[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....✍🏼``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* PAGE..........1 TO 5 Tuk'i yake cikin nutsuwa da alamarsa yana cikin nishadine wakar larabawa yakeji yanabi yana gyada kansa da murmushi akan fuskarsa Wayarsa ta dau tsuwwa kirane ya shigo saida ta kusan katsewa kana ya dauketa nan take yasha mur fara,ar fuskarsa ta gushe lokaci guda bakin ciki ya xiyarceshi baya qaunar mu,amalarsa da yr nacin nan Lubna sonshi take tamkar ta haukace shikuma kinta yake wulakanta ta yake amma taki hakura Yaja tsaki tareda ajiye wayar amaxauninta ta sake kira akaro na biyu yakatseta tareda kashe wayar gabaki daya Adai dai round about na danjar dangi yaja ya tsaya da saurinsa ganin wasu makafi zasu gifta ta gaban motarsa tareda yarsu data rike musu sanda Allah ne yataimaka dabai gogesu ba yakurawa yarinyar ido fara ce kal gashinta har gadon baya bazata wuce shekara sha tara sha takwas ba amma dai baxatai ashirinba danma tanada garin jiki Ta gaban motarsa suka gifta sukaje gindin motar dake gefensa suna bara Take yaji zuciyarsa ta tsinke tausansu yaratsasa gasu dai fes dasu amma da alama babu karfi ba matallafi Yarinyar ta dauke masa hamkali jinta yai har kokon ransa kyanta yafi tafiya dashi tamkar balarabiya haka ya fasaltata Dai dai glass din motarsa sukaxo suna barar Ya zuge glass din ahankali take Allah yabashi sa,a suka hada idanu da ita baisan sanda yasakar mata murmushiba " Allah ya tsare Allah yak are mallam ataimaka mana da sadaka sbd Allah da annabi. Muryarta ta sukurkutar masa da zuciya dan bakinta kawai yake kallo Dubu daya ya miko mata yana murmushi Da rawar jiki ta karba fuskarta cike da mamaki Tace " banida canji " "rike duka " yammata nabaki sadakarta sbd Allah da annabi kinji. Da gaggawa tahau gyada kanta fuskarta da fara,a alamun jindadi ya ziyarci ranta tace " Allah ya karba ya biya bukata. Kafin yai magana ta janyo hannun iyayenta dake gefenta sunyi gaba Yabisu da kallon tausayawa tabbas saiya taimaka mata kota wata hanyar ne domin zuciyarsa ta kamu danja tai musu alamar tafiya haka yaja motarsa yai gaba yana aiyano yarinyar aransa domin yaci alwashin saiya dawo gareta kota halin k 'akane *****- ****** ****** Sai da Dr ma,aruf yajera kwana uku yana xuwa shatale talen dangi gun danjar nan duk don yaga wannan yr makafin amma baiganta ba sai hankalinsa ya tashi matuka gashi baisan wanda zai tambaya ba tunda ba sanin sunanta yai ba Akwanakin ukun nan shiyasan halin daya kasance domin yanda yake ganin rana haka yake ganin dare Fuskarta kawai ke mata gixo muryarta na masa burari akunne Akullum sukuku yake wuni ko agida saida aka gano shi domin mahaifiyarsa gaba ta tusashi da tambayar meya faru dashi kwana biyu taga canji atare dashi B 'oye mata yai domin ba yanxu yakamata tasaniba balle yasan ma babu fanin sanin ga mum din nasa tunda yasan halinta ba kaunar mu,amala da talakawa takeyiba gashi kuma tana so ya auri diyar kanwarta Lubna Ko agun aiki baya da kuxari aikinma gefe yake dashi dan dai babba ne babu me takura masa balle abashi quiry. Abokinsa Dr lurwan kawai yagayawa matsalarsa shima saida ya matsa kana yagaya masa Aiko dayake shi din me damuwa da damuwar sane tuni akwana na hudun da baijeba yatusashi agaba suka je bakin danjar Ckn sa,a suka hangosu daga nesa Dr ma,aruf nahangosu yaji wani sanyi aransa da murnarsa ya nuna wa Dr lurwan su da hannu Dayake ackn go slow ake ta koina acunkushe gun yake da abun hawa Gashi bata bangarensu makafin suke ba Kusan minti sha biyar ba,a basu hannu ba Gashi yadaina hango yarinyar da iyayan nata Ko da cunkoson ma yarasu da aka basu hannun gefe sukai farking suka hau hange ko Zasu ganosu amma abin mamaki ko kusa ko alama babu makafin nan da yrsu Ran Dr yai matukar baci yahau tsaki Dr lurwan shiya kira wani me saida biscuit yahau tambayarsa makafin nan matashin yace dasu ai yanxu suka tsallaka titi suka tafi. Dr lurwan yace " ko kasan gidansu kanina? girgixa kansa yayi yace " walh bansaniba don basu dade da fara xuwaba bakine. Dr ma,aruf ya doki gaban motar yana jan hucin takaici Lallabashi abokinsa yayi suka hau mota suka tafi akan gobe zasu dawo... *Auntyn S &S*💘 & *Fresh Ummiey xeey* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....✍🏼``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* _Auntyn S & S_ *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *PG. 10-15* Jikin Aminatu yai matuqar sanyi jin yaron yanuna mata wanda ke kiranta take tafassara wani abu ckn ranta a dabarance saita nemi gindin bishiya ta zaunar da makafin iyayan nata tace dasu tana xuwa Ta nufi inda Dr ma,aruf yake da takunta ckn nutsuwa tafiya take gwanin burgewa tana wani rangaji fakistan ne ajikinta duk da sunsha jiki amma sunmata kyau Yakurawa surarta idanu yana hamdala ga Allah " tabbas anyi halitta anan! Yafada ckn ransa da sallamata isa gareshi yayindashi yaxurfafa a tunanin Aminatun Saida tai masa sallama sau biyu kana hankalinsa yadawo jikinsa Yayi murmushi yana kallonta yace "Ranki ya dade zinariya barkanki da isowa " " ZINARIYA! kuma? Ta tambayai kanta Tayi mamaki da saurinsa hakan zai mata inkiya me dadi Saitayi farin ckn hakan har taringa ayyanawa aranta inama dai sonta xaice yake ai da kakarta ta yanke sa,a da burinta ya cika Gashi kyakykyawa gamasu gdn rana wanda kullum take addu,ar Allah yakawo mata me nera wandaxata huta iyayanta su hutada bakar rayuwa me dauke da bakin talauci Harkasa ta gaidashi fuskarta dauke da murmushi Shima murmushin yake yace "ranki ya dade Allah yasa nakasance da sa,a akan abinda nazo mk dashi domin abin me muhimmancine. takama baki tace "to! Wannan wane abune haka!? ya fito sosai daga motar tareda jingina jikinta yace "dafatan dai kin " shaidani? Ta Girgiza kanta tace "ko kusa ban dau muryaba bankuma gane kaba. Yai jim kana yace "Amma dai baxaki mance da mutumin daya baki sadakar dubu dayaba kwana hudu daya wuce ko.? Tayi murmushi data tuna tareda daga kanta tace "na tuna kam,kamar ma kai ko? Tafada tana kare masa kallo Ya gyada kansa yace "kwarai nine dafatan banyi laifin gaggawar dawowa gareki ba domin baxan boye mk ba nashiga wani hali akanki zuciyata ta azubtu akanki ckn kwanakin nan natakura da tunanin ki dafatan zan samu karbuwa ? duk da jin hakan yaiwa Aminatu dadi amma saitaji wata kunyarsa ta rufeta kamar ta tsaga kasa ta shige dan wani kwarjini yai mata kawai saita rufe fuskarta da mayafinta Ya fahimceta to amma yanason jin ta bakinta dan haka saiya canxa salon akalar hirar da cewa "ikon Allah ban karbuba knn da har naga anrufe fuska lallai kice namiki tsufa kenan? Tayi saurin girgixa kanta " a,a walh bahaka bane " to yane ?ai inhar ana sona to abude fuska inyi tozali da murmushi mekyau Basaita saki mayafiba tana murmushi amma takasa hada ido dashi Yaji dadin hakan dama son mace me kunya sai shima yahau murmushin yace "madallah naji dadin hakan to yaya sunan zinariyar nagaskiya ? tace '" Aminatu " "nice name nikuma sunana ma,aruf ni likita ne sannan Aminatu da Aure nake sonki niba yaro bane don natafi shekara arba,in babu wasa ckn lamarina da gaske nakeyi Aminatu ya kin amince inzo gdnku ingabatar dakaina ? ta gyada kanta "Na amince. "Da kyau naji dadi Amma inaso kiyi min abu daya danki farantamin rai. Takalleshi da dara daran idanunta tace asanyaye "menene abun haka? yace "inaso daga yau yazama rana ta karshe da zaki kara fitowa bara. Dam!! Gabanta yabuga ikon Allah kajimu da mutum tace aranta " to inmunbar fitowa bara wazai ringa na abinci muda muke talakawa miskinai "Ni zan ringa tallafa muku da komi Aminatu zandau duk wata dawainiyarku bazan gajiyaba Tamkar yaji abinda take zantawa aranta yabata amsar datake sonji " da wuri haka? tafurta ahankali Ya daga mata kai " kwarai bazan gajiya ba kumaba,fatana kibani hadin kai inga nacimma burina na aurenki kinji. Ita duk abin kamar a film take kallonsa kuga mutum me kyau mr kudi agaban " yar makafi yana nuna mata so harda batun aure anya gaske "? " gaske ina sonki Aminatu kema kina sona? taji ya watso mata wannan tambaya kanta nakasa bakinta yamotsa ahankali tace " Eh ina sonka. Yace " ok godiya nk yanzu dai ki koma gunsu dan muje gidan ingano Ta juya ahankali takoma gun iyayanta takama musu sanduna suka nufi gida Da yake gidan ba nisa har suka isa DR Ma,aruf nabinsu abaya dayaga sunshiga dan karamin gidan kasa saiya faka akusa dashi Mintinanta kalilan dashiga tafito gareshi sukai sallama akan zai dawo gobe sui hira Da zai tafi yakawo kudi yabata taki karba futuk haka yahakura Har yaje gida yana tunaninta tabbas Matuka Aminatu tayi masa ta koina hanakalinsa kuma yakwanta sai tunanin ta inda zai fara taimakonta da kuma yanda zai gayawa momynsa zai Auri *"YAR MAKAFI....* *MUJE ZUWA..* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```Written by...👉🏽``` *Fresh UⓂmiey Xeey* Da *Nabilancy Luv*💘 *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *Page 5_10* Aminatu yarinya ce me nutsuwa kyakykyawar yarinya asalin iyayanta "yan chadine basuda kowa agarin kano tun wata rigima data kacame suna garin meduguri da allah yabasu ikon guduwo garin kano basu komaba alokacin aminatu nada shekara biyar su biyu rak suka haifa Aminatu da kaninta Abdulrazak shi Abdul kyanda ce takasheshi yanada shekara biyu yarasu Asalin faruwar makantar mahaifan Aminatu shine rashin lfy ta lokaci guda abin kamar almara mahaifinta shine yafara kwanciya ciwo dayake yanada sugar kuma suga nakama ido harta makantarsa tun yana gani dishi dishi har lamarin ya tsaurara ganinsa ya gushe gaba daya Itako mahaifiyarta inna halima ganin nata yagusheni alokacin tana tsakar gida tana girki hadari yataso gari yai bakikkirin wata guguwa ta turnike gari anata iska tunda wata kura ta shigar mata idanu taga duhu yagilma mata shikenan fa tadawo gani dishi dishi wannan shine sanadin rashin ganinta tar To wannan fa kaddara data samesu shine dalilin dayasa suke futa yin bara amma kafin faruwar hakan mahaifin aminatu mallam garba mutum ne me zuciyar nema domin tun dawowarsu kano yake yin aikin karfi don ganin yarufawa kansu asiri Yai sana,ar saida icce akofar gida yayi garuwa sannan yana kan zuwa kasuwar singa dako tsautsayin yasameshi Makwabcinsa mallam Ahmad mutumin kirki yana taimaka masa dama shi yafara sani zuwansa kano kuma yarikeshi rikon amana tamkar dan,uwa Wani xubinma yakan biya masa hayar gidan dayake yi duk da shima bawani me karfi bane malamin makaranta ne a secondry ta maza daga bayane ma Yazama principal Yarsa daya budurwa sa,ar aminatu ce kuma sun kulla kawance sunanta murjanatu saidai halayyarsu ta banbanta don murjanatu tanada tsageranci sannan tun tana karamarta yarinyace mr son abin duniya ga karyar tsiya da fi,ili Yanda take son Aminatu tana mata alkairi yasa aminsunci yai karfi aminatu ta aminta da ita tare sukai pri da sec duk a makarantar gwamnati amma ita aminatu tana SS Two ta tsaya da zuwa ganin iyayanta sun makance take futa yi musu jagora akullum domin su samo abin da zasuci abaka ****-- Aranar da Aminatu tai gamon katarin haduwa da Dr ma,aruf yabasu sadakar dubu daya aranar ba karamin dadi tajiba murna fal cikinta domin tagaji da futa yin barar nan dan dai ma batada girman kai ne Murjanatu tasha zugata akan tadaina futa bara amma ta kiya don batada matacciyar xuciya batason wataran agoranta mata da tana zuwa kwadayi gara ace mata tana bara yafiye mata hakan Ko aranar da Dr ma,aruf yabasu dubu guda saida suka kare kana suka futa bara sbd cancana musu tayi kudin sukai kwana uku domin sunada garin tuwo da baban murjanatu yake dan yo musu awo Aminatu itace komi na gidan shara wanke wanke da girki da kuma yiwa iyayanta wanki Aminatu kyakykyawa ce yr duma duma fara ita ba gajera ba ita ba doguwa ba tana kama da larabawan misra Gashinta har baya yake gata da dimple tana kokarin gyarawa don bata da kaxanta ****** Yana office zaune yana faman karkada biro akan file yai shiru da alama ya xurfafa tunani ne Wayarsa ce takatseshi da ruri yai furgigit ya duba yana ganin me kiran yai tsaki tare da dagawa " hello meyafaru ? daga can bangaren Lubna ta lumshe idonta tareda jan wani numfashi tace "Yaya kana ina haka? pls ina son ganinka. Akaro na biyu yasake jan tsaki yace "kiyi min uban me? Lubna kinsan fa bana son damu ko ? Tace "oh my god!wai yaya ma,aruf me yasa kk min haka ne dan Allah inkatsanine basaika fadamin ba walh akanka zan iyashan poison dan sonka zai iya cutarni inhar baka aminta daniba dom walh inaji ina gani bazan iya ganin ka auri wata ba niba... " ke! Dakata mahaukaciya! Ya fada da karfi " kiyi duk abinda zakiyi ke kk jiyo tunda ke zararriya ce Yadatse wayar yana huci Ya mike ya hade files din dake table din ya fito ya kulle office din yabar asibitin batareda lokacin tashinsa yayi ba Daga can tsalleken shatale talen rawun din yai fakin ya fito da kafarsa guda waje yana faman leka kansa ko Allah zaisa yaganota Can kuwa Ya hango makafin tana tsakiyarsu rike da hannunsu yahango wani yabasu sadaka da sauri jikinta na rawa ta karba Wani abu yaji ya tsaye masa aransa na tausan ta Ya yafito wani yaro me pure water dasauri yaron ya iso gunsa ya mika masa ruwan Dr ma,aruf ya girgixa kansa yace masa "ba siya zanyiba taimakona zakai ka kira min waccen yarinyar da take tare da makafin can. Yaron yakallo inda take yace "to ' ya tafi da sauri kira masa ita Dr ma,aruf ya kura mata ido daga nesa tabbas ayau za,a wuce gurin domin zai bayyana mata soyayyarsa sannan zai dakatar ta zuwa bakin danjar nan yin bara.... _Muje zuwa_ [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....✍🏼``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *Pg 15-20* Tunda Dr ma,aruf yatafi Aminatu takasa sakat da ranta na tunaninsa domin ta zurma itama taji yai mata bawai don bata taba yin soyayya ba ayanxun hakan ma akwai wanda yake mata matukar So Aminullah yana son Aminatu itanma tana sonsa sbd yanda yake dawainiya da ita tun tana karamarta duk abinda yasamo ita yake kawowa naci kona amfani acan bayan layinsu yake talaka ne bayada aikinyi domin karatu ma yakeyi ajami,ar Zaria agidan kawunsa yake zaune Aminullah saurayi ne shima kyakykyawa dogo saidai baki ne bakinsa me kyan nan Yarone shi me zuciyar neman nakansa don duk lokacin dayaxo hutu kano baya yarda ya zauna zaman kashe wando amajalisa yakan futa garejin yayansa kokuma yai yn buga bugarsa a kasuwar yan wayoyi inya samo ya amfanawa kansa ko yazo ya saiwa masoyiyarsa Aminatu wani abun Har tausansa Aminatu takeji na yanda yake mata dawainiya shi bame shiba Aminatu nada burin taga tayi auren jindadi sbd yanda take ckn kuncin talauci babu mataimaki sai Allah sai makwabcinsu mutumin kirki baban kawarta A yau da Dr ma,aruf yaxo mata da soyayyarsa sai tunaninta yafara canxawa ya burkita mata lissafi domin hankalinta yafara karkata akansa Nafarko taga yafi Aminullah kyau sannan tasan agareshine hutun da take fata zaixo mata Gidansu murja tashiga kawarta domin ta labarta mata wannan abu amma saita tarar murjan bata nan taje gidan yayarta karkasara <><><><><><<><><><> "Momy yau naxo miki da wata magana me dadi dafatan zaki karbeta hannu bibbiyu. Cewar Dr ma,aruf yana zaune kusa da mahaifiyarsa Hjy Zulaihat ta gyara zamanta tace '"to Allah yasa ta gamsheni babana. Yace "wato momy akwai wata yarinya da muka hadu da ita kwanan nan ina sonta momy kuma so nake ayi aurenmu da wuri... "Dakata ma,aruf! Takatseshi da bacin rai "Kana so kacemin wata kake da niyyar aure ba lubna ba? Dan ma wulakanci harka dubi kwayar idona kace da wuri kk so ayi muku aure to kasani hakan bazai yiyuba har sai inka amince zaka Auresu atare Ya canxa fuska da bacin rai shima yace "hakan bame yiyuwa bane momy yama za,ai kice haka nifa ban taba fada muku cewa ina son lubna ba to ana me zan aureta ni walh da in aureta gara naita zama haka ba aure..."haka kace min babana?bakaji kunyar idona ba harkake ikirarin bazaka auri diyar yar uwataba danma kiyayya har kace da ka aureta gara kaxauna haka ba aure lallai nagode da wannan tijarar da kk shirin yimin "Momy ba tijara zan miki ba kawai dai nafadi gaskiyar xuciyatane bana son lubna Aminatu nake so kuma ita zan aura Ya mike tsaye "to bada yawuna ba bakuma zan amince ka auri wata aminatu ba inhar ba lubna aka fara aura ba. Ya kalleta zai magana kuma ya fasa yafice ransa na quna Lubna dake labe tanajinsu ta fashe da wani kuka me tsuma rai hajiya zulaiahat ta kallo inda lubnar take ta yafito ta tace "zonan Autar Mami kada ki bata hawayenki abanxa kiyi shiru. Ta taho da sassarfa ta fada jikin momyn tana gunsheken kuka "wayyo nashiga uku momy yaya ma,aruf zai auri wata ba niba. "Ke dena fadar hakama in har ina duniyar nan ma,aruf baida matar data wuce ke kada ma ki bata hawayenki abanza dole ne ya aureki "To momy yace fa baya sona yasamu wacce yake so. "Eh ahakan zai aurekin inkunyi auren ai dole zai soki kiyi shiiru in dady yadawo zamui maganar ayau za,a gama magana dolene yazaba ko ya aureku duka kokuma ya hakura da aminatun dan baxan bari wata tafara shigowa ba bakeba. Tahau goge mata hawaye ita kuma tayi shiru tana maida numfashi don momy ta faranta mata ranta Lubna kyakykyawa ce fara ce siririya doguwa mahaifanta masu kudine ajahar yola karatu take a BUK tun da tafara karatu take agun hjy zulaihat shekara biyar knn digree takeyi sosai take son yaya ma,aruf tun tana nuna masa yana burus da ita har ta iya furta masa koda kuma tafada masa baiyi accept da soyayyarta ba bata hakuraba taci gaba da nuna masa So din Har gyaran dakinsa takeyi donta burgeshi akullum Kafin yafuta yake baiwa atika yar aiki mukullin dakinsa yace ta gyara masa Ita kuma saita karba ta gyarashi fes ta turare dakin da turaren kamshi na meduguri original me faranta zuciya Ranar da yagane ita keyi ma haushi yaji bai kuma gode mataba daga ranar ma yadaina barin mukullin Duk wata hanya da zasu hadunma baya bari Ko waya ta masa dakyar yake dagawa amma ita ko ajikinta Kawayenta Aziza da Nabila sunsha bata shawara akan ta hakura kawai tunda bazata kaita gaci ba amma sai tace dasu mahakurci mawadaci wataran za,a dace kuma tana masa son da bazata iya rayuwa ba inbashi _To fa nan fa ake yinta muje zuwa_ *Auntyn S&S*💘 [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....