da har yanzu bai dena fita ba. A hankali ya murɗa handle ɗin bakin sa ɗauke da sallama, chan ƙarshen gado ya hango ta tana murƙususu, da sauri ya ƙarasa tare da tallafo ta, wani zafi jikin ta yayi wanda ya ƙara tsorata Mahfouz. Daga ɗakin ya soma kwaɗawa Zayyad kira, Zayyad wanda dama jiran abinda zaisa yaje ya ganta yake ya miƙe a sukune ba tare daya ankara da kallon da Ummi ke masa ba. Ko ƙofar mai iya maidawa ya rufe ba ya nufi inda suke a zaune, da sauri ya amsheta yana faɗin "Mahfouz ɗakko first aid box a ɗaki na kan bedside drawer." Da "toh" ya amsa yana ficewa. Fitar sa ba daɗewa Ummi ta shigo itama tana tanbayar "meke damun ta?" "Ban sani ba Ummi." Bai daɗe ba ya dawo da first aid box ɗin ya miƙa wa Zayyad, jikin sa har ɓari yake wajen amsa, da gaggawa ya soma bata taimako, nan take kam ya gano matsalar, abinci yasa aka kawo mata bayan yayi mata allura. Mahfouz da kansa ya fita ya kawo mata abinci, da ƙyar da rarrashi taci kuma bawai dan batajin yunwa ba, sai dan Zayyad dake wajen. Hakanan taji batason ganin shi, batason ya raɓe ta ko ƙadan, sabida sanadin haɗa auren su ke neman ruguza soyayyar Zaid dake cin ta a rai. Shi kuwa Zayyad yayi hakan ne gudun faruwar matsalar zuciyar ta, a iya binciken da yayi ya gano rabon ta da abinci kusan tun jiya da safe. Wunin ranar dai haka Khansa'u tayi shi babu walwala, ga wutar ƙiyayyar Zayyad dake ruruwa daga chan ƙasan ruhin ta, daidai ta minti ɗaya batason jin koda ƙamshin turaren sa. Ta rasa wa zata faɗawa damuwar ta taji daɗi, Nasreen dake taimaka mata da shawarwari, a wannan gaɓar itama ta rasa me zatayi, dukkanin su babu wanda ya kawo Zayyad ba ɗan gidan bane, a cewar Khansa'u ma wai asiri yayiwa ƴan gidan ya rufe bakin su. Toh a kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, yau kimanin watanni uku da faruwar wannan lamari, abubuwa da yawa sun faru tsakanin watannin nan ciki kuwa harda sa ranar Zayyad da Khansa'u da akayi, watanni biyu masu zuwa. Tun Khans na ɗaukar abin da wasa har zuciyar ta ta fara gasgata su Abba basa cikin hankalin su. Kamar yadda Mahfouz ya saba kaita makaranta ya ɗakko ta, tun bayan da aka sa ranar auren su, yauma tafe suke a hanya babu mai cewa da wani ƙala, wanda ba haka suka saba ba, haka har suka isa gida babu wanda yace da wani ko sannu. Zaune take yau ma a ɗaki kamar yadda ta saba zama ta faɗa duniyar tunani har Haseena ta shigo bata sani ba. Firgigit tayi yayin da taji hannun mutum a jikin ta, ganin Haseena ce yasa ta koma ta kwanta kamar yadda take, cike da tausayawa Haseena tace "Ukhty meya sanya kike ɗaurawa kanki damuwa hakane, meyasa kikeson sanya kanki cikin yanayin da likitoci suka hane ki daki shiga?" "Hmm, bazaki gane ba Haseena, ki ƙaddara kece a akace ki auri ya Zayyad, yaya zakiji? Haseena tayaya Zayyad zai zama mijina, bayan kinsan ciki ɗaya muka fito, ko ku a makaranta ance muku hakan zai iya faruwa?" Ba tare data jira amsar Haseena ba ta ƙara da faɗin "wallahi Haseena na yarda Abba ya zaɓamin koma wanene zan aura, amma ba ya Zayyad ba." Ta ƙarasa maganar da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciyar mai sauraron ta. Sosai ƴar uwar tata ta tausaya mata itama zuciyar ta cike da tunanin abinda su Daddy da Abba suka yanke wanda ba daidai bane a musulunci. Kafaɗar ta ta dafa kana tace "kiyi haƙuri Ukhty, ni a ganina wannan keɓewan da damuwan da kike ɗaurawa kanki bai dace ba, nasan cikin mu babu wanda zai iya tunkaran Abba da wannan maganan, why not ki samu Ummi ko Mummy ki fahimtar dasu rashin dacewar hakan, kinga idan akwai wani abu a ƙasa ma saimu sani." "Haseena basu da niyyar sanar dani komai, kuma ina mai miki rantsuwa da idan ba'a kaiwa ya Zayyad gawa ta ba toh shi sai an bar gidan da gawar sa, saidai In nima a kashe...." "Meye haka kikeyi sis, kinsan me kike faɗa kuwa, ya kike abu kamar wacce bataje makaranta ba? Kamar yadda nace kiyi ki gwada mu gani, idan har shawarar batayi ba then we shall think of other ways. Amma maganan kisa ki cire shi pls, kinsan makomar duk wanda ya kashe rai ba tare da sharuɗɗa uku da musulunci ya yarda dasu ba toh wuta ce makomar sa. Try and ask Ummi, I knw she might tell u okay?" Kai kawai Khansa'u ta gyaɗa tana ayyana irin azabar data tanadarwa Zayyad, muddin bai samu Abba ya ya sanar dashi ya fasa ba.... _______________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/3, 7:55 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* The writer of 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 21 & 22... _________Yammaci ne mai ɗauke da sassanyar iska tana kaɗawa sosai, yayin da hadari ya tattara komai nasa ya tsaya a tsakiya yayi baƙi, wanda ke nuni da ako wani lokaci ruwa kan iya sauka. Zaune take tsakiyar ƙaton royal bed ɗin ta, gefen ta plate ne mai ɗauke da chips da ƙwai sai zoɓo dake hannun ta, gaba ɗaya ta tattara hankalin ta kan film ɗin da ake nunawa a MBC 2 wato (Alice in wonderland), wayar ta data soma ruri ce tasa hankalin barin kallon, sosai gaban ta ya mugun faɗi ganin mai kiran nata, saida ta kusa katsewa sannan ta ɗauka tare da karawa a kunnen ta. _kada ki gasgata min labarin da nakeji baby, dan Allah ki faɗamin ba gaskiya bane ba_. Shine abinda aka faɗi daga ɗaya ɓangaren, da ƙyar ta danne kukan dakeson taho mata tace "dear bamu gaisa bafa." Bata kai ga rufe baki ba ya ƙara da cewa " _wani irin gaisuwa kikeson muyi, bayan kinsan yadda na daɗe ina nuna miki ƙauna, ke shaida ce nakan sadaukar da farin ciki na duk dan ke ki samu naki farin cikin, na nuna miki so iya so, abu ɗaya ya hana ban furta miki ba, gudun kar a samu matsala, gudun kada furta miki ya zamo silar rushewar alaƙar mu, ashe duk abin da nakeyi baki taɓa gani ba kuma baki taɓa lura ba? Yanzu ya tabbata aure zakiyi da gaske kenan?"_ Hawayen da tayi ta ƙoƙarin riƙewa ne ya gangaro kana tasa hannu ta share tace "ka yarda dani Zaid, wlh ban taɓa tunanin cutar dakai ko yaudarar kaba, amma kasan ba laifi na bane, meyasa baka furta min kalmar so ba har saida bakin alƙalami ya bushe? ka sani a bari ya huce shike kawo rabon wani, meyasa ka riƙe abin a ranka har saida Abba ya yanke wannan hukuncin, meyasa ka zaɓi wahalar da zuciyar ka akai na, wallahi ban taɓa gasgata abinda Nasreen ke faɗa min game da alaƙar mu ba sai da aka haɗa aure na da ya Zayyad...." Kukan da yaci ƙarfin tane ya hana ta cigaba da magana. A ɓangaren Zaid kuwa shima hawayen yake fitarwa, chan cikin zuciyar sa na masa suka yana jin raɗaɗin zafin rabuwar da zaiyi da Khans, haƙuri ya soma bata har kukan ya sassauta sannan ya ƙara da faɗin _"na fahimce ki dear, sannan irin tamu ƙaddarar kenan, Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi yayi mana jagora_". Yadda kawai yayi maganar tasan zuciyar sa nayi masa zafi da ɗaci kan maganar, cikin kuka take masa magana kamar haka "kayi haƙuri Zaid, kada ka ɗauka hakan a matsayin yaudara wallahi ko kaɗan bani da niyyar yaudarar wani a rayuwa balle kuma kai, zan aura ya Zayyad ne kawai sabida biyayya badan ina sonshi ba, zan aura ya Zayyad ko dan nasa farin ciki a cikin zuƙatan iyaye na, duk da nasa akwai *ɓoyayyen sirrin* da suke ɓoye wa, nasan babu yadda za'ayi in aura ɗan uwa na, sannan zan aure shi da zuciya ɗaya, saidai bansan ko ƙiyayyar da nake masa zata hanani cutar dashi ba, wlh yadda nakejin tsanar shi a raina bazan iya misalta shi da komai ba. Zaid idan harni rabon kace ina mai tabbatar maka dako sama da ƙasa zata haɗe saina zama mallakin ka, idan kuma harni ba rabon ka bace ina mai maka fatan alkhairi da samun mace ta gari mai ilimi da addini da tarbiyya." tana gama faɗi ta katse wayar tare da kifewa tana wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya da ban tausayi. Haƙiƙa duk wanda yasan Khansa'u a baya ya ganta a yanzu saiya tausaya mata, dukkan rayuwar ta ta sauya tun bayan rasuwar Zayd ɗinta, bacin ramar da tayi ga uban tunani data sanyawa ran ta tamkar a kanta aka fara irin wannan auren. Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi, gefe guda shaƙuwa mai tsanani ta ƙara shiga tsakanin familyn biyu, saidai har yanzu babu wani sauyi a wajen Zayyad da Khans, sosai take iya bakin ƙoƙarin ta ta cusa soyayyar Zayyad cikin zuciyar ta amma abin yaci tura, musamman idan ta tuna da shi ɗin aboki ne kuma ɗan uwa ga Zayd ɗin ta. Kullum takan roƙi Allah ya cire mata duk wani aniya mara kyau data ƙudura kan Zayyad bayan auren su, takan roƙi Allah ya bata ikon zama ƙarƙashin sa tare da biyayya kodan samun lada wajen mahaliccin ta da kuma wanzuwar farin cikin iyayen ta. A haka kwanaki suka yita shuɗewa suna zama tarihi, yayin da kwanaki auren su Zayyad keta matsowa. Ana saura sati uku Mummy tazo da kanta ta ɗauka Khans zuwa gidan ta, nan Khansa'u ta fara shan gyara kala-kala wanda ta sani dama wanda ya zama baƙo a gareta, gefe guda ma Anty Jumayna na aiko mata dasu sosai, wani lokaci ma da kanta take zuwa ita da babyn ta *Ayaan*. Sosai ta sauya cikin sati biyu kacal ta koma wata kyakkyawar balarabiya, dama gata ba daga baya ba wajen kyau ga hanci tamkar alƙalami, ga cika data ƙarayi kai abin sai san barka. A ɓangaren ango Zayyad ma ba'a barsa a baya wajen shirye-shirye ba, Abba ba sosai suka zage damtse wajen ginawa yaran nasu tangamemen gida, dan sun lura Zayyad bayi zaiyi ba, dan yadda yake abubuwa tamkar mace mara jini a jika. Washegari ya kama laraba, tun safe Nasreen ke gidan su Ameesha wajen Khansa'u, kasancewar sunyi hutun ƙarshen semester abin yayi daidai da bikin, sosai Nasreen ke mata tsiya ita kuma ta cika tayi fammm in ranta yayi dubu kuma ya ɓaci, amma hakan baisa ta daina mata tsiya ba, babu yadda Khansa'u ta iya hakan yasa ta daina damuwa ma, dan idan da sabo ta saba da halin Nasreen. Sosai suma suke shirye-shirye duk da rabi da kwatan komai Nasreen keyi saidai Khans ta bita da ido, tun Nasreen na basarwa harta gagara saida ta yiwa Khans magana ta hanyar faɗin "wai ke me kike nufi ne? Kin barni ni kaɗai ina ta shiri sai kace bikina.." Dogon tsaki Khans taja kana tace "idan kin gaji ki ajiye mana, aiba dole bane ko!" Dariya Nasreen ta kwashe dashi wanda ya ƙular da Khans kafin tace "haba uwargida a gidan yayan mu Zayyad, me kuma yayi zafi? Maida wuƙar, ai bance miki na gaji ba, ko ni irin kice." Throw pillow ɗin dake hannun Khans ta jefa mata yayin da Nasreen ta kauce tana sakin dariya. Khansa'u kam ranta yakai ƙololuwa wajen ɓaci, ji take kamar ta tashi ta rufe Nasreen ɗin da duka, hannu tasa ta share hawayen baƙin cikin da Nasreen ke ƙunsa mata. Nasreen kam bayan ta gama dariya ta gyara zama tana faɗin "duk wannan abin da kikeyi na ɗan lokaci ne, da kanki zaki zo ki cemin duk duniya babu wanda kikeso sama da Zayyad, kaiii amma zanso inga wannan ranar, ni kam saina tuna miki da abubuwan da kike faɗi kafin auren ku." Nan fa Khans ta taso ta nufo Nasreen, ita kuwa ganin haka yasa ta miƙe tayi hanyar barin parlon, kiciɓis sukayi da Mummy na ƙoƙarin shigowa, nan kuwa Nasreen tayi bayan ta ta ɓoye tana ta ƙyaƙyata dariyar ta. Ah ah! Ku tsayamin, meke faruwa ne, meye haka kukeyi kamar ƙananan yara? "Mummy tun ɗazu yarinyar nan ke tsokana ta, na ƙyale ta na ƙyale ta amma taƙi bari," Khansa'u ta faɗa tana sakin kuka haɗi dana shagwaɓa. Kai kai kaii! Kinga fa Nasreen ki dena taɓamin shalele na, inba haka ba kuwa zamu sa ƙafar wando ɗaya. Nasreen dake bayan Mummy ne tace "Mummy nifa ba wani abu nayi ba, kawai daga nace uwargida a gidan Zayyad, shikenan ta fara dukana da pillow wai akan me zance mata uwargida, wacece amaryar?" Waro idanu Khansa'u tayi kana tace "kiji tsoron Allah Nasreen, wlh Mummy ni ba haka nace mata ba." "Na san baki faɗa ba, taho muje kisha maganin ki," Mummy ta faɗa tanajan hannun Khans zuwa kitchen yayin da Nasreen tabi Khansa'u da gwalo. __________________________________________ Kuyi haƙuri kun jini shiru kwana biyu, hakan yana da nasaba da abubuwa da suka dan yimin yawa. ________________________________________✍️ BABYLORH💓💖 (shalelen women writers) 07069929131 [10/8, 10:20 AM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ _*WOMEN WRITERS ASSO...*_📚 By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* The writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading...... 