✍🏼``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* page.....20-25 Aminatu na zaune atsakar gida ta zabga tagumi tana tunanin rayuwarta da kuma soyayyar Dr ma,aruf data kunno gareta Sallama taji daga zaure saida gabanta ya fadi jin muryar Aminullah ta manta shaf yana zuwa duk karshen sati Ta amsa masa sallamar ahankali tana kallon shigowarsa ta xuba masa idanu sai taga yakara wani kyau Ya karasa gareta yana murmushi yaja kujera yr tsugunno yaxauna kusa da ita Tace "sannu da zuwa ashe kana tafe, Yace '"yawwa Aminata ashe kunanan baku futaba.? tace "eh ai mundaina ma futar. Yace " amma naji dadin hakan sosai dama ba son zuwanku bakin danjar nake ba aminata dan bayanda xanyine banda karfin rikeku amma naji dadin daina xuwanku bara domin keba kalar yin bara bace Amina dan dai bakyajin maganata ne. Tace "to yanzun dai aita wuce ya karatun? yace "Alhamdulillah gashi munfara exam ta semester karshe ayau xan koma baxan kai monday ba sbd gobe 8:00am munada exam bandama naxo karbar wasu kudade gun kawu bala da baxan zo ayau ba. Tace "to Allah yataimaka "Ina maman ko bacci sukeyi? tace "mama tana daki ba bacci takeba shiko baba yakwanta wai kansa ke ciwo tun safe wataqila ma yai baccin Aminullah yace "yasha magani kuwa? Tace "nabashi panadol daxun, Yace "to Allah yasawwaka bari naje gidan kawun ina ganin baxan dawo tanan ba zan wuce sbd kada nayi dare dandai ma baxan iya shigowa kano inyi uxuri injuya banganki ba da baki ganniba. Tayi murmushi tace "bakomi Allah yataimaka yasa kagama karatun lfy. "Amin. aminata bari nakoma. Ya mike tareda lekawa dakin maman yagaidata tasa masa albarka dayake tagane muryarsa Ya ajiyewa maman dari biyar yafita Aminatu tarakashi har kofar gida suka dan taba hira ta mintina sukai sallama takoma ckn gida <><><><><><><><><> Aminatu tana gama baiwa murjanatu labarin Dr ma,aruf murjanatun ta hau tsalle harda juyi ta rungume Aminatu tana cewa " wayyo dadi kasheni Allah mun gode maka daka kawo mana hutu ammafa naji dadin wannan labarin kawata kai jindadi oyoyo kinga abinda nake gaya mk ko,nasan ke kalar manyace shiyasa akullum nake fada mk kirabu da Aminullah kima cire sonsa aranki kinga dai yanzu ko ban fadaba nasan zakiyiwa kanki fada tunda nasan babu yanda za,ai ki dau madaci ki bar xuma. Aminatu tace "hhhhmmm kawata jinki kawai nake yama za,ai nabar Aminullah akan wani Dr ma,aruf kema kinsan innace zanki aminu naxama maci amana kinsanni da gudun wulakanci fa ina tsoron masu kudinnan na zamani da anga kai ba dan kowa ba sai aringa wulakantaka dan haka nikam baxan rabu da aminullah ba dan ina sonsa Galala murjanatu tayi tana mata banxan kallo kana tace akufule " to wawuya wacce ke neman kulla aminta da wahala me nasama yaci balle nakasa me zakiyi da wani aminullah ayanzu ga me arxiki kuma ma saurayi shima danyen jini ko bakya sonsa shima. Aminatu tace "bawai son dr Ma,aruf ne banayi ba yaburgeni tako ina kuma akwai abunda nake hange agareshi da zai min amfani kuma kinga nasan zai dauken wata kewar in Aminullah baya nan kawai dai ina ganin nafi cancanta da Auren Talaka kamata ne Haushi yaturnike Murjanatu bata sake magana ba ta mike bako sallama ta fice tayi gidansu dab Aminatu ta qularta takuma ki daukar maganarta Ita murjanatu haka take akwai saurin fushi dan dai Aminatun mejin maganar tane kuma batada zafi gashi suna son juna shiyasa amincinsu yai tsayi <><><><><><><><><> Yana zaune gaban mahaifinsa yasunkuyar dakansa yayinda dadyn nasa yake zaune akan 2 siter yana masa magana anitse "Me sunan mallam naji abinda yake wakana akanka momynka ta gayamin komi jiya nakumaji dadin zakayi aure babana saidai me yasa zaka ki yruwarka ka kawo bare ckn gida alhalin ta dade tana sonka kana ganin inka kita bazaka wargaxa musu xumuncinsuba kada maminta taxo tanakin haushinka da momynka tace kun guji " yarta kun daukaki wata alhalin akanka taki zaman gabansu tadawo gidanmu da zama haba me sunan mallam kaduba lamarin mana Dr ma,aruf yagyara xamansa anitse shima yahau nasa bayanin yace "wato dady bawai kin lubna nakeba kawai dai aurenta ne baxanyiba tunda ga wacce naiwa Alkawari ina son Aminatu fiyeda lubna don ita lubna ma son yanuwan taka kawai nake mata sannan akwai wasu dabi,unta da banaso nasan kuma baxan iya rabata dasu ba tunda akullum tana nuna ita yr kantace kaga kuwa dady maganin ayi kar asoma. Dadyn ya gyada kansa ckn gamsuwa yace "tom zan tattauna da momynka anjima zanfahimtarta kabani lokaci zannemeka a ina yarinyar da kk so take? Nan yai masa kwatancen unguwarsu Aminatun " to nagane tashi kaje yanda duk mukayi zan nemeka gobe muji yanda za,ai. Dr ma,aruf na futa gidan abokinsa ya wuce Dr lurwan dayake weekEnd ne yana gida Matarsa Ummi taje unguwa shikadai ne agidan dan haka Dr ma,aruf yana neman rakiyarsa gidansu Aminatu yatashi yabishi ba musu amma tsiya yaringa masa "gaskiya tuxurun nan kaci sa,ar yau madam batanan amma da ba inda zanje tunda weekEnd dai ta ma,aurata ne Dry Dr ma,aruf yayi yace "naji nikam aje arakani basai anmin goriba nima insha Allahu komi yakusa zuwar min karshe........... [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Muna matuqar jin dadi ganin yanda wannan novel ke functioning masoya muna godiya Allah yabar kauna masu kira da masu turo sako mungode muna sane daku muna tare daku ako da yaushe i love you all_ Pg 35-40 Da kuka tashigo falo tana qunsheken kuka tamkar wacce akai mata dukan tsiya da taga momy bata falon saita nufi bedroom dinta Can ta tarar ta tana gyaran sif aiko saita kara sautin kukan nan momyn ta rude ganin yanayin Lubnan da alama ba lafiya ba wannan kuka haka take hankalinta ya tashi Ta isa ga lubnan da sauri tajanyota jikinta ta kwantarta akan cinyarta tana shafa kanta Tayita tambayarta me aka mata haka Amma fur lubna takace ce mata komi don kukan yaci karfinta Saida tayi me isarta kana ta dago da kanta ta kalli momy ido jajir tace "momy yayane yaci min zarafi gaban sakatariyarsa yaimin tatas ya xagen iyaye yace babu wanda ya isa yasakashi ya aureni babu kuma me hanashi auran Aminatu domin itace ruhinsa Takarasa maganar tata tana shirin yin wani kukan Momy tahau shafa kanta tace " yi shiru babyna kada kitada hankalinki abanza daina bata ma hawayenki bai isa ya zartar da komiba inba izininmu walh inhar ina raye saiya aureki lubna Aminatun banxa kima yi shiru yr nan. Tayi lamo ajikin momy tana ajiyar xuciya ranta yai fari qal burinta yakusa cika Momy tace "zaixo yasameni barima dady yadawo yau za,a yita ta kare gara asan abinyi inko ba hakaba xanbi dashi ta karkashin kasa tunda akwai malamai aduniya zansa ayi maganinsa zai amince da aurenki ko yanaso ko bayaso asa masa sonki asa masa kuma tsanar aminar bashikenan ba. Taja ajiyar xcy ta kalli momy tana murmushi tace "dama hakan akai momy domin yaya yanada wuyar sha,ani kuma inba hkn akai ba zai iyamin wulakanci in anyi auren Momy tace "yi shirunki diyata barni dashi kibarmin komi ahannuna . <><><><><><><><><> Dawowarta knn daga kasuwa tayo musu yar siyayya ta kunna wutar ice ta wanke tukunya ta dora ruwan tuwo Tana xaune kan tabarma tana tankade taji sallamar kawarta murjanatu Ta amsa tana kallonta Murjanatu tanemi guri kusada Aminatun ta zauna tana fadin "kin dawo knn ainaxo daxun bansamekiba kinje kasuwa inji mama. "Walh kam bandade da dawowa ba nayo mana siyayya. Murjanatu tace "ah lallai tasamu knn ai haka akeso don babu batayiba kawata. Aminatu tace "bari kedai kawata walh banda yau da Dr ma,aruf yaxo yabanikudi da bansan ya zamuyi ba yau. Murjanatu tace "kai amma naji ddi wannan doctor gaskiya xa,aje dashi Allah yasa rabon kine shi. Aminatu tayi shiru kawai Murjanatu takalleta da mamaki tace "naji kinyi shiru bakice aminba kawata wai me kk nufi ne? Kina nufin bakya sonsa cin kudinsa xakiyi ki yaudareshi sbd wani banxa aminullah ? Aminatu ta ajiye rariyar jikinta asanyaye tace "narasa ya xanyi murja inason burni inason kauye aminu mutum ne baikamata abarsaba sbd halinsa hk doctor ma mutum ne nasan yana sona shima amma munfi shakuwa da aminullah banaso aga kmr ni nayaudareshi ne. "Aita fada mana kada ki biye ta mutane ki cuci kanki ko xakice min bakya son Dr ma,aruf? ta girgixa kanta ahankali tace "ina sonsa mana. " to walh bari kiji aminatu gara ki tsaida xuciyarki ta daina rawa inko ba hkba zamu bata ke barima kiji inhar baki daina batun aminullah ba zamu bata kuma inhar baki baiwa Dr ma,aruf damaba to zandaina shiga sabgarki sbd baxai yiwu arxiki nabinki kina guduwa ba me ake da soyayya da talaka awannan marrar haba aminun me. Ho ! Murjanatu akwai fada gata yr baranbaran Aminatu tazuba ido tana kallonta tasan halin kawarta sosai akan hakanma saitayi fushi me nisa da ita lallai murja ta dauka da zafi to ita ya zatayi? murjanatu ta mike tana zura takalmanta tace "nina tafi gida saikin shigo... "To inna gama girkin zanshigo. Aminatu tai tsai da ranta tana neman mafita shin wanne zata tsayar Aminun ko ma,aruf din????? *fans kutayata zabi mana*🤣🤣🤣 [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Dedicated to all masoyan book dinnqn.....mungode_🔥 *Pg 30-35* Murmushi Aminatu take zabgawa ranta fari kal ganin mamanta a farin ciki Kudin da Dr ma,aruf yabata ne ahannun mama tana shafasu tana godiya ga Allah cewa take " oh! Ni maryamu inama inada ganin wannan yaro dana je gareshi inya dawo inmasa godiya na wannan hidima Allah yasaka masa da Alkairi Amma fa ki kula aminatu ina jin tsoron samarin wannan zamani kada ya hilaceki da kudi ya yaudareki ta hanyar banxa ki amince kikula da kanki sosai aminatu Aminatu takai lomar karshe na teba bakinta tayi murmushi tace " haba mama da wayona fa zankula kada ki damu dan wannan ma da aure yake sona nice ma matsalarsa dan ina ganin baxan iya aurensaba alhalin Aminullah yana raye kinaga baxa,ace nai butulciba Mama tace da ita " a a Aminatu kada ki jahilci kanki wanda duk kkji zuciyarki takwanta dashi shixaki aura baxan hanaki ba domin mijinki shi zaki aura duk wanda kkga kin zama matarsa to haka Allah yatsara kawai dai kiringa tashi ckn dare kina addu,a kibaiwa Allah zabi kinji. " to mama ammafa inajin Aminullah kinsan yana kokari akaina banaso yakasan ce munrabu zai iya shiga damuwafa Mama tace "Aminatu knn kina son Aminu dayawa shima kuma wannan din kina sonsa to ya knn.? " narasa ya xanyi mama " da yanda zakiyi mana banace kiyi addu,aba zaki samu mafita da yardar Allah daya miki xabin alkairi shikenan. " to mama Allah yazaba min mafi alkairin. " amin yar nan ga kudin boyesu gunki " mama barsu agunki zanringa karba in za,asai wani abun. " dakin wari wanda xakiyi mana awon gari sai in boye wasu akarkashin tabarma. Nan aminatu ta debi dubu uku ciki tafita donyi musu awo. <><><><><><><><<<<> Yana zaune a office dinsa kansa aduke sai faman cike wani file yakeyi Sallamar sakatariyarsa ne yakatseshi yadago kansa anitse yana kallonta bayan ya amsa mata sallamar da tayi Sa,adatu yarece irin kedaran nan marasa fasalin kira gata baka kuma hausa bata cikataba "Ranka ya dade ogah kayi bakuwa, Yace " kije kice wacece ita? tajuya da sauri ckn yn mintina ta dawo tasanar masa cewa "wai sunanta LUNA...🤣 saida ya dara don ya fahimci Lubna takeso tace Nan take kuma yahada rai metaxo masa kuma har office. "Kiji kice mata aiki nake takoma gida Jin kadan da fitar sa,adatu yaji anbude kofa anshigo Lubna ce yar naci Daga makaranta take ta biyo Wasu riga da siket ne na material ajikinta sunkamata tsam kirjinta har burtsowa yayi yaji matsa Karamin mayafine ajikinta ta rataya suwaga me sarka Fuskarta na dauke da space baki High heel ne akafarta tana tafe kamar ta karye tana karairaya Yasake hade ransa ba raini alamarinsa Amma ko ajikinta tanemi kujera ta zauna tana kallonsa Saida tagaidashi sau biyu kana ya amsa mata a wulakance Tace "yaya wai meyasa kk min haka ne? Kada sonka yakasheni dan Allah kasassauta min mana waima dame aminatun nan tafini ne? Yadago kansa ya kare mata kallo yace " abinda yakawoki office dina knn? To yanzu kuwa zakijishi Kinga na farko tafiki kamun kai kuma tafiki nutsuwa da tarbiya sannan bata bin maxa har gun aikinsu.... takatse shi da sauri " to amman dai nasan nafita kyau da wayewa kuma da alama ko ban fadaba ita din yr matsiyata ce..,. Ya daga mata hannu " karya kk aminatu tafiki kyau da kyan jiki amma bata sakewa tabayyanashi ga maxan titi sannan bandamu da ko ita yr talakawa bace ko yr masu kudi tarbiya da nasaba nake nema kuma nasamu Harta bude baki zatayi magana yadaga mata hannu tareda nuna mata kofa yace "maxa tashi kifutar min dg office kada kisake zuwarmin inda nake inkoba hakaba zakiga abindaxan mk banza mara kamun kai. Abin ya qona mata rai ta kufula tace " ni kk xagi yaya? " anzageki mara kunya ko xaki ramane? Ta mike tana goge kwalla tace " walh ko kanaso ko bakaso saika Aureni kuma zakaga ni. Ta fuce fuuuuu tana kukan bakin ciki. Yaja wani mugun tsaki yanajin wata sabuwar tsanarta aransa..... , *Tofa muje xuwa Auntyn S and S* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Always remember to smile. You may not know it, but someone might be dying to see that smile everyday._ PG 25-30 Tana Zaune atsakar gida tana yankan kubewa danya zuciyarta ta lula atunanin mazaje biyu awani bangaren zuciyarta tafi rinjaya akan Dr ma,aruf amma kwadayayyar zuciyar kenan kammalalliyar xuciyarta kuwa bata shawara take akan Aminullah dinta domin tana nuna mata inhar ta auri Dr ma,aruf wahala zatasha agunsa da gun yan uwansa sbd kasancewarta yr talakawa kuma yr makafi tunda mafi akasarin auran datakeji anyi saitaji ance ana wulakanta maryar ko ansakota sbd kasancewarta yar marasa karfi ko ace anfi fifita yar masu kudi akan yr talakawa insu biyune agun mijin kokuma ace uwar mijin tasa yakara aure ya auri daidaishi yar manya To ire iren wannan ma kesa zuciyarta rawa akan Dr ma,aruf Ammafa ta wani bangaren zuciyarta lashe money na kwadaitarta akan daular duniya dajin dadin zaman duniya tana bata shawarwari akan kada ta wuce jin dadi domin inhar ta auri doctar wahalar da take ciki takau kumafa hakane(ai konice mexanyi da madaci bayan ga xuma 🤣) Afirgice ta dawo hayyacinta dataji shigar wuka a yatsunta ta yanke kadan ta rike gun ta ajiye wukar dama saura kadan ta gama adai dai lokacin kuma wani yaro yai sallama yace ana sallama da ita awaje Takalleshi tace "kaje kace wanene" Kafin yadawo ta mike da sauri tazuba kubewar ackn ruwan miya dake kan wuta yanata tafasa ga kamshin daddawa yar bichi yakauraye gidan Dama teba ce ta tuka tana kula yunwa takeji kamar taci babu tayi tsaki data tuna kuma futa zatayi "aiko inhar ban sanshiba ba inda zanje. Tafada ckn ranta Yaron yadawo yasanar mata cewa " wai Dr ma,aruf ne. Wani farin ciki taji yaziyarceta " kace ina zuwa. Ta wanke hannu da sauri jinin kadanne yazuma ayatsun nata Tashiga tagayawa mamanta sannan ta dauko hijab ta fice fuskarta fayau ba kwalliya amma kyanta yafito tamkar balarabiya haka take aminatu ta dabance inbatai kwalliyar bama ganuwa take koda kunnenta ma ba dankunne bata muni Tayi musu sallama tareda rusinawa ta gaidasu Sun yaba da hankalinta Dr lurwan yahau tsokanarta "ke yammata kinfa rikota min aboki gashinan bayada xance sai naki abokina yana miki so na gaskiya dan Allah aminatu kema kisoshi tsakani da Allah kirikeminshi gashinan amana kada ki yaudareshi baisan so ba sai akanki kuma kinfi kowace mace sa,a da kk sameshi donshi mutum ne adali metausan nakasa dashi gashi da amana kuma kaifi dayaneshi baida riko balle saurin fushi ga yammata na rubibin neman soyayyarsa sun kasa samu kinga kuwa ke kinsamu abagas saiki rike mana amanarsa dafatan kin dauka amina? Tayi murmushi ahankali kanta akas tace "kada ka samu damuwa nadauki amanar nan fatana dai shima yarike amanar. Dr ma,aruf yai mata wani kallo na so da kaunar juna yace "indai rikon amana ne ai kinxo gdn zinariya. Tayi kyakykyawan murmushi har dimple dinta yalotsa takalleshi ckn wani shauki tace " to ai hakan akeso Nima zan rike. Nan suka taba hira tana Allah Allah su tafi don cikinta sai kuda yake na yunwa ga tunaninta miyar data dora Tarasa me zatace musu dansu tafi takoma gida Kamar yaranfota yaga tana dan yatsina Yace "ya dai zinariya qalau kuwa? tace "bakomi "A,a saikin fada naga wani yanayi daya ziyarceki fa "Cikina ke ciwo tun daxu dama amma fa yama lafa Ta shafa cikin "Sannu zinariya shiga gida kisha magani. Tace " ai nasha dazufa "To bari mutafi kije ki kwanta kinji. Dayake saida suka biya ta store yai mata siyayyar kayan kwalliya da na tande tande Ya daukosu aleda yamika mata ta rusina takarba da godiya Dr lurwan yakoma mota yabarsu suyi sallama Dazai tafi yabata rafar yan dari dari na dubu biyar Taso taki karba amma data tuna basuda komi na kayan abinci sai garin kwaki daya rage gwangwani uku aiba shiri tasa hannu biyu takarba da biyayya tana godiya Sukai sallama yatafi itama tashiga gida ranta fes hartaji yunwar ta ragu ganin nera ( huuuiu kudi mahadin rayuwa 😉) take taji dayar zuciyar nasake tunasar mata da abinda tagaya mata daxun Take taji ta aminta tabbas Za,aje da Doctor ma,aruf..... *MUJE ZUWA* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _(ZAFAFAA🔥🔥🔥)_ _🗣🗣ina kuke masoyan wannan littafin da kuma ranar na nadama...Muna mai muku albishir da wani Sabin littafin *SAFNA ME SUNA DANGANTAKARMU* yananan tafe, Karku bari a Baku labari domi littafin ya bada abubuwa da Dama..._ *PAGE 40-45* A durkushe yake agaban momy da dady kansa akasa yanajin momyn tana ta masa fada abinda yaiwa Lubna baice komiba Hakama dadyn baiyi magana ba har saida tagama bambaminta kana dadyn yakalleta yana murmuahi yace "ayi hkr momy zan ari bakin babana inbada hkr baxai sake mata cin zarafi irin hakaba..."niba haka nakeson jiba. Dady sarkin yan raha yasan halin matarsa sarai yagyara zama yana murmushin yace "me kk son ji ?fadi ko meye inda hali sai muyi miki. Ta hade rai tace "nasan kana goyon bayansa tun ba yau ba bakasan laifinsa don haka tunda yana jin maganarka inaso kasa ya amince da Auren lubna inko ba hakaba za,aga fushina ackn gidan nan koma inbar muku gidan gabaki daya inhar ba a faranta min da wannan ba. Dariya dadyn yayi harda tafa hannu yace "ho momyn mu kuma Auren dole zakiyiwa dan naki... takatseshi "au wasa ma kamaida abin ko? yace " a,a ba haka bane mamaki kk bani ai tunda naga wai namiji xakiyiwa dole alhalin ko mace ayanxu andaina mata auren dole. "To naji dolen xan masa inkaso kataushe shi inkuma kaso kazugashi yabujire walh aga bacin raina. Dayaga serious ne abin nata saiya juya ga Dr ma,aruf yace "babana kaji dai abinda momynka tace yanzu ya xa,ayi da xancen aminatun zaka hkr ne ka auri lubna don farin cikin momynka ko yaya? Dr ma,aruf ya dago kansa yana sharce gumi agoshinsa na tashin hankali yace " dady walh ina son aminatu hk itanma tana sona. "Nasani wai ma aminatun nan waye baban tane?bani kwatancensa ko nasa aymin bincike akansa inyaso saika auresu duka gaba ki dayansu ko hankali yakwanta. Cewar dady Dr ma,aruf yace "babanta talaka ne kuma makahone suna zaune a unguwar rimi basuda kowa agarin nan sai Allah amma asalinsu yn chadi ne inaso inga nataimaki aminatu don mahaifiyarta ma makauniyace Amma daga baya suka samu makantar Allah ne yadora musu..."kace kawai "yar makafi ce! cewar momy tafada ranta abace "Walh baxata sabuba baxaka kawo mana "yar miskinai gidan nan ba yar talakawa yar matsiyata gara ma tun wuri kabinne maganar ta kafin mubata dakai..." dakata Zulaihat bazan lamunci ki kuntatawa danmuba akan son ranki babu ruwana da talaucin iyayanta ko makantarta wannan duk na Allah ne shine meyin komi ga bayinsa kuma akwai jarabta wanda muma bamu wuce yajarabcemuba dan haka ki sassauta masa ki bari yazabi wacce yakeso. Ta harxuka "walh Alhaji kaji na rantse bazai kawo mana yar makafi ba saidai inhar ya Auri zabina afarko inyaso daga baya saiya auri yar matsiyatan daga baya shima bada yawu naba. Harta mike zata bar gun yadakatar ta "kinga zauna zulaihat a tsaida maganar da zata yiwu bana so ki fifita yr "yar,uwarki akan wacce danki yakeso ki sassauta dan Allah Yakalli Ma,aruf yace " babana kaji dai hukuncin da momynka ta zartas dafatan xakayi abinda tace ka Auri Lubna daga baya sai ka auri zabin naka. Idonsa yakada yai jajir yace "naji dady nakuma amince inhar za,a barni na auri aminatu domin itace zabin raina. Dady yakalli momyn yace "to kinji ya amince dan haka kijanye kudirinki da kk ce ba yawunki akan auransa da aminatu tunda yazabi farin cknki. Tace " hhhmmm aini kuma babu qauna tsakanina da *"YAR MAKAFI* me ake da auran yr matsiya wacce ba,asan daga inda ta fitoba. Taja tsaki ta mike ta barsu nan tahaye sama abinta Kama kansa ma,aruf yayi jin yana sara masa momy tasa masa tension Dady yatausaya masa don yasan ciwon so nan yahau tausar sa yana cewa "kayi hkr halin momynka har yanzun yaki canxuwa kabari in anyi auranku da lubnar sai ayi da aminatun ckn wata biyar ko shida kuma saikayi transfer din aikinka ka koma wani garin da zama da aminatun kabar lubnan anan takarata ita momyn ba shikenan ba tunda matar shige bata daraja (kunjifa uba me son farin cikin dansa ho l! Dady knn)😊 Ko dayaje zance gun Aminatu bai nuna mata komiba don xuwansa na uku knn sunsha hirarsu ta masoya tasaki jiki tana nuna masa qauna Murjanatu taxo sungaisa yabata dubu uku yace tasa kati tayi masa godiya Waya yakawo mata yr karamar android techno me dauke da layin MTN Yabata dubu goma tayi masa godiya don ayau kam yasata farin ciki koda yatafi tashiga gida da murna tagayawa mama tabata wayar taita shafawa tana shi masa albarka Haka babanta ma yasa albarka ta dankawa baba kudin yace "ajiyesu agunki mana Aminatu aikece gidan Aranar kasa bacci tayi ma,aruf yafaranta mata ranta lallai dole ta amince dashi domin jin dadin duniya yana gareshi tunda aminullah baida kudin daxai sai mata waya balle harya iya bata dubu goma iya gejin kyautarsa dari biyarce. Tofa tun daganan son ma,aruf yafara samun matsuguni azuciyar Aminatu Zasu dau tsahon awa suna waya ta soyayya sunfara sabo inyai kwana uku baizoba sai taji wani iri Murjanatu ma tana taka rawa akan soyayyarsu don itake dorata akai Akullum takan nusarta akan taso Dr ma,aruf shiyafiye mata domin yanzu ba gwaninta bane yin soyayya da talaka wanda baida aikinyi Dr ma,aruf yai kwance malemale axuciyar Aminatu yakan kawo musu kayan abinci buhu buhu ko yadauketa yakaita store yai mata siyayyar kayan kwalliya sannan sutura me tsada yake sai mata yatanadar mata babban tela kwararre yana bashi kudi me tsoka yana tsara mata dinkuna Mayuka masu kyau da tsada tadawo shafawa aiko fatarta har kyalli tadawo yi tabbas kyan Aminatu yanata fitowa tamkar balarabiya Turarikanta masu tsada har murjanatu take daukarwa duk da murjan ma tana gara mata samarinta masu kudine yawancinsu duk sugar dadyne masu nera Dr ma,aruf yasai musu gidan da suke ciki sannan yasa aka buge aka sake masa fasali ginin bulo da bulo yasha fenti yai kyau Abu daya daya burge Aminatu yakara mata kaunar Dr shine taimakon dayai mata wanda bakowa zai iya mata ba yabiya kudi a asibitin malam aminu kano don yiwa babanta aikin ido Satinsa guda ana abu guda da Allah yataimaka cikin ikon Allah saiga ido yasamu Amma kuma dishi dishi yake gani a ido daya Ahakan ma angode Allah Aranar da aka sallamoshi farin ciki suka kasance mara musaltuwa agidan baba yaringa shi masa Albarka Mama cewa take "wannan yaro yagama mana komi Allah yasa rabonkine. Aminatu tace "mama kema yace ai xai sa ayi mk aikin. Maman tace "to Allah yabada iko Allah yasaka masa da alkairi dai. Dayaxo da