3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_ 23 & 24... ________Shirye-shirye daga ɓangaren biyu ba kama hannun yaro, ɓangaren Abba da Ummi sosai suka miƙe tsaye akan Zayyad wajen ganin yayi dukkan abinda ya kamata, kuma Alhamdulillah, abin sai san barka. Haka zalika ɓangaren Mummy, sosai takejin daɗin sauƙin kai da kara irin na Mummy, duk da dama chan basu nuna bambanci tsakanin su balle kuma yaran su, Khans ta samu dukkan abin da take buƙata wajen Mummy abin sai godiya. *5 DAYS LATER* Duk da an kammala shirye-shirye sai dai abinda ba'a rasa ba, hakan baisa sun daina hidimomi ba, yayin da a ɓangaren Khansa'u ganin abin take tamkar a mafarki, tayi kukan har saida hawaye ya koma yana fita da ƙyar a idanun ta, ba komai take tunani ba illa zaman da zasuyi da yayan ta Zayyad, gashi duk wanda ta tanbaya tsakanin su Mummy sai suƙi faɗa mata matsayin Zayyad a gidan, haka ta cigaba da tunane-tunanen ta, tabi tachan ta ɓille ta chan. Toh Zayyad ɗin ma kusan hakan take a wajen, ko ince kishiyar hakan, fargabar sa guda, shine yadda Khansa'u zata kalle sa a matsayin miji, domin ko ƙwayar idanun ta ya kalla babu abinda yake gani sai tsantsar ƙiyayyar sa a gare ta, ƙarara take nuni rashin so a garesa wanda bai taɓa tunanin hakan daga gareta ba. A da ko wuni Khans tayi bata ganshi ba saita tanbaya saidai In yana hospital, wani lokaci har driver take sawa ya kaita wajen yayan nata, irin kulawar da Zayyad yake bata matsayin ƙanwa, da irin wanda take bashi a matsayin ɗan uwan ta, bai taɓa tunanin dan an haɗasu aure zasu rushe ba, harga Allah bazai ce baya son Khans ba, domin ta haɗa duk abinda namiji ke fatan samu wajen mace, toh amma akace son maso wani wahala ne, baya taɓa tunanin ko nan kusa Khansa'u zata ƙauna ceshi, amma ya ɗauki alwashin dukkan abinda zatayi masa zai ɗauka insha Allah, da waɗannan tunane-tunanen dai kawai yake yawo yayin da in ya tuna da Allah kuma sai yayi godiya ya nema musu zaman lafiya da fatan albarka wa auren su... *RANA BATA ƘARYA* _(sedai uwar ɗiya taji kunya)_. A yau Juma'a da misalin ƙarfe 1:30 na rana, (wato bayan sallahr juma'a) dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren *ZAYYAD MUHAMMAD* da ƴar uwar sa *KHANSA'U MUHAMMAD SHEHU* kan sadaki naira dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba. Nan fa aka soma yiwa Zayyad fatan alkhairi, gefe guda kuwa Zaid ne tsaye shima ya halarci ɗaurin auren, inda yakejin zuciyar sa tamkar ta tarwatse (nikam nace Allah ya baka haƙurin rashi Zaid). ★★★ "Haba Khans, meyasa kike haka ne wai, ya kikeso muyi? Kinsan dai idan Mummy tazo ta ganki haka baza taji daɗi ba, dan Allah ki tashi kiyi wanka ki shirya, mu kaɗai ake jira, koma menene sai muyi magana daga baya, amma yanzu ba lokacin magana bane, ɗazu ma dana fita Mummy ta tanbaye ni ke nace mata kina wanka, yanzu so kike ta shigo taga akasin haka? Dan Allah ki tashi." Nasreen dake zaune ta faɗa cikin ƙaguwa. Kallon ta kawai Khans tayi kana tayi murmushi wanda yafi kuka ƙuna tace "consider yourself as me Nasreen, na tabbata kema hakan zakiyi ko fiye da hakan." "I can feel your pain dear, bt this is not the right time to talk about this, ki fahimceni jiran mu akeyi, wallahi nasan bakyajin daɗi, kuma Allah yana tare dake, tashi dan Allah." Babu yadda Khans ta iya hakanan ta miƙe ta shiga bathroom tana sharar hawaye mai tsananin ƙuna da zafi, ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta fito, da taimakon Nasreen ta soma shiryawa kana ta fito mata da kayan da zata saka, ita kuma ta fita kiran mai kwalliya. Khansa'u ta daɗe a tsaye tana kallon kayan kafin tayi jahadin sanyawa, tana gama sawa daidai su Nasreen sun shigo tare da mai kwalliyar. "Wow!" Kawai Nasreen ta furta daga bisani tace "kinga yadda kika fito kuwa? Sak amarya." Harara Khans ta watsa mata tana miƙewa, wayar ta ta ɗakko tana son kiran Haseena, amma me? Message ta gani kan screen ɗin wayar ya shigo awa 2 da suka wuce. Ganin daga inda saƙon ya shigo ne yasa ta saurin buɗewa, saƙo ne kamar haka _"Assalamu alaiki ƴar uwa! Ina mai matuƙar tayaki farin cikin kasancewar yau a ranar auren ki, ina miki fatan alkhairi tare da fatan Ubangijin talikai ya baku zaman lafiya. Happy married life in addy.! Saƙo daga Zaid.."_ Kuka ne ya taho mata da ƙarfi wanda ta kasa danne shi har saida ya samu nasarar zubowa, duk yadda kakai ga rashin imani ka kalli Khansa'u a wannan lokacin saika tausaya mata, jin ƙafafun ta ta neman yaada ta yasa ta durƙushe kan gwiwoyin ta, da sauri Nasreen dake fitowa daga toilet ta matso tare da kama ta tana tanbayar ta ko lafiya? Sosai Khans ta bawa Nasreen tsoro dan bata taɓa irin wannan kukan ba, nan itama ta soma taya ta, ganin Khans bata da niyyar tsayawa yasa Nasreen karɓar wayar dake hannun ta, saida ta karance shi tsaff, kafin wani siririn hawaye mai ɗumi na tausayin Zaid ya zubo mata, yayin da gefe guda bataji daɗin shigowar saƙon ba, dan sunsha wuya kafin su shawo kanta tabar kuka, ga kuma wani kukan ya kunnu. Ameesha da shigowar ta kenan taga suna kuka yasa ta fice cikin sanɗa ba tare da kowa ya ganta ba, babu jimawa ta dawo ita da anty Jumayna, faɗa ta soma yi musu kan su kaɗai ake jira amma sun tsaya suna kukan shashancin banza da wofi, da kanta ta ɗago Khansa'u ta zaunar da ita bisa stool kana tayiwa mai kwalliyar alama da ta soma aikin ta. Ba tare data damu da wata shegiyar kwalliya ba ta cigaba da hawayen ta, da ƙyar mai kwalliyar ta shawo kanta aka soma, cikin ikon Allah kuwa har aka gama bata ƙara yin wani hawayen ba, Nasreen da Ameesha suma saida akayi musu sannan duk suka miƙe suka fita, amaryar na tsakiyan su kanta ƙasa. Ba laifi tayi ƙoƙari wajen danne kukan ta har yamma, lokacin an soma hada-hadar yin sallar maghriba, wani sabon wanka ta kuma yi, anty Jumayna ta feshe ta da turaruka masu sanyin ƙamshi wanda saika matso kusa da ita sosai zakaji, gefe anty Jumayna ta ɗan matsa tana ƙarewa Khans kallo a zuciyar ta tana faɗin "da yanzu da Zayd za'a ɗaura.., Allah yaji ƙanka da rahma." Da mamaki Khans ta kalle ta kafin tace "anty wa kenan?" Ita kuwa anty Jumayna bata ma san abinda ta faɗa ya fito fili ba, nan ta wayince tare da cewa "babu komai, wancan farar rigar zaki saka kafin na dawo." Tana gama faɗi tayi waje abinta, tabar Khansa'u baki buɗe. Bayan sallahr Isha'i aka soma shirin kai amarya gidan ta, manyan motoci ne na alfarma Zayyad ya aiko dasu, a gurguje aka ɗauka amarya da babbar ƙawar ta Nasreen, sai dangi da abokan arziki. Alhamdulillah, gidan amarya yayi kyau matuƙa gaya, ba ƙaramin kuɗi aka kashewa gidan ba, saidai muce Allah yasa rai akayi mawa. .....ƴan kai amarya basu wani jima ba duk aka watse, sai su anty Jumayna da Ameesha da kuma ƙannen Khans wato Haseena da Ayeesh sai Nasreen, wani wankan anty Jumayna ta ƙara sanya Khansa'u tayi, a wannan karon wani fitinannen turare mai matuƙar ƙamshi ta sanya mata a cikin ruwan wankan, nan dai tayi wanda ta fito suka bata waje ta shirya cikin grey Abaya da mayafin ta, sosai kuwa tayi kyau matuƙa, tsokana kam tasha shi wajen Nasreen harda na Allah ya isa, da haka sukayi mata sallama tana ta faman kuka wiwi da hawaye, Nasreen kam me zatayi inba dariya ba, har cikin ta ya kusa ƙullewa, da haka sukayi mata sallama suka kama gaban su. Suna tafiya kam ta tashi ta cire rigar tasa doguwar rigar bacci mai kauri da kwanta.... ________________________________________✍️ Daga alƙalamin 💍BABYLORH💍 (shalelen women writers) [10/9, 7:48 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* The writer of 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 25 & 26... _______Ba jimawa da tafiyar su anty Jumayna Zayyad da abokan sa suka shigo gidan, sun ɗauki ƴan mintina kafin suka bar ango tare dayi masa saida safe. Zayyad ya daɗe ƙofar ɗakin Khans yana tunanin shiga, fargabar sa ɗaya abinda zai shiga ya tarar, ya sani sarai bakin daya furta tsana toh tabbas zai aikata koma meye. Ya kai kimanin mintina 10 sannan ya shiga bakin sa ɗauke da sallama ciki-ciki, dan ba kowa ne zaiji ba. Kwance ya same ta akan gado tana sharar bacci, a hankali ya taka ya isa gare ta tare da tsura mata idanu, a hankali take fidda numfashi haɗi da ajiyar zuciya akai-akai. Ya daɗe tsaye kafin ya zauna bakin gadon ya ɗora ledar hannun sa kan side drawer, hannun ta ɗaya ya kama ya kira sunan ta a hankali. Kamar a mafarki taji ana kiran ta da kuma muryar wanda bata ko mararin jin muryar sa balle ganin sa, a hankali ta buɗe idanun ta daga baccin daya ɗan sace ta, lokaci guda ta wani murtuke fuska tamkar wadda batasan meye dariya ba, da sauri ta fuzge hannun ta daga nasa tana mai matsawa kana ta tashi zaune, murmushi yayi dan yasan dole za'a rina, a hankali ya ɗago ya kalle kana yace "abinci na kawo miki, kada ki kwanta da yunwa." "Bana buƙata," ta furta tana mai kau da kanta gefe. Ƙara gyara zaman gilashin idanun sa yayi kafin ya ƙara cewa "kiyi haƙuri Khans, banaso in zama marar adalci a gareki, cin ki da shan ki yana wuya na yanzu, idan har bakici ba hakan na nufin rashin kulawa ta a gareki kenan, ki daure kici dan Allah badan ni ba." "Ha'a! nace maka bana buƙata ko? Banjin yunwa ne idan da inaji ai zanci," ta ƙarasa tare da juya masa baya taja bargon ta. Badan yaso ba Zayyad ya miƙe cikin sanyin gwiwa ta kama hanyar fita, har ya kama handle ɗin ƙofar, sai kuma ya jiyo ya kalle ta na ɗan wasu daƙiƙu, kafin yasa kai ya fice. Bai tsaya ko ina ba sai ɗakin sa, zuciyar sa cunkushe ya rasa me zaiyi yaji daɗi, wanka ya shiga yayi ya dawo ya sanya singlet da three-quarter, saida yayi Sallah kamar yadda ya saba a ko wani dare kafin ya kwanta, sosai ya daɗe kan sallaya yana kwarara musu addu'a kafin ya koma kan bed ɗinsa ya kwanta, ya daɗe kafin bacci ɓarawo ya ɗauke sa. Kiran sallahr asuba ne ya tashe sa daga baccin daya dauke sa, cikin sanyin jiki ya miƙe ya nufi bathroom, wanka yayi haɗi da alwala sannan ya fito ya sanya dark-ash jallabiyya ya fito, jin ana ƙoƙarin tada iqama yasa bai tsaya tashin Khans ba saiya dawo. Ana idar da sallah ya dawo, dan baiso lokacin sallah ya wuce matar tasa, koda ya shigo direct ɗakin ta ya nufa, saidai bata kan gado, motsin daya jiyo a bayi ne ya tabbatar masa da tashin ta, ya juya zai fita kenan ya hangi ledar daya shigo da ita jiya, ajiyar zuciya ya sauke yana mai mamakin abinda ya hana ta ci, ko tana tunanin ya sanya wani abu ne? Toh amma me zaisa ya sanya mata abu aciki bayan ita ɗin matar sa ce ta Sunnah.... Fitowar ta ce ta katse masa tunanin sa, dressing mirror ta nufa direct ba tare data lura da mutum a ɗakin ba, sosai ya ƙurawa jikin ta kallo yana mai jin wani tsananin ƙaunar ta na shigar sa. A hankali take tsane ruwan jikin ta kafin ta ɗauki mai ta soma shafawa harta gama, perfumes ɗin da anty Jumayna ta bata ta ɗauka ta soma feshe ilahirin jikin ta dashi, duk abin da takeyi a idanun Zayyad, bai koyi ƙwaƙƙwaran motsin da zata san yana ɗakin ba. Juyowar da tayi ne ta lura dashi, wani uban ihu ta fasa tana kare jikin ta, ihu kawai take zabgawa tamkar wadda taga dodo, da sauri Zayyad ya ƙarasa inda take ya zagaye ta da hannayen sa yana furta "maintain dear! Ni me." Sai a lokacin ta bar ihun tana ɗagowa tare da ƙare masa kallo kafin kuma ta haɗe rai, harga Allah ba ƙaramin tsoro taji ba, dan batayi tsammanin ganin mutum ba ko kaɗan, a hankali ta janye jikin ta daga hannun sa ta nufi wardrobe tana furta "meya kawo ka ɗaki na, inace kowa da nasa ɗakin?" "Well, nazo tashin ki kiyi sallah ne." "Toh nayi, shikenan?" "Amm...aaa abincin dana kawo maki jiya naga bakici ba, meyasa." Yana ambaton abinci taji cikin ta yayi wani irin ruri, dan rabon ta da abinci tun jiya da rana, sedai batason yasan tanajin yunwa hakan yasa ta dake tare da faɗin "dan ka siyomin abinci banci ba shine kake tuhuma ta?" Ba tare data jira cewar sa ba ta nufi inda ledar take ta ɗauka, ƙamshin kazar daya bugi hancin tama saida ya ƙara mata yunwar, amma sabida taurin kai irin na Khans ta gwammaci ta zauna da yunwa. Har gaban sa ta iso da ledar a hannun ta, ta kamo hannun sa ta zura masa ledar tace "ga shinan," tana gama faɗi ta tafi ta barsa tsaye tamkar wanda aka dasa, ta shige dressing room. Zayyad, tunda ta riƙe hannun sa yaji jikin sa ya ɗauki wani baƙon yanayi dako zai mutu Khansa'u baza ta taɓa bashi kanta ba, tunda ya rungume ta a jikin sa yayin da take ihun nan ya somajin sha'awar ta na taso masa, yayi ta ƙoƙarin dannewa amma yana neman kasa wa, baya son ya ƙuntata mata daidai da ƙwayar zarra, hakan yasa bazai iya ƙwatar haƙƙin sa ta halin ƙarfi ba, dan yasan ma wahala kawai zai sha, amma with time insha Allah zata bashi da kanta, saidai baisan ko kafin lokacin ya illatu ba. Daga haka ya fice daga ɗakin, ficewar sa kuwa yayi daidai da fitowar Khans daga dressing room, wata harara ta zabga masa tana raka bayan sa da tsaki. Shi ko gogan ɗakin sa ya nufa ya faɗa kan gado yana jizar leɓe tare da runtse idanu, lokaci guda kuma ya soma zufa numfashin sa na fita da ƙarfi, ya daɗe a haka kafin yanayin nasa ya soma raguwa, har yazo ya tafi, sai abinda da ba'a rasa ba, a hankali ya miƙe ya shiga toilet ya sakar wa kansa ruwa mai zafi sosai, ya daɗe kafin ya fito, cikin wata dakakkiyar shadda ƙirar getzner sky blue color ya shirya, da baƙin takalmi sau ciki haɗi da hula zanna bukar, sosai yayi wa kayan kyau kamar dashi akayi, sai zuba ƙamshi yakeyi tamkar angon gaske, wayoyin sa ya kwasa tare da car key ya fito, ɗakin ta ya nufa tare da kama handle ɗin ya murɗa, amma yaji ƙofar a kulle, mamaki ne ya kama sa na dalilin rufe ƙofar nata, a hankali ya soma knocking, amma taƙi buɗewa, ga shessheƙar kukan ta da yake jiyowa, sosai yake tausayin ta, baiyi ƙasa a gwiwa ba ya cigaba da knocking yana kiran sunan ta amma taƙi buɗewa, ga kukan ta da har yanzu bai dena fita ba. Dabarar data faɗo masa ne yasa shi fita waje, saida ya zuba wayoyin sa a mota sannan ya zagaya ta bayan gidan, cikin sa'a kam ya tadda window ɗin ta a buɗe, da ƙyar ya iya rarrashin ta ta buɗe masa ƙofar ya zagayo, tanbayar ta ya somayi me aka mata amma babu amsa, tanbayar duniyar nan yayi mata amma taƙi basa amsa, ya rasa ya zaiyi da ita, ita bata bar kukan ba sannan bata amsa ɗaya cikin tambayoyin da yake mata ba. Ganin lokaci na tafiya yasa shi gyara zaman sa yana fuskantar ta, "Bie~bie dan Allah ki daina kukan nan banaso, ki sanar dani abin da yake damun ki zan taimaka miki insha Allah, dan Allah badan ni ba." Share hawayen ta tayi ta gyara zama itama kana tace "dama ficewar ka kayi, da yafi, faɗa maka damuwa ta bashi da wani anfani dan ba magance min shi zakayi ba." Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "me zakici in kawo miki?" "Banason komai, ka barni da yunwa ta inma kashe ni zatayi ta kashe ni, tunda baka da asara." Bayajin daɗin kalaman dake fitowa daga bakin ta, yadda take masa magana tamkar ƙanin ta ko sa'an ta na mugun ci masa rai, amma bazai taɓa karya alƙawarin daya ɗauka ba koda hakan zaiyi sanadiyyar shafewar tarihin sa a doron ƙasa. Ba tare da yace da ita ƙala ba ya miƙe ya fita, sai bayan kusan 45mins sannan ya dawo hannun sa ɗauke da leda guda biyu, ajiye mata su yayi akan ɗan ƙaramin table ɗin dake ɗakin ya fita, kasancewar jiran shi akeyi zasu sallami baƙin da suka hallara wajen auren nashi... Tana daga bayi ta jiyo shigowar Zayyad wanda bai daɗe ba ya fice, sai kuma taji yayiwa motar sa key ya fita. Koda ta fito gaba ɗaya ɗakin ta gauraye da wani daddaɗan ƙamshi na abinci, nan take cikin ta yayi wani irin ruri, babu shiri ta nufi inda ledar take ta buɗe. Takeaway biyu ne a jiki, gaba ɗaya ta fito dasu tare da buɗewa, fried rice ne a takeaway ɗaya, sai ɗayan kuma papper chicken, ɗaya ledar kuwa yoghurt ne guda biyu sai ice cream roba biyu shima. Abincin ta soma kaiwa hari, kona bakin ta bata cinyewa take ƙara danna wani, sai da ta cinye shi tasss tayi nak abin ta ta ƙara korawa da milk sannan ta miƙe. Dressing room ta shiga ta soma duba kayan da zata saka, karap idanun ta suka sauka kan wata navy blue ɗin atampa Holland mai matuƙar kyau ɗinkin riga da skirt, sosai kayan sukayi mata matuƙar kyau musamman yanda aka ƙawata ɗinkin da stones masu matuƙar ƙyalli, bata wani tsaya kwalliya ba ta kashe ɗaurin ta ta shafa lip gloss ta fito. Saida ta gyara ɗakin tsaff sannan ta kwasa kayan data gama cin abinci ta fito dasu, dustbin dakai takeaway ɗin, sauran yoghurt da ice cream ɗin kuma ta sanya su a freezer ta dawo parlor. Zama tayi bisa kyawawan kujerun da suka ƙawata parlon nata bayan ta kunna TV, nan ta hau kallon ta hankali kwance..... __________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* _(shalelen women writers)_ 07069929131 [10/11, 1:05 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ _*WOMEN WRITERS ASSO.....*_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* The writer of 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 27 & 28.... _________Zayyad bai dawo gidan ba sai kusan ƙarfe 12:30 na rana, kasancewar abubuwa da suka sha kansa game da hidimomin bikin da kuma abokan sa. Saida ya biya ya amso musu takeaway sannan ya shigo gida, kwance ya sameta kan kujera tana bacci, kamar zai tashe ta sai kuma ya soma tunanin abin da zai biyo baya, ganin lokacin sallah yayi yasa ya soma bubbuga hannun kujerar da kanta ke kwance haɗi da kiran sunan ta, firgigit tayi ta farka, karap idanun ta suka sauka kan na Zayyad da yayi mata rumfa, ko wannen su samun kanshi yayi da kasa ɗauke idon sa akan ɗan uwan sa, har kusan minti ɗaya kafin Zayyad ya dawo hayyacin sa, nan ya soma kame-kame yana sosa ƙeya, Khans kam tsintar kanta tayi da jin haushin kanta data tsaya tana kallon sa, ji tayi kamar ta rufe Zayyad ɗin da duka dan haushi amma ba dama. Ba tare da tace dashi ƙala ba tayi wucewar ta ɗaki, sororo Zayyad ya tsaya ya bita da ido, yana mamakin wannan mugun halin da Khans ta samo, duk ta inda yabi wajen shawo kanta saita zille. Kitchen ya nufa da kayan hannun sa ya ajiye sannan ya fito, shima nasa ɗakin ya shiga, yayi wanka ya shirya cikin navy blue T-shirt wadda aka rubuta sunan sa a baya da manƴan baƙaƙe kamar haka (DR. ZAYYAD), farin three-quarter ya sanya kana ya nufi masjid, dan zuwa lokacin har an soma kiraye-kirayen Sallahr azahar. A ɓangaren Khansa'u itama tana shiga ɗaki toilet ta nufa, wanka tayi haɗi da alwala sannan ta fito ta shirya cikin white Dubai Abaya mai matuƙar kyau da sheƙi, sallah tayi itama kana ta koma gaban mirror, gashin kanta ta soma gyarawa harta gama ta naɗa mayafin abayar. Wayar ta ta soma nema tayi game amma bata ganta ba, sai a lokacin ta tuna da ta baro ta a parlor, nan ta fito ta ɗauka juyawar ta yayi daidai da shigowar sa ɗauke da sallama, ciki-ciki ta amsa tayi ciki abinta ta faɗa gado ta soma buga game. Murmushi kawai Zayyad yayi ya shiga kitchen, gaba ɗaya takeaway ɗin ya juye masu a plate ɗaya ya haɗo masu da yoghurt da ruwa ya nufi ɗakin nata, (hmm nikam nace su ya Zayyad ko yaushe ka samu fuskar cin abinci tare da ita oho). Koda ya shiga game ɗin ta take hankali kwance dan bata ma ji shigowar sa ba, sosai kuwa abin ya taɓa zuciyar Zayyad amma ya basar, dan a tunanin sa taji sallamar sa amma taƙi amsawa. Kan centre carpet a ajiye tray ɗin a abincin kafin yayi mata magana, a wannan karon batayi gigin maimaita abinda tayi na ƙin cin abinci ba, amma fa taƙi yarda suci, juyin duniyar nan tace baza taci abinci dashi ba, kuma baza taci ragowar sa ba, sedai in ya yarda ita taci ta rage masa. Zayyad dai baice komai ba ya tura mata tray ɗin gaban ta yaja gefe, dan yanzu al'amarin ta ya dena bashi mamaki, ba kunya ba tsoron Allah kam taja abinci ta soma ci, saida taci mai isarta sannan ta sha ruwa ta miƙa masa. Da yake shi ɗin ba baƙon zafi bane yasa hannu ya amsa ya soma ci, saida ya cinye tasss tana kallon sa tana wani yatsine fuska harya gama shima ya kora da ragowar nata ruwan. Haushi sosai ya bata amma bata nuna ba, da kansa ya kwashe abubuwan da suka ci abincin ya fita dasu. Toh haka zaman su ya cigaba da wakana na yau daban na gobe daban, amma abin godiyar shine Khans bata taɓa yunƙurin cutar da Zayyad ba, shima kuma yaji daɗin haka, hakan yasa ya ƙara zage damtse wajen shanye dukkan wani rashin mutunci da wulaƙanci nata. A haka har suka ɗauki kusan sati biyu, babu wanda yazo mata daga ita, sannan Abba ya hanata zuwa yace saiya nemeta. Harta ga ƙawar ta Nasreen kuwa, kiran duniya ta mata amma taƙi zuwa, sau tari takan zauna taci kukan iya kuka har ta godewa Allah, Zayyad kam Allah ya isa babu irin wanda bai sha ba, dan a cewar ta shine silar faruwar komai. Toh! Yau ma zaune take riƙe da wayar ta a hannu tana kiran Nasreen a karo na sau ba adadi, saida ta kusa katsewa sannan Nasreen ta ɗauka da muryar bacci, nan fa Khans ta fashe da kuka tana faɗin "haba Nasreen, yanzu kema kin biyewa tsarin su Abba, sau nawa kike ganin kirana a wayar ki amma baki biyo baya? Baku san halin da nake ciki ba amma babu wanda yayi gigin zuwa duba ni, yanzu in ma mutuwa nayi saina ruɓe sannan zaku sani?" Da ƙyar Nasreen ta iya danne dariyar dake cin ta tace _"oh oh! Sorry Mrs Zayyad, yau nake shirin zuwa gidan ki wlh."_ "Nasreen dan Allah da gaske? Bana son wasa pls" "Tsaki Nasreen ɗin tayi kana tace _"ni sa'ar wasan kice?"_ Murmushi kawai Khans tayi tace "dan Allah kada ki shanya ni, ina jiran ki sai kinzo." Daga haka suka katse wayar, nan Khansa'u ta tashi ta shiga kitchen, jollof ɗin taliya da busasshen kifi ta ɗaurawa Nasreen ɗin, dan shine best food ɗin ta, tana gamawa ta haɗa zoɓo shima, ta sanya a fridge ta nufi ɗaki, wanka tayi ta shirya tsaff, cikin pink ɗin shadda ɗinkin doguwar riga ta kashe ɗauri. Ba jimawa kuwa taji ana doorbell na ringing, da sauri ta tafi dan tarbar ƙawar tata, tana buɗewa kam suka rungumi juna suna dariya, har saida Nasreen ta gaji tace "sake ni da Allah, kada ki ɓalla masa ni." Dukan su suka sa dariya suka shiga ciki, fira suka ɗan soma taɓawa na yaushe gamo kamin kuma suka shiga ɗaki, saida Khansa'u ta dawo ta ɗauka dukkan kayan abincin ta shiga dasu, nan suka ci suka sha sannan suka soma serious talk. Saida Nasreen ta tsaya ta ƙarewa Khans kallo sannan tace "wai ke Khans sai yaushe zaki amshi Zayyad a matsayin miji ne? Kada ki cutar da ɗan mutane fa, dan shima yana da gata kamar yadda kike dashi." Tsaki Khansa'u tayi tace "Nasreen kinfi kowa sanin koda akayi auren mu ba sonshi nakeyi ba, toh me zaisa in amshe shi a matsayin miji?" "Hmm, Khans kenan. Amma kinsan yana da haƙƙi a kanki kamar yadda kema kike da haƙƙi akan shi ko?" Cikin rashin fahimta Khans tace "me kike nufi?" "Ina nufin kamar yadda yake baki haƙƙin ki kema its your responsibility ki biya masa dukkan haƙƙin sa, wlh nayi tunanin zuwa yanzu kin aje dukkan wasu makaman yaƙi kun zauna lafiya, Khansa'u sati biyu ba, kwana goma sha huɗu amma baku taɓa fahimtar juna ba, ko ince baki bashi haɗin kai ba, dan nasan Zayyad na iya bakin ƙoƙarin sa, ki sani Khans wlh sai Allah ya tambaye ki, dan wannan cutarwa ce, idan dashi yake miki haka za kuji daɗi?" "Ke da Allah ki ƙyale ni, zaki fara cikani da surutun naki, ni idan bazaki bani shawarar yadda zan rabu dashi ba toh ki ƙyale ni." Waro idanu Nasreen tayi kana tace "lallai abin babba ne," a ranta kuma tace in kinsan wata bakisan wata ba. Tashi duk sukayi sukayi alwala kasancewar la'asar ta gabato, da ƙyar Khans ta yarda suka shiga kitchen dan saamawa mijin nata abinda zaici in ya dawo, tuwon shinkafa sukayi masa miyar egusi taci kifi da nama, pineapple juice suka haɗa masa dashi, bayan fitar Khans, Nasreen ta leƙa ta tabbata da ta tafi, saita ciro wani tablet daga aljihun doguwar rigar ta, guda biyu ta ɓallo ta sanya cikin wannan pineapple juice ɗin da sukayi ta maida fridge. Koda khansa'u ta dawo wani juice ɗin suka ƙara haɗawa a karo na biyu, saidai a wannan karon watermelon and cucumbers juice sukayi, saida suka gama komai Nasreen taja Khans zuwa ɗaki ta zaunar da ita, ta soma mata magana kamar haka "idan har da gaske so kike ki rabu da Zayyad cikin sauƙi, toh ta wannan hanyar zaki ɓullo masa, kada ki riqa hora sa da yunwa dan wlh bazai rabu dake ba, kullum dare safe rana ki masa abinci, amma bance ki riƙa sake masa fuska kuna hira ba, kodan kada ya raina ki, so a hankali a hankali ni kuma zan riƙa daura ki kan abinda zakiyi step-by-step, Amma fa ki tabbatar duk abinda ake ciki kin sanar dani. Yanzu wannan drink din da mukayi guda biyu, kada kisha pineapple juice ɗin ki bar masa, nasan zai kashe masa jiki ta yadda duk abinda kikace yayi zaiyi, ni zan wuce yanzu, ki tabbatar kin sanar dani halin da ake ciki, sannan kije kiyi wanka, kada kuci abincin sai bayan Isha'i, kada kasala ta hanashi yin sallah." Ta ƙarasa tana miƙewa. Itama Khans miƙewan tayi tana mai matuƙar jin daɗin shawarar ƙawar tata, dan a jikin ta takejin aikin su zaiyi kyau. Hakan kuwa akayi, Zayyad ya shiga gida dap da maghriba sabida patients da suka masa yawa, sannan ya dawo a matuƙar gajiye tayadda har ya manta bai yi musu takeaway ba, Khans da taji shigowar sa tayi murmushin mugunta a ranta ta furta 'ka shigo hannu Zayyad'. Tana jin shigar sa ɗaki yana waya, da alama abokin sa ne, batayi yunƙurin bin sa ba, illa fitowa da tayi ta shirya komai kan dinning ta nemi waje ta zauna tana jiran fitowar sa. Ta ɗauki kimanin mintina talatin, dan har ta cire tsammanin fitowar sa ma, kawai taji ya murɗa handle, nan ta gyara zaman tare da zaman sexy night gown ɗin dake jikin ta. Karap sukayi ido huɗu da Zayyad dake ganin abin tamkar mafarki..... __________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/12, 7:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* The writer of 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 29 & 30... ________Wani tsinkakken yawu Zayyad ya haɗiye yanajin jikin sa na masa wani irin chanji da bazai iya fassara shi, da ƙyar ya iya ƙarasowa dinning area ɗin ya zauna ɗaya bisa kujerun dinning ɗin, har lokacin bai ɗauke idanun sa kan Khans ba. Inda-inda ta shiga yi na tunanin yadda zata fara, dan tun daga kallon farko da Zayyad ya mata wani bala'in kwarjinin sa ya mamaye ta, da ƙyar ta miƙe cikin jarumta ta soma serving ɗinshi tana murmushin yaƙe kafin kuma murmushin ya koma na mugunta, sai da ta gama serving nashi tsaff, itama tayi wa kanta ta zuwa nata watermelon juice ɗin sannan ta zauna, shidai Zayyad baki buɗe yake bin Khans da ido yana tunanin anya ita ce? "Bismillah koh?" Tace tana sakar masa wani murmushi mai tsuma jiki, tamkar wani robot (mutum mutumi) haka ya koma, a hankali ya soma cin abincin yana jin daɗin abincin har tsakiyar ƙwaƙwalwar sa, akai-akai sukan saci kallon junan su kuma saisu cigaba, har dai suka gama. Bayan kammalawar su da kusan minti 5-10 Zayyad ya soma jin kanshi na juyawa, ga azababbiyar sha'awa take bijiro masa kamar zaiyi hauka, idanun sa sun kaɗa sunyi jajir tamkar garwashin dake ruruwa, tun yana dannewa har cikin sa ya soma murɗawa, a daddafe haka ya miƙe ya shiga ɗaki, Khans da dawowar ta kenan taga shigar sa ɗaki, wata uwar dariya ta sheƙe da ita harda riƙe ciki, kukan da wayar Zayyad ta somayi ce tasa ta maida hankalin ta wajen, (Daddy) shine abinda ta gani yana yawo kan screen ɗin wayar, kamar zata ɗaga sai kuma ta miƙe ta shiga ɗakin Zayyad ɗin, 'wow' ta furta cikin ranta, domin ɗakin Zayyad ɗin ƙarshe ne wajen haɗuwa da ƙayatuwa, komai na ɗakin milk and coffee ne kama daga furnitures zuwa curtains har center carpet ɗin, wata ƙofa data gani ta nufa tana mai ƙarewa ɗakin kallo har ta isa ga ƙofar, a hankali ta tura ƙofar tana leƙawa kamar wadda tazo sata, dressing room ne wanda ya taka nata kyau, taɓe baki tayi taja ɗan siririn tsaki ta janyo ƙofar. Ƙara ta saki tana runtse idanun ta jikin ta na kyarma, Zayyad daya daɗe wajen yana kallon duk abinda takeyi yayi murmushin gefen baki, a hankali ya ƙarasa dap da ita, yasa hannun sa ya zare wayar ya ajiye, har lokacin jikin ta bai bar kyarma ba kuma bata buɗe ido ba. Rungumo ta yayi jikin sa yana shafa bayan ta a hankali, yanajin yadda take jan numfashi, nan take ya soma romancing ɗin ta cikin fitar hayyaci, ganin abin nasa na neman wuce gona da iri yasa Khansa'u yunƙurin dakatar dashi, amma inaa? Zayyad tuni yayi nisa bayajin kira (Hhh su Khans next Idan aka tashi gina ramin mugunta a gina shi gajere). Yarap suna faɗa kan gado, Khansa'u na kuka da magiya amma Zayyad kamar mara imani, duk yadda takai ga ƙwatar kanta ta kasa, yabi ya tokare da dukkan sassan jikin sa, tsoron ta bai ƙaru ba saida ya raba ta da dukkan kayan jikin ta, shi kam dama towel ne a jikin sa, dan daga wanka ya fito, da lalube ya nemi switch ɗin wutar ya kashe musu. Addu'ar saduwa ya karanto cikin disashewar murya, lokaci guda Khans ta saki wata wahalalliyar ƙara ta cigaba dayi masa magiya, bai ko bi ta kanta ba, sukuwar sa kawai yakeyi tamkar wani doki, nidai ina zaune harna wani lokaci inajin yadda kukan Khans ke fita a wahale. _Wato abinda bata sani ba shine, lokacin da Khans ta koma ɗaki, Nasreen ta zuba ƙwayar tada sha'awa cikin pineapple juice ɗin da sukayi, hakan yasa tayi duk abinda zatayi ta hana Khans shan juice ɗin, Nasreen tana da manufar ta nayin hakan, dan yana ɗaya daga cikin abin da takeson ya gyara zamantakewar auren nasu._ Bayan wani ɗan lokaci Zayyad ya kunna wutar ɗakin, innalillahi wa inna ilaihi raji'un na furta a zuciya ta ganin Khans kamar sumammiya, koda na lura da kyau naga ashe ba suma tayi ba, wasu siraran hawaye kawai ke gangara kan kunnen ta tana daga kwance, tayi Allah ya isa wa Zayyad yafi a ƙirga, tayi dana sanin shigowa turakar Zayyad yafi sau shurin masaki, gashi ya karɓe budurcin ta wanda batayi niyyar basa ba a banza ya barta da wahala da gajiya. Wani kukan ta sake saki amma a wannan karon mai sauti ne. Zayyad baice da ita komai ba ya miƙe a hankali ya nufi toilet, saida yayi wanka sannan ya fito ya cicciɓi Khans, tayi ƙoƙarin zillewa amma taga ita zata sha wuya, dan wani raɗaɗi kawai kasan ta keyi, hakanan ta haƙura har ya kaita toilet ɗin. Duk yadda yaso ta bari ya mata wanka amma taƙi, babu yadda ya iya hakanan ya fita ya zauna jiran ta a ɗakin. Khans kuwa duk yadda ta motsa taji zafi sai ta sakawa Zayyad Allah ya isa, a halin da take ciki ma in akace ta rufe Zayyad ɗin da duka, tsaff zatayi. Cikin ƴan dabarun ta tayi jiƙa-jiƙan ta ta fito, (dan banace wanka ba). Daga yanayin tafiyar ta ma zaka tabbatar da ba wankan Allah da Annabi tayi ba, sosai tafiyar taba Zayyad matuƙar dariya wanda saida ya kasa riƙe dariyar ya ɗan murmusa, haushi ne ya mamaye Khans ta ɗanyi magana ciki-ciki wanda banji mai tace ba. Bata ko damu da kallon da Zayyad ɗin ke mata ba, tayi hanyar ƙofa abinta, da sauri Zayyad ya miƙe yasha gaban ta tare da furta "ina kuma zaki?" Harara ta watsa masa tace "inda ka aikeni." (Nikam nace su Khans baki baya mutuwa). Murmushi yayi ransa cike da farin ciki abin sa baiko damu da baƙar maganar taba ya ƙara da cewa "sorry dear, ki zauna pls, bari in kawo miki kaya." "Bana buƙata Zayyad, ka bani hanya in wuce," ta faɗa cikin tsawa. Ba tare da Zayyad ya shirya ba ya matsa, gudun kada ya jawa kansa, wucewar ta tayi ba tare data ƙara kallon inda Zayyad yake ba. Koda ta koma ɗaki wani marayan kuka ta saki tana latse-latse a wayar ta kamin ta kara a kunne, bugu biyu kuwa aka ɗaga tare da furta _"kawas ya ake ciki?_" Kuka Khans ta ƙara saki tana mai cewa "na shiga uku Nasreen, shikenan Zayyad ya gama dani a duniya, ya cuceni wlh, na shiga uku ni Khansa'u," ta kuma rushewa da wani kukan. _"subhanallahi, ke meke faruwa ne, me Zayyad ɗin ya miki kike wani kin shiga uku?"_ Tiryan-tiryan ta zayyanewa Nasreen kaff abinda ya faru, ta kuma ƙara da faɗin "dan Allah Nasreen ki samomin flusher gobe ki kawo min, wlh na tsani Zayyad, bazan iya haɗa jini dashi ba wlh, na roƙe ki Nasreen." Sosai ƙawar tata ta bata tausayi amma kuma taci dariya, cikin salon yaudara ta soma rarrashin ta har ta samu tayi shiru ta kuma tabbatar mata da zatazo goben insha Allah, nan sukayi sallama ta kashe wayar. A hankali ta kwanta ba tare data cire towel ɗin jikin ta ba taja bargo. Dukkan abinda Khans ta faɗi a kunnen Zayyad ta faɗe su, sosai yaji babu daɗi jin yadda ƙanwar tasa ta tsane shi, ya daɗe nan tsaye yana tunani barkatai gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, cikin jarumta yaja ƙafar sa da yakejin ta masa nauyi ya tafi ɗaki. Alwala ya shiga yayi ya fito ya tada sallah harya idar, ya daɗe kan sallayar yana roƙon Allah yasa yayi ajiya a cikin Khans tare da neman kariyar Allah ga duk wani hari da Khans zata kaiwa cikin, akan sallayar ma bacci yayi gaba dashi....... ____________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/13, 1:01 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* 🪶_*WOMEN WRITERS ASSO...*_📚📚 The writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 31 & 32.... 📖____________Haka rayuwar auren su ta cigaba da wakana, tun bayan faruwar wannan al'amari Zayyad bai ƙara sa Khansa'u a idanun sa ba, bata taɓa fitowa sai ya bar gidan, sannan kafin ya dawo ta koma ɗaki, duk yadda yakai ga ritsa ta a gida ya kasa, ga abu har ana neman sati 5, harya soma jin haushin kansa ma. Idan kuma ya zauna yayi tunani, sai yaga ba laifin sa bane, lokaci ɗaya sha'awar da bai taɓa zaton akwai ta a duniya ba ta taso masa, baiga wani aibu aciki dan ya sadu da matar sa ta sunna ba da har zata ƙaurace masa. Yau ya kama Friday, tun bayan da aka sakko sallahr juma'a ya nufi gida, dan bayajin zai iya zuwa asibiti balle kuma ya duba patient, koda ya shiga gida a tunanin sa zaiga Khans a parlor amma sai yaga akasin hakan. Yanke shawarar zuwa ɗakin ta yayi bayan yaje ya ɗakko extra key ɗin ƙofar, cikin sa'a kuwa ya buɗe tare da faɗawa ɗakin, zaune ya same ta tana shan oat milk, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallon TV, koda taga shigowar shi batayi mamaki ba, dan tasan bazai rasa spare key ba. Cikin takun nan nasa mai kama dana isa yake nufar inda take, kallo ɗaya zaka masa ka gano yana cikin damuwa, amma baiyi ƙasa a gwiwa ba ya zauna gefen ƙafafuwan ta ya kafe ta da ido. Tun da ya shigo harya ƙaraso, bai samu arziƙin kallon mutunci daga Khans ba, duk da ma tunda ta kalle shi sau ɗaya bata ƙara mararin kallon wajen ba harya zauna. "Ina mai haɗaki da girman Allah daki juyo ki saurare ni muyi magana," Zayyad ya faɗa cikin sigar tausayi. Ba tare data kalle sa ba tace "ina ce kunne keji? Dan haka ka faɗi abinda ke tafe dakai, idan kuma babu ka bar min ɗaki dan banason ganin ka." Wani abu ne yazowa Zayyad wuya, ya tokare yaƙi gaba yaƙi baya, amma bai bari ta lura ba, cikin jarumtar su ta maza ya ƙara da cewa "kunne ji kawai yakeyi Khans, hankali ke auna maganar ita kuma ƙwaƙwalwa ta bada amsa, dan Allah ki saurare ni." "Ina jinka," ta faɗa tana kafe sa da mayun idanun ta masu sanya dukkan wani lafiyayyen namiji cikin halin ha'ula'i. "Wata biyu ake nema da bikin mu Khans, amma dukkanin mu bamu san meye daɗin aure ba, ta sani cewa baki sona, amma ban ɗauka tsanar da kika min yakai har kiji bakison haɗa jini dani ba. Yau ko bani da asali mahaifin ki ya zaɓa miki ni ya kamata ki karɓa da hannu bibbiyu, tunda kin shaida bazai zaɓa miki wanda za'a zo ana dana sani daga baya ba. Tun tasowar ki kika ganni gidan ku, wanda kikayi tsammanin ciki ɗaya muka fito, ban taɓa ɓata miki ba kema kuma haka, hasalima bayan Mahfouz babu wanda kuka shaƙu dashi kamar ni, duk da kuwa nasan ni ɗin bamai son shiga jama'a bane. Amma meyasa daga haɗa auren mu dake kika ɗauki tsanar duniya kika ɗora min? Alhalin kinsan bani nace Abba yayi haka ba, banaso in zama macuci a gareki, haka zalika banso kema ki riƙa cuta ta a zaman auren mu. Banso maganar nan tayi girma takai bakin manya, domin nasan bazamu kwashi ta daɗi dasu ba, ina roƙon ki daki sassauta ƙiyayyar ki a gare ni, ki riƙe ni mijin ki kamar yadda Allah ya zaɓa miki ni a matsayin miji." "Zayyad kenan, kana tunanin zuciyar da aka cuta zatazo taso wanda ya cuce ta ne? Ka rabani da farin ciki na Zayyad, a dalilin ka Zaid ya barni yana kuka, wanda bansan halin da yake ciki ba yanzu. Da ace kana sona kamar yadda ka faɗa da bazaka zo ganina a irin wannan halin ba, da tun lokacin da akeson haɗamu zaka cewa Abba bakaso, dan nasan maganar ka kaɗai zaiji, bazamu taɓa iya dawowa kamar yadda muke dakai ada ba Zayyad har sai ranar daka miƙamin takardar saki na," ta ƙarashe hawaye na biyo kuncin ta. Wata uwar razana Zayyad yayi, jin Khans na musu fatan saki, abinda ko a mafarki bai taɓa zato ba, yana son Khans iya son da daya rabu da ita gara ya mutu shahidi. Sosai zai baka tausayi a wannan lokacin. "Ina sonki ƙwarai Khans, kuma na tabbata koba yanzu kema wataran zaki so ni, amma maganar saki kam bazan iya ba ko kaɗan." "Shikenan Zayyad, wallahi kayi sallama da bala'i da masifa kala-kala harsai ka gaji da kanka ka sake ni, zaka gani." Jin hawaye na ƙoƙarin zubo masa yasa ya miƙe ta sauri yayi waje, da fitar sa kam wani zazzafan hawaye mai raɗaɗi ya zubo masa, ya daɗe tsaye yana tunanin ta yadda zai ɓullowa Khans amma ya kasa, cikin sanyin jiki ya ƙarasa zuwa ɗakin sa. Kamar kuwa yadda Khans tayi alƙawarin ƙuntatawa Zayyad bata fasa ba, na yau daban na gobe daban, na yanzu daban na anjima daban. Ko da wasa hakan bai taɓa sa Zayyad ƙoƙarin sakin ta ko ramawa ba, dan yasan kowa da irin tasa ƙaddarar, ta yiwu shi irin tasa kenan. Ganin abin yaƙi ci yaƙi cinyewa bashi da niyyar sakin ta yasa ta kiran aminiyar ta Nasreen, saidai cikin rashin sa'a Nasreen bata ƙasar, sakamakon strike ɗin da makarantar su ta tafi yasa baban ta fita da ita ta ƙarasa karatun acan. Khans tayi baƙin cikin rashin ƙawar tata a ƙasar, dan bata san ma ta tafi ba, kasancewar kashe wayar ta da tayi na kusan satuttuka, tasan kuwa Nasreen ɗin ta nemeta. Toh a ɓangaren Nasreen itama bata ji daɗin tafiyar ta ba, dan kuwa tasan Khans bata fasa ƙuntatawa Zayyad ba. *3 WEEKS LATER* Kamar yadda ya saba zuwa ya duba lafiyar ta kafin da bayan ya dawo asibiti, yau ɗin ma hakan take, duk da hakan bai hanata yi masa rashin kunya da wulaƙanci. Yadda ya saba shiga ya ganta yau akasin haka ya tarar, dan bai taɓa shiga dap da Isha'i ya same ta kwance ba, da ɗan sassarfa ya ƙarasa inda take kwance ya yaye duvet ɗin data rufa ya tallafo ta, zafi rauu yaji jikin ta ya ɗauka, ba shiri ya ajiye ta ya fita, bayan ƴan daƙiƙu ya dawo ɗauke da box, allura ya haɗa ya ƙara ɗago ta. Cikin rashin tsammani Khans taji saukar allura, aikam ba shiri ta saki wani wahalallen ƙara, bai bi ta ihun ta ba, ya sake ɗakko wani syringe ɗin, cikin dabara ya ɗauka jinin ta ya fice ya barta ta ba tare da ya ce komai ba. Ya fita da kusan daƙiƙu arba'in da biyar sannan ya dawo. Ɗaya daga ledojin daya shigo da ita ya buɗe ya fiddo magungunan ciki kafin ya buɗe ɗayar ya fito da farfesun kazar daya taho mata dashi. A hankali ya ɗago ta daga kwancen da take gaba ɗaya jikin ta ya saki, feeding ɗin ta ya somayi a hankali har ta ƙoshi, wajen shan magani ne dai saida ta bashi wuya, bayan mintina 30 haka ya miƙe ya shiga toilet ɗin ta, sosai yabi ilahirin ko ina da kallo ganin shi a tsaftace kamar ba'a shiga. Ruwan wanka ya haɗa mata ya taimaka mata ya kaita bayin, kasancewar yasan bazata bari ya mata wankan ba yasa shi ficewa. Saida ya gyara wajen sannan ya dawo ya zauna, tagumi ya zabga tare da tunanin ta inda zai fara gayawa Khans ciki ne da ita, domin yasan zata iya yin komai ta zubar dashi. Yana nan zaune harta fito, da alama ma ta samu ƙarfin jikin ta, ko kallon inda Zayyad yake batayi ba ta shige dressing room, ba daɗewa ta fito sanye da doguwar riga ta bacci mai kauri, wardrobe ta buɗe ta ɗauki hijabin ta ta nufi inda prayer mat yake tayi Sallah, tana idar Zayyad ya miƙe tare da damƙa mata maganin ta a hannu, ya kuma yi mata bayanin yadda zata sha sannan ya fice. Washegari gari ya kama saturday, da wuri Zayyad fita sabida yana da theater da zaiyi karfe 8, saida yaje ya duba jikin Khans tare da tabbatar da tasha magani, ya kuma jaddada mata shan na rana, sannan ya fita, dan baya da tabbacin dawowa da wuri. Bashi ya dawo ba kuwa sai 4pm, ɗakin ta ya fara shiga dan duba lafiyar ta, ya samu ta fito wanka. Harara ta watsa masa tana wucewa gaban mirror, babu wanda ya furta ƙala har ta gama shafe-shafen ta kafin ta juyo ga Zayyad dake zaune riƙe da wayar sa da tata tace "wai kai Zayyad me kake nufi ne? Daga kawai bani da lafiya sai kazo ka taremin a ɗaki kai a dole kana ban kulawa ko? Toh idan ma tunanin ka ciki gareni toh ka cire wannan tunanin, dan bazan taɓa haihuwa dakai ba, ba kaƙi saki na ba, indai wulaƙanci ne ka ringa gani kenan." Murmushi kawai Zayyad yayi a rashi, a zahiri kuma yace "your excellency, nazo dubawa inga ko kinsha magani ne." "Toh idan bansha ba lafiyar ka ko tawa? Banson shisshiga cikin lamarin da bai shafi mutum ba." Shidai baice da ita komai ba harya shiga dressing room ta fito sanye da wata milk ɗin swiss atampa mai ɗankaran kyau ɗinkin riga da skirt sun ɗame ta sosai, dan ita kanta saida taji kamar ta ƙara ƙiba, ga boobs ɗinta da suka cicciko kamar mai shayarwa. "Kayi sallah ne da kazo ka zauna kana ƙaremin kallo?" Ta ƙarasa cikin sigar faɗa. Ba tare da Zayyad yace da ita komai ba ya fice (domin kunsan Zayyad ba mai son magana bane). Tunda Zayyad ya fita bai sake dawo wa gidan ba sai bayan sallahr Isha'i ɗauke da takeaway ɗin daya saba yi musu, dan ko zasu shekara ba abinci Khans baza ta dafa ba, tun wanda tayi kwanaki, bata ƙarayi ba. Kwance ya sameta tana chatting da Nasreen mutanen ƙasar waje, fuskar ta ɗauke da murmushi wanda ya matuƙar ƙara mata kyau, sosai Zayyad ya shagala da kallon ta dan kuwa rabon da da yaga murmushin ta tun kafin auren su, balle kuma dariya. Tafin da tayi ne yasashi firgigit ya dawo hayyacin sa, ƙeyar sa ya sosa kamin ya soma ƙoƙarin magana wayar sa ta soma ƙara, "Abba kuma." Ya furta a bayyane cike da mamaki, ɗagawa yayi tare da sanya speaker bakin sa ɗauke da sallama. Cikin wata iriyar murya Abba ya amsa, ba tare daya amsa gaisuwar da Zayyad ke masa ba yace _"dakai da matar ka kuzo gobe Inason ganin ku, kada ku wuce ƙarfe goma."_ daga haka ya katse wayar ba tare daya jira me Zayyad ɗin zai ce ba, kallon juna duka sukayi, fuskar Zayyad cike da fargaba yayin da Khans ko ɗarr batayi ba. Har Khans taci abinci ya bata magunguna dai jikin sa a sanyaye, babu walwala ko kaɗan, dan yana tunanin abinda zasuje su tarar goben, har bacci bai iya yi ba sai daƙyar baccin ya sace shi, yayin da Khans ta shari nata baccin hankali kwance.... ```Toh danjin ya zata kaya tsakanin Abba dasu Zayyad, ku cigaba da bibiya ta danjin cigaban labari.``` ~A madadin ni Babylorh dana rubuta kuma na tsara nake cewa *Assalamu alaikum*~ ____________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/14, 12:12 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* 🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚 The writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_ 33 & 34.... 