dare gunta tayi masa godiya harda kwallarta Yace "meye naki namin godiya iyayanki nima nawa ne aminatu saura mama ma zanyi mata buking asatin nan itama ayi mata ai abun zaizo da sauki itanma tunda dukansu bada makantar sukaxoba waraka zata samu insha Allah. "Allah yanufa " tace ckn sanyin murya Yace "amin. Aranar yanaso yagaya mata zancen lubna amma yakasa domin yana tunanin halin dazata shiga Saida yaje gide awaya suna hira wajen sh dayan dare yafara sanar mata cewar yanada matsala agida anbashi yar kanwar mamansa kuma ance lallai saiya aureta kana ya auri aminatun da wata biyar gaba. "Aminatu ina sonki kada kidamu lubna tasan bana sonta ke nake so dan haka kada kisa damuwar hakan aranki kuma wata biyar kamar yaune Tace "yaushene za,ai muki auran? "Satin sama sukasaka dan Allah kada kishiga damuwa my zinariya i really love you baxan barkiba bakuma zata samu fada azuciyata ba kece uwar gidana ko a aljanna aminatu Yajita shiru yaxaci ma ta kashene to ashe kuka take nan hankalinsa yatashi yaji tamkar yakoma gidan nasu danya rarrasheta Yai ta bata baki dakyar tayi shiru yaita gaya mata kalamai masu sanyaya rai tareda alqawura kala kala nan ranta yadanyi fari Da safe kuwa jikinta asanyaye taita yin ayyukan gida Tashiga gidansu murjanatu sula kule adaki take gaya mata Aiko ran murja inyai dubu yabaci " jar uba wannan ko tsinan niyar mayya ita dan rashin aji namiji bai sonta amma ta nace toko zamui maganinta walh ba xama zamuiba tashi zakiyi muje gun wani malamina ayi aikin daxaiji yafasa yabujire musu saiya fara auranki tukun. Aminatu tace "nifa gara inhakura dashi dama irin wannan matsalar nake gudu. "Ke banxa ce matsala dake tsoro to bari kiji aure keda doctor kamar anyi dan haka dole kixo muje gun aramma yayi wani abun akai. Aminatu tace "to bari ingama ayyukan gida sai muje. <><><><><><><><><> Lubna ta zabga tagumi yayinda tagama waya da kawayenta Aziza da Nabila tagaya musu zancen bikinta da yaya ma,aruf Momy ce tashigo taxauna kusa da ita tajanye mata hannun datayi tagumin tace mata "to sarkin "yn saka damuwa arai so kk kirame kafin auran Lubna tace "momy haryanzu yaya yaki tsayawa mui maganar biki sai binkansa nake yana wulakantani narasa mafita. Momy ta tausaya mata tace " sha kuruminki diyata nasamo wani malami zamuje anjima Aramma ne acan tsaunin yadakwari ya iya aiki kawata hky bilkisuce zataxo gobe muje inaso yai aiki akan yadaina son Aminatu sannan asaka masa sonki aransa yaji ba kowa agabansa saike ko ya kk gani. Da murna lubna tace "haka ne momy naji dadi nagode da taimako Allah yakara girma. " amin, tashi maxa kije kixubo abinci kici. " to momy " Cikin murna ta nufi kicin don ranta yai fari momy tasata afarin ciki tabdijan aiko inhar yaya ma,aruf yashiga hannunta zaiga wulakanci zata rama duk abinda yai mata.... *Auntyn S&S &Ummiey Xeey* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* _auntyn S&S_ *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* (ZAFAFAA🔥🔥🔥) *PG 45-50* A tsaunin yadakwari nan dan tsibbun da murjanatu ke zuwa yake da sassafe tayiwa Aminatu rakiya xuwa can Yayinda murjanatu taringa kutsawa da ita har " yar bukkarsa Suntararda wasu mata su biyu sukaja gefe suna jira kafin layi yaxo kansu Ba,a dau lokaciba yagama ganin matan saisu Gaban Aminatu nata faduwa waiyau itace daxuwa gun boka duk akan namiji lallai Abun babbane Allah yakawo mata dauki bata fatan ta dore da xuwa Suna zaune agabansa murjanatu tana rattaba masa yanda takeso abun yakasance "So muke yaji yakara tsanar yarinyar aransa sannan yabujirewa iyayansa akanta ya tirje inba Aminatuba yabar gabansu kada yai musu biyayya yabijire kawai Take bokan yace "angama kudire naira dubu hamsin na aikin sannan in angama aiki xaku bada na rago da xa,a yanka ayi amfani da jinin. Gaban Aminatu yafadi jin kudi tsububu ita ina taga dubu ashirin ma balle hamsin damafa matsalar xuwa gun bokaye knn barnan kudi Murjanatu tace "Allah yaja da zamaninka dubu sha biyar mukaxo dashi saidai aimana lamuni makawo ragowar daga baya tunda duk ana tare. Yahau girgiza kansa yana fadin "maxa kutashi ku koma baxanyi aikin ba inba andire rabin abinda na bukataba wannan shine lamunin. Murja babu bakin magana tasan halinsa ba,a masa magiya magana daya yakeyi Nan takama hannun Aminatu jiki asanyaye suka fuce Ahanya Aminatu tace " kinsan aikinsa da tsada kk kawoni gunsa ni ina naga wadannan tsububun kudaden sha biyar dinma dan matara sune inbanda ma ma,aruf din yana bani ina zan samesu gaskiya nahakura kawai abinda Allah yai Annabi sai ceto. Murja tagalla mata harara tace "ke kinji matsalarki walh karaya gako da tsoron tsiya to bagudu baja da baya sai munyi abinda mukai niyya zamu sake wani gun akwai me sauki akan tudu can xamuje ko goma baxai bidaba. "Nifa nahakura kawai tunda shima nasan damunje tsadar zai mana Murja tace "aiko me ya bukata aikinki zaici hakan don babban aikine kuma ba daya za,aiba don haka biyo bayana sai munje Aminatu tace "nifa baxaniba nafasa gara naje nasai mana buhun shinkafa na ajiye Murjanatu taharareta tace "banda wanda doctor ya ajiye muku har buhuna 2 don son iyawa da son asani zaki kara siyan wasu to ai saiki siya din inkudin ahannunki yake Aminatu ta dage akan baxata ba murja kuwa tace walh saitaje inko ba hakaba su raba gari tana son tayi "yanci ne Adole aminar ta hkr tabita xuwa kan tudu gun wani malamin ammafa baikai na yadakwari zafi ba Suna barin yadakwari da mintina saiga hjy zulaihat da lubna sunxo suma gunsa Kawar hjy zulaihat ce takawosu gun itace idon gari tana zuwa yau da gobe Hjy bilkisu tana gaba suna baya Suka xaxxauna gabansa shiko yanata tsibbace tsibbacensa Hjy bilkisu tagabatar masa da hjy xulaihat tareda nuna lubna tafadi dalilin zuwansu akantane Momy zulaihat ta fayyace masa komi tareda fada masa yadda suke so abin yakasance "so muke ya amince da auran nan na lubna da muka hada ayi komi ckn sauki yayi rawar jiki akai acire ms son aminar yadawo son lubna fiye da Amina sannan ya mance da batun aminatu kana yaringa rawar jiki akan lubna duk abinda tace yabi ba musu. Boka yace "angama adiremin dubu dari yanzun nan. Take ba fargaba balle musu ko neman ragi momy ta dire masa dubu dari Yace "aiki na akwana uku yakeci zakuga komi yakasance ammafa a wata uku xai iya karyewa tunda ba fadar Allah bane saidai inkunso zaku dawo ku dora wani akai "To ai wannan ba wani abu bane mudai muga yacin tukun inyaso madawo adora daga inda aka tsaya. Inji momy Lubna ranta fari qal zata ringa juya ma,aruf lallai duniya sabuwa yaya ma,aruf zai zama nawa . Tafada aranta Bayan yabata magunguna dazata ringa wanka dasu danasha da kwalli daxata saka sui toxali saina abinci dazata saka masa in anyi aure harda na tsarki don inya sadu da ita yaji baxai iya rabuwa da itaba( kai jama,a Allah yashiryamu yadawo damu hanya.) <><><><><><><><><> Sai bayan sallar azahar su aminatu suka dawo rubutune leda biyu yabata wai intasha zataga biyan bukata dubu biyar ma yabukata Murjanatu nata mata mita "gaki kamar wayayya amma sai ahankali gun malamin ma saina mk dole zakije alhalin kanki xaki gyara aidai kowa rai yaiwa dadi ba ya maishi. Itada tsabar gajiyar datayi ko uffan batace da itaba jan kafa kawai take tana tuba ga Allah don tana ganin anyi na karshe Tashiga gida agajiye tilis Sallah tafarayi sannan ta leka dakin mama tasameta da kwano agabanta taci abinci dama takan zuba abinci akula ta ajiye mata kusa da ita sbd inbata nan ko zataji yunwa Dayake ma babanta yana dan futa da sanda duk da idonsa daya yana gani abun yaragar mata yakan taimakawa mama inbatanan "Sannu mama kinci abincin knn. "Naci tun daxu aminatu kun dawo knn.? mundawo mama baba fa? mama tace "yanzu yadan dogara yafuta masallaci. Aminatu taxuba nata a palte ta koma dakinta don taci abincin itama Tana daukar wayarta daniyyar takira ma,aruf sai taga missed call dinsa har 5😳 Tuni tabi baya da sauri Bai dagaba saida takatse yabiyo baya "Hello zinariya ina kkje haka naita kira no answer? Tace "nafuta gidansu murjanatu sai yanzu nashigo. "Ok dama inason ingaya mk ne zanzo indaukeki anjima muje store kizabi irin atamfofin da kk ra,ayi domin kala daya zansiya muku keda lubna baxan bambanta ba. Tace "to dear saikazo. "Ki zauna ackn shiri ana magriba zanxo. " allah yakawo minkai lfy. Nan sukai sallama Alokacin dayake wayar yana dinning table yana cin abincine yyinda lubna ke labe tanajinsa tsaf duk abinda yace da Aminatu Bakin ciki fal ranta takaici yatsaye mata yanzu dan wulakancima ita datake amarya yawan kayan ta da kalar babu bambamci da wacce ba ita za.a auraba lallai wannan abin nasa yakai kololuwa zakuwa tayi maganinsa kwanann nan Dayake ta saka kwallin da ka bata dan haka ta tunkareshi yayin data kirkiro murmushi taja kujera taxauna kusa dashi Yaga xuwanta gun amma baikalletaba Ta gaidashi ya amsa dakyar kansa akasa Tace " barka da hutawa yayana angona to be. Ya dago dakansa xai mata bala,i jin takirashi da angonta Amaimakon yai bala,in dayai niyya sai yaji wani abu ya tokare masa kirji idonsa yatsaya cak akanta yakasa daukan mataki n dayai niyya Kallon kallo sukaiwa juna Baice da ita komiba amma yaji tayi masa kwarjini sosai Itako tasan me hakan ke nufi na ganin sauyi gareshi Tasan aiki yafara ci "Saima nan da kwana uku " Tafada ckn ranta Shiru yaratsa atsakaninsu na yn mintina har zatayi magana saitaga ya mike yabar gurin Ko abincin bai gama ci lemon daya tsiyayo akofi zaisha nan yabarshi baishanba. Ta dafe kanta wannan wane irin mutum ne abunma yafara cinsa amma baigama rusunaba bakomi muje zuwa aidole zakayi laushi wanda tashin ma saida ixinina zakayishi Ta dauki lemon tasha tana dariyar mugunta "yaya ma,aruf kakusa zama nawa nikadai ka kusa mantawa da Aminatu *"YAR MAKAFI....* _MUJE ZUWA._ [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *PG 50-55* BAYAN Sallar magriba tana kan sallaya ta idar da sallah tana jan carbi yaro yashigo yasanar mata cewa ana sallama da ita awaje Tabashi umarni dayaje yasanar cewar tana gatanan zuwa Tasan ma,aruf ne ta tashi da sauri tashiga dakinta tayi emergency make up Tafito tasanarwa mamanta zata futa zasuje siyayya da ma,aruf maman tayi mata adawo lfy Amota ta tararsa baikashe motar ba Tana shiga ya kada kan sitiyari yacilla kan motar titi Ta gaidashi tana kallonsa Ya amsa yana cewa "zinariya kinyi kyau fa. Tace "wane kyau kuma na zurmuko hijabi. "Aini hakan ma burgeni kk yi gara da kk sayamin jikinki tunda gun jama,a xamuje Tayi murmushi kawai A jippatu atamfofi ya siya mata guda goma sha biyar manya daga sharaton sai exclusive da holland Kaloli masu kyau leshika kala biyar ne manya swiss swiss Shaddoji gezna biyu ne yan dubu ashirin Materiyals uku da dogayen riguna biyu. Suka shiga sahad store yasiya mata mayafai da turarika da kayan make up Saida aka lode kaya amota yakalleta yace " to kudi sunyi low abari gobe madawo mukara sauran amma shoprite zamuje sunkawo takalma " yan ubansun da jakunkuna Tace "ko yaushe ma asiyesu kawai tunda ba yanzu xa,ai auren ba wata shidafa kace gaba. Yace "ainafiso komi yakammala saidai injira daurin aure da axuwan amarya ko kuwa? Tace "to ita Lubnar kuma vanga kadau mata komiba ko kwazo da ita daga baya ? Ya harareta yace "da nayi niyyar insai muku komi kala daya amma daga baya nafasa zanbaiwa hajiya kudi kawai suje tare su siya banda lokacin kawota nan. Batace uffan ba dama jan bakine amma daya fadin hakan saitaji dadi don tanajin kishin lubna aranta da xata fara shiga gidansa kafin ita. Saida yatsaya yahuxa suya yasiya mata naman kaza guda biyu da lemuka sannan yakaita gida Yaune ranar shigarsa gidan na farko yataya daukar kayan suka shiga dasu har ciki Yagaida iyayanta har kasa Dasuka gama shigarsu yai musu sallama amutunce sannan yadire musu kudi dubu gomane yarage ajikinsa sukaita godiya dasa masa albarka Haka kawai taji ayau tana masa wani irin so mara misultuwa kamar kar yatafi takeji shima jikinsa asanyaye yai mata sallama yanajin wani abu akanta Koda yatafi saida yayo mata waya sunyi kusan awa daya suna hirar soyayya. Ta tashi ckn dare tayi mafilfili takoma bacci. <><><><><><><><><> 09:00 am Agurguje yafito yana balle botiran gaban rigarsa zaitafi gurin aiki yayi latti yana saukowa daga bene ita kuma tana kokarin hawa Aiko taji dadin gamon nan domin yau kwana ukun boka ta cika kuma tana son ganin mafarin aikin Ckn kissa ta tareshi da sauri tana fadin " yayana harka fito ina kwana. Harda rankwafawa Yakalleta ransa asake yace " lafiya kanwata. Taji wani shork tareda jin nice aranta "lallai abu yayi. Tayi fari da kashe ido "Bari natayaka gyara maballan ko ? Yayi murmushi " a,a bari kawai nagode fa. " a.a ai baniso kasha wuyane kuma gara infara tying aikina tun ayanzu ko? Takashe idanu tana murmushi Yace "kwarai hakane. Yasakar mata tahau ballewa tana dan shafa wuyansa Bai hanata ba yabita da kallo yarasa dalili ji yayi ta birgeshi sosai gashi yakasa hanata Yace " nagode bari natafi nayi latti aikene dani jingin a office. " gashi ina sonyin magana dakai kuma ba. Yace " ok to ayimin hkr zan dawo da wuri domin ki. Tayi murmushin jin dadi tace " ok no worry i am waiting 4 you . "Allah yatsare yadawo min dakai lfy ayi tuki da kula pls. Yatsinci kansa da kai hannu yashafa kumatunta yace "nagode zan kula bye. Yatafi yana daga mata hannu itama tana daga masa Aguje takarasa hayewa saman tana kwallawa momy kira "Momy! Momy! Momy!!! kina ina ne kixo kiji news Momy tafito da sauri daga dakin dady tana fadin "meya faru diyar momy Tafada jikinta "walh momy abu yaci yaya yasaki jiki dani bakiji kalamaiba walh harda cewa xai dawo da wuri daga gun aiki domin ni kai momy aikin boka yayi yakamata aje akara masa kudi. Dry momy tayi tace " af ai dama nagaya mk kukanki yazo karshe saikin dara kadan kk ganima tunda yau abun yafara saikin bani lbr Nan momy takira hjy bilkisu kawarta tana rattaba mata labarin aiki yafara ci. (Kaji jaka jama,a wai har murna take akan aikin asiri yaci danta. Towallah saikinyi nadama muje xuwa) Agun aiki kasa katabus yayi duk tunanin lubna ne yacikashi taringa masa gizo tana masa makirin murmushinta Yayinda yatingajin kewarta aiko duk aikinsa a office sukuku yayishi gashi takaicinsa baida nambarta yaja tsaki daya tuna hakan. Dr lurwan yace "yadai mutumin qalau kake kuwa tunda nashigo inata sallama baka amsaba kuma naji kanata tsaki meya faru haka? "Meye ma bai faruba lurwan. "Ko Aminatu ce..."wacece hakan???Yaja tsaki Da mamaki lurwan yace "meke faruwa tsakaninku ne yada tsaki? Dan kaji sunanta to tabbas akwai wani abun kodai tabata maka rai ne? Dr ma,aruf ya daga masa hannu cln bacin rai yace "dakata mallam ba wannan ne agabana ba inkuma zancen wata amina ne yakawo ka to kajirani awaje innafito inda lokaci sai muyishi amma yanzu aikina yafita "To!😳 ikon Allah . Inji dr lurwan yafada yana kama baki da mamaki " to Allah yakyauta. " Amin. Yafada yana duba agogon hannunsa don biyu tayi kuma yanaso yakoma gd da wuri sbd Lubna duk hankalinsa ya karkata kanta..... *AUNTYN S&S*👌🏼 ce💘😊 [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *PG..55-60* Baki har kunne Murjanatu keta daga atamfofi da lesika fadi take "Allah yakashe yabamu kawata domin kuwa wannn kaya daya hada mk sai yar wane da wance ke samun irinsu ji atamfar da muke gani ajikin yan karya dan Allah, Ta daga sharaton tace "kinga wannan nasan ta doshi dubu talatin ko? Aminatu ta mirgina kai gefe tana dariya tace "kai murja sai abarki ina zan sani nida kawai dauka nake ina lodawa kuma total akai masa yabiya. Murja tace "gashi basu rubuta ba ajikin atamfar balle mugani. " to meye amfanin ganin ma tunda inkasaka kowa yasan kasa me tsada. "Ke walh badai kowa ba dan wasu saninsu baikai nanba. Ai kedai ki godewa Allah Allah yabaki miji haka nake so walh inga masami mijin da zaice muhado lefe da kanmu mama dake cikin daki tana jiyosu tace da murjanatu "kema Allah zai baki murja Abu na Allah saikiga kin samu fin hakan. Murja tace da mama " to mama atayamu da addu,a dai. Aminatu ta xungureta tace "kefa bakida ta ido. "Meye na zancen ta ido don nace atayani da addu,ar samun mijin wuce sa,a shine nayi rashin kunya kinjiki waima. Ta mutguda baki Ta mike tsaye da nufin tafiya gida bayan ta rufe kayan tana fadin. " to kuma kawata yaushe za,a kammala siyayyar ne ? Aminatu tace " yace a ckn watan nan dai saima yagama nawa zai yiwa lubnar nata sai angama siyan komai za,a sai akwatina. Murja ta tafa da yar shewarta tace "lallai kawata kin ciri tuta kin zama tagaban goshi tunkan ki shiga kinga Aikin malam yaci ko. Aminatu tace " ke inma dai yacin bazan sake komawa ba dan badaniba a aikata sabon Allah nadade da sanin babu kyau bin malamai nikam banason nakoya. Murjanatu takawar da maganar da cewa " wannan keta shafa kidai samu ki shigan tukun gaba kyasan abin yi nidai duk randa xaku koma karasa siyayyar kigayomin inxo nabiku rakiya inganewa idona duniyar kaya ko nan gaba nima nakai wanda zan aura yaga duniya. Aminatu tahau mata dariya kai murjanatu "yar ayi ce halinta sai ita. <><><><><><><><><> Tana ganin azahar tayi tahau shirin tarbar ma,aruf tunda yace mata zai dawo da wuri Ta tsala kwalliya da wata doguwar riga me duwatsu tabi jikinta kusan abubuwan sun bayyana kansu Ko dankwali bata daura ba kai yaci attach anyi mata kalba dogaye har gadan baya suka kwanto Fuska taci make up antsatso kyau Dayake gwanace wajen make up domin da ace zata bude gun yin kwalliya datayi suna donkam zatayi ciniki bana wasa ba sbd ta iya kwalliyar canza kamanni Lemo ta hada masa na musamman ta hada masa me dauke da sihiri aciki Daya dawo ruwa kawai ya watsa yasako jallabiya yasauko kasa don neman abinda xaisaka acikinsa don yayo sallarsa a masallaci Karo sukaci dasauri taja baya cikin kissa tace "wayyo kayi hkr yayana bada sani ba nabugeka Yayi dry yana kallonta ckn shauki yace " bakomai amaryata Tace " sannu da dawowa. "Yawwa mexa,a samamin akicin ne yunwa nakeji. Yahau shafa cikinsa yana kare mata kallo Cikin kissa ba fargaba atareda ita takama hannunsa ta nufi dining dashi ta xaunarsa Wani yar yaringaji ajikinsa tareda sha,awarta Ta xuba masa shanyayyun idanunta tace "zauna jira ni na yan mintina natanadar maka delicious Tayi hanyar kicin tana karkada duwai😊 Cancakas hankalinsa na kanta idonsa kirrrr!agun da takeso yakalla din ( makira 🤣 Duk wani iri yake jinsa ayau tabbas ji yake son lubna nakwarara axuciyarsa jinta yake ba wata tamkarta xai iya fada da kowa akanta Tadawo da flet arufe ta ajiye agabansa ta bude kuskus ne yana tiriri da miyar ganye akayishi miyar tasha kifi me tsoka ga kanshin curry ya cika gurin Tace "jirani again kadan indauko maka ruwa da lemo inxo inciyarka da kaina. Kasa magana yayi saidai gyada kai yana xuba mata na mujiya kawai Ta dawo hannayenta da jugs na tangaren lemone aciki na kas kuma ruwa mesanyi Ta diresu tana cewa inje in dauko karamin kofi? Yace "jeki mana amma kiyi sauri nakagu inci girkin nan me dadi. Tayi murmushi tace " sha kuruminka nawan dankaifa akayi bari nadauko nadawo. Data dawo dab dashi ta zauna taringa bashi abincin abaki yana amshewa yanaci yana lumshe idanu Yaci dayawa haka lemon duk yashanye ruwanma bai sami gurbiba acikin nasa Ta goge masa baki da tissue tare da cewa ko akaro? Yagirgixa kansa yace "a,a tawan nakoshi nagode da kulawa ina godiya ga Allah daya ke zaki zama matata ba Aminatu ba. Ckn jin dadi da kissa tace "itan ma ai xata xama matar taka nan ba da dadewa ba. Takashe masa ido tana jiran jin abinda zai fada akai. Yasha mur yace "daina fadar haka ada ne wannan zancen amma ayanzu nayi kansil haba lubna namiji me mace irinki mexai da wata ai bukata ta kare in aka sameki kinfi sauran matafa. Abinda take sonji knn azo gurin. Tasan dole tasha yabo yau Ta kada idanu tace " dagaske yayana? Kai amma naji dadi kana nufin kafasa auren aminar? Yace "kima daina min xancenta inkina son ganin farin cikina, don tunata babban bacin raine agareni. Tayi farrrr! Da idanu tace "to nadaina nawan tashi kaje ka kwanta inka wartsake sai inzo dakin muyi hira. Yace "ok to godiya nake anaji dani dai. Tace "ba dole ba angon "yan kwanaki. Yace "kishirya yau muje siyayyar kayan lefenki Tace " naga kabaiwa hjy kudin harsunje da hjy bilkisu sunsai min komi Yace " nawa na dabanne inkuma nasun sun miki to abarsu. Da sauri tace " haba dai ai naka sune abin faharina ni ason samuna ma kamaisheni yar gata katura da kudin ta account asiya maka komi adubai aturo maka su ko kuwa? Yace "ok inhakan kk so ai sai ayi tunda akwai sauran time ba sati biyu bikin ya rage ba? Tace "eh mana ko kana manta lissafine ? Yace "inafa. kishirya kawai muje tare dake kizabi komai da kanki zaifi Tayi tsalle harda dan fadawa kirjinsa tana bugawa na sigar shagwaba tana cewa " wow! yayana amma naji dadi i love you Yace "i love you too my wife. Ai da gudu tayi gun momy don ta kai mata rahoton yanda abin yakasance Momy ta jinjina