📖____________Washe gari dukkanin su suka shirya suka tafi amsa kiran da Abba yayi musu da misalin 9:30 na safe. Tun a hanya jikin Zayyad ke basa akwai wani abu a ƙasa har suka ƙarasa gidan, sosai Khans keta farin ciki da murnar zataga ƴan uwan ta da Ummin ta yau. Saidai, mamaki ne ya cika su dukan su biyun lokacin da suka shiga suka tadda duka familyn na wajen har su Mummy, alamu kuma ya nuna su kaɗai ake jira. Wani mahaukacin mari Abba ya saukewa Khans a fuskar ta, fuskar sa ta nuna tsantsar ɓacin rai a tare dashi. Dafe da kuncin ta Khans ta ɗago idanun ta sun kawo ruwa suna shirin sauka ta furta "Abb...." Ai bata ƙarasa ba Abba ya kuma wanke ta da wani marin da bayan hannun sa, wanda saida yasa Khans kusan kifa wa badan Zayyad ya taro ta ba, sosai takejin zafin marin na ratsa can cikin tsakiyar ƙwaƙwalwar ta, ba shiri kuka ya kufce mata kamar zata shiɗe. Hankalin Zayyad kuwa yakai ƙololuwa wajen tashi, musamman yadda shatin yatsun Abba suka bayyana tangaran akan kuncin ta, ta take kuwa fuskar tayi jajir tamkar tumatir, abinka da farar fata, ga gefen bakin ta da shima yake fidda jini kaɗan-kaɗan. "Calm down pls, nasan abin da tayi bata kyau ta, amma irin wannan marin zai iya yi mata illa, ko ya kashe mata kunne ko ya mata illa a ido, control your temper pls, faɗa da nasiha ya kamata a musu gaba ɗaya." Daddy da dake riƙe da kafaɗun Abba ya faɗa yana mai ƙoƙarin zaunar da Abba bisa kujera. Babu abinda Abba keyi sai huci, jin zuciyar sa yakeyi tamkar ta fito ya tsoma ta a ruwa sabida zafin da take masa, hannu yasa ya karɓi ruwan sanyin da Mahfouz ke miƙa masa, saida yasha da kamar mintina biyar sannan ya soma magana, "kin bani kunya Khansa'u, haƙiƙa kin bani kunya, nayi zaton na haifi ƴaƴan da zasu rufamin asiri, nayi zaton na haifi ƴaƴan da zasu karɓi zaɓin da nayi musu hannu bibbiyu, nayi zaton na haifi ɗiyar da zance tayi kuma tayi koda hakan bazai mata daɗi ba, ashe duk haukan banza na nakeyi, in miki gata amma kina ƙoƙarin kwance min zani a kasuwa, kinason tozarta ni Khansa'u, ni Khansa'u!!!" Cikin rashin fahimtar inda zancen Abba ya dosa Zayyad yace "amm Abba wani abu ne ya faru?" "Rufemin baki Zayyad, ko kaɗan kaima banji daɗin abinda kayi ba, na ɗauka ni mai share maka damuwa ne, nayi tunanin ni mai sama maka mafita ne a kan rayuwar ka gaba ɗaya, ashe samm ba haka kuka ɗauke ni ba. Kasan haka rayuwar auren ku ke tafiya, amma baka sanar dani ba Zayyad, kayimin adalci kenan?" Gaban Zayyad ne ya faɗi jin zancen zaman auren su da Khans, sai da ya saci kallon Khans da har lokacin hannun ta bai bar kuncin ta ba, sannan ya maida kallon sa a Abba cikin in'ina kuma yace "A'a Abb......Abba, b...ba..babu abinda k..ke faruwa, wani yace bama zaman lafiya?" Wayar Abba dake kan table Abba ya ɗauka cikin ƙufula ya kunna wani record da ake magana kamar haka (```toh idan ma tunanin ka ciki gareni toh ka cire wannan tunanin, dan bazan taɓa haihuwa dakai ba, ba kaƙi saki na ba, Indai wulaƙanci ne ka ringa ganin sa kenan....```) Ba Khansa'u dake rusar kuka ba kaɗai, hatta Zayyad saida gaban sa yayi wani mummunan faɗuwa, dan baisan sanda ya cire hular kansa ya soma fifita ba. Abu kamar a mafarki, shi dai yasan ba shine yayi recording abin nan ya kawo musu ba, toh a ina suka samu? Ko aljanu ne suka kawo musu! Ha'a, toh kodai wani yaje gidan ne jiya? Toh amma basuji motsin kowa ba balle shigowar su, toh ko Bala mai gadi ne? Toh amma ai ko parlon su baya shiga balle yayi gigin zuwa ƙofar ɗakin dayan su, tunani barkatai haka ya riƙa zuwa ma Zayyad, yayin da har lokacin zufar bata bar keto masa ba. Khansa'u data daskare a wajen na ɗan wani lokaci a ranta tace "lallai ma Zayyad, wato har kayi isar da zaka haɗani da mahaifi na, muyi magana dakai jiya ashe recording kakeyi, har ka iya kawowa su Abba? Lallai ka ɗibo ruwan dafa kanka, tunda ba kashe ni za'ayi ba zakaga abinda zai biyo baya, wlh dani kake zancen..." Sai bayan da recording ɗin ya gama ne Abba ya ɗago ya kalli Zayyad dake ta faman fifita yace "zaka cemin wannan ba muryar ka bace, ko kuwa ba muryar Khansa'u bace? Ko zaka cemin ba kaine kake cewa kazo ka duba ko tasha magani ba? hmm!" Ya ƙarasa yana bubbuga ƙafar sa a ƙasa na ɗan wani lokaci. Shiru parlorn ya ɗauka na ƴan daƙiƙu kafin Daddy yayi gyaran murya yace "zo nan ƴa ta." Cikin shessheƙar kuka ta miƙe a hankali tana taku tamkar wadda ƙwai ya fashe mawa aciki, ta lura da uban hararar da Abba da Ummi suka mata, wanda ya matuƙar sanya jin wasu sabbin hawayen na antayi wa. Har kusa da ƙafar Daddy taje ta zauna sannan Daddy ya ƙara da faɗin "ƴa ta banyi tunanin zaki ɗibi ƙasa ki watsa mana a ido ba, Zayyad ko ba ɗan uwan ki bane shi a ƴan uwan taka, shi ɗin ɗan uwan ki ne a musulunci, shin abin da kikeyi ya dace kenan? Ce maki akayi bashi da gata ko me? Kiji tsoron Allah Khansa'u, mijin ki yana da haƙƙi akan ki, ko babu igiyar aure tsakanin ku, kiyi masa magana mai daɗi ma jin daɗi ne, kuma sadaƙa ne, yanzu idan Allah ya ɗauki ranki a haka kina tunanin kina da hujjar da zaki gaya wa Ubangiji ne? (Bakison shi) hujjar da zata kare ki a wajen Allah ne? Kiji tsoron Allah, ki guji ranar da Allah zai kama ki da wannan abin, yau ga iyayen ki na fushi dake akan wanda kike iƙirarin bakiso, hakan bai isa ya nuna miki irin soyuwar da yayi a zuƙatan su ba, idan ke mai hankali ce daga yanzu da muke maganar nan bazaki ƙara gigin muzguna masa ba, balle kuma ki riƙa furta baƙaƙen magana akan sa." Sosai Daddy yayi mata nasiha mai matuƙar ratsa jiki sannan ya ƙara da faɗin "ki tashi yanzu ki nemi yafiyar iyayen ki akan abinda kika musu." Jiki a matuƙar sanyaye ta miƙe ta isa gaban Abba da tunda Daddy ke magana kansa ke a ƙasa harya gama bai ɗago ba, durƙusawa tayi tare da kama hannun sa yayi saurin ƙwace wa, "kayi haƙuri Abba na, ina roƙon ka daka yafemin laifin dana maka, insha Allah bazan ƙara ba, zaka same ni mai biyayya ga mijina in Allah ya yarda." Cikin jin daɗin maganar ƴar tasa ya ɗaura hannun daman sa a kanta tare da sanya mata albarka, kowa ya amsa da Ameen. A sannu ta kuma miƙewa ta isa gaban Ummi, nan ma yafiyar ta nema tare da alƙawarin zata yiwa mijin ta biyayya. Hatta Mummy da Daddy bata barsu a baya ba, suma ta roƙi yafiyar su, a taƙaice dai basu bar wajen nan ba saida iyayen nasu suka sanya wa rayuwar auren nasu albarka. Daga Zayyad har Khans babu wanda zaka kalla baka tausaya masa ba, Zayyad ne mai jarumtar rarrashin dama, toh a halin yanzu shima rarrashin yake buƙata, har suka fito zasu tafi Khans bataga Mahfouz ba, hakan yasa ta tanbayi Zayyad cikin sanyin murya. Waya ya ɗaga ya kira Mahfouz ɗin, babu daɗewa kuwa sai gashi, amma abin mamakin Zayyad kawai ya yiwa magana ya soma ƙoƙarin juyawa. "ya Mahfouz." Khans ta faɗa hawaye na cika idanun ta, cak ya tsaya ba tare daya juyo ba. Ƙarasa tayi ta tsaya a gaban sa tana faɗin "ya Mahfouz baka ganni bane?" "Na ganki Khans, sai akayi ya?" Batayi mamakin maganar ba, amma bata mata daɗi ba ainun, cikin danne kukan dake taso mata tace "ba komai, dama naga ban ganka bane shine ya Zayyad ya kira ka. Ya Mahfouz idan na maka laifi ne dan Allah kayi haƙuri, idan kuma akan abinda ya faru ne na maka alƙawarin daga yanzu haka bazan ƙara ba." Sosai yaji daɗi a ransa, amma bai nuna mata alama ba, saima ƙara tamke fuska da yayi yace "Allah yasa." Daga haka yabi gefen ta ya wuce ba tare daya jira mai zata ce ba. Hannu tasa ta share hawayen daya gangaro mata, sannan ta nufi motar da Zayyad keyi mata horn, alamar ita yake jira. Tana shiga yaja motar suka nufi hanyar gidan su, har suka isa babu wanda yace da wani ƙala, hasalima banda shessheƙar kukan Khansa'u babu abinda ke tashi a motar. Shi kanshi Zayyad kasa rarrashin ta yayi, sabida tuna masa da wani memory da akayi a wannan taron, amma har ƙasan ruhin sa yakejin zafin zubar hawayen nata. _Wato abinda basu sani ba bayan dowowar Zayyad gida da shigar sa ɗakin Khans, su Haseena da Ameesha suka zo, suna ta sallama amma shiru ba'a amsa ba, sai suka yanke shawarar duba ɗakin Khans, Haseena dake a gaba ta kama handle ɗin ƙofar zata buɗe kenan ta jiyo muryar Khansa'u na gawasa Zayyad magana, Ayeesh da wayar ta ke hannun ta ita ke recording komai, sannan suka yanke shawarar komawa gida ba tare da sun shiga ba. Koda suka koma gida direct sashin Mahfouz suka shiga tare da sanar dashi abin da ya faru haɗi da audio ɗin da sukayi recording, sosai ran Mahfouz yakai ƙololuwa wajen ɓaci, ya amsa wayar tare dayin forwarding zuwa wayar shi sannan ya goge wanda ke wayar tasu, bashi ya samu ya sanar da Abba ba sai bayan Isha'i, shima Abba sosai ranshi ya ɓaci, nan take ta kira Zayyad tare da ce masa yazo gida._ ★★★★★★ Toh Alhamdulillah, kamar yadda Khans tayi alƙawarin gyarawa, bata saɓa ba. Sosai take iya bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta farantawa Zayyad kodan farin cikin iyayen ta. Shima Zayyad sosai yaga chanji daga wajen matar tasa da yawa, dan yanzu tana abinci, ta gyara ko ina na gidan har ɗakin sa, kuma takan yarda su kwana tare wani lokacin, saɓanin da da bata komai, gyaran gidan ma na ɗakin ta kawai takeyi. Har ƴar aiki Zayyad ya kawo mata dan ta riƙa taya ta aiki, dan a matsayin ta na mai ciki yawan aiki ba nata bane, duk da har yanzu bata san jiki bane, dan bai wuce wata 3 da ƴan ɗoriya ba, tana dai lura da yanayin yadda jikin ta ya chanza, ga ƙwadayi da take fama dashi, sai kuma magungunan da Zayyad ke kawo mata, wani lokacin kuma ya ɗauke ta suje asibitin sa ya duba ta ya dawo ta ita. A lokacin da cikin ta ya shiga wata na huɗu ne ta gane ciki gare ta, tasha kuka harta godewa Allah, dan har lokacin daidai da minti ɗaya bata taɓa jin son Zayyad ba, amma tayi alƙawarin sanya shi da iyayen ta farin ciki, zata raini cikin kuma ta haife da yardar Allah. Yauma tafe suke a hanya sun dawo asibiti, ga mamakin Khans a maimakon su tafi gida sai taga ya ɗau hanyar gidan su, saida marin da Abba ya mata ya dawo mata, tasa hannu ta shafa wajen idanun ta suka kawo ruwa. Zayyad dake gefe na saida ya lura da hakan, sosai shima yaji ba daɗi har dai suka ƙarasa. Basu sami kowa a gidan ba sai Ayeesh da Haseena suka tabbatar musu da sunje taron ƙarshen wata, basuyi ƙasa a gwiwa ba, suka nufi gidan Daddy dan dama achan akeyi. Sosai kuwa akayi murna da ganin su, dan kuwa alamu sun tabbatar da Khans ta cika alƙawarin data ɗauka. "Sarakan yawo, daga ina kuke kuma wa yace muku muna nan? Nan nasan badan Allah kuka zo ba, wata ƙilama baku taɓa zuwa gaida Daddyn ku ba," Abba ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi. "A'a! Ya haka kuma, haka mukayi dakai basu taɓa zuwa ba, kuzu kunji ƴaƴana, zo ku zauna." "Auuu! Haɗemin kai zakuyi kenan, toh shikenan, daga ina haka da ranan nan?" Abba ya kuma maimaitawa a karo na biyu. Munje asibiti ne Abba, dawowar mu kenan mun biya ta gida, Haseena tace kuna nan." Zayyad ya faɗa yana sosa ƙeya. "Subhanallahi! Waye ba lafiya ɗana?" Daddy ya faɗa yana dafa kafaɗar Zayyad ɗin. Inda-inda ya somayi yama rasa me zaice, dan baisan ya furta asibiti bama, nan take kuwa suka gano komai, musamman ma Ummi da Mummy da tun shigowar su suka ƙyalla ido kan Khans suka ga komai. "Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah sarki, Alh. Muhammad shi ya fara faɗomin a rai," Daddy ya faɗa fuskar sa cike da tausayi. Ƙasa sosai Zayyad yayi da kanshi ya share siririn hawayen daya taho masa da handkie ɗin hannun sa. "Meyasa kake kuka?" Khansa'u ta faɗa cikin sigar tanbaya a hankali. "Ba kuka nakeyi ba, abu ne ya shigar min ido," ya faɗa yana sakar mata murmushi a ɓoye. "A'a Zayyad! Ni yanzu ina ganin babu wani ɓoye-ɓoye kuma, ya kamata ace zuwa yanzu matar ka tasan komai game dakai," Mummy dake zaune ta faɗa tana mai tausaya Zayyad ɗin. Shidai Zayyad baice komai ba, kuma bai ɗago ya kalli kowa ya, Abba ne ya soma magana kamar haka "..... ```Ina masu buƙatar jin labarin Zayyad, toh ku tara dani idan Allah ya kaimu gobe ɗauke da labarin Zayyad insha Allah``` ```Kuyi haƙuri yadda na yayyanke labarin, banaso yayi tsawo dayawa ne shiyasa.``` ___________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/16, 8:18 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* 🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚 The writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_ 35 & 36.... 📖____________"Hakane Zayyad, ya kamata ta sani," saida yayi gyaran murya sannan ya cigaba da cewa " ```Alh. Muhammad Usman, wanda akafi sani da Alh. Muhammad Shehu (wato takwaran Abba), haifaffen garin Katsina ne kuma yaya a gurin Hajiya wato Ummi, mahaifin su ya kasance mutum mai ɗumbun dukiya, ga ilimi Allah ya bashi, inda rabi da kwatan kuɗin sa yake sadaukarwa al'umma su. Ni kaina zan shaidi Alh. Muhammad akan halayyar sa da mutane musamman maƙwaftan sa, domin ya ɗauke su tamkar ƴan uwa. Sai dai Allah ya jarabce sa da wata azzalumar mata, tun bayan rasuwar mahaifiyar Zayyad, a lokacin yana da watanni 8 a duniya. Matar ta kasance tana azabtar da Alh. Muhammad da kuma ɗansa Zayyad, ta haɗawa Zayyad zagon ƙasa dan mahaifinsa ya kore sa a gidan amma batayi nasara ba, domin duk duniya Zayyad shine babban ɗa kuma mafi soyuwa a zuciyar sa. Wannan ke tsole mata ido, kuma yake ɗaga mata hankali, dan so take ita da ƴaƴan da zata haifa su su gaji dukiyar, duk yunƙurin ta na kashe Zayyad ta gaza samun nasara, hakan yasa take azabtar dashi, ta dake shi ta jijji masa ciwo, wata rana ma ta hana shi kwana gidan, sabida mahaifinsa matafiyi ne.``` ```Ana haka Alh. Muhammad ya soma wata iriyar cuta wadda aka rasa ta mecece, har ƙasashen ƙetare an zaga dashi amma duk abu ɗaya suke faɗa, bayan cutar sa ta hawan jini, babu abinda suka gano tattare dashi. Kamar gaske, Alh. Muhammad ya soma samun lafiya, dan har takawa ma ya somayi, kwatsam wata rana ya fita shan iska tsautsayi yasa ya faɗi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar ɓarin jikin sa, yasha wahala matuƙa, dan duk lokacin da ciwon sa ya tashi ba ƙaramin jigata yakeyi ba. A kwana a tashi Alh. Muhammad saida yayi watanni goma a asibiti, a safiyar ranar asabar Allah ya ɗauki ransa. Karima (wato matar Alh. Muhammad) tasha kuka kamar gaske, a haka har akayi arba'in ɗin mahaifin Zayyad bata taɓa nuna wariya ga ɗan ta da Zayyad ba, ashe akwai abinda take ƙullawa.``` ```Wata rana, bayan kusan wata biyar da rayuwar Alh. Muhammad Hajiya (mommyn Khans) taje gidan domin duba halin da ɗan ɗan uwan nata ke ciki, amma abin mamaki sai ta taji suna magana da wata ƙawar ta, jikin ta daya bata akwai abin da suke ƙullawa yasa ta tsaya daga bakin ƙofa, Karima da ƙawar tane suka ta saƙa da warwarar yadda za'ayi su ɓatar da Zayyad a duniya, a lokacin Zayyad baifi shekaru ɗaya da wata watanni tara zuwa goma ba, nan sukayi ta tunanin yadda zasu yar dashi, nan take kuwa ƙawar Karima ta bada shawarar a bawa area boys ɗin layin su fitar dashi, nan kuwa Karima tayi na'am da hakan, suka yanke shawarar da daddare zasu aiwatar da komai, in yaso sai suce ya ɓace.``` ```Jin haka kuwa yasa hankalin Hajiya mummunan tashi, haka ta fito zuciyar ta cike da fargaba da kuma yadda za'ayi ta ceto Zayyad daga mugun manufar su akan Zayyad Nan take ta yanke shawarar taje ta samu area boys ɗin, in yaso suyi yarjejeniya ta biya su. Hakan kuwa akayi, toh su da yake kuɗi suke nema, ai ba musu suka amince, a daren ranar kuwa suka aiwatar da komai ba tare da sun sanar da Karima komai ba. A taƙaice dai Zayyad tun yana shekara ɗaya da wata goma yake tare damu, daga lokacin ya samu kwanciyar hankali, duk da ba wayau gareshi ba a lokacin, amma har ya girma baya shiga harkar mutane balle kuma wani abu ya faru dashi. A lokacin da muka sanar da Zayyad cewa ba mune iyayen shi ba, muka sanar dashi tarihin rayuwar sa, yayi kuka matuƙa harya gode Allah, duk daga wannan rana kuwa magana ke yiwa Zayyad wuya, duk da cewa yana da wuyar sha'ani kafin ku saba, amma da zarar kun saba dashi shikenan, nasan kema kin fahimci haka ƴa ta.``` Saida Abba yaja nannauyar ajiyar zuciya sannan ya cigaba da faɗin "wannan dalilin yasa na yanke shawarar haɗa auren ku, domin nason ke kaɗai zaki iya kula da marayen Allah ɗiya ta, duk da kuwa a baya kin nemi ki watsamin ƙasa a ido, amma yanzu Alhamdulillah naga kun daidai ta. Wannan zancen da nake miki, har yanzu Karima bata san Zayyad na raye tare damu ba, kuma har yanzu tana nan tanacin duniyar ta da tsinke, domin sosai nake lura da duk wani shige da fice nata. Kwanaki ma naji ance wai ɗan ta data haifa ma ya rasu, a dalilin haɗarin mota da yayi. Tun da Abba ya soma magana har ya gama Khansa'u ke faman kuka tamkar wadda ranta zai bar jikin ta, kuka take sosai na nadamar abubuwan da tayi wa Zayyad da irin wulaƙancin da tayi masa, kuka take na tausayin Zayyad da kuma irin rayuwar da aka so jefa shi amma Allah ya kiyaye shi da tsarewar sa, ganin bata da niyyar dakatar da kukan ne yasa Daddy cewa "Ba kuka zakiyi ba ƴata, addu'a kawai zamu cigaba dayi, Ubangiji ya cigaba da tsare mu a duk inda muke da kuma sharrin masharranta, kai kuma Zayyad Allah ya ƙara maka haƙuri da juriyar rashi, nan dai ya ɗanyi musu nasiha da kuma faɗa kan saɓawa juna, kana yace su tashi su tafi. Jiki a mace dukkanin su suka miƙe suka fita, har suka shiga mota Zayyad bai iya furta komai ba. Saida ya kwashi kusan mintina goma kafin yaja wata zazzafar ajiyar zuciya kana ya zaro hankie daga aljinun sa ya share idanun sa da sukayi jaa, sannan ya tada motar suka tafi. Koda suka koma gida ɗaki Zayyad ya shiga, wunin ranar Khans bata ƙara sanya shi a idanun ta ba, tun tana saka ran fitowar sa koda zuwa masallaci amma shiru, kuma tana tsoron shiga ɗakin nasa sabida batasan da wani ido zata kalleshi ba. Ganin har an kira sallahr maghriba bai fito ba yasa ta yanke shawarar shiga duk abin da zai faru ya faru, dan duk abinda zai mata, baza taga laifin saba, don tayi masa shima. Saida tayi sallah kana ta jera masa abincin sa a dinning ta nufi ɗakin, bakin ta ɗauke da sallama ta shiga kanta a ƙasa, daga can ƙasan maƙoshi ya amsa mata wadda ke bayyanar da dasasshiyar muryar sa, zaune yake akan sallaya har ta ƙaraso inda yake. Durƙusawa tayi kan gwiwoyin ta a gaban sa, har lokacin bata kalli fuskar Zayyad ba, balle taga wani irin kallo yake mata, wasa ta somayi da yastun hannun ta kafin tace "ya Zayyad dama naga baka fito bane shine nace bari inzo in duba ka, kuma na gama abinci yana dinning yanzu haka." "Yanzu nakeson in fito dama, tashi muje," ya faɗa yana miƙewa daga kan sallayar da yake. Itama mara masa baya tayi tanajin ta wani iri, dan ta kasa haɗa ido da Zayyad ɗin ma. Saida tayi serving ɗin shi sannan tayi serving kanta. Duk da ba wani yunwa yakeji ba, dan jin cikin sa yakeyi a cunkushe, yayi kusan loma uku kamin ya tsaida kallon sa ga Khans dake jujjuya cokalin ta yace "Khans yadai? Naga kinyi shiru kuma bakicin abincin." Murmushin yaƙe tayi daga bisani tace "..... ____________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/17, 10:24 AM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ The writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 37 & 38.... 📖____________"amm y...ya Zayyad, dama... dama...," Sai kuma tayi shiru. A hankali Zayyad ke karantar ta, yana son gano abinda yasa taƙi sake wa, sai da ya ɗauka cup ɗin ruwa yasha sannan yace "faɗi ko menene, zan fahimce ki insha Allah." A sannu-sannu tabar kujerar da take zauna ta taka har inda Zayyad yake kana ta durƙusa gaban sa, "ya Zayyad, nasan a a zaman mu dakai na ƙuntata maka, haƙiƙa na cutar da kai mijina, dan Allah ba dan hali na ba, ina roƙon ka da girman Allah ka yafe min, wallahi nayi nadamar hakan, ina so in wanke kaina sannan in zamo mata ta gari a gare ka, dan Allah ya Zayyad kayimin wannan alfarmar, bazaka ƙara samu na da wani halin banza ko bad intentions akan ka ba," ta ƙarashe tana haɗa hannayen ta biyu yayin da hawaye ya gangaro kan fuskar ta. Toh Zayyad dama bai taɓa riƙe ta a zuciya ba balle kuma har abin da take yi masa ya dame sa, yaji daɗi matuƙa da bai sha wuya sosai ba kafin ta sakko, dan ya yafe mata ba wani abu bane, ko da kuwa ba nadamar gaskiya tayi ba ya san wata rana zatayi, ƙoƙarin shi ɗaya yanzu, shine ya dasa soyayyar shi a zuciyar ta, dan har yanzu bashi da tabbacin son sa ya kamata.... Jin yayi shuru ne yasa Khans ɗagowa kana ta dafa kan cinyoyin sa tace "nasan yiwuwar hakan da wuya, dan Allah ya Zayyad ka taimaka ka yafemin, ta haka ne kaɗai zan iya samun rahamar Ubangiji na." Murmushi yayi wanda ya bayyana kyawun sa sosai sannan ya miƙe tsaye, hannayen sa yasa ya ɗago ta itama kana yace "ya kamata ki san cewa mijin ki bai taɓa ƙullatar ki a rai ba, balle kiyi tunanin idan kin nema yafiyar sa bazai yafe ba. Allah SWT ma muna masa laifi, kuma idan mukayi tubar gaskiya muka nemi gafara yana yafe mana, toh wanene Zayyad da bazai yafewa matar sa rabin ran sa? Na daɗe da yafe maki matata, sabida haka ki daina damun kanki ko kaɗan, sabida kada ki mana asarar wannan," ya ƙarasa yana shafa cikin ta daya tafi flat, tamkar ba ɗan mutum ne aciki ba. Da mamaki takai idon ta kan hannun sa dake kan cikin ta kana ta ɗago ta kallesa. A idanun ta ya gano tanbayar da takeson yi masa, hakan yasa ya saki dariya tare da manna ta da jikin sa, ya rungume kayar sa, ko ince kayan sa. A hankali yake mata raɗa (whispering) wanda ni kaina banajin me suke cewa, sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka kafin yaja hannun ta zuwa ɗakin sa, wanka ya shiga yayi ya haɗo da alwala, itama shiga tayi tayi alwalar yazo ya jasu sallah, zassha'awa🥰. A taƙaicen taƙaicewa dai tun daga wannan lokaci rayuwar auren su ya sauya gaba ɗaya. Kulawa babu irin wanda bata ba Zayyad, ta mai dashi shalelen ta tako wani fanni, sosai kuwa yakejin daɗin hakan, nan shima ya zage damtse wajen ganin ya faranta mata. Toh a kwana a tashi ba wuya wajen Allah, yau cikin Khans yayi kimanin wata biyar, dan har ya bayyana gashi ƙarami, idan ba ka lura da kyau ba bazaka gani ba, sosai cikin ya zauna ɗass acikin ta yayi mata matuƙar kyau. Zaune suke a harabar gidan sanye da kayan sport, Khans sai maida numfashi take kamar wadda tayi gudun famfalaki, Zayyad dake gefe sai dariya yake mata kamar zai kifa. Ruwan dake kusa da ita ta ɗauka ta ɓalle marfin gorar ta kafa kai, saida tayi rabin ruwan sannan ta ajiye tana sauke numfashi kafin tace "gaskiya baby na gaji, daga yau ka riƙa yi kai kaɗai, ni bazan iya ba, nayi wanda zan iya." Dariya kawai Zayyad keyi kafin yace "ke kika ce zakiyi ai, ni bance ki tayani ba." "Oh hakama zakace?" "Sorry ma'am, ki shirya da yamma insha Allah zamu fita." Tsallen murna tayi tana dariya, dan a tunanin ta gida zasuje, dan tunda aka sanya ranar auren Haseena da Ameesha bataje ba, "shikenan sai ka shigo, nikam kaga tafiya ta," ta ɗauki robar ruwan ta tayi ciki. Da kallon ƙauna kawai Zayyad ya bita kafin shima ya miƙe yabi bayan ta. Da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar kowannen su ya shirya tsaff, kasancewar su atampa atampa na takura mata yasa ta zumbula doguwar rigar ta ta Abaya golden color mai matuƙar kyau, ta riga sa shiryawa hakan yasa ta nufi turakar sa dan dubawa ko ya gama, "fatabarakallahu ahsanul khaliƙeen" ta furta sa'ilin da sukayi ido huɗu dashi, a kowace daƙiƙa ganin kyawun sa take yana ƙaruwa tamkar ba jinin Nigeria ba, cikin baƙin yadi mai santsi, hular kansa zanna bukar ce mai kwalliyar baki da fari, takalmi baƙi yasa kana ya kwasa wayoyin sa yana "muje koh?" Inaaa! Ai bata ma san da ita yake ba, dan ta daɗe da shagala da kallon sa, har ya matso dap da ita bata sani ba saida ya hura mata iska sannan ta dawo hayyacin ta, murmushi tayi tana mai sada kanta da ƙasa dan sosai taji kunyar sa, shima murmushin ya mata yaja hannun ta suka fita har harabar gidan. Brown ɗin Lexus RX 2018 suka shiga suka ɗau hanya. Sunyi tafiyar kusan mintina 30 kafin yayi parking a wani babban shopping mall ƙayatacce kuma haɗaɗɗe, fita yayi ya zagaya ya buɗe mata itama ta fito kana ya sawa motar lock suka shiga. Sassanyan ƙamshi ne kawai ke bugar hancin mutum tun taga ƙofar shiga, sun yi kusan tafiyar minti biyar sannan suka isa wani sashi na zallar kayan yara jarirai da dama sama dasu. Sosai Zayyad ya jida kaya kala-kala dan har saida Khans ta tausaya masa, tana tunanin fitar kuɗin, tayi-tayi dashi ya bari su riƙayi a hankali amma yaƙi, a cewar sa bayaso suna yawan zuwa siyayya, babu yadda ta iya haka ta ƙyale shi har suka gama, suka nufi inda zasu biya kuɗin, suna tsaye ana yi musu calculating yayin da Zayyad ke danne-danne a wayar sa. "Dr. Zayyad?" Wata ƴar matashiya da zata iya girmewa Khans ko kuma suyi sa'anni ta faɗa. Ɗagowa yayi dan ganin wanda ya kira shi ɗin, da mamaki ya amsa dan shi bai santa ba, balle yasan nata sunan. Ƙara washe baki tayi tace "sannu ya gida? Been a while." "Alhamdulillah" ya bata amsa a taƙaice. "Uhm baka gane ni ba ko? Sunana Zeenat Ibrahim Ɗangaske also knwn as Nina, nasan kasan Alh. Ibrahim ɗan gaske ko?" "Eh na sanshi." "Mahaifi na ne then, zaka iya tuna lokacin da kazo kayi treating ɗina da bani da lafi...?" Kafin ta ƙarasa Khans ta buga wani uban tsaki tayi waje, da ido Zayyad ya bita dan yasan kishi take. Tana nan tsaye wajen mota har Zayyad ya fito wanda saida ya kwasa mintina goma aciki kafin ya fito ɗin, har ya fito ya sanya kayan a booth ya buɗe motar bata kalla inda yake ba, saida yayi yayiwa motar key, suka bar harabar asibitin kamin yace "ranki ya daɗe, fushi kuma akeyi dani ne?" Wani abune ya kawo mata kuya yaƙi gaba yaƙi baya ya tsaya cak, tsabar baƙin ciki. Kamar ta fasa ihu haka takeji amma tayi shiru batace dashi komai ba, maganar duniyar nan Zayyad yayi amma ko uffan bata ce ba, bata ma san yanayi ba har suka isa gida. Bata jira ya gama daidaita parking ɗin bama ta ɓalle marfin motar ta fice, tanajin yana ƙwala mata kira amma tayi kunnen uwar shegu dashi tayi gaba, shima baiyi ƙasa a gwiwa ba ya mara mata baya, har takai bakin ƙofar ɗakin ta zata buɗe Zayyad ya cin mata tare da shan gaban ta, "haba babyna, kina ji tun daga waje nake kiran ki amma kiyi banza dani? At least u should have listen to my explanation first, before kiyi fushi haka, ita fa wannan yarinyar da kika gani mahaifin ta mutumi na ne, muna mutunci dashi sosai, sannan yakan kira ni in duba yaran shi in basu da lafiya, har dashi kanshi ba, so i once treated her lokacin da tayi wani ciwo, shine data ganni tayi min magana fa. Ni banma gane ta ba, dan kamar ma ba'a ƙasar take ba, coz tunda na duba ta lokacin ban kara ganin ta ba ko naje gidan, ki yarda dani habibty nothing more." Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "amma kasan da bakayi kyau haka ba da baza ta maka magana ba, kaga fa yadda nake ta wani washe maka baki kamar wani mijin ta, sai fari take maka kai kuma kana biye ta, yadda kayi kyau wadanda suka fita ma ai zasu tare ka." Sosai maganar taba Zayyad dariya matuƙa, dan saida yayi da gaske sannan ya danne dariyar shi, yasan halin kayar ki sarai idan har dariyar ta kufce masa akwai ƙura matuƙa, ƙara narke fuska yayi alamar rarrashi yace "extremely sorry bibty, kinsan so na hana ganin muni, maybe ma ke kadai kike ganin kyawu na. Yanzu ma ki rasa dawo zakiyi kishi sai wannan? Haba bibty karki bani kunya mana, ni Ina dake a doron ƙasa wace ce ta isa tace zata shiga tsakanin mu, ai tayi kaɗan, so kwantar da hankalin ki, Zayyad naki ne ke kaɗai." Murmushi ta sakar masa kana mai lafewa a jikin sa, dan sosai take samun natsuwa duk lokacin da take jikin sa, sun ɗauki kusan 2mins a haka, kafin a hankali ya zame ta a jikin sa yace "bari in shigo da kayan." Da toh ta amsa masa tana shiga ɗaki. Mayafin kan ta ta zare tana mai ƙure fanka dan sosai takejin zafi kamar ta kama da wuta, kayan jikin ta ta cire da zunmar shiga wanka, dai dai Zayyad ya shigo da kayayyakin, ganin haka yasa shi saurin cire nashi kayan a cewar sa tare zasuyi, dariya Khans tayi ta faɗa toilet ɗin ba tare da tace dashi komai ba, ganin haka nikam nace bari nayi musu sallama nikam... _____________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929231 [10/19, 8:28 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* 🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚 The writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_ 39 & 40.... 📖____________Haka rayuwar auren su ta cigaba da wakana cikin farin ciki, kwanciyar hankali da ƙaunar juna, Inda cikin Khans keta ƙara girma yana fitowa. Kamar yadda ya saba janta su fita da safe da kuma yamma, yau ma hakan ce ta kasance, tafe suke da yammacin ranar asabar suna tafe suna labari, Khans kam duk tafiyar minti ɗaya sai ta tsaya ta huta da haka har suka iso gida, kan kujera ta faɗa tana sauke numfashin gajiya, kafin ta miƙe ta shiga tayi wanka. A kusa tare suka fito, dan shima yana shiga ɗakin wankan ya faɗa, cikin skyblue jallabiya mai kyau da santsi ya fito, ta matuƙar amsar jikin sa inda ya sanya farin silipar ɗinsa ya fita, ba daɗewa sosai ya dawo ɗauke da takeaway, dan yanzu Khans ta dena girki, sakamakon duk abinda ta girka in ƙamshin ya buge ta saitayi amai, wani lokacin ma tana tsaka da girki zata kwara amai, hakan yasa Zayyad dakatar da ita har zuwa ta haihu. Babu jimawa sosai ya dawo, bai tadda ta a parlor ba, kitchen ya shiga ya ɗaukar masu plate kana ya shiga ɗakin ta. Zaune ya tadda ta kan sallaya ta mimmiƙe ƙafafu, murmushi yayi yace "mummyn babies duk gajiyar ce haka?" Bata rai itama tayi kafin tace "ai wlh ya Zayyad duk kai kaja min wannan gajiyar, ni babu inda zanje gobe gaskiya, wanda nayi a baya ma Allah yayi albarka, amma gaskiya na gaji, kullum mutum yayi ta yawo kan hanya, haba." Dariya ya kwashe da ita kafin yace "baby ke nake samawa sauƙi fa, kinsan Allah yanzu ma aka fara, daga nan har ki haifemin ajiyar dana baki, kinga daganan saiki daina, amma yanzu kam inaa.." ya ƙarasa yana buɗe musu abubuwan daya shigo dasu. Takeaway uku ne, ko wanne ɗauke da lafiyayyen abinci, ɗaya shinkafa da miya ne sai nama a sama, ɗaya kuma ɗauke da farfesun kaji yayin da ɗayan ke ɗauke da lafiyayyar waina da miyar egusi. Wainar dake ta tiriri tana fidda daddaɗan ƙamshi ran Khansa'u ya biya, sosai taji tana so taci, dan tana tunanin zai zauna acikin ta. Nan taja plate ɗin ta soma ci, kamar abin arziki har taci ɗaya da rabi taji ta fitar mata a rai ko ƙamshin ma batason ji, ture plate ɗin tayi tare da kawar da kai, Zayyad dake cin shinkafa ne ya ɗago yana "lafiya?" "Banason jin warin wainar, ka ɗauke plate di..." Ai bata ƙarasa ba ta soma amayar da abinda taci tamkar zata amayar da hanjin cikin ta, da ƙyar Zayyad ya samu Aman ya tsaya yana mai matuƙar tausaya wa matar tasa. Sosai cikin ke matuƙar wahalar da ita tunda ya shiga wata biyar, abin da batayi ba farkon cikin, da kanshi ya gyara wajen tare da taimaka mata wajen gyara jikin ta. Zama yayi kusa da ita na ɗan wani lokaci kana yace "yanzu me kikeson ci?" "Zogale" ta faɗa a marairaice tare da kwantar da kanta saman kafaɗar sa. Agogon hannun sa Zayyad ya kalla, ƙarfe 7:30pm ya gani, tunanin inda zai samu dafaffen zogale ya somayi, gashi shi ba iya dafawa yayi ba, dan samun zogale ba abune mai wahala ba, dan akwai shi a lambu, samun wanda zai dafa ne matsalar. *Mummy* ita ce ta faɗo masa a rai, nan ya miƙe tare da sanar da ita bari ya yaje ya dawo. "Toh" tace masa tana gyara zaman ta saman gadon. Tuƙi yake cikin ƙaguwa da son ya isa wajen Mummy kafin dare yayi, cikin lokaci ƙalilan kuwa ya isa, sosai Mummy tayi mamakin ganin sa yanzu daya kamata ace yana masallaci, dan Isha'i ake kira. Saida suka gaisa sannan ta tanbaye shi lafiya? Ƙeya ya sosa kafin ya sanar da ita abinda ke tafe dashi cikin kunya. Dariya sosai Mummy tayi kafin tace "su Zayyad sarakan kunya, toh sunkuyar da kan me kake kuma, ni kakejin kunya kome?" Shi dai Zayyad bai ce komai ba sai murmushin kunya da yake ta yi yana sosa kai. "Toh maza yanzu tashi ka tafi masallaci dan Aliyu bai daɗe da fita ba shima, nayi mamaki ma da baku haɗu ba, zan san yadda za'ayi ka kai mata zogale a daren nan, harda rama ma." Dariya yayi yace "yauwaaa Mummy na, shiyasa nake sanki, sai na dawo," ya faɗa yana mai ficewa. Da murmushi kawai Mummy ta raka shi tana mai jin ƙaunar sa a ranta. Yana fita itama Mummy ta miƙe ta fito tana ƙwalawa Tanimu mai gadi kira, da hanzari ya ƙaraso tare da ɗan duƙawa yana "ranki ya daɗe gani." "Yauwaa Tanimu, dan Allah zogale zaka samo min a lambu yanzu kaji, zanyi anfani dashi ne da gaggawa. "Ah haba hajiya, ai bama sai kin roƙa ba, yanzu za'a kawo." Ya karasa tare da miƙewa ya nufi lambu da sassarfa, ba daɗewa ya dawo ɗauke da zogale mai yawa kuwa, sosai Mummy taji daɗi, dan tanason aikin Tanimu bashi da wasa ko kaɗan. Cikin lokaci ƙalilan suka gama tsinke zogalen da gyarawa ita da Laure da Kubra masu aikin ta. Har ta dafa Zayyad da Aliyu basu dawo ba, hakan yasa ta danna kiran Zayyad, amsawa yayi tare da furta "muna hanya Mummy," daga haka ya katse. "Yaya daga zuwa masallaci kuma sai kuje ku zauna kamar masu gadin masallacin." Dariya duka su biyun sukayi kafin Aliyu yace "Mummy munje gidan mune fa, ba wani waje muka je ba." "Ku kuka sani, kai kuma ga zogalen nan ka ɗauka maza ka kama hanya ka koma gida, sannan ka dawo da yarinyar nan gida da zarar cikin ta ya shiga wata na takwas ta haihu a gaban mu, kar kace zaka karɓa haihuwar ta." Turƙashi, anya zan iya kuwa Mummy? ya faɗa a ransa, a zahiri kuma yace "toh Mummy na gode." Ya ɗauka yana fice wa. Ba shi ya isa gida ba sai kusan ƙarfe 9 na dare, a parlor ya tadda ta tana zaman jiran sa, riƙe da ayaba a hannun ta taci kwatar ayaban. "Madam, ga zogalen." A gajiye ta ɗago taja warmer ɗin zogalen gaban ta, buɗewa tayi tana yatsine fuska, lafiyayyen haɗi Mummy tayi mata, harda ƙarin lettucce (latas) a akai, da yankakkiyar albasa haɗi da tumatir da sweet papper da sauran su, tururi kawai yake fitar wa mai daɗin ƙamshi. "Spoon" ta faɗa tana mai da kanta kan kujerar, a hanzarce Zayyad ya miƙe ya nufi kitchen, ba daɗewa ya dawo ɗauke da cokali ya miƙa mata. Ci biyu uku tayi ta ture, dan ji take idan ta cigaba daci zata iya yin amai. "Yadai bibty, mai ya faru?" "Ba naci" ta furta a taƙaice. "Baki ci kuma? Haba Khans, yanzu Mummy ta dage ta dafa miki sannan kice ba kici! Bayan kuma ke kikace kina so!" "Ni nace ina so dear, amma yanzu banaso, dan Allah ka ɗauke, wlh ko warin shi banson ji. Ni kaga banason yawan hayaniya ma, dan Allah kayi shiru. Da ido kawai Zayyad ya bita, dan ta soma bashi mamaki ma, ace mutum yana buƙatar abu, kuma a kawo masa yace bayaso? _Haba Zayyad sai kace ba likita ba, kasan ko wani ciki da irin nasa laulayin ai, sai kayi mata uziri_, wata zuciyar ta bashi amsa. Jan warmer din yayi gaban sa ya ɗibi spoon ɗaya yakai bakin sa, tsabar daɗi ma ya hanashi magana saida yayi spoon uku kafin yace "bibty yanzu wannan kike cewa baza kici ba, lallai anyi babu ke, ashe haka yake da daɗi dama, anya ba gidan Mummy zan koma da zama ba kuwa? Kullum ta riƙa dafamin.... "Ya salaam" ta faɗa tana dafe kanta, daga bisani kuma ta miƙe tayi hanyar ɗaki ta barshi a wajen. "Ohh tafiya ma zakiyi ki barni?" Bata bi takan tanbayar shi ba tayi shigewar ta ɗaki, dan ko kaɗan batason furta wani harafi balle kuma kalma. Kan gado ta haye bayan ta sauya kaya izuwa na bacci, ta kuma kashe bulb ta bar side lamp kawai, lallausan duvet ɗin gadon taja ta kima shi a kanta. Bayan wasu ƴan daƙiƙu da shigowar ta ɗakin Zayyad ya biyo bayan ta, _"toh fah_" ya furta a ransa kafin kuma a zahiri yace "abin babba ne, shi ne zaki kwanta amma baza kice min inzo mu kwanta ba?" "Khans kuwa tuni bacci yayi gaba da ita, bata ma san yanayi ba." Ganin tayi shiru ne yasa shi ƙarasowa inda take kwance, fuskar ta ya leƙa yayin da ya sauke idanun sa kan luntsuma-luntsuman nata idanun masu ɗauke da zara-zaran eyelashes mai cika da baƙi, a hankali take sauke numfashi tana jan wani. Miƙewa yayi tare da cire jallabiyar jikin sa ya faɗa toilet, wanka yayi ya fito kana ya shirya cikin singlet da boxer ya haye gadon shima. Kamar a mafarki Khans ke jin ana shafa mata jiki har ta farka, ganin Zayyad manne da ita ne yasa ta haɗe rai tace "ya Zayyad dan Allah ka barni inyi bacci." "Toh ni me na miki kuma? Kar ki damu, yi baccin ki ƴar flower ta" ya faɗa yana shafa goshin ta zuwa lallausan gashin kanta, a haka ta koma baccin, ganin haka nima na tattara alƙamina ina maiyi musu fatan asuba ta gari. ★★★★★★★★★★★★ *2 MONTHS LATER* Da ƙyar take takawa har ta iso kan three-seater ɗin da Zayyad ke zaune, a hankali ya taimaka mata ta zauna ya jingino da ita jikin sa, sai sauke numfashi take tamkar wadda tayi gudu, cikin tausayawa Zayyad yace "yaya jikin naki?" Murmushi tayi tana mai ƙara lafewa jikin sa tace "da sauƙi hubbee, amma ba ya jiki ake cewa ba, ya nauyin jiki ake cewa." Dukkan su dariya sukayi kafin Zayyad yace "toh ya ƙarfin jiki?" "Yauwa ko kai fa, Alhamdulillah...." Wayar Zayyad dake ƙara ce ta kashe ta, lovely mom ne ke yawo kan screen ɗin, kamar bazai ɗaga ba, dan baya so tace ya kawo Khans gida wallahi, sai kuma ya ɗaga bakin sa ɗauke da sallama, amma mishi tayi da "wa'alaikumus salam." Saida suka gama gaisawa kafin Mummy tace "Zayyad yaushe ka zama mai kunnen ƙashi ne?" Kallon Khans yayi suka haɗa ido, ko wannen su fuskar sa ɗauke da mamaki, "Mummy me nayi kuma?" "Oh me kayi ma kake tanbaya na? Toh ka dawomin da ɗiya ta gida yanzun nan, kaji na gaya maka." Daga haka ta kashe wayar ba tare data jira amsar Zayyad ba. Samm Zayyad baiji daɗi ba ko kaɗan, haka ya haɗawa Khans kayan ta, da kuma na baby haɗi da wanda zasu kai asibiti lokacin haihuwa, tamm ya cika booth ɗin da kaya suka tafi, bashi ya baro gidan ba sai ƙarfe 10:30 na dare, shima saida Mummy ta kore shi, haka yana ji yana gani ya tafi ya bar Khans sai ɗacin rai yakeyi, ita kuwa Khans me zatayi in ba dariya ba..... _____________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/22, 8:31 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* 🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚 The writer of: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_ 41 & 42.... 📖____________Yana dawo wa gida direct ɗakin sa ya faɗa tare da nufar toilet, wanka yayi haɗi da alwala sannan ya fito. T-shirt da three-quarter ya sanya kana ya soma nafila, ba shi ya kwanta ba sai kusan ƙarfe 12:30, ji yayi gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idanun sa, lokaci ɗaya yaji yana tsananin begen matar sa, lokaci ɗaya yaji wani matsanancin kewar ta ta kamashi, juyi kawai yake akan gadon badon yanajin daɗin kwanciyar ba, ji yake tamkar wanda yayi shekara dubu babu ita. Wayar sa ya janyo tare da danna kiran Khans, amma a kashe! Tsaki yayi gami da jefar da wayar gefe haka har bacci ɓarawo ya sace shi. Toh a ɓangaren Khansa'u ma hakan take, ji take kamar tayi tsuntsu ta koma wajen mijin ta, dan tayi kewar shi sosai, ji take baccin ma ba lallai ya mata daɗi babu Zayyad ɗin ta kusa da ita ba. Duk wani motsi nata Mummy na lura dashi, kuma tuni ta harbo tsuntsun ta, dan tasan kewar mijin ta ke damun ta, "wai Khansa'u baza ki kwanta bane? Sai faman juyi kike kamar ana tsikarin ki." Mummy data gaji ta tanbayi Khans. Murmushin yaƙe Khans tayi kana tace "Mummy baccin ne kawai bai zo ba." "Be zo ba ko baki kira shi ba?" Ita dai batace komai ba ta ƙara juyawa kamar wadda tayi shirin bacci. Miƙewa Mummy tayi ta kashe mata wutar ɗakin ta fita. Ai kamar jira take Mummy ta fita, ta miƙe tare da ɗaukar wayar ta, number Zayyad tayi dialing harya katse ba'a ɗaga ba, ƙara dialing tayi still ba'a ɗaga ba. Kamar a cikin bacci Zayyad kejin wayar sa na vibrating, koda ya ɗakko wayar matar sa yaga ta kira har sau biyu yasa shi saurin dialing, ai kam bugu biyu ta ɗaga tare da sakar masa kukan shagwaɓa, jugum yayi na ɗan wani lokaci kana yace "baby ni ya kamata nayi kuka ai ba ke ba, ni da Mummy ta jamin kwanan kaɗaici ba tare dana shirya ba, kinji gidan kuwa? Tamkar prison, babu daɗi wlh, nayi kewar ki to the essence that no words can express it." Ajiyar zuciya Khans ta sauke tare da tausayin mijin nata kana tace "ya Zayyad nima anan ɗin haka yake, wlh bacci babu kai kwata-kwata babu daɗi, nayi kewar ka nima matuƙa." Sosai suka taɓa hira ba laifi cike da ƙauna da kewar junan su, sai kusan 1:30am suka kashe wayar. Washe gari da sassafe saiga Zayyad a gidan Mummy, baki buɗe Mummy ke bin sa da ido harya ƙaraso, gaida ta yake amma inaa bata ma sani ba, tsabar mamakin daya cika ta. "Zayyad" ta furta cikin tabbatar wa. Ƙasa yayi da kansa kafin ya ƙara cewa "ina kwana Mummy?" "Hmm Zayyad ni kam kafi ƙarfi na, sai dai na zuba muku ido kuma." Shi dai kunya ce ta lulluɓe shi sosai kamar ƙasa ta tsage ya shige. "Oyoyo babban yaya" Ameesha data fito cikin shirin makaranta ta faɗa, murmushi ya mata kawai suka gaisa ita kuma ta nufi dinning dan tayi breakfast. Mummy kam miƙewa tayi ta kama hannun Zayyad ɗin, bata tsaya ko ina dashi ba sai ɗakin Khans da har lokacin bacci takeyi, "ku gaku tantabaru koh? Toh ku cinye juna ƙarewar soyayya" tana gama faɗi tayi waje tare da ja musu ƙofar. Daɗi kamar zai sheƙe Zayyad ya ƙarasa har inda take kwance cikin blanket, shafar