mata tace "aikoda asiri yai tasiri to kema kin taka rawar gani diyar arxiki inaso ma kice masa kinason kayan furnitures a dubai din kisa yasai miki komi har electronics Tayi dariya "haka za,ai momyna. <><><><><><><><>><> Kwana daya,kwana biyu Aminatu taji dr ma,aruf shiru baikirata ba bakuma sako ita takikkira no answer ta tura masa sakwanni shiru ba reply Abin yaita damunta gashi takasa gayawa mama dan itanma saita shiga damuwar Saida aka kwana biyar ta kebe da murjanatu take sanarta Aka ta dora hannu tamkar anyi rasuwa tace " nashiga uku ni murjanatu shine kikai shiru har wadannan kwanakin bakixo munje nemansa ba. "To murja ina zamu je nemansa nida ko gun aikinsa bantaba xuwaba bankuma taba tambayarsa asibitin dayake aikin ba Murja ta harareta tace "Amma aike kam kincika mashiririciya walh danice har gidan iyayansa saina gano walh bansan irinkiba aminatu Amina tayi shiru tace "banajin qalau murja jikina nabani akwai wata akasa nikam Allah dai yasa ba hanashi aurena akaiba dako ancuceni dan ayanzu xuciyata tacika da qaunarsa babu gurbin wani zanshiga matuqar damuwa i. Narasashi gashi yaxame mana bango yarufa mana aairi takoina yaimin sabo da kudi ta yanda xan shiga wani hali i aka samu akaai dan Allah murja kisamo mafita Aminat takalleta da jan idonta dake shirin kawo ruwa tace "fadi meye mafitar murja. Murjanatu tace "mafita dayace jal mukoma gun mallam yaduba mana lamarin. Aminatu tace " murja inafa tsoron... "tsoron abu daya yakamata kiji shine talauci wanda annabin mu da kansa yanemi tsari dashi kinga kuwa inhar kk shirya xama dashi na kud da kud saiki zauna karkije gun mallam. Aminatu da xuciyarta takarye shedan yakawo mata ziyara tace "to yanxu ya xa,ai banda kudi ahannuna dayawa. " inbabu kudi amina ai akwai kayan kudi kifito da atamfofi kamar biyu ko uku muje musaida akasuwa muje gun me zafi donkinsan da zafi zafi akan bugi karfe gun na yadakwari xamu koma sbd na yadda da aikinsa don talaka ma bai nufarsa aikinsa akwai kyau zakuma ki fada da bakinki. Amina ta amince take tunda bataga amfanin komiba atare da ita inbabu Doctor ma,aruf..... *Ikon Allah sai kallo muje xuwa fans* *Auntyn S&S*💘👌🏼 *and Fresh Ummiey Xeey*💋💋 [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Shout out to all our fans....munajin dadin yanda kuke comments, Wannan page din Nakune....We love you Irin Sosai dinnan domin da bazarku muke taka rawa... *#OnE LoVe😍❤*_ Enjoy reading😘 *PAGE 60_65* Anyi biki nakece raini tundaga ranar kamu har ranar yini gidan momy acike yake dankam Mahaifan lubna ma nan sukazo akayi komi ckn mutumci da bajinta don mahaifinta me haline yayi kuma rawar gani wajen siyan kayan furnitures masu tsada baiyi la,akari da wai Dadyn Ma,aruf yasiya mata komiba Kayan gara kuwa motar akori kura aka ciko dasu shinkafa manyan buhuna goma sha biyu samovita da kalwin vita da farar shinkafa ta tuwa buhuba sha bibbiyu ga pastocin mai na fari da ja sai bangaren maggi kaloli harda buhun sugar uku manya dana gishiri Sai bushashshen kifi dasu tumatirin gwangwani kai duk abinda suka san zata nema sunyi kokarin sako mata dashi donta wuce gori wanda kuma inzata shekara sunaci tana kyautar dasu bazasu kare da wuriba Ango sai rawar jiki yake da bazazawa yana narkar da nerarsa kawayen amarya ma su biyar yaiwa anko ita tasashi kuma dole yayin bai isa ya musaba Ankai amarya da kwana biyu mahaifiyarta ta koma gida dama shi babanta ana daura aure aranar yajuya sbd yanada meetting don haka dole akai ms uxuri ya wuce Ankai amarya gidan Angonta wanda ke karkasara gidane flat me kyau Sati guda ana lula soyayya ko futa kofar gida baya sonyi Hatta gun aiki ma saida yacika sati biyu hutun daya dauka yakare kana suka ganshi Dr lurwan a ckn mamakin abokinsa yake domin harya fara zargin ma ko wata qullalliya aka hadowa ma,aruf shiyasa yake susuacewa in lubna takirawoshi Duk aikin dayake saiya bari yayi nata uzurin wani xubinma kiransa xatayi tace dashi ita dai gaskiya tagaji da zaman ckn gidan ita kadai yadawo haka ko kuma ta aikashi wani gurun donyi mata siyayya Lamarin na lubna yabaiwa lurwan mamaki sbd yasan inhar dai ba abinda yake zataba to babu abinda zaisa abokinsa yaringa bin abinda tace ckn rawar jiki da tsoro karara atare dashi don basuyi haka da Zainab matar saba Dr lurwan yasha alwashin saiya taimakawa abokinsa zaisa ayi masa saukar karatun qur,ani inma da wani abun Allah yakadarsa yadawo dai dai Domin tausan abokinsa yakeyi kuma yana tausayim aminatu da abokin nasa ya goge shafinta arayuwarsa ji yake inama bai dade da aureba dayaje ya aureta don aminar tanada kyawawan halaye da za,a so Sau daya sukaje gidan momy tunda sukai aure shima da darene kuma wajen tara na dare suna xuwa da minti goma tabashi umarnin su tashi su koma gida Asannan dady yayi tafiya lokoja Momy bata damuba bata kuma sa abin arai ba saida taringa kiransa akan zaauyi wata muhimmiyar magana Yaki zuwa yaita jirgata kan zaizo to abin yai mata ciwo sosai arai saima da ya furta mata cewar ta tambayi lubna in ta amince da xuwansa saiyaxo inya taso daga aiki Mamakine yakashe momyn bata san ma sa,a taci ya daga kirantaba don yana gun aiki amma in a gidane baya daga wayar kowa saida izininta Watansu guda da Aure tazo musu har ckn gidan da wata safiya ta lahadi Lubna na falo tana shan tea sai ganin momy tayi kamar ancillota bagatatan Takurawa momy idanu da bacin rai afuskarta Haka itama momyn ranta abace tashigo gidan Lubna takalleta sama da kasa batace uffan ba Da momy taga lubna batada niyyar gaidata balle hartabata maxauni saita zauna kan kujera ta dubi lubnan tace "Ke tsagera rasai nazo ganin d'ana ne har gdnsa domin bansan nufin kiba nahanashi xuwa gun uwar. Lubna ta dire kofin shayi makira batace uffan ba saita mike tahaye sama don kiran ma,aruf din Tare suka sauko falon jallabiya ce ajikinsa Jikinsa yabashi wani abun duk saiya tsorata da ganim yanayin momyn nasa gashi kuma lubna tayi masa jan kunne Adaki Har kasa yagaida momynsa kansa akasa Ta kare masa kallo taga ya canza tamkar ba ma,aruf dintaba Ya rame yayi duhu sai tausayinsa yakamata fadan dataxo tayi masa saita fasa ckn rage murya tace dashi "ma,aruf meyasa bakason daga wayata kuma meye dalilin dayasa kadaina xuwa inda nake kacanxani kenan ko yaya ? Kansa akasa yahau girgixa kansa Lubna dake tsaye akansa tace " kayi shiru bata amsa mana koka manta abinda nace maka? ya dago da kansa cikin bin umarninta yace "kiyi hkr momy ba canxaki nayiba kawai dai Lubna ce bata amince da fitata koina ba shiyasa dan Allah kiyi hkr zan gyara intabani umarnin ingyara din...yi shiru haka! Lubna tace dashi Aiko ckn rawar jiki yakame bakinsa tsit baisake cewa uffanba Ikon Allah yau momy taga abinda yafi karfinta Lubna ta dubi momy tace "To kingani ganin idonki kuma kinji da kunnenki dan haka sai a adauke kafa Adaina mana zarya inko ba hakaba zakiga abinda zai faru agabanki ato Yau momy taga tsiya da wasali za,a rabata da danta Ta nuna lubna "ke fitsararriya butulu wacce batasan arxikiba har nixaki dubi idona ki gayamin haka kinmanta ranar danai mk aryuwa to ko inhaka zamuyi dake to daidai nake dake ni warkice dai dai kugun kowa domin niba uwar banxa bace kuma baxan lamunci kina wahalar min da dana ba akan kallagaggen aurenki mara amfani, Lubna ta mike afusace tace " saurara momy nifa ba...kau!kau! Karar marin da momy tayiwa lubna ne yafirgitani domin saida *Ummiey Xeey* ta tsorata ta futa afirgice daga falon _LOL_ Ma,aruf ma ya dago da saurinsa yakai kallonsa ga lubna data rike kuncinta takasa magana dan takaici tunda ta dade rabon da ayi mata wannan marin lubna takalli ma,aruf "me kake azaune da baxaka tashi kadaukarmin mataki ba kana ganin cin zarafinfa da akayimin shine kayi shiru ko. Tahau kuka makira Ya rikice yarasa tacewa yace "am...kin...san... dai uwatace babu abinda zan iya lubna kiyi hkr. Yajuya yadubi momy yace " momy agaskiya wannan ba adalci bane azohargida adaki mace akan tafadi gaskiya... momy tace toko zaka rama matane ? Dr ma,aruf yakasa cewa uffan kansa na kasa hannu Lubna tadora akai ta kwalla ihu tana gunsheke kamar an aiko mata da sakon mutuwa Momy tace " makira kiyi kukan jiniba karewa walh ke baki isa ki hanani ganin dana ba balle kishiga tsakaninmu kuma kisani zanyi maganinki saina karya mugun nufinki akan abin. Tana gama fadin haka ta fuce fuuiuuu Yajanyo lubnar ajikinsa yana rarrashi yana fadin " kiyi shiru kada kisaka nima nayi kukan matata walh naji wannan mari har raina kuma kinsan mahaifiya tafi gaban komi ba Ta tureshi tana fadin "nidai kayi wani abun akai kokuma ayau ba sai gobeba nabar maka gidanka don baxan yardaba gara nakoma gaban iyayena da in xauna wata can tana dukana Yaji ciwon kalmar data fada wai wata can! Amma yakasa katabus saima rarrashi harda cewa "barima kiga nafara daukar matakin Yakira dady awaya yarattaba masa abinda yafaru Dady yace " yaushe rabon daka kirani ma,aruf wato sai yau sbd anbatawa matarka rai shine yau harda kawomin karar momynka ayau lallai abu yabaci babana natabbata lubna ba haka tabarkaba dan bana garine amma da zarar nadawo zansa ayi maka wani taimakon tunda naga kafara xautuwa yau kaine dakai karar momynka guna.... Da sauri lubna ta warce wayar ta kashe dif! Domin a handsfree take taji komi takuma gane nufin dadyn Shiko dady cixar yatsa yayi yana fadin "lallai xatona yatabbata yau babana ne ke kashemin waya sbd bangoyi da bayan abinda akayiwa matarsaba hakika yakamata yai axama yadawo koya saka ayiwa ma,aruf addu,a akan lamuransa don abin yafara bashi tsoro <>¡>¡>¡>¡>>¡>¡>¡>¡> Momy tana zuwa gida ta yarda gyale tafada kan doguwar kujera tana kukan bakin ciki da nadama Ayau tun ba,aje koina ba tayi dana sanin wannan hadin bata zaci lubna zata iya yi mata hakanba Wayarta tayi ruri da sauri ta daga saitaga hjy Hauwa,u ce kanwarta mahaifiyar lubna Ta xaci abin arxikine to ashe bugowa tayi taji dalilin daya saka momyn ta marar mata " ya Momy kasa magana tayi don tsananin.mamaki ganin yanda kanwarta taringa xazxaga mata rashin mutunci harda fadin itafa yarta ba jaka bace da za.a ringa jibgarta me tayi da harma ayi mata gori ga mari ga tsinka jka. Cilli mimy tayi da wayar ta tarwatse domin bataga amfanin saurarar maganar hjy hawwaba don saisuyi uwar watsi Dama saida dady yasha fada mata hakan xata iya faruwa domin xumunci yakam baci tahanyar auren hadi gashi tun ba,aje koinaba yabace abinda yake jiye mata knn Taringa kukan xuci tana cixon yatsa takuma sha alwashin saita koma tayi gu. Mallam ankarya sihirin To abinda bata saniba ita lubna komawa tayi daga baya takara kudi akai aka bata wasu kalolin mallakar masu xafi dayafi nafarko domin lubna da gaske takeyi.... *Auntyn S &S da Fresh Ummiey...muna sonku* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Dedicated to Zauren Ummiey Xeey and taskar Nabilancy_ you're Guy's are amazing domin muna ganin soyayya😍😍❤❤ *PAGE 65-70* Lubna ta zage ta dage wajen ganin ta mallaki Dr ma,aruf ta koina ta yanda duk abinda zaiyi na kankin kansama sai yai shawara da ita inhar abin bai mataba hanawa take kuma dole yahanu Account ta bude sabo tana shakeshi da kudi na ganin irin yanda ma,aruf ke jikata da nera takan yawan turawa mahaifiyarta kudi dama itake dorata akai ayanzun Hatta malaminta tana shaka masa nera koba aiki xai mataba saita ziyarceshi ta bashi makudai Dr ma,aruf rayuwar kawai yake amma ankarkatar masa da hankali Momy tashiga damuwa sosai naganin danta baya xuwa inda take ga dady baya gari Takanyi kuka ita kadai ta goge hawayenta takanyi nadama mara adadi Takira Dr lurwan abokinsa awaya yaxo har gida ta fada masa damuwarta da halin da ake ciki Cixar yatsa yayi sosai najin abinda momyn tayi tun afarkon auren Yace " zancen gaskiya momy ke kk bata abin kuma ke kk janyo masa koma mene duk halin da ma,aruf yake ciki kece yanzu gashi kinfishi shiga damuwa nasan shima dan babu yanda zaiyine amma zan samo mafita Malamai yakamata mubaza ayita addu,a akan Allah yakarya kadarin Baxamu zuba ido yana cutuwa ba domin lamarin na lubna babba ne Momy tahau goge hawaye tana fadin " aini abin ma yadaina bani mamaki domin yafi karfin tunani na lubna taci amanar zumunci ban zaci xatayi min hakan ba ga mahaifiyarta ma tabi bayanta tadaina zumuncin dani akan naiwa yarta hukunci taji haushina harda bugomin waya tana cimin xarafi bakaji ba lurwan abin babu dadifa Dr lurwan ya girgixa kansa yace " kayya amma abin ba dadin ji momy hakuri zakiyi kada kisa abin aranki yaxo yai mk illa ki kwantar da hankalinki Allah zai shige mana gaba zakiga tamkar ba,ai ba ya wuce kedai kitayashi da addu,a Momy tace " to lurwan naji nagode Allah yabar zaman tare. Yace " amin. Nan yai mata sallama yatafi <><><><><><><><><> Aminatu ce zaune jigun tayi tagumi hannu bibbuyu abin duniya yai mata yawa komi yatsaya mata cak Dr ma,aruf yaki dawowa gareta koda wasa bai taba kirantaba tunda yai aure gashi harta gaji da kaiwa malamin tsubbu kudinta to inama kudin suke komi yakare mata dan abinda ke ajiye tayi dabara tasiya musu kayan abinci sai sauran kayan da suka rage mata lesika swiss kala biyu ta saidasu dubu ashirin ashirin faduwar dubu goma ta samu tabaiwa mahaifinta kudin yana juyawa domin danyen kayan miya yake kasawa abakin titi gwalgwaji dayake yanzun yana gani da idanu daya dayan kuma dishi dishi yake gani sai yake saka glass wasu ma sai anfada musu zasu sani ba,a ganewa akwai yaron dayake tayashi zama agurin To rufin asirin da suka samu knn ta wannan bangaren don batajin ko sun rasa komi su dawo yin bara ayanzu tagane ba ajinta bane Hawayene yaxubo akuncinta tasa bayan hannunta ta goge tana tuna Aminullah daya dawo daga karatunsa yagama yai final yaxo mata da murnarsa amma bata tareshi da farin cikiba asalima aranar tayi masa korar kare ta rufe idanu tace masa itafa ayanzu baya gabanta yanemi wata asalima Aure da soyayyar sun fice mata arai gara ma yabarta ta huta ya saurara mata kada yasake nufota Aranar Aminullah yashiga matuqar damuwa kansa ya kulle don kasa fahimtarta yayi tunda yasan dai ba fada sukai ba kafin yatafi Don haka yasami murjanatu ko zaiji wata maganar daga bakinta Abinda murjan tayi masa saida yagwammace kida da karatu domin itanma rufe idonta tayi taringa masa zazzaga dama ba qaunarsa take da aminann ba Harce masa tayi indai kai ba maye bane to yakamata karabu da aminatu tunda yanzu dai tace batayi gara kaje can gaba kanemi tsararka kaima inka duba ai xaka gane cewar miyar ba kalar tuwon bace. Kai ranar aminullah yaga takaici da bakin ciki domin baisan yanaiwa amina so me yawa ba sai da yaga idanunsa sun kekeshe kasa dan dai bacci barawone amma baisan zai iya runtsawaba aranar Yayi zaton ko wasu sabbin samari ne masu hali ke hurewa aminar kunne saikuma yaga sabanin hakan yakan kewayo da dare yazauna nesa dagidan yaga ko zaiga me mota yaxo xance gunta sai yaga babu me zuwa gun aminar Kai ko da rana yasha zuwa yalabe anesa yaga ko suna futa yawo da murjane amma sai yaga duk ba hakan bane zarginsa dai bai tabbata ba Don hakan saiya yankewa kansa hukuncin barin garin kano yakoma gurin wani kawunsa da zama acan zariya Zaman doke yaringayi badan yaso hakanba tunda bakowa yasaniba kuma xuciyarsa na kano gun Aminatu Haka yaita hakuri harya fara sabo yasami aboki wanda ke alayin suka kulla abota ataikaice ma baban abokin nasa dayai ne yasama masa aiki ama,aikatarsu yafara xuwa kuma da taimakon Allah sai Allah yafara buda masa don awata guda saigashi yasai lipan sabo gadagau Murjanatu tashigo gidan tanata kwada sallama taji shiru Maman aminatu nacan daka tana bacci Itako amina ta lula atunani Murjan ta tako ahankali taxauna agefenta ta cire mata tagumin data xabga Suka kalli juna ahankali aminar tahau goge kwallar dake malala akuncinta Murjanatu tace " haba Aminatu wannan meye kuma hakan saikace wata me babbar matsala wacce baxata yankeba zaki saka kanki adamuwa haba kawata komifa yakusa xuwar mana karshe. aminatu tace " kayya murja aidole nayi kuka tunda damuwar da nake ciki takasa yayewa banga kuma ranar da xatazo karshenba kullum kwanakin ja suke yi amma shiru dr ma,aruf ko waigen baya bayayi alhalin malam yace zai dawo gareni nan ba dadewa ba to waishinma sai yaushe? Murjanatu tace " ki kara hakuri kawata yanzun ma nazo mk da labarin wani malami wanda aikinsa keda ban mamaki domin aranar daka aikata abinda yasaka zakaga aiki da cikawa.... " aiko ba indaxanje domin banida abinda xan bashi gara ma kibarni da takaicin wanda na barnatar abaya. Murja tace " sha kuruminki kawata shi wannan har abashi zai iya mana yana lamuni harsai in burinka yacika xaka kawo masa kudinsa kuma akudi kalilan sannan ma zanbashi wani abin kada ki damu nidai fatana da burina naga doctanki yadawo gareki yasaki ballagaxarcan lubna. Murmushi Aminar tayi tareda cewa " to naji yaushe zamuje.? "Ko yanzuma tashi muje ashirye nake " cewar murjanatu Nan takintsa ta xura hijab sukaiwa mama sallama data tashi suka fuce Basu sha wahala ba wajen xuwa gun mallamin Saidai abinda ya girgixa Aminatu tashin farko dataji abinda yabukata takawo masa zaiyi aiki dashi wai tasamo cindon hannun wani hamshakin mutumin zaiyi aiki dashi inkuma ba hakaba ta samu gashin gaban namiji baligi takawo inkuma da dama ta hado da cindon zataga yanda Dr ma,aruf xai dawo gareta agigice dakuma maganar Aurenta aranar da akai aikin. Duk da aminar ta shiga tunanin inda zata samo wananna abun amma ranta yadau hasken jin ma,aruf xai dawo mata nan ba da jimawaba. Ahanya da suka dawo daga gun malam murja nata bata baki da xugata cewa take "aikawata wannan abubuwan xagewa zakiyi asamo don ayi aikin nan da wuri. Aminatu tace " towaike a ina zan samo wadannan kayan masu wahalar samuwa kowanne akwai hadari Kina ganin inma inada wani me kudin dayake dauke da cindo ahannunsa tayaya zan yanko abu ajikinsa inkawo batareda yasaniba? Kokuma tayaya zanyanki gashin gaban namiji nida ba kwanciya nake da maxaba inma ina kwanciyar dasu tayaya zan yanko abu ajikinka kana kwance bakajiba? Murja tayi dariya tace " bakiji me mallam din yace bane ce mk fa yayi kije ki lalibo wanda duk kikaga yanada abinda muke nema sai axo asameshi agaya masa zai fadi dabarun da za,ai din asamo kk sani ko wani maganin da xai kadar da hankali zai baki? Aminatu tace " to naji komi ma xai iya faruwa amma abinda nakeso kigane murja a ina xan sami hamshakin me kudi nida ko futa bamayi balle aganni sai intayi dalili xa.a ganmu atiti. Murja tace " hhhjmmmm kece dai bakya futar amma ni ina futa fa hajiyata dan haka inhar xaki futa toki biyo layi don cimma burin.... Aminatu takatseta da cewa " """!! Kina nufin karuwanci kk futa? To bada niba murja Murja tayi dariya tace " waya gaya mk karuwanci ne futan a,a sam abinda nake nufiba infuta inje titi intsaya innaci kwalliya kamar irin ina jiran wanin nan saikiga manyan masu kudi suna tsayawa zakuma kisha mamaki inhar akaga farar fuskar nan taki walh aranar sai an hada go slow Aminatu tayi shiru tayi wani dan naxari na sakanni kan tace " to zanyi hakan nima duk dan cikar burina amma gaskiya gara inje inda ba,a sanniba domin bayan ansami abinda akeso basake xuwa zanyiba. Murja tayi dry tace "dama mana kedai kawai kishirya muje da dare zakiga abnin mamaki saikin fi kowa kasuwa. Amina takama baki da mamaki " Au, ashe da mutane dayawa knn agurin? " sosai ma keda wa yake zama tabdijan kin dauka kowa kansa akwallaba yake kamar ke ai yanzu inka zauna zakaga zama dan haka kiyi shiri da dare atafi bulayi kawai. Nan aminar tadau gurguwar shawara ta amince akan zatabi murjan nemo saurayi me kudi.... 