sumar kanta yayi yana lumshe ido, a hankali take buɗe idon ta har ta sauke su kan Zayyad, ihu ta saki haɗi da dariya yayi saurin toshe mata baki kafin mom ta leƙo tace wani abu ya mata. Zare ta a jikin sa yana "maintain mana, kar kisa Mummy tazo ta katse min jin daɗi." Murmushi ta kuma yi kafin tace "kamar kasan mafarkin ka nakeyi." "Wow! Bani labari." "Ba wannan ba dai, kazo ɗauka na ne?" (Ni kam nace kuji marasa kunyan mutane🙈🙈) "Hmm, kinsan ko me zai faru Mummy bazata bari in tafi dake ba, dama dai Ummi ce da sauƙi." Marairaicewa tayi tare da langwabar da kanta kan kafaɗar sa tace "toh sai yaushe zamu koma gida kenan?" "Sai kin haife wannan inji Mummy" ya faɗa yana shafa ƙaton cikin ta. Hira suka ɗan taɓa zuwa ƙarfe 8 sannan ya fito tana biye dashi, sauri-sauri yake domin yana da patients sosai a asibiti, da kallo kawai mom ta bisu dan su suke abin amma ita kejin kunya, har dai Khansa'u ta dawo Mummy ta galla mata harara, dariya Khans ta kwashe dashi tana shigewa ɗaki, dan baccin ba sakin ta yayi ba. Gida ya nufa direct, yana shiga wanka yayi ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya ya fita, zuwa 9:20 ya isa asibitin ya soma gudanar da abin da ya kaishi. *THREE WEEKS LATER* Tafe yake kan hanyar sa ta zuwa duba lafiyar matar sa kamar yadda ya saba kullum safe da yanma, yau ya kama Friday, kasancewar baya komawa asibiti duk ran Friday. Da isar sa gidan da Khans ya fara tozali, ta shirya tsaff cikin maroon Abaya da ratsin baƙi mai matuƙar kyau, yayin da ta ƙawata fuskar ta da murmushi mai susutu mijin nata. Tsaye yayi yana bin ta da kallo har ya sauke duban sa kan cikin ta da yake haihuwa yau ko gobe, "oya u knw we don't have time, tashi mu tafi" Zayyad ya faɗa yana miƙa mata hannu. Kamawa tayi ta miƙe suka nufi fita yana riƙe da ita har suka isa parking lot, gidan gaba ya buɗe mata ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga mazaunin direba yaja suka fice. Bai tsaya ko ina da ita ba sai gidan su, suna shiga suka yada zango a parlor, kallon gidan Khans ta somayi tana mamakin yadda ya gyaru tsaff tamkar da mace a ciki, bata ankara ba taji Zayyad ya rungumo ta ta baya, wani zazzafan nishi ya soma sauke mata akan wuyan ta kafin ya furta "i miss u so much bibty" ya ƙarasa yana ɗaukar ta cak zuwa ɗakin sa, ji yayi ta ƙara wani nauyi sosai da ƙyar ya iya ƙarasawa da ita kan gado, saida ya sauke numfashi kafin ya soma romancing ɗin ta zuwa wani lokaci da akalar tasu ta sauya salo. A gurguje ya taimaka wajen yin wanka shima yayi kana suka fito, gida ya maida ta har zuwa lokacin kuwa su Mummy basu dawo ba, nan ya zauna suna ɗan taɓa hira, duk da rabin hirar duk shi yakeyi, lura da yadda take cijan leɓe ne yasa shi matsawa kusa da ita yana tanbayar ta ko lafiya? "Babu komai" ta bashi da murmushi kan fuskar ta. Shigowar Mummy ce ta sashi saurin sakin ta tare da matsawa kusa da ita, yana mai sada kanshi da ƙasa kafin kuma ya zame daga kujerar yana gaida ta. Cikin fara'a ta amsa masa tana mai faɗawa kan kujera, dan ajiye take, miƙewa Zayyad yayi yayiwa Mummy da Khans sallama ya tafi. Tun Khans na iya daurewa da ciwon da marar ta keyi har ta gagara saida ta bayyana, Mummy bata kawo komai ba, dan a zaton ta normal ciwo ne, ruwan wanka ta haɗa mata na magunguna da kuma nasha tasha tayi tsarki da wanka dashi. Bai wani tafi ba, amma ya rage babu laifi. Wasa-wasa har kwana uku Khans na fama da matsanancin ciwon mara, sai da ta soma naƙudar da bata shirya ba a kwana na ukun. Zayyad Mummy ta kira cikin kiɗima ta sanar dashi, babu jimawa kuwa sai gashi, dan yana asibiti lokacin, sosai ya tausaya mata ganin yadda ta fita hayyacin ta gaba ɗaya. Asibiti suka nufa tare dasu Mummy, gwaje-gwaje ya somayi mata, nan take ya gano da ciwon yakai kusan kwana uku tare da ita, tunani ya somayi tun ranar da sukaje gida, "ya salaam* ya furta a ransa suna mai cigaba da bata taimakon gaggawa. Sosai take shan baƙar wahala ga kuma sakamako daya nuna ba haihuwa bace, nan take Zayyad ya soma jin raɗaɗin zafin ciwon ya jikin sa, domin yama rasa ta yadda zai soma ceto ranta dana abinda ke cikin ta cikin gaggawa gudun samun matsala. Shirya ta yayi tare da umartar Nurses su shiga da ita theater room kafin ya dawo, yana gama faɗi ya fice tare da nufar office ɗin sa.... _____________________________________________✍️ Daga alƙalamin *BABYLORH* (shalelen women writers) 07069929131 [10/27, 8:23 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍 _(the famous arabic poetess)_ By 💍BABYLORH💍 *(shalelen women writers)* 🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚 Marubuciyar: 1. *RUSHDAH* 2. *MARAICI NA* loading..... 3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_ 43 & 44.... 📖____________A gurguje nurses suka fito da ita suka nufi ɗakin theater, ba jimawa shima ya dawo tare da wata doctor suka shiga, wahala iya wahala Khans tasha, a gurguje nurses ɗin suka fito da ita zuwa theater room, ko ina daga sassan jikin ta zufa ne ke fita. Babu jimawa shima Zayyad ya dawo tare da wata doctor mace cikin shirin yin theater. Sosai Doctor Na'eema da Zayyad ke nuna bajintar su wajen ciro babyn, amma inaa abu na nema ya zarce tunanin su, da ƙyar suka sami damar zaro kan yaron har suka ciro shi. Sun daɗe sosai matuƙa, kafin komai ya kammala, Zayyad da kanshi ya gyara ta tsaff sannan aka wuce rest room da ita. Ba ita ta farka ba sai bayan kusan awa biyu bayan Cs ɗin, zuwa lokacin kuwa dangi duk sun hallara, su anty Jumayna, Ummi da yaran ta su Haseena da auta Ayeesh da Ameesha, kai mazan ma ba'a barsu a baya ba, dukkanin su sunyi jugum suna jiran farkawar ta. A hankali ta soma buɗe idanun ta sai kuma ta rufe har dai ta Idasa buɗe su, duk da bawai sosai ta buɗe idanun nata ba, sabida hasken daya gauraye wajen ya kuma yiwa idanun ta nauyi, hannun ta ta ɗaga ta sauke shi akan cikin ta a hankali, jin babu cikin yasa ta kai kallon ta kan cikin dan tabbatar wa idanun ta. Ummi dake gefen gadon zaune ta kalla da idanun ta da suka kumbura sukai jajir, sai kuma ta maida duban ta ga Mummy dake kan kujera hannun ta riƙe da jariri, sai da tabi dukkan mutanen wajen da kallo kana tayi ƙarfin halin furta "Ummi ya Zayyad fah?" ta faɗa cikin disasshiyar murya mai cike da rauni da tausayi. Kafin ta rufe bakin ta sukaji sallamar Zayyad ya shigo, hakan yasa kowa yayi ba tare daya bata amsa ba, tunda ga amsar tambayar tata ta gani. Ƙarasawa yayi har inda take kwance, tare da kama hannun ta wanda ke riƙe da carnular, a sannu ya zare mata kasancewar ruwan da aka sa mata ya ƙare, sai da ya faki idanun Ummi da Mummy sannan ya kashe mata ido ɗaya tare da sakar mata murmushi. Kanta kawai ta iya kawar wa gefe, dan magana, dariya ko murmushi bashi da hali a halin yanzu. Kwanan su takwas a asibiti suka dawo gida, zuwa lokacin Khans ta ɗanji sauki babu laifi, nan aka soma shirye-shiryen yiwa baby (Muhammad Al-ameen) taron suna. Sosai kuwa Daddy da Abba haɗi da shi Zayyad ɗin kansa suka nuna one love wa jikan su jinin Zayyad. Washe gari aka shirya liyafar gudanar da taron, kuma Alhamdulillah komai ya tafi yadda ya kamata kuma yadda aka tsara, inda yaro yaci sunan mahaifin Zayyad kuma mahaifin Khans, amma suna kiran shi (Areef). Bayan suna da sati biyu bikin Haseena da Ameesha ya iso, anyi shagali kamar yadda suka saba gudanarwa a familyn, wato ɗaurin aure da walima kawai, (sauran Ayeesh, Allah nuna mana naki😌) Ameen. *7 MONTHS LATER* Zaune suke a dinning suna dinner cikin so da ƙaunar juna, Areef keta tsala ihu dole sai ya hau kan table ɗin, Daddy Zayyad🙈 ne ya miƙe tare da miƙa masa hannu, ai da da kuwa ya tafi yana dariya wanda ya bayyana haƙwaran sa guda takwas. Ciki suka shiga, kasancewar Zayyad dama ya gama cin nashi, Khans ce dai sai yanzu take ci, tana gamawa itama ta mara musu baya, koda ta shiga wasa ta taddasu sunayi, Areef sai ƙyaƙyata dariya yakeyi, kamar me!! Washe gari ya kama Sunday. *3:00 PM* Cikin wata maroon shadda Khans ta shirya ita da rabin ranta kuma zuciyar ta gaba ɗaya wato Zayyad, sunyi kyau matuƙa, dan sosai kayan ya karbi jikin su, Areef kam cikin riga da wando ƴan kanti ta shirya sa, sakar baki nayi ina kallon Areef ganin yadda ya mugun yiwa kayan kyau, ga tsantsar kamannin sa data bayyana da Zayyad, sai kuma farin Khans daya ɗakko ya sirka da kalan hasken baban sa, ya bada wani kala na daban mai matuƙar kyau, inda suka bambanta da Zayyad, shi yana da san wasa da magana, shi kuma Zayyad shiru-shiru ne. Tare suka fito Zayyad riƙe da Areef a hannu, ita kuma tana riƙe da side bag ɗin ta, mota suka shiga Zayyad yaja su, basu tsaya ko ina ba sai Ado Bayero mall. A 360 Zayyad ya figi motar zuwa inda zai daidai ta parking ɗin sa, sosai hankalin jama'a ya dawo kansu, suna jiran fitowar mai motar ganin yadda yake driving kamar zai tashi sama, kasancewar glass ɗin tint ne shiyasa basuga wanda ke ciki ba. Zayyad ne ya fara fitowa cikin salo da ɗaukar ido, yana takun sa na ƙasaita har ya ƙaraso mazaunin gaba ya buɗe tare da karɓar Areef daga hannun ta, bayan kamar minti 1 itama ta fito nan suka sakarwa junan su murmushi mai cike da saƙonni, kaii abin sai wanda ya gani. A tare suke ɗaga ƙafa su sauke, tafiyar su kaɗai ya isa ya yaja hankalin ka wajen kan su, fuskar mutanen wajen kaɗai ya isa ya bayyanar maka da yadda suka birge kowa sannan suka dace da juna. Ɓangaren play ground suka nufa first, nan Areef ya soma zillo kamar zai ƙwace kanshi, wajen wasa da mota suka nufa tare da sanya shi a ciki, shikam banda jin daɗi babu abinda yakeyi, dan Allah ya zuba masa wayau kamar wanda ya shekara, sosai kuwa yayi wasa, camerar Zayyad kamar zata fashe tsabar hotuna. Kasancewar Zayyad nason wasan tsere yasa suka nufi inda ake hawa doki, daidai wasu suma da bazasu wuce sa'annin Zayyad ba suma sunzo kan karawa dashi a harkar tseren, nan kuwa suka shirya ko wanne yahau dokin sa, ɗaya zuwa uku aka ƙirga ai kam dawakai suka soma gudu, wani kuka da dokin Zayyad yayi haɗi da miƙewa yasa ilahirin wajen ɗaukar ihu da tafi, yadda dokin Zayyad ke gudu kaɗai ya isa ya tabbatar maka da ƙwarewar sa a harkar, dan duk wani ja da yake yiwa dokin yasan inda ya dosa. Zayyad shine yazo first, inda wa'incan sukayi bracket (2). Banda murmushi babu abinda ke bayyana a fuskar Khans harya ƙaraso inda suke, hannu yasa ya karɓi Areef suka nufi wajen sallah. Suna yin sallah suka nufi wajen cin abinci, basu suka baro wajen ba sai kusan 6 tare da shopping ɗin da Zayyad yayi musu. ★★★★★★★ A kwana a tashi ba wuya wajen rabbussamawati wal ardi, yau Areef ya cika shekara ɗaya a duniya, ya ƙara wayau yayi haske yayi ɓul-ɓul abunsa zassha'awa. Tafe suke kan hanyar su ta dawowa daga gidan anty Jumayna, hold up daya cunkushe hanyar yasa Zayyad bai bi ba, yabi ta cikin layika kawai, karap idanun sa suka sauka kan wasu mata almajirai da suke bara a bakin hanya, samun kansa yayi dason taimaka musu, hakan yasa yayi parking ya kuma fita a motar, su su biyar ne a wajen kuma saida yabi ko wannen su da 2k, ya juya da niyyar tafiya kenan yaji an ambata sunan shi. *"Zayyad"* Cak ya tsaya na ɗan wani lokaci sannan ya juya da niyyar son ganin mai kiran nasa, wata baiwar Allah ce matso daga inda take zaune tana hawaye, "Zayyad kai ne!" Ta kuma furtawa a karo na biyu. Tsugunnawa yayi daidai tsawon ta, kasancewar a keken guragu take yace "baiwar Allah kin sanni ne?" Kukan da yaci ƙarfin tane ya hana ta magana, Zayyad baiyi yunƙurin hana ta ba, a cewar sa kukan zai iya sama mata relief. Ganin lokaci na tafiya yasa Zayyad faɗin "baiwar Allah baki ce komai ba." "Darl lafiya kuwa?" Khansa'u da isowarta kenan ta faɗi. Ɗaga mata hannu yayi, alamar shima bai sani ba. Ɗagowa matar tayi tana faɗin "haƙiƙa sakayya ba sai anje lahira mutum ke gani ba, ni shaida ce tun a gidan duniya mutum ke ganin sakayyar shi, haƙiƙa wanda yaɗau duniya gidan zama tabbas zata koya masa darasi. Na cutar dakai Zayyad, na azabtar dakai, dan Allah ina mai haɗa ka da Allah kayi min afuwa ka yafe min ko Allah zai dube ni da idon rahama." Ta ƙarasa tare da rushewa da wani kukan. Tunda ta soma magana Zayyad ya sunkuyar da kai, dan sai a lokacin ya lura da Karima ce matar baban sa, hannu yasa ya share zazzafan hawayen da suka biyo kuncin sa tamkar zasu ƙona fuskar sa. "Ban taɓa riƙe ki a rai ba, kuma na ɗauke ki tamkar mahaifiya ta data haife ni, na daɗe da yafe miki duniya da lahira, Ubangiji Allah ya yafe mana baki daya kuma ya gafarta mana." Daga haka ya miƙe tare da kama hannun Khans suka nufi mota, yana jin kukan ta dake ɗauke da tsantsagwaron nadama amma bai tsaya ba yaja motar sa zuwa gida, har suka isa babu abinda ya shiga tsakanin su na magana. Khans da kanta ta kira Ummi ta sanar da ita komai, Ummi dai batace komai ba, illa fatan shiriya da tayiwa masu hali irin nata, da kuma fatan Allah ya yafe mata, hatta su Daddy da aka gaya mawa suma addu'a da sukayi kenan. Nan kan familyn ya ƙara haɗuwa, gefe guda kuwa sai ƙara haɓɓaka sukeyi, dan Haseena da Ameesha dukkanin su su sauke ribar so suma, inda Haseena ta samu mace Ameesha ta samu twins duka maza. Abin sai godiyar rabbi. *ƘURUNGUS* Anan na kawo ƙarshen wannan littafi nawa mai suna *KHANSA'U* Ina mai bawa readers haƙuri, da rashin typing da banyi ba kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon wani uziri mai girma. Ina ƙara bawa readers haƙuri da yayyanke musu labari da nayi, hakan ya faru ne sabida gujewar yawan pages, Dan ba kowa ke jurar karanta littafi mai yawa ba. A ƙarshe ina mai roƙon Allah daya yafemin kan kurakuren da nayi acikin wannan littafi, tare da fatan zaku kasance tare dani a littafai na na gaba masu suna: *HALIN ƘADDARA* da kuma *ƳAR LESBIAN CE*🙏 Fatan alkhairi ako da yaushe fans, Ina ƙaunar ku. *BABYLORH* CE😎 07069929131