🤔 tabdijan Allah karaba mu da neman duniya dakuma shegun kawaye masu kaimu su baro. *Ummeiy Zeey* Da *Auntyn S & S* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* 70-75 Da misalin karfe taran dare ta tsala kwalliya da wani material me shegen kyau sai walainiya yake stone ne rututu me shining ajikinsa Riga da skert ne yafito mata da sharp dinta yakama mata kirji na shanunta sun nuna Gyale karami ta yafa tasaka takalmi me tsini Fuska tadau make up tafito dan zuwa gidansu murjanatu Saida tafito tsakar gida gabanta ya fadi tuno abinda xai futarta wai yau itace da futa neman maxa da kanta! Oh masifa batayi ba walh! Ta fadi aranta Takalli kofar dakin iyayanta taga harsun rufo Yanayin sanyi ake ciki dama da wuri suke bacci da sunyi ishsh,i zasu kwanta balle dama su bamasu takura bane tasan ma batada matsala dasu Tafuta ahankali ta janyo kofar gidan tarufota ta yanda inta dawo xata budeta cikin sauki A zauren su murjanatu sukai kicibus itama ta tsala kwalliya da shadda doguwar riga anmata fitted me kama jiki Dariya sukaiwa juna yayinda murjan tayi saurin toshe mata baki tace " yi ahankali idon baba biyu gashi can yana karatun jarida karya na sharara masa nace walima zamuje na saukar karatu tun 8 aka fara mune bazamu da wuriba dayake dake nace zani bai hanaba don ya yarda dake ta gidana. Dariya Aminatu tayi ahankali tace ckn rada " to muje dan mudawo da wuri kada mubata lokaci. Suka fito daga gidan Aminatu nata raba idanu tana kalle kalle dan bata son " yan unguwa su gane yawo zasu ji takema tamkar snfahimceta dayakema aranar ana mugun sanyi babu yawan jama,a alayin ko gun me shayin dake akan layin baifi mutum biyuba ba kowa Hankali kwance suka futa a unguwar suka sami dan sahu atiti Club road suka nufa titin central aka kaisu murja ta biya Aminatu sai zare ido take abin na bata mamaki na ganin dai daikun mata akan titin suna tsatstsaye kowacce tasha make up tamkar zasuje gdn biki ko suna Murja ta kama hannunta tace " kinga ba kallon mata yakawomu ba zo muyi ta can jikin falwayar can mu tsaya ko Allah zaisa adace. Tabita xugui xugui abaya tana takun burgewa itanma murjan takun yauki take tamkar ta karye kafa tasha coge Ko minti biyu basuyi da tsauwaba kuwa saiga wata katuwar jeep tatsaya agabansu murja taja ajiyar zuciya ita kuma Aminatu ta kalli can gefe Ya ziro da kansa ta tagar motar yana cewa "yam mata ji mana. Murjanatu takalleshi ckn yauki da yanga tace " dukkanmu daka ganmu educated ne ba jahila balle dakikiya dahar zakai mana kiran kucakai inxaka futo ka fito domin da ajinmu. Yayi murmushi tareda kashe motar yafito yatako har gabansu yatsaya tareda fadin " ai girman kujerar kune dolene infito ko banyi niyya ba kuma ajin dana gani atare dakune ma ya tsaidani hajiya. " ba sunana hajiya ba kirani murjanatu kai tsaye. Yace " to malama murjanatu wannan kawar taki fa ansiya ko insiya? Tayi wani shakiyyin murmushi tace " aiko tayawa ba,aiba don tsayuwarmu knn ka iso gurin da bakaxo da wuri bane badai zance maka daka makaro don bazaka tadda ko sahun kafar taba Yace " lallai nacika me sa,a domin samun kamar wannan babyn agun nan sai an tona to gimbiya meye sunanki? Aminatu tayi fari da idonta wanda batasan ma ta iyaba sai aranar tace dashi " sunana Amina' Yace "gud suna me dadi first born dina ma sunanta kenan sunan marikiyata data rasune Tace " Allah sarki. Yace " to ya xa,ayi knn, atafe nake domin daga tafoya nake nabiyo tahanyar nan dan nasami abokiyar da zata tayani kwana domin niba dan kano bane daga yola nake zankuma wuce zamfara ko za,a biyoni hotel mukwana tare? Murjanatu tayi caraf tace " me zai hana inzaka biya da tsoka kadai san akwai banbancin kudi kwana da yini ko? " ah sosai kuwa ai wannan me kyan ma kudin kwana biyu xan bata a kwana daya kuma cash saita dankesuma ahannu kana zata faranta min Yakalli Amina da gabanta ke faduwa taji xancen kwana tace " nashiga uku me nakeji. Yace da ita "to mekyau kin amince? Murjanatu ta gyada mata kai dayi mata alamun ta amince kawai. Nan aminar tace masa " ba matsala na amince. Yabude bakin aljihu yadebo kudi dabaisan yawan suba yabaiwa murja tace " ga tukuici yar,uwa Takarba jiki na rawa tana godiya lallai wannan me gwabi gwabine za,a dashi Yadubi aminatu yace biyoni mota muwuce Yatafi mota ita kuma tace da murja " nashiga uku kawata xanko iya kwana da kato, walh gudowa xanyi in kwana ince dasu mama me? Aminatu tace " toke da me zaisa ki kwana dashi baki san shiba in dan yankan kaine kuma fa, kedai kitabbatar kin shaka masa maganin da mallam yabayar da xarar kinga hankalinsa yagushe saiki gudo. Aminatu tace "to ai kuma wata daban muda muke bukatar samun cindo. Murja tace " ke murnar ganin kudi tasa ban miki albiahir ba naga cindon agefen hannunsa kato ma kuwa daya mikon kudi nagani kwantar da hankalinki kawata buri zai cika kedai kiyi abu ataka tsantsan. Nan xuciyar Aminatu tayi sanyi hankalinta yakwanta jin akwai abinda suke bida atare dashi Ta gyara yar jakarta suwaga me sarka akadarta sukai sallama ta tafi gun motarsa ta shiga da addu,a abakinta Yakalleta da murmushi akan fuskarsa yace " to kyau muje ko? Ta gyada kai kawai Yaja mota sukai gaba. Nan tabar murjanatu nata murnar samun makudan kudi ga burinsu zai cika tashi guda basu sha wata wahala ba Tanaso ta kirga kudin tana jin tsoron mutane don mutum mugun icene kada ayi mata aika aika in anganta da kudi sbd gurin tamkar da rana haka yake da haske manyar fitilu burjuk koina ga mata sunfara cika Ita tananan har kusan goman dare babu wanda yatsaya gabanta dan haka saita yanke shawarar tafiya gida kawai tunda dama ita kudi take bukata kuma tasamu wanda in wani xai bata hakan ma xata iya samu Tana tafe kafin tasami abin hawa wata mota ta tsaya agabanta Mamallakin motar yaita mata horn Ta tsaya taba jiran fitowarsa Yaxuro da kansa yace mata " hajiya shigo arage muki hanya mana. Babu jan aji ba komai ta bude gaban motar tashiga tana fadin "wash amma kataimakeni fa don yau masu abin hawa sunyi karanci atitin. Yakalleta yana kashe mata ido yace "sanyin yau aiyayi yawa dole wasu zasuki fitowa nima dole ce tafito dani Yasunan malamar? Yatambaya yana mata makirin kallo Takashe ido guda tace " murjanatu Amma ana cemin Janah. Yace "nikuma sunana Alh Labaran ina unguwar koki sannan ina business a kasuwar kwari ina muka nufa? Tace " gida mana. Yace "to baxamu wuce musha ice cream ba? Tace " ba matsala muje mana. Nan yakarkata akalar motarsa xuwa fine time. <><><>><><><><><><> Mukoma ga Aminatu mana A babban hotel yakama daki Tahir Daki me tsada yabiya suna ciki yasa aka kawo kayan cima iri iri Taki cin komai Ya matsanta mata amma tace akoshe take Dakyar tadau ruwan faro tabude tayi makwarwa uku ta ajiye Shiko dayake yunwa yakeji yacika cikinsa Yakalleta yace " kinsan anfiso in za,ai harka atabbatar ancika ciki komi zaifi tafiya dai dai kema yanzun in kika jiki da nauyi saikinfi min sha,ani ko? Taso ta hade rai amma sai ta tuna wani abu ta dan murmusa idonta akan katon cindonsa dake hannun hagunsa Yakai hannunsa yacire mata gyale yadora kan jakarta Yahau kiciniyar cire mata riga Tasa hannu ta turarsa tareda matse zip dinta tahade ranta Yayi murmushi yace " sorry nafahimta wato ban biyaba tukunna ko? Aina sha,afa ne, Ya dauko jakarsa yaxuge ya danko makudan kudi ya xuba mata cikin jakarta Tasaki ranta kadan amma gabanta naci gaba da faduwa domin batajin zata iya bashi kanta don budurcinta da take adanawa na doctor ne insha Allah Allah yataimaketa ya mike yace "bari nadan shiga toilet na fito pls tashi kicire kaya mana. Tace " to. Yashiga toilet tayi saurin janyo jakarta ta dauko wata " yar hoda ackn leda ta rike ahannunta tana jiran fitowarsa Minti uku saigashi ya fito dashi sai dan fant Ta rintse idonta domin bata taba ganin tsiraicin namiji hakaba Yaxauna daf da ita yahau ahafa yana son ya xuge mata riga Allah yabata sa,a babu wata wata bai fargaba ta shaka masa hodar ahanci Nan take yahau yin tari ahankali idonsa yajuya take yakada yaji ya masa nauyi yahau lumshesu Jikinsa yasaki yajishi yai week Ko hannunsa baxai iya dagawa ba Yafado jikinta ita kuma ta wullashi kan kujera yafada rigijaaaa Bacci ne yai awon gaba dashi baccin sihiri domin ko munshari bayaja tamkar wanda ya mutu Anan tasami damar bude gefen jakarta ta dauko sabuwar reza agidanta Ta lulo hannunsa na hagu tayanke katon cindon Saida tsikar jikinta tayi yarrrr! Bata zaci zata iya ba amma data tuna a inda suke komi zai iya faruwa kada wani yaxo a ma,aikatan hotel din debar kayan abincin da aka shigo musu dashi saitahau azamar boyewa Jini saida ya bata gurin tasa cindon aleda ta wulla ajaka Ta mike da sauri ta rataya jakar akafada ta rufa gyalenta tayi hanyar waje Kafin tafutan saida ta juyo ta kare masa kallo taganshi jipgi guda akwance Da ace kudine yakawota da saita sake bude jakarsa ta loda to amma ba afabanta suke ba tunda tasami abinda takeso Saida ya leka koina taga babu masu tahowa kana tafito Tamkar mara gaskiya inka ganta kafafunta sai sassarfa suke tamkar zata fadi Ta wuce reception mutum biyune bata kula suba ko kallonsu batayiba Daya yana mata magana tayi banxa dashi gabanta na dakan uku uku Taja ajiyar xuciya dataga ta wuce su babu wanda yabiyota abaya To ashe ba anan gizo ke sakar ba Saida taxo get zata futa taji wani security yakwalla mata kira Tun daga nesa yafahimci kamar batada gaskiya shiyasa yatsaidata Ya iso kusa da ita yace mata "ke daga ina haka? Tayi shiru kanta akasa tarike jakarta kam Yasake tambayarta ckn daga murya "Nace daga ina kk? Tace " ciki mana. " ciki room nawa? Gabanta ya fadi ita inama ta duba. Kai tsaye tace masa "walh ban rike ko room nawa bane. Data fada masa dakin da saiya sakata agaba sunje to amma duk da hakan saiyace da ita "Meye kk sauri kamar xaki tashi sama Tayi shiru yace "badake nakeba "Ina sauri inje gida nayi darene fada nake gudu. "To meye ajakarki haka? Takalleshi atsorace gabanta yafadi akaro na biyu "nashiga uku asirina yatonu ni Aminatu shikenan sai kwanan gidan yari nasan baxan tsiraba ayau..... *Auntyn S&S*💘 Da *Ummiey Xeey* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *UⓂMIEY XEEY* _Kutayamu addua, Bata da lafiya...Allah ubangiji ya baki lafiya yasa kaffarane... Allah ya kawo maki sauk'i dear...Ina yinki sosai...Karki damu Allah na Sonki sosai domin bayinshi na kwarai yake jarabta da ciwo....Get well soon dear..💞💞_ *PAGE 75-80* gaban Aminatu bai daina faduwa ba,haka jikinta yafara rawa dakyar tasamu ta dake tareda kankame hakarta akada kam Securityn ya matso dab da ita yana karewa fuskarta kallo yana wani miskilin murmushi Bata yadda sun hada idanu ba kanta na kasa tana addu,ar kubuta aranta Yakawo hannu zai karbi jakar yana fadin "bari na duba jakar inga nawa muka samu intayaki kirgawa ko kanwata. Yafada yana kallon fuskarta da murnushi kan fuskarsa Ta hade ranta tare da fadin "kada ka sake katabamin jaka tunda ba aikena kayiba inkudine sai abaka konawa ne amma banyarda da sai ansamin hannu ajakaba Tana gama fadin hakan ta xuge cikin jakar yana lekowa yana muzurai ta bashi yr one k biyu ta zuge tayi masa sallama agaggauce tayi gaba tafice ahotel din tana hamdala ckn ranta da Asirinta bai tonuba gashi cindon yana gefe gefen jakar acan ciki aleda baka Tana futa tayi saurin tarar dan sahu sai unguwarsu Alokacin data isa gida tayu sa,a bakowa a unguwarsu anyiyyi bacci domin goma da rabi da muntina Ta tura gidansu ahankali tashiga duk da makafin iyayan nata ba fada zasui mataba insunjiyo tayu daren Da Sassafe bayan ta gama dumamen tuwo ta xubawa iyayanta takai musu daki tashige bandaki tayo wanka sannan tashirya ta xumbula hijab tafuce gidansu Murjanatu Itanma tashirya tunda tasan da tafiya gun dan tusbbun don shikam da safiyar Allah akafi ganinsa don in rana tadaga layi ake tararwa makil gun yakeyi da mata Sun sami ganinsa da wuri yayinda suka bashi abinda suka samo wato cindon yakarba yabata turare yakumace ta saurari yau zuwa gobe zataji kiran ma,aruf awaya ko kuma taganshi akofar gidansu. Da murna suka baro gunsa yayinda murjan keta famfata akai <><><><><><><><><> Abangaren momy kuwa takwashe komi tagayawa dady tun dawowarsa daga lokojan Shima saida idonsa yagane masa don yafi sati da dawowa amma ma,aruf baixo masa sannu da zuwaba yaimasa waya ma baixo gidan ba saidai yasameshi a office yatausayawa dan nasa domin duk yarame ya futa hayyacinsa Basuyi wata kwakkwarar magana ba sai gaisuwa kawai daya hadasu Yayinda dadyn yatashi hankalinsa yahada kan manyan malaman unguwa unguwa yabasu abin sadaka suka dukufa yiwa dansa addu,a Akwai wata juma,a ma dayaje har office din Dr ma,aruf din yasakoshi agaba suka tafi masallacin juma.ar sbd za,ayi masa saukar karatu Bayan an idar da sallar juma,a aka tsaya yin saukar karatu Wanda akeyi dominsa ma saida suka bashi qur,anin yana kusa da dadyn yana rike da alqur,anin jikinsa asanyaye yabude inda yaga kowa ya bude yafara karatun dayaga suma sun fara Ma,aruf yanada sani akwanyarsa tun yana shekara goma aduniya ya sauke alqur,ani sannan dayakai matashima yayi saukar hadda Tabbas banda asiri kaddara ce da baxai cishiba kuma yaci ma,aikin Allah ma banda haka ma,aruf akwai ibada kuma yana amfani da saninsa Yayinda aka gama saukar karatun akayi sadakar yan qur,anai masu ixu bibbiyu sannan aka raba carbuna Anan wani amintaccen malamin dadyn me suna malam badamasi yabaiwa Dr rubutu yace maza yashanyeshi agun Ba musu yasha kana malam badamasin yace nasati guda zairinga bashi don haka ko yazo ya karba dakansa kokuma zairinga aikawa dady saiyaje can gunsa yakarba kada yayi wasa fa Yaja kunnansa sosai Dady shiya dage akan dan nasa domin akullum in ankawo masa rubutu daga gidan malam badamasin saiyaita yiwa Dr waya har saiyabiyo ta office dinsa yasha kana hankalinsa ke kwanciya A ckn satin ckn ikon Allah komi yafara dawo masa dai dai yafara dawowa hankalinsa Hayyacinsa yafara komowa jikinsa saiya zauna yaita tunani shi kadai yana mamakin yanda akai ya auri lubna Ko a office saida yarutsa abokinsa Dr lurwan yana masa tambayoyi akan ya akai ya auri Lubna dole yasan yanada masaniya akai Dr lurwan bai boye masa komiba akan irin abubuwan daya ringa faruwa Har hawaye yaxubda Dr lurwan yaja kunnansa akan kada yanunawa lubna ta farat ta daya kurenta yabi asannu tukun Kuma yace yadage dayin axkar da addu,o,in kwanciya bacci kada yaringa sha,afa don anfi cin mutum yaki in yai sake da yinsu Dt Lurwan yaiwa dady waya yafara labarta masa yanda tafara kayawa Sosai dadyn yaji dadin kasancewar abun Lallai Allah Almusawwiru ne tabbas duk wanda yariki Allah da Alqur,ani zaiga haske ackn lamuransa koda aduhu yake to inya dage duhun xai yaye Dady yaiwa momy albishir nakaryewar asirin jikin danta Itanma murna tayi sosai tamkar tasa ruwa akasa tasha domin kullum itanma ackn addu,a take Akan Allah yajuyo da hankalin danta kansu yafitarshi atarkon shedaniya lubna abd afarko taci alwashin xuwa gun wani boka azariya yakarya sai kuma lurwan yaita mata wa,azi akan babu kyau xuwa gun boka yaita gaya mata dimbin zunuban da ake kwasa da kuma makomar me riko da zancen bokaye da yarda da abinda suka fada To tunda ta wullar da shirka ta dukufa akullum yi masa addu,a Ita yanzu abinda yafi daga mata hankali yanda yar,uwarta da suke subiyu rak aduniya ta juya mata baya akan " yarta tabbas ta tafka babban kuskure wajen hada wannan Aure gashi abin yasha mata kai Dady yaringa tausarta yana kwantar mata da hankali Taringa cewa dadyn " dole inyi kuka dady domin nasan Alhakin *yar makafi* ne yake bibiyata nayanda nashige hakkinta akan dana Na tabbata da ita agidansa da wadannan abubuwan basu faruba Dady yace "ai komi da kk gani arubuce yake agun Allah dole sai hakan ya faru kuma kaddararsa kenan dan haka komi yaxo karshe kuma. Abangaren Lubna abubuwa sun fara tsaya mata cak lamarin yafara bata tsoro naganin yanda ma,aruf yaje juya mata baya a gadon Aurensu Inta sakashi yai mata abu take zai hade rai ko yabita da mugun kallo Jikinta yafara bata lamarin yai sanyi knn In yana gida sai yaita tsare mata gida baya fara,a sannan yadaina cin abincinta ko wani lemo ahannunta tana gani xai shigo da take away yaci abinsa ko kallonnta bayayi Data gayawa maminta ta waya saita dorata akan bata again sbd cemata tayi to xaman me takeyi dabata koma gun malamin nataba asake taro matashi kada abin yabaci Haka tayi niyya kuwa domin komawa tayi gun dan tsubbun nata tayi masa jawabin komi Wata dariya yaringayi mata yana cewa " saidai kiyi hakuri yarinya kibi wata hanyar domin kuwa kin gama cin duniyarki da tsinke abu yakarye tun tuni wanda baxai taba gyaruwa ba sbd iyayansa atsaye suke akansa da addu,a inkuma kk matsa zan mutu koke ki mutu saidai in wani wajen zaki canxa badai nan ba domin babu abinda xan iya mk. Haka ta tashi jiki asalube takoma gida Data fadawa maminta yanda sukai da bokan saita hauta da fada " to dan yafadi hakan ke kuma saiki zauna lallai kisani xaman gida yakusa faruwa akanki domin kinsan tunda akai hakan Zulaihat baxata barkiba agidan danta don haka maxa kinemo wani malamin ayi wani abun akai Duk ta furgice ta baxama neman malami amma abin mamaki duk inda taje zance dayane akance mata tabari abun yalafa inko ta dage komi xai iya faruwa sbd ayanzu wutar tsanarta ke ruruwa zukatan mijinta da iyayansa Dole ta hkr tasake dabara ta kwantar da kai tahau masa biyayyar karya Itace gaidashi abinda batayi ada ko inxaisa takalmi tayi sauri tasunkuya tayashi Baya hanata amma baya amsa mata gaisuwar ko fara,a yakeyi inyana waya data doso shi yake hade rai don baitaba jin irin tsanartaba sai alokacin Haja taita jurewa tana ahnaye bakin cikinaa domin har hantararta yakeyi Abinda yakeyi mata ada kafin aure kadanne akan nayanzu data saiwa kanta tsanar Lurwan abokinsa shiya shige masa gaba sukaje har gaban momy yadurkusa har kasa yabata hkr akan abunda yai mata bada saninsa ba Taringa share hawaye tana cewa " kayya babana ai ninajanyo nice ummul,aba,isin komi niya dace na nemi yafiya agunka Fatana dai ayanzu inka yafemin kaje kabaiwa Aminatu hkr sannan in bata tsaida mijiba sai atura manya suyi magana Wani sanyi yaji aransa data tuna masa aminarsa yasan amina nasonsa bakuma zatayi fushi dashiba Addu,a yahauyi akan Allah yasa aminar bata fidda mijin aureba Dr lurwan shiya rakashi har gidansu aminar Alokacin tana kan sallaya ta idar da sallar ishsha,i tana laximi tana neman tuba nayanda ta aikata sabo arayuwarta Saijin sallamar yaro tayi atsakar gida wai ana sallama da ita Taji mamaki amma data ji yaron yace taxo inji Dr ma,aruf saitaji wani sanyi tareda cewa yaje yace tana xuwa. Ba bata lokaci tafuta Har kasa tagaidasu yayinda dr ma,aruf yatsira mata idanu Lurwan ne yafara magana yace " Aminatu saikika ganmu ko? Tace " Eh mana ainayi mamaki kodon ba abin mamaki bane tunda tunda ango natareda amarya wacce akafi sonta fiye da kowa....Dr ma,aruf yatsata da sauri " kada kice haka zinariya ina ckn wani haline wanda fadar sama babu dadin ji kada atsaya tone tone ma yanzu dai yafiyarki nazo nema na alhakinki dana dauka ba sonki nadaina ba amina har yanxu kece axuciya kuma nadawo da zummar in aureki koda agobene Ranta fari qal tayi murmuahi tace " to ai babu matsala domin nima xuciyata har yanzun kaine saidai fatana karike alqawari kada asake kwatawa Da sauri yace " insha Allahu hakan baxata sake faruwa ba yanzun dai yi mana magana da baba. Tajuya ahankali tasami baba adakinsa tagaya masa zuwan su Dr ma,aruf Shima baban yaji mamaki yakuma yi farin ckn dawowar Doctan Sungaida babanta ckn mutunci sannan sukayi masa bayanin komi basu boye masa ba Yatausaya wa ma,aruf nan yabashi addu,o,i na tsarin jiki Godiya ma,aruf yayi yakuma cewa baban nan da kwana biyu iyayansa xasu zo don atsaida ranar aure To tun daga nanfa hankalin masoyan yadawo jikinsu akwana biyu suka sake curewa tamkar basu rabuba Murjanatu ta tayata murna sosai Yayinda dady yahada tawagar abokai da wani dan.uwansa sukaje gidansu aminatu suka kai kudin Aure aka tsaida sati guda Asatin momy tahado lefe da kudinta kuma taita jan kunnen ango akan kada yasake yanunawa lubna alamar ma zaiyi aure don tana tsoron kada tayi wani abin afasa Dady yaringa dariya yace "yau naga uwa na tsoron makircin "yarta toki kwantar da hankalinki ma babu wanda ya isa ya tsaida abinda Allah yanufa komi xatayi akai baxai taba tasiriba don muna tayin addu,a akai muma Momy tace " walh dady ni nafison ma yasaketa kawai ko hankali yakwanta. Dady yace "akan me babu inda zataje barta ta zauna adakinta kuma gida daya xasu zauna gara taga takaici ko yayane tunda matar shige bata daraja ita dakanta zata kori kanta...... To wannan kenan *muje xuwa nabilancy luv and Ummiey xeey* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* 😘 *Shout out to you guys.............* _Emnoor Ahmad don💞_ _Neenah cool💞_ _Baby Ameesha💞_ _Muneerah💞_ _Mariam tijjani💞_ _Mar°ahmad 💕 And_ _All the members of Zauren UⓂmiey Xeey💞💞_ Thanks for your love, Ina matukar godiya da addu'anku kuma Alhamdulillah, Ina samun sauk'i....Allah yabar zumunci... *Ameen* *PAGE......80..85* Sati Daya yarage ayi biki aka kai lefe gidansu Aminatu akwatina takwas shakare da tsadaddun kaya kawayen momy da "yan unguwane sukai mata kara suka kai lefen Yar uwarta ko leke balle suyi waya mahaifiyar Lubna hjy hauwa,u. abinda momy ma bata saniba hjy hauwa,un kara kullatar ta tayi aranta naganin Ma,aruf zaiyi Aure basu hanashiba tasanma da gayya akai hakan dan a bakantawa yar tane Abin yataba zuciyar momy duk da tasan abinda yafi hakan ma na iya faruwa atsakanin su Dr ma,aruf sai doki yake ji yake tamkar ayanzune zaiyi aure gani yake ma afankon sa yake domin lubna bata gabansa bata isheshi kallo ba kowa safgarsa yakeyi garama ita takanyi masa shishshigi alamarinsa shike gwasaleta Ankai lefe da sati guda yana gida da safe yafito awanka yana shiri zaifita yaje suyi rabon IV shida Dr Lurwan Lubna ta fito ta zauna akusa dashi ya matsa daga jikinta yana tattare katin daurin Auren daga kusa da ita Takalleshi anutse tace " yaya inada magana me muhimmanci. Batare daya kalletaba yace "abarta saina dawo daga rabon IVn Aurena. Ta yamutsa fuska da takaici da qunci aranta tace " yakamata kasaurareni bawata doguwar magana bace. Yace "ok inajinki kiyi sauri kada kibatamin lokacina. Yafada yana duba agogon hannunsa Ta gyara xama tace " naje asibiti anyimin awon fitsari angano inada shigar ciki wata biyu. Yakalleta da sauri Tasaki ranta ganin kamar zataci nasara Tace " Allah yasa abinda ke cikina yasami karbuwa agun mahaifinsa domin in kaki bashi kulawa bansan yazanyi dashiba. Ya murmusa yace " to naji Allah ya inganta Amma ba haka naso ba naso ace matar danafi kauna Aminatu Autar mata itace zata fara samarwa momy jikan fari aduniya bake ba. Ya mike tsaye yana zuba kati ackn wata leda Tahau goge hawaye tana fadin " amma dai ko me xakace dai danka ne baka isa ka haramtawa kanka shi ba tunda kaikayi ajiyar kafin arabamu...."waye ya raba mu? Yawatso mata tambayar baxata Ido ckn ido tace dashi " kafi kowa sani ai tunda har marina tayi agabanka kuma tashiga tafuta taga kadaina sona alhalin ita ta kulla soyayyar. Ya fahimci da mahaifiyar sa take sai yayi murmushi kawai baxai taba nuna mata damuwar sa akan duk wani abu daxatace akan abinda momy tasa akai masaba don karta samu kofar caccaba masa magama kullum Tayita kuka tana fadin maganganun dataga dama Shiko yai burus da ita yadauki jakarsa yafuce Takaici yasa tahau cilli da kayan dakin tun daga kan bedsheet har filillika da kayan kan mirro Tayi tsammanin zaiso abinda ke cikinta domin da likita yagaya mata tanada cikin ba karamin farin ciki tayi dashiba Tunda tasan dole in akace dan fari za.a soshi fiye da komi zakuma adokanta dashi haka tasan jikan fari nashan tattali agun kakanninsa To amma tun ba,aje koina ba taga hakanta baxai cimma ruwa ba tasan tunda uban dan yaki nuna farin ciki ba tantama kakannin ma baxasuyi dokin zuwanba Tayi shiru tana tunanin mafita Can tace aranta "dolene na sake wani shirin zanyi maganin ka yaya ma,aruf da duk wani da xai hanani rawar gaban hantsi koda zan rasa raina ne. Ankarbi lefe daga gidansu Aminatu anyi karamci da mutumtawa yan unguwa da makwabta sunyiwa maman Aminatu kara sosai An yaba kayan lefe yayinda aka basu tukuici me tsoka suka tafi suma suna yaba musu <><><><><><><><>><> Anyi biki cikin kwanciyar hankali yayinda amarya tace ba wata bidi,a da zatyi itakam albarkar aure take nema Angon yaji dadin hakan kuma ta burge kowa Amma su murja ba.a so hakanba Part din aminatu komi need yasha tsaddadun furnitures da ango yaxuba mata komi shiyasiya labulaye masu tsada yan ubansun haka kayan wuta da kayan kicin shida Dr lurwan sukaita zaryar siyayya Duk abinda sukai a part din Aminatun lubna bata san sunyiba balle wataran aiyiwa aminatun gori Kayan gara kuwa taxo dasu na burgewa da yabawa iyayanta sukai mata Babanta yayi bajinta Sadakinta dubu hamsin ta mallakawa babanta kyauta tace yakara jari domin su rike kansu Iyayanta sunyi mata addu.a sosai don sun rabu lfy kafin akaita gidanta saida aka fara kaita gidan surukanta sukai mata nasiha Dady yaji dadin ganin wannan rana Dan sa ya auri cikar burinsa Haka momy tamkar ta lashe aminatu dan so da qauna Kai tsaye aka wuce da ita gidanta amma har dakin kishiyarta lubna aka kaita akai musu nasiha tareda danka amanar amarya ahannun uwar gida Ba yabo ba fallasa tace ta karba badan tasoba ganin idon mutane ne yahanata yin tijara don taciwa zuwan aminatu gidan wani buri ta kudiri aniyar saita axabtarta ta yanda xata bar mata gida da kafarta...... <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> Bayan Aminatu Amaryar Dr ma'aruf, Sun fita daga dakin Lubna, Hannu tasa akai ta fara kuka mecin Zuciya, Wani bakin ciki taji a ranta wai yau ma'aruf zasu raba wajen kwana, Wani zuciyan kuma tace Karki damu Ba dadewa a gidan zatai ba zan koreta Bangaren Su mumy kuwa anyi biki Alhamdulillah, Ita kanta dataga Aminatun hankalinta yafi kwanciya da ita, Take Sanar da Dady ita YAR MAKAFI ta mata da ganinta akwai biyayaya Dady" Yace uhm Allah dai yasa albarka ai tun farko abun da naso na Nuna miki kenan kika kasa ganewa, Dadyy Yace nima yarinyar tamun Gaskiya, Sai mui musu fatan zaman lafiya, mumy tace Hakane *Su Dr ma'aruf Ango* Suna zaune da matarsa Aminatu, Ya kalleta Yaji wani farin ciki ya mamaye ko INA na jikinshi dan har kwakwalwarshi, Murmushi yake tayi, Duk da akwai mayafi a cikin Aminatu bai hana taga Murnar da mijinta yake ciki ba, Bude fuskarta yayi, Yace Amarya ta bude mana in Ga Kyan fuskarnan naki Tana Dan jin kunya amma haka nan ta sake jiki saboda ita ma burinta ya cika Nan dai suka tashi sukai yanda addini ya koyar damu kafin a kwanta idan an kawo amarya...lol °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Lubna kuwa tana ganin 11pm yayi hankalinta ya tashi, Ta ayyana a Zuciyarta yau dai ba Su ba 1st night Toofaa Su Ma'aruf kuwa sunyi wanka sunyi Sallah, Ma'aruf ya mike, yasa jallabiya, Gaban Aminatu ne fadi, A zuciyarta tace tabdijam, Tana kan sallaye Yace zo muje mu kwanta ko zinariya, Uhm hmmm uhmm tace" ya gane nufin ta se yai shuru, yazo gabanta Yace" haba dear ki tausaya mun mana, ki duba halin fa na shiga some month's back, kwata kwata se ahankali, Aminatu Tace" uhm hakane, Nan ta mike duk jikinta a sanyaye hade da kunya Taje gefen gado ta zaune, zuwa kusa da ita yayi ya cire mata mayafin dake jikinta sannan ya koma ya kashe wuta toofaa, Ya dawo gareta ya fara cire mata kaya, tun tana bata so hardai Mu kaji wasu sound na tashi ....Nan muka bar dakin da gudu nida _Nabilancy_ lol Suna cikin tsakiyar soyayyarsu sun tsunduma, Tun Aminatu na kuka har ta hakura, Makira kuma lubna tana jin abubuwan nata wakana ta fara bugu musu Kofa tana kuka, Tana ma'aruf cikina, Cikina, Cikina, kazo ka kaini asibiti, Shi kwata kwata baiji ba Dan hankalinshi baya jikinshi, Aminatu taji nan ta tureshi tace' Ya habibi...matarka na kira, Wai cikinta, Wani tsaki yaja ya kara kankame Aminatu Yace" please forget about her, Ita kuma Lubna haushi yabi ya isheta kaman tai hauka, ganin Ma'aruf be fito ba ta shige daki, Cikin tsakar Daren nan ta kira maminta, Ta Sanar da ita abun da ma'aruf yai mata Maminta tace" karta sama damuwa badai Yar makafi bace, Sai sun Ga bayanta Lolz..ranar dai Lubna batai Bacci ba Dan takaici da bakin ciki Su Dr kuwa an kwana an hantse, Tun asuba Suka tashi suka gyara jikinsu Yai mata godiya sosai da ta Adana mai budulcinta, Ita dai Meenah uhm kawai tace Dan taji abun da taji, Haka dai Suka ci gaba da cin amarcinsu, har One week Aranar da Aminatu tacika sati agidan mijinta aranar ne yatara su dukansu afalonsa domin yayi musu nashi nasihar tareda tsara musu yanda kwanan girkinsu zai kasance Sunfi minti talatin azaune suna jiran uwar gida lubna amma shiru bata fito ba Harya gaji yasake kiranta awaya saicewa tayi yayi mata hakuri gatanan dai zuwa cikinta ke juyawa amai tagama yanzu Yana kashe wayar yakalli Aminatu data kagara takoma dakinta Yace ""kiyi hkr fa xinariya kinsan harka inta hada daku mata dole saida hakurin kinji wai batajin dadin cikinta ne amai ma tagama ayanzun xata fito inta gama kintsawa nasan kin gaji ko baby nah? Yakarashe fada yana kashe mata idanu Tayi murmushi tace " bakomi habibi muyi mata uxiri tunda ba ita kadai bace Tana rufe bakinta saiga lubna tafito tana yatsina duk fuskarta acukule kamar tafasa kuka ganin yanda Aminatu ke zaune ajikin ma,aruf gashi ta tsula kwalliyar burgewa tayi kyau kamar a saceta Wani kishi yatsaye mata arai Ta nemi guri kusa da ma,aruf itama very tight ta zauna kusa dashi ta matse dashi sosai tana wani shagwabe fuska Yagano nufinta Sai ya kyasawa Aminatu ido alamat ta matsa itanma Aminatu ta fahimta wayis, sai ta matsa adabarance Yakalli lubna da bacin rai yace " ke wane shirmen banzane wannan kinzo kinwani kwakubeni kamar zaki shige jikina ko kunya mutane bakyaji. Cikin tsiwa tace dashi " wane kunya zanji nida mijina nasan babu wacce ta isa ta hanani ne tunda kafin asan dadin jikin namiji nina fara sani kuma kome za,a dandala dai ajikinka saura nane ba.a isa anuna min kwarewa ba walh dan ba wayewa akafini ba ato inma da rawar kai aka shigo to amaidashi bakin kofa....ke saurara haka.! Ya daka mata tsawa tayi shiru da sauri Yafahimci inda ta dosa yakuma san sai yayi dagaske zata bar gasa wa aminatu magana Yakara hade ransa yace "ki saurara da kyau kijini ba hauka yataramu ba kuma ba neman rigima akace muxo yi nan ba kibude kunne kijini dakyau Lubna tayi tsai da ranta take ta nemo nutsuwa ta antaya akanta domin taga mutumin nata babu wargi Ya matsa daga jikinta data kwakubeshi kamar takoma cikinsa Yaxamo babu wacce ta rabeshi cikinsu Yafara musu nasiha afarko kana yafara da tambayat lubna yanda zasuyi girki dakuma yanda xa.a raba kwana Tayi yatsina taturo baki tace "nikam kwana dai -dai nakeso karinga mana don banison karinga nisa dani sbd muna bukatarka akusa damu nida son dinka. Yayi murmushi kawai yakalli Aminatu yace " to kefa yayi hakan ko kinada naki tsarin? Da sauri lubna ta tari numfashinsa " duk wani tsari nata ai ba tasiri zaiyiba garama tayi shiru domin tsarin danai dole shi za,abi Ran Dr ma,aruf yabaci abinda yatsana da mutum kenan katsalandan fadi ba.a tambayeka ba Yace " ke na tambaya ko yaya? Kada nasake nasake jin bakinki inhar ba tambayarki nayiba stupid Ta kule tahade girar sama data kasa jin ya xageta agaban kishiyarta (Ke Kikaja Lubna Allah yakara) Aminatu tace " habibi aiduk yanda kace hakan xamuyi koda satine ai kai zaka tsara tunda kaine damu kuma kaine me kwanan banda tacewa amma ni shawarata anan tunda yayata tace kwana dayan takeso to ayi hakan mana kaga kada danka ya cutu ko kuwa? tafada tana dan murmushi na kissa Yace " babu wani zancen d'a na domin sai yazo duniya za.a kirashi da d 'an tukunna don haka kusani kwana bibbiyu zan ringa yi muku kuma kowacce tayi girkinta daban tunda kowacce nada store da kicin abangarenta don haka banison nan gaba inkama wata da neman rigima Yanuna lubna yace" danhaka ke lubna yau ina sashinki fakat kowacce ta tashi ta koma bangarenta Aminatu ta mike da sauri takoma bangarenta Shikuma yamike yafuce don gidan momy yakeson yaje zasu futa da dady Lubna tahau cixar yatsa tabbas inbatayi wani abun akaiba to zata xama koma baya agidan kirkiri ma kada taxo tana gani Aminatu taci abinci akanta don namiji shike badakai Takira wani malaminta awaya tasanar masa abindake faruwa da ita Nan yace mata saitaxo da wuri yahada mata mallaka da kuma magungunan tsari kafin tata taxo karshe agidan..... *Wannan kenan* For Comments 08164640126 *Lolz..I knw you guys are eager to see what will happen next...Awwnnn kuci gaba da biyomu a sannu* TEAM YAR MAKAFI *(Y.M)* _Ummiey Xeey and Nabilancy_ [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* _INA KUKE MAKARANTA...KUKASANCE CIKIN SHIRI DOMIN SHAHARRIYAR MARUBUCIYAR NAN *NABILANCY💘* NANAN KAWO MUKU WANI LITTAFI ME SUNA_ *TARAIRAYA* Karku bari a Baku labari *PAGE 85...90* Aminatu na zaune Afalonta tana kallon Arewa 24 Nabila Nasir nagabatar da shirin yan drama wato kundin kannywood Ta bada hankalinta agun taji daga can _compound_ ana rafka sallama Ta rage volume tana amsawa tareda xubawa _door_ din ido saida tayi tsai kana tagano muryar kawarta murjanatu ce Da murna ta tarota suka zauna a three siter suna fara,a Murjanatu takama baki tana kallonta da mamaki da sha,awa tana cewa "kai kawata tabarakalla masha Allah kinganki kuwa? Aminatu ta murmusa tareda gyara xama tace "bana son zolaya murja meye na mamaki da ganin nawa Haka? "bari kawai kawata kin canza da yawa fa kalli fatarki har wani sheki take kamar silva ga wani fari da kk kara kodai anyi tintibe ne Ta kama baki tana dariya tace " hhhhmmm to nagodewa Allah dana samu canji mekyau ammafa bawani tintibe danayi don nasan nufinki ciki ko? To babu komi. Tafada tana shafa cikinta Murjan tahau fadin " haka dai kk ce. Nan suka hau hira har kusan wani lokaci Kana Aminatu ta tashi tashiga kicin tayi musu girki shaf shaf makaroni jalof tasha kifi sannan ta hada musi lemo me sanyi dake tanada furji a kicin din Nan murja ta kwashi gara Da suka gama sukai sallah biyu tayi Murja ta karkace tace da Aminatu " waini ina matar gidan ne naji bangarenta shiru kada dai xaman doya da manja kukeyi? Aminatu tace " ni ina ruwana da shiga safgarta ai tunda nazo gidan nan sau daya muka hadu banda ranar dana shigo gidan nan Murja tace " aikon dai kada kiringa shige mata dan walh inta sami guri zata iya cutarki Domin lubna muguwa ce natabbata ayanzun hakan xatayi yanda tayi takoreki agidan nan balle tasan kece matar SO Sannan kuma abinda nakeso dake shine kitashi tsaye kema ba zama xakiyi ba afitarki da asiri zagewa zakiyi kiringa mallakar mijinki baji bagani inkin zauna kiga zama ba ruwana Aminatu ranta yabaci da kalamin murja tace " niko ayanzu me xanyi banda bautar Allah da rike mutumcin Aurena sabon Allah yayi hagu nikuma nayi dama masu yima Allah yaganar dasu amma nikam nabarshi wanda mukai ma ada kullum cikin neman yafiyar ubangiji nakeyi dan haka kada ki kara minxancen yin asiri ma dan baxan yiba Murjanatu taringa kallon Aminatu da mamaki najin tana mata banzan kalamai Tace " lallai aminatu kin haukace ashe wayonki yafara yin baya to aiko baki isaba dole ne kiyi abinda xaki kwatowa kanki yanci gun miji yaxamo kin wuce uwar gida akullum yaringa ganin haskenki akanta don...." ke dakata murja natu akullum mijina yana ganin haskena kuma inada " yanci agunsa wayo kuwa indai akan nabar yin sab'on Allah ne to daga yau akirani da gab'uwa ma ato. murjanatu taga abin na Aminatu gaskene saita kule harda harxuko mata sbd tasaba yi mata hawan kawara ko tai mata dole Sai taga sabanin Yanda sukeyi ada taga wannan karan Aminatu ta butsare mata harma taga kamar ba aminatun taba domin itanma kanta tayo da fada da masifa tana fadin " kada ki kara dagamin murya akan nafadi gaskiya baxai yiwuba kixo har cikin gidana kiyimin dole baki isaba mijina ne kawai ya isa yasani tilas shima bata wannan hanyar da kk biyomin ba don tunda nadawo hanya banga wanda ya isa yasani na koma b 'ata ba never walh Murjanatu ckn bacin rai tace '" Aminatu yau nikikewa haushi aka? Amina ckn karaji tace " siya kikayi kuma har dakina kk shigo dole ki karbi abinda kk gani dan haka kada ki kara xuwar min gida da wannan fuskar inhar baki canxa kudirinki akan aurenaba kin dawo hanyar arxiki toki rike xumuncinki kawai wanda mukai ada ya isa amma nikam ayanxu natuba nabi Allah, Da ma tun farko ba halina bane, Kece kika jani kuma Alhamdulillah, yanzu na gane gaskiya... Murja tayi galala tana kallon amina da takaici cike fal rai tace " yanzun waini kike kora harda min gorin gida. Eh lallai dama haka dan talaka yake . "Nagode Amina" Kinzama kaxa samu kiki dangi dan haka kirubuta ki ajiye ni murjanatu isyaku inhar nafuta daga gidan nan baxaki kara ganina ba inko kk kara ganin kafata tokiyi duk abinda kk ga dama da ita. Tana gama fadin hakan ta figi jaka da gyale ahanu tafice harda guntun hawayen bakin ciki. ( yalla maxa ki kara gaba makira uwar shagalallu abi wani sarkin dama Fans din Aminatu basa qaunarki barema yan taskar Nabilancy da zauren ummiey Xeey akule suke dake da kika bata musu Zinariya lol murjanatu nashirin futa daga cikin gidan ta tura get zata futa afusace ita kuma lubna tana shigowa gidan Sukai kicibus Tsayawa sukai suna yin kallon kallon Babu wacce tacewa kowacce ko kanxil suka kara gaba kowacce na wassafa magana aranta Ita murjan ayyanawa take tabbas taga kyan lubna kuma taga wayewarta dole ne takwace miji gata yar masu kudi Dariyar mugunta tayi data futa a get din domin tasan wataran sai aminatu tayi kuka sbd tirjiyar datayi mata don tasani lubna yarbin malamai ce ba barinta xama zatayi agidan ba Ta kada kafada " jiki magayi ai. Idone nawa ta baya ta rago Itako lubna rayawa take "watoma har Aminar ta sami guri dahar danginta suka fara musu zarya agida toko sunkusa zuwan karshe tunda ba gidan ubansu bane kuma basuga guri ba takusa koro musu yar,uwa gida domin tasamo wani magani mesuna bankada kishiya dawa wasu kuma kance masa korata gida. Ba kowane malami keda basirar hadawa ba don yanada wahala wajen samun mahadinsa takashe kudi sosai kafin ta mallakeshi..... <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> Bayan tafiyar murjanatune Aminatu tai tagumin bakin cikin akan abubuwan data aikata, tana mai nadamar aikata Hakan, kukane yazo mata wata zuciyar tace ba kuka zaki ba, ki tashi kiyi abun da ya kamata, Aiko ta mik'e ta shiga toilet ta dauro alwala tazo tai Sallah tai karatun Qur'ani ta dakko charji tana ta ja tana Neman gafarar Allah, haka ta wuni tanayi seda Aka kira magrib sannan ta tashi saboda ma'aruf ba part dinta yake ba Bayan ta idar ta Sallah, Ta dakko wayanta ta tura ma ma'aruf text din love kamar haka... _Mijina INA alfahari dakai, Allah ya bar mana kai mijin Lubna da Aminatu, A gaskiya ina kewarka sosai, Ka kula mun da kanka Kaji mijina_ tai sending, On his way back, yana driving yaga text dinta murmushi yayi, a ranshi Shima ba karamin kewarta yakeyi ba, Driving yakeyi but be hana shi tura mata reply ba.. shima ya tsara text dinshi kamar haka _"Baby Luv, I miss everything about you, please take good care of your self kafin na dawo, I love you so much_ yai mata sending Tana karantawa taji wani Sanyi a ranta tace awwn...then ta ajiye wayar ganin ba part dinta yake ba, ta tashi ta dafa indomie da kwai se mango juice... Bangaren Lubna kuwa ganin har 7:PM ma'aruf be dawo ba ta cika tai fam, Ta ayyona a ranta da ace Aminatu ne da girki da yanzu ya dawo, Wani tsaki taja taci gaba da makeup dinta, Ta sako wasu Riga da wando, Ba laifi dai sun mata kyau lol, Tana zaune tana cin cingum, taji horn din motarshi, Wani dadi aranta taji, Ta tashi ta feshi dakin da tirare, Yana shuguwa Wani kamshi ya dakeshi, Ya kalleta dai, A zuciyar shi yana me Kyan dan majiji kawai, yai wucewarsa daki ba tare da Yace mata komai ba Yana shiga yai wanka, Ya sako Riga da Wanda three Quater, yazo fallow ya zauna tazo kusa dashi ta makalkaleshi wai she's missing him, Matarsa Ce be koretaba domin tana da hakki akan shi, kallonta yayi Yace where's my dinner? Nan lubna ta fara zare ido tace" am am inasha take away zakai mana Ya kalleta wulakance Yace akwai komai a gidan nai maka take away? Tace uhm uhm me kakeso to Ya daka mata tsawa, bana bukatar komai, Daki ya shiga ya dakko wayarshi, Ya kira zinariya, tana ganin call dinshi kamar bazatai picking ba sai kuma ta dauka, Yace hello baby Tace" yes dear andawo lfy? Yace lafiya lau, dama na kirane in akwai sauran abinci nazo na amsa Lubna bata da lafiyane bata samu tayi ba, Yasa hand free lubna naji Aminatu tace ayyah Bansaniba ai da gaba daya na hada nayi, Amma akwai indomie, kazo ka amsa to, inyaso sai na dafa Wani, Wani haushi da takaici ya is he Lubna, Yace" Ok ganinan zuwa. Yana gama wayar ya ajiye wayarshi, ya wuce part din Aminatu, Ganin ya fita ta dauka wayanshi ta fara bubawa, Wani Haushi sosai taji da taga conversation dinsu na love, kaman ta fasa wayan Dan kishi wai har YAR MAKAFI, ta fita Iya Love Shi ku ma'aruf Yana shiga part din Aminatu Wani Hug yai mata hade da hot kiss, yana sa mata albarka, Aminatu ta tureshi tace kaga Ba girkina bane Kar.......yagane nufinta kawai ya amsa Indomie ya wuce part din lubna na zauna yaci ya koshi, Lubna tace yunwa takeji yai mata nuni da kitchen alamar ta shiga ta dafa wannan na MATAR shi Shi ne. lolzzz ```Muje xuwa fans muna godiya muna kallon kowa da tasa soyayyar Allah yabar kauna kunayin mu munayinku luv u``` [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* _❣❣Awwnn our fans...we heart you Dearies...muna ganin comments dinku da yadda kuke son wannan novel din namu.....We love you buhut buhut❣❣_ *PAGE.....90<>95* Hakadai rayuwarsu ta ci gaba, Yanzu gaba daya Lubna ta rasa meke mata dadi, Ma'aruf kuwa Alhamdulillah daidai kwargwado yana ba kowa hakkinshi, amma kana gani ba sai ka tambaya ba yafi son Aminatu, Domin ta rike addua'a da addini Sosai, Idan ma'aruf na dakinta to rabi sallan dare ne rabi kuma suci soyayyarsu, Abun Ba karamin ma ma'aruf dadi yayiba, Domin tabbas yayi dacen mata ta gari, tana temaka mai sosai Wajen tsare addininshi Lubna kuwa saboda jaraba ta rasa gane Wai me Aminatu ta keyiwa ma'aruf ne, wai yafi son ta this and that dai, Sau tari lubna na jefan Aminatu da mugun Abu amma da yake ta rike Allah, ba abun da ke Samunta, Shima ogon nasu da yake yanzu a tsaye yake wannan kenan <> <> <> <> <> <> <> <> <> Akwana a tashi ba wuya, Aminatu ne kwance akan cinyar ma'aruf da yake weekend ne, ba Inda zaije kuma ya fado kan girkinta, Ya kalle agogo yaga 10AM Yace" Baby please ki tashi mu shirya Yau zamu je ziyara waje da yawa fa, batai mai musu ba ta tashi ta shiga wanka har yana tsokanarta ko ya zo yai mata ne tace A'a da sauri Dan tasan indai yazo to se sun kusan azahar, yace See you wasa ma ni nake miki nima bari naje nai Wanka, aiko shima ya shige toilet yai wanka, Basu bata lokaci ba suka fito suka shirya dama yace Susa Purple shaddan da sukai Anko na ranar bikinsu, Aiko Haka akai suka fito tamkar yaune ranar auransu Suka fito harabar gidan Aminatu ta jirashi yaje yai ma Lubna sallama tace" zata bishi yace Nop, ba yau ba, Wani haushi ya isheta Kaman ta kwalla ihu, Yana fita daga dakin tahau hawaye. Tana jin ya tada moto ta leka ta window, ganin shigar da sukai iri daya nan kanta ya fara juyawa saboda tsananin kishi aranta tace" metai wa ma'aruf ne haka...Mudai mukace ta bincika kanta lolz Suna tafiya suna soyayya abunsu har suka Isa gidan Abokinshi Dr Lurwan da matarsa Zainab suma suna shirin fita shan ice cream, Nan dai suka gaggaisa a tsattsaye sukace se next time sunanan zuwa susha hira, Dr lurwan yace Lolz in zakazo kazo da dayar Matar naka musha hira Duka, Dr ma'aruf yace rufan asiri in ba ai hira ba Asha dambe kuwa Duka suka kwashe da dariya, Su sukai motarsu Suna Su Dr Lurwan hakahaka °°°°°°° Tafiya kadan Su dr da zinariya sukai se gasu gidan mummy (Maman ma'aruf) suna shiga mummy ta amshesu hannu bibbiyu, Ganin yanda ma'aruf yai kyau ko yana gidan ta be beyi ba, lalle namiji yai dace da mata shi yaji dadi kam, Aiko mummy ta Kara ja musu kunne akan Su kara rike addini sosai, sukace ba komai Insha Allah, Nan Aminatu ta cire gyelenta ganin mummy batai wani gyaran gida ba, ta gyara mata ko ina harda daura mata abinci kafin Su tafi, Ba abunda mummy take Ce mata illa sa mata albarka, Dr ma'aruf ne yace Su tashi Su tafi, mummy tace INA zasu yace gidan Su Aminatu, mummy ta tashi ta shiga daki dakko kudi masu yawa ta baiwa Aminatu ta kaiwa iyayanta kuma tananan zuwa insha Allah, Aminatu taji dadi sosai, tai godiya suka tashi suka tafi <><><><><><><><><><><><> Tafiya suke ba'a dau lokaci ba se Ga Dr ma'aruf a kofar gidan Su Aminatu, Aminatu duk ta kosa ta sauka taje taga iyayanta, yana kashe motar, Aminatu tai tai ta bude kofar ta kasa Ashe ma'aruf ne ya kulle, Ta kalleshi zatai mai magana kenan ya kashe mata ido yace" *I LOVE YOU, I'M FOREVER YOURS* sannan ya Sakar mata murmushi, Sunkuyar da kanta tayi, Tace _I love too my habibi_ kannan ya bude da sauri ta tafi cikin gidan da gudu, shi kuma ya tsaya sakko da kaya a bayan bot, Sega murjanatu Zata fita, tana ganin DR ne kuma tasan tabbas tare da Aminatu sukazo sai ta fasa fitar Da zatai a cewarta Aminatun zatazo ta sameta a gida Nan dai Ma'aruf ya shiga aka zauna anata hira sosai, mama da baba se sa mai albarka suke, sukace Ga Aminatu nan amana, Yace ba komai, Ma'aruf ya gyara zama Yace dama munzo ne akan maganar aikin Da Za'ai wa mama, Zuwa next week insha Allah zanzo a dauketa mukaita ai mata aikin a ido, Nan sukaji dadi sosai ma'aruf yasha addua kala kala, mama harda murna tace ikon Allah idan Allah yasa zan sake gani zangani, sukace hakane, ma'atuf yace zasu tafi sukai sallama suka wuce gida Bangaren murjanatu kuwa har magrib, taga Ba labarin Aminatu, bata zoba ranta a bace tace lalle ma da ki kikeyi *Bayan Kwana biyu* ranar Monday *Aminullah* ne acikin mota yasha shadda me tsada yana hanyar zuwa Kano, tun randa Aminatu ta mai wulakanci be sake waiwayon kano ba...Ya tafi zaria har Allah yasa ya hadu da uban gida me kudi ya daurashi akan dukiyanshi, Da yake aminullah akwai tsoron Allah kuma baya cin abun da ba'a bashi ba haka ya sama karbuwa wajen uban gidansa, Tafiya yake har ya Isa kano, bayan yaje gidan iyayanshi be wuce ko INA ba sai gidan Su Aminatu, Yana zuwa yai parking, Da yake uban Aminatu ya ganeshi aiko suka shiga har cikin gidan, Nan shima ya kawo musu sha Tara ta arziki, ya tambaya INA Aminatu akace tayi aure, beyi mamaki ba SBD ha rabuwan da sukai, Yace OK dama nazone zuwa gobe mama zan kaiki asibitin Makka ai miki aikin ido dama already tun kafin nazo anyi booking komai _Too faaa Ga Ma'aruf kuma fa aminullah Duka sunada burin kai mama ai mata aikin ido...kuci biyumu hope kuna jin dadin labarin_ Mama tace" dannan da ka bari mijin Aminatu munyi magana dashi, Yai murmushi Yace" mama karki damu duk dayane, Kinga ni munyi maganar na bada kudin komai da komai, nan ko suka amince washe gari suka tafi asibitin duk bada sanin Su Aminatu ba... ikon Allah cikin sa'a anyi dayake ba wani aiki sosai bane se Ga mama ta fara gani garau, Kwanansu 4 aka sallamesu, bakuga murna ba wajen mama da da baba gashi basu da waya balle Su Sanar da Aminatu, Aminullah kam yasha addua kamar ba gobe °°°°°°°°°° Murja najin labarin Aminullah yayi kudi ta fara Neman hanyar da zatamai magana, Ko zai aureta, Aiko yai banza da ita Dan be manta wulakancin da tasa Aminatu tai mai ba, yasan ita ta zige ta tsab, sai yasa Yace duk randa ta Kara mai magana se ya babballata lolz Murja tace yau na shiga uku, Aminullah nan da na ke mai kallon a wulakance yau shine yai kudi harda moto, Ikon Allah naga ta kaina ni murjanatu Bayan an gama Komai Aminullah ya koma zariya abunshi, Bangaren Su Aminatu kuwa, Ran Saturday, sukazo gida da Dan maganar yanda za'ai ma Mamanta aikin, Suna zuwa sukaga abun mamaki, Mama a tsakar gida tayi kyau tana shara, nan ma'aruf ya kalle Aminatu, itama ta kalle shi. Har suna hada baki mama kinfara ganine da kike shara? Dagowa tayi ta kallesu tace mu shiga daga ciki mana yayana Nan suka shiga ta basu labarin yanda akai tundaga farko har karshe Aminullah ne ya biya komai akai mata,!! Ma'aruf kuwa se Tambaya yake waye wannan Aminullah, a INA yake ganin no need ya sani Aminatu tace" wani bayon Allah ne dake kula damu tun kan Mu hadu sai ya bar garin nan Ma'aruf be kawo komai a ran shi ba, Yace Allah sarki, Allah ya saka mai da alheri. Amma munyi murna sosai Tun alokacin Aminatu ta saura, Jinta take wani iri, inama Aminullah ta aura, Ganin yanda tayine Ma'aruf Yace menene? Ita mahaifiyarta ta gano setai mata nuni da ido tace ba komai Haka nan tace Ba komai, dakyar dai suka wuni agidan ta koma gida cike da tunanin *Aminullah* Bayan kwana biyu kuma still Aminullah ya dawo akai ma gidan kwaskwarima, akai fenti Sosai yayi kyau matuka kamar sabon gida Iyayanta sunyi Murna sosai sukasa mai albarka, Allahu Akbar Aminullah, ahanyar komawarshi gida yai hatsari ya mutu...Rayuwa kenan Nan danan aka kira gidan Su Aminullah akace ya rasu, kan kace meye labarin ya bi ko INA a unguwar domin Shi mutun ne me tausayawa mutane, duk ansanshi Nan Murjanatu ta kira Aminatu sanar da ita, Wani jiri ya kwashe Aminatu ta fada kan kado Kash......kuci gaba da biyomu TEAM YAR MAKAFI [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* _When Someone Walks Out Of Your Life, Let Them. They Are Just Making More Room For Someone Better To Walk In!_ *PAGE.....95...100* _QUARTER FINAL_ Ma'aruf ne ya shugo ya ganta a kasa, ya girgizata yaga alamar kamar bata nunfashi. Da Sauri ya dauketa sai asibiti, Akai mata temakon gaggawa sannan daga bisani ta farfado, Ma'aruf ne ya sanar dasu mumy, Sannan yaje gidan iyayan Aminatu ya dakko Su ya Sanar dasu besan meke faruwa ba Nan dai kowa yai jigun jigun iyayan Aminatu sunsan Komai, bude idonta tai ahankali Tace" Ina Aminullah Dan Allah, Nan ma'aruf ya tsareta da ido be gane me take cewa ba, Mamanta ne tazo kusa da ita tace" Aminullah, Allah yai mai rasuwa, wani rintsa idonta tayi hawaye suka fara zubu mata, da ita kadan tasan me take ayyanawa a zuciyar ta Ma'aruf ne Yace" Aminatu ganin iyaye sai yasa be ambato sunan da yake kirantaba zinariya ko Sweet baby, Yace" Dan Allah kiyi hakuri, though bansan ya kuke dashi ba kiyi hakuri, Nasan dawainiyar da yakeyi da iyayanki kiyi hakuri, Allah yafi mu sonshi, Nan ta kalle mamanta, Mamanta ta kashe mata ido alamar ta hakura karta nuna komai, Nan ta Dan tashi daga kwanchan, Da jin kina a jikin gadon, nan mummy tai ta mata sannu, kowa yana ta mata sannu, ana cikin haka saiga murjantu ta fado Wani kallo Aminatu tai mata da saida yan hanjinta suka kada, Murnajatu, ta gaishe da kowa da kowa tai musu ya hakuri, Kamar Aminatu bazata amsa ba se Kuma tace" Alhamdulillah, Nan murjanatu tace" Su mummy kui tafiyarku zan tsaya da ita nai jinyarta kuje Ku huta, Sukace" kai amma mungode, Allah sa miki albarka, Murjanatu tace" Ameen Ameen <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> Bangaren Lubna kuwa, shuru shuru har dare ma'aruf be dawo ba, gashi a dakinta yake, Ta hada mai abinci da juice me dadin gaske, tasha kwalliya kamar Sabuwar amarya, Ga ko Ina na dakin Kamshi yakeyi, har 9 taji shuru, kasa hakura tayi tazo har part din Aminatu ta kwankwas taji ko Ma'aruf na part din, nan taji shuru, zama a kofar part din tayi, Hannu tasa akai tana kuka wannan wani irin tsane Ma'aruf ke mata, da taga bame bata amsawa daki ta wuce ta dakko wayanta Kira tayi ringing 1, 2 yai picking, Yace" Lubna, tace" my Dr kana inane najika shuru, Yace" eyyah I wanted to call you bansa ma natsuwa ba, Aminatu ne ba lafiya ta fadi dazu a toilet, So I'm inanan zuwa anjuma, Eyyah tace duk da bason Aminatun take ba seda ta tausaya mata sannan ta kashe wayan tace kuma mtswww Allah ya Kara, se tauyemun hakkina ake akan wannan *YAR MAKAFI* Ma'aruf yana gama waya Aminatu ta kalleshi tace" ka tafi gida Ga murjanatu nan zata kula dani, Yace" kin tabbata? Murja da katsalandan tace" yap, Aiko yai tafiyarshi, Yace" idan akwai wani Abu a kirashi Bayan ya fitane, Aminatu ta kalle murja tace" meye ya kawo ki? ba mun raba jaha ba? Murjanatu tace Dan Allah kiyi hakuri, Wallahi nima mutuwar Aminullah dinnan ya sa na dawo hanya, na gane lalle duniya bata da tabbas, nima INA rokon Allah ya yafemun duk laifukan da nayi, Kuma Nima ki sani a addu'a Allah ya fito min da miji na gari da sauran yan'uwa da basui aure ba, Allah ya hada kowa da miji na gari Aminatu tace" *Ameen* yanzu naji magana, Nan dai Suka kamo wata hirar, Aminatu tace" hirafa ba Namu bane, Mui ta istigfari da hailala da salatin monzon Allah har bacci ya kwashe mu, Murja natu tace" haka ne Washe gari, Da safe da ma'aruf yazo, a dai dai lokacin da Aminatu tai amai, yana gani zuciyarshi ta bashi wani Abu, Anya ba ciki gareta ba Dan Sing of pregnant ne morning vomiting, Nan ko ya kira Nurse, aka mata PT test, Nan take ya muna Positive+ Alamun Ciki ne, Nurse din tace musu congrats, Ma'aruf ya rungumo matarshi, kwanansu biyu aka sallamesu Bayan An sallamesu ne, Ma'aruf Yace tai shuru Kar ta yarda lubna tasan tana da ciki, Dan sunsan halinta zata Iya zuwa tai asiri, duk da yanzu Alhamdulillah, ba abun Da zai Iya kamasu da yardan Allah Lubna ta shugo tai mata Sannu da jiki bekai Zuciya ba, Ganin yanda dakin ya tsaru yafi nata nan ma hankalin ta ya tashi, Ta da koma Daki Maminta ta kira take Sanar da ita, tace karta damu, Lubna tace" ke mamin nan Kullun na kira sai kice karna damu kinsan bakin cikin da nake kuwa? maminta tace" ke baki da kunya ko? Nan ta fara wasu maganganu ta kashe waya, Maminta tai tsaki itama °°°°°°°°°°°° Bayan Sati daya, Ma'aruf na lura da Aminatu duk rai Dan baki ta rame, daga ganta kasan akwai abun dake damunta, Ma'aruf ne Yace tazo suje bedroom akwai maganar Da zai mata, tana tafe yana binta a baya, suka zauna ya janyota jikinshi Yace" Zinariya, what's wrong with you, Duk kin bi kin chanza ko abinci bakya ci sosai remember I'm your husband, be kamata kina boye mun Abu ba, Ta nunfasa tace Hakane, wlhi rasuwar Aminullah dinnan yake damuwa, Yaji kishi sosai ya dai daure Yace" ya kuke dashi? Ta share hawaye tace" he was my 1st love, tun kan mu hadu da kai komai yake mana, Dukda Beda hali, amma ta dalilinshi na sama rayuwa me kyau, yana karatu lokacin a ABU zariya sai kai kuma ka kunno kai, Kasan Zuciya Murjanatu ta ziga ne wai Ga kai me kudi mezanyi da Aminullah, Lokacin da Kai aure baka kulani tayo Neman aure na namai wulakanci, Yaje wajen Murja ko zata shawo mai kaina itama nan tamai tatas, Shine tunda ya tafi zariya wajen uncle dinshi bansake ganinshi ba, Aminullah ya soni kamar me, ya share mata hawaye, Sai da Ga baya yana zuwa yana wa Su mama ihsani, Yakaita aka gyara mata ido yanzu haka ma ya gyara mana gida, shine a hanyarshi ta komawa yai accident taan gama fada Aminatu ta rushe da kuka a jikinshi tace" na cuceshi Amii ka yafemun Ma'aruf ya tausaya mata sosai, Dakyar ya shawo kanta Yace" yanzu tashi ta kare, Addua za'ai mai kawai, sannan ko da taga bata aureshi ba ,haka Allah yaso, matar mutun kabarinshi, kuma wani beta auran matar wani, tace" hakane, Yace" ki dena kuka, Addua"a zaki mai kuma zan bada kudi asai butuci da charbi, da a fanso al'qur'anai akai masallatai da sunanshi, ladan wqjen shi zai kai, Nan ta kalle Ma'aruf tace" kai amma nagode. Nagide, Yace" Ba komai Allah ya gafarta mai tace" Ameen tun daga ranar ta sake jikinta amma Kullun cikin Addua ta kema Aminullah *Bayan Watanni kamar uku* Akwana atashi babu wuya agun Allah yau Aminatu nada wata biyar agidanta tana samun tarayraya agun mijinta yayinda take ganin soyayya agun iyayan mijinta domin kuwa har xuwar mata momy keyi part dinta kawai suyi hira takoma gida batare da taje sashen lubna ba sometime lubnar naganin fitar momyn a mota driver yatafi mayarta gida takanji haushi sosai naganin fifikon da akai musu tsakaninta da *yar makafi* tasan kuma dan a cisguna matane dan haka bata taba nunawa afuskaba takan dai hadiye bakin cikin ne amma maminta nayawan tausarta akan kada ta damu inta haihi dole zasu sosata don zasu shirya asiri sosai wanda baxai karyeba Alokacin cikinta na wata bakwai ita kuma Aminatu cikinta yana wata hudu amma lubna batasan dashiba Dayake ita doguwa ce sai cikin yabi jikinta takara yin mulmul ta gyagije tayi kyau da yar kiba Cikin Aminatu nashan kulawa gun ma,aruf don har an fara zuwa awonsa °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Sosai yake tarairayar cikin nan bayason yaga tana aikin wahala in yana part dinta shike mata wanka harda wankin undis dinta dasu bra abinci ma abaki yake bata itakon tayita yi masa shagawaba inta narke ajikinsa tayi lamo tamkar wata mage Dayake lubna ba.a tare suke ba shiyasa batasan irin wainar da ake toyawa akan cikin aminatun ba Da ace zatasan koda kadan daga ciki tabbas da ansha rigima don dole zatace ana nuna mata bambanci Tunda akai scanning aka gano tagwaye ne maza acikin Aminatu sai abin yafi na da Tamkar wata baby haka yamaida don kulawa da lele Lubna da Aminatu, ya basu dubu dari na kayan baby, nasu kuma hamsin hamsin amma ita Aminatu dari biyu yabata tunda twins ne Account ya bude mata ta xubesu aciki Yakan yawan kaita gidan iyayanta amma sai awani karo tayi kusan wata bataje ba Haka dai rayuwarsu taci gaba da wakana.....bakuga Love din da ma'aruf yake nunama Aminatu ba tamkar zai mai data ciki idan suna tare Lubna kuwa ta zabga asiri amma INA duk a banza saboda Kadarinta yanzu ya Riga ya karyeeee *Muje zuwa masoyan Aminatu* [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *Neenah cool😍 and deejeh Queen😍* _Wannan page din nakune,.. Awwn aci gaba da gashi Allah ya Kara Basira_, readers Ku nema book din *NIEMATULLAH da SIRRIN AL_AJAB* _na Neenah cool da deejah queen domin sunzo muku da salo daban...._❣❣❣❣ *PAGE....100-105* RANAR wata Talata Lubna ta dawo daga awo gajiye ta shigo gidan domin tabiya kasuwa tayi siyayya Tashigo cikin gidan kenan tahango Aminatu tafito daga part dinta Ta tsaya jiran karasowar Aminatun tana kare mata kallo daga nesa Tabbas ta diga ayar tambaya akan Amina da alamar cikine da ita dan gashinan ya dan turo Doguwar riga tasaka takamata daga saman kirjinta takama hips dinta daya kara fitowa ga breast dinta sunfirfito suncika tantsan Kyan da Aminatu takara shiya furgita lubna domin ita ayanzu bata son takalli madubi ma sbd yanda halittunta suka canxa tayi baki dama mai ne ga hancinta yayi fos ya kara girma bakinta yakara tudu lebe yafito sambal Duk ta kumbura na masu ciki Lallai tasan karamin ciki aminatu kedashi tunda tayi tsulelen kyau fiye da yanda taxo gidan Wani kishi da tsanar aminar yakaru aranta Aminatu tahau murmushi data kataso kusada lubnan tace mata "Sannu da dawowa uwar gida. "Yawwa amarya kin futo shan iska ne.? Aminatu tace "walh wai me gadi zanbaiwa sautun inyaji duriyar me farin yalo yasiya min. Murmushin yake lubna tayi takuma gaskata xatonta tave " ayya aidana san abukatarsa kike dana taho muki dashi daga kasuwa " laaa bama komi nagode za.a samu ai tunda lokacin sane kuma sukan wuce akai akai. Nan lubnar ta wuce kawai tana ta kallon Aminar tanajin wani abu cikin ranta me daci data kasa hadiya Tana shiga dakinta ta zube akafet ta rafka tagumi Ashe duk murnar datakeyi akan itace zata ajiye tarihin baby agidan ashe aminar ma nakan hanya azatonta ko aminar bame haihuwa bace duk da watan aminar na shida kenan agidan Waya tasaka tayi kiran maminta Mami na dagawa tace " to uwar yan korafi yau kuma meya faru? "Meye ma bai faruba mami un expected naga waccan *"Yar makafin* da ciki walh mami bakiji yanda zuciya ta ke tafasa ba kamar in mutu nakeji Mami tayi tsaki tace " waike lubna kishi haukane kina son ki kashe kanki abanxa alhalin wanda kk dominsa bakida fada agunsa har yanzun meye ne abin damuwa dan kinganta da ciki yanda fa yake mijinki itanma mijintane kuma abinda baki saniba ayanzun haka Yarinyar nan ba *YAR MAKAFI* bace domin iyayanta sunbar makanta inada labarin ma,aruf yayi ruwa yayi tsaki wajen gani buduwar idanunsu yakashe kudi sosai yakaisu asibiti anyi musu aikin ido yanzun suna gani radau dan haka kicire ma dawuwa aranki kiyi ta kanki ki kawarta daga sabgarki kawai. Lubna tace " yanzu mami kenan goyan bayanta kkyi? "Ba goyan bayanta nakeba aname xan goyi bayan wacce taxama makiyiyar "yata kawai dai so nake kicireta aranki kada kisaka damuwarta ta dameki In Allah yasaukeki lfy sai musan abinyi domin baxamu bari tahaihu ba zamu saka akashe dan ko yr tunkan taxo duniya sannan daga baya ita kuma muyi maya kurciya dan ki mallake gidan da me gidan da iyayan nasa koya kk gani? Ajiyar xuciya taja tareda cewa " to mami naji nagode xanyi yanda kk ce sai anjima. Tana kashe wayar tahau tunanin maganar mami datace mata iyayan aminatu sun warke daga makanta Tayi mamaki ashe yaya ma,aruf shiya kashe musu kudi akai musu aiki amma kwata kwata bata saniba lallai namiji dan kunama ne Yakuma cika munafuki duk wani abu na Aminatu baya tinkararta dashi ga cikima da aminar kedashi har yafito amma sai yau taji to asirinsu ya tonu kuma xatayi maganin abun °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Sati biyu bayan faruwar wanna lamari Aminatu tana dakinta tabaje agado tana bacci ckn kayan baccinta tsalele ga dan cikinta kurbibi ya turo Itace da girki ta ajiye komi need a dining tagaji da jiran me gida shine tagudo daki bacci yai awon gaba da ita don tagaji da yin kallon Bai taba kaiwa dare har goma irin hakaba Atsammanin ta ko gidan Dr lurwan yatafi yashantake acan duk da bai taba mata hakan aranar girkin taba sai ana lubna yake hakan Can cikin baccinta taji wayarta dake gefen stool din gado tadau tsuwwa Ta bude ido da sauri takai hannu ta dauka takara akunne taji muryar habibi ne "My habibi ina kashiga ne _i miss u, pls come to me my husband_ yace mata " pls sorry my zinariya bangaya mk tun wuriba muna hospital da lubna ne naso gaya mk na sha,afa yanxu ma akai min albishir ta haihu mace kena fara gayawa sannan yanzun zan gayawa momy Ta tashi zaune da sauri ckn murna tace " _oh my god i am very happy my habibi_ Allah yaraya yasa cikon musulinci ce. Yace "Amin. Nagode zamu dawo gida nan da 11 in angama gyara babyn da uwar. nan sukai sallama tana kashe wayar taji "yan cikinta sun motsa Takai hannu tashafa tana murmushi don tasan wannan murna kenan suke yi na xuwan yayarsu duniya Itanma tayi murna domin itakam bata kullatar lubna tana kuma son su zauna lafiya itace dai lubnan mara son azauna qalau Tunda cikinta yai wata hudu twins suka fara motsi amma motsin na yau na daban ne shiyasa ta raya cewa motsin taya murna sukeyi Da ma,aruf yadawo yashigo yatararya har kan gadon yajata jikinsa yakai mata hot kisa yace " Allah yakawo ranar da kema zaki haihu ki huta sweet babyna Ta narke masa " habibi haihuwa da wahala ko? Kamar zatayi kuka Ya zaro ido da dariyarsa yace " huui! Babyna ina zan sani nida ba tayata nakuda nayiba Kya tambayeta inkinje ganin babyn Tace " tashi muje yanzun nagano "yata. Yace " no!no! Not now abari sai gobe don yanzun its my time Yakamo hannunta yace " lets go pls dear i am very hungry Tace " to habibi muje kafara watsa ruwa tukunna ko? Yace " dadai anfara bani abincin zaifi kinga inna koahi sai inwatsa ruwa daga nan ba sai gado ba. Tayi dry tace " angama ranka ya dade. <><><><><><><><><> Momy tazo barka sau daya bata sake dawo waba Balle dataga jaririya baka kirin me kama da lubna sai tahau cewa wanna yar ba gida tayo ba Aiko dai lubna ta kullaci momy sosai bayama da mami taxo ta shirya karya da gaskiya ta gaya mata akan maganar Maminta tahau taxauna ko gidan momy batajeba tana gidan yarta suna qulle qulensu na tsiya Aminatu takan shigar mata su gaisa suyi yar hira tadawo sashinta Wani xubinta bata ganin fuska da uwar ta taxoma kallon banxa take samu agunsa saita dauke kafa Zainab din Dr lurwan ma dama bataxo ba sbd basa shiri da lubnar tadai ce sai ranar suna zataxo Rigima sosai ta sarke atsakanin ma,aruf da lubna kan cewa ita dole sai anyi partyn suna a hotel kuma saniya takeso yayanka ba tinkiyaba Shiko yace tabbas baxata masa doleba tinkiyoyi biyu yasiya kuma suna ba a inda za.ayiba inba acikin gidansa ba saidai in tahada kayanta tabar masa gida To dama ko akan sunan da za,a rada wa babyn sun so suyi yaja taja dole yabar mata Yaso yasaka sunan momy tunda yaga a scainiing Aminatu duk maxa zata haifa balle yasaka mata Shikuma yana son yaga yafara da sunan mahaifiyarsa Dole dayaga abin xai xama rigima aji kansu yabar mata sunan datake so na maminta Hauwa,u wai baby jeedah za,ace mata Koda momy taji yanda sukaima dadin hakan taji tace ita dama yanda bata kaunar lubna to baxataso taga sunanta adakin taba yabari kawai in Allah yayi asaka nan gaba adakin Aminatu inhar ba haihuwa ce ta tsayaba tasan wataran xata haifi macen itama To tunda taji yace mata inhar tadage akan ayi suna ahotel to saidai tabar gida Saita kufulu ta gayawa maminta wacce ke zaune agidan anware mata daki Dayake mamin nada kawaye akano shiyasa itanma takeson ayi suna ahotel din don sun shiryi karya itanma lubna duk kawayenta yan karya ne Mami dakanta ta sameshi tace masa yabari ayi sunan ahotel tunda bada kudinsa zasuyi ba Nan yarufe ido yace ga fili game doki ai tunda dai yagindaya sharadi yananna kan bakansa inhar lubna tafuta dasunan zuwa hotel partyn suna to abakin auransa Ran mami yabaci ganin yarainata agabanta yagaya mata hakan Ta nunasa da yatsa tace " agaban ma,aruf dama bakada kunya yaushe kaxama haka donka kunyata ta zakace hakan kome? Yakalleta ido cikin ido yace "aranar da kk fara yiwa uwata rashin kunya aranar nima naxama hakan. Yana gama fadin haka yashura takalmansa yafice yabar gidan Agaban kawayenta akai hakan dan haka saita kara kulewa Ana gobe suna kuwa suka kule adaki suna kitsa mugun abu Domin mamin ke gayawa lubna cewar angano mata wani boka acan zariya akan dutse zasuje in tayi arba,in domin bazata juri ganin ana wulakanta taba. Sai asannan hankalin lubna yakwanta Allahu Akbar kabiran Allah kenan kana taka yana tasa awashe garin suna dai ba.a tashi da jaririya baby jeedh ba domin tun asuba rai yai halinsa Sai tashi sukai sukaga ba numfashi Ashe da gawa suka kwanama Dama da mura atare da ita donma uwar batada lurane amma ko adaren da ummiey xeey ta taba jikinta taji da dumi datazo barka Aiko dai mejego tasha kuka kamar ranta zai futa Ko maminta saida tazubda hawaye domin sunci buri Aminatu ma taji ba dadi Shikansa ma,aruf saida yaji xuciyarsa ta tsinke don yaji son jaririyar aransa ba yanda xasuyine Tunda Allah yafisu sonta Momy da dady sunzo har gidan sunyi gaisuwa da jajantawa Haka abokan ma,aruf sunxoxxo Dr lurwan ma yaxo da matarsa zee Maman Aminatu ma da murjanatu da babar murjan sunzo Wannan shine zuwan maman na farko gidan tunda idonta yabude aiko dai tayaba da kyau da tsarin gidan Aminar Sai yamma suka tafi gida suna tare da momy asashen aminar sunashan hira abinsu Lubna taga samu taga rashi har rama tayi na yini guda idanunta sun rufta tayi xuru xuru bataci komoba aranar Har ranar da jeedda tayi kwana uku da rasuwa bata daina kukaba.... *Su Lubna sai hakuri Allahn daya bada akecin buri yakarbi kayansa Allah yajikanki baby jeeddah* 😭😭😭😭😭😭😭 🤣🤣🤣 [7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *Kadan daga cikin masoyan "yar makafi sauran kuyi hkr abin dayawa wadannan ma writers ne* kada kuce munyi sonkai 😆 lolz *khadija candy*🌹 *khadee waziri*🌹 *Fateey tambary🌹* *Nusaibah*🌹 *Ummu Aleesha*🌹 *Ayush*🌹 *Aisha*🌹 *HAJJA*🌹 *YBK*🌹 *MAMAN SHAKUR*🌹 *Khaleesat haidar*🌹 *Ummu xuwairat*🌹 *and so so so on.... we HRT you🌹🌹🌹🌹* *PAGE 105..110* _SEMI FINAL👌🏼_ BAYAN sadakar bakwai kafa ta dauke sannan baki suka koma garinsu Mami ma aranar tayi shirin tafiya Dr ma,aruf ko lekowa baiba balle suyi sallama yana fitowa daga sashen Aminatu yashige motarsa yafice gun aikin sa Saijin tashin motarsa sukai Lubna tayi kwafa tace " mami kinga irin wulakancin mutumin nan ko, walh nagaji da wannan wulakancin da yake min nikam gara murabu kawai yafiyemin. Mamin takaiwa bakinta bugu tace " kul nasake jin haka daga bakinki burin namu bai cikaba xakice hakan. To tsaya kiji ma dabarar danake shirin hada miki donki samu ma,aruf ahannu da iyayansa Kinga idan mukai asirin da Amina tabar gidannan bayan munkashe abinda ke cikinta sai ayi asirin da zaixamo komi saida ixininki zaiyi haka murufe bakin iyayansa balle su gane har suje su karya kekuma inkin haifi namiji kai koda macece sai musan yadda xamuyi muga munsa masa guba a abinci yamutu inyaso kinga kin mallake komi nasa kenan Lubna tayi shiru ta xurfafa dogon tunani " kuma fa hakane " Da murnarta tace da mamin " wai! Aiko dai harna hangoni naxama miloniya mami dan walh mutumin nan yanada kudi sbd yanzu har kamfani yakedashi agefe guda banda karin girman da akai masa agun aiki. Mami tace "yanzu dai inna tafi baxan dawoba sai kinyi kwana ar,bain da haihuwa zanzo mutafi zarian gun hatsabibin bokan da akai min kwatancen. Lubna taji dadi sosai taringayiwa mami godiya naganin yanda takeson taga tayi rayuwa mekyau agidan miji ( Allah yakyauta lubna wato dan,uwanki kk so ki kashe ko ? To Allah yatoni asirinku) Awashe garin da maminta takoma garinsu ita kuma aranar ta tashi hankalinta naganin ma,aruf yadawo dakinta da kwana (oh ! Su lubna jarababba abari ayi ar,bain mana ko sati uku🤔 Taringayi masa waya bai dagaba ta tura masa sakonni tace kamar hakan _Yaya yau fa asashena kake domin yau zan karbi girki banyarda kakai kwana na ga wataba inkuma baka dawominba to kaida Allah ban yafeba_ yana ganin sakon yayi tsaki ya goge Yagano yau lubna akwai abinda takeji zaikumayi maganinta Alokacin daya dawo gidan kai tsaye sashen Aminatu ya wuce ko kallon part din lubna bai ba Tana zaune afalo tana kallon mbc 2 yai mata sallama ta amsa tareda tasowa dakyar ta tareshi Tarumgumeshi tana masa welcome da hotkiss agoshinsa Yai mata kyakykyawar runguma ajikinsa yarukota ahankali suka koma kan 3siter suka zauna Ta tashi da nufin takawo masa ruwa me sanyi yai saurin zaunar da ita yace "zauna kawai na yafe nasan me xakiyi kuma nace kirage wani abin yanzu kinyi nauyi banison kina aikin wahala my madam. Tayi murmushi tace " kai habibi kabarni nai aikin lada mana kadaina hanani cikin da har yanxun baikai bakwai ba kawai dandai kafata tanamin nauyi ne kuma ai ana son mudinga motsa jikinmu kada kasa naxama malalaciya mana. Yace " to aiban gane bane amma nikam baniso kisha wahala gaskiya Ta cire masa kot din jikinsa ta dauki jakarsa tayi daki dasu Bayan yaci abinci suna xaune wajen tara na dare taga anata kiran wayarsa yafi biyar bai dagaba Tagaji ta dauko da nufin mika masa saiya girgixa kai Ta duba taga lubna ce Tace dashi "why!? Metayi maka ne? yace " neman rigima takeyi Zinariya banison rabuwa dake kinamin abinda nakeso inajin dadinki gashi lubna nashirin rabamu wai ita adole ayau saina dawo dakinta nikuma banyi shirin hakanba uphead kawai tasamin doka nikuma bata isaba haka kawai zata katsen farin ciki alhalin ita bata isa sani farin cikinba Aminatu tace " haba dear meye laifin macen da take bukatar mijinta kada kaga aibunta itanma _may be she is missing you alot_ kayi hkr kakoma mata ayau din meye aciki.... ya katseta da tsarewar ido yace "wato kingaji dani ko? ta girgixa kanta da sauri tace " no, kawai dai banison ashiga hakkintane tunda ta bidi mijinta kada adanneta dayawa Yace "har yanxun fa mejego ce ita ko sati uku fa batayi da haihuwa ba kawai dai tanason taga nashiga takurane Nan Aminatu taita rarrashinsa tana tausarsa domin Lubna dai bata daina yo wayarba har saida yadaga da tsawa yace mata gashinan zuwa kana ta hakura Bai shiga sashen nataba bama saida yatabbatar yasami farin ciki daga zinariya kuma lokacin daya je dakin natama har tagaji tayi bacci wajen 11pm fa Kota kanta baibi ba yakwanta abinsa a can gefe guda agadon Saida safe taganshi wajen 7 ta tashi sallah shiko ma harya fara shiri don yafito wanka daure da towel yafito yanufi kayansa yaciro a drower yasaka Tabishi da kallo kawai lallai tagane ayanzu adole yake zaune da ita kuma zatayi maganinsa Tashige toilet don dauro alwala Yabita da kallo yana tsaki anyi asara dai mace ba rikon ibada sallar asuba sai safe alfijir yaketo hhhhmnn ibada ai sai zinariyarsa Da yayaje gun Aiki tunanin zinariyar sane yadameshi bini bini sai yayo mata waya yaji lafiyarta Irin nuna kulawar dayake mata ne yasaka taji aduniya tagama samun jindadi batajin akwai macen datayi dacen miji irinta domin tasani sanin kanta akwai bambanci atsakaninta da lubna tasan tasha gabanta agun miji da dangin miji da iyayansa Akwana atashi dai watan haihuwar Aminatu yatsaya sai mama tayowa Dr ma,aruf waya kan cewa ko zai aminta tadawo da Aminatu gabanta sbd haihuwar farice Ma,aruf baiyi alkunyaba yace "mama kiyi hkr walh baniso inyi nisa da aminatu akusa dani dan Allah ayimin alfarma abarta ta haihu agidana momy xata bata kulawa tamkar kina kusa da ita Mama ckn tausayawa tace masa "to shikenan ma,aruf anbarta Allah yasauketa lfy. Yace " amin nagode mama. Sukai sallama yakashe <><><><><><><><><> Alokacin da Lubna tayi kwana arba,in da haihuwa ne suka ajiye agenda itada mami naxuwa xaria Meeting point dinsu atasha ne Da sassafe lubna tafito ta tafi tasha don haduwa da mami ranar ma,aruf ba.a bangarenta yake ba Dama tayi masa karyar xataje dubiyar kawarta Aziza tahaihu anmata operation Tasan kuma baya daukarta amota balle yace zaikaita Har can hankali kwance tafice Sun isa zaria lfy yayinda suka sami zuea har gun bokan dake kan wani tsibiri Inkaga halittar bokan babu kyan gani bakine kirin ga katon baki wawakeke ga kunnuwa kamar girman fankassu ga idanu manya manya jajaye hancinsa rusheshe ga muryarsa gwangwaran dayai magana saikaji amsa kuwwarta Babu tsoro atare dasu tunda sun saba ganin hakan Bayan sun zayyane masa abinda yakawosu ne boka yanemi makudan kudi ahannunsu ba musu suka dire masa don lubna tazo da uban kudi tun aranar da ma,aruf xaibar dakinta tayi taiming ta saci dubu dari akudinsa ckn durowarsa dataga yashiga toilet tasan inba tsayawa yai yakirgaba da wuya yagane don kudaden masu yawan gaskene. Mami tace da boka "muna so ne akadata daji in ankashe dan dake cikinta sannan kuma shi ma,aruf din yadawo ahannun lubna yaxamo sai abinda tace dashi arufe bakin iyayansa kada suga komi balle su tashi da addu,a Boka ya kyalkyace da mummunar dariya dasaida suka toshe kunnuwansu yace " angama kutashi ku koma. Yabasu wani turare da maganin da zata saka masa a abinci yace sujira nanda kwana biyu zasuga abinda xai faru itakuma lubna ayau da dare xata haifi bakwaini amma matacce. Da murna suka bar gurin bokan Lubna hankali yakwanta taringa hangota tahau karagar mulkar ma,aruf komi yadawo hannunta Lumshe idanu taringayi ackn mota har wani bacci me dadi yasureta Dayake motar hayane itanma mamin baccin ne yakwasheta da tafiya tayi nisa Motar shiru wasu na bacci wasu sun nutsu Yayinda drivern keta kwarara gudun wuce sa.a Da tsautsayi kuwa ya gwabzawa wata trailer yaxo yin over taking nan wata mota dake binsu abayama ta buga musu duka suka kife kuwa Hhhmmm Ansha wuya anmummutu domin motar bayansuma babu wanda yai rai Garama motarsu lubna mutum takwas sun mutu mutum biyar sun jikkata ckn matattun harda maminta don bata farkaba sai akiyama tun baccin data koma Allahu Akbar haka duniyar take dama mutuwa ba iya xuwar maka aduk irin halin da kk ciki ko taxo maka kana tafe ko kana kwance ko kana xaune ko aikin Alkairi kona tsiya Mukam muna rokon Allah dayasa muyi mutuwa mekyau Allah yasa mudace amin Lubna tasamu karaya akafa kanta yabugu sosai Ba ita tasami farfadowa ba ma sai ckn dare a asibitin Aminu kano ta ganta Ta dawo hayyacinta dan haka saita firgita taringa kuka tana kiran maminta Wata likita tajata ajikinta tana bata hkr "kiyi shiru sis Allah yayiwa maminki rasuwa har ankaisu makwanci tun daxun ke kuma kigodewa Allah ma da kk ganki araye Lubna ta rushe da kuka tana fadin "wayyo mamina kintafi kinbarni nashiga uku. Ta yunkura zata sauko agadon saitaji karafa akafafunta da sauri likitar ta rikota takomarta tace mata "kiyi ahankalifa kinsami karayane akafafunki neel dinki sun tsage baxaki iya tafiya da kankiba har sai anyi mk aiki. Nanma ai dada tunxurata likitar tayi bata saniba saitasa hanni aka ta fashe da kuka Kanta yasha bandage Likita tace " da kinyi shiru baiwar Allah domin wannan kukan bakomi xai harfar mikiba sai ciwon kai. Wani likita yashigo dakin da nurses na take masa baya Yakalli likitar dake dakin yace " sis zee ta farko ashe patient din taki. " eh walh tafarka gatama sai fama nake da ita takiyin shiru. Likitan yamatso kusa da lubna yakalleta anutse yace "baiwar Allah kiyi shiru domin takima ahaka tayi kyau sbd wasu ma kamanninsu ne ya canxa keko gashi har mijinki da yaxo yagane ki banda kanki da kafafunki babu inda muka ga ciwo wasu ko suna can suna iface iface sunfita hayyacinsu ma don wanima daxu akai asibitin mahaukata dashi Lubna ta dafe kirji jin wai ashe mijinta har yaxo asibitin Tace da likitan " kace mijina yazo likita ya akai kukasan shine mijin nawa? likitan yace " eh to indai sunansa Dr ma,aruf to shine don mun sami nambarsane awayarki da aka kawoki sannan ma dayaxo yace tabbas ke matar sace kafin yaxone ma yai mana tirjiya yace shikam baisa matar da ta tafi zariya ayau Da aka kirashi da layinki ne harya yarda yaxo Kuma daya ganki har hawaye yaxubda munbashi wayarki da wasu kayayyaki da jakarki suna gunsa yanzuma yana can waje shida danginsa bari muje muturo miki shi. Gaban lubna yafadi hankalinta yatashi yau yaxatayi asirinta yagama tonuwa tunda har ma,aruf yaji cewar zaria taje itada tace masa dubiya zataje gidan kawa Gashi jakarta na gunsa fatanta Allah yasa baiga magungunan da boka yabata ba...... *Awwnnn Ummiey xeey and Nabilancy* [7/27, 6:30 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 *'YAR MAKAFI...* ♦ ♦ ♦ ♦ 🎗 🎗 🎗 🎗 ```written by.....``` *FRESH UⓂMIEY XEEY* Da *NABILANCY LUV💘* *ALHAMDULILLAH* _Muna godiya ga Allahu Subhanallahu wata'ala da Ya bamu ikon gama wannan labari *YAR MAKAFI* Allah Yasa mu amfana da abinda yake cikinsa wanda yake daidai._ _Kuskuren dake ciki Allah Ya yafe mana Ya kawar da hankulanmu daga aiki dashi._ *Special thanks to* Zauren UⓂmiey xeey❣ Taskar Nabilancy❣ Novella's lodge❣ Musan kanmu❣ Excellent writers and lots more❣ *Our fans baki bazai Iya zayyanuku gaba daya ba domin kuna da yawa....Allah dai yabar so da kauna* *LAST PAGE....... 110...115* *🔚🔚🔚🔚🔚* Nurse dinne taje ta kira Ma'aruf, Da sauri ya shugo Su mummy da Aminatu suna biye dashi, kallo daya tai musu hankalinta yai mugun tashi, Nan take nadama yazo mata, Wato Aminatun da mummy data tsana yau sune sukai mata rana Aminatu ne ta kalleta Tace" sannu Lubna, Allah ya tsare na gaba, cikin kuka.Lubna tace" Ameen nagode Ma'aruf kuwa wani banzan kallo yai mata A zuciyarshi yana tsanar halayenta, <><><><><><><><><><><><><><><> Bayan kwana biyu ma'aruf ya bada kudi akai mata aiki a kafa, Duk da bazata Iya tafiya kwata kwata ba SBD ta sama karaya sosai, Aminatu kuma tana mai tausayin Lubna, Domin kwata kwata batai ma kanta adalci ba Lubna Kullun cikin kuka da bakin ciki Ga maminta da take goyan mata baya yanzu bata nan, ita kam kaiconta rayuwa baya mata dadi Lubna na Kwance, a gadon asibiti, ta rasa yanzu ya zatai, Ga maganin da suka amso yana cikin Jakarta, kuma yana hannun ma'aruf ya ajiye a cikin matarsa, Saida Aminatu tazo gaisheta tace" dan Allah ki amso mun jakata a wqjen ma'aruf, Aminatu tace" to shikkenan Ta tashi ta Tafi tai wa ma'aruf din magana Kallonta yayi Yace" ke meyasa bazaki fita harkanta ba, Aminatu tace" se kai mata uziri ai da lafiyanta qalau INA ruwana da ita, nan ya bude back site din cikin motar ya dakko jakan, Ji yai gabanshi ya fadi, then before ya mika wa Aminatun jakan ya bude, Aiko yana Budewa yaga wani Abu a bakin Leda, Ma'aruf ya bude ya gani Yace" kai.......!!! Aminatu zo muje, cikin ward Suka nufa Ma'aruf na tafe Aminatu na binshi a baya, Sukai sa'a ba kowa, Lubna dake kwace yanda taga Ma'aruf seda hanjin cikinta ya kada. Zuwa yai gabata Yace" asirinki ya tono meye wannan? Gabantane ya fadi gham tace" uhm Magani ne, Ma'aruf Yace" banza makira, Yaudai asirinki ya gama tonowa, Bazaki fadamun ba? Tai shuru se hawaye ke zobu mata tace" Dan Allah Ku yafemun, Ma'aruf ka yafemun Aminatu ki yafemun tun ba'aje ko INA ba na Ga karshe na. Ma'aruf wani dogon nunfashi yaja Yace" kin ma kanki kuma ni NA SAKEKI SAKI UKU, Da sauri Lubna ta kalleshi tana Yau na shiga uku ta sake kuka nan take ta kira mumyn Ma'aruf Shi kuma ma'aruf yana gama fadan ya saketa yai ficewarshi. Aminatu kuma ta bishi tace" haba habeebieee meyasa kai saurin yanke wannan hukuncin Kallon ta yayi Yace ta chanchanci hakane, Itadai Aminatu batace komai ba, Amma Sam abun be mata dadi ba Mummy na zuwa direct dakin Da Lubna take , Nan ta ke Lubna ta fara kuka tana Mummy shikkenan yaya Ma'aruf ya sakeni. Na shiga uku, na mutu Mumyy ne ta sake baki ita tama rasa me zatace mata, Dan abun da Ma'aruf yayi shine dai dai amma Ai an gudune ba'a tsiraba, Yanzu dai dole lubna hannunta zata dawo tunda Maminta ta rasu Nan dai Mummy take ta bata hakuri, har ta sama Dan sauk'i aka sallamesu Shikkenan yanzu ba Ma'aruf ba lubna aure ya kare Koda suka koma gida daddy yayi fada sosai akan da be sake ta ba, Ma'aruf Yace hmm Dady ita ta ja ma kanta, <><><><><><><><><><><><><><> Bayan watanni biyu Aminatu ta Haifa yara yan biyu maza, dayan bezo da rai ba sai daya ya rage....Awwnnn bakuga murna ba wajen iyayansu, balle ma mummy da Dady sunga Farkon jikansu, Aminatu kuwa haihuwar datai kamar an kara mata kyau, da Lubna taji Aminatu ta haihu kuka tayi sosai tace" tabbas Gaskiya ne za'a Dade anayi amma karya ba inda zai kai mutun yau Ga karshena nice a kujeran guragu, nan ta fashe da kuka Mummy kam tausanta take akan tayi hakuri ko yanzu ma lokaaci me kura ba akan ta gyara halinta Allah sarki Lubna nan danan nadama yazo mata ta koma koda yaushe cikin istigfari, Tana Neman tuba akan duk abun da ta aikata, Kullun Ma'aruf tazo tana Neman gafara Yace" ya yafe mata °°°°°°°°°°°°°° Ranar Suna aka sama Yaro suna Aminullah, *Al'ameen* dama ma'aruf ya mata alkawari zai sa sunan Aminullah tunda yaga yanda take damuwa kuma Kullun tana yimai addua'a Anyi suna awwnn abun se Wanda ya gani, Murjanatu sune yan kan gaban Komai da komai, Itama ta sama miji bayan babban Sallah za'ai auranta lol ********** Yanzu lubna ya fallawa wa Allah komai Nata, dama haka akeson mutun Ko yanzu 6e bace ba idan kana mugun halaye ka gyara, tun yanzu, Allah dai yasa mui cika da kyau da imani (Ameen) Ma'aruf yanzu hankalinshi kwance, Aminatu namai komai, Ga Aminullah se kara girma yake yana samun kulawa sosai. Ansake karawa Ma'aruf girma a wajen aiki, yanzu yasai fili guda biyu, daya ya ginawa Aminatu da gyaran da zata Haifaimai nan gaba, dayan kuma ya Gina mata gidan Gona.... Lubna kuwa idan taji abun alheri Setai musu addua tace" inama Ma'aruf ya maida ita, Da zatamai biyayya yanda beyi tinani ba...lolz Nabilancy tace" its too late awwn Aminullah ya girma yana da shekara daya da rabi yayi kyau amma idan ka ganshi zakace yakai 2years, Aminatu ta sake samun ciki ta Haifa yara mata yan biyu kamansu daya da babansu, Daya aka sa mata Sunan mummyn ma'aruf dayan Kuma aka sa Mata sunan Maman Aminatu Anyi suna Iya suna.... Time din da Aminullah ya ya cika shekara Biyu aka mai birthday Ma'aruf ya kan kai Aminullah gidan Mummy, idan Lubna ta Ganshi tai tamai wasa tana son yaron har cikin ranta Allah sarki Time din da Aminullah ya Dan fara magana, ranar sun zo dukansu gidan Mummy, Gaba daya suna zaune yan biyu sun fara rarrafe, Aminullah kuma yana wasa, Ga Aminatu, Ga Ma'aruf ya Mummy da Daddy Aminullah Yace" Allah sarki, Mummy Anty Lubna naban tausayi, Kowa na cikin dakin yai shuru suna mamakin Kalaman Aminullah Nan Lubna ta fara hawaye ta kira Aminullah yazo, tace" kai mun addua kaji? Gaskiya kam taba kowa tausayi, balle ma Aminatu sarkin tausayi da akwai yanda zatace Ma'aruf ya dawo da ita da zai tace lol Hakadai Rayuwarsu taci gaba awwn . Anyi bikin murja ita yanzu tana da ciki l Yan biyun Aminatu suma sun girma har an sama wani cikin Ma'aruf Yace ba a gda zata haihu ba Dubai zataje ta haihu..... Awwnnn rayuwa ya musu dadi Awwn Bamusu muka gama muku wannan littafin ba, Muna godiya sosai yanda kuka nuna kunason book dinnan MUNGODE Munanan kawo muku wani littafin me dadin gaske and Kar ku manta Littafin Nabilancy *TARAYYA* nanan fitowa kar Ku bari a abaku labari Nabilancy Love And Ummiey Xeey Ke.ma.kowa fatan Alheri